‘YAR NAJERIYA An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT LITTAFIN SUMAYYAH ABDULKADIR Takorikabara@gmail.com Babbangoro2015@yahoo.com SADAUKARWA Sadaukarwa ne ga dukkan ALBINOS din Najeriya….You are special a yadda Allah ke son ganin ku. “YAR NAJERIYA FARKON FARI (HASNA 'YAR INNAR TA) Na taso cike da dokin ranar zuwan ziyarar ‘yan makaranta, ba don komai ba sai don na san Inna zata kawo min kanzo, kuli da kwaki, wadanda su ne abinda nake samu a kowanne visiting, sabanin sauran dalibai masu uba a raye, idan aljihun Inna da dan nauyi (in ta samu surfe mai yawa) kafin zuwan ranar ziyarar mu to tana hadomin da mankuli wani lokacin har da busashishiyar yakuwa (rama) wadda zan dade ina jikawa ina kwadantawa. Makarantar mu makaranta ce ta hadakar ‘yan Najeriya (UNITY COLLEGE) wadda nayi nasarar samu sabida hazakata ba don ina da gatan zuwan ta ba. Duk fadin kauyen mu na fi kowa kwazo a karatun boko da na muhammadiyya har wani suna ake kira na da shi (Huda-Huda ‘yar Inna) wasu su ce (Mungu Park ‘yar Inna) sabida tsabar son karatu na da son Inna ta. Bayan son karatu Allah yayi ni da tsafta, wadda aka ce it ace cikon addini, duk da irin halittar da yayi min wadda ta banbanta data sauran al’umma, kai bazaka ce girman kauye bace kuma tashin kauye sabida yadda nake kula da tsaftar jiki na. Tsaftar da Inna ke kan ce aljanu ke sani yin ta, domin ta wuce misali. Na taso ban san kowa ba sai Inna ta ban kuma shaqu da kowa ba sai ita, mahaifi na tun ina ciki ya rasu, kuma nice kadai diya ga iyaye na. Sannan ba kowa ke son mu’amala da iri na ba (da mutum mai irin halitta ta). Mahaifi na Mal. Dabo dan asalin karamar hukumar Kabo ne ta jihar Kano, wanda sana’ar sa ta iyaye da kakanni itace ‘jimar fatu’. Da wannan sana’a yayi aure ya kuma rike Inna ta da mahaifiyar sa Kaka A’I. kakata A’I bata tare da mu yanzu haka tana can garin Kabo. Mahaifiya ta ‘yar asalin garin Kachako ce inda ci-rani ya kai mahaifi na ya auro ta, bayan auren su ya taho da ita garin su wato Kabo suka zauna gida daya da mahaifiyar sa A’I. duka-duka auren bai rufa shekara biyu ba ciwon ajali ya kama mahaifi na Malam Dabo, kuma bai dade yana jinya ba ya amsa kiran mahaliccin sa. Mahaifiya ta Inna Zulai ta cigaba da rainon ciki na a gidan mahaifi na har ta haife ni. Na zo da halittar data barranta data kowa a gidan mu, ga dai kyau har kyau amma zabiya ce, don haka ni ban gado fatar jiki na ba a wajen iyaye na kudurar Ubangiji kadai ta sa aka haife ni haka. A lokacin ne manema suka fara kawo mata caffa, don haka A’I tace ta yaye ni ta bata ni ta samu ta yi aure, amma Inna ta kafe kan cewa ita ba auren da zata yi raino na kawai zata yi har karshen rayuwar ta, sabida irin halittar da Allah yai min, da ba kowa ke son raba ta ba, sannan bata son tayi wani aure da zai sa a kira ni AGOLA. Zaman mahaifiya ta da kakata A’I sai ya canza salo bayan rasuwar mahaifi na, sabida A’I ta dage sai ta yi aure shine mutuncin ta kuma ta gaji da dawainiya da mu, ta kan ce da wannan zabiyar ‘yar taki wadda ba miji zata samu ba. A karshe ba tare da shawara da ita ba ta amsawa wani malamin makarantar sakandire Malam Saminu da ya nace yana son auren Inna ta. Rannan A’I ta fita makota sai dawowa tayi ta tarar babu mu babu alamun mu a gidan, Inna ta goye ni mun bar Kabo cikin bacin rai don har ta fara gayyatar daurin auren Inna ta, muka koma garin Kachako gidan su mahaifiya ta, iyayen ta duka sun kwanta dama gidan na gadon su ne ita da Yayan ta Sama’ila. Yaya Sama’ila na zaune a gidan da matar sa Hajjo, sai mahaifiya ta ta share daya bangaren na iyayen su muka yi zaman mu. Nan Inna ta fara tunanin sana’ar da ya kamata mu fara don mu dinga samun na cin abinci kasancewar Yaya Sama’ila shima fama yake da kan sa ga nauyin iyali duk da haka yana da matukar zumunci akan Inna ta duk abinda ya samu daidai karfin sa yana bata, sana’ar sa itace noman Rake. Garin Kachako na nan a karamar hukumar Albasu ta jihar Kano. Gari ne ni’imtacce da al’ummar garin duka masu zuciyar nema ne, kusan babu wanda bai da kwakkwarar sana’ar da yake cin abinci da ita, tashin farko muka soma sana’ar danwake da wake da shinkafa a tashar Kachako. Kuma babu laifi muna samun rufin asiri, ni nake wanke kwanuka tare da mikawa masu bukata in an saya. Da muka dan yi karfi muka buga rumfar kwano anan cikin tasha muka saka dogayen bencina guda biyu suna kallon juna. A wani marece Yaya Sama’ila ya shigo yana ta fada kamar zai ari baki wai akan Dagaci yace ya kai su Hassan makaranta su daina sayar da Rake, cikin fushi yace “in sun daina sana’ar Rake shi Dagacin ne zai ciyar damu? Karatun nan da aka ce yana maida ‘ya’ya kafurai su kuma fi karfin iyayen su zan dauki Hassan da Hussaini in kaisu? Mu da bamu yi karatun ba me ya same mu? Hajjo na kara zuga shi da cewa “ah to dai, ka biyewa Dagaci ya lalata maka ‘ya’ya su zama ‘yan daba in bazasu saida rake ba”. Innata na jin su haka kawai sai taji tana min sha’awar ni in yi karatun ni da banida future, ‘ya’ya iri na dole su nemi madogara a rayuwa ko su kare a bara bisa titi, madadin bin ta tasha dana ke yi muna sayar da danwake. Sanin halin YaYa Samaila yasa bata yi shawara da shi ba ta wanke hannu tayi lullubi ta kama hannu na muka tafi gidan Dagacin garin Kachako. “Allah ya taimaki Dagaci ga ‘ya ta HASNA’U marainiya ce, ina so a sata makaranta, daga nan har zuwa lokacin da zata isa aure, duk da bana jin zata iya samun mijin aure”. Dagaci ya sanyawa Inna albarka yafi cikin Kwando tare da cewa “‘yar ki mutum ce lafiyayya kamar dan kowa, ki daina maida ita koma baya sabida Allah yayi mata halittar zabiya, inama sauran jama’ar gari zasu yi koyi da Innata, da mun fita daga duhun jahilci mun shiga sahun ilmin zamani da ke kara karfi a kauyuka a wancan lokacin. Daga wannan lokacin na fara karatun firamare tare da ‘ya’yan Dagaci da wasu tsirarun ‘ya’ya da ga al’ummar kauyen mu duk da karatun ba wani mai inganci bane amma mun koyi Huruful Hija’iyyah da rubutu da karatun haruffan boko dana Hausa. Sanda na gama karatun firamare ba da jimawa ba gwamnatin Tarayya ta kafa UNITY COLLEGE KACHAKO, a matsayin mu na wadanda suka samu alfarmar yin firamare mune dalibai na sahun farko (pioneers) a Kachako wadda ta hada dalibai daga kowanne yanki na Najeriya ciki har da ‘yan kudu da yammacin Najeriya. Na fara Unity Kachako da kafar dama domin babu jimawa kwakwalwata ta dinga budewa karatu yana shiga, sai a lokacin nasan a firamare ba karatu muke ba, ga islamiyya muna yi da yamma a renakun mako, ga abinci wadatacce gwamnati na bamu a wancan lokacin makarantu sun fi samun gatan gwamnati sabida neman masu yin karatun ake yi ruwa a jallo. Ubangijin da ya halicce ni sai ya halicce ni ba kala daya da sauran mutane ba, bansan cewa halitta ta abin kyama bace kuma abin gudu sai da na fara sakandire, inda ya kasance makarantar kwana, na gane ba kowa ke son mu’amala da ni ba haka ba kowa ke cin abinci dani ba, ke ko kayana babu mai tabawa sabida Allah ya halicce ni ZABIYA. “Albinism” halittar Allah ce ga daidaikun bayin sa, yadda yake halittar kowa haka yake halittar zabiya, yawanci gado ne amma ni ba gado bane, farin mu ya wuce misali sannan bama jure zafin rana, gashin kanmu ba baki bane kamar na kowa, sannan masu halittar “albino” na fama da raunin gani (short-sightedness). Duka ban gane haka ba sai da na fara shiga shekarun balaga, a baya na dauka fari na is normal sabida babu mai goranta min ko kira na ‘zabiya’. Sai zuwana Kachako da naji ana kira na ‘Hasna-Zabiya’. Sai na gane ni ba fara bace mara lafiya ce, abin kyama ga wasu daidaikun al’umma. Amma hakan bai sagar min da gwiwa ga neman ilmi ba, na saka a raina bazan taba aure ba, zan yi ilmi har sai naga karshen sa. Wanda zai sa in samu abin yi da zan kula da kai na da Innata. Yau ta kasance ranar ziyarar dalibai, tun safe mun sha wanka mun zuba wankakken uniform muna jiran iyaye da ‘yan uwan mu. Ta fanni na nasan babu wanda zai zo min sai Inna, don haka ina daga layin farko na masu rarraba ido don jiran nasu amma har kusan azahar babu Inna ta. Sai na koma gindin wata bishiyar darbejiya na zauna abin duniya ya ishe ni, na hada kai gwiwa amma ba kuka nake ba, tunanin halin da Inna take shi ke damu na, don bata taba tsallake rana bata zo min visiting ba. Ga yunwa da ta fara galabaitar da ni. Sai nasa kai na a tsakanin gwiwoyi na, ni kadai nasan irin damuwar dake cunkushe a rai na. Bazan manta ba shekaru na goma sha shidda a lokacin. Kamshin masculine turare na ji a hancina mai karfi sannan naji ana Magana a kai na. “Are you alright?” Da farko ban zaci da ni ake ba sai da aka kara maimaitawa tare da sunana “Hasna’u are you okey?”, Da sauri na dago ido na dubi mai Magana; he’s tall and slim, shi ba fari ba shi ba baki ba, gashi nan dai wankan tarwada mai kyawun siga kuma ma’abocin tsaftar jiki wanda kallo daya zaka yi masa ka fahimci ilmi ya wadata a tare da shi. Sannan bai nemi komai ya rasa a rayuwa ba. Kusan zan iya cewa na taba ganin sa sau daya ko biyu, a rashin sani na shine wanda zai juya duniya ta daga yadda take zuwa ga inda ban taba mafarki ba, zuwa ga inda bana fatan kai kai na, shine wanda zai juya kaddarori na daga yadda nake fatan su. Sannan shine tsanin da zan taka ya ruguzo da ni daga kan kyakkyawar turbar dana ke kai. Da bai shigo rayuwata ba da watakila komai ya cigaba da tafiya min normal a yadda Allah ya halicce ni na kuma mallaki ‘mental well-being’ dina dai-dai. Kada ki ce ko kyawun sa da tsaftar sa ne ya rude ni a’a, wata irin ‘kamala’ ke gare shi da kwarjini mai daukar hankali da ba duk ‘yan adam suka mallaka ba. A cikin muryar sa akwai ‘maturity’ da ‘tone’ mai nuna sanin ciwon kai, yana daga cikin masu kula da asibitin makaranta, ko likita ne ko ma’aikacin jinya shine abinda ban sani ba, sau biyu na je clinic da bani da lafiya kuma shine ya bani magani ya kuma sa nurse ta yi min allura. “I’m alright Sir”, na bashi amsa a lokacin da na dago idanuna masu rauni da suka kada suka yi jawur, na dube shi, haduwar idanun da ya janyo rushewar duk wani tubali da na aza harsashin rayuwa ta a kai. Na cewa har abada bazan yi aure ba….tunda ni ZABIYA ce….. ***** SAHEEB DAN MAMAN SA!!! (IN WANI YA KI KA DA WUNI...) Tun gani na da shi na farko, zuciya ta bata kara zama lafiya ba, rayuwa ta bata kara komawa daidai ba har yau shekaru talatin a gaba. Ya jirkita rayuwa ta upside-down ta duk yadda yake so, ya hargitsa tunani na ya mayar da shi yadda yaga dama, ya zamo silar da na san cewa ZABIYA ma mutum ne kuma mai 'yanci, amma kuma shigowar sa cikin rayuwar tawa ba farin-ciki ta haifar ba sai akasin sa. In ma da farin-cikin to takaitace ne na wani dan kayyadadden lokaci. He gave me love but the people around him gave me hatred. “What are you crying for Hasna’u?” Ya tambaya cikin kulawa. Ban yi niyyar Magana ba amma sai naji bazan iya share shi ba, duk da na san ba abinda zai iya akan kawo min Inna ta. Ko gano min dalilin rashin zuwan ta. “’Yan gidan ku basu zo bane?” Ya sake tambaya kafin in bashi waccan amsar. Ganewa da yayi cewa hankali na ba ya jikina sabida yunwar da ke sakadata. Ban san san da nace masa. “Ai ni bani da ‘yan gida, Innace kawai take zuwa min kuma bata zo ba. Ba kuka nake yi ba hutawa nake yi Sir” “baki da Wa ko Ya, kuma baki da kanne? You have no relatives? Baban ki fa?” Muryarsa is husky mai zurfi da kauri ta 'yan boko mai ratsawa har cikin zuciyar mutum. Murya raunane nace, “tun ina ciki Babana ya rasu, ni kadai ce a wurin Inna ta”. Sai ya ce “to dan jira ni ina zuwa ko?” Kafin in ce komai ya juya cikin takun sassarfa ya bar wajen. Bai jima ba ya dawo da farar leda a hannun sa ya mika min, sannan yace. "Zan turo kanwata Nusaiba ta kawo miki abinci, ita muka zo wa visiting. Though i'm working here. Na hango ki anan na dauka kuka kike yi, don na san ki tun da jimawa a clinic”. Hannu biyu na sa na karba, tare da cewa. “Thank you so much Sir”. Ya taka a sannu ya bar wajen, amma kamshin kakkarfan masculine turaren sa bai bar shiga hanci na ba. Na bishi da kallo ina kiyasi, a very soft-hearted gentleman indeed! Har sunana ya sani, to ta ina? Sai na tuna da sanda na je clinic an tambayi sunana kuma an rubuta a folder. Na maida duba na ga ledar da ya bani, wadda sanyin abinda ke ciki ke ta taba cinya ta, na fiddo gorar dake ciki yoghurt ne mai sanyi kuma mai girma, sai ruwan FARO mara san yi. Har karkashin zuciyata nagode masa, na kuma yi masa addu’ar alkhairi. Ashe har yanzu akwai sauran mutane masu son taimako saboda Allah? “Nusaiba zuba abinci ki kaima waccan yarinyar ta karkashin bishiya?” Kyakkyawar budurwar 'yar hutu wadda aka kira Nusaiba, da ganin ta ka san she's born from a silver spoon, ta juya tana kallon inda Yayan nata ya nuna mata, da sauri ta juyo ta dube shi cikin mamaki. “Waccan zabiyar?” Har tana kwalalo ido waje. Ya kalle ta da mamaki “ZABIYA ba mutum bane?” Sai Maman su ta dago daga kan waya da take dannawa ta dube su tana tambaya. “Menene wai? Ya kamata ku tashi mu tafi rana ta yi” tace da ‘dan nata dake tsaye, amma duk hankalin sa yana kan Hasna’u. Nusaiba ta ce “Mama wai Yaya ne yace in kaiwa zabiyar can abinci” Mama ta ce “Zabiya kuma? A kwanon wa za’a kaiwa zabiyar abinci ba dai nawa ba?” Nusaiba ta yi dariya amma suna hada ido da Yayan nata ba shiri ta hadiye dariyar ta. Sabida mugun kallon da ya wurga mata. Kawai sai gani suka yi ya sunkuya ya dauki plate yana zuba abincin da kan sa, ya loda soyayyen naman kaza da salad ya rufe yayi gaba abin sa. Nusaiba ta ce “oh ni ‘ya su Yaya SAHEEB akwai jaye-jaye”. Mama tace “in ya dawo da plates din ki zubar, dan kankanbar tsiya kawai da fin kowa iyawa.” “Take this food Hasna’u”. Da farko ban yi niyyar karba ba, amma intonation din cikin muryar sa ya nuna how much he cares ga son na ci abincin, da yadda ya damu da kadaicin da ya riske ni a ciki. Sannan Inna ta sha ce da ni ba’a maida hannun kyauta baya. Hannu biyu na san a karba, a karo na biyu, tare da cewa “nagode Sir” “Sunana Saheeb”. “nagode Uncle, ni kuma sunana Hasna’u Dabo. Zan iya cewa kana da kirki Uncle?” Murmushi yayi yace “maza ki ci ki kai musu plate din ki koma hostel, saura kadan lokaci ya cika, tunda Mamanki ta kai har yanzu bata zo ba to bazata zo ba, khair insha Allah”. Daga haka ya bar wajen, ni kuma har ya kule na kasa dauke ido a kan sa. Ina mamakin kyakkyawar zuciya irin tasa. Tunda nake ban taba cin abinci mai dadin wannan ba, kunne na har wani irin kaikayi yake yi, sannan ga nama zuqu-zuqu dana kasa tantance na kaza ne, ko na zabo ne ko na dawisu ne don dadin sa, nayi masa cin hani’an na dau plate din zuwa inda suke, har sun fara haramar tafiya. Suna nannade katon kilishin da suka zauna a kai. “Kin gama Hasna’u?” Ya fada tun kafin na karaso gare su. “Na gama Uncle kuma nagode sosai”. Na fada ina mika masa farantin, tare da kokarin russunawa don gaida Maman na su, sai ji nayi an tankwabar da shi ya fadi kasa. “Me zamuyi farantin da zabiya ta ci abinci? Allah kayi mana tsari da mummunar haihuwa”. Ban taba jin kalaman da suka doke ni irin wadannan ba, duk da ba yau aka fara goranta min halitta ba. Amma wannan matar babba ce ban zaci irin wadannan kalaman na rashin darajta dan adam daga bakin ta ba. Yawanci duk masu yi min gorin zabiya tsaarrraki na ne sai ko Hassan da Hussaini 'ya'yan Kawu na. A nan makarantar dai dalibai 'yan uwa na basa mu'amala da ni amma ba'a faya goranta min da kakkausan harshe irin haka ba, sai da ace "Hasna - Zabiya". Sai na juya sannu a likkafa hawaye cike da ido na na bar wurin. Ina jin shi yana “haba Mama! Haba don Allah Mama! Ubangiji da ya halicci dan adam ya karrama shi……”. Sauran maganganun ban bari sun shiga kunnuwa na ba domin takawa na yi da gudu na karasa hostel ina mai nadamar karbar abincin su. Saidai wannan karamci na wanda ya kira kan sa SAHEEB ya kasa dakushewa daga zuciya ta. To haka 'yan adam muke dama kowa da halin sa, sai ka ga da ya fi uwa hankali, kuma a hakan dai ita ce mahaifiyar sa. Tun daga wannan ranar na soma daurawa kaina damuwa wadda a baya bana damun kai na. Ganewa da nayi cewa halitta ta abin kyama ne ga wasu bangaren al’umma. Damuwar da ba ni kadai ta soma yi wa illah ba, har da karatu na. Performance dina yayi kasa sosai lokacin da aka hada continuous assessment, ni da nake daukar na daya sai gani kowa ya doke ni. Mr Samson shine class master din mu kuma shi ya fara noticing something is wrong a tare da ni, duk da cewa dama can ni din ba ma’abociyar walwala bace amma bana wasa da karatu. Ganin wannan fadowa kasa da nayi warwas, yasa Mr. Samson kira na staff-room. “Hasna do you know that your marks are poor? ( Hasna kin san cewa makin ki bai yi kyau ba?) Kina da damuwa ne ko baki da lafiya ne?” Idanuwa na sukayi rau-rau suna shirin zubar da hawaye. Mr. Samson ya dage sai ya ji abinda ke damu na, ni kuma na rasa me zan ce masa. Da zan iya, da na ce masa so nake ya samo min mai, wanda in na shafa zan koma baka (kirin). Ko mutane sa daina kyama ta da goranta min. The stigma attach to my disability is tormenting my heart. To amma bazan iya gaya masa hakan ba kada ya ga rashin hankali na, (canza halittar Allah) sannan sauran malaman duka sun bada hankalin su a kan mu. Kowa so yake ya ji dalili na na komawa ba fuss a karatu. Sabida kowa da ya sanni ya san mai kokari ce kuma zaqaqura. Daga dalibai har malamai. Sai kawai na samu baki na da cewa “bani da lafiya ne”. Don dai na samu Mr. Samson ya kyale ni. Domin kuwa bai da maganin abinda ke damu na. Mr. Samson ya ce “Oh my dear, me ke damun ki?” “Bana iya barci, zuciya ta tana min wani irin ciwo, ido na baya gani sosai, in dare yayi sai da lalube nake shiga bandaki”. Daya daga cikin malaman mu yace "you need to see a doctor Hasna, if possible za’a kai ki babban asibiti ki ga ophthalmologist”. “Kafin nan za’a kai ki clinic ki ga Dr. Saheeb ku tattauna shi zai san likitan da ya dace ki gani, da asibitin da ya dace a kai ki a yi miki glasses”. “SAHEEB! SAHEEB! A ina na taba jin wannan sunan??? “Haba shiyasa naga tana copying note ba daidai ba” inji Malam Lawal. “Short-sightedness is part of their defect ai, da wuya ka ga zabiyan da ke da cikakken gani” inji Uncle Salisu. Mr. Samson wanda malamin bautar kasa ne kuma kabila amma mai kirkin gaske da kula da daliban sa, shi ya sa ni a gaba ya kai ni har clinic din makaranta da kan sa. Dan asibitin namu karami ne wanda yafi dacewa a kira shi dispensary. Su biyu kacal ke aiki a cikin sa shi da Nurse Saratu, sai kuma cleaner mai tsabtace asibitin. Lokacin da muka shiga rubutu yake a cikin wata folder, nurse din kuma tana sakawa wata student karin ruwa, da alama ita ya gama dubawa. Ko da Samson yayi masa sallama alamar ya zauna yayi masa da biron hannun sa ba tare da ya dago don ganin masu shigowa ba. Sai da ya gama rubutun sa tsaf, sannan ya dago ya dube mu. Wasu irin idanuwa gare shi masu sheki da haske (sparkle) da suka sa na kasa dauke ido a kan sa ba tare da na san kallon sa nake ba. Ina jin Mr. Samson yana gaya masa matsaloli na tare da cewa “ina jin tausayin zabiyar nan, don Allah Saheeb ka duba ta sosai”. Dago kan sa da kallo na da yayi da sparkling eyes din sa, da kuma kallon haushin da ya watsawa Mr. Samson saida suka sa na kusa narkewa a kujerar gaban sa da na ke zaune sabida tsoron idanun sa masu matukar kwarjini. “Ita ta ce ma ita abun tausayi ce? Don kawai tana exceptional child? You are to be encouraging her on her defect, not to weaken her. Words like yours are not encouraging at all". Mr. Samson ya ce “I’m sorry Saheeb, Hasna is among my favourite students, dawowar ta kasa a aji ya dame ni, i don't mean to devalue her." Ya ce “ka je zan yi Magana da ita”. Bayan fitar Mr. Samson cigaba yayi da rubutun sa, har sai da ya gama sannan ya aje biron ya dube ni, a cikin idanun sa concern ne da kulawa tsantsa. “Hasna’u zan iya sanin abinda ke damun ki? Da yasa har malaman ki suka yi noticing cewa kin yi kasa sosai a karatu?” Hawaye suka cicciko ido na, amma ban san meyasa ba na ji shi kam zan iya gaya masa hakikanin damuwa ta, na samu confidence a tare da shi tun lokacin da ya taimake ni ya bani abinci, ya kuma ce da mahaifiyar sa da ta kira ni 'zabiya' Ubangiji da ya halicci kowanne dan adam ya karrama shi”. Tun daga wancan lokacin na ji ina respecting din sa sannan ya dade da zama cikin rai na na kasa manta shi. “Uncle Saheeb, so nake na koma baka (black), ina nufin kalar 'yan Africa, don Allah idan akwai maganin da zai maida ni baka ka bani, ina da ciwo a cikin raina, babu inda yake min ciwo sai zuciya ta tun lokacin da na gane fari na abnormality ne ba kyau bane. Uncle ko kawa banida ita a makarantar nan sabida ni zabiya ce…. A gidan mu su Hassan da Hussaini ba mai alaqa da ni sai mahaifiya ta, ban taba ganin mutum iri na ba a garin mu bakidaya, meyasa ni kadai ce zabiya? Kuma meyasa aka haife ni haka? Ji nake na tsani kai na bana ko son ganin fuska ta a mudubi”. Zuciyar Saheeb ta yi wani irin nauyi, ya dade bai manta yarinyar ba, sabida ita duk sanda ya ga zabiya sai ya waiwaya ko ita ce. Ya dora fuskar sa akan tafukan sa ya soma Magana cikin lallashi. “who told you ke kadai ce zabiya a duniya? There are millions of Albinos around the world wadanda nasu yafi naki muni. In kin duba ke kam naki da sauki akan wadanda ko kuda ne ya sauka akan fuskar su sai yayi musu tabo. Amma a haka suke rayuwar su cikin godiyar Allah. In kina so ki rayu kamar kowa, sai kin cire damuwar abnormality din ki daga ran ki, kin sa a ran ki cewa haka Allah ke son ganin ki, ki fidda maganganun mutane da damuwar su a ran ki domin ba duka keda imani akan Ubangiji ke halitta yadda yake so ba. Me yasa kike son komawa baqa? Hasna you are special a yadda Allah ya yi ki. Wasu makafi ne, wasu kurame ne basu ji basu gani. Wasu kuwa duk an hada musu rashin ji da rashin gani. Wasu kuwa guragu ne basu da kafa. Su kuma su ce me Hasna? Sai su ce lallai sai sun bawa kan su abinda Allah bai ga damar basu ba? Hasna’u ki karfafa imanin ki, in ba haka ba zaki karawa kan ki lalura, kwakwalwar ki ta tabu da damuwa. Kin ga lalura ta karu kenan. Ni na gaya miki in kika cire wanan damuwar a ran ki, kika tsaya ki kayi karatu mai nagarta AN AMAZING HUSBAND na zuwa, wanda ba zai taba kallon abnormality din ki a matsayin nakasa ko abin kyama ba”. Murmushi nayi, murmushin da ban taba yin irin sa a tsayin rayuwa ta ba, babu wanda ya taba gaya min maganganu masu dadi da karfafawa irin na Uncle Saheeb. Koda kuwa ace ya fada ne kawai don ya faranta min, ba hakikanin gaskiyar kenan ba, na yi alkawarin bin duk abinda ya ce don tsira da lafiya ta, ba zan so kam in zamo mentally-retarded bayan zama albino ba kuma. Na alkawartawa rai na daga yau zan so kai na, zan koyawa kaina (self-love and self-determinatio) tare da rungumar kaddarar da Ubangiji ke so na da ita. Maganar da ya ambata ta cewa amazing husband na zuwa idan na tsaya na yi karatu ita kadai nake da inkari (ja) a kan ta. “Na ji duk abinda ka ce Uncle Saheeb, na kuma yi alkawarin bin duka shawarwarin ka, amma ka cire maganar amazing husband na riga na sa a raina har abada bazan yi aure ba. Karatun kadai zanyi ta yi har sai naga karshen sa (idan ana gani), amma bazan taba yin aure ba uncle, ban taba sanya raina ba”. Uncle Saheeb, sai ya kura min ido, zuwa can ya ce “if that is your decision I must say it’s a WRONG decision (idan wannan shine hukuncin ki sai in ce gurbataccen hukunci ne). Wanda ke nuna still kina kalubalantar Ubangijinki da halittar da yayi miki. Aure sunnah ne kuma Allah ya halatta shi akan kowanne musulmi mai lafiyar da zai iya aure. Don haka Hasna’u ki cire wannan doctrine din daga zuciyar ki, ki sa a ran ki duk sanda Allah ya kawo miki miji za ki yi aure. Uncle Samson ya gaya min kina da issue da idanun ki”. “Eh Uncle bana ganin rubutu dai-dai akan allo, kuma in dare yayi sai da lalube nake shiga bandaki”. Uncle Saheeb ya dube ni cikin ido, duk da haka babu alamar tausayi na cikin kwayar idanun sa. Wani yanayi ne a cikin idanun sa wanda ya sha gaban in kwatanta shi da komai, sabida da ban taba gani a tare da kowa ba. “Now, tell me about yourself, ‘yan wane gari ne ku kuma meyasa Innar ki bata zo visiting ba?” “Rashin zuwan Inna ya kara min damuwa don bata taba fashin zuwan ba tun da na fara makaranta. Mu ‘yan garin nan ne amma asalin Babana dan Kabo ne”. Na gaya masa tarihi na bakidaya. (Uncle Saheeb tun daga wancan lokacin har zuwa yau bai daina tunanin hanyoyin inganta rayuwa ta ba). “Go to your class Hasna’u. In an yi hutu tunda saura sati biyu zan zo har gidan ku na kai ki asibitin Murtala ki ga ophthalmologist. Insha Allah you will have a fitted glasses wanda zai taimaka miki. “kin min alkawarin daga yau kin cire damuwar halitta daga ran ki ko? Zaki komawa karatun ki yadda kike yi a can baya? If possible har ma ya fi na baya?” Ina murmushi na gyada masa kai. "Madallah Hasna, now go to your class, an kusa kada kararrawar tashi”. Na juya na fita daga clinic bayan nayi masa godiya mai yawa. Da gaske na ji zuciyata ta yi wasai daga kuncin data ke ciki. (Counselling pays). ****** Hasna’u na bada baya ya janyo system din sa, ya shiga internet sai ya samu kan sa da kasa cigaba da yin aikin da yake yi,sabida tunanin Hasna’u, ya hau yin kyakkyawan bincike a kan albinism. Ko akwai treatment din sa a likitance? Abinda ya fara cin karo da shi shine “Albinism is inheried condition (wato gadon sa ake yi cikin jini) amma Hasna ta ce ita ba gada ta yi ba. Zai iya yiwuwa cikin ancesstors din ta wani ke da shi bata sani ba. Binciken sa ya cigaba da gaya masa cewa; “It happens beacause they have less MILANIN than usual in the body. Melanin gives skin, hair, and eyes their colour. Except for vision problem, most people with albinism are just as healthy as anyone else”. (Yana faruwa ne a sakamakon rashin melanin yadda ya kamata a cikin jikin dan adam. Melanin shine abinda ke baiwa fata, gashi da ido kalar su. In kika dauke matsalar raunin gani, yawancin zabiya lafiyayyu ne kamar kowa). Sai ya koma tambayar menene MELANIN? MELANIN is the pigment that is responsible for our beautiful variety of skin tones and shades, eye colours and hair colours. Not only melanin provide pigmentation for human skin, hair and eyes, it also provides protection against the harmful effect of ultraviolet (UV) rays. Sai ya koma binciken menene treatment din sa a likitance? “Because albinism is a genetic disorder it cannot be cured, treatment focuses on getting proper eye care and monitoring skin for signs of abnormalities”. (Tunda ya kasance gadar sa ake cikin jini, to ba shi da magani, treatment dinsa daya ne kula da lafiyar ido yadda ya kamata da kula da fata koda zata samu sabon sauyi) Darmatologist and ophthalmologist sune professionals wadanda Zabiya ke gani akai-akai. Saheeb, sai ya hada kai da tebirin sa, yana tunanin hanyar da zai bi ya tallafi rayuwar zabiya HASNA’U. Hasna’un da ya fahimci bata da wani cikakken gata bayan mahaifiyar ta, wadda itama bata da karfi. Abu na farko daya tsayar cikin ran sa shine tsayawa lafiyar idanun ta da fatar ta for any abnormality sign, don kada ta rasa ganin ta gabadaya, ta hanyar kai ta ga kwararren ophthalmology Dr. Abubakar Turaki Abdullahi, sannan da zuwa ya binciko halin da Innar ta ke ciki, wanda ya hana ta zuwa ganin ta. Daya al’amarin dake sakadar ruhin sa yaki yake da shi ko ta halin kaka da karfin tsiya don bai ga ta ina yiwuwar sa zata kasance ba in ya tuna an ce “It’s a genetic disorder!” -TAKORI ***** BANGO ABIN JINGINA (ME YA HANA INNA ZUWA?) A duka kwanakin da suka biyo baya da Hasna’u yake kwana yake tashi a ran sa. Don haka bayan kwana uku da zuwan Hasna’u clinic ya bi kwatancen da ta yi masa ya shiga cikin garin Kachako. Karo na farko da ya taba shiga garin tun fara service din sa. Gwamnatin Tarayyah ta turo shi asibitin ‘Unity College Kachako’ domin hidimtawa kasa, a matsayin sa na wanda ya karanci MBBS. Da tambaya da kwatance kuma dama aka ce zabiya baya taba buya a cikin mutane, musamman a karamin gari kamar Kachako, don haka bai sha wahala ba ya gano gidan Kawu Sama’ila. Ya sauka daga kan machine din okada da ya kawo shi ya taka zuwa kofar gidan sannu a hankali, abinda ya dau hankalin sa shine cincinrindon mutane kamar ana daurin aure, sai da ya lura kuma ya gane fuskokin su duka babu walwala kuma kowa alwala yake yi, alhalin ba lokacin kowacce sallahr farilla bane, ba jimawa kuma kafin ya yanke shawarar abin yi ya ga an fito da gawa cikin makara an fara daidaita sahu. A matsayin san a musulmi sai ya ambaci “innalillahi wainna ilaihi rajioun” duk da bai san waye ya rasu ba, ya kuma bi sahu don dama da alwallar sa, akayi sallahr jana’izar tare da shi. Koda aka idar kowa ya wuce makabarta banda wani dattijo da ya zauna akan kututturen iccen darbejiyar kofar gidan. Sai ya karasa gare shi yayi masa sallama. “Sannu samari, daga ina? Wa kake nema?” Dattijon ya tambaya cikin mutumtawa. “Na zo neman gidan su Hasna’u-Zabiya, wadda take makarantar kwana”. Dattijon sai ya dube shi da dukkan alhini ya ce “nan ne gidan, bari maigidan ya dawo sun tafi makabarta kana gani” “Allah ya jikan musulmi Allah ya bada hakuri, ai ba wurin sa na zo ba, na zo ne wajen Babar Hasna’u in isar mata da sakon diyar ta, ni likitan su ne na makaranta”. Dattijo sai ya ce “Allah sarki dan nan, Allah sarki Hasna’u – Zabiya. Da rabon bazaku gana da Inna Zulai ba, ita aka tafi kaiwa makwanci, yau watannin ta biyu kenan a kwance tana jinya sai yau Allah ya hutar da ita”. Saheeb sai ya durkushe a wurin yana fadin “Innalillahi wainna ilaihi rajioun”. Ya nemi waje gefen dattijon nan ya zauna ya rasa abinda ke masa dadi. Tausayin Hasna’u ya kara ninkuwa a ran sa and he vowed to himself to become her guardian and also a shoulder to lie on (bango abin jingina) ko da wannan shine abu na karshe da zai gabatar a rayuwar sa. Yayi hawaye ya share har babu adadi. Ba jimawa su Kawu Sama’ila suka dawo. Dattijon nan yayi masa nuni da Kawu Sama’ila “ga Yayan ta can ya dawo, je ka yi masa taaziyya”. Ya karasa har gaban Kawun ya tsugunna ya gaishe shi yayi masa gaisuwa, sannan ya gabatar da kan sa matsayin likitan ‘Unity College’ da abinda ya kawo shi wato duba ma Hasna Innar ta da kuma abin alhinin da ya tarar. Ya kare da yi masa ta'aziyya. Kawu Sama’ila ya ja shi suka zauna tare a gindin bishiya yana ta gode masa tare da sanya masa albarka. “Wato dan nan ina tausayin Hasna’u, bata saba da kowa ba sai uwar ta, ga ta da kebe kai daga cikin al’umma (alienation), idan ka ga irin shaquwar da suka yi sai ka ji cewa lallai Hasna’u yanzu ne zata yi maraici na baya ba komai bane tunda ko sanin uban bata yi ba. Ko barci baya raba su, sai in ta koma makaranta. Kullum zancen ta shine, “ranar da babu ni, Yaya Sama’ila ko yaya Hasna’u zata yi?” Sai in ce mata Allah da ya halicce ta shi zai bata yadda zata yi”. Hirar mu ta karshe bayan masassara ta kwantar da ita shine ta ce ta san Hasna’u na cikin damuwa na rashin zuwan ta ganin ta a makaranta, tunda bata taba fashin zuwa ba, nace mata ni zan je in gano mata Hasna’u” sai cewa tayi "yanzu ta kusa cika shekaru sha bakwai, na san ba miji zata samu ba, ko yaya rayuwar ta zata kare?” Nace mata “Zulai ki daina irin wannan tunanin Allah shi yake komai, kuma muddin ina raye Hasna’u zata yi aure kamar kowa tunda dai na haifi ‘ya’ya maza, in ‘ya’yan kowa sun ki ta ‘yan uwan ta Hassan ko Hussaini bazasu ki ta ba. Sai ta yi murmushi tace “gara kowa da su in dai a kan Hasna’u ne” nikuma nayi mata alkawarin muddin ina raye, to Hassan ko Hussaini wani cikin su zai auri Hasna’u”. Tunda Kawu ya fara bayanin sa yake saurare attentively har Kawun ya dasa aya. Bai ce komi ba, don bai da abin cewar amma hakika Hasna ta gaya masa Hassan da Hussaini ‘ya’yan Kawun ta sun fi kowa kyamar ta. To ina ga an aura musu ita? Amma su kadai suka dace da auren nata ko babu komi jinin ta ne ‘yan uwan ta ne, but Hasna is talented a karatu despite her disability, talent din da ke bukatar nurturing ba wai auren wuri ba, auren da za’ayi ne kawai don a rufa mata asiri ba don ana son ta ba. To amma shi wanene da zai hana Kawu yi wa ‘ya’yan sa aure in shi ba auren ta zai yi ba? Rasss! Ya ji gaban sa yayi mummunan faduwa. Abu daya zai yi in har yana so ya taimaki rayuwar Hasna’u shine YA AURE TA!!! To amma ya aureta ya kai ta ina? What of the genetic factor? Mama will NEVER allow him to bring ALBINO to her family talkless of matar data riga ta yi masa wato Fa’izah diyar aminiyar ta. “Kawu ina rokon alfarmar kada a fadawa Hasna mutuwar Innar ta sai ta dawo hutu, saura kwana goma su dawo”. Ya fada da wata murya kamar ta wanda ya sha duka hawaye na kundumbala cikin idanun sa. “Sannan ina neman alfarmar a bar ni in kaita asibiti a yi mata gilashi ranar da suka yi hutu ni da kaina zan dawo da ita har gida cikin amana, idan har ka amince da ni. Gilashin zai ceci ganin ta da take gab da rasawa”. “Samari na amince maka ka ji? Ka kaita ayi mata ka dawo min da ita, Allah yayi maka albarka, in iyayen ka na raye Allah ya kara musu lafiya da nisan kwana, idan kuma sun rigaye mu Allah ya kai ladan taimakon da kake da niyyar yi wa Hasna’u kabarin su”. "Amin ya Allah Kawu, ubana ya rasu mahaifiyata ke raye, sai kanwata daya Nusaiba. Sunana Abubakar Saddiq amma ana kira na SAHEEB” “Sannu ka ji Sahabi? Sahabi abokin Manzo, Allah ya baka masu yi maka kai ma”. Da wannan suka yi sallama da Kawu Sama’ila, yana shirin barin kofar gidan wani saurayi na tahowa dukun-dukun da shi idanun shi jajawur, in ba shaye-shaye ba ba abinda zai maida idon namiji haka, ya kalli Saheeb ya watsar, yasa kai zai shige cikin gida. “Kai Hassan don jakar ubanka baka san kanwata ta rasu bane? Ban ganka a makabarta ba kuma yanzu zaka wuce mu baka yi mana ta’aziya ba, ga bako kana gani amma ko ka gaishe shi?” Bai tsaya ba ya cigaba da tafiyar sa yana fadi cikin kunkuni “to Baba ina ruwa na don uwar zabiya ta kwanta dama? Bakon ka kuma meye gami na da shi? Garin kwashe-kwashen ka sai ka janyo wadanda zasu yi kidunafun din ka”. Da haka ya shige cikin gida, kunya kamar ta kashe Kawu Sama’ila, sai da ya gwammace bai kula shi ba. Saheeb yayi kamar bai ji su ba ya sa takalmin sa ya wuce don gab yake da fashewa da kuka da ya gane wannan ne mijin Hasna’u. Mijin da sai wani babban ikon Allah ne zai hana ta auren sa. Mr. Samson ne a cikin ajin yana bada darasin sa na lissafi. “Set Theory” is our today’s topic. Who can tell me what is set in mathematics?” Kamar ko yaushe ya san ita kadai ce zata daga hannu, kasancewar ta masoyiyar darasin sa na lissafi, saboda tsabar son ta ga subject din kafin a yi musu topic ta je labirare ta dubo shi ta yadda in ya zo ya fara koyarwa sai dai ya zama kamar tishi a gare ta. Amma ga mamakin sa yau bata daga hannu ba. Ta hada kai da tebir bata ma san me ake a ajin ba. Har Mr. Samson ya zo gaban tebirin ta ya tsaya, ya kuma kira sunan ta bata ji shi ba. Sai ga sallamar Saheeb wanda baya zuwa classes area sam, amma yau sai gashi har ajin su Hasna’u, gabadaya a hargitse yake kamar bai samu barci sosai ba kuma bai yi wanka ba, bayan ya dauki iznin hakan daga principal ya kuma gaya mata abinda yasa yake son ganin Hasna’u din, ba wani abu bane lafiyar ta zai bincika don tana gab da fadawa depression kuma ga rasuwar mahaifiyar ta ba tareda ta sani ba. Ya gaya mata Kawun ta shi ya bashi iznin kulawa da ita har zuwa asibitin Murtala da zasu je ranar hutu. Principal Haj. Maimuna Dikko, ta yi mamaki kwarai, what is special a kan zabiyar nan da kowanne malami bai da zance sai nata? And now Dr. Saheeb, yayi tattaki har cikin kauye sabida Hasna’u zabiya, lallai ne there’s something unique, something special associated with Hasna’u Dabo, wanda su Malamai da suke tare da ita suka yi noticing. “Samson what’s wrong with her?” Ya fada hannayen sa biyu zube cikin aljihu, sounding worried, gaban sa na faduwa, cike da tsoron ko wani yayi masa riga malam masallaci ya gaya mata mutuwar Innar ta. “I don’t know Dr. But she’s absent-minded”. “Hasna! Hasna!!” Saheeb ya kira sunan ta da dan karfi, tare da kwankwasa tebirin nata. Firgigit ta tashi ta hada gumi kashirman idanun ta sun kada sun yi jazir. Mafarkin da ta yi jiya da inna shi ya daga mata hankali. Sai ta ji uncle Saheeb na fadin. “taso ki biyo ni clinic”. Duk attention din ‘yan ajin sai ya dawo kan su, masu kyabe baki nayi, masu mamaki nayi. Dr. Sahib Bello Wamakko, ya kasance mai farin jinni a wurin ‘yammatan Unity Kachako duk da kasancewar bai dade a makarantar ba kuma ba mai sakin fuska bane. A rashin sanin sa 70% na ‘yammatan unity masu ji da kan su yana matukar burge su. Ya riga ta shiga ofishin sabida tafiyar data ke yi tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki. Nurse Saratu na gyara kantar magunguna ta gan su sun shigo. A yadda ta ga Hasna’u sai ta tabbatar ba lafiya ba, ga fuskar ta kara yin jajawur kamar da ka taba jinni zai yi tsartuwa. “Have a seat” in ji Saheeb. Ya fada yana gyara mata kujerar gaban sa. Ta zauna, amma ta kasa ko duban sa. “What happened Hasna’u?” Girgiza kai ta yi alamar babu komai. Shi kuma ya cigaba da lallashi yana tambaya. “Ni ba Yayan ki bane yanzu? Baki san har gidan ku na je ba? Kowa da kowa yana gaishe ki, ga wannan Inna ta ce na kawo miki” ya fada yana mika mata wata katuwar Ghana must go shake da kayan masarufi na alfarma. Kallo daya ta yi wa kayan ta hau girgiza kai. “Ba Inna ce ta aiko da wadannan kayan ba”. “Why do you say so?” ya tambayeta cikin rashin jin dadi, feeling somehow yau yayi karya don ya farantawa Hasna’u. “Ina ta gan su? Da dai kanzo, kwaki da kuli da mai da dunkule ka kawo shine zan yarda Inna ce ta aiko” “to naji na yi karya Hasna’u, shikenan, har zuwa gidan ku dana yi shima karya ne ko? In baki sani ba har Hassan na gani da malam Audu makocin ku da Kawu Sama’ila da ita Innar kan ta”. A take fuskar Hasna’u ta washe, jan ya ragu, har ta yi murmushi. Ganin hakan ya cigaba da yi mata bayani. “na je na karbo iznin Kawu ne na in kaiki asibiti ranar hutu, daga nan in maida ke gida. So ki shirya da wuri ranar hutu don mu samu ganin likita a cikin Kano”. Bata san meyasa shi ta yarda da shi ba, bata san me ya sa kome ya gaya mata sai zuciyar ta ta yi amanna ba, haka bata san me yasa shi SAHEEB take da kyakkyawan confidence da trust a kan shi ba. Ta ji ta yarda zata iya bin sa ko Birnin Sin ne, ba tare da ta ji ko darr ba, ta amince ba zai cutar da ita ba. Ta kuma yarda ya je gidan su, wadannan kayan ne dai bata yarda daga hannun Inna suka fito ba, they are solely from Saheeb, yace inji Inna ne don yayi mata wayo ta karba. “Kai dai uncle ka gaya min gaskiya, cewa kai ka yi provision din nan, ai ba zan ki karbar kyautar Yaya na ba. Amma ina kudin surfen Inna zai sayi wannan? Jarin abincin ta ya dade da karyewa”. Ta fada with so much love and affection ga Innar ta cikin sautin muryar ta. Saheeb, sai ya ji hawaye na son zubo masa, yayi maza ya juya yana lalube a cikin loka yana hadiye hawayen sa. Ba zai yarda ya zama wanda zai labartawa Hasna’u mutuwar Innar ta ba in ba haka ba har abada bazata daina ganin bakin sa ba. Gara ya bari suje lafiya su dawo lafiya in yaso Kawu Sama’ila ya fada mata da kan sa. “Naji-naji ni Saheeb shikenan Wamakko na yi wa Hasna karya, kwashe ki tafi hostel ki aje su ki koma aji”. A raunane tace. “I’m sorry uncle, ba nufi na ka yi karya ba, tuntuben harshe ka yi” Saheeb ya saki wani kasaitaccen murmushi yana duban ta yace “Hasnah? To shikenan naji tashi je ki, kuma kwana bakwai na baki ki cinye su. Kafin hutu ya kare zan karo wasu” “a’ah Uncle. Ko cikin zani gare ni ban iya cinye wannan a kwana goma”. “Yar dariya yayi wadda bata taba ganin yayi irin ta ba. Sannan yace “pls go with your BAGCO, na sallame ki”. Barci yake so yayi amma ya kasa, sai juyi akan gado. Scenes din yau a clinic ke dawo masa filla-filla. Why is things happening like that? His heart taking another direction, WHY? For Allah’s sake ina zuciyar sa ke son jan sa? She is Albino wadda in ya aure ta duka rabin ‘ya’yan sa sai sun zama albino. Amma akwai abubuwa masu dimbin yawa da suka fizgi hankalin sa a kan ta, abubuwa da yawa da suka gabata sun yi attracting din zuciyar sa, kwakwalwar sa da ruhin sa akan HASNA’U regardless of her skin, hair and eyes colour. There’s something beyond BEAUTY that haunted him as a man, wadanda tausayi shine jigon su. Sai kuma extraordinary characteristics na Hasna wadanda mazan kwarai kadai ke duba su, mazan jiya ba na yau ba, masu dattaku da ilmi. As a medical doctor wanda ya gama shekaru bakwai na MBBS, a yau sai ya ji ba abinda yake so yake buri irin yayi specializing a ‘Dermatology’ ba don komai ba sai don ya din ga kula da fatar HASNA’U!!! ****** BAKIN KANON-DABO (MAGANA ZARAR BUNU….) Kwanaki goman suka zo suka shude kamar kiftawar ido, a cikin kwanaki goman nan Hasna’u gata nan ne dai, ita ba mara lafiya ba ita ba mai lafiya ba. Uncle Saheeb bai kara neman ta ba yana can yana ayyukan sa amma komai yake yana tuna Hasna’u, yana Allah-Allah ranar hutu ta zo su tafi Kano tare. Yana so yayi amfani da wannan damar ya kara sanin Hasna’u ya kara jan ta a jiki ta saba da shi ta yadda zata iya gaya masa kowacce irin damuwa take ciki. Ya alkawartawa ransa zama bango abin jinginar ta wanda har nauyin karatun ta zuwa jami’a zai dauka in har Kawu Sama’ila zai bar ta. Aka ce yau da gobe kayan Allah, a kwana a tashi ba wuya yau Asabar ranar hutu ta zo. Tun asubah da Hasna’u ta dawo masallaci sallahr asubah bata koma barci ba, wanka ta yi ta sanya wankakkun uniform din ta wadanda ta ninke suka kwana kasan filon ta suka bada Karin guga. Sayayyar da Saheeb yayi mata tana nan cikin bagco ko rabi bata cinye ba. Cancanawa tayi ta ta yi don ta kaiwa Inna itama ta ci kayan dadin da ta ke da tabbacin ba ita ta aiko da su ba. Kusan itace farkon fita daga hostel zuwa bakin get da bagcon kayan ta guda biyu, daya kayan sanyawar ta ne a ciki daya sayayyar Saheeb. Tun jiya Jumaah an basu hutu wanda in suka dawo zasu zana SSCE. Hasna’u zata gama Unity tana da shekaru goma sha bakwai cif. Watakila da ta san abinda zata je ta taras a gida da ba ta ci wannan wankan da wannan gugar ba, yau har kwalli ta saka wanda bata saba sakawa ba kuma ya taimaka wajen daidaita kalar kwayar idanun ta. Daga nesa ta hango Uncle Saheeb na tahowa, kyakkyawan matashin basakkwace dogo siriri, fatar jikin sa luf-luf ta ‘ya’yan hutu wadanda suka dama suka kutsa cikin zuzzurfan ilmin boko mai tafiya da zamani, ya dau wanka ya dau kananan kaya masu daraja samfurin ARMANI CODE riga da wando designers kalar fari da ratsin baki, kai kace bakin fatar kasar Ethiopia ne, musamman da ya kawo siririn gilashi mai haske irin nasu na likitoci ya saya kwayar idanun sa. Tun kan ya iso gaban ta kamshin turaren sa ya riga shi wanda har ta riga ta gane shikadai ke da wannan masculine kamshin a fadin makarantar wanda bazata ce ko na wane turare ne ba. “Hasna’u are you ready?” Ya tambaya muryar sa na ‘yar rawa, in ya tuna abinda zata je ta taras a gida. Da far’ar ta tace “ai tun tashin asubah ban koma barci ba Uncle, sabida yadda na matsu in ga Inna, ko barci ban samu ba jiya don bamu taba dadewa irin haka bamu ga juna ba”. Saheeb sai ya juya ya kama tafiya, bayan ya sunkuya ya dauki bagcon nata guda biyu cikin kokarin hadiye kakkarfan hawayen da ke son balle masa. “Biyo ni Hasna muje, we’re almost late”. A parking lot na staff ta ga sun doshi wata kankanuwar mota mai kyau, dark blue, tunda Hasna take bata taba shiga motar gida ba sai yau, daga motar Rake sau Bus din kauyen su. Kofar gaba ya bude mata bayan yasa kayan ta a booth ya rufe. “Hasna mu je ko?” Ya fada yana rufe mata kofar motar, treating her just like a queen of the queens with care and caution. Koda ta zauna ya rufe mata kofar ya zagaya ya zauna a mazaunin sa, sai ya sunkuyo yana sanya mata belt. Hucin sassanyan numfashin sa ya sauka a wuyanta sannan wannan kakkarfan masculine scent din ya nashe ta har fiye da kowanne lokaci. Ji tayi numfashin ta yayi sama, yana sassarfa tamkar zai dauke. Saheeb bai kula ba tsakanin sa da Allah belt ya sanya mata don ya san bata iya ba. Saida ya karanta addu’a a fili ta neman tsari daga sharrin karfe sannan yayi reverse ya fita daga harabar Unity Kachako suka hau kan burjin da zai kai su titi. Sai ya kunna mata a|c ya kuma kunna sautin Shaikh Abdurrahman AS-Sudaith cikin Suratul Nisa’i. Shiru ya ratsa a motar baka jin komai sai sautin Sudaith-Abdurrahman da kuma karar a|c wadda ta soma takurawa Hasna’u. Tunda take bata taba jin sanyi mai ratsa jiki irin wannan ba. Sai ya lura tana takure jikin ta cikin hijabinta kamar mai jin sanyi. Ya rage gudun motar yana tambaya “ko in kasha ne Hasna’u?” “da dai ya fi min” ta bashi amsa da sauri. Murmushi yayi ya kasha a|c din suka cigaba da tafiya. Barci mai alaqa da yunwa suka soma fizgar Hasna’u, tayi hamma ya kai sau uku Saheeb na hankalce da ita, yadda yake hankalce da duk wani motsin ta cikin motar baya kula da tukin motar haka. “Yaya dai Hasna, barci?” “Umh” kawai tace, tana cigaba da hamma. Sai ya mika hannu zuwa kujerar baya ya dauko wani dan madaidaicin foodflask ya mika mata. “ungo nan ki ci wannan kan mu isa Kano, eat fast, I cooked it for Hasna’u. Tun jiya na fere dankalin nasa a firij ina idar da sallah na soya shi”. Hasna’u sai taji dariya na son kwace mata don bata taba jin namiji da girki ba. “Uncle baka da mata ne?” Ya lura dariya take tana kunshe baki ta kuma karbi flask din da hannu biyu. Ya dubeta da kyakkyawar siga sannan ya maida kai ga tukin sa yana murmushi. “Ana dai nema min har an kai kudi, amma ni gani nake ban isa aure ba”. Dariyar Hasna’u ta fito fili yanzu, “me yasa kake ganin hakan? Katoto da kai haka? A garin mu kamar ka zaka samu yana da ‘ya’ya hudu”. Ya rage gudun motar yana kallon ta keenly. “kice kema an kusa yi miki aure, tunda kin kusa gama makaranta”. Nan da nan fuskar Hasna’u ta canza, wani yanayi mara dadi ya bayyana, duk abinda zai jawo mata gori da tozarci akan halittar ta tana gudun shi, ta san kuma aure shine a haqqu na janyo mata babban tozarci, don haka ta dade da haramtawa kan ta shi, kamar yadda Innar ta ma bata sa a ka ba. “Kin yi min shuiru Hasna ko baki ji me nace ba?” tayi dan murmushi mai ciwo wanda ya fito daga kasan ruhin ta, a hankali ta yi Magana, wadda ba don ya kasance cikin masu kyakkyawan ji ba, da bazai ji ta ba. “Da dai a ce ba ZABIYA bace!!!" Ta bashi amsa a gajarce. Zuciyar Saheeb ta yi wani irin nauyi, wani ignition ya soki ran sa, sai da yayi nadamar sa ta yin maganar da ya ga hawaye sun tsatstsafo a idon ta. Sai ya tuna Hasna kwarin gwiwa take bukata daga kowa ba nuna raunin ta ba, ko nuna mata yes, ita din nakasahshiya ce. Muryar sa da karsashi yace. “Shi zabiyan ba mutum bane? Koko shi zabiya bashi da human feelings?” Hasna’u ta yi shiru, don bata san ma’anar sentence din sa na biyu ba. Daga bisani ta ce “a wurin mafi yawan mutane hakane Uncle Saheeb, ba'a dauki zabiyan mutum komai ba, kamar wani aljani ake kallon sa. Just because of skin, eye and hair colour wanda ya barranta da nasu. Duk da haka akwa mutane kalilan, very few, irin wannan da ke gefe na. (Ta dube shi da murmushi) kafin ta cigaba da cewa "Zuciyar ku daban take da ta sauran al’umma. Na gane hakan tun daga ranar da na hadu da kai, sai dai ka yarda irin ka din baku da yawa. You are extraordinary Uncle…..”. Saura kadan ya karawa motar dake gaban sa, sabida yaddda kalaman Hasna’u suka girgiza shi, kallon wadda bata iya banbance komai yake mata ashe da hankalin ta da kyakkyawan tunanin ta. “Hasna…!” Kawai ya iya ambato, sai ya rasa mai zai ce yayi shiru. Daidai lokacin da suka shigo Hotoro. Hasna’u ta wara ido tana kallon birnin Kano, ta Dabo cigari ko da me ka zo an fi ka. Bata taba kiyastawa haka Kano take da girma da kyau ba. For the first time yau gata a Kano mai sunan Baban ta (Kanon-Dabo). Kai tsaye Murtala Mohammed Specialist Hospital suka nufa. Dama tuni ya musu booking na ganin likita tun kafin su zo don ya san mutane a wurin, amma koda likitan ya duba Hasna’u cewa yayi is better yayi referring din su zuwa Aminu Kano Teaching Hospital su ga Dr. Turaki (duba littafin KULSUM). Koda suka je Aminu Kano sun dade akan layi kafin su samu ganin ophthalmologist din. “Ocular Albinism shine albinism mai taba lafiyar ido, kuma shine na Hasna.'u. Ka san Albi ism din kala-kala ne. In this case, a person might need to wear special glasses or 'contact lenses' don ta huta da saka gilashi kullum. Saidai kulawa da shi da wahala. Yanzu in kun amince zan saka mata 'Eccentric Contact Lenses' mai kyau a cikin idon ta. Bayan mun auna 'nearsightedness (myopia) farsightedness (hyperopia) and astigmatism' din ta yanzu. Ku kwantar da hankalin ku ‘Ocular Albinism’ baya kasha ido gabadaya. As she grow older idon ta zai ke gyaruwa. Kuma contact lenses ba’a sanin da shi a cikin idon mutum, sabida a kan kwayar ido ake saka shi”. Inji Dr. Turaki Gaya. Saheeb yace “it will be difficult for Hasna’u ta iya kulawa da 'contact-lenses' sabida a kauye take kuma babu wanda zai taya ta kula dashi, disposable din kuma zai yi mata wahalar samu akai-akai, don haka ayi mata glasses kawai”. Dr. turaki ya yarda da shawarar sa don haka ya tura Hasna dakin awon ido, bayan an rubuta prescription aka bata zabin gilashi karami mai kyau ta zabi wani shade dan siriri, Saheeb ya biya komai aka bashi sanda zai dawo ya karba. A cikin AKTH ya kaita restaurant ta ci abinci mai rai da motsi, tana ci tana kallon sa ganin shi ko ruwa bai sha ba. Sai ta aje cokalin ta ta tura mishi plate din gaban sa. “Na koshi Uncle”. Ya dago daga kan wayar hannun sa cikin damuwa ya dube ta ya ce “babu dadi ne?” Tayi rau-rau da ido tace “gani nayi kaima baka ci komai ba tun safe” sai yayi murmushi yace “kada ki damu da ni ni namiji ne, kuma sau biyu nake cin abinci a rana, amma yanzu to mu cinye tare”. Ya debo abincin a spoon ya kai bakin ta, ta rufe ido cikin jin kunya amma sai ta kasa tankwabe wannan nagartacciyar kulawa ta Uncle Saheeb, ta bude bakin ya saka mata. Sannan shima ya diba ya ci. With one spoon, one plate haka suka cinye abincin. Tun Hasna’u na jin nauyi har ta ware suka ci suka koshi, daidaikun mutanen dake cikin restaurant din sai kallon su suke. Da suka gama tsaf ya bata tissue ta goge bakin ta yace. “Yanzu zamu je gidan mu kiyi sallah nima in yi, sai mu kama hanyar Kachako”. Da sauri ta dago ta dubeshi da blue eyes din ta, sannan ta girgiza kai tace “a’ah Uncle, ka nema min masallacin mata inyi a nan”. Seriously Dr. Saheeb ya ci magani “sabida me bazaki gidan mu ba Hasna'u?” Ba komai Hasna’u ta tuna a wannan lokacin ba sai Maman sa, wadda ta ce “Allah ya raba ta da mummunar haihuwar zabiya", kuma ta kwashi kafa ta je har gidan ta? Ta gan su again tare da Saheeb? Kamar ya san tunanin da take yi sai y ace “ta shi mu je, in dai Mama ce bata nan ta tafi seminar Abuja. Nusaiba ce kadai a gidan”. In ta juyawa maganar Uncle Saheeb baya ai ya zama rashin adalci da rashin kunya, ta gama gane Saheeb ko me zai yi zai yi ne for her own benefit bai da wata riba a ciki. Sannan ba zai taba cutar da ita ba. A hankali yake zura hancin motar zuwa cikin get din gidan wanda ke a sahun farko na unguwar Giginyu. Hasna’u ta daga ido tana kallon gidan su Uncle Saheeb, ko cikin mafarki bata taba ganin kyakkyawan farin gida kamar sa ba, hawan bene ne mai tsayi wanda ya kunshi sassa uku. A lokacin da maigidan ke raye daya nasa ne, daya na Sahib wanda ya kasance da namiji kwaya daya da Allah ya basu sai sassan Haj. Muneera wadda ‘ya’yan ta ke kira Mama, daura da dakin ta dakin auta Nusaiba ne. Alhaji Bello Wamakko tsohon ma’aikacin SHELL ne. Wanda ya rike manyan mukamai a SHELL Company a lokacin rayuwar sa. Ya auri Muneerah a Kano wadda sabida ita ya bar Wamakko ya dawo Kano don tace bazata iya zaman kauye ba haka bazata iya zama a Sokoto ba. Ko a lokacin da yake raye kowa ya san mama itace mijin shine matar. Mama akwai son nuna isa da son ‘ya’ya kamar agwagwa. Haj. Muneera ‘yar siyasa ce ta gani kashe ni domin har mukamin senator ta yi, a yanzu kuma tana cikin shuwagababnnin jam’iyyar su. Bayan rasuwar Alhaji Wamakko Mama bata kara yin aure ba sai rainon ‘ya’yan ta biyu, dai dai gwargwado mahaifin su ya bar musu dukiyar data ishe su rayuwa har suka tsaya da kafafun su. Saheeb (Abubakar Wamakko) kamar yadda abokan sa ke kiran sa yayi karatun sa a jami’ar Ahmadu Bello inda ya karanci MBBS (Medicine), a yanzu yana hidimar kasa a matsayin karamin likita karkashin hukumar hidimtawa kasa (NYSC). Shekarunsa 27 cif. Yayinda kanwar sa Nusaiba da suke kira Nusy take da shekaru 18. Zata kammala Unity a bana. Set din su daya da Hasna’u sai dai aji kowa da nasa, kuma babu wata mu’amala data taba hada su bayan ta ranar da suka wulakantata. Amma ta san ta, don jefi-jefi tana ganin ta. Yayi parking a inda suke adana motocin su cikin wata rumfa mai ban sha’awa sannan ya juya ya dubi Hasna’u wadda ta saki ido da hanci tana kallon komai kamar cikin mafarki. Yanzu wannan muhalli ne da ‘yan adam ke zaune? Shi kansa Saheeb ta jinjina masa yadda ya iya barin wannan gidan ya tafi kauye ya zauna don hidimtawa kasar sa. “welcome home Hasna, yanzu muje wajen Nusaiba ki sallah, if possible kiyi wanka don kiji karfin jikin ki, sai mu kama hanya, amma lallai ne kan mu isa Kachako sai magriba”. Hasna’u ba tace komai ba ta fito ya rufe motar, ta wani corridor suka bi sai gasu a wani yalwataccen falo komai dake cikin shi ruwan goro ne da ratsin lemon green. Nusaiba ce a zauna a daya daga cikin luntsuma-luntsuman kujerun falon tana sanye da doguwar riga ta atamfa kanta babu kallabi, gashin kanta mai yawa sosai, tana kallon tashar Bollywood tana shan cornflakes a cikin wani bowl. Sahib ne yayi sallama amma Hasna’u a cikin cikin ta tayi tata sallamar. Zuciyar ta na dar-dar don bata san irin tarbar da zata samu daga Nusaiba ba. Da sauri ta juyo tana kalonsu suna shigowa. Dogo da doguwa, black and white, cikin uniform din makaranta. A hankali idanun Nusy suka hau kara girma. Wannan zabiyar again? Bata san cewa a fili ta fada ba. Saheeb yayi kamar bai ji ta ba, ya ce “Nusy ga bakuwa ta ki kaita tayi sallah pls yanzu zamu kama hanyar Kachako, in tayi sallah sai tayi wanka”. Nusaiba ta zaro ido tana kallon sa da idanu a zazzare. “Yaya Saheeb? A toilet din wa? Kuma da soso da sabulun wa? Zabiya ce fa!”. Saheeb ya kifa kai a jikin kofa ya rufe idon sa yayin da Hasna’u ta sunkuyar da kan ta. Sai da tace bazata zo ba ya takurawa baiwar Allah. Ya manta Nusy ba hankali. Gata da kyankyami. Shi ba'a bun ya dake ta ba ya firgita Hasna’u ko ya zageta Hasna’u ta ji mummunar kalma ta fito daga bakin sa. Kawai sai ya kama hannun Hasna’u ya jata zuwa ciki. Dakin Nusaiba ya kaita, ya bude mata toilet yace "shiga kiyi alwallah in kin fito ga darduma. In kika yi sallah sai kiyi wankan mu tafi” idon ta fal hawaye tace “kayi hakuri Uncle bazan yi wanka anan ba innaje gida zan yi” baya so ya tsaya ya ga gangarowar hawayen idon ta dson haka ya fita. Rasa yadda zata yi tayi amfani da komai dake cikin toilet din tayi, she has never been in a place like this, gashi komai kal-kal tana tsoron kada ta bata wani abun. Da kyar ta yi alwala a tsaye cikin sink ta fito. Ta tada sallah kenan taji muryar Saheeb yana ta yiwa Nusaiba fada. Maganar da ya fada a karshe ita ta kusa sa ta sakin fitsarin da ta makale mata a mara bata yi ba don gudun kada ta batawa Nusaiba toilet. “Gara ma tun wuri ki sayo majanyi da zanin goyo ki soma shirin goya ZABIYU, domin wannan zabiyar ce uwar ‘ya’ya na insha Allahu!!! Fitsarin ya kwace ba shiri daga marar Hasna’u ya jika wandon makarantar ta tun daga sama har kasa………. ****** DAGA ZARAR BUNU…… (KARAMAR MAGANA TA ZAMA BABBA) Saheeb, yana falon su a zaune yana jiran fitowar Hasna’u cikin tsananin bacin rai bayan shigewar Nusaiba dakin Mama. Ya ji shiru-shiru har wajen mintuna talatin ba Hasna’u, sai yayi tunanin ko ta canza shawara tana wankan ne don haka ya cigaba da jiran ta yana yi yana duba agogon hannun sa yana tsaki, don ba karamin bata masa rai Nusaibah ta yi ba har bai san sanda yayi furucin da ya yi ba, kuma an ce Magana Zarar Bunu ce… ta riga ta fita, bashi da ikon mayar da ita. Tsoron shi Allah tsoron shi kada ta je ta hada shi da Mama, don haka yayi maza ya bi ta dakin Maman, ilai kuwa yana gab da shiga ya ji ta tana waya ya kuma tabbatar ba da kowa bane da Mama ne “…..wannan zabiyar ta Unity ya kawo mana gida har yana neman duka na don nace bazan bata soso na da sabulu na tayi wanka ba har da cewa……”. Saheeb ya yi maza ya doke wayar daga hannun ta ta fadi kasa, ya bi ta ya take da takalmin sa ta wargaje. Nusaiba ta kwalalo ido tace . “Yaya Saheeb! My phone?” “An fasa din, bakin ki ma ina gab da fasa shi in kika fada mata abinda kikai niyya. Wallahi Nusaiba ki fita harka ta na ga alama raini ya fara giftawa a tsakanin mu” ta zumburo baki ta sunkuya tana tattare fasashshiyar wayar ta, sai yasa takalmi ya take mata hannu sai da ta saki kara don azaba. Ya ce “wallahi Allah na kara jin zancen zabiya a bakin ki ko a kunnen Mama sai na fyato ki. Ni sa’an ki ne ko abokin wasan ki? Ina ruwan ki da duk wanda zan kawo gidan nan? Gidan ki ne ko na Uba na ne?” Nusaiba ta soma hawaye. Tace “tun kan ka auri zabiyar kenan? Ranar da ka aure ta ashe raba ni zata yi da kai. You never talk to me in this manner Yaya Saheeb sai akan Zabiya, don haka kasa a ranka wallahi (I hate her with passion) kuma ta yi kadan ta aure ka. Na ji bazan gayawa Mama abinda ka fada ba amma kasa a ran ka bazan taba son Zabiyar ka ba. I want my darling brother back to me….this is not my Yaya Saheeb…”. Ta fashe da kuka sosai. Saheeb sai ya ji jikin sa yayi sanyi, wai meke da Zabiya ne da al’umma ke kyama haka? Ya dauka digon maniyyi ne ya samar da kowanne dan adam kuma shi ya samar da Zabiya? In haka ne kenan ashe duk daya muke (irrespect of skin colour) sai wanda ya fi tsoron Allah? Kanwar sa Nusaiba needs a counseling on disability ba fada duka ba. Ya zauna a kusa da ita yace “Nusaiba-Nusy, you are my only sister da bani da kamar ta ya kamata ko me na zo da shi ki fahimce ni, ni ban ce auren ta zan yi ba, tausayin ta nake ji. Na yi alkawarin kulawa da rayuwar ta a matsayin ta na marainiya ba uwa ba uba ga nakasa. Ina son ganin rayuwar ta yi kyau kamar ta kowa despite her abnormality. Kin san yawan ladan dake cikin hakan? Ita din miskiniya ce dake bukatar tausayi da jin kai daga al’umma, amma irin abinda kike yi a kan ta jahilci ne, mai ilmin addini in ya san farkon sa bai san karshen sa ba, kada ki manta kema mace ce, kuma haihuwa zaki yi nan gaba kadan, kin san irin halittar da zaki haifo? Zaki so al’ummar duniya su taru su juya mata baya don tafito ba irin sauran mutane ba? Nusaiba yanzu haka Maman ta ta mutu, yau sati biyu ba tare da ta sani ba!” Ya karasa fada yana kifa kansa a kafadar ta, Nusaiba could not believe it, da taga hawaye cikin idanun sa. “This is serious!” ta fada a fili, “Yaya Saheeb da gaske son yarinyar nan ka ke yi?” Kai ya shiga girgizawa har yanzu kan sa a kafadar ta. Yace. “Nusaiba I don’t know, son ta nake ko ba son ta nake ba. All I know shine zan sadaukar da rayuwa ta don ganin tata ta yi kyau. Zan iya batawa da duk wanda ya tozarta ta” Nusy ta ture shi daga kusa daga ita tace “Har Mama, har ni?” Ya dago a hankali ya dube ta idanun sa sun kada, a hankali yace “I tried my best to make you understand amma kina komawa wani direction din daban. Now, face your business and leave me”. “I will not leave you Yaya Saheeb, I must get my brother back, yarinyar nan ba haka ta barka ba”. “Me kike nufi da ba haka ta bar ni ba?” “It’s possible charming din ka tayi, in ba haka ba meye hadin zabiya da Yaya na Saheeb duk ‘yammatan da ke fadin duniya da irin matar da Allah ya baka mahaifiyar ka ta zaba maka? Sai ka kare a disease?”. In bai kai zuciyar sa nesa ba zai kare ne da yiwa Nusaibah dan banzan duka, haka take da kafiya da taurin kai kamar Mama, shikuma as softhearted as their father late Alh. Wamakko. Kullum yayi gabas, Nusaiba da Mama sun yi arewa. Fita yayi ya bar ta a dakin zuciyar kowannen su na tafasa, ya nufi dakin Nusy ganin har zuwa lokacin Hasna bata fito ba. Ya duba cikin dakin bai gan ta ba, ya karasa kofar toilet din yana kwankwasawa, shiru ka ke ji, babu Hasna’u babu alamar ta. Da sauri ya fito waje yana tambayar mai aikin su Tani dake shanya ko ta ga wata farar yarinya da uniform? Tace ta fice tun dazu. Da sassarfa ya karasa wajen maigadi yana tambayar sa mintuna nawa da fitar yarinyar? Maigadi yace tafi minti biyar da ficewa. Sai ya koma ya fada mota ya kunna yayi reverse ya durfafi get da mugun gudu, tuni maigadi ya wangale get din don bai taba ganin Saheeb cikin gaggawa haka ba tunda aka haife shi. Domin kuwa a kan idon sa aka haife shi a gidan. Tafiya yake a gefen titi yana mamakin meyasa Hasna’u zata yi masa haka? Daga ki yi sallah ki fito? Sai ki kama hanya alhalin baki san kowa ba cikin gari irin Kano? Ba mamaki bacin ran abinda Nusaiba ta yi mata ne yasa ta ga gara tayi tafiyar ta. Gumi ya shiga barko masa da ya tuna ya karbo amanarta ne wajen Kawun ta, in bai ganta ba me zai ce masa? Ko daure shi aka yi bashi da hujjar kare kan sa, tunda har principal ta san suna tare. Bai kai karshen fita daga layin su ba ya hange ta tana tafiya a gefen titi tana ta zuba sauri kamar zata tashi sama, yayi maza ya sha gaban ta da motar ya sauke glass daga ciki yace. “Hasna’u”. Yadda ya kira sunan ta da rauni, sai zuciyar ta ta idasa karyewa, dama idon ta jike yake da hawaye. “In kin yarda ni Yayan ki ne Saheeb kuma bazan cutar da ke ba, taimakamin ki shigo motar nan in maidawa Kawu Sama’ila amanar sa dana dauko, daga nan ki yanke hukuncin duk da kike so akan alaqar mu, ni dai ta fanni na ba gudu ba ja da baya wajen zamowa bango abin jinginar Hasna’u, kiyi hakuri ko me ya faru ni na jawo miki, saida ki ka ce min bazaki je ba sabida gudun hakan, ni kuma ba don komai na takura kije ba sai don ina so ki saba da karbar kalubale kowanne iri daga mutane mai dadi ne ko mara dadi? Rayuwa bata taba yiwuwa without challenges from people koda kuwa a ce ke kika fi kowa kyau a duniya sai an samu wanda zai ce kyan nan naki ba alkhairi bane, shaidan zaki zamewa mijin ki. I want you to Open your heart and mind and learn how to accept critcsm no matter how bitter, shigo mu tafi kin ji Hasna’u?”. Idan ta ce zuciyar ta bata ragargaje da dadin kalaman sa ba ta yi karya, haka idan tace bata yarda da duk abinda yace ba ta cika butulu. Amma abinda bai sani ba shine ba abinda Nusaiba ta yi mata ne yasa ta barin gidan su ba wutsiya a zage ba tare da ta jira shi ba, sai don tana so ta kawo karshen wannan alaqar, alaqar da ta fara lura bazata haifar mata da Da mai ido ba kuma karshen ta nadama zai zama. “Ki nemo majanyi da zanin goyo kifara shirin goya ALBINOS domin wannan zabiyar itace uwar ‘ya’ya na, Insha Allahu”. Wadannan sune kalaman da suka fiddo ta daga gidan Wamakko helter-skelter, ba tareda second thought ba. Domin bai yi kalaman da sigar da za’a ce wasa yake ba, haka intonation na muryarsa a lokacin da yake furta su kaifin sa yafi na takobi, domin maganar ta fito ne kai tsaye daga karkashin zuciyar sa ba tareda shi kansa ya san ya yi ba. Amma a maganar sa ta yanzu yace zai bata zabi akan alaqar su, fatan sa kawai tayi masa alfarma ya maida amanar da ya dauko. In har zaya bata wannan damar, to yau ce rana ta karshe da alaqar tasu zata kare. Allah ya kai su gida lafiya. Da kansa ya fito ya bude mata kofa ta shiga, ya maida ya rufe silently sannan ya koma nasa mazaunin. A yadda yake tukin motar tamkar tayoyin ta sun yi faci, kuma a gefen titi don ma kada ya sha zagi daga motocin gaban sa da bayan sa. Ji yake kamar kada ya maida ita wannan gidan nasu da ba abinda zata fuskanta a cikin sa sai wahala, tunda babu sanyin idaniyar ta Inna, to in bai kaita nasu gidan ba wanne zai kai ta? Ko dai kawai ya gudu da ita ne ya nema mata shelter? Anya in yayi hakan Kawu Sama’ila zai taba yafe masa? Ya yarda da shi ya amince masa bari ya tabbatar da wannan yardar, ya tabbatar masa har yanzu cikin ‘yan adam akwai masu amana. Sai da suka hau babban titi dodar ya tuna bata son A|C sai ya kashe, ya kunna mata sautin Khusairi cikin Suratul-Al-Imran. Kamar ya san surar da take matukar so kenan kuma a ita suke a islamiyyar su ta cikin UNITY wato daga ita sai Baqarah sai saukar su, wanda zai zo daidai da kammala SSCE din su. Sai ta hau bin karatun a zuciyar ta wata irin nutsuwa na shigar ta, tsoron Allah na kara samun gurbi a ran ta. Ta ji dama su dawwama suna wannan tafiyar ita da Saheeb, watakila daga yau bazata kara ganin sa ba, don ta riga ta yankewa kanta kawo karshen alaqar su, kada tausayi da jin kai irin nasa su sa ya saki layi ya hau kan turbar wanda su duka ba zai bulle dasu ba. Suka tsaya a Wudil ya je ya sayo mata soyayyen kifi ragon ruwa da ruwan sha, daga shi har ita an rasa mai Magana, zukata kadai ke kiyasi, kowanne kuma da abinda yake kiyastawa daban da na dan uwan sa. Ita tana tunanin hanyar kawo karshen alaqa, Saheeb yana tunanin hanya mafi dacewa ta maida alaqa infinite. Sai a lokacin da ya ajiye mata kifin ne ta ji kamshin sa ta dan motsa kadan tace . “Bana cin kifi, inada allergy da cin kifi”. Ya dube ta a hankali da lumsassun idanun sa yace. “Dama shi yasa na so tafiyar nan, don in san likes and dislikes din ki, and I know a lot in one day, ga tsoro kamar farar kura”. Murmushi ta dan yi ta juya kan ta ga taga, bata ce komai ba. Ya cigaba da tuki har suka kusa albasu, lokacin shidda na yamma ta yi, ya tsaya a garin albasu ya saya mata lemun La-Casera mai sanyi guda biyu sannan ya shiga wani shago ya dinga sayayya. Sabulun wanka dana wanki, omo, maclean, brush, deospray, hypo, Dettol soap, Vaseline da sababbin panties, always pad, indomie, kayan tea da kuma slippers ya sayo cikin katuwar bagi ya zo yasa a kujerar baya. Ya je ya bi jam’in sallahr magriba a kofar shagon sannan ya zo ya tadda Hasna’u ya tada motar. “I’m sorry for keeping you waiting Yayan naki akwai kailula” “Sallah fa ka yi, to ai dole in jira ka don Inna ta ce it ace sama da komai”. Saheeb ya juyar da kai kamar bai ji ta ba, zuciyar san a kokawa da hawayen idon sa. Daga nan basu kara Magana ba har suka shiga Kachako, kawai ta ga yana daukar hanya babu tambaya domin tuni ya rike gidan Kawu Samaila. Kugin karshe da motar ta yi a kofar gidan Kawu Samaila ne. Ga yara suna ta wasan dare an kunna aci bal-bal wasu kuma na gefe suna sayar da soyayyar gyada marau-marau. Hasken motar yasa duk suka dare suna ihu. Duhun dare da ya shigo yasa basu san su waye a cikin motar ba don Saheeb ya kasha fitilar. Ta juya da zummar yi masa godiya ta fita sai ta hango idanun sa cikin hasken farin wata suna wani irin sheki da maiko kamar na hawaye amma dai basu gangaro kan kundukin sa ba. Tace. “Yaya Saheeb bani da bakin gode maka, sai dai in ce Allah ya yi maka sakayya da aljannah madaukakiya ya ji kan ka kamar yadda ka ji kai na. Allah ya shige maka gaba a kan dukkan al’amuran ka ya baka duka binda kake nema a rayuwar duniya”. Ta murda handle din kofar da zummar ficewa, amm sai ta ji shi gadagau (a kulle). Ta juyo tana duban sa da idanun bidar dalili? Sai y langabar da kai yace mata. “Abu daya nake nema yanzu a rayuwa ta, ki taya ni rokon Allah to make it easy for me wurin mallakar sa, ta ko’ina na juya na hanga na hango it is not easy, duk da haka ban fidda rai ba kuma ban ja da baya ba, sannan gaba na bai fadi ba. Tunda Allah ya ce “La taqnadou min rahmatullah…”. Hasna’u tayi murshi, he’s always bold, kuma dama ita ta tsani ragwan ta, tana son mutum mai yarda da kan sa da jajircewa bisa ra’ayin sa. “Idan alkhairi ne a gare ka Allah ya baka, idan ba alkhairi bane Allah ya musanya maka da mafi alkhairi sa. Ka dinga sanya tagociya a addu’ar ka sabida ba duka abinda muke so bane yake zame mana alkhairi ba”. Ta sake kokarin bude mota amma ko gezau. Da ta juya saida tayi nadamar juyawar a karo na biyu. His eyes are sparkling tamkar hasken wata dan daren goma sha hudu. A cikin su wani yanayi ne mai wuyar fassarawa wanda bata taba gani cikin kwayar idon kowa ba. Muryar ta na dan rawa tace “ka bude min in fita Yaya Saheeb, nan kauye ne, bai kamata muyi ta zama cikin mota ba”. Da wata irin murya kasa-kasa yace. “Idan kuma na fito na tsaya a zaure a ce na zo zance ko?” “ZANCE?” Hasna’u ta maimaita Kalmar cikin sigar tambaya don kuwa da gaske bata gane mata ba. “Eh mana, idan na fito zauren ku muka tsaya muna Magana ya zama zance irin na saurayi da budurwa”. Da sauri Hasna’u ta lullube fuskar ta da hijabin ta tana fadin ‘’ka bude min kofa Yaya Saheeb”. “An ki a bude, sai kin gaya min sunan saurayin ki?” “Ya ilahi!” Hasna’u ta fada a fili amma ta kasa sauke mayafin da ta rufe ido da shi, shi kuma yace bai bude kofa sai ta gaya masa sunan saurayin ta. Da ta ga lokaci yana ta ja, sannan yaran gidan su sun fara taruwa suna shafa motar sai tace masa a hankali kamar cikin rada. “Banda abun ka waye zai so zabiya ne? Ni fa ka san Allah ban taba yin Magana da wani namiji ba bayan malamai na a class ko staff room. This is out of my vocab-bank (vocabulary Bank)”. “And it must be included in your vocabulary bank, because at this stage da kike ciki na gab da kamala makaranta its either ki zabi miji ki gabatarwa Kawu, ko ya aura miki duk wanda ya ga dama”. Hasna’u a ran ta tace “ashe kuwa zamu shata babban layi ni da Kawun, nan kusa ban ga ranar aure na ba, daga ni har Inna karatu muke so na yi”. Murmushi Saheeb yayi, domin shi mutum ne mai karfin ji, abinda take zaton a zuciyar ta ta fada ya gama shigewa kunnen sa. Ya kuma gamsu da abinda tace din na bazata bari a yi mata aure yanzu ba, kafin nan zai tunanin mafita ga rayuwar su, koda kuwa hakan na nufin…. Ya dauke ta ne ya gudu da ita inda basu da kowa a daura musu aure. Idan Mama ta ki. “Ka yi wa Allah Yaya Saheeb ka bude min kofa in fita”. Ta fada kamar zata yi kuka. “Sai na gama kallon mata ta!”. Hasna’u bata san lokacin da ta bude light blue eyes din ta tana kallon shi ba, kallon mamaki da tsoro, hadi da firgici. Wadannan sune kalaman da har abada bazata manta ba, domin sune mabudin littafin kaddarorin ta masu dadi da marassa dadi. Sune kuma suka maida zarar bunu…. ta zama babbar maganar da ta kai ta har matakin da take kai a yanzu. Ya lura da irin kallon da ta ke yi masa na firgici da tsoro, sai ya lumshe mata lumsassun idanun sa tare da daga girar sa guda daya. Ya saki lock din motar ya fita ya zagaya ya bude mata, amma sai ta kasa fitowa tamkar an sa glue an manne ta a kujerar. Bai takura mata ba, ya koma booth yana sauke kayan ta yana baiwa yaran suna shiga dasu gida. Suna ta ihu “ga zabiya ga zabiya ta dawo”. Wani bakin ciki yazo ya tokare Saheeb a kahon zucci. Why not al’umma bazasu kira mai nakasa da sunan yankan sa ba? Sai dai a kira shi da inkiyar sunan nakasar sa?” Suna gama shiga da kayan sai ga Kawu Sama’ila ya fito da sauri da far’a yana “maraba lale da mutanen Kano, ya bashi hannu amma Saheeb sai ya tsugunna akan gwiwowyin sa bai bashi hannun ba yana gaishe shi with due respect. “Ayi hakuri kawu mun yi dare, hakan ya faru ne a bisa layin ganin likita” Kawu yace “babu komai Sahabi, ai na san yadda ake ganin likita a Kano, kwanaki da ido ya matsa min ai can naje, Murtala, kada ka so ka ga wahalar da na sha sai I yanzu na dawo gida”. Ya maida duban sa ga Hasna’u tana fitowa daga mota jiki a mace kmar wadda ta sha duka. Ya ce “ka gaya mata ne?” Da sauri Saheeb ya girgiza kai “a’ah Kawu, gara kai ka gaya mata da kan ka” “to babu laifi ka je, Allah ya kiyaye hanya nagode Allah yayi maka albarka. An yi gilashin?” “Eh an yi, ji bi zan karbo in kawo maka, insha Allah”. Babbabn abinda yake burgeshi da yaron kenan, komai zai ce sai ya hada ta da Kalmar “insha Allahu”. Daidai lokacin da Hasna’u ta karaso tana gaida Kawu, ya dube ta da tausayawa yace “shiga gida gani nan, kicewa Hajjo ta baki abincin ki”. “Ai ya saya min abinci na ci Kawu, Sallah dai zan yi in kwanta in huta” Kawu y ace “to maza ‘yar albarka, shi din kun yi sallama ne?” Hasna tayi maza ta shige gida bata tankawa Kawu ba. Ya yi murmushi yace “ai Hasna’u bata son Magana Kawu, in ma nayi mata sai ta ga dama take tanka ni” Kawu yace “haka take fa, uwarta ma Allah ya jikan rai haka take, sai su wuni basu kula kowa cikin gidan nan shiyasa sam basu da abokin fada, basu da abin yi sai sana’ar sayar da abinci da surfen su”. “Kawu a gaya mata ta lallashi, ta kyakkyawar siga, a nuna mata dukkan mu na haka ne Inna bata yi gaggawa ba muma duk jiran tamu muke”. Kawu yace “je ka kada kayi dare da yawa, na san yadda zan bi da ita, gashi ba iya kwanan zaure zaka yi ba da ka kwana dakin su Hassan in ya so da sassafe ka tafi”. Murmushi yayi ya juya yan fadin “ba kwanan ne bazan iya a nan ba, watarana zan zo na kwanan, yanzun ina kan uzuri Kawu”. Kawu ya ji dadin abinda yace masa yayi ta saka masa albarka. Kawu Samaila bai koma gida ba sai da Saheeb ya ja motar sa ‘kia-picanto’ a hankali ya bar harabar gidan sa. Sannan ya juya ya nufi gida, zuciyar sa cike da kaunar yaron da kuma alhinin abinda zai gayawa Hasna’u. ****** MUTUWA MAI TONON ASIRI..... (WANDA YA RASA UWA SHI KE DA KUKA). Hasna’u na shiga gida kai tsaye bangaren su ta nufa da sassarfar ta, Hajjo matar Kawu na zaune kofar dakin ta tana kallon ta ta shige bata ce mata komai ba, kayan ta da aka shigo da su duk Hajjo ta sa an tule mata a kofar dakin Innar ta. Don ma kada a fara cewa a dakin ta zata zauna. Tun daga kofar sassan take kwada sallama tana fadin. “Inna kina kusa? Inna gani na dawo!” Ta sa kai a rumfar, duhu dudum, ya bakunci idanun ta, Inna bata kunna aci-bal-bal da ta saba kunnawa ba, ko mai yasa?. “Inna lafiya kike zaune cikin duhu haka? Wai kina ina ne ko gyaran murya bazaki min ba in sallah kike yi?” Ta fada tana lalube a cikin dakin. Sai ta jiyo gyaran muryar Kawu daga bayan ta, yana haska tocilan yana tahowa. Yace “Hansai dakko kayan ki ki biyo ni” cikin damuwa tace “Kawu ina Inna ne? Ko bayi ta zaga?” Kawu yayi gaba bai kula ta ba, sai ta bishi da gudu-gudu cikin alamu na fara shiga rudu, har ta riga shi shiga dakin nasa. Saura kadan ta bangaje shi. Ya zauna yana haska 'light blue eyes' din ta wadanda sai sheki suke yi kamar idon mussa (mage) yace. “Zauna Hansai ki bani hankalin ki kin ji? Hakika Ubangiji baya dorawa rai abinda ya san bazata iya dauka ba. Ya san ZAKI IYA! Shi yasa ya dora miki”. Hasna’u ta fiddo iyakacin 'yan kananun idanun ta da iyakacin girman su tana kallon Kawu Sama’ila. Ya cigaba dacewa “Kullu nafsin za’ikatul maut, daga ni har ke bamu tsira ba, jiran ta muke yanzu ne? Gobe ne? Anjima ne? Tana tafe bazamu taba iya guje mata ba sai fa in lokaci bai buga ba”. Hasna’u dai kallon sa take tana jiran ta ji karshen wannan wa’azi da bata ga dalilin sa ba. Daga tambayar sa ina Inna? Kawu yacigaba da jawo aya da hadisi yana fassarawa akan muhimmancin yarda da hukuncin Ubangiji mai dadi ko mara dadi wajibi ne ga dukkan musulmi. Wanda ya yarda Allah shine mai bayarwa kuma mai karba a duk sanda ya so. Ya kasa fitowa fili ya fadi maganar dake kunshe a bakin sa, sai dawurwura yake, a ran sa yana fadin "da na sani na shigo tare da Sahabi, na ga ya fini kaifin harshe", ita kuma bata katse hanzarin sa ba sai da ya rasa sauran hadisin fade sannan ya nisa…. Ya ce “Hansai Zulai ta sha jinya ta wata biyu, masassara ta kwantar da ita, ba irin maganin da ban sayo mata ba, an yi jike-jike har ba adadi a karshe na kaita asibiti a birni. Kwanan mu biyu da dawowa daga asibiti jikin ya dan yi kyau, kuma likita ya ce tayifot ce ta kama mata hanji, an dora ta akan gwaje-gwajen da suka dace, kafin akai ga yi, da safe na shiga don in kai mata koko, sai gani na yi rai ya yi halin sa…”. Hasna’u ta runtse idanun ta kafin ta ce. “Kawu menene rai yayi halin sa?” Yace “halin sa na bakon kan hanya mana! Ya tafi inda aka turo shi, ta rasu!” Zai cigaba da wa’azi sai gani yayi Hasna’u ta mike ta fita da gudun gaske, dakin su ta koma tana lalube tana kiran sunan Inna! Da iyakacin muryar ta. Da iyakcin makogaron ta. Wanda hakan ya janyo hankalin al’ummar gidan duka aka taho sassan. Kawu ya zo ya kamata ganin tana buga kanta da bango har goshin ta ya fashe. Yace “Hansai kice “Innalillahi wainna ilaihi rajioun…. Kada Allah yayi fushi da ke”. Ina! Hasna bata ji me yake cewa ba, jinni ke fita daga goshin ta a lokacin. Duk da cewa fatar zabiya tana da karfi amma ta buga kan sosai da bango hoping itama Allah ya dauki ranta kafin abinda Kawu ke fada ya zama tabbatacce. Kawu ya rike ta tamau yana ta ambata mata. “Ina lillahi wainna ilaihi rajioun…. " Bai gushe yana yi ba sai da ya ji ta kama. Kuma bai saketa ba, sai da ta sulale da kanta ta yi kasa. Koda ya duba sai gane bata numfashi, Hajjo tace "Hassan maza kawo ruwa kada ‘yar ma ta mace mu shiga uku” Hassan yace “Hajjo don Allah ku bar ta ta karasa, kowa ya huta, in ta rayu me zata yi mana banda karawa Baba nauyi? A bar shi ya ji da mu, mu lafiyayyu da muka zame masa dole, ku barta tabi Uwar ta”. Kawu ya saki Hasna’u yayi kan Hassan da mugun duka Hassan ya gudu, Kawu ya fadi, sabida babbar rigar sa da ta tadiye shi, ya bugu sosai, Hajjo ta ce. “Oh ni Hajjo! Duk akan zabiya zaka hallaka kan ka? To wallahi ‘ya’ya na basu shirya zama marayu ba, in ka mutu kuma ka san inda zaka kai zabiyar ka”. Kawu bai san sanda ya fashe da kuka ba ya dawo kan Hasna’u yana dingishi. Atika ce ji tausayin Kawu ta kawo ruwa a kofi wato autar Hajjo ya hau shafa mata a fuska yana kiran sunan ta. "Hansai, Hansai, Hansai diya ta!" An dauki lokaci kafin Hasna’u ta yi ajiyar zuciya, shima Kawun yayi, ya kwance dankwalin dake kanta ya daure goshin ta. Daga nan ta mike zaune, sai kuma ta ja gefe ta sanya kai a tsakanin cinyoyin ta ta soma kuka…. Hakika kuka rahma ne ga dan adam a lokacin da zuciyar sa ba ta da sassauci. Hasna’u tayi kuka ta yi kuka kamar ranta zai fita, kuka irin wanda bata taba yi a rayuwar ta ba. Kukan sabo da kewa… kukan kauna da soyayya, kukan da ba zai dawo da UWA ba, balle UWA irin tata da ta sadaukar da rayuwar ta domin inganta tata. Hajjo da ‘ya’yan ta suka yi tafiyar su, amma Kawu akan Hasna’u ya kwana, don ya kasa tafiya ya bar ta cikin wannan mawuyacin halin, shima sai a lokacin mutuwar ‘yar uwar sa ta doke shi ta dawo masa sabuwa. Suka hadu su ka yi ta kuka shi da Hasna'u. Bai fita ba saida aka kira sallahr asubahi, bayan ya zuba mata ruwa a buta, ya roke ta tayi sallah ta yi wa uwar ta addu’a. itace kadai tsakanin su yanzu. Hasna’u tayi alwala ta tada sallah amma koda tayi sujjada bata iya addu’ar ba sai kuka. Kullum Inna ce ke tada ita sallah suyi tare. In ta tuna wai bazata sake ganin Inna ba ko yin Magana da ita sai taji zuciyar ta kamar zata fito ta bakin ta. Koda gari ya waye ba wanda ya bi ta kanta a gidan. Kowa harkar gaban sa ya shiga yi yadda ya saba. Ko gaisuwa babu wanda yayi mata. Tana can takure akan gadon bonon Inna ta dauki zanin atamfar Innar ta lulluba ta rungume rigar ta, hawaye na bulbula. Hawayen da basa dawo da UWA a lokacin da DA ya rasa ta. Koda Kawu ya fito don tafiya kasuwa yace da Hajjo dake rabon dumame da koko. “Hajjo in ce ko kin mikawa Hansai nata?” Hajjo ta aje ludayin da take damun kokon da shi ta jefa masa harara ta ce “da can ni nake basu?” Yace “ai yanzu ba mai batan, dole duk abinda kika baiwa ‘ya’yan ki ki bata”. Hajjo tace “tabdijam! Dole fa ka ce! Hakan kuwa ai ba mai yiwuwa bane tunda kuwa su talla suke da sayar da Rake su kawo min, ita ko ‘yar makaranta ce bazai yiwu ‘ya’ya na su sha rana su nemo abincin su in dauka in bata ba, sai dai in itama in dinga dafa mata Rogo tana kaiwa kasuwa kamar yadda Atika ke yi”. Kawu ya ce “amma kin san Zabiya baya son rana ko? Uwar ta ko surfen data ke wuni yi kina gani bata bata ko sau daya ta ce ta taya ta ba, wane talla wannan halittar Allah zata iya yi miki?” Hajjo tayi mirsisi tace bata bada dumame saidai yaje ya sayo mata a waje. Kawu yace “sai aka yi rashin sa'a sunana Samaila amma ba sauna bane, da za’a gindaya min yada zan yi da gida na, dole kullum kika dafa ki bata ko ni a cire min kwano a gidan a dinga bata nawa, ai nima ina fita in nemo in kawo to a bata wanda na kawo. Hajjo tace nayi rantsuwa kuwa daga yau na cire ma kwano a gidan nan har sai ta koma inda ta fito”. Duk abinda suke yi din nan a kunnen Hasna’u. yanzune ta tabbatar ta zama marainiya ta kowacce fuska amma a baya babu wanda ya kai ta gata. Yanzu ne ta tabbatar wanda ya rasa uwa shi ke da kuka kuma mutuwa TONON ASIRI GARETA. Kawu ya shigo da kwanon dumamen yana kiran sunan ta “Hansai kin tashi?” Ta daga masa kai “ga nan dumame to ki ci” ta girgiza kai alamar bata ci. Yace “kada ki soma cewa zaki hora kan ki da yunwa, hakan bazai dawo da Zulai ba, saidai ya sanyata cikin damuwa. Maza karbi ki ci in je in nemo miki ruwan shayi mai zafi ki warware hanjin cikin ki”. Ta karba ta ajiye a gefe ba don zata iya ci ba, sai don so take ya fita ya bata waje, she want to be alone tayi tunanin makoma ga rayuwar ta. Zai fita kenan yaci tuntube da manyan bagco guda biyu, ya tsaya ya bude yana dubawa, sai ya ga duk wani kayan bukatar dan adam yana cikin wadannan jakunkuna daga na ci har na amfani. Cikin mamaki yace. “Hansai, wannan kuma daga ina?” A hankali ta kai idon ta ga kayan amma bata ce komai ba. Domin ta gane daga inda suka fito. Jakar farko sayayyar da kai mata unity ce ya ce inji Inna, ta biyun kuma wadda yayi a Albasu ce a hanyar su ta dawowa bata san ko wa ya yi wa ba. Ajiyar zuciya ta kwace mata, amma bata ce komai ba. Shima Kawun sai ya gane daga inda kayan suke ba tare da ta bude baki ta gaya masa ba. Ya jinjina kai yana mamaki yace. “Sahabi ko?” Kai ta gyada masa. Sai ya dawo ya zauna akan karaunin dakin yana fuskantar ta yace “Hansai, me ke tsakanin ki da wannan yaron ne?” Kai ta girgiza masa da sauri alamar babu komai. Yace “a’ah Hansai, in kin ga kare na sunsunar takalmi dauka zai yi. Ni na gaya miki akwai wani abu a kasan ran sa game dake, amma lokaci zai fada miki idan ni baki yarda da ni ba. Saidai kuma hakan ba mai yiwuwa bane domin bazan kai ki inda zaki wulakanta ba, ke ba uwa ba ke ba uba ba, don haka na riga na yanke hukuncin da zai fishshe ki, in ya so ni ayi ta haifomin jikoki zabiyan ina kula da abuna, dama Kakar mahaifinmu ma Zabiya ce, nafi kyautata zaton wajen ta kika gado". Yana fita Hasna’u ta lula a tunani? Ko me Kawu yake nufi da cewa ya riga ya yanke hukuncin da zai fishshe ta? Ta ji dadin abinda yace da yace ba zai kai ta inda zata wulakanta ba, wanda ke nufin ba abinda zai rude shi ya sarayar da martabar ta, koda abinda yake hasashe din ya zama gaskiya akan Uncle Saheeb. Wunin ranar zungur Hasna banda sallah ba abinda ke tada ta daga gadon bonon Inna. Bata tashi jin sababbin hawaye sai ta yi sujjadah. Bata ci komai ba tun safe har dare, tana ji Hajjo da Kawu na fada kamar zasu yi dambe da yamma da ya dawo wai tunda ya ce Hasna’u bazata yi talla da rana ba, to dole tayi mata tallan gyada a kofar gida da daddare ko a dandali. Kawu yace “Kinsan Allah Hajjo? In kin ga Hansai ta yi talla, to ki tabbata bana numfashi”. Tace “da ranka da lafiyar ka, da idon ka da jin ka, sai Zabiya tayi tallan Rogo da gyada”. Ya riga ya san halin Hajjo, bata sa kanta abu ta fasa, shi yasa yau litinin ya ki fita kasuwa ya zauna a soro yayi shimfida, ya kunna radio ya aje tum-tum din auduga ya kishingida a kai, shi bai yarda ba gadin ‘yar sa yake kada a dora mata tallan Rogo. Kawu ya ce. "Kasuwar ma na daina zuwa kowa ya ci uban sa. Rigima uban wa ta kashe? Nima rigimamme ne". Motsi kadan Hajjo ta leko soro ta ga ko ya gaji ya tafi? Sai ta gan shi daram-dakam ya kunno jakar magori ko taskar labarai. Hussaini wanda shi kadai ke zuwa makaranta a gidan ya dawo da azahar ya gan shi a soro. Yace. “A’Ah Kawu yau baka fita bane?” Yace ban fita ba din, kun bani ajiya ne? Ko kuna bi na bashi? Ko a kan ku nake zaune?” Hussaini yace "Allah ya bada hakuri daga tambaya? Ai ba ni nakar zomon ba, kuma ba nina kashe uwar Zabiya ba. Na lura tunda Zabiya ta dawo hutu kake cikin bala'i da kowa a gidan nan”. Kawu ya rarumi takalmin sa ya maka masa yana cewa "uban ku zaku ci daga ku har uwar take mai zuga ku ku min rashin kunya". Hussaini yayi ciki da gudu yana kiran Hajjo. Hajjo tace "rabu dashi, mutuwar kanwar sa ta sa ya zama kansa da motsi. Ni kuma ba mai aje min zabiya a gida, Atika tazo haihuwa ta haifo min jika Zabiya saboda yawan ganin Zabiya. Dole yasan yadda zai yi da ita. Wajejen karfe sha biyu na rana wata mota kanknuwa 'dark-blue' ta yi fakin a kofar gidan Kawu Samaila. Kawu yaji hucin motar (don sam bata kara) amma bai kawo gidan sa aka zo ba. An dauki mintuna kafin mai motar ya fito yana rufe kofar ta da keys din hannun sa, wadanda ke makale jikin wani kyakkyawan key-holder. Ya isa soron yana sallama da wata lallausar murya. Kawu ya amsa yana zuqar turare mai dadi a kofofin hancin sa kafin ya ce. “Wa nake gani kamar SAHABI!” Ya rage tsawo yadda bazai buge da gajeriyar kofar zauren ba ya shigo yana fadin “ni ne Kawu, ba fa Sahabi bane sunan, har yau ka kasa fada dai-dai, SAA-HEEB”. Kawu yace "koma menene duk abokin Manzo yake nufi, shigo daga nan kusa gare ni ka zauna, ka sha hanya”. Ya tsugunna har kasa ya gaida Kawu sannan ya zauna a gefen sa yace. “Yaya Karin hakuri Kawu? Kuma yaya Hasna'u ta kara ji?” Kawu yace “Ai na ga boni! Kai dai akwai ka da wayo, shine ka zame ka barni da jidalin Hansai, wallahi har goshi ta fasa. Yau kwana biyun nan bana jin ta ci abinci ko loma daya ne. ban taba ganin mai son Uwa irin Hansai ba”. Da Kawu ya san yadda maganar ta doke shi da bai fada masa ba. Kwana biyu ba cin abinci? Ta fasa goshi? That delicate and fragile skin? Murya can kasa yace. “Zan iya ganin ta Kawu? Ni in na bata abinci zata ci, idan na bata baki zata saurare ni”. Kawu "ya ce da na ga ta fara borin nan kamar na mai iskokai sai da na tuno ka ai, na ce da na sani kai ka gaya mata". Ya kwalawa Atika kira ta fito da sauri, idon ta a kan Saheeb, yace "maza kirawo min Hansai, ki ce tazo in ji Sahabi”. Kafin ta kira Hasna’un sai da ta fara gayawa Hajjo ga wani dan gayemai mota ya zo wajen Zabiya. Hajjo tace “dadi na da ke Atika dabbanci, waye zai zo wajen zabiya?” Ta ce “Hajjo toh? Fito da kan ki ki gan shi”. Ai kuwa Hajjo sai ta yi lullubi ta je soron kamar zata leka waje neman yaro, ta gansu suna cin rogo da soyayyar gyada shi da Kawu. Ta ce. “Gafara dai!” Kawu ya zabga mata harara shi kuwa Saheeb sai yayi kasa yana gaishe ta. “Samari me kake nema? Ko ka yi batan kai ne?” Kawu ya ce “a’ah makuwa yayi, kinsan kowa makakke ne irin ki, da auren ki Hajjo? Ki fito cikin maza ba iznin mijin ki?” Ta wuce ciki tana cewa “meye laifi na don na zo in gaya masa gaskiya? Ka san Zabiya abinda yasa ake haifar su a haka, an sadu da uwar su tana jinin al’ada”. Ba Saheeb kadai ba hatta Kawu kunya ce ba ‘yar kadan ba ta kama shi mai tattare da bakin-ciki da takaici. Yana so ya baiwa Hajjo amsa daidai da wacce ta fada yana tsoron kada su raba abin fade a gaban bako mai daraja a gareshi irin Saheeb. Duk sukayi mata shiru, sai ta wuce ciki tana fadin. “Ni dai na gaya maka gaskiya”. Kawu yayi ajiyar zuciya Saheeb kuma ya sunkuyar da kai, Kawu yace “wato su mata duk girman su da shekarun su tumaki ne Sahabi. Banda haka da tuni na rabu da Hajjo domin zaman nan daka ga na yi gadin Hansai nake kada ta dora mata tallan rogo, yarinya gata nan kamar ta-kitse-ta-kitse in je ta narke a rana”. Saheeb ji yayi nan duniya ba wanda ya tsana irin Hajjo, da yana da iko yau duka zai yi mata ko ya daureta har sai igiya tai rara kafin ta dorawa Hasna’u tallah. “A tambayeta ko nawa ne cinikin rogon zan dinga bata kullum, amma don Allah don Annabi Kawu kada a daura mata tallan nan, fuskarta zata yi dabbare dabbare in ta sha rana ko kwaro ya cije ta, sannan basa jure zafin rana ko kankani”. Kawu yace "ai na gaya mata 'sai bayan rai na' sai dai in daina fita neman abinci in yi ta gadin Hansai har zuwa ranar da zan daina numfashi”. “Balle ma baza a yi haka ba, a kira ta muyi lissafi, duk sati sai in din ga kawo mata kudin tallan amma dole kaje harkokin ka kuma Hasna’u bazata yi mata talla ba, in ta dage wallahi Allah zan kai ta HUMAN RIGHT”. Atika ta shigo tana zumbura baki tace “Kawu nayi-nayi ta zo ta yi min banza, na gaya mata saurayin tane ya zo amma ko kallo na bata yi ba, ina jin fa ta zama kurma”. Kawu ya rasa abinda zai raruma ya maka mata sai ya dauki rediyon sa ya saita bakin Atika da ita...Saheeb yayi maza ya rike rediyon, Atika ta gudu”. “Ni dai na haifi jarraba, yara duk sun biyo halin uwar su na rashin iya magana, Hussainin dana ke dan jin dadin sa shima kwanan nan ya fara daukan halin su, dazu sai da ya gwaba min magana” ya soma matsar kwallah. Saheeb yana cewa. “Kayi hakuri Kawu addu’a zaka yi musu ba kuka ba”. Kawu ya tashi ya shiga gidan da kansa domin ya turo Hasna’u. “Hansai na turo kizo kika ki zuwa ko?” Ta sake rushewa da kuka bata ce komai ba. A wurin ta ta riga ta gama yanke alaqa da SAHEEB WAMAKKO, bata bukatar komai daga gare shi tunda yayi ZARAR BUNU..... ya haura limit din da yake kai na Yayan ta. Dama alakar tasu ta Yaya da kanwa ce, tunda kuma yanzu yace ba ita bace ai shikenan, itada shi haihata-haihata.... Masu iya magana sun ce "tsuntsun da ya ja ruwa... shi ruwa kan doka, ba zata jawowa rayuwar ta tozarci ba. Wanda ta fara gani a wurin uwar sa da kanwar sa kadai ya ishe ta misali". Shima Kawun yayi maganar duniya bata tanka masa ba, yayi lallashin ya gaji, gashi bai iya zuwa ya ce da Saheeb ta ce bazata zo ba, a karshe yace. “Ko dai gaskiyar Atika ne kin kurumce?” Ta motsa bakin ta a hankali tace “da kunne na!” Yace “to alhmdulillahi, sakarci ne abin kenan!”. Sai ya juya ya fita. A zaure ya tadda Saheeb yana safah yana marwa yana naushin hannun daman sa cikin na hagu, Hasna’u kawai yake son gani da halin da take ciki. Wannan wane irin damalmalallen gida ne wadanne irin mutane zata rayu da su haka? Abu daya ya rage masa damuwa da ya fahimci Kawu Samaila tsayayyen mutumne akan ra'ayinsa matar sa bata juya shi amma a yadda ya fahimta gabadaya ‘ya’yan basu da tarbiyya. Kawu y ace “biyo ni Sahabi”. Ya bi bayan Kawu zuwa cikin gida ta kofar shiga sassan su Hasna’u. **** HASSAN (DA GASKE WATA KUSAN TAFI WATA?) Tana kudundune cikin zanin Inna a can karshen gadon bonon ta, rabin gashin kan ta ya fito, wanda ba baki bane gabadaya, a kwana biyu kacal tayi mugun ramewa, ‘yan idanun sun kara kankancewa daga ‘light-blue’ sun koma ‘ash colour’. Ba zaton ta ba tsammani, kawai sai ganin Uncle Saheeb ta yi a gaban ta. Ya tsaya hannayen sa biyu zube cikin aljihu staring at her straight in to her eyes with so much sympathy and pity, bai zauna ba daga tsaye motsa baki yace “HASNAH!” Saukar muryar sa ke da wuya cikin kunnen ta da gangar jikin ta, sai ta ji duk wani rauni na duniya da maraicin duniya ya rufto mata….. ‘this is indeed a shoulder to lie on’, zata so ta kwanta a wannan kafadar… tayi kukan ta mai isar ta a inda ta san za’a lallashe ta a gaya mata mai dadi, amma babu dama tunda ta san ba muharramin ta ba ne ba. Kawu sai ya kasa tsayawa tare dasu ganin sai kallon juna suke bakin sun a motsi idanu fal hawaye, ya juya ya fita. Saheeb ya tsugunna a gaban gadon bonon Inna yasa gwiwoyin sa a kasa, cikin raunin murya yace “pls accept my heartfelt condolence, Allah ya jikan Innar mu da Rahma….”. Ai kamar jira take sai ta kifa kai a jikin bango, ta bude sabon shafin kuka. “Hasna’u come and cry on my shoulder…..idan kukan zai sa ki ji sanyi? Amma mafi a’ala, mafi fa’ida, mafi dacewa ba kukan bane, addu’a ce a gare ta. Hasna’u da gaske yau kwana biyu baki ci abinci ba?” Ta soma share hawaye da zanin Inna, tana sheshsheka irin ta wanda ya ci kuka ya koshi. Gashin kanta yake kallo mai kama da na tsofaffi amma sai yaji bazai taba cewa da ita tayi dying ba koda Allah ya cika masa burin sa na auren ta, zai zauna da ita (against all odds in her natural defect and abnormality) kuma zai gaya mata bakin gashin mata ba komai bane face irin nata watarana, suma duka fading zai yi, amma akwai lokacin da zai gaya mata hakan ba yanzu ba. Bagcon da yayi mata sayayya ya janyo sai ya tarar ko tabawa bata yi ba, ya dauko ‘juice’ din ‘exotic’ da madarar ‘hollandia’ ya dauko kofi cikin kwanukan dake gefe a wanke, Inna sarkin tsafta ta wanke ta kife abin ta, babu ko ledar tsakar daki a dakin sai karauni, amma ko’ina kalkal yake sannan gadon su babu shirgi sam sai wani kodadden zanin gado, sun shirya kayan sawar su su cikin kwandon roba mai murfi. Ya zuba jus din cikin kofi ya bata sannan yace cikin lallashi “akwai risho in dafa miki indomie?” ta bude idanu tana kallon sa kawai, yace “Hasna bazaki yimin magana ba?” Ta juyar da kai bata ce komai ba, mikewa yayi yana duba kayan wajen don duk wani kayan amfanin su Inna bata barin shi a waje, ilai kuwa rishon ta na nan, harda ashana a kasan shi, ya dau karamar tukunya ya zuba ruwan swan a ciki ya kunna, tun ruwan bai yi zafi ba ya zuba indomin da maggin ta, shi dai burin sa ta ci wani abu koda danye ne in dai zai shiga hanjin ta. Kan minti goma indomie ta dahu ya juye a plate ya kuma kasha rishon ya kawo mata. “Ki karba ki ci, in kin ki ki zan yi miki dura wallahi” ya aje plate din a gabanta yana kuma nade hanun riga. Ba shiri ta karba ta soma ci kamar mai cin dussa, loma uku tayi ta ture don daci yake mata a baki, Saheeb ya ce “Hasna ko sai na baki a baki ne?” Ta daga ‘light-blue eyes’ din ta ta kalle shi, sai aka yi sa’a shima ya dago yana kallon ta. Murmushi ya sakar mata, murmushin da ya kusa narka zuciya da ruhin HASNA’U, ya haifar da wani ‘chemistry’ mai karfi a tsakanin su, ya kuma debo abinci akan spoon ya nufi bakin ta da shi. Sai ta kasa wofantar da wannan kulawar a karo na biyu ta bude dan jan bakin ta ya saka mata abincin. A haka sai ga Hasna ta tashi da plate din indomie tsaf batare da ta san lokacin da ta tashi da shi ba. Ya zuba mata ruwa ta sha. Sai taji gardin ruwan hannun Saheeb ya fi na kowanne ruwa da ta taba sha a rayuwar ta. Yasa hannu a aljihun sa ya dauko galasses guda biyu a cikin akwatin su ya ce, “ga su na karbo, will you do me a favour ta wear it for you?” (Zaki yi min alfarma in saka miki?) Ya fada yana ciro kyakkyawan glass din daga gidan sa. Yace “in rana tayi zai yi duhu, in dare yayi ya yi haske, ki kula da su sosai su zama ‘companions’ din ki, barci kadai zai raba ku, sai ko wanka. Kin dai ji abinda Dr. Turaki yace in kika kula da sanya su kina girma ganin ki na kara gyaruwa”. Ya sa mata glass din, kada kiso ki ga yadda yayi wa karamar fuskar Hasna kyau, kuma da yake rana ce yayi duhu sosai sai ya boye kalar kwayar idanun ta, ta zama kamar baturiya, banda gashin girar da yake fari. “Lallai kin iya zabin gilashi, inye!” Inji Saheeb, a kokarin sa na son kawo murmushi fuskar ta. Bai yi nasarar hakan ba amma ta mike kafar ta daga tankwashetan data yi. Kafar sumul da ita fara sal kamar ta jarirai, babu kaushi ko kadan. Yace “Hasna’u yanzu har in tafi bazan ji muryar ki ba? Kina so in kasa nutsuwa gobe ma in kamo hanya in dawo?” A yadda ya marairace mata sai ya bata tausayi, bata taba ganin mutum irin sa ba, saukin kansa ya yi yawa, abinda bata sani ba ita kadai yake wa saukin kan, kuma in yana gaban ta ji yake bashi da komai, ba shi da kowa sai ita. A hankali ya ji siririyar muryar Hasna’u na fadin; “Na gode Uncle Saheeb, Na gode for all the assistance, care, and concern showed to me. My world has never meet a person like you. You are an ANGEL. I must say thank you! Amma don Allah don Annabi na roke ka daga yau kada ka sake dawowa in dai waje na zaka zo. Ina nufin alaqar mu ta kare daga yau”. Ta fada tana mai sunkuyar da kan ta kasa, wasu hawayen masu zafi na kwararowa. Saheeb ya bude baki yana kallon ta with astonishment, sannan ya girgiza kai ya ce “ko zan iya sanin hujjar ki?” “Hujjata itace our relationship has no meaning, has no direction, has no focus….” Da sauri ya katse ta da cewa “a wurin ki ba? Amma a wuri na yana da shi, haka a wurin Ubangiji yana da shi. Annabi SAW ya hore mu da mu kalli matar da zamu aura kafin a daura mana aure. Ni Saheeb kuma neman aure nake yi, kamar yadda kowa ke yi, yau din nan ba sai gobe ba zan gayawa Mamana a zo nema min auren ki”. Hasna’u ta dube shi da idanun tausayi, cikin ran ta tana fadin tausayi na ya sa Uncle Saheeb ya zare! Ko in ce yana gab da zarewa! Kamar ya san me take fadi a ranta yace “ki yi min kallon zararre da kyau, dama gobe zan je Zaria wajen aminin mahaifi na, in gaya masa ya zo shi wajen Kawu ya kawo sadaqi na. ana kamala SSCE a shafa mana fatiha”. Da fadin haka ya mike tsaye, hannayen sa cikin aljihu. Hasna’u ta bi shi da kallo da ‘light blue eyes’ din ta tana tausaya masa cikin ran ta, something is really-really fishy in his brain don mutum mai hankali bazai ce zai auri zabiya ba! Zabiya ai sai zabiya dan uwanta ba wannan sardidin lafiyayyen matashin ba, wanda ko a masu lafiya shi ajin farko ne. Tana tausaya masa don ta san ya dauko hanyar da su duka bazata bulle da su ba, ya dauko rigimar da ba zai iya ba, ya dauko fadan da yafi karfin sa….. tsakanin sa da Kawu, da tsakanin sa da Mama. Watakila har da sauran al’ummar dake zagaye da shi. Ciki har da kanwar sa ciki daya. Har ya fita bai bar sakar mata murmushi ba, murmushin da bazai taba gushewa daga zuciyar ta ba, murmushin da ta tabbatar shine na karshe da zata gani daga kyakkyawar fuskar sa don ta san tabbas in har ya fadi abinda yake niyya ga Maman nasa, to kuwa zata taka masa katoton birki ne, watakila har daga yin aiki a ‘Unity Kachako’. Fitar Saheeb ba jimawa Kawu ya shigo, daka gan shi ka ga wanda ke cikin rudani, yace “Hansai, saura wata nawa ki gama makaranta?” A hankali ta ce “uku” “daga ukun an gama ko?” “Eh an gama Kawu sai kuma shiga Jami’a” yace “akwai jami’a a Kachako ne? Ko ke ce zaki bude University of Kachako?” Tace “a’ah babu, dama mun yi da Inna Kano zani in yi” ya kama baki cikin mamaki “kije Kano fa kika ce, da wane muharramin?” Hasna’u tayi shiru, ya e “to Hansai ni ba zan takura miki ba, amma dole in miki aure yanzu, auren da hankali na zai kwanta da shi. Don haka tun kafin Sahabi ya furta neman auren ki gara in miki aure, don bazai iya neman wata alfarma a gareni in hana shi ba, har ga Allah ina son yaron nan, kuma ina miki sha’awar aure sa, domin kika aure shi kin gama samun soyayyar miji. Amma ki sani, muddin kika aure shi to fa shi kadai kika aura jinin sa da dangin sa har abada baza su so ki ba. Sannan bazaki taba yin daraja a idanun su ba, ba zasu taba son abinda kika Haifa ba, musamman in ya zo a ZABIYA, ban kuma isa in tsawatar ba in wani cikin su zai taba mutuncin ki. A bisa hakan, da wasu dalilai da dama, na yanke shawarar aurar dake ga dan uwan ki HASSAN gobe-goben nan ba sai jibi ba, kafin Sahbi ya sake dawowa da kokon alfarmar da bazan iya maida masa alkhairin sa ba, kin ga hakan ya fi dan dama-dama tunda yana dan zuwa makaranta yanzu, kuma yana dan jin Magana ta ba kamar da ba. Idan kika auri Hassan dukkan ku kuna karkashin iko na komai zai zo da sauki, sanna ‘ya’yan ki suna tare da jinin su iya wuya iya zabiya ana tare. Amma me kika gani? Don ko shi Hassan din ban gaya masa ba sai na fara neman amincewar ki tukunna. Ba zan yi miki auren dole ba, ‘yan zuqe-zuqen nan da yake yi duk dainawa zai yi da zarar nauyin aure ya hau kan sa”. Hasna’u ko motsi ta kasa. Mutuwa mai tonon asiri!” Anya Kawu da gaske yake kaunar ta yake yi ko son kan sa? Da sanin sa zai aurawa dan wiwi ita? (MARIJUANA)? Kawai don Allah ya yo ta ZABIYA ana neman yadda za’ayi da ita? Ba gara-gara Hussaini ba shi da baya shan komai kuma yana zuwa makaranta? Amma ai ya fi ta sanin akwai Hussainin ya zubar mata lalataccen don su taru su rufawa juna asiri. Ta yarda da duk abinda ya fada akan Saheeb gaskiya ne, ta yarda bazata iya zuwa jami’a ba tunda babu Inna, wannan burin ya zagwanye! Ta san da Inna na raye koda jan gindi sai ta kai ta Kano jami’a ba tareda ta ji koda darr ba kuma ba tare da ta nemi taimakon kowa ba sai aikin karfi da lafiyar ta. Wasu hawaye suka gangaro daga idanun Hasna’u. Hawayen da ta tabbatar har abada bazata daina zubar da suba har zuwa karshen rayuwar ta, idan ba har Inna ce ta dawo duniya ba. A wannan gabar da Kawu ke son jin ra’ayin ta na eh ko a’ah zata auri lalataccen dan sa Hassan bata da zabi, bata da wani hope, bata da wani sauran buri a rayuwa bayan na fatan cikawa da imani. Dama karatun karatun shine kadai burin ta, Kawu ya ce bazai taba yiwuwa ba tunda ba’a Kachako bane. Bai san cewa Annabi SAW y ace ku nemi ilmi ko da a birnin Sin ba, kuma bai iyakance mace ko namiji a wajen neman ilmi ba. Ta dubi Kawu, da rinannun idanun ta, wadanda ke cike taf da hawaye, yayi zuruuu! Yana jiran hukuncin ta…… Kawun ta mai fada da kowa har da ‘ya’yan cikin sa a kan ta, Kawun ta da baya bari a nuna mata yatsa bai karya shi ba, Kawun ta daya da ya rage mata a duniya don an ce Kakar ta ta Kabo ma ta rasu da jimawa, shi da bai kyamaci hada jinni da ita ba bai kira haihuwar ta mummunar haihuwa ba, so yake ma ta haifo Zabiyun shi ta kawo masa. Kawunta shakikin Innarta guda daya a duniya ya kyautu tace masa bazata iya auren dan sa ba don yana shan wiwi? Ai ana barin halas ko don kunya. Masu iya Magana suka ce “Naka sai naka…. sannan in ta saki Kawu da iyalin sa wa za ta kama??? Abu daya ta iya tambayar Kawu a wannan lokacin da yake zake da jin amsar bakin ta. “Kawu karatu na fa na Unity saura wata uku in gama shi?” Yace in don wannan ne da auren ki ki je ki karasa ki dawo ki tare a dakin ki. Hassan bazai hana ki ba, in ya hana zan saka kafar wando guda da shi”. Bayan wannan bata kara tambayar shi komai ba. Sai da yace. “Kin amince ko Hansai? Ki duba hujjoji na da idon basira, bana nufin son kai ko yi miki dole cikin lamarin nan sai don an ce ko me zaka yi kayi shi da tsinkaye”. Hasna’u ta ce “Kawu duk hukuncin da ka yi a kaina, daidai ne”. Tana gama fadin hakan ta rufe ido kamar mai barci, Kawu yayi ta sanya mata albarka. Ya ce gobe ta tashi da wuri tayi wanka karfe goma za’a daura aure. Yana bada baya taji cikin ta ya hautsine, da gudu ta sakko daga gadon, ta amayar da girkin SAHEEB tsaf, sannan ta samu sa’ida. Ta kwanta a dandaryar kasa tana maida numfashi a hankali, tana rokon ubangiji da ya dauki ranta kafin wayewar garin. Domin ta tabbata Hassan dan uwan ta ne amma bai dauke ta a mutum ba, balle akai ga zancen kauna ta aure, Kawu kadai ke son ta cikin gidan nan, daga Hassan har babar shi Hajjo da kannen sa babu mai kaunar ta. In comparison to SAHEEB BELLO WAMAKKO wanda ke son ta da dukkan zuciya da ruhi soyayya ta fisabilillahi daga indallahi, ‘yan Uwan shi ne kawai da Maman shi baza su so ta ba, in haka ne ‘challenges’ na auren Hassan da ‘challenges’ na auren SAHEEB duk daya ne babu banbanci, so it was da duk wani miji da zata aura. Gara ma na SAHEEB akwai soyayya da gatan miji (wanda shi ya fi komai dadi da muhimmanci ga mace) idan babu na wadanda ke zagaye da shi. Duka wannan tunanin ta na yi ne kawai ba don tayi wata hobbasa ta ceton kai a kai ba. Ta tattara komai ta mikawa sarki Allah, amma zabi ko jayayya da Kawu Samaila ba nata bane, ta bar wa Allah komai yayi duk yadda ya ga dama da rayuwar ta……… SUMAYYAH ABDULKADIR. ***** MAMA (DAGA BAKIN UWA) Tuki Saheeb yake amma hankalin sa ba ya jikin sa, a kan titin da zai mai da shi Kano bayan ya baro Hasna’u a kauyen Kachako, tunanin ta ina zai fara yake yi, yayi alkawarin zama bango abin jinginar Hasna’u. Hakan ba zai taba dorewa ba ba ta hanyar aure ba. Idan a da tausayin Hasna ya ke ji to yanzu son ta yake yi, so guda daya mai tsayawa a zuci, soyayya daga indallahi daga inda bai zata ba. Mama is such a kind of person da dosar ta da maganar da bata gamshe ta ba sai mutum ya shirya. Amma kuma dole itan zai fara dosa, in ya so in ta ki, sai ya nemi Barr. Dalha wato aminin Alhaji Wamakko dake zaune a garin Zaria. Ya soma shirya duk kalaman da zai yi amfani dasu wajen lallashin Mama, yana yi yana rehearsal don kalaman su zauna sosai a kwakwalwar sa. Hasna’u will become his wife no matter what…. Mother of his children, koda kuwa su duka zasu zamo albino ko rabi su zamo albino, he will take care of them to the rest of his life by becoming a DERMATOLOGIST. Amma dole ya nemi albarka da yardar Uwa, Mama ba daya take da sauran iyaye ba ta fannin kula da su da nuna musu soyayya she is super excellent, and also a sacrificing mother, duk wahalar siyasa da fadi-tashin da take a rayuwa don ta nema musu farin ciki ne da rayuwa mai kyau shi da kanwar sa. Amma kuma ya jima baya son halin Mama, domin kwata-kwata ta hana su alaqa da ‘yan uwan Alhaji da ke Wamakko, ba don komi ba sai don su din talakawa ne, gata dai ‘yar siyasa, wadanda kowa ya san talaka shine tinkahon su, amma a wurin Mama talaka ba komai bane face hanyar samun shugabanci, tsakanin sa da ita amfanin sa lokacin zabe ne kawai, ta yi amfani da shi ita da ‘ya’yan ta su ji dadi, shi kuwa ya cigaba da shan ranar sa. Tunda uban su ya rasu bata kara barin su sun je Wamakko ba, sai shi ne da yayi hankali bayan gama jami’a yake zuwa jefi-jefi a boye yana taimaka musu yana musu ihsani. Ta yaya zai yi ta karbi Hasna’u shine abinda ke damun sa, bayan ya san ta dade da yi masa mata wadda ta ke ganin itace daidai da shi, Fa’izah ce diyar aminiyar ta Senator Ladi, duk wani aure sun fi so su yi a junan su ‘yan siyasa, ko ba jam’iyyar su daya ba don duk inda ta fada ya zamo sha. Shi kwatakwata tarbiyyar yarinyar bata yi masa ba domin kuwa rainon Lagos ce, ita kan ta Mama uban Fa’izah ya fi ta kudi domin har deputy Gov. Yayi can da jimawa na jihar su Taraba. Amman kuma duk inda ake neman kyau to akwai shi a Faiza tunda babanta dan Taraba ne Maman ta ce ‘yar Kano. Ya karbi Faiza ne a kan cewa bashi da zabi domin kuwa a lokacin yana final year yana karatu a jami’a, a cewar shi a lokacin shi bai da idon kallon mata he’s a goal oriented. Maman ta zabo duk wacce ta yi mata tunda ta takura da y agama NYSC zai yi aure. Yanzu kuwa ba idon shi ne ya kyallo mace ba, zuciyar shi ce da ruhin sa. Ba kuma ya jin akwai abinda zai sa ya fasa auren Hasna’u, idan a da tausayi ne tsakanin su yanzu ya tabbata soyayya ce. Ko Hasna bata son sa, shi yana son ta zai aure ta a haka, in ya so a hankali ya koya mata soyayyar. Babu abinda zai dorar da dangantakar su ya cigaba da tallafawa rayuwar ta idan ba aure ba. Bai taba jin ma yana son yayi aure ba sai yanzu, ji yake kamar yayi fiffike ya gan shi gaban Mama su yi duk wacce zasu yi. Bai iso gida ba sai yamma lis, cikin sa’a da ‘Rolls-Royce’ din Mama ya fara cin karo a ma’adanin ta tabbacin ta dawo gari. Da yayi parkin sai da ya tsaya ya karanta addu’a, addu’ar neman rinjaye. Ya kara rehearsal kalaman lallashin Mama. Sannan ya fito ya shiga cikin gidan. A falo ya tadda su ita da Nusaibah suna kallon tashar MBC3. Mama da glass din ta a idon ta, kullum ya dube ta sai yayi tazbihi a ransa sabida kyawun ta da kuruciyar ta da har yanzu suke tattare da ita, kuma ta ki aure don kada a kira su agola. Shi kan da zata yi auren sai ya fi masa kwanciyar hankali sabida mazan dake karakaina a gidan su da sunan siyasa suna damun sa. Ya kudurce sai ya raba Mama da siyasar nan in har don su take yi, da zarar ya gama karatun sa ya samu aiki mai kyau, in Nusaiba ce ai ta gama sakandire ta tsaida wani cikin masu zuwa wajen ta tayi aure, itama Maman ta yi, shima yayi, a rufe harkar siyasa, in ta kama a rufe gidan Wamakko ne bakidaya a rufe kowa yaje ya tara nasa iyalin. Yayi bautar Allah. Da wannan tunanin ya shiga gida. Yana shigowa Nusaiba ta sulale ta bar wurin don ta san ta gama hada masa bom din da zai tashi da shi yanzun nan. Yayi sallama Mama ta ki amsawa. Ta dai juyo ta dube shi sama da kasa ta gan shi a gajiye kuma da alama doguwar tafiya yayi. Shaddar jikin sa ta yi sqeezing, ta kara gasgata abinda Nusy ta fada mata cewa budurwa yayi a kauye kuma Zabiya, har gidan ya kawo ta tana Abuja, in zata iya tunawa itace Zabiyar da ya baiwa abinci a Unity Kachako ranar visiting. Lokacin da Nusy take gaya mata Mama ta kusa yin sabo bayan ashariyar data dankara, don haka yanzu da ya shigo ya zauna a gefen ta da sauri ta matsa gefe. A kyamace (disgustingly) ta ce. “Ka je ka yi wanka da soso da sabulu da Dettol, sannan ka wanke hannu da sanitizer, sannan na amince ka zo inda nake” kallon rashin fahimta ya yiwa Mama, yau shi ake cewa ya je yayi wanka tamkar wani karamin yaro?” Mama ta buga masa tsawar data kara ruda shi, “kaje ka yi wanka nace Saheeb! Sannan ka zo ka gaya min daga ina kake?” Babu alamun wasa cikin sautin Mama, don haka ya mike zuwa bangaren sa, yana fadi a ransa Nusy ta jika masa aiki, kuma da sannu zai sa kafar wando daya da ita, sai ta gwammmace bata san shi ba. Yayi wanka ya sanya farar jallabiyya ta zaman gida ya fesa turare sannan ya dawo falon, Mama na nan zaune inda ya bar ta har zuwa lokacin, sai cika take tana neman wanda zata batse da shi. Saheeb ya zo ya zauna a kujerar dake fuskantar ta, politely yace. “Na yi yadda kika ce Mama” “Daga ina kake?|” Ta tambaya da sauri tana zaro manyan sparkling idanun ta irin nasa. Kai tsaye babu ko darr, yace “Kachako” “Ba an yi hutu ba?” Saheeb yayi shiru. Mama ta yi kwafa tace. “Sannu da dawowa daga wajen Zabiya ‘yar kauyen Kachako, Saheeb ashe baka da hankali? Ashe karatun ka na banza ne? Tunda kuwa bai gaya maka hereditary and genetic ba? Kafin ma in yi zancen Fa’iza kenan da kasa aka kaiwa kudin aure. Yo ko babu Fa’iza ni Muneera meye hadi na da Albino? Kai ni tunda nake ma na taba jin wani mai lafiya ya aure su? Haihuwa mai jaye-jaye, yau haihuwa zata janyomin bala’I cikin gida da cikin jinina, to ka sani Saheeb over my dead body!” Tunda ta fara Saheeb kan sa ke sunkuye, har ta dasa aya, ta kuma nuna shi da dan yatsa “nayi waya yanzun nan da Perm.sec na NYSC, Kano, an canza maka PPA (Place of Primary Assignment) zuwa asibitin Nassarawa Kano. Dama ai tun farko sai da nace bazaka je kauyen nan ba kace in na bari ba komai taimako ne, kai ga ka waliyyi sarkin taimako, daga taimako ka kashe ni ina tsaye, a haifomin albino cikin gidan Wamakko, idan na kara jin ka je garin Kachako ma ba gidan su Zabiya ba ALLAH YA ISA BAN YAFE MAKA BA!” SAHEEB. Ya dago idanun sa cike da hawaye yana duban Mama. “|Mama kada ki yi min haka, kada ki yanke hukuncin da zaki zo kiyi nadama, ba’a yiwa Da baki, idan ana so ya bar abu. Mama kiyi min alfarma ki saurari kalaman baki na, ki bar ni nayi wanna JIHADIn nikuma na amince ki aura min duk wadda kikeso su zama su biyu. Don Allah Mama ki taimake mu ni da Hasna’u. Mama daga ni har Hasna marayu ne amanar Allah a hannun ki. In ta haifi zabiyan ni ina so ko bazaku rike min ba, in yaso wadda kika aura min ta Haifa miki masu lafiya”. Maama ta lailayo ashar ta yarfa masa (abinda bata taba yi masa ba) tace “ko kai ne Romeo don soyayyah, ko kai ne kafi kowa tausayi da taimako bazaka auri yarinyar nan ba, na fada na kara fada over my dead body zaka auri Zabiya ABUBAKAR (Karo na farko data ambaci sunan sa na hakika tun daga lokacin da ta haife shi ta yi masa laqabi da Saheeb. Tana gama fadin haka ta mike tayi daki. Nusaiba dake make bayan labule tayi maza ta futo zata shige dakin ta sai ya gan ta, da mugun sauri ya bi bayan ta, tana shiga yana shiga ya maida kofa ya kulle, yasa key din dake jiki ya murda ya cire ya zura shi a aljihun wandon sa. A kasan jallabiyar da yasa dogon wandon jeans ne baki, sai ya fara zaro belt din shi jikin sa har rawa yake ya soma dukan Nusaiba, ya riga ya tsara duk abinda zai gayawa Mama ta amince masa ba tareda bacin rai da tashin hankali ba, Nusaiba ta lalata komai da tsugudidin ta bayan sai da ya gargadeta kan ta fita batun sa da Zabiya. Nusaiba ta soma ihu tana kiran Mama, amma kofar dakin da windows duka masu karfi ne Mama bata ji ta ba, sai da yayi mata lilis yaga tana neman shidewa sannan ya yarda belt din ya bude kofar zai fita, (feeling somehow relieved) ya rage bakin-cikin sa. Suka ci karo shi da Mama wadda sai a lokacin ta ji kukan Nusaibah ta shiga dakin da gudu shi kuma ya fice da sauri, ya zari mota ya bar gidan da wani mahaukacin gudu, saura kadan ya take maigadinsu. Gudu yake shararawa na fitar hankali akan titin zuwa Zaria, ya manta ko karfe nawa ne lokacin, duhu ya riga shigo sabida hankalin sa ba ya jikin sa, gudun da yake yi sai da motocin gaban sa da bayan sa suka rika aiko mai da fitilun zagi. Burin sa ya isa Zaria wajen aminin mahaifin sa, ya san shi kadai zai iya tankwara masa Mama ta bar shi ya auri HASNA’U. Hasna’un da bata shigo rayuwar sa da sauki ba ta shigo ne da karfin gaske, ta dusar hasken sauran mata daga idanun sa. Daga uwar sa sai ita a wadanda yake so yanzu, yake burin kasancewa da su, baya jin in duk duniya zata taru a kan sa zai fasa auren ta….. Iya abinda zai iya tunawa kenan, sai bude ido yayi ya gan shi a ambulance ana dawo da shi Kano. Mummunan hadarin ya faru a daidai garin Kura ta jihar Kano tsakanin miotar sa da wata karamar peogeot504 da ya bugawa. Allah ya so kusa da jami’an tsaro ne aka kira ambulance nan take aka kwashe su jina-jina zuwa asibitin Malam Aminu Kano wanda shi ya fi kusa akan na koyarwa na Zaria. LABARIN HASNA’U ‘YAR NAJERIYA YANZU ZAMU FARA SHI. BA MU TABO KOMAI BA HAKA BAMU FARA KOMAI BA. HASNA’U HAS A LONG JOURNEY AHEAD KAFIN CIKAR BURIN TA NA ZAMA CIKAKKAR MUTUM KAMAR KOWANNE DAN ADAM DESPITE HER ABNORMARLITY\DISABILITY. AL’UMMAR NAJERIYA NA BUKATAR ‘COUNSELLING AND ENLIGHTENMENT’ A KAN ‘DISABILITY AND INCLUSION’ WANDA SAURAN KASASHEN DA SUKA CIGABA TUNI SUN YI ADOPTING MUHIMMANCIN NAKASASSU A CIKIN AL’UMMAH A TSARIN KUNDIN TSARIN MULKIN SU DA DOKOKIN SU. BA’A ISA A TABA MUTUNCI DA LAFIYAR MAI NAKASA BA. NI SUMAYYAH ABDULKADIR (TAKORI) A YAU ZAN YI WA AL’UMMAR NAJERIYA WANNAN ENLIGHTENMENT DA HARSHEN HAUSA IN FORM OF STORY WRITING, DON A SAMU FAHIMTA KYAKKYAWA TSAKANIN NAKASASSU DA MASU LAFIYA A HULDA TA AURATAYYA. KOWA YA DAINA KALLON KOWA DA MUGUN IDO (MASU LAFIYA NA KALLON NAKASASSU BA MUTANE BA, NAKASASSU NA KALLON MASU LAFIYA A MARASA TAUSAYI DA RASHIN ADALCI). TA YADDA AURE YANZU YA KOMA SAI TSAKANIN NAKASASHSHE DA NAKASASHSHE DAN UWAN SA. DA GASKE ZABIYA MA MUTUM NE KUMA ZABIYA ZAI IYA AUREN MAI LAFIYA KAMAR KOWA? IN ZAI IYA WHAT ARE THE OBSTACLES? WHAT ARE THE HINDRANCES? WHAT ARE THE CHALLENGES? KUMA WHAT ARE THE POSSIBLE RECOMMENDATIONS? MAMA KO SAHEEB WANENE KE DA NASARA A KAN KUDIRIN SA? DA GASKE KARATUN HASNA’U YA KARE A UNITY? HASSAN FA? ZAI YARDA YA AURI ZABIYAR SHI KAMAR YADDA KAWU KE SO? DA GASKE WATA KUSAN TA FI WATA??? NI DAI TAKORI NA SAN SAU-TARI BARE ZAI IYA SADAUKARWAR DA DAN UWA NA JINI BA ZAI YI MAKA BA. AMMA ANYA HASNA’U ZATA IYA TSALLAKE AUREN HASSAN??? YANZU NE ZAMU SHIGA LABARIN HASNA ‘YAR NAJERIYA GABA-GADI. OUR THEME IS “GREEN WHITE GREEN, ONE NATION BOUND TOGETHER….. NO DISCRIMINATION ON DISABILITY”. N500 3094856450 SUMAYYAH KABARA FIRST BANK FOR COMPLETE STORY SHAIDAR BIYA 07030137970 An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT