An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels [12:17PM, 02/02/2017] 🙆🏼‍♂@lh@ji🙆🏼‍♂: [1/6, 9:06 AM] A A Dboy: *YAR TALLAH NEW EPISODE* *CHAPTER 1* Tafe tAke tana rusa kuka wiwi,,,,,wiwi Duk ta hada miyau majina da hawaye ta dame fuska gaba daya Rungume take da tiren tallan tata wanda ba komai a cikinsa sai ihu take kwararawa tana kiran wayyo kudina wayyo ni kudina Mutane sai kallonta sukeyi masu tausayi daga cikinsu su kirata suji abinda ya faru su lallasheta ta tafi A haka taita saqawa ta lunguna harta iso layin gidansu Tunda ta iso layin rabi,u wanda bai wuce dan kimanin shekara goma sha huduba kejiyo sautin kukanta yana duqe yana faman wanke wanke Yai niyyar miqewa karaf sukai ido hudu da inna laure Ta watsa masa wani irin kallo simi simi ya koma yaci gaba da wanke wanken Tace munafuki dan iska wlh ka sake tashi baka gama wanke wankennaN ba saina karya maka qafafu Ta qara jan tsaki ta hankade labule ta shige Daki Rabi,u yai saurin tsame hannunsa daga wanke wanken ya kwasa yai waje da gudu A bakin kofar zauren sukai kicibus yace waya tabakine saude? Ta qara fashewa da wani kukan wanda yafi nada sauti Rabiu ya qara janta jikinsa kiyi haquri saude fadamin meke faruwa? Tadan sassauta da kukan tace kudina yaya kudin tallah na wani ya kwaceminsu Rabiu ya dafe kirji ido waje yace garin yaya saude? Kinsan halin inna laure kuma dukanki zatayi Ta qara fashewa da kuka wayyo yaya dan allah ka roqeta karta dakeni Ya danyi jimm kiyi haquri saude babu yaddah zan iya kixo muje kawai ta dakekin Ta qanqameshi wayyo yaya wlh yankani zatayi Idanunsa suka kawo kwallah ya cije yace zo muje saude insha allahu bazata dokekiba kinji? Kai kawai ta daga masa tana share hawaye yaja hannunta suka shiga ciki Tsaye take a kofar daki da alamun ta cika ta tumbatsa jira kawai take a tabata ta bashe Saude ta qara fashewa da kuka wayyo allah na wlh yaya dukana zatayi Inna laure ta zaburo tayo kansu In dokeki don ubanki laifin me kikayi? Hala kin dawomin da sauran raguwar alalen ne ko?ta fada lokacin data shaqo wuyanta Ina kudun suke in gani? Ta qara fashewa da kuka tace wani ya kwace kutumar ubannan wani ya kwace? Aiko yarinya yau zaki daku a gidannan don wlh saina lahira ya fikijin dadi. Ta jata kiyyyyyyyy..... A qasa har zuwa bakin rijiya ta janyo igiyar guga zaki fadamin ina kudina suke ko saina miki dukan mutuwa da igiyar gugannan? Cikin kuka tace wlh wani ne ya kwace ya ruga tace lallai yarinya aiko jikinki zai gaya miki ni zaki kawowa zancen banza zancen wofi Tasa qafarta ta tureta ta fadi ta dinga lafta mata igiyar gugar kamar badan mutum take duka ba Hankalin rabiu ya tashi yaddah yaga qanuwar tashi keyi gashi tasa qafa ta take mata ruwan ciki. Wani irin kuka ya kwace masa ya duqa a wurin yana bata haquri Inna laure tace au har kanada bakin magana munafiki xonan daman ai jiranka nakeyi ta shaqoshi ta hadesu guri guda taci gaba da jibga tamkar zautacciya Hankali tashe inna mai dan wake ta zagayo gidan ko lullubi babu a tare da ita Kai jama,a lafiya maike faruwane a gidannan? Inna laure ta tsaya da dukan tana huci. Barni da yan iskan yarannan mai danwake nema suke su samin hawan jini. Niqi niqi ina fama dasu inkai gwauro inkai mari wai dondai a samu a rufama kai asiri amman yan iskan yaran basu gani kawai an mutu an barni da jaraba yanxu ace kamar saude wai har tasan taje tallah ta boye kudin wai tace wani ya kwace sbd mugun hali irinna wannan munafukin annamimin dake koya mata Inna mai danwake tace eh kam gaskia baku kyautawa kankuba. Yanxu ku harkunfi son aita jibgarku irin haka idan kun boye kudin kuci me dasu fisabilillahi Tadan numfasa tana kallonsu kafin ta qara zaro ido a,a laure yaya nake ganin yarcan kamar bata motsine"" Ta qara matsawa tana tattabata ta dago da sauri hankali tashe tace wlh laure bata motsi. Tace kai haba mai dan wake da gaske kike? Inna mai danwake ta daga hannun nata ta saki taga ya tafi ragwaf alamar ba rai Inna laure ta kwasa da gudu tana gyara daurin zani fadi take iya karfinta na shiga uku ni laure Dis is just d begining [1/6, 9:06 AM] A A Dboy: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚 [1/7, 5:48 PM] A A Dboy: *YAR TALLA* *CHAPTER TWO 2* Inna laure ta kwasa a juge tana fadin na shiga uku ta isa bakin randa ta ciko tasa da ruwa taxo ta sheqa mata gaba gaba daya yarinyar ta firgita ta tashi tana fadar wayyo inna kiyi haquri mai dan wake ta riqeta ke yi shiru da allah aita kyaleki Inna laure ta sauke wani nannauyen numfashi ta shiga zare na mujiya Mai dan wake ta miqe tana fadin ni na tafi amman dan allah laure ki dinga kula kisan irin dukan da zaki dinga musu don karkije ki daure kanki da kanki Inna laure ta sake jan kwaron numfashi kafin tace insha allahu zan kiyaye mai dan wake ta fice abinta Laure ta juya ta shige dakinta ta barsu a nan Saude ta rarrafa ta nufi dan uwan nata Wanda ke zaune ya hada kai da gwiwa yanata faman kuka Saude ta raba jikinsa ta kwanta ya qara janta a jikinsa sosai Bata jima da kwanciyaba barci ya dauketa sai faman jan ajiyar zuciya take Akai akai Malam bala yayi sallama ya shigo gidan nasa hannunsa saqale dana iklima yarinyar da bazata wuce yar shekara goma sha daya ba Qanwar saude ce don ita yanxu tana shekara sha biyu ne a duniya Malam bala ya shigo tsakar gidan tare da miqama iklima baqar ledar dake hannunsa ta karba ta shige dakin mahaifiyarta tana tsallen murna Malam bala ya kalli rabiu fuskarsa ba yabo ba fallasa yace bakin munafiki kallon uwar me kakemin? Me mugun halin tsiya hala wani abun kukai aka dakeku ko? Inna laure ta hankado labule ta fito kamar an bankadota ai daman jiranka nake malam wallahi yau saika biyani kudina in dorama yarinyarnan tallah ta boye kudin wai tace an kwace Na rantse da allah ban daukar asara Malam bala yace ai daman tunda na gansu zazzaune anan nasan wata ta'asar sukayi Yan iskan yara masu tsinannan hali wanda sukai gadon Halin tsiya niko yarannan dada inda zan kai Su wallahi dana kaisu na huta da bala,in su Tace ahto nidai kudinane sai an biyani Babu mai doramin asara alalata ta murtala biyuce da goma Malam bala yace toya zanyi ai dole na biyaki tunda allah ya hadani da jarababbun yaya Kiyi haquri idan na dawo daga kasuwa gobe saina biyaki miqomin buta nayi alwala Laure taja kwafa ta juya ta koma dakinta ta dauko masa butan ya nufi bayan gida Ta watsama rabiu harara sannan ta wuce dakinta ta samu iklima ta zazzage baqar ledar sai diban kilishinta takeyi Ta miqa hannu zata dauka yar tasa kuka tana tirje tirjen qafafuwa inna laure tayi saurin ajiyewa Ga abinkinan sarkin rigima. Ai nasandai duk cinki baki iya cinye wannan kilishin Yarinyar ta turo baki irin na shaqwababbun yaya taci gaba tacin abinta Duhun magaribane ya fara ketowa sauro suka fara duduma a jikin rabiu ya lallaba ya kwantar da saude saman siminti Ya lallaba ya nufi dan akurkin dakinsu ya shinfida musu yar yagalgalallan tabarman kaba irin mai cin jikinnan Sannan ya dawo ya lallaba ya dauketa da qar Ya kaita dakin ya kwantar da ita ita kadai ta mamaye tabarman don haka shi saman simintin dakin ya kwanta babu ko filo balle abun rufa Ga duhun dakin. Ya runtse idanunsa dukda yanada yakinin yunwace ke kwankwasarsa bazata barshi yayi barci ba Tunanin mahaifiyarsu ya fado masa kamar yaddah kullun yakeyi kafin ya kwanta Wasu hawaye suka cika masa idanu masu zafi tabbas yasan wahalar da sukesha somon tabice Akan wanda mahaifiyarsu tasha a gurin mahaifinsu Nasiharta gareshi itace ta dawo masa tamkar yanxu take masa su tace Rabiu don allah don annabi ko bayan raina. Ka kula da rayuwar qanwarka karkabar rayuwarta ta gurbata a duk halin da kuka tsinci kanku a ciki kaga ita mace ce dole tana buqatar taimakon wani wanda zai jibanci lamarinta Nasan kaima kana buqatar taimako amman a duk yanda rayuwa taxo rabiu yinta ake Nasan kodani ko bani dole ku rayu bakuda mataimaki sai allah. Rabiu kuyitayimin addu,a in rayu kodan saboda ku. Nima inason in rayu sbd ku Baisan sanda kuka ya kwace masa ba saida yaji saude jikinsa tana jijjigashi. Tace yaya kuka kake? Yayi saurin hadiye kukan tare da goge hawayensa Ya lalubo hannunta ya riqe kafin yace ba kuka nakeba dariyace nake na tadaki ko? Tace a,a yaya yinwa nakeji cikina sai cixona yakeyi tun safe banci komaiba na tafi tallah har yanxu Ya salam ya fada a fili sbd rashin sanin abinyi Saude ta kwantar da kanta a kan cinyarshi tace kaji cikina sai kuka yake ko yaya? Bai tanka mataba ta qara girgizashi cikin muryar kuka tace yaya abinci zanci Rabiu ya kwantar da murya yace dakinyi haquri kin kwanta kinga da safe ba saiki karya ba Tace wlh bazan iya barciba yace to lallaba ki kwanta ina xuwa Ta zame daga jikin nasa sai shi kuma ya miqe ya fita Duk suna kwakkwance a tsakar gida cikin gidan sauro sbd lokacin zafine Sai radio ce keta faman babatunta a banza Rabiu ya lallaba sadab sadab ya isa har inda suke ya dauko langar fura ya lallabo ya shigo Dakin ya zauna yana fadin tashi saude ga fura na samo miki kisha Ta tashi da hanzarinta ya lalubo bakinta ya kafa mata langar furar tasha iya shanta sannan shima yasha kadan ya rage sauran ya lallaba ya tafi don mayarwa Yana qoqarin ajewa kenan iklima ta farka tana fadin laure zansha fura Rabiu yai saurin durkusawa a wurin jikinsa nata faman bari Inna laure ta tashi tana haska fitila da niyyar dauko langar furar Taga mutum a durkushe wuri guda Ta fasa wani uban ihu wayyo allah malam baraw barawo Malam ya tashi a firgice ya rarimo adda yana ina yana ina ? Kafin ya fito daga ciikin gidan sauron rabiu ya kwasa a guje yayi dakinsu yana famar rawar jiki Malam ya fito yana ina barawon yake laure? Tana rawar murya tace nan nan na ganshi duqe wlh Malam bala yaja tsaki to idan nan kika ganshi yana ina ? A,a ka. Haska mana ya dauko touc light ya tafi yana haskawa har zuwa zaure ya dawo yana fadin kedinnan Wallahi kinada matsala. Yanxu haka inuwa wani tsuntsun kika gani kinxo kin rikita mutane da wani barawo Laure tace malam nifa mutun na gani anan duqe Yace to idan da mutum kika gani da ban ganshiba ko laya yayi ya bata? Don allah ki koma ki kwanta kinji Laure tace niko malam wlh bazan iya rintsawa ba don da idona naga mutum nan tsugunne Malam bala ya shige gidan sauransa yana fadin ai saikiyita zama ke kadai Sai a lokacin hankalin rabiu ya kwanta ya saki wata ajiyar zuciya ya lallaba ya kwanta abinsa Bai jima da kwanciya ba bacci barawo ya sacesa Qarshe shida na safe laure ta hankado kofar dakin nasu ta gansu sai sharar barcinsu kawai sukeyi wani takaici ya kamata ta juya ta debo ruwa cikin kwanon sha ta daga labulen ta sheqa musu a firgice duk suka tashi sukai wuqi wuqi kamar ya,yan zakaru Inna laure ta taba baki cikin masifa tace Hmmmmm Ya labarin [1/7, 5:49 PM] A A Dboy: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚 [12:17PM, 02/02/2017] 🙆🏼‍♂@lh@ji🙆🏼‍♂: [1/8, 4:40 PM] I love my mum: *YAR TALLA* *CHAPTER 3* Inna laure ta tabe baki cikin masifa tace nan har lokacin barcin safe gareku? Sannunku yayan hutu to saiku tashi Kai kaje ka jido mana ruwa ke kuma kije ki share mana gida ki tafi kai markadan waina Ta saki labulan ta juya tai gaba Babu wanda yace komai cikinsu rabiu yadau jarka ita kuma tadau robar markaden ta fice babu alwala bare wanke ido Rabiu ya jido ruwa yafi jarka goma Saida ya ciccika komai na gidan sannan ya fara gyaran gidan Saude ta dawo daga markaden tana hada wuta iklima ta fito riqe da kofin shayi da qaton biredi a hannunta Saude tai saurin tashi daga hura wutar Da take ta kalli iklima tana miqa mata hannu sanmin zo indan gutsira kadan kinji? Rabiu yai saurin kwAbarta ke da,ala kyale mata abinta Saude ta bata fuska nidai don allah zanci Yace toki bari idan na samu kudi zan siyo miki Ta qara bata fuska nidai zanci Kullum saikace zaka samu kudi kuma ba samu kakeba Rabiu yadan kura mata ido kafin yace insha allahu yanxu zan samu kinji? Kai kawai ta daga masa yana juyawa ta miqama yarinyar hannu iklima tace ban badawa Ta juya ta shige dakin nasu tana fadin laure wai kinji wai in san mata biredin ni kuma nace ban badawa Laure ta hankado daki tana fadin au biredin yar tawa kike sama ido Wato ta kawo miki keme cikin ci ki cinye ita kuma ta fadi ta mutu kenan ko? Ta shaqo wuyan rigarta tana fadin dan ubanki kin sabacin irin wannan ne ? Ko sAlon kici kiyita zawo yar banza kawai wuce ki bama mutane wuri ta hankadeta saidata fadi Ta zuya ta kalli rabiu kai kuma zakaci gaba da aikin gabankane ko kuwa?ko zaka rama matane? Bai tanka mataba ya duqar da kansa yaci gaba da sharar da yake Ita kuma taja kujera ta zauna taci gaba da hada kullun wainarta Malam ya kwalama rabiu kira. Ya ajiye tsintsiyar ya tafi Ya watsa masa kallon banza kafin yace. Ungo ka bata munafuki wanda yai gadon mugun hali Rabiu ya amsa jiki na rawa ya fice Dan guntun biredi ne wanda bazai wuce gutsira biyu ba. Sai dan ruwan shayinda ba ko madara Rabiu ya miqa mata ta karba cikin rawar jiki Ta tura biredin duk a baki tana tauna da kyar sbd yaddah ya cika mata baki Rabiu ya kalleta yace kisha a hankali kar kiyi amai bata kulashiba ta Ta kafa kai ta shanye ruwan shayin tas tana lashe kofin Inna laure ta kafa mata dundu wanda yasata amayo duk abinda taci yayo waje cikin takaici tace shegiyar yarinya mai kama da mayyah maqerin kofin zaki tando duk wanda kikasha bai isheki ba? Munafuka tashi kibar wurin kona haureki Ta saka kafa ta tunkudeta Saude ta kwasa da gudu ta nufi dakinsu tana kuka mai sauti Rabiu ya rakata da kallo inna laure ta daka masa tsawa zakaci gabane kokuwa binta zakayi Dan iska mai kama da igiyar shanya Rabiu ya durkusa. Ya soma kwashe aman sautin kukan nata na tsinkulansa a kirji Laure ta gama tuyar wainar ta kukkulla a farar leda naira. Biyar biyar ta zuba mata a cikin bokiti ta dauki ta goma ta miqama rabiu sannan ta kwalawa saude kira Ta fito tana matsar hawaye laure taja tsaki au kukan kike har yanxu kenan? Baki bugu bane shiyasa tashi ki dauka gatanan ta murtala huduce kiyi maza ki dawo kinsan alala nanan tana jiranki Saude ta durkusa ta dauki bokitin tana fadin ina tawa? Inna laure tace eh lallai ai dadin sai yayi miki yawa kisha shayi kici waina ai dadin sai yayi miki yawa yar gidan uban waye ke a garinnan? Batace komaiba ta lallaba ta wuce rabiu dake kusa da ita ya kamo hannunta ya damqa mata nashi wainar ta fice tana murna Inna laure taja tsaki tace matsalarkace nidai ko suma zakadingayi sbd yinwa wlh tallah saika gamamin duk ayyukana dondai na rigada na fita haqqinka Zakara kawai mai neman suna ka bada kwaya kaci tsakuwa Bai tanka mataba yaci gaba da aikin nasa Yana gamawa inna laure ta tattaro kayan iklima masu himilin yawa ta watsomasa ta wurgo masa kullin omo maza ka sabe mata kayannan Rabiu ya durkusa yana tattare kayan bayansa na faman cijewa ya nufi bakin rijiya ya soma wankin Malam bala ya fito daga dakin hannunsa riqe da wani dan takurerren buhu na zuwa kasuwa harya wuCe yadan dawo kadan yace kai rabiu idan ka gama wankin ka shiga daki ka tattaro nawa ya wurgo masa naira hamsin ga wannan nan kasai omo Kuma banason wankin banza don wallahi na dawo naga basu fitaba komin dare saika sake wankesu kanajina ko? Ya karba da hannu biyu gamida daga kai alamar eh Saidaya kammala na iklimar gaba daya sannan yaje ya siyo omon talatin garin goma sugar goma Yaxo ya jiqa saidaya kumbura sannan yasa suga ya fara sha Baiyi cokali biyuba ya tsaya gamida kafama kofin garin idonsa ya cikoda hawaye Wata rayuwa can ya tuno lokacin da mahaifiyarsu ke jiqa musu gari ta tasasu gaba shi da saude susha. Ita kuma ta zauna a gefe tana kallonsu Ko cokali daya ba zatayiba duk kuwa da yinwar da zata tashi da ita ta wuni da ita Tausayin mahaifiyar tasu ya dirsar masa ya tuno yar uwarsa saude yanxu haka yasan da yinwar a cikinta Yaja numfashi sannan yaci gaba dashan garin Laure ta giftashi kamar zata wuce don taka me yakeyi ganin garin rogone yasa ta wuceshi kawai ba tare data tankashiba Shima kuma bai tankataba yasha garinsa ya rage sannan ya tashi ya tattaro kayan mahaifin nasa yaci gaba Karfe daya na rana saude ta dawo daga tallar wainar tana aje bokitin laure ta miqa mata tiren alale idon yar ya ciko da hawaye wahala ya isheta Ga wahalar yawo ga azababbiyar rana ga uwa uba yunwa ita kenan tallah ba dare ba rana Har yaran unguwa sun nada mata suna da YAR TALLA ina kika fito tallah ina zaki tallah ina kika dawo tallah Saude ta daura tiren saman kai wasu hawaye suka gangaro kuncinta laure ta tafa hannuwa na shiga uku Muhammadu dan Abdullahi mezan gani ni laure ? Tallar ce bakyason zuwa to dawo ki ajiye ki zauna ki huta yar hutu zoki ajiyemin tunda baki zuwa Saude ta wuce tana faman sharbar hawaye laure tace uhm hum yarinya kenan ai dama kin adana hawayenki don tallah yanxu kika fara alalata ta murtala hudu ce da goma ki dauki ta gomar kuma wallahi ragin sule idan kikayi a jikinki zan fanshe sannan ko kanxo bance ki dawomin dashiba [1/8, 4:41 PM] I love my mum: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚 [1/8, 4:42 PM] I love my mum: *YAR TALLA* *CHAPTER 4* Tace kuma wlh ragin sule kikayi a jikinki zan fanshe sannan ban yarda da ki dawomin da ko kanxo ba anan muka tasaya Saude dai bata kulataba ta wuce tana sharbar kwallah Rabiu dake wanki ya tsame hannunsa daga cikin ruwan wankin ya dauko kofin garin ya bita da gudu Ya jawo hannunta ya kaita kan dakalin wani kofar gida ya zaunar da ita gamida sauke tiren tallar a gefe ya zuba mata idanuwansa Kukan me kike? Tallar ce bakyason zuwa? Saude ta girgiza kai alamar a,a tana share hawaye da bayan hannunta Rabiu yace idan ba tallar bace bakyason zuwaba to menene? Taja majina tanata faman sheshsheqa kafin tace na gaji yaya kafata ciwo take gashi banida takalmi ga zafin rana fasona sai jini yake famanyi Wani irin abu ya tsikari zuciyar. Rabiu ya tsirama kafar ido Wasu hawaye suka cika a idanuwansa gashi bashi da ikon iya taimaka mata Don shi kansa kafar tashi babu takalmi. Tabbas da tausayawa qaramar yarinya kamar saude tayi tafiya babu takalmi Yaddah ake tsala rana yau ga uwa uba kafar duk ta tsatstsage da faso Rabiu yasa yatsa ya goge kwallar data tarar masa muryarsa a sanyaye yace Kiyi haquri kije insha allahu zan samar miki takalmin da zaki dinga sakawa dakin dawo kinji? Ta daga masa kai ya miqa mata kofin garin ta karba ta shanye ta miqa masa kofin Ya amsa ya karbi tiren ya dora mata ta tafi Yana tsaye yana kallonta harta bace Sannan ya juya ya koma gida Laure ta watsa masa harara tace ni naci uwar zariyama ballentana bita zaizai Bai tanka mataba ya duqa yaci gaba da wankinsa harya gama Ya shanya wankin sannan ya nufi kofar dakinta ya durkusa daga waje Inna na gama ina alalata Inna laure ta dago daga kwancen da take saman katifa ita da yarta Ta watsa masa wani kallo tace abincima wato har kaso biyu zaka dinga ci kenan Koba dazun na giftaka naga naga kanacin garin kwaki ba? Dallah ni tashi ka bani wuri ta doka masa tsawa Rabiu ya miqe tamkar almajiri ya nufi bakin rigiya ya janyo ruwa guga guda yayi alwala ya nufi dakinsu yayi sallar asuba da azahar a hade Sannan ya kwanta nanfa gajiyar daya kwaso ta rufeshi Saude tasha yawon tallarta harta godema allah amman alalar ko rabi bata samu ta saida ba nanfa idonta ya ciko da hawaye ta soma bin jama,a tana hadasu da Allah su siya Danladi ya tabo abokinsa ilu kai baba yarinyar canfa tana cikin matsi ina yawan ganinta a cikin tasharnan anya ba zamu far matAba kuwa? Ilu yace nimafa na dade ina wannan tunanin to amman abinda ke tsoratani yarinyar karamace sosai karkaje ka balloma kanka ruwa Danladi yace kaiko da mugun baki kake idan zakaxo muje mu fasa kawai kaxo muje malam Mu jata kangon alhaji sani Ilu yace kuma hakanefa to taro mana ita ni bari naje na duba mana wurin na tabbatar da tsaro Ya dire daga kan teburin da yake ya nufi gurinda saude take duqe gaban wani direban j.5 tana zazzage masa alala a kwano ilu ya iso waje yace ke yarinya idan kin gama sayar masa kikaima wancan gashi can zai siya tace to ta miqama direban alalan ya karba ya somaci ita kuma ta rabe gefe tana jiransa ya gama ya bata kudin da kwanon ta qara gaba Direban ya soma ci gaya dago sai yaga ta kura masa ido ji take dama bakinta yakekai alalar sbd tsabar yunwar dake cinta Direban yadan daga murya yan mata ya kike kallona ko na miki ne ? Saude tayi saurin dauke kanta yayi daria yaci gaba da cin alalarsa Karen matar dake can gefe yace sai oga baka tambayeta ko tana ciki bane Yace kai share wannan bata inda ke mata dadiba Karen motar ya sake bushewa da daria yace sai oga allah yabar mana kai Baice masa komaiba ya qarasa cinye alalar ya wurga mata robar ta zabura ta miqe gamida saka kwanon cikin tiren ta qarasa inda yake domin karban kudin ya kura mata ido yaya akayine? Tace kudin zaka bani Ta nawace? Saude ta numfasa kafin tace ta murtala daya da gomace Yasa hannu a aljihu ya ciro kudi masu yawa ya dubeta Yace yanxu idan na baki wadannan kudin zaki barni nayi lalata dake Saude ta zaro ido tana kallonsa Ya sake maimaita mata a karo na biyu Idonta ya ciko da kwalla alamar zatayi kuka Yace a,a meye abin kuka yanmata karbi kudinki kisan inda kikai kuma karna sake ganin kafarki ta tako inda nake Idankuwa ba hakaba saina turmusheki A wurinnan ya miqa mata kudin karbi ki wuce tasa hannu zata amsa hannunta na rawa ya hada hannun da kudin ya riqe yana dariyar mugunta Meye sunanki yan mata? Ta janye hannunta jikinta na rawa tabar wurin a hanzarce har tana tafka tuntube wani dan kamasho da yawo giftawa ta wurin ya tintsire da daria yana fadin dan baba kabar iya shege kabi Allah kaji Ya miqe yana fadin kai garba mufa duniya gaba muka bata ba baya ba Garba yace shegen sama kura taga biri Allah ya kauda abin kunya Yace ba aminba mu abin kunya binta muke tana guduwa Allah ka hadamu da abin kunya duk inda yake Duk wurin sukasa ihu ana sai oga allah yabar mana kai Ikon allah mai tsaida wando ba zariya saude dai bata sake bi ta kansu ba ta nufi inda danladi ke zaune saman teburin cikin tasha tace kaika aika a kawo maka alala ko? Yace eh zubomin ta murtala biyu Dadi ya kama saude don tasan daga wannan ta siyar tana murna ta zuba masa tasa masa mai da yaji Ya zauna ya harde gamida lashe alalannen tas yana lashe baki Saude na zaune tana kallonsa yana gamawa ya dubeta Kinada canjin naira dubu? Saude ta waro ido ita tunda takema bata taba riqe naira dubunba ballentana harta samo canjinta Ta girgiza masa kai alamar a,a Yace to ya za,ai kenan ko kuma xo muje na samo canjin saina baki kudinki Ta mike ta tattara kayan ta bishi Suka soma tafiya ganin suna shirin fita daga tashar yasa ta dubeshi tace Ina kuma zamuje? Yace ban gane ina zamujeba canji zan nema in baki kudinki Saude tadanyi shiru maganar yayanta ya dinga dawo mata cikin kunne tamkar yanxu yake gaya mata Saude ki kula banda aje tallah ki tafi samo canji banda kuma kibar mutum ya tafi samun canji shi kadai Kuma karki sake ki yarda wani ya jaki zuwa wani guri koda kuwa nan da canne Saude ta dubeshi a,a gaskia nidai kazo muje cikin tashar a samu canjin kaban kudina don yayana ya hanani bin wani Ya hade rai jini da yar iskan yarinya sai kuma akacemiki kowa dan iskane. To karki bini ki karbi kudinki zauna Ya wuce zai tafi hankalin saude ya tashi tasan kan kudinnan yau inna laure kashetane kawai ba zatayi ba tayi saurin riqo rigarsa tasa kuka Nidai wlh saika bani kudina Ya juya a fusace ya danna mata wani mugun zaki ke dan ubanki bazaki sakeniba? Ta qara cacimo rigarsa nidai wlh saika bani kudina idan naje gida a haka dukana za,ayi Haushi ya kama danladi yasa hannu ya dauketa da wani wawan marin dayasa saidata kife. Ya juya zai wuce wani magidanci ya kwaso a guje yana kiran Tsaya nan danladi karka sake ka matsa mugu mai kai mata? Yayi saurin juyowa jin muryar ogansa Gabansa ya fadi yai saurin juyowa yace wlh oga yar iskan yarinyace wai dan uwar yarinyarnan waini zata tsare nace Nace taje ta samo canjin dubu tace babu nace muje na samo na bata taqi yarda toya takeso nayi da itane oga ? Ya tallabo saude gamida fadin yanxu don rashin imani wannan yar qaramar yarinyar zakaima irin wannan marin? Yanxu wannan yarinyar fisabilillahi meta sani? Ya zaburo cikin irin muryar yan shaye shayennan yace oga zaginafa tayi yace idan ta zageka kai yanxu zagi nawa kai mata a gabana ko kunyata bakajiba Yi hakuri yarinya kinji allah ya saka miki bani dubun na canja muku Yadan sosa qeya a,a ai gurin ilu zan amso dubun na samo canjin mutumin ya girgiza kai yana fadin allah ya shiryeka ya zaro kudi cikin aljihu ya kalli saude. Kudin naki har nawane? Cikin muryar kuka tace murtala biyu da goma ne Ya girgiza kai ya bata sannan ya kalleshi na ranta maka ka samo canjin ka kawomin kudina Dan ladi ya turo baki yana dan harare harare ya wuce kamar zaikai duka Mutumin ya dubi saude yace wuce ki tafi kinji allah zai saka miki yace ai harda laifin iyayenku mata dake turoku tallah cikin maza basu san da irin mazan da zaku hadu ba don ko cikin masallaci zakukai tallah sbd tsoron allah sai an samu mutanen banza ballentana cikin tasha inda yayan banza ke taruwa wadanda daman can lalatattu ne ya za,ai ace bazai,ai barnaba fisabilillahi balle ke yarinya qarama Wuce kije allah yayi miki sakayyah Haka saude ta wuce gida jiki na rawa da yamma lis don tuni rana ta fadi a lungun gidansu ta hadu da rabiu cikin taron jama,a wai ana duban wata Saude ta lallaba ta janyo hannun rigarsa yayi saurin juyowa yana kallonta yayi murmushi tana fadar Tun daga nesa na hangoka duk ka keresu tsawo Rabiu ya dungureta yana daria yace ke kuma sarkin sharri ko? Daria itama tayi tana fadin anga watanne yaya? Yace a,a munadai dubawane amman munasaran za,a ganshi kedai ki zauna da niyyar azumi gobe Tace ai nima tsayawa xanyi yaya ka dagani inga watan Yayi murmushi yana fadin so kike yau inna laure tayi kujera dake kenan ko? Ya riqo hannunta Yace wuce mu tafi kinga har yara su fara tsokanarki Saude ta juya taga dandazon yaran daketa tsalle suna waqa Yar tallah qazama yar tallah bata wanka yar tallah bata wanki yar tallah bata sallah yar tallah saidai yawon tallah Ta dago idonta cike da kwalla ta kalli yayanta tace aidai yaya ina sallah ko? Kai kawai ya daga mata sbd yaddah abin ke sukarsa a zuciya ya daura hannunsa saman kuncinta inda shatin yatsu suka kwanta wurin yayi jajir abinka da jar fata Muryarsa na rawa yace waya mareki haka saude? Muryarta na rawa ta shafa wurin tace wanine ya mareni a tasha yaya wai don naqi binsa ya samo canJi Rabiu yaja numfashi ai gara dabaki bishiba saude shida allah Sai a lokacin ya lura da jinin daya kwanta a idonta yAja hannunta suka tafi yanajin zuciyarsa na suya fiye da radadin marin da taji Suna shiga cikin gidan inna laure dake duqe bakin rariya tana tsane gero ta dago ganin kwanikan duk sun baci da qasa Jar ubannan kai badai barin alalar kikaimin yauba ? Saude tace a,a na saida wanine ya mareni harna fadi waidon naqi binsa ya samo canji Inna laure ta daka mata tsawa ke gafara can munafuka tantiriya idan yace ki bishi ya samo canji to sai meye ? Koyana iskanci dai ai bazaiyi da keba a balla qashi ko,a karya qafa bani kudina ni ki wuce Saude ta warwaro kudin a habar zani ta miqa mata. Ta karba gamida kirgawa taga sun cika cas ta ninkesu ta soke akai Rabiu ya dubeta dauki gora kije kiyi alwala kiyi sallah Inna laure ta zaburo bazatayi Maza ga kudi kije ki siyo icce ki daura sanwar tuwo kai kuma ka tattara kayan tallar ka wanke Idon saude ya ciko da kwalla ta kafama yayan nata ido Laure ta zaburo mata to yar iska gama kallon nasa kixo ki amshi kudin Ko ubankima bai isa ya hanaki yin tuwonnan ba ballentana wani banza jaki can zakizo ki karba kokuwa sai naxo nayi miki dukan kawo wuqa????? [1/8, 4:43 PM] I love my mum: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚 [12:17PM, 02/02/2017] 🙆🏼‍♂@lh@ji🙆🏼‍♂: [1/8, 4:44 PM] I love my mum: *YAR TALLA* *CHAPTER 5* Tace to yar iska gama kallon nasa kixo ki amshi kudin don ko ubanki bai isa ya hana kiyi tuwonnan ba ballentana wani banza jaki can zakizo ki karba ko kuwa? Anan muka tsaya Rabiu ya turata alamar taje ta karba Laure ta maka mata rankwashi akai wanda yasata fasa wata uwar qara sbd azaba Ta wurga mata kudin tana fadin munafuka nafa alamar watarana sai kin nemi kifi karfina a cikin gidannan Dole saina gyara miki zama ta haureta da qafa Zaki tashi ko sainaxo na casaki? Yar iska kawai lau yayyar banza kawai Saude ta yinkura ta tashi gamida ficewa tana kuka Rabiu ya rakata da idanu yana tausayin kansa rayuwarsu na bashi tausayi A ganinshi babu yaran da suka taba samun kansu cikin halin kunci kaman yanda shi da qanwarsa ke ciki yanxu. Yace ya allah gamu gareka Laure ta wurga masa murfin kwano ya zabura gamida dawowa hayyacinsa yayi gaba yana tattara kwanukan Laure tace daka barta ta tafi kaita tunani ai gara ka bita can kuyita Kwakwale kwakwalenku dan iskan banza da wofi kawai Maganar ta soki rabiu yai saurin wuceta sbd yaddah maganar ta daki zuciyarsa matuqa ji yake kamar bata taba masa abinda ya qona masa zuciya irin na yau din ba Saude ta dawo daga siyo iccen ta zauna ta hura wuta gamida daura ruwan tuwo a lokacin har ta fara sarewa da wahala a jikin murhun ta soma jinyar qafafuwanta ta samu daqar ta kammala tuwon da miyar kuka a bakin murhun taci tata ta miqe tayi alwala ta shige dan akurkin dakinsu domin jero sallolin da batayiba Washegari aka tashi da azumi don haka saude ta samu sauqin wahalar sosai Dukda aikace aikacen gidan da tayi itada yayanta bata wata sha wahala ba Saida azahar inna laure tasata dauki markaden tiya uku aka kai markade aka markado shi ta sake daukoshi akai ji take tamkar wuyanta zai karye sbd nauyi Data kawo markadenma qin sauke mata tayi ta barta dashi akai Saude tasa kuka don allah kiyi haquri ki saukemin inna kaina zai karye Laure dake zaune tana kwadon zogale ta dubeta a harzuqe kin fara ko? Wato nabar kwadon zogalen naxo na sauke miki sbd inajin tsoronki ko? Ta maida kai taci gaba da kwadonta tana fadin bankadaddiyar yarinya masifaffiya Iklima dake kwance gefenta tace laure bani ruwa insha karya azuminnan zanyi bazan iya kai azuminnan ba Laure tace a,a ko aike kikasa kanki tuntuni nake fadin ki ajiye ki ajiye kikaqi waike sai kinyi. Ta miqe gamida dibo mata ruwan cikin randa mai sanyi ta kawo mata ta miqe tasha iya shanta tayi wurgi da modar Laure tace a!a mai makon ki bani in mayar sai kiyi wurgi da ita Iklima tayi tsaki ta janyo kwanon kwadon dake gabanta ta soma ci Laure taja kwafa sannan ta miqe ta dauko modar ta mayar sai a lokacin ta nufi saude data dafe wuyanta da takeji tamkar zai karye Laure tace shin zaki tace ko na tace? Donna lura wuyanki ya isa yanka Saude ta wuce ta nufi rijiya sannan ta dibo ruwan ta taceshi tas tana Tana gamawa rabiu ya dawo daga markaden qosai Da alamar shima a gajiye yake Laure ta dubi saude maxa ki hadamin wuta ki hadamin kaskon suya ki hadamin murfi biyu dayan murhun kuma ki dora ruwan koko Ba yaddah ta iya haka taci gaba da hada hadar hada wuta babu ko tausayawa Laure ta soya kosai sannan ta sheqa koko cikin bokiti Qarfe shida tace su dauka sukai makarantar malam hadi tasan almajirai zasu siya Rabiu ya dauki kokon ita kuma Saude ya dora mata kosan Laure ta kwala musu kira suka dawo Tace kuma ban yarda da ku daukarmin ko kayan sile ba kuje ku dawo kayan buda bakinku nanan zan ajiye muku suka amsa da to sannan suka fice Cikin ikon allah kuwa suna zuwa ana kiran sallah Alhaji bashir wani tsohon mai kudine a cikin layin yaxo zai shiga masallaci ya tsaya wurinsu ya zaro dari biyar ya miqawa rabiu yace ya kirga kosan da kokon ya bada sadaka,,,dadi ya cikasu shi kuma ya shige masallaci abinsa Rabiu ya kirga kayan gaba daya na dari hudu da hamsinne Yayima almajiran wurin sadaka da koko da qosan Ana gama sallar alhajin ya fito rabiu ya fada masa ko kayan nawane yace tosu riqe canjin Sannan yace musu kullun su rinqayin sadaka da koko da qosan zai rinqa biya Ya zaro wata dari biyar din ya basu rabiu ya amsa cikin ladabi suka cika da murna Alhaji bashir din yace kuma ku dinga diba kunaci kunji?suka amsa da to sannan ya wuce abinsa Suma suka wuce gida rabiu ya canja kudin ya dauki canjin yankan da suka rage yaba laure sauran kudinta dadi ya cikata za,a ringa siyan kayana kenan kaga babu bandaro (kwantai) kenan ta dubi Saude jiki maza ki dauko muku koko suka tsugunna a tsakiyar gidan tamkar almajirai sukasha sannan saude ta miqe ta dauko musu sanwar dimamen daya rage tun na sahur sukaci suka koshi duk da kuwa miyar kukar tayi tsami ta lalace amman a haka suka cinye tuwon tas. Gaskiane da hausawa sukace da babu kwara ba dadi Sun gamaci suka tafi sallar asham a masallaci suna dawowa su duka suka kwanta a gajiye kamar matattu Qarfe uku na dare laure ta tashesu wai su tashi susa sanwar tuwon saidawa na asuba Saude tasa kuka saboda bacci da gajiya dake cinta Laure ta haskata da cocila au kukama kika tsayayi kenan ni inanan ina jiranki? To malam zoka gani da idonka saude na zagina Malam bala ya zaburo tamkar shayayye Zagi kuma laure wani irin zagi ba dadin ji?ya hankade labulen dakin ke ba magana ake miki ba yar jakar ubannan shine kika zauna kinama mutane kuka Idanda uwarkice ta dawo daga lahira ta sanyaki aikin ai bazakiyi kukanba ko? Fitonan inji wanda kike zagi Saude tahau rantse rantse abinka da yarinta kuma ta rikice sai fadi take wallahi baba karya take ban zageta ba na rantse da allah ban zageta ba Malam yace shin zaki fito ko saina shigo dakin? Rabiu yace kayi haquri don allah baba wallahi bata zageta ba Malam yace au karya tayi mata kenan? Ta zabura ta boye bayan rabiu tana kuka tana bashi haQuri amman bai sauraretaba yasa hannu ya fisgota daga bayan nasa ya jata a qasa kiyyyyyyyy Har waje ya janyo igiyar guga ya shiga laftarta ta ko ina bugu bana hankali ba baya ko duban inda zai doka sai ihu take tana roqonsa Rabiu ya duqar da kansa qasa baya ko iya motsi hawayene kawai masu zafi dake diga daga idanunsa Saida yayi mata dukan bala,I ya farfasa mata jiki sannan kuma ya tabbar da ko motsi batayi sannan ya kyaleta harya wuce ya dawo ganin alamun kamar ta suma yasa ya janyo ruwa cikin guga ya sheqa mata ta sauke nannauyen numfashi yace sannan ki tashi maza ki dora tuwon siyarwan don lokacin sahur ya gabato [1/8, 4:44 PM] I love my mum: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚 [1/9, 9:55 AM] A A Dboy: *YAR TALLA* *CHAPTER 6* Saida yayi mata dukan bala,I ya farfasa mata jiki sannan kuma ya tabbar da ko motsi batayi sannan ya kyaleta harya wuce ya dawo ganin alamun kamar ta suma yasa ya janyo ruwa cikin guga ya sheqa mata ta sauke nannauyen numfashi yace sannan ki tashi maza ki dora tuwon siyarwan don lokacin sahur ya gabato Anan muka tsaya Rabiu ya miqe ya rarrafa wajenta gamida jawota jikinsa yana sharar hawaye baisan sanda wani irin kuka maiban tausayi ya kubce masa ba saida yai mai isarsa sannan Ya janyeta ya tafi hura wutan tuwon don daman ya iya tuwon duk da ba sosai ba don tun yana yaronsa inna laure ke sanyashi kafin saude tayi kwari amman abinda ba aikinkaba har saude data girma daga baya taxo ta fishi iyawa Saidai yau haka ya zage bakin kokarinsa yayi tuwon da miya laure ta murmula musu naira biyar biyar ta zuba tuwon a baho miyar a bokiti gamida basu fitila Rabiu ya dauki kwanon tuwon akai kana ya dauki na miyan a hannu yace saude ta koma ta kwanta shi zaije ya siyar har bakin tasha yaje dukda rashin kyan hanyar ya samu wuri ya zauna inda yan garuwa direbobi da matasa ke zama Acan yayi sahur dinsa daida akai sallar asuba sannan ya dawo saidai bai saida duka ba Laure tahau fada tsohon munafuki ai daman don mugunta kaqi tafiya da sauden don kaje ka dawomin dashi Inda kun tafi tare ganinta ai wanda baiyi niyyar siyabama sai ya siya tunda yana ganin mace amman shine kai ka kwasa ka tafi Zan gani duk uban daya daure muku gindi a garinnan yau zan ganshi don sahur din da za,ai na gobe da ita zakaje Munafikin bazan da wofi wanda yayi gadon baqin hali insha allahu qarshenku bazaiyi kyau ba Yaddah uwarku ta mace a wulaqance kuma haka zaku bita daya bayan daya Rabiu ya ajiye mata bahon ya wuce zuciyarsa na faman suya da tuquqi mai ciwo Wasu irin hawaye suka dinga zarya a saman kumatunsa Yana isa dakin tun kafin ya zauna ta zaburo ta nufo dakin ta hankade labule saika fito munafukin allah kaxo ka jido mana ruwa ka tashi wannan yar iskan taxo ta fara aikin gida ita kuma aiba wani kuka ajeba da zaku kwanta kuyi barci shikuma yai muku aikin gida maza ku taso Rabiu ya goge hawayensa sannan ya tayar da ita zazzabine fal a jikinta tausayinta ya kamashi ya kamata suka fito yana nashi aikin yana nata har suka gama basu suka zaunaba saida rana ta haske gari gaba daya Sannan suka kwanta hakanma badon tasoba saidon babu sauran ayyukan da zasuyi matanne amman da bata barsu sun kwantan ba Sun samu barci yakai na awa biyu kafin masifaffiyar ta tashesu ta turasu markade daganan basu sake samun zamaba har dare Haka rayuwa taci gaba da tafiya cikin kunci da takura har azumi yakai ashirin da tara kowa nasaran gobe sallah duk inda ka gifta anata yankan kaji Wasu natakai markaden abincin sallah inda su rabiu da saude ke tsugunne kan dakalin dakinsu duk sun zubawa inna laure ido wacce ke zaune a bakin murhu saman kujera sai faman suyan naman shanu take Iklima yar baba (sunan da take kiranta dashi kenan)sai faman kaiwa da komowa take tana miqa faranti ana tsomo mata Suna tsugunne harta kammala suyar ta zuba cikin babban langa ta juye man tayi daki tabar iklima zaune waje tana yagar nama Malam bala yai sallama niqi niqi da laidoji a hannunsa Rabiu ya tarbeshi da sannu da zuwa ya miqa hannu zai karbi kayan dake hannun nasa ya noqe yana fadin A,a barshi kawai gyaramin tabirma kawai na zauna a bakin dakina Rabiu ya kwasa da hanzari ya gyara masa tabarman ya zauna Sannan shima ya koma wurinsa kamar daxun inna laure ta fito daga daki tana fadin A,a malam sannu da zuwa ya amsa yauwa laure sannu da gida taja ta zauna kusa dashi Mu muka samu kuma malam? Ya watsa hakorannan kaman an watsa wake miya kamin yace kayankune na amso muku daga wajen tela sannan na qara biyawa ta kasuwa na qara hado muku sauran kayayyaki wasu kudine nai sa,a wallahi akaimin biyan bashinsu yanxunnan Inna laure taja ledar tana fadin sannunka kuwa malam bari mu gani Ta janyo ledojin tana zazzagewa Atamface soso yar yayi aka dinka mata ita da yarta kala bibbiyu sai takalmi danko kowa guda guda sai tsakiya ta wuya data hannu kowa da nashi sai gyale kowa da nashi Dadi ya cika laure aiko saita rangada guda aiyiriri wallahi tallahi malam ka biyamu allah ya qara budi kaji Shi kuwa sai ji yake kansa na qara fashewa ji yake dada akwai saura cikin aljihunsa daya qara zazzage mata saboda yaddah ta kodashi Laure ta yafito iklima dake zaune tanacin namanta Iklima ta kwaso da sauri cikin doki ta zauna tsakiyarsu tana daddaga kayan Dadi ya cikata ta miqe tana gwargwadawa tana tsallen murna Saude dake zaune ta daga kai ta kalli yayanta idonta cike da hawaye yaya ni ina nawa kayan? Rabiu ya kalleta cike da tausayawa yace kiyi haquri kema anjima zan siyo miki naki kinji? Kai kawai ta daga masa hawayen da suka taru idonta suka gangaro yasa hannu yana goge mata Inna laure ta miqe ta tattara kayan ta shige dasu daki shikuma malam ya dauki buta yai bandaki Rabiu ya dubi saude murya qasa qasa yace bari inje in siyo miki naki kinji? Kai kawai ta daga masa ya miqe ya shiga dakin nasu ya bude kayan qyaure ya ciro kudin da yake tarawa yan hamsin hamsin din da alhaji bashir ya dinga bar musu ta cikon koko da kosai Tun farkon azumi har zuwa yau ya fito ya fice abinsa Kai tsaye kasuwa ya wuce ya zaga sosai ya samo mata yan kanti doguwar riga da wandonta naira dari bakwai sannan ya siyo mata yar qaramar abayarnan mai hade da kyale waddah akema laqabi da gemun shaidan lol ya siyo mata wannan naira dari biyu da hamsin Sannan yasai mata takalmin dari biyar Daman kudin dubu dayane da dari hudu ya tara kuma ko naira bai dawo da itaba don saima da aka biyoshi bashin naira hamsin Yayi sa,a daya dawo ba kowa a tsakar gidan don haka ya wuce dakinsu kai tsaye Saude na kwance tayi rigingine tana kallon sama daka ganta zakasan tana cikin damuwa ya zauna gefenta yana fadin tashi saude ga kayan na siyo miki Ta tashi cikin doki ya zazzage mata kayan ta daddaga tana gama gani ta fada jikinsa domin murna shima ya rungumeta yanajin wani sanyin dadi na ratsa zuciyarsa Ganin farin cikin qanwar tasa ya fiye masa komai a duniya Washe gari itace ta kasance ranar qaramar sallah idan ka duba jama,a sai hada hada ake kowa yana cikin murna da farin ciki yara da manya Kowa yana cikin sababbin kaya cikin tsabta da kamshi Haka gidan malam bala shida matarsa da yarsa suna cikin wadanda suka raya wannan rana sunsha kwalliya cikin sabuwar sutura amman banda Rabiu da saude Don tunda garin allah ya waye suketa faman aiyukan gida suna gama aiyukan kuma saude tahau kai abinci gidaje yara sai tsokanarta suke qazama qazama yau abin ko kadan bai dametaba sbd itama tasan yau zatayi tsabtar kamar kowa itama zatayi kwalliyar da take ganin iklima nayi ta shafa jan baki tayi kwalliya a fuska tana gama rabon abincin ta zura guga a rijiya cikin rawar jiki don itama tayi kwalliyarta tayi yawon sallah Yan matan unguwar tasu sukai sallama da yawansu don aqallah zasukai goma duk sunsha kwalliya ji take babu na biyunta Saude ta amsa musu sallamar dasuketa rerawa Yar baba nanan?suka tambaya saude tace tananan a daki suka wuceta suka shige ita kuma taci gaba dajan ruwanta tana shirin wankane suka fito suna labarin zuwa masallaci daganan su wuce yawon barka da sallah Saude tace dan allah larai nima ku tsaya nayi wanka mu wuce tare Larai ta watsa mata wani kallo tabdijam waye zaije yawo dake yar tallah duk nanma wacece qawarki? Tayi shiru tana kallonsu Salame tace ai sunanki ta kira kinga kenan kece qawarta Larai tayi saurin fadar allah ya sauwaqe saidai ko yar gidansu takebi yar baba yar uwarta yar baba ta turo baki allah ya sauwaqe niba yar uwata bace yar tallar gidanmuce yarinyama tace zata bini ba sai inci uwartaba Lantana tace to a ware kowa ya ware muga wanda zatabi kowa ya ware ya daddaure fuska Saude ta hadiye kukan dake neman kubce mata tace ai nima yara yanxu zanyi wankana insa sababbin kayan da yayana ya siyo min inyi kyau Yar baba tace ke matsa can kyan gidan ubanwa zakiyi kullum sai qazanta jibeta da wani hancinta can sai kace kajeren wando duk sukasa daria harda tafawa sannan suka fice Saude ta dauki ruwanta ta nufi ban daki tana fadin aidai allah ne ya bani Tayi wankanta ba soso ba sabulu don dama ta saba ta fito ta shiga dakinsu batada ko man shafawa ballentana kayan kwalliya Don haka kayan kawai ta dauka ta sanya ta saka sabon takalminta Da gyalenta tayita juyawa dukda ba kallon kanta takeba amman ji take tamkar babu wanda ya kaita haduwa Rabiu ya riqe labule dariya ta kwace masa yaddah yaga tanata faman juye juye sai kace mai rawa tayi saurin juyowa Tace yauwa shigo yaya wai don allah nayi kyau? Rabiu yai murmushi mai hade da daria kamin yace aike daman kyakkyawace qanwata ba kayanne zasu fito da kyankiba kyankine zai fito da kayan kisha kuruminki insha allahu indai ina raye saina fito da boyayyen kyanki a idanun duniya dauko kusar can kixo in kwance miki kanki duk shi ya bata kwalliyar Saude tayi saurin dauko masa ya zauna ya kwance mata tas ya sharce mata yasa tsumma ya daure mata shi ya lulluba mata gyalen ta miqe zata fita Sai kuma ina? Tadanyi jim kafin tace waje zani yace to bari inci abinci sai in sameki kofar me gari zan daukeki muje kiyi kallon sallar Dadi ya kamata harda tsalle. Ta fice Inna laure na zaune saman kujera tanacin soyayyen nama wanda ko qashi batabamasu saudenba ballentana susa ran tsoka Cikin rudu da kidima laure ta dauki sallallami laila ha illallahu muhammadur rasulillahi Mezan gani yau ni laure saude zonan dan qashin ubanki Ta zaburo ta shaqurota ta maqure uban waye ya baki kayannan? Yar iska kudina kike sata a gidannan ban saniba,,, Ta dauketa da mari da qarfinta kokuwa maza kika farabi iye? Saude ta fara ihu tana kakari sbd shaqar da tayi mata Laure ta hankadar da ita har kanta ya bugu da bango ta shiga kwalama Rabiu kira wanda tundata soma dukan nata yakejin kamar ya hadiyi zuciya ya mutu sbd baqin ciki ya fito daga dakin ya nufota yana fadin gani Laure ta daukeshi da wani mahaukacin mari wanda ya sashi dafe kunci ta nunashi da dan yatsa cikin bala,I bakinta har kumfa yakeyi Gidan ubanwa aka samu wannan kayan sata kukemin a gidannan ban saniba? Aiko sai laure tasa ihu yau na shiga uku na lalace abinda nakeji a waje yau ya shigo cikin gidana ashe da yan fashi nake zaune ban saniba Lol Su laure manya [1/9, 9:55 AM] A A Dboy: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚 [12:17PM, 02/02/2017] 🙆🏼‍♂@lh@ji🙆🏼‍♂: [1/12, 5:44 PM] I love my mum: *YAR TALLA* *CHAPTER 7* Laure ta dauke shi da wani mahaukacin mari wanda ya sa shi dafe kunci, ta nuna shi da dan yatsa cikin bala,i “Gidan uban wa aka samu wannan kayan sata: kuke min a gidan nan k0 kuma me?" Rabi‘u ya girgiza kai cike da kunar zuciya ya girgiza kai alamar a’a, ta hayayyako masa. “To gidan uban wa ta samu wadannan kayan?” Rabi‘u ya hadiye wani abu da ya tsaya masa a. zuciya kafin ya fada mata. yanda a kai ya samu kudin tun kafin ya karasa rufe baki ta sake dauke shi da wani gigitaccen mari cikin zafin zuciya take fadar. “Ni za ka dauka ‘yar iska ni zaka nunawa iyakata, Karya kake Rabi’u baka isa ba wallahi tallahi kaci karya ka kwana da yunwa baka isa kaja daniba,yandanaga bayan uwar data haifeku kuma bazaku gagareniba, don haka ka taka a sannu wallahi idan kai wasa sai na rufe babinka a duniyar nan k0 sunanka babu wanda zai sake ambata a garin nan. . janyo Saude ta shiga cire mata kayan tana fadin. “Ban yi niyar ta sanya sababbin kaya ba, kuma kai baka isa ka sata sanya suba.” Ta cire kayan gaba daya ta hankadar da ita gefe ta wuce daki tana. faman huci. Rabi‘u ya runtse idanuwansa yana jin zuciyarsa kamar za ta fashe saboda baqin ciki da takaici kukan Saude ya dame shi a zuciya ya tallabo ta a jikinsa ya wuce daki da ita, ya dauki kayanta masu datti ya saka mata ya ja ta a jikinsa ya rungume yana lallashinta. “Ki yi hakuri ki daina kukan nan haka kinji ’ insha Allahu zan siyo miki wasu ki yi shiru kinji ' ban san yawan kuka Da qyar ya samu ya lallashe ta ta yi shiru, har wani barci mai nauyi ya dauke ta sai ajiyar zuciya take saki akai akai, tausayinta ya dirar wa Rabi’u. Tabbas bacin ita da ta rage masa yana ga da ya gudu ya bar garin, to idan ya gudu bai san halin da gudar qanwar tasa zata shiga ba, a dole ya zauna, dole zai yi hakuri ya ci gaba da fuskantar rayuwar dake tunkarar su. ' Ya runtse idanuwansa wasu irin hawaye masu zafi suka shiga zubo masa a idanuwa suna sauka saman kan Saude wacce baccinta ya yi nisa sosai. yasa hannu yana goge hawayen da suka Bata. masa fuska. Haka rayuwa ta ci gaba da taflya babu abin da da ya cansa sai ma abin da ya qaru, kullum da wahalar dake kunno kai. A tallar Saude kuwa sai ma abin da yayi gaba. Wata rana da safe Sande ta dawo daga markade Ta zauna bakin murhu' tana hadawa Laure wuta, Malam Bala ya fito riqe da hannun ‘Yar Baba tana sanye da sababbin kayan makmantar boko, koran wando da farar riga da koran kallabi da farar abaya, ta sha takalminta sandal da farar safa, ta goya jakar: goyan ta. Saude ta tsaya da hura wutar tana kallon su cike da sha’awa yanda ‘Yar Baba ta yi kyau cikin sababbin kayan, har bata san lokacin da ta mike ta soma bin su ba don kar ma su Bacewa ganin ta. Tinqis-tinqis ta ringa bin su har suka iso makarantar ba ta tsaya aka ba ta labari ba hae: cikin oflshin Head Master ta bi su ta yi tsaye tana kallon su. Malam Bala suka gaisa da Head Master sannan ya gabatar masa da ita matsayin sabuwar daliba, shugaban makaranta: ya riqo hannun ‘Yar Baba yana fadin “Ai tuni wannan ta wuce shiga aji daya dan ta kai shekara goma zuwa sha daya, sai dai a kai ta aji uku idan ma ta maida hankali sosai maimakon ta shiga aji'shida sai ta wuce fom one kawai.” Malam Bala ya shiga yi masa godiya, Head Master ya dubi Saude da ke tsaye tana zaro ido ya ce “Ke kuma fa lafiya, k0 tare ku ke” ‘ Malam Bala ya yi saurin juyawa yana kallon inda Saude take tsaye Yasa sallallami ya mike yana fadin, “Yanzu biyo mu ki ka yi ‘yar jakar uba.” Ya fizgo ta yana rankwashi yana zagi. Head Master ya yi saurin miqewa ya riko shi yana fadin, ‘Don Allah ka yi haKuri Malam ka kyaleta yarinta ce kawai.” _ Malam ya cw, “Haba, haba yanzu wace yarinta ce wurin wannan iskanci ne dai kawai.” Head Master ya ce “A’a kar ka ce haka kila abin ne ya bata sha’awa hala ita ba ta makarantar neko? Malam Bala ya cc, “Ba a sa ta ba ita talla take.” Head Master ya ce, “Kai abin nan yana ci mana tuwo a kwarya wai yanzu yarinya kamar wannan a kashe ta a kashe rayuwarta da talla, kullum muna fadakar da iyayen yara a kan su kula da hakkin. ‘ya’yansu a kan su don kiwo ne a gare su Allah ya ba su amma ba sa ji. Wallahi mafi yawanci ‘yanmata wurin talla nw suke lalacewa, don a wurin talla ne yarinya za ta saurari maganganun da ba su kamata ba. A wurin talla ne yarinya za ta ji batsar da tunda take a duniya bata taba jin taba. A wurin talla ne yarinya ke sanin abin da ke faruwa tsakanin namiji da mace, ba tare da shekarunta sun kai ta sani ba. Malam idan na soma karanto maka illolin talla sai mu kwana anan ba mu idar ba, sai kun je inda matatarar maza suke ka iske mace ta kawo talla kaji ikon Allah, daga nan sai ka fara ganin namiji ya ci abu ya ce ba zai biya ba yarinya na ta bin sa yaqi ya bayar, ka ga ta riko rigar shi sai ya ba ta ya kwace, ka ga yana gudu tana bin shi daga haka sai ka ga kokawa ta tashi, wata rana sai ka same su suna wasan banza da zabgegen saurayi da gandareriyar budurwa mts!” Mts! Ya ja tsaki cike da takaici yana fadin. “Abin dai sai gyaran Allah.” Jikin Malam ya yi sanyi ya yi wa Head Master sallama ya tisa Saude a gaba suka tafi yana jin wani abu na yi masa yawo a zuciya. Yana yin sallama a gidan Laure ta yo kan su tana ' fadin, “Ina ka kamo wannan watsatstsiyar yarinyar? Tun dazu nake nemanta na karade gaba dayan gidan nan ba ta nan tun dazu na gama waina hatta sandare ina nemanta." Ta fizgo Saude da ke gabanta tana faman kuka, “Ina ki ka je ‘yar iskar nan? Yawace-yawacen bin ' mazan ne naki ya fara k0 Allah ya baki sa,a, wadanda ma suka fiki basu ci riba ba ballantana ke ‘yar ‘ tatsutsuwa, daga ki hura mini wuta ki sa qafa ki fice har in gama wainar ta sandare sannan ki dawo Malam yace, ‘Gaskiya Laure ki qarasa ido kan yarinyar nan don yanzu Malamin makarantarsu ‘Yar Baba ya rinka gaya mini irin abubuwan da yaran nan ke yi idan sun tafi wurin talla ki rinqa ja mata kunne Wallahi kar taje ta dauko mana abun kunyar da ba zamu iya saukewa ba." Laure: ta ja tsaki tana fadin, “Yo ‘yarinya Ma : ta sake ta kwaso abun kunyar ai sAi ta san inda ta nufa, don wallahi korarta za mu yi daga gidan sai dai ta nemi wasu iyayen." Malam yace, “Gaya mata dai.” Yasa kai ya shige dakinsa. Laure ta haure ta da qafa, “Tashi ki sauki tallar ki tafi muguwa kuma Batan sisi kikai min sai na ci ubanki cikin gidan nan kin dai san halina ba ni da kyau ba ni da dadl wallahi." ‘ Saude tana kuka ta duka ta dauki wainar ta fito tana sharar hawaye. A waje su kai karo da Rabi‘u yana ta bunzuma sauri yana ganinta ya nufo ta. “Saude ina ki ka je ana ta neman ki ba inda ban jeba cikin unguwar har kin tada mini hankali.” Saude tasa bayan hannunta tana goge hawayenta tace, “Ai Baba na bi zau kai ‘Yar Baba makarantar boko shi ne da muka dawo Inna Laure ta doke ni.” Rabi’u yace, “To ke in ban da abin ki me ya: kaiki bin su Baban na dai san ba cewa ya yi ki raka shiba ko? Taqara share hawaenta tana fadin “Eh, ai ni na bisu Yaya ina san makarantar in tafi can yanzu? Rabi’u yace, “Haba Saude ya za ai ki tafi kowa sanya shi ake baki ga ita ma Baba ya sanya taba?” ‘ Ta ce, “To, kai ma ka sanya ni yanzu.” Ya dan yi shiru yana nazarin wasu al’amura, Saude ta riqo hannunshi tana girgiza shi, “Don Allah nima ka kai ni ka ji Yaya?” Ya tsura mata ido yana kallonta zuciyar shi cike da al’amura masu yawa yasa hannu ya dafa kanta cike da tausayawa ya ce, “Ki yi haquri Saude insha Allahu za ki yi karatun boko, duk rintsi sai na ga kin yi ilimi dole zan cika burin mahaifiyarmu Saude kullum maganarta a kan karatunki ne insha Allahu zan cika mata wannan burin, dole zan nemi kudi k0 dan saboda kek0 dan saboda rayuwarki insha Allahu ba zan bari rayuwarki ta lalace ba, ki je tallar l Ki dawo kin ji?” Kai ta daga masa ya sake ta ta wuce sannan shima ya kama hanya ya yi gaba . Al’ amarin ya damu Rabi’u matuqa a zuciya yana san Kanwar shi ta yi karatu k0 dan wata rana ta taimaki kanta da kanta, koda baya raye tunda Allah kadai ya san gawar fari. To wacce sana’a ma zai yi yanzu a duniya? Tunanin da ya fado masa kenan, in dai ba ya rinqa' sana’ar Baban Bola ba, sai dai ita wannan sana’ar dole sai kana da jari a hannu ka rinka tara naka kana siyan na wasu kana hadawa. Ya ja numfashi sosai yana nazari, can abokinsa Halliru Maigini ya fado masa. Tabbas shi ya kamata ya nema don yanzu ya tabbatar yana da qarfin da zai iya sana‘ar ginin, ya mike daga kwancen da yakw: ya fito ya yi gaba, yana jin Inna Laure na Kwala masa kira bai kula ta ba, don yanzu yanda yake jin zuciyarsa idan ta ci gaba da takurawa rayuwarsa gab yake da daukan mataki (Namiji kenan). Cikin sa’a kuwa yana zuwa wurin abokinsa ya raka shi har “wajen mai gidansa ya amince ya karbe shi ya sanya shi cikin yaransa masu nazari da koyan aiki yace zai rinqa ba shi dari biyar duk safiya, amma ban da ranar da ba a fita aiki ba. Dadi da murna suka kama shi a ganinsa yanzu ya samu sana’ar da zai taimakawa rayuwar Kanwar tasa da ita, don haka har ya qagara gobe ta yi don ya fara . zuwa aikin shi ma ya ga yana rike naira dari biyar tashi ta kan shi. Mahaiflyarsa ta fado masa a rai, wayyo ina ma tana raye tabbas da ya zamo daya daga cikin ‘ya'ya masu kyautatawa iyayensu. Kukan Saude ne ya dawo da shi daga duniyar tunanin da ya lula ya zabura da sauri ya yo waje, ya iske Inna Laure zaune ta dora qafafuwanta kan ta tana ta mintsini ta ko’ina ita kuma sai ihu take, tana roqonta. Rabi’u ya jingina da bangon dakinsu yana kallon muguntar da take mata ‘yar Baba ta ruga ta dauko bakin wuta ta mikawa uwar tana fadin, “Karbi ki dake ta Laure.” Rabi’u ya dauke idanuwansa ba zai iya kallon wannan muguntar ba. Sai da Laure ta tabbatar ta yi mata burdun-burdun da tabbuna sannan ta sake ta ta haure ta tana fadin ‘Tsinanniya ‘yar iska gobe ma idan halin ki ne ki sake Batar min da kudi.” Saude ta kwaso da gudu ta fada jikin Rabi’u tana ihun kuka ya ja hannunta suka nufi dakinsu, ya zaunar da ita gaban shi yana lallashinta, yasa hannu yana goge mata hawayen, mur‘yarshi a sanyaye yake magana “Kiyi haquri Saude kidaina kuka kinji insha Allahu komai ya kusa zuwa qarshe nan ba da jimawaba komai zaizama tarihi,yanzu haka nasamu aiki gobe ma zan fara zuwa, share hawayenki nan ba da jimawa ba wadannan hawayen zasu daina zuba kinji?” Ta daga masa yana gage mata hawayen ya ce, “To ki yi murmushi mana kobakiji dada bane?’ Dariya ta shiga qalqalawa tanayi kamar wata tababbiya shi kan shi har ta ba shi dariya ya dungure mata kai yana daria itama tace ala dole saita rama. Lol kuma sance dani donjin yaddah laure da rabiu zasu kaya Naku har kullum Dboy [1/12, 5:44 PM] I love my mum: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚 [1/15, 6:40 PM] I love my mum: *YAR TALLA* *CHAPTER 8* Rama ya rike hannuwanta duka da ta yunkuro zata dokeshi sai ya tura hannun ta daki kanta, ya yi tayi mata dariya. Sun shagala sosai kuma kana ganin suka san suna cikin nishadi ba su ankara ba sai dai suka jiyo muryar Laure na fadin “Sannun ku ‘yan iska watsatstsu, taBarar ceta motsa kenan shi yasa aka shiga daka k0 jin kira ba ayi dakyau aikana qoqari gara kayi amankaka lashe abin ka, ka ga tuwanka manka kenan. Kuyi iskancin ku san ranku babu mai hana ku, ai dama barewa ba tayivgudu danta ya yi rarrafe ba gado kuki ai dama abun, kun tsotsa,ne ku yi sha’aninku kun ji.” Ta = saki labulan ta juya ta yi gaba. Rabi’u ya girgiza kai yana jin tamkar zuciyarsa Zata fashe saboda bakin ciki, idan akwai abin da ke daga masa hankali duniya ya dungunzuma masa lissafi to bai wuce a tuna masa abin da ya faru a * baya ba, wanda ke daga masa hankali ya dagula masa lissaii duk wata annashuwa ta shi take take Bacewa Ya jingina da bango yana kallon Saude ya jirkita ta kwanta jikinta a sanyayc. ‘ Washe gari tunda safe Rabi’u ya yi jidar ruwansa gamida duk wasu aikace-aikace da ya san zai yi qarfe takwas daidai na safe ya sa kai ya fice abinsa b tare da ya fadawa kowa inda za shi ba. Saude ta dauki taller wainarta ta tafi sarfiyar yau jikinta jinshi take babu dadi ko kadan da kyar ta samu ta iya saida wainar a hanya ma amai sau biyu tanayi harta samu ta iso gida da kyar, ta mikawa Inna Laure kudin tana neman faduwa, saboda juwar da ke barazanar kayar da ita. Inna Laure ta zuba mata idanuwa cike da jin haushi kafin ta ce. “Wannan lambon kuma na mene ne kl ke faman yi? Duk na kar ki dauki taller alalan ce k0 me?” Saude ta girgiza mata kai alamar a’a tana nishi. Inna Laure ta ja tsaki tana fadin “To sai ki wuce ki dauka ga alalan can ta Murtala shida ce da goma Saude ta langwaBe kai cike da jin jiki ta ce, “Ki yi hakuri don Allah Inna wallahi ban da lafiya bazan iya ba.” Inna Laure ta waro ido waje tana fadin, “Uban me ki ka ce? Ni ki ke fadawa ba ki da lafiya Saude? To Allah yasa mutuwa ki kekina dawowa wallahi sai kin dauki tallar nan, ‘yar iska na lure kwanan nan wani tashan balagar tsuntsaye ce ke cin ki, kuma wallahi zan tatsiye miki ita tas za ki tafi ki dauka ki bani wuri k0 kuwa?” Saude ta wuce tamkar wadda ta yi ciwon shekara goma ta dauka ta fice, tana tafiya tana hutawa k0 ta sule ba ta kai ga siyarwa ba ta zauna saman dakalin qofar wani gida tana faman kakarin amai numfashinta na fita sama-sma tun tana sanin inda Har ya kai ta flta hayyacinta ta fadi can gefe sime. Wani mutum da ke tahowa ta Iayin cikin shirin masallaci kasancewar yau Juma’a ce ya yo kanta a gigice ya jijjiga ta amma ba ta k0 motsi, kafin ka ceme mutane sun taru a kanta ana ta tambayar wanda ya san ta, amma babu saboda kullum dai ana ganinta tana wucewa babu wanda zai ce ga daga unguwar da take tahowa, tun kafin a tafi masallaci har aka dawo sallar Juma’a, amma ba a samu wanda ya san unguwar su Saude ba. Yamma liqis Rabi’u ya dawo daga wurin aikinsa ya yi dumu-dumu da yashi da suminti kana ganinsa kaga mai aikin Kasa, ya yi sallama ya shiga gidan. Laure da ke zaune a bakin rijiya ta dago tna kallonsa ya giftata zai wuce ta zabura ta mike ta cimimiyo rigarsa tana fadin "Daga gidan uban wa ka ke dan iska tun safe ina gararin neman ka rumfa-rumfa ban gan ka ba daga ina kake?” “Daga wurin aiki.” Ya ba ta amsa kai tsaye Laure ta maimaita, ‘Aiki. Aiki fa ka ce? Eh lallai Wuyanka ya yi kwari wato harka san ka kakkare Ka tafi wurin aiki, tabbas lallai wata rana sai ka Shaqeni shi kenan jeka jeka kawai." Ta fada tana . murmushi Rabi’u ya wuce dakin su kai tsaye ya cire rigar ya kwanta saboda gajiyardaya kwaso ga shi abinda ba ka sababa. A take bacci barawo ya sace shi, kiran salla ne ya farkar dashi Ya tashi a gigice saboda rashin ganin Saude ya fita tsakar gidan amma batanan abinda batataBa ba yanufi kofar dakin laure ya duka daga bakin qofar muryarshi da alamun rudani yace, “Inna ko $aude tadawo?” Laure ta watsa masa wani kallo kafin tace,“Ban saniba tana indata dawo da baka gantaba Ko kudice dazan Goyata?” Gaban Rabi’u ya yi mummunar fad'uwa hankalinsa yayi masifar tashi.To inatake? “Shin ba zaka tafi kanemota baneba zakatsaya kallon jama’a ne?” Muryar mahaifinsu ta katse masa dogon tunanin dayake ciki Ya yunkura ya mike jikinsa asanyaye yafice.'shin ta inama zai fara neman nata ne? Wayyo Allah Ya Ubangiji kada kajarabeni da abinda bazan iya daukabaYaAllah kasa duk inda Saude take tana hannu nagari. Abinda yake fada kenan azuciyarsa,yayanka yayi hanyar rewa Tasha dukda yanada yaqinin zuwa yanxu an rufe tashar amman babu yaddah zaiyi yanashan kwanar layin nasu ya Ci karo da jama’a wani na rungume da Saude wai za,a kaita gidan mai unguwa. Hankalin Rabi'u ya yi masifar tashi ya tsare su yanavfadin qanwarsa ce su kai masa ‘yan tambayoyin da za su yi masa sannan suka ba shi ita ya nufo gida hankali tashe tun a hanya yake ta faman rusar kuka don shi duk a tunaninsa mutuwa ta yl. , Yana shiga gidan ke Laure ta zabauro masa wai ina kayan tallarta, ita ta sana’aarta take ma. Wani_abu ya zowa Rabi’u iya wuya yanda ko kadan mahaifinsu bai damu da halin da Sauden ke ciki ba. Ya shimfideta a tsakar gida jikinsa na rawa ya nufi rijiya ya janyo ruwa ya shiga Sheqa mata, cikin ikon Allah ta farfado m har tana magana, ko motsin kirki ba ta yi, saidai sambatun datake tyi iri irin wanda ya zare hankali Rabi’u yana kuka ya nufi dakin mahaifin nasu ya durqusa gabansa yana fadin, “Don Allah Baba ka ba ni kudi in kai ta asibiti ta farfado, amma ba ta motsi kada ta mutu.’ Malam Bala ya ce ‘Rabi’ u ta mutu mana, ai ranta ba a hannuna yake ba, ban da ikon sanyawa ta rayu haka kuma banda ikon hanata kaxo sai wani rawar jiki kake akan ciwon d bai taka kara ya karyba Don nasan baxai wuce bugun iskaba da masassara Ka je ka kira Malam Maidala yaxo ya yi mata rukiya ga naira hamsin ka siyo panado ka bata ta sha.‘ Ya wurga masa kudin. “Tashi ka tafi.” Rabi’u ya mike yana jujjuya kudin a hannunsa wani sabon kuka ya Kara kwace masa ya sa kai ya fita, kamar yanda ya ce haka ya je ya kira Malamin yazo ya dubeta shida kan'shi yace ba iskabane zafin zazza6i ne, don haka a kai ta asibiti. Ya dawo ya sanar da mahaifin nasu, a lokaicn har ya kwanta. _ Don haka a fusace ya tashi yana fadar, Wai menene zaka dame ni da zarya shin wai nina dora mata ciwon ne k0 k0 me?” Rabi’ u yace, “Kayi hakuri Baba, Malam ya ce ciwonta na asibiti ne zazzaBi ne mai zafl.” Yace ‘To shine har saika tadani ina baccina, tunda yafada maka zazzabine kaje katsinko ganyen dalbejiya kai mata surace mana, haba ban san matsawa wallahi.” Rabi’u ya mike jiki a sanyaye hawaye na faman zarya a kuncinsa, tsanar mahaifin nasu ta qara mamaye masa zuciya gaba daya. A lokacin karfe sha daya na dare ne haka ya shiga dakin ya dauki Saude a kafada ya tafi chemist da ita. A lokacin Bala mai allura‘ na' qoqarin rufe , chemist din nasa Rabi’u ya dube shi, ‘Don Allah Malam Bala marar lafiya na kawo na ga kana kokarin tashi.’ Mal. Bala ya waigo yana kallonsa kafin ya ce, “Ashshal Waye ba shi da lafiyar?” Ya ce ‘Wallahi Saude ce tun dazu zazzabi ya kamata hadda su suma, yanzu haka k0 motsi bata ”yi Bala mai chemist yace, “Ashsha! Ai kasan ni ban san sunansu na gaskiya ba, ‘Yar Baba k0 “Yar Tallar wacce cikinsu?” Rabi’u ya' dan ja fasali kafin ya ce ‘Yar tallar dai’ Bala mai allura ya ce ‘Ikon Allah, saukota na ganta.’ Rabi’u ya sauko ta yana nuna masa har a lokacin sambatun ta kawai take. Bala mai chemist ya ce “Ai wannan zafin zazzbine wallahi maleria, wato zazzaBin cizon sauro, gaskiya Rabi’u ku gaggauta kai ta asibiti don Wannan ciwon bana zama bane hadari ne babba dole ana buKatar likitoci. kamar biyu zuwa uku a kanta.’. Hankalin Rabi’u ya Kara masifar tashi ga shi bai ajiye ba, bai ba wani ajiya ba, nairarsa dari biyar ta aikin yau, ita kadai yasan ya mallaka sai hamsin dinda Baba ya ba shi. Ya dubi Bala mai allura yana fadar. “Don Allah Malam idan da akwai taimakon da zakamin ka taimaka min ai mata kafin zuwa safe na ga abin da Allah zai yi, amma wallahi yanzu ban da halin tafiya asibiti ” Bala mai allura ya ce‘Ai babu wani taimakon da zan iyayi yanzu anan nafada maka hatsarine a wurina na duba ta cikin wannan yanayi da take ciki.’ Rabi’u ya kifa kansa a ka Saude yasa wani irin kuka mai ban tausayi, ya zai yi da rayuwarsa tunda baidashi baidawada zai taimakamasa yana kallo rayuwar ‘yar uwarsa za ta salwanta, saboda kawai ba shi da shi... Kuka yake sosai. Sosai kamar ransa zai fita I will be back in no time Via Dboy👍🏻 [1/15, 6:40 PM] I love my mum: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚 [12:17PM, 02/02/2017] 🙆🏼‍♂@lh@ji🙆🏼‍♂: [1/17, 7:43 AM] A A Dboy: *YAR TALLA* *CHAPTER 9* We miss 1page cours d page is damage I cnt c writting clearly Rabiu ya shiga mazaunin direba ya ja suka tafi. Kai tsaye Federal Medical Center suka nufa a lokacin har shabiyu na dare,ne da ‘yan mintuna. Suna zuwa kuwa abin kada ma'aikacin wurin cikin gaggawa aka wuce da ita Emagcncy Room da ita, Malam Bala mai allura ya tsaya sai da ya kammala masa duk wasu ‘yan shige da ficen daziayi masa sannan yayi masa sallama ya tafl office don dama aikin dare yake. Rabi’u ya dinga zabga masa godiya kamar zai kwanta masa, abin har ya soma bashi kunya. ‘ A asibitin suka kwana washe garida safe likitan daya dubata yaace yakoma ya tawo da ‘yar uwarta mace ta kula da ita, hankalin Rabi’u ya tashi ya ce, “Ai bata da ‘yar uwa.’ Likitan ya ceto gaskiya ba zaiyiwu zamanka wurin jinyaba dole saika samu mace yar uwarta koma wacece wadda zatayi jinyarta A dole Rabi’u ya mike ya tafi zuciyarsa na faman suya, ya nufi gida a qafa a lokacin karfe takwas 'na safe Yana isa gidan ya samu Babansu a gidan ya duqa ya gaisheshi yawaigo cikin Bacci yana kallonsa kafin ya ce Rabi’u ka cika dan kanka yanzu gidan uwar wa ka kwana?” . ya sassauta murya kafinn ya ce “Na kai Saude Chemist ne daga nan mai Chemist din ya ce yana taba ta yace wai dole sai an kai ta asibiti shine ya daukemu yakaimu asibin acan:aka kwantarda ita,yanzu haka ita tana can asibitin tama samu sauqi sosai, don har tana iya gane wanda ke kanta‘. Yanxu likitanne ya ce in'zo in taho da ‘yar uwarta mace, wadda za ta yi jinyarta.” Kafin Malam yace wani inna laure ta hankado labule ta fito tana fadar. “Ai k0 sai ka nemi ‘yar iskarda zata zauna zaman jinyar badai laure ba donni hangar asibitinma banabi ballantana in wuce ta gefensa, miyau wannan ban iya hadiya cikin asibiti, don haka ma kar ku sake ku sani a lissafi Malam ya ja ihsali kafin ya ce ‘Ni duk ba ma wannan ba Laure, shin kudin da za a biya a asibi'n ubanwa ya ajiye zaibada nidai banidasu kuma ban ajiye ba, nan na ce kar ka kai ta asibitin nan ammadayake kaibadan arzikibane shine saida kakaita don kanunamini iyakata. Totundakai dankankane basai kayi yaddakasoba,‘nidai kaga tafiya ta kwandala ban maganinta.’ Yana gama fada ya juya ya fice Laure ma ta hankada labule ta shige dakinta ta bar shi nan. Rabi’u ya mike jikinsa amace ya rasa inda zai saka Kansa haka yayita gararamba a gari data qarshe da yaga vashi da mafita Dole ya juya ya koma asibitin Lokacin da rabiu ya gama koro masa bayani Mamaki ya kama, likita yace ynxu yarinya kamar Saude a kasa samun wanda zaiyi Jinyarta ‘ba shi da mafita haka ya. Rubuta masu sallama aka ba shi allurai da magunguna Ta ji sauki sosai, dukda ba Karfi jikinta sosai. Suna dawowa gidan laure ta watsar dasu watsar k0 kallonsu batayiba Rabi‘u ya dauki naira hamsin ya fita ya siyo mata shinkafa da wake da mai da yaji ya zauna ya ba ta ta ci sosai, .sannan ya ba ta magungunanta ta sha, ba ta jima ba bacci barawo ya sure ta, shi ma ya raba gefe ya kwanta Washe gari tunda safe laure ta hau tuyar waina markadan ma da kanta ta kai shi, mamaki ya kama Rabi’u to wa take tunanin zai daukar mata tallar wainar? Ba ta tankawa kowa ba har sai da ta gama tuyar . Wainar ta daddaura sannn ta mike ta nufi dakin da suke Saude ce kawai zaune tana shan ruwan shayi da biredin da Rabi’u ya siyo mata a waje. Laure ta tabe baki kafin ta ce, “Aikin banza harara cikin duhu da kuwa cikin babbar riga, saiki tashi ga tallar waina’ can na jiran ki idan kin gama Saude ta yi saurin dagowa tana kallonta idonta ya kaWo kwalla Laure ta daka mata tsawa. Ko ba za ki tallar ba ne kika noqe kika kwalala min“ Wasu ‘yan iskan idanuwan ki can masu kama” ; Dana kwarkwata, maza ki taso ke nake jira.” Ta saki labulan ta juya ta yi gaba abin ta. Hawayen da suka taru a idanuwan Saude suka ziraro suka biyo kuncinta take shayin ya fita daga ranta ta ajiye ta mike ta flto har a lokacin babu Karfi ajikinta, donji take tamkar iska za ta dauke ta. Inna Laure ta miko mata tiren wainar tana fadar, “Ga ta nan ta Murtala goma ce ki kawo min kudina cas ban ceki Batar min da k0 sile biyar ba.’ Saude ta duqa ta dauka tana sharar kwalla, Rabi’u daya shigo ya sauke jarkar ruwan da ke kansa yana kallonta jikinsa a sanyaye ya ce, “Ina kuma zakije keda bakida lafiya?" , Laure ta hayayyako masa -“To marar kunya ga kai ga fata ai ba a tambayar me aka yanka k0 idon ka bai gane maka talla ta dauka bane?” Rabi’u ya hadiye abin da ya zo masa iya wuya ' kafin ya ce “A gaskiya daukar alhakin zai yi yawa, yarinya daga sallamo ta daga asibiti jiya, yau kuma a daura mata talla gaskiya da sake ai ba ita kadai ba ce diya cikin gidan nan ba, ita ma ‘Yar Baban ai ta isa tallar a dora mata mana k0 k0 ita kadai ce diya, amfanin nawa ake mata a cikin kudin tallar?” “Eh lallai wuyan ka ya isa yanka, tabbas wato kai nan har girman ka ya kai ka fada mini magana. To ubanka ma ya yi kadan ballantana kai, uwarku ma ba ta yi min wahalar kawarwa ba ballantana kai qaramin kwaro tallar za ta tafi idan ta tafi ka hanata Rabi’ u ya ce, ‘In dai cin zalin dan wani wani abun a zo a gani ne ai sai a yi mu gani idan abun na tsakani da Allah ne ni me yasa ba za ki dora mini tallar ba sai ita mace?” Ta zaburo ta yo kansa tana fadar, “Kai kar fa ka yi min rashin kunya kaji bari ganin ka ka kawo Karfi wallahi hakan ba zai hana in dake ka ba, wallahi wancan faskaren zan sa maka dan iska kawai. Bari uban naka ya zo in ji idan shi ya sanya ka kai min rashin kunya idan kuma wani ke zoga ka sai in ji.” Rabi’u ya qure ta yana fadar, “Ai wallahi na gama zama wata Katuwa ta dake ni yanzu tunda na gane abun duk rashin kunya ne dan an ga babu uwarmu a gida don haka nima zagewa zan yi yanzu mutum na dukana ina Bare masa kai sai dai a kwashe shi a sume wallahi.’ Laure ta saki baki tana kallonsa cike da mamaki, yaushe yaron nan ya zama haka? Yaushe ya koyi ' rashin kunya irin wannan? Lallai dole ta dauki ' mummunan mataki a kansa. Bayan sati daya da sallamar Saude daga asibiti da maraice ta dawo daga tallan alala, tana ajiye tiren Inna Laure ta mika mata tsintsiya tana fadar, “Maza ki share gidan nan ki dora sanwar tuwo da miya ki yi Wanke-wanke.” Saude ta amsa da , ta dauki tsintsiyar ta share gidan tas sannan ta dora sanwar tuwon ta tafi tana wanke-wanke, Rabi’ u ya yo sallama ya shigo, Saude ta bi shi da kallo duk ya yi gaje-gaje yana rike da bakar leda Saude ta yi masa sannu da zuwa ya amsa cike da kulawa, sannan ya wuce ya shiga dakinsu. Sannu a hankali Saude ta kammala ayyukanta saboda ciwon qirjin da ya addabe ta. ‘ Ta nufi dakinsu a gajiye ta kwanta tana faman numfarfashi da kyar, Rabi’u ya tsura mata idanuwa gaban shi ya yi wata masifar faduwa ganin yanda alamun girma suka fara tsirowa daga jikinta, tabbas girma ya fara zuwar mata ya zame masa wajibi ya zage ya nemi kudi ya hadiye wani yawu mai daci wanda ya tsaya masa a makoshi, sannan ya janyo ledar da ya shigo da ita ya miqa mata, ta amsa, ta mike tana dubawa. * Kayan makaranta ne riga da wando da hijabi, dadi ya kama Saude cike da zumudi ta ce, “Yaya nawa ne?” Kai kawai ya daga mata ta mike cikin zumudi za sanya Rabi’u yayi saurin hanata yana fadar, ‘Kar kisa karki sakasuyanzu.”Tazumburo baki tana fadar “Kaidon Allah gwadawa fanyi Harareta kafin yace. “Ba dai anan ba, idan gwadawa zakiyi fita tsakar gida sai ki gwada.’ Ta narke masa. “Kai don Allah Yaya saboda me?” Rabi’u ya zuba mata ido kafin ya ce ‘Wai ke ba ki san kin girma ba ne wai har yanzu ?” Saude ta yi saurin kallon kanta kafin ta ce, “Ni din na girma Yaya?” Ya ja wani dan gajeran tsaki ya koma ya kwanta ya juya mata baya. Saudc ta zauna kusa da shi tana fadar, “To yaushe za ka kai ni makarantar Yaya?” “Gobe da safe.” Ya ba ta amsa ba tare da ya kalle ta ba. Ta yi wani ihun murna. ta kwanta gefen shi kanta saman kafadar shi tana fadar. “Wallahi harna qagara goben ta yi Yaya, in gan ni a makaranta. To wai kuma Yaya me za a koya mini?” Rabi’u ya juyo Ya ja kunnenta yana fadar, “To sarkin tambaya, bari in kin je kya gani, barci nakeji karki matsa mini da tambaya ki Juya ki kwanta kawai Saude tace Ai ba ka ci abincin ka ba.” Jeki“ ‘ dauko idan ta gama . . kwasan nina koshi Ta dan zuba masa ido ‘To me kaci Ya zaburo mata, “Kin ga tashi Kije kin. ji, ban san yawan tambaya.’ ldonta ya ciko da hawaye, muryarta a sanyaye tace “To yanzu da yunwa za ka kwana kenan'?" “Oh! Kaina Saude na ci abinci, naci abinci naci abinci a waje haba." Ta yi wani takaitaccen murmushi sannan ta juya ta fita. A bakin murhu ta iske nasu abkin murhu a Wata danéakaiiiyw lmga wadda ta gaji d1 Salan gandi taga tuwon wanda bai wuce cin mutum daya ba, shi ma ba dan ya qoshi ba. Haka Saude ta ta koma daki ta cinye tas sannan ta fita ta maida kwanon ta dauro alwala ta dawo daki ta yi salla sannan ta kwanta Washe gari tunda safe Saude ta yi Shara ta kai markade, ta dawo sannan ta debo ruwa cikin rijiya ta rafta tayi wankanta babu soso babu sabulu, ‘ tana gamawa ta fito ta nufl dakinsu Laure na kallonta bata dai tanka mata ba, sai Ma tsakin da take ta faman ja akai akai. Saude ta dauki kayanta ta sanya sababbi tas sun mata kyau sosai, Rabi u da ya dawo daga dibar ruwansa ya shigo yana kallonta cike da sha’awa yace“tace yya nayi kyau Yace eh mana Saude ai ke kyakkyawa ce ”Ta kada kai tana fadar, “Amma kullum mutane sai su rinka ce mini Kazama mummuna har yaran unguwar nan wai ba za su yi kawance da niba, sai dai da ‘Yar Baba, wai ita ce Kawarsu mai tsabta, ba ‘yar talla ba, amma Yaya ai ka ce ina da kyau k0?” Tausayinta ya kara kama Rabi’u, yaji tamkar zai mata kuka ya daga mata kai alamar eh, babu alamar kuzari a jikinsa. Saude ta sanya takalmanta sannan ta mike ta dube shi. “Taso mu jc Yaya, kada rana ta yi.” _ ‘Rabi’u ya mike suka fita yana riqe da hannunta zuciyarsa cike da tausayawa. Laure da ke zaune saman kujera ‘yar tsugunne gaban murhu tana qukkulla waina, ta ga sun fito, ba ta san lokacin da ta ture tiren ba ta tashi tsaye idonta a warwaje tana fadar. “Me nake gani ni Laure, me zan gani haka?” Rabi’u ya kafa mata idanuwansa kafin ya ce “Makaranta zan kai ta baki gani ne kayan makaranta ne a jikinta." ‘ ' Laure ta ce, “Karya ka ke wallahi idan ka ga Saude ta yi makaranta to ba na numfashi ne, don har abada ba za ku taBa morar‘ rayuwar duniya ba, in dai ina raye kuma Saude talla za ta yi min ban yi niyar ta yi karatun bokon ba, wato abun ma ya zama gasa kenan, tunda an sa ‘Yar Baba kai ma bari ka kulla ka sanya ta. To ba ka isa ba wallahi ka yi kadan ka nuna mini iyakata ban ga bayan ka ba kowaye kai wallahi.” Rabi’u ya gifta zai wuce yana fadar, “To sai ki gayawa kaji dan su tantabaru tashi suke." Laure ta sa hannu ta riko Saude da qarfi tana fadar qarya ka ke wallahi ba za ka kai ta makarantar ba talla za ta yi min yau sai na ga qarshen danyan kanka ba dai kai dan rashin kunya ba ne. Rabi’u ya ce “Sakar ta kar ki karya ta, tunda ba ke ki ka haife ta. ba, ba ki san ciwon taba.” Laure ta ce, “Aikin banza ruwa biyun k0 ka manta nan aka karma uwarku da kwarto cikin daki?’ Ai dama shi dan zina har abada bai ganin kowa da mutunci, dan iska dan asara.” Bakin ciki ya cika Rabi’u zuciya ta zo masa iya wuya cikin Bacin rai ya ce ‘Wallahi ni ba dan asara ba ne kuma uwarmu ba mazinaciya ba ce face ke ce babbar la’ananniyar da ki ka tura mata sharri, kuma insha Allahu a sauna sai sharrinki ya qare Tun kafin ya rufe bakivLaure ta share shi da wani gigitaccen mari mai kummatar da qaramin yaro cikin zafin nama Rabi’u ya. dago Zai shara mata nasa marin ya ji an rike hannunsa, cikin Bacin rai Malam Bala ya shiga dauke shi da nashi marin hagu da dama. , Rabi‘u ya dafe kunci da baki wanda tuni har ya fashe jini ya kwararo cikin qunar zuciya Malam ke Lol ya abin ya kene mu kubiyonii donjin ci gaba sannan idan naga comment da yawa dan anjima xan iya sake muku post. [1/17, 7:44 AM] A A Dboy: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚 [1/17, 7:48 AM] A A Dboy: *YAR TALLA* *CHAPTER 10* Dan iska wulakantacce Allah ya tsine maka Rabi’u ban ga amfanin rayuwar ka ba. Yanzu uwar taka ce za ta mare ka har ka daga hannu za ka rama, don kana marar kunya lalatacce. To bari in tsine maka ka je can ka Karasa lalacewar ka tunda kai din ba dan mutunci ba ne, yaro jinin sunna ya yi haka alhalin kana dan iska kishiyar uwa ba uwarka ba ce, k0 k0 hudubar da uwar taka ta tafi ta bar maka kenan? In ban da na shigo da yanzu marinta zakai da gaske, « don kana marar kunya.” Laure ta sa kukan munafurci tana fadin, “Kuma Malam wai kan abin da bai taka kara ya karya ba yaron nan ya dinga marina har yana fadar shi zai zamo ajalina wai dan kawai na ce bai kamata ya sanya Saude makaranta ba da kan shi ya bari har ka zo ya yi maka magana. Shi kenan yaron nan ya shiga zagina ta uwa ta uba wai har: yana fadar shi zai zamo ajalina....” Ta Kara fashewa da kuka, ‘Wallahi Malam bazan iya zama ba, yaron nan ya kashe ni a banza a woli ba, wallahi tafiya ta zan yi in bar masa gidansu tunda yana da gaskiya gidan ubansa ne Malam ya ce ‘Da alla bar' wannan magamar Laure kar ma ki ja yaron nan ya Kara raina ki gidan ubansa da wa ya fada masa, ina uban nasu yake nan yaranda akaimin wuru-aka manna min tsiya~ Ya juya yana kallon Saude da Rabi’u yana fadar, “Baku sanibane koba a taba fadi maku bane kama uwarku da kwarto Kiri-kiri akayi iyayenta suka koreta dalili kenan tabarku tatafi yawon karuwanci yace wlh kukaci gaba da takuramin ko matata a shirye nake dana koreku daga gidannan Rabi’ u ya riqo hannun Saude suka nufi dakinsu suna: shiga ya jingina kansa da bangon daki yana wani irin kuka maicin zuciya. Itakanta Sauden kukan take yanzutafara fahimtar suwayesu dakuma matsayinsu acikin gidan duk da qarancin shekarunta hakan bai hana ta fahimci dalilin tsanar da ake masu ba tasa hannunta ta riko hannun Rabi’ u tana fadar “Wai Yaya da gaske ne abin da aka fada? Yaya da gaske mahaifiyarmu karuwa ce mu ma bamu da iyaye?” Rabiu: ya waigo yana kallonta hawaye sun gama bata masa fuska ya Kara riko hannunta yana girgiza Ya girgiza mata kai cikin muryar kuka ya ce, “Karki soma wannan tunanin Saude nasan kowacece mahaifiyarmu don ni na rayu da ita :nasan kowace ce ita, ita din mutuniyar kirki ce knma ‘yar manyan mutane. Saude ta ce, “Yaya idan har mahaiflyarmu mutuniyar kirki ce to me yasa ta watsar da mu ‘yan uwanta suka guje mu ta bar mu mu kadai mina rayuwa cikin qunci da wahalar rayuwa?” Rabi’n ya ce, “Saude mahaiflyarmu na son mu kamar yanda kowace uwa ke san danta, dole ce ta dolece ta rabata damu badan tasoba kiyi mata uzuri Saude duk qunci da wahalar da ki ke ciki bai kai wanda ita . ta shiga ba.” . Saude ta ce, “To,amma ” Ya daga mata hannu da sauri alamar ba ya san jin abin da zata fada, sannan ya juya ya fice ya bar mata dakin Wani kuka ya qara zuwar mata ta kwanta ta ci gaba kukan abinta. tanajin zuciyarta. na suyakamar garwashi,yamaza ai Rabi’u yace mata qarya ne abin da su Baba da Laure suka fada a , kan mahaifiyarsu alhalin almomi sun nuna gaskiyar Shin idan har mahaifiyarsu tana son su me yasa ‘ ta tafi ta barsu babu k0 waiwaye? Shin idan mahaifiyarsu mutuniyar kirki ce me yasa ‘yan uwanta suka kore ta? Shin idan har ta tsare kanta me Zaisa mahaifinsu ya zargeta harya kyamacesu da zama yayansa? Tambayoyin data jeroma kanta kenàn Wanda bata da mai amsa mata su 1 page is missing am sorry ya farkar da ita, don haka ta dauki kayan ta koma gida babu cinikin ko sisi. K0 da ta maida alalen Laure ta yi ta masifa, tun fadar, “Na lura mugunta ce kawai yau ki ka sa mini kuma ‘yar iska ke zata karewa a je min kayana ki.’ wuce Saude ta samu ta ajiye kayan ta yi daki da hanzarinta, don dama barci ne fal a cikin idonta ta samu ta kada kafadunta ta kwanta, wani bacci mai nauyi k0 ya yi awon gaba da ita. Inna Laure ba ta ba su alalan ba sai da gari ya ' waye a lokacin ta lalace sannan ta miqo masu ita waisu karya da ita. Rabi‘u ya kai ya zubar ya ciro kudi ya siyo masu koko da qosai suka karya, sannan ya tafi wurin aikinsa, Saude kuma ta tafi talla. Da yamma likis Saude ta dawo daga talla, Laure ta ba ta dakan kunnun jego wanda ta karBo a makotansu da akai haihuwa, kawai saboda neman suna, shishshigi cusa kai ba kwarjini. Saude na cikin dakan ta debi gyalenta ta fice ita da ‘yarta. Suna fita Saude ta ajiye dakan ta kwanta bakin turmin tana hutawa a lokacin Rabi’u ya dawo daga ‘ wurin aikinsa shi ma ya kwaso gajiyarsa ya zauna kusa da ita cikeda tausayawa ya ce, “Sannu ya jikin na ki ne?" Saudc ta ce, “Da sauqi sai dai ciwon kirjin da ya matsa mini yanzu." Rabi‘u ya ce, “Allah ya sauwaqe karbi wannan bari inje chemist na siya miki magani." . Saude tayi saurin sa hannu ta karBa tana: dubawa leda ce baqa guda sai farar leda guda. Ta bude: soyayyar doya ce da kwai a ciki, dadi ya kama ta yauzu: itce zata ci doya da kwai. wanda tunda take a duniya bata taba cinta ba. Ta yi saurin kallonsa da Washe fuskarta tana fadar. “Wayya Allah na Yaya, yau zan ci doya, tunda nake fa ban taBa cin taba wallahi.” Rabi‘u ya yi murmushi yana kallon ta, sai da ya tashi zaibar wurin sannan ta bude baqar ledar. Ta yi wani tsalle ta tashi tana fadar. “Wayyo dadi, Yaya kayan kwalliyana ne?" Ya daga mata gira, ta buga wani uban tsalle ta dafa shi taba fadar. “Wayyo Yayana na gode kwarai wallahi dama ina so nima in rinka lrin kwalliyar su ‘Yar Baba, inyi; kyau k0 Yaya?” Ya daga mata kai alamar eh, tasa dariya ta ciro madubi tana kallon kanta tana ta faman gwalegwalen idanuwa. “Kai Yaya wai dama haka nake, Yaya kalli idanuwana ‘yan qanana-qanana, yanzu kuma Yaya wannan bakin nawa har cokali yana iya shiga ciki?" Ya buga hannun shi saman tafin hannun shi alamar oho tayi daria Tace yaya ji haqorina har yayi tsaho da yawa' Rabl'u ya kwace madubin yana fadar, “Ke tashi kiyi aikinki saude ta shagwabe masa “kai Yaya don Allah ka bari in gani wallahi ban gama ganiba Rabiu ya saka madubin cikin ledar yana fadar, “Idan kin shigo dakin kin gani ai naki ne bana: wani ba, kin ta gani harki gaji. Dauki doyarki ki ci kinji Ta ture doyar can tace tana turje-turjen qafafuwa, Rabi’u ya dauki doyar yana fadar, “bazakici ciba ke nan to bari in cinye abuna dama ba qoshi na yi ba rago miki.” nayi Saude ta yi saurin riqo rigar shi tana fadar. ‘Yi haquri' don Allah ka ba ni :na daina.‘ Rabi’u ya sakar mata ya wuce yana dariya, ta zauna tana ci tana lumshe ido har ta gama, sannan ta mike ta ci gaba da dakan yajinta iya qarfinta. Ta samu ta gama, sannan ta wucc daki ta janyo kayan kwalliyan tana duddubawa, ta zauna ta manne fuskarta radau da kwalliya abin kada sabon shiga, duk ta yi wa fuskarta dame-dame man da kwalli Washe gari ma tana gama sallar Asuba ta janyo kayan kwalliyar ta hau ranbadawa a fuska, shi dai Rabi’u yana zaune yana kallon ikon Allah. Tana gamawa ta mike ta nufo shi tana fadar. “Yaya duba ka gani wai nayi kyau?“ Rabi‘u ya yi wani takaitaccen murmushi kafin yace. “Sosaima, don sai yanxu na Kara tabbatar da kamar ki da Mamar mu daya, sak kamar an tsaga kara wallahi.” ' Saude ta gyara zama tana fadar, ‘Wai Yaya don Allah ya Mamarmu take, baqa ce k0 fara k0 doguwa k0 gajeriya?" Rabi‘u ya yi murmushi kafin ya ce “Mamanmu fara CE fat don har ta fiki . kuma doguwa ce mai Dan jiki kadan, yadda. Kika ganki haka take.” Ta ce “To yaya tana son mu?" Rabi‘u yace, “Sosai ma kuwa don ranar da zata rabu damu tasha kuka fitar hankali keko saida a kai da gaske sannan aka Banbare ki daga jikinta kina ta tsalla ihu a lokacm kina da shekara shida a duniya.” Saude ta yi wani murmushi kafin ta ce “To Yaya yanzu tana ina?” . Ya girgiza mata kai yam: fadar, “Allahu a‘alamu." Ta dan yi jim kafin ta ce “To Yata tafitabar mu?” me akai mata? Kafin ya kai ga ba ta amsa Inna Laure ta hankado labule tana fadar, “To tif da taya ‘ talla sai a tashi a tafi tallah hakanan Saude ta mike cike da alamun gajiyawa a fuskarta ta fice ba dan ta so ba. Ta tafi tallar da ta zame mata waki’a farilla. Da daddare ciwon mara hade da ciwon ciki mai tsanani ya rufe Saude tamkar ba za ta kai ba, ta ringa murkususu a tsakar daki ita daya a lokacin Rabi’u bai dawo ba. Laure na jin ta, amma k0 ta kula ta kanta. Haka Rabi’u ya dawo ya same ta hankalin shi ya yi masifar tashi, ya juya ya koma ya siyo mata magani ya ba ta, amma a banza, sumanta biyu cikin dare. Yanda suka ga rana haka suka ga dare daga ita sai Rabi’u cikin daki babu wanda ya leqo balle ya ji halin da take ciki, don Malam ma bai san abin da suke ciki ba. Cikin ikon Allah ana kiran sallar Asuba, jini ya zowa Saude, a take kuma ciwon marar ya dauke, don haka ko motsi ba ta iya yi ba daga inda take ta kwanta sai bacci mai nauyi ya dauke ta. Sai a lokacin Rabi’u ya samu kwanciyar hankali ya tisa ta a gaba ya rabka uban tagumi yana kallonta hawaye masu zafi suna biyo kuncinsa zuciyarsa ta cika da tausayinta, har gari ya fara haske sannan ya “farka ya mike ya je ya yi sallah ya dawo ya samu ya dan kwanta saboda baccin dake cike cikin ldanuwansa. Cikin barcinsa ya ji tamkar ana rabka sallallami, Rabi u ya bude idanuwansa da su kai masa wani irin nauyi saboda bacci, ya ga Inna Laure na fadar “Malam! Malamll zo ka ganewa idon ka ikon Allah Malam zo ka gani.” Malam Bala ya fito daga dakinsa yana fadar, “Ni ko kinsan bansan irin wannan kiran natashin ”hankali.” Laure ta qara hankade labulen dakin sosai tana fadar, “Ai wannan idan ma akwai abin da yafi tashin hankali to shi ne dubi yarinyar nan Saude kalli siket dinta.” Malam ya qara tura kai cikin dakin tsawon wasu ‘yan sakanni kafin ya ce ‘Kamar jini nake gani Laure?” Laure ta turo wuya gaba tana fadar, “To duba da kyau jini ne daman tun jiya nake jin ihun yarinyar nan na dauka wani iya shege ne ashe yaron nan ne ya haike mata.” Gaban Malam ya yi wata mummunar faduwa ya juya yana kallonta a razane bakinsa na fadar, “Ki bari don girman Allah.” Laure tabe baki tana fadar, “Ga alama nan.” Idanuwan Rabi’u suka yo waje don sai a lokacin ya lura da yanda jini ya Bata siket din Saude sosai kamar anyi Barin manja a jikinta abin kaga kaya masu haske da santsi, hankalin shi ya yi masifar dugunzuma. Malam ya ce “Lallai kam yaran nan ka cika la’anannen Allah yau kam sai na gwada maka irin nawa rashin imanin ni za ka jawa abun kunya, ka yiwa qanwarka fyadeee dan iskan to wlh daga rana irin tayau ka gama haikewa ‘ya’yan jama’a.” Ya juya a zafafe sai ga shi ya janyo wani qaton faskare, Laure ta riqe tana fadar. A,a don Allh kayi haquri Malam karka kashe shi.” Malam ya goce yana fadar, ‘Wallahi yau sai dai akwashi gawarsa cikin gidannan inya so nima a kashi yayi kukan kura gamida yin kansa da faskaren Wooooohoho jama,a wai ya abin yakene mu kubiyo ni donjin yaddah wannan taqaddama zataci gaba da kayawaaaaaa [1/17, 7:49 AM] A A Dboy: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚 [12:17PM, 02/02/2017] 🙆🏼‍♂@lh@ji🙆🏼‍♂: [1/17, 7:54 AM] A A Dboy: *YAR TALLA* *CHAPTER 11* ya janyo wani qaton faskare laure ta riqe tana fadar. a a dan Allah ka yi hakuri Malam kar ka kashe shi.” ° Malam ya goce yana fadar, ‘Wallahi yau sai dai akwashi gawa'rsa cikin gidannan inyaso nima a kashe ni.” Ya nausa cikin dakin ya hau Rabi’u da duka kamar Wani zautacce, bakin ciki, mamaki da tsantsar tashin hankali su suka hana Rabi'u komai saidai kare kansa da yake, sai da yaga Malam makasar sa yake: nema sannan ya mike ya yi waje Hayaniyar su ce ta tayar da Saude daga baccin da take, ta tashi sai zazzare idanuwa take, don ita ba ta San abindake faruwaba,taga dai Malam nata faman shan kwalla yana dukan Rabi’u ta tashi itama cike da . tashin hankali kafin ta motsa ‘ Rabi’u ya ruga malam ya bi shi har , “Sai na kashe ka la’anan nan Allah, Allah ya isa tsakanina da kai, wallahi kar in sake ganin ka cikin *gidan nan, kai cikin garin nan ma idan ka bari muka hadu sai na halaka ka munafukin Allah.” Ya juyo ya dawo gidan ya tattara masa ‘yan zummokaransa ya fito kofar gida ya watso su yana fadar, “Ka san inda dare ya yi maka, ka ji na fada maka, Allah ya yi wadaran ka, yasa ka hadu da mummunan hatsarin da za a kasa gane ka, Allah ya wulaqanta ka yanda kai min Allah ya yi maka wanda . ya fi shi, dan iska. Insha Allahu sai ka wulakanta, Allah ya daga maka hakali ya hana nutsuwa a duk inda ka ke” Laure ta fito tana fadar, “Don Allah Malam ka shigo gida haka nan tun'da dai ka kore shi ka ga har ‘ mutane sun fara taruwa.” ' Malam Bala ya dawo gidan ya ci gaba da 'zazzaga masifa tamkar wanda ba ya cikin hankalin shi, Saude dai na kallon su kuka kawai take tamkar ranta zai fita, ga jinin da ya bata mata jiki wanda har a lokacin bai daina zuba ba Ta lallaba ta mike ta saka hijabinta ta fito wajen tana neman Rabi’u can ta hango shi zaune saman dakalin Kofar gidan Malam Akilu mai Rauhanai ya hada kan shi da gwiwa da ‘yan kullin tsummokaransa a gaban shi. Wani sabon kuka ya Kara kwacewa Saude ta nufi inda yake tana kiran sunan shi, Rabi’u ya yi saurin dagowa yana kallonta fuskar shi sharbe-sharbe da hawaYe, ya yi mata nuni da hannu ta Karaso inda yake. ' Saude ta karasa ta durkusa gaban shi ta fashe da 'wani irin kuka mai ban tausayi, tausayin kansu ya kara kama Rabi’u ya samu da kyar ya iya tsaida nasa kukan, muryar shi a dakushe ya soma magana ba tare da hawayen sun daina zuba daga idanuwan shi ba. “Saude kin ga yanda Allah ya yi damu kuma k0? , Ki yi hakuni na san Ubang‘iji na sane da mu ba mancewa ya yi da mu ba, kuma shi ya san yanda zai yi da mu, tashin hankalina Saude a yanzu daya ne ' yanda zan tafi in bar ki ban san a wane hali zan barki ba wace irin rayuwa ce za ki fuskanta bayan bana nan, ban sani ba.” Yasa hannu yana goge hawayensa kafin ya ce, ‘Dole zan tafi', dole zan bar garin nan Saude ki yi hakuri ki rungumi rayuwa a duk yanda ta zo miki kar ki yarda ki sabawa Ubangiji a duk halin da kika tsinci kanki ciki, na dadi k0 kishiyar hakan. Na ‘ san insha Allahu Ubangiji ba zai bar rayuwarki ta lalace ba." ‘ Yasa'hannu cikin aljihunsa ya ciro wasu kudi ‘yan, dari biyar~biyar da alama kudin aikinsa ne ya raba biyu ya miqa mata rabi yana fadar, “Ga. wannanki riqe a hannunki kiyi amfani dasu insha Allahu zaki rinqa samun aikena a duk inda na shiga a fadin duniyar nan.” Ya ajiye mata kudin saman jikinta ya mike yana fadar, “Allah ya hada fuskokin mu da alheri." Saude ta yi saurin miqewa ta riqe shi tana wani irin gunjin kuka mai daga hankali. “Don Allah kada ka tafi ka bar ni Yaya wallahi mutuwa zan yi idan ka tafi Wayyo Yayana!” Ta qara fashewa da wani gunjin kukan. Rabi’u ya dafa ta yana kallon idanuwanta kafin ya ce, “Ki yi haquri Saude ni kaina ba dan na so ba zan tafi inbarkiba,da zaiyiwu da dole dake zantafi, amma ba yanda zan yi ne tunda ke macece amma na yi miki alkawarin duk inda make a duniya ina tare da.... Ya kasa fadar abin da yake son fada saboda kukan da ya kwace masa shi ma. Ya zame hannayenta daga jikinsa yana fadar, “In har kina sona da gaske Saude kada ki sake cewa komai ki juya ki koma gida ni na tafl sai wata rana.” Ya dauki jakar kayansa ya juya yana tafiya yana sharar hawayen da ke zuba daga idanuwanshi kamar an kunna famfo, Saude ta duka a gun tana wani irin gunjin kuka tun iya karfinta. Rabi’u na jin ta amma bai waiwayo ba saboda yanda yake jin zuciyarshi na Barazanar tarwatsewa gaba dayanta ga shi a lokacin ba jama’a da yawa a waje saboda safiya ce sosai. Tunda Saude ta duka ba ta sake tashi a gun ba, tun tana kukanta iya karfinta har muryarta ta disashe. ~ Rana ta soma mutane suka fara fitowa daga gidajensu duk wanda zai wuce sai ya yi mata magana, amma ba ta tashi ba, tana duke cikin Kasa tana' kuka, ba ta ankara ba sai dai taji saukar duka ta ko ina’ tana dagowa ta ga Inna Laure, ta mike ta ‘ kwasa da gudu ta nufi hanyar gida, ita kuma ta raka ta da jifa. ' Tana shiga cikin gidan ma nan ma Malam ya dora mata da na shi dukan yana zaginta tare da yi mata mugun baki. Inna Laure ta shigo babu alamun ' tausayawa“ a fuskarta ita ma ta hau zaginta tana fadin * “’Yar iskar ai ba yau suka fara ba, ai dole ta zauna tana~ta aikinkuka karabata da jin dadinta munafuka.” Ta hankade labule ta shiga daki ta dauko mata wasu tsummokaran kayan ‘Yar Baba wadanda ta gama da su ta watso mata tare da wando da tsumman dunzugu, ta gwada mata yanda za ta sanya sannan ta ‘ dora mata tallar wainar. Haka Saude ta dauki tallar ta tice daga gidan tana matsar kwallah. Haka ta je tallar ta dawo ba taci komai ba, sai kukan da take ta faman yi. Haka ma da rana ta dauki alala ta sake tafiya, ruwa kawai ta iya sha a wurin ranar yau, duk inda ta gifta sai ta ga tamkar za ta ga Yayanta amma k0 mai kama da shi bata gani ba haka ta karaci yawon tallar ta ta dawo da yamma likis. Ta samu Inna Laure da dillaliya suna tsakar gida saman kujera ‘yar tsugunne taya ni gulma suna hirarsu har da shewa. Tana shigowa Laure ta nuna ta da baki tana fadar. “Kin gan ta nan fa dillalliya, wan: ai aikatau ga wannan ai tallar cc kawai ta dacc da ita.” Dillaliya ta ce, “Haba dai a ganin ki dai, amma in da ni ce da wannan wallahi Abuja zan tura ta kawai." Saude ta qula ta gaishe da dillaliyar sannan ta mikawa Inna Laure cinikinta ta mike ta wucc dakinta. Tana jin Inna Laure na fadar, “Hmm! Dillaliya kenan ai ni duk wanda ya ci tuwo da ni miya ya sha, to shi kuwa k0 miyar ma bai sha ba don in fada miki dama cike nake da shi don har na fara tunanin in zuba masa shinkafar Bera a abinci ‘ya ci kawai, sai dai a wayi gari ya yi mushe. Ai in fada miki ina tashi. da Asuba na 'ga yarinyar jinin ya zo mata, ai a take dabara ta fado mini, ni kaina sai da na shiga daki na yi ta dariyar qeta yanda na ga Malam na sharar ‘yar kwalla.” I Duka suka sa shewa suka tafa. Can Saude ta jiyo diilaliya na fadin “Ke wai ba zaki saro gyada ki soya mata ta rinqa zama kofar gida ba na ga sabuwa ta fara shigowa wallahi ciniki za ta yi ta rinKa zama nan kofar gida da daddare.” Laure ta ce “Ai k0 kin kawo shawara bari gobe Talata inje ‘Yar Kutungu da kaina in siyo mai kyau in zo in soya mata Ai shi yasa nake son ki kawata Akwai ki da bada shawara mai kyau. Saude ta lallaBa ta kwanta tana jin zuciyarta na tuquki wasu zafafan hawaye suka rinka biyowa kuncinta ba ta da mai lallashin ta yau dakin ya yi matA bakikkirin, saboda rashin rabin jikinta, Yayanta a cikinsa Sai yanzu ne ta gane marainiya ce ita marar gata, yanzu ta yarda da maganar Yayanta da yake ce mata bata da. gata a. duniya, ba su da kowa sai Allah. Ashe da gaskiyarsa. Ta sake rushewa da wani sabon kukan lokacin da ta tuna da lokacin da ya dawo daga aiki jiya ya kawo mata kayan kwalliya. * Ta tuna da irin yanda yake lallashinta idan ya ga ta shiga damuwa duk ~ yanda zaiyi sai ya yi ya tsaida hawayen nata, ga shi yanzu baya nan. Tabbas ta rasa gata a duniya ta rasa jigon rayuwarta. don tana ji a jikinta da wuya. idan za ‘ tasake ganinsa tunda shi kan shi baisan inda za shi ba yanzu, wala ya mutu k0 ya yi rai. Shin k0 yana a wane hali yanzun ma? “Wai k0 ba da ke nake ba ne Saude kina ji ina ta faman kiran ki?” Saude ta jiyo muryar Laure, don haka ta zabura ta mike ta goge hawayenta ta yo tsakar gidan a lokacin dillaliya ta tafi Laure ta watsa mata harara kafin ta ce, “’Yar iska duk uban me kike ina kiran ki kin yi min shiru?” Saude ta yi shiru tana kallon yatsun qafarta hawayen da suka taru a idanuwanta suna diga qasa, Laure ta ja tsaki tana fadin. “Ke dai kya kai su in kaya ne wuce ki ki dora mini sanwar tuwo, idan kin dora ki zo ga kayan wankina can na jika ki wanke mini su.” Saude ta yi saurin dagowa ta kalle ta, Laure ta ce, “Bakallona zakiba cewa zakiyi bazakiba kawai sai in san kin isa.” Saude ta juya ta wuce jikinta amace, saboda ita dai ba ta taba yin wanki ba, don kayanta ma kale daya ne, duk wani wankin gidan Rabi’u ne ke yinsa. To ta inn ma za ta fara? Ba ta da zabin da ya wuce ta dora sanwar sannan ta wuce bakin magudanar ruwa ta ci gaba da cuda kayan Sai da ta yi da gaske sannan ta samu ta gama aiyukanta saboda ciwon qirjinta da ya soma taso mata ga mararta da ta kulle da bayanta, ta kwanta tana faman numfarfashi. Rayuwa ta dawowa Saude sabuwa gaba daya, al’amura sun karasa damalmale mata, duk wata .wahala da dawainiyar gidan gaba daya ita ke yin ta, ga yawan tallar datake yanzu hartafi tada tayi ta safe, ta yi ta rana, ta yi ta dare. Duk ta bi ta Kara lalacewa ta fige ta zama tamkar kwarangwal, kazantar da take ciki har tafi ta da, ga alamun girma na zuwar mata, amma kullum rayuwana Kara dagulewa take tana Kara shiga cikin matsi da kunci. Kullum a wurinta jiya ta fi yau. Tun tafiyar Rabi’u bai sake dawowa ba, ba ta kuma Kara samun labarinsa ba. Lokaci ya yi ta tafiya kusan shekara biyu kenan da tafiyarsa kullum sai ta yi kukan rashinsa wanda ba ta da kamar sa. Sai dai ta yi ta share hawayenta ta kwanta ta yi barci, qunci da wahalhalun rayuwa sun yi mata yawa har wani lokacin ta rinqa jin gara mutuwa da irin rayuwar da take ciki. Musamman abubuwan da ‘Yar Baba ke mata ya na damunta, ko'dan ta ga ta fita girma ne duk da Saude a lokacin tana da shekara sha shida, ita kuma ‘Yar Baba na da shekara sha biyar, amma tafi Saude garin jiki, saboda ita irin girman jikin nanne da ita gab-gab mai irin manyan gaBoBin nan. Don ita Saude ‘yar siririya ce sosai, kamar a hure ta 'ta fadi, sai dai tsawo kamar an ja ta. Ita kuwa ‘Yar Baba gajeriya ce mai Kiba sosai tana da manyan mazaune da wadatar na shanu, ba laifi 'ita ma kyakkyawa ce tana da dogon hanci da manyan idanuwa sai dai qaton baki ne kawai ya kware ta mai cike da haqora kamar an watsa wake a miya. ‘Yar Baba har tafi mahaifiyarta wurin‘rashin mutunci da rashin tausayi ga gadara da ' rashin kunya da tsinannan surutu, kamar aku, ga shi' Inna Laure da Malam Bala sun dauki son duniya sun dora mata, duk wani abin da suka samu yana kanta. Shi yasa ‘Yar Baba ta tashi da kwalliya ‘yar gayu ce sosai, suttura komai tsadarta za ka ganta jikin ta, matsatstsu na fitar hankali, kuma ba laifi tana yin kyau matuka, amma idan ka kalli Saude to zaka iya cewa gara jiya da yau. Yanzu haka Saude tafe take rungume da bokitin alala, tana gab kawowa kofar gidansu ta hango wata qaramar mota Joker ta yi fakin mai bakin gilas, ta qurawa motar ido a lokacin da ta ga na cikin motar, dan iya saninta ba su da wasu ‘yan uwa masu 'mashin' ma balle mota Ta Kara gyara rungumar da ta yi wa bokitinta tana kallon motar, ta zo daf da ita ne ta ga an bude an fito. ‘Yar Baba ce da wani saurayi suka fito daga gidan baya na motar hannunta na riqe da irin manyan ledojin nan na shopping. Ba ta ankara ba ta ji ta rafka tuntuBe har takalmin da ke Kafarta ya tsinke dama sun sha duniya duk sun side ga su daban-daban, wato wari da wari, wani ya fi wani. Hakan yasa tasa reza ta ragewa babban tsawo, gaba daya takalman duk sun sha faci da Leda. Ta durkusa ta dauki takalminta ta wuce cikin gidan nasu tana gyarawa, duka suka raka ta da kallo, tana jin saurayin na fadar, ‘Wannan kuma wace ce?” ‘Yar Baba tabe fuska kafin ta ce “’Yar talla ce gidanmu take tana yi wa Baba ta talla. Wani abu ne?” Saurayin ya girgiza kai kafin ya ce “A’a, haka kawai amma dai gaskiya kazama ce, wallahi bakijiba data wuceni harzuciyata saida ta tashi. " Daidai nan Saude ta shige cikin gidan tana jin zuciyarta na mata wani irin kunci. Tana shiga cikin gidan ta ajiye bokitin tallarta, ta miqama Laure kudin cinikinta sannan ta dauki abincin dake ajiye bakin murhu babu k0 murfi sai kudaje ne ke bi yabe yaBe. Saude ta dauka ta nufi bakin qofar dakinsu ta zauna ta soma cin dumaman tuwon. ‘Yar Baba ta shigo niki~niki da ledoji Inna Laure da ke zaune gefen tabarma ta washe baki tana fadar. “Oyoyo! Ga ‘yata, taho nan zauna, zo zauna mu ga me aka farauto mana ‘Yar Baba ta cire takalmanta masu mugun tsini ta ajiye ledojin saman tabarmar, ta cire dan karamin mayafinta mai kamar matacin koko, saboda shara~ sharansa ta zauna, gaban rigar nan an yanke shi sosai, maman nan nata ya yo waje kadan ne kawai ke cikin rigar, Inna Laure na kallonta k0 a jikinta ita ta ledojin ma kawai take. Babu abin da ke cikin ledojin sai kayan makulashe kala- kala, su sweet, cingam, biskit, choculate da sauran tarkace, daya ledar kuma wasu hadaddun kayan shafawa ne irin na manyan mata. Bakin Laure ya Ki rufuwa‘ta dubi ,‘Yar Baba taha fadar, “Wannan kuma ina ki ka same shi ‘Yar Baba, dan wane ne a garin nan?” ‘Yar Babe ta tabe baki tana taunar cingam kafin tace, “Wallahi ban san k0 dan waye ba, nima jiya na hadu da shi na dawo daga makaranta.” Laure ta rafka guda kafin ta ce, “Da kyau ‘yata tauraruwa cikin taurari, mai farin jini, shi yasa. kullum nake Kara son ki dan anan dai haihuwa ta yi rana, Ki dai tsaya ki nutsu ki dage ki shake mana wuyan duk wanda ki Kikeso in ja shi in zaga birni in ratsa Kauye nasa ai masa daurin huhun goro ‘Yar Baba ta sa dariya tana fadar, “Kai shi yasa nake son ki Laure.” ‘ Ta mike tsaye tana fadar, “Hmm! Gaskiya wani abu na ci min tuwo a Kwarya, gaskiya Laure yarinyar can tana zubar mini da aji a gaban samarina.” Laure ta zaro ido “Wace yarinyar?” ‘Yar Baba ta yamutsa fuska kafin ta ce, ‘Yo wace ce in ban da waccan Sauden banzar kullum tana cikin Kazanta wallahi da ta wuce ki har wani wari za kijitanayi. Agaskiya nibazan iyaba indaitaga ina zance ta koma ta samu dakali ta zauna sai na gama, wallahi take ake yi mana daukar matalauta.” Laure ta ce, “Ai waccan mai kama da igiyar shanyar ni kaina abun na damuna da ta tunkaro ki harwani Karni-Karni za ki ji tana yi ita k0 warin jikinta ba ta ji.” ‘Yar Baba ta ja tsaki ta wuce daki tana faman juya mazaune kamar mai rawar taBa-kaka. Wani irin abu ya yiwa Saude tsaye a zuciya, wai harsu sunada bakinda ’zasu kiratada kazama, alhalin sunfi kowa sanin kayanta a duniya kala uku ne sumana Laure ne data gaji da gurza tasakar mata, duk sun sha gamin baki. Daidai da man shafawa bata da shi a gidan, to balle sabulun wanka k0 na wanki, sai idan ita ce ta gaji da yawo da kazantar ta ta siyo omo na goma cikin kudin tallarta idan ta dawo tayi wanki tadiba aciki tayi wanka. Idan ba zata manta ba rabon da fatar jikinta ta ga man shafawa tun kayan kwalliyar da Yayanta ya siyo mata shekaru uku kenan da suka wuce da ‘yan kwanaki. Ta mayar da ‘yar kwallar da ta ciko mata ido ta ci gaba da cin tuwon da ta keji tamkar dutse saboda yanda yake mata tsaye a qahon zuciya. Da rana Saude tana zaune saman bencin cikin tasha ta tasa bokitin alalarta a gaba tana kallon jama’a na ta kai wa da kawowa, can ta hango Garba Gurgu yana nufowa inda take yana faman tsangala kafa da shanyayyan hannunsa guda can gaban qirjin shi a makale yana kadawa irin na wanda ya shanye Saude ta Kara hade fuska dan a duniya idan akwai wanda ta tsana, to bai wuce Garba Gurgu ba, ga shi dattijo dan a Kalla ya kai shekara sittin, ga shegen iyayi kamar wani qarami. Yaro Garba ya qaraso har inda Saude take zaune yana ' faman watso hakora kamar an zana ABCD. Saude ta daukc kanta ta ci gaba da kallon wani waje. Garba ya cangala ya zauna saman dutsen da ke gaban ta. “sannu da hutawa Hajiya Saude ya kasuwar?” Saude ta jiyo muryar nan kamar an kunna injin markade saboda girmanta, ta dago idanuwanta tana Lol i relly feel unhappy for rabiu [1/17, 7:54 AM] A A Dboy: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚 [1/19, 5:11 PM] I love my mum: *YAR TALLA* *CHAPTER 12* kallon shi sai faman sosa gemu yake wanda ke _ faman yi masa kaikayi duk ya yi wani quda~quda da alama ba za a rasa kwarkwata a cikin saba, saboda tsabar qazanta da kurar duniya da ya sha. Saude ta dame zuciyarta ta amsa masa don k0 kadan ba tajin za ta iya yi masa wulaqanci saboda girman shekarunsa dan ya yi jika da ita. Garba ya Kara watso haqoran nan wadanda su kai kore fatau kamar gansa-kuka yana fadar, “Haba Saude na ga alamar kamar ba ki san magana dani, ki yi hakuri ni masoyinki ne ba makiyinki ba kuma ni aurenki zanyi bawai wasa zaikawoni wurinkiba yanzu haka idankika amince min mahaifinki kawai zan nema a yi magana.” Saude ta watsa masa wani kallo mai kama da harara ta zumburo baki kafin ta ce, “Ni fa ba anre zan yi ba yanzu Ya yaqe baki yana fadar, “Haba Saude ke yanzu idan bakiyi aureba saime zakiyi?idan ki ka amince: ki‘ka aure ni, killa ceki zan yi a‘gidana, kin gama zuwa talla idan ma kina tunanin matana hudu ne to a shirye nake dana saki daya daga cikinsu Ya kikacene Saude?” ’ Haushi ya kamata ta mike afusace tadauki bokitin tallarta ta yi gaba ta bar shi nan zaune Garba Gurgu ya yi dariya yana girgiza kai yana fadar‘ “Yaro yaro ne.” Ya mike yana cangala qafa shi ma ya yi gaba abin sa. Bayan Saude ta gama tallarta da yamma likis ta koma gida a gajiye ta samu ta ci abinci ta yi sallar Magariba, sannan ta dauki tallar dare ta fita kofar gida ta zauna da ‘yar fitilar aci-balbal. Kamar daga sama ta hango shi tsangal-tsangal haushi ya cunkusheta ta bade fuska a zuciyarta ta kudiri aniyar idan ya sake ya zo inda take sai ta cire kunyarsa daga idanuwanta ta yi masa rashin kuunya tunda ta lura bai san girmansa ta gani ba ta daga masa kafa ba Da mamakinta sai ta ga ya yi wa kofar gidansu tsinke, ta saki baki da idanuwa tana kallon shi, ta ga ya kira wani yaro ya tura shi cikin gidansu. Yaron bai jima ba ya fito tana kallon su can sai ta ga mahaifinta ya flto sun tsaya suna gaisawa, gabanta ya yi ’mata mummunar faduwa hankalinta ya yi masifar tashi ba dai Garba wurin mahaifinta ya zoba. Wayyo Allah na shiga uku! Abin da ta iya fada kenan wasu zafafan hawaye suka shiga zarya a kuncinta tana kallon yanda mahaifinta ke ta faman washe bakivyasa hannu ya karBi kudin da Garba Gurgu ya ba shi, sannan suka sake yin musabaha, sannan ya shiga gida shi kuma ya wuce abinsa ba tare da ya kalli inda take ba. Saude ta ta kwashi kayan tallarta ta nufi cikin gida. A tsakar gida ta samu mahaifin nata na fadawa “Laure kin ga wani abun murna k0 wai mutumin nan Garba Gurgu ke son Saude Laure ta rangada kuda ta ce, “Kai amma abun ya yi min dadi wallahi, ka ga sai a hada su su duka da ‘Yar Baba. don ita ma ta ce yaron nan mai zuwa wurinta da jar motar nan ya ce zai turo ai maganar aure Malam Bala ya ce, “Ai ko haka za ai dama ni na amsa masa, yanzu haka ya ce jibi za a kawo kayan nagani-inaso yanzu haka har kudi ya ba ni kin gansu dubu biyu. Kai gaskiya mutumin nan yana da mutunci.” Laure ta ce“To, ai sai ka tsakuro mini nawa tunda ba kai kadai keda diyar ba Malam ya ce, “Kefa tsiyarki ke nan duk abin ki ai kya bari' na mutu sannan ki rufe ni ai k0?” Ya ja tsaki ya cimimiya kwarar dubu guda ya cilla mata ya juya zai tafi ya ga Saude tsaye rungume da kayan tallarta hawaye sun gama bata mata fuska. Malam ya ce, “Ke kuma fa lafiya?” Cikin muryar kuka Saude ta ce “Ka yi haquri Baba don Allah wallahi bana san shi ba zan iya aurensa ba, sabo... Malam ya katse ta ta hanyar fadar, “Ke dalla Saurara mini kin jiki Ba kya son shi sai wa ki ke so?” Saude ta yi shiru tana faman shashshekar kuka Malam ya sake fadar “Na ce idan ba kya son shi, sai ubanwa kike so?Munafukar Allah,nankikaso ki jibge mana kita zama kitsufa a tasha kina talla, tunda kebaki da tunani ko Allah yataimaka kemaya kawo miki dauki, tunda ki ka tashi akwai bakon takalmin da ya taBa zuwa wurin ki da sunan so, iye? Amma shi ne har kina da bakin magana. Shekarar ki nawa yanzu a duniya? Kin zauna kin jibge babu mai taya ki kek0 kishin kanki ba kya yi, kina kallon ‘yar uwarki kullum wannan ya shiga wannan ya fita, harda masu motoci, amma saboda rashin kishin kai ba ki taba damuwa ba.” mts! Ya wuce yana fadar. “Idankinada wandakikeso to saikituro shi ai lokaci bai qure miki ba daga nan har ranar daurin aurenki Wani irin kuka ya Kara kwacewa Saude, ta aje kayan tallar ta yi dakinta da gudunta tana. wani irin kuka mai tsuma zuciya. Laure ta ja tsaki tatattara kayanta tana fadar, “Ke dai kya kai su idan kaya ne dan bakin ciki sai dai ya kashe ki don na gaba ya riga ya yi gaba har abada ba zaki iya kamo taba.” Saude ta sha kukanta har ta godewa Allah bata . da mai lallashinta haka ta kwanta har bacci barawo ya sure ta. Haka ta farka yau idanuwanta duk sun ‘ kumbura sun yi jawur saboda kukan da ta sha jiya. Haka ta je tallanta ta dawo jikinta ba kuzari kana ganinta ka san tana cikin matsananciyar damuwa. Ta yi zaman daBaro kan sumuntin tsakar dakin, don kuwa dakin bai da arzikin k0 qaramar tabarma Saude ta jingina da bangon dakin ta rafka wani ; uban tagumi ko tunanin me take? Oho ‘Yar Baba ta dago labulen tana mata wani shakakken kallo kafin ta ce “Idan kin gama tagumin sai ki fito ga kayana na ki hado ki wanke mini. ‘ Saude ta dago da jajayen idanuwanta tana « kallonta, haushi da baKin ciki suka turnuqe mata zuciya, tuni dama batun yau ba take jin takaicin abin da ‘Yar Baba ke mata ba sai ka ce ita ce babbar, ita ma kuma ita ce karamar. ‘Yar Baba ta ce, “Ki ka tsaya kina kallona da wasu kananan idanuwanki can masu kama da na kwarkwata kixo ki min wanki na ce Takaici ya kuma turnuke Saude cikin fusata ta ce, “Wai ‘Yar Baba me ki ka dauke ni ne jakar ki ko kuma me? Karfa ki manta a girme na girme ki,amma ki rinka! yi min abu kamar wata yar da ki ka haifa. Ai ba ‘yar wanki ki ka aje ba, da ki ka dama can da ina miki Inna ce ke sani, amma ke baki isakisani inmiki wanki ba” “ ‘Yar Baba ta ce ‘Eh, lallai wuyanki ya isa yanka, har ni ki ke gayawa magana yau k0 Saude dan kin ga Laure ba ta nan lallai za ki san kin yi da diya ba shegiya ba, za ki gani.” Ta juya ta yi gaba. Saude ta ja tsaki ta IaIIaBa ta kwanta ta ci gaba da nazarin abindayadameta. Bata ankaraba saidaita ji saukar kayan wanki a jikinta ta zbaura ta mike tana kallon mai wannan aikin. 0000000000 “Wato kenan har‘ yar iska ce har kin yi girman da ‘Yar Baba za ta sanya ki ki mata abu ki zage ta ki ce ba zakiyi ba. ‘ To yau sai na ga uban da ya ,tsaya miki ki dauke su maza ki je ki wanke mata, ki shanya ki zauna su *bushe ki linke ki kai mata daki, tantiriya marar kunya, ai na godewa Allah morewa ta dama na ga rayuwarki ta wulakanta, kuma na yi nasara, in dai ina numfashi kin auri Garba Gurgu kin gama, bankadaddiya yanda na ga bayan uwarki da wannan takadarin ke ma sai na ga naki. ’ " Ta ja tsaki ta wuce tana fadar. “Munafukar banza!” . Wasu irin hawaye masu dumi suka zubo daga idanuwan Saude tasa bayan hannunta ta goge sannan ta' shiga tattara kayan wankin ta wuce tsakar gidan, Ta. wanke su gaba daya abun bakin cikinta har da bireziya da dan paint, saboda kawai tsabar raini da wulakanci. Rayuwa kenan. Kamar yanda mahaifinta ya ce za a. kawo kayan nagani-inaso, haka kuwa aka yi Garba Gurku ya aiko mata da kaya cikin Gari ya yi zafi, dinkakkiyar atamfa ce ta roba riga da zani sai dakakkiyar abaya kwaya daya, sai takalmin roba shi ma guda daya da sinqin sabulu guda da Katuwar ’kwalbar mai dangwali-yaBa, sai naira dubu a sama. Laure ta dauki naira duban sannan. ta mikawa Saude kayan don ba abin da ya yi mata a cikin kayan. Wasu irin hawaye masu zafi suka ziraro daga idanuwanta tasa hannu ta karBi kayan ta wuce daki ‘ da su. Tana shiga ta wurgar da su tsakar dakin ta durkushe tana raira wani sabon kukan mai cin zuciya. Tabbas tana cikin halin da ya kamata a tausaya mata,Yayanta ya ringa yi mata gizo cikin idanuwanta ko wane hali yake yanzu? Saude ta sha kukanta ta gaji ta lallashi kanta ta yi shiru Abu wasa-wasa lokaci ya ci gaba da tafiya, Garba Gurgu ya ci gaba da yi wa Saude hidima, idan abun kirki ne sai Laure ta rike, idan kuma ta gajam tagajan ne sannan za ta ba ta, ita k0 ba ta taba kallon kayan ba don yanda ta tsani mai kayan haka su ma kayan ta tsane su. ‘ Ranar: wata Laraba Saude ta dawo daga tallar safe, misalin qarfe daya na rana, Laure tace yau ba tallar rana ta je ta shirya za ta je ta dubo ‘yar Garba Gurgu da ta haihu ta dawo gida wanka jiya ya zo ya gayawa Malarn. . Wani bakin ciki ya tokarewa Saude wuya, ta rasa ma abin da za ta ce saboda takaici, ta wuce dakinta ta yi kwanciyarta, har aka soma kiran sallar La’asar, Laure ta ji shiru ta leko dakin nata ta ganta a kwance idonta biyu k0 motsin kirki ba ta yi. Laure ta dauki sallallami tana fadar, “Yanzu zuwa ki ka ki ka kwanta dan kin raina mutane, ya yi miki dadi sosai wallahi. To sai ki fito ki shirya in ga ubandaya isa ya hanaki kije dubiyannan ki ciro cikin kayan da yake kawo miki ki sanya kin ji na gaya miki” Tana gama fada ta juya ta wuce abinta. Wasu irin hawayen bakin ciki suka zirarowa Saude ta yunkura ta mike jikinta ba kwari, ta fito ta janyo ruwa cikin rijiya ta dauko sabulu guda cikin kayan nasa da ya kawo mata ta nufi bandaki ta yo wankanta wanda rabon da ta yi irinsa ba za ta iya tuna shekarar ba. Tana gamawa ta fito ta nufi dakinta ta janyo mai ta shafawa fatar jikinta, ta zazzaga farar hoda a hannunta tamurzawa fuskarta, ta bude ledar da kayan ke ciki kala uku .ne daga wata atamfa ‘yar roba sai wani yadi mai santsi an yi masa dinkin riga da wanda, sai wani leshi marun an masa dinkin jaka tsaye. Saude ta dauko shi ta saka ta Ciro takalmin robar ta sanya ta kawo milk din hijabin da ke cikin kayan ta sanya, sannan ta fltO zuciyarta na faman suya. A lokacin Laure da ‘Yar Baba na zaune gaban murhu ana ta faman soyen kaji da sanrayin ta ya kawo Saude ta dubi Laure da idanuwanta wadanda suke san zubar da hawaye ta ce, ‘Na fito.” Laure ta dago tana kallonta, alamun mamaki bayyane a fuskarta qarara, wanda har ta gaza danne shi a zuciyarta sai da ta furta. “Saude ke ce haka? Dube ta ‘Yar Baba ki ga abun mamaki.” ‘ Kallo daya ‘Yar Baba ta yi mata ta dauke kanta tare da jan tsaki, Laure ta kada kai kafin ta ce, “To sai ki tafi k0 wa ki ke jira?” Haka Saude ta kama hanya jikinta a sanyaye ta yi. gaba. ‘ ‘ Gidan Garba Gnrgu yana can qasan unguwarsu ta baya, haka Saude ta taka~ da qafa. Gidan qaton gida ne ginin qasa,~rabin katangar duk ta zube a Kasa wanda aka sa buhu aka zagaye. Saude tasa qafarta cikin dogon zauren wanda aka fito da Katuwar kwata ta tsakiyarsa har tsakar gidan, gaban ta ne ya shiga faduwa lokacin da ta sa qafa cikin soron gidan, ba ta san irin tarbar da za a yi mata ba, ta san mugunta ce kawai ta sa Laure ta ce ta zo gidan ba wani abu ba. Saude ta yi sallama a tsakar gidan wanda yake a hargitse sai ka rantse da Allah bai’taBa ganin Shara ba ga wasu manyan tukwane da murahu a tsakiyar tsakar gidan ko’ina komatsai ne a tsakar gidan ba masaka tsinke, ga yara nan suna ta faman tsalletsallensu a tsakargidan sai ka ce ba su taba ganin ruwa ba a rayuwarsu saboda tsabar Kazanta. Saude ta Kara daga murya tana sallama sannan matan da ke ta faman zirga-zirga suka ankara da ita aka amsa mata tare da . yi mata maraba, jikinta a sanyaye ta qarasa cikin, gidan tana danne fargabar zuciyarta. Daya daga cikin matan ta janyo kujera ‘yar tsugunne ta miqa mata ta zauna suka shiga gaisawa, wasu su biyu babu riga a jikinsu sun saki nonuwa a waje sai ka ce silifas suna ta harkokin su babu abin da ya dame su, sai Karamar su ce keda daurin qirji. Kai da gani ka san an yi masu kisan Kuli, an kashesu ko kadan baza akirasu da mata ba. Saude ta qakaro wani murmushi wanda iyakarsa saman laBBanta kafin ta ce, “Na zo ganin jariri ne.’ Babbar cikin su ta ce, “Au! Ni dai na ce ba mu. , waye ki ba, suna daka ki shiga ki gan su.” mu kishi da jikannu wallahi, ba ta yiwuwa da sake an bawa mai kaza qafa” A daidai nan Saude ta fito tana qokarin sa takalmanta ta ji matar na fadar, “Munafuka ashe Ieken asiri ki ka zo in dai gidan Malam ne ki shigo kema ki zauna, sannu a hankali za ki koma yanda muke ” Sauran matan dai babu wadda ta tanka, harkar gabansu kawai suke. Saude ta sa takalminta dai ta yi waje, tana jin Garba ya biyo ta yana fadar. “Tsaya Saudatu ki ga dakin ki.” Bata tsaya kulashiba tayi gaba da hanzarinta sai sauritake dankokadan batasan ta hada ido dashi, munin shi da qazantar shi kadai ta isa tasa ta tsane shi, to balle ga shi tsohon najadu ga nakasa kai shi dai abun ya yi masa yawa. Bata ankaraba tanata tafia cikin sauri tana zancen zuci, ba ta ji horn din da ake faman kwarara mata ba, saidai taji an hankadata gefe hankalin Hamid ya yi masifar tashi, ya yi saurin yin fakin din motarsa ya fito a guje: ya nufo inda take yana kokarin daga ta, Saude ta yi saurin mikewa dan gudun karya tabata shimaya dago da niyar yabata hakuri, su kai four eyes, ido hudu, wanda ya haifarwa Hamid da bugun zuciya mai tsanani. Cikin tsoro da rudewa Saude ta soma ba shi hakuri, kallonta yake ido cikin ido wani abu na faman zarya a cikin kirjin sa muryarsa a sanyaye ya ce.‘ Ai nine zanbaki hakuri nidana kadeki kiyi haquri wallahi ban lura da keba ne.” Saude ta kada masa kai sannan ta wuce shi abin ta. Hamid ya yi saurin bin ta yana fadar, ‘Don Allah dan tsaya mana ‘yanmata.” Saude ta waigo tana ’ kallonsa, ya dan gyara tsayuwarsa kafin ya ce ‘Don Allah idan ba za ki damu ba ki fada mini sunan ki.” . “Saude.” Ta ba shi amsa a taqaice. Ya girgiza kai yana fadar, “Na’am Saudat, don Allah idan ba za ki damu ba kimin kwatancen gidanku Saude ta waro ido tana kallon shi, alamun mamaki bayyane a fuskarta ta kasa ma magana, ya danyi murmusa kafin ya ce, “Ki yi hakuri kar kice na fiya shishshigi da yawa;” ' Saude ta dauke kanta kafin ta ce, “Lafiya dai ko? ‘ “Lafiya kawai dai ina so inxo in Kara duba kine don ban sani ba ko wani abu ya same ki.” Saude ta wuce shi tana fadar, “Ni babu abin da ya same ni.” Hamid ya yi tsaye yana kallon tafiyarta hatta kusa Bacewa ganinsa, ya ja wani taqaitaccen murmushi murmushi mai sauti tabbas yau zuciyarsa ta samu abinda takeso,zaicigabada binta harya samu ya samo kanta. Ya juya ya shiga motarsa ya bi ta a baya harkofar gidansu ya rakota batasanai ba, sannan ya koma abin sa. Saude nashiga gida, Laure ta bitada kallo kafin ta ce, ‘Wai kin je gidan nasu kuwa?” Saude ta daga mata kai alamar eh laure ta yatsina fuska kafin tace “Amma abinda mamakine da akace min amaryarsa mugun kishine da ita aina dauka sai sun karya miki qafar baya.” Ta ja tsaki mts! “Sai ki wuce kafin tallar yamma ta qarisa Saude ta wuce dakinta simi-simi ba tare da ta sake tankawa ba. Tana shiga daki ta kwanta, wani irin abu ya tokare mata zuciya, ta lumshe idanuwanta fuskar mutumin nan ce ke mata gizo, har yanzu hancinta baidaina shakar kamshin turarensa ba mai sanyin kamshi. Dama yace yanasonta tabbas da saitayi kukan dadi. Makaskanciya irin ta a ce irin wannan namijin yasota aidakamar wuya wai gurguwada auren nesa. K0 ‘Yar Baba da ta fita komai ba ta samu kamarsa ba, ballantana ita mafi kaskanciya mai tsananin rauni Taja wani gwauron numfashi tare da saurin kawar da abin dake zuciyarta, don ta san k0 a mafarkinta hakan ba zai taba samuwa ba. Washe gari Saude ta dawo daga tallar safen ta, sannan ta dauro alwala ta yi sallah; sannan ta fita’ tsakar gida ta zauna, Laure ta sauke alalar aka zazzage mata a bokiti ta dauka ta fice abin ta. Hanyarta ta kullum yau ma ta ita ta bi idonta na saman hanya ta wuce ta qofar gidan Alhaji Bashir, Hamid da ke zaune saman teburin maigadi ya ga tahowartaya zabura ya mike, ya dubi Malam maigadi yana fadar. “Ina zuwa Baba bari in dawo.” Bai jira abinda zai ce ba ya yi saurin bin ta dan kar ta Bace masa. Saude ta tsinci muryarshi na fadar. “Assalamu Alaikum. ” Ta waigo tana kallon shi da mamaki a fuskarta ta kasa bude baki balle ta iya furta wani abu, Hamid ya yi murmushi kafin ya ce, “Ruwan zuma ne ni ba madaci ba na kasance mai began ki tun a lokacin da na soma ganin ki ba wai sha katafi ba, mene na tunanin a kan hakan?” Saude ta fara nutsuwa tana kallon kyakkyawar fuskarsa, wadda ta qawatu da dogon hanci da yalwatattun idanuwa wata nutsuwa 'ta dirar .mata muryarta a sanyaye ta ce, “ZaBina ba tsakanin zuma k0 madaci ba ne, kyakkyawan zabina shi ne yawaita ayyuka, masu kyau da gujewa munanan dabi’u na kasance mai zurfin tunani da. Kwakwalwa ba da zuciya‘ ba, me ye tunanin ka a kan hakan?” Hamid ya dan saurara kafin ya ce, “Ikon Allah ga .shi nima yanzu haka Dady jirana yake, amma ba damuwa, ki fada masa zuwana gobe insha Allahu zan dawo.” Saude ta amsa da to, sannan ya juya ya tafi ta raka shi da idanuwanta. Ikon Allah mai tsaida wando ba zariya. Mamaki da al‘ajabi su suka dabaibaye zuciyar Saude, har yanzu bata fidda ranta da cewa mafarki take ba, za ta iya farkawa a kowane irin lokaci. Ba Washe gari Saude ta dauki tallar wainar .ta. Bayan ta siyar karfe sha daya da ‘yan mintuna ta dawo, Laure ta hada' ta da sanwar alala duk da matsananciyar ranar da ake kwalawa haka ta zauna a tsakar gidan gaban murhun sai gumi ke tsiyaya a jikinta. Tamkar daga sama yaro ya shigo ya yi sallama, Saude ta amsa tana kallon shi, ya ce, “Wai' ana sallama da Malam in ji wani mutum a waje.” Saude ta nuna masa dakin Laure da hannu tana fadar. ' “Shiga can ka fada masu.” Yaron ya wuce ita kuma ta ci gaba da abin da take, yaron bai yi minti biyar da fita ba Malam Bala ya fito cikin shirin tafiya masallaci kasancewar yau Juma‘ a bai fita kasuwa da wuri yasa kai ya fice Tsawon wasu mintina da suka haura goma zuwasha biyu sannan‘ ya dawo gida yana faman Kwalawa Laure kira‘ . “Laurel Laurel! Laure!!! Wai kina ina ne nake ta faman kira kin yi shiru Ta hankado labule ta fito tana fadar, “Wai ya akai ne, ka keta faman kwala min kira sai ka ce yaki?” Malam Bala ya yi kwafa, “Amma dai ai kin san ruwa baya tsami banza, kin san dai daga jin kiran‘ nan kin san da walaki.” Laure ta ce ‘To mu gani a qasa Ya ce, ‘Tabarma zaki ba ni dan gidan Alhaji' Bashir ne yazo wai wurin ‘yata yana son a bashi izinin turo iyayensa maganar aurenta.” Inna Laure ta zaro qananan idanuwanta haqoran nan suka yo gaba sai ka ce kamfanin cokula ta ce “Kai don Allah yana ina? ’ Malam ya ce, “Yana waje “A’a bari a kai masa tabarmar.” Ta juya daa ‘hanzarinta ta nufi daki ta janyo masa tabarma bayan qaure ta fito fana fadar. “Ga shi Malam ka shimfida masa a soro gatanan zuwa.” Ya amsa ya juya da hanzarinsa har yana tuntube Inna Laure ta nufi dakinta can kurya kan gado bonanza ta shiga inda ‘yar Baba ke kwance tana faman sheka baccinta Inna Laure ta shiga tashinta.’ ‘Yar Baba ta bude ido da kyar cikin magagin barci. ‘ ‘ Ki tashi da alla kin ji aikhairi yazo mana har ‘ cikin gida, da rana tsaka.” IKilima ta ja wani’ tsaki ta juya daya barin ta ci gaba da baccinta, Inna Laure ta Kara bubbuga ta Ta zabura a fusace. “Wai mene ne don Allah za ki dame ni kawai ina baccina Inna Laure ta ce, “Ki tashi banza arziki ne ya zo mana da qafafuwansa dan gidan Alhaji Bashir yaron nan ya z0 wai neman auren ki tashi banza, banza ki shirya.” ‘Yar, Baba ta zabaura ta tashi zaune idanuwanta a warwaje tana fadar, “Kai Laure don Allah da gaske ki ke?” Laure tace, ‘A’a ai sai ki tashi ki gani da idon ki yana soro shi da Babanki.” IKilima ta buga wani uban tsalle ta dire daga kan gadon, saboda doki, ta kwasa da gudu zata fita Laure ta yi saurin riqo ta. “Ke da Allah tsaya haka za ki je sai ka ce wadda ta tabu, ai sai ki ja ya ce ya fasa, maza ki shirya da Allah karya gaji da jira. ’ ‘Yar Baba ta dan nutsu kafin ta ce, “Ba za ki gane bane Laure yaron ya hadu yanda ba ki tsammani kyakkyawa ne, kuma dan gayu, daga qasar waje fa ya dawo ya kammala digiri dinsa. Laure idan na aure shi wallahi na gama more miji, ai duk samarina korarsu zanyi "Ta dan yi shiru kadan kafin ta ce “To wai ma me zan sanya?” Laure ta ce, “Ki sa wannan shaddar taki sabuwar Ginznar nan tana yi miki kyau sosai.” ‘Yar Baba ta kada kai alamar ta game, sannan ta juya ta bude akwatinta ta Ciro shaddar dinkin riga da siket ne ya sha aiki matuka, ta saka kayan wadanda suka dame ta matuka komai na jikinta ya flto. ‘ Ta zauna ta yi kwalliyarta sosai ta kawo dankwalinta ta 'kafa daurin‘nan mai suna ture-kaga tsiya, sannan ta saka dan kunne da sarka, ta mike ta janyo wani dan ficicin gyalenta mai kama da matacin koko saboda shara sharansa ta yafa, ta saka takalminta mai tudun dunduniya ta saka, ta dauko wata gingimemiyar jaka saikace waddazatabiki ta rataya a kafadarta, ta juyo tana kallon Laure tana wani murza idanuwa. “Toya kika ganni?”‘ Laure ta ce, “Kin hadu qarshe ‘yata ai shi yasa nake qara son ki, dan kuwa kyan ki daban yake dana sauran mata shi yasa kullum sai an mana sallama.” IKilima ta sheke da dariyar jin dadi na kwarzantawar da Lauren ta yi mata ' Malam ya hankado labule “Wai me take Jira ne har yanzun kunsam jirafa bashi da dadi Inna Laure ta ce, “Ai ga ta nan fitowa Malam, ya yi hakuri. ” Malam Bala ya saki labulen ya juya ‘Yar Baba ta dubi Laure ni“Na tafi Laure.” “A’a mu je in taka miki.” Laure ta fada tana yake hakora. A tare suka fito, Saude na durkushe a gaban murhu sai faman hawaye take saboda hayakin da ya turnuke ta, har ba ta iya ganin gabanta sai sharbar' mijina take. Suna isowa inda take Laure ta dube ta, ‘To ‘yar iska munafuka wutar ce ba za ki hura ba k0 so ki ke alalan ta jike a cikin ruwa, annamimiya munafuka.’ Ta duma mata wani uban kulli wanda ya sa ta yunkurin amai ta zabura ta mike tana faman sosa inda ta 'maka mata dundun. . Ta ce ‘Wallahi Inna itatuwan ne danyu sun ki su kama.” Inna Laure ta haure ta da kafa, ‘Kan ubanki ke da danyun yanzu dan kina munafuka wadannan itacen' sune danyun,to idan ma kinbarta tayi danya dan kanki,danni yaddah kika fita da ita haka zaki saida ta ko ta kwabo ban ce ki dawo da ita gidan nan ba, wuta kuma kar ki hura ki yi shekaru dubu anan Saude ta surce majina tare da goge ruwan hawayen da ke zuba daga idanuwanta, ta duke. ta ci gaba da hura wutar da baki, amma illahirin zuciyarta LOL YA abin yake NE GUN WA HAMID YAZO IKILIMA KO SAUDE MUCi GABA Dakasancewa DA ADmin Dboy DONJIN yadda WANNAN TAQADDAMA ZATACI gaba DA KASANCEWA [1/19, 5:11 PM] I love my mum: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚 [12:17PM, 02/02/2017] 🙆🏼‍♂@lh@ji🙆🏼‍♂: [1/19, 5:14 PM] I love my mum: *YAR TALLA* *CHAPTER 13* a cunkushe take saboda duk abin da ake tana jin ‘Yar Baba ta tabe: baki ta wucc soron gidan, Saude ta tsaya da hura wutar tana kallonta idonta ya ciko da hawayce Hamid yana zaune a barin tabarma yana karkada kafafuwansa ya yi irin zaman nan na masu cin tuwo, ‘Yar Baba ta jingina da bangon soro ta kafe shi da ido cikin ido tana wani murmurtsa idanu. Hamid ya tsaya yana qare mata kallo cike da mamamki ya ce, “Ke kuma fa wace ce?” ‘Yar Baba ta‘yi wani qasaitaccen murmushi irin na gogaggun yan duniya kafin ta ce “Ai ni ce iKilima wadda aka fi kira da ‘Yar Baba, da alama baka gane ni ba ko?” Ta Kara jan wani munafukin murmushi tana fadar. “Kowa ma idan nasa kayan nan haka yake fade: beganeni:ba ashe dama haka nake da kyau hummml Kayan suna mini kyau sosai.” Wani takaici da haushi suka kama Hamid cikin takaici ya ce, “Ke da Allah saurara kin ji bana can shirme da sakarci kin, Saudat na ce a kira mini ita nake nema ba wai keba kin gane? ’ ‘Yar Baba ta ji tamkar ya watsa mata ruwan zafi a zuciya cikin Bacin rai ta ce, “Ai ba ita Baba ya ce kana nema ba ni ya ce kana nema Hamid ya dan sassauta murya, “Kin ga kiyi hakuri don Allah ki je ki kira mini ita ta sanda zuwana please ban san ku biyu bane a gidan." ‘Yar Baba ta waro ido tana kallon shi bakinta na fadar, “Kutumar... wallahi ba zan je ba har ma ta isa in kula ta ‘yar tallan gidan namu ba zan jeba wallahi, sai dai ka daskare a nan.’ Ta juya za ta tafi Hamid ya yi wani murmushin takaici ya zura hannu cikin aljihu ya ciro kudi‘ yan dan biyar biyar sababbi dal guda hudu ya miqa mata. ‘An shi ga wannan ladan kiran nata idan ba za ki kira ta don Allah ba. ” ‘Yar Baba ta sa hannu ta fizge kudin tana fadar, “Ai raba mugu da makami ibada ne” Ta juya ta yi cikin gida. Laure ta tarye ta tana fadar, ‘Ya akai ne?" ‘Yat Baba ta fashe da kuka tana fadar, “Wai Laure wai ba ni yake so ba, wai SAUDE yakeso.’ Laure ta ja wata ashariya ‘Kan habbm.... Bake yake soba uwar wa yake so?” ‘ “Yar Baba ta nuna' mata kudin da ya 'ba ta, “Kin gama waiyabani inkiramasa ita Laure tace daukomin mayafina naje na sameshi ‘Yar Baba ta kwasa da gudunta ta dauko mata mayafinta ta baza saman kafada ta nufi soron kamar an hankada ta. Hamid yana zaune hmnunsa riqe da qatuwar wayarsa yana wasa da ita, yana ganinta ya fadada fuskarsa da fara’a. “Sannu da fitowa Umma barka da rana.’ Inna Laure ta amsa fuskarta ba yabo ba fallasa sannan ta gyara tsayuwarta tana fadar, “Kai ne bakon Saude?” Ya dan sunkuyar da kai qasa alamun kunya kafin ya ce “Eh nine Umma.” Laure ta kuma gyara mayafinta mai kama da an kwato shi daga bakin kura ta ce “To Saude dai da ka ke ganinta shegiya ce ‘yar gaba da Fatiha, ce yarnan da ka gani kuwa ni ce mahaifiyarta nina haife ta da cikina, kuma ka san an cewa shi dan gado sai ya zarta to Saude kuwa har tace ban iya ba, dan wurin gantali da yawon bariki gari gari babu inda Saude bata zaga' ba. Kai in taqaice maka har cikin shege sai da ta yi.’ Wani irin abu ya dakarwa Hamid zuciya mai zafin gaske ya samu da kyar Ya iya hadiye shi kafin ya iya fadar, “Amma Umma da mamaki a gaskiya ba zan Boye miki ba Saude ba ta yi wa rayuwarta adalci ba sululu kenan macijin sari ka noqe Ki yi hakuri Umma insha Allahu ba zan guje mataba don wannan qaddarar ta fada nayi miki aIqawarin auranta a hakan in ceto rayuwarta.” Laure ta ce, “A’a ahir!.Dinka karka fara don ba zaka taba iya ceto Saude ba saboda kin Allah irinna yarinyarnan ya wuce tunanin ka” Laure ta sa kukan munafurci har da su fyace majina. Hamid yana kallonta saidata gaji dankanta ta dan sassauta ta ci gaba da fadar, ‘Dan nan shu’umancin Saude yana ci min zuciya wai yarinyar hartasan tanemi mace ‘yar uwarta,bacin mazan datakebi yandakasan karyar mazahaka take. Na zubarwa Saude ciki yakai biyar a asibiti har sun haddace mu, sun gaji idan mukaje ma yanzu kararmu sukace zasuyi wai saboda zubdawa Saude cikin da muke yakai iyaka.” Hamid ya ce“Duk wannan ba matsala ba ce Umma, wallahi ahakan insha Allahu indai saude mai shiryuwa ce sai na shiryar da ita.” Inna Laure tace, “Kai malam,Saude bazata taba shiryuwa ba saboda ba ta tsoron Allah k0 kadan babu Allah a ranta.” Hamid ya ce “Ai Umma Islamiyya zan sanya ta insha Allahu kekanki saikinyi mamakin yanda zata shiryu ta nutsu.” Inna Laure tace“Dannan kenan bakasan Saude ba har yanzu, ai kwakwalwarta a dode take ba ta daukar komai ba ka da abin da Saude ke iya dauka ballentana harta iya haddace shi.’ Ya ce, “Ai Umma babu abin da yafi qarfin addu’a, sai mu taya ta da addu’a insha Allahu za mu yi nasara amma ni ina son ta kuma wallahi aurenta zanyu Inna Laure ta harzuka cikin haushi ta ce “Tokai baza,a auramaka itadinba ‘yatadaicetonayi mata miji koka tashi kabarnan yanzunnan wallahi k0 in maka ihu kwarto, dan iska kai ana gwada maka Annabi kana rintse ido.” Hamid ya mike ya ajiye mata bandir din yan dari bibbiyu na dubu ashirin ya ce, “Zan tafi Umma ga wannan a sai sabulu zan dawo sati mai zuwa da fatan za ki sauko daga dokin qiyayyar da kika hau, na gode Ya juya ya fice daga soron ya bar Laure tsaye dakam tamkar wadda aka kafe sai zazzare na mujiya take a kan kudin, wani abu na yi mata zarya a zuciya ta duke ta suri kudin ta yi cikin gida tana kwalawa Saude .kira Sande da take duke gaban murhu ta yunkura da niyartatashi, amma ina dukanda Laure ta soma kai mata yasa ta duke babu shiri, Laure ta janyo bakin wuta tana faman dukanta sai ka cc yaqi fidi take. “Yau sai na kashe ki har lahira in ga ta soyayya, ke nan har kin isa wani ya ce yana son ki a hakan. To idan ma farar fatar ce ta janyo shi yau sai na lalata ta.” Tun Saude na ihu har ta soma Kokarin kwatar kanta, ‘Yar Baba ta tare ta tana fadar, ‘Laure fuskar za ki toya ki lalata mata ita mu ga ta kyau da iyayi.” Saude .ta sa wata irin kururuwa, ta kwace daga hannun ‘Yar Baba ta yi dakinta ta maida qofa ta rufe, tana jin Laure na fadar k0 ta bude ko ta cin nawa dakin wuta amma ba ta motsa ba. Kuka take sosai kamar ranta zai flta, dan Laure duk ta tattaya mata jiki da bakin wuta abin ka ga jar fata duk jikinta ya yi jawur. Ai kuwa nan ta sulale Kasa ta zauna tana faman kukanta. Tabbas ya zame mata wajibi ta cirewa zuciyana kwadayin wata rayuwa mai dadi, dan ta tabbatarwa kanta Inna Laure ba za ta taBa barinta ba, tasa hannu tana sharar kwalla. Inna Laure ta sake bubbuga qofar tana fadar, “Sai ki flto ki daukar mini talla ta in ba haka ba in karya kyauran in shigo.” Yadda ta ke dukan kyauren da Karfinta ya tabbatarwa Saude za ta iya ma abin da ya fi hakan, ta ta miKe tana kallon kayan jikinta, tun leshin da ta saka ne ta je gidan Garba Gurgu ne a jikinta, har yanzu ga shi Laure duk ta qona shi. Ta dauki hijabinta ta sanya ta bude kofar ta fito, Laure ta kai mata wani duka tana fadar. “’Yar iska munafuka!” Ta watsa mata kayan hannunta, ‘Karbi maza ki canza kayan jikin ki duk wani abu da ki ka san na kwalliya ne a cikin dakin nan ki ki miqo mini shi yau sai na ga qaryar soyayya ai dai sai da kyan aka soyayyar ko to zan gani.” Saude ta amsa ta koma dakin, wata kodaddiyar atamfa ce riga da zani ba dankwali, rigar sai a hada irinta mutum hudu su shiga ciki ga ta duk ta yage saboda tsufa. Sai zanin Jaka tsaye ya yi matukar shan jiki ya sha gamun baki har wuri hudu, ga shi babu dankwali 'sai wata abaya, hawaye suka ciko a idanuwan ta tausayin kanta ya kamata ta cire kayan jikinta ta sanya wadanda ta ba tan, sannan ta tattara komai na cikin dakin ta fito da shi. Laure ta kwashe tana fadar “Munafukar banza, kuma wallahi ki sake in ji labarin kin tsaya kin saurari matsiyacin yaron nan na rantse da Allah sai na lahira ya fi ki jin dadi, ‘yar iska tambadaddiya.’ Ta sa qafa ta haure ta sannan ta wuce Saude ta dauki bokitin tallarta tasa kai ta fita, tana faman sharar kwalla. Rayuwa kenan ita dai ta san ba ta daga cikin wadanda sukai sa’ar rayuwa a duniya. Tana tafe tana sharar kwalla tana zancen zuci, ba ta ankara ba sai dai ta ga mutum a gabanta, wani irin kallo yake mata mai cike da mamaki muryarsa a sarkake ya ce Lafiya Saudat, wace irin shiga ce wannan laflyarki qalau kuwa?” ' Saude tasa hannunta guda tana goge hawayenta, ta soma magana cikin kuka. “Lafiyata lau don Allah ka yi hakuri ka flta daga rayuwata na roqeka.” Hamid ya girgiza kai yana fadar, “Impossible, wallahi abin da ba zai taBa yiwuwa ba kenan, sai dai idan har son ki zunubi neto na ratayawa kaina alhakinsa, amma ba zan taBa barin ki ba.” Saude ta tsaya da kukanta tana kallon shi kafin ta ce, ‘Me yasa ba xaka rabu da ni ba, k0 kana san jefa zuciyata ne cikin bala’in da ba zan iya flta ba? . Wannan kukan da ka ga ina yi duk ta dalilinka ne.” Hamid ya ce “Na ji na dauka, amma don. Allah ki yi hakuri ki bani kadan daga cikin labarin ki ni nayi miki alkawarin taimaka miki da duk wata gudun mawar da kike buqata." Hawayen da suka tsaya da zuba daga idanuwan saude suka Ci gaba da zubowa tana sharBar majina kana ta fara magana. “Kamar yanda ka sani sunana Saude, tunda na . tasona bude idanuwana na ganni tare da Yayana,shine uwata shi ne ubana shine komai nawa. Bai barin nayi kuka , kullum burin shi ya samamin farin ciki da gatan da na rasa a rayuwa, Ni kuwa burina kullum in matsa masa in sanya shi yimin abinda baidai konyinsa Hamid ya ce, “To yanzu yana ina shi Yayan naki? ‘ Saude ta Kara rushewa da kuka kafinn ta ce . an raba ni da shi, su suka raba ni da Yayana.” Ya ce, ‘Su waye?’ Muryarta na rawa cikin kuka ta ce, “Baba da inna Laure.” Hamid ya ja wani numfashi mai nauyi yana jin yanda take ta faman kuka da shashsheka tausayinta mai tsanani ya shige shi, muryar shi a sanyaye yake magana. “Ina mahaiflyarki da mahaifinki su ke?" Saude ta ce, “Ban san inda mahaifiyata take ba, Ban taBa ganinta ba, wannan kuma da ka gani shi ne mahaifina, Inna Laure kuma matarsa ce ‘yar Baba ita kuma qanwata ce Hamid ya sake sauke wani nannauyan numfashi ya fahimci yarinyar tana cikin matsala, ya zuba mata idanuwansa farare tas cikin sanyin muryarsa ya ce, “Ki yi hakuri Saudat na fahimci irin abin da ki keji a zuciyarki, ki kwantar da hankalin ki insha Allahu na yi miki alqawarin taimaka miki da dukkanin karfina in dai ina raye sai na daga darajarki a duniya, sai kuma na wanzar da murmushi a idanuwan da Yaya ya bari cikin hawaye.” Ya dan qara numfasawa kafin ya ce “Ki je " 'lallar ki dawo, zan zo da daddare in same ki wurin tallarki za mu yi magana, amma don Allah ki daina kukan nan haka nan kin ji?” Saude ta daga masa kai tana goge hawayen da ke fuskarta, ya dan tsura mata ido da murmushi a kumatunsa ya ce, “To dan yi murmushi mana beauty *Dukda batasan abindayace ba,ammatayi murmushin kuma kalmar beauty din ta yi mata’ dadin sauraro a kunne. Sai da ya ga tafiyarta sannan shima ya juya ya tafi zuciyarsa na raya masa abubuwa masu yawa. Da yamma likis Saude ta dawo daga wurin tallarta Laure ta jibgo uban wanki, sannan tace ta ' dora sanwar tuwan dare. Saude ta duka a gun ta yi kukanta har ta gaji sannan ta ja ruwa ta dora sanwar ta dawo ta ci gaba da wankin. Ana gama sallar Magariba Malam Bala ya dawo gidan, Laure ta shimfida masa tabarma a tsakar gida ta kawo masa fura da mafici ta zauna gefensa. Malam Bala ya bude furar ya soma sha, sannan ya dubi Laure yana fadar, “Wai ya suka yi da yaron nan ne Laure?” Ta taBe baki tare da furta, “Uhmm! Malam kenan, ai yaron dan iska ne takadari kana ganinsa kamar na kirki suna hira da ‘Yar Baba ya nemi taushe ta cikin zaure Allah ya rufa asiri yarinyar nan ta yi ihu, na kwaso da gudu na raka shi da bakin wuta har waje, mutane na ta bani hakuri suna fadar in kyale shi ai ni’wannan abu ya ci min zuciya wallahi har kuka na yi. Yanzu dan kawai an gan mu talakawa matsiyata shine za a shigo har cikin gida a ci zarafin mu. Kai Malam wannan abu da me ya yi kama?” . Tunda ta fara zancen ‘ya’yan cikin Saude suka fara juyawa wani irin gumi ya shiga tsatstsafo mata, take juwa ta kwashe ta, sai dai ta ganta zaune a gefen bokiti. Malam da tunda ta fara zancen ya hau sallallami, ai sai ya rufe furar yana fadar, “Wai harni za a ciwa mutunci a garin nan Laure na rantse miki da Allah sai na yi kararsa kotu, kuma ta addinin Musulunci.” Laure ta ce ‘Aa, Malam abin ai duk bai kai na kotu ba wurin mahaifinsa za ka gobe tunda sassafe ka kai qararsa ka ce ya jawa dansa kunne ga abin da ya yi maka in ba haka ba za ka sa hukuma ta (shiga tsakaninku.” Bakin ciki ya cika malam Bala ya zabura ya mike ya suri buta ya nufi bandaki. Laure ta tabe baki ta raka shi da harara a zuciyarta tana fadar sauna kawai. Ta yunkura ta mike ta dubi Saude da ke 'zaunc ta ce, “Toke kuma tsohuwar munafuka kin zauna kin kasa kunne kina sauraran jama‘a sai ki tashi ki dauki tallar gyadar ki tafl idan kin dawo kin qarasa wankin tunda cinikin na yauzu ne." Saude ta lallaba ta mike tana jin tamkar za ta fadi ta dauki tallar ta ficee, kuka maya gagareta idanuwanta sun yashee babu komai cikin zuciyarta sai duhu. ' ‘K0 minti goma bata yi da zama ba ta hango shi ya nufo inda take; yau sanye yake cikin manyan kaya, ‘na wani lallausan yadi milk colouz; mai hasken gaske dukda a'cikin duhu ne amma bata kasa ganin shekin yadin ba, kansa yana sanye da hula baka yasa bakin takalmi a Kafafuwansa, tun kafin ya Karaso kamshin tuiarensa ya daki hancin Saude ta lumshe idanuwanta, sai a lokacin wasu hawaye suka tarar mata ’ Hamid ya yi mata sallama tare da durKusawa gabanta, muryarsa a sanyaye ya ce “Sannunki yan matana barka da Kokari.” ' Saude ta bude idanuwanta tana kallonsa. hawayen da suka taru a kwarin idanuwanta suka ziraro ‘ ‘ Hamid ya mike tsaye ya ciro farin hankicif Dinsa daga cikin aljihu ya miqa mata, Saude ta girgiza masa kai don ta san k0 rike hankicif dinma kadai ta yi sai ya yi dauda, to balle ta goge fuska dashi wai sunan wani wai shi ‘ Danduwala. . Hamid ya sake mika mata hankicif. din yana fadar :‘Wallahi sai kin goge garama ki karBa kawai” ‘ ' Jim yanda ya yi saurin rantsuwar ne yasa Saude ta amsa ta goge hawayen, ya ce, “To bani abuna” Ta yi wani dan taqaitaccen murmushin da bai , wuce kan labbanta ba ta ya qara goge fuskar shi da shi sannan ya saka a aljihu yana fadar. “Wannan tafiyar yau ba ta ki ba ce wurin Baba nazo don haka ni kin ga taflyata." Bai jira abin da za ta ceba ya juya ya tafi abinsa zuciyar Saude ta qarasa karyewa ta kifa kanta saman kayan tallar tana rera wani irin kuka mai cin zuciya. . Hamid ya karasa Kofar gidan da qarfin zuciyarsa ya aiki yaro ya yi masa sallama da Malam Bala. Yaron bai jima da fitowa ba ya ce ga ‘ shi nan zuwa, sai ga Malam Bala ya fito da alama masallaci za shi saboda an fara kiran sallar Isha’i, yana ganin Hamid a qofar gidansa ya ja ya tsaya yana fadar. “Malam laflya?” Hamid ya durKusa har qasa yana gaishe shi. Malam Bala ya ce“Kai dakata ban san rashin kunya ka ji har ni za ka dauka mutumin banza da WOfl, to ka je komai ka yi dan kanka ka, Allah ya isa tsakanina da kai, duk da ka gan ni talaka ina da wadatar zuci.” Mamaki ya kashe Hamid ya dago yana kallon Malam muryar shi cike da rudani ya ce Don girman Allah ka yi hakuri Baba wallahi ban san abin da nyi ba wanda kake fadarsa a yanzu« Malam Bala ya ce ‘Ai dama ba zaka san abin da kake; fada a kansa ba, tunda ka ci idon dan akuya ' amma abin da nake so da kai anan shi ne ka tashi ka ba ni Wuri kar in sake ganin ka gifta k0 qofar gidan nan, kuma zanje in samu mahaifin naka ya yi maka tsakani da‘ ya yana mutumin banza kawai’ Yana gama fada ya juya zai tafi, Hamid na kiran ‘ Baba don Allah ka saurare ni, amma bai kula shi ba , ya yi gaba Wani abu ya tsaya zuciyar Hamid, ya lallaba . ‘ ‘ya mike jikinsa ya yi masa masifar sanyi ya nufi ’ inda Sande take zaune tana faman raira kukanta. ‘ ‘ « Tausayinta ya lullube shi ya kura mata ido ' na wani dan lokaci kafin ya soma magana muryarsa a ' sanyaye ya ce“Ba zan hana ki kiyi kuka ba Saudat, « dan zubar hawayenki ya zama dole na fahimci abin da aka shirya mana, amma don Allah ki yi haquri kamar yadda na dauki alkawari’n taimaka miki ba . zan fasa ba Saudat da yardar Allah sai na ga rayuwarki ta inganta, kar ma Wannan abun ya dame ki ki yi hakuri kinji share hawayen ki karma ki Jawa kan ki . ciwon kai” ' Ya samu ya lallasheta ta yi shiru sannan ya tafi zuciyarsa na faman saqe-sake ‘ Washe gari da sanyin saflya Malam Bala ya shirya ya nufi gidan Alhaji Bashir saboda yanda Laure ke ta faman ingiza shi. A kofar gidansa ya same shi zaune saman mota da News paper a hannunsa yana dubawa. Malam ya yi masa sallama, Alhaji Bashir ya dago tare da amsa masa cikin sakin fuska ya miqa . masa hannu su kai musabaha. Malam Bala ya ce ‘Dama Alhaji wajen ka nazo.” Alhaji Bashir ya ce, ‘To mu shiga daga ciki k0?” “A’a daga nan ma ya isa, Kara na kawo maka.” Alhaji Bashir ya ce, ‘Kara kuma tawa?” Ya ce ‘Danka Hamid na kawo maka qararsa ka ja masa kunne dan kuwa ya shiga har cikin gidana zai keta mini haddin‘ ya shi yasa na zo wurinka na kawo maka kashedinsa, don kar naje in dauki mataki kaga anatare babu dadi,don haka nazowurinka kai masa kashedi da iyalina.” Alhaji Bashir da ya nutsu yana kallonsa mamaki ya dabaibayeshi muryar shi a sanyaye ya ce, “Lallai ka haifi yaro ba ka haifl halinsa ba, don Allah ka yi haquri Malam in dai nina haifi Hamid ya gama bi k0 ta gefen gidanka kayi haKuri don Allah, don Annabi.’ Malam ya ce, “To ni dai kashedi na kawo maka ka ja masa kunne.’ Alhaji Bashir ya ce, ‘Insha Allahu.” Sannan ya juya ya Lafi buzun-buzun. Alhaji Bashir ya sauke wani gwauron numfashi, sannan ya yunqura ya nufl cikin gidan zuciyarsa a cunkushe ya shiga falon gidan, babu kowa a falon sai Hajiya Hanifa tana tsaye tana goge-gogenta a falon, yana shigowa ta tsaya da aikin da take tana kallon maigidan nata bakinta na fad'ar. “Latiya dai k0 Alhaji?” Muryarshi ba dadi ya ce, “Ina yaron nan yake?” Hajiya Hanifa ta ce, “Yana dakinsa ka san ai bai farka ba yanzu.” Alhaji Bashir ya ce tado mini shi maza-maza. Jikin Hajiya Hanifa na rawa ta nufi kofar dakin Hamid din. ta kwankwasa masa yana kwance nannad‘e cikin bargo yana Sheqa barcinsa, saboda rashin baccin da ya samu jiya. Ya bude idanuwansa tare da yunkurawa ya mike, yazo ya bude kofar, Hajiya ta dube shi kafin ta ce “Ka je Abbanka na falo yana jiran ka Ya amsa da. to, sannan ya juya ya koma ciki ya nufi bandaki ya wanko bakinsa da fuskarsa sannan ya fito ya dauko jallabiyarsa ya sanya ya fito Alhaji Bashir yana tsaye inda yake har Hamid ya qaraso yana qokarin dukawa ya gaishe da mahaifin nasa, ya ji saukar wani gigitaccen mari ya ratsa . Kunnensa ya dago da sauri yana kallon sa, cikin Bacin rai Aihaji Bashlr ya soma fada“Ni zaka dauka dan iska k0 Hamid dama abinda. ka koyo kenan a qasar wajen da na tura ka. Ni zaka jawa; abin fada a cikin garin nan. To baka isaba., maza ka tattara yanaka-yanaka ka koma Kaduna, yau ba sai gobe ba ka je ka kula da kamfanina tunda aikin gwamnatin bai zama dole ba, ba zaka zauna nan ka ja mini abun kunya ba, dama shi yasa da aka ce ka je ka nemi yarinyar nan Zainab kaqi saboda ba ka gaji da barbada ba, ka yi daidai ka kyauta tashi ka ba ni wuri.’ Jikin Hamid ya yi matukar yin sanyi ya miqe a sanyaye tare da fadar, “A yi h akuri." Ya juya ya koma dakinsa ya kwanta, tunani ya addabi zuciyarsa ‘ya rasa hanyar da zai bi ya taimaki yarinyar nan, ya ‘ lusmhe idanuwansa yana jin wani abu na masa yawo. Ya san fushin mahaifinsa yana fushi da shi ya yi kwana uku, tabbas kuma dole ya tafi Kaduna tunda ran mahaifin nasa ya Baci, ya lallaBa ya mike ya cire jallabiyar da ke jikinsa ya fada bandakin da ke cikin dakinsa. Saude ta dawo daga tallan safenta ta iske Laure Zaune itada Malam Bala suna tattauna magana! Hamid, ta a jiye bokitin wainar ta 'bama Laure kudin, ta karba tana kirgawa sannan ta ,dubeta tana fadar. “Jeki ga wake can ki kai markaden alala.” Saude ta amsa da to, sannan ta wuce Malam Bala ya dubi Laure yana fadar, “Kin ga na ma mance, Malam Garba ya fada min za"a kawo kayan sa ranar yarinyar nan gobe Laure ta cc, “Ai garama a gaggauta Malam mu kawar da yaran nan mu huta.” ‘ Iya abin da da Saude ’ta ji kenan ’ta fice tana jin tamkar za ta kifa saboda tashin hankali da fargaba. Haka ta je ta kai markadan ta dawo ta dafa alalar duk Laure na zaune tana kallonta, ta gama ta zauna ta Kirga mata a bokiti, sannan ta dauka ta tafi Hamid da ke kokarun sanya jakarsa a mota ya hango ta ya rufe motar da sauri ’ ya nufo ta da murmushi a fuskarsa ya ce, “Ranki shi dade barka da fitowa.” Saude ta waigo tana kallonsa kafin ta gaishe shi da dakusasshiyar muryarta. Hamid yargyara tsayuwa yana fadar. “Dama ke nake jira ki taho mu yi magana da tun dazu na Hamid ya ce ‘Kinga wannan fitowar wallahi Kaduna zan tafi yanzu yanzun nan mahaifina ya tura ni amma karki damu kwana uku kaWai zan yi in dawo saboda maganar ki, akwai wata hukumar kula da haqkin mata zanje ofiss din su a kan maganar ki Saude ta daga masa kai alamar eh ya yasa hannu cikin aljihu ya Ciro kudi masu yawa ‘yan yan naira dari biyar biyar guda ashirin ya miqa mata yana fadar ‘Ga wannan ki riqe ki yi amfani da su kafin in dawo.” Saude ta zaro idonta wadanda suka ciko da hawaye, ta girgiza masa kai alamar a’a, Hamid ya hade fuska yana kallonta ya ce “Karbi na ce mana me ye haka?” ‘ Ganin yanda ya hade fuska yasa Saude ta sa hannu ta karBa tana fadar, “Na gode.’ Ya zaro wata waya cikin aljihunsa ‘yar qarama mai kyau ya mika mata. “Ga wannan ki riqe ta hannun ki zan rinka kiran ki mu yi magana.” Saude ta karBa ya juya yana fadar, “Sai na dawo.” Saude ta juya da niyar taflya su kai ido hudu da ‘Yar Baba tana tsaye tana kallon su, suna hada ido ‘Yar Baba ta ja kwafa tana kada kai ta wuce 'Hankalin Saude ya yi masifar tashi wasu zafafan hawaye suka biyo kuncinta ta ji tamkar ta zubar da kudin saboda firgita, cikin tsoro ta je tallar yau ta dawo cike da tsoron irin hukuncin da za ai mata. Haka ta shigo gidan ‘tana faman sanda kamar munafuka a tsakar gida ta samu Laure da dillaliya suna zaune. Ita iyan tana kan tabarma, ita kuwa dillaliya tana kan kujera ‘yar tsugunne. Saude ta durkusa tana gaishe da dillaliyar sannan ta mikawa Laure kudin tallar nata, ta karBa ta sake mika mata hannu. “Ba ni sauran wanda kwarton naki ya baki Jikin Saude na rawa ta ciro kudin da wayar ta mika mata, Laure ta shiga jujjuya wayar a hannunta da kudin tana taBe baki ta dubi dillaliya tana fadar. “Duba ki ga fa.” Dillaliya ta karba tana gani, ta dago tana kallon Laure tana fadar, “Amma ni sai nake ganin kamar wata banza ce ta sauko muku daga sama, kawai ki yi kwance-kwance kinada abun duniya idan ma yaudara ce ta kawo sa ke dai me ya dame ki ita ta jiyo.” Laure ta ce, “Hmm! Dillaliya kenan ba zaki gane ba yaron fa da gaske aurenta zai yi ba wai da wasa ba.” Dillaliya ta dan yi shiru kafin ta ce, “To yanzu ya ki ke ganin za a yi?” Laure ta ce, “Gaskiya na fara tsora ta da lamarin nan karfa danhakin dakaraina yazo yatsone maka ido. Shi yasa na kira ki kawai ki dauke ta ki tafi da ita AIKATAU cikin gidaje har zuwa lokacin bikinta shekara guda za a sanya ranar daurin aurenta sai ki taho da ita kawai kin ga na yi maganin takadaranci k0 ba haka ba?” Dillaliya ta ce, “AI ko kin kawo shawara Laure, Abuja ma zan tafi da ita gidan wani sabon dan Majalisa, mai tashen kudi, wata kawata ce ta yi min maganar kai masu ma’aikata gidan, don haka ta shirya gobe zan zo in dauke ta da sassafe mu tafl, duk wata kina da dubunki biyar zan rinka karBo miki na albashinta.” Dadi ya kama Laure ta ce “Allah ya kai mu Kawata, tun Asuba ma zan tasheta.” Dillaliya ta ce, “Amma kina ganin ba za mu samu matsala da mahaifinta ba?” Laure ta ja wani gajeran tsaki tana fadar, “Ke kuma da sokawa zance wuqa kike wannan qotan wake san ya shi a lissafi ai sai yanda na yi da shi.” Dillaliya ta ce “To shi kenan babu matsala ‘yar uwa. ‘ . Duk labarinsu Saude tana jiyo su daga daki tana zaune saman simintin dakin kanta na jingine da bango, wasu irin hawaye ne masu zafin gaske kebin kuncinta. Wayyo duniya ita dai ta san ta zo duniya a rashin sa’a. Haka ta ci gaba da rera kukanta babu mai‘lallashinta. Washe gari Karfe takwas kamar yanda dillaliya ta fada ta zo cikin shirinta Laure ta tiso qeyar Saude a gaba, ta hada ta da dilla'iyar tana faman zuba mata kashedi. ‘Kl kulada aikin da za,a baki kuma banda dan hali, dan wallahi kika sake ki ka yo abin da za a koroki ki ka dawo min lokacin dawowarki bai yi ba wallahi saina shake ki kin mutu kin ji na fada miki, kuma kinsan zan iya Ta zaro naira dubu cikin kudin da Hamid ya ba ta, “wanda ta kwace, ta mikawa dillaliya tana fadar. “Ga wannan kiyi kudin mota.” Dillaliya ta karBa ta tisa Saude gaba suka tafi. Sai a lokacin wasu hawaye masu zafi suka samu damar zirarowa daga idanuwanta, tana ji tana gani suka nufa tasha cikin‘ yar qaramar motar nan Kurkura. Suna sauka dillaliya ta kama masu motar Abuja suka “ hau, dama. saura mutum uku, aka samu wani namiji yakarasa cikon na ukun direbaya dauhanyar Abuja. ALHAMDULILLAHI MASHA ALLAH _ Sai mucewa matafiya Allah ya kaisu lafiya. . Mu hadu a littafi na biyu Donjim yaddah wannan lbrn zaici gaba da kaYAwa [1/19, 5:14 PM] I love my mum: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚 [1/22, 10:28 AM] I love my mum: *YAR TALLA* BOOK 2 *CHAPTER 14* TUNda suka fara tafiyar Saude ke raira kukanta, a hankali har sai da suka kusa kawowa Suleja, sannan wani bacci mai nauyi ya dauketa Ba ita ta farka ba sai da ta ji Dillaliya na tayar da ita, Saude ta bude ido ta ga har sun kawo tasha, mutane na ta fita, sannan ita ma ta bi ayarin masu fitan Tun da suka sauka tasha Saude keta faman zare na-mujiya, ta zo garin da ba nata ba, za ta iya rantsewa tunda take ko gidan Mutum Daya bata taBa zuwa ba, to balle ta tsallaka Kano k0 wani garin da ke kusa‘ da su, amma yau ga ta cikin ‘Abuja tsamo-tsamo. Ikon Allah. . Dillaliya ta tsaida musu tasi tasha suka shiga, Saude dai na biye da ita da idanuwa sai faman waige-waigen idanuwa take. A hankali ta ga sun shigo cikin rukunin wata unguwa wadda kai tsaye za a kira ta da G. R.A Unguwar shiru ba ka Jin motsin komai sai kukan tsuntsaye da haushin karnuka ga manyan shuke shuke da suka sa titin unguwar tsakiya, kowane gida ka kalla ka san na wani kusan ne, gaba daya babu gidan da bana wani babban mutum ba a unguwar. Saude na cikin kallon jerin gidajen ta ji Dillaliya na fadar. “Nan za ka ajiyemu.” A hankali Saude tabi kofar gidan da aka ajiye su din, wanda za ta iya rantsewa tunda suka taho gidaje kadan ne suka kai shi kyau da tsaruwa. Saude ta zuro qafafuwanta ta fito kamar yanda ta ga Dillaliya ta yi, ta tsaya ta biya mai tasi din sannan ta yi gaba Saude ta bi bayanta. Kai tsaye katafaren gate din gidan suka nufa makeken gaske mai kama da Kofar shiga gari, ga wasu manya-manyan shuke-shuke da suka zagaye gidan gaba daya. Dillaliya ta tsaya tana latsa wata ‘yar karamar na’ura da ke like a bangon gidan. ' Wani irin tsoro da faduwar gaba suka bugi Saude anya kuwa, ba tahowa akai da ita a saida ita ba, don tana da yakinin wannan ba gida bane sai dai k0 wata ma’aikata ta sarrafa naman mutane Ba ta gama tunanin ba ta ji qarar tura gate din take ta yi ido hudu da wasu manya-manyan qarti har hudu, bakikkirin da su majiya qarfi, sun bude qofar, suna qokarin shiga suka ga wata bakar mota yar dunkulalliya mai daukar hankali ta ratsa ta shiga cikin gate din Dillaliya ta janyo hannun Saude da niyar su shiga, qartin nan suka yo kansu da wata irin masifaffiyar tsawa wadda tasa ‘yan cikin Saude juyawa gaba dayansu,fitsari ya fara kwace mata a wando, ita kanta Dillaliyar ta firgita, don cikin rawar murya take fadar. “Ku yi hakuri wurin matar gidan muka zo ni ce wadda na taBa zuwa da Hajiya Kande, wan,,,,,, “Shut up! I don ’t speak Hausa.” , Tuni ‘yan cikin Dillaliya suka juya, .don ita dai k0 zo in kashe ki da Turanci ba ta sani ba, ido ya ' raina fata ta dubi Saude tana fadar. ' ‘ “Me suke cewa?” Cikin muryar kuka Saude ta ce, “Ban sani ba nima.” Dillaliya ta harzuka “Yanzu ashe duk makarantar da ki ke zuwa asarar kudin tara kawai ake baki san komai ba?’ ‘ Saude dai ta yi shiru ba ta ce komai ba. Mutanen nan suka maida kofa suka rufe suka bar su nan tsaye, Dillaliya na ta faman saukewa Saude kwandon masifa, don ba ta iya Turanci ba. Kunji fa rashin‘ kunya. A hankali motar da ta shigo cikin gidan mai bakin gilas' ta faka a qatuwar harabar da aka tanada dan ajiye motoci, aka bude gidan direba da hanzari, wata ‘yar budurwa ta fito cikin shigar suite baqaqe da gani ba zata wuce shekara talatin ba , Tana fitowa ta bude gidan bayan motar tare da ja gefe ta kama, wata kyakkyawar mace ta fito, mai masifar kyau kai ka ce Balarabiya ce k0 Baturiya saboda tsananin kyau da hasken fata Tana sanye cikin shigar wani danyen leshi mai kyan gaske, wanda tsadarsa ta tasamma dubu dari da wani abu, an yi masa dinkin riga da siket matsatstsu irin dinkin matan manya na Legas, dan qaramin mayafi ne saman kafadarta wanda ta dora shi kawai ta yi a gefen kafadarta, kanta an kafa mata wani masifaffen dauri mai kama da daurin inji, qafar nan tana sanye cikin wani masifaffen takalmi mai tsinin gaske da ‘yar Karamar post din su a hannunta Idonta na sanye da wani qaton bakin gilas wanda: ya mamaye rabin fuskarta. A, Kai tsaye za ka lye. kiranta da ‘first Lady’ saboda haduwarta. Tana fitowa daga motar ta dubi yarinyar ’da ke tsaye, cikin wata irin murya mai kama da rada rada ta soma magana cikin harshen turanci. “jeki shigo da su.” Yarinyar ta amsa da ‘okey Tare da juyawa da sauri ta wuce ita kuma ta nufi cikin gidan nata tana wani irin taku, da wata irin faskekiyar waya a 'hannunta. ; Dillaliya da ta gaji da ruwan bala’i sai kuma ta yi shiru tana tunanin mafita, can dabara ta fado mata ta Ciro ‘yar qaramar wayarta baby Nokia ta lallatsa lambar Hajiya Kande ta kara a kunne; tun kafin ta soma magana ta ji an bude wata qaramar kofa yarinyar. Tace come and enter Dudda Dillaliya ba ta san abin da ta ceba, amma ta fahimta ta hanyar yi masu nuni da hannu da yarinyar ta yi, don haka ta zabaura ko kallon Saude ba tayiba tayiciki, don haka itama tamike da sauri ta bi ta Kan Saude ya yi masifar daurewa lokacin da ta shiga cikin harabar gidan, gabanta ya shiga wata rugurguza da bugawa mai tsanani, yarinyar ta yi masu jagora har zuwa wani qaton ginin bane hawa hudu, wanda tamkar da gilas kawai aka yi shi, dama da hagu duk iri daya ne, suka nufi Bangaren dama suka tattaka wata matattakala wadda ba tafi hawa shida ba, sannan suka ratsa ta wata Kofa mai fadi, anan ma mace ce tsaye qikam kamar an kafe ta, tana sanye ita ma da bakaken suita jikinta, sai da ta sa wata ‘yar na’ura ta daddana a jikinsu sannan suka ‘ wuce cikin kofar da za ta sada ka da qaton falon gidan. Saude ta bi matar da kallo a zuciyarta tana fadar, ikon Allah yanzu ita kuma wannan aikinta kenan” Kamshin rom freshner da turaren wuta dan Maiduguri shi ya dakar masu hanci su duka hakan ya tabbatar masu da sun iso falon, qaton gaske wanda aka zagaye da kujeru saiti uku, kuma kowane kalarsa. Kai batun ma in tsaya in, labarta muku haduwar falon duk wani bata lokaci_ne na barwa mai karatu ya yi image dinsa a zuciyarsa.‘Yarinyar wadda zan iya kira da Ingozi ta yi» masu nuni da cikin falon suka tafi suka zauna dirshan a ‘qasan kafet din duk da kujerun da ke zube kamar a cikin store. Yarinyar ta juya ta tafi abinta tabar. su nan zazzaune kamar masu zaman gaisuwa,; sai :rarraba idanuwa suke ba Sauden ba na Dillaliyar ba, wadda sai ka ce ba ta taBa zuwa ba. Tun suna tsammanin fitowarta har .suka soma . cire rai da za ta fito, don sun share fiye da awa biyar a zazzaune suna zare namujiya, sanyin AC sai kada su yake suna faman karkarwa. Tuni sun gama’fidda rai da fitowarta, ga gajiya ga wata~ masifaffiyar yunwar da ke kwakwalarsu, sai faman gyangyadin gajiya suke. , Kamshin turarenta shi ya farkar dasu; gaba daya Suka wartsake suna daidata nutsuwarsu,. idanuwan Sande na zube a kan matar wadda ta nufo inda suke tana lallatsa faskekiyar wayar da ke-hannunta,*Allah mai halitta abin da Saude ta iya fada kenan a zuciyarta, saboda yanda ta ga tsabagen kyau kwance a jikin matar, wadda ba za a kira ta da doguwa ba ba kuma gajeriya ba ce, sai dai a kira ta da tsaka-tsaki. Ba ta da qiba sosai, amma kuma ba ‘siriri ba ce sosai dai tana da jiki daidai-daidai. 1page is missing A yanzu ma takalmi ne mai tsini a kafarta, sai dai babu gilas yanzu a fuskar tata. Ta karaso cikin falon ta fada kan kujera ta dora kafa daya kan daya ba tare da ta dago ta kallesuba idonta na kan wayar hannunta ta rinka amsa: masu gaisuwar da suke ta faman kwarara mata Duk azaton Saude za ta basu hakurin shanyar dasu da ta yi amma sai taga kwata-kwata ma hankalinta baya kansu yana kan wayar dake hannunta ne falon ya dan dauki shiru, Dillaliya na nazarin ko ta fara. Maganane Cak matar ta mike wadda ba zata haura shekara talatinba ba, muryar nan tatat kamar mai rada ta soma magana. ‘Ki yi hakuri baiwar Allah ina da abin yi yanzu haka kikaga nazo nazauna dan insaurareki dama na lura kamar akwai wani important issue ne shi yasa na ce aje a shigo da ku, yanzu banida lokaci inada apointment da karfe sha daya.’ Tana maganar tana taflya. ’ Dillaliya ta fara bada hakuri cikin rawar murya tana fadar, “Ki yi hakuri ranki shi dade, wailahi na dan saurara ne ki fara magana kada in fara kiga kamar na yi rashin da’a a gabanki, dama ba wani abu ba ne yar aikin da kika ce kina so CE na kawo miki guda tun wancan watan‘ lokacin da mukazo ni Da Hajiya Kande taya ku murnar cin nasarar lashe zabe kika ce kina san yar aiki guda mai nutsuwa za ki Kara shi ne na tsaya na binciko miki na kawo miki Matar ta dan dakata daga tafiyar da take ta waigo a hankali, ta daura dara-daran idanuwanta kan Saude tana qare mata kallo sama da Kasa, tamkar wadda ta ga wani abun kyama a tare da ita, ta dauke kanta tana ‘ latsa wayarta cikin rashin kulawa ta ce, “Is okey. ” Ta dan karkace tasa hannunta saman hannun kujerar ta janyo sai ga wata ‘yar loka, shake da kudi bandir-bandir yan ‘ dubu-dubu, ta zaro masu yawa ba tare da ta Kirga ba ta cillawa Dillaliya tana fadar, “Ki hau mota, sai da safe.” ‘ Ba tare da ta~ saurari godiyarta ba ta yi gaba abin ta, dad'i ya kashe Dillaliya ta tashi jiki na Bari. tana fadar, “Ke kuwa kin yi nasara Saude, da ta dauke ki don Hajiya Kande ce min ta yi ta kawo mata yara ‘yan mata sun fi guda talatin tana cewa ba su yi mata ba, don haka saiki kula ni dai kin ga tafiya ta.” Ta mike ta bar Saude na zare namujiya, zuciyarta na faman kaiwa da kawowa, a yanzu ma kukan ya gagare ta' saboda tashin hankalin da take ciki yanzu ya fi gaban kwatance, tunaninta daya yanzu wace irin rayuwa ce za ta yi a gidan da ba ta san kowa ba? Wane irin‘ qalubale ne yanzu kuma za ta fuskanta? ' Ta Iumshe idanuwanta Kirjinta na barazanar ‘ fashewa, ga‘ bacci, ga yunwa, ga gajia, ga uwa-uba fargaba da tashin hankali da suka‘ dabaibaye zuciyarta. Tana nan zaune tana muzurai ta ga wata dattijuwar mace ta shigo falon sai dai ita da ganinta Bahaushiya ce wadda shekarunta ba zasu wuce arba’in ba. Ta dubi Saude cike da kulawa kafin tace, “Ki taso muje in nuna miki masaukin ki.” Saude ta yunkura ta mike tana jin tamkar za ta. kifa saboda rashin kuzari. Ta wata hanya ta ga sun bi ta cikin falon sai ga su sun flto wani Karamin bedroom shi daya, ba wasu karikitai a cikinsa sosai, ‘ karamin gado ne kwara guda mai kyan gaske kwanciyar mutum guda, sai wardrobe dinsa a gefe, shi kenan sai kafet da ke malale a dakin mai laushi. Matar ta juya ta dubi Saude tana fadar, ‘Nan shi ne dakin da Hajiya ta ce a sauke ki da fatan za kiyi . farin ciki, don gaba daya ma’aikatan .gidan nan masaukinsu a waje yake sai ga ki ke daga ~zuwan ki anwareki, natayaki murna." ‘ Saude dai ba ta ce komai ba don ita abin da ke cikin zuciyarta yafi gaban wannan. Ta zauna gefen gadon wanda ya sha lallausar shimfida ta ci. gaba da bin dakin da kallo, wanda take ganinsa ‘tamkar wata aljannar duniya. Matar ta sa kai ta fice saboda ganin hankalin Saude baya kanta. Ba ta jima da fita ba sai ga ta ta dawo hannunta riqe da plate da ke rufe, tare da pure water ta ajiyewa Saude ta juya ta fice. Jikin Saude har rawa yake wurin saukowa ta bude plate din, ta kafe idanuwanta saman abincin. Shinkafa ce jaloup babu ko wadatar kayan miya a cikinta. Saude ta sa cokali ta soma ci, sai dai bakinta ya gaya mata dan ba ta yi tunanin shinkafar za ta yi dadi a yanda ta ganta ba. Hannu ba ka hannu kwarya haka ta rinqa cin abinci, lokaci guda ta kawar da shi, sannan ta dauki ruwan ta fasa ta shanye shi tas. Tana sauke ledar ta saki wata‘ nannauyar gyatsa, idonta ya soma lumshewa ta yunkura ta haye kan gadon ta kwanta. Tana kwanciya wani barci mai nauyi ya dauke ta. Ba ta sake motsawa ba sai lokacin da ta jiyo ana ta kiraye-kirayen sallar Asuba, ta yunkua ta mike tana faman zazzare idanuwa can ta hango wata kofa jikinta na rawa ta nufe ta, ta bude ta tsaya sororo ‘ tana kallo; 'an qawata wurin da kayan qawata bandaki. ‘ ' ‘ Da sauri Saude ta maida ta rufe dan ita a zatonta wani dakin hutawa ne, ta dawo ta zauna tana san yin sallah amma ba ta san inda za ta kama ruwa ba, balle , ta dauro alwala. Da ta gaji da zama ne ta koma ta kwanta. ‘ Sai dai a yanzu ba barci take ba. idonta biyu, tana kwance tana tunani, wai ita ce yau a kwance saman lallausan gado irin wannan, ko a mafarkinta bata taba tunanin hakan ba. Fargabarta guda yanzu yanda ta ga matar gidan da ganinta tasan bata da mutunci, dan tunkan su hadu wani irin tsoranta ya mamaye zuciyarta‘ Tana nan kwance tana juyinta, ita kanta ba ta san awannin da ta kwashe ba, ta ji motsin ana shigowa dakin ta yunqura ta tashi zaune tana kallon mai shigowar. Matar Jiya ce ta shigo da sallamar ta, a yanzu ma hannunta na dauke da plate da cup a sama sai ruwa guda daya a dayan hannun ta ajiye, Saude da ke kan gado ta amsa mata sallamar ta tare da gaishe ta, ita kuma matar ta dan zuba mata idanuwanta kafin ta ce“Yau dai kin yi kwanciyar kadaici k0 ya ki ka ji gidan namu?” Sande ta yi murmushi ba tare da ta tanka ba, matar ta Kara gyara zama tana fadar, “Kin ga dai matar gidan sai kin yi takatsantsan dan ba ta da kirki, yanzu dubi duk dukiyar mai gidan nan amma abincin su daban na masu aiki daban. Haushi ya kama Saude a duniya ita akwai ta da surutu da naci amma ba ta iya gulma ba, dan haka cikin qosawa ta dubi matar tana fadar, ‘Don Allah inane bayan gida in je in kama ruwa har yanzu ban samu na yi sallah ba ” Matar ta ce, ‘Wane bayan gida kuma bacin wancan.” , Saude ta waro ido tana fadar, “Yanxu wancan kewaye ne?” Matar ta yi murmushi tare da fadar, “Taso muje in nuna miki yanda za ki yi amfani da 'su Saude ta yunkura ta mike ta bi bayan matar. Daya bayan daya ta rinqa nuna mata yanda ake amfani da komai da yake kwanyar tata a bude: take, a take: ta dauka, don haka suka fito, matar ta tafi ita kuma ta haye saman gadon ta janyo plate din ta bude, soyayyan dankalin turawa ne da kwai sai ruwan tea dan tsururu mai kama da fitsarin godiya. Dadi ya kama Saude yau za ta yi karin kumallon ‘yan gayu. Ta tisa dankalin tana ci tana faman santi a zuciyarta yanzu dama wannan shi ne rayuwar da masu aiki ke yi a gidajen da aka kai su aikatau? A gaskiya suna morewa don ita in dai za ta rinka samun abinci mai rai da motsi irin haka, to ai ba aikin da za,a sata a ,ciki batayiba bayan ta kammala sannan ta kwashe kayan ta ajiye gefe ta mike ta nufl bandakin ta dauro alwala ta tayi sallarta. Tana gammawa ta kishingida saman kafet din aiko nannauyan barci ya dauketa saiji tayi matarnan tazo tana tashinta ki tashi hajia nason ganinki A falo yanzu nan da minti biyar Hajiya zata sauko ta ki gana da ita.” ‘Yan cikin Saude su kai wata masifar juyawa, alamun tsoronta ya bayyana a fili qarara. Matar ta-yi murmushi ta mike tana fadar. “Hajiya na da matukar kwarjini a idanuwan kowa, ki dake ki fltO yanzu dan kar ta riga ki fitowa ki samu matsala.” Ba ta jira abin da Saude za ta ce ba ta juya ta fice, ta yunkura da hanzarinta ta nufi bandaki ta wanko fuskarta da bakinta jikinta sai faman rawa yake tamkar wadda za ta gana da Azara’ilu ta fito falon, Wanda yake tas-tas tamkar ba a shigwarsa saboda tsabar gyara. Saude ta raba daga qasa ta zauna zuciyarta na barazanar fashewa, don ta san yau za ta wuni anan ba ta fito ba. Sai dai da mamakinta ba ta kai minti biyar da zama ba ta jiyo Kamshin turarenta mai kwantar da hankali, zuciyar Saude ta tsananta bugawa da sauri-sauri, tamkar ana buga ganga, da Kyar ta iya daga kai kadan ta dan saci kallonta. Sanye take da wata dakekiyar shadda baka ‘yar Mali, dinkin riga da siket sun bala’in kama ta, an yi mata aiki da jan zare da fari da kuma kore, kwalliyar nan da gani ta kanti ce, tun daga hannuwanta zuwa qafafuwanta da wuyanta gwala-gwalai ne sai daukar ido suke takalmi ne baki mai masifar tsini a Kafarta. A yanzu idanuwanta rufe suke da baKin gilas din da . ya mamaye mata fuska,‘da makullin mota rike a hannunta tana kadawa, ta qaraso ta zauna saman daya daga cikin kujerun da ke baje a falon ta dora Qafa daya kan daya tana kadawa Saude ta zube tamkar mai shirin yi mata sujjada. Asma ta taBe baki tana yatsina fuska tamkar wadda ta ga abun Kyama ta daga mata hannu. “Ya isa bana san yawan gaisuwa, ya ya sunan ki?” . ~ Muryarta na rawa ta ce, “Sande.” Ta yamutsa fuska tamkar ba .za ta sake magana ba can ta ja fasali kafin ta ce, “Malama Saudat na san dai kin san nan k0 gidan waye a qasar nan aka kawo ki ba ki da bukatar sai na maimaita miki?” , Ta dan yi shiru tamkar wadda maganar ke mata ‘ wahala kafin ta ci gaba, “A dan jiya zuwa yau nasa a , dan yi mini binciken ki a bugi cikin ki dan a fahimci idan kina da yawan surutu. Is oke zuciyata ta nutsu da na dauke ki aiki, ni dai ba mazauniya ba ce ‘yar siya ce ba ni da time din kaina ma ballantana na wani, kullum cikin sabgogina nake; Don haka na ce a samo mini yarinya mai nutsuwa wadda _zata kula da maigidana. za ki tsaya ‘yar aiki a sashin maigidan, idan ki ka gaza kula da shi kuma zaki fuskanci fushina. Aikin ki shine zaki rinqa kula da abincinsa, abin shansa, gyaran sashinsa, wurin hutawarsa. Ki nutsu ki fahimci abubuwan da yake so da wanda baya so akwai lokutan da baya san magana, ki nutsu ki fahimta kar ki kuskura ki rinKa cika shi da yawan magana, baya san yawan kallo koda yaushe yana bukatar abu mai sanyi kusa da shi Yana cin abinci sau hudu a rana, yana shan fruits da daddare around 12:am kuma yana shan coffee, yana tashi daga barci qarfe bakwai, yana motsa jiki a lokacin da ya farka yana gamawa zai sha tea, sannan ya tafl ya watsa ruwa. Yana karyawa da misalin Qarfe goma na safe. ‘ Wannan shi ne tsarinsa, da fatan za ki kula, duk yan aikin da na daukar masa rashin fahimtarsa ne da basayi kesa inakorarsu. Ayanzu kece damata ta qarshe daga ke idan ki ka kasa kula da shi ba ' buKatar a Kara kawo masa wata, don haka ki tsaya ki nutsu ki fahimce shi ban san sakarci, idan kin yi aiki irin yanda yake so ni zan rinqa biyanki nera dubu ashirin duk wata. Da fatan kin fahimta?” Saude ta daga mata kai a sanyaye, amma . a kasan zuciyarta ta yi masifar karaya, don ta san ba ma zata iya ba yaudarar kanta kawai ta yi da ta amsa. ' Asma ta yunkura ta mike ta dubi matar da ke tsaye wadda da alama ita ce ma’aikaciyar sashinta, tace “Ki ba ta kayan ta saka, aikinta zai fara daga [1/22, 10:28 AM] I love my mum: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚 [12:17PM, 02/02/2017] 🙆🏼‍♂@lh@ji🙆🏼‍♂: [1/24, 9:31 AM] A A Dboy: *YAR TALLA* *CHAPTER 15* gobe qarfe biyar na yamma, ina da taro a Hotel sai na dawo." Ta juya ta fice abin ta babu maganar mayafi Matar ta mikawa Saude wata leda tana fadar, “Wadannan su ne kayan da za ki saka.” Saude tasa hannu ta karbi kayan jikinta a sanyaye. Matar ta yi wani takaitaccen murmushi tana fadar, “Ya na ga farawa da iyawa har kin yi la’asar, haba Saudat kar ki karaya mana ki batawa Hajiya rai kin dauke ni matsayin Auntynki ki yarda da abin da zan fada miki, ki sawa zuciyar ki za ki iya abin da aka saki da kuruciyar ki ai babu abin da zai gagare ki-Maigidan ‘mutum ne mai saukin kai yanayin rayuwarsa irin ta Turawa ce idan dai ki ka nutsu komai zai zo miki da sauki, kin ji?” Saude ta daga mata kai alamar eh sannan ta karbi kayan ta koma Bangarenta ta fada kan gadonta da. kayan zuciyarta na barazanar fashewa. Tsawon Iokaci ta dauka tana saka da warwara, , sannan ta yunkura ta tashi zaune ta zazzage kayan daga ‘cikin ledar tana daddagawa. Suite ce baKaKe riga da siket sai ta cikin fara, ta tsaya tana kallon kayan sun burge ta sosai, ta linke su ta maida a leda. Ta yunkura ta sauka daga kan gadon ta janyo abincin da Aunty ta kawo mata ta bude Tuwon shinkafa ne da miyar agushi, Saude ta zauna ta ci abincinta sosai ta gama ta mike tayo alwala ta dawo ta yi sallah sannan ta koma ta kwanta. Sai dai fargabar da ke zuciyarta babu abin da ya canza yinin yau haka ta yi shi, ba kuzari a jikinta tana tsoron abin da zai iya faruwa idan ta kasa yin abinda Asma ta sanya ta ba ta san irin hukuncin da za ta yanke mata ba qila ma ta iya kashe ta kawai. 'Zuciyarta ta kara tsinkewa wasu irin hawaye masu zafi suka taru a idanuwanta, watakila ajali ne ya kawo ta gidan, tasa hannu ta goge ‘yar kwallyar da ta tarar mata ta juya daga gefen da take ta lumshe idanuwanta, amma ba barci take ba. Washe gari Saude na zaune a qasa gefen gadonta, tana tunanin da ya zame mata jiki, zuciyarta ta lula duniyar tunanin Hamid da irin kulawar da ya. ba ta a rayuwa. K0 a yanzu ba ta fidda rantaba tana ji a jikinta za ta koma gida ta same shi, tana ji a jikinta shi ne mijin da zai aureta su yi rayuwarsu cikin kulawa da Kauna. Aunty ta turo kofa ta shigo tare da sallama, Saude ta bude idanuwanta tana amsawa. Aunty ta tsaya daga bakin kofa tana fadar, “Ya na gan ki anan zaune, k0 kin manta ne yau ne ranar da aikin ki zai soma?” Saude ta kalli tace Na sani Aunnty ba ta ce sai Karfe biyar ba?” Annty ta yi wani takaitaccen murmushi kafin ta ce “YallaBai ya yi tafiya zuwa qasar China sati ukun da suka wuce, don haka yanzn za ki tashi ki fara gyara masa Bangaren shi ki zauna har ya iso.” Ta wurgowa Saude makullai tana fadar, “Ungo wannan sune makullan bangaren sa.” Saude ta cafe lokacin da bugun zuciyarta ya tsananta, Annnty ta juya tana fadar, “Ki tashi ki shirya ina falo ina jiran ki na raka ki Bangaren nasa.” Saude ta taKarKare ta mike ta nufi bandaki ta dade a tsaye zuciyarta na faman kaiwada komowa, sannan ta daure ta watso ruwan ta fito, ta zauna bakin gadonta ta ciro kayan daga cikin ledarsu ta sanya kamar yanda Aunty ta nuna mata, ta mike tsaye siket din bai Karasa isowa kasa ba ya dai wuce gwiwoyinta, sannan ta janyo hijabinta ta sanya sannan ta kawo takalmin da ke cikin kayan ta saka wanda yake sawu-ciki, sannan ta fito ta samu Aunty zaune tana jiranta tana fitowa suka jera suka fita. ~ ' Gaba daya suka fita daga wannan shashin, suka . nufi daya Bangaren wanda ke hagu. Aunty ta karBi makullin ta bude sashin suka shiga, komai na sashin irin na wancan ne, babu abin da ya bambanta. Aunty ta mika mata makullin tana fadar. “Ga shi ki goge komai ki gyara,idan kin gama. Ki zauna har ya iso, da ya iso ki karbi jakarsa ki kawo masa abu mai sanyi kin ji?“ Saude ta daga mata kai ' alamar eh. Sannan ta juya ta tafi ta bar ta tsaye tana faman bin katafaran falon da kallo. To ta ina ma za ta fara? Ita dai a iya ganinta ba ta ga abin da ya yi datti ba, ta taBe baki sannan ta fara takawa saman matattakalar ‘ ‘ benen ta shiga cikin falon, kai tsaye wani qaton falo ne ta fara shiga wanda, har yafi na farkon haduwa da tsaruwa. Idanun Saude suka sauka saman wani makeken hoto wanda yake jingine a kasan gefen bango, ta danci gaba da bin hoton da kallo. Wani kyakkyawan namiji ne ajin qarshe wanda shekarunsa ba zasu‘ wuce talatin da biyar ba, kallo daya za kai masa ka tabbatar ya hadu tamkar wani Balarabe, yana rungume da Asma sunyi murmushi'su duka, sun yi * masifar kyau, dama duk kyan Asma bata kai mutumin ba, duk da yana namiji, don shi kalar kyansa yafi kama da na Larabawa saika rantse Balaraben Saudiyya ne Saude ta wuce a hankali ta shiga zagaye falukan sashin da bedroom din dake ciki, ita kanta tana ,tausayin kanta saboda sashi~sashin dake ciki sun kai goma, haka ta dauko mofa da tsintsiya da tawul da .bokiti ta fito ta shiga gyaran sashin,‘ Sai da ta gyara ko’ina da ina ta goge tare da kunna bona bonar da ke falukan kowacce ta zuba turaren 'wuta a ciki, sannan ta dauki room fresner ta dinga feffesawa a ko’ina da ina, ta Kara gudun A.C sannan ta rurrufe ko’ina kamar yanda Aunty ta fada mata, ta dawo falon qasa ta zauna gefen kujera tana faman zare na mujiya, sanyin A.C na ratsa ta. A take tamkar ta kwanta saboda tsabar gajiyar da ta yi. Misalin Karfe biyar da ‘yan mintina Saude ta ji an turo Kofar falon ta zabura ta tashi tsaye kirjinta na wani masifar bugawa da qarfl da qarfi. Shi daya ne ya shigo yana sanye cikin shigar Kananan kaya, sai wani yaro da ke bayansa wanda ke sanya da suit, yana rataye da irin jakar ma’aikata. Ahmad ya tsaya yana watsa mata wani irin kallo wanda ya Kara hautsina mata‘ yan hanji, muryarta da rawa ta fara fadar, ‘Sannu da zuwa ‘ Shut up! You are very stupid, get the hell out of here Jikin Saude ya hau Bari ko’ina na jikinta rawa yake ga shi dai ba ta san tsiyar da ya fada ba, amma yanda ya kwatsa mata tsawa, ya tabbatar mata da korarta yake don haka jiki na Bari ta gifta zata wuce, Ahmad ya kara daka mata tsawa. “Wait, na ce ki tsaya.” Saude ta ja ta tsaya, sai faman kyarma, take, don yanda ta ga tsantsar Bacin ransa ta tabbatar zai iya kai mata duka cikin bacin rai yace hope baki dai hau min sama ba?" Saude ta yi shiru tana faman rawar murya, yaja wani dogon tsaki ya wuce ciki, jikin ta yana rawa ta wucc, sai faman harde qafafuwa taka , har tabar falon. A tsaye ta samu Asma sanye da wata doguwar riga milk colour, ta dora dan qaramin mayafi saman kanta wanda ya tsaya iya wuyanta, gilas dinta yau a hannu yake tare da makullin mota da alama fita za ta yi. ‘ Saude na shigowa ta tsaya tana kallonta, cikin tsantsar takaici take kallonta, jikinta ya qara yin la’asar tana shirin dukawa ta gaishe ta ta ji saukar wani mahaukacin mari' har sau biyu, dama da hagu, * wanda yasa sai da ta kifa cikin takaici Asma ke fadar. “Ashe ke dakikiya ce ban sani ba sakarya, jaka ce keba? Dube ki, dubi abinda da ke jikin ki, yanzu da wannan bakin abun ki ka shigar masa ne? Oh! Kin gama dani, amma kin ci sa’arsa da ya kyale ki da kin gane baki da wayo, don na tabbatar yau k0 ' ruwa ba zai iya hadiya ba.” Ta ja tsaki mts! Ta juya ta dubi Aunty wadda ke« tsaye tace, “Rabi maza Id debo mata kayan shafawa da turarurruka, ta cire wannan bakin abin ta shirya, ki tabbatar ta koma ta ba shi hakuri, Wallahi idan ki ka sake yaqi amincewa da ke zama ‘yar aikinsa na rantse miki sai kin fuskanci fushina kin ji na rantse.” Ta'Karasa maganar da karfi, sannan ta juya ta yi gaba abin ta. Wasu irin hawaye masu zafl suka biyo kuncin Saude, wayyo Allah wannan wace irin rayuwa ce ta samu kanta a ciki? Au'nty ta dafa ta muryarta a . sanyaye. . “tace kizo mu je, kada dan wannan abun ya razanar daké, na san za ki iya yin abin da ma yafi wanda aka saka ki, idan dai har kin sawa ranki zakiyi, za ki yi Saudat, please zo muje.” Saude dai ba ta tanka mata ba ta juya ta bi ' bayanta suka nufi wani sashi daban, ta tura wata '» kofa sai ga su sun fada wani dan falo irin na ' Sauden. ‘ Aunty ta bud‘e wata loka da ke jikin bango sai ga kayan kwalliya kamar su ci kansu, ta dauko leda ta dibar mata masu yawa, tun daga man shafawa, sabulan wanka, kayan kwalliya har da turarurmka, sannan ta bude wardrobe ta ciro dan qaramin hijabin nan mai tsayawa iya wuya wato himar kalar ja ta mika mata tana fadar “Ki yi sauri ki je ki gyara ki tafi, dan na san yanzu haka akwai abubuwa da dama da yake buqata.” Saude ta karBa ta fice jikinta amace. Sai data sake wani wankan sannan ta fito ta shafa mai a jikinta ta kawo wata ‘yar qaramar powder fara ta shafawa fuskana, ta sa man lice a bakinta, sannan ta mike ta mayar da kayan jikinta, ta dauki qaramin hijabin ta rufe kanta. Wani irin abu ya cunkushe mata zuciya, tunda take a duniya bata taba irin wannan shigar ba ace kana dan Musulmi amma ka flta a haka, kai duniya! Takaicin kanta ya kamata, k0 tsayawa ta dubi kanta ba ta iya ba ta dauki turare ta fesa guri uku kawai sannan ta fice zuciyarta na faman kai kawo. Tsoronta ya qara tsananta lokacin da ta iso bakin sashin nasa ta daure ta yi ta maza ta sa kai cikin falon cike da fargaba. Turus! Ta ja ta tsaya ‘yar sallamar da take shirin yi ta makale mata a makoshi, wani irin tsoro da fargaba mai tsanani suka dirar mata Kwance yake tsakiyar falon saman kafet ya yi daidai. daga shi sai gajeran wando ba k0 singlet jikinsa, ya yi matashi da hannayensa fuskarshi na kallon sama, idanuwan shi a lumshe suke kamar mai barci. Saude ta runtse: idanuwanta ba ’tana shirin ta juya da sauri ta-«koma sai kuma ta tuna Da maganar Asma da take fadi“Wallahi idan kika sake Yaqi amincewa dake a matsayin yar aikinsa sai kin fuskanci fushina. " [1/24, 9:31 AM] A A Dboy: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚 [1/24, 10:13 AM] A A Dboy: *YAR TALLA* *CHAPTER 16* Saude ta ja ta tsaya tare da juyowa , muryarta na rawa ta sake yin wata sallamar, Ahmad ya bude idanuwansa wadanda suka kada sukai jawur, yana kallonta, kallon da ke tabbatar da tsananin tsananta cikin idanuwansa ya sake she idanuwansa kafin ya soma magana tamkar wanda yake sanyin rada. “Ba cewa nayi kar ki bari in sake hada hanya da ke ba? Okay ba kiji ba kenan, shi ne ki ka dawo k0?” Muryar Saude na rawar disko ta ce hajia ce tace min Ba ta qarasa fadar abin da za ta ce ba ya zabura a Qufule yana fadar, “Wuce ki bar falon nan,‘idan kuwa ki ka bari raina ya baci za ki hadu da abin da baki yi tunani ba. Gate out! ” ‘Yan cikin Saude suka Kara Juyawa, wannan shi ne gaba kura baya hayaki, wasu irin hawaye suka biyo kuncinta ta durqusa a gabansa cikin kuka tana ‘ fadar, “Don Allah don Annabi ka‘yi min rai ka yi haquri wallahi idan na koma na ce mata ka kore ni kasheni za ta yi don Allah ka yi hakuri ” . Ahmad’ya tsaya yana kallonta tsawon lokaci yana jin tamkar ya shake ta saboda takaici, don a duniya idan akwai abin da ya tsana‘to bayan kuka Ne k0 cikin film baya Kaunar ya. ga ana kuka, ' Ya ja tsaki mts! Tare da fadar “Tashi na ji ya ishe ni haka.” Muryarta a raunane ta ce “Na gode. ”* Bai tanka mata ba ya juya ya koma kan kujera ya yi kwanciyarsa abinsa tsawon Iokaci babu wanda ya Tanka can dai Saude da ta lura idan za su kwana a haka bai damu ba sai ta mike ta dan matsa kusa da shi kadan ta durkusa tana fadar, ‘Ko kwai abin da ka ke buqata in kawo maka?” Ahmad ya dan tsura mata ido= kadan, kamar wadda ta zage shi sannan ya juya tare da kada mata yatsun hannun shi ba tare da ya yi‘ magana ba, zuciyar Saude ta Kara tsurewa, don ta lura mutumin ya tsane ta da wuya idan kuma zai bata mazaunin mai aikin nasa. Kwalla ta cika mata idanuwa cikin muryar kuka ta soma magana, “Don Allah to in kawo maka wani abu mai sanyi.” " ‘ “Na ce miki a’ a, a’a shin wai k0 dole ne?” Yanda yake mata maganar ya firgita ta, saura kadan da ta fadi saboda razana. hawayen da suka taru a kwarin idanuwanta suka samu damar biyo kuncinta. ' Ahmad ya ja wani gajeran tsaki yana fadar, “Oh! My God, jeki kawo mini koma meye zaki kawo, k0 baki Jiba?” Ya fada a harzuke Saude ta mike a razane ta nufi gurin firij din ta , bude, lemuka ne kale-kale sun fi kada ashirin jikinta sai rawa yake ta rasa wane za ta dauko masa, can idonta ya sauka kan fresh milk ta kwali, tasa hannu ta dauko masa tare da kofi na tankaran guda mai gindin turmi ta rufe firij din ta nufo inda yake. Ta durkusa a gabansa tasa hannu ta gage hawayen da ke zuba a idanuwanta sannan ta balle murfin ta tsiyaya masa fiye da rabin kofi din, ta miqa masa, ba musu ya sa hannu ya karba Saude ta sauke wata nannauyan ajiyar zuciya, wadda ta janyo hankalinn Dr. Ahmad ya dan zuba mata idanuwansa kadan sannan ya dauke kansa. Ta yunkura ta mike tana fadar, ‘Sai da safe.” K0 uffan baice mata ba har ta fice Kai tsaye dakinta ta nufa ta kwanta zuciyarta ta lula duniyar tunanin abin da ya faru dazu ya rinqa dawo mata ita kanta ta ba kanta tausayi dan zama tare da miskilin mutum irin wannan ba Karamin aiki ba ne, shin k0 yaci abincin ma ko k0 haka nan ya kwanta? Allahu ‘A'a lamu. Ta daga kanta tana kallon agogon dake manne a bangon dakin karfe goma da‘ yan mintina, ta qara ' juyawa sosai a kan gadon, dan to san saura ‘yan mintina lokacin shan coffee dinsa ya yi, yanzu dan kawai zai sha wani coffee har sai wani ya je ya hado masa saboda san kai kawai irin na masu kudi 1page is missing Saude ta zabura ta durgusa tana gaida shi, k0 inda take bai kalla ba ballantana ta sa ran zai amsa, don haka taja bakinta ta tsuke tana kakllonsa ya isa gaban firiji ya bude ya dauko robar ruwa guda, ya murde murfin ya daga sama yana kwararawa cikinsa ya sha ya kusan rabi sannan ya ajiye ya waigo da niyar wucewa. Saude ta yi saurin sunkuyar da kanta ta ci gaba da abin da take, don tsoron kar ya ‘ kama ta tana kallonsa. ' Bai kula ta kanta ba ya haye sama abinsa. Saude ta girgiza kai a zuciyarta tana mamakin miskilanci irin nasa, don har ma ya zarce matar tasa , ' tunda ita duk abin da kai za ta yi magana, amma shi sai dai ya kore ka. Ta girgiza kai ta ja gefen kafet ta zauna tana muzurai; , Da misalin Karfe goma saura minti biyar Ahmad ya sauko daga sama kamshin turarensa ya mamaye falon gaba daya, Saude ta dan dago a hankali ta saci kallonSa sanye yake da wani yadi mai laushin gaske sky blue, ya sha aiki da farin zare. Yadin mai Sharashara ne hakan ne yasa akan iya hango farar singlet dinsa da short nirker din da ke jikinsa, farar fatar . nan ta yi wani luwai-luwai kamar jikin Jariri. * * Ya ja ya zauna kan kujera da waya rike a 'kunnensa yana magana cikin harshen Turanci, Saude ta yunknra ta mike ta fita daga falon ta bi wata ‘yar kwana da ke gefe sai ga ta ta Bude qaton dakin dafa . abinci wanda ma‘aikata ke ciki, harsu uku duka mutum daya ne Bahaushiya a cikinsu. To su wai me yasa ba sa son daukar Musulmai zalla aiki ne? Ba ta da mai amsa mata wannan tambayan, don ‘ haka ta karb0 break din yallaBai din sannan ta fito. A bakin kofa su kai karo da Aunty ta zo daukar wa Hajiya nata suka gaisa, sannan ta wuce, ta nufi falon nasa. : : Yana zaune kamar yanda ta bar shi har yanzu bai gama wayar ba, Saude ta dora tiren kayan abincin saman dinning table sannan ta koma can gefe nesa da shi ta zauna tana jiransa ya gama wayar amma da alama bai da niyar gamawa har wani kashe murya yake yana zuba shagwaBa, sai. kace wani qaramin yaro, duk kunya ta ishe ta, ji take tamkar ta zuba da gudu, don duk da ba ta. san abinda yake cewa ba, ' amma zuciyarta ta ba ta da matarsa yake wayar Ashe dama yana dariya irin haka? Lallai k0 da wa yake wayar nan, to an jiKa ta a shanye Ba ta ankara ba tana duniyar tunani sai dai ta ji muryarsa na fadar, “Kawo abincin nan Saude ta zabura har tana neman faduwa ta mike, ta nufi dining din ta dauko kayan karyawar tazo ta gabansa ya nuna mata kan kafet din ta aje masa anan sannan ta koma ta zauna Ya watsa mata wani kalla mai, kama da harara kafin ya ce, “Waye kika ajiye ya yi serving din. " Saude ta waro ido tana kallonsa cike da razana don ita dai ba ta san abin da yace ba, ya ja tsaki tare da fadar, “Na ce waye zai zuzzuba abincin?” . Saude ta yi saurin matsowa tana fadar, “Yanzu zan zuba.” Ta dauki kofi ta zuzzuba kayan tea, sannan ta zuba ruwan ta cika kofin d taf-taf ta juya da cokali ta mika masa. Ahmad ya zuba mata dara-daran idanuwansa cike da takaici ya ce, “Yanzu duk wannan Waye zai shanye shi? Kin tattakura kin shaqare kofl da ruwan tea dan rashin hankali mts!’ Ya karBi shayin ya rage fiye da rabi a wani kofl din, sannan ya soma sha. Jikin Saude ya Kara yin sanyi, tana tsoron ta zuba masa abincin ya gwasale ta, muryarta a sanyaye ta‘ ce, “Abincin kamar yaya za a zuba?” Bai kalli inda take ba ma ballantana ta sa ran zai tanka mata, zuciyar ta ta Kara tsinkewa, ta yi ta maza ta dauki plate da cokali ta bubbude kulolin, soyayyar doya ce da miyar swse sai daya kular yam ball ne Wanda ya ji nama da kwai, sai dayar farfesun nama ,ne da dankalin turawa, wato~ papper chicking, sai gasashshen biredi an masa wani yanka mai kyau an dora saman plate, wato sandwich. Saude ta turo masa . plate din biredin, sannan ta zuba masa farfesun naman a plate din sai ta debi yam ball din ta zuba masa a gefen bredin, ta maida saman ta rufe. “Bai tanka mata ba ya rinqa cin abincinsa sannu a hankali har ya gama, sannan ya dago ya dube ta kamar wanda aka tilastawa sai ya kalle ta ya ce, “Tashi kawo mini morning fresh ‘Yan hanjin Saude suka duru ruwa, yau na shiga uku! Wani abu ne kuma haka? Yanda ya kafa mata idanuwa yasa a dole ta yunkura ta mike. To ina za ta dosa? ‘ Ta tsaya cikin falon tana faman diminiya, tadan juyo kadan ta ga idan yana kallonta su kai ido hudu, gaba daya ya tattara nutsuwarsa a kanta, ai kuWa take ta Kara tsurewa to k0 dai tsintsiya yake nufi, don ta lura da ya yarda wani dan qashi a kasa. ‘ Ta ja wata ajiyar zuciyar samun mafita, sannan ta dauko ‘yar tsintsiyar da take share-share da ita a falon ta nufo shi, ta durkusa tare da fadar, “Ga ta.” Haushi da takaici suka kashe Ahmad. ya watsa mata wani mugun kallo wanda yasa duk wata laka ta! jikinta ta mutu ya ja tsaki mts! Yana fadar. ‘ “Ke jakar ina Ce? Wannan ita ce morning fresh din? Idan ba ki sani ba ba za ki tambaya ba, sai kawai ki je ki ta shashanci, ki kawo mini tsintsiya inyi tsiyar me da ita?” Ya girgiza kai cike da takaici yana fadar, “Kai Allah dai ya wadaran dakikin mutum stuppid girl ni Fice ki bani wuri, na daina hada ido da ke, sakarya kawai.” Zuciyar Saude ta Kara karyewa idanuwanta suka ciko da hawaye muryarta na rawa tace, “Ka yi hakuri don Allah. ” Ya watsa mata idanuwansa tare da Jan wani dogon tsaki “Mts!” ‘ Saude ta yi saurin sunkuyar. da kanta Kasa, yana kallonta cikeda tsanarta ya ce, “Ki fadawa Madam, ina da meeting yau kar ta ga ban sa an kawo mata sakon nan ba sai, zuwa gobe komai kr nan mu hadu ta network.” Yana gama fada ya mike ya sa kai ya fice ya bar Saude a tsaye, wasu siraran hawaye suka biyo kuncinta tadurkushe a gun. Wayyo ni Allah na ya. Ubangiji ga Saude na san baka mance da ita, ba ya Allah Ubangiji ka cire ni daga' wannan rayuwar qangin“ bautar da rashin galihu.’ A hankali ta fashe da wani irin kuka mai cin zuciya, sai da ta yi mai 'isarta bata da mai lallashinta sannan ta share ’hawayenta. Ta diba tiren abincin dake gabanta t duba ba wani da yawa yaciba sannan itama ta zauna ci tsakura kawai tayi saboda yanda take jin zuciyarta babu dadi. Tana gamawa ta mike ta fita da kwanukan sannan ta dawo ta gyara falon tamkar ba a taba shigowa ciki Ba sai da ta gyara ko’ina ta yi turaren Wuta ta sassaki labulayen tagogin ta qara gudun AC ” a koina sannan ta rurrufo falukan ta fice, ta nufi can Bangaren. , Babu kowa a falon qasan sai Aunty tana turaren wuta, ta gaishe ta cike da girmamawa, Aunty ta bi ta da. kallo tamkar mai karantar, wani abu. Muryar Saude a sanyaye ta ce “YallaBa‘i ya ce“A fadawa Madam ba zai dawo ba sai gobe Aunty ta ce, “To ki hau sama ki fadawa Hajiyar da kanki.” Saude ta dan yi jim cike da tsoro. Aunty ta katse mata tunanin da fadar, “Kije mana Saudat tunanin me ki keyi haka?” Saude ta girgiza kai sannan ta wuce ba tare da ta ce uffan ba, ta tattaka matattakalar benen ta haye sama. A karo na farko kenan da ta fara hawa saman. ‘ Haka kawai ta tsinci gabanta na faman faduwa,_ wani irin tsoro mai tsanani ya dirar mata, ta rinqa bin falon da kallo aljannar duniya, lallai ba banza ba masu kudi ke mantawa da ni’imar da Ubangiji ya yi masu ba. Muryarta na faman sarkewa ta yi sallama‘ har sau biyu. Babu wanda ya amsa ga shi kuma tana jiyo hayaniyar mutane a falon da ke gefe, don haka ta Kara matsawa tare da yin wata sallamar. Tun kafin ta karasa rufe bakinta ta ji an watso mata wata dunkulalliyar ashariya cikin ta ya duri ruwa, kafin ta yi tunanin juyawa ta ga Asma gabanta, tun kafin ta karasa tantance ta, ta ji saukar wani mahaukacin mari a kuncinta gefen dama da hagu. Saude ta durkusa ta dafe kuncin lokacin da ta ga wata wuta ta gifta mata a idanuwa, cikin takaici Asma ke fadar, “You are very" stupid, ke jakar ina ce? Da ina meeting za ki shigo ki distubing dina banza sakarai shashasha, uwar me aka yi ne da ta sa ki ka shigo mini har falo?” Saude ta durkusar da kanta qasa daga duqen da take, hawaye suka soma zarya a kuncinta, cikin muryar kuka ta ce “Ki yi haquri dama Yallabai ne ya aiko ni, ya ce ya yi tafiya sai zuwa gobe da yamma za.. ‘So What! Na ce sai me? Da ya aiko ki sai ya ce ki iske ni duk inda nake ki fada mini, iye?’ Ta ja wani dogon tsaki mts! Kafin ta ce, “Da alla gate out on my parlour’ Ta sake kwatsa mata tsawa, “I say gate out k0 ba kya jine?” saude ta zabura ta mike ta bi hanyar da take nuna mata jikinta na rawa, Asma ta sake jan wani tsaki tana fadar, ‘Stupld kawai.’ Sannan ta juya ta koma ciki abin ta. Saude na fita kai tsaye bangarenta ta fada kan gado ta fasheda Wani irin kuka mai cin zuciya wayyo Allah yau ta ga ta kanta, wannan wace irin rayuwa ce ta samu kanta a ciki me cike da qaskanci da wulaqanci ni Saude? Kuka take ‘sosai bata da mai lallashinta. Rayuwa kenan. ,,,,,,,,,,,, ,,,,,,,,,,,,,, Haka rayuwar Saude ta ci gaba da tafiya cikin kaskanci da rashin galihu, kullum tana cikin bauta, ita da bayi ba su da bambanci, ’sauqin‘ ta ma tun a gida ta riga ta saba da wahala. Yanzu haka rakube take gefen kujera bayan ta gama. gyara falon ta gaji, ta rakube gefe tana kallon tashar Saudiyya, wani shiri da suke yi duk karfe biyar na yamma. ‘ Dr. Ahmad ya sauko daga sama yana sanye da kayan wasanni na kwallo, gajeran wando da singleti sai takalmin ‘yan kwallo, Saude ta saci kallon shi kadan. Kayan sun masa kyau sai ka ce irin turawan , nan da ke buga wasan kwallon kafa, ba tare da ya kalli inda take ba ya wuce abinsa yana fadar. “Ki biyo ni da robar ruwa mai sanyi.” Saude ta zabura ta mike ta nufl wurin kantar da -ake ajiye lemoka ta bude ta Ciro robar Faro guda kwalin lemo guda tare da kofi guda daya tabi bayansa A qaton filin wasan‘ dake gefen lambun gidanta“ same shi yana ta faman tika kwallo shi daya, duk ya hada gumi, Saude ta rakube gefe rungume da tirenta hannu tana kallon ikon Allah, zuciyarta na _ raya mata wasu abubuwa da dama cike tàke da mamakin Yallabai din tana mamakin yadda duk abin da ya yi sai ya yi masa kyau, tunda take bata taba ganin muninsa ba, kullum ma kamar~kara masa kyau ake. Shin dama akwai mutum irin haka? Ba ta ankara ba sai dai ta jiyo sautin muryarsa na fadar. “Wai ke k0 kurma ce ne?’ Saude ta zabura da saurinta ta nufe shi jikinta na rawa, ta durkusa‘ gabansa cikin rawar murya tana ~ fadar, “Ga ni.” Ya ja tsaki cike da takaici kafin ya ce, “Hankalin ki yana ina ne lokacin da na wage murya nake ta kwalo miki kira? Me ki ke kallo ne a jikina wanda har ya dauke miki hankali? Tunanin me ki ke’?” ‘ ' Ya sake jan wani dogon tsaki ya gif‘ta ta ya‘wuce yana sharce gumin goshinsa da hannunsa, ya bar ta a duke da tiren lemuka tana faman rarraba idanuwa, tsoro ya kama ta dan ba ta san irin hukuncin da zai yanke mata ba. Haka ta daure ta dake zuciyarta ta bi bayansa, tsaye yake gaban na’urar sanyaya ruwa, ya tara kofinsa yana zubowa, Saude ta durkusa. gabansa muryarta a raunane ta ce, “Don Allah don Annabi YallaBai ka yi hakuri, insha Allahu na yi maka alkawarin ba zan Kara ba.” nazarin wani abu a fuskarta, ba tare da yace uffan ba ya dauki ruwansa ya durawa cikinsa ya ajiye kofi din ya yi mata nuni da hannu alamar ta wuce kawai, ya yi gaba abinsa ya haye sama. Saude ta girgiza kai zuciyarta na cike da mamakin miskilanci irin na dan adam. Duniya kenan. ‘ Da misalin Karfe tara na safe Saude ta kammala ayyukanta gaba daya, ta kunna turarukan wuta a ko’ina sannan ta dauko room freshner ta faffesawa labulayen falukan da kujerun‘ Dr. Ahmad ya shigo falon daga shi sai dan qaramin gajeran wando duk ya hada gumi, da alama daga motsa jiki yake. Kai tsaye ya wuce ya tsiyaya ruwa a kofl ya sha kusan kofi biyu, sannan ya wuce abin sa. Har ya taka step din da zai kai ka falon shi na sama ya waigo ya kalli Saude fuskarsa ba yabo ba fallasa yace “Kije ki sanar da kuku yau ina da baqi da misalin qarfe sha daya na safiyar nan ya tanadi duk abin da ya san za a iya bukata." Yana gama fada ya yi gaba ba tare da ya tsaya ya saurari amsawarta ba. Saude ta maida kayan sannan ta fice da sauri dan isar da sakon da aka aike ta. Tana dawowa ta same shi tsaye a falon sanye da farar jallabiya a jikinsa yana waya ta ja gefe ta zauna. Ya‘yi wayarsa ya gama sannan ya matso inda ~ take ya‘ mika mata wani key yana fadar, “Karbi wannan key din ki bude wancan falon ki gyara anan zan sauke bakin nawa.” Saude tasa hannu biyu ta karba, ya juya ya koma sama, ita kuma ta mike ta nufi kofar: da niyyar budewa, amma abun ya faskara, saboda gaba dayan kofofin gidan odar waje ne in ba wanda ya saba ba. ’don ko wancan karan da za ta shigo falon nasa ’anty ce ta“ bude mata, Ta dan nutsu tana tunanin * .yanda Suka bude a wancan karon', cikin ikon Allah ta ~samu ta bude kofar sannan ta shiga. Katafaren falo ne dogo mai girma wanda ya ji kujerun silba masu kyau sunkai ashirin sun sa wani dogon char a tsakiya. Kai da ganin haduwarsu ka «san odar waje ne. Ga falon ya ji wani lallausan kafet ya mamaye gaba dayan falon wanda aka Kawata shi Dukda falon ba wani datti ya yi ba, amma haka Saude ta gyara shi sosai ta goge ko’ina da ina ,hatta jikin bangwaye wadanda gaba dayansu “tayil ne sai da ta goge, gaskiya ta sha wahala sosai harta samu ta gama, ta zauna ta turare falon da turaren wuta ta feshe shi da air frshner masu kamshin. gaske ta kunna A.C din falon, gaba daya falon ya shiga fitar da wani sanyayyan kamshi mai ni’ima. . ” Saude ta juyo da niyar tifowa shi kuma ya shigo ta yi saurin matsawa ta zube Kasa tana'fadar, “Sannu da fitowa YallaBai an kammala.” Bai tanka mata ba ya Wuce ta yana bin falon da kallo da alama shi ma yanda falon ya dauki qamshi ya burge sa, shi yana kallon falon ita. kuma tana kallonsa, tunda take da shi ba ta taBa ganin yasa qananan kaya ba sai yau, dan sai ta gama yafi mata kyau fiye da kullum. Ganin zai juyo sai ta yi saurin dauke idanuwanta tamike tayi gaba, bataredata bariya kamata tana satar kallonsa ba. Tana fitowa ta ja gefe ta zauna a falon tana kallonsa ya fito yana wani takawa tamkar wanda ba ya san taka qasa. Ba tare da ya qaraso inda take ba ya ja. ya tsaya hannayensa zube cikin aljihu, cikin sanyayyar muryarsa ya ce, “Akwai katon din lemma da , robobin ruwa da aka kawo suna cikin‘ kanta, za mu shiga meeting karfe sha daya, kin ga yanzu Saura minti goma ina so sha daya da rabi ki dauko lemu da ,ruwa kizo ki jajjera a gaban kowacce kujera, lemo daya robar ruwa guda. Akwai meat pie an nadeshi guda biyu cikin tissue sai ki ajiyewa kowacce kujera guda'a gaban teburinta. Ina fatan kin gane?” ‘ Saude. Ta daga masa kai alamar eh ya ce “Okey, kuma idan za ki shiga ban da surutu, ban ce ki yi wa kowa magana ba da akwai kayan da zaki karba ki canza.’ Oya ban san wasting din time je ki.” ‘ ‘ Saude ta lallaBa ta mike ta fice abin ta tana jinjina girman wadannan bakin a wurinsa. Tana shiga'Aunty ta miko mata leda ta karba ta nufi ciki, ta watso ruwa ta flto. A tsaitsaye ta shirya duk da yanzu ta dan nutsu ta shafa hoda da dan mai ‘a labbanta, ta sawa idanuwanta kwalli, tunda ta lura bakin kunya ne za a yi, ta zazzage kayan daga ledar Suit ne irin na jikinta, amma na yanzu wando ne da siket ba, kuma bakake neba sai rigar.cikin ce mai kalar jini,‘ harda belt irin ta mata. Mamaki ya. kama Saude shin k0 sun manta ita diyar Musulmai ce ba arniya ba? Taja ta zauna gefen gadon tana mamakin yanda za ta ratsa mutanen nan da wadannan kayan, ta dafe kai tana jin tamkar ta zabga da gudu. Bugun agogon dakin yasa ta yi saurin dago kai qarfe sha daya daidai ta buga, Saude ta yi saurin miqewa ta saka kayan wanda suka zauna mata a jiki cif da cif tamkar dama an auna ta, ta saka bakin takalmin kayan sawuciki bakake marasa tudu Ta janyo karamar himarta ta saka, wadda take ganin ta yi mata qankanta nesa ba kusa ba, bayan da ta Karasa ta fice da hanzarinta, tana faman rawar jiki, sai kace angon kare Karfe sha daya da rabi daidai ta dauki katon din lemo guda da katan din faro tan nufi falon taron wanda take jiyo sautin magana sama-sama a yi da Hausa a yi da Turanci. Saude na shiga ta ji tamkar ta zabga da gudu, saboda yanda ta ga mutane sun kai ashirin Turawa bakar fata, shi kuwa uban gayyar yana zaune a kujerar da ke tsakiyarsu, da abun magana a gefen teburinsa, tsoro ya kama ta abin ka da bagidajen mutum ta samu ta yi ta maza, ta shiga zabga sallama, babu wanda ya amsa a cikinsu, mamaki ya kama ta to su kuma wadannan wane irin mutanene da ba su amsa sallama? Ta sa kai ta shiga tana faman muzurai kamar wata marar gaskiya. ‘ Ta durkusa “Ina kwananku?" Babu wanda ya . kalli inda take ma balle ya san abin da‘ take hankalinsu na kan jawabin Dr., wani irin abu ya yi wa Saude tsaye a Kahon zuciya, don ita a ganinta su ma sun yi niyar ci mata fuska ne. Don haka ta shiga jera ruwa da lemon kamar yanda ya fada mata, ta koma ta Kara dauko wasu sannan ta qarasa jerawa ta koma ta dauko meat pie din su ma ta jejjera. Tana gamawa ta tsaya gaban Dr. wanda ke dan rubuce‘ rubuce a saman wani Karamin littafl, sannan ta dan rissina. YallaBai a kawo maka abincin ka nan ko sai ka fito zakaci Wani irin kunya da haushi da takaici suka taruma Dr Ahmad ya ji tamkar qasa ta tsage ya shiga ciki. Jin ya yi. shiru yasa Saude tunanin k0 bai ji bane ta sake maimaitawa. “Yallabai nan za a kawo ma abincin ko,,,,,,,, Tunkafin ta karasa rufe baki Dr. Ahmad ya rufe matashi da’wani zazzafan marin daya rudarda ita, ya nuna mata hanya. ‘get out stupid girl Bace' min da gani bagidajiya kawai.” Saude ta dafe kunci cike da kaduwa ta juya simisimi ta fice Tana fitowa daga falon tamkar wadda aka zungura ta fashe da kuka mai ban tausayi, ta kifa kanta akan kujera tana kukan ta babu mai lallashinta, ita kanta bata san tsawon lokacin da ta dauka ba sai dai ta jiyo motsin mutane alamar za a tito. Ta zabura ta boye: bayan kujera tana jin su sàida suka gama fita gaba daya, sannan ta fito cike da tsoro. Kai da _ ganinta kasan tana‘cikin tashin hankali dan bata san irin hukuncin da zai yanke mata ba yau, duk da bata ga laifinda‘tayi’masa ba, ammata lura ya dau zafi da * ita ta qara fashewa da kuka Ya Allah Ka fidda ni tausayin kanta ya kama ta. Ita dai batayi sa,ar zuwa duniya ba tunda tazo batasan masoyanta ba duk inda ta shiga da. [1/24, 10:13 AM] A A Dboy: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚 [12:17PM, 02/02/2017] 🙆🏼‍♂@lh@ji🙆🏼‍♂: [1/25, 9:29 AM] A A Dboy: *YAR TALLA* *CHAPTER 17* masu Kin ta take haduwa, a duniya yayanta ne kawai ya taBa sonta, sai kuwa Hamid, mutum na farko da ya nuna mata qauna da soyayya ita kanta duk da ba ta san meye so ba, amma ta san tana san Hamid dan ta san wahalar da take sha gidan su ta linka ta nan gidan sau goma, amma kullum burinta ta samu ta bar " gidan ta koma gida k0 ta hadu da Hamid dibta kuIlum addu’arta kenan musamman idan ta zo kwanciya bacci. “Wayyo Allah ya Ubangiji gani gare Ka Jin alamun taflyar da ta yi, ya sa ta saurin dago kai. Dr. ne ya dawo daga rakiya, gaban Saude ya yi Wata mummunar faduwa ta yi saurin ja da baya tana ba shi hakuri, da kukanta dan gani take dukanta zaiyi Dr... ya ja ya tsaya cak yana kallonta ya ma rasa me zai mata ya huce haushinsa, ya lumshe idanuwansa lokaci guda ya bude ba tare da ya yi magana ba ya matsa da niyar isa inda take ashe bai sani ha ta ajiye tiren kayan abinci a gun « Sai dai ya ji ya yi karo da wani abu, ya fasa wata ‘yar siririyar qara ya durkusa, ya rike babban dan yatsansa, wanda tuni har ya soma zubar da jini abin ka da lallausar farar fatar da hutu ya jika, hankalin Saude ya yi masifaffan tashi, tayi kan shi tana _ fadar ~ ‘Wayyo Allah na shiga uku na lalace "ta rike kafar tana kuka, ‘Wallahi ba da gangan na ajiyeba Na rantse da Allah ” ya runtse.idanuwansa ba tare da yace da ita komie ba “ta rasa yanda za ta yi ta kalli kan kayan abincin ashe, da yar qaramar wuqar yanka cake da ita ya ‘yi karon harta yankeshi hankalinta ya qara masifar tashi yanda ta ga jini na zuba ba wai kadan ba; ta rude ta cire himar din » kanta tasa hakori ”ta"yaga shi ta yagi kadan ta daure masa dan yantsan Dr ya bude idanuwan shi da Kyar yana kallonta yanda tabi ta gigicc ta rude fada take, ‘Sannu Wallahi bada gangan na ajiyeba, ganin yanda ta fita hayyacinta yasa ya nemi fushinsa, ya rasa. Ya'sake lumshe idanuwansa sbaoda radadin da qafar kemasa yce ‘Dauko min wayata in kira likita. ” .Hankalin, Saude ya: qara "tashi da taji an ambaci likita, ashe abin mai girma 'ne. Ta. sake rushewa da :kuka ita ko yau ta san hukuncinta mai girmane taje ta dauko masa wayar ta rankwafa ta mika masa, ita ta zauna daga gefe tana 'kallonsa Hankalin ta ya kara tashi tsoronta daya kada ’ jininsa ya qare, don ta ji ance jinin mutum na Karewa mutuwa zai yi, ta sa hannu ta gage hawayenta cikin muryar kuka ta “ce“K0 in kawo ‘maka gishiri ka barbada tunda jinin yaqi tsayawa?” Dr. ya waro ido yana maimaita gishiri kuma? Saude ta qara marairaicewa “Don Allah in kawo maka kada jinin ka ya qare.” Yanda ta yi maganar a shagwabe shi ya narkar da zuciyarsa ya ji har cikin tsikar jikin shi. : Ta sake langwaBe kai “In kawo?”-. Bai san lokacin da ya daga mata kai ba, Saude ta zabura ta mike da gudu ta fice, Dr. ya raka ta da manyan idanuwansa masu saurin daukar hankalin‘ yan matan zamani ‘ Meke son faruwa da ni ne? Ya tambayi kansa. Tambayar da ba shi da mai amsa masa. Saude ta dawo da sallamarta, ta durkusa ta mika mesa gishirin, ya lusmhe idanuwansa ba tare da ya yi magana ba, ta ce, “In barbada maka?" ' Ya daga mata kai alamar eh, ta durkusa ta ‘ ‘warware danrin' sannan ta soma barbada masa gishirin, inda naman ya Bantale, bai san lokacin da ye saki qara ba ya rike hannunta saboda azaba. » ‘ Saude ta watsar da gishirin cikin’ ta rike qafar tana fadar, “Yi hakuri don Allah‘da zafi ko?” Ya girgiza mata kai alamar a’a, ita kanta ta san ya fada ne kawai. Ta rankwafa kanta ta shiga hura masa .da iskar bakinta , tana yi tana sharar kwalla yau Allah kadai ne zai crce ta a gidan. ' Wani irin‘ tausayin; yarinyar ne ta kama kowace Kofa ta 'jikin sa tausayinsa da ya gani Karara a idanuwanta ya narkar da zuciyarsa, ya ji tamkar yasa hannu . ya shafi gashin kanta wanda kana kallon shi kaga gashin Fulani‘: ta daure shi tamau kamar gammo a kanta, ya Kara laushe idanuwansa a hankali. ;*A haka har likitan yazo ya same su, ta yi saurin , share hawayenta tare da gaishe da likitan ya amsa cikeda kulawa sannan suka gaisa da Dr. ya zauna yana fadin garin yaya haka? Dr cikin sanyayyar muryar shi ya ce ‘Tsautsayi kawai likita yace to allah ya kiyaye gaba .” Ya fada yana kallon shi cikin kulawa ya Janyo yar akwatin‘sa ta duba marasa lafiya, ‘ saude ta miqe da hanzarinta, Dr ya, dubeta. . ‘ Yace ina zaki kuma Cikin sarkewar murya irin ta wanda ya gaji da kuka ta ce, “Zan fita ne ba zan iya kallo ba.” Ya zuba mata idanuwansa yanda take maganar yaf8 komai daukar hankalinsa, ganin bai ce komai ba yasa ta juya ta fice ita kanta ta soma tsarguwa da kallon da yake mata yau, wanda ta kasa hada shi da irin Wanda ya saba yi mata a da. Kai tsaye Saude ta wuce daya Bangaren, tana shiga falon ta yi karo da Dillaliya a rabe gefen kujera ita kadai sai ka ce munafuka. Saude ta karaso da azamarta cikin doki ta zauna tana fadar “A’ a Dillaliya kece yau a gidanmu, sannu da zuwa, ina wuni?" Dillaliya ta watsa mata wani kallo mai kama da harara, kafin ta ce“Ina ne gidan naku? Lallai samun wuri tusar asuba, ashe ke nan har gidan , ya zama naku, kai gaskiya ne, an zo birni an asha jar 'miya ai dole a mance mafari. To idan kin manta bari in tuna miki gidanku na Katsina, a Katsinar ma qarshen gari inda k0 wutar nefa ba ta wadaci unguwarku ba, gidanku na nan gidan qasa an masa faci da buhu yana nan yanda ki ka bar shi kuma za ki koma ki same shi munafuka an samu wuri an Bade sai juya mazaunai ake ke da matar gidan baku da bambanci, fata ta murje anyi * kilin To ki sani kin kusa komawa gida,'dan an sa ranar auren ki wata biyu yau saura wata guda, keda Garba Gurgu, yana nan yana jiran ki." Gaban Saude ya yi wata mummunar faduwa ta ji ‘ tamkar ta dora hannuwa aka ta rusa kururuwa, saboda tashin hankali da kaduwa. Ta kifa kanta da kujera ta saki wani irin kuka mai ban tausayi. Dillaliya ta’ tabe baki tana fadar, “Kuka kama yanzu’ ki ka fara ni kam ina amsar albashin ki zan wuce yanzun nan don tun safe nake nan a jibge kamar kayan wanki, ungo wannan nataccen saurayin ki Hamid ya ce a kawo miki.” Da sauri Saude ta dago kanta don ganin abin da take mike mata. Wata doguwar ambulan ce, ta sa hannu ta karBa jiki na rawa. Dillaliya‘ ta ce, “Har na shiga mota ya zo da kansa har tasha ya kawo mini, ya gama ni da Allah ,in kawo miki,‘ ke kin san in bacin ya biya ni kudi masu kauri ai ba zan kawo ba. Saude dai jujuya takardar kawai take, tana jin wata irin soyayyar Hamid na mata yawo a zuciya, jin bai manta da ita ba shi ya mantar da ita kukan da take. Ta mike cike da dokin san ganin abin da ke cikin *‘ambulan din, Dillaliya ta dube ta, ‘Gidan wa za ki ai ba mu gama ba, kiyi maza ki tattaro mini abin da kika tara ko‘kina nufin haka nan ki ka zauna ki ka saki baki da ciki kina ta kwasar dadi ke da ki ka iya cin dadi.” Cikin sanyin jiki Saude ta ce ‘Ki yi hakuri Dillaliya wallahi ban ajiye komai ba, tunda na zo babu abin da aka ba ni.” Dillaliya ta cce“Ke dalla tashi' can har sai an ba ki keba ki iya ‘yan tattare-tattare ba, duk dan wani abinda kikaga anyi sake dashiki tattaraki boyeba Saude ta ce “Subhanallahi! Haba Dillaliya sata fa kenan?” Dillaliya ta ce “Ke gafara can sakarya ai idan ba ki sata kin Boyeba bikinki yazo ke za a bari da abin kunya, idan ko kin sata kin bada an boye miki ai kin san abin da ki ka yi ” Wani inn takaici ya kama Saude wai a tura mutum sata yanzu idan‘ yar tace ta sanya ta? Cikin sanyin muryarta ta ce, “Bari in shiga Dillaliya ki gaida gida ki gaida su ‘Yar Baba da Inna Laure da Baba na gode Dillaliya ta hayayyako mata cike da masifa “Idan ubanki ya ba ni kudin motar ba saiki tilasta ni na gaishe su ba, munafuka, mutuniyar banza, ai duk kyan gawa dai cikin Kasa za a turbune ta sai mu ga qarshen jin dadi da kyau.". Saude dai ba ta kula ta ba ta fice abin ta, tan shiga bangaren ta, ta fada kan gadonta ta zauna zaman Dirshan ta balle ambulàn din ta zazzago abinda ke ciki Wasu kudi suka fado yan dari bibbiyu rafa guda tare da yar qaramar wayar saluka Saude ta shiga jujjuyawa cike da mamaki ta qara zazzagawa saiga wani zobe ya fado tare da wata yar takarda da aka cika da kyakkyawan rubutu ta zubama rubutun ido dukda batasan abinda aka rubuta dinba amman rubutun ya burgeta ta dauki zoben nabazurfa dan sirir tana jujjuyashi shima zoben ya birgeta ta zura zoben a dan yatsanta qarmi na hagu Zuciyarta ta kwadaitu dason sanin abinda ke rubuce a cikin takardar Ta linketa da kudin ta boye sannan ta dauki wayar tana lallatsawa dukda bata iya wayaba amman zuwanta gidannan ta iya kunnawa da kashewa da kuma amsa kira sbd akwai wayar tarho da akasa a dakin don kiran gaggawa Saude ta kunna wayar tana qara jujjuyata wayar na kunnuwa kira na shigowa dukda batasan lambar wayarba amman zuci yarta ya bata hamid ne don haka hannunta na kyarma ta daga kiran ta kara wayar a kunne tareda sallama Wani sanyin dadi ya bugi zuciyar hamid lokacin da siririyar muryarta ta daki kunnensa muryar da har ya fiddah rai da sake jinta a duniya cikin doki dajin dadi yake magana Amin wa,alai kumussalam ya habibati saudat nasan zuwa yanxu saqona yaxo gareki hakane? Murmushin dake fuskarta ya qara qawatuwa kafin tace hakane yaya hamid dillaliya ta kawomin dazu ashe baka mance daniba yaya hamid? Hamid yace wat? Haba sudat ai idan har zan iya mancewa dake to wlh zan iya mancewa da kaina saudat soyayyata gareki ta gaskia ce kuma ta ginu ne tun daga lokacin dana fara ganinki kuma inhar ba daina numfashi nayi ba sudat bazan taba barinki ba sainaga kin taka wani matsayi a rayuwa na miki wannan alqawarin Cikin farin ciki dajin dadi saude tace na gode yaya hamid Yayi wani murmushi wanda har saida ta jiyo sautinsa yace gaskia saudat dina ta fara girma haka bakinki ya bude ? Murmushi kawai tayi bata tankaba hamid yace saudat nasha wahala lokacin dana dawo na iske bakyanan wlh saida nayi tamkar zan haukace kamin in samu insan inda aka kaiki amman bansan ko waccce anguwa bace ba a cikin abuja saida na biyo ta hannun wannan matar yanxu ya kike ganin za,ayi don muna cikin matsala fa Saudat an fada miki ansa ranar aurenki? Saude tace eh an fada mini Toya kike gani abuja zanzo in sameki ko ko ya za,ai ? Cikin kidima saude tace ina? Ka rufamin asiri masu gidan bazasu bariba Saidai kawai ka bari inna samu dama kawai na gudo Hamid yace to yaushe ?donni nanda sati daya jirginmu zai tashi zuwa qasa mai tsarki aikin hajji birina kafin satin duk yaddah za,ai ayi kawai a daura mana aure don wlh saudat ina tsoron in rasaki Saude taja‘numfashi kafin ta ce, “Insha Allahu Yaya Hamid duk yanda zan yi kafin satin zan yi ba za ka rasa ni ba da yardar Allah.” ' Dadi Ya kama Hamid nan ya ci gaba da jan ta da hira, su kan Su ba su san sun ci lokaci ba sai da suka jiyo ana kiran sallar Magariba.” Hamid ya ce “Lah! Saudat kin ga kin shagaltar dani mun ci lokaci har haka, bari in je in yi sallah zan kira ki zuwa dare kin ji sweaty na?” Dariya kawai ta yi shi kuma ya kashe wayar, wani sanyin dadi ya cika masa zuciya. Ta murgina ta sake mirginawa cike da shaukin soyayya kusan sai nace ban taba ganinta cikin irin wannan farin cikin ba ‘ ’ “” Washe gari Saude na cikin shirin tafiya aikinta, ta ji karar wayarta, ta matsa inda ta Boye ta ta dauka ta kara a kunne tare da rairo sallama Hamid ya amsa tare da gaishe ta, ta amsa ba sai dai ta maido masa da gaisuwar ya amsa suka gaisa sosai, can ya nisa kafin ya ce“Kin san me wai ashe jiya yayanki yazo gidanku, ban sani ba sai daga baya na samu labari?” Cikin zakuwa Saude ta ce, ‘Kai don Allah Yaya hamid yanzu yana ina don Allah?” ~ Hamid ya ce“Nima abin da yasa na baro Kaduna ke nan cikin daren na zo Katsina, amma sai na samu wai matar gidanku ta sa mahaifinku ya yi masa korar kare, suka dinga watso masa kaya waje cikin daren ya bar Katsina, amma ya barma maqotanku saqo baki Saudat ta fashe da wani irin kuka mai cin zuciya ji take tamkar ta shake kanta saboda baqin ciki Hamid ya ce, “Ai kuma nifa ba wai na fada miki ba ne don ki tayar da hankalin ki ba, ki yi hakuri tunda ya dawo yanzu wata rana ma , zai sake dawowa, don wallahi tallahi na yarda da Kaunar da ke tsakanin ku na san in har yana da rayuwa ba zai mance da rayuwarki ba Saudat ki yi haquri don Allah kin ji?" Haka dai ya yi ta lallashinta sannan ya kashe wayarsa. Saudc ta qara fashewa da kuka mai cin zuciya dama she Yaya Rabi’u yana raye? Ashe ‘dama bai mance da niba? Shin kowace irin rayuwa yake yi a Lol labari dai nata tafiya cikin kwanciyar hankali kuma ta wani barin sai nake ganin kamar Dr Ahmad nason ya fada tarkon sofa idan ya fara son saude ya kuke ganin zata kaya tsakanin asmau da sauden hamid da saude da kuma garba gurgu da saude kai akwai rikici fa mu tara donjin ci gaban wannan qaya taccen labarin idan naga comment sosai zanci gaba anjima idan kuma kukaqi to sai gobe kenan naku har kullum Admin Dboy🤔 [1/25, 9:29 AM] A A Dboy: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚 [1/25, 10:39 AM] A A Dboy: *YAR TALLA* *CHAPTER 18* 1page is missing Gaban Ahmad ya yi wata mummunar faduwa cikin sanyin jiki yace, “Lafiya kuwa me ke damun kine? Tamkar ba zata tanka masa ba saboda yanda kukan yake. neman Kin tsayawa, sai da ya sake‘ maimaita mata tambayar, sannan ta samu ta tsaida , kukan cikin shakakkiyar muryar da ta gaji da kukan Tace “YallaBai me yasa rayuwa take zuwa da abubuwa marasa dadine irin haka? YallaBai me yasa rayuwata kullum ba na ganin haske sai duhu a cikinta? Me yasa rayuwa ta kullum take neman rugujewa ne saboda wahala?” YallaBai shin ..... ” Kuka ya ci Karfinta ta kifa kanta a kan cinyarta ta ci gaba da raira abin ta. Wani irin tausayin ta ya mamaye zuciyar Dr. Ahmad, ya durqusa gabanta a hankali har tana jiyo kamshin turaren da ke fatar shi. Muryarsa a sanyaye ya kira sunanta ‘Saudat Wanda ya sa ta dago kanta da sauri don bata taBa zaton ya san sunan ta ba, kuma yau ne karo na farko da ya taBa kiran sunan nata. Ya ci gaba da magana, ‘Saudat k0 me rayuwa ta ' bada hakuri aka a karba, ki karBa' duk abin da rayuwa ta zo miki da shi ki rungume shi, sai ki ga Ubangiji ya taimake ki a duk inda ki ke, yawan kuka ba zai kare ki da komai ba sai ma ya haifar miki da . wani ciwon. Kalle ni Saudat.” Ya fada da siririyar » murya, ta dago da jajayen idanuwanta tana kallon , shi, ya mika lallausan hannun shi yana goge mata hawayen: “Ki daina zubar da hawayen ki irin haka, alhalin ba ki tanadi mai share miki shi ba.” Saude ta’ yi saurin janye fuskarta cike da jin kunya da nauyi, ya dan razana tare da fadar “Oh am sorry Ya mike ya ciro hankicif daga cikin aljihunsa ya mika mata. Ta karba ta soma share hawayen ta gama ta miKa masa ya karBa ya mayar aljihu, sannan ya ce “Tashi mu je ciki, kin ci abinci kuwa?” Shiru ta yi don rabonta da abinci tun jiya don haka ba musu ta mike, suka nufi falon kai tsaye Suna shiga ta nemi gefen kafet ta zauna bai tanka ‘ba Ya wuce kai tsaye wurin firij din da ake aje kayan gwan'gwani ya bude ya ciro wani qaton cake tare da ~ lemo guda da fresh milk ta kwali, sai chips a wani Qaramin plate wanda ya ji dafaffen kwai da madara ' ga shi ya dauki sanyi. Ya nufo inda Saude take zaune ya ajiye mata a gabanta, sannan ya ja gefe ya zauna saman kafet din yana' fuskantarta, da hannu ya yi mata nuni da ta ci, ba musu ta sa hannu ta dauki milk din ta fasa, ta bade cake din ta rinqa hadawa tana ci. Cake din * ya yi mata wani masifar dadi don sai ta ce tunda take “ ba ta taba cin abu mai dadinsa ba ita kanta ta yi mamakin wanda ta cinye, don chips din kasa cin shi ta yi don ba ta saba cin irin shi ba. Ta daga madarar ta shanye tas, don sai da ta ji babu wuri a cikinta, duk abin da take yana zaune yana kallonta tana gamawa ta mike da niyar tattara kayan, ya daga mata hannu. “Bar shi kawai za a tattara.” Kallon shi kawai ta yi sai dai ta gaza magana. Don haka shi ya katse shirun ta hanyar fadar, “Kije kawai ki huta', kin'ga kin sha kuka kada kan ki ya yi ciwo, kin ji?’ ' Saude ta amsa da to a hankali, sannan ta juya zata tafi hartakai bakinkofa tajiyakira sunanta ta' waigo tana kallonsa. Tamkar wanda aka matse bakinsa aka ce dole sai ya fadi abin da yake son fada ~ ya ce, “Please kar ki sake yin kukan nan don Allah.” Saude ta daga masa kai alamar to, ya ce, “Kin yi alkawari?’ Da kai kawai ta amsa masa, sannan ta . juya ta fice A yanzu mamaki yake ba ta ba ta taba tunanin yana da tausayi da jin Kai irin haka ba, ashe dama yana da kyawawan halaye irin haka ya Boye su, Allah Sarki, ko da yake ai rayuwarta abin tausayi ce ga duk wani mutum mai imani. _ ' . Ta zauna bakin gadonta ta janyo Wayarta miss ‘ call biyar ta gani, ta san kuma duk aikin Hamid ne, ‘ Allah Sarki soyayya. Ta ajiye wayar karkashin Kanta ta kwanta. Hirar ta da shi jiya cikin dare ta dawo mata tamkar yanzu ‘suka yin ta, ta yi wani ”murmushi tare da yin wani juyi . Da safe misalin Karfa takwas ta nufi Gangaren Dr Ahmad da mamakinta yau kwance ta same shi cikin falon Kasa, saman doguwar kujera da News paper a hannunsa yana dubawa, yana sanye da wando three quater wanda ya wuce gwiwarsa sai bakar singileti a jikinsa. Saude ta durkusa tare da ‘ ”gaishe shi.’ Ba tare da ya dago kansa daga karatun da yake ba ya amsa mata gaisuwar. Saude ta mike ta soma aikinta kamar yanda ta saba, sai da ta kammala tsaf sannan ta soma turare falon da turaren wuta, kamar wadda aka cewa dago kanki, karaf su kai ido hudu, ‘gaba daya idanuwansa da hankalinsaya tattara su a ‘kanta.~ ‘ ’Saude ta ji ta yi wata masifaffiyar tsarguwa, cikin basarwa irin ta gogaggun maza ya‘ yi mata alamar kira dakansa, jikin Saude ya Kara yin sanyi ita dai ta fara tsorata da irin kallon da yake mata, ba yanda ta iya haka ta ajiye bonar din ta nufl : ' inda yake ta dan durkusa kusa kadan tare da fadar, _ “Ga ni‘ Yalla Bai.”. Idonsa na' kanta kamar mai san karantar wani abu cikin idanuwanta ya ce“Ya kamata a tsaya da aikin nan haka a kawo mana abun karyawa k0 ke ba ki soma jin yunwa ba ne?” Yadda ya yi maganar cikin "salon nuna tausayinsa a kanta shi ya ba ta mamaki Saudat ta sunkuyar da kanta qasa‘ tana kallon yatsun hannunta, sannan ta amsa, da to muryarta a sanyaye, bai tanka. mata ba har ta mike ta fice daga falon, ya koma ya kwanta ya dora hannun shi guda a kan shi ya lumshe idanuwansa komai yake tunani? Oho. Saude ta karBo break din ta kawo da sallamarta ta ajiye masa. tiren kayan abincin a gabansa tare da fadar, ‘Ga abincin. ” Dr. Ahmad ya yunkura ya tashi zaune ya sauko daga kan kujerar ya zauna a gabanta tare da harde qafafuwa tamkar wani karamin yaro ya ce, “Zubo mana. ’ Saude ta yi saurin kallonsa tana san tambayarsa shi da wa amma kwarjinsa ya hana, don haka ta sunkuyar da kanta. Ta dauko ' plate biyu za ta zuba Dr. ya sa hannu ya janye dayan yana fadar, ‘Plate guda za ki zuba mana.” Ba ta musa ba ta dauki saving spoon ta , debo soyayyar agada (Plaintain) tare da alalar nama da kwai sai soyayyar da nama cikin dankali ta zuba su kowane gefe da gefe a tsakiyat plate dim sai ta zuba wata hadaddiyar miya kadan sannan ta tura plate din a gabansa ta rufe kulolin, sannan ta dauki kofi guda biyu ta zuba kunun madara da gero tasa ‘cokula ta miqa masa. Dr. Ahmad ya zuba mata manyan idanuWansa da dan murmushi a fuskarsa ya ce, “Sannu.’ Ba ta amsa ba saboda yanda ta ji nauyin yanda ya mata sannun, kamar ba yallaBan da ta sani ba. . Da kan shi ya matso da plate din a gabanta shi ma ya matso tare da miqa mata kofl guda na kunun Gaban Saude ya yi wata mummunar faduwa ta yi saurin matsawa tana girgiza masa kai alamar a’a. Dr. ya hade fuska tare da fadar. “Karbi mana meye haka?” Yanda ya yi maganar cikin tsawa ya sa ta saurin mika hannu ta karBa. Ya ce “To sa hannu mu ci maza.’ Ta yi saurin kallonsa idonta 'ya ciko da kwalla ta gaza yin magana, Dr. Ahmad ya girgiza kai cikin damuwa ya ce “Abincin ne ba zaki ci ba shi ne za ki yi kuka?” Ta yi saurin girgiza masa kai,alamar a’ a Ya kada kai cike da damuwa ya mike ya koma kan kujera ya kwanta ya lumshe idanuwansa ba tare daya yi magana ba. ~ Wani irin abu yayi wa Saude tSaye a zuciya, shin wai ita me ya maida ta ne? Yanzu abincin ma da zai ci sai ya wahalar da rayuwarta a kansa, abin da yake mata ya soma ba ta tsoro. Ji take tamkar ta mike ta bar masa falon, in ya ci ma k0 bai ci ba ruwansa. Bude idanuwansa da' ya yi shi ya katse mata tunanin take cikin sanyayyar muryarsa ya ce “Na takura ki k0? Ki yi hakuri kina iya tafiya kawai. ’ ‘ Gaban Saude ya yi wata irin masifar .faduwa cikin muryar kuka ta ce“Ka yi haquri dan Allah ’ Ya dauke kansa kafinn ya ce “Aini banyi fushi ba.” ‘ . . Damuwar da ta gani qarara a fuskarsa ne ta Narkar da zuciyarta, ita kanta tana mamakin kannta -. yanda hankalinta ke tashi idan suna tare bata san lokacin da bakinta ya bude ba sai dai ta ji tana ‘ fadar “Ka yi hakuri yanzu ai zan ci.” A hankali ya dago yana kallonta, ta ta" sunkuyar da idanuwanta kasa, wani takaitaccen murmushi ya yi tare da saukowa daga kan kujerar ya: zauna gefenta. Da kan shi ya dauko kofi din kunun ya mika mata, ta sa hannu ta karBa cike da jin nauyi ta soma sha, dadin kunun ya ratsa mata kwanya ashe haka yake da dandano a baki, tun tanajin nauyi har ta dake ta ci sosai tana cire hannunta yana cire nasa.‘ a Ta dan zuba masa idanuwanta, ya daga mata gira, alamar ya aka yi? Shiru tayi “ta kwashe kayan ta dawo ta gyara wurin da sukaci abincin sannan ta qarasa inda yake zaune yanacikin karant jaridarsa, ta dan durkusa. _ “Zan tafi Yallabai ko akwai wani abin da~ ka ke so?” ' Dr. Ahmad ya dago da kansa ya kalle ta a nutse~ kafin ya ce, “Me yasa za.ki tafi nan ba falo ba ne? Me yasa ki ka kasa sakin jiki?” Saude ta yi shiru ba tare da ta iya cewa komai ba Dr. ya girgiza kai tare da fadar samu guri ki zauna ina san mu yi magana.’ Ba musu ta samu gefen kujerar da yake zaune ta zauna a saman kafet. Dr. Ya wurgar da jaridar kan kujera tare da gyara zama ~sosai ya harde yatsun hannunsa guri guda sannan ya kira sunanta. ‘ “Saudat, kiyi hakuri da takura ki da nake ki daure ki ba ni labarin ki ina san in ji labarin ki na damu da in san wace ce ke kuma me ye dalilin kawo ki aikatau maimakon a inganta rayuwarki da ilimi k0 dan ke ma ki amfanar da wasu a gaba?” Saude ta yi shiru tana tunanin dan abin data sani a cikin rayuwarta, idonta ya ciko da kwalla-ta dago tana kallon shi da sarqaqkiyar muryarta ta ce “YallaBai babu komai a cikin rayuwaba sai duhu, . babu abu guda na haske a cikinta, idan ma na samu to ya suBuce mini. ban san komai a cikin rayuwata ba sai wahala da. Qaskanci, haka rayuwar tawa ke tafiya... ‘ Kukan da take riqewa ya soma kwace mata, ta sa hannu tana goge hawayen kafin ta ci gaba ‘ “Ni dai nasan ance an haifeni ne a gafin Katsina, kuma na bude idona a cikinta, don haka na ci gaba da rayuwa a yanda tazo mini a ciki, "tunda nayi wayo na ganni a: gabana Yayana Rabi’u sai mahaifina Malam Bala, sai kishiyar mahaifiyata Inna Laure da yarta iKilima wadda ake ce mata ‘Yar Baba.’ » A nan ta Iabarta masa gaba dayan labarin rayuwarta har ya zuwa yanzu. Tana gamawa ta kifa kanta a saman cinyarta tana kuka. Tausayinta ya qara kama Dr Ahmad wanda yake jin tamkar ya". zubar mata da hawaye, ya tausayawa halin da ta ’ tsinci rayuwarta tun tana yar karamarta har girma ta mallaki hankalinta, amma Inna Laure ba za ta bar ta haka ba wannan wace irin macece? ‘ ; Ya kira sunan ta cike da damuwa ya ce.“Ki yi hakuri Saudat insha Allahu sai kin yi,alfahari da rayuwarki ni zan maye miki gurbin Yaya Rabi’u da kuma Hamid in dai ina numfashi. Saudat sai kin yi ‘ dariya da farin ciki kamar kowace mace, ki kwantar”da hankalin ki ki daina kuka haka kinji?” ‘ _ Kai kawai ta daga masa alamar eh ya zaro ~ hankicif cikin aljihunsa ya mika mata ta karBa ta’ share hawayenta sannan ta mika masa ya karba kafin yace, “Yanzu ki tafi kije Ki kwanta daga masa alamar eh? Ya ce to shi kenan,‘kidab bani lokaci zan danyi tunani a kan matsalarki kafin. in “ samar miki mafita da fatan‘dai ba zaki yi fushi da; Duk abinda rayuwa ta sake baki ba zaki karba da hannu biyu Saude ta daga masa kai alamar eh yace to allah ya kaimu Jin yayi shiru yasa ta miqe ta nufi hanyar fita har takai bakin korar taji ya kira sunanta ta waigo tana kallonsa yace ki kawomin coffe yau da daddare kai kawai ta daga masa ta juya ta fice abinta koda ta koma bangarenta ruwa kawai ta watsa ta koma ta kwanta a binta wani barci ya dauketa ba ita ta farkaba saida wayarta ta dameta da qara tasa hannu ta dauka cikin magagin barci jin muryar hamid yasata saurin watstsakewa daga baccin suka shiga hira sunfi awa biyu a haka sannan sukai sallama da niyyar zai qara kira zuwa anjima misalin qarfe goma daidai saude ta fito daga bangarenta ta fita kai tsaye kichin ta nufa ta dauko flasks din coffe da qananun kofinan da yakesha dasu ta nufi bangarensa dasu saidai tun kafin ta qarisa ta hango bangaren nasa dun dum babu alamar hasken wuta tsoro ya kamata gashi bata taho da wayartaba ballentana ta haska kuma babu damar ta koma Wayyo allah taji tamkar ta fashe da kuka Taja ta tsaya cak tana tunanin abinyi tun kafin ta Qarasa nazarin taji wani haske mai Karfi ya taso da saukar ruwan sama mai Karfi ai bata san lokacin data kwasa da gudu ba ta yi Bangaren nasa, ba ga shi duk ta jike Tamkar daga sama ta ji ta yi tuntuBe da wani abu ta fasa wata uwar qara ta saki kayan ta kwasa a guje, karaf sukai kicibis ta da mutum, ta sake kwala wani qara mai qarfi cikin dabara ya rungume ta sosai a jikinsa yasa hannu ya kunna wutar falon. Amma har a lokacin ‘ ihu take tana, zullon kwacewa, hannu yasa ya tallabo qeyarta ya juyo da fuskarta saitin tasa su kai ido hudu. Sai Alokacin ta tsaya da ihun ta saki wata _ . ' nannauyar ajiyar zuciya cikin muryar kuka ta ce ‘Wallahi ka tsorata ni na zata, na zata... ’sai kuma tayi Shiru Yanda take maganar a shagWaBe ya barge shi har bai san lakacin da ya saki wani murmushi ba yasa dan yatsunsa ya lakace mata hanci yan fadar, . “You ar so beautiful Ya lumshe idanuwansa tare da mata wani murmushi,wadda ta tsaya iya makoshinsa kawai ' Sai a lokacin Saude ta lura da irin rikon da ya yi mata ta yi saurin zame jikinta da na shi a kunya ce saboda yanda ruwan. ya jika kayanta duk suka mammanne a jikinta tamkar ba ta sa komai ba ta juya da gudunta ta bar falon tana ji yana kiranta amma ba ta tsaya ba, haka ta koma sashin nata cikin ruwan. ' Tana shiga ta hada kanta da bangon falon tana jin tamkar qasa ta tsage ta shige ciki, saboda kunya da nauyi. Ai k0 ba za ta sake yarda su hadu ,ba duk rintsi kai dole ma in bar gidan. nan, wannan abun " kunya har ina, musamman idan‘ matar gidan ta samu labari ai ita ta san ta kade har ganyen ta. Kunya ta isheta tarinqa jin tamkar tarusheda kuka. Ta samu ta yi ta maza ta cire kayan ta dauko tsohon zaninta ta yi daurin Kirji da shi ta haye kan ‘ gadonta ta ja bargo ta kwanta. Amma sai me? Da ta rufe ido sai ta ga tamkar ga Dr. Ahmad nan zai rungume ta, ta zabura ta tashi zaune tana muzurai, ga qamshin turarensa da ya mamaye ta, ta yi wani gajeran murmushi tare da komawa ta ‘kwanta: ta runtse idanuwanta a haka bacci mai nauyi ya dauke ta. Washe gari tunda ta farka take zaune tana san zuwa wurin aikin nata, amma kunya ta hana ta, ji ‘ take ba za ta iya sake hada ido da shi ba, don haka ta gidan. Ita kanta ba ta san ta dan lokaci ba sai da ta soma jin cikinta na kukan yunwa, ta daga kanta ta kalli agogo. Sha daya da mintina, tana shirin tashi zaune ta ji an turo Kofa an shigo. Ta yi saurin tashi tana fadar, “Sannu Aunty.". Ta amsa da “Yauwa Saudat laflyadai ki kek0?” Saude ta ce “To da sauqi dai kaina neke dan ”ciwo.” ‘ . Ta ce, ‘Ayya, Allah Sarki kije Hajiya na neman ki tana falo.” Gaban Saude ya yi wata mummunar faduwa, ta ce, ‘Lafiya dai k0 Aunty? Allah yasa ba wani laifl na yi ba. ‘ Aunty ta ce “To laflya, YallaBai ne ya aiko kiranki.’ _ Hankalin Saude ya Kara tashi alamun tsoro ya . bayyana karara a fuskarta, ta mike jiki amace tana fadar, “Ga ni nan zuwa.” Cikin sanyin jiki ta canza kayan jikinta sannan ta fito zuciyarta na faman bugun dardari. harta qarasa .falon ta hango’Asma, tsaye riqe da Kugu, tana sanye da wasu riga‘da siket sari tare da 'mayafinsu tamkar wata .Ba’indiya, takalmin nan mai shegen tsini a qafarta. A danyi nesa da ita Saude ta tsaye ta durkusa tare ‘ da fadar, ‘Ina kwana Haj iya.” . Asma ta watso mata wani razanannan kallo kafin ta ce ‘Shut up ke nan har marar kunya ce wace ce ke? Uban waye uban ki a garin nan da har za kiqi zuwa aiki saboda jin dadi har Dr. ya aiko kiran ki, me ki ke ji da shi a cikin gidan nan? Me ki ka taka'? , Banza sakarya jaka‘ yar qauye. Yau k0 rashin lafiya ki ke dole za ki sanar in ba daibakisan inda kankiyake ba, tunda an ajiye miki wayar tarho da za ki iya kira da ita ki sanar, amma ke isasshiya kin yi shiru abin ki wato idan ana so a neme kito ki -sani wannan shi ne laifinki na biyu cikin manyan laifukan da ki ka aikata a gidan nan duk ran daki kikai na uku,kisani aranar”zakikarbi takardar sallamar ki kinji na fada miki” Tana gama fada ta juya ta haye sama a zafafe Jikin Saude ya yi sanyi matuqa, ta lallaba ta mike ta fice zuciyarta a cunkushe da baKin cikin yanda aka wulaqanta ta ba tare da an saurari uzurinta ba. Rayuwa kenan , Haka ta sa kai ta shiga falon tare da sallamar’ta, tsaye yake tsakiyar falon ya goya hannayensa a baya yana jin sallamarta ya yi saurin waigowa ya nufo ta da hanzarinsa Lafiya Saudat me ya same ki? Ba dai ruwan jiya , neya saki zazzaBi ba?” Saude ta girgiza kai alamar a’ a, sannan ta durkusa tana gaishe shi, bai iya amsawa ba ‘ ya sake jefo mata wata tambayar ‘Ban yarda ba Saudat idan lafiyarki qalau me yasa yau ba ki zoba?" Saudat ta Kara dukar da kanta qasa tare da fadar, ‘kaina ne yake ciwo kadan shi ya sanya.’ Dr. ya ce ni dai na sani, :nasan baki da da lfy Saudat bari in kira likita ya duba ki, kin ci abinci ' ‘ kuwa? . Da sauri ta ce ai na warke. Dr ya. girgiza mata kai a’a Saudat ban san wasa da lafiya, taso ki ci abincin kafin yaz0. Ganin yana shirin riko hannunta yasa tayi saurin tashi da kanta ta bi shi ya nuna mata tsakiyar kafet ta' zauna sannan ya nufi dining ya dauko kayan abincin ya kawo mata, yau da kan shi ya zuzzuba mata ya tura mata a gabanta tare da fadar. , ‘Don Allah ki daure ki ci.” Kai kawai ta daga masa, sannan ya wuce ya dauki wayarsa ya kira likitansa. Yana cikin wayar ne Asma ta sawo kai falon tana wani taku sai ka ce wadda take filin. gasar iya taflya, Dr. ya zuba mata idanuwansa cike da tuhuma. ‘ Karaf idonta ya sauka kan Saude wadda tuni hanjin cikinta ya shiga juyawa saboda tsananin firgita da tashin hankali, Asma ta ja ta tsaya tana ,fadar. “Me nake gani haka Dr? ‘Yar aikin ce kecin abinci a faod flask dinka, kam babban ....... ’ Kai jama,a akwai rikici fa sai kunjini agaba donjin yaddah zataci gaba da kayawa naku har kullum admin Dboy🤔 [1/25, 10:39 AM] A A Dboy: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚 [12:17PM, 02/02/2017] 🙆🏼‍♂@lh@ji🙆🏼‍♂: [1/27, 10:11 AM] A A Dboy: *YAR TALLA* *CHAPTER 19* “Me nake gani haka Dr? ‘Yar aikin ce ke cin abinci a food flask dinka, kam babban ....... ’ Ya watsa mata wani kallo lokacin da ya kashe wayar ya ce “To k0 rai ya yi baki ne? Ai dai anawa take ci ba a baki ba k0? Ya yi mata tambayar cike da ‘ isa da gadara. _ “ Asma ta qara shaqa kafin ta ce ‘Hmm! Dr. kenan amma dai .ka san wannan ba qaramin kaskanci bane da zubdawa kai girma ka yi bak0? A. Zo a iske yar aikin ka na cin abinci a kwanan ka, ‘yar aikin ma ‘yar Kauye, jaka dakikiya, wadda talauci ya yi masu daurin ..... Dr. yayi saurin daga mata hannu ‘ya isa haka Asma, kin sanni sarai ban san cin fuska don Allah tunda ban aika miki da katin gayyata ba ki bar nan, banasan ciwon kai.’ ' Takaici ya kashe Asma, ta matsa daf da shi tare da sassauta mur'ya ta ce ‘Yanzu Dr saboda ‘yar aikin ka ka ke cimin fuska haka?” ‘ Ya ce ‘Amma kin sani Sarai ba a gaya mini yanda zan yi ko?’ Haushi ya kama ta ta juya a zafafe ta bar masa falon, ya taBe baki ya juya wurin Saude wadda “ lomar abinci ta yi wa tsaye a maqogaro tun dazu ta gaza hadiyewa, saboda tsabar firgici da tsoratar da ta Dr. ya zauna bakin kujerar dake fuskantar ta yana fadar. “Ki nutsu ki ci abincin ki sosai ga likita nan zuwa.’ Hawayen da suka taru a kwarin idanuwan ta suka gangaro cikin kuka ta ce, ‘Wayyo Allah na ka ja mini Allah kadai ya san abin da za ta yi mini yau na banu na lalace! ’ Dr. yace ‘Kuka kuma Saudat? Yanzu nan har an yi abin kuka? Lallai ashe kina da kukan jini nan gaba. ’ Saude ta Kara rushewa da kuka, ‘Wallahi gida zan tafi” Dariya ta kama Dr. ya ce, ‘Ashe matsoraciya ceke lallai Saudat na tabbata da Asma ta ji haushin ki da k0 sama da qasa za ta hade anan ba za ta kyale ki ba, ta riga ta san halina ne sarai don haka ba ta damu da ke ba ta kaina za ta dauki matakin don haka ki ma kwantar da hankalin ki ki ci abincin ki ’ Saude ta ture abincin tare da fadar, ‘Na qoshi.’ “Me? Ai wannan ne baki isa ba k0 ki dauka ki cinyc shi ko yanzun nan in kira ta ince kin cetazo ta kwashe kwanukan kin gama.’ Saudc ta yi saurin waro ido waje tare da janyo abincin da saurinta ta ci gaba da ci, ya yi dariya a , zuciyarsa sosai ya ce matsoraciya. Tun kafin ta gama cin abincin likitan yazo ya duba ta sosai tare da rubuta mata wasu magunguna, ya kira direba yasa ya je ya siyo mata su, ya dinga lallashinta yana rokon ta a kan ta rinka shan magungunan, sannan ya ba ta ta tafi Cikin tsoro ta shiga sashin nasu don gani take Asma na nan na jiranta. ' . Tana shiga sashinta ta maida qofa ta rufe ta ajiye magungunan ta haye kan gado ta janyo wayarta da .taketa faman ruri tun dazu ta ci gaba da wayarta. Washe gari da yamma tana zaune a bangaren Dr. tana aiki, zuciyarta sai faman sake-saken neman mafita take saboda wayar da su kai da Hamid jiya da daddare Dr. ya sauko daga samansa yana sanye. da qananan kaya irin na hutawar turawa, ya tsaya daga gefen kujera yana kallon Saude wadda ke durkushe tana 'goge goge ‘ . Jikinta ya ba ta tamkar ana kallonta, don haka ta yi ‘saurin waiwayawa, tsaye ta gan shi a gabanta ya harde hannuwansa a kirji tamkarmai nazarin wani abu. Saude ta yi saurin durkushewa tana masa sannu da fltowa, bai amsa mata. ’ba‘ sai ma ya sake gyara tsayuwarsa. “Me yasa baki san hutawa?” Saude ta dan kalle shi kadan kafin ta ce ‘Ai aikina ne shi yasa.’ Dr. yadan dauke kai kafin yace, ‘Ai kin kusa barinsa, saki wannan aikin ma taho mu fita mu sha iska.” Bai jira abin da za ta ce ba ya yi gaba abinsa, Saude ta raka shi da idanuwanta. To me yake nufi da ita? Ba dai korarta za su yi ba? Da sauri ta zabura ta bi bayansa. . Hadaddan wurinn shakatawa ne wanda aka kashewa dubban nerori wurin Kawata shi, don an zuba abubuwan ban sha’awa da debe kewa. Saude ta . koma jikin wani dodon roba, tana kallon Dr. wanda ke wasa da dan biri, can ya dago ya yafito ta da hannu alamar ta zo duk da tsoron da ya cika mata zuciya haka ta dake ta tafi inda yake, ta tsaya daga gefe tana kallon su, ba ta ankara ba ta ji ya fizgo hannunta ya hada da na birin, yana wa birin magana cikin harshen turanci. Mutuwar tsaye ta yi don tana bala’in tsoron sa sosai, don ma yana dan Karami, sai ta ga ya ’fadi' Kasa alarnar gaisuwa. Dr. ya yi dariya yana kallonta ya ce “Ana gaishe kifa?” Kallonsu kawai take bata ‘ iya yin magana ba, birin ya mike yana ta faman zazzagaya ta yana tsalle-tsallen murna. ' , Dr. ya janyo hannunta suka nufi wani.‘ qaton lilo na roba mai matattakala ya dan kalle ta da murmushi a fuskarsa ya ce “In hau za ki jujjuya ni’?’ ‘Duk da haushin riKon da ya yi mata ya kama ta sai da ta yi dariya saboda yanda ya yi maganar. Ya ce, ‘Okoy, dariya ma na baki to bari in dora ki in jujjuya ki.’ Tun kafin ta yi wani yunkuri ta ji ya sure ta ok ya dora saman lilon. Saude ta fasa wata uwar kara saboda razana, don ita gaba daya ma lilon tsoron shi take yi, dariya ta bawa Dr. sosai na kauyancin nata, don haka yana dariya yana jujjuyawa da ita, mutuwar zaune ta yi ta . runtse idanuwanta tana sauraren ikon Allah, shi kuwa dariya kawai yake mata, yana zolayarta ganin ba shi .da niyar daina juya ta yasa ta bude idanuwanta tana shirin kuka, ta hau rokonsa. ‘Don Allah don Annabi ka sauko da ni.’ Dr. ya tsaya da lilan ya matsa yana fadar, ‘To sauko tunda ba kya so.’ Saude ta waro idanuwa don ta san ko da kudi aka bata bazata iya saukowa ba, ya yi murmushi tare da mika mata hannunsa ta rike sannan ya sauko da ita, yana mata dariya yace matsoraciya duba ki ga aku na .kallon ki. ’ Saude ta yi saurin juyawa, caraf ya riKo hannunta ya ja ta da saurinsa. Haushi ya kama ta yanda ya maida ita kamar Karamar yarinya. Saman wasu kujerun roba ya zaunar da ita shi ma ya zauna, suka sa zagayayyan tebur din a tsakiya. Saude ta bi abin . da aka dora' saman tebur din da kallo, wanda a kai ‘ ‘ rafin din shi gwanin burgewa. Dr. ya miKa hannu ya dauko ya mika mata ta tsaya tana kallon shi ya miqa mata tare da fadar. “Karba mana.’ Ta mika hannu ta karba,tana kokarin bude rafin leda din. Dr. ya yi saurin tsaida ita yana fadar, ‘tsaya tsaya waya fada miki idan aka bawa mutum gift budewa yake'a take bakauyiya ai bari ake sai an tafl.’ Yana maganar cike da zolaya. . Saude ta zumBuro baki" jin ya kira ta da bakauyiya, dariya ta kama shi ya ce, ‘A’a ‘yanmata ashe kin iya fushi irin haka?” Ta dauke kanta ba tare da tace Kala ba. Ya ce, ' ‘Wai fushin ki keyi da gaske am so sorry, tuba nake -kaina bisa wuyana.’ Dariya ta kubce mata yanda ya yi maganar a ladafce sai kace ba YallaBai din da ta sani ba, ganin dariyarta yasa ya mikc yana fadar “Taso muje kin ji ana ta kiran sallah a_ masallaci.’ ‘ Saudeta tashi ta mika masa gift din da ya bata, ‘ya dan zuba mata idanuwansa babu alamun wasa a fuskarsa ya ce ‘Da shi za ki tafi kyauta ce daga gare‘ ni.’ Yana gama fada ya juya ya yi. gaba abinsa, ba tare da ya saurare abin da za tace ba. Tsabar mamaki da kaduwa su suka hana Saude furta komai, har sai da ya kusa bacewa ganinta saunan ta iya wage murya tana fadar, “Na gode kwarai.’ Hannu kawai ya daga mata ba tare da ya juyo ba ya Bace abinsa, ita ma ta yi gaba cike da zullumin abin da aka nannade haka. Tana .shiga dakinta ta fada kan gadonta ta yi zaman dirshan ta shiga bude kyautar, ta ciro wani kyakkyawan kwali mai kyan gaske da zanen waya waya a jikinsa. Saude ta bi hoton wayar da kallo kai da gani ka san ta yi tsadar gaske, a zuciyarta ta furta ‘Allahumma arzuquni" tasa hannunta ta bude kwalin. Gabanta ya yi wata mummunar faduwa ta yi ‘ masifar firgita ganin sabuwar wayar kwance cikin kwallin, ta ciro ta tana jujjuyawa, touch screen mai shegen kyau, wadda ta san ko da kudl aka hada ta ba za ta iya kunnata ba. Saude ta riqe wayar tare da dafe kai, yau na shiga uku ni Saude, wai me ke shirin faruwa da nine? Wasu irin hawaye suka ziraro daga idanuwanta ta lura mutumin nan so yake ya jaza mata bala’in da ba zata iya dauka ba, yanzu tsautsayi yasa Hajiya ta samu labari ya kenan? Motsin taflyar da ta ji ne ya sa ta zabura ta maida wayar cikin kwalinta ta tura a qarkashin filonta, tana faman‘muzurai. Aunty ce ta shigo da sallamarta suka gaisa sannan ta ajiye mata wata leda Saude ta mika hannu ta janyo ledar tana duddubawa. Sabulan wanka ne dana wanki tare da kayan shafawa da mayuka, ta ajiye‘ leadar gefe ta koma ta kwanta tana fatan gari ya waye ta je ta maida masa wayarsa, don ba zata yarda ba ya jaza mata tashin hankali da bala’in da ba za ta iya dauka. Ba Dole nema ta runtse ido ta fada masa‘ ya fita daga rayuwarta ita dai ba kowan kowa bace hakan kuma ba yana nufin ba ta san mutuncin kanta bane da wannan tunanin bacci barawo ya sace ta. Washe gari da safe Saude ta tafl Bangaren Dr. Ahmad babu kowa a falon nasa don haka ta zage ta shiga aikace- aikacenta qarfe goma daidai ya sauko daga samansa yana sanye da jallabiya sabuwa ruwan toka mai hade da hularta Suna hada ido da Saude ya yi saurin qarasa saukowa daga matattakalar yana fadar, “Zo. nan Saudat." * A hankali ta dago ta kalle shi tare da gaishe shi cikin girmamawa kamar yanda ta saba. Ya amsa' a tsanake sannan ya jefo mata tambayar da ta sanya ta saurin dagowa tana kallonsa, ya qara‘gyara tsayuwarsa tare da maimaita mata tambayar. “Na ce laflya ba ki bude kyautar da nayi miki ba Ko baki iya bane?” Ya karasa maganar cike da tuhuma. ; Saude ta dukar da kanta tana kallon kafet din dakin cikin nutsuwa ta soma magana. “Kayi haquri Yallabai ba wai ban yaba ba ne kawai dai na ga kyautar ba ta cancanta dani bane shine yasa nayi' tunanin maido maka, amma ka yi hakuri Dr. Yayi wani takaitaccen murmushi tare da zama saman hannun kujera ya zauna yana kallonta a nutse kafin ya ce ‘Dama ita kyauta cancanta ce ke sawa ayita idan kuwa cancanta ce to ke kuw kin ' wuce wadda a kai miki kinfi qarfin hakan. Kuma idanma ba ki sani ba ina so yau ki sani dangantakata dake tamkar hannu da ido ne yanzu sannu a hankali zan shafe hawayen da ke kwaranya daga idanuwanki insha Allahu sai na wanzar da dariya a idanuwan dake ta zubar hawaye, kin fahimta?” Saude ta girgiza masa kai tana fadar, ‘A’a Yallabai yin hakan yana nufin zaka tsamo ni daga rijiya ka jefa ni kogi ne Yallabai ka yi tunani zan iya shiga matsala wajen Hajiya, na tabbatar idan ta samu labarin kudirin da kake nufo ni da shi zata dauki kowane irin mataki a kaina, Dr Ahmad ya kada mata kai yana fadar, 'Ko kusa Saudat babu wandu ya isu ya yi wu mutum ”abinda Allah bai masa ba haushin me Asmu za ta ji don kawai ina kokarin taimaka miki meye abin da zai tunzura ta a ciki? Ni ban ganshi ba, kuma koma akwai ba zai dame ni ba, zan yi Kokari har sai na sauke alkawarin da na dauka.” Idon Saude ya ciko da hawaye cikin muryar kuka ta ce, ‘Na san ba zai dame ka ba YallaBai amma ni zai dame ni, wata qila ma ya zamo silar barina duniyar gaba daya. ’ Dr. Ahmad ya ce, ‘Hakan ma ba za ta kasancewa ba Saudat ki daina ma fada.’ Saude ta ce, ‘Idan ya kasance fa?” Shiru ya yi yana kallonta Saude ta yunkura ta mike hawayen da suka ciko daga idanuwanta suka samu damar zubowa cikin kuka ta ce, ‘Zan bar gidan nan dole zan bar shi, dan ina tsoron abin da zuciyata ke hangowa ina jiyewa kaina, dan idan ma wani abu ya same ni babu wanda Zai yi kukan rashina, babu ba ni da shi.... Kuka ya ci Karfinta sosai. Dr. Ahmad ya yunkura ya zagayo ta gabanta yana kallonta cikin sanyayyar muryar shi ya soma magana. ‘Duk inda ki ka nufa a fadin duniyarnan sai na nemo ki, babu inda za ki shiga ki layance min. Ina tare da ke Saudat har: sai na ga kin yi dariya sai na ga rayuwarki ta inganta kin samu farin ciki mai dorewa na yi wa kaina wannan alkawarin kuma zan cika shi ko da hakan yana nufin rasa komai na a rayuwata.’ Saude ta yi saurin juyawa tana kallonsa ya daga’ mata kai yana fadar, "Tabbas kisa ido kiyi kalio.’ ‘Ya juya a sukwane ya fICe daga falon ya bar ta nan tana kallon qofar da ya fita. Wani irin kuka ya zo mata, tsoronta daya a duniyar nan matarsa Asma; don ta san ba lallai bane ta yi musu kyakkyawar .zargi ba, tana tsoron ta yi musu mummunan zargin da zai‘sa ta yanke mata hukunci daidai da zarginta. Saude ta Kara rushewa da kuka don har ta hango irin bala” in da za ta iya fuskanta Haka ta karasa aikinta tas ta bro Bangaren nasa, yinin yau haka ta yi sa a kwance. Da daddare kuma Hamid ya kira ta ya Kara caza mata Kwakwalwa. “Wai Saudat me ke damun ki ne shin k0 kin mance da yau saura sati uku auren ki? Na lura hankalin ki kwance yake tun yaushe nake fama da ke kina gocewa. Saudat idan harkin soma san Garba ne ki fad'a mini in fidda raina kawai, amma don me za ‘ki ta yi min yawo da hankali ki ce yau ki ce goba, idan kin san ba zaki iya fitowa daga gidan ba ki 'fad'a mini ni in zo da kaina in dauke‘ki.’ 'Saudat ta ja numfashi ba ta taba tunanin ya iya bude wuta haka ba, ta ma rasa ta indaza ta fara, don . haka ta kwantar da murya ta ba shi hakuri tare da yin . masa alkawarin duk rintsi gobe za ta gudu ta bare ‘ Abujar. » , Abun duniya duk ya ishi Saude tunaninta daya yanzu hanyar da za ta bi ta bar. gidan ga YallaBai yana nema ya taso ta gaba tsoronta daya ma yanzu kar ya ruguza mata al’amuran ta, wannan tunanin ne ya hana Saude barci da wuri sai kusan biyu da wani abu na dare ta kwanta, don sai da ta harhada kayanta tsab na barin garin. . Sallar Asuba ma da kyar ta iya yin ta saboda baccin da yaci qarfinta. A kan sallayar ma wani sabon baccin ya sake dauke ta. Ba ita ta farka ba sai qarfe sha daya da mintina. Ita kanta ta yi mamakin tsawon lokacin da ta dauka tana bacci, don haka ta mike da hanzarinta za ta shiga bandaki ta ji kukan wayarta, don haka ta dawo ta dauka. ' Tun kafin ta qarasa sallamar ya katse ta ta hanyar fadar, ‘To yaya kin taho k0 kuwa yanzun ma ba ki samu damar ba? . Saude ta sauke numfashi tare da fadar, ‘Nina fada maka Yaya Hamid insha Allahu yau zan bar gidan nan duk rintsi, saboda ni kaina nafi ka kaguwa dana bar gidan nan don Allah ka kwantar da hankalin ka insha Allahu babu abin da zai faru.’ Ya ce, ‘Hmm! Saudat kenan na lura ba ki san irin son da nake miki ba shi yasa har kike fadar kar in damu wallahi yanzu kasancewa ta da ke ne kawai zai ba ni farin ciki a rayuwata, don Allah Saudat kada ki ci gaba da nisanta kan ki dani please; ’ Tausayinsa ya kama ta ita kanta ta soma jin irin yanda yakeji yanzu don haka cikin sanyin murya ta ce, “Kayi hakuri Yaya Hamid ni kaina. ina jin yanda kake ji a yanzu, kuma nan da wasu ‘yan awanni zan maka kyakkyawan albishir.” . Hamid ya ce Allah yasa ki gaggauta kin ji?” ’lnsha Allahu.” Ta ce cikin sanyin murya, sannan ta. kashe wayar ta mike da nufin maida ta wurinta, zuciyarta ta yi. wata mummunar bugawa. A tsaye yake jikin qofar ya harde hannuwansa a kirji ya tura mata idanuwansa da ke sanye cikin farin gilas gaba daya ya tattara duk wata nutsuwarsa a kan Saudat ta ji.tamkar ta kurma ihu saboda tsaba: tsor da kaduwa duk ta dabarbarce,. , Dr. Ahmad ya take a hankali har zuwa gabanta ya mika: mata hannu, “Ba ni wayar.” Ba musu ta miqa‘ masa wayar hannunta na rawa. Ya ce, ‘miqo min har da waccan da na baki.’ Jikinta na faman bari ta juya ta dauko masa, ya karba kawai ya juya ya fiCe abinsa ba tare da ya ce da ita komai ba Saude ta fada saman gadon jagwab kamar an zuba kayan wanki har wata zufa ke tsatstsafo mata, ta daura hannu a kai .Wayyo Allah na! Ya Ubangiji gani gare“ ka , Asma. ta fado kamar an an jefo ta, ' ' Saude ta Zabura ta miqe a tsorace tana kallonta, Ta tsaya tana watsa mata wani malalacin kallo. Saude ta durqushe a gun, tsantsar firgici ta bayyana a fuskarta bakinta sai kyarma yake wurin fadin ‘In...ina... ina wuni Asma ta tabe baki tare da jan wani dogon tsaki, ta shiga zagaye dakin tamkar mai neman wani abu ta kai ta kawo ta kai ta kawo, ta dinga binciken ta sai data gaji sannanta juyatafice batare datace uffan ‘ba. Saude ta yi suman tsaye, me keson faruwa ne da ita ne? Ta yi masifar firgita, ita dai ta san ta shiga . tsaka mai ‘wuya, don da za a auna ta a lokacin babu abin da zai hana a tabbatar da hawan jininta, kukan ma ya gagare ta sai muzurai kawai take yi. ' Wasa-wasa lokaci ya soma tafiya tana nan zaune, ” tabbas idan ta yi wasa lokaci zai qure mata, don gangar jikinta ce kawai zaune a gun amma zuciyarta na wurin Dr. Ahmad. Qokon ta daya Allah yasa ya yanke mata hukuncin da za ta iya dauka. Wasa-wasa ta lurawankin hula zai iyakaita dare,don hakata yanke shawarar tashi ta je ta ba shi hakuri, ba yanda ta iya haka ta lalalBa ta mike: jikinta amace ta nufi Gangaren nasa. Sallamar da take shirin yi ta makale a makogoranta, tsaye yake goye da hannayensa a baya wadanda ke rike da wayoyin da ya karba wajenta, duk da bayansa take saboda ya bada baya, amma hakan bai hana ta fahaimci yana cikin yanayi marar dadi ba, tsoronta ya qaru matuka tana fargabar ya yi mata mummunan zargi. Jin shigowarta yasa Dr. juyawa a hankali yana kallonta da jajayen idanuwansa ba tare da ya ce mata kala ba. Saude ta durkusa a gabansa muryarta a sanyayc ta ce ‘Don Allah ka yi hakuri Yalla6ai wallahi ba... Dr. ya yi saurin daga mata hannu alamar ta dakata, ya yi taku daya zuwa uku ya matso gabanta cikin razananniyar muryarsa wadda ke fita a hankali ya fara magana. “In yi hakuri laifin me ki ka yi min? Kina tunanin raina ya baci ne don na kama ki kina kula maza?” Ya girgiza kai. “K0 daya Saudat ko a jikina, ko da kuwa duk mazan duniyar nan samarinn ki neba zai rage ni da ‘ komai ba, illah dai kawai na tausayawa rayuwarki da ke qoKarin rugujewa, ke yarinya ce Saudat ba za ki gane waye da namiji ba sai ran da ya buga miki irin nasa tambarin, ranar ne zaki fahimci irin wautar da ki kai a baya. Ni ba zan takura ki ba in ce dole sai yanda nake so za ki yi rayuwa ba, a baya wauta na yi da rashin bincike wanda yasa na dauka zuciyarki shararriya ce babu wani datti a cikinta, ashe ban sani ba tuni kin shigar da soyayyar da take nema ta makantar da ke ta kai ki ta baro ki.’ Ya dan yi shiru yana kallonta yana girgiza kai, sannan ya mika mata wayarta. “Ungo ga wayarki.” Hankalin Saude ya qara masifar tashi ba ta san lokacin da idonta ya kawo kwalla ba, sai dai ta ji zubar su saman kuncinta. Dr. ya waro ido cike da mamaki kafin ya ce ‘Kukan me za ki kuma Saudat ai na dauka firgicin ki‘na raba ki da masoyin ki ne da na yi kuma sai na ce na bar ki da shi, to me ye kuma abin kuka?” Saudat ta sa hannu tana share hawayenta, wanda sukaqi tsayawa ta soma magana cikin kuka. “Ka yi hakuri wallahi ba da wani namiji nake magana ba Hamid ne.” Nan ta kwashe labari ta ba shi tun daga sakon da ya aiko Dillaliya da shi har zuwa wayar da suka yi. ~ Dr. ya ja numfashi kafin ya ce ‘Saude kenan, a dan labarin da ki ka ba ni na fahimci kina son Hamid shin haka ne?” Saude ta ji tamkar ya dora mata Dala da Gwauron Dutse aka, ta rasa abin da za tace masa ma. Dr. ya sake cewa, ‘Da ke nake magana fa Saudat kin mini shiru Da kyar ta iya dagowa ta kalle shi, ya yi mata masifar kwarjinin da ba za ta iya kallon idanuwan shi ta fadi abin da ke zuciyarta ba. Murya: shi a sanyaye ya sake maimaita mata tambayar a karo na uku, ba ta san yanda a kai ba sai dai ta samu kanta tana mai girgiza masa kai, alamar a’a. Shin meye dalilin saude na cewa batason hamid mu tara donjin yaddah zataci gaba da kayawa [1/27, 10:11 AM] A A Dboy: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚 [1/28, 12:05 PM] I love my mum: *YAR TALLA* *CHAPTER 20* Dr Ahmad ya ajiye wata nannauyar ajiyar zuciya kafin ya ce “Ki je zan neme ki.’ Saude ta share hawayenta ta mike a sanyaye tafi Dr. Ahmad ya bi ta da rinannun idanuwansa wanda sukai jawur. Saude tana shiga dakinta ta fada kan gadonta ta fashe da wani irin kuka mai sauti, ita kanta ba za ta iya misalta tashin hankalin da take ciki ba, zuciyarta na wurin Hamid ta san dole ya neme ta tunda ta sanar da shi yau za ta bar gidan, shin idan ya kira ta bai same ta ‘ba wane irin zargi zai mata? Kila ma ya rabu da ita. Wayyo ni Allah na! Ta Kara rushewa da wani sabon kukan. Yinin ranar haka ta yi shi babu wata walwala a tare da ita. . Da yamma liqis Dr. Ahmad ya aiko aka kira ta, don haka ta wanke fuska ta murza mai da hoda, duk wai don karya gane kukan data sha, sannan ta fice. Da sallamarta ta shiga falon nasa, yana zaune saman daya daga cikin kujerun falon, ya harde tamkar wani basaraken Balarabe, shigar ta manyan kayan ta yi masa masifar kyau ta Kara fitowa da cikar kamalarsa da kwarjininsa. Saude ta durqusa dan nesa da shi kadan kafin ta ce, ‘Sannu dahutawa YallaBai.’ Dr. Ahmad ya dan zuba mata idanuWansa kafin yace, ‘Me ya samu idanuwan ki Saudat, kuka ki ka rinka yi tun tafiyar ki k0?" Da sauri ta girgiza masa kai alamar a, a ‘Hmmm! Saudat kenan me yaSa kike san boye mini damuwarki alhalin duk wani motsin ki sai zuciyata ta fassara mini shi Ya girgiza kai tare da fadar ‘Tashi mu je ki min rakiya cikin gari.’ , _ Da hanzarinta ta yi saurin daga kai tana kallonsa Dr ya mike; tare da fadar kar ki ce komai biyo ni kawai. Saude ta mike. jikinta a sanyaye tana shirin fashewa da kuka yana kallonta bai kula taba ya yi gaba abin sa. ’ Saude ta bi shi tana matsar kwallarta ita dai so yake kawai ya jaza mata tashin hankalin da ba za ta iya dauka ba kawai. Suna fitowa harabar gidan ta samu masu tsaron lafiyarsa wadanda suke a lungu da sake na gidan sun nufo sa, wasu kuma sun nifi wurin motocinsa wadanda yake fita da su Dr. Ahmad ya daga masu hannu kawai ya nufi wata shareriyar Jeep mai qofa takwas fara mai bakin gilas, daya daga cikin masu gadin nasa ya take da gudu ya bude masa kofar baya ' Dr Ahmad ya juya yana kallon Saude wadda ke tanya tamkar‘ yar kaciya, ya yi mata nuni da hannu alamar ta shiga ta ji tamkar ya dora mata dukkanin tashin hankalin duniya ta ja ta tsaya cikin tsananin kidima Dr Ahmad ya dan matsa daf da ita muryarsa Kasa kasa ya ce ‘Za ki shiga k0 k0 sai na dauke ki na shiga dake da kaina?” . Ganin yanda ya matso ta ya tabbalar mata zai iya yin abin da ya fada din don haka ta janyo dauriyar duk duniyar nan ta dorawa kanta, ta taka a sanyaye ta ’ shiga motar, tana zama shi ma‘ya shigo aka maido masu kofar aka kulle Saude ta ji ta yi mutuwar zaune idan ta ce bata cikin tsananin rudu da kaduwa ta san ta yaudari kanta. Ta lumshe idanuwanta tana sauraren bugun zuciyarta ta san ita yau tata ta Kare ba abin da zai hana Asma na samun labari tasa bindiga ta. Harbeta Shiru babu wanda ya yi magana a cikinsu. Sai Dr. Ahmad neya dan mika hannun shi ya latsa gefen motar, sai ga wasu hadaddun labulaye sun zagaye motar , ya mika hannu ya bude na’ura mai KwaKwalwa (Computer) din da ke gabansa wadda ke jikin motar ya kunna, sannu a hankali ta kama tamkar talabijin din bango. Ya koma ya jingina ya ci gaba da latselatsensa ba tare da ya kalli inda take zaune ba, kowa da abin da yake sakawa a zuciyarsa. Ba ta san sun iso ba sai dai ta ji an bude masu qofar, Dr. ya rufe computer din ba tare da ya kalle ta ba ya ce ‘Fito mu je. ’ Bai tsaya ba ya sa kai ya fito don haka ita ma ta ziro qafafuwanta ta fito tana kallon harabar wurin da suka shigo. wurin gyaran jiki ne wanda ya amsa sunansa a cikin garin Abuja daga sama an yi rubum da manyan .. baki a jikin wani karfe ANNURI beauty QUEEN rubUTun ya bada hasken ‘ Dr Ahmad ya yi gaba Saude na biye dashi har suka iso cikin masu take masa baya daya yayi saurin isa ya bude musu qatuwar kofar ta gilas tareda gaishe suka shiga qaton wurin mai kamar an gina shi da' zallan gilasai Da kyar Saude ke dosana kafarta’ dan gudun kar ta fasa gilas din Suna shiga ciki su kabi wata qofa mai kama da ofis,‘ Dr. ya tsaya gaban wata mata cikin Harshen turanci su kai magana sannan ta miqa masa wata yar lakarda ya yi wani dan rubuce rubuce ya miqa. mata itasa hannu, ’ sannan ta mike ta yi masa nuni da wani kujerar dake gefe da dan tebur dinta guda a gabanta; wanda aka dora News paper a sama, ta kawo masa lemu da cake sannan taja hannun Saude. . “Come and enter my frnd Saude ta ce ikon Allah ai ke kika san shi Tasa hannunta cikin na Saude suka shiga cikin wani qaton wuri nena gaske wanda aka zubama duk wani" injin ‘ k0 wata na’ura ta gyaran jiki ‘Matar ta kira wata babbar mace Bahaushiya wadda ba zata wuce shekara arba in ba ta nuna mata Saude su Sukai kai magana cikin harshen turanci da matar ta mikawa Saude‘hannu da murmushi a fuskarta tana fadar. “You are welcome my sis. ' Saude ta yi sukuti tana kallonsu cike da takaicin turancin banzan da suke mata. K0 matar ta lura ne? Oho ta canja harshe zuwa Hausa. “Sannu da zuwa ‘yar uwa mu je k0?” Ba musu Saude ta bi ta suka nufl Bangaren gyaran gashi, ta zauna a kai mata gyaran gashi sosai sannan suka wuce Bangaren gyaran jiki, inda a kai mata dilka da halwa lokaci guda, daga nan a kai mata gyaran qafa da na akaifa. Tun kafin a qarasa dama Saude ta gama tsurewa da tsabar kyan da ta gani kwance a jikinta, ita kanta ba ta taBa sanin haka ta hadu ba sai yau, don k0 Indiya sai haka, saboda idan baka san ta ba aka ce maka Ba’indiyace ba yanda za ai kai musu. ' Ita kanta ta san sun ci lokaci, don k0 da ba ta duba agogo ba ta san dare ya ja sosai. Ana gamawa suka fltO inda Dr. Ahmad ke zaune rike da jarida yana dubawa suna Karasowa ya ajiye jaridar ya mike yana kallonta tamkar wadda ta fado daga sama, lokaci guda kuma ya lumshe idanuwansa ya bude ya juya ya koma wurin ‘yar Baturiyar nan wadda ke ta latse-latse cikin computer ya mika mata A.T.M dinsa tasa ta cire kudin sannan suka flto daga wurin. Ita dai Saude kallonsa kawai take, amma tambayoyi ne cike fal da cikinta, wanda ta tabbatar ba * ta da mai amsa mata su sai shi kadai. Suna mota wanda suka shiga kamar dazu direba ya ja su suka fice daga » harabar wurin Saude ta lalubo duk wani karfin halinta kafin ta iya bude baki ta kira sunansa. “YallaBaii’ ,. Dr. Ahmad ya dago da idanuwansa daga saman wayarsa yana kallonta kan ya ce, ‘Ya dai Sande?" ““ Ta dan sha Jinin jikinta kafin ta ce ‘Ina so in dan ‘ yi wata‘ yar tambaya.” ce Dr ya dauke kansa daga kanta kafin yace, ‘Tun » kafin ki yi tambayar na san abin da za ki tambaya don haka ki yi haquri ki hadiye zan ba ki amsa da kaina ‘ idan lokaci ya yi.-’ Za ta sake magana ya daga mata hannu, hakan yasa ta ja bakinta ta tsuke a dole, ta bar zuciyarta na faman‘ dukan tara-tara. Suna isowa gidan ta .kwasa da sauri da niyar ta riga shi shiga gidan, Dr. ya yi saurin tsayar da ita ta hanyar kiran sunanta, ta ja ta tsaya cak ‘ Da kansa ya Karaso har inda take ya daidaita tsayuwarsa a gabanta kafin ya soma magana, ‘Ki shirya gobe da safe za mu fita.” Saude ta yi saurin dago da fuskarta tana kalloh shi shi ma ya zuba mata idanuwan nasa wanda babu alamar fargaba a cikinsu,idanuwanta suka kawo kwalla cikin muryar kuka ta soma magana. “Ni wallahi ,ba zan je ba na gane so kawai ka ke ka jaza min bala’in da ba zan iya dauka ba na rantse da . Allah babu inda zani .... ‘ Ta Kara rushewa da kuka. “Don Allah don Annabi ka taimake ni kar ka jaza min bala‘in matarka don Allah...’ Dr. Ahmad ya yi wani murmushi wanda ya tsaya iya laBbansa kawai kafin ya ce, ‘Ashe kina da baki haka? Da kyau. To ki dai shirya‘ fita gobe koma me ye zai faru ai kina iya daukarsa idan kuma ba ki zoba to ki tabbatar ni da kaina zan shigo in dauke ki kin san kuma zan iya, don haka sai da safe.’ . Ya juya ya yi gaba ya bar ta tana masa rakiya da kallon da ke cike da mamakinta karara, don a yanzu hawayen ma sun daina zuba. Mamaki da fargaba suka kashe ta, ita kanta ba ta san tsawon lokacin da ta dauka a tsaye ba, don sai da ta yi da gaske sannan ta iya jan qafafuwanta ta yi gaba. Tunane-tunane da damuwa yau su suka hana Saude barci da wuri, shekarunta sun yi Karancin da za ta iya yankewa kanta hukunci, da ta gaji da tunanin sai ta kifa kanta samaun filo ta shiga kuka mai sauti, sai da ta yi mai isarta sannan ta yi shiru don kanta, babu wanda ya lallashe ta, sai ajiyar zuciyar da take ajewa akai akai. A' haka barci barawo ya sure ta ba tare da ta sani ba. ' Tun da garin Allah ya waye Saude ke zaune saman gadonta ta zuba uban tagumi da hannuwa bibbiyu, kana kallonta za ka tabbatar da tsantsar damuwarta, ba « ta ankara ba taji an turo kofa za a shigo. , Gabanta ya yi mummunar faduwa ta zabura ta miKe tana faman muzurai don duk a zatonta Dr. Ne Aunty ta turo Kofa ta shigo da sallamarta Saude ta ja wata ajiyar zuciya sannan ta koma ta zauna Aunty ta ‘ ‘dube ta da kulawa kafin ta ce, “Lafiya kuwa Saudat?" ‘ Saude ta dake kafin ta 'ce, ‘Me kika gani Aunty?” ‘Na ga duk kin yi wani wurjanjan ne kamar ba kya cikin hayyacin ki.” ' Saude ta girgiza kai ‘A’a lafiya ta qalau kawai dai .tunani me.” ~ Aunty ta dan zuba mata ido kafin ta ce, ‘Kai Saudat ban yarda da ke ba jeki gaban madubi ki kalli ‘ kanki da kyau, ki ga yanda kika koma, wannan kyan da daukewar lokaci guda na mene ne?” Gaban Saude ya kara mummunar bugawa duk ta dabarbarce ta rasa abun fada. ' Aunty ta girgiza kai tana wani murmushi wanda ‘bai kai zuciyarta ba ta ce, ‘Saudat ke nan ni ba tun yauwa ba na fara zargin ki, sai dai a yau na kara . tabbatar da zargina, Saudat gyaran jiki ki kaJe,” Gaban Saudat ya Kara wata mummunar bugawa a “ karo na biyu, idanuwan nan suka yo warwaje . Aunty ta ce“Hmmm! Saudat kenan me yasa ki ke Kokarin yaudarar kan 'kine? Me yasa ki ke nema ki dorawa zuciyarki wahala ne? Shin Saudat kin yi tunanin wannan kyan naki zai iya daukar hankalin maigidan nan ne? K0 kusa wallahi k0 da wasa don Yallabai ya wuce duk wani tunaninki ’ ki Don idan har kyau na daukarsa to duk inda ake Zuwa auro: kyakkyawar mace a fadin duniyar nan: 'yana da kudin da zai iya aurarta ke k0 siyowa ake yi yana da kudin siyan ta. Saude duk yanda baki tunani ba Yallabai ya wuce da sanin ki nasan YallaBai tun kafin ya auri Asma’u asalina ‘yar aikin gidan su ce. Saudat wallahi . wallahi yar gidan shugaban Kasa har falon Hajiyarsa ta zo nemansa, amma ya fice ya bar mata gidan bai kula ta kanta ba. Saudat duk yanda ki ke ganin YallaBai ya wuce ’nan, don jin kansa da mazantakarsa ya wuce yanda kike ganinsa a cikin gidan nan, don ni kaina ba zan iya kirga yawan ‘yan matan da ya yi ba tsakanin Abuja da sauran jahohinnan ba. Saudat ina guje miki daukar Dala da Gwauron Dutse aka, don idan ki ka bari Asma’u ta samu labari ina mai tabbatar miki sai kin raina kanki. Don k0 da ki ke ganin kamar ba su damu da juna ba, to wallahi suna son junansu don kuwa auren soyayya su kai kamar za su cinye junansu. ‘ Asalin Asma ‘yar asalin nan Abuja ce mahaifinta shi ne Ministan kudi na Nigeria a lokacin kafin ya sauka daga kujerar. Mahaifinta abokin mahaifin Yallabai ne ba zan taba mantawa ba sun taba zuwa gaishe da mahaifin Yallabai da Asma da mahaifinta da mahaifiyarta a lokacin shi mahaifin Yallabai yayi yar rashin lafiya. Anan ne suka hadu da Asma da Yallabai, tun farkon soyayyarsu sun ‘tiffita qasashe masu yawa, Soyayyarsu ta dauki tsawon lokaci kafin a tsaida maganar aurensu A lokacin ne kuma iyayensu suka sanya su harkar Siyasa Cikin sati biyu a kai bikinsu aka gama cikin ma ’aikatan da aka bai wa Asma Hajiyar Yallabai ta ‘ hada masu dani na dawa gidansu da zama. A lokacin basa wannan kasa basa wancan kasa cikin wata guda ba baifi su zauna nigeria sau biyu ba Daga baya ne kuma aka fara kamfen to sannan ne suka zauna aka fara yaqin neman zabe ita da shi duka kowa yana neman tasa kujerar shi yana neman dan majalisar tarayyar Abuja, kuma cikin ikon Allah kowa ya samu. To a lokacin ne fa kowa ya kama gabansa, haduwa ma sai ta yi masu wuya suna cikin gida daya, amman sai suyi wata wani lokacin basu hadu ba, sai dai k0 cikin dare, amma idan wannan yana Nigeria to shi wannan ya bar kasar,idan wannan ya dawo to wannan ya tafi wurin meeting. Haka dai abin ya ci gaba da kasancewa Kafin zuwan ki Asma ta samarwa YallaBai ‘yan ' aikin da zasu rinka kula da shi sun fi biyar duka an karesu kowacce da tata matsalar har zuwa kanki Saudat da ki ke ganin Asma ba qaramar mai arziki ' bace duk yanda ki ke tunanin rashin mutuncinta ya wuce nan musamman a kan mijinta‘ Don tana da masifaffen kishin da ba ki tunani zata iya yin komai a kansa, don haka Shawara ‘nake baki Don ina sonki saude ki kama kanki tun kafin Yallabai ya lura da takun ki, idan kunne yaji Ta tabe baki tare da juyawa ta fice Saude ta saki wata ajiyar zuciya mai qarfi shin in ban da abun Aunty ma ita ko giyar wake ta sha ai ba ta fara hada kanta da YallaBai ba, balle da hankalinta .dama abin da take gudu kenan mummunan zargi, shin yanzu ma idan suka sami labarin fitarsu jiya ya kenan? Ta girgiza kai cike da fargaba ta yunkura ta mike don tsoron kar ya zo da kansa ya Kara jaza mata wani zargin, ta zura takalmanta sannan tafi ta nufi bangaren nasa. : Tana shigowa falon shi kuma yana saukowa daga matattakalar benan, sanye yake da shigar qananan kaya, koriyar riga da bakin wando sai takalmin qafarsa “ na fata, yau babu gilas a fuskarsa don haka kana ganin fararen idanuwansa fat masu kama da farar takarda, sumar kannan tasa ta sha gyara sai sheki take hannunsa na rike da makullin mota. , Saude ta durkusa a qasa jikinta a sanyaye tana gaishe shi. Dr. Ahmad ya amsa mata cike da kulawa kafin ya ce, ‘Saudat ya na ga kamar kina cikin damuwa laflya dai k0?” ' Kai kawai ta girgiza masa alamar ba komai Dr. Ahmad ya Kara matsowa daf da ita ya sa hannu ya mikar da ita tsaye cikin raunanniyar muryarsa ya ce,‘ “Ban yarda da babu komai ba Saudat, ki fada mini me .ke damun "ki, ?" Ya yi tambayar yana nuna kansa,’ , Saude ta girgiza masa kai alamar a’a. ‘ Ya CE to waye?" Idonta ya kawa kwalla ta yi shiru ba tare da ta yi magana ba, dan tana motsa ~ bakinta kuka ne zai kubce mata Zuciyar Dr ta cika da tausayi muryarsaa sanyaye ya ce ”‘Saudat kina cikin damuwa na fahimci yanda ki ke ji a tawa zuciyar kiyi hakuri insha Allahu komai ya kusa zuwa qarshe Taso muje Saudat. Ta yi saurin kallonsa da idanuwanta dake cike taf ‘da kwalla tana qokarin yin magana ya dora danyatsansa saman labbanta alamar ta yi shiru kar ta ce komai, sannan ya yi gaba abin sa. Saude ta lallaba ta mike ta bi shi tana goge kwallarta. Yau da kan shi ya ja motar cikin wata qaramar mota ‘yar dunkulalliya mai‘ kofa biyu wato sport car, iya shigar mutum biyu ce mai bakin gilas irin wanda duk nacin ka ba ka isa ka gane wanda ke ciki ba. _ Kai tsaye wurin da suka je jiya ta ga sun nufa ita ‘dai kallonsa kawai take kamar jiya haka suka shiga ya' yi rubuce~rubucensa aka shiga da ita wajen 'Washing and dressing. > ‘ Cikin awannin da ba su fi uku ba aka gama mata ’ kwailiyarta tsab cikin wasu hadaddun kaya . ready made riga da siket English wears bakin siket da falmaran mai jinin kart. Falmaran din ya kawo mata ‘har kusan kugu mai dogon hannu sai bakin siririn gyale wanda aka nade mata tamkar nadin Larabawa ya tsaya iya wuyanta Gyaran gashin da , akai mata ya zubo ta gefen fuskarta ya sauka har fadarta; Rigar ta ciki ta kamata sosai surarta dukta bayyana ta bi ta lafe jikinta, falmarar din mai budaddan gaba ce hakan yasa babu abin da ta rufe . Takalmin kalar baqi ne mai mai tsini sai jakarsu ‘yar Post mai dan girma. Suna‘ gama mata suka sa camera suna mata hotuna dan su~kan sun san ta yi masifar haduwa k0 gasar sarauniyar Indiya zata iya kyan da zata yi kenan. Ni kaina dai marubuciyar ban san Saude ta hadu haka ba sai yau, lol ta koma tamkar wata jugunanniyar hadaddiya wayayya classical. Shi kan shi uban gayyar duk yanda ya so daurewa sai da ya tofa , “Kai Saudat wannan cinyewar fa haka? Dama haka ki keda kyau ko dai idona gizo yake min wallahi am so suprise Saudat dai iyakar ta ido, sannan ya biya kudin suka fito A mota ma sai dai ya dubeta, “Kin san wallahi kin yi kyau gaskiya Momy za ta yaba da ke Saudat ta yi saurin kallonsa, ‘Momy kuma?” Ya daga mata kai “Ita fa dan yau yawo zamu sha tun daga gidan sister Farida har gidan Uncle B da ‘ gidanmu inda aka haife ni yau za ki ga Momyna da Dad dina ai za ki yi farin ciki ko?”‘ A sanyaye Saude ta daga masa kai amman zuciyarta cike take da zargi da kuma dumbin fargaba ' Tafiya su kai mai nisa sosai kafin su iso Maitama, Dr. ya ja ya tsaya a bakin gate din wani gida wanda ya ke zagaye da manyan furanni masu kyan gaske ya yi horn ,maigadi ya bude sannan ya cinna hancin motar cikin gate din gidan. Ya samu wuri ya yi fakin ya dubi Saude fito mu je ranki shi dade k0 sai na fita na bude miki? Saude ta yi saurin watsa masa wani kallo mai kama da harara. Ya yi wata dariya harda kyalkyalawa kafin ya ce ‘Wannan kallon fa yallabai ne fa.’ Saude ta yi saurin turo kofar ta fito tana gunkuni irin na shagwababbun yara Dr. ya fltO daga motar yana zolayarta. Maigadi ya kwaso da gudu ya nufo su ya zube gaban Dr. yana kwasar gaisuwa, ya Ciro kudi masu yawa ya mika masa ya shiga godiya tare da kirari. Dr. ya dubi Saude ‘Mu je’ Ba musu ta juya ta bi shi suka nufl cikin gidan. . Ita dai ta gama saduda duk yanda Allah ya yi da ita mai kyau ne ta riga ta fidda rai da rayuwar gaba daya. A bakin qofar falon suka tsaya yana Kwankwasa qofar, can ta ji wata murya na fadar, “Who is knocking?” “Brother. ”Daga can suka ji ta fasa wata uwar Kara da takun gudunta. Dr. ya murmusa ya kalli Saude tsakiyar ido ta yi saurin janye idanuwanta. Tana bude qofar ta yi wani tsalle ta fada jikinsa tana dariya, Saude ta saki ido da bakl tana kallon su. Ikon Allah su kuma haka tasu dabi‘ar take? ,ckin dariya take fadar. Woo my my bros; ,nayi kewarka.” ‘Dr: Ya yi dariya tare da janye ta daga jikinsa yana nuna mata Saude tare da fadar “You see her did Is my Saudat ' Da sauri ta maida hankalinta kan Saudat, ta sake juyowa tana kallon shi tana fadar, “Are you sure?” ' Ya yi wani takaitaccen murmushi yana fadar, yes am sure my sis.’ " Ta yi wani tsallen murna ta dafo Saudat tana fadar “Wow my bross wallahi na ji dadi sosai, Saudat ‘ sannu da zuwa mu shigo don Allah.’ ‘ “* Saude dai kallon su kawai take tana dafeda . kafadarta har cikin falon, tsararran gaske wanda ya ji kayan alatu na more rayuwa iri-iri Da kanta ta zaunar da ita tana fadar. ‘Zauna nan my sis, da me dame ki ke so a kawo miki yanzu, tun daga snacks, lemo abinci, fruits, duk komi ki fada don wallahi naji dadin zuwanki my bross na gode fa.” Murmushi kawai ya yi mata, ta Kara jawo Saude a jikinta ‘Na ce don Allah ki saki jikinki munfa riga Mun zama daya yanzu dan na san nan ba da dadewa ba ' zaki shigo cikinmu haka ne? ” Saude da ke jin manganun tamkar saukar markade ta yi tamaza ta daga mata kai. Faridat ta ce ‘Gud ai dana sani.’ Ta dubi Dr kai kuma fa yaya me ka keso k0 , , duk kun bani zabi? Ya ce a a karki wahalar da kan ki dan yanzu haka gidan Uncle B za muje daga nan za mu wuce gidansu Dad, don haka kl kawo mana lemo kawai Faridat ta bata fuska ta hau diredire tana fadar, wallahi ban yarda ba Allah Dr. ya yi wata qasaitacciyar dariya kafin ya cc, ‘Wai ke har yau ba za ki girma ba k0 kin manta ke ki ka aje Affan da Ummy ta?” Dariya ta yi ta juya ta bi wata hanya cikin falon nata, tana fita Saudat ta yi saurin kallonsa tana shirin yin magana ya yi saurin daga mata hannu alamar ta yi shiru, a dole ta ja bakinta ta tsuke Gaba daya falon ya dauki shiru sai dai kukan A.C da talabijin din da ke ta faman haukanta ita kadai. Ba tafi minti goma ba sai ga ta ta dawo dauke da wani qaton tire ta ajiye saman tebur, lemukan kwali ne guda hudu sai kofuna masu kyau sai robobin Faro biyu, sai fruits kala-kala sai wani tangaran din da aka zuba dambun mama a ciki, sai daya plate din hadaddan chips din dankalin turawa ne. Farida ta dube su. “Don Allah kuba ni minti goma zuwa sha biyar k0 dan wani abu ne marar nauyi in girka muku.” Dr ya ce‘Kin san Allah sauri muke wannan ma is okay. ” Ya tashi ya matso inda Saude take zaune da muryarshi qasa-qasa yace, ‘Tunanin me ki ke Madam”? Kallonshi kawai ta yi ba ta tanka ba. Faridat ta yi murmushi tana fadar, ‘Wallahi Yaya ' ka yi zabe: kuma mai kunya, amma Bufullatana ceko?”* Murmushi ya yi tare da fadar, ‘Bana san sa ido fa.’ . Ta yi dariya tana fadar, ‘Ai dan Safwan baya nan ne “ wallahi daka sha tsiya, ya tafi ya dauko su Affan daga makaranta, amma don Allah yaushe za ku dawo don . gaskiya ni dai wannan zuwan ba nawa bane Dr. yace‘Sai ki tambayi Madam din dan in gobe ta ce in dawo da ita kin san zan iya.” Farida ta yi. saurin riko hannun Saudat tana fadar, ‘Don Allah don Annabi ki taimaka Anty Saudat ki dawo kin ga dai ni yanzu qanwar ki ce Yanda ta yi maganar ya tilastawa Saudat yin dariyar da ba ta shirya ba, har da Kyakyatawa a haka Farida ta ja ta jikinta har ta samu ta saki jikinta da ita sosai kamar sun dade da haduwa, kasancewar Farida mai shegen surutu ga barkwancin tsiya da iya bada labari. Inda suka bambanta da Dr kenan ita tafi shi Magana shi kuma bai da magana sosai; amma kamar su daya kamar an tsaga kara, har wajen tsawon kana ganin su ka ga ‘yan gida ‘daya. .. ~ Da wayo da wayo sai Dr ya yi da gaske sannan suka samu suka bar gidan Farida, ta hadowa Saudat ~ kayayyaki cike da wata qatuwar jaka mai girma Kirkinta ya bawa Saudat mamamki, kwata-kwata ba ruwanta da Jin kai k0 miskilanci irin na Dr Suna cikin mota sun dau hanya Saude ta dube shi da alamun damuwa karara a fuskana tace ' “Zuciyata na cikin duhu kuma a cike take da sarkakarkun al’amura masu rikitarwa ina cikin rudani ’ don Allah ka fidda zuciyata cikin duhun da take ciki ka fada min me yasa kai wa ‘yar uwarka Karya a kaina, k0 shi ma hakan duk yana cikin taimakon nawa‘ne?" Dr. ya yi wani? murmushi ba tare da ya kalle ta ba ya ce, ‘Kamar kin sani duk yana ciki, kuma daga yau deel din namu zai Kare da fatan kin gane?’ Ba‘ta ce masa komai ba ta yi shiru zuciyarta na kaiwa da , kawowa Katon gate ne ta ga sun tinkara katafaren gaske ‘ mai kama da‘ qofar shiga gari.. Saude ta saki hanci da ido tana kallon gate din yayin da shi kuma yake faman horn, masu gadi biyu ne suka bude kofar Sannan suka ‘shiga katafarea gidan ya sauke gilas din motar: yana ; gaisawa da masu gadin sannan ya wuce. Kai tsaye Katuwar rumfar da aka tanada dan ajiye , motoci ya nufa ya faka motar tsakanin motecin da su kai jerin gwano a cikin rumfar Dr. ya bude motar yana . kallon Saude ya ce,’ ‘Yau ga ki har gidansu YallaBan ki, da fatan kin yi farin ciki.” . Kallon shi kawai ta yi ta juya ta bude murfin motar ' ta fito, shi ma ya fito yana fadar “A’a ba ki yi farin cikin ba kenan? Lallai yarinya aiko zaki fadawa Momy Ya yi gaba ta bi bayansa Ma’aikatan gidan da ke ta faman aikace-aikacens u, , ‘ mai ban ruwa nayi mai aske fulawoyi suna ganinsu .suka nufo su suka zube suna kwasar gaisuwa, ita dai ' Saude ta gaza amsawa duk kunya ma ta ishe ta, yanda suke ta faman kiranta da Hajiya, a zuciyarta ta ce Allah Sarki ai duk mu ne dan ta san da sun san wacc ’ce ita da ba su gaishe ta ba. ' Suna wucewa Dr. ya dube ta ba walwala'a fuskarsa ya ce, ‘Duk wanda ya gaida ke ki rinKa amsawa, don za su dauka wulaqanci gare ki. ’ Ba ta ce masa komai ba ta ga sun nufl wata Katuwar kofa ya tura suka shiga cikin katafaren falon. Ne Babu kowa a cikin falon sai ‘yan aiki guda biyo suna ta faman goge-goge suna shigowa suka zube suna kwasar gaisuwa, Dr. ya nunawa Saude wurin zama * sannan ya nufl wata kofa, ‘yan aikin kuma suka fice suka bar Saude na ta faman zazzare namujiya a cikin falon. . Tsawon mintinan da suka kai goma , sannan ya tito hannun shi sarke dana wata magidanciyar mace dan ba za a kira ta da tsohuwa ba, saboda a qalla shekarunta ba zasu wuce arba’in da _ ‘yan kai ba. Tun kafin su qaraso Saude ta yi saurin‘ saukowa Kasa daga saman kujerar da take sama, matar ta wage baki har hakoranta suka bayyana wanda aka likawa hakorin Makka, ta ture Dr. wanda ke rabe da . kafadarta ta riqo Saude tana fadar. ‘ “ ‘Kai ni sakar ni ka ji tunda baka gaji'ya sannun ki da zuwa Saudatu zauna nan kinji Ta zauna tare da ita saman kujera, tana amsa gaisuwar da Saude ke mata cikin sarkewar murya Momy ta dubi Dr. tana fadar, ‘Kai sai ka cemin amaryar taka Bafullatana ce gaskiya nayi murna saki jikin ki Saudat mu gaisa ki dauke ni tamkar mahaifiyarki kinji ko?’ Kai kawai ta daga mata Momy ta yi murmushi cike da jin dadi tana fadar, ' ‘Allah Sarki je ka kira Dad dinka na san yana Bangarensa yana jiran ka Dr ya mike da zumudinsa ya fice. Yau dai Saude ta ga ikon Allah ta ga inda soyayyar da da mahaifa take yanda suka rinka nan nan da ita tamkar zasu goya ta don Dad din na zuwa Dr cewa ya yi sai an yi siyan baki * Kamar wasa dattijon yace ‘Au! Kace gaisuwa da neman iri ku ka zo.’ Dr, ya ce, “Eh Dad ba komai “dad yace To amaryar taka za ta je Saudiyya?" Dr yace eh “Za ta Dady ” ~ yace ‘To an biya, mata.” * Dr ya ce, ‘Ai bai isaba Dad wallahi inafa son ta da yawa " Dad ya ce, ‘To ka hau sama ka dauko mata makullin Motar da nayi niyyar yi mata takwuici.” ; musamman sbd ita nasa aka kawo motar daga london jiyannan kuma aka iso da ita maza jeka dauko mata makullin a sama Lol jama,a asha karatu lfy [1/28, 12:05 PM] I love my mum: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚 [12:17PM, 02/02/2017] 🙆🏼‍♂@lh@ji🙆🏼‍♂: [1/28, 12:10 PM] I love my mum: *YAR TALL* *CHAPTER 21* Dr yayi wani tsallen murna yana fadin kai thank u very much dad ya sumbaceshi kamar wani yaro momy tace “tunda dad dinka kadai ya siyi bakin don sai ta zage ta yi magana har sai mun ce ya isa haka. Dr. ya ce, ‘Wlh A a Saura ke Momy.” Dariya suka sa masa Momy ta ce ‘Ai kyauta ta tsakanina da ita ne babu mai ji bare ya gani.” ~ Dad ya ce, ‘Ai kuma bamu yarda da wannan wayon ba mu gani a qasa.” Momy ta ce, ‘Ai tsakanin ‘ya da uwa babu mai shiga don ni yanzu na bar maka wannan da baya girma yau na dawo nan. " Dad ya ce ‘Ba komai ai dama tare muke koya kaya kace my son?“ Dr. ya ce ‘Ai k0 dai Dad fada mata mu dai mu gani a qasa ; Hajiya ta ce, ‘Hummm! Kan ku ake ji "Ta janyo hannun Saude tana saka mata wani zobe tare da abun hannunsa, sannan ta bude sarkar ta sanya mata da kanta ta cire mayafinta tasa mata yan kunnanyen Masu shegen kyau. * Dr ya kaure da tafi‘ yana fadar ‘Kai Mamy gaskiya baki ya siyu." Dad ya ce, ‘Sai ku taso muje mu yi lunch Gaba daya ba musu duka suka mike hannun momy sarqe dana Saudat, Dad kuwa yana dafe da kafadar Dr suka nuf1 dinning area A tare suka ci suka sha ana ta barkwanci basu suka bar gidan ba sai bayan sallar Magariba. Zuwa Saudat. gidansu Dr. Ahmad yau ya Kara mata darasi a rayuwa iyayensa sun nuna mata qauna tamkar zasu goya ta abin daya karayar mata da zuciya wanda ya sa ta kuka mai cin zuciya ‘ Dr Ahmad da ke tuqi ya dago ya kalle ta kadan sai a lokacin ya lura da kukan da take ya maida kan shi saman. titi muryarshi a sanyaye ya ce, “Kukan me ki ke kuma?” Tamkar bazata tankamasaba, saidatayi dakyar ta iya tsayar da kukan nata kafin ta ce, ‘Dole ne inyi kuka Yallabai ta yanda kai , wa iyayenka qarya don kawai ka cimma wata manufa ta ‘ ka, ni dama na sani tun fakro ka tsane ni kana san ka ‘kore ni amma ka rasa hanyar da zaka bi kar Hajiya ta bata ranta, amma ni da ka bi ta ni ba sai kabi ta wannan hanyar ba ta nuna kana sona ba, don hanya ce ta tarwatsa rayuwata wallahi, idan daga nan ka sauke ni ba za ka qara ganina a gidanka ba har abadan ‘ abada" ‘ Ta qarasa maganar tare da qara rushewa da wani sabon kukan ‘ Dr ya taka birki tare da sauka daga saman Iitin ya . koma gefe ya_faka motar ya kunna fitilar dake cikin Motar ya jirkito yana kallonta gaba daya ya tattara duk _ wata nutsuwarsa a kanta, cikin sanyin muryarsa ya kira Sunanta. “Saude kenan wallahi tallahi tunda nake ban taba tunanin tarwatsa rayuwarki ba kullum fatana shine in ga rayuwarki ta inganta dubi idanuwana Saudat kalleni don Allah.’ Ya fada. tare da riKo hannunta wanda ya tilasta mata kallon nasa. Tayi saurin sauke idanuwanta saboda wani irin kwarjinin dayi mata ga alamun damuwa nan bayyane kwayar idanunsa Dr yaci gaba da fadin “Ki kalle ni sosai Saudat idan har kin san abin da ake nufi da. so to zuciyata na dauke da dumbin soyayyarki da qaunarki', kuma duk abin da ki ka ji ina fada da gaske nake a shirye nake da auren ki a kowane Yanayi.” Saude ta yi saurin dagowa a razane tana kallon shi, tsabar rudu da kadauwar da ta yi ya yi bala’in firgitar da ita, a nutse yake kallonta ba tare da ya sake magana ba cak kukan Saude ya tsaya ta soma magana tana kallon tsabar idanuwansa, cike da kaduwa ga muryar har ta soma: disashewa saboda kukan da ta yi cikin sarqakKiyar murya ta soma fadar. “Dan Allah don Annabi ka rufa mini asiri kar ka Sake furta wannan kalmar wadda za ta. zamo makamin rugujewar rayuwata wallahi ka fi qarfina ta kowace fuska, kai ba sa an aurena bane karkama klsake fada" don Allah don Annabi." Dr. ya lumshe idanuwansa ya harde a tsanakke ya soma magana ‘Ba kya sona kenan Saude Juyo ki kalle ni ki fada mini ba kya sona, fadi kawai Saude ta ji tamkar yana buga lugudan tashin hankali a zuciyarta ta runtse idanuwanta tana jin tamkar zuciyarta za ta yi bindiga. Dr. ya sassauta murya tamkar mai shirin‘fashewa da kuka ya ce ‘Saudat wallahi ina son ki, so kuma irin na gaskiya wanda babu wasa a cikinsa, kuma wallahi a shirye nake da na fuskanci kowace 'irin jarabawa ce a kanki, ki amince min don Allah inamai tabbar miki ba za ki yi nadamar damqa mini zuciyarki ba. ’ Shi yasa na fara kai ki wurin“ iyayena kafin in furta abin da ke zuciyata,‘ duk da ba su san wace ce ke ba, amma abun zai zo da sauki don gari na wayewa gobe zan mai da ke Katsina idan kuma kin amince na nemi auren ki ’ Cikin kuka Saude ta ce ‘Ta yaya zan mince in je fa rayuwata cikin matsala? Wace ce ni da zan iya kishi da matarka? ‘Yar wace ce ni a qasar nan da zan so miji kamar ka? Yallabai kafi karfina kai ba sa an aurena ba ne wallahi.’ Dr ya ce‘Ni ba wannan na tambayeki ba Saudat ' shi aure sa a da sa a ne? Wa ya fada miki? Ai shi aure cancanta ce kawai, Kuma da ki ke maganar kishi da Asma, wace ce ita, ta isa ta hana abin da Allah ya“ Qaddara. Saude nina ganki kuma nace ina so kuma mutum ko aljan bai isa ya. hana ni sonki ba har sai idan kece kika ce ba kya sona, kuma insha Allahu na san ba za ki fada ba, haka ne?” Ya yi maganar tare da matsar yatsun hannunta wadanda ke cikin hannunsa, Saude ta runtse idonta tana jin wani abu na yi mata kai komo a zuciya. To k0 shi ne son? Ta tambayi kanta. Dr. ya girgiza ta tare da fadar, ‘Bude idon ki Saudat ki kalli masoyin ki ki furta abin da ke ‘ zuciyarki, shin kina sona za ki aure ni?” Shiru ya ratsa wurin ta kasa cewa uffan. Dr. cikin sarkewar murya ya ce, ‘Don Allah ki yi magana ki ce wani abu, please Saudat. ” Kunya da nauyinsa suka dabaibaye ta ta samu ta duke da qyar kafin ta iya magana cikin wata likitacciyar murya ta ce, ‘To ka sake ni in fada.” ‘ Da sauri ya saki hannun nata yana fadar, ‘Na saki fadi." Saudat ta dan yi jim tana tunanin abin da zai iya Zuwa ya dawo anan gaba don haka cikin raunanniyar muryana ta soma magana. “Yallabai ni ba sonka ne ba na yi ba, asali ma kai abun alfahari ne ga duk macen da ta same ka ballantana makaskanciya mai tsananin rauni. YallaBai zuciyata ce cike, da fargabar abin da zai iya zuwa ya dawo, wallahi ina tsoron tashin hankali ban son abin da zai sanya rayuwa ta damuwa ko ya yake.’ Cikin farin ciki Dr. ya ce, ‘Haba Saudat ai matukar ina “ciki Kin gama zubar da hawayenki a kan damuwa, sai dai k0 hawayen soyayya wanda farin ciki ke sawa a ‘ zubar dasu saboda shauki irin na soyayya.’ Kuka da dariya suka kwacewa Saude Iokaci guda, ‘tasa tafin hannu ta rufe fuskarta, Dr. ya yi murmushi . tare da Juyawa ya yi wa motar key yasa mota hanya suka cigaba da tafiya » tare da waninsu ya sake magana ba. Horn din da ta ji yana wa maigadi shi ya tabbatar ~ mata sun iso Cinna hancin motar cikin gate din gidan ya yi daidai da bugawar zuciyar Sanue dif zuciyar ta ** tsaya da aiki a take. Ina ga k0 Asma ce za ta fito, Saude ta ji muryar Dr na fada wanda ba ta ma fahimtar me yake fada ba saboda tsabar rudu da kaduwa da take ciki. Saude ta runtse idanuwanta ganin Asma ta nufo motar tasu, Dr ya ji tamkar ya juya sai dai babu dama don kuwa tuni masu gadi sun riga sun rufe gate kuma k0 kafin su sake budewa ya tabbatar ta iso. . Don haka ya yi dabarar bude motar ba tare da ya gyara fakin ba ya fito yasa key ya kulle motar ya nufe ta tun kafin ta Karaso yana fadar “Saukar yaushe My dear.” ,, Turus ya ja ya tsaya saboda k0 kallon shi ba ta yiba ta wuce shi ta nufi wurin motar, gaban Dr ya yi wata masifaffiyar faduwa ba wai don yana tsoron Asma ba, a a saboda Saudat don ya lura ta yi matukar ’ 'firgita da ganin Asmar matuqa don haka Jikinsa a ‘ sanyaye yabi bayan ta Tana qarasawa gaban motar ta ja ta tsaya ta miqawa Dr. hannu, ‘Bani key da motar." Ta fada cike da gadara. Dr. ya ja ya tsaya a gabanta cikin nuna halin ko’in kula ya ce, ‘Ba zan bayar ba kina da ajiya a ciki ne?” Cike da mamaki Asma ke kallonsa kafin ta iya bude baki ta ce, ‘ba zaka bayar ba ni ka ke fadawa haka Ahmad? Hmmm! Da kyau ba zan yi mamaki ba tunda ka dauki ‘yar iska kun flta kun gama yawan iskancinku kun dawo ai dole za ka sawa mota key tunda Allah ya toni asirinku. . Amma ka sani daga rana irin ta yau ka gama marmarin fita da kowace. karuwa don sai na sa ka yi nadamar da baza ta taBa qarewa ba wallahi, dan ba irin Asma ake wa irin wannan tozarcin da wulakantar ' ba a cikin gidanta, mayaudari, munafuki kawai.’ Tana maganar tana kwance dankwalin kanta. Ta hau daura damara a qugunta tamkar mai shirin shiga filin dambe ta durkusa ta kwashi duwarwatsun da aka baza a harabar gidan ta hau jefa su a gilas din motar tana fadar. “Wallahi yau sai dai k0 ni ko ke a gidan nan ‘yar iska wallahi sai na yi ajalin ki, karuwar banza." Dr. da ke tsaye ya yi saurin rike ta yana fadar, ‘Wai me ye haka Asma kina da hankali kuwa ki ke abu kamar ba. educated ba, wannan ai hauka ne ki ke da RaShin hankali a gaban mutanen da suke a qarkashin ki wannan ai kanki kike jawa abin fadi a duniya.’ Asma ta kwace daga riwon da ya yi mata tana haki ta ce ‘Kai da alla ni rufe min ba ki kai har wani mutunci ne ka 'sani bacin wanda ka zubarwa kanka a bainar jama’a, ai idan akwai wani sakarai marar hankali to bayan ka yake, mutumin da ya maida ‘yan aikin gidansa abokan cin garinsa, ai sai yanzu na fahimci abin da ke korar duk ‘yan aikin da na kawo maka, kuma wallahi ba zan taBa rufa maka asiri bu sai duniya ta san abin da ka aikata, kuma yarinyar nan yau sai na halaka ta. Bai ankara ba ta rarumi wata qatuwar adda wadda ake aske fulawowi da ita, ta sauke madubin motar, wanda ya yi daidai ta fasa qara Saude wadda ke zaune a gaban motar. Dr. ya yi saurin rike Asma yana fadar, ‘Wai ke wace inn mahaukaciya ce wallahi za ki jawa kan ki aikin dana sani, dan na rantse da Allah idan ki ka kashe yarinyar mutane wallahi sai na yi shari’a da ke Da sauri ta kalle shi bakinta a sake cikin sarkewar murya take fadar, ‘Za kai shari’a da ni Ahmad akan karuwar? Lallai kam da na nuna maka kai Karamin dan bariki ne. To bari in kashe ta sai kai qarar tawa." Dr. ya qara rike ta gam kafin ya ce “Asma ya kamata ki shiga hankalin kifa dan kin sani sarai ba zan lamunci wannan haukan naki ba, don ban ga abin da a kai ba, wanda zai sanya ki wannan jakancin ba idan mun fita da Saudat sai me ‘yar aikina ce ina da Right din fita da ita mu yi siyayyar abin da ake buqata. dan me za ki nemi tarwatsa mini tunani haka kawai?" Asma ta girgiza kai, ‘Lallai Ahmad ka cika dan akuya yanzu a kan karuwar ne ka ke kirana da jaka, lallai kam ana yi, kun tafi siyayya ne shi yasa ku ka . tafi ku biyu babu k0 da direba, kuma ta zauna a gaban ° mota. Kai gaskiya ne ai na ga hakan, amma sai dai abin daka manta k0 ranar da ka fara ganina a duniya da hakorana talatin ka gan ni cur, ballantana ka maida ni . Karamar yarinya, wadda ba ta san abin da take ba. Kuma wallahi tallahi na rantse maka da Allah sai na yi ajalin ‘yar iskar yarinyar nan jaka sakarya daqikiya ballagaza wadda iyayenta suka sadaukar da ita saboda abun duniya, wallahi daga yau ta gama karuwanci da kowa.” Dr. ya cc, ‘Hmmm! Asma kenan kina ba ni mamaki yanzu har iyayenta sun miki laifi dan sun Sadaukar da ‘yarsu ta zo ta yi miki abin da ki ka gaza Min a rayuwar auren ki ashe har sun miki laifi?" ldanuwanta a warwaje ta soma fadin, ‘Ban gane ba? Dama na dauke ta aiki ne don ta maye gurbina?” Cikin rashin damuwa ya ce “Yes k0 kin dauka ‘abinci shi ne kawai matsalata ni ba mutum bane? Dole kwai wani abun da nake buqata bayan wannan, dole ‘ lna buqatar kulawa ta mace, sai dai bata gurbatacciyar hanya wadda take haramun ba, don sanin kanki ne ni Ba mazinaci ba ne shi ya‘sa na yanke hukuncin auran Saudat don na ji dadin maye gaba dayan gurbin ' naki wanda sabgogin yau da kallum suka saki ka "watsar.” Cikin tsananin firgita da razana Asma ta kwace daga rikon da ya yi mata tana fadar, ‘Kutumar ubannan Kai karya ka ke wallahi tallahi karya ka ke Ahmad ba ka isa ba na rantse maka da Allah babu ‘yar matsiyatan da ta isa ta shigo cikin gidan nan batare da na nuna mata bakin rijiya ba wajen wasan makaho ba ne.’ Dr. Ahmad ya ce Ai ko sai dai kada a Kara; domin zuciyar Ahmad ta riga ta yi nisan da mai rai ba zai gane iya adadin gudunta ba, kuma ina mai tabbatar miki k0 da malaman da ke Barno da Nijar. malamanki ne ba ki isa ki hana wannan lamarin ba. Da fatan kin gane Asma ta hau ja da baya da baya tana fadar ‘Ni. .ni Ahmad wallahi qaryarka ta sha karya wallahi ba ka isa , ba Ta durkusa tana kokarin daukar addar daya yar a ‘ ‘qasa, wadda ya kwace daga hannunta. ‘ Dr ya kalle ta yana fadar, ‘Wallahi idan ki ka matsa kusa da motar can a bakin auren ki ’ Yaja wani dogon tsaki ya juya ya yi gaba ya bar ta ' ta fasa wani gunjin kuka ta durkushe a gun Dr ya fada motarsa sai dai ganin halin da Saude ,ke ciki ya daga masa hankali kuma ya ga madifar" dauriyarta don gilas din motar da ya fashe sai da ya yanki goshinta, jini ya zuba sosai duk ya bata mata fuska, hankalin sa ya tashi ya tayar da‘ motar ya fice daga gidan ba tare daya sake kallon inda asma take ba, ya nufi asibiti da ita. Suna zuwa kuwa aka karbe ta akai mata dresin din ciwon aka rubuta mata magunguna, sannan suka baro asibitin. A cikinsu babu mai magana kowa da abin da yake sakawa a zuciyarsa. Can Dr. ya dan waigo ya kalli Saudat sannan ya maida kallonsa a kan titi cikin sanyayyar muryarsa ya ce. “Don Allah don Annabi ki yi haquri Saudat kada dan wannan abun ya daga miki hankali k0 kadan, ni daina ce ina son ki kuma ni zan zauna da ke ba Asma ba. To insha Allahu na yi miki alqawarin farin ciki da jin dadin rayuwa a duk inda suke zan nemo miki su, fatana ki’ rayu cikin farin ciki da walwala, kar ma abin datayi dinnnan yadameki kinji?" ‘ Kai kawai ta daga masa alamar eh, amma qasan zuciyarta cike yake da tsabar rudani da tsoro. Dr. ya ~ tsaya ‘Gidan Abinci’ ya yi take away sannan ya dawo suka wuce. Kai tsaye daki ya kama a wani hadaddan hotel mai tsadar gaske kwana daya, ya ba ta makullin dakin mai lamba 12, sannan ya ajiye mata ledar take away din ya gwargwada mata komai a cikin dakin Wanda yake da qaton falo da bedroom sai bandaki da dan wurin hutawa. Sannan ya dube ta a nutse, “Dafatan dai babu wata matsala?” Saude da kc tsaye tana kallon shi ta sunkuyar dakai qasa muryarta a sanyaye ta ce, “Babu.” Dr. ya ce ‘Okey zan wuce mu jeki rufe dakin ki tabbatar kin kulle sosai sai Zuwa da safe,,insha Allahu zan dawo sai mu wuce Katsinan a tare kin ji ko?” " , Saude ta dago da idanuwanta wadanda suka ciko da kwalla ta daga masa kai, Dr. ya dan tsura mata idanuwa jikinsa a sanyaye ya ce ‘Saudat hawaye nake gani a idanuaki me ye kuma?” Saude ta sadda idanuwanta tana wasa da yatsun hannunta ba tare da ta ce uffan ba Dr Ahmad ya Kara matsowa daf da ita cikin sanyayyar muryar shi ya kira sunanta “Saudat me yasa ki ke san tayar min da hankali ne? 'Me yasa ba kya son ganin nutsuwa ta? Kinfi son ki ganni a firgice ne, iye Saudat?” Kai kawai ta girgiza masa ba tare da ta kalle shi ba Ya ce, ‘To meye? Ba kya san in tafl ne in zauna tare . da ke. " Da sauri ta daga masa kai don kuwa abin dake zuciyarta kenan, don gani take tamkar idan ya tafi ba zata sake ganinsa ba. Ya yi murmushi wanda ya bayyanar da haqoransa kana ya ce “Ki sha kurumin ki My dear insha Allahu babu abindazai faru kedai kiyanida addua kawai kinji?” . ‘ A hankali ta daga masa kai ya ce ‘Yauwa ko ke fa, ‘ kikwanta ki hutakinji, kiyibarci mai dadi saida safe. ”Ya ja mata hanci yana dariya sannan ya fice. Saude t maida qofar ta rufe ta koma ta jingina da ; kyauren idanuwanta a lumshe zuciyarta na bijiro mata ’ d wata irin matsananciyar soyayyar Dr. Ahmad wanda take jin a yanzu tamkar ta bishi ta zauna a tare da shi, farin cikinta da fargabarta ba zasu musaltu ba. Farin cikinta dai shi ne ta samu namiji daya tamkar da goma ajin duk wata isasshiyar mace. Fargabarta kuwa itace. Shin kuwa zai iya auren ta don ita ta san ya riga yafi qarfinta ta kowace fuska, to idan ma ya ' aureta ta ya za ta yi da matarsa Asma, don yau ta ga. bala,in da: take fada mata. A hankali ta ja Kafafuwanta ta nufi bedroom din; kai tsaye bandaki ta nufa ta dauro alwala ta fito ta yi sallar isha,i sannan ta tashi ta haye saman“ madaidaicin gadon da ya sha shimflda ta alfarma ta zauna ta jawo take away din da ya ajiye mata ta bude ta ci abin da za ta iya ci saunan ta kwanta, ba dan tana jin barci ba sai dan ta samarwa gangar jikinta hutu Tunda {a kwanta ba ita ta farka ba sai Karfe shida saura ‘yan mintina, ita kanta ta yi mamakin tsawon lokacin data dauka tana barcin, don haka ta mike ta nufi bandaki ta dauro alwala ta fito ta yi sallah, sannan ta zauna tana lazimi tsawon lokaci sai da ta gaji don kan ta ta mike ta koma ta kwanta zuciyarta ta lula duniyar tunanin gida da irin abin da za ta iya fuskanta a can din. Rayuwarta ta baya a gidan ta dawo mata tare da tunanin masoyinta Hamid, har yau har gobe tana jin son shi a zuciyarta,“saboda shi ne mutum na farko da ta Tara so a rayuwarta kuma shi ne mutum na farko da ya fara burin taimaka mata Kwankwasa kofar da ake ne ya sa ta saurin tashi ta taje ta bude qofar, Dr. ya shigo yana sanyé da shigar wani sabon yadi milk colour, mai laushin gaske an yi masa aikin hannu a jikin rigar Yana .sanye da hula sai takalminsa na fata 'idonsa na sanye da siririn farin gilas, gaba daya kamshin turarensa ya mamaye falon. Saude ta durkusa tana gaishe shi cike" da girmamawa, Dr. ya amsa yana fadar, ‘Daga yin knock sai ki bade kofa ba tare da kin tambayi k0 waye ba baki san nan batel bane? Komai na iya faruwa fa.” Muryarta a sanyayé ta ce, ‘Ai na san kai ne Dr. ya ce ya a kai ki ka sani? Ta dan yi jim kafin tace ai ka ce min zaka zo da safe. Ya dan yi wani murmushi kafin ya ce ashe ba ki da mantuwa kinsan in bayan dana manta ban nuna miki yanda za ki yi kisa a kawo miki break ba da ba zan zo nan ba sai wurin sha biyu da wani abu Ya ja ya zauna tare da tura mata katuwar jakar da ke hannunsa ya ce duba ki ga kayan nan idan sun miki saikisa yanzu sai mu tafi.’ Saude ta zauna saman * kafet tare da janyo ledar gabanta ta shiga bubbudewa a ~ sanyaye ’ Dogon wando ne baki irin mai kama qafafuwan nan an masa adon pink color sai rigarsa » Shima ma pink mai adon baki, rigar mai yankakke wanda ake kira da v neck Rigar mai dongon harnu ce,,,sai wata duguwar riga har qasa itama pink cclour ita ma mai dogon hannu, tana da yankakken gaba sai siririn mayafinta. ~ Ta ajiye kayan ta janyo wani qaton kwali ta bude” takalmi ne a ciki baki da ‘yar qaramar pose irin wadda ake makalawa a hannu, ‘yar qarama, sannan ta Ciro wata ‘yar jaka, saitin kayan shafawa ne a ciki hade da sabulu da turare kayan sun bala’in Burge ta har cikin ranta, shi kan shi ya fahimci hakan ‘ a idanuwanta, don haka muryar shi a sanyaye ya ce. “Sun yi kyau k0?” Murmushi kawai ta yi ba tare da ta tanka ha, ya *mike tareda fadar kije ki shirya dame zakikarya ? Me za,a kawo miki?” Saude ta sunkuyar da kanta tare da fadar, ‘Komai aka kawo min." Cikin zolaya ya ce, ‘Ba dai komai ba k0 zaki ci shinkafa da miyar kwadi?” Da sauri ta kalle shi ido waje, ya yi wani siririn murmushi kafin ya ce ‘Ye’s nan ba abin da ba sa dafawa har miyar dodon kodi.’ Saude ta Bata fuska tamkar zatayi amai tace ‘Nidai a,a ‘ Ya yi wata dariya irin wadda ba ta taba sanin ya iya ta ba da alama yanda ta yi maganar cikin shagwaba ya. yi masifar barge sa tare da daukar _ hankalinsa, ya matso daf da ita yana kallonta da ya ce, ‘Dan qara‘ maimaitawa mu ji please. ’ Kunya ta kama ta ta juya da sauri ta yi ciki ta bar shi nan tsaye harde da hannu a qirji yana kallonta har ta bacewa ganinsa, ya yi wani murmushi tare da ‘lumshc idanuwansa ’ Saude na shiga bedroom din ta fada saman gadon dakin ta rungume filo cike da murna haka kawai ta ji wani irin farin, ciki ya baibaye ta, ta lumshe idanuwanta tana mai son tuno wani abu can ‘ kamar wadda aka tsikara ta zabura ta mike da gudugudunta ta fada bandaki ta watso ruwa a gurguje ta ‘dauro alwala ta fito ta yi nafila raka’a biyu tare da roKon Ubangiji ya kare ta daga sharrin Inna Laure, don tanaji ajikinta wannan karon idan akahanata auren Dr. mutuwa kaWai za ta yi. Tana gama addu’ o ’inta ta mike ta janyo ‘yar jakar kayan shafawar ta fito da su ta mutsa mai lotion a jikinta, sannan ta shafa hoda ta sa abun ‘ gyaran gira ta gyara girarta, har ta soma sai da ta sa . maskara ta gyara ta, sannan tasa brown eye a girarta ta bi bakinta da sassaiikan jan baki pink colour; sai ka rantse da Allah kalar lebanta ne haka. Saude ta mike ta janyo kayan ta saka dogon § ' wandon: wanda ya kama ta tsam-tsam sannan ta ”’ kawo rigar ta sanya, wadda ta bi illahirin jikinta ta ta lafe, Saunan ta kawo dogUwar rigar ta dora ta * Warwaré gashin kanta ta Kara daure shi sosai, ta yi masa tamkar gamma a baya, ya zama tuntu sannan ta » ‘ kawo gyalen rigar ta yi kamar rawani da shi. Ta Ciro takalmin mai tsini ta saka, ta dauko pose din ta saka sarkar da mahaifiyar Dr. ta ba ta a ciki saboda rigar ba a hada ta da sarka sai dai ta bar dan kunnen a kunnenta tare da abin hannu da zobe Ta dauki turaren ta faffesa ko’ina na jikinta, saunan ta tsaya gaban madubi tana qararewa kanta kalla, Barakallahu! Masha Allahu ni dai abin da zan ‘ iya cewa kenan don a gaskiya na san Saude ta hadu qarshe, ita kanta ba ta san tana da wannan kyan haka ba Masha Allah. Ta fito daga dakin cikin nutsuwarta, Dr Ahmad dake zaune saman kujera yasa kayan abincin a gabansa bai san lokacin da. ya mike ba yana kallonta, hatta qaraso gabansa ta durkusa a gabansa. “Sannu da hutawa YallaBai." Dr‘ Ahmad ya koma ya zauna jiki a sanyaye sannan ya amsa da yauwa sannu Saudat, kin sha kyau wallahi irin wannan haduwa haka. Murmushi kawai ta yi, Dr ya dake dan karya bada: kansa yace Bismillah maza ki karya mu tafi tana murmushi ta janyo tiren kayan abincin ta bude tea flask, ne sai kayan hadinsa, . *. sannan soyayyan kwai da agada, sai wani kwanon tangarab shi; kuma farfesun zallar tsokar kaza ne ' Saude ta dauki kofi ’guda biyu ta hada masu ruwan tea din sannan, ta miqa masa DR : ya tsaya yana kallonta kafin ya ce ‘Waya fada miki ban 'karya ba?", ‘ Murmushi kawai ta yi tare da qara mika masa kofi din, yasa hannu ya karBa ya hada da kofin da hannunta ya riKe yana Kokarin ya hada ido da ita, yana muryarshi a sanyaye ya ce Thank you. ” Saude ta zame hannunta ji take tamkar ta zabga da gudu, ta. yi ta maza ta dake ta dauki kofin din tea din ta soma tsotsa tamkar wadda babu makoshi a bakinta. Duk abin da take Dr yana kallonta bai ce mata Kala ba, ta yi ta tsatsar abincin, sai da ta gama sannan ya mike ya dauki makullin motarsa ya dube ta‘Muje ko?’ Da to kawai ta amsa ya yi gaba sannan ta bi shi a baya, ya tsaya ya yi ‘yan abin da zai yi cikin hotel din sannan ya fito suka shiga mota suka dauki hanya kowa da abinda yake saqawa a zuciyarsa. Dr. ya miqe. hannu ya kunna masu karatun Alkur‘ani mai ginna. Don haka Saude ta koma jikin makarin kujerar ta" ‘ kwanta ta. lumshe idanuwanta tana sauraron karatun,‘ zuciyarta kuwa ta harba zuwa gida, fargaba mai~ tsanani ta shige ta tana tsoron makircin Inna Laure ‘ tana tsoron abin da zai iya zuwa. ya dawo. = hanya. Babu mai magana a cikinsu kowa da abin da“ A haka barci barawo ya sace ta, ba ita ta farka ba sai da ta ji yana tayar da ita an kusa zuwa Welcom to Katsma, saude ta yi firgigit ta bude idanuwanta wanda hakan ya yi daidai da bugawar zuciyarta. Innalillalhi’ ta yi saurin fada da qarfinta. Dr ya yi saurin kallonta da hanzarinsa yana , fad'ar lafiya? Ta’ dan ja numfashi kafin ta ce, ‘Wallahi ji na yi gabana ya yanke ya fadi, Dr. ya' juyo ya dan kalle ta kafin ya maida kallonsa kan titi ya ce, ‘Ki rinka maimaita innalillahi wa inna ilaihirrajiun . insha Allahu ko ma me ye zai zo miki da sauki.’ Saude ta amsa da to, sannan ta nuna masa kwanar unguwarsu kafin a qarasa welcome to Katsina, haka ta rinka nuna masa hanya har suka iso kofa: gidan nasu, gaban Saude ya Kara wata muguwar bugawa .. ganin manyan rumfuna a kakkafe a kofar gidan da ' ‘yan tsirarun mutane a ciki. Saude ta dafe kirji, ‘Wayyo Allah na k0 dai Baba ne ya rasu?” Dr ya yi saurin kallon Kofar gidan kafin ya ce "A a ba mutuwa ba ce, dan ga hunhun goro can a gefe’ « Saude ta sauke wata ajiyar zuciya kafin ta ce, ‘Ina Jin ko‘ yar Baba aka daurawa aure yau.’ * " Dr; ya lumshe idanuwansa ya bude a hankali kafin ya ce, ‘Watakila, ki shiga ki gani sai‘ki min sallama da Baban. Saude ta amsa da to tare da bude murfin motar ta fice. Tun kafin ta fito dama hankalin mutanen dake zazzaune ya dawo kan hadaddiyar motar ta Dr wadda ta dauke illahirin hankaiinsu, duk da ba za ka ; iya ganin wanda ke ciki ba saboda bakin gilas din da ‘ke gare ta Saude na fitowa daga motar kallo ya koma kanta, sai ka ce ba mutum ‘yar uwarsu ba, mutanen dake zazzaune a rumfar ba za su wuce goma ba tun daga nesa ta dan gane mutum uku mahaifinta neda ‘ kuma qannansa guda biyu, sauran kuwa ba ta san k0 su waye ba * . Saude ta qaraso ta durqusa har kasa ta gaishe ' su, tamkar za su kwanta mata suke amsawa, saboda ’ tsabar girmamawa; amma ban da mahaifinta wanda ya Kara kafe ta da idanuwansa muryarsa a sanyaye yace, “Wace ce wannan kamar Saude?” Saude ta ce, ‘Ni ce Baba.” innalillahi ’Yanzu Saude ke ce ki ka koma haka? Ina Dillaliyar da suka tafl _ ; dauko ki dazu?” . Gaban Saude ya fadi cikin sanyin jikinta ta ce, = “Ai kobasu kai ga zuwa ba, Allah yasa dai lafiya?“ Malam Bala ya ce, ‘Yanzu dai tashi ki shiga Ciki u ’ Kawu Isiya ya ce ‘Wai wace Saudan ce ka ke fada ban fa game ba?” Malam Bala ya ce, ‘Saude dai wadda aka tura a dauko a can Habuja amarya ita.” ‘ Kawu Hamisu ya ce, ‘To wancan mai motar fa da ya kawo ta?” Ba ta saurari abin da ya ce masu ba ta yi cikin gidan abin ta da sallamarta, mutane ne ke ta kujibakujibarsu an cika tsakar gidan nasu‘makil da mata, an girke manyan tukwane da murahu Sai faman tuKin ' tuwo da sanwar miyé ake, kana gani k0 ba a fada maka ba ka san hidima ake. Sude ta gaishe su sannan ta wuce dakin Inna Laure wanda shi ma yake ciké da jama’a, duk gungun matan ~ da Saude ta gani kafin ta gaishe su su sun gaishe ta, ana fadar sannu da zuwa Hajiya, ba ta damu ba don a‘ lokacin burinta kawai ta ji hidimar me aka a gidan nasu. ' ' Ta "samu ta kutsa dakin Laure ta gaishe da jama’ar sannah ta wuce har bakin’ gadonta inda take zaune ita ~ da ‘Yar Baba an ‘sha ankon shadda an kashe dauri sai faman zufa ake. ‘ Saude "ta~ qaraso har bakin gadon inda Inna Laure inna laure ce ta fara fadar ‘Sannu da zuwa Hajiya kar dai ince. harda ke aka taho kun ji Saqon bazata haka, sai aka ce muku an daurawa yarinya aure yau din nan.’ . ,Saude ta . durkushe a bakin gadon muryarta a sanyaye ta soma fadar, ‘Bikin wa ake Inna Laure?" ‘ . Gaban Laure ya yi wata masifaffiyar faduwa ’wanda ya ja mata wata muguwar zabura daga ita har ‘ ‘Yar Baban. Inna Laure ta mike tsaye tana gyara daurin zani tana fadar. “Me nake gani haka me zan gani Saude ke ce ki ka koma tsohuwar karuwa haka? Innalillahi wa’inna ‘ ilaihir raji’nn! Jama’a ku taya ni figa yan uwar kishiya ta zama zakara. Saude mu za ki zubarwa da mutunci a gari mu za ki jawa abun kunya abun fada, wayyo ni . ' Allah naga ta kaina ‘ .Sai ta fashe da kuka ta fadi qasa. Sumammiya jama,a sukayo kanta suna fadin a taimko da ruwa laure tayi dogon suma ‘Yar Baba ta kalli Saude sama da qasa ta watsar ta ja wani uban tsaki tana fadar, ‘Aikin banza ai . dai dadin abun da ba a san. asalin balbela ba da sai ta ce daga Masar take, kuma duk rigar qadangare bai isa ya zama kada ba a Kadangaren nan dai na shi zai zauna. . Idan kina jin dadi ne kin tafi birni kin goge to babu , abin da gogewar ta ki zata ‘ta Kare domin yau dinnan za a wuce gidan Garba Gurgu don tuni an daura auren, ‘ ki da shi a safiyar yau kuma wallahi tallahi wani abu ‘ idan ya samu mahaiflyata sai na dauki fansa a kanki munafuka kawai.’ . ‘ Tunda ‘Yar Baba ta furta daurin auren nata Saude ta sulale qasa tana wani gunji mai kama da gurnan,ji take numfashinta na wani sam -samA kamar zai dauke. Ta rushe' da wani irin kuka mai daga hakali, ta zabura ta yo waje a guje tamkar marar hankli ta tsallake mutanen da ke waje da gudunta tana jin mahaifinta na kwala mata kira, amma ba ta tsaya ba Dr Ahmad wanda ya gaji da zaman motar ya fito ya jiggina da motar yana latselatsen wayarsa ya ganta Ta fallo a; guje hankalinsa ya yi masifar tashi ya nufe ta yana qokarin rike ta, ta durkushe a gabansa tana wani irin gunji kuka ya rikice cikin tsananin rudani' ya riko ta yana fadar, “Me ya faru ne Saudat? Waye ya rasu ne, ki fada min?’ Sande ta. Qara rushewa da wani kukan ba tare da ta saurara ba‘ ta shiga qakarin fadar, ‘Na mutu.. na mutu... na lalace... YallaBai.., an daura min aure yau..’ ‘innalillahi wa ’inna ilaihirrajiun Abin da Dr. Ahmad ya iya fada kenan tare da juyawa ya kifa kansa saman motar. « ALHAMDULILLAHI Wohoho jama nasan da yawanku kunyi missing din laure to mun dawo qauye ya abin zai kasancene da DR AHMAD wai INA YAYAN SAUDE SHINE MASOYIN SAUDE HAMID FUSHI YAYI YA HAQURA DA ITA KO YAYA SHIN WA ME ZAI FARUNE IDAN SU DILLALIYA DA ASMA AKA HADU YA AUREN SAUDE DA GARBA GURGU ZAI KASANCE wadannan amsoshin tambayoyin naku na cikin YAR TALLA BOOK3 WANDA ZAMU FARA GOBE AMMAN IDAN NAGA COMMENT SOSAI NAKU HAR KULLUM ADMIN DBOY👍🏻☝🏻 [1/28, 12:10 PM] I love my mum: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚 [12:17PM, 02/02/2017] 🙆🏼‍♂@lh@ji🙆🏼‍♂: [1/30, 10:24 AM] A A Dboy: *YAR TALLA* BOOK 3 *CHAPTER 22* Saude ta sulale qasa tana wani gunji mai kama da. gurnani ji ta ke numfashinta na sama‘sama kamar zai dauke, ta rushe da Wani irin kuka mai daga hankali, ta zabura ta yo waje tamkar marar hankali ta tSallake mutanen dake waje da gudunta. Tana jin mahaifinta na Kwalla mara kira, amma ba ta tsaya ba Dr wanda ya gaji da zama a motar ya fito ya jingina da motar yana lallatsa wayarsa ya ganta ta fito a guje,hankalinsa ya yi ‘ masifar tashi ya nufe ta yana KoKarin rike ta, ta durkushe a gabansa tana wani irin gunjin kuka. Dr ya rikice cikin tsananin rudani ya rike ta yana fadar, “Me ya faru ne Saudat? Waye ya rasu ne? ki fada min." Saude ta Kara rushewa da wani kukan ba ‘ tare data :saurara ba ta shiga qokarin fadar, “Na mutu... .“mutu , na lalace. yallaBai * an d‘aura min aure da Garba . “Innalillahi wa" inna ilaihi raji ’"un Abin‘ da Dr Ahmad ya iya fada kenan tare da juyawa ya kifa kansa saman motar gabad'aya ya ma rasa a wace duniya yake Malam bala ya qaraso da hazarinsa yana fadar keko wannan diya allah ya wadaran halinki yanxu sbd dibar albarka shine zaki kwaso a guje kina ihu kamar wata tabin iska shin ba,a gaya miki yanxu muryarki al,aura baceba iyee? Sauce najin abinda ya fada ta sake rushewa da kuka tana fadar wayyo allah na shiga uku na lalace malam bala ya dauki sallallami kafin yace anya saude da hakalinki kuwa yanxu budewar idon taki taki har takai kiyo waje kina kururuwa? To maza tashi ki shiga ciki mutuniyar banza mara mutunci zaki tashi ki wuce ko saina jefeki Saude ta tashi da sauri ganin yana niyyar jefeta da wani hogen daya rarumo ta fada cikin gida tana kuka sai a lokacin Dr ya dago idanuwansa da suka kada sukai jajir cikin dasashshiyar murya yace kayi haquri baba don allah inason magana dakai Malam bala yace Ohoo daman kaine mai hure mata kunnen? , . Dr. ya girgiza masa .kai, yana jin zuciyarsa tamkar zata ballo ta fito ya ce,‘ “K0 daya ni dai ne wanda ta ke aiki a ' gidana, inda aka kai ta aiki" Malam Bala ya ce “Auho, to bismillsh mu shiga daga soro ai ban fahinta ba, mu shiga in kira maka innar tasu ku gaisa'Ba musu Dr. ya bi shi~suka shiga cikin soron gidan, sannan Malam Bala ya shiga cikin gidan ya sa Inna Lami qanwarsa uwa, daya uba daya ya ce ta kira masa Laure ta taho kuma da tabarma Yana tsaye ta shiga ta fito masa da tabarma tare da fadar, “Lauren tana zuwa" ‘ ’ Malam Bala ya, juya ya dawo ya ‘ shimfida masa tabarma suka zauna, Dr, ya dubi Malam Bala suka gaisa sosai cikin girmamawa Sannan Dr ya qara gabatar da kansa Baba nine wanda Saude ke aiki a gidana, na maido ta. ne saboda wani muhimmin abu wanda maganar aurenta da ta sanar ds ni a «yanzu ya tarwatsa komai amma Baba kayi haquri da abin da zan fada maka a yanzu kai _ masa kyakkyawan kalla da kuma, kyakkyawar ” . fahimta Baba kai ka haifi Saudat ka fi kowa sonta, kafi kowa sanin ciwonta, kuma amana ce a gare ku abin tambaya a gobe kiyama idan ku ka cutar da ita ku ka wofintar da rayuwarta wallahi sai Allah ya kama ku a kan hakan duk dakuwa kukukahaife ta. ' Baba, Saudat tana da masu sonta da aure a nan garin, da kuma ni kaina, sannan Saudat yarinya ce qarama Baba bai kamata ku_ tankWare rayuwarta ku zaba mata mijin da bai cancanta da ita ba don kawai saboda, wani dalili naku ka yi haquri Baba na san kuna da hakkin zaba mata mijin da ya yi muku, amma Baba’ zaba " mata mijin da ya‘ dace da rayuwarta don Allah don Annabi Baba ka dubu girman Allah ka yi wa rayuwar yarinyar nan adalci ' Tunda Malam Bala ya sadda kansa bai dago ba, komai yake tunani oho! Inna Lame ‘ wadda take labe a tsaye hannunta dafe da kofa . tana sauraren duk bayanan Dr. tace, “To muna godiya Alaramma, Allah ya biya. Sai a tashi a tafi umma ta gaida assha, kuma abin da . :ka yiwa "yarmu Allah ya sa ayi wa taka, mun . kai diya aiki ka hure mata kunne ka lalatata ka maida mana, ka iske kuma za a yi mata aure kana Kokarin hanawa kai shaida, saboda dandin bai iske ka ba? To ta fada mana komai, kuma ba abin da za muce maka sai mu ce ka je Allah Ubangiji ya yi mana sakayya". Dr Ahmad wanda ya ji maganganun tamkar: saukar markade, ya dago da sauri yana kallonta cike da mamakin maganganunta ya Kasa cewa komai, su Malam Bala ne ya Daga kai yana fad'a, “Ya Isa haka Laure, koma cikin gida don Allah” Inna Laure ta ce, “Ka bar ni da wannan‘ babbab shaidanin mai munafurcin kashe aure ya maida mana diya karuwa, kuma saboda rashin imani ya biyo ta har gida ya ce kar a yi mata aure‘ tunda bai gaji da lalatar ba. Malam ka kalli Saude sosai na rantse maka da Allah cikine daita”. ldanuwan Malam suka yo warwaje * saboda tsabar dukan da maganar tata tai masa a Kirjinsa. Cikin rudu ya mike yana fadar“Laure ki shiga gida haka wuce ki tafi” Ganin maganganun nata sun yi tasiri a zuciyar Malam yasa ta juya tana matsar kwalla a munafurce ta gefe tana kallonsa “ Malam ya dubi Dr. Ahmad zuciyarsa na huci yace “Malam mun gode kwarai amma don Allah ina rokonka ka tashi ka tafi don Allah”. . Dr ya danne mamakin da ya cika masa zuciya, cikin qarfin hali ya bude baki da niyyar yin magana. Malam ya daga masa hannu cikin tsananin fushi ya ce. “Babu abin da za ka fada don Allah don Annabi ka tashi ka fita ko na samu zuciyata ta sassauta”. ‘ Dr. ya mike tsaye cikin halin jarumtaka, don gabadaya zuciyarsa' rugurguza ‘ta ,ke tamkar za ta Balle Kirjinsa ta fito fili. Ya danne abin da ke yunkuro masa kafin ya iya Karfin halin fadar “Ka yi hakuri Baba, wallahi tallahi na rantse maka da Allah ban aikata abin da kuke zargina da aikatawa,ba kuma na amince zan tafi amma don Allah ka bani minti biyu in magana da Saudat a gabanka Malam ya zabum masa “Kai Malam ka ga ka bar nan tun muna shaida juna, don wallahi Saude ba za ta sake fitowa ba sai idan za,a tafi da ita dakinta, ka ji na gaya maka". Dr Ahmad yaji tamkar anwatsa masa tafasassan ruwan zafi mai qona zuciya. Ya lumshe idanuwansa yana jin tamkar mala’ikan mutuwa ya taho ya zare masa ransa koya’ huta, ya bude idanuwansa da kyar ‘wadanda suka ida rikicewa ba ka ganinkomai ‘ cikin shi sai tsananin ja tamkar garwashin wuta. Ya zura hannunsa cikin aljihu ya zaro ' gabadayan canjin da suka yi masa saura, yasan bazasu haura dubu hamsin ba, ya ajiye a kasa ' tare da fadar kayi hakuri a bata wannan canjin insha l Allahu ko tana gidanta ne zan yi mata aike” Ya juya ya fice yana kokarin dauke kWallar da ke neman~zuraro masa . Malam ya duka ya dauki kwalin yana . faman juyawa a hannunsa, Laure da ke labe tana jiran ta ji yadda zasu qare ta zabura ta yo ' c'iki'n soron ta yi caraf da kudin tana fadar yauwa "‘KaWo su nan Malam". ‘ Shi hatta ma ba shi tsoro ya sakar mata ~ ya tsaya yana kallonta, ta soke a zani tana . fadar “Allah ya ga tsimurmular da muke muna ta fama da Tv Stand ba kayan kallo yanZu k0 ka ga wad‘annan sai a siyo ma ‘yar baba irin wannan talabijin din wadda ake lika wa jikin bango da ‘ kafet din tsakiyar daki su kadai ne dama ba a siya ba” . Malam Bala ya ce“Haba Laure, yarinyar nan ita aka ba wa kudin nan, kuma kina sane daga katifa da zanin gado da labule babu abin da aka sai mata, yanzu wadannan ba ' sai a Kara a sai wani abun ba?” Inna Laure ta ce, “Haba Malam ka sani fa sarai irin mutumin da ‘yarbaba ta aura, dan masu da shi fa dan gidan hali, ne za su rike; mana ita da mutunci? Ita ko Saude Garba ne fa ka sanni na sanka, kar ce ta san kar to mu wahalar da :kanmu na me? Dakunan fa naji ‘yan jere na fadar daki daya ne ya ware mata mai girma, to me za mu zuba a cikin daki daya? Ai da ma Dan gado ne da katifa toga katifar nan ko zuwa gaba ai: idan Allah ya hore ai sai mu yi mata gadon k0 ya ka ce Malam‘?" ’ Malam Bala ya ce, “Shikenan aje a yi k0 ma . ‘ me za a yi. ni dai na rabu da yaran nan lafiya nan da awa daya za a wuce da su gidan Yaya Maje”. . ‘ Laure ta amsa da, “An gama Malam ’Sannan ta juya ta nufl cikin gidan ta bar shi yana kwashe tabarma. Tunda Dr Ahmad ya fita ya fada , motarsa ya kifa kansa saman sitiyarin motar bai sake dagowa ba,» duniyar gabadaya «ta shiga juya masa, ya rinka jin tamkar ana sa guduma ana sassaka masa kirji Ya dauki tsawon lokaci a kife tamkar matacce jijiyoyin kansa suka tattashi rado rado abunka ga jar fata, kamar an zana su, wani irin ciwonkai mai zafi ya sauko masa, ya. dagO‘ kansa da Kyar wanda ya ke jin ya yi masa bala’in nauyi ya mika hannunsa a kwabar jikin .motar ya dauko biro da takarda ya yi wani dan rubutu layi biyu ba tare da ya flta ba, ya kira yaro cikin dasasshiyar muryarsa ya ce, “Ka san Saude?" ‘ "‘ .Yaron yace, “Yar talla, wadda ku ka zo yanzu tare? Dr». ya ce, ‘Ita don Allah karBi ka kai mata, ka tabbatar ka ba ta hannunka da nata, kar fa ka ba wa kowa kaji?” ' Yaron ya amsa da, “To". Sannan ya juya ya nufi gidan a guje. Dr. Ahmad ya maida murfin motar ya rufe ya yi mata key, ya ja sannu a hankali ya bar unguwar. Saude wadda tunda ta shigo gidan ta fada dakinta wanda aka maida shi na zuba tsummokara ta zube a Kasa ba tare da ta damu dadattin dayayiba, tashiga rusarkukamai ‘ tada hankali ji ta ke gabadaya ta tsani rayuwar. Yaron ya shigo tsakar gidan inda jama'a ke ta hidimarsu ya tambaya, “Ina! Saude?” Inna Lami ta nuna masa dakinta, yaron ya nufi dakin, ya iske‘ ta kwance Kasa~ tana sharBar kuka, ya ce “Ga shi inji mai mota a waje ya ce na kawo miki”. Saude da ke kife tana kuka a dago da kanta a hanzarce tana kallon yaron ta karBi takardar hannunta na kyarma tana qokarin warwarewa kamar tasan abin da aka rubuta ta zuba wa kyakkyawan rubutun ido wanda ta ke jin tamkar shi ne ta ke gani, yaron ya juya ya tafi ya barta tana kallon rubutun da ba zata iya karantawa ba, illar jahilci”. Ta fada ta qara durkushewa ‘ta dukunkune takardar ta sake Ta qara fashewa da wani sabon kuka mai ban tausayi.. Yaya Rabi’u ya fado mata a zuciya, ta tuna rayuwarta da shi, da irin yadda yake rudewa idan ya ga hawayenta ya yi ta rarrashinta, rayuwa ke nan, ga ta yau tana kuka ba ta da wanda zai ce ki yi shiru balle har ya rarrasheta. Yau ta yi' kuka kamar ikon Allah idanuwanta suka kumbura suka yi luhu-luhu, ga bangaren kanta da ya dauki ciwo a dole ta saurara da kukan saboda yadda ta ke jin kan nata kamar zai rabe biyu. Ta tashi zaune ta jingina da bango ta ‘ rafsa uban tagumi tana tunani mai tarwatsa zuciya, Inna Lami ta tah0 dakin ta turo mata robar tuwo wanda aka yaba wa miyar taushe ta ' ce, “Ga shi nan idan kin gaji da kukan ki dauka ki ci da sauri, don yanzu za a wuce da ku gidan uban wanka”. Ta wurgo mata bakar leda, “Ga wannan atamfar uban wanka ceda takalma ‘yan Maradi da abaya wanda za ki saka a tafi, maza don ba ke za a tsaya jira ba”. Tana gama fada ta juya ta yi gaba abinta ta bar Saude na bin ledar da tuwon da kallo, a yanzu idanuwanta sun KeKashe babu abin da suke sai zogi da radadi mai ciwo k0 motsin kirkibatayiba, har Inna. Lami tadawota ~ dauki sallallami, “Wai Saude ya ki keso da mune, kefa kawai akejira,karma kici tuwon kanki kidaukikayan kisaka mushine ‘ matsalarmu” Ta yi tsaki ta juya abinta. Saude ta Ki motsawa daga inda ta ke don yadda ta ke ji. zuciyarta k0 kashe ta za su yi ba za'ta saka kayan ba, har yanzu ji take kamar a mafarki ne komai ke faruwa. Ba ta fidda rai ba da za ta farka a kowane lokaci ta ganta a gidan Dr. Ahmad don haka ta soma linke takardarda Dr. Daya aiko mata ta daure a haBar riga tamau. ' Inna Lami ta dawo ta tsaya daga bakin Kofa cike da masifa ta ce “To sai ki fito tunda ba zaki sauya kayan ba, wlh ko,a tsirara ne sai mun kai ki, ehe”. . Sayde ta yi maza tana faman muzurai, tana faman kaiwa da kawo wa, idonta ya sauka inda su ‘Yarbaba suke tsaye da .qawayenta, sun sha anko ana ta shewa. Yar baba ta watsa mata harara tare dajan dogan tsaki Saude ta sunkuyar dakanta bataredata kula ta ba, Inna Lami ta ce ‘Taho nan, ‘Yar baba mu je ai muku nasiha gaba daya Ta sa hannu ta rike ta Saude na biye da ‘ susuka shigadakin da Lauretake. Badai wata'nasiharkirki bace duk habaici ne ta ke yaba wa Saude, ta yi abinta ta gama sannan lnna Lami tatisasu gaba har~ wurin Malam Bala shima nasiha ce dakuma 'jankunne kada waddatasake talullubo zaninta wai da sunan yaji balle wani abu wai shi jaWarci, duk wadda ta sake ta kashe aurenta, to saidai tasan indazata nufa sannan yayi musu ,. fatan alkhairi daga nan aka dauke su da motoci ’zuwa gidan uban wanka, shi ma'ya yi musu nasihar tasa. Ana gama sallar magaruba ” .motocin kai amarya suka zo, qananan motoci ~ masu shegen kyau guda biyar, mijin ‘Yarbaba yaturo dasu na daukar amarya. Shi kuwa Garba gurgu a kori kura ce kwara guda daita za a dauki amaryar adauki ‘yan gidansu don haka mutane duk suka kwashe suka nufl motocin‘ daukar ‘Yarbaba da. Kyar .. aka samu wasu mutum biyu dattijai wadanda za su raka Sauden. Haka aka kwashe aka tafi da amaren, Saude ta lumshe idanuwanta kukan ma ya Ki yiyuwa, idanuwan sun qafe sai radadi suke, zuciyarta sai faman bugawa ta ke da sauri da sauri tamkar za ta tarwatse. ‘ Direba ya ja wani dogon birki kiyyyy! Ya tsaya a kofar gidan, ginin kasa wanda aka shafe da farar kasa, tsohuwa ta riko hannunta. “Fito mu je ‘yar nan ki shiga da qafar dama, da kuma bismillah”. Saude daina ‘ jin maganganun nasu tamkar amSa kuwwa a kunnenta,ne fuskarta na . rufe da hijabi suka shiga cikin gidan mai dogon zaure wanda doguwar kwata ta raba biyu. Suka isa tsakar gidan ‘yan tsaffin na fadar, “Gafaranku dai masu gida”. Babu wadda ta kula su daga cikin matan gidan sai‘ yan yara ne ke ta tsallen murna, an kawo musu amarya su suka nuna musu dakin nata aka shiga da ita, cikin dakin wanda duk cikin gidan shi kadai ne ya ci arzikin aka filasce shi da siminti, aka goga masa ‘yar farar Qasa ciki da bai, babu komai a dakin sai tsohon yadin zanin gado da fululuwansa guda biyu, dakin ya sha sabuwar ledar Kasa an kuma zagaye bangon dakin da sabuwar sitara sai ‘yan kayan ma’aikacinta a gefe. Tsohuwa Iya ita da kawarta' hare suka zaunar da Saude a gefen katifar ba tare da sun zauna ba, ta ce, “To mu za mu wuce Saude sai mu ce Allah Ubangiji ya ba da zaman laflya, a yi ta dai hakuri da rayuwa a duk yadda ta zo watarana sai labari, mu dai mun wuce”. Saude dai dake kife saman katifar k0 dagowa ba ta yi ba ballantana su sa ran za ta tanka su ma ba su saurari tankawar tata ba suka fice abinsu. A soron gidan suka hadu da ango an sha sabon farin yadi da sabuwar hula, bakinnan an cika shi da dusar goro, fuskar nan tasa babu annuri sai sambatu yake, “Yo harni za a yaudara? Ai karya ne wallahi, duk wanda ya ci tuwo dani miya ya sha. Yauwa bayin Allah da ma ku na biyo, ku koma ciki yadda ku ka Kunso tsohuwar karuwarcan ku ka kawo min haka za ku koma ku dauko ta ku koma da ita, ba a gidan Garba ba, k0 da ku ka ganni haka nakasasshe to ban gaji da rayuwar duniya ba". ' Tsohuwa Iyah ta tafa hannaye tana fadar, ‘Muhammadu dan Abadallah, Malam Garba me ya yi zafi haka?” Garba ya taso mata, “Abin, da ke cikin wuta, kin ga tsohuwa ina ganin girmanku kar ki sa in dankara miki ashar ku shiga ku fiddo ta in ba haka ba wallahi zan yi abin da ba a tunani,don dukan mutuwa zansa ai muku a cikin gidannan harda ita tsohuwar karuwar ku fiddo ta in kulle dakina kon tsinke ‘babu babu abinda zai fita bayan ita in kunje ku fada wa tsohon banza na ce na ba shi nan da kwana uku k0 ya aiko min da duk abin da ya san na kashe ko kuma in sa kayan dakin a kasuwa ku fada masa na sake ta saki uku”. Daga nan ya juya yana tsangala qafar ya . bar su a sore Hare ta dafa Iya tana fadar, “Yau munga takanmu ni hare kinga koma kifitoda yarinyar nan mu maida ta hannun iyayenta, " wannan nakasasshen banzar zai iya fiye da duk abin da ya fada” Don daman ance gurgu yafi mai qafa iya shege Iya ta ce, “Aikuwa na gani bari in fito da ita". Ta Juya ta koma cikin gidan. Lol jama,a ya abin yakene ku biyoni donjin yaddah zataci gaba da kayawa [1/30, 10:24 AM] A A Dboy: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚 [12:17PM, 02/02/2017] 🙆🏼‍♂@lh@ji🙆🏼‍♂: [1/30, 4:30 PM] A A Dboy: *YAR TALLA* BOOK 3 *CHAPTER 23* Saudat na kife a katifarta tana rusar kuka, Iyah ta shigo, “Saude tashi maza mu tafl" ,, Saudat ta dago da sauri tana kallon Iyar da jajayen idanuwanta, ji take tamkar zolayarta ta ke Iyah kuwa ta mika hannu ta kamo hannun Saudat tana fad'ar, “Tashi. maza mu tafi, yau mu ai mun ga ikon Allah”. ‘ Saudat ba ta iya yin musu‘ba ta mike ta bi Iyah suka fito, inda suka iske har hare ta kai qofar gida don haka suka rufa mata baya suka rankaya, Saudat jin abin ta ke tamkar cikin mafarkinta, to me ke faruwa ne? "‘ """"""""""". '"""""""" Tunda Dr Ahmad ya yi wa motarsa key ya dauki hanya tafiya kawai yakr amma ba tareda yasan irin tunaninda yakeyiba gudu yake saman titi ba na wasa ba, tamkar wanda ke dambe da iske,, Allah dai ya kawo sa garin Abuja. . ~ Babu inda ya yi wa tsinka sai gidan iyayensa; yana faka motar tasa ya kulle murfin , motar ya sa qafa ya shiga tamkar'wani mara lakka‘ ya na cikin gidan nasu, da ‘yar siririyar sallamar da shi kadai ya san yayi ta. ‘ Babu kowa a falon shiru babu komai sai kukan AC,kamar wand aka hankada ya fada saman doguwar kujera ya rungume fitan kujerar ' tare lumsha ,idanuwansa tamkar wanda ya sha wani abin maye, yana shakar sanyayyen qamshin turaren wuta dake tashi,sannu ahankali yana falon tsawon mintunan da suka haura talatin babu wanda ya fito falon , sai can Hajiyarsa ta fito daga falonta da alama ma ma fita za ta yi don’ sanye ta ke da atamfa super Holland wadda . aka yi wa dinkin riga da siket, ta da wani qaton mayafi wanda tsadarsa ta tasar wa dubu talatin. Hannunta na riqe da hannunta na riqe da qaramar jaka bazaka taba cewa ta haura shekaru arba”ba, amma nan sittin ne hard ‘yan kai. < Kodayake k0 shi uban gayyar a yanzu talatin da shida ne ke kanshi Ganin Dr a falon ya bawa Hajiyar mamaki Dr. ya bude idanuWansa da gyar yana . kallonta tamkar wanda ya yi cutar shekara guda wuyansa tana fadar, “Lafiyarka kuwa Ahmad? Me ke damunka ne " Dr. ya dago hanunsa da kyar ya dafa kansa .kafin ya ce “Momy kaina kamar zai rabe biyu, zuciyata fashewa za ta yi”. Hajiya ta dimauce ta soma kiran sunan Allah tana fadar, “Yau ni na shiga uku Ahmad tashi mu je in kai ka Maitama District Hospital a duba min kai". Dr. ya girgiza mata kai, “No Momy ki kyale ni don Allah, ciwona ba na asibiti bane, bugun zuciya ne idan na dan samu relive zai damau. . Ta ce“Kamar ya zai daina Ahmad? wacce irin damuwa ce wannan da ta ke qokarin kai ka kabari?” Dr. ya ja dogon numfashi kafin ya ce “Momy sun hana ni Saudat, wallahi Momy ina sonta, taBa zuciyata ki ji yadda ciwo ke‘ nuqur kusar zuciyata". Momy ta dan zuba wa dan nata ido, kafin tace “To ita Saudat din sukace bazasu baka ita baka ita ba sai kace wani mai mugun hali? Duk duniyar nan da ma akwai inda zakaje neman aure ahana ka?”Dr. ya girgiza kai “Wallahi Momy baza su barni na auretaba don Allah Momy ki ba ni shawara, ya zan yi?” .. Hajiya ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya kafin ta raBa kusa da shi ta zauna, ta cusa hannunta 'cikin sumar kansa tana sosa . masa cikin Sigar rarrashi ta ci gaba da fadar. “Don Allah ku zamo mai tawakkali Ahmad, ka zamo mai juriya da rungumar abin da Allah ya qaddara maka, ka sani bai hana ka Saudat don ba ya sonka' ba, sai don kawai ya jarrabe ka Ya gwada imaninka, haba dana kai _ din fa mai kwarin zuciya ne, ina kwanjin dana ’ Sanka da shi? Haba dana ka zamo mai juriya kaji?" ‘ ' Kai kawai ya iya daga mata ta ce ’ “Yauwa nawan daure ka tashi mu tafi aSibitin ’ Doctor ya duba ka yanzu mu dawo” , Baimusa ba yayunkura dakyar tana riqe da hannunsa suka fice ta sa direba ya jasu 'cikin babbar Jeep dinta suka nufi asibitin. Iyah na"riqe da hannun Saudat har suka isa gidan, ita dai tafiya kawai ta ke, amma ba ta san inda ta ke jefa Kafarta ba, sunsa qafa cikin zauren gidan ta ji gabanta ya yi wata mummunan faduwa, irin wadda ke sa mutum ya yanke jiki ya fadi. Suna shiga tsakar gidan suka yi karo da Inna Laure, wadda ke qoqarin hada hankalin gidan kasancewar duk ‘yan bikin sun watse tunda har isha ta karato ga shi kuma hadari ya gangamo a garin. Suna shiga tsakar gidan Inna Laure ta zabura ta mike tana fadar, “Me nake gani haka kuma ni- Laure, ba ku kai ta gidan nata ba ne k0 ya ya aka yi?” Iyah ta ja hannun Inna Laure ta damqa mata Saudat. “Ga amana mun maido, yarinya mijinta yace ya mata saki uku saiku nemi dalili a wajensa, mu kuwa mun tafi Allah ya ba mu alheri”. Suka juya suka yi gaba abinsu. Inna Laure ta hankade Saudat da ke hannunta tana kwalla wa Malam Bala kira, wanda ke qoKarin fitowa daga dakinsa yana zuba sallallami, kira yake“Me kunnena ke jiye min Laure?” Inna Laure ta taBe baki. “Abin da ka ji Malam ni ma shi na ji”. Malam Bala ya nufi Saude ya nuna ta, “Ke kuwa wannan yarinya ban ji dadin haihuwarki ba, wannan nan uwarki ta haifa min jaraba da alaqaKai, kalu’inna lillahi wa"inna ilaihi raji’un, keko yau sai kin bar gidan na gaji ba zan iya ba wallahi na gaji. . .” Saudat ta fashe da wani dan marayan kuka na rashin sanin madafa, ta dora hannuwa biyu a kai, ta rasa abin da ke mata dadi, tashin hankalin da ta gani Kiri-Kiri a idanuwan mahaifin nata shi yafi firgitar da ita, ta zuba wa Malam Bala ido wanda ke jin zuciyarsa tamkar za ta tarwatse saboda tashin hankali, wasu irin hawaye masu zafi suka biyo kuncinsa, cikin tsananin takaici da bacin rai ya ce. ; “Ai dole ya sake ki Saude, don idan ba dan iska irinki ba babu namijin da zai iya zaman aure da ke, amma ina so ki sani ni na riga na sauke nauyin da Ubangiji Ya dora min a kanki, don haka sai dai ki nemi inda zaki amma ba dai gidana ba, yadda ki ka taho haka 'zaki juya ki tafi duk gidan uban da zaki, kuma tsakanina da ke Allah ya isa ban yafe miki ba” Saude ta ji kalamansa tamkar saukar . ruwan zafl a jikinta ta durkushe a gurin tana wani gunjin kuka. ' “ Malam Bala ya dube ta a fusace, “Eh ’zamama kikayi kenan kina kukan rashin kunyar, ai ko zaki bar gidan nan a nakashe”. Ya juya ya rarumo muciyar Inna Laure‘kafin ta yi yinkuri ya muka mata a baya .Saude ta fasa wata uwar Kara ta sheme a qasa Malam Bala ya hau maka mata muciyar ‘ ' iya Karfinsa, ya hau fadar, “Ni za ki dauka dan iska? Ni zaki kawo wa shakiyanci a cikin gida? ‘ ‘ Ganin yana shirin kisan kai yasa Inna Laure ta riae‘Ke shi, ta soma ba shi haquri, sai data yi da gaske sannan tasamuya ya. kyaletaya ta nufi dakinsa yana sharar gumi, duk da kuwa ba ’ «lokacin zafi bane a lokacin. ~ , . Saude kuwa ko kwakkwaran motsi ba ta yi, saboda doguwar sumar da ta yi. Haka duk suka shige ciki suka barta ayashe tsakar gida kamar ba dan mutum ba. Tsawon lokaci wani irin iska mai hade daguguwa yataso tare dasaukar wasu ruwan sama masu qarfi tsawon lokaci ruwan na dukan Saude kafin ta fara motsawa sannu a hankali ta bude idanuwanta a hankali abubuwan da suka faru suka rinka dawo mata tamkar bidiyo. Ta runtse idanuwanta da sauri tanajin tamkar zuciyarta zata tarwatse, ta yunqura ta mike da kyar wata irin tsanar ’mahaifin natane maitsani ne tarinqaji zuciyarta batada wata bukatar data wuce barmasa akurkin gidansa dukda wani irin masifaffen ciwon da jikinta ke mata amma hakata takarkare ta fito daga gidan dukda juwar da ke faman rufe mata idanuwa. ga kuma tsananin ruwan saman, ga-tafiyar tata tamkar: ta ‘yan kayo saboda tsamin da jikinta yayi Cantaji andanno mata oda abayanta da qarfin- gaske Saude ta ji har cikin dodon kunneta tamkar zai rabe biyu gashi kuma an danne odar an Ki saki. Saude taji tamkar ta zuba da gudu saboda yadda ta ke jin hatta ‘yan ‘ cikinta na amsa kuwwar odar sai dai ba qarfin jikin da za ta iya yin gudun, don haka ta durkushe a gurin. Cikin takaici Hamid ya Balle murfin motar ya leko da kansa cikin ruwan cike da masifa yana fadar, “Ke k0 wacce irin mace ce ‘ ana miki oda ba ki ji, kawai ki zauna saman hanya k0 aljana ce ke ai kin kauce daga saman hanya donkar waniyazo ya takaki cikin rashin sani”. Saukar muryarsa a dodon kunnen Saude ya sa‘ ta saurin waiwayowa don tabbatar wa cikin wata rikitacciyar murya Hamid ya kira sunanta tare da zabura ya fito daga cikin motar ya nufo ta yana fadar, “Saude ke ce kuwa, ko dai gizo ki ke min?” Ya durkusa a ‘gabanta, “Lafiya Saude me ya fiti dake daga gidanki cikin wannan damunan?” Cikin kuka Saude ta some fadar. "Sakina ya yi Hamid, ya sake ni". Hamid ya dafe kai, “Innalillahi wa’inna ilaihirrajiun Wayaji miki wannan ciwon a jiki haka? Dubi yadda jini ke zuba a jikinki”.‘ ‘ Sai a lokacin ma ta lura da wani irin kwasheshen ciwo da ta ji a gwiwar hannunta. . Hamid ya ce “Tashi !maza mu tafi asibiti kada jininki ya Kare”. ' Ganin tana ta KaKaniyar tashi ya sa ya sure ta da kuzarinsa ya sata a mota ya maida ya rufe, ya zagaya gidan direba ya shiga ya ja, kai tsaye ya nufi medical center da ita. Cikin .ikon Allah yana zuwa ya samu likita Dr. Mariya ta karBe ta aka wuce Emergency room da ita, abu kamar wasa sai da ' aka shafe fiye da awa guda Hamid na nan' zaune babu wanda ya fito, tsoro ya cika masa zuciya tun yana addu’a a zuciya har ta fara fitowa fili. . . Can cikin ikon Allah sai ga Dr. Mariya , ta fito,Hamid ya zabura ya miKe ya nufe ta yana fadar,“Lafiya dai k0 likita?” Dr: Mariya ta yi murmushi kafin tace *‘Ka kwantar da hankalinka Malam Hamid * insha Allahu ‘yar uwarka za ta samu sauKi ‘ amma yanzu ka biyo ni ofis akwai wasu yan ; tambayoyi dazan maka Cikin karyayyar zuciya hamid ya amsa da, “To". Sannan yabi ta ofis din Sai da ta zagaya ta zauna ta cire gilashin fuskarta sannan ta nuna masa wurln zama, Hamid ya ja kujera ya zauna yana kallon magidanciyar matar, wadda a qallah ba data wuce shekaru arba‘in. Ba Dr. Mariya ta gyara zamanta tare da tattaro duk wata nutsuwa, kafin ta ce “Malam Hamid don Allah akwai wasu ‘yan tambayoyi da nake so in maka, da fatan za ka yi min. uzuri, ka kuma fada min gaskiya, amma fa kayi hakuri". Hamid ya qara tattara nutsuwarsa sosai yana kallonta, kafin ya ce “lnsha Allahu" Doctor Mariya ta yi wani murmushi kafin ta ce “To na gode kwarai“. Ta dan ja numfashi ta ci gaba da cewa, “Da ma ba wata magana ba ce kan maganar ‘yar uwarka ce Saudat a katinta na ga ka . rubuta sunan unguwarku wadda ke cikin Dandagoro haka ne? ‘ Ya daga mata kai alamar eh ~ Ta girgiza kai, "To amma Hamid ka ce. Saude Kanwarka ce, don Allah ka yi haquri ka fada min gaskiya, ya ka ke da Saudat tsakaninka da Allah?” Hamid ya dan zuba mata idanuwa yana mamakin tambayar tata, kafin lokaci guda ya sauke numfashi; “Duk cikin magarta babu wadda na fada miki ba daidai ba, Saudat Kanwata ce wani abu ne likita?" Dr. Mariya ta koma ta jingina da bayan kujerarta cikin sanyin jiki ta girgiza masa kai alamar a’a kafin ta buda baki, “Saudat ta samu tsagewar qashi a hannunta na dama sannan a qafarta ma ta goce, sannan akwai buguwa a qashin bayanta duk da dai buguwar ba ta cossing din wata matsala ba, amma na yi . ‘ mamakin irin wannan manyan ciwuka haka a . jikin mace, kuma qaramar yarinya ga shi ka ce ba hadari tayi ba, ba komai ba”. Hamid ya ce “Wallahi ba hadari ba ne, duka ne kawai". Dr. Mariya ta ja wani tsaki-kafin ta ce “A gaskiya akwai marasa tausayi a duniya, yanzu ko dabba ai ba a yi mata irin wannan dukan ba”, Ta qara jan wani siririn tsaki sannan ta ja dan siririn gilas dinta ta sanya a idonta, tare da janyo biro ta yi wasu rubuce-rubuce ta yage ta mika masa, ya sa hannu ya karBa tare da miqewa ya yi mata godiya ya fice. Dr. Mariya ta kwantar da kanta saman makarin kujerar tana kallonsa har ya fice daga ofls din nata. Hamid bai bar asibitin ba har garin Allah ya waye yana ta faman zurga-zurga siyo wannan auno wannan, karbo wancan har sai da aka kira assalatu sannan ya tafi masallaci ya yi sallah, a lokacin an daura mata karin ruwa, yana gama sallar ya dauki mota ya fice don hado mata‘ abin karyawa, sannan ya wuce gida, kai tsaye restaurant ya nufa ya yo take away sannan ya fito ya siyi fruit da kayan tea da duk abin da yasan za ta iya bukata sannan ya dawo asibitin a lokacin kuma ya iske Doctor na ta nemanshi aka ba shi wani list din abubuwan da zai siyo, kuma sai ya fita asibitin, Hamid ya sauke numfashi don yasan yana zuwa yanzu Dad dinsa ya gama Kuluwa don tun cikin daren jiya ya keta faman kiran wayarsa yana fad‘a masa ga shi nan za shi nan, daga qarshe ma sai ya kashe wayar gabadaya tabbas ya san kuwa sunada dabi a gidan yau. Ya zura hannu cikin aljihunsa ya ciro wayoyin tare da kunna su sannan ya yi gaba yana ta faman sauri kamar mai shirin "tashi sama, ba shi ya samu ya yi saitin din komai ba sai wurin daya saura na rana, shi ma kuma yana kokarin tafiya Dr. Mariya ta tsayar da shi za ta rubuta masu sallama. Hamid da ke zaune bakin gadon na Saudat ya ji wani farin ciki ya kama shi, ya dafa gadonda Saude ta ke zaune a kai, wadda ta sha ledojin ruwa biyu, ta yi fayau kuma tana nan kamar an kulle biredi, muryarsa a sanyaye _ ya ce, “To yanzu idan aka sallame ki ina ki ke ’ ganin zan kai ki Saudat kafin in nemo mana mafita?" Saude ta lumshe idanuwanta wanda .damuwa ta ke cike fal a cikinsu, Hamid ya sake kiran sunanta, “Ki yi hakuri Saudat ki manta, insha Allahu lokaci ya yi da zaki dandani zaqin rayuwa ke ma kin ji?" ' Saude ta bude idonta da kyar tana kallonsa, aka turo Kofar dakin aka shigo daga ita har shi suka zuba wa mai shigowar idanuwa, ba kowa ba ne sai mahaifin Hamid, fuskarsa ba yabo ba fallasa ya shigo ‘ Dr. Mariya na bayansa da takardu riqe a hannunta. Yana qarasowa tun kafin Hamid ya yi wata magana ya cire hannu ya zabga masa wani mari wanda ya sa shi saurin dafe kunci, Alhaji Bashir ya nuna shi da dan yatsa, ni za ka dauka mutumin banza ka nuna ‘ wa duniya ban isa da kai ba? Wato har wannan ‘ yarinyar ta fiye maka mu k0 Hamid? Kai yanzu in bacin ma ba ka da zuciya har ka sake kallon yarinyar nan wadda ubanta ya nuna bai sonka, bai Kaunar tarayyarka da ita, amma shine kake like ka nace har ka ke bibiyarta da aurenta? To wallahi ba za ka zubar min da mutunci ba, cikiri satin nan zan daura ‘ maka aure da duk wadda tayimin tunda nalura auren ka keso, wuce mu je mutumin banza kawai, na san babu abin da ke dibarka ~ sai wannan kyan fuskar” . Hamid ya zaro ido tare juyawa baya, muryarsa a sarKake ya ce“Dad ka tafi zan zo don Allah 'ka dubi halin da yarinyar nan ta ke~ . ciki, ba ta da kowa sai ni sai Allah idan na tafi ' na barta zata iya shiga kowane irin hali, don “ Allah Dad ka yi haKuri ka ba ni awa daya", Alhaji Bashir ya zuba masa idanuwansa cike da mamaki, kafin ya ce, “Ka san kuwa abin da ka ke fada Hamid? Wato har wannan abin yafi ni ke nan k0? Yanzu kai har kana da ~ hujjojin kare kanka idan iyayenta suka samu labari, yanzu har ka manta cin mutuncin da mahaifinta ya zoya yi mana har gida ke nan? To wallahi tallahi ka Kara minti biyar a nan ban yafe maka ba, mutumin banza kawai”. Ya juya a fusace ya bar dakin, Dr. Mariya ta matso daf da Hamid muryarta a sanyaye ta ce“Hamid ka yi .hakuri ka bi mahaifinka kada fushin Allah ya tabbata a kanka”. ' Idon Hamid ya kawo Kwalla cikin sarqewar murya ya ce, “Doctor ba ta da kowa baiwar Allah ce idan na tafi na barta ban san halin da za ta samu rayuwarta ba, na tabbatar tafiya in barta ita ce silar da rayuwarta‘ za ta salwanta". Dr. Mariya ta sa hannu ta dafa kafadarsa tana fadar, “Ka je Hamid nayi maka alqawarin rike Saudat a hannuna' daga yau har zuwa lokacin da za ku satelin da mahaifinka, na yi maka wannan alkawarin". _ Dadi ya kama Hamid ya soma zuba mata godiya, ya zaro wasu sauran kudin da suka rage masa ya mika mata, wadanda bai san ko nawa ba ne. “Ga wannan don Allah ki fara rikewa a hannunki kafin in dawo”. Dr. Mariya ta girgiza masa kai. “A’a, kai dai kawai ka je, ga Katina mu .yi magana”. Hamid ya karBa yana godiya, sannan ya zuba da gudu ya flce don tsoron cikar lokacin. Yana fita Dr. Mariya ta wuce ta nufi qofa, ta maida ta kulle sannan ta juyo ta dawo inda Saude ta‘ ke, wadda tunda mahaifin Hamid ya shigo ta lumshe idanuwanta tana maimaita innaIiIIahi saboda yadda ta kejin zuciyarta na barazanar tarwatsewa. Dr. Mariya ta dawo cikin dakin ta ja kujera ta 'zauna tana fadar, “Bude idonld ki kalle ni nan Saudat". Sosai Saudat ta bude idanuwanta wadanda suka yi jajawur tana kallonta, kafin ta ce, “Saudat waye mahaifinki?" Saude ta ji tamkar ta caka mata wuqa a kirji cikin dusasshiyar muryarta ta Malam bala. . Dr. Mariya ta ce, “Mahaifiyarki fa?” Saude ta dan yi shiru tamkar ba zatayi magana ba, kafin ta bude baki cikin muryar kuka,tace “Ban santa ba, banma taba ganinta ba tunda na tashi na ganni da Yayana Rabi’u da matar mahaifina Inna Laure, tunda na tashi ban san dadin uwa ba, ban san wani ' gata ba wanda da ke samu wurin mahaifinsa ba saboda ni. . .” . Saude ta saurara daga bayanin da ta ke saboda hawayen da ta gani suna zubowa daga idanuwan matar, idanuwan Saude suka yo warwaje muryarta a sarqaqe ta soma fadar, “Lafiya dai Doctor, me ya faru?” Dr. Mari'ya ta riko hannunta gam ta rike tana motsowa cikin kuka ta ce; “Saudat nice mahaifiyarku, nina haife ku da cikina tun... ” ‘ Kuka yaci qarfunta ta soma wani kuka mai cin zuciya. Saude kuwa dif ta tsaya da kukan nata tana kallon matar muryarta na sarkewa ta ce “Kece mahaifiyarmu? Idan ke ce ' mahaifiyarmu me ya sa ki ka tafi ki ka barmu? Me ya sa ba ki sake waiwayarmu ba ki ka manta da mu ki ka watsar da rayuwarmu kika wofintar da mu, k‘i ka bari aka tarwatsa mu, muka sha wahala muka rasa mataimaki a duniya, kowa ya tsane mun . Dr. Mariya ta yi saurin rufe mata baki cikin kuka tana fadar, “Ya isa! Ya isa haka Saudat wallahi ban bar ku ba sai don hakan shi ne mafita, ban watsar da kuba sai don ina jiye muku tsoron wahalar da za ku iya fuskanta idan na ce zan tafi da ku alhalin ni ma ban san inda zan nufa ba, ku yi hakuri Saudat ina .yayanki?” ‘ Saude ta runtse idanuwanta wasu hawaye suka ziraro mata, cikin kuka ta ce “Sun raba mu tun shekarun da suka wuce Baba ya kore shi ban sake ganinsa ba, ban san halin da yake ciki ba. Nan ta labarta mata labarin rayuwarsu tun farko har izuwa yau. ‘ Dr. Mariya kuka ta ke sosai ta rungume Saudat a jikinta suna jin dumin juna, soyayya tsakanin uwa da da ta rinka shigarsu tsawon lokaci kafin. su saki juna, Dr. Mariya ta ce, “Taso mu je gida Saudat ki huta in baki tarihin .mahaifinku da irin taskun da na shiga a lokacin aurena da shi". -. . Ta riqo Saudat ta taimaka mata ta miqe, ta dauki makullin motarta suka fita har zuwa harabar asibitin inda aka tanada don ajiye motoci. [1/30, 4:30 PM] A A Dboy: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚 [12:17PM, 02/02/2017] 🙆🏼‍♂@lh@ji🙆🏼‍♂: [1/30, 9:54 PM] I love my mum: *YAR TALLA* BOOK 3 *CHAPTER 24* Taso mu je gida Saudat ki huta in ba ki tarihin mahaifinkuda irin taskun da na shiga a lokacin aurena da shi". Ta riqo Saudat ta taimaka mata ta mike, ta dauki makullin motarta suka fito har zuwa harabar asibitin inda aka tanada don ajiye motoci. Ta bude wa Saude gidan baya ta shiga ta maida ta rufo sannan ita kuma ta zagaya ta shiga mazaunin direba ta yi wa sabuwar motar key qirar Jeep mai taya a baya suka hau hanya kai tsaye Goruba road suka nufa a road ta tsaya qofar gate din wani madaidaicin gida mai kyan gaske da wadatar furanni masu tsayi ta yi' oda kusan sau biyar sannan aka bude gate din gidan ta cinna hancin motar a ciki maigadi yana daga mata hannu ta yi cikin gidan kai tsaye harabar wurin ajiye motoci ta nufa ta raba motar tata kusa da wata Matris sabuwa dal ta kashemotar ta fito sannan ta bude wa Sande ita ma ta fito ta riko hannunta ta ratayo a wuyanta saboda taji dadin taka qafar sannan suka shiga falon inda qofa ta ke a gefe suka nufi falon kai tsaye Bai da girma sosai, madaidaici ne wanda ya cinye saitin knjeru guda da show glass tare da kayan kallo da santa table a tsakiya. Suna shiga falon qananan yaran da ke zaune suna wasa suka yo kansu suna, “Oyoyo ga Momy”. Saude ta bi yaran da kallo, ‘yan qanana \ masu Dr. Mariya ta yi wa Saude masauki saman kujera sannan ta bi ta kan yaran ta rungume su a jikinta tana amsa sanu da zuwan nasu, ta nuna masu Saude, “Bakuga Antynku bane? Kuje ku gaishe ta”. Yaran gnda biyu mace da namiji suka durkusa gaban Saude suna fadar, “Ina kwana Aunty”. ‘ Saude cikin karayar zuciya ta amsa da lafiya lau tana kallonsu, macer ce ‘yar babbar wadda ba za ta wuce shekaru shidda ba, sai namijin wanda bai wuce uku ba, Dr. Mariya ta ce, “Kannanki ne, Nabil da Nabila suna karatu ne a nan Saude su duka da maigidana Alhaji Ashiru yana aiki a central bank yanzu kizo muje ga dakin baqi can ki wanka kici abinci ki huta, sannan inzo muyi magana". , Saudat ta amsa da, “To”. Sannan ta mike suka nufi dakin. . Karamin daki ne mai dauke da gado da kujeru Kwara uku sai kayan kallo. Falon ya yi kyau sosai saboda yadda aka qawata shi da kayan dakwareshin masu kyau, akwai toilet da dan wurin hutawa a cikin falon. Dr. Mariya ta juya ta fito ta bar Saude taqarewa falon kallo ganin abin ta ke take tamkar a mafarki wai ita ce yau da mahaifiyarta, ikon Allah ko’ina Yaya Rabi’u ta san da zai samu labari ba qaramin murna da farin ciki zai yi ba. Dr. Mariya ta sake shigowa rungume da sabuwar jallabiya a hannunta ta ajiyewa Saudat tana fadar, “Ki je ki watso ruwan ga jallabiya nan ki saka nasan za ta yi miki a Saudiyya na siyo ta”. Saude ta amsa da,‘ “To na gode”. Dr. Mariya ta yimurmushi kafin tace, “Me ye abin godiya kuma Saudat? Don Allah ki saki ranki ki rinqa kallona a matsayin mahaifiyarki kin ji?” Murmushi kawai Saude ta yi tare da ‘sauke idanuwanta qasa Dr. Mariya ta juya ta fita sannan ita ma Saude ta yunkura da kyar ta mike tana tsangala kafar da kyar ta shiga bandaki ta watso ruwa ta dauro alwala ta fito ta murza mai a jikinta sannan ta kawo jallabiyar baka ta saka ta nade kallabin rigar a kanta sannan ta yi sallarta ta daga hannuwanta ta soma tana godiya ga Allah da Ya muna mata wannan ranar, Dr. Mariya ta shigo ta kawo mata abinci ta juya ta fita, Saude ta shafa addu ar ta mike ta nufi inda kulolin abincin suke ta bubbude, tuwon shinkafa ne da miyar alayyahu ta ji naman kasuwa sai gasasshen kifi da kayan lambu wanda ya ji curry da kayan kamshi, sannan kunun aya cikin jug wanda ya ji kwakwa da dabino da madarar gari. Saude ta zauna kasa tana tsatstsakurar abincin ba wani da yawa ta ci ba ta ajiye ta sha kunun aya sosai, sannan ta dauki magungunan da ta ga an ajiye mata ta sha, ta mike ta‘nufi kan gadon ta kwanta. Wani bacci mai nauyi ya dauke ta ba ita ta farka ba sai gab da maguriba ta mike ta nufi bandaki ta dauro alwala ta fito ta yi sallah,‘ tana nan zaune Dr. Mariya ‘ ta shigo da sallamarta, tana sanye da wasu riga da siket na wata atamfa super wax mai kyan gaske Ta raBa saman gadon ta zauna tana jiran Saude ta kammala Saude ta shafa addu’ar ta waiwayo tana gaishe da Doctor. Cikin fara’a ta amsa tare da fadar, “Sannunki da qoqari, ai na dauka kina nan kina bacci, kin san marar lafiya bai san motsa jikinsa saukinki ma ba ki da Kan-jiki”. ‘ Saude ta dan yi murmushi tana kallon inda a ka yi mata dressing din ciwonta". Dr. Mariya ta ce, “Da ma ina so mu yi° magana ne shi ya sa na bari ki huha ki dan samu natsuwa Saudat zan ba ki tarihina gabadaya ta yadda zaki cire qullatata a zuciyarki, da farko 'dai ni . ‘yar asalin Dandagoro ce mahaifina da mahaifiyata a can suka haifeni ni da yayana, kuma a ciki muka girma sana’ar mahaifinmu ita ce Kira, ana ce masa Lawai maqeri mahaifiyata kuma sunanta Badiyya, ita kuma tana sana’ar kitso da saka, asalin mahaifiyata bafulatana ce kuma gabadaya ita muka biyo. Tunda na tashi ina qarama ta na iya saKa " harna fara girma mahaifina ya sani a makarantar boko a lokacin ina. da wana Yaya Sani sai ni sai turamu Yayana ya yi karamin bokonsa‘ daganan ya tafi Sakandiri har zuwa Polytechnic inda ya yi N C. E dinsa, amma bai samu aiki ba a lokacin duk da unguwarmu yaya Sani ne kawai wayayye , don shi me ya fara wucewa. gaba da sakandire. Ina firamare aji bakwai, lokacin har aji . bakwai ake yi, watarana na hadu da mahaifinki Bala, a lokacin ina da shekaru sha uku, shi kuma a ‘ lokacin yana, saurayi don” bai wuce shekaru asirin ba, na hadu da Bala yazo Yaya . Sani' ya yi masa wani lissafin kudi ya buga masa da calculator. Suna zaune saman dakalin. Qofar gida suna magana, ni kuma na dawo daga makarantar allo da yamma na gifta su na gaishe su zan wuce Yaya Sani ya kira ni na dawo na durkusa a gabansu’, “Ga ni” , Ya ce, “Je ki kawo mana ruwan alwala”, ‘ ‘ na amsa da, “To” sannan na tafi cikin gidan na ajiye allona na samu Umma a zaune akan tabarmar kaba tana yi wa wata mata kitso ’ ' na gaishe da matar sannan na wuce bakin randa na zuba‘ musu ruwan a butoci na fito na kai musu, na dawo gida na ci gaba da ‘sanwar tuwon da Umma‘ ta. dora,‘ban san wainar da aka toya ba a waje tsakanin Yaya Sani da Bala ba kwatsam washegari Umma ta aike ni kai kudin daShi nan bayan gidanmu, na shiga gidan kafin in fito yaro ya shigo wai ana kiran ‘ Mariya. Gabana ya fadi, don nadai san ko sauraren Samari ban fara ba,kamar' kar na fita matar gidan tacemin,“kije kiga ko waye ki ka sani k0 yayanki ne?” Jin hakan da ta fada ya sa na samu kwarin gwiwar fita, a rakube na same shi jikin bango ya harde hannuwansa a Kirji yana ta faman mazurai. Ganin Bala mamaki ya kama ni, ni dai na san ba haduwa muké ba, duk da. kuwa yana dan unguWannu don bama ruwana da shiga shirgin maza. ” Na dan tsaya nesa da shi na gaisheshi, ya washe baki yana amsawa kamar wanda aka , yi wa wata kyauta, nace, “Ga ni” Kallona ya yi sosai kafin ya ce, "Nasan zakiyi mamakin kiran danayi miki ko?” ” Ni dai kaina na kasa, Jira kawai naké in ji yace, ga inda zai aike ni Shikuma batare da ya tsaya sauraran amsata ba ya ci gaba da cewa ‘ . “Ba komai bane ya 'sa na kira k8ba , ,Mariya wallahi Sai don na bude miki abin da ke cikin zuciya saboda na ga barinsa a qirjina bai ,da wani amfani Ni dai Mariya ina dawainiya da sonki a zuciyata ba wai yanzu ba ‘wallahi tunda dadewa amma Allah bai Sa na taBa fada ‘wa kowa ba sai jiya na sanar da‘yayanki Sani, amma sai ya nuna mini gaskiya in yi haquri don kuwa ke karatu za ki har gaba da sakandiri za ki wuce, don burinsu sai kin zama likita, ba yadda ban yi da shi ba amna ya Ki daga qarshe ma har dan saBani muka samu da shi a kanki. Na haqura na tafi gida, amma wallahi Mariya ban iya samun bacci ba a daren jiya, , idan na rufe idanuna hotonki nake gani yana yi min gizo, duk yadda naso in rarrashi zuciyata abin ya faskara, don haka na yanke shawarar~ ’ zuwa wurinki da qoqon barana don Allah Mariya ki taimaka ki soni koda da kwayar zarra ne” Ni a lokacin sai na rinka jinSa tamkar ; : mafarki don tunda nake babu saurayin da ya taba tara ta da irin wannan maganar sai shi, don haka ban wani dauki abin da muhimmanci ba na dubeshi kafin in ce “Ka yi haquri, kamar yadda Yaya Sani ya fada maka ni ba aure zan yi ba, karatu zan yi, na gode, sai anjima”. Ina ji yana ta faman kirana, ama ban tsaya ba don ni a tsorona kada wani dan gidanmu ya wuce ya gan ni. Abu kamar wasa Karamar magana ta zama babba, don kuwa duk inda za ni sai na ga Bala, k0 makarantar boko' 'ko ta allo, k0 kasuwa za ni ke kamar ana fada masa ga ni nan zan fita, kuma in dai siyayya zan yi ko ta nawa ce shi zai biya kudin, duk wulakancin da zan masa ba ya ji, ya zame min kamar wani kaska na rasa yadda zan yi da shi, tun ina wulakanta shi, har ta kai ga na gaji na sa masa ido, daga baya ma sai ya koma ba ni tausayi saboda yadda ya ke shan wulaqanci amma bai taBa bata ransa ba, idan aka aike ni kasuwa. Siyayya kuwa k0 ta kai ta nawa shi zai zaro : Kudi ya biya ya yi tafiyarsa ya bar ni in rasa yadda zan yi da kudin a hannuna haka na dinga Boye su a cikin buhun kayana don tsoron kar ‘ wani ya gani in shiga uku, wasa-wasa na tara 'kudi masu tarin yawa. ~ ‘ Ahaka ahaka Saudat har saida Bala ya sarke min Zuciya na manta da duk wulakancin ‘ da nake masa ta kai ta kawo ma in ban ganshi ba, ko bacci ba na iya yi a dantsakanin mu fa ‘ soyayya mai qarfi ta shiga tsakaninmu, amma babu wanda ya sani a gidanmu. ‘ Idan Bala yana son mu hadu sai ya ' rubuta ‘yar takarda ya soke a kyauren gidanmu da ma na sani kullum sai na duba kyauren don in ga k0 ya soke sakonsa, idan ya sanya in dauko in ruga in Boye in karanta, bai dai wuce. sakon mu hadu Wuri kaza, karfe kaza, kuma duk abin da nake in dai ya ce yana jira wuri kaza sai nace k0 ban da lafiya ne kuwa. ' A haka watarana . Bala ya soke . takardarsa da yamma na dawo daga kai nika na“ , gani na duba, yana son mu hadu bayan gidanmu bayan sallar magaruba, dadi ya kama. ni don da ma mun kwana biyu ba mu hadu ba, don haka ina shiga gida na sauke wa Umma nikan a tsakar gida na suri bokiti na nufi bakin rijiya .zan jawo ruwa, .Ummana :dake zaune saman kujera‘ yar‘ tsugunne ta dube ni yadda nake ta rawar jiki kafin tace “Wai saurin me ki ke haka ne Mariya? Me zakiyi da wannan ruwan? ’ , ' “Wanka” Na bata amSa a takaice ‘ Umma ta ce, “Wanka kuma bacin wanda kika yi da rana?” na amsa Ba tare da na kalle ta ba nace zan Kara ne Umma, Maman su Bilkice tace in shirya in raka ta dubiya, Kaninta bai da lafia” Umma ta ce “Dubiyar ce kuma Mariya har sai an yi mata wani ado sai ka ce wanda zashi gidan biki?” ‘ “Yo Umma a‘i kamar gidan bikin ne ldan kinfa san gidansu gidan‘ yan gayu ne”. INa maganar tare da kinkimar bokitin ruwana na nufi bayi ba tare da na tsaya na saurari abin da za ta ce ba, Umma taja numfashi ta ci gaba da abin da ta ke. “ Kafin a yi sallar magriba na gama, Shiryawa tsaf cikin sabon yadin bambalasta wanda aka yi min dan doguwar riga mai ' .hade da zani sun sha aikin surfani, yadin mai kalar jinin kare, duk daba wata kwalliya aka" iya ba a lokacin amma na yi kyau sosai Dan daman can ‘kyakkyawa ce, fara“ ce tas; ‘yar siririya kamarke Saudat,saidai ninafiki manyan idanuwa, ga gashina har baya baki sidik ya yi min saje a gewayen fuska, kina kallona kin ga kyakkyawar bafulatana ‘ , Na zaro gyalena na flto tsakar gida a lokacin Ummana tana kicin tana tuqin tuwo na leka kicin din tare da fadar. ‘ “Umma na tafi,sai na dawo” . ta amsa Itama a lokacin ma hayaki ya ishe ta,don k0 waigowa ba ta yi ba ta ce min, “A dawo lafiya, kada ai dare”. Na amsa mata da, “To Umma” . . Na nufi hanyar fita, qanwa ta Zuwaira ta taso za ta biyo ni na haurar da ita ina. ji tana kuka nayi gaba abina, don a lokacin Wasu » masallatan har sun gama sallah. : Ina fita nayi karo da Yaya Sani ya dawo daga kasuwa, ya watsa min harara, “Gidan uban wa zaki?” ‘ . . Na dabarbarce ina in ’ina, sannan na samu na fada masa, “Raki.. .ya zanayi, kuma ‘Ummama tasani" ,, "‘ Yayi tsaki ba tare daya sake kulaniba “ ya yi cikin gida abinsa. [1/30, 9:54 PM] I love my mum: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚 [12:17PM, 02/02/2017] 🙆🏼‍♂@lh@ji🙆🏼‍♂: [9:59PM, 1/30/2017] A Dboy: *YAR TALLA* BOOK 3 *CHAPTER 25* Na saki qafa don kar ya fito ma ya ’hango ni na san halinsa sarai, bai da kirki don bacin yan kirkin na kansa na san da da bugu zai maida ni gida, na saki qafa na zagayo ta' bayan gidanmu tun daga nesa na hango Bala zaune saman wani dan kututturen ice yana jirana Na karaso da sallamata tare da' gaisha shi, ya mike tsaye yana amsa min da fara’a a ‘fuskarsa ya bani wurin da' yake na zauna shi kuma ya tsaya daga tsaye yana fadar. ' “Sannunki da zuwa mai kyau, da ma ’ .zuciyata ta ba ni kina hanya”. ' * “ Na yi murmushi kawai ba tare dana tanka masa ba * Bala ya ‘ce, “A gaskiya Mariya abin da yasa na ce kizi nan saboda mu tattauna wata magana ne, kin ga dai kun yi interview, result kawai ku ke jira yanzu kin kammala firamare dinki ya kamata a zo a tsayar da maganar“ auremnu haka nan, ni dai na fara gajiya, , mahaifina har yamin maganar auren da kansa, : . tunda bakin gwargwado dai kin san inada sana,a kuma zan iya, rike ki da ita ke bama keba, ko' mata. hudu zan iya riKeWa don haka ban ga amfanin zaman haka ba, k0 ya kika ce?" . Na dan yi jim ina dan nazari, ni kaina zan so auren fiye da zama haka duk da ban san me ye qunshe a cikin auren ba, amma ina sonsa musamman da masoyina Bala. Na dago a hankali ba tare dana bari mun yi ido hudu ba na soma magana. “To amma ai ka san Yaya Sani ya fada maka karatu zan yi, kuma duka gidanmu so suke ma idan na gama sakandire in wuce makarantar asibiti" Bala ya katse ni ta hanyar fadar, “Assha! Asshaii Haba Mariya da hankalinki' yanzu saiki barikinaji kinagani aturaki wani karatu to idan kin gama karatun sai wa ya aure ki? Kin san dai yadda masu karatun nan ke tsufa ba sa samun masu aurensu sai tsaffin, Alhazawa. Gaskiya kiyi tunani da kyau Mariya,don yadda ki keda kyan nan da siga , ‘ kyanki aure kawai, amma Wallahi idan aka tura ki karatu an kashe ki, kuma an wargaza " miki rayuwa”. ‘ Ni dai na yi sukuti ina saurarensa, bayaninsa na shiga ta ta ko’ ina, ban ankara ba sai dai na ji saukar kara a jikina, na zabura na zabga ihu. Yaya Sani ya cukwikwuyo gyale na kamar wata Akuya ya shiga zabga tada karan a hannunsa ina ihu har sai da ya karkarye a jikina. Bala ya‘ rud‘e ya shiga riqe shi yana magiya, Yaya Sani ya dago a fusace, “Sakar ni mutumin banza idan ka sake rike ni wallahi za ka, ga abin da zai faru, munafuki, maciyi amana, yanzu ashe har za ka iya taimaka wa wurin lalata tarbiyyar qanwata? To Allah ya isa amma ka sani babu ni babu kai har abada, kuma wallahi idan na Kara ganinka da ita hukuma ce za ta raba mu. Ke kuma mu je gidan zakici ubanki yau”. Ya ja ni kamar wata Akuya yana duka tun saman hanya har muka iso gida. Ya wurga ni gaban Umma, ta zabura ta rike ni da hanzarinta tana fadar, “Me ye haka : kai kuma ka keyi, ba ka da hankali ne?" . ’ Yaya Sani ya soma magana cikin tsananin Bacin rai, “Umma yarinyar nan Sai kinsa mata ido, lalacewa za ta yi wallahi, Umma yanzu wai har ta san ta shirya taje su hadu dasaurayi ta debi gyale ta same shi don tana‘ yar iskar yarinya?" _ " Umma ta dauki sallallami cike da firgici tace “Ana ka gansu dan nan?” ' ‘ ’“a bayan gida na gansu ita da Bala dan gidan Malam Nata’ala mai tumaki, tana zaune suna zace” . “Yau na shiga uku ni Binta, yanzu abin ‘_fada ki ke son kija mana ne a gari Mariya? Ina ‘ganinki sumu-sumu ashe kin iya munafurci . to ?’ Tasa kafata haureni, “Matsakibani. wuri munafuka. Da kayi mata dukan mutuwa inji uban da ya aike ta wurinsa, kuma Babanku na dawowa kamar bisa kunnensa akayi, yan sai na ga ta iskanci” . ‘ Haka Umma ta sa Yaya Sani ya yi min jan bugu kamar zai kashe ni, tana kallo ta sa masa ido, sai dai saukina guda ba a fada wa Babe ba, don nasan idan shi ne wataqila sai ya nakasani,amma dukda haka na bugu. ga shi Umma ta. juya. ' min baya, ba ruwanta dani, bata kula ni, bata tankamin dan idan natanka matama bata‘ Amsawa, ta cire sanya ni aiki, hatta girki ta daina sani nayi ke na shiga tashin hankali, , fushin Umma ta ya qara jefani cikin damuwa amma dukda haka banmantada Balaba a zuciyata har, kullum burina in fita . in ganshi, amma abin ya ci tura, an daina aikena,. ’makarantar allon ma ba a barina zuwa, ga shi makarantar bokon bahu‘ muna jiran sakamako ‘Kwatsam ranar asabar ina kwance a daki da yamma, Ummana ta dago labule, “Ke tashi ki shirya ki tafi makarantar allo”. ‘ Tana rufe bakinta ta saki labulen ta_ yi gaba abinta. Wani dadi ya kama ni, na buga wani uban tsalle ‘yau zan ga masoyina, na nufi Kuryar daki na dauko hijabina da alkur’ani mai ‘girma, na zura takalmina na yi gaba “‘Amma abin haushin ban ga Bala ba wurin daWowa ma har ta qofar gidansu na biyo, amma ban ganshi ba Haka na dawo gida raina a Bace, ina ‘ “ dawowa kuma na iske wani bakin labari, Yaya Sani ya sama min makarantar kwana. Hankalina ya yi maSifar tashi don kuwa yanzu na cire zuciyata da karatu, aura kawai nake so, na shige daki kamar maitakaba inaji anata lissafin abubuwan da za a siya min, ni dai jinsu kawai nake,amma nasan saidai akai waniba dai Mariya ba. Da daddare na kasa haquri ji nake kamar zuciyata za ta tarwatse, da kyar na samu bacci ya dauke ni. Abin haushi kuma ba mu daina haduwa da Bala ba, sai dai abu kamar wasa na ga an fara yi min siye-siye katan din indomie, kwalayen madam, gwangwanayen ldii, comtlex, busasshen dambu da na fura da garin ‘ rogo, tuwon ruwa da sauran dai abincin ‘Ni dai kallonsu kawai nake ban san abin da ake ciki ba, sai da na ji rade-rade cikin satin nan za a kai ni makaranta, ai k0 kamar na taka rawar hauka don ranar da kaina na shirya da daddare najé har gidan su Bala na aika yaro ya kira min shi, na yi sa’a kuwa yana nan. Ya fito da zumudinsa yana fadar, “Da ‘ ma yanzu nake shirin na fito duk ma yadda za a yi mu hadu da ké mu hadu". , . Na gyara tsayuwata ina kallonsa, murya ' ta a raunane na soma magana,‘ “Ka san ina cikin matsala Yaya Sani makaranta zai kai ni bodin wallahi ’ ' Ya tsaya da sauri yana kallona hankalinsa a tashe kafin ya ce kuma Mariya, ke kuma sai ki ka ce yaya?" Na ce, “Ni dai wallahi ban so, amma ban kai ga fada wa kowa ba”. Bala ya dan ja numfashi kafin ya ce “Ai wannan wauta ce Mariya, inda kina son kasancewarmu a tare sai ki cire kunya da tsoro ki'flto fili ki fada abin da ke zuciyarki, na san dai babu mai izawa a sa ki wannan karatun sai Yaya Sani duk shi ne ke da abin, kuma shi ke iza Umma, amma nasan ai Baba ba zaiqi goya miki baya ba”. Na dan yi jim ina saurarensa, ina juya maganganunsa a zuciyata, can ba hango Yaya Sani da wasu abokansa sun nufo inda muke. _ Tun kafin na ida tunanin abin yi na ga Lawwali abokin Yaya Sani ya kwaso da gudu da ya kafa ya kwashe Bala ya fadi qasa. Ai ban san iokacin da na kwasa da gudu ba, Yaya Sani ya kwaso ya biyo ni muka yi gida, ina shiga soro na yi karo da Baba yana ' shirin fitowa, ya rirrike ni yana fadar, “Ku tsaya, kyale ta kar ka sake ka buge ta, ai shi kangararren yaro duka ba ya shiryar da shi sai dai addu’a, inda kun sanar da ni wannan labarin tun wuri da ba a kai haka ba, kyale ta kawai. Wuce ki shiga ciki”. Ya sake ni na shige gida. Kai tsaye na wuce zan shiga dakin Ummata ta tsaida ni, “Tsaya kar ki sake ki shigar min daki, ki zauna nan don ban hada shirgina da karyar maza zauna nan”. Sunan da Umma ta kira ni da shi yafi komai tarwatsa min zuciya, na ja na tsaya jikin bango ina mazurai. Yaya Sani ya shigo yana kallona, kallo mai cike da tsana, ya ja tsaki. ‘ “Kin dai ji haushi, sakarya jakkar yarinya wadda ba ta san abin da ta ke ba. Wallahi ji nake na tsane ki, kuma idan har ba ki sauya hali ba, ba za mu taBa shiryawa ba, kin kuma daura aure da wahala wallahi”. Umma ta ja tsaki kafin ta ce, “Hmmn! In dai maza ne ai gata nan ga su nan, wallahi in dai a karatun maza ne yarinya za su biya miki iya yadda kanki zai iya dauka, kar ka so ka tona zuciya ta kaji yadda ta ke zogi da har ban son in waiwayo in kalli yarinyar nan, duk duk ki rasa ma yaron da zai hure miki kunne sai Bala? Da ma can ni yaron bai kwanta min ba, na tsane shi ban sonshi wallahi". Yaya Sani yace, “Al shi ke nan yau sai ya gane kurensa, don Lawwali a yau sai ya nakasa shi”. Yana fadar nakasa na ji tamkar ya soka min mashi a Kahon zuciya, ai ban san lokacin da na fasa wani ihu ba na durqushe a gurin na hau birgima. Ran Yaya Sani ya yi masifar Baci ya yo kaina da itacensa ya fara dukana. Wallahi Saudat ban san lokacin da bakina ya bude na hau surfa masa zagi ba, kira nake,’ “Allah ya isa wallahi ban yafe ba, ai da ma na san ba ka qaunata, kuma karatun ban yi, tattara kayana zan yi wallahi in bi shi”. Mamaki da takaici su suka hadu suka sa Yaya Sani ya tsaya da dukana yana kallona inda Umma ta hau sallallami harda kukanta tana fadar, “Yanzu Mariya saboda wannan dan iskan ki ke bude baki kina zagin dan uwanki haka? Yau na shiga uku ni Binta, Mariya idan ba ki kwashe kayanki kin bi yaron an ba kin raina Allah da ya halicce ki, ki tafi kibi shi, ni dai in har ina raye baki isa ki auri yaron nan Idan kikaga kin aureshi saidai in bana numfashi,mutuka yarinya” ., ’ ' Saudat abu wasa-wasa har dare ya tsala sosai sannan mahaifina ya dawo,naji yana fadin wa Umma wai wurin mahaifin Bala ya je ya samu bayanan. , Umma ta ce, “To idan ka same shi me zaka ce masa Malam.” Ya ce, ,“Babu ruwanki, na riga na gama yanke hukunci, kibar ni kawai”. Umma ta ce “To barka Malam”. Haushi ya kama ni ban ji hukuncin da Baba ya yanke ba, amma na kwana da shirin ,gari na wayewa zan tattara kayana in bar gidan, a wautata a amma da hauka irin ta zuciyar data kamu daso. Kiran sallar farko Saudat a kan kunena akayishi ba wani bacci na yi ba,gyangyadi ne kawai, na lallaBa na tashi na d'auko biro da takarda na rubuta wa Bala wasika zan tafi garin “ Kano ta dabo tumbin giwa yaro k0 da me ka zo an fika zan sauka tasha in zauna in jira shi na gama rubutun na’ lunke takarda na lallaBa na shiga. dakin Umma» can _ cikin; quryarta don a lokacin ita tana dakin Baba, na dauko buhun kayana na Ciro kudin da Bala ke ba ni na Kirga naira dubu biyar ce wadda a lokacin ta kai darajar dubu hamsin a yanzu. Dadi ya kashe ni na dauki hijabina na saka na rage kayan cikin buhuna don in iya dauka, sannan na kinkima na fito, babu wanda ya gan ni har zauren gidan, dana sararaf na .zare na budr na fice abina. Garin tsit sai mutane jefi-jefi, sauqin abin ma hasken asuba ya fara na kwasa da qafa har bakin titi, na tsaida mashin ledis na hau na tafi tasha da ni na yi sa’a kuwa na samu mota ta kusa cika, sai dai abin takaici, ina qokarin shiga motar na ji ana kwallo min kira, na waigo in ga mai kiran nawa, Kawu Ummaru ne shaf na manta da yana zuwa tasha saida Kuli-kuli. Na ji tamkar in zunduma da gudu ya Karaso yana fadar, “Ina. zuwa_ da wannan kinkimeman buhun haka na ga kina qoqarin shiga motar Kano?” ‘ Kin san marar gaskiya k0 cikin ruwa sai . ya yi gumi yake ga shi dama ni can ba ma'abociyar Karya bace ban ma iya ta ba, nayi tsuru-tsuru ina muzurai. Sai naga ya kamo hannuna yana fadar, “Wuce mu je gidan, mu tafi maza”. Na turje na sa masakuka, hankalin kawu ya tashi ya tsaya yana kallona kafin yace -“Lafiyarki kuwa?” ' Da wautata na sanar da shi gudu zan yi don an Ki aurar min da Bala, kin ji wauta‘ fa wai ni duk a sona na son ya bar ni in shiga' mota in tafl, na ji karan motar na. fad'ar, “Kano saura daya! Kano saura daya! !” [9:59PM, 1/30/2017] A Dboy: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚 [12:17PM, 02/02/2017] 🙆🏼‍♂@lh@ji🙆🏼‍♂: [1/30, 10:00 PM] I love my mum: *YAR TALLA* BOOK 3 *CHAPTER 26* Da wautata na sanar da shi gudu zan yi don an Ki aurar min da Bala, kin ji wauta fa wai ni duk a sona na son ya bar ni in shiga mota in tafi, na ji karan motar na fadar, “Kano saura daya! Kano saura daya! !” Kawu ya shiga. lallashina tare da yi min alqawarin shi zai tsaya min a yi min auren, haka ya rarrashe ni ya zaunar dani cikin kasuwar ya gama saida kulinsa, a lokacin hat rana ta fito sannan yazo muka hau mashina « muka dawo gida. , A lokacin da muka iso gida karfe sha , daya na safe ta wuce muna shiga gida muka same su hankali tashe an zagaye garin ana nemana hankali a tashe; Muna shiga Kawu ya basu labarin komai Baba ya shiga godiya, shi kuwa Yay'a Sani da haushi ya kashe shi bacin yawon da ya ci na nemana, ‘ saks kafa yayi ya fice yanajin zuciyarsa tamkar zata fashe saboda tsabar takaici Babama yasa kai yayi tafiyarshi da kawu‘ Ummaru suna jajanta lamarin, Ummata kuwa wadda takaici ya kashe zuba min idanuwa ta yi tsawon lokaci tana kallona kafin ta hau fadar, ‘ “Uhum, qalu innalillahi yanzu mariya abinda kika zabarwakanki kenan? Ke yanzu harkinsan kitattara kaya kibi namiji Mariya yanzu har Bala ya iya hure miki kunne ke nan k0? Dame muka rageki agidannan meki ka nema ki ka rasa?” Na zumburo baki kafin inyi maganardata tunzura Umma. “Yo abin da abinfa aka hana ni in banda Bala?" Umma ta watsa min harara kafin tace, "Balan banza da wafi, Bala har sa an aurenki ne in bacin kina hauka, yaron da k0 sakandire baiyiba, firamaren ma bai kammala ba”. ‘ Na dauke kai ina fad‘ar *‘Ai dai ya iya karatu da rubutu”. , Haushi ya kashe Umma ta wawuro takalmin qafarta tajefoni da shi tana fadar. . ‘Tashi ki bani wuri ‘yar iska mara kunya zan ga ta tsaurin ido wallahi duk Dan duk, duniyar nan babu uban da ya isa ya aura miki shi in dai ina raye, sai fa idan gudduwa zakiyi, to wannan fa! Amma wallahi baki aurensa”. Haushi ya kama ni jin ikirarin da Umma ke yi, cikin takaici tunanin yadda za a iya hana ni auren Bala lallai kau ba a isa ba, kin ji fa .. wauta da sakarci. Ashe abin da ba mu sani ba Baba yana cab kai tsaye gidan su Bala ya nufa ya yi sa’a ya iske mahaifinsa zaune saman tabarma a qofar gida suka gaisa, Baba ya ce “Da ma jiya na z0 ba ka nan, to da ma ba wata magana bace ' maganar danka ne Bala, nasan ba ka san abin da dake faruwa ba. , Bukatata a nan ni dai daya ce, don Allah ka aika a kira makwaftanka guda biyu suzo‘ yanzu ina son mu daura auren Mariya ‘yata da danka Bala ammafa kayi haquri nazomaka da magana haka gagab, akwai abin da na hango mana ne wanda da ni da kai duka ba zamu ji dadinsa ba, don na san ba kasan danka na zuwa wurin yata ba, kamar yadda ni ma ban > san tana fitowa ‘wurinsa' ba, amma yanzu tunda Dan na gani da idona to mafi alkhairin abin shine a ' " halasta musu juna tun kafin su aikata abinda bai kamata ba Malam Maimmaki 'ya 'zuba a fuskarshi idanunsa cike da mamaki kafin yace ‘Wallahl tallahi ban san abin da ke farawa, amma don Allah ka yi haquri, ka masa hankalinka mu ‘zo mu yi abin nan a tsanake Bala dai danka ne, kuma Mariya ma yata ce Baba ya ce, “A’a Malam kar mu‘yi haka da kai, ka taimaka min don Allah don Annabi ka kira makwaftanka su zama shaidu in sauke nauyin da ke kaina Malam Maitumaki ya ce, “A‘a ai gaggawa aikin shaidan né, kuma aure dole sauda’ sadaki”.Baba ya ce “Ga Wannan naira dubu biyar ce na biya masa ‘ Malam Mai tumaki Ya bude baki zai yi magana Baba ya tsaida shi da hannu yana fadar, “Don Allah kar ‘ka ce komai ka yi fatan alkhairi kawai": yace To “Allah ya saka da alkhairi Babaya ce:“Amin" Daga nan aka aika kiran makwabtansu : ' biyu suka hadu da Baba da Kawu Ummaru da mahaifin Bala aka daura mana aura a kan ‘sadaki naira dubu biyar sannan kowa ya watsé. ’ Baba ya dawo gida a lokacin ina daki ina tisa buhun kayana a gaba na rafsa -uban tagumi, na ji an Kwallo min kira, na kwaso da sauri na fito jin murya Baba. .. Ina zuwa na ganshi tsaye a tsakar gida, tun kafin in Karaso ya ce, “Kama koma ki dauko hijabinki ki fito mu tafi Na danyi jim ina kalonsa ya dan daga murya, “Na ce kizo mu je k0?” Na juya da sauri na koma daki na dauko ‘gyalena na fito, Umma ta dube shi tana fadar, “Inazakada ita Malam ?” Ba tare da ya dube ta ba ya ce, . “Gidanta”' Umma ta ce, “Ban fahince ka ba Malam”. Ya wai go yana kallonta kafin ya ce “Gidan aurenta zan kai ta an d’aura aurenta ‘ ~ ' yanzu ita da Bala, ga ma sadakinta '* Ya mika min kudin ~ Dukda tsaurin idona da tashen balagar tauntsayen dake kaina saidanaji gabanaya fadi namika hannu dakyar nakarbi kudinda ya mikomin na saurara abinkamar almara, Umma tahau Sallalalami hardakwallanta tana fadar Yau na shiga uku ni Binta, yanzu Malam bintakan maganarkayi kadauramata auren?" ‘ Baba ya watsa mata wani kallo kafin yace,"sokike ingirketa agidan ina kallonta taje ta jajibo mana abin kunya a gari k0 me?” , Umma ta qara rushewa da kuka, ‘Wayyo Allahna shi kenan ta faru ta Kare, kin samu abindakikeso,amma wallahi tallahiki sani bada yawunaba wannan aurenkuma wallahi kar ki sake ko a hanya ki nuna kin taba haduwa da mai kamannina, babu ni habu ke har abada”. ' Baba ya ce,"‘Ka ji zancen banza, ke da zakiyi mata addu'a kuma saiki hauyimata mugun alkaba’i? ai ke da ita sai dai fatan alkhairi yanzu tunda kin samu kin rabu da ita lafiya , . Umma wadda takaici da bakin ciki ke cin zuciyarta ta duqa ta suri Zuwaira ta yi gaba tana fadar “Ai kuma sai dai ka yi da wani ba dai Binta ba” Ta yi gaba tana sharar kwallarta. . Baba ya ce, “Ke taso mu je kinji”. Ni kuwa na mike cike da farin. ciki da dokin yau na samu abin da nake so. Muna ' ,zuwa qofar gida muka hadu da Yaya Sani ya rako a guje ya ja ya tsaya kamar zai fada Wa Baba yana ta faman haki Baba ya dube shi. ‘ “Kai kuma lafiyarka?” Yana faman shessheka ya hau fadar, “Wai da gaske Baba an daura wa Mariya aure ,da Bala?" Baba ya ce “Eh an daura mata, wani abu ne?" * Idon da na kura wa Yaya Sani yasa na tabbatar da duk‘wata lakka ta jikinsa ta tsaya da , idonsa ya ciko da kwalla, muryarsa a“ ‘ sanyaye ya ce, “Amma Baba bai kamata a. Bawa Bala auren Mariya ba, don bai biyo ta ‘ hanyar da ta dace ba wurin neman aurenta . Baba. Mariya yarinya ce mai kwakwalwa da . haZaKa irinta gwamnati ke nema don daukar dawainiyar karatunsu don taimaka wa yan uwansu mata, musamman a bangaren asibiti Baba Bala bai dace da Mariya ba don bai san muhinmancin karatun boko ba, asalima ba shi da abin gaba daya wuce . Baba ya nisa kafin ya ce, “Nafika sanin haka Sani, amma kada ka manta wacce ka ke ’ son ka yi yaqi don inganta rayuwar tata ba ta san kana yi ba, ba ta da wannan‘ butin, ra’ayinta daya aure, shin me zai sa mu tauye. mata hakkin? Kana tunanin idan naKi aurar da ita Allah va zai kama ni ba? Wallahi Kin yi mata auren nan Sani sai ya zame min abin ' bibiya a gobe qiyama, shin ka ga laifina don na sauke amanarAllaha a kaina ?‘ " Yaya Sani ya girgiza kai wanda hakan ya yi daidai da zubar tarin hawayen da suka Cika kwarmin idanuwansa, ya juya ya shige gida ba tare da ya ce min Kala ba, sai a lokacin zuciyata ta dan karye kadan na bi Baba muka ““tafi zarai-zarai daganisai shi, har zuwagidan "“su Bala Kinji fa wata kai amarya a nan bahu .‘yan rakiya duk da a addinance hakan yana da kyau. Muna zuwa gidan su Bala Baba ya yi sallama da Babansa, ya mika masa ni. Mahaifinsa ya ce ai Bala yana ciki bari a kirawo shi yanzu ya dawo daga kasuwa. Ya shiga sai ga shi ya dawo shi da Balan, ya zube gaban Baba yana faman godiya. Baba yace, “Ya isa haka Bala, ai ba ni za ka gode mawa ba, ka gode wa Allah kawai, don'Shi Ya‘ ba ka Mariya, don haka ga ta nan amana a wurinka, ka sani idan ka zalunce ta k0 ka ha'ince ta don kana ganin kamar sadaka ce a wurinka sai Allah ya kama ka, ni dai nauyi ne da Allah ya dora min, kuma ba mutane ba kawai hattamala’iku sun shaida na sauke don haka na barku lafiya”. Bala ya hau godiya shi da mahaifinsa, Baba ya juya ya yi tafiyarsa ya barmu, mahaifin Bala ma ya juyo kanmu ya yi mana nasiha sosai, sannan ya ce ya je ya gyara mana dakinsa mu zauna. ' Haka ya juya ya nufi cikin gidan, na bi Shi a baya ina kallon gidan don ban taBa shigowa ba saboda babu mace a cikin gidan, mahaifiyar Bala tun yana dan shekara sha' ~biyar ta‘ rasu, kuma mahaifinsa bai Kara aure ‘ba saboda ya. tsufa sosau, girma ya kama shi,‘ ‘ ' don lokacin da aka haifi Bale. ma har ya cire rai . da haihuwar a duniya sai ga shi Allah ya azurta shi‘ da Bala, daga shi kuma bai sake ba ‘ Allah ya yi wa mahaiflyar tasa rasuwa. ‘ Gidan ginin kasa ne, amma bai sha jiki sosai ba, yana dauke da dakuna uku, daya na mahaifin Bala, daya na Balan, daya kuma na ajiye~ajiyensu, sai qaton tsakar gida shareren gaske wanda aka raba biyu ana kiwo a cikinsa, sai qaton iccen bedi a tsakiyar gidan mai malalan kasa don babu sumunti. ' Bala ya tura kyauren dakinsa ya juyo yana min alama da na shiga, kamar kar na shiga har sai da ya sake yi min magana sannan na daure na sa qafa na shiga cikin dakin, ba wani mai girma ba ne sosai, yana dauke da katifar maza wadda aka lullube da bargo sai dan karamin tebur wanda aka dora wata ‘yar qaramar talabijin da bidiyo a sama. Shi ke nan abin da ke dakin, sai ‘yar hanga ta katako wadda aka sargafe kaya sannan ‘kafet din da ya mamaye dakin, wanda ya ci uwar quta. Kin san abinki da samari bazaki taba tabbatar da tsabtar saurayiba saikinga dakinsa lol (gayu a. ganku a .titi kar a ganku a masaukinki Saudat in takaice miki haka na zauna dakin nan na gyara shi tas-tas kamar ba shi ba, washegari Bala ya fita kasuwa ya yi mana siye-siye, tun daga kayan abinci har zuwa na sawa irin wanda za mu bukata. Da kayan shafa wanka, turaren wuta, sabbin labulaye, karamar radiyo, Saudat haka Bala ya dawo da kaya niqi-niki don a lokacin yana samun kudi sosai saboda tun daga Dandagoro har zuwa cikin unguwarmu babu wanda ke saida kayan koli sai shi, don haka yake samun kudi sosai. Sannu a hankali lokaci ya shiga tafiya Saudat ina ganin , soyayya, qauna da kulawa fiye da yadda ba ki zato, hatta mahaifinsa idan ya tafi kasuwa ya dawo da kunShin nama na. A haka harna samu ciki, irin mai masifar laulayin nan kamar ba na kai ba, amma daga gidanmu babu wanda ya leko ya ga ya nake, da Bala ya je ma Yaya Sani wulakanci ya yi masa, don haka ya dawo gida cike da takaici, ya fada wa mahaifinsa shi ne shi kuma ya ba shi shawara da ya je ya dauko diyar Qanwar mahaifiyarsa Laure wadda aurenta ya mutu ta ke zaune gida: ” ' Bala ya amince saboda jin jikin da ‘ nake, ban iya yi wa kaina komai bane 'haka ya tafi ya dauko min Laure, aka gyara mata dayan dakin ta zauna. Laure ita ke kula dani, duk wata dawainiya tawa ita ke min, tana gefe tana kallonmu ni da mijina duk abin da nake so shi yakemin inamai ’ tabbatar miki babu abin da' zai hana a kawo‘ shi. ’ Idan kuwa na ce ina son abu jikinsa har rawa yake ya je ya samo min k0 a ina, da ya shigo ya rinka tambayar Laure ya nake, ya jikina da sauqi dai k0? Na ci abinci k0 ban ci ‘ ba? Idantaceban cibaba hakazai zauna yatusa ni agabayana rarrashi kamar zaiyi kuka har ya sai ya samu na ci, haka mahaifinsa idan ya tafi kasuwa siyo min wannan kawo min wannan, ke na ga gata da soyayya. A haka Saudat ciki ya cika wata biyar na huta da laulayi a lokacin ne kuma naje gida ni da. Bala, amma Umma k0 kallonmu ba ta yi ba ita da Yaya Sani suka watsar da mu a makar gida sai Zuwira ce wadda ta fara taflya ta tattako ta maqalqale ni na rungume ta ina jin SOyayyarta a zuciyata donni a wautata” wai gani nake ita kadai ce ke sona, ba ta guje : niba, haka na qaraci zamana na tashi muka dawo “ gida ba mu ma tsaya Baba ya zoba . ‘ Wulakancin da aka yi mana ya yi wa Bala ciwo, haka ya yi ta maimaitawa ni dai Ina jinsa ban tanka ba, don idan da zai tona tawa .zuciyar na san da ya tabbatar tafi tasa hawa da jin zafi, ni a ganina k0 don kyau da sauyawar da na yi yasa Umma bata saurare muba don ta' tabbatar Bala yana sona sutturar kanta dana naje gidan tsadarta ta kau dubu goma a lokacin kuwa dubu goma ba nan ba ce, kayan ' dubu goma sai dai dan wane da wane, amma hakan bai sa Umma ta duba qokarinsa ba ni kaina ta san ai na canza don na yi dumurdumur da ni, haske na ya Kara. fitowa na zama kamar wata. baturiya saboda kyau, ba yadda muka iya dole nena share na manta, sai dai Bala ‘ bai .mance ba don duk lokacin da na ce masa zan' je gida sai ya ce ban 'zuwa ba yadda zan yi . a haka nazo na haihu, babu wanda yazo ta Bangarena gidanmu, sai dai Babana daya zo har gida ya ga ' jariri ya yi masa addu‘a, ya bani ‘dubu biyu da niki niqin kaya sannan ya tafi, daga shikuwa k0 kare bai ce komai ba. ‘ Sai dai Laure ceke dawainiya da ni ita ke dora min sanwar ruwan zafi safe da yamma ’ta kwashe ta kai min kewaye ta yi wa jariri wanka, ta yi girkin abinci a gaskiya a lokacin ta yi dawainiya kodayake ta saba da wahala tunda a can gidansu wankau ta ke na kudi da surfani. A kwana a tashi har na yaye Rabi’ u, ban Kara zuwa gida ba, a ganina tunda sun Kini ni ma na manta da ~su kin ji wauta fa, ' haka rayuwa ta ci gaba da tafiya tamkar bani da ‘ iyaye a garin, saboda Bala ya bar min Laure ita ke min komai na hidimar gidana iyakata ni dai inwanka nida dana mutafi wurin maigida. ~ , Ashe abindaban saniba Laure tana nan tana jin haushinmu kamar ya kashe ta ni k0 sakaran ban taBa sani ba, don ban yi zaton za ta iya jin haushinmu ba, saboda yadda nake ' ‘ kyautata mata ni da maigidana. . Lokaci na tafiya ban sake haihuwa ba a tsawon shekara bakwai a lokacin ne kuma mahaifina ya rasu, to a nan ne na dan yi hankali na dauki dana muka tafi gidanmu na zauna a can har sai da aka yi sadakar uku duk yadda Ummana ke shasshare ni sai data tanka min duk da ba wata maganar arziki ba ce muka yi, anagama sadaka na tattara na koma gidana, to a nan fa labari ya sauya don ban sani ba ashe na bar baya da qura, haka kawai na ga Laure na min wani kallo-kallo, ga shi shi kuma uban gayyar ya hau shasshare ni da na yi masa magana sai ya hau ni da fad'a dana yi laifl da ban yi ba duk daya wai an yi wa tuwo Barin miya. Abin duniya duk ya dame ni ya ishe ni, ga shi ba ni da wanda zan fada wa matsala ta, a haka dai na yi ta hakuri ga shi a lokacin ban san na samu cikinki ba, sai da laulayi ya matsa min, amma Bala ko a jikinsa ya watsar da mu ba-ya kula mu ni da dana balle abin da ke cikina. Rayuwa duk ta dagule min, na zauna na zama wata kalar tausayi, kin san halin da mace ke shiga idan miji ya juya mata baya abin ba dadi, sai dai in qule daki in yi jugum. Ban“ taBa mantawa da ran Wata laraba ba ina zaune a daki shiru ' Laure bata ,kawo mana abinci ba ga shi k0 abun karyawar ‘ da ta yi mana da safe, ban samu cinsa ba nan na’bar wa Rabi’u ya yi ta wasada shi ’har wurin uku na rana babu abinci babu dalilinsa‘ A dole na takarqare na mike na fice shiga kicin din, sai dai abin da na gani sai da ya so tarwatsa min zuciya, na na tsaya turus ina kallon Laure wadda ta zabga uban goho ta takarkare tana ta faman barbada magani a kwanon miyar Bala, ban tanka mata ba har sai ' da ta gama barbade-barbadenta tas! Ta kawo cokali ta jujjuya miyar ta maida ta rufe, ta mike tana boye maganin a habar zaninta. Muka yi ido hudu, a take jikinta ya hau rawa ‘ tana faman karkarwa can kuma ta ja tsaki ta rabA ta wuce ta barni tsaye da. mamaki a zuciya. ; Can na girgiza kai na dauki kwanon miyar na fito na zubar ’da ita, da ma miyar danyar kubewa ce na dawo na zauna da' kaina na takarkare na sake dora wata miyar' ta busasshiyar kucewa na yi na gama na debi * nawa na ajiye masa nasa da kyar na samu na ; tuttura abincin ama zuciyata tamkar za ta tarwatse. Bayan la’asar Bala ya dawo. daga kasuwa tun kafin in fito kuma ta riga ni fitowa ta tare shi ta shimfida masa tabarma jikinta na rawa ta tafi ta kawo masa abincinsa da ruwan randa masu sanyi cikin kwanon sha. A lokacin ni kuma na fito na tsaya daga bakin qofa ina kallon ikon Allah, Bala ya ja kwanon miya ke nan ya bude suka yi ido hudu da miyar busassiyar kubewa ya yi sa‘uriin dago kai yana kallon Laure. “Wannan miyar kuma fa? Ba ni na ba da danyar' kuBewa ba nace a kawo miki ba, k0 ba a kawo ba?” Laure ta karya kai cike da kisisima kafin tace, “To ai ‘yan ba ni na iya yau :su suka ' dauki miyar suka zubar suka shirya tasu ta musamman”. Bala ya yi saurin dago kai yana kallona. , “Ban gane kin zubar da miya ba, kan wane dalili?" Jikina ya yi matukar yin sanyi ganinyadda ya zaburo min na daure na durqusa ‘ gabansa muryata a sanyaye :nace kayi Mai gida bari nayi ban sani ba Shi ya‘ sa na sake maka wata, amma ina neman wata alfarma a taimaka a maido girkin gidan nan wurina”. . . Bala ya zaburo, “Ke gafara can rufe min baki, ki dai ce wani mugun halin kika tsiro da shi, kuma wallahi ba zan dauka ba, ba ma zan laminta ba, tsabar almubazarannci kawai ki dauki abinci ki zubar saboda ba ke ke nemowa ba k0?” Zuciyata ta kara ganin yadda Bala ya hau ya ke ta zuga min masifa haka, idona ya kawo kwalla na mike cikin kuka ina fadar, “Allah ya ba ka hakuri Na juya na shige dakina na barsu. Ban san abin da suka kitSa ba, da zai fita ya . hankado labulen dakin ya leqo ya wurgo min dari daya, “Ga shi nan sai ki yi cefane a dafa taliya da daddawa, da ma nasan dan sauran na samab kike mawa, to ga shi nan sai ki dauka kiyita zubin adashe". ‘ Ya juya ya yi gaba abinsa'ya barta ‘ tana tattauna maganganunsa a bakinta iya, haka na mike na ta Karkare duk da bana jin qarfin jikina na dora sanwar taliyar, na [1/30, 10:00 PM] I love my mum: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚 [12:17PM, 02/02/2017] 🙆🏼‍♂@lh@ji🙆🏼‍♂: [10:59AM, 2/1/2017] 🅰 " 🅰" D"🅱🅾Y: *YAR TALLA* BOOK 3 *CHAPTER 27* gama na dibi tawa da ta dana na dibar masa nasa na zuba na mahaifinsa na kai masa, sauran kuma na barshi a tukunya. Na yi gaba abuna, amma abin takaici da ya dawo na ce masa ga abincinsa, sai ‘cemin ya yi ya Koshi ya . ci abinci a waje. Haushi kamar ya kashr ni, amma babu yadda na iya haka na hakura na yi kwanciya ta na barshi zaune yana wasu ‘yan bincike- binciken na gaira babu dalili. Washegari ma bai tsaya karyawa ba ina kicin ina hada mana abin karyawa ya sa qafa ya fice abinsa ya ajiye min kudin cefanen rana. Ai ban san lokacin da na fadi qasa ba ina kuka wiwi na shiga uku yau na Mace. Babu mai rarrashina don babu ma Wanda yasan ina yi, na karanci kukana na share hawayen na mike na nufi katifa na raBa inda Rabi’u yake kwance yana sharar baccinsa na ' kwanta, na rufe idanuwana duk daba bacci nake ba, haka na dauki tsawon lokaci ba tare * dana bude ido ba balle in kalli abin karyawar ‘ dana hada. Ba Rabi’u ya farka daga baccinsa ya dauki abincinsa yana ci, ina jinsa ban kula ta kansa ba sai kusan sha biyu saura sannan na mike Ina rarrashin kaina na dauki kudin cefanen na aiki Rabi’u ya siyo min kayan miya da sauran kayan girki na zo na zauna na dora sanwar jalof din shinkafa da wake da alayyahu da kifi. Zuciyata ta yi ta tashi saboda qarnin Dan sau biyu ina rugawa bakin maguji ina kwaraya amai, amma haka na daure na kulle hancina da kallabina nayi girkin na gama, wani irin ciwon kai mai zaf1 da juwa suka sauko min, na nufi dakina na kwanta k0 motsin kirki na kasa, ga Rabi’u sai kwaramniya yake min' a dakin yana wasansa.‘ Bala bai tashi shigowa gidan ba sai ana' . sallar maguriba, nayi kuka har nji ba dadi, amma yana shigowa haka na daure na dauki abincinsa na je na kai masa. K0 lura ya yi da rashin walwalata da alamun na sha kuka kuma, na ga ya bude kwanon , abincin ya sa cokali ya debo ya kai bakinsa, , idona na kansa na ga ya Bata' fuska tare da furzar da abincin bakinsa a tsakar dakina ransa a bace ya hau masifa “Ke wannan wane irin iskanci ne? bakin. buhun gishirin kubce miki ya yi ki ka kwaraya shi a ciki k0 ko me?” , Da mamaki a fuska ta na maimaita, “Gishiri kuma?” Don ni na sani a girkina ma babu ‘gishiri k0 kadan saboda‘ magin da na zuba yana da yawa, Bala ya zaburo min. Sai kizo ki kwashe abinki”. Na mike jikina a sanyaye na durqusa gabansa na sa ‘cokali na debi abincin na kai bakina, ai sai dai na ji tamkar zan mutu lokacin da na hadiye, saboda azababben gishirin da ke ciki, zuciyata ta karanta min makarkashiyar da . ' aka yi min. Na daure na dago da kai muryata a sanyaye nace “Ka yi hakuri don Allah, wallahi hannuna ne ya kubce, amma bari yanzu in fora maka wani abun mai sauKi”.‘ . Ya kwatsa min tsawa. “Ke tashi nan ki ba ni wuri,nizaki kawo wa feleke saboda bakin ciki, amma daga yau kin gama girki a gidan nan don na lura da wasu halayen banza da kike bullowa da su kwanan nan kuma kr za ki sha wahala wallahi , don‘Laure dai ‘yar uwata ce, kuma ke ba ki isa ki shiga tsakanina da ‘yar uwata ba, wallahi”. ‘ Ya mike yana karo da kayan abincin ya fice yabarni nan a tsugunne. " ‘ Kwallar da ta cika min idanuwa ta soma zurarowa, wato ba zai iya rabuwa da yar ’ uwarsa ba saboda ni, amma ni na rabu da nawa ; ‘yan uwan da iyayen saboda shi? Wayyo Allah ga ni gare Ka. Na kife a gurin ina wani irin kuka, sai yau na fara yin nadamar da‘ bazaimin amfani, ba na yi kaico a rayuwata da son da ya rufe min ido. ' Yau na yi kuka kamar zan mutu, bani da mai rarrashina, har Rabi’u wanda ke bacci ‘ ya farka ya taso ya rungume ni, shi ma ya saka nasa kukan, a dole nayi shiru naja shi a jikina ina rarrashinsa. ~ ‘ Saudat al’ amuran suka ida cakudewa na. rasa wanda zan kai wa kukana, ina ji ina gani Bala zai dawo gidan ya shige dakin Laure su. sha hirarsu sai na yi bacci sannan ya shigo ya raBa ya kwanta ba ni da bakin magana kuma , Ga shi Laure ta daina girki da wuri sai yamma, don ta san Bala ba ya dawowa da wuri duk na bi na tsumbure na rame na lalace na fige abinki ga mai ciki. Bala’in Bala ya ishe ni, ga yunwa na je na same shi ina kuka, nace ya fada min laifin da na yi masa; Ai k0 ‘ranar kamar ya hadiye ni ’ danya ban dahu ba, don kadan ta hana ya kawo min duka, haka na tashi ina kuka. Na ' kasa haquri na tafi wurin mahaifinsa ina kuka na fada masa duk abin da ake min a gidan, ransaya yi masifar Baci, don a lokacin shi ya dawo zaure ya bar mana gidan. Ai k0 a take ya tisa ni gaba muka shiga cikin gidan, yace in wuce dakina ya nufi dakin Laure ya ce maza ta tattara kayanta ta ‘tafi gida,aishi bai sa adaukota donta tarwatsa zaman lafiyar ma’aurata ba. Ina jin Laure na ba shi hakuri, amma ya ce ina! Sai ta tafi, yana tsaye ta hado ‘yan komatsanta ya ba ta kudin mashin ta yi gaba a lokacin kar kiso ki tona‘ zuciyata ki ga farin ciki, don ni a ganina annoba ta tafi. To ashe an kashe maciji ne amma fa ba a sarekanba. Don Bala na dawowa ya leka dakinta ya ga ba ta nan, ya leqo wurina. * “Ke Ina. Laure ta take?” Gabana ya fadi yadda na ga fuskarsa ba annuri amma na dake na ce. “Kaje ka tambayi Baba” _ ‘ Fuuu' Ya Wuce ba tare da ya sake kula ni ba, ni dai na bi keyarsa da kallo, a zuciyata ina addu’ar Allah ya daidaita tsakanina da 'mijina, kominti gomada fita baiyiba saiga ‘shi ya dawo kamar an hankado shi, ya tsaya a kaina yana zazzaga min. “To marar mutunci, munafuka wadda bata qaunar zumuncin Allah, wato ‘yar uwar .tawa yanzu saida kikasa aka koretadaga gidannan? Tokinyi daidai amma inasoki sani wallahi ba baki isa ki raba ni da‘ yan uwana ba, don ke kina ganin kin rabu da naki" yan uwanbaki isaba, babu macen data isa taraba ‘ nida ‘yan uwana wallahi baki isaba”. ‘ Ya juya fuuu ya sake ficewa daga gidan gabadaya. Saudat duniyar ta yi min zafi, rayuwar ta quntata a gare ni, na yi kuka har kaina ya dauki ciwo, amma babu mai rar-rashing ga ciki a jikina. Abin duniya ya yi min yawa Bala ba ya shigowa gida sai na kwanta kuma kafin in tashi zai kakkaBe rigarsa ya bar gidan, ya ajiye min naira ashirin kudin cefanen miya ga shi a gidan babu abin da ya rage sai masara, haka zani wanketa inbada aniko mana inyituwon kwaha biyu, sai dai in canza miya. Amma shi k0 jikinsa don ba ci yake ba, sai dai mu ci ni da dana, don mahaifinsa ma yanzu fura kawai yaké iya sha, ba ya cin duk wani abu mai nauyi saboda ciwonsa don haka shi ma bai san abin da ake ciki ba. . Wataranar juma’ a ina zaune a dakina bayan ‘“ na gama sallar isha’i ina karatun alkur‘ani mai girma, na ji shigowar Bala, abin ya ba ni mamaki lokacin da na ga ya shigo dakin ya zauna bakin katifa. i" Na tsaya da karatun da nake na shafa addu’ata sannan na waiwayo na gaishe shi ya 'amsa fuska ba yabo ba fallasa na mike a sanyaye da niyyar in kawo masa ruwan randa mai sanyi da abinci ya tsaida ni ta hanyar fadar * “Tsaya meza ki kuma?” Na dan waiwayo na kalle shi murya ta a sanyaye nace. “Abinci zan kawo maka”. Ya girgiza kai. “A a a qoshe nake, zauna ki huta abinki”. Wani irin abu ya nusar min zuciya. idona ya ciko da hawaye na koma na zauna tare da janye kwallar da ta ziraro a kuncina, Bala ya ce. “Magana nake son yi da ke Mariya idan kina da lokaci” Ba tare da na dago na kalle shi ba, na ce “Ina sauraranka” Ya muskuta ya gyara zama kafin ya fara dogon bayaninsa ‘Mariya, kin dai san iya so na soki a duniya, kuma har yanzu ba wai daina sonki na yiba, don haka inaso kiwa abinda Zanfada kyakkyawan kallo da kuma kyakkyawar * fahimta kikuma bani hadin kai idan harkina son zamanmu lafiya, don yanzu maganar nan . da ake mun gama magana da Laure, zan auro ta za a daura mana aure nan da sati mai zuwa, har sadaki na ,ba’ ta don haka na yanke shawarar zuwa in fada muku keda‘ Baba dA fatan ba za a samu matsala daga wajenki ba , ‘A lokacin ji na yi kamar yana caccaka min wuka a zuciya, idona ya canza kala, wani irin tukukin bakinciki ya sarkemin na mike a harzuke jikina har bari yake kamar wata‘ yar dambe na fara magana kuka ya Kwace min, amma ban fasa ba “Lallai Bala kun cika maciya amana, yanzu don cin amana duk ka rasa wadda za ka aura a duniya sai Laure? Wallahi ka cuce ni ka yaudare ni, ka raba ni da dangina da ‘yan uwana kuma Allah sai ya saka min Ban ida rufe baki ba na ji saukar wani gigitaccen mari a kuncina wanda ya sa har sai da na duke, ya nuna ni da dan yatsansa. ‘ “Kenan harkin isaki zageni banza, Kenan harkin‘isa hanani yin abin da bayi niyya? To ba ki isa ba, aure k0 ki so k0 kada ki so yinsa za a. yi kin ji na fada miki”. Ya juya a zafafe ya bar dakin, ya bar ni tsugunne rungume da kunci' na. ma rasa a ' duniyar’ da nake ranar maganar kuka ma babu ita, don idanuwana sun kekashe ga shi 'ba damar in tafi gidanmu don na san Umma ba ma saurarena za ta yi ba Abin Allah sai ga shi yana zuwa wurin Baba ya hau shi da fada har yana kumfar baki ya ce ba da yawunsa ba, bai amince da wannan auren ba. Bala ya yi juyin duniyar Baba ya haqi yaddah, a dole ya haqura don ba yaddai zai yi. Sai dai zamana da Bala babu abin da ya canza don sai ma ya dauki gaba da ni, yadda ki ka san ni .na hana auren k0 gaishe shi na yi ba ya amsawa, duk na bi na gigice na rame ga ciki ya fara girma amma rayuwa sai a hankali, ni da Rabi’u muna fuskantar quncin rayuwa. A haka har cikina yazo ya tsufa na haife Ki a wannan karon Ummana ta zo ita da Yaya * Sani, hakan ya tabbatar min da sun fara saukowa da ni. Ummana ta ba ni kyautar kaya niqi-niki, shi kuma Yaya Sani ya yi min kyautat kudi dubu biyar a nan ne na samu labarin ya samu Aiki a cikin birni a babban banki first bank har ya yi auransa a can na yi masa murna sosai. Sun dade sannan suka tafi, amma na lura sun dan fahinci halin da nake a ciki, domin Bala bai siya wa jaririya k0 hankici ba Babu kaya a jikinta cikin zanina na qudundune ta, data ce ina kayanta ‘nace Bala ya; tafi ya ’siyo yanzun nan. Ta hau fada haihuwa tun jiya amma ace ba a tanadi kayanda za a sawa yaro ba, babu k0 sabon dan goyo saboda sakarci? Ta Ciro riga guda cikin kayan da ta kawo min mai tsada ta saka wa jaririyar Ranar suna kuwa Saudat na sha kuka har na gode wa Allah, don Bala bai yanka rago ba abincin suna ma masara kawai ya bari tiya biyar ya kama gabansa, . har yamma babu labarinsa. Na ci kuka har na gode wa Allah don nasan abin gori ne a gari a ce ba a yanka wa yarinya rago ba. Haka na ciri dubu uku da dari biyar cikin kudin da Yaya Sani ya ba ni na bada aka siyo min madaidaicin dan taure aka yanka, sai a‘ lokacin mahaifin Bala yasan ba a yi yanka ba, ya yi fada har ya gode wa Allah ya Ciro kudi daga cikin aljihunsa ya bada aka siyo tikekiyar tunkiya aka hada aka yanka da yamman nan likis gab da magruba. Bala bai dawo gida ba sai qarfe sha dayan dare mahaifinsa ya yi masa tatas har ’ yace zai iya tsine masa a kaina. Shi dai hakuri _kawai ya ba da ya shigo gidan ya qare min tanadi da wulaqanci. . Da safe kuwa sai cewa ya yi abin yanka biyu ya yi min yawa ni da wa ban san yadda aka yi ba, ashe ya sabe tunkiyar ya fice da shi ya kai wa Laure. Ya barni da dan tauren Ke Saudat na ga bakin cikin rayuwa don a lokacin ji na yi tamkar in hadiyi zuciya in mutu k0 daidai da rana daya Bala bai taBa .. cewa a kawo ki ya ganki ha, inda na samu sauki ma mahaifinsa don ya nuna maki so kamar ya had‘iye ki, duk da kina' Jaririya amma » da ke yake zama a kofar gida sai idan kin yi ?fitsari ko kuka yace akawoki abaki kisha minti goma kuma zai sake aikowa a kawo ki * ga yayanki Rabi’u wanda zance tamkar shi aka * haifa mawa don da Baba ya aiko a“dauke ki zai biku idan za adawo dake tare dashi haka idan za a sake fita, wannan ne ya dan rage min ‘ radadin da ke damuna. Ga shi Umma na min aike yanzu akai‘ akai tana aiko Zuwaira kanwata wadda a lokacin ta fara zama budurwa, shekararta goma tana aiko min ita da‘ yan abubuwan bukata k0 _ ‘yan kudi don a lokacin Umma tana samun "kudi sosai wurin Yaya Sani ya tsare musu .komai “ . Kwatsam mahafin Bala Allah yamai rasuwa mutuwar‘da ta daga min hankali a lokacin kina da wata 'biyu, na ji mutuwar Baba fiye da~ yadda na ji ta mahaifina aka zo aka yi sadakar uku kowa ya watse. Ranar da aka yi arba’in Saudat, ~a washegari aka daura wa Bala aure da Laure, a . ranar‘kuma aka yi mata jere ta tare. Bani da labari sai dai na ga jama’a na ta shigowa ana jejjera kaya ban tambaya ba har suka gama suka tafi da daddare na ji gudar ‘yan kawo amarya a lokacin zuciyata ta tabbatar. min da abin da nake zargi na shige dakina na yi kuka ~ har na ji babu dadi, na share hawayena na ci gaba da hidimomina a cikin gidan Ummana da ta samu labari aiken kudi ta yi min masu yawa ta ce in ja jari in rinka sana’a saboda zama hakan ba zai min ba. Kin ji uwa mai dadi. ‘ Yaya Sani kuma ya zo garin da kansa yasa aka yi min sabbin kayan daki masu kyau da tsada, wanda ko na amaryar ba zasu kama kafar nawa ba don da ma kin san ba a yi min kayan dakiba, dan uwa mai dadi Nan fa kishi ya Balle Laure da habaice’ habaice har tana fadar, wai Yaya Sani sun” Samu labarin tsafi yake a birbi, kin jifa! Ba ka da damar da arziqi zai sameka yanzu ance yankan kaikake, nidaibankula ta ba hidima ta da yarana kawai nake Ga shi har a lokacin Bala bai damu da ni ba balle ‘ya’yana sai ma ta kai ta kawo ba ni da girki a cikin gidan, kullum ita ke sanwa, . kuma ita ke kwana da miji, suka bi suka hade min kai abincin da zan ci ma aka daina ba ni, da na yi wa Bala magana ya hau ni da fada wai bai riKe ni ba, idan ba zab iya ba ga hanya nan shi ba zai iya ba, ai yana da labarin idan an ba .ni abinci zubarwa nake wai ni mai dan uwa, mai kudi, to in zauna dan uwan yaci da ni. Haka ya qaraci Kankancinsa ya yi tafiyarsa. . Na shiga rudani ga ‘yan kudin da ke hannuna duk na cinyesu a ranar haka muka wuni, washegari ne da na ga yunwa na neman kashe mu a dole na mike na sabi ‘yata na goya na kamo Rabi’u na kullo dakina na leka ~ _nafada wa Laure zan je gida don Allah idan ‘Bala'ya dawo ta fada masa, na ba ta makullin dakin. , Ta amsa a daKile n muka tafi, ina tafe juwa tamkar za ta kayar dani DanivSaboda yunwa, ga Rabi’u na ta kukan zaici abinci duk da kuwa da girmansa don'. yana dan shekara takwas a lokacin Kai tsaye gidan Umma muka nufa a yanayinta ya tabbatar min da ta ji dadin zuwan namu,n2a kuma yardar wa kaina ta yafe min ' laifina a yanzu sai dai da alama tana min kallon tausayi. ' ' A gidan mun ci mun sha, kamar cikinmu zai Bule. Muka yi sa’ a Umma ta gyara kaji guda shidda na zauna na soya mata su ta dibar mana kusan rabi da kwalayen lemuka masu "yawa da ledar kayan marmari, haka muka dawo gida niqi-niqi da naira dubu ta abin 'hawa. Muka dawo gida wajajen magriba ban 'samu kowa a tsakar gidan ba,‘ ‘ na leqa dakin Laure na karBi makullina na bude muka shiga na ajiye niKi-niqin ledojin naje na dauro alwala na dawo nayi sallah sannan na zauna na baje kayan Ina cicciro wadanda zasu lalace. Da wuri Na ji an hankad'o labule na tsaya ina kallonsa, ya shigo dakin yana faman muzurai, na gayar da shi amma bai amsa ba, don haka ni 1 page is missing Ya runtse idonsa yana maimaita innalillahi Wa’inna ‘ilaihi raji’un, ya bude ,su _sun kada sun yi jajawur muryarsa na rawa ya ‘ soma fadar, “Da ma an dade ana gaya min halinki amma ban taba yarda ba, sai yau da na ga zahiri ba zan ce miki komai ba Mariya ki je ke da Allah, ba zan ce miki komai ba”. Ya juya ya fice tamkar zai fafi a Kasa tunda na sadda kaina qas'a ban iya dagowa ba, zuciyata ce ke ta faman kai kawo tamkar za ta fasa kirjina ta fito fili, babu abin da nake maimaitawa sai innalillahi daga qarshe kuma sai na kife kaina a qasa na sa wani irin kuka mai ban tausayi. Rabi’u da ke .zaune kusa dani ya sa hannu ' “Mama ki tashi ki yi shiru . ’ Da dai ya ga ban da niyyar yin shirun shi ma sai ya kifa kansa a kaina yasa nasa kukan. , Tsawon lokaci muna a haka babu mai tada wani sai da'na gaji don kaina na ji kaina ya fara bugawa alamar ciwon kai ne zai sauko min, na lallaba na mike na kinkimi dana na dora kan gado, ni ma na kwanta a gefen Keko kina ta sharar baccinki muka rinka. sauke ajiyar ‘ Zuciya a tare har bacci Barawo ya sure Rabi’u amma ni idona babu alamar bacci a cikinsa yadda naga rana haka na ga dare. ’ Washe gari haka na tashi jiki ba kuzari' zuciyata ta yi min masifar nauyi koba a auna ni ba ina da tabbacin jinina ya hau saboda yadda kaina ke wani irin masifar ciwo ga juwa ga nauyin kirji duk dai alamun mai hawan jini. Ga lamarin ba sauqi don sai‘na ce ma gara jiya da yau don bala’in na yau ya fi na jiya tashin hankalin yanzu ya linka na yau dan na fuskanci wulakanci da cin mutunci da muzanta ‘ a lokacin nan don bar sai da na gwammace dama ba a halicce ni a duniya ba. : ~ Ga ciWo ya zoya tiso ni gaba kamar zan mutu daga ni sai dana Rabi’u muke jinyar, shi “ke yi min komai daidai da shiga kewaye sai na dafa shi, ya kai ni har bakin qofa, amma‘ Bala bai taba yi min sannu ba balle ya ce mu je ya kai ni asibiti, bala" in ciwo ya ishe ni a lokacin ne na rinqa ba wa Rabi u nasiha a kan ya kula da rayuwarki k0 bayan raina don ni na riga na. gama. hango mutuwata kararafa na tsumbure gabadaya babu ruwa a jikina balle wadataccen. jini, ciwo ya ishe ni a jiki Saudat na hango mutuwa karara a dole na aika wa Ummata ta zo da kanta ta sa aka kai ni asibiti aka kwantar da ni 'waii ina dauke da ciwon zuciya mai tsanani, kuma ba ni da jini da ruwan a jiki a kalla ma ina buqatar Jini leda shidda da Karin ruwa leda takwas ba musu aka kara min. . Kwanana goma a asibiti aka sallamo ni amma Bala ,sau daya‘ya zo ya ganni shi ma a tsaitsaye don ko' zama bai yi ba nairarsa bai ~, bayar ba, haka ya zo ya yi tafiyarsa abinsa. ' Ummana ta ji haushi sosai har ta yanke shawarar ba zan koma gidansa ba ta wuce dani gida. Kwanana daya kuma ta tattara ni ta maida ni 'gidana tare da siye-siyen madarar yara mai yawan gaske da su saralak, biskit, kifin gwangwani da sauransu, tace in yaye ki haka nan zan fi samun Karfin jikina. A lokacin kina da shekara daya da watabiyar aka yaye ki, a lokacin ne kuma Laure ta haihu, ta haifi yarta mace aka sa mata suna iKilima Ranar suna an sha bidiri rago biyu aka ' yanka, an sha kidan kwarya ranar kamar za a tada‘ gidan ni dai ina géfe na zama "yar kallo. don k0 karabiti ban kai ba . Bayan sati daya da yin suna ina kwance a dakina da daddare misalin qarfe hudu na asuba na rinka jiyo maganar Laure da ‘Bala a tsakar gida tana fadar “ ' “Wallahi maigida da idona na ganshi ya ' shiga dakinta, k0 kewayen ban shiga ba na fito”. ‘ Bala yace, “Shiru ba ni toch light din in hashaska da kaina”. _ Gabana na ji ya yi wata mummunar faduwa. don na fahinci bako muka yi a gidan (Barawo) ban ida tsurewa ba sai da na ji ana laluben qofata ai ko na firgita na tashi na koma can quryar gadona ina faman rawar jiki, gabana ya sake yankewa ya fadi' lokacin da na ga an haske ni da fitila na takure a cikin tsananin firgici .‘ ‘ Me zan gani? Wani shirgegen qato ne kwance a kan gadon nawa ta gefenki yana ta sharar bacci Bala na haske shi ya zabura ya ya rarumi rigarsa yana fadar “Mariya sai anjima” ‘Ya fita a guje ya hankade Bala da ke shirin riqe shi har ya fadi. Ya mike ya kuma bi shi, Saudat ba zan iya misalta miki irin tashin hankalin dana shiga ba a lokacin, musamman da Laure ta sa ihu tana kiran makota su .zo an kama kwartuwa ranar na ga tashin hankali da idona. . Kan ki ce me gidan ya cika da jama’a ana ta kallona, wasu na zagina suna Allah ya tsine wasu na jifa ta da takalma a Kofar gida kuma matasa sun taru‘suna jiran na fito a jefe ni k0 su cinna Wa gidan wuta, Saudat ranar na shiga halin ha’u’la’i har gari ya waye tangaram mutane ba su bar gidanmu ba‘ sai ma Kara taruwa ake ’ Ana haka wani mummunan labari yazo min wai matasan unguwar sun je sun kunna wa gidanmu wuta, wayyo Allah na ai na kusa , shidewa a wurin, ni kuka ‘ya’yana yayyaBe da ni‘su ma suna yi. ‘ A haka mai unguwa ya shigo gidan namu shi da bataliyar ‘yan sanda tare da Yaya Sani da kuma Bala a bayansu nan fa jama’a suka! hau « gudu mai unguwa ya durqusa gabana yana fadar. ' “Mariya ina so mu yi magana ‘da ke tsakaninki da Allah ki fada mana saboda kin ga dai yadda komai ya tarwatse so muke mu yi wa rayuwarki adalci don yanzu haka “matasa sun kunna wa gidanku wuta, ga mahaifiyarki har qanwarki babu wanda aka fidda da rai, kin ji aikin jahiliyya, don haka ki ji tsoron Allah ki sani idan kin fadi qarya k0 gaskiya duniyar ta riga ta zo karshe a wurinki, muna so ki mana rantsuwa a kan randa kika fara neman, maza, kuma ki rantse ‘ya’yan nan na Bala ne~ Dacin zuciya da tashin hankali su suka tsayar da kukan da nake labarin -mutuwar Ummana yafi komai tarwatsa min zuciya, na riqaa girgiza kai kamar wata marar ,hankali don gaskiya a lokacin ban da bamhanci da mahaukaciya. ’ ‘ Mai unguwa ya ce, “Ba kada kai muka sa ki ba, rantsuwa ce zan fada ki maimaita idan . har kin san kina bisa gaskiyarki". Na yi shiry ina kallonsu daya bayan daya, kamar ‘yar mage Rabi'u na tsugune a gefe rungume da ke, yana kallonmu ya ci kuka har ya gaji.‘ Mai unguwa ya ce, “Ki je ki dauro alwala”. _ .Ba musu na je na dauro alwalar na dawo, ya miqo min alkur’ani izifi sittin na karba na tashi tsaye' na daura a kaina, na mike na yi yadda ya ce, ya karanto min rantsuwa ya ce in maimaita, na rinka maimaitawa ina rantsuwaa kan ban taba sanin wani namiji bayan Bala ba, kuma ‘ya’yana nasa ne, idan na taBa Allah ya tarwatsa ni, Ya halaka ni, Ya wargaza rayuwa ta, Ya yi rugu-rugu dani, Ya sa kar na gama lafiya, Ya hana ni ganin annabin rahama, kuma Yasa in tashi tare da fir auna, ina yi suna kabbara har na maimaita sau uku. Mai unguwa ya juya ya dubi Bala. “To kai ma kana da ja? Idan har kana da ja to kai ma za ka rantse“ kamar yadda kayi a ' kan‘ ya ’ya ba naka bs ne, idan har ka rantse to za a bar mata yaran nata saita nemi ubansu”. . Bala ya sunkuyar da kai zuciyarsa na' Kuna yadda yake jin ya tsane ni haka yakejin ya tsani ”yaran, amma k0 da wai bai Jin zai " .iya rantsuwar saboda girman hadarinta,don haka muryarsa a sanyaye ya ce “A’a Allah ya Rara’ laiiya, a gaskiya ni “ ba zan rantse ba, na dai san ‘ya’ya ba nawa bane, ban da haufi amma tunda al’amarin yaxo , ~da haka na karbe su, amma ita kam ban iya ci gaba da zama da ita, don haka na sake ta saki uku”. . ' . ‘ Yaya Sani ya bude baki da kyar da muryarsa wadda ta dusashe ya ce. “Tashi mu je Mariya” Na yunkura na mike na kamo hannun yarana, Yaya Sani ya ce , “Wadannan nan za ki barsu ai ba da su ki ka zoba” A take na durkushe a gurin na fasa wani uban gunjin kuka na rungumesu wayyo yarana. ' Yaya Sani ya fincikoni a fusace ina ihu ina komai haka ya bamBare ni daga jikin .yarana yana jana wani yaro ya fado gidan a. gigice ya fadi gaban Bala yana fadar YallaBai kasuwa ta kama da wuta tun jiya ‘ da daddare ta ke ci, har yanzu ba ta mutu ba, shagonka ya qone kurmus, ba a fidda ko haki ba”. Bala ya dora hannuwa bisa kai yana neman ,tai‘makon Ubangiji. Yaya Sani k0 kallonsa bai yiba ballantana -ya jajanta masa ya ja ni muka bar gidan ina ihun A, haka muka bar gidan wanda ban qara taka shi ba har yau, da ma tuni motar ambulance ta kwashe su Ummana a nan birni aka rufe su ranar na yi kuka’ kamar zan mutu. Haka naci gaba da zama gidan Yaya Sani wanda ke zaune a Kwangiwa road shi da matarsa Fadila a sannanne na ci gaba da karatuna har na tafi na yi doctoring degree dine. a A. B. U Zaria, ina cikin karatun ne na hadu da Abban Nabil a Saudiya na je aikin hajji, yana da mata guda da ‘ya ’yansa biyar muka daidaita, na aure shi. Ina gidansa na kammala karatuna shi ya samar min aiki a Medical Céntcr Hospital da ke nan Katsina, da yake nan ya ajiye “ni shi kuma yana aiki a babban bankin Abuja, uwargidansa ma tana can. Yana zuwa duk Week da iyayensa ma ‘yan asalin nan ne Kankia, yanzu haka ina da yara kwara biyu, Nabil da Nabila sai ‘yar aikina Mairo, sai direba sai kuma maigadi mu kadai ne a gidan nan". Saudat ta lumshc idanuwanta wadanda ta kejin sun cicciko da hawaye, lallai mahaifinta ya aikata babban kuskure wanda ita kanta ba ta jin za ta iya yafe masa, ya. gallaza musu bacin ‘gallazawar da ya yi wa mahaifiyarsu, lallai dole mahaifiyarta ta manta da su don ta ma daina ganin laifinta Lol to jama,a munji lbr malam bala da uwargidansa maria Kuci gada da biyoni don xamu koma tsundum cikin asarin lbr [10:59AM, 2/1/2017] 🅰 " 🅰" D"🅱🅾Y: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚 [12:17PM, 02/02/2017] 🙆🏼‍♂@lh@ji🙆🏼‍♂: YAR. TALLA. QARSHEN BOOK3 CHAPTER28 Doctor Mariya ta rungumo Saudat a jikinta hawaye cike da idonta, ta ce “Ki yi hakuri Saudat, ku yafe min, wallahi ban watsar da ku ba don son zuciyata,ba sai don kawai ba yadda zan yi, amma yanzu na yi miki ' alkawarin zan ba ki duk wata kulawa ta uwa wadda ki ka rasa a baya”. ' Saudat ta lumshe idanuwanta hawayen da suka cika su suka rinqa zuraro wa cikin sanyayyar muryarta ta amsa da, “To Momy”. Kamar yadda ta ji su Nabila na ce mata. Dr. Mariya ta dan zame jikinta kafin ta ce ’ “Tashi ki sallah kinji ana kiran magriba, ni ma zan'shirya yanzu mu je gidan Yaya Sani, don tuni nayi masa waya ga mu nan zuwa”. . ‘ Saudat ta amsa da to, Dr. Mariya ta mike ta‘ Fice Saude ta raka ta da idanuwanta har ta Bace, wani irin tausayin mahaifiyarta ne ta ke ji, dan a ganinta tafi shiga wahalar rayuwa. " Saudat ta mike ta nufl bandaki ta dauro alwala ’ta fito ta yi sallah, sannan'ta mike ta nufi gaban madubi ta kara gyara fuskarta ta shafa hoda ta goga wa laBBanta man lebe mai danko, sannan ta gyara girarta ta tattada gashin idonta da mascara, ta gyara nadin gyalen kanta sak ta fito tamkar wata cikakkiyar balarabiya. Tana cikin fesa" turare ne a. jikinta Dr. Mariya ta shigo da sallamarta, a yanzu tana sanye ne da dogon hijabi milk kalar atamfar jikinta da makullin mota a hannunta, ta mika wa Saudat wasu fararen takalma flat shoe masu kyau. Saudat ta saka sannan suka jera suka fice, a falo ta hadu da ‘yar‘ aikinsu Mairo dattijuwa wadda ba ta wuce shekaru hamsin ba. Tana ganin 'Saude ta hau gaishe 'ta, kunya ta kama Saudat, ta gaza amsawa sai da ta juyo mata da gaisuwar ta amsa cike da girmamawa sannan ta dubi Dr. Mariya tana fadar. “Amma Hajiya qanwarki ce wannan ko, na ga kamar taku ta yi yawa”. Dr. Mariya ta murmusa kafin ta ce “Mairo ke nan, yanzu nan har kin ga kamarmu?” Mairo ta Kara wangale baki tana fadar. “Sosai ma wallahi Hajiya, har wurin tsawon da basken fatar hancinku ma iri daya ne, ' wallahi sai ace kanwarki ce Dr Mariya ta sa dariya tana fadar. “A’a lallai Mairo idanuwan nan naki har yanzu da Kwarinsu, to ‘yata ce, Yayar su Nabila ce . wadda na baro su kauye ita da yayanta, ai’ina jin‘ na ba ki labarinsu k0?" Mairo ta zabura ta dafo Saudat tana fadar. . Sannu baiwar Allah, ashe zan ganki ban ' mutu ba? Ai ko Hajiya wallahi ga kama nan ita da ‘ Nabil kamar danta ba kaninta ba, Allah sarki”. Dr. Mariya ta yi murmushi da jin sokanar Mairo ta dubi Saude' “Mu je kinji in dai Mairo ce ba ta gajiya sai tasa mu kwana anan”. ~ Nabila ta sarko hannun Saudat tana fadar “Don Allah Aunty zan je” . Kafin ta yi magana Nabil ma ya dafe ta yana fadar. " ' . ‘ ’ " "‘" “Ni ma don Allah Aunty aje dani’_’. Saudat ta yi sukuti tana kallon fararen ; yaran ‘yan shamal-shamal dasu Dr. Mariya ta ce. “Kuyi haquri ba da Wanda za mu je, kuje Mairo ta dauko muku Ice cream a firij”. . . Saudat ta langwaBe kai tana: kallon mahaifiyar tata, ta ce. *« ‘ ‘ “Don Allah Momy a je dasy; Mariya ta yi murmushi tana fadar. Kun ci arzikin Auntynku, oya, muje“ . Suka rungume Saudat suna ‘tsallen '. ~ murna, suka tafi cikin wata qaramar mota. Qirar End Of Discussion sabuwa dal, Dr Mariya ce ke. jan motar Saudat a gidan gaba, sai Nabil da: Nabila a gidan baya. suna ta“ yan tsalle-tsallens u. ‘ Dr Mariya ta dubi Saude kafin ta ce ' “Oyoyo my sister, zomu shiga". Nabila ta dafo ta tana fadar. “Aunty Shukura yau ba za ki dauke ni ba.” Shukura ta janyo hannunta tana fadar. “Yau ba ta ke nake ba Nabila, ta sister na ke ina dan Momy mai qaton kai ~ Nabil 'da ya labe bayanta ya sa dariya ya ruga wurin Dr. Mariya don ya san rankwashinsa za ta yi. A haka suka shiga cikin qaton falon, inda Alhaji Sani yake zaune da matarsa Hajiya Fadila sai Yusuf da Abdulhakim duk qannen Shukura ne; suna shiga Hajiya Fadila ta nufo su da fara’a a fuskarta ta riqo Saudat tana fadar “Taho nan mu gaisa Saudat, sannu kinji” .. Saudat ta yi wani murmushi ta durkusa tana gaishe su, Alhaji Sani ya mika mata hannu yana fadar. " “Zo nan Saudat, z0 in ganki, taho kusa da ni kinji”. ' Saudat ta ja jiki ta har inda yake zaune, ya sa hannu ya dafa kanta yana kallonta cike da . tausayawa ya ce “Allah Sarki, ashe da rabon zaki gana da' mahaifiyarku? Allah Sarki rayuwa kenan yanzu ni k0 za ”a, kashe ‘ni ina zan iya ganin wannan in ce Saudat ce? Ai sai in yi zaton irin bakin larabawan nan ne wa zai ce wannan irin Bala ce?” . Duka falon aka sa dariya‘ ban da Saudat, wadda ta sunkuyar da kanta tana wasa da kwalliyar rigarta. Shukura ta rankwafo ta wuyan Saudat tana fadar.‘ ‘ “Me za,a kawo miki, ’fruit k0 snacks, k0 abu mai nauyi?’ Saudat ta dan saci kallonta tana murmushi, ‘ ta ce. “Komai ki ka kawo . Shukura ta yi wani dan fari da ido, kafin ta mike da kuzarinta Alhaji Sani ya dubi Dr: Mariya yana fadar. “Kin ga abin Allah k0? Ban taba kawo wa a raina yarinyar nan za ta rayu ba, na mafi ganinta ‘ ga shi Rabi’un, saboda kin ga shi namiji ne duk' ‘ inda ya sa gaba zai iya rayuwarsa. Ki dai ci gaba da addu’ a shi ma Allah ya bayyana mana shi”. Dr Mariya ta amsa da, “Amin yaya, amma da kamar wuya, saboda yaron fa korarsa uban ya yi da girmansa”, Alhaji Sani ya ce“Wannan maganar banza . ke nan, ki shirya ku je garin duk inda danki yake' ya fada miki ai ba zai yiwu a uba ya kori da kuma ya ce bai san inda yake ba, ba sai mu yi kararsa ba idan ma sayar da shi ya yi”. Ya dubi Saudat “Amma ai ya barku kun wuce gaba da ‘ sakandire k0?” Saude ta girgiza kanta cike da damuwa, kafin ta ce “Ai ba a ma sa mu makarantar ba” Mamaki, haushi da takaici suka kashe Alhaji Sani sai dai ba yadda zai yi, haka ya hadiye, yanzu a cr kana da kyakkyawar diya kamar Saudat idan ba ka sa ta makaranta ta yi karatuba aikakasheta, kakashekanka. ‘ Shukura ta shimfida tabarmar lambawa ta jets gaban Saudat da kayan ciye~ciye da lashelashe abin harya soma va wa Saudat mamaki. Sai da suka yi da gaske sannan ta iya sakin‘ jikinta suka ci abincin dasu Nabila, basu suka bar gidan ba sai bayan sallar isha, bayan Alhaji Sani da Dr. Mariya sun ajiye magana jibi za ta je har can kauyen da kanta. Shukura ta‘ makale ita ma za ta, Alhaji Sani ya ce duk abin kukai anan zan nemar wa Saudat karatu Dadl ya cika Saudat yadda ta ga manyan mutane sun nuna mata kulawa da soyayya, har kukan dadi tayi a boye, don rashin Yaya Rabi’u kusa; da ita da ta ga irin tasa murnar da farin cikin, shi da ya san Momyn taSu ya zauna da ita, yazo ya ga cikin daular da ta ke Saudat, ta qara juyawa da kwanciyarta saman' lallausan gadon da ya sha shimlidun alfarma, ta kalli gefrnta inda Nabila ke kwance tana sharar baccinta don kuka ta sa ita wurin ' Aunty yau za ta kwana ta bar Nabil tare da Mairo Yau Saudat ta yi bacci mai dad'i da nutsuwa, duk da Dr. Ahmad ya yi wa zuciyarta kane-kane amma hakan bai hana ta bacci mai dadi ba. Washcgari tunda ta yi sallar asuba ta koma ta kwanta, sai da Mairo ta kwankwaso‘ qofa ta dauki Nabila za a yi mata shirin makaranta, tana daukar Nabilar kuma ta maida qofar: ta rufe ta koma ta.yi kwanciyarta. Ba ita. ta farka ba sai qarfe tara daidai na safiya, tana tashi ta nufi bandaki ta watso ruwa ta fito ta maida doguwar rigarta ta yi ‘yar sassaukar kwalliyarta sannan ta zura takalminta ta fito falon gidan. ‘ ‘. Babu kowa a falon sai Mairo da keta faman goge- gogenta, Saudat ta dan duqa ta gaishe ta, Mairo ta amsa cike da girmamawa, Saudat ta zauna gefen kujera muryarta a sanyaye. ta ce “Momy fa?” Mairo ta cc “Tana kicin tana. hada wa Alhaji abin karyawa, jiya ya dawo garin cikin Dare Saudat ta kada mata kai tana saurarenta. ‘ . " Mairo ta ce .“Me za a kawo miki Saudat? Akwai kunun tsamiya da soyayyar doya da kwai, kuma akwai ,farfesun kifi, akwai ruwan tea idan kuma da akwai akin da ki ke so sai ki fada a kawo miki”. ‘ ’Saudat ta 'girgiza kai' kafin ta ce “‘A kawo min doya da kunun‘ tsamiyar Mairo ta amsa da, “An gama”. Sannan ta juya ta nufi kicin, Saudat ta gyara zama ta jingina bayanta da makarin kujerar tana kallon qatuwar talabijin da ke makale a bango tana ta qaraji ita ' kadai. Dr. Mariya ta fito daga kicin ta nufo Saudat tana fad'ar. ‘ ’ “Wai har kin tashi kenan?" Saudat ta yi saurin yunkumwa tana gaishe da mahaiflyar tata, Dr. Mariya ta amsa tana fadar “Jiya da daddare Alhaji ya shigo gari ina kicin ina hada masa abin karyawa, na hada ' muku tare, nasan ai za ki so kici abincin momynki k0?“ ‘ Saudat ta yi dariya tana fadar. “Ina so mana". * ‘ _ Dr Manya ta ce, ““Okey, give me just five minute only” , ‘ '” , Ta juya da. hanZarinta ta bar Saudat na maimaita yaren da mahaifiyar tata ta yi, wanda in za a hadata da wuqa bata San abinda take nufi ba. ta maida hankalinta wurin ' kallonta. . Kamshin sanyayyen turare ne ya daki ‘ hancinta, ta yi saurin daga kai tana kallon mai shigowar, babban mutum ne wanda a kalla shekarunsa za su haura hamsin da biyar baKi ne mai haske, dogo mai kyakkyawar fuska da dan siririn sajensa iya kunne, doguwar jallabiya ce a jikinsa milk colour sabuwa dal mai hade da hularta. ,Suna. hada ido da ,Saudat ya sakar mata ,wani lafiyayyen murmushi, Saudat ta ja jiki tana gaishe shi Ya amsa lokacin da yake zama saman kujerar da ke fuskantarta muryarsa a sake ya ce. “Saudat k0?” Ta daga masa kai alamar eh. , Ya ce “Masha Allahu, matso nan my Saudat, taso matso kusa da ni ‘yata”. Saudat ta ja Kafafuwanta ta matsa inda yake, ya sa hannu ya dafa kanta yana fadar ’ ‘ “Nayi farin cikin ganinki sosai don da ma na yi wa Hajiya magana zamu samu lokaci muje dubo' «ku to ashe ma Allah zai yi ikonSa Allah Alhaji Ashiru yace “Da dai yafi”; . ka ji ‘yan boko ba a maganar islamiyya sai boko, boko, shin ko a gobe qiyama wace irin rawa bokonnan zatataka? ‘ Dr Mariya ta ce, “Mu je ga abin karyawa can saman tebur”. Alhaji Ashiru ya mike yana kallon Saudat,” yace’ “Taso mu je ‘yata mu karya”. Ba musu ta mike saboda yadda Dr Mariya .ta zuba mata. idanuwa, kai tsaye saman kujerun dinning table suka hau suka zauna, Dr Mariya ta zuzzuba musu komai a faranti, ta turawa kowa a gabansa. ne da kwai sai kwallon doya tare da soyayyen dankali, da soyayyar plaintain, ta ‘ hada wa kowa ruwan tea mai kauri ta tura masa, sai qamshin ’ citta yake ‘* » Saudat ta saki ciki tana cin abincin kamar yadda ta ga kowa na yi, jefi jefl har suka kammala Alhaji Ashiru ya mike yana fadar “Bari in shiga daga ciki na dan kwanta na . huta, around 12 saiki tayar dani” . Dr Mariya ta amsa da, “To” Sannan ya juya ya shige ciki ~. Can Dr Mariya ta dago tana kallon Saudat “Wai ya maganar Dr. Ahmad ne Saudat bana ji kin ce ya aiko miki dawata takarda ba a lokacin da ki ka fada masa an daura miki aure ba?” ‘ Saudat ta amsa da, “Eh” . Dr. Mariya ta ce“T0 ina ta ke?" . Saudat ta ce“Tana cikin haBar rigata na kulle a kayan dana cire jiya”. . . Dr. Mariya ta ce “Okay, tashi ki dauko min. Saudat ta mike ta d'auko mata takardar wadda taji dauri duk tayiyaushi Dr.Mariya ta karba. tana dubawa babu komai a saman takardar sai lumbar waya da suna. Dr. Mariya ta dauki wayarta wadda ke ajiye a saman tebur ta lallatsa lambar ta kara a kunne ta kira yakai sau uku amman ba,a daukaba ta tuno aimanya irinsa basa amsa kiran bakuwar number don haka tayi masa rubutacccn sako ta tura K0 minti biyar batayi da tura sakonba akakira Dr. Mariya ta danna' amsakiran sannan tasa a kunnenta tare da fadar. ’ “Assalamu alaikum,‘ barka da wannan lokaci”. Cike da girmamawa Dr. Ahmad ya hau gaisheta tamkar yana gabanta, Dr. Mariya ta amsa ita ma cike da kulawa ta ’ " ‘ “Sunana Dr. Mariya Sani, nice mahaifiyar Saudat nasab za ka yi mamakin kiranka da nayi . Dr Ahmad ya amsa. da, “Haka ne Momy, amma Allah ya sa Saudat din lafiya?” Ta dan yi murmushi kafin ta ce “Sai godiya ga Allah,nakirane dama in maka godiya akan abin alkhairin da kayima Saudat, na gode kwarai Allah ya saka da alkhairi". Dr. Ahmad ya sauke ajiyar zuciya yana fadar “Amin Momy, na gode kwarai wallahi, na kuma ji dadi da ya kasance Saudat ta hadu da mahaifiyarta, wannan yana daga cikin burina a rayuwa, na gode wa Allah". Momy ta ce, “Babu komai ni ke da godiya, ga Saudat din”. Ta miqa wa Saudat kan wayar ta ta mike ta yi gaba abinta. Saudat ta kara wayar a kunnenta, tare da sallama, lokacin da muryarta ta dira kunnen Dr. Ahmad sai da ya zabura ya tashi zaune daga kwanciyar da yake yana fadar. “Saudat kece amin wa 'alaikus salam, daman zan Kara Jin muryarki Saudat harna cire rai, .ya ki ke ya maigidan?” ~' Saudat ta dan ja numfashi kafin ta soma ba Shi labarin duk abubuwan da suka faru, Dr Ahmad ya sauke wani gwauron numfashi kafin yace “Da ma nasan hakan za ta kasance Saudat saboda dama can anyikine donni kadai ketawa cce Saudat ni naki ne insha Allahu, knma zan tabbatar miki da hakan duk abinda. Nake yau sai nazo Katsina, kisaurare ni nanda qarfe biyar na yamma za ki gan ni gidanku. Ba wa Momy wayar ta bani adreshin gidan”. ' Saudat ta amsa da, “To”. Sanan ta mike ta nufi falon da ta ga ta shiga, qaton falo ne mai dauke da kayan alatu na jin dadin rayuwar duniya. Tana zaunc kan kujera da system a Gabanta tana. danne-dannenta,‘ Saudat ta mika wa . Momy wayar ta karBa ya sanar da ita zuwansa ta ba shi adireshin gidan da lambar gidan, saunan ta mike ta nufi Bangaren Alhaji Ashiru ta sanar da shi . Da kanta ta dauki mota ita da Saudat suka shiga kasuwa ta yi siye-siye masu yawa na tsadaddun dogayen riguna, arebiyan dres Indiyan dires riga da siket masu tsadar gaske, sai ' data sai mata kusan kala shida *da tsadaddun ‘ takalma masu kyan gaske, sai kayan shafa da turarruka masu kyau , Daga nan suka wuce gidansu Shukura suka taho da ita saboda gobe zasu tafi qauye a tare, ta ‘dauko dan qaramin akwatinta suka taho. Ba qaramin dadi Saudat tajiba dasuka tahoda Shukura. ‘ Karfe biyar saura Momy ta ga Saudat zaune itada Shukura afalo anata hirar makarata momy ta ‘ zuba mata idanuwa kafin tace “Waike ba bako zakiyibane,bazaki tashi ki shirya ba?” Saudat ta ce, “Shiri kuma Momy? Ai a shirye nake Momy tace“Lallai,to mazaki tashi ki canza wani shirin yanzu ki je ki watso ruwa, ke kuma Shukura ki zaba mata kayan da zata sanya, bari inje kicin'inga idansun kammala aikindana saka su”. Duka suka amsa da, “To Momy”. ~ Ta juya ta fita, Shukura ta dubi Saudat tana fadar. “Kebakicewa bako zaki kika wani tule a ‘nan?Ai wallahi danasani yauda harwurin gyaranjiki zamuda acanza ayimiki makeup Saudat ta waro ido tana fadar “Kai Shukura, me ya kai har da wani Gyaran jiki?“ Shukuratace, “Aukebaki da labarike nan? Saudat yadda hadaddun maza wayayyu masu ajike tsada ai doletun kina agida saikinbi matakan mallake naki saurayin; ‘ ‘ Tun daga kwalliya, daurin kallabi, sa kaya masu kyau, fesa turare mai kamshi, fesa mouth freshner saboda wurin magana. Kashe murya da yin lafuzza masu ma’ana da burgewa, iya jera kalaman soyayya cikin sassanyar murya, iya lallausan kallo cikin kwarewa da kissa, ‘yar zolaya ki zolaye shi cikin sigar wasada dan ba shi dariya kadan a cikin hira da‘ yar shagwaBa cikin sigar jan hankali, da kuma kamun kai a matsayinki na yar mutunci. Wannan sone kadan daga cikin abubuwan dake sawa budurwa ta mallake saurayi, wallahi Saudat da soyayya nake da an sha kallo". Saudat ta yi murmushi kafin tace“To me , yasa ba kiyi?” ’ Shukura ta tabe baki, ta ce “Wallahi Abba ne bai bari ba, amma duk da haka ina dan taBa wa sai dai a waya ne kawai, shi ‘ ma Ummi ba ta sani ba, nasan da ta ci ubana don , har: yanzu ban kammala digiri dina ba fa” . Saudat ta nufi kewaye tana fadar ~ . :‘Ke kima gode wa Allah kin samu an tsaya miki kinyi karatun" -. Ta tuna ita nata ubanda kansa ya hana ta ‘ karatu, yasa‘yar uwarta makaranta tun daga" firamare har sakandire, amma ita bai saka ta ba. ‘ .Ta lumshe idanuwanta a daidai lokacin da ta sakar wa kanta shawer ‘ » Bayan tagamo wankan tafito tasamu har Shukura ta gama fldda mata kayan da za ta saka, * wata hadaddiyar’ doguwar riga ce wadda aka yi wa adon jajayen fulawowi sannan aka jejjera ararcn duwarwatsu a ciki, rigar ta yi masifar kyau irin mai kama mutum ce daga sama daga qasa ta bude sosai tana da dogayen hannuwa irin masu tsukewa daga qasa su ma an qawata su da adon rigar, sai kallabin rigar, Shukura ta hada mata da wani takalmi fari mai dan tsinin dunduniya kadan. Saudat ta zauna tana fadar. “Ke kuma wannan ce ta burge ki?” Shukura ta ce, “Ai ki sa ki gani ba qammin kyau za ta yi miki ba ' Saudat ta zauna bakin madubi tana murza mai a jikinta. . Shukura ta mike tana fadar. ‘ ' “Tsaya ki gani Saudat in miki makeup ” Ba musu Saudat ta zuba mata idanuwa kawai tana kallonta, kwalliya sosai ta yi mata da hodoji da air pencil, air liner, jan baki mascara da ' sauran kayan kwalliya. Ita kanta Saudat tsaye ta yi tana kallon kanta a madubi, ta waigo da fara a a fuskarta tana ' kallon Shukura ta ce “Kai k0 dai kin je makarantari koyon kwalliya ne? ai wannan k0 shago ba za su nuna miki komai ba”. ‘ Shukura ta yi dan'dariya kafin ta ce_ “Ke kuma kin hadu kamar sarauniyar qasar waje Duka suka sa dan'ya, Saudat ta janyo kayan ' za ta sa, Shukura ta ce “Ke tsaya-tsaya". Ta dauko wani sabon turare irin mai laushinnan mai suna soft ta gogamata a dukkanin gabobin jikinta har: zuwa bayan kunne wuya, mara da qirji, sannan ta ce “Sanya kayan". Tana sanyawa ta kawo turaren the warior body Spray ta ba ta ta fesa a can cikin jikinta, sannan ta mika mata turaren x5 ta fesa wa ,kayanta, ta ba ta qananan ‘yan kunne ta makala’ a kunnenta, sannan ta gwada mata irin nadin da za ta yi wa gyalen rigar irin na ‘yan matan jami’a, ita kanta Saudat din ta san ta yi kyau na ban mamaki, don haka ba ta da bukatar wani ya Kara fada mata Shukura ta janyo jakartata ciro mouth freshner mai qamshin water milon ta feffesa mata a baki don Kamshi da dauke datti, ita kanta yau Saudat ba za ta ce ga kalar Kamshin da ta ke ba, tana cikin sa takalmin Dr‘ Mariya ta leko tana fadar. ‘ “KarBi ga waya ana kiranki”. ‘ Saude ta karba ita kuma ta juya ta yi gaba abinta, Dr Ahmad ya ce “Ga ni a qofar gidanku”. Saudat ta cr, “To minti biyu”, ‘ Ta kashe wayar tana kallon Shukura ta ce Yar uwa ga shi a waje”. Shukura ta mike, “Bari in je in shigo miki da shi". Saudat ta ce “Yauwa”. Shukura ta ja qaramin mayafinta ta dora saman kanta, sannan ta fice, tunda Dr. Ahmad ya. hango ta zuciyarsa ta ba shi ‘yar uwarta ce saboda yanayin jilkinsu iri daya ne dogaye duka, amma basu da kwari sosai, suna da doguwar fuska mai dauke da dogon hanci da dan siririn baki, don ita Shukura ma manyan' idanuwa gare ta sosai masu kalar kyau, farare tas~ tas da su, don dai ita baqa ce amma irin bakinnan mai haske wato black beauty kenan, sabanin Saudat dake jajawur kamar a taBa jini ya' fito. Shukura ta hango wata tsadaddiyar mota ' mai kyan gaske, sabuwa dal mai kala da yanayin jirgin sama. Shukura ta ja. ta tsaya don ba ta taBa "ganin irin motar ba tunda ta ke a duniya, ga shi farar motar mai bakin gilashi ce, baka iya ganin * Wanda ke ciki Da hanzari ta ga an bude qofar motar kujera mai zaman banza, wasu mutane su biyu suka fito da hanzarinsu suka bude gidan baya na motar. " ‘ . A hankali yasA qafarsa guda ta fito Qasa sosai, sannan ya sauko da gudar ya fito gaba daya. Shukura ta zuba masa idanuwanta kyakkyawa ne na qarshe, abin da zuciyarta ta fada ke nan, ta nufe shi da nutsuwarta tana fadar. “Sannu da zuwa, ba zaka shigo daga ciki ba?” ’ . Dr. Ahmad ya girgiza mata kai kafin ya ce. “Mata: tana da girma ne sosai motar, ba kowace haraba ba ce za ta isa a yi kwana da ita a ciki ba, muje kawai”. Shukura ta yi gaba, ya rufa mata baya har cikin qawataccen falon, ta yi masa masauki sannan ta wuce kicin ta yi wa Momy magana ta nufi daki ta kirawo Saudat wadda ta yi zaune gaban madubi ta zuba tagumi da hannuwa bibbiyu tana kallon kanta, amma a zahiri zuciyarta ta lula duniyar Dr. Ahmad wai yau gani ta ke abubuwan ‘ suna faruwane kama a cikin mafarki, wai yau ita ce za su hadu da Dr. Ahmad a matsayin masoya to ke bata san lokaCin da tayi wani murmuShi ba, Shukura ta tsaya daga gefenta tana fadar ‘ ‘ ’ “To saiki tashi yana falo”. Saudat ta ji wani irin yarr a jikinta, ta ta miqeta nufi kofa har: za ta fita ta juyo tana kallon Shukura ta ce “Don Allah ki zo ku gaisa". Shukura ta ce, “Ki fara zuwa ina tafe Ba ta sake magana ba ta juya tafice ta same shi a hakince saman daya daga cikin kujerun dake falon, yana latse~latse a wayarsa. Tana shigowa kamshin turarenta ya daki hancinsa, ya dage da sauri yana kallon mai tahowar, suka yi ido hudu. ‘ Saudat ta yi wani murmushi ta juya da sauri ta nufl falou Momy ta fada mata tana nada kallabin jallabiya a kanta, Saudat ta ce “Momy ga shi yazo Tace“Kije yanzu zamu fito da Alhaji sai mu gaisa”. *_ Saudat ta juya ta yi gaba A tsaye ta iske shi a yanzu, ya zuba ‘_ hannaye cikin aljihunsa, Saudat ta Karasa har inda ' yake ta zube saman gwiwoyinta tana fadar. " " ‘ “Sannu da zuwa Yallabai, barka da ina wuni Dr Ahmad ya zuba mata kyawawan » idonsa masu kamar an diga gold yace. Shi ne ki fito kika koma don kija min 'rai saboda kin sani sarai ina cikin qishirwar son ganinki k0? Allah yadda na mike din nan na rantse da sai dai ki gan ni bayanki” Ya bude hannayensa “Taho gareni don Allah Saudat’ ; Saudat ta yi saurin rufe bakinta tana dariya, Dr. Ahmad ya zauna ya tattara nutsuwarsa a kanta, kafin ya ce “Saudat kin qara kyau wallahi kamar ba keba,irin wannan kamshi haka aisaikija intare a nan” . Murmushi kawai ta yi, Dr. Ahmad ya gyara zama kafin ya ce “Wallahi Saudat farin cikina a yau ba zai misaltu ba, duk yadda zan kwatanta miki ba zaki gane ba, don Allah ina Momy dinmu in sa ta cikin idanuwana ko na ji sanyi, wallahi ba kiji da na ji muryartaba sai na ji kamar da Mom dina nake magana, wallahi na ji ina qaunarta ni ma”. Saudat ta yi murmushi tana amsa sallamar Momy wadda suka shigo cikin falon, Alhaji Ashiru ya amsa. “A‘a wa nake gani yau a gidan namu, wai. Ahmad kai ne da kanka?" Dr Ahmad ya zabura ya miqe tare da washe bakiyana fadar ‘ Lah wai Daddy da ma nan ne gidanka na Katsinan ashe?” Alhaji Ashiru ya ce“Ai k0 dai nan ne ai shi Alhajinka ya sani, don har ya ya taBa zuwa Dr Ahmad ya ce, “Ikon Allah ashe gidan Daddyna nazo . ~ Ya durqusa yana gaishe su, duka dadi ya cika su don haka cikin fara‘ a suke amsawa. Alhaji Ashiru ya juya yana kallon Dr Mariya ya ce “To ai ke wannan tuwona maina ke nan, wannan dan Yaya Alhaji ne babban wanmu wanda , aka yi wa aure tun last four years, bai taBa zuwa‘ gidan nan ba tunda muka yi aure, kullum in nayi magana sai ya ce kishi yake taya Hajiya, to yau ga ' shi har cikin falonki tasa ta kawo shi, don haka kema sai ki Juya kambunki". ‘ Dr. Ahmad yana murmushi ya ce. “Lah wallahi kawu ba haka bane kasan abubuwan ne sai a hankali, amma dai tuba nake ai yanzu zan rinqa zuwa” . . Dr Mariya ta ce “Ai dama :zaka rinka . zuwa mana tunda yanzu taka ta kawo ka” . ' Duka suka sa dariya ban da Saudat wadda tunda ta sunkuyar da kanta ba ta kara dagowa ba, . sai ta koma ita ce sarakuwar. su kuwa hira ce sosai “suka Barke har Shukura ta shigo aka dasa da ita, sai lokacin ne Saudat ke dan sa baki kadan~kadan har sai da aka kira sallah, sannan suka fice suka tafi . don sauke farali. Suna dawowa Momy tasa Mairo ta kawo abinci aka da dasa wata hirar a nan suka" tsaida ranar zuwa qauye sati mai zuwa don tsaida , maganar auren. Dr. Ahmad bai bar gidan ba, sai qarfe goma na dare, Saudat ta yo masa rakiya har bakin gate, ’ya tsaya yana kallonta muryarsa a sanyaye ya ce “Yau zan yi bacci har da munshari Saudat na tabbatar a wannan karon zan mallaki abin da zuciyata keso, lallai na yarda babu abin daya fi qarfin Ubangiji k0 ba haka ba my dear"; , Saudat da ke faman wasa da ‘yan yatsun hannunta ta yi murmushi kawai ba tare da ta tanka masa ba, Dr. Ahmad ya bi ta da kallo gabadaya idanuwanta na saman yatsun hannu nata, ya miqa hannunsa ya riko duka hannayen ya janyo ‘ ta gabansa. Da sauri ta waro idanuwa tana kallonsa, ya sakar mata murmushi tare da hure mata idanuwa' da sauri ta idanuwanta tana murmushi qasa-qasa “ ‘ ya ce. * . “Ki bari sai kin koma gida kin kwanta sannan ki bude kin ji? Alkawari?” ’' Ta daga masa kai alamar ta yarda sannan . ya. sakar mata wani siririn murmushi kafin yace 'Sida safe, ki kular min da kanki, bacci mai dadi". . Ya shafi kanta daidai lokacin da ta ke Qokarin juyawa don haka ta qara sauri yana kallonta harta bace ya sauke wata nannauyar‘ ajikyar zuciya sannan ya juya ya fice. _ .Bacci ya kaurace wa idanuwan Saudat, ji ta‘ ke tamkar' ta taka rawar murna duk ta damu Shukura da juye~juye, sai faman juya takardar da ‘yasa mata ahannunta take koda batasan meye ya rubuce ba, amma ta san cheque ne na banki, don haka yau zuciyarta fes ta kwanta. Tun da gari ya waye suka hau shirin tafiya Qauye, Shukura ta shirya cikin wasu riga da siket na wani swiss‘ lace mai shegen kyau da tsada, dinkin ya bi jikinta ya hau kalar fatarta kasancewar leshin light blue mai adonda "ruwan qasa-kasa, gashin nan ya sha gyara an daure shi a gefen kunne sannan ta nada daurin kallabinta mai suna touch Iight irin na ‘yan matan yanzu. . Gyalenta da takalminta duk farare ne, sai ‘dankunne da sarka na gwal tare da abin hannunsa ta yi kyau sosai kasancewarta dama . kyakkyawarce ajin farko ’ Saudat kuwa riga da siket neta saka dark brown mai adon yardin gwal a jik; irin na Indiya .ta gyafa gashin kanta ta daure shi a baya ta saki jelarsa' a gadon bayanta sannan ta nada gyalen _ kayan saman kanta ta sake shi bai rufe kwallliyar kayan ba, siririn dankunnenta na gwal da abin ‘ hannu wanda mahaiflyar Dr. Tasa ba tasa abin wuyan ba saboda rigar kayan ta rufe har wuyanta ta kawo takalminta golden mai tsinin dunduniya ba qaramin kyau ta yi ba, yar' indiya sak! Sannan suka fito falo inda Momy da Alhaji ke jiransu, Saudat ta bi Momynta da kallo wadda ke sanye da riga da siket na atamfa sai ta dora ' baqar doguwar riga a sama mai adon jajayen fulawoyi irin mai tsukakken hannun nan ce Ta‘ daura kallabin atamfar a kanta sannan ta dora kallabin rigar a kan nata, ta saka takalmi da jaka jajaye, hannunta da kunnenta da wuyanta ma gwal ne mai tsadar gaske. Haka su Nabil da Nabila sun hade cikin ‘yan kanti kamar ~ ‘ ba" yan Nageria ba. ’ . ' Dadi ya cilka Saudat, wai nan duk yan uwanta ne da mahaifiyarta, wayyo rayuwa ke nan, sai da suka gaisa da Momy da Alhaji sannan ta bawa Momy cheque din da Dr Ahmad ya bata Momy ta warware tana dubawa tare da zare ido, ta ce “Kai wannan kudin Sunyi “yawa is too much, ya yi yawa abin duba ka gani Alhaji five , Hundred thousand fa”. ‘ Alhaji ya ce “Ta gode kwarai ai kyautar soyayya ba ta yawa; ki bude mata account kawai ki zuba mata a ciki . Hajiya ta amsa da, “To”. Sannan suka mike suka nufi tebur suka karya gabadaya sannan suka fice su shiga wata Katuwar motar Alhaji suka tafi humer jeep baka mai kyan gaske, shi ya ja su da kansa, har zuwa cikin Dandagoro. Jefi-jefl akan taBa hira inda Saudat saurarensu kawai take, amma z'uciyarta ’ ta shiga duniyar tumani da sake-sake ganin al’amuran ta ke tamkar a cikin mafarkinta suke , Faruwa jira kawai take ta farka a kowane lokaci_ba. . ‘ALHAMDU LILLAHI Masha Allah. Mu hadu a littafl na HUDU kuma na karshe ldan mai kowa mai komaI ya kai mu NAKU HAR KULUM A,,I,,S TABA KA LASHE kadan daga cikin yar tallah book4 Dukkansu suka fito suka shga gidan saudat na riqe da hannun nabiLa shikura na gefenta sai nabil a gefen momy alhaji ashiru ya zauna yana jiransu a mota sallamar da sukene ta janyo hankalin inna laure take kuryar daki tana tattara komatsai tayo tsakar gidan tana fadar marabanku sannunku dai Turus taja ta tsaya gamida dafe kirji cikin tashin hankali da kyarmar murya ta soma magana su waye ku daga ina? Momy ta gyara tsayuwa gamida cewa ikon allah abin da mamaki idanni baki ganeniba ai ina tunanin wannan yarkice kya ganeta tayi maganar tana nuna saude inna laure ta fadi qasa jabar kamar an tile kayan wanki tana kwalama malam bala kira malam bala ya fito daga kewaye a gigice hannunsa riqe da buta yana fadin kai laure wannan irin ihu haka ai saikisa juwa ta kwasheni in fadi babu gaira babu dalili Inna laure ta dinga nuna masa momy tana fadin malam dubamin ka gani wacece nake gani kamar maria Cikinfirgici malam bala ya siki butar ta fadi facal yayo kansu yana fadin wacce mariyar kike nufi ‘YAR TALLA- BOOK4 CHAPTER29 ZUciyar Saudat ta shiga duniyar tunani da sake- sake ganin al’amuran ta ke tamkar a cikin mafarkinta suke faruwa, kuma har yanzu ba ta fidda rai ba da za ta farka a kowane ba lokaci. Minti sha biyar ya kawo su har kofar gidan Malam Bala, inda Saude ke nuna masa hanya har suka iso, ya faka motarsa a qofar tsohon gidan. Dukkansu suka fito suka nufi gidan, Saudat na rike da hannun Nabila, Shukura na gefenta, sai Nabil a gefen Momy, Alhaji Ashiru ya zauna ya jira su a mota. Sallamar da suke ce ta janyo hankalin Inna Laure da ke quryardaki tana tattara komatsai, ta yo tsakar 'gidan tana fadar, “Marabanku; sannunku da...” Turus taja ta tsaya tare da dafe qirji cikin tsananin tashin hankali da kyarmar murya ta soma fadar. “Su wayr ku, daga ina?” Momy ta gyara tsayuwa kafin tace “Ikon Allah abin da mamaki, idan ni ba ki gane ni ba, ai ina tunanin wannan ‘yarki cr kya gane ta?” Ta yi maganar tana nuna Saudat. Inna Laure ta fadi qasa jaBar kamar an tile kayan wanki tana kwalla wa Malam Bala kira, dukkansu suka yi tsaye suna kallonta. Malam Bala ya fito daga kewaye a gigice, hannunsa rike da buta yana fadar. “Kai Laure wannan irin ihu haka ai sai ki sa juwa ta kwashe ni in fadi ba gaira ba dalili”. Inna Laure ta rinka nuna masa inda Momy ta‘ ke tana fadar. “Malam duba min ka gani, wace ce wannan Kamar Mariya”. ? Malam Bala ya ajiye butar ya nufo inda suke yana fadar, “Wacce Mariyar ki ke nufi?” Yana qarasowa inda suke yaja ya tsaya, suna kallon-kallo shi da Momy, alamun firgici da kaduwa sun bayyana cikin idanunsa. Dr. Mariya ta yi mmmushi kafin ta ce “Kallona da ka ke tamkar wadda ta fado daga sama, na san ba :zai rasa nasaba da ganin ba-zatar da nayi maka ba a lokacin da daga kai har matarka ku ka saki jiki da na bar muku duniyar shi yasa. ku ka wofintar da rayuwar bayin Allah, ku ka gallazamusu, kuka cuta musu don kawai ba su da kowa, amma me ya sa ku ka manta cewa, duk abin da kuke Ubangiji na nan Yana kallonku, kuma duk daren dadewa sai ya saka wa mai haqqi hakkinsa, musamman ma bayin Allah wadanda basu da alhakin kowa?‘ Kuka cuta musu, ku' ka gallaza musu kuka tozarta rayuwarsu daga qarshe ma ku ka tarwatsa " . min su kowa ya kama gabansa don kawai ka tsani , uawarsu a kan Iaifin daba bata ji ba ba ta gani ba; wannan shi ne sakamakon soyayyar da Kaunar da na maka? Lallai da haka shi ne ‘sakamakon . soyayya to da ba ta yi rana ba, Sai dai da yake Allah ba azzalumin bawansa bane, sai dai idan shi bawan ya zalunci' kansa, sai 'ga shi bai bar rayuwata ta tozarta ba kamar yadda kai kaso, Ya daga daraja ta a duniya, Ya kuma cika min burina tahanyar azurtanida ilimida nagartaccen miji Wanda ya fi ka komai a rayuwa, Ya kuma sake ba ni wasu ‘ya’yan, sannan daga karshe Ya hada ni da ‘yata gudan jinina, tabbas babu abin da zance da Ubangiji sai godiya. . ’ ' Abu daya ya kawo ni wurinkn shi ne ka sanar dani inda dana yake in kuma ba haka ba wallahi sai na zauna kotu da kai, don sai ka bani‘dana, cutarwar da kayi musu kuma wannan kai da Allah, Shi zai yi hisabi a tsakaninku, -don haka ka sanar dani inda dana yake . Tsananin firgici da kaduwa su suka girgiza ‘ zuciyar Malam Bala ‘ har ya ji qafafuwansa na Kokarin gaza daukarsa; ya matsa jikin bango'ya jingina'yana faman maida numfashi a wahalce" Laure da ke durqushe a kasa ta zabura ta mike tsaye cike da qarfin zuciya ta cire kallabin kanta taci damara kamar irin‘sabbin mahaukatan nan ta soma magana tana tafa hannaye“Kam babban abin da malam ya hana, mu za ki gwada wa qaryar arziki tsohuwar karuwa, kin je kin yo hayar kaya shi ne za ki zoki mana bariki? To qarya ki ke, wallahi idan kin fasa zuwa kotun kin raina Allahn da ya halicce ki, ke wanda ma ya ba ki hakuri Allah ya tsine masa, mu din nan sai dai mu ga bayanku ba dai ku ku ga bayanmu ba . Dr. Mariya 'ta yi wani qasaitaccen murmushi, ta cire gilashin da ke manne a fuskarta tana kallon Laure kafin ta ce, ‘Ai ita da ma . tabarmar kunya da hauka a ke nade ta, don haka ban kuma kasa dake ba ballantana har ki kwasa". Ta juya kan Malam Bala ta ci gaba da fadar, “Zan tafi Malam, na ba ka nan da sati guda ka nemo min inda dana yake kafin in dauki mataki, ga kuma Saude a hannuna Allah ya jefo min daga sama don haka na rungumi abuna, zan dawo rana irin ta yau don karbar dana, na barku lafiya”. Inna Laure ta yi caraf ta damke hannun Saude tana fadar, “Wallahi babu inda za ki je da ita, nan zaki barta a gidan ubanta, don mijinta yazo yace shi bai sake ta ba, dole kuma'ta koma gidan mijinta Yanzu-Yanzun nan”. Ido waje Saude ke kallonta' gabanta na. Faman bugawa da sauri da sauri, Momy kuwa dariya tayi cikin ajikafin tace “Kadadai ace shirme da‘ jahilcin' naki har ya fara taba kwakwalwarki? Ai k0 shi uban da ya haifi Saude bai isa ya hana in tafi da ita ba ballantana karabiti”. Kamarki ba 1nn Laure ta Kara hayayyakowa tare dA cukwikwiyo rigar Sauden Malam Bala yace “Sake ta su tafi” . Ta juya tana kallonsa a kidime tana fadar “Wallahi babu inda za ta Malam,Dan duk garinnan banga ubandaya isa yasa ta tafi da ita ba ,Na ce ki sake ta k0?” Malam Bala ya fadi a harzuke fuskarsa dauke da tsananin bacin ran da bata taba ganin irinsa ba a tare dashi A dole ta saketa din zuciyarta na barazanar tarwatsewa ta rasa inda za ta tsoma ranta ta ji sanyi, kawai sai ta durkushe a Kasa ta rusa wani irin kuka mai ta hankali. ~ ‘ Momy da Shukura suka tasa Saude a gaba ‘suka fice batareda sunsake bitakantaba. Suna ficewa daga gidan Malam Bala yaja yan qafafuwansa ya nufi: hanyar dakinsa, bai ko kula: Laure ba, abin da ya qara firgitata ke nan Kara .kidimewa zuciyarta cike da firgicin tonon asirinta. Suna fitowa daga gidan suka shiga mota, Alhaji Ashiru ya ce, “Wai har kun yi me?” “Momy ta ce, “Mun tafi kawai Alhaji”. Ya dan waro ido kafin ya ce “Amma na za ta za ku yi min magana da shi ko da fitowa ce ya yi mu gaisa, k0 ba ku samu mahaifin nata bane?” Momy ta kwantar da kanta a kan makarin kujerar kafin ta ce “Manta da su kawai‘Alhaji, muje ai sai da mutunci ake zumunci”. Bai ce komai ba ya yi wa motar key, Momy ta ce, “Saudat ta nuna musu gidan iyayen Hamid. Saudat ta’amsa da to jikinta a sanyaye, zuciyarta cike da kasala. A Kofar gidan su Hamid maigadi ya sanar musu iyayen nasa sun yi tafiya zuwa Zaria, sai dai Hamid din shi kadai, Momy ta ce ya yi musu magana da shi. Maigadin ya juya ya nufi cikin gidan, bai jima ba ya dawo ya sanar da su yana zuwa. Suna nan zaunc cikin mota daga’ gate din gidan, yana sanye da wani farin yadi mai sheki ya daura wa wuyan hannunsa wata tsadaddiyar agogo baka, mai kyan gaske ya dora farin gilashi saman dogon hancinsa da makullin mota a hannunsa, da alama fita zai yi. Kai tsaye wurin motar tasu ya nufo idonsa a kan Momy tun kafin ya ida Karasowa ‘ yana isowa ya rusuna ya gaida Daddy, sannan ya gaishe ta yana fadin, “Doctar kece a gidanmu?” ~ ‘Dr Mariya ta fadada fara'arta kafin ta ce “Aiko nice da kaina Malam Hamid, ai dole ne ma “ inzo ko dan qaunar da ka nuna wa Saudat ya zame min wajibi inzo in yi maka godiya, kuma in maka albishir da cewa Saudat yata ce nice mahaifiyarta nina haife ta da cikina" Hamid ya waro idanuwa waje yana fadar, “Yarki kuma DR? Kina nufin dama kece mahaifiyarta‘?” , Momy ta amsa da, “Tabbas nina haife ta da dan uwanta Rabi u”. ~ Wani irin dukulallen farin ciki daki zuciyar Hamid. ya daga hannunsa sama yanA yiwa Allah godiya. Saudat kuwa kallonsa kawai ta ke a . zuciyarta tana jinjina ma soyayyar da bawannan »ke mata ‘ ‘ Momy“ ta ce “Za mu tafi Malam Hamid, da fatan zumunci mai Karfi? zai shiga tsakaninmu” « Hamid ya amsa da “insha ,Allah"‘ Amma idansa na kan Saudat wadda ke ta faman haske shi ‘ da lallausan murmushi “ Yace “Mamy ki bani adireshinku insha Allahu dana dawo daga tafiya zanzo Babu musu Momy ta ba shi dan qaramin card din da ke cikin jakarta wanda ke dauke da adireshin gidan da lambar gidan, sannan Dady ya ja motar suka tafi Saudat na daga masa hannu har suka Bace wa ganinsa. Wani irin abu ya caki zuciyar Hamid, ya sa dan yatsansa ya lakace ‘yar guntuwar kwallar da ta taso masa, shi da ya sani Allah ya jarabce shi da soyayyar Saudat, irin son da ba zai iya misaltuwa ba, wai yau Saudat dinsa ce ta zama haka? Rayuwa kenan. Ana kiran sallar azahar suka iso gida, don haka Alhaji Ashiru na sauke su ya wuce masallaci don ya bada farali, su kuma suka shige gidan, Momy ta wuce bangarenta su ma suka nufi nasu Bangaren don gabatar da sallah a cikin lokaci. Bayan sallar la’ asar kuma Shukura ta koma gida saboda gobe tana da lecture a school. Kwanansu uku da dawowa ya kama ranar alhamis, Saudat na kwance a falonta ita da Nabil da Nabila tana kallonsu suna home work da aka ba su daga makaranta, Momy ta shigo felon kafadarta na rataye da katuwar jaka, ‘sai rigar likitoci sagale a dayan hannun da alama dawowarta daga ofis ke nan. Duka yaran suka zabura suka nufe ta a guje suna fadar, “Oyoyo my Momy, welcome". Ita ma da fara‘a a kan fuskarta ta rungume yaran a jikinta tana shafar kawunnansu. Saudat ta yunkura ta mike ta nufi inda " ' Momy ta ke ta karbi jakar hannunta da Iafkwat dinta: ‘da mayafin jikinta ta nufi Sangarenta kai tsaye kicin ta nufa ta jero kulolin‘ .abinci a babban faranti tareda kwalin lemo', da ruwa masu sanyi ta nufo falon, inda ta samu’ . Momy har ta yi wa kanta masauki saman tallausan ' kafet din falon, yaran duk sun zagaye ta suna ta_ shirmensu. ‘ Saudat ta ajiye mata kayan abincin a gabanta, ta soma bude kulolin tana mata sannu da zuwa. Momy ta rike farantin tana fadar. “Barshi kawai Saudat, kije falon waje Hamid nanan ya zo zaku gaisa” . . Saudat ta washe baki tana fadar. ' ~ “Kai Momy, ashe bai mance dani ba, yau fa kwana uku . ke nan da dawowarmu daga -Dandagora, amma bai zoba shi da ya ce ‘a * washegari zai zo?” Momy ta ce “Ah to, ni kaina da na ganshi a yanzu sai da nayi mita, amma dai yace ba ya garine shi ya sa, dawowarsa kenan. Tashi ki je kar yaga an barshi shi kadai. _ ‘ Saudat ta yunkura ta mike ta nufi kan gadonta ta jawa farin mayafinta ta yafa, ta saka takalminta flat Shoe shi ma fari A tsaye ta same shi cikin falon ya nannade hannayensa a qirji ya zuba wa qaton hoton da ke jingine a bangon daki ido, na su Nabila da Nabil ne wanda .aka yi musu a harabar wurin shakatawa da ke cikin park dukkansu sun yi matukar kyau tamkar ‘ya’yan da ke rayuwa cikin dusar qankara. Saudat ta qaraso cikin falon da ‘yar siririyan sallamarta, bakinta na dauke da murmushi. Hamid ya yi saurin waigowa yana kallon mai shigowarr tare da amsa mata sallamar Saudat ta tsaya dan nesa da shi tana fadar, “Saudatu ya tabbata kan Yaya Hamid wanda ya manta da ita tsawon kwanaki uku babu shi babu alamarsa”. . Tunda Hamid ya waigo ya ganta ya kasa koda kyafta idanunsa balle ya janye su daga kanta, girman da Saudat ta Kara da cikar jikinta shi ya fi . komai daukar hankalinsa, da kuma shigar alfarmar da ke jikinta. Ba komai bane a jikinta, illa wani tsadadden code lace dark blue mai ratsin fad-fad a jiki, dinkin riga da siket, kalar leshin ta dace da yanayin farar fatarta, don haka dinkin ya yi matukar kwantawa a jikinta. Yafi mayafin da ta yi Ya zauna kafadarta ya dace da ita, ya fito da sigarta ta nutsattsiyar budurwa. : Hamid ya lumshe idanunsa ya bude guda yana fadar, “Allah ya huci zuciyar Saudat, wai kin ga yadda kika ka koma kuwa?’ ‘ ‘ ‘ Saudat ta yi murmushi har da sunkuyawa ta zauna tana fuskantar katon teburin da aka qawata da kayan ciye-ciye dana sanyaya makoshi. ~ ~ “ ' ‘ Hamid ya durqusa a gabanta yana kallonta da idanunsa dake fallasa asirin zuciyarsa, ya kira sunanta . “Saudat, wallahi ina sonki, irin son da ba zai . misaltu ba, daidai da daqika guda ban taBa ' mancewa da keba a rayuwata, kina nan makale a zuciyata wallahi ranar da kuka zo gidanmu a ranar na bar Katsina na tafi Abuja, isowa ta ke nan wallahi. Saudat zuciyata ta gaza hakuri sai da nazo ki yarda da ni don Allah kyakkyawata". Dariya ceta kwace wa Saudat saboda ganin yadda duk Hamid din ya bi ya rude kamar wani zautaccce, shi ma ‘yar dariyar ya yi yana sosa qeya alamar ya danji kunya shi ma. A daidai nan ne kuma Dr. Ahmad ya sawo kai cikin falon da‘ yar siririyar sallamarsa, waddai ta makale amakoshi. * ' Saudat ta dago kanta a dan razane ta dubi ' inda yake Wani razanannen kallo ya watsa mata ta cikin siririn farin gilashin da ke manne a fuskarsa, Lokaci guda ya dauke kansa tamkar allah bai ajiye ’ Awajen ba, haka ya gifta su ya shige falon cikin gidan. Saudat ta sauke wani gwauron numfashi tare da maida hankalinta inda Hamid yake Murmushi ya sakar mata tareda fadar, . “Wannan shi ne abokin takarar tawa kenan?” Saudat ta sunkuyar da idanunta qasa tana dan wasa da bakin gyalenta don har ga Allah Hamid yana da muhimmanci a rayuwarta, duk da ta sani sarai ba za ta iya hada soyayyar Dr. Ahmad da ta kowa a zuciyarta ba. Hamid ya yunkura ya mike hannayensa zube a cikin aljihunsa yana kallonta da fararen idanunsa. Saudat ta yi qasa da idanunta ta kasa hada ido da Hamid din sai kawau ta tsinci kanta da jin matukar nauyinsa. Hamid ya yi wani malalacin murmushi Wanda ya tsaya iya labbansa kawai, muryarsa na dan sarqewa ya ce “Tsananin son da nake miki Saudat, da dumbin qaunarki da ke zuciyata ba zai ingiza ni ga take gaskiya ba. Saudat na yi miki rantsuwa da Allah ke ce kadai macen da na tabaa so a rayuwata, kuma haryau bana tunanin da akwai kwatankwacinki. A ranar da kuka zo gidanmu kuka ganni a ranar aka daura aurena da Kausar ‘yar qanin mahaifina 'Amma nasa qafa na bar Katsina zuwa Abuja‘ ban“ sonta, banida muhallin da zan iya :ajiyeta a a zuciyata, tunda na. tafi sai jiya na dawo. A yanzu haka mahaifina ya yi fushi , , don haka mahaifiyata ta ba ni shawara na tafi Kaduna Wurin matata, wannan ne ‘ kadai abin dazai Shirya tsakanina da mahaifina. Yanxu’ haka tafiyar tawa ce zuwa Kadunan shine na kasa daurewa har sai na tsaya na ganki sannan na wuce. Saudat ba zan shiga haqqinki ba, idar har kin ji zaki iya aurena a yadda nake a ‘ yanxu na ba ki sati daya ki yi shawara duk abin da ‘ kika ”yanke zan dawo sai ki sanar dani”. “' Ba tareda ya tsaya sauraran abin da zata cebaa ya zaro ambulan daga cikin aljihunsa ya dora mata a hannu sannan , ya juya ya fice abinsa. Saudat ta mike jikinta a kasale ta ‘ nufi qofar shiga babban falon gidan. Ba ta ankara ba sai dai ta ji sun yi karo yana qokarin fitowa ita tana qokarin shiga, ta yi saurin ja da baya tare da dafe goshi, kallo daya yayi mata ya Juya ya dauke kai da sauri ya raBa ta zai wuce. . Saudat ta yi saurin rufa masa baya tana ' kiransa baida alamar tsaya ba balle harya .sauraré ta hakan ya sa ta Kara da gudu~gudu ta , sha .gabansa. 'Don Allah ka tsaya ka saurareni Ta yi magar tamkar zata rusheda kuka. Dr. Ahmad yasa ya tsaya a gabanta yas‘hannayensa a aljihu tare da kafa mata ido. Saude ta langwabar da kai ' “Don Allah kar ka horar dain da fushinka, wallahi ba zan iya jurewa ba” . . Dr Ahmad ya watsa mata harara kafin yace“Idan har ni ban horar da zuciyarki da fushina ba, ai ke kya tarwatsa tawa zuciyar da masifar kishinki kauce ki bani hanya in wuce : Ya qarasa maganar tare da sa hannu yana ture ta daga gabansa Saudat ta Kara tokare hanyar cikin muryar ' son fashewa da kuka ta ce “Haba don Allah yallaBai, Yaya Hamid ne fa ba wani ba”. Dr. Ahmad ya qara watsa mata. wani kallo, “Okey, Yaya Hamid ne shi da yake ba namiji baneba k0? K0 kuma shi din ba sonki yake ba ko? Da Allah matsa bani wuri malama na wuce”. Wani irin qululu ya tokare zuciyarta ganin yadda ta ke rarrashinsa yana qars botsarewa. ta juya da hanzarinta tana sharar kwalla ta shiga ciki. Dr Ahmad yabita da idanunsa dukda ‘ zafin da zuciyarsa keyi bai hana shi jin tausayinta ba, sai dai shi kansa bai san kalar zuciyar shiba da kishi yakan sa ya kasa sarrafa kansa ba yadda ya ' iya haka ya juya ya fice daga falon YAR. TALLAH CHAPTER30 Saudat'na Shiga falon taga Momy zaune hannunta rike da waya da alamar. magana ta gama tana shirin giftata. ta wuce, Momy ta rika , hannunta. saudat ta waigo da sauri tana kallonta, 'don haka ta dawo ta raBa ta zauna zuciyarta babu "dadi. , ~ Momy ta kira sunanta, “Saudat dan rigimar nan naki ba zai miki haqurin ki fara karatu ba, naga alamar rigimamme ne na gaske, don haka nayi tunanin a tsaida magana kawai in yaso ko a gidanki kya yi karatunki idan kina da rabo har gaba da sakandire sai ki wuce a gidanki don haka yanzu zabi yana wurin ki shin tsakanin Hamid da shi Ahmad din waye kike jin kina so a cikinsu” Saudat ta dago a sanyaye ta dubi Momy kafin ta ce, “Duk ina sonsu”. Momy tayi wata tatacciyar dariya ta ce, “To idan kina sonsu duka Saudat wa ki ke son aura A ciki kuma?” Saudat ta yi shiru zuciyarta naci gaba da ' harbawa, ta. sani sarai soyayyarta a yanzu tanaga ’ wurin Dr.“ Ahmad, to amma ta juya wa Hamid baya ‘ ' anya ta yi wa soyayyar da ya yi mata adalci? To shi kuma Dr din fa? ‘ ‘ “ Momy ta katse mata tunanin da cewa . “Ki yi tunani da kyau Saudat, duka mutanen biyu duk suna qaunarki amma ni a nawa gamin Ahmad shi ne wanda ya cancanta ki aura, amma ki yi tunani da zuciyarki". Saudat ta dago kai tana kallon Momy zuciyarta na faman harbawa ta ce “Momy na zabi Dr din in har ke ma ya yi miki Momy ta dora hannu saman kafadarta ta dafa ta tana fadar, “Hakan shi yafi cancanta Saudat, tashi kije Allah ya yi miki albarka". Saudat ta amsa da, “Amin”. Sannan ta mike cikin sanyin jiki ta nufi dakinta, ta fada kan gadonta a rufda ciki ta dafe kanta da hannaye biyu tamkar mai shirin kurma ihu, ta lumshe idanu tana jin zuciyarta na bugawa da qarfl, tamkar za ta ballo Kirjinta ta flto waje. Sai dai ta samu taimakon wata dunkulalliyar damuwa da ta tokare ta ta hana ta baro kirjin harta fito fili, tana so ta ji halin da Dr. Ahmad yake ciki, amma kuma tasan babu dama. Tana nan kwance har aka kira sallar magriba don haka ta miqe ta nufi bandaki ta dauro alwalla ta fito ta nufi kan sallayarta ta zura dogon hija‘binta ta tayar da sallah, tana gamawa ta kishingida a saman sallayar ta Iumshe idanunta tamkar mai jin bacci, amma babu komai a zuciyana sai dumbin damuwa. . Ta yi nisa a duniyar tunanin da ta lula ta ji an kwalla kiran sallar isha’I, a dole ta mike don ba ‘ da farali. ., saida ta gama sallar harta mike ba, zata Kara kudundunewa akan sallayar tamkar mai jin ‘ sanyi, inda rai da zuciya keta aikin rarrabe tsakanin Aya da tsakuwa anya dana dauki Dr. Ahmad ta bar Hamid ta'yi wa soyayya adalci? ‘ ‘ Ba ta ji shigowar Nabila ba, sai dai ta ji ta dafa ta tana fadar, “Aunty kizo inji Ya‘ya yana falo yana jiranki” ' Saudat ta yi saurin tashi zaune tare da rike hannun Nabilar tana fadar, “Wane falon Nabila?” ‘ “Falon Daddy da baki”. Ta ba ta amsa. » Saudat ta dan yi jim tamkar mai nazarin wani abu tamkar kuma wadda aka tsikara ta zabura ta mike ta shuri takalmanta ta fice ta nufi falon da yake ta sa kai ta shiga tare da ‘yar siririyar sallamarta, ba don Allah ya yi ta ita din mai ji bace sosai daba yadda za a yi ta iya jin amsa sallamar da ya yi a can qasan makoshi irin ta wanda damuwa ta galabaitar da shi. ‘ Jikin Saudat ya yi sanyi matuqa, ta zubawa fararen idanunsa ido, yana zaune saman kujera ya , tallabe kansa da hannaye biyu ya zuba wa kaifet ido. Jikinta a mace ta IallaBa ta zauna. saman kujerar da ke gefenta, ta kasa dauke idonta a kansa. sawon mintuna biyar falon tsit baka jin motsin komai a ciki sai iskar A. C zaman shirun ya fara damunta tana son kawar da shirun, amma kuma bata san k0 ta Wacce hanya zata biba, to k0 hakuri zata ba shi? Idan ma hakurin ne ta ya ya za ta ba shi? K0 Shukura za ta kira ta bashi kan wayar ta "lallasar mata shi.. ' Ba ta ankara ba sai dai ta ganshi a durkushe a gabanta, kirjinta ya yi wani mummunar bugawa saboda yadda yawa Kafafuwanta, ta yi saurin ja da baya cikin kujerar, hakan ya yi daidai da riqo hannuwanta duka biyun da ya yi, tare da kiran sunanta cikin wata irin kasalalliyar murya wadda ta tilasta mata dago kanta ta kalle shi, gabanta ya yi wani mummunar faduwa, fararen idanun nan nasa tamkar an watsa barkono, gabadaya ya birice, ya canza tamkar ba shi ba ne wannan tsayayyen daktan jarumi mai razanar da ita ba. Ta runtse idonta da karfi saboda wani irin abu da ta ji yana tsurga mata zuciya. Dr. Ahmad ya kira sunanta da wata irin dakusasshiyar murya, “Saudat ki bude idonki ki kalle ni don Allah, kar ki tsane ni wallahi ina sonki, irin son da duk duniya babu mai yi miki kwatankwacinsa. , Saudat ki taBa zuciyata za kiji ki saurari zuciyata zakiji, ki kalli zuciyata za ki game irin guguwar da ke binne a cikinta, Saudat ina sonki son da zan iya salwantar da rayuwata a kanki, .. wallahi Saudat ina cikin fargaba tunda na bar gidan ' Karkiji yaddah zuciyata kr cikin baqin ciki a dole na dauro alwala na zauna ina ta ambaton Allah Saudat na yi sa’ a bakin .cikin ya gushe, amma damuwar da nake ciki ba ta barni ba har a lokacin nan na kasa runtsawa, gani nake zuciyarki na wurin‘ Hamid; da alama kuma za ki iya barina ki “ koma gare shi a kowane lokaci, wannan tunanin ne ya tilasta min dawowa Saudat don in sanarda ke cewa, idan har kika kuskuren juyawa zuciyata baya, to tabbas’ a ranar zakiji mummunan labari ~cewa na rasu, don ba zan iya rayuwa ba matukar babu ke a tare danibs Shirun da Saudat ta ji ne ya tilasta. mata bude idanunta tare da kallon inda ta ke sa ran' yana zaune, amma da mamakinta tuni har ya kai bakin kofa, ba ta san lokacin da ta mike ba, tare da kiran sunansa. Ya waigo da sauri tare da daga mata hannu. Karki ce komai Saudat soyayya ta zarce duk yaddaki ke tunaninta, don soyayya gamon jini ‘ ce ba wai gamma gambiza ba, so haduwar zuciyane ba wai tilasta shi akeyi ba Kuma linzamin so ' hankaline ba wai son rai ba. Saudar kar ki tilasta wa kanki ki soni don kawai kina tunanin ya kamata ki so ni, ba zan kasance mai son raiba na tilasta miki aurena ba alhalin ba nine a zuciyarki ba. Tun ranar da na soma sonki na kasance bani da. wani buri da Daya wuce son nagana dauwar dafarinciki ‘ zuciyarki, na dandana miki zaqin rayuwar da ba ki taBa dandana ta. Va Kuma kp a yanzu haka abin yake Saudat, dolene na baki farin cikinki k0 da hakan yana nufin rugujewar tawa rayuwar dole zan ba ki shi, kuma na yi miki alkawarin sadaukar wa Hamid da soyayyata matukar shi ne farin cikin rayuwarki”, Saudat taji wani abu ya tsarga mata zuciya mai kama da tsinin mashi, hawayen da suka tarar mata a idanu tun dazu suka samu damar biyo kuncinta, kuka nena gaske ya kwace mata, Wanda ta rasa dalilin yinsa. Dr. Ahmad ya yi saurin nufo ta, jikinsa na. kyarma yana Kokarin riko ta, ta yi saurin ja da baya tare da fadar “Karka taBa ni don Allah na rokeka, idan‘ har son da nayi maka bai gamsarda dodon kunnenka ba don Allah ka fadamin kalaman da zan yi amfani da su don su gamsar da kai, ni dai in har na san abin da so yake nufi, to saboda kai 'ne in har dai abin da nakeji a zuciyata shine so, to YallaBai na soka, so kuma kai kadai irin wanda ba zai taBa Karewa ba har abada" Shi ‘kuma hamid din fa ya zaki yi da shi Saudat? Yana sonki kamaryadda nake sonki, babu wani dalili da zaisa ki amince da daya daga acikinmu don kawai kina ganin rashin kyaumtawar ki guje masa Saudat ni na fadada bakina na aminca miki ki zaba wa 'zuciyarki abin da take so, k0 da ‘ kuwa hakan yana nufin bani za ki zaBa ba, kuma hakan ba zai sa na karya alkawarin dana dauka ba, na daukaka darajarki da duk....... “Ya isa don Allah ya isa haka!” Saudat ta yi maganar muryarta a sanyaye cikin kuka ta ci gaba da fadar, “Don Allah ka kyale ni haka, idan na ce ban so Hamid ba YallaBai karya nake, sai dai ina so ka gane abu guda shine, irin son da nake wa Hamid ba shi nake maka ba, sonka a cikin zuciyata ya sha bamban da irin nasa, don kuwa ka san shi murmushi yafi dariya. _ Abu guda kawai na sani shine, ba zan iya rayuwa ba inba tare da kai ba, idan har ina da rabon samun farin ciki da ‘ jin dadi a rayuwata to kai ne farin cikina, kai ne jin dadin rayuwata”. Da sauri ya nufe ta tamkar ‘zai kamo ta, sai ka ce wani zautacce, muryarsa harsarkewa ta ke Wurin fadar, “Da gaske Saudat kin amince za kl “ zama tawa? Za ki kasance da ni yanzu da har abada? Saudat don Allah ki amince ki zama tawa ni . kadai, wallahi a yanzu kece farin cikina, ke kadai kika ragemin, kin amince min na turo da ‘ da sadakinki gobe, ki fada min Saudat, ke nake saurare”. Kai kawai ta iya daga masa ba tare da ta bar zuciyarta ta yi wani dogon tunani ba Farin cikinsa ba zai misaltu ba a lokacin ita kanta Saudat ta tabbatar da hakan saboda yadda ta ga ya dawo cikin nutsuwarsa lokaci guda ya koma kan kujera ya zauna tare da sauke wata nannauyar ajiyar zuciya. Ya jingina kansa akan makarin kujerar yana sauke numfashi cikin nutsuwa, idonsa na kan Saudat wadda ta kasa zama. Dr. Ahmad ya qakaro wani dan murmushi kafin ya ce, “Kin min tsaye akai kina kallona k0 so ki ke ki gano munina ne?” Saudat ta yi saurin janye idanunta a kunyace tare da‘ yar dariyarta Kasa~qasa. Dr. Ahmad ya dan. kishingida kadan a kan kujcrar yana fadar, “jeki samo min dan wani abu in ci kada yunwa ta san yadda ta yi dani A, dan sanyaye Saudat ta kalle shi, shi ma 'idanunsa a kanta suke adole ta juya ta nufl kofa don kwarjininsa ba zai barta ta furta abin da ke bakinta ba. Kai tsaye kicin ta nufa ta soma dawainiyar sama masa can abin da ta san zai iya ci, sai dai babu komai akicin din sai sauran farfesun dare wanda ya ji kayan yaji, don haka ta zubaruwa a kettle ta kawo garin citta da karunfari da ganyen ta zuba, sannan ta jona a wuta ‘ Tana nan tsaye harya tafasa sannan ta juye masa“ta dora saman tire ta dora kofi daya tare da cokalin shan tea, sannan ta dora kular farfesun tasa filet da madaidaicin spoon sannan ta bude tirij ta dauko cake manya guda biyu ta dora a gefe, sannan ta dauka ta shiga falon da yake da sallamarta har a lokacin yana nan a kishingidensa; . Saudat ta durkusa a gabansa ta zuba masa tare da tsiyaya’masa ruwan zafl a kofi ta sa masa lipton da coffe tare da madara da sukari kadan ta juya ta miqa masa ya sa hannu ya karBa, bakinsa dauke da murmushi ya ce “Na gode kwarai” Murmushi kawai ta yi ta mike ta koma kujerarda ke fuskantarsa ta zauna. Tana kallonsa sai da ya cinye komai ita kanta ta yi mamakin irin yunwar da ya kwaso, shi .kansa ya lura da irin kallon da ta ke masa. Ya mike tsaye da dan murmushinsa yana kallon agogon dake daure a hannunsa, ya ce “Ni zan wuce, idan har kallona da ki ke me cike da tuhuma ya wadatar da ke Murmushi kawai ta yi, ta mike tana tattara, kayan daya ci abincin, ya dan mirgina kai ‘ ”‘idan kin shiga gida ki sanar da Momy manya zasuzo gobe insha Allahu misalin qarfe hudu na yamma” Allah ya kai mu’ amsa a takaice tare da bin gefensa za ta wuce saboda kwarjininsa da takrjin ya cika mata falon. Shi kansa ya lura da hakan, cikin zolaya ya ce. “Ba sallama kuma Madam ko har na angwance tun yanzu ne?” Ba ta juyo ba ta yi gaba abinta saboda dariyar da ta ji yana mata, ta tabbatar zolayarta yake son yi, don haka ta yi cikin gida abinta. Washegari misalin karfe sha daya na ‘safe; Saudat na kwance a falonta saman kafet ta' yi matashi da filon kujera tana kallon wa'azin Shekh Ja’afar da aka sanyo na Sunna T.V mai taken‘ ‘Suffatus salatun nabiyi'. ' A Kasan zuciyarta kuma tunani ne barkatai, tun jiya data yi mafarkin Yaya Rabi‘u’ ta kasa nutsuwa, tunanin dan uwan nata ya addabi ' zuciyarta k0 karyawa ta kasa yi, burinta bai wuce na ta koma Dandagoro bA don ta karb saqon da Hamid ya sanar da ita Yaya Rabi’ u ya bada makotansu a ajiye mata, ta san gidan ba zai wuce gidan Inna mai danwake ba, don gidanta ne ke manne da nasu, kuma nan ne kadai gidan da suké ' shiga ita da Yaya Rabi u alokacin suna tare Bataji shigoWar Momy a falon ba, sai dai‘ ta ji ta dafa ta tana fadar, “Bacci ne k0 kuma dogon tunani?’ “” Saudat ta yunkum ta tashi zaune tana kallon , mahaifiyar tata wadda ke kokarin zama a kan kujera, ta ja remote ta rage sautin akwatin talabijin ‘ din tana fadar. ‘ “Yanzu Alhaji ke sanar da ni yau za su je wurin Babanki don nema wa Ahmad aurenki, ni dai cewa ma, na yi,,kawai a kyale shi aCi gaba da ,hidima a nan, Alhaji ya ce ba zai yiwu ba, dole a ba shi hakkinsa a matsayinsa na mahaifi. * Ya ki ke ganin za a bullo wa tsarin bikin, don rana kawai za akira ban da asabar din gobe ta sama za a daura auren, kin ga dole musan abin da za a shirya don kar IOkaci ya qure mana. Ki min lissafin duk abin duk abinda kike so, don zan tura a Dubai . za a hadp komai” ,. . ' Saudat ta sunkuyar da kanta tana wasa da yatsu. Momy ta kafa mata idanu muryarta a saayaye ta ce, “Saudat lafiyarki kuwa, me ke damunki?” ‘ A hankali ta d‘ago kanta ta kalli mahaifiyar ' Kata da idanunta, wadanda suka ciko da kwalla, ta , hadiye dunkulalliyar damuwar da ta ‘tokare mata . zuciya, kafin tace “Momy yanzu shi kenan Yaya Rabiu ya bace kenan har abada?” YAR. TALLAH CHAPTER31 Momy taja wani gWauron numfashi kafin tace “Inji wa ya fada miki Saudat? Ni naji a jikina Rabi,u yana raya, kuma yanzu haka na_ baza ‘ *cigiyar‘sa tun daga gidajen talabijin, radiyo, mujallu da kuma jaridu tare da ofisoshin jami,an : tsaro insha Allahu Saudat zai bayyan, ki kwantarda hankalinki kinji Saudat ta daga mata kai kafin ta ce, “Tun *’ ina Abuja Hamid ya sanar da ni Yaya Rabi’ uv ya ba da sako a makwabta a bani nasan gidan Inna mai danwake ne shine nakeson inje inkarbo Momy ta ce, “A‘a ba zan iya barinki ki je ba, sai dai inwa Alhaji magana ya sa k0 direba ne yaje ya karbo miki hakan ya yi miki?" ‘ Kai kawai Saudat ta iya daga mata alamar eh. ’ . ' Tace “Okay lissafo min abubuwan da ki ke *bukata, kodai kin bani wuqa da nama ne? . Saudat ta amsh da, “Eh Momy”. Dariya Momy ta yi kafin ta ce ‘Wannan fillancin naki ya yi” yawa Saudat, anya kuwa?” ‘ ‘ Dariya kawai Saudat ta yi mahaifiyar tata ta fita ta barta , Misalin karfe budu na yamma Shukura taxo , “ gidan da‘ yar qaramar jakar kayanta, dadi ya cika' Saudat don kwana biyun da tayi babu ita ba’ " 'qaramin kewarta tayiba Shukura ta sauke jakana a kan gado tana fadar “Amarya kin sha kamshi, wannan fara arfa duk ta murnar amarcin ne?” Saudat ta waro ido cikin dariya ta ce“Kai _ don Allah meye na zolaya kuma? ’ ‘ ' Shukura ta fadakan gadon tare da rungume ta tana fadar, “Ba wani nan zolaya, gaskiya na fada” ' Saudat ta tabe baki ta zauna a kan kujera tana fadar, “Ai da ma Hausawa sunce idan baka iya sharri ba ka koyi kage” ., Shukura ta ce, “Ba wani nan, haka nan ki ke nuna wa Momy kauyanci amma irinku sululu kasau kunfi kowa iya shege Saudat ta yi dariya tana fadar, “Yau kuma da mita ki kaxo gidan kenan?” Shukura ta ce “Ai dole in miki iya shege, don Momy ta kira ni wai na tattaro na taho mu zauna don ta lura kina bukatar huduba ta, ni kuwa Tasan ba wani nan k0 karya na fada?" Saudat ta mike tayi hanyar‘fita daga falon tana fadar, “Ni ban iya abin da kika iyaba”. 1 Shukura ta tuntsure da dariya don ta san ta Qular da ita. , Washegari da safe suna zaune a falo Shukura na karanta wa Saudat wani littafin Hausa mai suna KADANGARUN BARIKI, Momy ta turo Ta turo .Kofar ta shigo tare da fadar, “To sai ku tashi ku shirya yanzu maza direba ya kai ku gidan Maman ‘ Sumayya maida tsohuwa yarinya” . ' ' Shukura ta zabura tana fadar, “Wow Momy! Da gaske?” . ‘ Momy ta yi murmushi tare da Juyawa tana fadar, “A’a da wasa”. , ~ Shukura ta dafe Saudat tana fadar, “Kai . amma wallahi Momy tanaji dake Saudat, lallai zaki rudar da DR wai baki taba jin labarin Maman Sumayya a Abuja ba?" Saudat ta girgiza mata kai a hankali, don ita ‘ dai ba ta fahinci inda maganar tasu ta dosa ba. , Shukura ta ce, “Lallai, da mamaki don a * fadin Nigeria babu jihar da sunan matar nan bai , zaga ba, kaya ta ke siyarwa ‘yan gaskr, tun daga kan, gyaran gashi, gyaran fata, sabulluka zuwa mayukan gyaran fata, kayan manyan mata kuwa wannan daga qasashen Larabawa ta ke hada su. Ke dai bari ‘ mu je za ki gane wa idonki” Saudat ta ce, “Ita kuma amarya har wani . gyara na daban ake mata.” , Shukura ta yi wani takaitaccrn murmushi kafin ta ce “In ban da abinki Saudat, idan akwai . macen da ta ke bukatar gyara a bayan amarya ta ke ko kuma macen da ta haihu ita amarya ana bukatar ‘ komai nata ya xama na musamman ne tun ba ke da" Zakiyi aure gidan kishiyaba, ya kamata ta ko’ina , mijinki' ya san da bambanci, tun daga tafukan , hannunki, labbanki, fatar“ jikinki, da kuma fuskarki, sai kuma can ainahin wanda wannan kuma aikin manyan mata ne musamman idan auren na Soyayya ne Abin da dai nake so ki gane shi ne ranar bikin kowace mace to awurinta wannan babban ra'na ce da babu irinta a rayuwarta, musamman idan auren na soyayya ne. A ranar daurin aurenki kowa burinsa ya ga irin kwalliyar da zaki yi, kek0 da ‘yan gidanku ne suna son qare miki kallo a wannan ranar, shi yasa wasu matan tsabagen son gyaran jiki har gyaran ‘sai yazo ya yi yawa, ya feSo musu 'da quraje a fuska k0 da ba bata da wadannan kurajen a da. Don haka a matsayinki na aMarya ya kamata ki kula da kanki, akwai sirrikan abubuwan da ke gyara amare na farko a matsayinki na amarya ana bukatarki da yawan sham ruwa sirrin hakan shi ne, kar jikinki ya yankwane. Sannan ana bukatar amarya da cin “ya yan itatuwa hakan zai taimaka wa fatar jikinta matuka, ‘ sannan ana bukata: amarya da ta yawaita sham , kankana, ita ma za ta taimaka mata matuka wurin gyaran fatar jikinta, haka kuma cin ganye irin su. latas da kabeji, suma za su taimaka kwarai. Ta yinkura ta nufi bandaki tana fadar “Bari in fara watso ruwa mu shirya tun kafin Momy ta sake biyo mu” . Ta zame kayan jikinta ta shige bandakin don watsa wa jikinta ruwa. lko sai mai tsaga ido Allah Almusawwiru, mai yadda Ya so, tabbas na yarda komai nufi ne na Ubangiji, kuma al’amarin aure tamkar layin . kasuwa ne idan layi yazo kanka k0 bakaso sai an maka, kamar yadda arziki bai isa ya guje wa ‘mai shiba, haka shi ma rai bai isa yaqi mai shi ba, haka matar mutum ba ta isa ta guje‘masa ba k0 ana ’ ha-maza ha-mata, auren da Ubangiji ya qaddara to fa sai an daura shi duk tsananin wuya, kuma duk dadi don duk nisan dare gari zai wayr. Hakan ce kuma ta kasance don yau ita ta kasance ranar juma'ar da za a daura auren Saudat a asabar In ka duba gidan Dr. Mariya acike yake da yan uwa da abokan arziki na kusa da na nesa, don ‘ a ranar ne za a yi kamu, wanda Dr. Mariya ta shirya . Biki ne ake ba wai na wasa ba, don kudi ta ke kashrwa tamkar tana tsinto su mafiyawancin abubuwan da ake yin amfani dasu a wurin bikin duk daga qasashen waje ta bada saqonsu aka taho mata‘ ‘ dasu DukvWanda ya ”san Saudat kuwa yancu” idan* ya ganta da wuya idan zai iya ganeta Cikin sati ~daya ta yi wani fitinannan haske, don har wani .yalo-‘yalo ta ke, fatar jikinta ta yi wani luwai- luwai ’sai sheki ta ke tare da daukar ido tamkar jikin tarwada, cikia lokaci guda ta rikide tamkar wadda aka Kara wa kyau da fari. Kodayake irin manyan kudin da Dr. Mariya ta saki wurin gyara ‘yar tata sun isa ace ta maf1 ; haka. don k0 gyaran jiki sau uku aka mata arana, safe da yamma da kuma lokacin kwanciya bacci, don daidai da Kunshi daga Abuja ta dauko mai zanen da ta yi musu, gyaran gashi ne aka yi musu ’ a babban wurin gyaran gashin da ke G. R A,abinka da ma da mai abin don haka gashin ya isa saukowa , har tsakiyar bayanta, ga wani baKi da sheqi da yake na musamman. Haka dinkunan fitar .biki duk a Lagos ta ba da aka dinko mata wasu kuma a -. Dubai sai shaddojin ne ta bada aka dinkosu a Maradi. Yanzu haka Saudat ce da Shukura baje a falo suna duba kayan fitar kamun da za su sanya a yau, Momy ta turo kofa ta shigo da sallamarta, ta ' tsaya daga bakin kofa jikinta a sanyaye ta ce “Direba Ya daWO yanzu‘ amma har yau dai mai . danwake ba ta dawo ba, sai dai maigidanta ya ’tabbatarda cewa, duk abin da aké ciki ba za ta rana ita yau ba tare da ta dawo ba" ‘ Cikin nutsuwa Saudat ke kallon mahaifiyar tata, cikin sanyin jiki da sanyin murya ta amsa da, “Allah ya kai mu Momy, Allah Ubangiji ya bayyana mana shi ma kafin lokacin” . , Momy ta amsa da,“Amin”. Kafin ta dau wani nannauyan numfashi tana kallon Shukura ta * ce “Ya kamata fa ku yi azamar shiryawadon Karfe hudu daidai za a fara kamun”. Shukura ta amsa, “Insha Allahu Momy yanzu za mu shirya”. ' ' Momy ta juya ta fice Shukura kuma ta mike tana fadar, “Tashi‘ yar uwa ki fara shafawa jikinki ruwan lallen nan kafin in fito daga wanka” K0 motsi Saudat ba ta yi ba ballantana ta sa ran amsawarta, hakan ya sa Shukura waigowa ta dubi inda Saudat ta ke, tare da fadar,“Lafiya dai Saudat. " " A hankali ta dago kanta tana kallon Shukura kafin ta ce, “Babu komai”. " Shukura ta girgiza kai, “A’a ban yarda ba Saudat, na lura damuwar fan uwanki na damunki amma ya kamata ki yi wa Momy uzuri, saboda yadda ta ke iya bakin qokarinta bai kamata ki Kara , daga mata hankali da damuwarki ba. Kina kallo tun ‘. ranar daki kace mata yayanki ya‘ bada sako gidan mai danwake a ajiye miki Momy kullum sai ta tayar da direba ya je gidan, amma har yau ba a yi nasarar sa'mun mai danwaken ba, tunda an ce ta je garinsu Ki kara haquri don Allah Saudat, insha Allah zaki ga sako mai dadi wurin mai danwake da zarar ta dawo tashi ki rage kayan jikinki in taya ki shafa ‘ Ba musu Saudat_ ta yun kura ta mike don ta sani haquri ya zame mata dole, k0 da ba a ba ta ba ita. ta ba wa kanta tunda dai babu wanda ya san inda Rabi’ un yake. Shi kansa Dr. Ahmad din yanzu iya kokarinsa yake mata a kan“ cigiyar dan uwan nata' saboda yadda ya ga ta damu a kansa. , ’ Da taimakon Shukura da kuma na matar da ‘ . Momy ta dauko mai kwalliyar amare, aka gyara amarya Saudat cikin wani tsadadden cotton lace mai laushin gaske kalar dark pink an qawata shi da bakaken fulawoyi da wasu qananun duwarwatsu, masu kama da yarfin gwal, daurin kallabin da aka kafa mata duk wanda ya kalla ya san daurin‘shago ne don ba irin wanda muka sabayi bane gashin ’ nan nata an saki kadan gefen fuskarta sauran kuma an nade shi an saki jelarsa a kan gadon bayanta inda aka kawata wuyanta da kunnenta zuwa yatsun hannunta da tsadaddun gwala-gwalai Sannan suka dora ta a kan bakin takalmi mai matsanancin tsini sai ka ce wadda ta hau tsani sai yar qaramar jakarsu wadda ba ta wuce girman tafin hannuba Amarya kam ta fita batun bayyana irin kyawun da ta yi ma bata lokaci ne, don k0 lokacin .da ta ke zama a kan kujerar da aka tanada ' don amarya, saf ta zauna tamkar mutum- mutumi, ko ace aljana don kyau, kai ka zata zana ta aka yi ba ‘ wai mutum bace “Ana kiran sallar magriba aka tashi daga kamun, a lokacin ne kuma Dr. Ahmad da abokansa ' ' suka iso gidan cikin tsadaddun motocinsu, don haka gidan ya kara rikicewa, Shukura ta shiga busy don ganin ta karrama angwayen da abubuwan ciye ciye da tande-tande. Saudat kuwa duk kunya da nauyin Dr Ahmad ne ya hana ta sakewa da kyar Shukura ta samu ta je ta gaishe shi shima sai da ta yi da gaske a lokacin da ta shiga falon da aka sauke su gogan nata yana kishingide saman doguwar kujera abokansa sun sa shi a gaba suna ta hayaniyarsu, ' inda shi kuma yake ta faman kallonsu yana cin , tuffa apple. Saudat ta ji tamkar ta nutse a lokacin da suka hada idanu, sai taga ma tamkar shima kara masa kyau akayi, farin yadin neke jikinsa ya Kawatar Da kyar ta yi ta-maza suka gaisa da abokan nasa sarakan surutu kamar zasu hadiyeta Kowa burinsa ya fadi albarkacin " bakinsa ita dai ta gaza tofawa sabuda kwarjinin da angon nata da ya cika falon, ji take duk girman dakin ya yi mata kadan, sauqinta ma daya Shukura da ta tare ma rigimar domin don kuwa ita wurin dan banzan surutu ba ‘daga baya ba. Dr. Ahmad wanda tunda ta shigo falon bai * ,tanka ba har sai da ya lura zolayar abokan nasa za ‘ ta iya nutsar da Saudat cikin qasa don kunya, ~ sannan ya yunqura ya mike a kasale tamkar wanda aka yi wa dukan tsiya. , Ya nufi inda amaryar tasa ta ke nutse cikin kujera ya sa hannu ya tayar da ita tsaye yana fadar, “taso mu bar nan Madam kada su samin ke ciwon kai Kamar jira suke suka yi kansa, amma bai kula suba yana rike da hannunta suka fice daga falon kai , tsaye harabar waje suka nufa, ya jawo musu wasu fararen kujerun roba suka zauna cikin rumfar da aka tanada don hutawa Dr Ahmad ya yi wani murmushi mai kama ‘ 'da dariya lokacin da yake Kokarin lallai sai ya hada , ido da ita amma ta Ki yarda shi dariya ma ta ba shi, ya tallabe kuncinsa yana fadar, “Oh ni Ahmad na ga ta kaina, haka zamu yi dake kenan?” Ya Kara sa dariya, “Lallai yarinya aiki ya , ganki bama kadan ba, amma fa kin yi kyau don‘ lokacin da ki ka shigo falon sai da nayi suman wucin gadi har wani kishi na ji ya yunkuro min yadda na ga kartan nan na kallonki shi ya sa na harna .gaza magana , Duk yadda zuciyar Saudat ta ke cike da alkunyarsa sai da dariya ta kwace mata jin yadda ya kira wayayyun abokansa da qartai, Dr. Ahmad ya kafe ta da manyan idanunsa yadda ta ke dariyar ’ tata cikih nutsuwa kallon da yake mata ya sa a dole ta gimtse dariyarta, hakan ya yi daidai da sauke wani gwauron numfashin da ya yi tare da lumshe manyan fararen idanunsa ya shafi sumar qeyarsa yana kallon farar moter da take shigowa cikin gate din ’gidan a dan nesa da su kadan aka faka motar daga ita har shi idonsu na kan motar. Zuciyar Saudat ta yi wata mummunar bugawa lokacin da mutumin da ke cikin motar ya fito shi da wata zukekiyar mace kai tsaye inda suke zaune suka nufo har a lokacin kirjin Saudat bugawa yake ta gaza k0 da kwakkwaran motsi. “Hamid dinne k0? ’ , Dr. Ahmad ya watso mata tambayar yana . kallonta Kai kawai ta iya daga masa don a lokacin har sun qaraso cikin sallamarsu inda Hamid ya miqawa Dr Ahmad barin fuskarsa ‘dauice da fara a suka yi musabaha Hamid na riqe da hannun ' Dr Ahmad ya taya shi murna tare da yi masa fatan aikhairi cikin sanyin jiki, Saudat ta gaishe shi amma ga mamakinta har a lokacin da fara,a akan fuskarsa ya amsa mata a. tare da yi mata fatan aikhairi ya nuna zukekiyar macen dake tsaye " wadda akalla shekarunta ba zasu haura ashirin da daya ba . Yacé, “Ga Kausar nan takanas 'muka taho‘ tare don ta taya ni murnar aurenki, ita ce amaryar ' tawa“. Ya juya kan Kausar din, “Kausar ga Saudat ’ Da‘ fara’a a fuskarta ta miqa wa Saudat hannu suka' yi musabiha cikin sigar zolaya ta dubi Dr. Ahmad tana fadar, “Godiya mara: adadi, .ka taimake ni tunda ka kasa‘ angona don da yanzu Kausar ta shiga cikin jerin sahun matan da za ayiwa kishiya a wannan watan,na gode ‘ Dariya suka yi su dukkansu ganin yadda Dr. '"‘ Ahmad ya Saki fuska babu alamar damuwa a yanayinsa ya sa Saudat ta saki jiki ta mike ta riko hannun Kausar tana fadar, “Bismillah‘ yar uwa mu shiga daga ciki mu gaisa sosai " Dr Ahmad ya mike shi ma tare da miqa wa Hamid hannu yana fadae “Ni ma abokina. mu shiga daga ciki gida na kula abin yar wariyar launin jinci ce”. , Duka dariya suka sa suka rankaya suka nufi cikin gidan Zuciyar Saudat fes, ba qaramin dadi tajiba Ganin yadda Dr. Ahmad ya karBi Hamid din cike da ‘ farin ciki. Ba Karamin mamaki‘ ta yi ba yadda Hamid ya samu labarin aurenta, kodayake auren da kullum sanarwa ake a gidajen tal'abijin da radiyo lallai ita kanta ta san ba Karamin matsayi Hamid yake da shi a Zuciyarta ba, har cikin ranta ta ji Kausar ta kwanta mata don kawai tana matar Hamid hatta rasa inda’za ta_saka ta, ta kawo mata wannan ta' kawo wancan har sai da Kausar ta dakatar da ita, ita kuma Shukura ta ci gaba da dawainiya da Hamid din. ' . Ba su suka bar gidan ba sai qarfe goma na dare don sai da suka gaisa da Momy da Alhaji . Ashiru sannan suka tafi a cewar gobe Hamid zai maido , Kausar gaskiya su duka sun yaba da ‘ matar Hamid din don ba qaramar kyakkyawar mace ya samu ba, wayayyiya kuma yar boko. ’ Ba Saudat ba hatta Momy da Shukura sunyi _ mamakin irin makudan‘ kudin da Hamid din ya baiwa Saudat wai ta. siyi abin da ta ke So, tunda ‘bai _ samuya siya mata komai ba. Lallai Hamid ya dauka Saudat da muhimmanci a rayuwarsa, haka da ma al’amarin Ubangiji yake .Washegari ita ta kama ranar asabar da misalin qarfe daya na rana aka daura auren " Saudat da angonta Dr Ahmad Mukhtar ; daurin aure ne wanda ya tara manyan mutane kala daban-daban tun daga gida Najeriya har zuwa sauran Kasashen qetara abbas daurin auren ya kafa tarihi a cikin Dandagoro ‘ Motoci suka dauki amarya da tawagarta zuwa gidan mahaifinta da ke Dandagoro don wai a can ne za,a dauki amarya, kamar yadda Alhaji Ashiru ya bukata ba don ran Momy yasoba ta amince Haka manyan motoci suka kwashi amare aka nufi gidan mahaifinta, amarya’ Saudat dake lullube 'cikin mayafl Kirjinta ya shiga dukan tara-tara don ba tasan irin tarbar da dandazon Jama,ar zasu samu a gidan nasu ba. Haka suka shiga cikin gidan mahaifiyar Shukura da DR murja qawar Momy na riqe da amarya har cikin gidan. Inna Laure da ke durkushe bakin murhu na ganinsu ta zabura ta mike tsaye tamkar sabon kamun hauka ' : Fuskar nan tata dukta gauraye da majina da ' hawaye saboda hayakin wuta ciki kaduwa take fadar, “Wannan dandazon haka fa sai kace na masu zuwa yaqi na menene? ' Dr Murja tace“Au maigidan naki bai Fada miki bane? To amarya ce aka kawo gidan ubanta a dauke ta a ciki”. ‘ Kida a ruwa mai tada haukan dodo tana fadar haka Inna Laure ta yo kanta da masifa, ‘ ‘Amaryar ukan abun uba za a kawo gidan ubanta, k0 ita uwar amaryar bata sanar muku ba ‘yar tata ruwa biyu bace? Ai ba ta da uba don haka an dai daura aure a gidan nan amma babu dan iskan da ya isa ya-shigo min gida don a ci min zarafi Mahaiflyar Shukura ta kwantar da murya ta ce, “Haba baiwar Allah meye kuma abin cin fuska don' dai kawai dan zaman da za a yi wanda bai =wuce na minti talatin ba?” Ai kamar jira ta ke ta koma kanta, “Ke rufe mani baki kin ji tsohuwar banza, ai da ma garin 'banza a farau-farau din wofi yake qarewa, gida dai nawa ne, kuma dole ku bar min abuna in ba haka "ba'wallahi sai in cinna wa gidan wuta mu hadu mu duka mu qone za ku fita k0 kuwa ba zaku fita ba?” Ai kafin wani ya ba ta amsa ta kwaso itacen da ke cikin wuta ta yo kansu * *‘ Malam Bala da ke kokarin shigowa cikin gidan ya yi wani kukan kura ya yi kanta ya rike ta ta 'baya, hakan ya sata fasa wani razanannen ihu tana kokawar kwacewa, ya murde hannunta ya na cewa [8:43AM, 06/02/2017] 🙆🏼‍♂@lh@ji🙆🏼‍♂: YAR. TALLAH CHAPTER32 Complete Bakida hankaline ya kwace itatuwan tana ihu tana tirje~tirje da zuba ~ munanan ashariya ya danna ta dakinta ya kulle, ko,a haka aka barta ya ishe ta azaba saboda tsananin zafin da ake kwararawa a garin ga shi dakin ba shi da tagar shan iska k0 kadan ’ Malam Bala ya nufo su yana basu hakuri akan abin da Inna Laure ta yi musu, ita kuwa Saudat idonta na kan mahaifinta, za ta iya cewa tunda take da shi ba ta taBa ganinsa ya yi irin kayan da ya yi ba, saboda tsadadden yadin da ke jikinsa wanda aka yi wa dinkin yar ciki da babbar riga, kayan sun sha aikin hannu. Dr.Murja ce ta ja mayafin Saudat ta rufe mata fuska, wanda haukan da Inna Laure keyi ya sa ta budewaba tare datasani ba Malam Bala ya kwasa ya nufi dakinsa yana yana raWar jiki, sai ga shi ya dawo dauke da manyan tabarmi shi da kansa ya shimfida mnsu a tsakar gidan suka zazzuna shi ‘kuma ya juya ya gita baifi minti sha biyar ba sai ga shi ya dawn do. wasu almajirai dauke da ledojin pure water dana kwalayen ‘ ,lemuka katan-katan‘ aka jibga musu, ita dai Saudat ta cika da mamakin abin da kr faruwa sun kwashe mintina talatin a gidan sannan angwaye suka zo daukar amaryarsu don haka Shukura da mahaifiyarta suka tasa Saudat a gaba har zuwa zaure inda mahaifinta yake don ta roqi gafararsa. Saudat ta durkusa a gabansa jikinta ya yi sanyi ba ta san abin da za tace da mahaifin nata ba, abubuwan da suka faru ne a baya suke dawo mata cikin zuciya, tamkar a yanzu ne suke faruwa. Tamkar Malam Bala ya san abin da ta ke tunani, sai ga shi yana furta, “Don Allah don Annabi Saude ki yi hakuri ki yafe min duk abin da na yi miki wanda ki ka sani da wanda ma ba ki sani ba. Na san na zalunce ku sai dai~ na san sharrin shaidan ne, don Allah don Annabi ki yafe min kafin na mutu wallahi ban san abin da-zan cr da Ubangijina ba, tabbas na ga ishara a rayuwata, kuma na yarda zakaran da Allah ya da chara k0 ana muzuru ana shawo sai ya yi, Saude ki yafr min don Allah don Annabin rahma “sunyi mamakin yadda kuka ya ci qarfinsa ba suboda tun yana maganar muryarsa ke rawa, ba karamin‘ sanyi jikin Saudat ya yi ba jin kukan dattijon. nata don haka ba tareda zuciyarta ta qara tuna mata komai ba ta ce “Ka yi hakuri Baba, ni ban rike ka da komai ba, wallahi na yafe maka’ Cikin kuka Malam Bala yace ‘Wallahi ni “ ba kiyi min komai ba Saude, inma kinmin ba yafe miki Allah Ubangiji ya yi miki albarka, Ya ba ku zaman lafiya da zuri’ a dayyaba Saudat bata iya amsawaba, sai dai Momyn Shukura ce ta amsa sannan ta kama Saudat ta mike suka rankaya aka nufi mota da amarya , Masu kai amarya suka dunguma a motoci, amma abin mamaki sai ga wasu daga cikin jama’ ar , unguwar cikin masu rakiyar amarya babu goro “ ballantana katin gayyata Har motocin daukar amarya zata dags Malam Bala ya kwaso da sassarfa yana daga musu ‘ hannu, suka tsaya ya nufi motar da Saudat ke‘ciki, ta taga ya mikamata wani Kunshi a baKar leda. Ta karBa cike da girmamawa, sannan motocin , suka rankaya da amarya sai garin Abuja, alqawarin, Allah ya cika, don karfe biyu na rana a gidanta ya yi mata wanda yake a unguwar ‘yan majalissu. Saudat ba ta kasa gane gidan ba duk da kuwa canje-canjen da ya qara samu, haka suka rankaya Zuwa bangaren amarya, sai dai mucr barakallahu fihi, masha Allah don Dr.» Mariya ta murza naira wurin fiddo da ‘yar tata don haka‘ tsarin gidan zuwa tsarin kayan ya qawatar da falukan da aka zuba suka yi dace da juna, don komai an sa shi cikin tsari, don haka duk wanda ya je kai amarya sai da ya firgiga wai ahakan ma donyawancinsu sun saba shiga irin gidajen amma ‘yan Dandagoro kuwa sai ga su darshe a kan marbles suna ta faman zare na mujiya, Shukura dai na rike da amarya, Saudat wadda ta ke jinta tamkar a saman gajimare wasu daga cikin dangin ango ne krta faman dawainiya da su tun daga abubuwan ci zuwa na sha harna tande-tande irinsu dambun shinkafa dambun nama, shinkafar kaza, soyayyun kaji, farfcsun kaji, donut, meatpie spring roll, fried rice, hadadden salad chips din kwai da dankalin Turawa, fruits kala-kala har da wanda ba su taBa gani ba da sauran kwalayrn lemuka da robobin ruwa masu sanyin gaske. Saudat dai da ke cikin mayafi tana jin karadin Farida qanwar Ahmad don ta fi kowa kai wa da kawo wa an agama sallar la’asar motoci suka kwashe ‘yan kai amaryar don dawo da su gida bayan an cika su da sha tara ta arziki. Sai a lokacin kuka ya zo wa Saudat ganin duk za su watse su barta, Shukura ce ta rungume ta tare da yi mata rada, sai ga ta tana kuka da dariya, lokaci guda duka suka rankaya suka tafi suka bar Farida rungume da Saudat kowa ya watse Su Farida da wasu ma ’aikatane ke ta faman gyare-gyaren gida, sai ga shi cikin dan lokaci Bangaren nata ya zama very need, babu abin da ke fita a cikinsa sai qamshin room freshner mai sanyin Farida ta dawo bedroom din da Saudat ke ciki ta zauna gefenta cike da kulawa ta ce “Aunty Saudat ki shiga bandaki ki watso ruwa sai ki dauro alwala don lokacin sallar magriba ya yi”: Saudat ta Ki k0 motsawa haka kawai take jin gabanta na faduwa ba ta da wani kuzari. ’ Faridat ta yi murmushi tana fadar, “Ho Aunty anya wannan dari-darin da ki ke a cikin * gidanki zai fisshe ki kuwa?” Ta Kara murmusawa, “To yi hakuri dai muje na raka ki ki watso ruwan” . Ta sa hannu ta riko Saudat din don haka ta sauko daga kan gadon tana Kokarin bin qofar fita, Farida ta ce, “Ina za ki kuma? Ki shiga bandaki din nan mana dama don kar a Bata. mikine ya sa na ce su shiga wancan bandakin da ke dayan falon”. ' Saudat ta dan yi sororo don ita dai ‘a iya ganinta ba ta ga wata‘ kofar bandaki ba don tsakanin falo ma da bedroom gilas ne ya raba ‘ tsakaninsu, don haka duk cikin falon babu wata alamar kofa. , Faridat ta mike ta nufi wurin gilas din ta danna‘ yar wata alama sai ga shi ya raba kansa biyu ya fidda wata‘ yar hanya wadda ta zarce har cikin . bandaki Farida ta shiga ciki, don haka itama: _ Saudat ta bi bayanta. Farida ta gwada mata. yadda Zatayi amfani da komai na bandakin sannan ta fita dan ta samu damar watso ruwan ' Tana fitowa ta samu Faridat ta qara gyara gadon har ta ciro mata kayan da zata saka don haka Saudat ta nufi inda sallaya ta ke ta yi sallar magriba ta zauna, har lokacin isha ya shigo sannan ta yi sallar tare da shafa’ i da wutiri wadda Momy ta . koya mata tare da wasu daga cikin ayyuka na addinin musulunci tana idarwa ta mike ta nufi kan gado inda Farida ta ajiye mata kayan da za ta saka, wasu lallausan yadi ne kalar baki mai taushin gaske wanda aka kawata shi da wasu fararen duwarwatsu masu haske. Saudat ta saka yadin a jikinta Wanda aka yi'wa dinkin riga da siket yadin ya bi jikinta ya lafe a farar fatarta. Farida ta shigo tare da ‘yar siririyar -sallamarta hannunta na rike da wani madaidaicin faranti da ke dauke da ‘yan wasu kananan kwanuka ns tangaram. Ganin Saudat ya sa ta ta saki murmushi, “Yauwa Aunty Saudat k0 ke fa? Ki dan yi make up k0 ya ya ne Murmushi kawai Saudat ta yi ta nufl gaban ,dressing mirro ta ja kujera ta zauna tana kallon gaban madubin .wanda ke shake taf da kayan x kwalliya irin na wayayyun mata da suka san kansu. Body lotion kawai .Saudat ta dauka ta murjawa jikinta, sannan ta murza wa fuskarta wata yar karamar hoda wadda ta ida fito da tsabar kyawun fuskarta, sannan ta shafa wa laBBanta wetlips gloss, sai da ta Kara gyara gashin kanta ta dame shi da farin ribbon kwara guda ta sake shi a baya, sannan ta yi sassaukan daurin kallabi a kanta wanda ya Kara fito da ita, ta dauki ‘yan qananan ‘yan kunnayenta da sarqa na diamond ta maqala a kunnenta ta 'saka ‘yar qaramar sarqa ta dauki turarenta body spray ta mammatsa a‘ gaBObin jikinta, ita kanta ta san ta yi kyau irin wanda ke nutsar da zuciyar maigida, ta juyo ta nufo inda Faridat ke tsaye tana tattara ‘yan komatsanta. Muryar Saudat na rawa ta soma fadar,“ina kuma za ki je don Allah : naga kin yi lullubi kina tattara jaka?” Faridat ta mike tana kallonta da murmushi a kan fuskarta, “Maigida ya yi kira Saudat, amma fa kin yi kyau sosai, nasan yayana zai yaba don Allah kada dai a yi masa rowa". Tayi maganar tana dariya tare da shafar beauty point din Saudat din ta juya a gurguje ta fice tana fadar, “Don Allah ki ci abin da na hado miki, please Auntyna". Saudat da ke tsaye ta bita * da , idanunta masu kama da madara harta ta fice ba yadda ta iya haka ta sadakas ta koma da baya ta zauna a kan gadon nata wanda kr fitar da , sassanyan Kamshin bed freshner Ta miKa hannu ta janyo tiren da Faridat ta ajiye mata ta soma dudduba abin da ke cikin‘ yan kwanukan da kofinan, na farko gasasshen nama ne wanda ya ji kayan yaji, sai na biyu wani' irin nama ne Wanda aka yi wa 'wata irin dahuwa mai danko, sai' kofi na farko tsumin markadaddun ‘ya'yan itatuwa ne, dayan kuma danyar madarar shanu ce , mai kyau. “ Duk da ba ta fahimci amfanin abubuwan a gare ta ba, ta daure ta ci sosai kamar yadda Faridar ta roKa. Ta dauki tiren ta fice da shi ta mayar da shi a kicin da ke falonta na biyu, ta tsaya tana kallon kicin din, komai na ciki tsab.tsab gwanin kyau, ko falon wani mai kudin sai haka, don haka maimakon ta bar kayan a haka, sai ta soma tara ruwa ta wanke ’su cike da sha’awar komai na kicin din Ba ta ji motsin shigoWar mutum a kicin din ba sai dai ta ji an rungumo kwankwasonta ta baya. * ” Ta fasa wata razananniyar Kara tare da juyowa hakan ya ba shi damar rungume ta . gabadaya a jikinsa tare da lalubar kunnceta cikin ’ sanyin muryarsa ya soma rada mata ‘yan guntayrn ~kalmomin da ta rinka jinsu tamkar a. cikin mafarkinta. Cikin sanyin jiki ta soma Kokarin zame‘ jikinta hakan ya sa shi rike hannayenta duka biyun 'yana fadar, “Sauara tsaya ki ji, bakinki kawai za ki ara min just minti biyar kawai’ Wani kallo ta watsa masa a razane tare da fizge hannunta za ta tsere ya yi'saurin damko ta yana dariya ya ce “Ke da wasa fa nake miki, wallahi a gajiye ma nake ba kiji gaBobina ba gaskiya na samu Saudat da wahala, mu tafl ki taya ni na watsa ruwa”. Duk yadda ta so ta kwace abin ya faskara saboda irin kyakkyawan rikon da ya yi mata a dole ta bi shi. ‘ Kai tsaye dakin baccinta ya nufa da ita, ya dire ta a kan gadonta yana fadar, “Zauna nan, bari na watso ruwan na flto” ' Ba ta tanka masa ba ya juya ya nufl wurin shiga bandaki ya latsa ya shige _ ita dai kallonsa kawai ta ke amma da shawararta yabima da bai cire baqin yadin da ke jikinsa ba, don ba Karamin kyau ya yi masa ba abinka ga farar fata. Ta lumshe idonta ta bude lokaci guda tare da komawa. da baya ta kwanta a kan gadon, hakan ya yi daidai da shigowar Asma ’cikin dakin. Kirjin‘ Saudat ya yi wata. mummunar bugawa tamkar saukar aradu, don dama tun dazu ta kasa nutsuwa tunda ta fahinci a gidan Asma aka kawo ta Asma ta shigo falon sosai tana kallon Saudat . ta kada kai tare da maida murfin kofar ta rufe tare da murza key, abin da ya ida firgitar da Saudat ke nan ta tashi zaune cikin matukar rudani tana kallon Asma wadda ta jingina bayanta da kyauren shigowar tana kallon Saudat bakinta dauke da wani malalacin murmushi mai cike da mugunta, sannan ta soma nufo inda Saudat din take zaune Cikin tsananin firgici da rashin sanin abin yi Saudat ta soma ja da baya. Asma ta ja ta tsaya tana fadar, “Ina za ki je ‘yan mata? Da ma kin tsaya don kashe ki zan yi wannan shi ne huquncin kuskuren da ki ka aikata ' wannan ranar ta yau za ta zamo darasi ga sauran ‘yan aikin da ke kokarin auren mazan iyayen gidansu. Wallahi yau zan kashe ki kuma na kashe banza, duk duniyar nan babu wanda ya isa ya bi ‘ miki hakki”. “ Kafin Saudat ta yi wani yunkuri tuni har A‘sma ta» kai mata cafka tana kokarin Shakar wuyanta kamar wadda ta sha wani abin maye, kira ' ta ke, “Yanzu zan kasheki sai dai yazo ya tarar da gawarki; amma ba dai ke ba don Asma tafi karfin ‘ ‘ ta. hada miji da kaskantacciya, wulakantacciya ~ matalauciya wadda ta yi gadon ;siya da talauci”. Kokawa ce ta kaure tsakaninsu, Asma na qokarin kama makasar Saudat,’ ita kuma Saudat na qokarin kwatar kanta sai dai qarfin badaya ba don Asma tafi Karfln Saudat k0 daga yanayin jiki ma tafita qiba, tunda ita har yanzu ba ta da Kwari kamar a kama a karya, don haka Asma ta samu nasarar kayar da ita ta janyo filon da ke kan gadon abin da ya jazawa Saudat kurma wani uba-uban ihu kenan, sai dai za mu iya cewa ihunka banza, kururuwarka wofl don kuwa babu wanda zai iya juyo ta. Tana qokarin danne fuskar Saudat da filo, ita kuma tana kokarin kwatar kanta tana ihu, a haka Dr. Ahmad ya fito daga bandaki yana dame da tawul da wani dan karami a hannunsa yana tsane jikinsa, idonsa da kunnensa suka yi mummunan gani da ji cikin kidima ya yi kukan kura ya dira inda suke, ya fincike Asma da Qarfinsa, amma har a lokacin ba ta daina boren sai ta cafko Saudat ba. Abin da ya sa shi kifa mata wani zazzafan marin da ya sa ta dafe kunci kenan cikin tsananin kidima don har wata wuta ta ga ta gifta mata cikin tsananin takaici da zafin zuciya ta ke kallon Dr, din da idanunta da suka ciko da hawaye jikinta ya yi sanyi matuka ta soma magana cikin muryér kuka. , “Ahmad ni ka mara? Ni ka mara saboda wannan abun? Lallai ka tsokano wa kanka tsuliyar dodo dan na“ rantse maka da Allah sai na halaka yarinyar‘ nan, sai na ga bayanta, sai na kawar da ita daga doron qasa. Kai in ban da ma asiri ya rufe _maka idanu wannan har mace ce wadda za ka 'wulakanta ni a kanta”. Ta ja kwafa tana girgiza kai, “Tabbas sai ka yi dana sanin abin da ka aikata min banza, butulu, mayaudari ai da ma duk dadinka da jaki watarana sai ya yi maka tutsu don da ma dan halas ne kadai ke maida halarci. . .” “Shut up! You are very stupid, get out! Sakarar banza na ceki bar nan”. Duk Dr. Ahmad ne’ ke maganar cikin tsananin fushi tare da nuna mata hanyar fita. _ Tsananin baqin ciki da takaici suka sa Asma yin wani malalacin murmushi tana kallonsa cike da ‘ qunar zuciya ta girgiza kai ' “ ba zan yi mamakin duk abin da ke fitowa daga bakinkaba Ahmad, amma ina so ka sani na shirya daukar dukkanin tashin hankalin da ka ke ganinka iya kuma ni din nan wallahi sai na sa ka zubar da hawaye, sai kayi nadamar sanina a rayuwarka.. “It is enough Asma I say get out!!” Ganin yadda idanunsa suka birkice ta san komai zai iya faruwa idan har ya yi irin wannan fushin don haka ta ja kwafa ba tare data sake . magana ba ta bude qofarta fice tana murza yatsunta alamar za ya gani ke nan. Tana fita ya maida Kofar ya kulle sannan ya nufo inda Saudat ta ke kwance tana faman shesshekar kukanta. Dr. Ahmad ya zauna bakin gadon tare da janyo ta jikinsa ya rungume ta sosai da‘yar sanyayyar muryarsa ya soma lallashinta, “Ya isa haka nan Saudat, kada kanki yazo yana ciwo, ki yi haquri kinji, duk abin da ta fada karya ta ke ba za ta iya ba”. Saudat ta dago kanta da sauri tana kallonsa cikin idanunta da ke zubar da hawaye ta ce “Yanzu abin da ta yi bai tabbatar maka da zata iya aikata abin da ta fada din ba?” Dr. ya Kara rungumrta, “Ki kwantar da , hankalinki zan Kara ja mata kunne sosai kin ji k0?” Ba ta iya ce masa komai ba sai ma ta mayar da kanta a kirjinsa tana kukanta kasa-qasa, Dr. ya tallafo kanta da hannunsa ya soma bin fuskarta yana lasar hawayen da suka Bata mata fuska, a hankali ya soma zarcewa har zuwa kan Wuyanta da‘ Kirjinta ya rinka bin gabobin jikinta har zuwa‘ tsakiyar kanta yana sinsinar lallausan gashin kanta wanda ya sha gyafa, sai daukar ido yake. Saudat ta tSinci kanta cikin wani irin yanayi ’ wanda bata taba tsintar kanta a cikinsa ba tsawon rayuwarta, ita kuka shi kuka duka an rasa mai rarrashin wani, kiran sallar farko shi ya dawo da Dr daga duniyar rudanin da ya shiga, iya jarunta da hakuri Saudat ta yi shi, sai dai duk yadda ta zata abin ya wuce tunaninta. Ta yi kuka har muryarta ta dusashe don ta azabtu ta kuma sha wahalar da ba zata misaltu ha, shi kansa ya rude ganin yadda ya wahalar da ita, don haka ya sure ta ya nufi bandaki da ita da kansa ya tara ruwa masu dumi a bahu ya gasa mata jikinta, sannan ya sa ta dauki niyya ta yi wankan janaba, ya taimaka mata suka flto daga bandakin kai tsaye saman gadonta ta haye, saboda yadda jikinta ke faman kwankwatsa. Cike da tausayawa ya raBa gefenta Ya shiga mammatsa mata jiki yana rarrashinta da kalamai masu dadi, har ya samu bacci ya yi awon gaba da ita, sannan ya mike ya nufi bandaki ya yo wankansa ya dauro alwala yazo ya zura jallabiyarsa sannan ya fito inda shimfidar sallarsa ta ke ya rinka. jera nafilfilu, , sai da ya ji ana kiran sallar asuba sannan ya sallama ya yi addu,o in da zai yi na godiya ga Allah, ya maida sallar asuba. Yana gamawa ya mike ya nufi inda Saudat ke kwance tana kukanta yana son tayar da ita. amma yana tsoron ya tsokano wa kansa rigima ba yadda ya iya a dole ya tayar da ita din yadda ya . zata kuwa hakan ya kasance don tana farkawa kuka ‘ ta sa masa ya samu ya rarrashe ta da taimakonsa ta dauro alwala ta yi sallar sannan Dr ya sure ta suka koma kan gadon suka kwanta yana rarrashinta tare da rirrike ta tamkar tsoka daya a miya Karfe sha daya daidai Saudat ta farka daga baccin da ya kwashe ta, ta bude idanunta sosai babu Dr. a gadon don haka ta lallaBa ta mike ta nufi bandaki don watso ruwa, sai da ta tara rowan dumi ta gasa jikinta sosai sannan ta yi wankanta sosai ta fito ta ja kujerar dake gaban madubi ta zauna. Ta janyo lotion ta murza wa jikinta, ta dauki kayan kwalliya ta yi ‘yar sassaukar kwalliyarta, ta qara gyara gashin kanta wanda ta cude da mayuka masu laushi, ta sa ribbon kwara daya ta daure gashin kanta ta fesa masa hair freshner, ta mike ta nufi wurin wardrof ta bude ta ciro wani swiss lace mai sulBi irin mai rawa-rawa kalar jinin kare maroon an masa adon' fulawa light pink dinkin riga da siket, Saudat ta saka kayan a jikinta wanda suka .dace da kalar farar fatarta. “Dinkin ya hau jikinta matuka ta nufi gaban madubi ta kafa daurin kallabinta sannan ta saka dankunne da sarka fashion kalar pink ta dauki body spray ta bi jikinta ta mammatsa ta nufi cover din ,da aka tanada dan ajiye takalma ta soma tunanin kalar da za tasaka. ‘ Dr. Ahmad ya turo qofar ya shigo da sallamarsa, Saudat taji tamkar ta aza da gudu don idan akwai wanda ta ke jin kunyarsa to bai wuce Dr‘. Ba a yanxu, shi kuwa kai tsaye inda ta ke ya nufa fuskarsa dauke da fara’a yana fadar, “Kai babyna wannan kyan fa duk nawa ne?” Ya ida maganar tasa tare da dora kansa a kan bayanta yana sunsunar kamshinta. . Saudat ta yi saurin zamewa za ta ruga ya sa dogon hannunsa ya riko ta yana dariya, tare da fadar, “Lallai yarinya kina tunanin za ki iya tsere min ke nan?” * Saudat ta sa tafukan hannayenta ta rufe Fuskarta da su tana jin tamkar Kasa ta tsage ta shige ciki, Dr. ya sa hakoransa ya cizar mata ‘yan yatsu abin da ya sa ta saurin bude fuskar tare da ‘yar siririyar Kararta cikin shagwaBa kenan ya lakace mata hanci yana fadar, “Marowaciya Allah da kin Kara hana ni kallon kwalliyarki sai na cinye miki bak8” ’ Saudat ta yi rau-rau da idanu tana kallon inda ya cizar mata. Ya yi saurin rike hannun yana fadar, “Ayya 'am sorry dazafi ko?’ Ba ta tanka masa ba ta zame hannayenta zata wuceshi ya yi saurin. cimmata yana fadar, ' ' “Tuba nake ‘yan matana mu je ki karya kin ji”. Bai saurari abin da za ta ce ba ya riqo ta suka nufi kicin, ya zaunar da ita a kan daya daga cikin kujerun da suka zagaye Katon dinning table din glass, ya cr“Zauna a nan yan matana, me za a kawo miko?” Saudat ta dago tana kallonsa sai a lokacin ta lura da shigar da ke jikinsa, baqin wando ne jeans da Karamar T.Shirt sai apron da ya daura fara tare da zungureriyar farar hula irin ta kuku, Saudat ta yi murmushi ta ma rasa abin da za ta ce masa. Ya dan matso daf da' ita, “Ina jinki Madam, me za kici?” ‘ Saudat ta dauke kanta tana fadar, “Ni fa da , kaina nake son in girka”. , Shi ma ya kwaikwayi maganar tata ta hanyar fadar, “To ai ni ma tuni na hada miki wani special girki wanda zai gargade miki kunnuwa” Dariya Saudat ta sa sosai, saboda salon da ya yi maganar da shi, shi kuma ya dauki faranti da serving spoon ya bubbude food flask din da ke saman tebur din ya kalle ta, “Me za a. zuba wa , Hajiyar , akWai soyayyar agada plantain, akwai pizza akwai soyayyen kwai, akwai sandwich tare da Lol ga asma ga saude akwai rikicifa [9:08AM, 07/02/2017] 🙆🏼‍♂@lh@ji🙆🏼‍♂: YAR. TALLA CHAPTER 33 da soyayycn kifi gasassun kaji a side kuma tafasasshen ruwan zafi ne me zan zubo wa gimbiyar tawa?” ‘ Saudat ta yi murmushi tana kallonsa ya riqe _ ludayin zuba abincin sai ka rantse wani kwararren . kuku nr ta lumshe idanunta ta bude lokaci guda tare da fad'ar, “Ni dai kunu nake son sha”. . ‘ Dr.ya ware ido cikin firgici yana fadar, ’ “‘Kunu kuma baby? Karfa kice min an karBi 'takardun ajiya ta jiya har an yi min sing?’ » . Saudat ta zumburo baki tana fadar, “Ni dai *wallahi bana so”. ‘ Ya langwaBe kai yana‘kwaikwayonta, “Ni dai wlh baba so”. Dariya ta Kwace wa Saudat harda kyalkyalawa, duk yadda ta ke Jin nauyin Dr sai da ya kangarar mata da idanu, har ba ta san lokaCin da . . ta saki jiki da shi ba a dolenta. Sun yi break dinsu sosai don da ya lura ma «Saudat tsattsakuran abincin take mikewa ya yi tsam ya janya ta jikinsa ya zaunar da ita ya shiga ba ta ‘ abincin da kansa Tun tana turjewa har ta gaji ta saki jikinta, saida ya tabbatar ta qoshi sannan ya kyale ta ya ja " hannunta suka mike suka nufi falo inda suka baje .inda yaketa Koqarin ya ga ta saki jiki da shi “ Karfe biyar na yamma taga ya yi shirin; fita zucayarta ta yi mata wani iri ta zuba masa idanu ba tare da ta iya tankawa ba Dr yana lura da yadda yanayinta ya sauya lolkaci guda, amma sai ya mika mata hannu, “Taso mu je Madam in zazzagaya dake kiga Bangarenki ki kuma gaisa da ' ma,ai katanki” ' Ba musu Saudat ta mika masa hannun nata ya janyo ta suka fice daga falon sai da suka ratsa 'faluka kusan hudu sannan suka hau matattakalar .bene suka sauka falon qasa; sannan suka koma falon da ya’ fi kowane girma a cikin gidan, a cikinsa kuma ke da Bangaren ma’aikatan har su'uku ‘yan mata biyu dattijuwa guda, sai kicin wanda yakr ta ' ,waje, nan kuma akwai mutum biyu masu girki kwararru mace da namiji. Sai da ya zagaya da ita ta ko’ina na Gangarenta wanda tsarinsa ya yi matukar burge Saudat komai na ciki ya yi mata, musamman wuraren shakatawa da wurin hutawarta. Suna gama zagayen gidan ya ja ta waje har inda harabar motocinsa suke da sunan rakiya, ai ' suna isa wurin motarsa ta tubure sai ya tafi da ita ' Dr ya riko hannunta yana fadar, “Tsaya kiji bafa dadewa zanyi ba, just minti talatin na dawo su Momy kawai zan je in gaisar, insha Allahu ba zan jimaba Saudat ta kWantar da murya kafin tace “Allah ya kiyaye” hanya Dr ya dan zuba idanu kafin ya ce Kinmin izini da gaske har cikin zuciyarki na tafi karfa sai na dawo in fuskanci fushinki” ‘ ' Saudat ta dan yi dariya tana fadar, “Haba ni na isa? Ai sai” Bangazar da akai kai mata ce ta katse maganar da take qokarin yi, ta yi taga-taga ta fada ‘_ kan motar da ke gabanta, kanta ya bugi motar, Saudat ta dafe goshi ta waigo tana ganin mai ,wannan aikin, ba ta yi mamakin ganin Asma ba wadda ta sha gaban Dr; har jikinsu na gugar juna. Saudat ta ji wani irin abu ya dakar mata zuciya tamkar saukar guduma, musamman yadda taga ya kafe ta da fararen idanunsa ba ya k0 son kiftawa, yana kallon yadda take magana cikin kissa da gadara “Zan yi magana da kai?” Ya mantar da tasa muryar kasan tata, “To ga shi kuma fita zan yi yanzu a yi haquri sai na ‘ dawo”. , . Ta watso masa wani fari mai kama da harara ' sannan ta juya a fusace ta nufi inda sabuwar ’ motarta ta ke mai baqin gilashi “ta fada mazaunin dircba tare da dagawa escort Dinta hannu ; ta ja abinta a guje ta fice DR Ahmad ya yi wani dan gajeran murmushl tare da kallon inda Saudat take wadda . tsabar takaici yasa ta wasu siraran hawaye suka biyo kuncinta, Dr. ya yi saurin janyo ta jikinsa yana fadar, "Am sorry tawan baki dai ji ciwo ba ko?” r Saudat: ta watsa masa wani kallo mai cike da tuhuma kafin tace “Au ban ji ciwo bama zakace . bayan kana kallon abin da tayimin , Ya ce, “To me zan ce mata Saudat? Ta yi tayine don ta Bata min rai, ke kuma ta sa ki Bata kwalliyarki to da na nuna mata ban damu ba ai ga shi ta tafi k0, kuma ke don ina tsaye sai ki ce ba za ki iya rama wa kanki fada ba sai dole nina rama miki Ai sai kuma na zama marar adalci a tsakaninku k0 ba kya so na zama adali ne?” Saudat ta zame jikinta cike da da haushi ta Nufi hanyar bangarenta. * Dr ya girgiza kai a zuciyarsa yana fadar, “Mata ke nan” ‘daniel ya bude masa gidan baya na motarsa, ya shiga sannan ya rufeshi kuma ya shiga gida gaba mazaunin direba ya ja shi suka tafi Waiwaye adon tafiya Inji Malam Bahaushe bari mu waiwaya baya muji shin wane ne Dr Ahmad Muktar? Profassor Mukhtar L Kabir shahararren dan boko ne, kuma fan kasuwa da sunansa ya kewaye Najeriya, kuma muhimmi a cikin lamarin da yawa na shidda a cikin masu kudin qasar nan. Bai taba rike wani mukami na siyasa ba amma kuma yana daga cikin masu fada a ji a harkar siyasa da mulki don yana tare da manya-manyan ‘yan siyasa tun daga na qasar nan har zuwa qasashcn qetare. Ahmad shi dan dansa na farko, sai da aka kwashe shekaru goma sannan aka yi masa kanwa Farida kuma daga su ba a sake haihuwa ba, tun tasowar Ahmad mahaifinsa ya so ya yi karatun boko mai zurfin gaske don haka yana kammala firamare ya tura shi qasar America a can ya yi sakandire dinsa ya hada doctoring degree dinsa a kan abin da ya shafi harkar siyasa da mulki. Yana kammalawa ya ce ya tsaya iya nan, duk da mahaifinsa bai so ba a dole ya kyale shi kasancewarsa na dan gaban goshi. ' Dr. Ahmad bai fara harkar siyasa ba sai da ' ya hadu da Asma don ita ce ma ta cusa masa ra’ayin yin siyasar amma shi ya yi karatunsa ne ba don yana ra’ayin yin mulkin siyasar ba amma saboda' ita shi ma ya tsunduma kan harkar siyasar wanda a yanzu ta rage saura ‘yan watanni su sauka kuma ya yi alkawarin yana sauka ba zai sake komawa ba don bai ga abin da yake nema ba da zai dora wa kansa wahala ba, a matsayinsa na dan majalissar dokoki ta tarayyar Abuja, amma fa inji shi saboda a ganinsa mulki wahala ne, kuma bala’I ’ ba kadan ba ga wanda ya kasa tsaida gaskiya da amana Wannan kenan . K0 da Saudat ta koma sashinta kai tsaye bédroom dinta ta nufa ta fada kan gadonta ta kwanta zuciyarta cike da haushin abin da Daktanta ya yi mata, da taimakon sanyayyen sanyin air conditioner wani nannauyan bacci ya yi awon gaba da ita. * Ba ita ta farka ba sai qarfe bakwai da rabi da yan mintina ta yi saurin saukowa daga kan gadon zuciyarta na mamakin yadda har ta bari ta yi baccin yamma ga shi har magruba ta kubce mata. Cikin gaggawa ta dauro alwala ta fito ta yi sallar magriba da isha tare da shafa’I da wuturi sannan ta tsaya gaban madubi daga tsaye ta yi ‘yar kwaliyarta marar nauyi, sannan ta nufi gaban wardrobe ta ciro kayanta ta saka English west riga da siket. ~ Fara: shirt silk sai dogon siket dinta baki irin mai fadin nan yana da adon fararen fulawowi ta warware gashinta ta daureshi da farin ribbon 'Kwara guda sannan ta makala wa kunnenta‘ yar: ‘ Karamar barima ta gwal ta yi kyau sosai, ta koma. tamkar irin yan matan turawan ta zira silifas na fata, sannan ta fito falonta ta tsaya gaban talabijin din da ke girke gaban bango tana canza channels .”Dr. Ahmad ya shigo da sallama Saudat ta amsa ba tare da ta juya * ta kalli inda; yakeba ya shigo cikin falon ya dire katuWar lrdar dake hannunsa mai dauke da' tambarin Alshukur shoppin mall ya fada kan kujerada alamun gajiya a tace da shi ya mika wa Saudat hannu, ‘Come on my baby, wallahi I am "‘ very tired zo in ji duminki kusa da ni ko na wartsake" . Saudat ta waigo ta dan kalle shi kamar ta share shi sai dai girman da yake da shi a cikin idanununta baza su barta ba, don haka ta nufi inda yake ta zauna kujerar da ke nesa da tasa tare da fadar, “Sannu da zuwa” Dr ya tsare ta da narkakkun idanunsa wanda ya tilastta wa Saudat kallon kafet ya koma ya jingina bayansa da makarin kujerar tare da fadar .“Zo ki duba ledojin nan ki ga abin da ke ciki”. . Saudat ta mike ta :nufi gefensa ta durkusa kan kafet tare da janyo ledar daya ta shigo da ita, ta bude kwalaye ne har guda biyu, manya sai dai daya yafi daya girma ta dan dago tana kallonsa yace “Bude mana Bare kwalayen” .tayi Saudat ta gyara zama sannan ta soma bue qaramin kwalin sai ga razananniyar ‘ waya iphone6plux kwance a cikin kwalin ta ajiye a gefe ta bude babban kwalin sai ga wata Yar qaramar abu mai kamar komfuta ta daago tana kallonsa da niyyar ta . yi magana ya katse ta ta hanyar saukowa dagakan ' ’ kujerar ya zauna gefenta ya karbi yar abar ya Kunna yace“Wannan da kike gani sunanta ipad kamar camputer yake zaki iya shiga yanar gizo da komai _ Ta ciki nasa an zuba miki abubuwa da yawa a ciki Wanda zai bude miki Kwakwalwa, kuma zai rage 'dinga debe Niki kewa idan har bana nan tunda ldan kinga ni din ba mazauni bane cikin watan man da wuya inyi kwana hudu a gida, saboda abubuwan da ke kaina ;NASA milki kudi a ciki nayi miki saitin komai a . yanzu zan fara koya miki yadda ake amfani da ita,. : Sai kuma wayar da nayi miki alqawari gata ' nan akwai akwai sabon sim a ciki na hada Saka miki kudi a ciki, akwai lambar Momyn Shukura a ciki idan za id kira su”. ' Ya zura hannu cikin aljihu sai ga key din mota ya miqa mata, “Wannan kuma makullin‘ . ‘mota ne saboda ko watarana za ki ji sha awar' ” yin tuki da kanki, saboda zuwa makarantar dana sai miki form din shiga makarantar social . development Abuja, karatune zakiyi nayan watanni zaki zama basic illetrate wata hudu zakiyi ki gama ki amshi certificate dinki sannan ki tafi ki karanci social welfare wata Tara , sai ki Kara karBar certificate wanda shi zai ba ki damar ki tafi jami’a ki hada difloma in kina da bukata ma har digin‘ dinki sai ki hada da fatan za ki maida hankali don ke maki zama wani abu watarana”. Tsabar jin dadi da murna Saudat har ta rasa . ta yadda zata iya furtawa wani Abu idonta ya ciko da kwalla idan akwai abin da take q auna a rayuwarta bai wuce karatu b a, ashe kuwa Ubangiji zai cika mata burinta, tamkar za ta yi kuka ta fara zayyano masa godiya. Ya daga mata hannu, “Ya ishe ni haka Saudat, ban miki don ki gode min ba, Ubangiji za ki gode ma wa don Shi ne Ya kwato miki, kuma idan kina sha‘awar shiga islamiyya to ita ma ki shirya ranar asabar mai zuwa in kai ki Da’awa akwai sashin matan aure sai ki rinka zuwa ranar asabar da lahadi da safe kawai, taso mu je in gwada miki motarki". Ya riko hannunta ya mikar da ita ba tare da ya sake bari ta fadi abin da ta ke son fada ba suka nufi harabar waje Ganin shirgegiyar motar da Saudat ta yi sabuwa dal ba karamin daga mata hankali ya yi ba, don ba irin motocin da ta saba gani bane a kan titi, ta qara wa motar kallomai suna Expedition baka mai bakin gilashi wadda ta mamaye wurin tsayuwar motoci uku ta” maida kallonta kan Dr. tana fadar Ni yanzu ya za a yi ' in iya jan wannan matar Yallabai? Tayi girma sai ai ta mamaye titi gaba daya ' Dr, ya tuntsure da dariya yana fadar, “Bakauya sai kawai Expedition ta mamaye titi, saboda tsabar shirmenki? Muje ciki daga gobe zan .fara koya miki tukin k0 don na ci dariya" Saudat ta bata fuska ba tare da ta yi magana ba, ya ja ta suka nufl sashinta yana Kara zolayarta, wurin koya mata ipad din ma sai da ya ci dariya saboda qauyancinta don Saudat dai ko a waya ba komai ta iya ba, to bare ta fahinci ipad cikin sauki ' ta ida qulewa ne ta yi zuciya ta yi ciki abinta, yana kiranta ta Ki kula shi don haka shi ma ya tattara ya ‘ biyo ta da tarkacenta . Washegari tunda safe Dr. ya bar gidan saboda meeting din da ke gare shi, don haka Saudat ta sha baccinta sai wurin azahar sannan ta shirya ta fito donta ‘karya kai tsaye dinning saidata wuce falo uku sannan ta isa don nan ne inda Dr ya sanar da ita ' kuku zai rinka shirya abinci, ta zauna ta karya , sannan ta koma falonta ta dauki ipad ta soma latse ’ latse, sai da ta gaji ta rufe ta dauki waya ta danna lambar Mammy wadda suka kWashe fiye da mintina talatin '” sannan ta kashe ta kira Shukura, itama sun dade suna hira kafin su yi sailama, tana mamakin k0 “katin nawa ne maigidan ya loda mata? ,Har bayan sallar isha Dr bai shigo gidan ba, harta fara tunanin k0 lafiya, hakan yasa ta sa‘ waya ta kira' shi, a daidai lokacin da yake shigowa gidan ya ce , “Shigowata kcenan Madam, na gaji sosai ki sameni a Bangarena don Allah”. Ba ta Bata lokaciba ta Kara gyara kwaliyarta ta fita daga Bangarenta ta nufi nasa Sangaren wanda ya sa bangarensu tsakiya, wato Bangaren Asma da nata. Tana shiga ta same shi baje a falo ya yi daidai yana kallon allon talabiji. ’ ' -Tun kafinta zauna ya ce, “Don Allah jeki hada min ruwan wanka a bandaki”. Ba musu ta hau sama ta shiga bedroom din nasa sannan ta shiga bandaki ta soma hada masa‘ ruwan, tana gamawa ta juyo ta fito suka hade yana tsaye gefen bed dinsa ya c ire kayan’dake jikinta, daga shi sai dan Karamin gajeren wando.‘ kallo daya Saudat ta yi masa ta raBa shi za ta wuceya sa hannu ya fizgo ta, yana fadar, “Gidan wa za kine yarinya? Ai ke za ki min wankan nan” _' Ganin da gaske yake yasa Saudat ta ’ .sOma qoqarin kwacewa, amma sai da ya sureta ya ‘shiga bandakin da ita, tana ta shure-shure ya ' tsumbular da ita cikin qaton bahon wankan da ta cika masa shi da ruwa, duk iya borenta sai da ya . .ya rabata jikinsa hakan ya tilasta . ta“ kyale shi ya yi mata wankan, ya yi nasa saman ya ; fito da tawul guda sukai Fitowarsu ta yi daidai da ihun da Asma ta kurma cikin tsananin firgici . “Me zan gani Ahmad? Me ye wannan?” . ‘ . Ta Shiga jadA baya tana nuna shi cikin tsananin firgici har ta fice daga falon ‘_ Saudat ta yi matukar razana da firgicin ganin yadda Asmar ta same su saida yasata ‘zubar da hawayen kunya da takaici don ta lura ma ‘ shi gogan love, a jikinsa sai ma Kokarin shirya tada , yake ba tare da ya bi ta kan hawayen da ta keba, ba _ yadda ta iya ta kyale shi har sai da ya zura mata _ sabuwar rigar bacci wadda ya feshe da sassanyan turaren romaine. _ Yana zura mata rigar Saudat ta fada kan gadon tana kukanta Kasa-kasa bai kula ta ba sai da ya saka kayan baccinsa riga da wando farare masu ,. Laushi da Kamshi sannan ya hayo kan gadon ya tankwashe qafafuwansa tare da fadar, “Tashi zaune ‘ mu yi magana” Ganin da ya yi vata da niyyar motsawa yasa shi janyo ta jikinsa ‘ yana fadin meye abin kuka Don dan ta Shigo ta ganki tare da mijinki Meye a ciki? kukin manta ni din mijinkine kuma ba , haramun muka aikatawaba? Haba Saudat ya kamata ki fara girma haka nan ai ke abin alfahari ne a wurin kishiyarki ta zo ta same ki da mijinki a haka k0 kamai kin kunsa mata wani abu a zuciya, kuma dole daga yanzu za ta fahinci keda ita matsayinku iri guda ne a wurina, amma shi warin, kukan me ye ma’anarsa?” Shiru ta yi sai dai ta sa bayan hannunta ta goge KWallar hakan ya sa shi ya gyara mata filon da ke gefensu ya kwantar da ita yana fadar “Ki wanta yanzu zan je in dawo, just a minute”. Bai saurari abin da za ta ce ba ya sauka daga kan gadon ya kashe wutar dakin ya kunna bedsid lamp ya fice kai tsaye Bangaren Asma ya nufa wanda rabonsa da shigarsa zai iya cewa ya kwash fiye da shekara kamar yadda ita ma bats shigowa nasa bagaren saida wani Kwakkwaran dalili A hankali ya taka qafarsa cikin bedroom din nata wanda sanyayyen Kamshin touch neke tashi babu haske a dakin sai lamp bed lamp duk da bai iya hango taba. akan gadon ba, amma yanajin shesshekar kukanta ' Sai da ya kunna: makyallin wutar dakin haskce ya gauraye ko' ina sannan ya nufi wurin gadon ya ja bed chair ya zauna yana kallonta tamkar ba Asma‘ da ya sani ba, ‘yar gayu mai tsananin kwalliya tamkar aljana amma duk ta firgita kanta gashin kan babu gyara duk da tsananin tsawonsa da laushinsa, amma ya turmushe babu alamar kwalliya a fuskarta, ‘yar doguwar riga ce baqa mai dogon hannu ta saka, babu k0 kallabi Asmar da ko ciwo bai hana ta yin kwalliya. " Ya gyara murya kafin ya ce, “Tashi zaune mu yi magana”. Ba musu ta tashi din, don ta fahinci shigowarsa dakin, ta tashi a zaune tana kallonsa ba tare da ta daina ku;kan nata ba. Dr. Ahmad ya miqa hannu saman bedside drower dinta yadauko tissue ya mika mata, “Karbi wannan ki goge hawayenki”. ‘Ba musu ta karBa tana gogewar shi kuma bai jira ba ya dora da fadar, “Me ya yi zafi haka Asma?” Tamkar ba za ta tanka masa ba, sai dai ma zuciya ta zarce duk yadda ta ke tunani, don ta azabtu ta kuma sha wahala a kan share ta da Dr. Ahmad ya yi tare da nuna mata da ita da rashinta duk daya ne a wurinsa kafin zuwan Saudat din harya zuwa yanzu. duk abin da ta ke yi juriya ce da karfin hali da nuna jarunta, amma ita ta sani Ahmad wani Bangare ne na rayuwarta ya koyar da ita darussan qaunarsa masu wuyar goguwa a shekarun baya da suka wuee tabbas idan ta rasa shi za ta iya shiga kowane irin hali. Cikin muryar kuka ta soma fadar,’ “Ahmad, dama ashe xaka iya ba sa wata mace a matsayi irin nawa a zuciyarka har ka iya' hada jiki da ita? Ahmad ina alkawari da amanar da “~ ke tsakaninmu? Ina soyayyar da ka ce kana min? ' da ma wannan ita ce kaunar da ka ke labarta min? : Ahmad za ka iya tuna rabonka da ka shigo nan inda-nake? Daidai da ranar da aka kawo maka amaryarka Ahmad ya kamata a ce ka shi go ka duba halin da nake a ciki amma k0 a waya ba ka nemceni ba k0 in mutu k0 inyi rai ba damuwarka ba ce, yanzu bar wannan kodaddiyar‘ yar matsiyatan ta fi ni daraja a cikin idanunka Ahmad yaUshe ka daina sona?’ Sai da ya Bata wasu ‘yan mintuna yana kallonta tare da mamakin wai yau shene ya ga weakness dinta (kasawarta) yau Asma ce ta sauke duk wani girman kanta da dagawarta tare da jin kai da jinkanta ”wai yau ita ce ke jero wadannan zantukan ta ajiye gayun , ta yi tuBus lallai‘ yan maza sun yi taushi. _ Ya dauke idanunsa a kanta ya ja aji kamar ba zai yi magana ba, ya basar, “To kedin da ki ke sona Asma me son ya amfanar don a matsayina na mijinki ba ni da wata daraja a wurinki, ba ki da lokacina baki da lokacin kulawa da ni da tarairayata a matsayina na mijinki, sai dai ki tura ‘yan aiki su bani kulawar‘ da nake bukata daga gare ki ‘saboda Yar Tallah will be airing this week tonight only ANYTHING BY 11 TO 12 [3:21PM, 08/02/2017] 🙆🏼‍♂@lh@ji🙆🏼‍♂: YAR. TALLA CHAPTER34 kawai kin raina ni,’ kina ganin daidai kike dani don kawai na baki ~‘yancin yin duk abin da ki ke so, ki rinka yi min gadara da isa? Don kawai kin ga ni din mai tsantsani ne, ban damu da harkar wasu mata ba, k0 k0 don kin fahinci ina sonki ne kuma kina da kyau shi ya sa kike min abin da ki ka ga da ma ni ban sani ba? Ba ki san daraja taba, balle darajar aurenaba shin ni dutse ne da zan kasa watsar dake na samu wata? Tunda matan ga su nan tamkar ledar pure water wanda suka kai ki da ma wanda ba su kai kiba”‘ ‘Asma ta dago da sauri tana kallonsa, ya “ daga gira. “Yeah, duk abin da ki ke takama da shi su _ ma sauran matan suna da shi, sannan don kuma a rashin kunya za ki nemi rusa min kwanciyar , : hankalin iyali don kawai kin ga ina kyale ki? Wallahi I will surprise u matukar ki ka Kara shiga, hurumin Saudat zan iya yi miki komai, Sannan da kike kiranta da matsiyaciya, kodaddiya, ai Saudat ta fiki komai a idanuna kuma don ina sonta na aure ta kamar yadda kema nake sonki na aure ki, kuma duk wani shirmenki da haukanki ba zai sa na rabu da ita ba don ita ce rayuwa ta, wallahi tun ranar da naga tausayina. a cikin idanunta na soma jin soyayyarta a zuciyata, kina tunanin'wannan soyayyar ta wasa ce? Ki gafarce ni Asma, da gaske nake ina son Saudat, wallahi I can anything please Asma ki taya ni mu so ta in har da gaske kina sona“ Wani inrin ihun kuka Asma ta saka saboda yadda ta rinqa jin kalamansa na neman tarwatsa ' mata zuciya, ta daga masa hannu cikin karaji tana fadar, “Stop it... don’t repeat dis word to me again please, ba sai ka bude baki ka fada ba zan gane ka daina sona ba, ba sai ka fada ba Ahmad zan fahinci ka gama dani ba, na yi condaim a wurinka amma don Allah ka kyale ni haka da wadannan zafafan kamalan naka masu qona min zuciya da sassan jiki”. Dr. Ahmad ya koma kan gadon tare da rungumo ta yana fadar, “Please Asma, wallahi ban fada miki wadannan maganganun don ranki ya Baci ba, iya gaskiyata nake fada miki, kuma ki daina fadar na daina sonki, wallahi har yau har gobe sonki yana nan a zuciyata, kuma a shirye nake da na ninka shi idan har ki ka gyara halayyarki, ki tuna fa ke din mai ilimi ce amma ki rinka abubuwan da mai hankali ba zai yarda da su ba, haba Asma”. Kukanda ta ke tare da sauke ajiyar zuciya shi ya tabbatar masa kalamansa suna shigarta, ya dago da kanta ya Dora a kan kiirjinsa yana share mata hawaye, tare da gyara mata gashin kanta cikin _ sassanyar muryarsa ya ci gaba da fadar, “Am sorry Asma, ki yarda da mi wallahi har yanzu ina sonki idan har ki ka sauke gadara da girman kanki zaki same ni a duk yadda ki ke so. A yanzu Asma ta daina kukan sai dai sauke numfashin da ta ke, Dr. Ahmad ya janye ta daga jikinsa ya barta a kan gadon ya nufi bandaki ya hada mata ruwan dumi da beltn robb sannan ya fito ya kinkime ta ya nufi bandakin da ita Sai da ya watsa mata ruwan ya wanke ta sol sannan ya fito da~ ita da kansa ya Ciro mata kayan baccinta ya bata ta saka, sannan ya kamo hannunta ya kwantar da ita a. kan gadonta ya ja lallausar bargonta ya. lulluba ta ya kashe wutar dakin tare da furta mata sai da safe. Ba ta da yadda za ta yi tana jinsa harya fice duk yadda ta so danne zuciyarta sai data fashe da. kuka, don ta sani a yanzu Ahmad ya yi mata nisa, ta riga ta yi sake har dan hakin da ta raina yazo ya tsone mata ido, duk yadda zuciyarta ta‘ kai ga. chashewa a kan al’amarin fa namiji a yanzu ba ‘abin da tafi bukata sama da shi k0 don ta lura yana neman subuce mata? ne ’ ’ Yau din nan ta kasance mata rana mai muni saboda kunnuwanta sun jiye mata mummunan albishir din rasawanda tafi so fiye da kamai a rayuwarta, kuma yau ne rana ta farko data fahimci. rashin kyautatawarta a zamantakewarta da mijinta kuma a yau ne ta gane kuskurenta bayan ta rasa shi, kuka ta ke sosai tare da nadama marar amfani. . . Asma mace ce mai zafin kai da izgili da raina mutane, ba ta da son jama’a k0 kadan shi ya sa ma k0 abokai ba ta da su, sai dai tana da raguwar zuciya, ba ta da juriya ko kadan nan da nan damuwa ke wujijjiga ta saboda ba ta saba da ita ba, don haka a yanzu tunaninta guda, hanyoyin da za ta bi don ganin ta karkato da hankalin mijinta a kanta sun koma irin zamansu na farkon aurensu. Bangaren Saudat kuwa tunda ya fita ta tsinci kanta da wani irin matsanancin kishi da damuwa ta gagara runtsawa, sai faman juyi ta ke tana duba agogo, amma har sha biyu saura bai shigo ba, zuciyarta ta ba ta yana wurin Asma, to me suke har yanzu da bai dawo ba? Wannan tunanin ne ya sa ta ' soma ‘yar kwalla, sai karfe daya saura kwata na dare ta ji ya turo Kofa, hakan yasa ta saurin jan bargo ta lulluBa tamkar mai bacci, tana jinsa ya hayo kan gadon ya ja ta jikinsa ya kwanta tare da lulluBe su da bargo ya soma shafar kanta yana kiran sunanta, amma ta Ki motsawa tana jinsa har ya gaji ya yi shiru, a haka bacci ya yi awon gaba dasu ‘ Da asuba ma suna kammala sallah Saudat ta mike za ta fice taji muryarsa na fadar, “Ina kuma zakije?” Saudat ta dan waiwayo kadan kafin tace' ‘Bangarena” . . Ya dan harare ta,“ “Okay nan din da yake gutsirarki ake k0? To dawo ba inda za ki". ~ Kamar kada ta dawo din hakata daureta ' koma kan gadon tana kokarin hawa ta kwanta ta ji ya tisgota ta fada kirjinsa, har tana buge fuska. Ya dago kanta yana fadar, “Wai fushin me ki ke da ni? Saudat laifin me nayi tun jiya ‘da na fita na dawo na lura kinata kumbura shiyasama nayita magana ki ka share ni, ki ka nuna bacci kike, oya fada ‘ min menene? ' Saudat ta kasa tankawa saboda irin riqon da yayi mata, dakuma rashin takamaimain amsarda zata bashi don tasan babu abin da ke damunta, wandayawucc kishi, dakunya kumatadubeshi ta 'fada masa hakan, saidai damamakinta tajiyana fadar, “Kishi ne ko Saudat? To sha kumruminki Ahmad naku ne kubiyu, kuma soyayyarki daban ce acikin zuciyarsa. Ki sani ni Ahmad ban buqatar kowa tunda na same ki, ban bukatar abinci in dai. inajin muryarki, bani da bukatar ruwa matukar ~ akwai miyau abakinki banbukatar iska indai 'akwai numfashi acikin kirjinki bananeman komai tundana sameki,karki kara damuwa balle har shaidan ya cusa miki wasu al’amura kisa. a zuciyarki kedin matata ce wadda nakc so’in Asma matata ce wadda nake so, dukkaninku an halicce ku ne da hakarkarina kuma kowaccenku tana bukatar farin cikinta daga gare ni, idan na wulakanta dayarku saboda 'daya ki sani Allah ba zai bar niba please Saudat ina so in yi adalci a tsakaninku”. Saudat ta lumshe idanunta tare da kwantar da kanta a kan kirjinsa tabbas abin da ta gani cikin idanunsa ya tabbatar mata da haqiqanin gaskiyar da yake fada, ya kara matse ta a jikinsa ta ji tamkar za ta rabu gida biyu ta bude baki da hanzarinta, .tana fadar, “Wayyo Yallabai, za ka karya ni”. maimakon ya sassauta mata rikon sai ‘ma ”ya qara matse ta a qirjinsa ta yadda .Saudat ke jin bugun zuciyarsa da sauri da sauri cikin wata irin , rikitacciyar murya ya soma fadar, “Yi haquri don Allah Saudat, wallahi ji nake tamkar in maida ke cikin jikina don Allah Saudat duk abin da ki ka zama a rayuwa kada ki Juya wa zuciyata baya”. Wani irin abu ya rinqa sukarwa Saudat ‘a Zuciya, tausayinsa ya kashe mata dukkanin gaBobin jiki, duk da ta fahimci ya saki layi amma hakan bai hana ta rungumar mijin nata ba, wanda ta kejin *tamkar a yau ne ta soma sonshi. a Cikin sati guda Saudat ta yi matukar shaquwa" da Dr. ta saki jikinta da shi ya koyar da ita darussa masu yawa, takuma bude kwakwalwarta ta dauka ba ta zubar da su a kwandon Shara ba, duk abin da ta lura'ya fiso atareda ita shi ta ke masa, har ma ta kara da kalar' nata salon don qarin ~ armashi. ‘ Yau ta tashi da son shiga kicin duk da kuwa yau din ne miji zai bar hannunta ya koma gurin Asma, tunda kwanakinta sun Kare, so ta ke ta yi girki da kanta, duk da ba wasu abubuwan kirki ne ta iya ba a bangaren girki, to amma gani ta ke gwamma nata girkin sau dubu a da wanda kuku ya yi musu daren jiya, wanda ya sa ta amai babu ' gaira babu dalili, shi kansa Dr. bai iya cinsa ba da ya kira kukun don jin abin da ya girka musu, sai cewa ya yi tuwon alabo ne da miyar manja,sai drinks din kayan itatuwa da madarar ‘ruwa, da danyan kwai, girkin sai kana Kasashen qetare. Abin da ya qara tayar wa Saudat da zuciya kenan take ta sa ya shigo kicin ya nuna mata yadda ake amfani da kayan na’ urorin kicin din nata har Dr na musu dariya. Don haka yau tunda sanyin safiya ta gama shirinta cikin wata doguwar rigar shadda ash colour wadda aka yi wa aiki tun daga sama har qasa bata daura kallabin rigar ba sai dai ta daura qan qaramin mayafl a kanta wanda ya tsaya iya kafadarta, ta zura takalminta flat shoe ash colour sannan ta fice; ta nufa kicin din ta bar Dr nata sharar baccinsa. Sai dai ba girin-girin ba ta yi mai, ga shi dai babu abin da babu ta bangaren kayan .abinci tun daga na gida Najeriya har zuwa na kasashen qetarc sai dai ba ta san yadda za ta sarrafa suba. Can dubara ta fado mata ta yanke shawarar ta girka musu alala da kunun gyada don a nan din ta san ita gwana ce don kuwa sune sana’ar Inna Laure, don 'haka ta nufi store ta debo wakenta ta zuba a turmin ta sa ruwa ta surfa sannan ta nufi wurin famfo ta wanke shi ta fitar da dusar ta bude freezer ta debo kayan miya wadanda suka daskarar da Kankara ta gyara su ta zuba a cikin wakenta, ta ' sa a blander ta markade suka yi laushi sosai sannan ta juye a roba mai fadi ta kawo spices ‘kala-kala ta zuba ta yanka alayyahu da albasa masu yawa, ta zuba ta sa manja da mangyada ta motsa sosai sannan ta daddaura a fararen ledoji ta zuba ruwa. a tukunYa ta zuba alelenta a ciki ,ta dora a kan gascooker sannan ta koma ta debo kullun gyadarta ta dama kunun gyada sannan ta koma tana gyara kicin din nata. Dr, wanda ya farka ya laluba ya ga ba ta nan . ya mike ya nufi bandaki ya watso ruwa ya fito ya ’shirya cikin qananan kaya bulue din jeans sai milk din T shirt ya gyara sumar kansa, sannan ya zura silifas dinsa na fatardamisa ya fice kai tsaye kicin din ya nufa, ya ja ya tsaya ya tokare bayansa da qofar kicin din tare" da zuba hannuwansa cikin aljihu yana kallonta. " Saudat ta juyo tana kallonsa lokacin da ta gama jera abincin a kan tebur din bakinta dauke da murmusln ta ce “Bismillah mana, ya za ka ci irin girkina, don Allah ka shigo” Ya tabe baki yana kallonta tare da make kafada alamar ba zai shigo din ba. Saudat ta nufe shi ta riqo hannayensa tana fadar, “Don Allah ka shigo ka gani ka taBa cin alala?” Bai tanka ba hakan kuma bai hana ta jansa ba har bakin‘ dinning table ta ja masa kujera ya ‘ zauna sannan ta budr kula ta ciro masa alala kwara biyu ta sa masa a faranti, ta tura masa tare da cokali mai yatsu ta zuba masa kunun gyada wanda ya ji madara ta mika masa tare da cokalin shan tea, ta , langwaBar da kai tana fadar, ‘Don Allah kaci kaji na iya?” Murmushi ya yi kafim ya cokana cokalin ya . soma ci bai tanka ba sai da ya cinye duka biyun tana zaune tana kallonsa zuciyarta cike da jin dadi, > ita ma ta zuba nata ta soma ci. Yana cinyewa ta dube shi na Karo maka, ya waro ido, “Haba Madam tausaya min bani dai kunun insha”. Ta miKa masa ya sa cokali ya soma sha a nan fa ta ga santi ya dube ta, “Amma wannan ‘ kunun da madara ake yinsa k0?” Saudat ta girgiza masa kai alarnar a’a, ya jinjina kai, “Amma Allah wannan ana iya bude kamfani a rinka yin na roba a rinqa siyarwa, ba qaramin ciniki za a yi ba don ‘ni ban taBa shan irinsa ba fa”. ' Saudat ta tuntsure da daniya, ta ciro mayafin kanta ta nufe shi tana fadar, “Kai yallaBai bari in yi maka waigi kada ka fadi”. Ya tuntsire da dariya tare 'da riKo ta yana Kokarin kwace kallabin suna dariya, nan fa kokawa ta kaure basu suka baro kicin din ba sai sha biyu saura, ya tsaya a falo tare da fadar, “Jeki dauko key din motarki mu je in miki rijistireshon din makaranta daga nan mu je islamiya in sai miki form sai mu wuce Hikima Driving School a nan za su koya miki tuKi tare da shaidar yin tuqi idan ba mu yi yammaci ba sai mu wuce mu gaida Momy”. Dadi ya cika'Saudat ta makale shi tana murna, sannan ta yi falonta da gudu ta dauko key din ta fito, yana nan tsaye inda ta barshi ta dafo kafadarsa kamar irin abokinnan nata, duk da kasancewar ya fita tsawo amma‘ ita ma din doguwa ce, haka suka fice tana ta zuba masa shagwabanta, shi kuwa sai Kara narke mata yake ita kuma tana Kara sangarcewa, shi da kansa ya ja su a motar: kasancewar mai bakin gilas ce Sai da suka fara zuwa wani studio aka yi mata passport sannan suka wuce social. development ya yi mata rajista da komai da kornai, suka wuce islamiyya nan ma ya siya form, a take ya yi mata komai, suka wuce Hikima ba su suka kammala da komai ba sai shidda saura na maraice, sannan Dr. ya nufi gidansu da ita. Sun yi sa’a kuwa Faridat ta zo don haka 'Saudat ta samu tattali da kulawar da ta dace daga Momy din har Farida zuwa Daddy kowa sai riritata yakce, ana wasa da dariya a nan nema taji’ Dr. zai yi tafiya jibi zuwa qasar Singpore ya yi sati biyu ya dawo majalissar Abuja, ya kwana guda sannan 'ya wuce America ya yi sati guda ya biyo ta Mexico city ya yi sati guda sannan ya wuto gida. Zuciyar Saudat ta yi mata ba dadi don a yanzu ta riga ta saba da mijinta ba ta qaunar abin da zai sa ya yi nisa da ita tun a lokacin ta soma jin ta fara missing dinsa basu baro gidan ba sai bayan sallar isha. Suna. dawowa kuwa ya wuce sashinsa, kai tsaye Saudat bandaki ta nufa ta watsa ruwa ta fito ta saka kayan baccinta riga da wando baqaqe masu . Iaushi ta daure gashin kanta da ribbon kwara guda sannan ta zira takalnan baccinta masu laushi ta fito falo ta fada kan kujera ta ja ipad dinta ta soma latse latse don a yanzu ta soma Kwarewa, duk a warin'ta shigowar mijinta ta ke saurare Shi kuwa tunda ya isa sashinsa ya watso ruwa ya saka riigar baccinsa mai budadden gaba, ya fito falonsa ya zaunakan kujerar falon ya ja Karamin tebur na gilashi ya! dora computer dinsa ya soma turn sakonni, a haka Asma ta shigo falon ta same shi ya dago ya dube ta ta cikin siririn farin gilashin da ke idanunsa, sanye ta ke da kayan bacci skinny dress kalar suminti sun mata matukar kyau tamkar saukar Kasar Saudiya don da ma can Asma kyakkyawa ce ajin farko Ta zauna saman kujerar dake gefensa cikin jan aji ta soma fadar, “Sannu da aiki dear”. Ya amsa da, “Yauwa, kina lafiya?” Ta dan tabe baki kafin ta ce, “Lafiya na shigo dazu ka fita” , Da kai kawai ya amsa mata ya ci gaba da abin da yake tsawon wasu ‘yan mintina falon ya dauki shiru, Asma ta mike ta koma kan kujerar da yake zaune, ta kutsa ita ma ta zauna ta raba jikinta a kan bayansa ta kwanta tana fadar, “So nake na kwanta da wuri saboda yau muna da wani meeting na gaggawa, qarfe biyu na dare”. ‘ Bai tanka mata ba sai dai sakonnin da ta aika masa a gab0bin jikinsa sun yi matukar tasiri wurin saukar masa da kasala , A dole ya rufe computer din ya mikar da ita ya shureta ya nufi dakin baccinsa ya kwantar da ita, ya mike da niyyar yace yayi wa Saudat sai da safe, Asma ta qankame shi tare da saka masa kuka tana fadar, “Haba Ahmad, don Allah boron ya isa haka, karka koma kana daukar alhakina, kana kallo fa da ajina da qimata da 'martaba ta na- karya su na z0 inda ka ke, amma ka Ki ka yafe min kuskurena haba Ahmad ka yafe min haka nan, don Allah wallahi ba zan iya jutre wannan horon ba” Duk yadda ya kai ga mazantaka a wannan karon lamarin yafi karfinsa ganin kasawarsa ya sa ta Kara qaimi wurin cakume shi tare da Kara kunna shi da salon kissarta. ‘ Saudat kuwa da ta gaji da danne-dannenta ta ji bacci ya some kwasarta ta duba agogo, Karfe sha daya da ‘yan mintina ta lalubo wayarta ta soma; danna masa kira tayi ringin harta tsinkebai dauka ba,tasake danna masa wani kiran harsaidatakusa tsinkewa sannan ta ji ya dauka cikin wata dakusasshiyar murya yake fadar, “Saudat bakiyi bacci ba har yanzu? Ki kwanta kinji dare ya...” Din-din taji an datse kiran. , Ta bi wayar dake hannunta da kallo tsawon lokaci zuciyarta na barazanar tarwatsewa a haka ta kwashe tsawon wasu mintuna kafin ta haurar da [pad din da wayar ta. nufi dakin baccinta ta fada kan gado, kishi babu dadi, sai dai haKuri ya zama dole tunda Allah ‘ya. halicce mu Shi Ya halitta auren mace sama da daya. ‘ . K0 da Saudat ta farka da safe bata fito k0 bakin aofar falonta ba, tana kudundune cikin bargo bata sauko ba, haka Ahmad ya turo kofar falon ya shigo. Da sallamarsa yana sanye da wata tsadaddiyar‘ shadda gezna fara mai laushin gaske ta sha aikin hannu, kansa na sanye da hula zanna baka kalar aikin shaddar sai siririn farin gilashi a idanunsa, ya daura bakar agogonsa ta fata wadda ta kwanta ‘ lallausar farar fatar hannunsa wadda bakin gashi ya yi wa kawanya. ‘ Ya yi matuqar kyau musamman yadda fuskarsa ke cike da annuri ya zauna bakin gadon da take kwance tare da yayc bargon da ta lulluba ganin kayan barcine a jikinta ya sa shi saurin duban ago gon dake girke saman bed side drower, qarfe sha biyu da rabi ya waigo yana kallonta lokacin da take gayar da shi, bai amsa ba sai dai ya jefe ta da tambaya, “Lafiyarki Saudat, baki da laflya ne?” . Ta girgiza masa kai ba tare da ta bari sun hada ido ba, tace, “Lafiya ta Iau. ' Ya girgiza kai, “Yarinta na damunki Saudat, yanzu don kina jin haushina shine ba zaki tashi ki wanka ki gyara jikinki ba?” Ya dan ja wani siririn tsaki, “To tashi tunda. *gani nazo kije kiyi wanka kigyara jikinki Saudat ta dauke kai cike da kunya. ta ce “Ni fa ba. yanzu zan yi ba” . Yace “Tokuma wannanne kobaki isaba". Ya sa hannu ya janyo ta tana turjewa, ya kyaleta yana fadar, “Kwanta keki ka sani qazama ke zakita tsami bawaniba donni kuwayanzu Katsina na nufa inyi wa su Momy sallama don so nake inyi isha agarinnan kuma zankai kararki wurin Momy infada mata baki wanka bare kwaliiya... ” Tun kafin ya rufe baki ta zabura ta tashi za ta dafo shi ya yi saurin mikewa yana fadar, “A’a qazama kar ki sake ki taBa ni ki bata min kwalliya, na yi wankana” ‘ Saudat ta bi shi tana kokarin ya tsaya ta ba shi sako wurin Momy, amma bai kula taba, ya fice yana faman tsokanarta. " A dole ta dawo tunda kayan bacci ne a jikinta ga shi ta k0 ina harabar gidan maza ne, tana dawowa dinning table ta 'nufa ta karya sannan ta mike ta koma bedroom dinta ta'nufi bandaki ta watso ruwa ta fito ta sakawata ‘yar sassaukar doguwar riga, sannan ta yi sallar azahar tana gamawa ta fito ta sauko falon qasa ta kira Mansura kukunta, wadda ke shirya abincin ‘safe dana rana, sai Emanuel shi ke dafa na dare. 'Mansura yarinyar ce wadda ba za ta wuce shekaru' ashirin da biyu ba, musulma ce amma ba bahaushiya ba, tana dai jin Hausa sosai, ‘yar asalin , qasar Ghana ce, Saudat ta yaba da girkinta don tafi Emanual iyawa, don haka ta kira ta don ta fara koya jama,a waishin ina yaya rabiu ne?zai dawo ko bazai dawoba? wani saqo ya bama inna mai danwake ta bama saude?meya faru dashi bayan malam bala ya sake masa korar kare daga gidansa a karo na biyu? amsar tambayarku na cikin YAR TALLA CHAPTER35 wanda zan kawo muku gobe idan mai sama ya nufemu da kaiwa kuma yasa ina numfashi naku mai qaunarku mai sonku har cikin ransa qaninku kuma abokinku YAR. TALLA THE END QARSHE CHAPTER35 ASHA KARATU LAFIYA mata. A yau inda aka fara da yadda ake sarrafa shinkafa, tunda suka shiga kicin sai karfe hudu na yamma suka fito Saudat ta nufl sashinta ta yi sallar la’asar. Dr. bai dawo gida ba sai sha daya da ‘yan mintina na dare a lokacin har Saudat ta. gaji da jiransa ta kwanta, don haka ya ajiye mata tsarabar da Momy ta bada a kawo mata, sannan ya fice ya koma bangarensa. Saudat ba ta samu ganin tsarabar tata ba sai da gari ya waye, bayan ta gama shirinta cikin Wani tsadadden materiyal ruwan zuma mai sulbi wanda aka yi wa dinkin riga da siket, matiriyal din ya haska ta sosai. Ta fito falon a nan ta yi karo da ledojin, ta zauna ta zubesu a falon tana duddubawa duk_ kayan girke-girke ne irin na Kasashen larabawa, sai wata hadaddiyar sarka ta azurfa wadda aka yi wa yarfin gwal a cikinta, sarkar ta yi matukar burge Saudat, ta tattara kayan ta maida kicin sannan ta dauki sarkar da yan kunnayenta ta makala, ai kuwa sun yi mata matukar kyau, sun haska ta fiye da wadanda ta fara sakawa daga farko. Ta nufi falonta ta karya, ra mike ta nufi Bangaren maigidan nata don yi masa sannu da zuwa ta kuma jin tadda ya samu Momy din da su Nabil da kuma Nabila. , Tana taka matattakalar dazata'sadatada falonsa sai ga Asma kuma na saukowa.‘ Gabanta ya yi wata mummunar faduwa, kallo daya ta yi wa ,Asma ta dauke idanunta ba tare da ta nuna ta ganta ba. Asma ta bi Saudat da wani razanannen kallo, zuciyarta na wani irin tuquqin baqin ciki, ji ta ke tamkar ta shakaro Saudat har sai ta mutu, hakan ya sa ta lumshe idanunta ta ci gaba da saukowa daga matattakalar bench tana kiran sunan Allah kamar yadda Ahmad din ya vata shawara. ‘ Saudat ta yi matukar mamakin yadda suka hada hanya da Asma salin'alin,to k0 ta fara saukowa me? kai da wuya don irin kallon da ta ga ta watsa mata babu komai a cikinsa bayan tsagwaron tsana da ‘ qiyayya, Saudat ta taho dakin tare da murda Kofar falon maigidan ta shiga da sallamarta. ~ Yana kwance saman gado daga shi sai short ‘ niker riga a jikinsa, ya dora ipad saman ’ kirjinsa yana lallatsawa, yana ganinta ya ture ipad din tare da miqewa tsaye ya rifito ta yana fadar, “Kun hade da Asmako? Allah yasadai bata miki irin haukan nataba?” ~ Saudat ta girgiza masa kai cikin sanyin jikinta. Ya shafi fuskarta yana fadar, “Allah har gabana ya fadi". ‘ Ya zaunar da ita saman gadon shi kuma ya zauna a Kasa yana fadar, “Jiya na dawo na sameki kina ta bacci, kin yi adalci kenan mijinki yana kan 'hanya amma har ki iya runtsawa ba tare: da kin kira ni kin ji ko na isa lafiya ba? Kai Saudat anya kin damu dani kuwa?” Saudat ta langwabe kai tana fadar, “Allah fa na kira ka ta Ki shiga Ya kada kafada tare da fadar “Allah ya sa da gaske ki ke”. Ta dan yi murmushi tare da fadar “Ni na zata fa zanzo in sameka kana shirin tafiya ne Ya girgiza mata kai, “Jirgin Karfe hudu ai zan bi na yamma, k0 kayan ma da zan yi tafiyar dasu ban hada ba” Ya langwaBe kai, “Allah ji nake tun yanzu harna. fara missing dinki my baby bacin karatunki da ba abin da zai hana na tafi tare da ke”; ‘ Saudat ta lumshe ido ta bude saboda yadda maganar tasa ta yi mata dadi, ta mike tana fadar, “Bari na hada maka kayan” Ya ce “Yauwa tawan, da kuwa kin kyauta” Saudat ta nufl bedroom dinsa inda ta samu duk ya wargaje shi komai ya yi watsawatsa Ta girgiza kai cike da takaicin yadda har ya iya rikita dakin baccin nasa haka. Ta kada kai, ta soma gyara masa tare da mayar da komai a muhallinsa, ta cire bedsheet dinsa ta canza masa sabo, ta gyara dakin ya dawo yadda ya kamata, ta dauko boner ta zuba turaren wuta ta jona a dakin. Nan da nan ya soma. fitar da wani sanyayyen kamshi * Ta nufa wurin ma adanar kayansa da takalma ‘ (walk and closed) budadde mai girman gaske, an jera komai a indayadace, Saudat batayi mamakin ' yawan kayan nasa ba k0 daga yadda ta lura bata taba ganin ya maimaita kaya ba. Ta dauki wani jakar kaya ’ trolley bag ta zuge ta ta soma shirya masa kayan a ciki komai set ta kce hadamasa‘ don ta fahinci maigidan nata ya yarda da tomarch. Asma kuwa da kyar ta iya kai kanta bangarenta saboda bacin rai da zafin kishi, kuka ta ke sosai, tabbas Ahmad ya wulaqantata, ya qaskantar da ita, wai yau ita ce ya hada kishi da ‘yar aikinta, ‘yar * matsiyata, yarinyar da ta ke gani daKiKiya, mara ~ ilimi, kuma ‘YAR TALLA! 'Tabbas Ahmad ba qaramin wulakantata ya yiba a idon duniya, wai a ce kamarta mijinta ya auro ‘yar aikinta, wannan wane irin cin fuska ne? Ta suri makullin motanta ta fice dAga gidan tana faman shar barkwalla tamkar za ta tashi sama haka 'ta ke tuqin don haka cikin Kankanin lokaci ta iso ‘Ministcr’ Quarters, maigadi na bude mata qaton gate . din gidan ta kutsa motarta, bata tsaya gyara fakin ba _ ta tsaida motar ta flce a guje ta nufi cikin gidan Hajiya Zakiya ita ce mahaifiyar Asma, ita ke nan tilo Allah ya basu mahaifinta kuma bai yi ’ shekara da rasuwa ba. sakamakon hadarin jirgin da ya, _ rutsa da shi a kan hanyarsa ta zuwa qasar Uganda bayan shekara biyu da ‘yan watanni da auren Asma Allah ya yi masa rasuwa. Asma ta shigo falon mahaifiyar tata wadda ke tsaye a gaban dinning table tana jera kulolin abincin rana ita da ‘yar aikinta, Asma ta fada jikin Umman tata ta rungume ta tana kuka mai daga hankali. Hankalin Hajiya Za'kiya ya yi matukar tashi, ta ruKo ta tana fadar, “Ke Asma lafiyarki? Me ya faru ne? Yau na shiga uku ni Zakiya Ta bambare ta daga jikinta tareda janta cikin falon ta zaunar da ita kan kujera, ta dauko ruwan tambulan mai sanyi ta mikamata, "‘Karbi ki sha don Allah zuciyarki ta yi sanyi’ Ta karBi ruwan ta soma sha, Hajiya Zakiya ta juya kan mai aikinta a fusace 'tana ‘fadar, “To ke kuma uban me ki ke jira ki ka yi mana tsaye a ka?” ‘Yar dattijuwar ta rusuna, “ yi hakuri Hajiya”. Sannan ta juya ta yi gaba jiki na rawa. Hajiya Zakiya ta raka ta da harara kafin ta maida kallonta a kan ‘yar tata ‘wadda ta kurbi ruwan ta hadiye da kyar tamkar ta kurbi madaci‘ _ Hajiya Zakiya ta dafo tana, Fadar me ya farune?” Asma ta sa bayan hannu tana goge hawayenta _‘ Cikin ‘muryar kuka ta soma fadar, . umma wlh zuciyata tarwatsewa zatayi bazan iya a gidan Ahmad ba, baqin ciki kashe ni zai yi ldan :naci gaba ‘ da zama a gidansa, Umma 'Ahmad ya wulakanta ni, ya tozarta ni na rantse da Allah na hakura da aurensa, ba -. dan bazan iya zaman Kaskanci ba. ..” Kuka ya ci qarfinta tamkar wadda aka aiko wa da sakon muntuwa. Hajiya Zakiya ta ja tsaki kafin ta ce “Amma wallahi Asma kina bani kunya, yanzu ke ba abin kunya bane a zo a iske ki kina kuka a kan da namiji da, kyanki da yarinyarki da komai ke k0 ni da make tsohuwa ba zan iya tsayawa namiji ya ci kashi a kaina ba tare da na nuna masa bambanci tsakanin ruwa da hawaye ba. Haba sma Ahmad din banza da zaki zauna yana wulakata ki a banza tun lokacin da ya bijiro da‘maganaar zai auri ‘yar aikin gidanki na ba ki shawara ki .bar masa gidansa inyaso ya biyo ki da takardarki amma sai kayi kunnen uwar shegu dani, ke ga ki mai miji, yo namijin banza kayan amai ma don zuciya ta ki tashi ba za ki barshi ba? Yo namijin me Allah na tuba? Ke kin san k0 sakinki Ahmad ya yi ba za 'a kwashe kwanaki ba tare da maza sun soma ’ go slow a kanki ba. Ki duba yadda Allah ya yi miki "” baiwarkyau, haba Asma sai ka ce ba ki duba madubi, ga maza nan birjik a gari sai kalar wanda ya yi miki amma ki maqalewa namiji guda kamar gam, sai ka Ce ba Asmar da ke cudanya da maza ba a kan lamarin siyasa, haba don Allah don Annabi ki rabu da yawonan. nan, ya sake ki haka nan k0 dole ne za ki zauna namiji yana qaskantar da ke ya bata miki suna a gari don kawai ya lura kina sonsa, ba ki iya rabuwa da shi kamar wadda aka yi wa asiri, haba don Allah don Annabi Asma ki guntile ,wannan Kaskantaccen auren naki don ban ga amfaninsa ba. . .” Asma ta zame daga rikon da Hajiyartata tayi ‘ mata ta kwasa da gudu ta yi Bangarenta wanda ta yi rayuwar ‘yan matancinta a cikinsa. Hajiya Zakiya ta raka ta da idanu cike da takaici idan akwai abin da ta tsana bai wuce Bacin ran ‘yar tata ba, k0 kadan ta tsani abin da zai Bata wa ‘yartata, ta ja tsaki ta dauko wayarta a gefen kujera ta danna wa sirinkinta kira. A lokacin yana zaune kusa da Saudat suna cin abincin rana, ya dauko wayar ya rusuna tamkar yana gabanta, ya soma gaishe ta. Hajiya Zakiya ta dakatar da shi ta hanyat fadar, Dakata ba gaisuwarka nake nema ba, ka gane ina gida ina jiranka ka iske ni da takardar sakin Asma ‘ yanzu-yanzun nan”. Ba ta saurari abin da zai fada ba ta datse wayar, ta bar Ahmad riqe da kan wayar. Saudat ta zuba masa ‘ido ganin yadda ya yi Kasaqe idonta na kanshi kafin ta ce “LafIya dai k0?" Ya yi saurin dawowa cikin nutsuwarsa ya ci gaba da cin abincin tare da fadar “No.lafiya lau ba komai" Ganin yadda ya saki jiki ya ci gaba da cin abincin shi yasa. Saudat ta saki jiki ta ci gaba da cin _ nata abincin ita ma. Suna kammalawa bandaki yanufa ya watso ruwa ya shirya cikin‘ qananan kayansa ya nufi . Bangaren Saudat ya same ta a kicin ita da Mansura tana ganinsa ta saki yankan 'alayyahun da ta ke ta nufe shi, tana fadar, “Ba dai tun yanzu xaka tafi ba?” Ya daga mata gira alamar eh, ta langwabe kai, ‘ “Kai don Allah duka yanzu fa qarfe biyu, kaida kace jirgin karfe hudu za ka bi?” ‘ Ya riko hannunta yana fadar, “Akwai inda nake so na dan biya shi ya sanya. amman zakimin rakiya k0?,, Jikin Saudat ya yi sanyi qalau, ba yadda ta iya haka ta bi shi suka nufi harabar gidan inda direbansa ke sa masa jakarsa a mota, sai masu tsaronsa har uku suna tsaitsaye a bakin'motar. Ya riko hannunta yana fadar, “To Madam sai na dawo, ki kula min da kanki, _ akwai kudi na nan na ajiye miki a bed side drower dinki, daga gobe za ki fara zuwa makaranta dircba zai rinka kai ki, don Allah ki maida hankali ban da shiririta, ban da biye wa tarkacen kawaye kinji?” Saudat ta daga masa kai alamar eh don‘ta san tana bude baki kuka ne zai kwace mata, Dr; ya lakace mata hanci ya fada. mota yana mata dariyar Karfin hali, don ya lura ta yi matukar kuluwa, shi kansa ba don ya so zai tafi ya barta ba, don "a yanzu Saudat ta -' ida zama wani Bangare na rayuwarsa wanda ba zai iya rayuwa in ba tare da ita ba Ya soma daga mata hannu lokacin da direba ya ja shi. » Saudat ba ta iya motsawa ba, tana tsaye har suka fice tajuya ta nufi cikin gidan tana sharar kwalla girkinda ba a karasada ita yauba kenan tana ~dakin 'baccinta ta fada kan gadonta ta qudundune tamkar mara lafiya. ' ' Dr Ahmad bai bar Nigeria ba sai da ya biya ta gidan su Asma, sai dai abin da Hajiyar ta yi masa ba qaramin kuntata masa zuciya ya yi ba, tunda ya durKushe a qasa bai iya dagowa ba, yana saurarenta ta inda ta ke,shiga ba ta nan ta ke fita ba. Shi dai bai 'iya tankamata ba har sai da ta gaji' don kanta ta yi shiru sannan ya soma magana kansa a qasa. ‘ “A yi haquri don Allah Hajiya, abu ne wanda Allah ya riga ya qaddara Sai ya faru babu makawa sai ya faru, amma aurena da Sauclat wani mukaddari ne na Allah wanda ba mu isa mu guje masa ba, amma Wallahi ba don ba ni son Asma ba, duk da komai ya faru badasa hannunta ba amma ni ban riqe ta da komai ba, aurena wani mukaddari ne daga Allah, wanda,,,, ‘ “Saurara min haka Malam, ai tun kafin a haife ka na san wannan guntun wa’azin, tunda da ma budurwar zuciyarka ta ja ka izuwa ga kisisinar: ‘yar . aikin gidanka har ka aure ta ai dole xakake fadar komai muqaddari' ne. Sai dai abin da nake bukata a yanzu .kawai ka rubuta takardar Asma ka ba ta: amma aure dakai tagama kodakuwa kaine autan maza banda rufewar ido k0 meye abin naci a tattare da kai? Yo a tauna qashi k0 a karya haKori?’ ’ Ahmad ya mike tsaye ba tare da ya saurari umarnin hakan daga gare taba, ya zura hannu cikin aljhu ya zaro bandir din‘ yan dubu-dubu har guda ‘ biyar, wato na naira dubu dari biyar kamar yadda ya ba wa Saudat ya ajiye a kan kafet yana fadar, “Ga wannan a ba ta Hajiya ta ‘yi maneji kafin na dawo, amma ni bazan saki matata ba tunda’ har yanzu ina sonta”. Bai tsaya sauraren abin da zatacevaya fice abinsa ya barta tana faman kumfar baki ,,,,,,,,,, ,,,,,,,,,, ,,,,,,, Al’ amarin rayuwa ke nan, a kWana a tsahi babu wuya wurin Allah, Saudat ta kwashe “Sati hud'u tana. zuwa makarantar boko da islamiyya, cikm ikon Allah kuma duk abin da aka koya mata saita dauke shi kasancewarta mai budaddiyar Kwakwakwa don hatta tukin motar da ta ke zuwa koyo cikin sati guda ’ta ' kware don haka a sati na uku ta fara hawa titi ita * daya, yanzu haka ita ke tuka kanta ta je makaranta ta , dawo gida Saudat ta Kara gogewa tai ‘ wani fresh tamkar ba ‘YAR TALLA ba fatar" jikinta yayi wani luwai luWai har ‘yar qiba ta yi Wadda ta da yanayin jikinta, ga wata wayewa data qara samu ta musamman. , » ‘ A yanzu haka Saudat ta ita rubutun 1Hausa, Turanci ne dai take dan daddagirawa Hausa kam ta yi matuqar iya ta, don har karanta littafan Hausa ta ke na Mambuta dabamdaban, ‘ abin da ya Kara bude kwakwalwarta da Kara wayarmata da kai, ta qara samun experience din yadda za ta kula da kanta da shi kansa maigidan kenan Yau asabar ce ta yi daidai da cikar DR Ahmad sati hudu da tafiya kuma itace ranar isowarsa cikin ikon Allah, don haka tunda ta tashi daga islamiyya Karfe sha biyu da rabi ta dan wuce wurin gyaran jikida kunshida kitso ba ita tabar wurin ba sai qarfe hudu na yamma, don haka tana dawowa‘ gidan kicin ta nufa don hada abin da zata. ma maigidan kamar yaddata sanarda Mansura tana son girkamasa dambun shinkafa tareda pizza da kuma alkubus cake, potatoes chicken sai lemun‘karas tareda Creamy mango. Duk wannan zaBi nena Saudat don a yanZu itake bada umarnin komaima kondan Ayanzu. takwarene don har littafan girkin tana . Za ki dauko Barzazziyar shinkafarki ki bakace ta, ki cire garin sai ki zuba wa ‘shinkafar ruwa ki tsiyaye ruwan ki sa hannu ki matse, don ‘yan ruwan da suka yi saura su tsiyaye tsaf. Sannan ki zuba ' Barjinki a madambaci ki rufe ki batta ta turaru minti" goma zuwa sha biyar, sai ki sauke ki zuba a mara mai dan fadi ki barbaje shi sosai. * Sai ki kawo mangyad'a mai dan yawa ki zuba ki jajjaga attarugu ki zuba ki yanka albasa qanana, ki Sai .ki kawo dafaffiyar hantarki wadda kika .‘ yanka gutsin~gutsin ki zuba kisa garin kurkur cokali " guda sai kisa magi da gishiri da curry tare da thyme dadan garin citta da tafarnuwa sai ki juya sosai . sannan ki maida a madambaci ki rufe ki barsu su turaru minti goma zuwa sha biyar, sai ki sauke. Ki zuba a farantin maigida ki kawo dafaffen kwanki ki Bare, ki ‘masa yankan fadi, sai ki jejjera a saman abincin. Ni ma haka na ga Saudat din ta yi, sai na ga ta sa wani faranti ta rufe Sannan na ga ta dauko kwano mai fadi ta kalli Mansura. ' ’ “Yanzu kuma zan hada Pizza”. Ga yadda na ga ta yi. PIZZA lol Saudat na idarwa ta fice daga kicin din ta nufi babgarenta don magruba ta kawo jiki, don haka tana shiga ruwa ta watso .wa jikinta ta dauro alwala ta gabatar da salla, sannan ta nuifi gaban madubi ta ja stool ta zauna, kwalliya sosai ta yi irin wadda ba ta san ta iya ta ba, ta mike ta nufi kan gadonta ta dauki sabuwar atamfarta cikin wadanda ta kai wa ‘yar islamiyyarsu ta dinko mata. Tana cikin fesa turaren cool water ta ji wayarta ta soma rurin neman agaji, ta yi sauri ta nufi kan bed side drawer dinta ta dauki wayar, ganin sunan da ya fltO a kan madubin baro-Bare ya sa ta yi saurin shafar kore da dan' yatsanta, sannan ta kara wayar a kunnenta cikin tsananin doki ta ce, “Yallabai ‘ har kun iso?” Daga can ta ji ya karya murya yana fadar.“Wayyo tamyau, don Allah ki gafarce ni, na iso, amma ba zan samu isowa ba yau, za mu yi meeting a majalissa” ' Ai Saudat ba ta san lokacin da ta datse kiran . ba, saboda takaici ta wullar da wayar a kan gado cike da Bacin rai, don ganinta idan ya yi mata haka bai mata adalci ba. Ta ja tsaki tare da mikewa da niyyar ta cire kayanta, ta ji an turo kofa tare da sallama. Ai bata san lokacin da ta wuntsira ta nufe shi ba, shi kuwa ya bude hannayensa ta fada cikin jikinsa. “Madam kin yi kyau, kin Kara girma, wallahi kamar musanya min ke aka yi”. Ta sa dariyar farin ciki, “Mu je YallaBai ka ci abincin da na shirya maka sai ka yi wanka ka huta”. Bai musa mata ba ya miketa riko hannunsa tamkar wani qaramin yaro ,suka fice, har dinning area, ta ja mass. kujera ya zauna sannan ita ma ta zauna. Duk abin da ta girka sai da ta zuba ta tura masa, babu abin da bai ci ya yi santiba Wayarsa dake kan tebur ta soma‘ruri ya mika hannu ya dauka, ganin sunan Momy ya sa shi saurin dauka ya kara a kunne, “Hello Momy ina wuni, eh ga ta ma”. Ya kara wa Saudat wayar a kunne, muryar Momy dinta ce ta ji tana fadar, “Hello Saudat, albishirinki? Yau na ga yayanki Rabi u, an ganshi yanzu haka yana zaune a falona“ Ai Saudat ba ta san lokacin da ta fasa wata uwar Kara ba, ta saki wayar cikin tsabar kaduwa ta soma fadar, “YallaBai an ga Yaya Rabi’u, wayyo Allah na bari in dauko mayafina mu tafi Dr. ya waro ido, “Muje ina Saudat? Ba ki san k0 Karfe nawa ba ne yanzu? Takwas saura fa". Saudat ta marairaice masa, “Don Allah ka zo mu je, wallahi ba zan iya runtsawa ba yau in ban ganshi ba, k0 ka sa direba don Allah ya kai ni”. Dr. ya dan yi kasaKe yana kallonta, yadda duk ta firgice lokaci guda a take kuma sai ya ji tausayinta ya kama shi, tabbas ta yi kewar yayan nata, za ta iya ma shiga kowane irin hali. Ya sauke kansa daga kallonta ya mike ya suri wayoyinsa da ke kan teburin, ya ce, “Dauko mayafinki kizo muje”. Sai kuma tausayinsa ya kama ta, k0 awa 'daya bai yi da dawowa daga wata tafiyar ba, sai dai ba yadda za ta yi, tana son ganin yayan nata a yanzu fiye da komai. Ta juya ta dauko mayafinta kalar atamfar ta dauko wayarta da jakar takalman kafarta ta tattara kudaden da Dr. ya ba ta wanda ko dubu hamsin ba ta taBa a cikinsu ba ta zuba a jakar, sannan ta fito. Yana nan tsaye inda ta bar shi yana jiranta. Yana ganin ta flto ya yi gaba ta biyo shi a baya, sabuwar motarsa ya shiga. ‘ Saudat ta dube shi, “Ba direba zai kai mu ba Yallabai?” Ya ce, “A’a mu je kawai na tuqa mu, zamu fi sauri”, , ' Ba ta sake tankawa ba ta zagaya kujerar da ke gcfen direba ta bude ta zauna, ta samu ya kwantar mata da kujera, don haka ta kwanta sosai, shi kuma ya yi wa motar key suka fice daga gidan suka hau hanyar Katsina, inda suke sauraren karatun alkur’ani mai girm wanda Dr. ya kunna musu a motar, hakan yasa kowane ya nutsu yana saurare sai ‘yar maganar da ba a rasa ba. Ba karamin gudu ne Dr. Ahmad , yake sharawa ba a kan titi, don Karfe goma da minti talatin ta yi musu a cikin Katsina a gidan su Saudat. Tun kafin ya ida tsayawa Saudat ta Balle murfin Kofar ta fito a guje, ta nufi cikin gidan tana Kwalla wa Yaya Rabi’u kira. Tana shigowa ' falon tana wurwurga idanu, can hango shi cikin doguwar kujera yana shan fan-milk, Saudat ta fasa wata uwar Kara ta kwatsa a guje ta fada jikinsa ta kankume shi tana ihun dariya. , * Shi kansa dariyar yake yana ambaton sunanta ‘ tare da Kokarin dago ta don ganin yadda ta koma amma taKi sakinsa, su Nabil da Nabila ma ‘suka rufa mata baya suka rungume ta suna murnar ganinta. ’ . Momy dai dariya kawai ta ke musu zuciyarta dauke da matuqar farin ciki da shaukin ganin sanyin idaniyar nata 'Dr ya yi sallama ya shigo falon rike da jakar Saudat da wayarta ya durkusa agaban Momy yana gaishe ta cike da girmamawa, Saudat ta zame daga jikin yayan nata tana kallonsa, kuka ta ke sosai shi kansa sai da kwallar ta zubo masa cikin karfin hali ya soma share mata hawayen yana fadar, “Ya isa haka Saudat, ba kuka za mu yiba, sai mu gode wa Allah” “ Dr Ahmad ya mike har zuwa inda suke ya mika wa Yaya Rabi u hannu yana fadar, “Your welcome Yayanmu, mun yi farin cikin ganinka” . Rabi u ya ce “Ni ma haka, amma yanzu cikin ,daren nan ta taso ka? ” Dr ya cc, “To ya na iya‘? Ai yayanmu yana da _ muhimmanci a rayuwarmu”. Dadi ya kama Rabi’u ya yi na’am kuma da zamowar Dr. Ahmad mijin ‘yar kanwar tasa. Saudat ta mike ta nufi wurin mahaifiyarta tana fadar, “Don Allah a ‘ina ku ka ganshi?” Momy wadda bakinta yaqi rufuwa ta ce, “Saudat, yanzu cikin daren nan ki ka taso mijinki, tsakaninki da Allah kin kyauta? Ai da na ‘sani da sai gobe na fada miki Saudat ta ce “Kai don Allah Momy, shi fa ya ’ ce mu taho”. Ta yi maganar tare. da satar kallon Dr. wanda aka yi sa’a shi ma ya kallo ta ta yi saurin dauke kai, “Don Allah Momy ina ku ka ganshi?” Momy ta ce, “Ta hanyar Inna mai danwake, tunda ki ka fada min Rabi’u ya bada sako a baki nake aikawa wurinta a kan a karBo min sakon mijinta ke fadamana vata nan ta yi tafiya zuwa garinsu har ‘ ,ta kai ga ,ina zuwa da kaina, amma ban yi nasarar ' samunta ba, tsawon wata daya da sati biyu sai yau na tayar da direba na tura shi kasancewar mijinta ya ba mu tabbacin yau ne za ta dawo. Cikin ikon Allah kuma ya yi nasarar samunta ta dawo daga garin nasu a jiya, aka yi sa’ a kuma ta bawa direban saqon cikin waccan jakar”. Momy ta yi musu nuni da wata ~leda mai tambarin Aminci Super Market Katsina, ta ci gaba da fadar, “Direba na kawo. min jakar na zazzage, ba komai bane a ciki sai wasu lesussuka guda biyu, atamfa super Holland guda, sai takalma da jaka da kuma sabuwar waya a cikin kwalinta tecno p.2 da'sabon layi a ciki. Jikina na rawa na kunna wayar sai ga lamba Kwara guda a ciki, a take na danna kira cikin sa’a kuma lambar ta tafl. Bugu biyu ya dauka muryar har rawa ta ke wurin sanar da shi k0 ni wace ce, shi kansa ya shiga rudani kuma k0 minti talatin bai Bata ba ya iso nan gidan”. , Saudat ta cd“Wayyo Yayana, Allah sarki ashe ba ka manta da ‘yar qanwarka ba? To yaya da baba ya kore ka kai ina ka nufa?" ‘ _ Rabi’u ya dan yi‘ murmushi kafin ya ce“Ai *duk halin da na shiga Saudat ban tunanin zan manta dakeba sai dai in har ba na numfashi, don a lokacin da Baba ya kore ni na dauki hanya ina ta tafiya amma ban san inda zaniba ina ta tafiya ga *gajiya ga yunwa ga duhun marece ya fara. Ina cikin tafiyar nanne na fara shigowa gari nayi karo da wata leda kamar zanwuce saikuma watazuciyar tabani shawarar induba ko Allah zaisa wani sauran abinci ne a. ciki in samu abin da zan ci. Da wannan tunanin na tsaya na dauki ledar,ina dubawa amma damamakina sainagawani kwali ina duba kwalin sai ga sabuwar waya a ciki, dadi yakamani nasamu abindazan siyar inci abinci, don haka da kwanrin gwiwata na ci gaba da tafiya harna shiga cikin gari da tambaya aka nunamin wurin saida wayoyi harna isa kasuwar tsaitsaye wadda ke cikin garin Katsina donna bada wayata a siya, sai dai abindaya dauremin kai shine farkon tayi aka tayata naira dubu dari da hamsin mamaki yasa na gaza cewa komai, shi kuwa mutumin dauka ya yi k0 ba zan siyar masa bane ya hau kora min jawabi. ‘ “Malam damaka siyarmin dawayarnan haka don ba wata uwar ribace zanciba don dubu dari da saba,in ake saida ita Cikin sanyin jiki nace yabada kudin babu kuma vata lokzaci ya qirgo kudi a aljihunsa ya _ mikamin nakirgasu naga sun cika sannan najuya nasoma tafiya.Saidaifa inda gizo ke saqar bansan gidanwa zannufaba, gadai kudi ahannuna ammabanda wurin zuwa don haka najana zauna asaman wani' dakalin dake wajen kasuwar na kira mai abinci na .siya na ci na qoshi, na sha ruwa na ci gaba da kallon titi, wannan mota ta wuce, waccan ta wuce a haka fa aka yi sallar magriba da isha, dare ya soma duk ina a zaune a nan fa fargaba ta fara shiga ta. ‘Banyi auneba naji andafani,harna dan firgita ashe mutumin dana siyarwa waya ne. ya zauna a kusa da ni yana tambaya ta, “Wai lafiyarka kuwa Rabi’u?” Jin ya kira sunana ya sa nayi saurin kallonsa, sai a lokacin na shaida shi ashe Yasayyadi ne dan dan oganmu wanda nake aikin Kasa a wurinsa. To in takaice muku nan na sanar da shi halin da nake ciki, na korata da mahaifina ya yi har tsintar wayar da nayi. Ya yi matuqar tausaya min, a nan yace in tashi mu tafi shi zai taimake ni. Yasayyadi ya kai ni shagonsa da yake kwana wanda ke like jikin gidansu ta waje nan na ci gaba da zama, kwanana uku Yasayyadi ya ba ni shawara da na fara sana’a, ni ma ya ga kamar masu shi go da shinkafa a Kasar nan suna samu k0 zan fara? Na amince, ya hada ni da wani abokinsa muka fara safarar shinkafa daga qasar Nijar zuwa Najeriya da ma ina da jari a hannu. Allah Ubangiji kuma ya sa min albarka, sai ga ni cikin fan kankanin lokaci na tara kudi masu kauri a hannuna, a lokacin ne na sanar da Yasayyadi ina son. shiga makarantar boko, shi ma ya yi na’am da shawarata, don shi a lokacin yana shekarar Karshe ta kammala digiri. Shiyayi duk wanicuku- cukun da akeyi na hada takardun firamare natafi js3 kaitsaye cikin yan watanni nazana. JSCE sannan na wuce SS one na maida hankali sosai a karatuna, wanda bai hana ni neman kudina ba. Abin ma kamar harda sa hannu don duk abin da na taba cikin ikon Allah sai ya zama kudi, a haka naci gaba da karatuna zan shiga aji biyar na tsallake na wuce aji shida. Ina kammalawa na zana jamb na yi sa’a kuwa na bugo point din da ake so, wato 200 point don haka ban " samu wani matsala ‘ba wurin samun admission a Umaru Musa ‘Yar 'Aduaa university suka ba ni Mass Com na soma karatuna cikin nasara ina level 2 na fara shigo da motoci daga waje zuwa Najeriya a lokacin ba zan rasa jarin da ya wuce naira miliyan ashirinba, don harnafara aje yara suma sunaci a qarqashina nayi gida nayi mota na tashi daga gidan su Yasayyadi na koma. gidana, a lokacin shi ma ya yi aure ya samu aiki da hukumar zabe ta qasa yana zaune da matarsa a lokwas din kofar: Maruba. A lokacin da na gama digirina aka turani garin Lagos in yi sabis dina, na tattara na tafi watana biyar aka bamu hutu naxo gida mahaifina ya sakemin korar kare a karo na biyu nanna bada sakon' kaya da wayagidan Inna mai danwake a ajiya miki' na juya na tafl ina kuka jin wai an tura ki aikatau, kwanana biyu na koma Lagos. A yanzu haka yau satina guda da kammala sabis dina inda na samu saqon tashin hankali, wai Allah ya yi wa Yasayyadi rasuwa, mutuwar ta gigita ni ba kadan'ba, don haka na dora wa kaina nauyin kulawa da iyayensa kasancewar bai taBa haihuwa ba, sai ga sakon kuma farin ciki ya same ni, wai mahaifiyata .da qanwata sun bayyana, wallahi farin cikin da na tsinci kaina bazai misaltu ba”. Saudat ta cce “Allah sarki yayana ka sha wahala, kuma ka samu duniya, shi ya sa na ga ka zama wani dan lukuti”. Duka suka sa dariya sannan Saudat ta ba shi labari tun daga ranar da ya tafi har ya zuwa aurenta.da Dr. Ahmad, Rabi’ u har kuka ya yi saboda tausayinta, don haka ya ce Dr. ya yi musu .alfarma gobe su je Dandagoro ya ga mahaifinsa, kuma ya ga Hamid; Dr. ya amsa da Allah ya kaimu sannan ya mike ya yi musu sai da safe. Momy ta ce “Au dana. 'zata a nan zaka kwana?" Dr. ya dan yi murmushi tare da fadar, Momy na riga na yi bukin a Katsina Hotel". Momy ta ce, “Amma da ka daure ka kwana Ahmad Abbanka ba ya qasar k0 Bangarensa ba sai ku sauka ba?” Ahmad ya ce, “Ayi haquri dai Momy? da safe zan dawo” " Ta ce, “To Allah ya kai mu” Ya amsa da, “Amin” Ya yi wa Rabi’u sallama ya fice. . Saudat ta sabi takalma ta bi shi da‘ zummar suyi sallah; yana tsaye bakin motarsa har ta Karaso ya bude mata qofar motar yana fadar, “Muje Saudat, wallahi na yi bala’in gajiya”. ‘ Saudat ta waro ido, “Muje fa kace Yallabai? Haba don Allah, ni gaskiya bazan iya binka ba”. ' Dr. ya zuba mata ido a raunane yana fadar, “Kin yi min adalci ke nan Saudat? Kin san dai a ‘ yanzu ina buKatarki kusa dani, ki tuna fa tsawon lokacin da na dauka ba mu tare”. ‘ Saudat ta langwabe kai a shagwabe._ tana , fadar, “Allah YallaBai ni dai kunya nake ji, kuma yau dai daya don Allah ka barni in gaisa da dan uwana". . Dr. ya kada kai tare da fadar, “Shi ke nan Saudat sai da safe”. Ya juya ya fada motarsa ya ja ta a hankali ya fice, zuciyar Saudat ta yi matuqar rauni sai dai ba zata iya yin abin da yake son ba, tajuya ta nufi cikin gidan ta ja ta zauna suka dasa hira da Yaya Rabi’ u da " Momy wadda da ta gaji ta mike ta shige dakinta ‘ Amma su kam yadda suka ga rana haka suka‘ , ga dare, sai da aka kira sallar asuba sannan shi ya tafi ~ , masallaci, ita kuma ta nufl Bangarenta in da ta dauro' alwala ta yi sallah, kana tahau kan gado ta kwanta. Sai dai ta kasa runtsawa, tunanin halin da ta jefa mijin nata a jiya ya tsaya mata a zuciya, ta lura tamkar fushi ya yi da ita don haka ta lalubo wayarta ta soma rubuta masa saqo kamar haka. ‘Tuba nake mai gidana, banji dadin abinda nayi makab wallahi yanxu haka ina kewarka kamar yadda kake kewata, ina bukatarka fiye da yadda kake buqatata, saboda a duk Iokacin da nake manne dakai sai injini na zama kamar wata tauraruwa,a cikin taurari Tana gama rubutawar ta yi murmushi tare da tura masa saKon ta koma ta kwanta, sai dai k0 minti biyu ba a yi ba sai ga amsa ta shigo, ta yi dariya don ta san da ma za a rina ta jawo wayar ta soma karantawa kamar haka. ‘A kodayaushe ki dinga tunawa ke daban ce a cikin duniyata, erro lets go am sorry plz Saudat ta maimaita karanta sakon ya fisau goma kafin ta tura wayar a cikin jaka ta koma ta kwanta, ba ta jima ba kuma bacci mai nauyi ya yi awon gaba da ita, wanda ba ta tashi farkawa ba sai sha daya. na safe. Tana mikewa bandaki ta nufa ta watsa ruwa ta fito, ta sake shiryawa cikin atamfarta ta sannan ta flto Sai dai da mamakinta ta samu Momy da Rabi’ u da Dr a falo suna hira, da alama sun dade suna hirar ; Ta durkusa ta gaishe su daya bayan daya, sannan taja gefe ta zauna tana fadar, “Da ma kun tashi Momy ba ki tayar dani ba?” ' ‘ Momy ta ce “A’a na barki ne ki hantse tashi ki karya maza ku wuce don ku daga can za ku wuce”. Saudat ta yi saurin dagowa ta kalli Dr. sai dai k0 inda ta ke bai kalla ba, hakan ya tilasta mata mikewa ta nufi dinning ta zauna ta karya, sannan ta dawo cikin falon Momy ta dauko mata jakar da Rabi’un ya ba ta, ta qara mata da ‘yan tarkacen tsaraba, sannan ta rako su. * , Saudat ji take tamkar kada ta tafi, sai dai ba ta ~ da yadda ta iya, haka ta shiga motar Dr. shi kuma Rabi’u ya shiga tasa motar sabuwa dal mai suna 206 suka rankaya suka tafi Momy na musu fatan alkhairi. ~ Sai dai lolkacin 'da suka iso gidan Saudat mamaki ya kashe' ta, ganin yadda ya canza ya dawo ginin bulo da bulo aka kawata shi tamkar gidan wani dan karamin ma’aikacin gwamnati, kanta bai ida daurewa ba sai da suka shiga cikin gidan wanda aka canzawa tsari duka falukan gidan aka hade su cikin guda, aka kaWata su da sabbin kayan alatu na rayuwa, duk kan Saudat ya kwance shi kansa Rabi’un bin gidan yake da kallo, ‘Yarbaba wadda ke zaune a““ gidan ita ta yi musu iso cikin falon tana ta faman rawar jiki, sannan ta nufl wata kofa don ta kira musu Malam Bala. Saudat ta cika da mamakin ganin ‘Yarbaban a gidan, lokacin da Malam Bala ya flto ya yi ido hudu da Rabi’u sai ga shi ya. xube ya fadi kuka yake wiwi kamar karamin yaro, yana roKon gafararsu kan Saudat bai ida kwancewa ba sai data ga ‘Yarbaba ta turo Inna Laure a keken tura guragu, Saudat ta rude . ta shiga tambayar abin da ya faru tunda ga Inna Lauren nan dai babu alamar rashin lafiya a jikinta, . amma daga Inna Lauren har ‘Yarbaba kuka ya hana su magana sai Malarn Bala ne ke fada musu. ‘ “Lalurar hawan jini ceta kayar da Inna Laure tun a lokacin da ya kulle ta a daki ranar da aka dauki Saudat zuwa gidanta yana zuwa ya bude 'daki ya ganta a sume hankali ya tashi aka kwashe ta aka tafi asibiti nan fa aka sanar mana jininta ya yi matukar hawa kuma qafafunta sun riqe don inba wani iko daga Allah ba, ba za ta sake taka su ba. Mijinki yaxo Saudat a lokacin muna asibiti, shi ya yi ta dawainiya ya ba da kudi aka wuce da ita asibitin Aminu Kano da ke cikin jihar Kano ya ba da .makudan kudade, kuma shi ya yi mana wannan gyaran, amma a asibitin can ma sun ce iya bincikensu ba su ga abin da ya rike Kafafuwanta ba, don haka suka sallame mu, k0 kwana hudu ba mu yi ba da dawowa gida sai ga ‘Yarbaba cikin wani mummunan ‘ hali, wai mijinta ya kwashe kayan dakinta ya siyar, ta yi magana shine ya yi mata dukan tsiya duk ya raunatata, ya yi mata tsirara ya turota waje ya ce ya sake ta Saki uku, sai dai makota ne suka ara mata tufafin da ta iso gida dashi. Yau satinta guda da dawowa shi yasa ku ka ganta ta yi kyan gani, amma kwanakin baya idan ku ka ganta sai kun zubar mata » da hawaye, ni nasan haqqinku Saudat ba' zai barmu ba matukar ba ku yafe mana ba, don Allah Rabi’u ka yafe mana ba don mu ba ba don halinmu ba”. ‘ Rabi’u ya ce“Ai ni ban' rike ku da komai ba baba, wallahi na yafe har cikin zuciyata”. Inna Laure ba ta da ta cewa, sai kuka sai ma ‘Yarbaba ce ta yi Karfin halin bude baki ta nemi gafararsu. Sun dade a gidan kafinsu yi musu sallama. za su tafi, Dr. ya yi musu kyautar makudan kudade, haka shi ma Rabi’u naira dubu hamsin ya bawa mahaifinsa da zummar idan ya dawo zai’ ga abin da ya kamata ya yi musu, Saudat kuwa dumtsowa kawai ta yi ba tare da ta san k0 nawa ba ne ta bawa mahaifin nata, ta ba wa Inna Laure sannan ta miKa wa ‘Yarbaba ‘yan sauran da suka rage. Ai k0 sun sha godiya da sa albarka, haka suka bar gidan kowa zuciyarsa cike da alhini, da ma haka rayuwa ta Kunsa, idan kai ne yau gobe ba kai bane, idan ba ciwo akwai ajali idan ba ajali akwai tsufa haka rayuwa take tAfiya a kwana a tashi mai maida yaro tsoho. Dr ya dauki matarsa suka koma gidansu suka Ci gaba da rayuwarsu cikin nagartacciyar soyayya da kaunar juna, Saudat tana bawa mijinta irin kulawar data kamata dukda karatunda takezuwa baihanata ba shi duk wata kulawar da ta san zai iya bukata dagagare ta ba. A yanzu karatunta ya yi zurti, don kuwa har ta kammala Basic Illetrate ta karbi certificate ta kuma ci gaba da karatunta na wata tara Wanda za ta karanci Social welfare, don haka ta dage “*dakaratun ta donma canjin jikindata'samu narashin kwarin jiki wanda likita ya tabbatar da ta samu shigar cikin wata uku, wannan albishir din ba qaramin faranta zuciyar Dr. yayi ba, an inda labarin cikin Saudat har a cikin ‘yan uwansa, ‘ saboda tsabar rawar qafarsa a kan haihuwa. Cikin Saudat yana da wata takwas ta kammala karatunta na wata tara a lokacin an soma siyar da form din jarabawar waec external da kuma jamb din ta cike abinta ba su zana jarabawar ba Saudat ta haihu' wata tara daidai ta sunkuto qaton danta mai kama da ubansa sak tamkar ya yi kaki ya tofar ' ‘ Ai k0 a wannan lokacin Saudat ta ga gata da soyayya don Dr, da iyayensa sun saki bakin aljihuna sun mata bajinta, kuma sun gwada mata ita din ta zama tasu ta zama wani Bangare na jikinsu wanda bai kankaruwa Ranar suna tazo yaro yaci sunan mahaifin Dr. wato Mukhtar, suna kiransa da Khalifa. A ranar Saudat ta ga dandazon jama’a ta ko’ina‘ daga danginta zuwa dangin mijinta, hatta Hamid ya kawo matarsa shi ma Rabi’u ya kawo Shukura wanda Saudat ta fahimci soyayya mai karfi ta shiga tsakaninsu, duk da Rabi’u ba wani girman Shukura ya yi ba bai wuce ya bata shekara hudu ba, sai dai Shukura ta ba ta Kwakkwarar amsa cewa yanzu auren met ake yayi, abin da ya sa Saudat dariya matuka, ta kuma tsuke, bakinta daga nan tunda ta lura abin yi za,ayi. . Bayan sati biyu da haihuwar Saudat ta tafi ta zana jarabawa cikin ikon Allah kuma kwalliya ta biya kudin sabulu don kuwa ta samu credit biyar a ciki har da Maths da English a jamb dinta kuwa Allah ya taimake ta ta buga point dari da cas'in da kyar aka sha dai ke nan, don haka Dr bai bata lokaci ba ya samar mata gurbin karatu “ jami’ar Gwagwalada za ta yi difloma dinta a kan social management, karatunta ta ke haikan Khalifa ya girma sosai, don kuwa ba inda bai zuwa da qafafunsa, don haka yana da shekara daya da wata shidda ta yaye shi, Wanda da kyar mahaifinsa ya amince. ' Hajiya Zakiya tana zaune a falonta tana karatun mujalla ta ga Asma ta sauko daga saman ‘ bane tana sanye da baqar jallabiya fuskar nan ta yi kozai-kozai alamar ta sha kuka harta gaji, hannun na" riqe da hand bag sai makullin meta, k0 inda Hajiyar tata ta ke ba ta kalla ba ta nufi hanyar ficewa daga falon Hajiya. Zakiya ta kwalla mata kira, “Ke Gidan wa za ki haka kamar korarriya?” . Asma ta waigo tana kallon mahaifiyarta da idanun da suka ciko da' hawaye, cikin muryar kuka ta soma fadar, “Gidan mijina zan koma Umma, na gaji da zaman da nake a gidan nan marar ma’ana, ni ba mai aure ba, ni ba bazawara ba, tunda Ahmad yayi alkawarin ba zai sake niba Umma tursasawar da ake masa ta isa haka, kuma kema ya isa ki gane mijina yana sona, Umma na gaji da zamA nan gidana zan koma in rungumi Kaddarar da Ubangiji ya dora min tun kafin inyi batan bagatattan”. Hajiya Zakiya ta zuba wa ‘yar tata ’idanu wadda ke ta faman sharar kwalla ta girgiza kai kafin‘ ta ce, “Ke yanzu don zubar da kai Asma mijinki yaqi zuwa bikonki shine zaki debi kafa ki koma da Kafarki wato ki nuna masa. bakida aji a kansa ke nan. ” Asma ta kada kai cikin kuka ta ce, “K0 daya Umma, zuwa biko ya wuce wanda iyayensa suka zo ki kaqi sauraransu, haba Umma ki tuna fa yau shekarata biyu a gidan nan amma kek0 kadan ba ki damu ba, Umma to ni na gaji gidana zan koma in rungumi mijina da abokiyar zamana tun kafin ta mallake min miji ita daya ya aiko min da farar takardar da ke kike buqata, tunda nazo gidan nan sau daya Ahmad ya taba zuwa bai kuma wara dawowa ba sai dai ya turo min kudi ta account dina, haba Umma yaushe kike tunanin zai so inda nake? Wallahi ni ba zan tsaya jira ba. . .” Ta juya a sukwane za ta bar falon. Hajiya Zakiya ta daga murya, “Asma tsaya ki Jl’. . ~ ‘ Asma tajata tsaya itakuma tacigabada fadar,“Kiyi haquri kidaina kukannan indai kina son mijinki na amince ki koma amma ki dan daga komawar taki k0 gyaran jiki ne in kaiki in kuma sake miki kayan bangarenki gabadaya yadda zuciyarki za ta sassauta, ni ba na son ganin kina damun kanki nima sai inji hankalina ya tashi”. ‘ Asma tagirgiza kai,“Wallahi Umma bazan iya tsayawaba saidai duk abinda zakimin ki iskeni da shi daga baya, amma gidana zan koma ni ma ko na haihu na ga gudan jinina don na gama shan kwayoyin planning har abada.. Batajira abinda Umman tata zatacebata fice a guje ta bar falon bata tsaya a ko’ina ba sai cikin mota ta tayi mata key taja ta bar harabar gidan. ‘ Saudat na tsaye a harabar gidanta tana manne da Khalifa a kafadarta duk da kuwa kibar da yaron ya mulka tamkar dan turawa ga shi jajawur da shi kamar « ya hada iri da zabaya. Rakiya cd sukayi wa Dr wanda zai tafi kaduna taron .bude wani sabon kamfaninsa. Saudat na ta zuba masa shagwabar ya tafi da su shi kuwa sai dariya yake mata yana zolayarta wai ba inda zaitafi daita saitayi kiba don Khalifama yafita nauyi, in ya yi wani zillon har kusa kayar da ita yake shi ya sa kullum yana hannun mai rainonsa. ~ Saudat ta ce Allah YallaBai gorinka ya fara isa ta hakanan, kodon kaganka kai yaddakazama wani dankareran katone? Allah ka kai kilo dubu ni Wallahi ma kana kwarata”. _ Dr. Ahmad ya kece dawata irin dariya jin Sharri irinna Saudat Ahaka kuma masu gadi sukabude get motar Asma ta danno cikin gidan dukkansu sukabi motar da kallo, Dr. ya gane ta don ga sunanta nan Baro-baro a saman lambar motar Asma ta faka motar: ta bude ta fito cikin matuqar sanyin jikinta ta nufo inda ~ suke. Kallo daya Saudat tayimata taganeta, k0 kadan 'zuciyarta babu alamar fargaba k0 firgici don kuwa a yanzu tana jinta daidai da kowace kalar mace duk matsayinta k0 iliminta, kuma a yanzu ba ta bakin cikin Asma tadawo su zauna dondama batun yanxu take wa Dr maganar dawo da Asma yana cewa zai dawo da ita,ba amma sai ta yi hankali. Asma na qaraso ta rusuna ta gaishe da Dr wanda mamaki ya kashe shi, wai yau shi ne Asma ke gaidawa, lallai ruwa ya daki babban zakara, ta juya kan ‘ Saudat ta mika mata hannu tana fadar, “Saudat bani dana inganshi”.saudat tamiqa matashi,ammayaro da iya shege yaqi zuwa sai ma ya sa kuka. Dr, yace shi yana fadar, “Kai Khalifa kuka za ka yi wa Antyn taka, ba ka kyauta ba”. Saudat ta juya tana fadar, “Ako ni nayi ciki Aunty Asma ki tafi da shi tunda Kuka zai miki Asma ta yi murmushi cike .da jin dadin karramawar Saudat a gare ta, ta ce“Ai k0 godiya nake Maman Khalifa, kyautar surbudeden 'da kamar Khalifa, aiko nayi da kanaji fa”. Murmushi ya yi tare da fadar “Kema inda vaki sa duniya a gabanki ba Asma da yanzu kin ajiye uku irinsu”. Asma ta langwaBar da kai kafin ta ce, “Ka yi haquri don Allah Ahmad, wallahi duk sharrin zuciya ne, insha Allahu hakan ba zai Kara faruwa ba, don Allah ka yafe min”. Dr. Ahmad ya kade kafada tare da cewa, “Allah yace na yafe miki Asma, ni dai har abada bazan taba sakinkiba don ina sonki, ba zan iya rabuwa da ké ba”. ‘ Zuciyar Asma ta cika da farin ciki ta dafa kafadarsa ta sumbaci Khalifa a kumatu tana fadar, “Na gode kwarai my dear". Al’amarin rayuwa ya sauya, Asma da Saudat sun samu fahintar juna, Asma ta cire duk wani girman kai ta taya Saudat tattalin maigidan nasu, a yanzu haka Saudat ta kammala diplomarta ta ci gaba da digiri cikin kwanciyar hankali, inda ta Kara haihuwar ‘yarta mace akasa mata sunan Asma. Tammat bi hamdu lillahi, Saikuma mun sake haduwa a wani sabon littafin Thanks all my friends Pls my fan's prayer for me Allah ya cikamin burinada kuma Allah ya cika muku burikanku na Alkairi Ameeeeeen *BISSALAM* An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels