An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels 🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀 *_'YAR CASKALE_* ( _Sanadin bakin uwa_ ) *NA* *KHADEEJA USMAN* *_(Real Tame Gari)_* *بسم الله الرحمن الرحيم* ___________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ___________________________________ 1⃣➡5⃣ *ALHAMDILLAH! ALHAMDILLAH!* *_AM BACK AGAIN_* *_Wannan buk d'in,sadaukarwa ne ga dukkan daukakin Marubuta na 🌈kainuwa writers asso...da Kuma masoya na a duk inda kuke a fadin duniya Allah ya barmu tare ya Kara Mana zumunci mu gudu tare mu tsira tare_* _Hussain ATK da dukkan masu taya mu posting din litattafan mu muna matukar godiya Allah ya saka muku da alkhairi ya barmu tare_ _Ban yarda wani ko wata su juyamin littafi ta ko wacce siga ba tare da izini na ba,yin hakan zaisa mu samu matsala Dan Allah a kiyaye_ ****** Sauri yakeyi kamar zai kifa,Dan ya na son yayi sauri yakai musu maganin. Malam shu'aibu kenan,cikakken bakano,asalinsa shida iyayensa 'yan Kano ne, a unguwar fanshekara,ya na da Mata guda d'aya da yaransu biyu,Isma'il shine babba sai mace *MARYAM* wadda ita ce karama yanzu ake goyo. Malam Shu'aibu da matarsa Huwaila,suna zaune ne a unguwar yamadawa,inda yake sana'arsa ta sayar da kayan marmari,dangin su lemo ayaba da dai sauransu.Huwaila macece Mai kirki da Sanin ya kamata,duk da cewar uban mijinta ya Dade da rasuwa,hakan yasa kullum Bata rasa abinda zata bayar tace akaiwa surukar tata,Dan malam Shu'aibu kullum Sai ya je gaida mahaifiyar tasa. Matsalar Huwaila fad'a da rashin lafazi,Sam bakinta Dad'i,ba ga wani ba ,Baga 'ya'yanta ba,malam Shu'aibu yasha fama da ita akan muna nan lafazi akan yaranta,amma Ta 'ki dainawa.Yanzu haka Maryam na da shekara goma yayin da Isma'il keda shekara Sha d'aya,Dan babu wata tazara tsakaninsu,Dan irin haihuwar nan ce ta zamani.Yanzu ma Isma'il ne ba lafiya,shine ta kaishi asibiti ,magungu Nan da aka rubuto,su ne malam Shu'aibu ya ta fi siyowa. Da sallamar sa ya shigo gidan,inda ya Fara jiyo hayaniyar ta tana fad'in"ai ke Kam anyi bak'ar matsiyaciya,ban San halinwa Kika kwaso ba,Danni kaf dangina babu Mai bakin Hali irin naki,sai dai ko can dangin ubanki Kika kwaso,ace yarinyar kullum sai kin Sani tsinin baki,da ace baki Yana Kara tsawo da yanzu nawa ban San inda yakai ba" Yarinyar dake tsaye idanunta feke ta tsare uwar dasu,babu ko alamun tsoro tace" Allah umma ko yanzunma bakinki ya k'ara tsawo ba kamar sanda na ke k'arama ba,Dan yanzu Kinga yadda bakinki ya koma",ta kamo le'benta na sama Dana k'asa ta jawosu. "Kinci kut......ta narka Mata ashar,Ni d'in ce bakina yake a hakan?" "Wallahi umma da gaske nake"ta fada kanta tsaye ."Zakici ubanki ne ,na rantse da Allah yau saina kusa kasheki a gidan nan". Jin abinda tace ne yasa Maryam din zumbura Baki ta nufi bakin kofa Dan fita daga dakin."wallahi Kika sake fita daga gidan Nan sai na farfasa Miki jiki,inba Haka ba shegiya uwata ta haifeni,Kuma jeki din in kina musu". Babu alamun tsoro ko ta fita daga dakin tana zumbura Baki tana gunguni,inda tayi kacibis da babanta tsaye a inda yake jiyo diramar su. Washe Baki tayi tana fadi'in ,"Lah baba! Sannu da zuwa,harka dawo daga siyen maganin?" Kama hannunta yayi Yana fad'in"yauw 'yar baba,laifin me kikayi ne naji mamanki na Miki fad'a?" "Kawai fa Dan tace na jire gida Kar naje ko'ina,shine fa Ni Kuma Ina Nan zaune sai zuwaira ta leko ta tsokaneni ,Wai an barni tsaron gida harda min gwalo,Niko na bita har gidansu na Kama bakinta nai ta naushi irin yadda Naga rannan johnsina yayi dashi da omega,shi ne fa jini har Saida yayi tsartuwa,wallahi baka gani ba baba,da kyar aka kwaceta a hannuna,ashe dai nima jaruma ce,shine fa aka zo aka fadawa umma ,shine takemin fad'a" . Girgiza kansa yayi sannan ya shiga shafa kanta,"Maryam me yasa bakya Jin magana ne,anya kina son mu shirya kuwa? Kinga Ni bana son wannan yawan fadan da kikeyi sai kace ahlin shagon dambe,ke kenan make wannan jibgi wancan,to indai kina son mu shirya Kar in Kara Jin Haka kinji ko?" "Zan daina Amma suma ka fada musu su daina cemun _'yar caskale_ " "Naji duk zansa a tattara mun yaran in musu kashedi,muje maza kibawa ummanki hakuri". "Tab ai yaseen nasan Dana Bata daban Bata ba sai ta dakeni ,gara ma inki bayar war" tana Gama fad'ar hakan tayi waje da gudu. Girgiza kansa kawai yayi,Yana addu'ar Allah ya shirya Masa yaran Nasa,tare da matar tasa ma,Dan wannan abin na Maryam yasan yanada nasaba da bakin da Huwaila keyi musu,Dan tun suna kanana in sunyi Mata abu, kamar barna,sai dai kaji ta furta ,"Kai amma wannan yarinyar anyi tsinanniya,ko Kuma anyi matsiyacin yaro,da dai sauran irin wadan Nan kalaman marasa amfani,masu cutar da rayuwar yaranmu,su durkushe,in sun girma mu rasa dalili,alhali wani lokacin muke jifansu da wasu lafuza marasa dadi ,muna ganin kankantar su ko rashin tasirin su,Wanda wallahi komai kankantar zagi Yana taka muhimmiyar rawa a gurbacewar tarbiyar mu a yau. Da sallama ya shiga dakin,inda ya isketa zaune tana yiwa Isma'il fadan yatashi ya sha farau-farau koya danji dama a cikinshi. Saida yasami guri ya zauna sannan shima ya shiga lallabar yaron akan yasha,da kyar yasha kadan sannan ta balla maganin ta bashi, aikuwa saiga amai. "Kut......."ta lailayo ashar ta makamai,bakin matsiyaci,Dan kaga Ina lallabaka,shine kake dada wani langabewa,to Dan kut.........kada kasha ka mutu ma,Kai Ni Allah ma yasa ka mutu In huta da jaraba,yaro inata bin kanka na rasa inda Zansa kaina duk saboda ciwonka,amma komai aka baka saika amayar dashi,ni a wahale Kai a wahale,Dan bak'ar k'eta,Kai ba jinjiri ba ba Kuma d'an yaye ba,to wallahi daga yau sai dai ka mutu ,idan na K'ara baka wani abu magani ko abinci Allah ya tsinemun".Ta karasa maganar tana huci. Da kallo malam Shu'aibu ya bita,Bai ce da ita komai ba ya shiga lallaba Isma'il akan yatashi ya k'ara Shan kunun Koda kad'an ne yasha magani. Itako ta shiga hada kwanuka tana gyaran gurin tana masifa. ****** Misalin Sha biyu na dare,bayan ya tabbatar Daya yaran sunyi bacci,Dan shima Bai Dade da shigowa ba saboda yanayin sana'ar tashi.A zaune yasameta tana kokarin kwanciya. Saida ya samu guri ya zauna,kafin ya Kira sunanta,"Huwaila"! "Na'am mallam". "Ina son zamuyi magana dake,duk da ba wannan shine karo na farko ba,amma Kuma Zan iya cewa wannan shine kusan gargadi na karshe da zanyi Miki". Ganin kamar Yana maganar ransa a d'an b'ace yasata nustsuwa.Ganin da yayi ta maida hankalin ta akansa yasa ya Fara magana. "Wato abinda ke faruwa ne game da furucin ki Akan yaran Nan,anya kuwa Huwaila kina da hankali,kin San dafi da Kuma illar bakin uwa akan 'ya'yanta, mummunan furuci ko ba ga d'an daka Haifa ba,ai baida amfani,bare Kuma ace ga yaranki,tun yaran Nan na Shan nono nake fama dake akan ki gyara kalamanki akan su,amma abu yaci tura,yanzu furucin da kikayi dazu akan Isma'il,idan hakan ta kasance wakeda asara,Kinga nidai inada damar k'ara aure,duk da kuwa bani da tabbacin Zan Kara haihuwar,amma ai daga ni har ke bamuda wata matsala mun tabbatar.Dan Allah na rokeki Dan girman Allah ki gyara kalamanki akan yaran nan,ke bama su ba har wasu yaran daba namu ba,shi yaro na kowa ne,addu'ar shiriya yakamata mu dinga yi musu bawai mugun Baki ba,Dan Haka Ina son daga wannan lokacin Dan Allah ki gyara lafazinki kinji Huwaila ta". Hawayen dake bin fuskarta ta share kafin tace"insha Allah malam bazan sake ba,nima sai bayan nayi sai abin yaita damuna,amma insha Allah Zan kiyaye". "Yauwa Huwaila,Dan Allah a dinga kiyayewa kin San shi harshe dafi ne me zafi,dan Allah bana so kinji". Gyada Kai tayi alamar toh,kafin ya jawo 'yar matarsa Yana me k'ara yimata nasiha cikin hikima. ************************* Tsaye take ta rike k'ugu gaban Rakiya me dambu,tana fad'in"baba Rakiya!wallahi daga yau bazan Kara kawo Miki karar ummita ba, jikinta ne kawai zai fada mata,gara ma kija Mata kunne Dan yaseen idan na kamata lallasar tishin yaji zanyi Mata,Dan karki ganta ma da tabo kice ban fada Miki ba,ki tanaji na magani tun yanzu".ta karasa maganar tana murguda baki. "Ke Maryam ki fita idona,Dan kaniyarki ni kikeyiwa rashin kunya,Dan wannan ba kashedin ummita Kika kawo ba,Ni kike jawa kunne a fakaice,Dan Haka anki ayi Mata fadan,ke ba'ai Miki fad'a ba sai ita,kinbi kin maida Mana Yara kamar jakai,kiyita lodar su kina musu bugun uwa da d'a,dama na fada duk ranar da abinki ya biyo takan ummita Ni Kuma ranar Zan gwada Miki Nima uwar zamani ce,shegiya fitinanniya". "Kenan bazaki Mata fada ba ko?" "Bazan yi matan ba,ta tsokane ki,gobe ma inta ganki Zan Kuma fad'a Mata ta tsokane ki,ai ba fin karfinta kikayi ba,Dan ma ita din saiwar sala ce, badan hakan ba,ai da inta rikeki ko kwacewa bazaki iya yiba,amma yanzun ma muje zuwa"ta karasa maganar tana bude tukunyar dambunta Dan ganin ko yayi,Dan so takeyi ta gama saboda yau ta d'an makara,dama yayar ummita ke fita dashi,wani Kuma ta sayar a gida,to yau Kuma gashi har ta shirya ita kawai ake jira,to iccen ne danye. Kwaaaaaaaaaaa! Taji saukar ruwa saman tukunyar dambun,Wanda tsabar ruwan Daya tumbatsa,har Saida ya antayo waje,ya leme murhun,toka tayo futar burtu tayiwa fuskar Rakiya fenti,tare da yiwa dambu decoration,Dayake bakinta bude yake sanda ruwan ya sauka a murhun,gaba Daya bakinta ya wanke da toka,inda hakoranta sun rikide sun koma ruwan tokar.Wata iriyar ashar ta narko,wadda tasa sauran tokar bakinta da bata Gama jikewa da miyau ba ta feso kamar ta zuki sigari,aikuwa a sukwane tayo Kan maryama dake rike da bakin bokitin k'arfe na wanka,Nan ko suka kasa tsere.mijin Rakiya da dawowarsa kenan daga kasuwa,Yana kokarin kafe kekensa yaga maryam ta fito a guje Rakiya ta dafo Mata,ya bude Baki kenan da niyyar ya Kira matar,gefen bokitin da Maryam ta rataya kamar jaka ya daki bakinsa,Nan take ya wuntsila daga shi har keken Nasa sai gashi a kwata,shima maimakon ya Kira sunan Allah ,sai ji kake ya runtuma ashariya,Yana me shafo bakinsa da jini ke d'iga,aikuwa ya shiga kiciniyar mikewa,duk da kansa dake Sara Masa,Bai hana sa Mara musu baya ba. Itako Maryam gudu takeyi iya karfinta,yayin da rakiya take biye da ita zaninta a hannu sai d'an under's din ciki Daya Sha bakar dauda. Sosai Maryam ke shiga lungu da Rakiya ga Kuma mijinta a baya,Yara da Basu San dalilin gudu ba suka dinga binsu duuuuu suna son ganin me ke faruwa. Itako Maryam ganin tafara gajiya gashi ta rasa gurin nufa kawai saita hango wata majallisar matasa,aikuwa ta nufi can tana fadin "ku taimakamin wayyo ni mahaukaciya ta biyoni",itako Rakiya Jin abinda Maryam ke fad'i yasata lailayo ashar tana Kara laftawa,tare da ikirarin idan har ta rik'e Maryam wallahi saita ga ta daina numfashi.Su kuwa matasan ganin yadda fuskarta tayi dumu-dumu da toka ga bakinta ya hadu ya hade,sai suka dauka da gaske batada lafiyar Nan ko sukayo kanta,ita ko Maryam ta labe tana mayar da numafashi. Sosai matasan suka shiga kiciniyar rike Rakiya,aikuwa ta shiga fizge-fizge,su kuwa sun sami abin bukata,nan wasu suka shiga lagudar inda yai musu a fakaice. Mijinta da karyo kwanarsa kenan yaga yadda ake tattabe matarsa,da sauri ya karasa ya shiga ture matasan yana zaginsu,nan suka kauce ita kuma Rakiya ta fashe da kuka tama rasa abinda zata yiwa yainyar nan,dan inta kamata saita ga ta daina numfashi........ _ina son inga comments din dazai girgiza ni_ *Alkalamin khady* ✍ 🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀 *_'YAR CASKALE_* ( _Sanadin bakin uwa_ ) *NA* *KHADEEJA USMAN* *_(Real Tame Gari)_* *بسم الله الرحمن الرحيم* ___________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ___________________________________ *ALHAMDILLAH! ALHAMDILLAH!* *_AM BACK AGAIN_* 6⃣➡1⃣0⃣ Maimakon Maryam tayo gida data samu ta sulale,aikuwa saita bazama,itace wannan lungu,itace wannan layin,makaranta Kam yau islamiyya ta yafe ta,tunda dama yau asabar ba boko,islamiyyar yamma data safen duk yau bataje ba,tasan ko yau Mai kwatar ta gurin umma sai Allah,shine tace gara kawai ta cika laifinta ya cika cif ayi Mata dukan gaba Daya.(Illar sabawa yaro da duka kenan,komai yayi duka,hakan shi kesa yaro ya zabure yabar Jin tsoron dukanma,gara tun Yana d'an karamin sa ki Saba Masa da kallo ki banbance Masa dai-dai hakan zai fahimci kallon me yake nufi,kada kice komai yayi saikin daka,ki Bari ki Tara tukun,yadda idan Kika rikeshi yasan bazakiyi Masa da Wasa ba,zaiji tsoron gamuwar ku matukar kikace Zaki dakeshi.Allah yabamu ikon gyarawa amin.) A can gida tuni labari yazowa Huwaila,aikuwa yaran Rakiya sunyi rashin mutunci,Dan cewa sukayi a Miko musu Maryam sai sun jajjaga ta,Dan sunji labari tasa uwarsu gudu a titi,Kuma tayi sanadiyar fadawar babansu kwata.Sai da Huwaila tasa aka kirawo Mata malam Shu'aibu yazo ya basu hakuri,da kyar suka hakura suka bar kofar gidan. ********************* Ita kuwa Maryam tana Nan labe ta hango Rakiya da mijinta sun rungumo juna,Rakiya nata gunjin kuka,yayin da mijin keta Bata hakuri,Yana fado Mata irin nau'ikan azabar da zasu yi wa Maryam in sun kamata.Zugar Yara na biye dasu duuuuu! Kunsan Yara in sun samu abun kallo kiris suke jira.A hankali ko Maryam tayi tsulum ta afka cikin yaran ta wage murya da karfi tace,"mahaukaciya 'yar macukule! ,Take ko zugar yaran ta amsa suka maimaita,aikuwa harda tafi Nan ma wasu yaran suka Kara tittidowa,Nan da Nan ko Rakiya ta juyo,aikuwa idonta ya sauka Kan Maryam tana bada wak'a.Ai kuwa sata kwace tayo kansu,nan kuwa Yara suka watse,ta tsaya tana zage-zage tana neman maryam.Itako Maryam lungun gidan su taje ta labe, tana son shiga gida a ranta Kuma tana cewa mudun tsokanar ta Bai cika ba. ***. ******. ******. *** Sai da duhun magariba ya gabato,sannan tasa kanta zuwa soron gidan,dayake soron biyu ne,Haka ta sadada ta leka, dai-dai lokacin ta hango umman nata na bude robar ruwa danta zuba a buta,aikuwa sai taga ba ruwan,ji tayi tana fad'in,"oh ni 'ya su,Kinga a shefa ba ruwa a robar Nan,Allah sarki Isma'il ,sabo da ka Saba zubawa na dauka yau dinma diba kawai zanyi ashe babu,Bari idan nayi sallah nazo naja ruwan duk da ba amfanin Jan ruwa da daddare,Amma ya zanyi" Haka taja ruwan guga Daya ta zuba a buta,ta shiga bandaki,bayan ta fito tayi alwala ta shige daki. Maryam na ganin wucewarta ta shigo gidan tare da nufar gurin rijiyar,ta bude babbar jarkar ruwan ta shige,bayan ta jawo murfin ta Dan Dora aka ta zameshi tana Jin iska,take bacci ya kwasheta cikin kankanin lokaci. Saida Huwaila ta idar da sallar,sannan ta fito Dan Jan ruwan,so takeyi taja da wuri dan ma yaza ma dole ne,da Sai da safe zata ja,to tasan bukatar ruwan na iya tasowa Kuma dole dai rijiyar za'a bude aja komai dare. Tana zuwa ta bude rijiyar,Saida ta jawo ruwan sannan ta Mika hannunta ta Jaye murfin robar tana fadin" oh Kinga na Manta ma ban wanke robar ba,Haka dai zan hakura in zuba da safe a wanke,na ciccika Mana butocin kawai" dai-dai tana kwara ruwan cikin robar ruwan,Wanda yasa Maryam sakin ajiyar zuciya ta farka. D'an jimm umma tayi,Dan saita ji kamar an sauke ajiyar zuciya Kuma daga cikin rijiyar,amma sai Kuma tayi tunanin Kila kunnenta ne,Dan Bata Saba Jan ruwan dare bene,yasa ta Jin hakan,aikuwa ta Kara zura guga tana cewa"yau Maryam Ina tausaya Miki ,Dan ban ma San irin bugun dazan yi Miki ba,laifi goma da ashirin,Allah ya dawo dake gidan kafin babanku ya dawo zanci ubanki,Dan nasan idan Yana Nan nace Zan dakeki hanawa zaiyi,dai dai ta jawo ruwan ta Kara antayawa cikin robar,Maryam ta Kuma sakin ajiyar zuciya saboda sanyi,kun San ruwan rijiya lokacin zafi. Daurewa kawai umma tayi ta kara zura gugan,dan wannan Kar kam da gaske taji anyi ajiyar zuciya,hakan yasa zuciyarta Fara rawa amma wai ita jaruma saita dake,taci gaba da antya ruwan cikin robar,jin da maryam tayi ruwan na neman kawo mata wuya,yasata mikewa ta buga tsalle ta fito jagab da ita,ta zura a guje ta shige dakinsu. Wata kara umma ta saki tare da karanta ayatul kursiyyu iya karfinta,tana nan tsaye Kuma ta kasa sakin gugan yana hannunta,irin d'an dutsen nan na rijiya ya rike gugan Nan umma tawage Baki tana kuka da neman agaji. Mallam Shu'aibu da shigowar shi kenan ya hango matarsa na makyarkyata da sauri ya karasa Yana fad'in"subahanallahi! Huwaila waye ya fada rijiyar,bawai garin jarabar Taki Kika jefamin Yara rijiya ba,ya fada Yana fuzge gugan hannunta,Yana lekawa rijiyar,ganin da duhu ba komai zai gani ba yasa ya juyo a fusace Yana fad'in,kin mun shuru ki fadamin meyake faruwa! Cikin rawar murya da tsoro tace 'matashiyar 'yar ruwa ce ta fito daga rijiyar ta shige dakina". Tsaki yaja,kafin ya saki gugan ya nufi dakin yaran,a zuciyarsa Yana fad'in yaga ranar da Huwaila zatayi hankali. A kudundune yasamu Maryam da kayanta jikakku,tunda yaga Haka ya tabbatar da itace tayiwa uwarta haka.karasawa yayi inda ta kwanta kusa da Isma'il ya tashesu duka,Nan Maryam ta shiga rarraba ido,Bai nuna Mata wani bacin Rai ba,yace ta tashi ta cire kayan jikinta,aikuwa ta mike ta canza ,Nan yake tambayar ta ko taci abinci,Nan ma tace mishi ah'ah ,yasan za'a rina,Dan haka ya fita dakanshi ya fita kicin ya zubo mata,yace taci Yana zuwa. Yana fita ya tarar da Huwaila tsaye bakin kofar dakinta Taki shiga,Yana zuwa yaja hannunta ta shiga tittirjewa,ganin tana cijewa ya juyo yace "Wai miye haka ne Huwaila?ba fa na son sakarcin banza wuce muje,Dan Yara na baro wurin Ina son magana ne dake a gaggauce". Ganin ya shige ciki Bai Kuma dawo ba yasa tayi shahada ta biyo shi,ta samu guri ta zauna tana waige-waige. Bai kulata ba yace,"dama ba komai ya dawo Dani ba sai akan Maganar Maryam, Huwaila bazan boye Miki ba,komai ya faru da yaran nan kece sila, wallahi na tabbatar bakinki ne,gashi yanzu kin samu a damuwa,kullum maryama da kalar tsokanar da zatayo,a tsokaneta Kuma ta jawo magana Nan ma,ba babba ba yaro duk Kan me uwa da wabi takeyi,gashi Bata Jin tsoron ko mu iyayenta Dan kin Gama horar da jikinsu da duka,tasan bazai wuce muma dukanta zamuyi ba intayi ba dai-dai ba,Kinga yanzu abinda ya faru dazu,yanzu Haka maganar da nake Miki mijin Rakiya ne yaje da yaranshi maza manya har gurin san'ata sunce wallahi idon su idon Maryam sai dai wata ba ita ba,na rasa abinyi da kyar aka Basu hakuri suka bar gurin.To shine nake fadawa malam Garba abinda ke faruwa shine ya bani wata shawara yace in Kai Maryam almajiranta kawai". Da sauri Huwaila ta d'ago ta kalleshi tace,"wace irin almajiranta Kuma malam ? Wai ma Isma'il kake nufi ko wa? Dan Naga dai shine namiji Kuma maza ake kaiwa almajirci ba Mata ba". Murmushi yayi kafin yace ," Maryam dai nake nufi kamar yadda Kika ji,malam Garba yace babanshi Yana da almajirai Mata,idan yarinya ta gagara to shi ake kaima,sannan Kuma cikin yardar Allah sai kiga yarinya ta kimtsu ta samu ilimi,sannan bawai bara sukeyi ba,zamu had a Mata kayane kamar zata boading school,shima Kuma acan gidansa ana Basu abinci Dan suna mu'amulla ne kamar yaran gidansa,Ina gudun abinda Maryam zata jawo Mana ne Nan gaba in mun barta Haka. Nanfa ya shiga gayawa Huwaila muhimmancin Kai Maryam makaranta. "Naji malam na Kuma gamsu,amma kasan fa halin Maryam,kana ganin bazata iya dawowa ba?" "Kada ki damu na shirya yadda za'ai tafiyar,Kuma yace min garin lungu ne can jihar jigawa ne". "Shikenan malam, Allah yasa karshen wahalar kenan" "Amin ya amsa,kafin ya mike Yana fadin ta hadawa maryam kayanta kala biyar,Dan da asubar nan zasu tafi a motar malam Garba. Haka ko akayi Daya tashi dawowa ya tahowa da Maryam harda robar almajirai,dasu gari da dakaken kuli magi dadai 'yan wasu abubuwan bukata na 'yan makaranta🤣. ********* Asubar fari suka fito aka tashi Maryam Huwaila ta sallara mata wanka,itadai Bata cewa komai,ana shiryata ana Mata nasiha. Gani sukayi malam ya fito da zundumemen buhu yace"maryama ta taho ki shiga Nan kinji" Make kafada tayi alamar ah'ah,Nan ya shiga.lallabata harta yarda ta zura kafafunta tace"baba kasheni zakuyi?" Zaro ido yayi yace "injiwa yace Miki kashe ki zamuyi?" "Gashi Nan zaku je ku jefani a ruwa". "Ah ah,madinan Nigeria zamu kaiki ki sauke farali,shiyasa muke son mu boyeki anan,kar Yara su ganki suce Suma sai anje dasu,bayan ke kadai ce 'yar gata...." Bai gama ma maganar ba,yaga ta shige buhun tana fadin"to ummana Allah ya kaddara saduwar mu,nidai yau Zan hau jirgi" sai Kuma ta fitoda kanta tace,"to amma baba a maleji zani ko Kuma a booth,da Naga za'a Sani a buhu?" "Ai a kujerar boye Zaki shiyasa,Dan Haka ma Zan yanka Miki inda Zaki dinga Shan iska bakida matsala kinji". Komawa tayi tana fadin,baba k'ulle bakin buhun muyi sauri Kar jirgin ya tafi,amma Allah ya taimaki ummita,da nace wallahi saina mata dukan tsiya,amma yanzun ma idan na dawo indai ban manta ba saina dake tan". Haka malam Shu'aibu ya daure bakin buhun,bayan ya yanka mata wani gurin,yace tasa hancinta dai-dai gurin,Dan ta dinga Shan Iska,Nan ya kinkime ta zuwa bakin motar. Malam Garba ya bude musu gidan baya yasata, shima malam Shu'aibu bayan ya shiga,yayin da Huwaila ke tsaye tana musu sallama da addu'a Allah ya tsare,tana Jin ba Dadi rabuwa da 'yar tata,badan rashin lafiyar Isma'il ba da da ita za'a ,Amma tana musu fatan sauka lfy da Kuma fatan samun shiriyar 'yar tata,ance kowanne yaro da kalar kuruciyar sa,to ita Kam ta Maryam ta dabance. Jin an tada motar Maryam ta saito bakinta saitin bular buhun tace"mama ke bazaki filin jirgin ba?" "Eh Zan biyo ku daga baya kinji mairo ta,ta fada tana goge kwallar data zubo mata. Haka aka ja motar suka tafi suna fatan sauka lfy. **** Da yake tsakanin Kano da jigawa ba wani nisa,Koda Tara tayi sun shiga garin,a irin hakan ne,malama Garba ya kalli malam Shu'aibu yace,"Amma fa munyi sauri,duk da ba wani nisa tsakanin Kano da jigawa,amma gashi har mun iso". Yana shirin bashi amsa,Maryam ta saito bakinta tace,"wace jigawa Kuma? Badai wadda nakeji a state and capital ba? Kenan a filing jirgin jigawa zamu tashi?"duk ta jero wannan tambayar tana jiran amsa....... _to readers Ku fada Mata gaskiya mana🤣_ *Gaskiya Naga ruwan comments jiya,na Kuma gode muku masoya Allah yakara kauna,Ku tayani addu'a Banda lfy wlh* *Alkalamin khady* ✍ 🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀 *_YAR CASKALE_* ( _Sanadin bakin uwa_) *بسم الله الرحمن الرحيم.* ____________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ 1⃣1⃣-1⃣5⃣ Sai yanzu suka San sun tabka katobara na ambatar sunan garin da sukayi,Dan Haka dukansu suka kalli juna da ido kafin malam Garba yace,"wato malam Shu'aibu,Inka fahimci wani abu, shi zuwa madina a biyo ta jigawa sai Mai babban rabo,yanzu dai kaga sunan fa garinmu na asali shine bakada suna,amma yaran zamani suke kiranshi da Kano,bayan Kuma in zaka shekara cewa a kaika Kano bamai ganewa,inhar ka fita daga garin,sai dai kace a kaika kanoma,Kuma fa Inka sake mutum Bai gane ba kace ya kaika Kano to lamari ya b'aci,Dan gidan wannan mashahurin d'an yankan Kai za'a kaika wato d'an kano,dan Haka gara kawai kayi zamanka inda Allah ya ajiyeka". Murmushi malam Shu'aibu yayi,danya fahimci inda zancen ya dosa,Yana shirin yin magana suka k'araso karamin kauyen,kofar gidan malam Jafaru mahaifin malam Garba. Jama'ar garin sunyi murnar ganin malam Garba,Dan haka duk alamajiran malam suka shiga murnar ganin d'an malam d'in,dan ko ba komai Yana kawo musu tsarabar lemo da biredi,kun San dai k'auye,duk k'in ka da biredi ko baka ci,to idan kaje k'auye ka kwana biyu,wallahi saika yi marmarin biredi😜 Tunda motar ta tsaya malam Shu'aibu ya zagaya ya kwance Maryam a buhu,wadda ya zuwa yanzu ta jik'e da zufa,aikuwa Yana bud'ewa ta Fara rarraba ido,Nan idonta ya sauka akan tarin yaran da suka kewaye su.Zaro ido tayi kafin tace,"baba yana ganni cikin ba'kak'en fata,ba dai ta filin jirgin k'auye zamu tafi ba?" Dariyar data bayyana hak'oransa ya yi ,sannan yace,"ai gurin bita muka kawoki,Kinga Yara can dayawa" yayi Mata nuni da tarin yaran dake zaune duk rike da alluna,sannan yaci gaba,"muna hanya aka fad'a Mana sai mun Fara kaiki gurin bita tukun,Dan haka muka kawoki anan in kin Gama haddace komai saiku wuce kawai,lokacin ma yarinyar ta k'ara girma ko?" Ya karasa maganar Yana shafa kanta,kafin ya kamo hannunta suka fito,yayin da suka doshi rumfar da malam Jafaru yake. **** Duk abinda yakamata ayi Kuma su Sani dangane da zaman Maryam anyi,Kuma Alhamdillah duk malam Shu'aibu ya gamsu,bayan sun gama ganawa akace a dauki jakar Maryam a shiga da ita ciki.Duk k'iriniya da rawar Kai da Kuma son ke ta hazo na Maryam Saida ta zubda kwalla da babanta zai tafi,bayan yayi Mata nasihan ta daina rashin ji da sauran k'iriniya,ta tsaya tayi haddarta Dan ta kasance a 'yan tashin farko.Haka suka rabu bayan ya bawa malam kud'i yace a dinga bata intana bukatar wani abun.Kuma itama ya zaro nera goma sabuwa fil ya Bata,hakan ya d'an sanyaya ranta. **** Bayan an shiga da kayan Maryam itama ta shiga gidan malam.Babban gida ne irin na k'auye Daya kunshi bangarori da dama,matan malam biyu,yayin da duk yaransa maza ne baida 'ya mace ko d'aya.D'akin da aka Kai kayan Maryam,d'akine da akayiwa kanta irin wadda akeyiwa almajirai maza,sai dai su abin birgewa harda katifunsu.kuma dakin duk da na kasa ne amma a lailaye yake da sumunti,Kuma an shimfida musu katon buhu,inda kusan duk Mai gata a cikinsu ita keda katifa,wasu Kuma bargo,wasu Kuma tabarmi,daki biyu ne irin hakan,yaran matasa ne 'yammata,sai Kuma irin su Maryam d'in,dan gaskiya kusan sune ma kanana. ***** Matan malam akwai iya salame itace uwar gida kasancewar mahaifiyar su malam Garba itace matarsa ta farko ta ladan noma Allah yayi Mata rasuwa da dadewa,a yanzu dai salame uwar gida itace yaranta duk manya maza,Dan malam Garba shi kadai ne mahaifiyar sa ta haifa.Sai matarsa ta biyu Zuwaira,ita ma yaranta duk mazan ne,amma kuma sune kanana,duk da ta daina haihuwa,autanta bazai wuce shekara 8 ba. Zaman gidan malam Garba shima zamane na kishi,irin kishin kauyen nan.sam matan Nan basuda mutunci yaran da aka kawo irin su Maryam,su keyi musu shara da wanke-wanke harda girki.Idan kaga suna haba-haba da yarinya,to sunsan 'yar masu dashi ce,iyayenta in sunzo suna musu abin hasafi,Kuma in an kawowa yarinya kayan dad'i suna sammasu. Tun daga kawo kayan Maryam da suka bude sukaga kayane na dangin irin namu ya ku bayi,Nan suka hau gatsine-gatsine,basuyi Mata wata tarbar mutunci ba. *****"************"****** A d'an wannan lokacin zamu iya cewa marayam ta sake,dan ba ruwanta da bakunta,sa kanta da tayi a zata keta hazo,yasa bata fara Nuna Hali ba,Kuma Bata Fara halartar karatun ba,tunda litinin aka kawota,malam yace ta huta zuwa asabar saita Fara daukar karatun. A iya wannan kwankin Maryam ta Fara fahimtar halin matan gidan,tazama mage Mai kwanciyar daukar Rai,saika rantse Bata San wani abu Wai shi rashin mutumci ba. Yau aka tashi a dakin su Maryam anyi sata,aikuwa Nan fa gida ya kacame aka shiga tone tonen kaya,dayake yarinyar da akawa sata,wata 'yar kaduna ce,Kuma 'yar masu dashi,sosai su Zuwaira suke karuwa da ita,hakan yasa sukafi kowa zakewa akan abin,nan ko suka shiga bincike kayan kowa,ganin Basu samu ba yasa salame tsayawa ta rike k'ugu tace" Ni fa gaskiya abin Nan akwai abin mamaki,tunda muke cikin almajiran malam babu Wanda yataba Mana sata,nidai inaga wannan yarinyar" ta nuna Maryam" inaga sata ta addabi jama'a da ita shiyasa suka dungumo ta suka kawota gun malam,Wanda shi kowacce tantariya a cewarsa zai iya da ita,to ai Sai ya zo yayi Mata kafi,tun kafin ta Gama damu". Dafe kirji Maryam tayi tare da zaro ido tace,"Ni d'in ce barauniyar ko wata?" Zuwaira ce tayi caraf tace,"uwar wace bakuwar zuwa da bamusan halinta ba inba ke ba". Hawaye Maryam tafara yi sannan tace" Ni d'in Nan 'yar Karamar yarinya Dani Ina Zan iya wani sata,Kuma ma idan nayi satar abinda kukace Ni da Banda aljihu Ina Zan boye,wallahi tunda kukaimin sharri da banyi ba ma nayi d'in". "Dan ubanki mu kike murgudawa Baki,sharri zami Miki ko me?" Maryam dai batace komai ba illah kuka data Fara yi, a zuciyarta tana jin ita Tama fasa zuwa makkan tunda akayi haka,gara azo a koma da ita gida tama yiwa ummita dukan datace zatayi Mata. Haka dai aka karaci tujarar aka gama,shi malam ma baisan abinda ke faruwa ba. ***** Ranar asabar kuwa kamar yadda Maryam taga kowa nayi itama Haka tayi,duk da ta tashi da kewar yayanta Isma'il da Kuma mamanta,tace ba yanzu zata tuna babanta ba,su din dai ta damu dasu da son gani,Dan tasan yanzu da umma ta lakada Mata duka yafi a kirga.Ina sonki ummana ta furta a hankali.Dayake duk kusan 'yammata ne shiyasa bamai bi takanta bare har ya tabota. Yau su Maryam an hallara a makarantar,rumfar malam ta cika,Yara da manya,dayake ya hada da yaran gari suna zuwa daukan karatun. Kamar a boko Haka malam ya dinga wa Maryam interview,bai samu komai ba,illah fatiha,Dan itama da kyar takaita,yayi mamaki kwarai,inda yasata ajin Yara aka Bata allo da aka rubuta basin mi'a ra,aka ce ta Fara da nan. Aji-aji abin nasu yake cikin tsari,Dan Haka ajin Yara aka kaita,duk da itama yarinyar ce,amma tafi son akaita cikin manya,aikuwa nan Saida ta bayyana a fuskarta Bata so ba. Tana zaune amma ba karatun take ba,wata yarinya dake bayanta,ta bude murya tace "malam ga wata Bata karatu". Aikuwa malam ya zaburo Yana fadin "wacece?" Nuna Maryam tayi,aikuwa ya tsulawa Maryam bulala,har Saida yayi Mata bulala biyar,Yana jaddada Mata Nan ba gurin Wasa bane.Kema dagas Maryam babu ko hawaye, aikuwa ta rasa me zatayi wa yarinyar ta huce,Nan ko ta dage ta gallara Mata mintsini,yarinya ko ta callara ihu,ko kafin malam ya juyo wata ta bude Baki da niyar Kai Kara ita data kusa da ita,aikuwa ta Maryam ta ankara,ta Kama kawunansu ta gwara,Suma ko kukan suka saka,Nan da Nan tahau rankwashin yaran da Kuma gwarawa wasu kawuna,kukansu ya karade ko'ina Wanda ya jawo hanakalin malam d'in,dama sauran wadanda ke karatu. Ganin malam yayo gurin da Dan ganin duk yaran sun rude yasa ta kwasa da gudu tayi cikin gida,Wanda tana shiga dai-dai salame ta gama miyar dumamen tuwo,Dan jiya miyar karewa tayi,shine malam yanzu ya Aiko yace a bashi dumame Dan hantsi yayi yunwa yakeji,shine salame gimbiya tace yadan dakata Babu Miya za'ai sabuwa,yace to a kada Masa miyar kubewa,aikuwa tana saukewa Maryam na shekowa,akuyar dake tsaye bakin danga ta zabura tayi ciki da miyar Maryam na bayanta,aikuwa har wani salo miyar ta bayar gurin zubewa ji kake lemmmmmmmm........ _nagode da addu'arku Alhamdillah,Ina sonku sosai fans,Naga comment dinku ya girgiza zuciyata,da yasa nayi Mana addu'ar Allah yakara kauna. *Alkalamin khady* ✍ 🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀 🌀🌀🌀 *_'YAR CASKALE_* ( _Sanadin bakin uwa_) *NÀ* *KHADIJA USMAN* ( _Real Tame Gari_ ) *بسم الله الرحمن الرحيم* ____________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ 1⃣6⃣-2⃣0⃣ "Kam balastin!" salame ta furta a fusace,hakan ko ya jawo hankalin Zuwaira dake d'aki tana magana da yaranta.Dukansu tsaye sukayi suna kallon maryam,wadda ta tsaya wuk'iiii tana kallon kowa.Ganin hakan yasa salame yo kanta tana fad'in"yau Banga shegen Daya Isa ya hanani cin uban yarinyar Nan ba,Ni dama tunda aka kawota Bata kwanta min ba Dan Haka yau sai kinsan kin taba salame". Shan gabanta Zuwaira tayi tana fadi'in"ah ah salame,gara ki Kira malam ki fad'a Masa,dan kin San Bai bamu izinin dukan dalibansa ba,Dan Haka Ni ba ruwana". "Dayalla gafara can tsohuwar munafuka,wato Dan ba miyarki aka zubar ba shine Zaki ce kada in daketa,ke uwar tausayi,harda wani yen yen yen! Mayam jeyi fata" tayi maganar tana kwaikwayon Wai maganar zuwaira.Dan haka saina daketa wallahi". Tsalle Zuwaira tayi taci d'amara tana fad'in" Ni Kuma zanga uban dazai tab'ata,miyace an zubar,Kuma ma ai akuyar lado ce ta zubar kibi akuyar Mana ki daka in gaskiya kike bi". Aikuwa Nan hayaniya ta kaure,yaransu ma suka shiga cikin rigimar,itako Maryam tana tsaye gefe tana kallonsu,ganin sai cacar Baki sukeyi sunki suba hammata iska yasata fad'in"mu in zakuyi kuyi dan Allah kubar sa Mana rai,nagaji da kallon tsohon yayi". D'aya daga cikin yaran malam me suna Idris ya kalli Maryam yace"A daina sa muku rai da me?" "Da fad'an Mana,in zasuyi suyi kawai musha kallo".Suna Shirin yin magana sukaji sallamar malam da gyaran murya,Nan da nan kuwa kowacce ta nutsu,dan duk bala'insu,to yanayi musu kwarjini kuma basayi a gabansa,Dan haka suka nutsu kowacce taja baya. Tsayawa yayi Yana Kare musu kallo kafin yace "Ku kuma lfy naganku tsaye kamar tab'are?" Zuwaira ce ta gyara tsaiwarta sannan ta ce,"wallahi malam gara da Allah ya kawoka,wai fa wannan 'yar kwiciciyar yarinyar ce,sabuwar dalibarka,ta shek'o da gudu inaga ko Kashi takeji,shine tsautsayi yasa tabi takan miyar da Yaya salame tayi,to shine fa tace yau saita Mata mugun bugu,shine na hanata nace tabari idan kazo ta fad'a maka,shine ta taso zata dakeni". "Ke uwar 'yan sharri!cewar salame,ni d'in ce nace Zan dakeki,to in dakeki ince na daki wa?" "Kin daki uwarki,shegiya Ni Zaki tambaya ma in kin dakeni kice kin daki wa? 'yarki ce ni ko k'anwar ki,in kina ganin damata ko zamu gwada ne.Jin hakan yasa salame fusata suka kacame da dambe.Su malam da ke gefe sai sukaja da baya,Dan wata mulmula da akayi da Zuwaira ji kake makkkkk an maka ta da k'asa.Ganin hakan yasa Maryam rugawa da gudu, ta dauko wata k'arama da wani sillen Kara tazo ta tsugguna saitin inda aka tàushe Zuwaira,ta shiga kid'a tana fad'in"jaruma! Jaruma! Baba Zuwaira jaruma! Wannan kid'an ya fargar da Zuwaira taji wani sabon k'arfi,aikuwa saita juye da salame ta shiga kintsimar ta,ganin haka yasa yaran sukayo caaa! malam ya dakatar dasu,Babu wanda ya raba su,malam ya Hana,saida suka gaji sannan suka Bari,bayan an daddaki bakin juna.Kuma har wannan lokacin maryam bata daina kid'an ba.Sai da kowacce ta koma gefe tana mayar da numfashi, itako Maryam ta janye fanteka gefe ta zuba musu ido bayan ta tallafe fuskarta da duka hannuwanta biyu. Shi kam malam baice dasu komai ba,illa zuwa da yayi ya kama hannun maryam yaja ta itako batare da Nuna tsoro ba ta bishi,Dan tasan dai bazai wuce ya daketa ba. D'akinsa ya nufa da ita,batare da yace da ita komai ba ya zaunar da ita Kan wani buzu dake gefe.Wata jaka ya jawo ya dauko wani daurin magani ya jawo wani kwano ya dauko d'aurin rubutu ya tsiyaya a Kofi ya hada da wannan maganin.Yakai wajen minti biyar Yana Kara tofa addu'a a ciki,sannan ya mikowa maryam yace ta karba tasha. Zaro ido waje tayi sannan tace"miyau d'in zansha malam?" "Wane irin miyau Kuma maryama,bakya ganin addu'a nayi miki,Dan haka yi hakuri karbi Kisha kinji mairoro" ya fad'a Yana Mata alamar rarrashi. Karba tayi takai bakinta da niyyar sha sai Kuma ta dawo dashi tace"tsakaninka da Allah malam ka wanke bakinka kafin kayimin addu'ar Nan?" Yak'e malam yayi yace "nawanke Mana baki gani ba tun safe nake asuwaki". "Tab da da asuwakin safe zaka tofeni wallahi bazan Sha ba" ta fad'a tana dungurar da kofin.Duk yadda malam yakai ga lallaba ta kin Sha tayi,hakan ko ya fusata shi,Saida ya dauko wata narkekikiyar bulala wadda yake maganin irin su Maryam da ita ya zuba mata,.Duk yadda ta Saba da duka Amma taji wannan bulalar ta dabance,aikuwa ta shiga canyara kuka,shi kuwa Saida ya tabbatar tayi laushi sannan ya kyaleta Kuma bayan ya tabbatar ta shanye rubutun,ya fada Mata da niyyar da zata Sha a zuciyarta amma sai cewa tayi a zuciyar tata"ka da Allah ya shiryeni". ************** Wannan dukan da malam yayiwa maryam Saida ya sata zazzabi,dayake kusan d'aliban suna da had'in Kai a wannan fannin Kuma ganinta k'arama yasa suka kula da ita.Babanta yayo Mata aike amma baizo ba hakan yasa ta samu k'arin wasu kayayyakin,wanda suke masu dadi,duk da take yarinya Amma ta lura da halin matan malam,Dan Haka saita Zama zakara me neman suna bada kwaya kaci tsakuwa,hakan yasa suka d'an Fara janta a jiki,duk da su a tsakaninsu babu wata jituwar kirki. Tun dukan da malam yayiwa maryam yasa ta nutsu,Nan shida kanshi malam ya Kira babanta Yana Masa albishir da ci gaban da aka samu,nan kuwa ya Nuna farin cikinsa har yake fadawa huwaila,wadda tace in an kwana biyu zasu zo suga Maryam din. ************************ Yau ta tashi da niyyar aiwatar da kudurin dake ranta,Maryam yarinya ce Mai ra'ayin rik'au,batada hak'uri Sam,duk da batada yawan shekaru,amma tanada akidar rama abinda aka Mata,sannan ga bak'ar mugunta a gun Yara sa'anninta,Sam batada tsoro ta Saba da duka da zagi,hakan yasa duk wani duka ko hargagin mutum baya tsoratata. **** Duk da irin kyautar datayiwa su salame,hakan baisa sun barta haka ba,Saida suka bi suka k'ara da wasu abubuwan a gabanta,Dan Haka tace Suma sunci bashi. Laraba me d'an bagalaje,irin narka-narkan matan Nan ne,saboda ma girmanta yasa tak'i auruwa,Dan gaskiya ita d'ince komai nata na musamman ne,hakan yasa dataga tak'i auruwa,saita Fara sana'o'i kala-kala,da sana'ar cikin gida takeyi,to kun San matan aure da cin bashi,yazamana idan mace taci bashinta,har gidanki har dakinki zataje ta jawo ki,in kin Bata kudinta kin tsira,in Kince Babu kuwa,Nan zata kamaki kamar 'yarta taita jibga,har sai anzo an kwaceki,hakan da takeyi ne yasa duk aka daina siyen kayan ta.Saita yanke shawarar komawa sana'ar yara,Kuma da biyar goma tana samu abinta.Tunda Maryam tasan da ita duk wani tattalin arzikinta ya Fara k'arewa a can. Yauma can ta nufa,tana zuwa kuwa laraba tahau washe Baki,Dan jininsu ya had'u Dana maryam,aikuwa ta tsugguna tana me kokarin bude murfin da aka rufe farantin d'an malele,Saida ta k'ara zambada yaji a iya Wanda zata iya siya,dayake yau batajin cin d'an ba galajen ,d'an malelen take sha'awa,kuma gashi yau yajin laraba yasha kafi zabo yayi chauuu dashi. Jin cikinta kamar ta shafa mota ga wani mugun kwadayi datakeji,ji take idan aka Bata farantin d'an malelen tana iya cinye shi.dan haka ta gyara zamanta saman wani d'ab karamin dutse tace,"Anti laraba kin San me?" Dai-dai tana make wata yarinyar data siyi d'an malele ta tsaya lasar faranti tace" sai kin fad'a mairo?" Gyara zaman ta kumayi sannan tace "Wai malam naji yace Yana sonki".Tsabar farin cikin Jin wannan kalmar me tsada yasa laraba ta saki Baki da hanci ta kasa motsi,illa jawo hannun yarinyar data make yanzu da tayi ta dan gwarar da ita,da kyar ta iya bud'e baki tace "cinye duka"Aikuwa yarinya ta gyara Zama tana washe baki,ganin haka yasa itama Maryam matsowa tana saka hannu suka hau cin d'an malelen,yayinda laraba take fad'in" taho farar yarinya me farin labari ki k'ara fad'a mun inji a wane kalar yanayi ya furta Miki Yana so na" "Um um Anty laraba, Bari in gama tukun"sam laraba tak'i barin Maryam ta sake da cin d'an waken,fad'i take ta taso inta Gama Bata labarin zata yi Mata Wanda yafi wannan dad'i,amma Sam Maryam tak'i bari.Ganin haka yasa laraba tasowa cak tayiwa Maryam daukar jarirai ta zauna ta d'ora ta bisa cinyarta tana fadin,bani labarin malam ja'afar d'ina ta fad'a tana karkada ido". "Nidai gaskiya Anty laraba ki daina marmar da idon Nan kina tsorata ni kamar fa zabi yar aljana haka Kika koma". Duk da taji haushi amma Dan Jin ance ana sonta ta maze tace to na daina fad'amin kinji,Dan in munyi aure da malam bazaki k'ara kwana d'akin Nan ba,sai d'akina kece 'yar tayin kwana na". 😳"amma ba gado d'aya zamu rink'a kwana ba dai ko?" "A gado d'aya mana,ai Ni yanzu banida wadda ta fiki". "Har babarku da babanku?" "Eh Mana,yanzu dai tashi muje nayiwa malam girki me dadi,ki tafar mishi da shi". Aikuwa suka rankaya gidansu laraba,ranar ma danba galajen harshi kyautar shi ta bayar. Danwaken fulawa tayiwa malam,aka daka Masa had'ad'd'en yaji Wanda yaji onga,itama Maryam an sammata nata nana ta k'ara ci ta sud'e kwano sai kace me cikin zani. Cikin kwanukan da aka d'ebi shekaru ana tarawa Dan jiran ranar aure.Ciki aka dakko falleliyar langa aka zubawa malam a ciki ,har Maryam ta d'auka zata tafi saita ajiye.Da sauri laraba ta kalleta tace "tawajena ya akayi ne?" "Ba komai,kawai jinai bazan iya Kai Masa bane,abin yayimin nauyi" Da sauri laraba ta matso tana fad'in"haba 'yar d'akina ,taimaka kikai Masa,kice Masa Nima Ina sonsa ungo wannan ma,ta ciro naira ashirin ta Bata, aikuwa Nan da Nan Maryam ta d'auka ta fice.Laraba dake tsaye mamanta na tayata murna kawai saita buga tsalle,Amma abin mamakin ko rabuwa da k'asa batayi ba,illa mazaunan ta da sukayi sama da k'asa da Kuma teb'arta datayi rawa. *********************** Tana shiga gidan cikin sa'a ta Sami duk ahlin gidan a hallare,aikuwa gaban Zuwaira taje ta mik'a Mata d'anwake,Koda Zuwaira ta bude ta gani nasha-nasha da Mai,babu tambayar daga Ina,kawai tahau juyawa tahau kasaf ta shi,bayan ta jefa biyu a bakinta tana fad'in "um um um,gaskiya kowace tayi d'anwaken Nan ta kwararriya ce",Nan ta mikawa kowa ya d'auka. Saida kowa ya cinye ana sid'e hannu sannan salame ta juyo ta kalli Maryam,wadda Dan tsabar dadin da d'anwake yayi,an Manta da ita data kawo a rabo ko Bata ba ai ba,tana gefe tadau wani siririn Kara tana Wasa dashi a k'asa taji salame nacewa"'yar albarka Ina Kika samu uwar d'aki harta Baki wannan danwaken,Dan nasan wannan na musamman ne". Batare data d'ago daga abinda takeyi ba tace"budurwar malam ce" Wata irin kwarewa Zuwaira tayi,wadda tasata Fara kelaya Aman danwaken dataci,itako salame cewa tayi "wane malam din Kuma?" Saida Maryam ta d'ago wannan karon,harda cewa zuwaira,"sannu baba" sannan tace "malam Mana,Daya dakeni rannan a dakinsa,malam dai na Nan gidan,baban su Idiris". Cikin hargowa da bala'i dukansu suka shiga fad'in,malam yaci amanarsu wace shegiyar ce wannan,harda Masa girki,wato shiyassa yau yak'i cin abinci yace a koshe yake,ashe dama abincinta yake jira,aikuwa yau zaizo ya samesu,Nan suka kalli maryam sukace ta fada musu wacece ta aikota. Cikin ko in kula tace" laraba tirela" A tare suka dafa kirji suka maimaita "Laraba tirela fa kikace!" Hakan yayi dai-dai da shigowar malam Wanda Bai San wainar da ake toyawa ba yace "me laraban tayi naji ana Kiran sunan ta..........." _kuyi hakuri wallahi Banda lafiya ne,Amma nasami sauki Amma ban warke ba,insha Allah idan na warware zaku jini sosai_ *Alkalamin khady* ✍ 🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀 🌀🌀🌀 *_'YAR CASKALE_* ( _Sanadin bakin uwa_) *NÀ* *KHADIJA USMAN* ( _Real Tame Gari_ ) *بسم الله الرحمن الرحيم* ____________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ 2⃣1⃣-2⃣5⃣ _Hakika masoya basa taba k'arewa a rayuwa,Allah yak'ara k'auna da zumunci amin_ _Gasikya ba abinda zance muku sai godiya_ *TAME GARI FANS NOVEL,1,2,3* *KAINUWA FANS* *HAUSA NOVELS GROUP 1,2* *HAZAK'A GROUP* *KOMAI DA RUWANKA GROUP* *MUTUNTA JUNA GROUP* *MASOYA NOVELS GROUP* *MUK'ARU DA JUNA GROUP* *KOWA NAMU NE GROUP* *Kai alk'ur,an Kuna da yawa bazanma iya lissafa ku ba,dukka wadannan groups din,sune Kan gaba wajen yimin comment,nagani Kuma nayaba na Kuma gode,Allah yabarmu tare yabamu aron rai da lafiya* _________________________________ Dukansu shiru sukayi suna huci.Shikuma cikin rashin lura da yanayin su yak'ara cewa"nace me laraban tayi ake Kiran sunanta?fatan dai ba wani yaron bane ya tsokano ta,Dan ni bana son rigimar yarinyar nan wallahi". Tsaki salame taja sannan tace"dama Ina zaka so Yara su tsokano amaryar ka,tunda kasan abinda ka k'ulla,ashe shiyasa kwana biyu in an kawo maka abinci sai kace ka k'oshi,dama kasan inda kake zuwa kake cika cikinka,to asirinka ya tonu yau d'in nan,Kai inba ma rashin Sanin kala ba,me zakayi da laraba tirela, yarinyar da naji Yara na fad'in da daddare tifa take Zama,shi ne Kai zaka je ka kwaso Mana ita ko,duk tabi dare ta markad'e mu ace munyi hatsari da safe,to nidai wallahi zan furta haram,kawai ka sakeni nace astagafirullah daga baya" ta k'arasa zancen tana girgiza.Itama zuwaira ta amshe da fad'in" kema kenan Yaya da kukayi aure tun zamanin k'uruciya har aka girma tare,bare ni sabuwar zuwa wadda ko yau ya shek'e zan iya aure in haihu,da dai a auromin laraba tirela a matsayin kishiya,wallahi na gwammace a kaini gidan mahaukata in dinga musu burushi". "Wai ni duk ku tsaya"ku wane munafikin ne yace muku zan k'ara aure,auren ma Kuma Wai yarinyar Nan laraba, yarinyar da aka Haifa a gabana". "Oho dai,ko ma dai Kai ka karbi haihuwar mudai bazamu yadda ba"cewar zuwaira,"Dan tun yanzu anayo maka wannan zazzak'an girkin Ina zaka iya hakura" "Wane girki Kuma? au shi munafikin har ce muku yayi tanayo min girki kenan? Samiran da aka kawo d'anwake salame ta dauko ta dungurar a gabansa tace"ga shaida Nan ai Kuma ga Maryam Nan ka tambayeta Dan ita ta aiko" "Hummm! Kawai malam yasami zarafin cewa,Dan ya lura yau sharri matan nasa sukeji,Dan Haka ya juya ya kalli Maryam dake zaune saman wani d'an dutse tana gwagwiyar taura yace"ke maryama waya Baki abinci ki kawo,Kuma wa akace ki kaiwa kikayi batan Kai Kika kawo Nan?" Saida ta tsotse kwallon ta yar sannan tace"Anty amarya ce tabayar a kawo maka,Kuma tace Wai kazo da wuri yau tunda ba makaranta,sannan Wai in fad'a maka,malum- malum dinka dakaje da ita rannan ita zakasa Wai kafi kyau,saika koma kamar halifa d'anka,sannan Wai ka tafi Mata da lemon Nan na jarka irin na jiya Wai taji dadinsa,Kuma Wai maganar kazar baba Zuwaira dakace......" Uban babanki!🙊 Malam ya furta a fusace bayan yayo kan maryam,wallahi kedai wannan ba k'aramar jaraba bace,ashe shiyasa aka had'oki aka kawomin ke,dayake uwarki 'yar k'aramar hukumar Gama ce,shine Kika zo ki gama ni da iyalina tun kin 'yar kankanuwar ki Ina ga kin girma Kuma,gashi marabina da ashariya tun banfi shekara shida zuwa bakwai ba,harna manta harrufan da ake hadawa ayi zagi,amma yau gashi kin sa na tunosu a guje,Dan haka yau sai jikinki ya fad'a miki,sai kin furta da bakinki cewar karya kike". Dukansu suka Sha gabansa suna fadin yafara bugunsu kafin ya daki Maryam,danta Fadi abinda yake boyewa shine zai musu borin kunya.Hakan ya Kara fusata malam, musamman Daya ga dukkan dalibansa sun taru suna kallon su,hakan yasa yafara ball da duk wani abu dake tsakar gidan yashiga sababi.Nan fa gida ya kacame,inda Yana Fadi matansa na Fadi,abinda Bai taba faruwa ba a tarihin aurensu,hakan yasa wasu daga cikin yaran suka ruga suka kirawo wasu daga cikin abokan malam dake zaune kofar gida. Sam ba Wanda ya lura da sulalewar maryam,tsawon lokaci ana fama da malam da matansa suyi shuru amma Abu ya faskara,shi yanaso su fahimci gaskiyarsa su yadda baida wata alaka da laraba,su Kuma sunki amincewa.Zuwaira ce ta mike tana fad'in,ai wallahi tunda kaki sakinmu to daga Kai har amaryar taka inta shigo zaku gane kurenk......" Maganar ta makale ganinta ta shigo famkam-famkam,aikuwa da matsiyacin gudu Zuwaira ta shige dakinta ta banko kofa,yayin da salame tace"ke kuma lafiya Kika wani shige d'aki ko ya tsorata ki ne da idanu,to Ni yanzu Sam kallonsa baya firgita ni,Dan Haka Bari na karasa abinda Baki fada ba,idona idon laraba wallahi sai dai buzun t........" Itama ta kasa k'arasawa ganin an budawa laraba hanya ta nufo ta. Wata irin k'ara ta saki tana fadin"na shiga uku malam,badai aikawa kayi aka kirawota ba,muna Nan muna tsara yadda za'ai muyiwa dakin da zata zauna saukar kur'ani ,shine ka aika a kirawota salon ka wahalar da amarya,sannunki da zuwa amaryar mu,yanzu nake cewa idonki idona saina gode Miki bisa dawainiya da malam" ta karasa maganar tana me karkade tabarma Dan laraba ta zauna.Aikuwa hankam-hankam ta shiga washe baki,ta juya ta nufi gurin Zama,Dan dama Maryam ce taje tace Mata Wai tazo malam nason ganinta zai musu nasiha,shine fa ta debo jiki ta taho,Dan Koda ta fadawa uwar cewa tayi taje kawai,inma ba matsala tayi zamanta sai su biyota da kayanta a daura aure da la'asar,ita duk Bata fahimci ma abinda matan malam din ke fada ba,shiyasa take fara'a, musamman data gansu duk Ahlin gidan a had'e hakan ya k'ara tabbatar Mata da gabatar musu da ita zaiyi,"kaiiii gaskiya malam d'an soyayya ne" ta furta a zuciyarta........ _Idan naga comment dayawa zaku Kara birgeni,sannan ga Wanda ke cikin group Dina,bazan gaji da shara ba,domin duk wadda Naga ta karanta babu comment ko tana zaman labe to zata jita a waje,sannan duk group din da kukaga na daina musu posting,to basa comment ne,Dan haka kada aga laifina Kuna Raina masoya._ *Alakamin khady* ✍ 🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀 🌀🌀🌀 *_'YAR CASKALE_* ( _Sanadin bakin uwa_) *NÀ* *KHADIJA USMAN* ( _Real Tame Gari_ ) *بسم الله الرحمن الرحيم* ____________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ 2⃣6⃣-3⃣0⃣ 🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣 Gaskiya na Dade Banga comment din Daya dinga bani dariya ba,kamar jiya da yau,Ashe Haka laraban malam keda masoya,to muje zuwa danjin yadda zata Kaya. 😂😂😂😂😂😂😂 ________________________________ Ji malam yakeyi kamar yayi hauka yau,Dan inya juya suka hada ido da laraba saita sakar mishi wani makahon fari,Wanda ke Kara sashi yaji wani yarrr,idan Kuma yakai duba ga inda take zaune yaga yadda ta mamaye fiye da Rabin tabarmar Saiya ji gabansa ya fad'i,Dan Haka ya kasa cewa komai,illah laraba daketa zuba mishi murmushin soyayya🙊. Suna a Haka Zuwaira ta Dan bude K'ofa ta leko,Dan taji batajiyo ihun kowa ba,hakan yasa tace Bari ta fito taga meke faruwa.Ganin Maryam dare dare bisa cinyar laraba daga fitowarta ta kasa hakuri tace" na shiga uku,ke laraba nono kike Shirin Bata kome? Wannan shi ake Kira tayani kallon lalle a duwawu,inba Haka ba,ai gara kice a kaiki gidan marayu in nonon ne yayi Miki nauyi kike son ragewa,saikije ki rabar wa marasa iyaye sadaka,amma ba kizo ki dauki tsohuwar yaye ba kice Zaki shayar da ita". Tunda ta Fara maganar laraba ta tsareta da ido,sannan ta Fara yinkurin sauke Maryam ta shiga kiciniyar mik'ewa.D'an autan malam ne yace" wallahi baba Zuwaira ki gudu,in laraba ta kamaki alkur'an dukan tsiya zatai miki,Kuma babu me iya kwatarki daga baba har babarmu gara ki gudu kafin ta mike". "Ba inda zani,ita harta Isa tazo har gidan mijina tace zata dakeni wallahi da saina b'ara Mata Kai gida biyu "ta fad'a tana rarumo k'atuwar tabaryar da suke surfe da ita. Itako Laraba,Sam hargagin Zuwaira Bai tsoratata ba,Dan Haka ta mike ta nufeta yayin da Zuwaira ta tattale ta d'aga tabaryar tana fad'in" kina k'arasowa Ina sauke Miki ita".Ganin da gasken zuwan zatayi yasa malam daka musu tsawa duka,tare da umartar kowacce ta dawo ta zauna.Cike da salo laraba ta juyo ta Fara bada wani taku Wanda take ganin zai jawo hankalin malam ji kake taffff,taffff,taffff.Malam baisan lokacin da yayi baya ba ya dafe bango Yana Kiran astagafirullah,saboda ganin manyan Kaya,yayinda ya dinga kallon matansa kamar wasu 'yan daudu,Dan gani yayi kamar halittun matan k'auyen aka hadowa laraba duka gaba da baya. Malam labaran ne ya shiga fad'in" subahanallahi,malam yi a hankali kada ka Fadi,yakarasa maganar Yana me kallon bayan laraba,a zuciyarsa Yana ayyana sai an Dora bokin ruwa ko kwarya ta zauna das a bayan laraba saboda tudun mazaune,"Masha Allah" ya furta a fili. Shikuwa malam nuhu Yama kasa motsi,illa ido Daya zubawa kowa a gurin,sai daga baya ya k'arasa ga malam din shima Yana tambayar lfy?,Yara kuwa duk suna Nan sun Sami t.v suna kallo.Ganin da salame tayi Zuwaira nata sababi shiyassa itama ta shiga nata sababin suka hadu gaba Daya. Da dai akaga za'a Bata lokaci Nan malam yace kowacce tasami guri ta zauna zaiyi magana.Dan tsabar biyayya irinna laraba dukawa tayi,ai abinka da ba'a sababa take Taji kamar ta tsugunna Kan k'aya,Dan yadda kafafunta sukayi mata,batasan lokacin data sulale ba tana haki. Bayan kowa ya nutsu dan har abokan malam suna Nan sannan yayi gyaran murya kafin yakai duba sa ga Maryam yace ta zo,.Kowa yayi tunanin bazata iya zuwa ba,amma kawai sai gani akayi taje gabansa ta tsugunna. Kallo yaci gaba da binta dashi kafin yace"Maryam" "Iyi" ta amsa "Hmmmm" yace ya girgiza Kai yace "kina kaunar Allah da annabinsa?" "Kaiiii sosai ma,Allah yasa Annabi ya ceceni" ta furta tana washe baki. "Ai kuwa bazaki taba samun ceton ma'aiki ba muddin baki Fadi gaskiyar abinda yake faruwa ba,Dan koma menene,to kece silar komai bakar munafuka" Hade fuska tayi jin ya kirata da munafuka,aikuwa saita kalli gefe tana gunguni. Nunata yayi da yatsa Yana fadin"wannan, wannan da gani uwarki tana zunduma ashar ta haifoki,Dan duk yaron da aka Haifa da Bismillah,bazaiyi abinda kikayi ba,Ni ba'ama taba kawomin makurar kangararru ba sai ke,Dan Haka ko ki fadamin gaskiya ko in tattara ki in maida ki gurin ubanki,tunda ba Dole sai a kanki Zan Sami lada ba". Jin yace zai maidata gida in Bata Fadi gaskiya ba,yasata Fadi a zuciyata"aikuwa wallahi bazan Fadi giskiya ba,tunda in ban fada ba za'a kaini gida,inje inci uban ummita Dan na rantse saina daketa".kawai sai gani sukayi ta mike ta rike k'ugu tace "yehhhh! Wani takalmi dake kusa da malam ya rarumo zai jefamata malam nuhu yayi saurin karbewa ya shiga bawa malam hakuri,ita Kuma akace ta zauna. Bayan ta zauna malam ya Kara had'e Rai yace" Zaki fad'a kowa yaji gaskiyar zance kokuwa?" Gyara Zama tayi, tai Zaman rak'uma sannan tace Zan fad'a yanzu kowa yaji,idan Kuma nayi karya a tambayi Anty laraba".Duka matan malam da harara suka bi laraba,sannan sukace "yauwa 'yar albarka yarinyar kirki Mai gadon fadan gaskiya,maza fad'i a gaban kowa yaji abin kunyar da malam yayi,Dan mun San bazaki yi Masa karya ba" K'ara muskutawa tayi sannan tace" dama um rannan ne da malam ya kirani yace Wai babana yace baida kudin dazai aikomin,amma shi ba matsala in Ina bukatar wani Abu in tambayeshi,sai nace Masa to Zan dinga tambayar ku in baya Nan,shine yace Wai ah'ah kada na tambayeku bazaku bani ba ko na tambayeku Dan son kudi Ne daku,shine na tashi Zan tafi yakirawo ni yace Wai idan nasan wata 'yar bazawara k'atuwa a garinmu inyi Masa kwatance zaije,Dan ya gaji da ganinku a bushe,shine fa nace Masa Ni duk wadanda na Sani a garinmu sirara ne,shine yace na tafi.To bayan kwana biyu sai ya kirani yace Ina zani nace Masa gun laraba inci danmalele,shine yace dama Yana nemana zai aikeni gurinta,Wai idan naje ince yace Yana sonta,shine na fada Mata daga Nan ta amince take kawo Masa abinci kullum ko Anty laraba?" Ta nuya akalar tambayar ga laraba,wadda sanyin Dadi yasa Banda murmushi ba abinda take zubawa,Wanda inba ka k'ura ido ba bazaka fahimci ma bakin nata bude yake ba,Wai Kuma har tana murmushi.Jin tambayar da Maryam tayi Mata danta k'ara burge malam,Dan gani takeyi duk ya shirya hakan ne cikin salon soyayya,Dan Haka ta lankwashe harshe da kashe murya tace"gaskiya ne,shiyasa ma nake sa masa onga a dukkan abincin da nake yimasa,danya cemin Yana son onga". Wannan karon kam malam ashar din gaske ya lailayo ya mike su malam nuhu suka rik'eshi Nan ko ya shiga fizge-fizge Yana son kwacewa,Dan shima ji yakeyi kamar ya kashe Maryam koya huta,Dan Haka ya shiga fadin"ku sakeni ala gafarta,ku barni in kakkarya yarinyar Nan inkira iyayenta Suzo su dauki gawar ta,Anya ma kuwa wannan yarinyar mutum ce,inko mutum ce da ganinta ba yarinya bace wallahi rikakkiyar wada ce kirar da can,Dan mu yaranmu na Nan Basu Isa su wassafa wadannan zantukan data fad'a ba".Yana kokarin Kara fizgewa sukaji hayaniyar mata duk kowa ya juya ga kallon bangaren da suka ji,suna jiran masu shigowa. Wata kyamu shasshiyar tsohuwace ta daddage ta rangada guda tana sannan tace"Alhamdillah yau nagodewa Allah Daya nunamin wannan ranar,jikata zata amarce,Dama nayi alkawari Ni zanyi Mata gara,Dan tunda laraba ta Fara girma nake tarin kayan gararta,Dan so nake duk mijin Daya aureta yasan ya auri 'yar gata,yanzu uwatata ta aikemin laraba tayi miji Kuma mijinma na gwadawa sa'a wato malam Shu'aibu Mai abin mamaki,Dan Haka muka tattaro duk kayanta gasu Nan mun kawo,inya so tayi zamanta har zuwa ranar da za'a daura aure,kaga kafin ranar ma tasaba da matan ka an k'ulla zumunci,in Kuma yanzu kake bukatar a daura mu ashirye muke" ta karasa tana Kara rangada uwar gud'a,wadda tasa duka matan malam hasala suka juya suka kalli malam,Sai dai me? Leme suka ga malam Dan tun maganar tsohuwa ta farko ya sulale ya Suma,nanko laraba ta tare kayanta,yanzu Haka ma kansa Yana cinyar ta tana yarfa hannu da matso kwalla......... 🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣 *Gareku team laraba* *Team Maryam* *Team matan malam* _A kafta_ *KU bani comment kuga posting,KU hanani kuga d'an Karen dankarewa* 😂 _mura nakeyi,irin Mai gigita mutum din Nan shiyasa na kasa katabus_ 😩 *Alakamin khady* ✍ 🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀 🌀🌀🌀 *_'YAR CASKALE_* ( _Sanadin bakin uwa_) *NÀ* *KHADIJA USMAN* ( _Real Tame Gari_ ) *بسم الله الرحمن الرحيم* ____________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ 3⃣1⃣-3⃣5⃣ _wallahi jiya da yau na Kuma Shan dariya,Naga alamar akwai masu halartar bikin malam da laraba_ 🤣🤣🤣 Masha Allah Ina yinku fans Dina fiye da yadda ma kuke yina😘 ************************* "Yau na shiga uku Ni salame,me Zan gani haka? Dama idan kaje zance akan katifar gargajiya ake d'oraka,wayyo ni Allah dauki Raina na huta da ganin wannan abin kunyar,ga 'ya'ya ga jikoki amma malam nashe-nashe akan cinyar mace Ku tayani gani jama'ar musulmi".ta karasa maganar tana d'ora hannu aka tare da razga sabon kuka.Itama zuwairar nata jidalin ta Fara da Kuka,Nan ko jama'a suka Sami abin kallo hatta 'yan kawo gara. Kukan laraba ne ya k'ara jawo hankalin kaka tace"mun shiga uku,daga maganar aure sai takaba,aikuwa Koda malam ya mutu laraba takaba tahau kanki Dan sai kinyi Masa kin Sami wannan ladan".Jin an ambaci malam zai mutu yasa laraba canyarewa da kuka,Wanda yayi sanadiyar farfadowar malam,Dan ji yayi kamar an busa Masa usur a kunne.Wata kyakykyawar mik'a yayi,danshi ya d'auka duk abinda ya faru mafarki ne,jin kansa a lallausan filo yasa ya dad'a bankarewa Yana addu'ar tashi daga bacci,tare da wage Baki Yana hamma yasa hannu ya rufe Baki Yana shirin mikewa idonsa ya sauka Kan Zuwaira dake huci.Ganin hakan ne yasa yafara karewa kowa kallo Dan tabbatar daba mafarki yakeba.k'okarin ja baya yakeyi yaji ya dunguri abu da sauri ya juya aikuwa sai ji yayi laraba tace, "Alhamdillah gishirin zuciyata Allah ya karbi addu'a ta Dana dinga yi cikin zuciyata,wallahi malam daka mutu yau Nima mutuwar zanyi" ta k'arasa maganar tana marmari da ido alamun kuka. Maryam dake gefe tayi caraf tace"in Allah ya yarda ma bazaku mutu ba saikun haifi Yara 'yan lukutaye inta taba musu kumatu ana Mana hoto a irin wayar babana".Wata irin fyaud'a malam yakaiwa Maryam Yana daga zaune,aikuwa ta goce ya maki kasa,a zuciye ya shiga fad'in"wallahi Maryam idan Kika shiga hannuna sainayi gunduwa-gunduwa dake" Tana dariyar shakiyanci tace"kaga ko sai ayi miyar biki Dani,ransa ne ya Kuma hasala ya k'ara yunkurawa Yana fad'in" wannan wadar yarinyar kisan gilla shi yafi dacewa dake a halin yanzu". "Haba masoyi"yaji laraba tace, kalmar data sashi makalewa jikin bango,itako tana matsowa tace"Ni bana son kayiwa Maryam komai,dan 'yar arziki ce,Ina sonta,in munyi aure ma gurina zata dawo da Zama ko darling?"ai Duka muatanen gurin kowa baisan sanda ya rungume Dan uwansa ba Jin kalmar da laraba ta Kira malam da ita.Shiko malam tsayuwar da tayi akansa ne Saiya ke ganin kamar giwa ce tayi Masa rumfa,Dan son ta kauce ya shiga furta"kwarai kuwa ai gurinki zata zauna" Jin dadin kalaman malam yasa laraba muskutawa ta zauna a gefen sa batasan da hannun malam a gurin ba,Dan inda ta yanka zata zauna ta dauka bazata kusanta kwarai dashi ba,ai kuwa ji kake kurusssss🤣hannun malam yayi k'ara yayin da malam ya kwalla wata siririyar k'ara,itako Laraba Fadi take,"oh Kunga na zauna akan Kara ban lura dashi ba",ta fada tana muskutawa gefe Dan Jaye Karan,aikuwa tayi ido biyu da hannun malam Wanda malam din ya zuwa yanzu kwallar azaba ce kawai ke shatata,su kuwa mutane tunda hannun malam yace b'asss kowa ya zaro ido yakuma rasa bakin magana. Cikin kidimewa laraba ta yunkura ta tashi danta matso gun malam sai ji tayi yace"kina k'arasowa Ina tsine Miki albarka" ya k'arasa maganar Yana yiwa malam nuhu alama dasu zo su d'aga Masa hannun sa.Cak laraba ta tsaya takasa motsi,yayin da Kaka tace" kul 'yar Nan,danki samu albarka muka kawoki gidan nan,Dan Haka duk abinda yace kada kiyi to ki bari,Dan bama fatan kiyi zawarci,Dan Haka zauna Nan idan Nan yake son ganinki" aikuwa sai laraba ta koma ta zauna,yayin da duk ahlin gidan malam dama makotan gidan na sauran bangarori suka shigo,Dan Jin gudar da kakar laraba tayi,yasa sukazo Dan ganin meke faruwa,nan suka iske wannan lamari Suma suka tsaya kallon t.v ,Dan haka kowa ya Kama k'unshe tashi dariyar,Dan hatta matan malam Saida suka Dara wannan karon,duk da takaicin dake cin zuciyarsu. Inda Allah ya taimaka Malam labaran ya iya ire-iren wadan Nan gyaran shiya duba hannun malam ya tabbatar karaya ce,Nan yace Bari yaje ya kawo kayan gyara.sam malam ma yarasa me zai yi, yau dayasan inda zaiga 'yan Boko Haram ,ba abinda zai hana Bai damka musu Maryam sunyi gaba da ita ba,inyaso yacewa ubanta ta gudu,Yana wannan tunanin ya juya ya kalli barayin da laraba take,yaga yadda ta kwabe fuska kamar taci sabulu,sai Wani kyafkyafta ido takeyi,Dan tunda taji Wai tajiwa malam d'inta ciwo duk hankalin ta ya tashi.dan Haka ta kwab'e fuska tana matsar kwalla. Koda akazo ana gyaran,Saida aka Kori yara,Dan malam sosai ya zage Yana ihu,Haka itama laraba kukan takeyi iya yinta,su kuwa matan malam Allah ya k'ara kawai sukeyi,itako Maryam tana daga gefe Banda dariya ba abinda take yiwa malam,inya d'an bud'e ido ya ganta,Saiya yunk'ura da niyyar maketa sai rik'eshi,da Haka har aka Gama gyaran,yayin da dangin laraba sukayi jugum-jugum Wanda hakan ke k'ara sa jinin malam hawa,amma Kuma idan yakai duba ga tarin buhunnan da aka shigo dasu,Saiya ji Kuma labari na neman sauyawa.Haka dai aka zauna shiru. Ganin la'asar tayi Kuma lokacin sallah yayi yasa masu yi suka yunk'ura da niyyar yi,amma matan malam duk suka tattare butocinsu da Kuma kayan ruwansu,suka ce babu Mai tab'a musu.Hakan yasa sauran matan gidan sukace Suzo bangaren su su yi ,amma Kaka tace ai sunfi k'arfin wulak'anci,yanzu zasu Nuna su ba matsiyata bane. A cikin wasu daga cikin wadanda suka rakota tace wata taje ta karbo musu butoci a gidansu Laraba,aikuwa ba'a wani jima ba sai jin tsayuwar mota sukayi a k'ofar gidan,Dan Haka cikin aka shiga kwada sallama Nan Kaka na Shirin yin magana saiga wadda ta tafi kawo butoci ta shiga fadin"a shema Kaka sauri mukayi Dan Ina zuwa na tarar da innar laraban ma ta dawo daga kasuwa wajen siyen kayan gado ana debo kayan tarkacen Kuma a cikin gida,zuwana ba jimawa suka kammala shine muka taho gaba d'aya,a Nuna Mana d'akin saboda maza zasu shigo da kayan katako..........." 🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣 *Team laraba gareku* *Wai Ina team malam ne,Ku fito a kafta*😂 *Alkalamin khady* ✍ 🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀 🌀🌀🌀 *_'YAR CASKALE_* ( _Sanadin bakin uwa_) *NÀ* *KHADIJA USMAN* ( _Real Tame Gari_ ) *بسم الله الرحمن الرحيم* ____________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ 3⃣6⃣-4⃣0⃣ _Idan laraba ke Saku dariya,ni comment d'inku ke Sani dariyar wallahi,gaskiya ba abinda zance muku fans sai godiya, Allah yak'ara k'auna, Duk masu comment wlh Ina gani Kuma Ina godiya kwarai,masumin addu'a ma duk nagode_😘 ************************* Dan tsabar mamaki ma shi malam daina Jin zugi da rad'ad'in ciwon hannunsa ya daina ji.Ita kuwa kakar laraba ta kafa ta tsare tana Nuna inda za'a ajiye kayan, dai-dai k'ofar dakin data zab'awa laraba.Kusan duk kayan tare da laraba aka dinga kiciniyar shigo da su dan zumud'i.Saida aka shigo da kayan kaf,kafin Kaka ta kalli d'ayan saurayin tace" yauwa laminu,Dan Allah in kun fita ka biya gindin gawo shagon haruna me siminti,kace Masa yazo Nan gidan malam ja'afar ana nemansa". Da "toh" ya amsa Mata yasa Kai ya fice,sannan tasa wasu yaran cikin wadanda suka kawo kayan Suma tace su d'ebo musu ruwa a rijiyar gidan.Haka ko akayi nana da Nan suka cika musu robar sabuwa fil, aka shiga alwala Nan suka shimfid'a k'atuwar tabarma a k'ofar d'akin da suka za'bar ma laraba.Duk kowa da kallo ya bisu,yayin da matam malam suka koma gefe suna gunguni,Dan suna tsoron suce wani abu laraba tabi takansu,Dan sun lura tun d'azu ita kad'ai sai had'a zufa takeyi,da alama jira takeyi ace kule ta casss. Duk inda suka waiga neman Maryam ba Wanda ya ganta ko yasan inda ta nufa. *********************** Itako Maryam daga Nan ba inda ta nufa sai gidan su laraba,dayake Babar laraba ta ganeta saita hau washe baki tana tambayar ta ko me akeyi a gidan? Aikuwa Maryam ta karkace duk ta zayyano Mata duk abinda matan malam sukayi harda cewa tai Wai sunce laraba kuncen yunwa ce,gashinan ya Nuna a jikinta Bata samun wadataccen abinci,yanzu Haka ma sunce you bazasu bawa malam tuwon dare ba. Aikuwa a fusace mahaifiyar laraba tasa aka Nemo Mata Yara,Nan tasasu suka shiga kamo Mata zakaru da kaji,Wanda kusan rabinsu duk na laraba ne da ake Bata,Kuma dayake kiwon ya karbeta sai sukaita yawa ba'a ci bakuma Wanda ya Isa ya taba Mata,wasu su mutu ana gani Amma baza'a yanka ba. Saida aka kusa kame Rabin kajin,tabawa yaran kudi tace sukai bakin kasuwa gurin Idi Mai gyaran kaji ya yanka ya gyaro. Yaran Basu wani jima ba suka dawo dauke da gyararrun kajin,Dan yanada Yaran da suke taimaka masa.maryam cewa tayi zataje ta dawo saita kaiwa malam d'in. ************************ Shikuwa malam bayan idar da sallar la'asar Dan wani zazzabi ne ya rufeshi Dan ciwon hannun nashi,ga takaicin abinda ke faruwa ga Kuma matansa da suka rufe idonsu sukaita zazzaga Masa rashin mutuncin da tunda sukayi aure Basu taba Masa ko kwatan kwacin sa ba,gashi yanzu Haka Wai bwasu kawu Nan laraba suna nan suna jiransa Wai maihaifiyar laraba ta aika musu akan shi malam din Yana son ganawa dasu,shi yasa abun ya hadu yayi Masa yawa. Malam nuhu dake gefensa ya kalleshi Yana nazarin malam d'in,da tun d'azu yaketa faman tunani yace" ala gafarta malam,Wai meye gaskiyar wannan maganar ne, Dan ni abin ya dauremin Kai,domin Naga kamar akwai alamun gaskiya a maganar yarinyar Nan,Dan Inka duba yarinya ce k'arama da batayi giraman da za'ace ta iya had'a irin wannan abun ba,Dan Haka ka fad'a Mana gaskiya musan abinyi mu sallami wadan can dangin turun tun kafin abin nasu ya motsa Dan kasan dai asali" "Wannan Haka yake" cewar malam labaran,gara ayi duk abinda ya kamata,dan banza bata kai zomo kasuwa" Jinjina Kai malam yayi wato ma kowa ya yarda kenan ko? Lallai baya raba d'ayan biyu yarinyar Nan Maryam tana da nasaba da jinsin arnan farko,wadanda Basu San ma da Allah ba,Basu tuna mutuwa bare su San da hisabi,Kuma duk yadda akayi daga k'aramar hukumar munafukai yarinyar Nan ta fito,dama ana cewa kano ta dabo tumbin giwa, Koda me kazo an fika,tabbas ya yadda,Dan gashi yau yaga yarinya ma k'arama ta fishi gulma da sharri da had'in husuma.Tabbas yanzu ya lura bashida wata mafita illa kawai ya amincewa auren laraba ,badan komai ba sai Dan shima ya rama karyashin datai,Dan shi ba mutunci ma wallahi a cinya zai karyata,ita kuwa maryam Kiran ubanta zaiyi yazo ya d'auki abarsa,Kai bama ita ba dukkan yaran dake gurinsa kowa yazo ya zo ya d'auki 'yarshi inya so ma yaran su koma fashi da makami ba abinda ya shafe shi,Dan an maida shi matattaran 'yan iska da yarinya ta Fara kangarewa sai a d'auko a kawo Masa,to shima ya kile yanzu ba wadda zai k'ara dauka,Maryam duk ta jamusu. Baiko bi takan su malam nuhu ba ya fita yana me cije baki,Dan ciwon da hannunsa yayi masa,a zuciyarsa kuwa,Yana kissima yadda zai Kama kashin laraba yai Masa karayar wulak'anci. A Haka ya fito ya samu kawun nan laraba su biyu.nana yace musu ai shi ya tura a kirawosu Dan Yana son a d'aura auren sa da laraba yau d'in nan.dukansu hamdala suka shigayi,daga bisani yace Yana zuwa.bai wani jimaba a d'akinaa na zaure ya fito da kud'i a hannunsa ya damkawa malam nuhu yace ya k'irga.Koda yagama k'irgawa yace" dubu ashirin ne cif" Gyada Kai malam yayi kafin yace" wannan sadakin laraba kenan Ina son kaimin walicci" Batare da gaddamar komai ba ko ya amsa da na'am. Nan suka dunguma zuwa masallaci,aka Kira liman da Dan sauran jama'a Nan take aka daura auren malam ja'afar da laraba,aka sadaki naira dubu ashairin lakadan ba ajalan ba. 🤣🤣🤣🤣🤣🤣 Tab zamusha biki alkur'an *Alkalamin khady* ✍ 🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀 🌀🌀🌀 *_'YAR CASKALE_* ( _Sanadin bakin uwa_) *NÀ* *KHADIJA USMAN* ( _Real Tame Gari_ ) *بسم الله الرحمن الرحيم* ____________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ 4⃣1⃣-4⃣5⃣ _fans Ni da ku,ba'asan Wanda dariyar zata jigata ba,ku Kuna dariyar laraba,Ni Ina dariyar comment d'inku,gaskiya ba abinda zace,kun bani nishadi dai-dai iyawarku Allah yabar k'auna ya k'ara zumunci amin_ ************************** Tuni labari ya iso cikin gidan an daura auren laraba da malam.Aikuwa Nan k'aramin bala'i ya tashi,domin kuwa su salame rashin mutunci kawai da ruwan bala'i sukeyi.Ita kuwa Kaka Koda haruna me siminti yazo,ce Masa tayi dama fenti suke so ayi musu,ba Bata lokaci ya fad'a Mata kudin,Babu ko neman ragi ta Lalo su a lalitar ta ta damka Masa da cewar yayi sauri fa.yana fita kuwa yaje shagon say Nuna kwarewa irin tasa da Kuma son janyowa kansa kasuwa,harda had'o me kala biyu Kuma na musamman da a ganinsa zai haskaka d'akin,wato yellow da Kuma dark blue😂,Haka ya tattaro yaransa suka d'unguma gidan malam aka hau haramar fente d'akin laraba batare da b'ata lokaci ba. Duk masifar da matan malam keyi ko a jikin laraba,domin farin ciki kawai ya cike Mata kowanne gurbi na jikinta,babu wata kusfa da bacin rai zai samu zarafin shiga,Dan Haka ko kallonsu batayi ba.Ganin Kuma anata fenti ya k'ara hasala su,Nan fa salame ta aika a kirawo yaranta idi da mamuda a can gidan biredi su zo su lakadawa su laraba dukan tsiya. ************************* A can gidansu Laraba kuwa,duk an aikawa yayyenta dake gidan aure,Jin kanwarsu ta auru duk suka dungumo zuwa gidan,batare da b'ata lokaci ba😳tab ashe laraba ba ita kadai bace hankatamar ba,sai dai duk ta fisu girma,Dan abun kamar bin bi akayi shi,wata tafi wata,to ita laraba sai nata yafi nakowa. Cikin matan kawunansu laraba wasu masu hankalin ciki suka zo da kyar da lallabawa suka tafi da laraba gida,akan anjima zasu zasu kawota kamar yadda al'ada ta tanada.Da kyar laraba ta bisu Saida Kaka ta lallaba ta tukun. Bawani mashahurin gyara sukai Mata ba,amma dai a kauye Kam ta gyaru. Shikuwa malam tunda aka d'aura aure aka nemeshi aka rasa,abinda Basu Sani ba kuwa malam wata hanya ya yanka ya Miki daji,Saida ya tabbatar yayi nisa da gari Kuma ba Mai ganinsa ya labe jikin wata bishiya kawai ya rushe da kuka.Sai da yayi me isarsa yaji har kanshi yafara ciwo tukun yayi shuru ya shiga tunanin hanyar dazai bi ya azabtar da Maryam kafin ubanta ya zo ya d'auke ta,haka kawai taja Masa,'yan kudaden Daya ajiye dan noman bana dazaiyi gashi tasa ya fito dasu,Shidai yasan aure sunna ne,shiyasa ma ya auri har Mata biyu,Kuma harga Allah su kadai sun isheshi,su kadai yaga zai iya ciyarwa da 'ya'yan da Allan ya bashi,amma gashi tsabar rashin mutunci irin na yarinyar Nan,tasa shi auren dole,in ba iskanci ba,ai da alama babanta Mata d'aya gareshi,meyasa Batace ya auri laraba ba sai shi,gashi dama yanada labarin bala'in cin abinci irin na gidansu Laraba da sukayi gado gun babansu,Wanda Koda ya tashi mutuwa sai a akori kura aka dauke shi ga tsayi ga kiba.shi yanzu babbar damuwarsa ba dama ya saki laraba,dan ana Masa kallon mutunci,Yana wa wasu wa'azi akan zamanta kewar aure aikuwa shi yanzu baya Bari asamu wata baraka daga gareshi ba. Tunawa yayi da uwar garar da aka kawo wa laraba,sai Kuma yaji kaso mafi yawa na damuwarsa ya ragu ,kawai bari zaiyi su kusa Gama cinye garar Saiya Fara gallaza Mata azaba da kafarta ma zata gudu.da tunanin wannan mafitar ya goge hawayensa ya nufo cikin garin,inda Yana zuwa ya iske jama'a cike suna jiransa danyi Masa Allah ya Sanya alkhairi, kasancewar sa babban mutum da kowa ke ganin kimarsa. ********************************* Kusan a gidan malam akayi shagali,Dan kusan Nan gidan dangin laraba suka tare,Wanda hakan yasa suka Dora babbar tukunya,aka shiga shagalin girki.hatta da awakin laraba haka aka kwanto su da kajinta,tace duk gidan malam ta nufa da abinta. Sai wajen karfe 9pm ma sannan aka samu zarafin Kai amarya,inda sai kaje kudaje haka jama'a suka dunguma gidan malam,yayin da idi da mamuda suke tsaye tsakar gidan suna jiran 'yan kawo amarya Suzo Dan su basu San fa laraba babansu ya auro ba. Famkam-famkam babbar yayar laraba ta shigo da sallamar ta, dai-dai idi na Shirin Kai duka,aikuwa caraf ta rike hannun Nasa,kamar ta samu gugguru ji kake rumus ta matseshi,Wanda yasa idi sakin ihun azaba.Zuwaira dake tsaye taga meke faruwa,da gaggawa ta shiga kad'a 'ya'yanta d'aki ta rufo har window duk da kuwa zafin da akeyi Bata bar musu ko kofar Shan iska ba.Ganin abinda ya faru ga idi yasa mamuda kallon salame yace,"Inna Wai dama zuri'ar gidan D'an lami k'ato baba ya d'auko?" Saida ta hadiye yawun takaici sannan tace"ai wadan Nan gara ma d'an lamin dasu,dubi fa yadda ta b'allamin hannun d'a kamar tasami karas,Dan Haka Kai dawo daga baya- baya tunda shi kaddara ta haushi ya had'u da mota k'irar bodi garin karambanin shi". Ganin yayar laraba tsaye tana huci yasa salame tahowa kamar marainiya tace"sannu Anty,ai Bai zaci Ku bane na dauka yaran da suketa lekowa ne Dan kartar kayan Amarya sunga sabon Abu,ashe kece cikin rashin Sani yakai Miki mazga" Ta fad'a tana karkarwa kamar wadda ruwa ya daka. "Itako yayar laraba cikin babbar muryarta tace"Ai na d'auka Hari ya kawo Mana dan anwa uwarsa kishiya zai kawo Mana wargi in Nuna Masa ko ni wacece". Cikin sauri salame tace" Haba shiya Isa,yaron da tun kafin zuwan wannan ranar shi kullum maganarsa d'aya umma laraba,har fad'i yakeyi yaushe wai za'a kawo musu ita Nan gidan shine fa nace Masa yau d'in nan,kin ganshi dayake ba girma saina jiki Wai yazo taryar Amarya,shine fa ya tsaya anan Yana korar yara ke Kuma kikayi Masa wannan cikin rashin Sani". "Hummm,ya kyauta" kawai tace,kafin ta sa Kai ta shige ta barsu anan,aikuwa kamar jira akeyi ta wuce Nan fa jama'ar kawo.amarya suka shigo duuuuu,wata cikin yayyen larabar itama batare data lura ba tabi takan idi dake kwance,garin zuwa gurinshi aka had'a da salame,Haka aka dinga bibbige su ana shigewa ciki,inda wasu ma takansu suke shigewa,tsabar azaba ma sun kasa ihun,yayin da mamuda tuni ya silala d'akin matarsa yayi luff. Cikin tsananin azaba salame ta tashi da kyar tana Kiran "idi tashi maza dokunan sun Gama wucewa".Da kyar ya bude idonshi ya kalleta kafin yace,"Inna har an Gama wasan sallar?"Kai dai tashi kawai Idi lallaba inkaika bangaren suwaiba ta gasama jikin ka". Haka suka rarrafa suka mike har zuwa bangaren matar idi itama Tasha dariya Jin sambatun da mijinta keyi. ********* A Haka aka jera kayan laraba,ko fentin Bai bushe ba,dakin kuwa yadau haramar warin fenti,Amma ko'a jikinta ,burinta a tafi a barta da malam d'inta,daga gefen dakinta kuwa aka kafa turken awakin ta kusan goma Sha biyu aka jeresu,kajima da akurkinsu aka taho,inda aka jera musu suma nasu gidajen har masu danyen goyo🤣. Maryam kuwa tana rike da fantekar kaji,taci taci har takai Mata Karo ,Dan Haka ta tafi dakinsu duk ta bawa 'yammatan da sukayi jugum-jugum suna ganin abinda ke faruwa.Kowacce Saida ta karba da aka Bata,sauran Maryam ta d'auka ta rike ta doshi dakin laraba dashi,inda laraba na hangota tajawo ta ta zauna kusa da ita,a takaice dai laraba ba wasu kawaye Maryam ce kawai,Dan auren kunsan na gaggawa ne.Kusan Zan iya cewa laraba ita ta Kori kusan mutanen da suka kawota,Haka dai kusan kowa ya watse aka barta da sauran yayyenta, fad'a suka yi mata akan ta rage wannan rawar Kan Kar malam ya rainata da sauran yaran gidan,Haka dai aka Gama Suma suka Kama gabansu,ko kallaon inda matan malam suke basuyi ba bare su Kai amarya kamar yadda akeyi bisa al'ada.An bar Amarya dai ita da Maryam inda suna fita tace Maryam ta Bata fantekar kajin Nan ta ajiyewa malam inya shigo saita bashi.Koda maryam ta Mika Mata fantekar kaji taga saura kad'an saiko ta shiga tambayar ta cikin masifa wayaci Naman da akayi Dan malam? ,Kai tsaye Maryam tace "ni ce",aikuwa a fusace Laraba ta yunkura tana fad'in,"kin San muhimmancin malam a gurina kuwa Zaki tab'a abinshi,to wallahi sai kin San kin ci Naman Nan" Murguda Baki maryam tayi sannan tace"Allah in Kika dakeni wallahi saina sa malam ya sakeki" Jagwab laraba ta koma ta zauna cikin marairai ce murya tace" waya ce Miki dukan ki zanyi,dama zaunar dake zanyi akan cinyata fa,amma tunda bakya so shikenan na Bari ,yi hakuri,inma Bata isheki ba cinye na bar Miki duka ma". Mika Mata k'aramar fantekar maryam tayi,sannan tace, "ah ah ungo ajiye Masa Ni na k'oshi tana kaiwa Nan ta juya tana fad'in " Anty laraba amaryar baba malam Saida safe" Wannan karon laraba Bata dakatar da ita ba,Dan dama so takeyi ta tafi ko malam d'inta ya shigo.amma harta gaji da jira ta bingire da bacci. ********** Shi kuwa malam yak'i zuwa dakin laraba ne Dan ciwon hannunsa,yafi son idan ya warke komai ma ayishi ta Kare,Dan wallahi Saiya karyata ya rantse,Hakan yasa har matansa ba Wanda yake shiga d'akin ta,duk yadau fushi dasu 🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀 🌀🌀🌀 *_'YAR CASKALE_* ( _Sanadin bakin uwa_) *NÀ* *KHADIJA USMAN* ( _Real Tame Gari_ ) *بسم الله الرحمن الرحيم* ____________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ 4⃣6⃣-5⃣0⃣ _Hak'ik'a ke d'in ta musamman ce,kamar yadda kike ta musamman a wajena, comment d'inki ya k'ayatar dani sosai nakuma ji Dad'i,tare da addu'ar Allah ya barmu tare.Wannan shafin sadaukarwa ne gareki Hafsat garkuwa besty na kiyi yadda kike so dashi kinji tawan_ 😘 ************************* Abu kamar Wasa,sai ga malam ya shafe tsawon kwanaki Bai ko lek'o cikin gidan ba,sai dai kawai ya aiko musu da abinda zasu d'an yi cefane,dayake ma kun San cefanen k'auye sauk'i gareshi.Dayake garar laraba duk kayan hatsi ne shiyasa ba wani kayan ta'bawa,hakan yasa dole matan gidan in sun dafa su bawa laraba nata,duk da salame dai na bayarwa ne kawai Dan gudun abinda zaije ya dawo.Itakam Zuwaira Dan tattalin lafiyarta ne,haka Kuma duk 'yan mata d'aliban malam suna zuwa gaisheta kullum,harda masu biyo Maryam a d'an tab'a hira,Dan Maryam kamar itace angon ma,laraba ba yadda batayi da ita akan ta zo su dinga kwana ba,amma tace bazata kwana ba,ita Maryam a cewarta indai ta kwana gado d'aya da laraba to kwananta ya k'are, Dan tasan juyi d'aya laraba zatayi sunanta ya Zama marigayiya Maryam.To a fannin 'ya'yan malam dai mamuda ma biyayya yakeyi shida matarsa da yaransa,hakama Idi,to itakam Zuwaira kadaran kadahan,dan harga Allah akwai tanadin datayiwa laraba,Dan saita zaneta ciki da bai d'inta,shiyasa bata nuna wani abu sosai.Itama salame hakan ne a ranta,dan haka haka tayi likimo itama. ******* Abu kamar Wasa,Saida malam ya shafe tsawon kwanaki bai ko leqo gidan ba,abin yayi matuk'ar damun laraba,inda tasami Maryam a tace taje tabawa malam hak'uri,aikuwa k'iri da muzu maryam sai tace bazata ba sai laraba tayi Mata d'anta malele,Haka zata zage tayi Mata ,inta fita saita dawo tace malam yace tayi hak'uri bak'i yayi ne,Haka kullum laraba ke siyawa malam kayan dad'i tace Maryam takai Masa,aikuwa Maryam tasamu abinda take so,tuni ta dinga cinye abubuwan tana zuwa ta tsarawa laraba kalamai, tace malam ne yace ta fad'a Mata,a haka har Saida 'yan guzirin kud'in da laraba tayo ya k'are,aikuwa ta aika Maryam gidan su.Da farko abar Laraba hanawa tayi,da Maryam ta dawo ta sanarwa laraba abinda Innarta tace,sai laraba tace taje tace Mata in bata bata ba zata dawo gidan wallahi tayi zamanta.Hakan da uwar taji jiki na b'ari ta dauko kud'i tabawa maryam tace takai Mata,gobe ma in sun k'are ta aiko,aikuwa Maryam tasami abin nema,kusan kullum saita je gidan su laraba tace a bata kud'i inji laraba ko ta dawo gida,ita Kuma uwar a 'yar ribar sana'ar da takeyi zata dauka ta bayar tana mita a zuciyarta.Maryam na fita zata tafi bakin kasuwa,itace cin ganda, ragadada, d'an bagalaje,cofe da acama,Kai duk dai kayan kwalama,gashi ta dinga wa laraba wayo tace ta dinga wa malam farfesun kaji kullum zai k'ara sont.Aikuwa ba b'ata lokaci laraba ta shiga kashin kajinta tana dirjewa malam Maryam na kwamushewa a cikinta. ******************************* *K'URUN KUS* Yau malam an warke sumul,Kuma yau tun safe Daya tashi yake k'ullawa da kwancewa ta hanyar dazai bi ya karya cinyar laraba,shin wane salo zaiyi Mata ya karyata a shammace,dan so yakeyi taji zafin daya zarce shi Wanda yasha.kasancewar baida lfy tsawon lokacin ba Wanda ya fita karatu,dama jira yakeyi Saiya warke rass ya rama karayar sa,sannan ya Kira uban kowacce ya zo ya d'auki 'yarshi.Ita Kuma Maryam Saiya tabbatar Daya Gama azabtar da ita ta yadda iyayenta ma said sun mance kamannin yadda suka haifeta,sai dai in sun dauko hotonta su tuna,sannan zaice Suzo su dauketa,ko yaje tasha yabada sakonta kawai a kaita gida.Kai Bari ma yakira su tun yanzu,dan a yau yake son ya kaddamar wa da Laraba ita Kuma Maryam gobe da safe,Dan Haka ya shiga lalaubar wayar d'ansa malam Garba,bayan ya d'aga ya sanar dashi ya sanar da mahaifin Maryam gobe Yana son ganinsa da gaggawa,Nan malam Garba ya amsa Masa da toh sannan suka gaisa,danshi baida labarin auren da mahaifin Nasa yayi. ***************************** Wanka sosai malam yasha,kafin ya baza turarensa irin nasu d'an d'uri mai kamshi.Kan Nan yasha aski ga Kuma gyaran fuska daya Sha,abin gwanin sha'awa.Dan ya kuntatawa matan nasa,bisa yadda suka ki yadda dashi a baya,suka dinga zuba Masa rashin mutunci,Dan Haka ya daura damarar ramawa shima. Kusan duk Wanda ke cikin gidan yau Kam ya San malam na cikin nishadi, inda ya tattara 'yan jikokinsa,ya raba musu alawa ya Kuma Basu sabulai yace su kaiwa iyayensu Mata,cikin Wanda ake kawo Masa yake ajiyewa. Sai da ya gama lekawa gaba Daya dakin matan nasa,Wanda dukansu Babu wadda yasami kyakykyawar tarba,in Banda ba'kak'en maganganu,shi dai murmushi kawai yayi ya fice Yana musu sallamar Saida safe. **** Tun shigowar malam Maryam tayi sauri taje ta sanar da laraba, kasancewar kowacce bandakinta a bayan d'akin ta yake, yasa laraba saurin tafiya tayi wanka,cikin sa'a kuwa harta Gama shiryawa ta bad'e jikinta da turarenta kala biyu,Habiba da balila ,aikuwa saita hau tashin kamshi ga kamshin da dakinta keyi irin na amare😜. Tunda ya doso dakin ya had'e ranshi,dan so yakeyi ya aro rashin tausayi da rashin imani ko iya na yaune kawai ya gwada su Kan Laraba.Ita kuwa Laraba tana zaune gefen gadonta,yayin da taci adonta cikin shaddarta aikin wuta kalar lemon green light,sannan Tasha bakin mayafinta,abinka da bakin mutum,saita fito tayi dass da ita wallahi, musamman da bakin Nan yasha jambaki kalar anti daba,ga Kuma jagirarata data Sha da jar jagira abin dai zasshawa,kwaliyyarta kirar zamani. K'asa-k'asa ta amsa Masa sallamar,kun dai gane, irin kunyar Nan ta amaren asali,shikuwa malam kallon gefen ido yakeyi Mata,Yana son ya gano ta fuskar dazai fi samun nasara wajen aiwatar da kudirinsa.Ganin yanayin zaman datayi yasashi murmushi a zuciyarsa,aikuwa ya tattaro duk karfinsa ya had'o tun daga kuruciya zuwa samartaka da tsufa, ya daddage ya tuma tsalle ji kake timmm! Ya tima a cinyar laraba,amma Kuma sai me,ji yayi tana fad'in"subahanallahi malam lafiya? Ince dai ba tuntunbe kayi ba".Ji yayi duk lakar jikinsa tayi sanyi, sakamakon duba da yakai ga hannun laraba yaganshi kwance bisa hannunta kamar ta dauke jariri,ashe lokacin Daya tuma d'in Nan a hannunta ya fad'a🤣. Wani zunzurutun takaici ne ya ziyarce shi,cike da jarumtar daukar fansa kuwa ya mik'e,ya k'ara buga uban tsalle wannan karon iya karfinsa,nan ma aka Kuma na d'azu sai ji yayi ta cafeshi tana yunkurin kwantar dashi gefen gado kamar wani danta takuma cewa"malam kwanta ka huta,Dan ba mamaki fa jirine ke d'ibarka,Kar kaje ka fadi kaji ciwo sannu kaji bari in kawo maka ruwa kasha"Dai-dai ta Gama kwantar dashi ta mike da kyar ta dauki kofin silba sabo fil ta nufi waje Dan kawo Masa ruwan. Tsabar takaicin rashin nasarar sa a Karo na biyu,Bai San lokacin Daya Kama fatar hannunsa ba ya gartsa wa kansa cizo,sannan ya saki ya matso kwallar takaici.Yana a Haka ya hango inuwarta tana shigowa,aikuwa sai ya yanke shawarar bin shawara ta uku,ya mike da sauri ya sakko,sai da ya tsaya Nan ma ya tattale kafafu kamar zaiyi dambe,sannan ya saita hanyar Yana jiran ta taho.Itako kanta tsaye ta nufo kofar Dan shigowa,bama ta lura da malam dake tsaye ba,ita dai kawai taga kamar wulgowar abu, kawai sai ta d'an kauce,aikuwa wata iriyar sufa malam yayi waishi a nufinshi ya sai ta Koda dantsen laraba ne ya karyata a kafada tunda yaga tana da makaran Kare Kai a cinya,shiyasa ya kawo wannan farmakin ita Kuma cikin rashin Sani ta kauce wannan sufar da yayi aikuwa ji kake kummm rakwacam,fuskar malam ta daki simintin tsakar dakin,yayin da jerin kwallayen da langunan da akayiwa laraba suka biyoshi suka danne........... 🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣 *Dariyata nafara yi tun yanzu,Dan nasan comment din dazan gani cikina Saiya kusa k'ulle wa Dan dariya.To masoyana Allah yabarmu tare* _sai kun Kara hakuri da yanayin typing din sai a slow wlh abubuwa sunyi yawa kudai ku Kara hak'uri_ *Alakamin khady* ✍ 🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀 🌀🌀🌀 *_'YAR CASKALE_* ( _Sanadin bakin uwa_) *NÀ* *KHADIJA USMAN* ( _Real Tame Gari_ ) *بسم الله الرحمن الرحيم* ____________________________________ *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ____________________________________ 5⃣1⃣-5⃣2⃣ _Ha'kik'a Naga zallar soyayya ga masoyana,nakuma gode da addu'ar ku, wadanda suka Sami zuwar min gaisuwa ma nagode muku sosai da sosai😘_ ************************* Ya ilahi! Laraba ta furta cikin siririyar muryarta da zata ja hankalin malam da ita.Da saurinta ta karaso tana me kokarin d'ago malam d'in,bayan ta kawar da tarin fantekun da suka rikito Masa,malam tsananin azaba da rad'ad'in dayake ji,sunma hanashi yinkurin yin komai.A haka Yana hi har laraba ta d'ago shi. Tozali tayi da bakin malam dake yoyon jini,gashi tashin farko bakin ya haye yayi suntum,hakan ba karamin daga hankalin laraba yayi ba.Cikin yanayin damuwa ta shiga fadin"na shiga uku malam tashi muje gurin sule me chemist Kar jininka ya k'are". Malam dayake jin garama ya mutu ya huta,Dan shikam wannan shekarar ya tabbatar a cikinta jarrabawar sa take, Yana Kuma da tabbacin guda uku ce,ta farko zuwan Maryam gidansa,na biyu auren laraba,na uku kuwa mutuwarsa ce,Dan Haka Yana jinta yai Mata banza ya kyaleta,illah kawai idan yaga zata tabashi Sai ya doke Mata hannu,hakan yasa ta fashe Masa da kuka. Ganin tana kuka ne yasashi cewa "Baki ma fara kuka ba tukun,Dan wallahi saina cika kudirina akanki".ganin bakin malam Yana rawa Kuma gashi Sam Bata fahimtar abinda take cewa yasata k'ara tsananta kukanta tace"nakuma shiga uku bayan wadda na shiga a baya,malam harshenka ya karye harka koma maganar gawa,wayyo Ni larabayye na mutu in malam ya mutu". Kallon ta yayi da sauri kafin jikinsa yafara mazari,kaddai laraba Mayya ce ta gano Masa mutuwar sa,shi Ina ma yataba Jin wani zance Wai na gawa,to kodai da gaske ne hasashen shi cewar mutuwa zaiyi,shiyasa har yafara warin gawa,shine Dan rashin hausa laraba tace Masa Wai zancen gawa.Da Gama wannan tunanin Nasa,Bai San lokacin Daya zabura ya makale laraba ba,wadda itama ta rik'e shi suka shiga rusa kuka,kukan da kowa da niyyar da tasa yake yinshi.Sun jima a Haka,inda laraba ta mike da kyar ta lalubo minsileta da tasa aka siyo Mata Dan tana shafawa a jikinta inda ke d'an Mata ciwo take shafawa saboda har yanzu gajiyar biki Bata Gama sakinta ba.Aikuwa jambaki tayiwa malam dashi,bayan tafi tudun leben ta shafeshi dashi,Wanda malam ya saduda yanzu badan Allah ba,Koda ya kalli laraba a kaikaice ya banka Mata harara kafin yace cikin zuciyarsa"Hummm ki gama wahalar ki yarinya,kwanton bauna zanyi Miki inta Miki kisan mimmike har saikin rame,duk wannan jikin naki wallahi saina maidashi kamar sillen kara" ya saki murmushi a zahiri,Wanda ya Kara kwab'e fuskar,laraba da karaf a idonta tace" sannu malam,kadaina Kuka haka,bari gobe da safe sai in dafa ruwa in gasa maka wurin sannu kaji mijina" Dammm! Kirjinsa ya buga,take yaji zuciyarsa tayi Masa d'aci,banda damuwa dayake ciki,daba abinda zai hana shi yiwa laraba d'an banzan Duka ya tattara ta a baro gobe yakaiwa iyayenta,amma yanzun ma Bari ya warke zai Rama ne. Laraba da kanta ta tallabi malam ta Dora Kan gado,sannan tajawo Masa bargo ta lullube abinta Dan taga Yana rawar sanyi.Shikuwa malam,sosai yaji dadin gadon, musamman da laushin katifa kirar zamani ta ratsashi,ga lallausan bargo da aka luntsume shi dashi,kawai sai yake Jin wani k'aramin nishadi,duk da kudirin dake ranshi na tarin daukar fansa.Laraba Bata Bari malam ya kwanta ba,Saida ta lalubo ciwo takwas ta bashi yasha, Bata San waya yadda shi ba ranar da aka kawota,da har zata jefa shi shara,sai Kuma ta bari dan gudun Kar a aiko cigiya,to gashi ma yayi Mata rana. Allah sarki baiwar Allah laraba,Sam kasa runtsawa tayi,tana kwance a katifar kasa,Amma ta zubawa malam Ido tana sharar kwallar tausayinsa.Duk abinda takeyi Yana kallonta sai Kuma yaji tabashi tausayi,Dan Haka ya rage yawan hukuncin da zaiyi mata,a Haka har bacci ya kwashe su. 🔅🔅🔅🔅🔅🔅🔅🔅🔅🔅 Tun asuba laraba tafarka danta d'ora ruwan zafi ta gasawa malam fuska kafin ya tafi masallaci.koda ta fito d'ibar ruwa,saita tarar gaba d'aya matan malam ba wadda randarta ke tsakar gidan,komai sun kwashe yau,hatta duwatsun girkin da sukeyi,bare Kuma azo maganar ice.Ashe dai Maryam tayi Mata dabara,da tace Mata jiya ta kawo a siyo Mata kananzir karta yadda ta dinga girki da ice,zatayi warin hayak'i,tunda ita 'yar gata ce,Kuma anyi Mata auren gata,to gara kawai ta nuna itama wata ce,kawai ta dinga girki a risho ta nunawa su baba salame ita wayayyiya ce.Shine ta bayar aka siyo Mata din ta zuba a rishon Dan dama da lagwani a jiki,Ashe zaiyi Mata amfanin kusa Dan a da ta dauka ba amfanin dazaiyi mata,duba da yadda taga tuwon gidan malam nada yawa,shiyasa,amma yanzu ta fuskanta ko a Dora ruwan zafi zai Mata àmfani. Randarta ta ruwa ta bude ta debi ruwan ta shige d'aki.Cikin kankanin lokaci ta Gama dafa ruwan,ta tashi malam da kanta ta zuba ruwan a wata roba me Fadi,aikuwa cikin hikima da tattali ta shiga gasa malam,Wanda yake jinsa kamar jariri,saboda Jin sabuwar tarairaiyar dayake Samu,aikuwa sai a zuciyarsa tuni ya yanke shawarar karawa laraba tsawon Zama a gidan bayan yagama morewa.Haka ta gama gasa Masa,Kuma Alhamdillah yaji Dadi sosai,aikuwa a gida ma yayi sallar asuba,Dan Bai samu fita ba, Dan har yanzu kansa na Masa ciwo.Dan Haka Yana idar da sallar ya koma ya dada luntsume wa cikin katifar sa mahadi ka lotsa😜 Tuni kuwa bacci yayi awon gaba dashi.Ita Kam laraba bata samu zarafin komawa ba,illa dauko kayan malam datayi Wanda jini ya bata,da kayanta da suka Baci lokacin data rungumeshi,ta zuba a bokiti,tana jiran gari ya ida wayewa a siyo Mata klin saita wanke su. 🔅🔅🔅🔅🔅🔅🔅🔅🔅 Su kuwa su salame,kusan sa iya cewa cikinsu babu wadda tayi baccin kirki,kowacce ta so ta leko ta ga meke faruwa a dakin laraba,amma Sanin gidan gida ne mutane,yasa ba wadda ta fito Dan Kar taje a ganta,amma Kuma kowacce window da kofarta a hangame suka kwana.Lokacin da sukaji rakwacam din Nan k'arar zubowar kwanuka,kowacce matsuwa tayi taga meke faruwa amma sai suka dinga jiyo nishin malam,hakan ya Kara daga hankalinsu,a takaice dai ba wadda ta runtsa Dan suna son suga Taya za'a kashe arna(d'orawa Kai wahala). Da farko sun dauka kwashe ruwan da sukayi da Kuma itace da murhu sunyi nasara.Itako laraba wani dan gidan Zuwaira da taga zai fita da bokiti karami zai siyo Koko,shi ta bawa ya siyo Mata klin din. Kusan a tare matan malam suka fito tsakar gidan,yayin da kowacce ta shiga sabgar gabanta, amma kuma hankalinsu naga ɓangaren ɗakin Laraba,dan ganin me zai wakana.Itako Laraba bata ko bi takansu ba,tana son zuwa ɗakin dasu Maryam ke kwana,amma Bata s dokar gidan ba,dan duk abin Laraba bata da ɗabi'ar shiga shirgin daba nata ba,amma kuma kai inka shiga nata,tofa nanne ake kuturun bala'i,dan danƙarar ka zatayi kamar uwar data haifeka. A gaban idonsu yaron yabata klin ɗin ta shiga wanke kayan da shaddar ta da ta malam.Sai da ta gama ta shanya duk suna kallonta kowacce idonta ya sauka aka dabbaren jinin daya kama zanin Laraba yaƙi fita,aikuwa nan da nan zuciyar kowacce tayi baƙiƙirin,tare da cin alwashin cima malam mutunci idan ya fito. Shikuwa malam bai sami zarafin farkawa ba saida rana ta take,ya miƙe da addu'a a bakinsa,yayin da yaga Laraba kwance tana bacci, ƙara miƙa yayi da hamma,dan wata kafirar yunwa yake ji,ga kuma fuskarsa da gefen bakinsa daya hau,dan ma Laraba ta gasa masa jiya,ya kuma ji daɗin gashin,dan tanayi ne cike da salo,ga kuma wani ƙamshi datake yi wallahi.Hararar ta ya shiga yi,a ƙasan zuciyar sa yace ba ƙamshi ba,saina gama zuƙe ƙamshin zan karairaya ki in ƙara dake gaba,ko ba komai ai na ɗan more.Haka yasa kai ya fito waje,ya nufi ɗakunan matan nasa.a zaune ya samesu,duk da suna zamani irin na kishi,amma hakan bai hana yau wani zumunci ƙulluwa a tsakaninsu ba. Koda yayi musu sallama ba wadda ta amsa masa dan sun hango shi amma basu kalli fuskarsa ba.Jin sunyi shuru yasa shi magana cikin faɗa"wai bakwa ji ne ina muku sallama kunyi banza dani?" Batare da sun ɗago ɗinba salame tace"kabari ka haɗiye naman daka ƙunso a bakin naka tukun ,inka kammala cinyewa sai mu sami zarafin tanka maka. Ran malam ya ɓaci dan duk abin matan nasa,bai taɓa fuskantar irin haka dasu ba,ko rikicin su sukeyi in yayi musu tsawa suna shiga taitayin su,amma ya fuskanci yanzu raini ya shiga tsakaninsu,dan haka cikin kakkausar murya ya shiga yi musu faɗa.Babu wadda ta tamka masa a cikin su,dan sunga ɓacin ran da basu taɓa gani ba.jin yana faɗan amma a cunkushe ,yasa Zuwaira ɗagowa da nufin bashi haƙuri,aikuwa tayi katari da fuskar malam. 😳zaro ido tayi,sannan ta kalleshi cikin sauri tace" Ala gafatta me ya sameka a fuska haka?" Salame da maganar Zuwaira tasa ta kallon malam ɗin itama,aikuwa saita sheƙe da dariya ta shiga tafa hannuwa tare da rangaɗa ƙaramar guɗa "lallai wani kaya sai amale,wannan shi ake kira tafashi kaɗa miyar farin shigar girki,Ni da mandali,lallai yau malam kasan kayo aure, ashe mu duk sauƙi muka biɗar ma yau kayi babban kamu,ah lallai na yadda namiji baya tsufa da son duniya da yin ƙara'i,amma inba haka ba ina sauro ina Giwa,Ni wallahi na ɗauka ma yadda wajen yake haka cikin ma,ashe hangen dala bashi ne shiga birni,su ƙuda an tafi kwaɗayi gashi nan ana shirin gamuwa da ajali" ta ƙarasa zancen tana dariyar shakiyanci. Cikin rashin fahimta Zuwaira ta kalli salame tace"wai ni yaya me kike nufi da Waɗan nan maganganun naki ne?" Dariya salame ta kuma sawa kafin tace"haba zuwai sai kace ƙaramar yarinya,ki kalli Ala gafatta da kyau zakiga hannun mata ya shiga aka sashi a kwana,ki dubi can,tayi mata nuni da kan igiyar da Laraba ta shanya kayan ta,ai da gani kin san kwanan zancen,dan haka malam Barka da arziki dan an samu abinda ake nema,sannan kuma Barka da tsira da rayuwa...." Bata ƙarasa ba malam yakai mata wani harbi da ƙafa ta kauce da gudu ta faɗa ɗakinta,itama Zuwaira hakan tayi,yayin da malam ya shiga masifa yana ball da komai na gabansa.Nan ma salame ta leƙo tana faɗin "ina ni ina tsayawa sabon ango mai ji da ƙarfi ya bugeni,ah ah bada ni ba,kai dai ka tsaya ayi maka inda bazaka iya ramawa ba,amma mu bazamu bari can a ɗime ka ba ,mu kuma kazo ka rama a kanmu" nan tajawo windon ta rufe ruff ganin malam ya nufota. Shikuwa malam yarasa meke damunsa kwanakin nan,"anya kuwa ba yarinyar nan ce Maryam ke da aljanna ba tabar kanta ta dawo kaina ba".tabbas da sake,dan haka dole yaje yayiwa kanshi ruƙiya yanzu. A hanyarsa ta shiga ɗakinsa na zauren ya haɗu da Maryam zata shigo"cikin daka tsawa yace"ke Dan ubanki daga ina kike?" Gyara tsaiwarta tayi sannan tace"Anty Laraba ce ta aikeni wai inyo cefane a dafa maka kaza?" "Au to to Haka ne, i maza kikai mata dan nasan tana can tana jiranki hanzarta" harta juya da ledar dake hannun ta sai.kuma tace"to baba malam ta yaya zaka ci naman? Naga kaji ciwo a bakin?" "Ke ban son shegantakar banza,idan an dafa kya ga yadda zanyi inci tunda ai ba bakin aka ciremun ba" "To idan tayi yaji fa?" Ta jefo masa tambaya."Ko uban yaji tayi ba abinda zai hanamin cin naman nan". "To idan.......,ke jakar ubanki nace,zaki wuce kikai kayan miyan ko kuwa saina zo,wallahi kadai wannan wannan yarinyar da magana a gurin nan,kima je ki haɗa kayan ki,dan nasa faɗawa ubanki yazo ya ɗaukeki,dan haka ki zama cikin shiri". Batare data ƙarasa saurarar abinda yake ƙarasa faɗi ba tayi cikin gidan da gudu.inda bata zame ko ina ba sai ɗakin Laraba,ta tarar tana shara nan ta samu guri ta zauna ta miƙawa laraba ledar dake hannunta tace inji malam yace a kawo mata.Cike da farin ciki Laraba ta kaɓar,ko da ta buɗe sai taga rogo,aikuwa tayi murna dan ta kwana biyu bata ci ba,nan ta baje tace Maryam tazo suci tace ta ƙoshi,itako ta cinye abin ta dan dama yunwa takeji.Sai da ta gama nan Maryam ta kalleta tace"Ina na baba malam ɗin?" "Me kenan?"cewar Laraba. "Rogon mana,ce Miki fa nayi ki raba biyu ki ajiye masa nasa". Cikin marairaice murya Laraba tace"wallahi banji ba,amma kije gida kicewa babarmu ta dafowa malam rogo" "Kam bala'i, cewar Maryam,ai wallahi ba ruwana dan kafin ma inje gidan ai yazo ya tambaye ki,kije kice masa nice ban faɗa Miki ba,ya dakeni Ni kuma inda ya sakeki,kawai ki tashi ki kamo wannan kazar taki budurwa a dafa masa,dan dama dazan shigo naji yana cewa wani abokin sa shi kaza yake son ci,mai romo da ɗan yaji-yaji.Yauwa wai ni Anty meye yasameshi a baki naga ya daddauje ya kuma kumbura?" "Wallahi faɗuwa yayi ina faɗa Miki, kwanukan Nan Kuma na jere suka faɗo masa,danma na shafe mishi da minsileta na gasa masa da ruwan ɗumi" Dariya Maryam ta shiga yi tuni muguntar Tata ta motsa,jin wai babanta zaizo ya tafi da ita,ai yaseen saita yi na karshe.Dan haka ta kalli Laraba tace"Ai Anty ba minsileta zaki shafa masa ba, Wannan baya warkar da ciwo da wuri,loko zaki kawo a siyo masa,sai ki shafa masa yanzu kafin kazar ta dahu Kinga ya ɗan ji dama saiya cinye kayar sa,amma yace irin ta rannan yake so wadda tayi masifar yajin nan" "Ke Maryam yaushe yace Miki haka,bayan kince abokin shi yake faɗawa". "To ai nima bance Ni ya faɗawa ba,ji nayi nima,dan haka tashi mu kamo kazar in tafi da ita bakin kasuwa a gyarota, sai in taho Miki da lokon daga can harda ma kayan miya.". Haka ko akayi suka kwamuso kaza,sannan ta bawa Maryam kuɗin gyaran dana loko dana kayan miya🤣 *Alƙalamin khady* ✍ 🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀 *'YAR CASKALE* ( _Sanadin bakin uwa_ ) *NA* *KHADIJA USMAN* ( _Real Tame gari_ ) *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* 5⃣3⃣-5⃣4⃣ _________________________________ *ALHAMDILLAH! Wannan shafin dukansa sadaukarwa ne ga Admin of admin wato yaya Hayat,ina farin cikin tayaka murnar ƙara shekara, Allah yaƙaro shekaru masu albarka,arziƙi da dukkan nasaran rayuwa,kasancewa cikin amincin Allah da tabbatar dukkan alkhairinsa* _HAPPY BIRTHDAY TO YOU YAYA HAYAT,ADMIN OF ADMINS_ 🎂 _____***************_____ A taƙaice dai,saida Maryam ta taya Laraba duk abinda Yakamata,idan tayi wani abun sai Maryam tace baiyi ba ta gyara,haka dai ta biye mata har suka gama dafawa malam kaza mai yaji da romo. Wanka kuti Laraba ta ɗauka,Maryam ta callara mata ɗaurin ɗan kwali,tace irinshi mamanta takeyi in tayi kwalliya,ta taɓa tambayar mamanta ya sunan ɗaurin,tace mata ɗaurin fati Muhammad.Haka dai tasa Laraba a kwana. Babu yadda Maryam batayi ba akan Laraba ta bata naman nan takai wa malam,amma Laraba tace ah ah,ita zata kai masa da kanta.Hakan yasa Maryam nuna jin haushinta amma sai taga wannan karon Laraba ko'a jikinta,hakan yasa ta tashi ta koma gefe tana ta tunanin yadda zata ɓullowa Laraba taci naman nan,dan Laraba wannan karon kai tabawa Maryam ita kuma taci ƙafafun ta ajiyewa malam kaza sukutum.Da farko Maryam bata damu ba da Laraba ta bata kai,dan tasan ita zata cinye kusan rabin kazar ko duka ma,sai kuma gashi Laraba ta gwanya mata. Haka taita saƙa wa lokacin Laraba ta shige ɗaki,dan haka ta ta tsaya jiran ta fito.Koda Laraba ta fito da hijabinta tana niyyar sawa nan Maryam ta tareta tana faɗin"ai karma ki wahalar da kanki Anty,yanzu malam ya aiko yace a faɗa miki gashi nan shigowa.Jin hakan yasa Laraba saurin ɗaukar langar ta ƙara gogewa ta faɗa ɗaki,tare da ɗauko turaren ta samfur ɗin wanda na faɗa muku a baya ta ƙara fesawa.Itako Maryam tashi tayi ta nufi ɗakin zauren na malam.sallama taitayi amma shuru ba'a amsa ba,kawai saita yanke shawarar leƙewa taga ko baya ciki ne.Tana yaye labulen ta hango malam lulluɓe da bargo yana hayaƙi,sallamar ta kumayi, nan ya yaye duk ya haɗa zufa da kyar ya amsa mata,"Baba malam meya same ka? Ko bakin naka kake gasawa ne da hayaƙi?" A kaikaice yake kallonta a zuciyarsa yana faɗin"kaji min shegiyar yarinya,ko ma meye ai ke nake yiwa,dan idanma aljanar kanki ce ta dawo kaina to na mayar miki abarki, kuje can ku ƙarata da iyayenki,dan gobe goben nan kina gidanku i War haka,ko ubanki bai zo ba Ni zan kaiki"amma saiya saki murmushi yace,"Eh bakina nake gasawa ko na ɗan ji dama". "To da zafi ne naga ka kwaɓe fuska zakayi kuka?"ta jefo masa tambaya. "Yaushe zanyi kuka kuma Maryam?" Ya faɗa yana ƙara faɗaɗa murmushin sa". "Gashi nan yanzu ma ka ƙara alamar kuka zakayi da yawa".Sai yanzu ya lura da abinda take nufi,wato murmushin dayakeyi shine kukan,nan da nan ya mayar da fuskar ya haɗe sannan yace" ke tashi ki bani guri dan gidanku,ba nace ma ki haɗa kayan ki ba,me kika tsaya yi kuma har yanzu. Gyara tsagunnon tayi tace"dama Anty Laraba ce ta aikeni nayo mata cefane,nakuma kai kaza aka yanko tayi maka farfesu,shine yanzu ma tace inzo in kiraka,ince maka komai ya kammala" Murmushin yakuma niyyar yi,tunawa da abinda Maryam zata kuma faɗi saiya haɗe kayansa yace"ina nan zuwa kinji jeki faɗa mata". Aikuwa da sauri Maryam ta koma ta faɗawa Laraba cewar ga malam ɗin nan shigowa fa,bayan ta sanar da ita wai ta ɗora ruwan ɗumi taƙara gasa masa bakin. Haka Laraba ta tashi da ɓarin jikin ta ɗora ruwan ɗumi,shikuwa malam bai samu shigowa ba dan yaga magariba tayi saida ya tsaya yayi sallar magariba da ishsha. Itako Maryam koda tabar ɗakin laraba ɓangaren matan malam ta tafi,babu wadda ta kula ta,dan sun san 'yar ɗakin Laraba ce yanzu.Ganin nan ɗin babu wani farin jini,yasa ta koma ɗakinsu gurin 'yan uwanta,nan suka shiga hira har magariba suma kowa ya tashi yayi sallah. Ko da malam ya shigo ya tarar da wannan Gara,ga ƙamshi nata tashi,saida ya lumshe ido,tare da haɗiyar miyagu,duk da bakinsa da ciwo,amma zaisa yanzu a ɗan ƙara gasa masa dan yaji daɗin cin abinda aka dafa masa,sai ma ya gama cin daɗinshi zaije yayiwa su salame rashin mutunci,danya lura yanzu sun raina shi wallahi.Cike da ladabi Laraba tayi masa sannu da zuwa,bayan ta idar da sallar ta,aikuwa ya amsa cike da jin daɗin siririyar Muryarta.Nan yasamu guri ya zauna a kan tabarmar da aka shimfida,babu ko jiran a gabatar masa da abinda ke kwanon yace" Ɗan taimakamin ki sake gasamin bakin nan kafin inci abin nan ko naji dama-dama". Cike da ladabi ta amsa da "Toh yallaɓai"(cikin salon da mamanta ta koya mata,da sunan da yayarta tace ta dinga faɗa masa dan jan hankali🤣)miƙewa tayi ta fice,yayinda malam ya bita da kallo yana kallon yanda kayan masarufi ke motsi😜. Haka dai harta dawo da ruwan ta ajiye ta ɗauko tsumma ta zauna gefensa,yayinda ta shiga ga sa masa a hankali tana masa sannu.Sai da ta gama ga sa masa sannan ta fito da lokon dake kan cinyar ta ta buɗe.Kallonta yayi yace"Amarya ba'a barin man nan kuwa sai nazo kwanciya a shafa,dan kinga abinci ai baya ciyuwa da maiƙo a baki ko". Mayarwa tayi ta rufe tana murmushi,yayinda ta buɗe masa murfin kwanon da ƙamshin daddawa ya bugi hancinsa,nan ko ya jawo kwano tare da jawo dankwaleliyar tsoka yasa a baki.Tsananin azabar da yaji yasa shi haɗiye naman tun bai gama tunawa ba.nan ma naman ya tsaya masa a wuya yasashi wata kwarewar data sa Laraba miƙewa da sauri ta bashi ruwa.Har naman ya wuce bai daina jin raɗaɗin a bakinsa ba,dan haka ya fuzge kofin ruwan ya kafa kai yana sha.Duk hankalin Laraba ya tashi,dan tsawon lokaci yana zaune ya jingina da bango Ya saki baki miyau nata dalala,nuni ya shiga yiwa Laraba da hannu akan ta kawar da kwanon kazar,aikuwa taja ta rufe.nan tayi tagumi dan bata da meke damun malam ɗin ba. Sun jima a haka, kafin malam yasamu raɗaɗin ya lafa,nan ya juya ya kalli Laraba cikin haɗe rai yace"Ke wannan wace irin dahuwa kikayimin,dake ƙoƙarin kasheni da raina kinji ɗan karen yajin dake ciki kuwa?". "Dama Maryam ce....." Zuruf suka ganta ta faɗo ɗakin tace"salamu alaikum gani Anty,an ragemun ne?" Baki buɗe Laraba ta kasa magana,shima malam haka,har Maryam ta fita da kwanon basu sani ba,saida malam yace"ke kika kira wannan tauraruwa me wutsiyar?" "Ni ban kirata ba wallahi ,inaga dama tana kusa ne,jin na ambaci sunan ta shine ta ɗauka ko kiranta nayi". Bai ce mata komai ba,sai zamewa da yayi ya kwanta,itama Laraba Batace komai ba,sai da suka ɗauki lokaci a haka kafin tace" yallaɓai katashi ka koma kan gado" laushin hannunta yasa shi lumshe ido dan haka ya miƙe da kyar. Ita ta kama shi dan a halin dayake ciki ko abinci baya sha'awar ci,dan haka suka ƙarasa ɗakin nan fa labari yafara canza salo,domin duk yadda yaso kawar da kai abu yaci tura,haka dai fa malam ya runtse ido ya kawar da batun ramuwa ya fara lulawa duniyar masoya da Laraba. 🔅🔅🔅🔅🔅🔅🔅🔅🔅 Gari ya waye duhu ya yaye,malam kam ya dangwali arziƙin Laraba,ya manta duk wata damuwa,jinsa yake yi kamar ba wanda yakaishi kasancewa cikin farin ciki,dan jinsa yake kamar bai taɓa kusantar irin wannan ba,dan haka tuni yayi watsi da batun ɗaukar fansa....... _Kuyi manage,wallahi yanzu ma daurewa nayi nayi muku zama ɗaya_ *Alƙalamin khady*✍ 🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀 *YAR CASKALE* ( _Sanadin bakin uwa_ ) *NA* *KHADIJA USMAN* ( _Real Tame gari_ ) *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* 5⃣5⃣-5⃣6⃣ " Kiyi maza ki shirya mana Huwaila,dan malam Garba yacemin yakamata muje da wuri,dan inaga malam ɗin baida lafiya ne,yake son aje a ɗauko ta tazo ta kwana biyu saita koma,saboda haka dan Allah kiyi sauri,shi Isma'il ɗin ya shirya ko?" "Gani nan malam hijabi kawai zansa, Isma'il yana ɗakin sa ai inaga ya shirya,dan tun ɗazu yayi wanka". "Yauwa to yi sauri dan Allah kin san jira ba daɗi". A hannu ta fito da hijabin tana faɗin"malam Allah dai yasa bawani abun matsayaciyar yarinyar tayi ba aka mana kiran gaggawa,amma ai kai kanka kasani babu yadda za'ai kwatsam ace azo a ɗauki yarinya sama ta ka,bayan kai da kanka ka faɗa cewa,malam ɗin yace sai anga nutsuwar yarinya tukun,sannan ake bada damar tazo gida ta kwana biyu,amma ban sani ba ko ciwon ajali ne yakama tsohon tunda kace ya tsufa". Ransa a ɓace yace"wai ke Huwaila yaushe zakiyi hankali ne?haka jiya ma inajinki kina cewa Isma'il maƙetaci la'ananne,shin ke wai har abada alkhairi baya fita a bakinki akan yaranki sai sharri,in sun lalace waye zai kaiki baƙin cikin hakan,shashasha, wadda bata san ciwon kanta ba" yaƙarasa maganar yana me ficewa a ɗakin. Taɓa baki tayi ta faɗa a hankali" kaji malam da wata magana,da kuma bana tsawatarwa ace na cika sakaci,to yaran yanzu kana tsawatar wa ma ya aka ƙare,bare ka zuba musu ido,to wallahi bada ni ba,inna kyalesu sakaka kuma a zagen" Tana kaiwa nan tasa kai ta fice a ɗakin,tana saka makulli a ƙofar ta shiga kwalawa Isma'il kira,jin yayi shuru ya tabbatar mata da ya fita wajen baban shi, kenan ita ake jira,dan haka ta ƙara sa kulle ko ina ta fice ta damesu a waje suna jiranta.Dayake tasan ran mai gidan a ɓace yake,saita buɗe baya ta shige abinta ita da Isma'il suka ɗauki hanya..... 🔅🔅🔅🔅🔅🔅🔅🔅🔅🔅 Tunda asuba malam inka lura dashi zaka tabbatar yana cikin farin ciki,haka yabi duk ya tashi jama'ar gidan nashi dan suyi sallah.Ko yau a masallaci malam ne yayi limanci, yayinda tsabar farin cikin dayake ciki yasa yau har karatu da wa'azi ya gabatarwa da mazan ƙauyen akan riƙon aure. Wajen ƙarfe takwas malam ya shigo gidansa,bayan yasa an sayo masa Lipton da Suger ,tare da ɗuma-ɗuman biredi ya shiga dasu gidan.Batare da damuwar komai ba ya ware iya na matansa kowacce,dan tunda akayi auren nan ya lura basa bawa Laraba abinci insun dafa(kunji fa malam sai yau yasan da hakan) Allah sarki 'yar marainiya bata ko damu ba,yanzu idan ya koma zaisa ta lissafa masa abinda ta kashe tsawon wannan kwanakin🤣 Duk wadda yabawa a cikinsu babu wadda tako kalleshi,shima bai damu ba,dan yasamu biskit ɗin zuciyarsa,dan haka ya shige ɗakin Laraba hankali kwance,baiwar Allah kun san dai yadda budurwa take duk girman ta in har Bata siyar da mutuncinta a waje ba,dayake zazzaɓi take ɗan ji,amma haka ta daure ta yi masa sannu da zuwa,ya miƙa mata Lipton da Suger ɗin,tare da lalubo sachet ɗin madara da bombita(oh su malam an iya almundahana ashe🤣)gashi maza tashi ki dafa mana shayi,sannan ki haɗa da waccan yarinyar mairamu,dan itama tare damu zata karya da ita,dan yarinyar na yaba da hankalin ta ba tun yanzu ba,bari ma in kirata mu ɗan taɓa hira kafin shayin ya dahu tunda naga a madafin zamani kike girki" ya ƙarasa zancen yana me fitowa ƙofar ɗakin,daga nan ya shiga kwalawa Maryam kira"Maryama! Kina ina mairamu?" Ya shiga tambaya yana daga bakin ƙofar Laraba. Daga cikin ɗakinsu ta amsa masa,ta fito sanye cikin kayanta masu kyau da hijabin ta.Sai da ta ƙara so gabansa ta ɗan tsugunna tace"Gani Baba malam" Washe baki yayi kafin yace"yauwa 'yar albarka taso dama neman ki nake yi shigo ciki kinji" ya faɗa yana me juyawa ya shige ita kuma Maryam ta miƙe tabi bayanshi. Zuwaira da salame dake can gefen ɗakunan su da yau ɗin nan suka tashi da sabon haɗin kai, kowacce saita ja dogon tsaki suka saki dariya a tare suka tafa. ************ Gefen tabarmar malam ya nuna mata ta zauna,aikuwa tasami guri ta zauna,tare da aro ladabin kunama tayi shiru.A haka har larabar malam ta kammala haɗa shayin aka kawowa kowa nasa,nan ko Maryam ta zage tasha abinta,dan saiya zame mata abin marmari,dan tunda tazo bata sha ba,danma ita ɗin hamburin hayam ce,ba ruwanta da zaɓar abinci, komai in zaiyi Mata maganin yunwa to tana maraba dashi. Bayan sunsha sun ƙoshi nan fa malam hira ta ɓarke,ya shiga bawa su Laraba labarin samartaka da irin gararin da yayi lokacin dayaje almajiranta,ita kam Laraba wani farin ciki take ji ,wai yau itace da miji suke hira.Yayin da ita kuma Maryam sam hankalinta na ga gida,danta matsu a zo a tafi da ita taje taci uwar ummita😡.Tana shirin tambayar malam shin yaushe su babanta zasu zo? Kawai sai taji ihun yara suna faɗin, ga yaya Garba! Ga yaya Garba na kano.Aikuwa a zabure ta miƙe tayi waje,yayin da sukayi ido huɗu da babanta suna gaisawa da wasu mutanen ƙofar gidan.A dai-dai nan ta ga Isma'il na ƙoƙarin fitowa daga motar.Da gudunta cike da murnar ta ta nufeshi,shima da sauri ya fito,a nan kuma taga ummanta itama ta fito aikuwa da gudu ta canza akala ta nufeta, tare da fashewa da matsanancin kuka,itama umman saida zuciyar ta tayi rauni,hawaye suka fara zubo mata na ganin 'yar Tata da tayi.Haka suka rungume juna,kafin malam Garba yayi musu jagora zuwa cikin gidan. Koda malam ya gansu ya nuna farin cikinsa,dan yanzu duk abinda ya shafi Maryam to yana daraja shi,dan shi Sam Yama manta shiyace Suzo su ɗauki 'yar su. 'Ɓangaren su salame ya musu jagora,yayin da suka shiga ɗakin salame,amma sam babu wadda tayi musu koda kallon arziƙi,hakan yasa jikin umma yin sanyi,ganin hakan da malam yayi ne yasa yakama yin yaƙe tare da cewa"Maryama idan sun gama gaisawar maza ki raka su ɗakin amarya kinji" yafaɗa yana me juyawa ya fice,dan su gana da mahaifin Maryam ɗin. Batare da ɓata lokaci ba kuwa Maryam tace"Umma tashi in kaiki ɗakin Anty Amarya dan ita tanada kirki,amma yanzu tsofaffin matan Baba malam sun koyo rashin mutunci". Jin furucin na Maryam yasa umma jin kunya,ta kalli salame dake duƙe tana leƙa ƙarƙashin gado,kome zata ɗauki oho,bata bi takansu ba har Maryam taja hannun Isma'il suka Umma ta bisu a baya,har zuwa ɗakin Laraba. A kwance take kan tabarma, dan zazzaɓi takeji,hakan yasa koda suka shiga da kyar ta iya ɗagowa ta amsa musu,dan ciwon da kanta keyi.Jinjina kai Umma tayi datayi arba da Laraba ,a zuciyarta tana jinjina girma da ƙudura irin ta Ubangiji,"Allah me halitta kenan" ta furta a zuciyarta,a fili ta shiga amsa gaisuwar da laraban keyi mata,bayan tayi musu nuni da gurin zama, Isma'il ma ya shiga gaisheta ta amsa mishi cikin sakin fuska kafin ta yunƙura da niyyar miƙewa."Wash Allah "ta furta a hankali,Da sauri Maryam tace," Menene Anty?" Cije baki tayi kafin ta furta" Bakomai" ta ƙarasa miƙewa da kyar ta je ta ɗebo musu ruwa.Nan ma da kyar ta zauna,duk umma na lura da motsin ta, amma saita kyale Ita kuwa Maryam sai hira take yiwa Isma'il tana tambayar shi ina 'yan layinsu,sannan ina su Rakiya? Nan take faɗa mishi ai ita tama fasa zuwa madinan nan,dan ta tambayi su Hafsa (waɗan da suke ɗaki daya)suka ce mata ai ba'a zuwa Madina ta ƙauye,nan suke faɗa mata duk wanda taga an kawo shi nan,to kangararre ne,dan haka wayo aka mata dan a kawota nan ɗin.Tunda taji haka tace itama saita nuna musu tanada wayo,badai ita za'a kai ba,to saita ce tafasa zuwa Madina a maida ta gida,kuma wallahi koya za'ai da ita bazata zauna ba. ************************ Tunda umma ta kalli Laraba ta fahimci inda matsalar take,dan koda take da ƙiba gamai hankali inya lura zaiga yadda tafiyar ta ta sauya.Ganin da umma tayi maryam taja hannun Isma'il sun fice wai zasuyi sirri,nan tasamu damar kallon Laraba tace"Ni kam amarya in tambayeki Mana?" "To Innar Maryam" cewar Laraba dake rawar sanyin zazzaɓi kaɗan-ƙadan. "Mene ne ya jawo miki zazzaɓi haka? Ko bakya kwana cikin gidan sauro ne?" "Ah ah,ai bama Musa sauro,kawai dai inaga dan....."sai kuma tayi shuru. Sosai Umma ta shiga nazarin ta,zuwa wani lokaci,sannan tace"kin gasa jikinki da ruwan zafi ne?"dan ta fahimci kamar abinda ya faru wannan ne na farko. Girgiza kai tayi a hankali tace"ah ah,dan ban san ma ana gasawa ba ai". Cike da tausayin ta,da kuma yaba tarbiyya irin ta yaran ƙauye tayi,domin dai duk da ana kiransu da kidahumai to Gara hakan,dan yanzu wata wayewar da buɗewar idon basuyi ba. Kallon ta tayi sama da ƙasa,taga yadda mazaunan nan suke,ta jinjina kai,to yanzu ya za'ayi a gasa wannan,dan ko bataga robar da zata ɗauke Laraba ba,amma dai bari tasa a samo ta wankan jego ko zata yi,dan haka tace " a ina za'a samu baho irin babban nan na wankan jego?" Kanta a ƙasa Laraba tace"ai inada shi,dan Innar mu ta siyomin tace wai mu fara tanadi ,robar tafi ɗa wuya". "Tohhhh ! Umma ta faɗa tana riƙe haɓa ,tare da mamakin abun,amma saita cewa Laraba ta ɗauko robar.Haka ta miƙe ta ɗauko robar ta kawota gaban umma,umma ta shiga gyaɗa kai a zuciyarta tana faɗin"lallai wannan uwa tasan 'yarta dan robar ma kamar ƙirar kamfani,dan kamar an auna larabar ne akayota fankaceciya.Miƙewa tayi tace" to ina madafin ku yake ?"a ɗora ruwan zafi". "Ai ni bana girki da ice Maryam ta hanani,sai da riho" Kallonta umma tayi tace au kema sunan mamanki Maryam kenan,lallai mama bata son 'yar nan tata tayi ƙaurin hayaƙi ko?" Murmushi Laraba ta sannan tace"Ah ah maryam fa 'yarki itace ta hanani girki da ice" "Wai kina nufin Maryam dai dana sani?" Gyada kai alamun ita. Dariyar takaici umman tayi,tabbas mai hali baya fasawa amma inba haka ba,yanzu Maryam yazatayi da wannan rushe shiyar idan ta tsokano ta,to a yadda take gani ko ita da Baban su Maryam ɗin ai sai sunci ƙaniyar su gurin ta,dayake ma da sauƙi dan taga akwai jituwa a tsakanin su,sai dai ta lura Laraba girman ne kawai ba wayo.Haka dai tasa Laraba ta kunna risho aka ɗora ruwan zafin. A banɗakin Laraba umma ta haɗa ruwan bayan takai robar,sannan ta ce Laraba ta tashi taje ta faɗa mata yadda zatayi cikin hikima. Umma na zaune kusan minti goma taga laraban ta shigo ɗakin kanta a duƙe.Umman ce ta kalleta tace "har kin gama gasa jikin naki?amma dai ba baki shiga ruwan nan da kyau ba,inba haka ba du-du-du mintinki nawa,dan haka maza ki ɗauko bokitin a ƙara zuba wani,in kin tsaya son jiki kece da wahala,dan kar kiga mijinki tsoho,su maza kullum jinsu suke kamar sabbin ƙyanƙyasa,dan haka maza miƙo a ƙara wani ruwan". "Dama ba ƙin shiga nayi ba ina zama ne sai robar ta fashe" "Ta fashe fa kikace?"umma ta faɗa tana zaro ido waje😳 *Alƙalamin khady* ✍ 🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀 *YAR CASKALE* ( _sanadin bakin uwa_ ) *NA* *KHADIJA USMAN* _Real Tame gari_ *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* 5⃣7⃣-5⃣8⃣ "Oh ni Huwaila,tunda roba ta fashe ya zamuyi? Gashi dai ba abin a samo daro ba ya ɗau zafi duk kibi ki ƙone,garin neman gira kuma a zo a rasa ido,ya muka iya,kawai ɗauko butar ki babba a zuba ruwan ki kama ruwa,gashin dama ai shine dai-dai tunda muna son ruwan ya shiga ciki ya gasa miki ciwon,to kodai ɗan ƙaramin tiyo zamu samu a zira a bakin botar sai kema kisa ko ruwan zai shiga? Kai nan ma ba dabara bace,kinga kawai kawo butar a zuba kar ruwan ya ƙone". Ita dai Laraba kanta a sunkuye Batace komai ba,har Sai da akace ta miƙo buta ta shiga ta ɗauko.Sai da umma ta haɗa mata ruwan ta sanar da ita yadda za tai sannan ta bata ta nufi ban dakin.Ita kam umma al'ajabi take tayi,a haka har larabar ta kuma dawowa ta haɗa mata wani ruwan ta ƙara watsawa😂. ********************** Suna nan zaune ba wata hira suke ba a tsakaninsu,sai ga malam ya aiko da Isma'il da kayan miya da ledar taliya, kasancewar yasan su salame sun koyo azzalumin rashin mutunci,yasan bazasu bawa uwar albarka koda ruwa ba.Duk yadda Laraba take ji,haka ta daure ta tashi ta ɗora musu taliyar,maman Maryam ta so ta bari amma tace zata iya.Koda ta kammala a kwano mai kyau nan ma aka zubawa malam,suma Baban Maryam nasu daban aka zuba musu shida malam Garba.Maryam kam ɓatan dabo tayi,sai da kowa yaci ya ƙoshi sannan ta dawo gidan.Isma'il ya gama cin abinci kenan,ya ɗago ya kalleta ganin ta faɗo ɗakin a guje ko sallama babu tana haki"Ke Maryam shi ne kika gudu kika barni kin san ban san gari ba ko?, Badan gidan nan bai da wuyar ganewa ba ai da na ɓata". Humm yaya Isma'il ai dan baka san ina naje bane shi yasa,da ko cewa nayi kazo muje bazaka ba,Anty Laraba ai kin san gidan su maraba da wari ko?" "Eh mana gidansu Iro mahaukaci". "Yauwa can,to dama rannan ne fa da na je ta wajen layin,kin san wai ɗaureshi ake yi,ni ban sani ba sai naga an ɗaureshi jikin bishiya, ina zuwa nace mishi sannu yaya,sai naji yace min yauwa,nace laifin me kayiwa me gari yasa aka ɗaureka?sai yace min babu komai,tsabar zalunci ne,shine nace masa idan na kwance ka nawa zaka bani? Shine yacemin biyar,Nikuwa na kwance shi,ina kwance shi kuwa ya riƙe Ni,yaita zabgamin igiyar nan,da kyar aka kwaceni,shine ban faɗa wa kowa ba nace saina rama,dana san yau zan tafi shine nace nasami bulalar malam ƙatuwar nan dayace yana dukan masu kunnen ƙashi da ita na ɓoye,yauma ina zuwa na tarar dashi a ɗaure, na kuma cewa in kwance ka? Yace "eh" na ce,idan na kwance ka nawa zaka bani? Yace ɗari,shi ne nace masa Ni kuma zan baka ɗari biyu kana so? Ya cemin "eh" shin Ni kuwa na fito da bulalata na shiga zabga masa,Allah yau ba kalar kukan da Iro baiyi ba,da farko ba wanda ya fito sai daga baya baban su kandala ya fito shi ne ya ganni ya biyo ni,wallahi da kyar na sha" ta ƙara sa maganar tana mayar da numfashin gudun datayi. "Na shiga uku na lalace! Dama har yanzu Maryam baki daina halin ba? Malam fa cewa yayi kin kintsu kin zama kamila mumina,ashe ƙarya ne,ai ni dama nasan da kamar wuya wannan matsayaciyar ace cikin ƙanƙanin lokaci wai ta nutsu,to wallahi yau sai dai abin ya ƙare akanki,mahaukacin da kika tsokano abin sai dai ya tsaya akan ke da kika jawo,ni kinga ma tafiyata, in an gama lallasa ki a kawomin ke nayi jinya,'yar iska kawai". Laraba dake tsaye jin abinda umma ke faɗi,dan haka ta tattaro jarabar ta ta da ta can tace"Ai wallahi indai ina nan ba wanda ya isa ya taɓa maryam,ba dai Iro bane kawai,to yazo ni zan lallasa shi,Ni na ma warke,Maryam jeki ki ƙara tsokano shi,yazo wallahi saina ci hancin babarsa". "Oh Ni Huwaila ! Nikam naga abinda yafi ƙarfina, ah kice malam mazahabar caskale ya kawo ki bawai ki shiryu ba,kidai ƙara tambaɗewa da lalacewa,dan haka tashi maza gara ma mu koma gidan nasan yadda zanyi ki daina wannan hatsabibancin,tunda gashi har da masu ƙirar katafila ke tare miki faɗa,ba dole abu yaci gaba ba tunda kunsa zalunci a harkar, kije ki tsokano ƙananan ɗiba,ita kuma ta markaɗe miki su,to kinga tashi maza musan nayi". Haka tá kama hannun Maryam tana faɗin taso 'yar jaraba ai banga ta zama ba tunda kika tsokano motsatstse". "To ai ban ɗauki jakata ba umma" "Ba buƙata ki barwa wasu almajiran ita,tunda baza'a rasa masu buƙata ba". "Dan Allah Innar Maryam ki barta karki tafi da ita kinga itace ƙawata,kuma ita ke bani shawara a komai,na rantse ki kyaleta duk wanda ta tsokano Ni zan tare mata". Numfashin takaici umma taja sannan tace,"kice Maryam ba koyon tarbiyya aka kawo ki ba kawai an kawoki koyon CASKALE,to wallahi bada ni ba,gara ki koma gabana duk abinda zakiyi kiyi shi da a gaban idona". Da matsiyacin gudu sukaga malam ya shigo,yayin da ya buga wani uban tsalle ya ketare kan Maryam ya afka ɗakin Laraba ji kake bamm ya banko ƙofar.Salame da Zuwaira na zaune kofar daku nan su su na aikowa su Laraba harara a fakaice dan suna jin duk abinda suke faɗa.laraba ta buɗe baki da niyyar tambayar malam sai ji tayi anyi ciki da ita amma bata faɗi ba sai dai ta motsa daga inda ta ke.Malam Garba ne da baban Maryam suma a guje yayin da duk suka ruɗe suka shiga laluben inda zasu ɓoye,daga can malam Garba ya shiga faɗin"yo ta nan Shu'aibu,biyo nan ɓangaren Inna salame".Suma su salame ganin mazan na gudu yasa suka shiga wurga ido dan ganin meke faruwa,aikuwa a guje malam Garba ya bangaje salame ,itama Zuwaira dake tsaye tana son ganin meke faruwa nan baban Maryam yayi gaba da haɓarta,wadda saida tayi wani juyi kafin ta kifa saman randar ruwanta nan kuma kowanne ya shige ɗaki ya banko batare da la'akarin ko wanne ɗakin suka shiga ba. Da nufin yin bala'i Zuwaira ta ɗago,amma sai me.Ido biyu tayi da Iro daya shigo a guje yana muzurai hannunsa riƙe da wata sharɓeɓiyar adda tsirararta,na ya shiga raba ido.Ganin hakan da sukayi duka hankalinsu ya tashi, kafin kace me salame duk da tsufanta ta kama katanga ta haura,Zuwaira dayake tanada ɗan jiki kaɗan ta miƙa mata hannu itama tana faɗin "yaya taimakamin nima na haye dan Allah kinji 'yar uwa". "Yau babu wannan zumuncin zuwai ,kowa yayi ta kansa ta ina na zama 'yar uwarki kedai nemi mafaka kinga nayi nan" Salame na kaiwa nan ta dira ta baya.Zuwaira na ganin hakan ta kama duru-duru,kawai saita nufi ƙaton rumbun gidan ta buɗe duk ƙaiƙayin dake cikin gero batayi tunani ba ta faɗa ciki. Idon Iro ne ya sauka akan maryam,aikuwa ya zaburo yayo kanta,ta fice a miliyan ya rufa mata baya.Jikin Laraba ne yakama rawa,nan umma ta kalleta tace"ke kuma ɓultuwa me kika tsaya jira,ba ke kika ce duk wanda ya taɓa Maryam zaki bashi kashin bala'i ba,to yau gata nan taje ta tsokano motsatstse sai ki je ki tare mata ai,dan wallahi Ni yanzu gida nayi ta taho daga baya tunda ita tajawa kanta,in Kuma kin kwatota ma tafi tare".Tana gama faɗar hakan ta nufi ɗakin da taga mijinta ya shiga..... *Pls managed* *Alƙalamin khady* ✍ 🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀 *'YAR CASKALE* ( _Sanadin bakin uwa_) *Na* *KHADIJA USMAN* (Real tame gari) 5⃣9⃣-6⃣0⃣ *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* Maigari ne zaune a gindin bishiya,tare da mutanensa ana gudanar da harkokin mulki irin nasu na masu sarauta.😂 A guje Maryam ta tunkaro su,da yake gurin a kan kwana ne ya sa ita ce a kan gaba,dan haka ita suka fara hangowa.Ita ɗin ma tsallen ta yi kamar yadda malam ya yi,ai kuwa sai ga ta ta tsallake maigari tare da tuge rawanin dake kansa. "Kaga irin marasa tarbiyya"cewar wani bafade da ya yi tozali da rantal ɗin kan maigari.Maigari da ya kumbura yana shirin zartar da hukunci akan wannan mai babban laifin,kawai sai idonsa ya hasko masa Iro ya nufo su da adda tsirarar ta,kafin ma ya ƙarasa magana tuni Iro ya iso inda suke,Hakan ya sa maigari faɗowa daga kujerarsa.Iro ko ta kansa bai bi ba ya tsaya raba ido yana son ganin inda Maryam ta yi. Ya jima tsaye yana zare idanu,su kuwa duk gurin jikinsu mazari yake yi.Cikin tsawa Iro ya ce "waye ubanta a nan?" Maigari duk da bai san wa ake nufi ba amma haka ya daure yace cikin rawar murya"ai ita ɗin shegiya ce" Zare ido Iro ya kuma yi,cikin wata tsawar yace" To waye baban babanta?" Wannan karon wani ne ya yi caraf ya ce "ai shima uban shege ne". "To shikenan tunda duk shegu ne,kai wannan" (ya nuna mai gari),kai ne babanta,kai kuma baban baban babanta".cewar Iro. " Mun ji mun amince mun karɓi wannan kyautar" duka suka haɗa baki. "To wa zan fara yiwa yankan rago a cikinku? Dan dama na ce tunda ta dakeni sai na yanka uwarta ko ubanta". Jin abin da ya ce ne ya sa su maigari ƙara tsurewa suka shiga roƙonsa a kan ya yi haƙuri.Ganin kamar suna daɗa tura shi ne ya sa maigari yin wata dabara domin ya zuwa yanzu ya fuskanci wadda ta tsokano Iro. "Kaga Iron Lantana ba dai kace harda uwarta ka ke nema ba?" "Eh ɗin"Iro ya faɗa yana zaro ido. "To maza shiga ciki,tana can ta goyata duk ka haɗa ka yanka su gaba ɗaya". Ai kuwa a guje Iro ya bi wata hanya ya shige wani gida.Su kuwa su maigari ba tare da ya sallami kowa ba suka hau kwasa a guje, shi ma bai damu ba ya tashi da sauri ya nufi bakin kasuwa ,a ransa yana me ayyana sai ya sa an nemo masa iyayen wannan yarinyar ya ci su ta ra. ************************* "Baban Isma'il buɗe ƙofar mana ni ce"cewar Umma dake tsaye tana bugun ƙofar ɗakin da ta ga mijinta ya shiga. "Ke dai in kin kuɓuta ki yi ta kanki ,amma ni ba zan fito ba wallahi" Ƙara bugawa ta yi ta ce "haba malam,yanzu dan abin kunya ɗakin tsohuwar mutane ka shige,to ni dai wallahi na yi nan,dan ga shi nan a saman rufin ɗakin da kake yana ɗaye kwano zai shigo".ji kake kararaf ana kiciniyar buɗe ƙofar duka ɗakunan,yayinda jin maganar da umma ta yi ya sa har malam Garba fitowa ba shiri. Dariya umma ta sa duk da halin da suke ciki ta ce" ba gashi yanzu kun fito ba,da ina ta magiya abu ya faskara,to ni dai malam na yi gaba sai kun taho dan wallahi ba zan zauna a ɗauki rayuwa ta a garin da ba nawa ba,dan haka ni nayi nan" Ta ƙarasa maganar tana nufar ɓangaren Laraba dan ta ɗauki jakarta. Turus suka yi dukansu, ganin Laraba tsaye tana ta rokon malam a kan ya buɗe ƙofar amma ya ce ba zai buɗe ba.Maryam da tun ɗazu tana maƙale a soro da sauri ta ƙaraso tana faɗin"Baba malam yi sauri ka fito gobara a ɗakinka na zaure" Ba shiri malam ya buɗe ƙofa har yana tuntuɓe dan sauri,saboda ajiyar sa da duk kadarar sa suna wannan ɗakin, su ma jin abin da Maryam ɗin ta ce ya sa suka rufawa malam baya.Zuwai dake cikin rumbu jin an ce wuta itama tayo tsalle ta fito🤣. ************************* Dukan su zaune suke an sanya Maryam a tsakiya sai raba idanu take.kowa huci yake yi musamman malam da ya zuwa yanzu duk wata martaba da Maryam ta samu a gurbin zuciyarsa ta goge,dan haka ya kalli su baban Maryam har da zabga musu harara a fakaice sannan ya ce" Da farko dai ba sai na ce komai ba game da wannan yarinyar, dan ku iyayenta kun fini sanin matsalarta sannan kuka yayibo ta kuka kawomin ni wato ga mai matattarar 'yan iska kangararru.Dan haka ina son kafin na yanke hukunci mai zafi a kanta inyi muku wata tambaya". Baban Maryam ne ya samu zarafin cewa " Allah gafarta malam ai mana afuwa dan Allah,dan wallahi zaman yarinyar nan a nan ya fi mana kwanciyar hankali,domin mu mun ga ci gaba a zaman nata". Malam ne ya ƙara muskuta zamansa sannan ya ce " tabbas kam an samu ci gaba da lalacewar ta ba,domin yarinyar nan tunda ta zo ban taɓa ganin ta yi wani abun arziƙi ba,kullum da kalar bala'in da za ta jawo". "To amma Abban Maryam ba kai kace min malam ɗin ya faɗa maka an samu ci gaba ba Maryam ta nutsu?" cewar maman Maryam. "Tabbas haka ya kirani ya faɗamin". "To inaga lokacin aljanuna maƙaryata sun hau kaina,dan haka nake wani zubin in suka zo yini nake bana cikin hayyacina,amma yanzu abu mafi sauƙi shi ne,ku tattara ta ku tafi da ita gida,nayi muku alƙawari daga nan zan dinga jifanta da addu'a, dan ita bata faɗuwa ƙasa banza,kuma ko ina akwai Allah". Maryam da daɗi ya kasheta ta ce" Baba malam Allah Ya yi maka albarka idan na tafi zan yi kewar ku wallahi,amma zan dinga mafarkin ku". Da sauri zuwai dake zaune ta kasa cewa komai tun ɗazu saboda aikin susa da take yi ta ce" Bama sai kinyi mafarkin mu ba, mu ma dinga yin naki". "Ai ba ma wanda zai dinga yin mafarkin wani a tsakaninmu,sai kace wasu mayu,kunga ku tashi kai Garba kar dare yayi muku a hanya" cewar malam. Laraba dake zaune jikinta a sanyaye tace"to amma yallaɓai inta tafi ni kuma da wa zan dinga hira kuma wazai dinga bani shawara?" Dariya zuwai ta sa tana faɗin" abin dariya wai yaro ya tsinci haƙori,sai ki koma saida ɗanta malele ko zaki kuma samun wata sha-sha-shar irinki" "Ni kike cewa sha-sha-sha?" "Ke ɗin mana ,ko da wata ne bayan ke". Zuwaira ta faɗa cike da masifa A harzuƙe kuwa Laraba ta hunƙura,ba tare da tunani ko tsammani ba zuwai taji an fyaɗe ta da kasa ai kuwa ta hau ihu,domin zauneta kawai Laraba ta yi ta fara murzar ta". Malam dai ya san ƙarfi bazai kwaci zuwai ba,kawai sai ya kama roƙon Laraba amma ta ƙi ji.Ganin haka yasa Maryam matsowa ta ce" Allah Anty idan baki ɗaga ta ba zansa Baba malam ya sake ki".Da sauri suka ga Laraba ta zame daga kan zuwai. Kowa da kallo ya bita,yayin da malam a ƙufule yace"ka ga irin tsiyar tata ko? Matata ma ita ke iko da ita bani ba tunda ita ce ta haifeni za ta sa na sake ta,to tun kafin ma lokaci ya ƙure ku tashi ku tafi,ke kuma in ta tafi kada ki sake jin maganata kiga idan ban sake ki ɗin ba da gaske". Maryam kam bata ƙara bi takan kowa ba taje ta ɗauko jakarta tana faɗin"Baba zuwai sannu ki gasa jikinki sosai.Anty Laraba ni tafiya zanyi sai mun kuma zuwa,ina addu'a Allah yasa ki haifi 'yar kululluɓar yarinya me kama dake,itama ta dinga ɗirkar mutane". Ba irin haƙurin da baban Maryam bai bawa malam ba,amma ya ce bai san zance ba sai an tafi da maryam.Haka suka fito da ita da kayanta,yayinda mutan gidan dake nan duk suka rakosu bakin mota.Ɗalibai irin su maryam kuwa duk sunji ba daɗi da wannan tafiyar ta Maryam ,Laraba ko kuka ta kama yi amma ita Maryam ko a jikinta suka shige mota ita da Isma'il da mamanta,wadda take jin kamar ta kama Maryam ta yi ta ɗirka. ************************* Suna gab da fita gari suka ga tawagar mai gari buguzun -buguzun sun nufi hanyar gidan malam.Su dai basu juyo ba suka ɗauki hanyar Kano. Sun shigo Kano da yamma baban Maryam ya ce da malam Garba ya ɗan tsaya zai siye wani abu,aikuwa ba jima da fita ba sai ga shi ya dawo hannunsa riƙe da zabgegiyar dorina mai baki biyu.Ita kanta Umma ta yi mamaki amma ganin fuskar nan tashi a haɗe ta tabbatar ransa ɓace yake.Su ma kansu su Maryam da Isma'il sun tsorata da ganin wannan bulalar ,amma haka dai kowa ya haɗiye ƙin jinshi har suka isa gida,yayin da Baban Maryam ya shiga yiwa malam Garba godiya nan suka shiga gida. Ba ƙaramin farin ciki Maryam ta shiga ba ganinta a gida,ai kuwa da sauri ta shige ɗakinsu da umma ta buɗe yanzu.Sai da ta sha birgimar ta akan katifarta sannan ta tashi taje kiran da ummanta ke mata. Yau kam umma an nutsu,domin nasiha ta shiga yiwa Maryam da ta nutsu ta daina rashin ji, aikuwa Maryam ta zama kamar mumina,yayinda take ta Allah-Allah umma ta gama ta je ta kama ummita ta yi mata dukan da ta yi alƙawarin za ta yi mata. ******** Sam ba ta samu sami hanyar fita ba sai bayan magariba da babanta ya fita Masallaci daga can zai wuce gurin sana'arshi,sai mamanta kuma ta shiga sallar magariba. Ko da ta shiga ɗakin umma ta iske ba ta ciki ashe tana kicin,aikuwa idonta ya sauka kan bulalar da babanta ya siyo nan ta sureta ta fito a guje.Umma ba ta lura da ita ba sai Isma'il,shima hanya yake nema ya gudu dan kar ya je makarantar dare shiyasa bai tona asiri ba. ****** Direct gidansu ummita ta nufa.Cikin sa'a har ta shiga ba ta gamu da kowa ba.A tsugunne take da hijabi a jikinta tana ɗibar ruwa a randa tana zubawa a buta.Sai da ta daddage iya ƙarfinta ta shimfiɗa mata bulalar. Da sauri ta ɗago tare da furta "wayyo Allahna! dan azabar saukar bulalar da ta ji,ta waigo dan ganin waye ya yi mata wannan aika-aikar. Aikuwa suka yi ido huɗu da maryam,ita ma Maryam ɗin waro ido ta yi dan ganin wadda ta daka wato Rakiya.......🙄 *Alƙalamin khady*✍ 🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀 *'YAR CASKALE* ( _Sanadin bakin uwa_ ) *Na* *KHADIJA USMAN* 6⃣1⃣-6⃣2⃣ *__________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_Dumin shiga shafin,mu na Bakandamiya dana shudin rubutun nan na kasa_* https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* Ganin Maryam tsaye yasa Rakiya faɗin"kam bala'i,yau ga naman danake jira ya kawo kanshi har gida,na rantse da Allah yau bamai kwatar ki a gidan nan wato annoba ta dawo ko? " Hahaha! Rakiya ta saki dariyar mugunta,bayan ta shafo inda Maryam ta zarkwaɗa mata bulalar taji kamar ma gurin ya ɗaye. Itako Maryam ba ƙaramin tsorata tayi ba,dan harga Allah ko da ta saba da duka da kuma tsokana, to abin nata bai kai ta daki manya ba,dan haka cikin karayar murya tace" dan Allah Baba Rakiya kiyi haƙuri, wallahi ba ke nayi niyyar duka ba,ummita nayi niyyar zanewa dan nayi alƙawarin dukan ta duk lokacin da muka haɗu,da naga hijabin jikinki na ɗauka itace,ban san cewa anko kukayi ba". "Ai kinga maryam,idan zaki dinga gwagwiyar dutse kina ɓantara kina ban haƙuri wallahi bazan haƙura ba.Marabin da a dakeni yarinya tun ina rigimar yaye,sai gashi yau da 'ya'yana zagada-zagada kin shaulamin tsumagiya,to wallahi yau kisa a ranki mai ƙwatarki ko cikin uwarsa ba'ayi ba bare asa ran haihuwarsa". Maryam na shirin magana baban ummita ya shigo yana gyaran murya"Assalamu alaikum.wai duk ina yaran suke ne aka bar gidan kaca-kaca,kullum ina faɗan wannan ƙazantar taku amma kunƙi ragewa bare insa ran zaku daina,ke Asiya ce nan ko ummita? Maza kawar da turmin can gefe dan Allah". "Ai malam ba Asiya bace ba ummita bace, yarinyar nan ce tamba ɗaɗɗiya wadda muke nema ruwa a jallo,itace ta shigo dan tsabar tsaurin ido wai zata zane ummita shine ni tahau lodata kamar ta sami 'yar ta". Haska fitilar hannunshi yayi da kyau,aikuwa yayi ido huɗu da maryam shima.Jikinsa har rawa yakeyi dan tuna abinda yarinyar tayi musu,wanda silar hakan har sai da suka kai ƙara gun me unguwa sannan suka sami salama ga tsokanar da mutane ke musu,dan ko sararin fita basu da shi.Dan haka batare daya ce ƙala ba ya nufi ƙofa dan ya rufe,nan yayi kaciɓis da duka yaran nashi zasu shigo kamar sun san abinda ke faruwa. Sai da suka gama shigewa kafin ya mayar da ƙofar ya rufe,domin dukansu basu san abinda ke faruwa ba.Shiyasa ganin babansu na rufe ƙofa sun ɗauka halin ne ya motsa,dan haka ba wanda yayi yunƙurin cewa wani abu dan sun san hali.Ganin Maryam da sukayi tsugunne gaban mahaifiyar su dan an kawo wuta haske ta ko ina yasa Asiya faɗin"wa nake gani kamar Maryam ɗin Huwaila?" Cikin sanyi ta furta "Ni ce Anty Asiya". "Bala'i,wato yau ni ɗin ce Anty? Lallai ma yarinya,har kinyi laushi tun baki karɓi hukunci ba, Inna ko kin fara azabtar da ita ne?" "A'a ni ban taɓata ba,dama ku nake jira kowa yazo ya fanshe haushin shi na tsawon lokaci,ku ɗaukar mana fansar abinda tayi mana". Jamilu babban ɗan gidan Rakiya yace"Ni dai abinda nake so in mata shine:A samomin manyan ƙusoshi da guduma zan buga su a jikinta shikenan". Caraf Raliya mai bi masa tace,Ni kuma bayan ka buga ƙusar zan bi in zazzaro su sai in buga mata allurai sannan nasami adda na sassare kan alluran tsinin kuma na jikinta". Asiya ce ta gyara tsayuwar ta itama tace" a'a Anty da yaya,ku bari saina feɗe fatar ta tukun tsokar ta bayyana in samu cokali nasa a wuta inbi naita ɗona mata a sassan jikinta". "Ummita ce tace bayan duk kunyi wannan ni kuma inta cizonta har sai ta suma ta farfaɗo". Rakiya ce tace yauwa 'ya'yan albarka,ni kuma bayan duk kun kammala waɗannan abubuwan,sai in samo buhun ƙanƙara a ɗebe rabin ƙarnƙarar sai a sata a tsaƙiya a loda mata ƙanƙarar a samanta shikenan". "Ni kuma zan ɗauketa na kai ta bayan gari na jefar a bola kunga mun fanshe haushinmu".cewar baban su ummita. Tunda suka fara ambato nau'ikan azabobin da zasuyi mata ta yankewa kanta shawarar mutuwa tun kafin su kashe ta,dan iya tsurewa ta tsure. Rakiya ce ta nufota tana faɗin" dan ubanki taso jamilu yafara nasa aikin amma sai me? Ga dai Maryam riƙe da bulala amma shuru kake ji bata ko motsi,a ɗan razane Rakiya ta kamo hannunta sai ta jishi a sake,dan haka cikin alamun tsoro ta juyo ta kalli sauran dake tsaye tace" malam ina ganin fa kamar yarinyar nan ta mutu fa". Zaro idanu duka sukayi kafin baban ummita yace"ta mutu kamar yaya ? Ya faɗa yana me ƙarasowa inda Maryam ɗin ke kwance.Hannunsa yasa saitin hancinta yaji babu alamun iskar numfashi dan haka a kiɗime yaja baya yana faɗin"shikenan Rakiya kun kashe 'yar mutane,dama ni tun shigowa ta na lura yarinyar bata numfashi ban dai faɗa bane sai yanzu dana tabbatar,dan haka kun jawa kanku masifa ni wallahi ba ruwana" ya faɗa yana me ja da baya. "Ah ah malam,wallahi sai dai ko in tsorata tayi zuciyarta ta buga lokaci ɗaya to amma ai bamu ji ƙarar fashewar komai ba,kuma ma ai lokacin daka shigo da ranta da lafiyarta malam kada ka jaza mana laifi mu kaɗai,kawai asan abin yi tunda imu-imune". "Ke Raliya maza kinga goyata kiga yadda za'ai". A firgice ko Raliya ta juya baya aka kima mata Maryam sannan Rakiya da sauri ta ɗauko zani aka tare kanta dake reto."maza sa hijabinki ku Kaita soron gidansu ku ajiyeta,dan gidan su babu yawan shige da fice maza kuje Allah ya rufa mana asiri". "Inna to ya za'ayi da azumin da akeyi idan an kashe mutum?" Cewar ummita. "Ke rabu da ni,ai rabawa za'ai kowa yayi nasa kuje dai ke Asiya ki raka Raliya". Ko nauyin Maryam Raliya bataji ba haka suka buɗe gidan suka fita, kasancewar an shiga sallar isha'i yasa ba wasu mutane a wajen har suka ƙarasa ƙofar gidan su Maryam. Sai da suka tabbatar babu wanda ya lura dasu sannan suka shiga zauren,da sauri suka kamata suka sauke tare da kwantar da ita,wanda har yanzu bulalar na hannunta suka juya suka fice da sauri. Suna ficewa Maryam ta buɗe idonta dan tabbatar da ta kuɓuta,ganinta a zauren gidansu yasa ta miƙe ta shige gida.wannan karon ma bata sami umma a tsakar gida ba,dan haka ta shige ɗakinsu ta kwanta tayi luf tana tunano irin azabar dataji su Rakiya na faɗin zasuyi mata,lallai mutanen nan basu da imani,kenan da ta mutu da gaske haka zasuyi mata,aikuwa saita san yadda tayi ta koya musu hankali. Tana nan kwance taji umma na kwala mata kira,alamun tunda ta fita umma bata nemeta ba kenan,hakan yasa taji wani sanyin daɗi na ziyar tar ta. Haka ta tashi ta fita,umma tace tazo ta ɗauki abinci taci(kuskure na biyu damu iyaye mata kiyi,yakamata ace mahaifiyar Maryam ta nemeta tun ɗazu danta gabatar da Sallah kasancewar takai munzalin da in batayi ba za'a iya dukanta,amma kunji ta abinci ma takeyi).haka ta fito taci ta ƙoshi tana ta tuna abinda zatayiwa su Rakiya gobe.Isma'il ma bai shigo ba sai ƙarfe goma da yasan babansa ya kusa dawowa. ************************* Da asuba baban Maryam ya tashi ya fita Masallaci.Tun tashinshi shi da umma Maryam ta farka,aikuwa ta shige ɗakin ummanta ta tarar tana banɗaki dan haka ta kai dubanta kan sallayar da umma ta shimfiɗa taga ƙaton farin hijabin umma data ajiye dan gabatar da sallah.da sauri Maryam ta ɗauke ta koma ɗakinsu. Tasan gidan buɗe yake,dan haka tana ganin ummanta ta shiga ɗaki ta zura da gudu ta fice. Sai da taje ƙofar gidan su Rakiya tasa hijabin yayin da ta tura ƙofar amma saita jita a ɓame. Bubbugawa ta shiga yi iya ƙarfinta.Su Rakiya da sukayi kwanan zaune suka jiyo bugu kamar za'a ɓalle ƙofar.bisa dole jamilu yayi ƙarfin halin tafiya dan buɗewa yaga waye. Yana zuwa cikin rawar murya yace" wa..ye?" "Ni ce" yaji ance. Jin kamar Muryar mace kuma ba cikin damuwa ba yasa shi zare sakatar ya ɗan ziro kai sai yayi kaciɓis da farin abu zulum a ƙasa,sannu a hankali yake bin ƙasan da kallo har zuwa sama,nan yayi ido biyu da fuskar Maryam data bursune da farar hoda. Wata ƙara ya kwalla ya nufi cikin gidan da gudu yana kiran fatalwa....... *Alƙalamin khady* ✍ An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels