An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚 LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA*🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀ *NA* _BINTA UMAR ABBALE_ ~*®BINTU BATULA👄*~ *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` _*LOODING:*_ _*{LADIDI K'WADAG'A🌚}*_ _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM_ _*NA FARA DA SUNAN ALLAH ME RAHAMA ME JIN K'AI ALLAH KAYI DAD'IN TSIRA GA ANNABI MUHAMMADU (SLW) DA ALIHIN SA DA SAHABBAN SA BAKI D'AYA*_ _*TSOKACI*_ _*WANNAN LITTAFIN K'IRK'IRAR RE NE DAGA NI MARUBUCIYAR BAN YI DAN WANI KO WATA BA, WANDA YAGA YAYI DAI-DAI DA RAYUWARSA TO A RASHIN SANI NE*_ *_KUNA INA DUBUN DUBAN MASOYA NA, A DUK IN DA KUKE INA MUTUK'AR ALFAHARI DAKU WALLAHI KUNA DA DA BABBAN MATSAYI A CIKIN ZUCIYA TA, HAKIKA BANA RAINA MASOYI DUK INDA YAKE INA MUTUK'AR K'AUNAR KU SOSAI DA SOSAI_* *_MACE MAI KARAMCI MACE MAI AMUNCI MACE ME MUTUNCI MACE MAI KIRKI MACE MAI DATTAKO MACE ME KYAWUN ZUCIYA MACE ME SON CIGABAN WANI MACE ME AIKI DA ILIMINTA_* _________________________ *_HAUWA S ZARIA MAMAN USUWAN_* _________________________ _*HAK'IKA WANDA BAI SANKI BA SHINE ZAI MIKI MUMMUNAR FAHIMTA, INA ROK'ON ALLAH YA SHIGA LAMURAN KI YA DAFA MIKI A DUKKANIN ABUNDA KIKA SA A GABA, UBANGIJI ALLÀH YA RAYA MIKI ZURI'AR KI*_ _*ALHERIN ALLAH YA ZO IN DA KIKE ZAINAB ABDULLAHI REAL SHAXXI KIN IYA KIN HUTA INA MIKI FATAN ALKAIRI A RAYUWAR KI PEGE D'IN FARKO NA SADAUKAR MIKI DASHI KIYI YADDA KIKE SO DASHI*_ _*ALLAH MAI MUTANE ALLAH D'AYA GARI BAM-BAM HAKA KURUM SAI UBANGIJI YA HAD'AKA DA MUTUM ME KARAMCI ME SONKA DA SON ABUNKA ALLAH NA GODE MAKA DA SAMUN KI K'AWATA TA KAINA INA MIK'O GAISUWA TA GARE KI*_ ________________ *FAUZIYYA MU'AWUYA* ________________ _ALLAH YA SHIRYA MIKI ZURIA YA BAKU ZAMAN LAFIYA DA MIJIN KI_ _*BAZAN TAB'A MANCE ALKAIRIN KI BA*_ _________________ *RAHAMA ALIYU* _________________ *WANNAN MA NAKI NE INA YINKI IYA WUYA ANA TARE*🤝🏻❤ *🅿1* *Misalin k'arfe biyar da rabi na yamma* Wasu yara na hango sun yanko da gudu suna ihu! tare da fad'in "Ladidiya me kwarkwata a tab'a kad'an ta sosai kai, a tab'a ta kad'an ta ce kwarkwata ta dame ta a tab'a ta kad'an ta ciro kwarkwata,ladidiya me kwarkwata yeeeee!!! Ladidiya me kwarkwata!!! Da k'arfi suke fad'a suna gudu sosai dukanin su da allo a hannunsu da alama daga makarantar allo suka taso. Can na hango wata yarinya " yar kimanin shekaru tara zuwa goma ta yanko da gudu, daga kwanar da suka futo,hannunta rik'e da allo take gudu tun k'arfin ta k'okari kawai take ta riske su ta samu na duka ta daka babu abunda ya dame ta. D'aya bayan d'aya suka dunga shigewa gida ba tare da ta kama ko d'aya ba, ya rage saura mutum biyu,, dukan su "yan hanyar sune,, gudu suke tana gudu, har ta riske su, rai a b'ace ta fuzgo hijab d'in d'aya daga cikin su, ta maka ta da k'asa,d'ayar kuwa ganin an kama " yar uwar ta ya sa ta k'ara k'aimi gurin gudu sai da tayi nisa sosai ta tsaya ta tsinci dutsina ta dunga jefo wa Ladidi su, ko a jikinta, tunda Allah ya sa ta kama guda ta taki sa'a, hawa tayi kan "yar mutane ta shak'o wuyanta tace" Dan ubanki wa kuke tsokana kuna gudu kuna cewa me kwarkwata,, Alawiyya ta fara k'ifk'ifta ido saboda tasan halin bak'ar muguntar Ladidiya sai kace me aljanu haka take da mugun k'arfi sosai take faffasa wa mutane baki,, cikin inda-inda tace"Wallahi bani nace su Shatu ne da Habiba suka fara tsokanar ki, don Allah kiyi hakuri" Ko a jikinta ta kai mata duka a baki tana cewa"Da dai ban ganki bane yarinya ni zaki rainawa hankali wallahi yau he na lahira ya fiki jin dad'i kin tab'owa kan ki bala'in....k'aik'ayi da taji kanta na damun ta dashi ne yasa ta daki kan da hannunta ta sosa sosai gami da dukan in da yake mata k'aik'ayi,, sai da ta tabbatar ta daina jin sosar ta dawo kan Alawiya ta kai mata mari a fuska, tace"Wallahi kika sake CE min me kwarkwata sai na ciro guda goma na sa miki a kanki" Alawiyya tace"Kiyi hakuri bazan k'ara ba"duka ta kai wa bakin tana fad'in ki k'ara mana sai na zubar miki da hak'ora shegiya mummuna kawai" Alawiyya tasa kuka ganin yadda jini yake zuba daga bakinta, ga hakurin ta guda na girgid'i kuma na gaba ne, hakuri kawai take bata. Sai da ta gama dukanta iya son ranta sannan ta d'aga ta, ta gyara d'aurin zanin ta Wanda ya d'angale sama har kusan cinyar ta ana hangowa ta d'auki allon ta ta k'ara gaba ta bar Alawiyya kwance a gurin,, Can ta hango gefan Hijab d'in Habiba ta b'uya a wani lungu da alama b'uya tayi ganin ta wowar LADIDI, sad'af-sad'af ta k'arasa gurin ta jawo hijab d'inta sai ga Habiba kwance a k'asa ihu ta kurma ta mik'e a sittin ta ranta ana kare Ladidi ta rufa mata baya. Tun daga nesa Lado me icce yace"Ga sababbiya nan fitanniya me k'arfin jinnu ta biyu maka "yar zata daka" Da Sauri Malam Harisu ya kalli inda Lado yake kallo aikuwa ya hango "yar sa Habiba na gudu Ladidi na bin ta a baya, mik'ewa yayi da sauri yana fad'in " Wallahi Ku bushiyar kuka ce a kan yarinyar nan bata Isa ta dukar min yarinya na na k'yaleta" Kai tsaye gurin babanta ta nufa tana baki! Tasan k'aryar Ladidiya ta k'are tunda ga ta ga Babanta bata Isa ta dake ta ba,, kafin Malam Harisu ya an kara kawai yaji an in gije shi guri guda saura kad'an ya fad'i LADIDI tayi kukan kura ta dura kan Habiba ta kwantar da iita k'asa gami da haye wa ruwan Cikin ta ta kama dukan kayanta. Cikin k'arfin Hali Lado me ice ya k'arasa gurin yana fad'in "Ke Ladidi me tayi miki kike k'okarin raunata ne, d'aga musu yarinya Dan ubanki in kin kashe ta Kakar ki me koko kika sa a bala'in" Hannun guda tasa ta daddaki inda yake mata k'ai k'ayi ta Sosa ta sosa yadda ya kamata. Ta cire hannun ta tana fad'in "Kai lado me ice babu ruwanka kuma kar ka k'ara zagin Ubana idan ba haka ba zaka fuskanci hukunci .........Lado ya zare ido yana kallon ta da jin abunda tace wai zai fuskanci hukunci Lallai Ladidi kunyar ta ragaggiya ce, yace"Au! Nima zaki zage ni ne mara kunyar banza da wofi" K'unk'uni Ladidiya ta fara yi tana fad'in "Wallahi ni ba mara kunya bace,shikkenan dan suna da gata sai su tsokane ni su gudu su masu iyaye nima ai ba daga sama na fad'o ba, Allah ne ya amshi ran iyaye na" Sam! Lado bai ji abunda take cewa ba,yasan dai bazai wuce zaginsa take ba, sai yaja bakin sa yayi shiru gudun ta zage can gurin sana'ar shi ya koma ya zauna,, yana kallo Malam Harisu ya nufi gurin yana zagin Ladidi aikuwa ta hau dukan "yar sa tana rama zagin akanta, fad'i take" Haka kawai ai uba bai fi uba tana dukan Habibu tana ambato sunan Harisu tana zagi babu abunda ya dame ta, ya k'araso gurin gami da Kai mata duka ta goce ya samu "yar sa,dariya ta kwashe da ita mik'e daga kan Habiba ta d'auki allon ta sai dariya take k'yalk'yalawa ta mayar dashi mahaukaci tace" Wai shi dole sai yayi irin dukan su Salman Khan da Ashe kumar mutanan hindiya hahahahaha, Habiba Baban Ku Ashe d'an hindiya ne"" Malam Harisu kamar ya d'ora hannu aka don bak'in ciki, yana kallon ta wuce bagaz!-bagazan! Tana tik'ar dariya. Lado yana gefe shima dariya kamar ta kashe shi fad'i yake"Kad'an daga iya shegen Ladidiya ta gidan Iya me koko kenan shiyasa na k'yaleta nayi zamana,, hahahaha" ya k'arashe maganar yana dariya A fusace Harisu yace"Ai wannan yarinyar dole ne ma inje in ja mata kunne gaban kakar tata me koko idan ba haka ba wallahi sai na kai k'arar ta gurin me gari" Ya k'arashe maganar yana d'ago Habiba dake kwance tana rik'e da bakinta inda leb'an ta na sama ya kumbura suntum! Lado yace"Ko kaje gurin me gari babu abunda za'ayi mata, kawai ka jawa "yar ka kunne ta daina shiga sabgar ta,, su daina tsokanar ta,Iya me koko tana da fada a gurin me gari wallahi babu wani hukunci da za'a d'auka kan Ladidiya" *COMMENT VOTE AND SHARE* [9/21, 8:18 PM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* *NA* _BINTA UMAR ABBALE_ ~*®BINTUBATULA👄*~ *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` _*LOODING:*_ _*{LADIDI K'WADAGA🌚}*_ _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ ______________________ ```We are here to educate motivate and entertain aur reades``` _______________________ _*DEDIGATED*_ *TO* _RAHAMA ALIYU_ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿2* Harisu yace"Dole ne fa naje na fad'awa Iya mai koko domin ta ja mata kunne kar watarana ta jiwa yarinya ta rauni, ta barni da siyan magani, ko ka manta ne ko wata uku ba ai ba, yarinyar ta karya "yar gidan Tanimu Harira,, yarinya sai kace k'ashi saboda da rama, sai mugun k'arfin tsiya malam, anya kuwa babu aljanu a tare da ita"? Ya k'arashe maganar yana goge gumi dake tsattsafo masa a goshi. Lado yace" Ka iya bakin ka dai in kaje gurin me koko kasan halin Masifar ta, domin kuwa ta tsani ace da Ladidi tana da jinnu" Harisu ya kama hannun "yar sa Habiba sukayi gaba, sai mita yake. Shiko Lado redio ya kunna abunsa yana sauraron dawowar shi yaji ya suka kwashe da me koko. Iya na tsaye da abun tata a hannun ta, tana gyarawa gefe guda kuma wata k'atuwar tukunya ce,cike da mark'ad'an gero da ruwa a gefe cikin wani duro,, tun d'azu take jiran dawowar Ladidi tazo ta taya ta zuba kullun gasara domin ta tace, saboda kokon gobe da safe, ko guntuwa bata da ita, gashi tun asubah ake mata layi na siyan koko. Gajiya tayi da jiran Ladidi ya sa ta mike tana mita taje ta fara gyara matacin tata,, kawai sai ga ta ta afko gidan babu ko sallama. Cikin mamaki ta kalle tace"Yau ba arzk'i kenan kin shigo babu ko sallama"? Zumb'ura baki tayi ta wuce bagazan-bagazan ta d'auki buta, ta duba taga babu ruwa a ciki wata tsohuwar rijiya ta nufa ta zura guga na gwangwani, ta jawo ta zuba a ciki ta jefar da gugan kan jar k'asar dake jik'e a bakin rijiyar ta shige ban d'aki abunta. Tunda Iya taga haka tasan da walakin goro a miya yau za'ayi kwanan masifa kenan in ba Allah ne ya rufa asiri ba, aikuwa tana tsaka da zan can zuci ne taji sallama daga can waje. Abun tatar ta rataye kan Igiya ta d'ora mayafi aka tana tafe tana amsa sallamar. Malam Harisu ta gani tsaye shi da "yar sa Habiba sai muzurai yake, Gyara fuska tayi ta sha kunu sosai tace" Amun wa'alaikassalamu da Harisu wannan sallamar fa kuma? Sai ka wacce taci bashi" "Ba dole in zabga Sallama iyi,, Ladidi tana nema ta rauna ta min yarinya dubi yadda ta fasa mata baki ya kumburi har leb'an kasa ya Tsage,shine Nazo na fada miki ki ja mata kunne wallahi ta kiyaye ni, kuma ta daina dukar mi " yata domin ni ba Tanimu bane ehe"! Wani kallo iya ta watsa masa tace"Kaji ka da wani zance Harisu, ni dai na san haka kawai Ladidi baza ta doki Habiba sai da dalili watak'ila tsokanar ta sukayi, ayyo! Shiyasa naga ta shigo gidan a fusace"! Harisu yace"Ai dama nasan baza ki yadda ba,, kullum idan an kawo miki k'arar ta sai kice tsokanar ta akayi to ni daina wallahi na fada miki ki ja mata kunne gudun abunda zai biyo baya " Mai Koko tace"To gatanan ga kanan Harisu, kun bi gun addabi marainiyar Allah ta'ala komai tayi a unguwa sai a hau zaginta da ai bata ta, nace Harisu ga Ladidiya nan ga kananan Ku zuba mugani tunda dai ka k'i ka tsaya balle in baka hak'uri" Katangar band'akin had'e take da ta soran gidan Duk abunda ake Ladidi naji ko gama kashin bata yi ba ta d'auraye jikinta ta futo jefar da butar tayi ta futa da sauri Tsayuwa tayi a tsakiyar su,, tana sosa kanta gami da duddukan sa,, da sauri Harisu ya matsa da baya domin baiyi tsammanin ta a gurin ba, tsidig! ya ganta, ita kan ta Mai koko ganin ta kawai tayi kamar an jefo ta,, Habiba ta rakub'e a bayan Baban ta tana zare ido.. Fashewa tayi da dariya, har yanzu hannunta na kanta tana sosawa tace"Harisu Dan Hindiya Hahahaha yanzu ma k'ara gwada naushi na ka gani ko zaka same ni,, Hahahaha ta cigaba da k'yalkyala dariya, ta kalli Mai koko dake b'oye dariyar ta tace"Kinga Iya wai Babansu Habibu ne d'azu ya kawo hannu zai naushe ni, sai na kauce da sauri ya naushi bakin "yar sa,, wai dole ga Ahe kumar wannan me k'arfin nan na hindiya" Iya ta sa dariya tana fad'in"Yo Ashe kaine ma ka fasawa d'iyar ta ka baki amma saboda neman magana ka kawo k'ara" Tsabar bak'in ciki bai bar Harisu yace Komai ba yaja hannun "yar sa suka wuce gida yana cizon ya tsa. Iya ta gimtse da dariyar da take tana kallon Ladidiya tace" Ina raba ki da kiwon kyalla kina kyalla ta haihu,, ki sani fa baki da wani gata a cikin wannan garin , ni da kike tunk'awo dani bani da k'arfi nema nake kullum duk a kanki, hakanan wannan k'aramin uban naki D'alha da yake fad'i tashi duk akan ya in gan ta miki rayuwa ne, kullum ina fada miki babu ruwan ki,, da yara unguwa ki daina dukan "yayan mutane kada watarana ki jawo mana masifar da baza mu iya ba, Yo in badan ma me gari yana daure miki gindi ba, ai da nasan mutanan garin nan sunyi k'uli-k'ulin kubura dake saboda yadda kika addabe su babu yara babu manya" Kartar kanta kawai take hannu bibbyu tace"Iya wallahi kin san halina bana barin bahi duk hegiyar da ta tsokane ni sai na zane ta,, da Alwayya da Habiba da Fainusa da Abule da Mariya ne, suke tsokana ta a makarantar allo sunayi min ihu bayan an tashi Wai me kwarkwata, to na kama biyu saura uku billahil lazi sai na zane su suma" Tsaki Iya taja tana fad'in "Kece ai ko ina sai ki ta sosa kai in ta kama ma ki d'auko ki kashe dan shashanci,, ni narasa wace irin kwarkwata ce wannan me mugun naci sai kace iska sam bata jin magani" "Tabd'ijam kin San yadda take cizo na kuwa iya wallahi in ina sosawa har dad'i nake ji" Ta k'arashe maganar tana dukan kanta gurin da yake mata k'yayk'ayi. Iya tace"Ni wuce muje ki d'auraye hannun ki k'azama ki tayani tatar kullu, ga magariba ta gabato" Ladidi ta tsani a kira ta da k'azama, haushin Iya ya kamata, tw zumb'aro baki gaba,, hanya futa daga gidan tana nufa Iya tace"Ina kuma zakije" "Ki samu wanda zai taya ki tatar tunda ni k'azama ce" Tayi fucewar ta. Mai koko tabi ta da kallo da baki a sake. *COMMENT VOTE AND SHARE* [9/22, 10:03 AM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* *NA* _BINTA UMAR ABBALE_ ~*®BINTUBATULA👄*~ *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` _*LOODING:*_ _*{LADIDI K'WADAGA🌚}*_ _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain reades``` _______________________ _*DEDIGATE*_ *TO* _RAHAMA ALIYU_ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ Da sauri ta biyo bayanta tana k'wala mata kira tayi mata banza,, ko juyo wa ba tayi ba, hanyar dandali ta nufa, girgiza kai kurum tayi ta koma cikin gida tana fad'in "Ubangiji Allah ya shirya min ke Ladidi" D'alha ne yake tafe yana tura baro dake d'auke da goba da mangwaro d'ata,, duk sunyi saura da alama yau kasuwa tayi kyau, can Ladidi ta hango shi ya karyo kwana, zai shiga gida, da sauri ta shige soron wani gida tana lek'en shi, har ya wuce, tai sauri ta futo da gudu ta bar gurin. A mutuk'ar gajiye ya shiga gidan, Mai koko na tsaye tana aikin tata sai sauri take saboda magari ba tayi,, guri ya samu ya aje abun sana'ar tashi,, ya zauna kan tabarma cikin gajiya, yace"Iya sannu da gida da aiki" "Yawwa Sannu ka dawo kenan"? "Eh Wallahi Allah yayi mana dawowa" "To masha Allah" Iya tafad'a ta cigaba da abunda take Kishingid'a yayi yace"Iya ina Ladidi take ne? Yau naga aiki yayi miki dare, ko ta futa yawon da tasaba ne"? Ajiyar zuciya ta sauke tace"Yanzu ta futa ashe ba ka ganta ba, tana futa kana shigowa" K'wafa yayi cikin b'acin rai yace"Wato yarinyar nan bata jin magana ko Iya"? "To yaya zakayi ne, sai kayi mata addu'a k'uruciya ce take damunta" "Nifa Iya babban bak'in ciki na da Ita rashin kamun kai da wasa da maza da take in taje dandali babu shirmen da bata yi wallahi" "To wai yaya zakayi ne D'alha, nifa bana son kana takura mata, nasan duk abunda take k'uruciya ce watarana zata daina" Shiru yayi ya daina wahalar da bakinsa domin yasan duk surutun da zaiyi Iya sai ta kare Ladidi duk wani iyashege da yarinyar take itace take daure mata gindi. Mik'ewa yayi ya d'auki buta ya futa waje domin ya d'aura alwala. Suna zauna gidin wata k'atuwar bishiyar mangwaro, sun kai su Tara zuwa goma duk sun kewaye ta itace shugaba,, duk sun mimmik'e k'afafunsu suna wasan *nanje na gidan gona* in an cinye mutum sai su kwashe da dariya har da burgima,, ihu! Suke suna fad'in Ladidiya don Allah yanzu ki sauke a kaina,, muga wa za'a kad'awa barbad'in tusa" "Ku tsaya!Ku tsaya kuji! Ku tsaya kuji"! Ladidi ce take fad'in haka. Tsit! Sukayi suna sauraron ta,, k'aykayin da taji kanta nayi ne ya katse mata abunda take so tace, cire d'ankwalin tayi ta jefar k'asa ta sanya hannuwan ta biyu ta dunga kartar kan tana lumshe ido,, dad'i take ji sosai in tana sosawa, shiru sukayi kowa yana jin tsoro kar yayi dariya ta doke shi,, tafi minti biyar tana aikin sosa kanta sannan ta cire hannuta tana muzurai,, kallonsu take ta sha kunu domin shaf ta mance a inda take idan tana Sosa kai kwata-kwata mance komai take,, so take taga ko akwai wanda zai mata dariya a cikin su, sai taga duk sun nutsu,, ba tare da ta mayar da d'ankwalin nata ba tace" Ku san me"? Had'a baki sukayi gurin fad'in "A'a sai kin fad'a" Dariya ta kece da ita tace"Wallahi duk wacce k'arshe ya sauka a kanta to ta saddak'ar da cewar sai anyi mata ihu an k'ada barbad'in tusa kuma har gida za'akai ta anai mata ihu! Kun yarda ko"? Ihu! Suke suna fad'in "Mun yarda" Mun yarda" "To kowa ya mike k'afarsa a sako daga farko" Mik'e k'afafun su sukayi, ta fara yi musu,, duk wacce ta futa sai ta koma gefe tana murna ya rage saura mutum biyu Murja da Indo kenan duk sunyi tsuro-tsuro dasu,, ita ko Ladidi sai dariya mugunta take musu,, Nan je na k'arshe ya sauka a k'afar Indo ta mike da sauri tana murna,, Murja ta mik'e da sauri zata gudu,, Ladidi ta tad'o k'afar ta, tafad'i gurin ,sai suka dauk'i ihu!!!!! Yeeeee!! "Murja warin wando Murja mai wari tusa,akad'a mata barbad'in tusa, a kad'a mata bar bad'in tusa!!!! Su ka ture Murja suna yi mata ihu!! Suna ja mata k'afafu saurin muryar Ladidiya yafu na kowa tashi a gurin. Hankalin masu sai da nama fura da nono da duk wani mai sana'a gurin ya dawo Kansu,, Mutari me nama yace " Wannan yarinya baza ta tab'a barinmu mu huta ba wallahi duk itace shugaba" Haliru me fura da nono ya nufi gurin a fusace yana fad'in "Bari naje nayi maganin su" Yana zuwa gurin ya d'aga murya yana fad'in "Ke " yar gidan mai koko, zan ci ubanki wallahi idan baki ja zugar ki ba kun bar gurin nan ko an fad'a miki kowa mahaukaci ne irin ki"? Tsittt! Sukayi jin abunda Halliru yake fad'a, Ladidi ta kura masa ido tana jin takaicin zagin da yayi mata, amma tasan abunda zata yi masa,, ganin sun daina ja mata kafa yasa ta mike da sauri zata gudu, Ladidi tayi saurin damk'e ta tana fad'in " Murja me warin wando Murja me warin tusa yeeee! a kad'a mata barbad'in tusa!!! Aikuwa sauran suka d'auka gurin ya k'ara kacamewa da ihu!! Halliru ya gama b'ab'atun sa ya hak'ura ya tafi domin ko sauraron sa ba suyi ba, haka suka tasa Murja suna ihu! gami da dungure mata kai, har suka kai ta gida,, sai kuka bak'in ciki take,,nan ta basu umarni tafiya kowacce ta kama hanyar gidan su, ita kuwa dandali ta k'ara komawa domin ta aiwatar da k'udirinta. Kan Halliru a ganinta tana raye babu wanda ya isa ya zagar mata iyaye ba ta hukun tashi ba,, Ta bayan gatangar da suke zaune ta bi,, sosai gurin yake da kwazazzabai gami da ra muka katangar ta d'ane sosai ta hau ta dura, a hankali ta tsuguna tana tattaro k'asar gurin,, zanin ta ta kwance ta zuba k'asar a kai ta nufi inda suke zaune,, Halliru na can gurin wani mai rake suna magana, shi kuma Mutari mai nama kasuwa ta bud'e ana ta cini ki,, da sauri ta bud'e doguwar robar dake cike da nono ta zazzage wannan k'asar me uban yawa da ta d'ebo ta cikin zaninta, ba tare da ta d'aura zanin ba ta bar gurin kamar walk'iya. Halliru ya dawo gurin da sauri hannunsa rik'e da wata roba me kamar kwanon sha, da ledoji a hannun sa,, wasu matasa na bin bayan sa, da sauri ya bud'e robar nono sa ya zura k'aton ludayi da yake motsa wa,, sai yaji gurin-gurin d'in dutsina da k'asa a ciki,, salati ya rafka da sauri ya zaro cocilan d'insa daga cikin aljuhu yana haskawa, innallahi wa'inna ilahi raji'un , nono ya rine! Ya koma jajazur dashi, ya kalli Mutari mai nama dake hada-hadar sallamar jama'a yace"Mutari"!!!!! *COMMENT VOTE AND SHARE* [9/23, 7:47 AM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* *NA* _BINTA UMAR ABBALE_ ~*®BINTUBATULA👄*~ *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` _*LOODING:*_ _*{LADIDI K'WADAGA🌚}*_ _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain aur reades``` _______________________ _*DEDIGATED*_ *TO* _RAHAMA ALIYU_ ```Komai yayi tsanani yana tare da sauk'i, cikar muminin mutum yarda da k'addara mai kyau da mara kyau, idan ubangiji ya jarrabe ka, da musiba ka karb'a hannu biyu kar kace wani ne yayi ma, ko da wani mutum ne silar faruwar haka to kasani babu abunda bawa ya Isa yayi face da sanin mak'agin ka, Ubangijin baiwa kenan alimul gaibu washahadati, ka mik'a masa al'amarin da sannu zai yaye maka damuwar ka, Allah kasa mu dace``` _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿4* Da sauri Mutari ya juyo jin irin kiran da Halliru ya kurma masa, baki na rawa yace"Akwai wanda yazo gurin nan bayan naje guri Umaru mai rake yanzu"? Cikin mamaki Mutari yace"Gaskiya babu wanda yazo kan kayan ka ina kallo tun d'azu" Kamar ya fashe da kuka yace"Zo kaga abunda akai min" Mutari ya baro gurin sa da sauri yazo yana dubawa,, salati yasa yana mamaki tare da fad'in"Wannan aikin Ladidi ne wallahi, d'azu ba kaje har inda suke ba, ina jin kana zaginta" Halliru yace"To kuma da kace baka ga wanda yazo gurin ba" "Tabbas ban ga kowa ba, amma na tabbatar da cewar Ladidiya ce zatayi maka wannan aikin, wallahi kasan ta kamar aljana take, sam ba'a ganinta a guri" Cikin fushi Halliru yace"Billahillazi sai sun biya ni kud'in nono na, idan ta saba yi wa wasu suna k'yaleta to ni wallahi bazan d'auki asara ba" Murmushi Mutari yayi yace"Shiyasa d'azu kamar in ce maka kar kaje inda suke saboda nasan halin yarinyar bata da mutum ci wallahi shiyasa kaga ni bana shiga sabgar ta, ko kaman ta lokacin da ta watso min ruwan kwata kaina kasan ranar har nama da gurasa basu tsira ba sai da ruwan kwatar ya same su,, ko da na je na fadawa kakarta hakuri kawai ta bani, da k'yar na kara tayar da wani jarin" Halliru ya tsuguna yana goge gumi, Ladidi ta kassara masa rayuwa ta rusa masa jarin sa, yau-yau d'in nan ya d'auko sabon nono duro guda dubu goma sha biyu yarinyar nan ta zuba masa k'asa a ciki,, kewaye shi sukayi suna bashi hakuri wasu na bashi shawarar kawai ya tafi ya fadawa mai gari a bi masa hakkin sa. Tana tafe tana d'aura zaninta,, gami da kad'e ragowar k'asar dake jikin zanin,, ta gyara d'aurin d'ankwalin ta,, ta cigaba da tafiya fagam-fagam! Ko tsoron dare ba tayi, Tara da rabi na dare, haka ta dunga wuce majalisa ta maza babu abunda ya dame ta,, har ta karya kwana zata nufi gida sai ta canza shawara juyawa tayi ta koma da baya, kwanar gidan kallo ta nufa,, tun daga nesa ta gango matasa sun cika rumfar kwanon ga hasken wuta nan tar! Masu gyad'a da daddafan k'wai da saurarnsu sai cini ki suke,, bayan gurin kallon bola ce,, gashi ba wani dogon gini bane wani gurin ma da langa-langa a ka rufe,, a hankali ta hau kan bolar ta daddafa ta d'ane kan k'aramar katangar,, kanta ta zura tana lek'awa, aikuwa taga matasa sun cika gurin suna zaune kan bainci wasu ma basu samu guri ba, suna tsatstsaye sai ihu! Suke da alama film din ya d'auko dad'i, sosai take zura kanta domin taga wane irin film ne da ake ihu!! Wani saurayi ne ya kare mata da tsahon sa, ji take kamar ta sauka ta zabga masa mari,, ihun da sukeyi yana hana aji komai sai wani take take ji babu alamun k'usha-k'usha,, kunne ta kasa sosai lokacin da Taji wannan saurayin yana magana dana kusa dashi "Gaskiya ina son film d'in nan wallahi, Sharukahn ya iya soyayya , nifa lokacin da ya rungume ta, he da na kusa suma dan dad'i wannan film din yayi kyau wallahi" Dariya d'ayan yasa yace" Ya sunan film din ma"? "Khoch-khoch hotaih" Hahahaha Gaskiya film din yayi ko nawa ake ce zan biya domin in kalle hi" Ihun!! da suka ji ne yasa suka mai da hankalin su kan Tv,, Ladidi tace"Hegu "yan iska ni da nasan ba na fada bane ma bazan zo b.... Maganar ta ta katse lokacin da Allah ya bata ikon hango akwatun tv an hasko Sharukan da kajol suna soyyaya da rungume-rungume! " Kan Uba!! Ta kurma wani uban zagi,, tsaki taja tana k'okarin dura kasa tace"Allah wadaran in tsaya in kalli wannan iskancin, nifa shiyasa na tsani wannan Dan film din gwara Salman kan,, yana da mutum ci,, dura tayi k'asa tana Jan tsaki sai mita take da ta sani bata zo ba, inda ta San ba fim din fada bane, Shiru gurin duk masu saye da siyarwa dake gurin sun tashi,wasu ma har sun soma futowa daga gurin kallon dana film din yazo karshe, ko a jikinta, ta kama hanyar gida fud'un-fud'un,, kamar daga sama, taji an cafki hannuta, ta juya a fusace! Ilu ne ya ke mata wani kallo yana lashe baki. Hararsa tayi tace"Sakar min hannu ko in ci abu ta kazar ka" Ilu yace"Ni kike zagi takand'a" ? Fuzge hannuta tayi a fusace! Ta tsani ya kira da wannan suna wai takand'a, tace"Uwarka ce takand'a bani ba" Mari ya kai mata, ta kauce da sauri,, hannuta yaja da k'arfi ya na kokarin kai ta wani lungu ta turje tana zagin sa,, yace"Dama neman ki nake ruwa a jallo Dan uban ki, d'azu kin fasawa k'anwata baki ranan kin zage ni ,to yau zaki gane kuran ki" janta yake tana turjewa, gami da durzar k'asa da kafafun ta, duk k'arfin sa sai da ya sare, ya kama haki!! Tace"Sake ni ni ba "yar iska bace" Yace"Sai ki gayawa wanda bai sani ba, Dan uwarki daga gidan Uwar ki kike shegiya jiki duk jijiya sai k'arfin tsiya" "Uwarka ka zaga ba tawa ba" tafad'a a fusace! Yace"Au! Baza kiyi shiru ba" ? "Sai kayi shiru zanyi, kuma wallahi zaka San ka zagi uwata" "To me zakiyi Takand'a" ? yafad'a yana mata dariya ta k'arfin hali, domin duk ya gaji yau ya kara tabbatar da cewar yarinyar ba ita kadai bace,, shamtar sa tayi yana fad'in "Zaga kuwa abunda zanyi yanzu" kafin ya ank'ara ta kwashe k'afafun sa da hannu daya ta zubar dashi a gurin ta falfala da gudu tana shek'a dariya babu ruwanta da dare. Ilu ya rike bayansa yana rintse ido sosai bayan sa ya bugu da wani dutse ya Dade a kwance a gurin "yan gidan kallo na ta wuce shi a kwance,, cikin takaici ya mike tsaye yana da ya sanin kula Ladidi gashi ta ji masa ciwo a banza. Mai koko na tsaye a soro cikin tararrabi, k'arfe goma da rabi na dare, Ladidi ba ta shigo gida ba, ta duba ko ina bata nan,, D'alha ya gama fad'an sa ya futa nema,, da ya d'auka abun wasa ne, sai da yaga an gama Taskar labarai, hankalin sa ya tashi, babu shiri ya bazama neman ta,, duk ya duba inda ya dace babu ita, ya nufo gida cikin gajiya da sarewa, zuciyarsa ta raya masa yaje ya duba gidan kallo, hanya ya kama yana tafiya yana addu'a a zuciyar sa,, da tafiyar ta ya gane ta,, b'uya yayi sai da tazo ta wuce sannan ya futo ya bi bayanta, abunda yasa ya b'uya shine yasan halinta in ta ganshi tana iya guduwa,, tana shiga soron gidan yana shiga,, ya sanya k'arfi ya k'wade mata k'eya d'ankwalinta ya fad'i kasa, ta rusa ihu! Wannan karon Iya bata hanashi dukanta ba, fad'i take " Kara mata ja'irar yarinya gantalalliya ta tayar mana da hankali" Ladidi ta buga wani uban tsalle ta afka cikin gidan tana kurma ihu!! Kamar Wanda aka kona mata jiki da ruwan zafi,, d'akin Mai koko ta shige ta zura sakata tana ihu! Tun k'arfin ta. *COMMENT VOTE AND SHARE* [9/24, 10:59 AM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* *NA* _BINTA UMAR ABBALE_ ~*®BINTUBATULA👄*~ *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` _*LOODING:*_ _*{LADIDI K'WADAGA🌚}*_ _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain aur reades``` _______________________ _*DEDIGATED*_ *TO* _RAHAMA ALIYU_ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿5* D'alha yace"Gashi kinji daga bakinta ko? can na gano ta ita kad'ai kan hanya tana tafiya ko tsoron dare ba tayi" Mai koko tace"Yanzu dai kayi hakuri mubar maganar sai da safe dare yayi" K'wafa yayi cike da takaici ya yar da abun dukan ya shige d'akinsa. Iya ta sassauta murya tana fad'in"Bude min kofa kinji ko,, bazan bari ya doke ki ba" Ladidi najinta tayi mata shiru,, "Na ce dake ya tafi d'akinsa ki bude min kofa nace ko" Banza tayi mata,, Sauraye sai cizon Iya suke babu abunda take so illa ta kwanta don tayi muguwar gajiya, rarrashin Ladidi take ta bude mata kofa,, k'eme-k'eme tak'i budewa, gyara kwanciyar ta tayi ta lumshe idonta bacci na fuzgarta, tana jin surutun da Mai koko take sam bai dame ta ba,, b'acin rai da takaici suka saka zuciyar Mai koko kamar ta buga gashi ko "yar tabarma babu a tsakar gidan ballantana ta shimfud'a ta kwanta,, ga duhu ga sauro ga danshin ruwa, bata so ta daga murya saboda dare kar D'alha yaji soro ta nufa a hankali ta kwanta kan dogon bainci da masu siyan koko suke zama tana addu'a a zuciyar ta, Allah ya shirya mata Ladidi. *TUSHEN LABARI* *K'auyan d'an kunkuru* k'auye ne dake cikin jahar kano,, ya had'a da Fulani a ciki amma ba sosai ba,, k'auye ne da yake da albarkar gonaki da filaye gami da manya-manyan bishiyun mangwaro ko ta ina,, Malam Labaran manomi ne wanda yake da gona guda d'aya yake noman d'orawa da gero a ciki,, da Abunda ya dogara kenan dashi yake ci da iyalinsa yake sauran bukatu, yana da mata d'aya da yara biyup duk maza, matarshi sunanta Furera, mace mai Neman na kanta tunda aka kawo ta gidan Mijinta take sana'oi iri -iri , domin ta dogara da kanta, dansu na fari sunan shi Aminu yana da lalurar sikila sai Dan uwanshi D'alha shi lafiyan sa lau, abunka da k'auye San basu maida hankali gurin ciwon dansu ba, sai dai in ciwon ya motsa masa suyi masa jike-jike su bashi, Cikin hukunci ubangiji ya mike ya cigaba da rayuwa kana kallo Aminu kasan bashi da koshin lafiya tare suke tafiya gona da mahaifin sa,, ko sunje can ma baya iya aikin koma, D'alha ne me karfi,, Malam Labaran yana da aboki D'an Fulani gurin zuwa kiwo suka hadu dashi,, inda Allah ya had'a jininsu ta kaisu ga had'a yayan su aure Aminu da Amina "yar Dan Fulani itama tana d'auke da irin lalurar Aminu, dake d'an Fulani ma'abocin jin redio ne, ya tab'aji suna fada cewar idan masu irin cutar zasuyi aure su dunga auran jinsu su, nan Labaran ya amunce, ya kuma Sanar da Aminu da Hurera duk suka amunce suna fatan alkairi,, lokacin yayi aka d'aura aure cikin aminci Amina ta tare gidan Mijinta Aminu inda gurinsa yake kewaye da langaga sai dai in zata shiga band'aki take futowa babban tsakar gida,, wata hudu da auran su, ciwon Aminu ya tashi kafin ayi wani yunk'uri ya galabaita mutuk'a jikinsa kamar babu jini ya dashe Tass,, wani makocinsu ya basu shawarar zuwa birni domin a duba shi, to suna cikin shirin tafiya ne, Allah ya amshi Abunsa , mutuwar sa ta girgiza mutane mussaman matarsa Amina tayi kuka har ta gaji " yan uwa na tasaunta tayi hakuri,, bayan sadakar uku kowa ya watse akabar mutan gida da kewar Aminu mutumin K'warai kenan, bayan sadakar ar'ba'in ne aka gano cewar Amina na da ciki, aikuwa Mai koko ta dunga kula da ita sosai har lokacin haihuwa yazo,, inda Amina ta fara zubar da jini abunda ba a so kenan ko mai lafiya balle mai sikila, hankali a tashe aka d'auke ta sai asibitin birni *(Murtala muhamad hospital)* ganin tana cikin halin taimako ne yasa suka shiga da ita dakin operation,, suka ce mijinta ya sa hannu aiki za'ayi mata,, Dan Fulani na kuka da rokon Allah ya sanya hannu Labaran ma ya sanya, to tun kafin a shiga da ita ta rasu,ganin cikin na motsi yasa suka shiga da ita cikin gaggawa aka Ciro yarinya mace, mai kama da uwarta. Cikin halin damuwa nurse ta futo ta sanar dasu halin da ake ciki, sosai suka shiga rud'u da tashin hankali daga bisani suka hak'ura suka barwa Allah, suka karb'i gawar Amina suka tafi domin yi mata suttura, mai koko na rungume da jaririya tana kukan zuciya. ***************** Mai koko ta d'auki son duniya ta Dora shi kan Amina da taci sunan mahaifiyar ta, dama kafin su baro asibitin sun duba ta sosai ko itama tana d'auke da ciwon sikila, Allah mai yadda ya so yarinya lafiyanta Lou sai dai k'ankanta, amma inda ans bata madara me kyau zata murmure. Malam Labaran bai yi shawara da kowa ba yaje ya sanya gonar shi a kasuwa nan take aka samu mai siya kasan cewar gonar tana da kyau kuma tana da fuska akayi ciniki aka bashi kudinsa, ya nufi asibitin cikin gari duk abubun buk'ata ya siyowa Amina ya siyo mata madara masu kyau, da kaya niki-niki ya shigo gidan, Hurera tai yi mamaki sosai nan ya zauna ya warware mata komai, tace"Malam da kayi shawara dani da baza ka siyar da gonar ka ba" yace"Saboda haka shine mafuta asurinmu ya rufu, Kinga madarar nan tana da tsada idan ba haka ba bamu da kud'in siya, kuma ko d'aukar me shayarwa mukayi dole mu biyata, tace"Hakane kuma to Allah ya rufa mana Asiri,, nan Hurera ta kara k'aimi gurin Sana'a har ta kafu da sanar Koko da safe,, shi kuma D'alha yake sana'ar sai da D'ata goba da mangwaro asirinsu na rufuwa,, Dake ranar lahadi aka haifi Amina yasa Mai koko take ce mata Ladidi shikkenan mutane suka rike suma suke kiranta da Ladidiya,, shekararta uku a duniya Allah ya amshi ran Malam Labaran ciwon kai tafarar daya,, Mai koko nauyi ya kara yi mata yawa, dake jaruma ce, sam bata karaya ba, ta cigaba da neman kud'inta, da kanta ta kai Ladidi makarantar allo tun tana da shekaru hudu,, tana zuwa cikin yara zaka ji gurin ya kaure da kuka Ladidi Duk ta doke su, har wad'anda suka girme ta dokansu take,,Malami ya doke ta tayi masa Allah ya Isa,aikuwa ya dawo wa da mai koko ita yace"Tana hana su karatu in taje dokan yara kawai takeyi ta hanasu karatu gashi in an doke ta tayi Allah ya Isa shi kam bazai iya ba" Mai koko tace"Kaje ai ba kai kadai bane me makaranta na kai ta wata, sai da akayi wata shida tukkuna sannan ta kaita wata makarantar nan ma bata canza zani ba,, tana zuwa makarantar karatun yara ya lalace domin duk gurinta suke komawa suyi ta wasa duk tsawan da malam zai musu basa jinsa. Nan ya fahimci zuwan Ladidi ne jawo haka, tunda da yana iya tankwara su, aikuwa sai ya ware ta a cikinsu in tayi futina yaci ubanta, ita kuma ta zage shi, gashi duk dukan da za'ai mata bata kuka sai dai idonta yayi ja, malam da yaga ba zai iya ba ya tattarata ya mayarwa da mai koko ita,, abunda ta fadawa malamin farko haka ta fada masa,, shekara guda bata zuwa makaranta, sai wasa da yawo kusfa-kusfa D'alha bai tab'a Ankara ba, dake da wuri yake futa baya dawowa sai gab da magariba, ya dawo ya wuce ta makarantar Allo yaga an tashi yana ta daga kai yaga ta inda Ladidi zata b'ullo bai ganta ba, sai yayi tunanin ko ta tafi gida, yana tafiya ya hangota kan katangar wani gida ta mike tsaye tana ta tafiya tana k'yalkyala dariya kanta babu d'ankwali, sai diddigagen gashinta da kwarkwata ta cinye rabi ta bar rabi, duk k'wanta nan burjik!! Kira ya kwala mata"Ladidi"!! Da sauri ta juyo jin muryar Kawunta ta hantsilo k'asa ko a jikinta ta mike da gudu tayi gida,,, girgiza kai yayi ya bi bayan ta. Sosai ya dunga fad'a Mai koko tace"Ai sai ka d'auke ta ta kaita da kanka ko wace makaranta aka kai ta sai su koro ta saboda tsabar bakin ciki sun tsani marainiyar Allah" Yace"Halin ta ne ya jamata zan kai ta, wata makatanar da kaina Wallahi da kaina zan dunga hukunta ta" Shiru mai koko tayi masa ya gaji ya shiru, ita ko Ladidi na bayan ta tana zumb'ura baki gami harare-harare ta tsane shi tunda kullum cikin takura mata yake. Washe gari da safe D'alha ya sa ta a gaba suka nufi makaranta ya damk'a ta a hannun Malam yace"Gatanan yayi mata hukunci in tayi laifi, kuma ya kula da karatun ta." *COMMENT VOTE AND SHARE* [9/24, 10:29 PM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* *NA* _BINTA UMAR ABBALE_ ~*®BINTUBATULA👄*~ *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` _*LOODING:*_ _*{LADIDI K'WADAGA🌚}*_ _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain aur reades``` _______________________ _*DEDIGATED*_ *TO* _RAHAMA ALIYU_ _*KU SONI TA ZARCE💝💝💝 NIMA NA NASO KU TA ZARCE❣❣❣IN HAR KUKA KUFCE! 😡😡A KANKU NI ZAUCE! 🤢 IN KUNJI😍😍*_ 😃😃😃😃😄😄😄😃 I will always saying thank you to my people love you so much,, muna tare insha Allah😘 *🅿6* D'alha ya kama hanya yai tafiyar sa, gurin sana'ar sa, tunda malam yayi mata gurin zama cikin yara take ta faman zabga masa harara sosai yayi mamakin yarinyar ko da yake dama yana da labarin ta sosai,, sai ya d'auke kansa kawai yayi kamar bai ganta ba,, ya cigaba da koyar da yara, yarinyar dake kusa da ita ta zura hannu ta mintsina yarinyar ta fashe da kuka, Sai tayi saurin cire hannunta tana kallonsa yana kallonta,, ya gane itace yarinyar ya kira da hannunsa, gurin zama yayi mata,, Ladidi taji haushin haka, tayi shiru tana zumb'ura baki, lokacin tashi nayi yayi musu addu'a duk suka mike sai ta d'auki takalmi wata ta b'oye, to yaga lokacin da ta d'auka, murmushi yayi ya kira yarinyar ganin tana kuka, Ladidi ya kira, taje tai masa k'erere aka yace"Bata takalmin ta" Zumb'ura baki tayi tace"Baya gurina fa" "Naga fa sanda kika d'auka kika b'oye bata kinji ko,, ni nasan kyautar da zanyi miki" Shiru tayi yace"Zan baki alawa" Aikuwa sai ta futo da takalmi da ta b'oye kasan zaninta ta jefawa yarinyar, da sauri ta d'auka ta sa, ta kalle shi, kai tsaye tace"Bani alawar" yace"Dama ba karatu kika zo ba" ? Daga kai tayi" yayi murmushi yace"To don Allah kiyi karatu ki nutsu kinga Kawun ki ya kawo ki kiyi karatu nayi miki alk'awarin bazan Doke ki ba kamar yarda ya fad'a" baki ta tura tace"Ko ka dake ni ba zafi zanji ba" dariya yasa yace"Nasan da haka ai,, shiyasa ma bazan tayar da hankalina ba". "Ni dai bani alawa ta" fad'a tana Sosa kanta,, Hannu ya zura cikin aljihun sa ya ciro Alawa guda biyu yace"Kullum nayi miki alk'awari zan dunga baki mutuk'ar zakiyi karatu in kin zo makaranta kuma zaki nuttsu ki daina tsokanar "yan uwan ki" Karb'ar Alawar tayi tayi tafiyar ta, ta barshi da baki a sake, girgiza kai yayi ya d'auki allon nata yana dubawa, duk girman ta, tana Alam tarakaifa. Wanda basu kai shekara goma ba ma sun shiga sabbi,, ita tana zaune, haka kawai yake tausayin yarinyar, yana fa yara guda biyar duk kamarta shiyasa in yaga yara na k'uruciya yake musu addu'ar shiriya Wannan shine silar zaman Ladidi a makaranta ko tayi nufin tsokona ko gudun makaranta sai ta fasa saboda alk'awarin alawar da Malam Salihu yayi mata, shi kuma kullum baya fashi, ana tashe zai bata,, gashi Yanzu tayi nisa a karatu ta kusa izu d'aya. Babu laifi tana gane wa. *WANNAN SHINE TOSHEN LABARI* Da Asubah D'alha ya futo da niyar zuwa massalaci, da cocilan a hannunsa yana haskawa, sai ya ga Mai koko na k'okarin saukowa daga bainci da alama itama tashin ta kenan, Cikin mamaki ya tsaya yana kallonta yace"Iya me kike anan"? Shiru tayi masa ta mike tana Sosa jikinta, yace"Da alama nan kika kwana meye dalili"? Cikin b'acin rai tace"Wannan ja'irar yarinyar ce ta rufe min k'ofa jiya babu yadda banyi ba ta bude min amma tak'i"D'alha mamaki sosai yake yace"Tak'i bude miki k'ofa me makon ki min magana shine zaki kwanta a soro cikin sauro Iya sai kinje zazzab'in cizon sauro ya kama ki"? K'okarin shiga cikin gidan take tana fad'in"Kai dai magana ta wuce, ai kayi tafiyar ka" Gyad'a kai kawai yayi ya wuce yana mamakin son da Iya takewa Ladidi wannan son shi a ganinshi cutar wa ne, domin shi yake k'ara lalata yarinyar. Har yaje massalaci yan sak'e-sak'en hukuncin da zai d'auka kan Ladidi domin ko me Iya zatayi sai ya doke ta ya rantse. Bayan an idar da sallah sun futo,, Halliru mai Fura ya tsaida shi suka gaisa,gani yayi Halliru na sha masa kunu yace"Malam Halliru lafiya ko" ? Halliru ya sauke ajiyar zuciya yana fad'in"Idan kaji kira daga mai gari kar kayi mamaki" Cikin mamaki D'alha yace"Me ya faru" Rai a b'ace Halliru ya kwashe duk abunda ya faru ya fad'a masa,, innalillahi wa'innailahi raji'un shine abunda D'alha yake ta Nanatawa yace"Don girman Allah Halliru kayi hak'uri wallahi in banda ka fada min ban san abunda yake faruwa ba, itama Iya ina tabbatar maka da cewar bata sani ba kayi hakuri don Allah kar ta kaimu ga zuwa gurin mai gari, wannan tonan asiri ne" Halliru ya sha kunu yace"Inyi hakuri kamar yaya? Kana nufin in zauna bani da abinyi kome? Na fada maka fa yarinyar nan duk jarina ta rusa kaje ka tambayi Mutari me nama zai fada maka komai" D'alha ya kwantar da murya yana fad'in "Duk baza ta kaimu ga haka ba,, yanzu ya kake so ayi" ? Kai tsaye D'alha yace"Kawai mu raba asara Ku bani dubu biyar ni nayi muku lamani" D'alha ya tsaya yana tunani daga bisani yace"Shikkenan insha Allahu zamu San abun yi ka kwantar da hankalin ka" Halliru ya saki fuska yana fad'in "Shikkenan sai na jika" Sallama sukayi kowa ya kama hanyar gida. Lokacin da ya isa gida, Mai koko na tsaye gaban wata k'atuwar tukunya da duguwar muciya a hannunta tana ta aikin motsa koko ga kwanuka har an fara layi,, kai tsaye d'akin ta ya nufa, sam bata yi tsammanin dokan Ladidi zai yi ba,, sai ihun ta kawai ta ji da sauri ta jingine muciyar ta shiga dakin da sauri,, tana fad'in "Au!! Dama dokan ta ka shigo kayi ko D'alha? Can na hango Ladidi k'arshen gadon k'arfen Mai koko sai ihu!! Take kurmawa babu ko k'wallon hawaye, D'alha ya zage k'arfi yana ta labta mata bulala,ya ki cewa komai,, Tace" Shikkenan kashe ta tabi iyayen ta, tunda kak'i ka saurare ni" yana haki! Yace"Da kin san abunda yarinyar nan tayi to da kin bani gudumawar abun duka" Cikin fushi tace"Kome tayi bazan bada abun duka a illata ta ba, ni dai nace ka daina dukanta in dai ni na haife ka" D'alha ya yar da abun dukan yana haki! Cikin b'acin rai yake warware mata abunda ya faru, sosai itama ta jinjina al'amarin, amma don k'arin abun haushi sai cewa tayi"Yo ai da ka k'yale shi yaje ya fad'uwa mai gari sai me, dan yaje, dubu biyar dai insha Allahu za'a bashi, ai k'imar mutum tafi kudi shi kud'i suka dama da zai zugo ka kazo kana dukan marainiyar Allah" D'alha yace"Ko yau ta k'ara sai na doke ta, in ta kama ma in sa ta a mari sai in daure mata k'afafu sai inga k'afafun yawo" "Tunda kai ai haka akayi maka sai ka daure ta magani" Mai koko tafad'a cikin takaici,futa yayi a fusace! Ta mai. da hankalin ta kan Ladidi dake ta faman sosar jikinta wani gurin har ya kwailaye, amma saboda dauriya da kafiya gami da jarumta ko kwalla babu a idonta k'ema gadas, sai da sunyi jajazuri! Tace"Kin kyauta kinji ko, aini kam bazan miki baki ba sai dai i n nema miki shiriya a gurin Allah idan kuma wani, shad'ainin ne yake sanya ki wannan Ibilicin to sai yayi magana mu sulhunta dashi, Allah ya bashi hakuri" tana gama maganar ta ta futa daga dakin domin ta fara jin hayaniyar yara a tsakar gida. Ladidi ta jima kan gado Tana Sosa jikinta dole fatar ta kwaile mussaman cinyar ta duk tayi rud'u-rud'u da duka, saukowa tayi daga kan gadon ta d'auki zaninta ta daura. fuskarta a murtuke ta d'auki dakkaken gawayi wanda suke goge bakinsu dashi, ta futa tsakar gida,, can bakin rijiya ta nufa ta d'auki buta ta zub ruwa nan bakin rijiyar ta tub'e wandon ta tayi futsari, ta fara durzar bakinta da gawayi, ranta a mugun b'ace, duk yaran da suke mata magana tana jinsu tayi musu banza. Al'wala ta d'aura ta shige d'aki, Ladidi duk k'injin ta tana sallah in lokacin ta yayi.Ko kwantawa tayi ta manta ba tayi ba, to lokacin ta nayi zata rama haka takeyi tasan lokotan ko wace sallahr farillah. *************** *************** *FLORIDA* Ta k'asar America,, had'and'un samari na gani zaune gurin shak'awa,, tsakiyar su lemu ka ne, masu sanyi da wani irin cin-cin wanda yaji madara da kayan had'i, suna ci suna hirarsu irin ta abokai, gefe guda kuma turawa ne suke ta sha'anin su, kai harda bak'ar fata ma, "yan k'asashe daban-daban kowa sai cin karansa yake babu mai damuwa da kowa, da yawa daga cikin su babu kayan arziki ajikin su, daga su sai wani tsinkakken wando wanda ya shige musu matse-matsi da tsinkakkiyar briziyya Wanda bata gama rufe musu nonowa ba duk gasu nan a waje, da gudu suke tsalle suna fadawa cikin ruwa suna dariya. Hakeem ya d'aga kansa yana kallon su,, fuskar sa a had'e yace" Dube su don Allah banzaye dasu sai nuna tsaraicin su suke, ashe dama abunda ya sa ka dame ni kenan kana so kazo ka kalli tsaraici, abunda Allah ya hana, haka kawai ina zamana cikin rufin asiri ka takura min sai nazo mun futa d'an iska kawai" Dariya Bash yasa yace"Kai don Allah fad'i gaskiya dai Yanzu ganinsu bai d'ebe maka kewa ba?, nifa wallahi dama da biyu nazo gurin nan,, so nake kafin mu koma in bawa idona hakkin sa" Cikin taikaici Hakeem yace"Kai wannan ya dama Wallahi nifa in ga mace cikin hijabi yafi min mutumci nama fi jin sha'awar ta akan in ga tsaraicin ta, don Allah tashi mu bar gurin nan" Ya fad'a yana mik'ewa tsaya,, mik'ewa Bash yayi yana fad'in"Ka dai fad'i gaskiya malam wa zaka nunawa ustazanci" banza yayi masa ya fara tafiya, wata beb ce ta futo daga cikin ruwa da gudu, daga ita sai d'an mitsitsin wando babu ko brziyya ta d'anshi, babu zato suka fad'i k'asa. *COMMENT VOTE AND SHARE* [9/25, 5:40 PM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* *NA* _BINTA UMAR ABBALE_ ~*®BINTUBATULA👄*~ *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` _*LOODING:*_ _*{LADIDI K'WADAGA🌚}*_ _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain aur reades``` _______________________ _*DEDIGATED*_ *TO* _RAHAMA ALIYU_ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿7* A mutuk'ar fusace ya hankad'e ta ta fad'i k'asa ya mik'e tsaye da sauri, cikin zafin zuciya! Ya damk'o wuyanta ya dunga rafka mata marika, lafiyyayu. Da sauri Bash ya k'araso gurin gami da fuzge yarinyar daga hannun shi yace"Lafiyan ka kuwa hana Hakeem, wannan wane irin zafin zuciya ne, ai tunda ka kawo kanka gurin nan kasan haka zata faru"' Cikin b'acin rai yace" Dallah Malam rufe min baki,kai me yasa ba tai maka ba sai ni? Saboda ni ta raina,ko an fad'a mata cewar d'an iska ne ni, kamar ka, da zata zo ta rungume ni" Yarinyar tana tsaye hannunta dafe da kuncin ta, sosai taji zafin marin da yayi mata, idanun ta sunyi ja sosai,, tace"Don nazo in jiyar da kai dad'i shine ka wulak'anta ni, a idon mutane,, kasan ni ko wacece kuwa"? Banzan kallo yayi mata yace"Rufe min baki ko in zo in k'ara miki wani, ko ke wacece bai dame ni, ke kika shiga gona ta, meye ruwan ki dani zaki zo ki samin najasa a jiki" Cikin takaici tace"K'arya kake kace bakasan mace ba, wannan idon naka da yake a bude, saboda kayi min yasa yana kusance ka" Cike da takaici ya kalle ta sama da k'asa yace"To ni bakiyi min ba, shashashar banza kawai baki da Abunda zaki rud'e ni dashi, ko kina musulma d'iyar Hausa Fulani kina aikata ashararan ci, ina jiran hukuncin da zakiyi,, Sunana Abdul Hakeem Abbas D'an kaka" Ya zura hannunsa cikin wandon jins d'insa ya ciro wani k'aramin kati ya wurga mata, yace"Wannan katin shi zai nuna miki duk inda nake, ina sauraron ki" yana gama fad'in haka ya bar gurin a fusace! Bash ya kalle ta, tana tsiyayar da hawayen bak'in ciki, girgiza Kai yayi baice komai ba ya wuce, cikin zuciyar sa yake fad'in "Baki san wanene Hakeem ba shiyasa kika aikata masa haka, ya san halin mutumin shi, da tsantse ni, baya son abunda zai had'a shi da wata mace mutuk'ar ba halalin sa bace. Cikin mota ya tadda shi yayi cikin-kicin da fuska,, sai kad'a k'afa yake, yana zama cikin motar ya balbaleshi da masifa,, Bash yace"Wai Ubana ne kai da zaka dunga min masifa nafa gaji wallahi abu ya ruga ya faru sai magana ta wuce", "Ank'i a daina maganar ai kaine babban me laifi a gurina haka kawai ka takura min lallai sai naje gurin,, Bash yace" Da nasan abunda zai faru da ban gayyace ka ba, nasan yau yini zakayi kana tsine min" Tsaki! Yaja yace"Daga yau in zaka je yawon ka kar ka k'ara takura ni dole sai naje,, kaje kayi tayi kai tunda baza ka fasa ba" Bash yasa dariya yana fad'in"Angama ogana, wai ni don Allah in tambaye ka mana"? Ajiyar zuciya ya sauke yace"Ina jinka" . "Me yasa kullum kake takurawa kanka ne? Kace kallon mace ma baka so kayi inaso ka sani wannan tsantsenin naka ba shine zai tsare ka daga Abunda kake gudu ba, na lura fa kallon India film American film baka cika yi ba,, kafi kallon Hausa film mussaman na " yan k'auye nasu Rabilu Musa d'an Ibro, Allah ya gafarta masa" Kai tsaye yace"Saboda nasan yaya nake shiyasa nake takatsatsan da kallon abunda zai tada min da hankali" Murmushi Bash yayi yace"To wallahi gwara ma ka kadaina takurawa kanka ka tsaya ka mori k'urociyar ka, kallo ne kawai fa, ba aikatawa kayi ba balle kace kana da zunubi" Hakeem yace"Na lura k'aranci ilimin addini yana damun ka Bashir, mu bar wannan maganar, kada rayuka su b'aci don yanzu zan maka abunda bakai zato ba,, kai ma addu'a nake ma kullum Allah yasa ka gane, in sha'awa na damun ka in ka koma gida kayi aure kawai shine mafuta, domin a halin da kake ciki zaka iya fad'awa halaka" Bash yayi shiru yana tab'e baki, Shiko Hakeem driving d'inshi yake fuskarsa a had'e. *WANENE ABDUL HAKEEM?* Abdul hakeem Abbas D'ankaka, matashin saurayi ne d'an kimanin shakaru Ashirin da tara, yayi karatun sa na primary socndry a kano inda ya wuce America can yayi degree d'in shi fannin engineering,, sosai yake da brain inda wani company, nan k'asar America suka d'auke shi aiki ya amunce amma da sharad'in sai ya koma gida ya sanar da iyayen sa, bayan haka kuma sam bashi da ra'ayin zama k'asar saboda lalaewar ta,, mutum ne mai tsantseni baza ka gane haka ba sai ka zauna dashi, amma kallo d'aya kayi masa zaka d'auka wayyaye ne, kan holewa ta duniya saboda yana da bud'add'iyar fuska da iya mu'amula, da fara'a da barkwanci ga shi idanunsa a bude so ke ko yaya ya zauna da kai na minti goma zai fahimcin halin ka, wannan yasa mutane suke masa wani bahagon kallo, Ubangijinsa ne kawai yasan waye shi, Sun had'u da Bash ne a company shima yazo interview, shine suke abota, tunda Bash yazo k'asar yake yawo gurare, yau sai da yaja ra'ayin Hakeem ya bishi haka ta faru. Bash d'an Sakwatto ne, iyayen sa da "yan uwansa duk suna can da zama,sab'anin Abdul Hakeem, da suke Abuja da zama amma asalinsa dan jahar kano ne. General Abbas d'ankaka tsohon soja ne da yayi ritaya shekaru goma da suka wuce,, yana da mace d'aya Hajiya Hasiya suna da " yaya uku rak, biyu maza d'aya mace, Abdul Hakeem ne babba sai Salim sai Salima itace auta yanzu ta gama scondry tana shirin shiga jami'a, Salim kuwa saura shekara d'aya ya had'a HND d'insa , Salim da Salima kamar su d'aya,, suna kama da mahaifiyar su, da ta kasance shuwa fara ce tas sune suka d'ebo kamanin ta, shiko Hakeem Sak mahaifin sa, yana da duhun fata ba sosai ba, kalar fatar shi abun kallo ce, sosai suke girmama shi gami da bashi girmansa, suna gudanar da rayuwar su a tsare babu baragada komai cikin ilimi suke yi ************************ ************************ Kwana da yini tayi bata kula Mai koko ba,kamar itace ta doke ta, Mai koko kuwa sai lallab'ata take tana botsarewa, dan kanta ta hak'ura ta daina fushin.... Tsayawa tayi kan Mai koko k'erere tace"Bani kud'in makarantar" ta kalle ta cike da takaici tace"Babu gaisuwa kawai kinzo kin tsaya min aka ina amfanin haka? Wai ke yaushe zakiyi hankali ne"? D'auke kanta tayi tana zumb'ura baki, girgiza kai kurum tayi ta d'auki wani gwangwani da take ajiyar kud'i ta ciro hamsin ta mik'a mata tana fad'in"Gashi ki d'auki goma ki dawo min da canji na" Karb'a tayi da sauri a zuciyar ta tace"Wallahi ko sisi bazan dawo dashi ba, ladan dokan da akai min" Mai koko tace"Allah ya bada me amfani don Allah banda tsokanar yaran mutane" Banza tayi mata ta futa fakam-fakam!! Tun a hanya ta siyi aya jik'akkiya da goro ba, na goma-goma ta kwance d'an kwalin ta ta kulle canjin talatin d'in,,, To yau ranar wanke allo ne domin a sauya rubutu, d'aya bayan d'aya kowa yake biya allon sa, in ya iya sai ya je ya wanke ya kawo wa Malam,, Da k'yar Ladidi ta biya nata Malam nayi mata gyara yace"Gaskiya ki bari sai wani satin sai ki wanke kafin sannan kin iya" hararasa tayi, tace"Ba gashi nan na biya maka, gaskiya ni sai na wanke kamar yadda kowa ya wanke" yace"Ban yarda ba fa" mik'ewa tayi da allon a hannuta taje ta wanke,, kallonta yake cike da mamaki yace"To yau kuwa Wallahi bazan baki alawar ba" Dariya tasa tace"Ka rik'e kayar ka yau ina da kud'in siya, ga gansu ma" tafad'a tana nuna masa inda ta daure, k'wafa kawai malam yake yana kallon ta tana wanke allo tazo ta aje gabansa ta wuce fud'un-fud'un tana fad'in "Kuma dole ai min rubutu". Malam addu'ar shirya kawai yake mata. Tare suka jero da Alawiyya yanzu sun shirya basa fad'a, Alawiyya tace" Zo muje gidan muyi kallo, jiya babanmu da yaje burni ya siyo mata tv da vidio" Dariya Ladidi tasa ta daddaki kanta, tana fad'in "Da gaske kike "? Alawiyya tace" Wallahi" Ladidi ta rike hannunta suka kama sauri,,, aikuwa suna isa gidan suka tarar an kunna, yara sun cika gidan sai kallo suke, wani film ne singam fasarar Hausa, Ladidi tayi tsalle ta shiga tsakiyar su,, shikkenan guri ya hautsine daga wani yayi motsi zata buge kansa ta ce ya kare mata,, idan aka zo gurin fad'a, sai ta saka ihu! Ta mike tsaye tana gwadawa, inda tsautsayi ta buge na kusa da ita,, tuni kukan yara ya cika babarsu Alawiyya tace"Kai kashe kallon zanyi Wallahi ya daina dadi baka jin komai sai kuka" Ladidi ta rarrafa gurin ta rirrike mata hannu tana magiya kar ta kashe ta daina, da k'yar babarsu Alawiyya ta hak'ura ,, gurin fad'a kazo Ladidi ta kurma ihu!! Ta kalli Iliya dake zaune gefen ta, tace"Iliya don Allah ya sunan afton nan ya iya fad'a wallahi, hehehehe, kaji har wani take ake masa,, *kama b'arawo suburbud'e shi, sa shi a mota oga Singam!!!!* hahahahaha ta kwashe da dariya ta koma ta zauna tana sosa kanta jikin ta sai tsuma! Yake,, aikuwa yaran da suke gurin suka rud'u da fad'in *"Kama b'arawo suburbud'e shi sa shi a mota Oga Singam!!!!!!* babarsu Alawiyya ta dunga dariya tana fad'in "Ladidi sai dai idan baki zo guri ba, ubangiji Allah ya tayar miki da wannan k'uruciyar iya haka". *COMMENT VOTE AND SHARE* [9/26, 11:14 AM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* *NA* _BINTA UMAR ABBALE_ ~*®BINTUBATULA👄*~ *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` _*LOODING:*_ _*{LADIDI K'WADAGA🌚}*_ _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain aur reades``` _______________________ _*DEDIGATED*_ *TO* _RAHAMA ALIYU_ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿8* Sai wajan magariba sannan film din ya k'are, suka futo daga d'akin huuuuuuuu! Sun rud'e da fad'in *"Kama b'arawo suburbud'eshi sa shi a mota Oga Singam!!!!"* Ladidi ce shugabar su, in ta fad'a su fad'a,, haka kowa ya nufi gidan su yana wannan wak'ar da Ladidi ta k'irk'ira gurin kallo, da wak'ar a bakin ta ta shiga gida,, Mai koko ta bita da kallo cikin mamaki tace"Babu sallama sai wak'a Ladidi"! Dariya ta fashe da ita ,tace"Iya kin same"? Mai koko ta girgiza kai cikin mamaki,, "Wallahi wani film muka kalla gidan su Alawiyya me mugun kyau!! Gaskiya afton d'ab bala'i ne, uhmmm! Kin ga yanda yake suburbud'an " yan iska kuwa!? Ta k'yalkyale da dariya tana Sosa kanta ta cigaba da cewa"Iya nake fad'a miki har wani take ake masa,, saboda tsabar jarumta,, na tambayi Iliya ya sunan afton yace bai sani ba,shine na tsara masa wannan wak'ar. *Kama b'arawo suburbud'e shi sa shi a mota Oga Singam!!!"""* ta k'arashe wak'ar tana wata mahaukaciyar dariya, tamkar wata shashasha, Dariya Mai koko tasa tace"Aikam wak'ar tayi dad'i Ladidiya ta Mai koko,, ke dai kina son kallon hindiya" Ladidi ta dunga dariya taji dadin yabon da Mai koko tayi mata tace"Shiyasa ai nake so Kawu ya siya mana kayan kallo wallahi" Iya tace"Ke kin san bazai siya, nice zan siya miki amma sai kin nutsu kin daina shashanci da rashin ji gami da fada da maza" da gudu taje ta rungume ta tana Fad'in"Iya na daina insha Allahu, yaushe zaki siya mana" tace"Ki bari in d'auki a dashi na, zan siya miki amma fa sai naga kin nutsu". Ladidi tayi ta murna Iya tace"Kije ki yi alwala kiyi sallah, sai ki zo kici abunci" ta mike da saurinta sai farin ciki take Mai koko zata siya mata kayan kallo ******* Zaune yake a cikin wani had'addan bedroom kana ganin tsarin shi kasan na hotel ne, wanda ya had'a abubuwan more rayuwa da jin dad'i kai daga nin tsarin hotel din kasan ba na k'ananun mutane ba, ko a american ma sai wane da wane,, waya ce a hannusa, magana suke da Dady d'insa Yace"Dady ina tafe a wannan satin insha Allahu" daga d'ayan b'angaran G.Abbas yace"Wace rana zaka zo kason ina son zuwa in duba gidan gona ta a Kano ko" Dariya Hakeem yasa yace"Dady har ka samu guri ka fara aiki bani da labari" ?Dady yace"Sai kazo zaka gani, guri mai kyau can wani k'auye ne,, k'aramar hukumar Ungwago,, gonaki hud'u na had'a a gurin, babu abunda ban dasa ba,, ga gurin kiwo da gurin hutawa, gurin ya tsaru sosai" "Kai Dady har ka kwad'atamin son zuwa wallahi, insha Allahu mun gama komai anan, sun bamu izanin tafiya, inan tafe ranar Monday" Dady yace"Sai ka zo,, ai tuni su Salim suka je suka ga guri" b'ata fuska yayi yace"Dady kayi min laifi" Dariya yasa, Hakkim ya cigaba da cewa"Nine ya kamata na fara zuwa na gani na sa albarka" Dady yace"Kai dasu duk d'aya ne, kasan don baka gari ne". "Na sani Dady ai in nazo can zan gudu inje in huta" Dady yace"Zakaji dadin hutawa kuwa domin gurin yayi". Hakkim yayi ta sa Albarka Dady yana amsawa da amin, sukayi sallama cikin so da kaunar juna Wanda Allah ya kimsa tsakanin iyaye da "yayansu. ****** D'alha ne ya shigo gida a gajiye,, Iya da Ladidi na zaune tsakar gida kan wata tabarma Duk ta zare ta zama saura, kibiya ce a hannun Iya tana tsefewa Ladidi kai sai mita take kan kwarkwatar dake kanta wacce tak'i jin magani Babban abun takaicin ma shine duk rabin kan ya cire wani guri da gashi wani guri babu,, ga uban amo sani da k'wan kwarkwata abun k'yank'yami,, tace"Wannan kan naki gwara kawai a aske shi kowa ya huta, ni kam ban tab'a ganin kwarkwata me naci ba,kamar taki" Zumb'ura baki tayi tana k'okarin fuzge kanta tana fad'in"Ita bata yarda ba aske mata kai,, cikin wannan halin D'alha ya same su,, ya zauna gefen Iya yana mai da nuffashi,, Iya tace"Sannu da alama ka shawo rana, Allah yasa nagama abunci" Girgiza kai kurum yake, yace"Wallahi kuwa, Iya talaka shine babban abun tausayi a duniyar nan,, raza zafi haka zaka futa nema wataran ma ka futa baka samo ba" tace"Sai hakuri ai, Allah dai ya bamu rabo me amfani" Ameen yace" mik'ewa tayi tana fad'in"Bari in kawo maka ruwa da abunci""" Kallon Ladidi yake cike da takaici yace"Don ubanki babu sannu da zuwa ko, kin iya zuwa ki karb'i kud'in makatanta babu fashi""" Hannunta ta d'ora kanta ta soso ta soso ta ciro kwarkwarta har guda biyu ta ajiye kasa ta sanya farce ta kashe, abunta,, yace"Ba magana nake miki ba"" kallonsa tayi babu tsoro tace"Kawu Sannu da zuwa " Tsaki yaja yana fad'in"Kazamiyar banza kawai" Iya ta zauna tana aje masa langa, me d'auke da Dambu na tsaki yaji gyad'a da alayyawu tace" Kayi mata addu'a mana k'uruciya ce" Kofin ruwa ya d'auka ya kai bakinsa sai da ya sha sosai ya aje yace"Iya nagaji da ganin wannan k'azantar ta kwarkwata, yanzu ina futa zan siyo reza ayi mata k'wal kwabo idan kwarkwartar taga babu gashi, tayi nata guri". Tace"Wallahi nima shawarar da na yanke kenan" Ladidi ta mike da gudu ta shiga d'aki tana rusa kuka,, D'alha yace"Kyayi kya gama askin shine mafuta... Ya cigaba da cin abuncin sa. Sai da ya cinye Tass yayi hamdala ga Allah, mik'ewa yayi ya wanko hannunsa ya dawo ya zauna yana fad'in "Iya kin San wani abu kuwa" ? "A'a sai ka fad'a" yace"Yanzu da zan dawo dake ta sabon titi na biyo. Wallahi gonarmu da ta Jatau da ta Malam Manu me mutuwa, wani me kud'i ya siya ya had'a guri guda ana ta aiki a gurin sosai gurin yayi kyau , yanda naji masu aikin gurin suna fada wai gidan gona za'ayi mishi gorin hutawa da gurin kiwo gurin noman kayan marmari, kin San b'angaran Manu biyu ne akwai gurin da yake noma kayan marmari goba d'ata Lemo da sauransu,, to naga an kewaye gurin da wani k'arfe za'a cigaba da aiki ,nace"Allah ya huttashe dani na shiga in dunga sarowa cikin sauk'i". Iya tace"Alhamdulilahi, aikuwa ka huta wallahi"'" ammafa ni lamarin masu kud'in nan na bani mamaki, haka kurum saboda kudi na cizon su sai su k'irk'iri abunda bai dace ba, a maimakon su raba kud'in ga mabuk'ata" *COMMENT VOTE AND SHARE* [9/27, 10:30 AM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* *NA* _BINTA UMAR ABBALE_ ~*®BINTUBATULA👄*~ *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` _*LOODING:*_ _*{LADIDI K'WADAGA🌚}*_ _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain aur reades``` _______________________ _*DEDIGATED*_ *TO* _RAHAMA ALIYU_ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿9* Kawu D'alha yace"A'a Iya ba duka masu kud'in suke da Wannan halin ba, wallahi akwai masu kirki da taimakon jama'a" "Gaskiyar ka,, akwai sosoi" Mai koko tafad'a haka dai suka cigaba da hira kafin aka kira sallahr magariba D'alha ya nufi massalaci, Ladidi take tai wa magana tayi mata banza sai shek'ar kuka take,, itama sai ta k'yaleta kawai ta dauro Alwala domin yin sallah. ********* Monday, 12:00pm jirgin su Abdul Hakkim ya sauka,, Dady da Salim da Salima sai ware ido suke suna jiran suga futowar sa,, A hankali ya dunga saukowa, kana kallonsa kasan yana cikin farin ciki,k'ayataccan murmushi ne d'auke a kyakykyawar fuskarsa mai cike da kyau da kwarjini gami da nutsuwa,, yana sanye da suit Wanda sukayi masa bala'in kyau, k'afar shi sanye da rufaffan takalmi blck sai shaining yake,, kunnen shi mak'ale da eir pix,, hannunsa guda k'atuwar wayar sa ce, d'ayan kuma trolly d'insa ce yana jan ta, Salima ta rugu da gudu, tun kafin ta k'araso ya maida wayar aljuhu, ya bude hannunwan sa,, rungume juna sukayi, dariya take tana yi masa barka da zuwa,, da murmushi a fuskarsa yake amsawa yana d'an dukan bayanta, Salim ya k'araso gurin cikin farin ciki yace"Broth barka sannu da zuwa, trolly din ya k'arba daga hannunsa, Hakkim ya dafa kansa yana fad'in"Broth na dawo lafiya ammafa na zo da sabuwar reza sai na aske wannan gashin naka da yayi tozo a tsakiyar ka,, bakaji broth na hana ka irin wannan aski na "yan iska"" Salim yasa dariya yana fad'in"Humm Babban yaya kaima fa irin sa ne a kanka" Dokan kansa yayi yace"A'ina ya zama ina naka,, nawa daban naka daban" 'yar dariya Salim yasa yana Sosa kai, haka suka k'arasa bakin mota inda Dady yake tsaye yana sakin wani kyatattacen murmushi ganin yadda iyalinsa suke so da kaunar junan su,, rungume juna sukayi Hakkim yace"Dady na same ku lafiya"? "Lafiya alhamdullahi sai dai munyi kewar ka, da sa idon ka" Dariya yasa yace"Gani na dawo zan d'ora inda na tsaya mutukar naga ba dai-dai ba""" Dady yace"Ai naga alama gashinan har kafara wa Salim k'orafi" dariya sukayi gaba d'anyan su, suka bude mota suka shiga,, Direba yaja suka tafi. ******** Kwanuka da kofuna ne a jere, tun daga cikin gidan har zuwa soro, kowa naso layi yazo kanshi, har da maza a tsatstsaye a waje suna jira a mik'o musu, yawancin su masu wuce wa ne,, shine take d'aura musu a Leda,, duk wannan aikin ita kad'ai takeyi tayi-tayi da Ladidi ta futo ta taya ta tak'i dake yau alhamis babu makaranta, tana cikin daki tana jin haushi, saboda ko yau da safe sai da Kawunta ya kara maganar aske mata gashi, shine take gaba da Mai koko tak'i kula ta,, hayaniyar yara ce tayi yawa kowa yana ganin kamar za'ayi masa zure,,, da sauri ta bankad'a labule ta futo, fud'um-fud'um, kai tsaye hanyar futa ta nufa,, Sam Iya ba taga futuwar ta ba dake ta juya baya,, tana zuwa inda jerin kwanunkan suke, sai ta fara d'ebo na k'arshe tana mai dasu gaba, na gaba ta dawo dasu baya,, ta hargitsa layi,, Iliya yana tsaye yaga kofunsa ya dawo baya yace"Ke Ladidi mayar min dashi inda yake sai da kika ga an kusa zuwa kaina zaki hargitsa layi" kai tsaye tace"Bazan mayar ba" ruk'e k'ugu tayi tana kallonsa,, a zuciye ya nufi inda kofunsa yake yaje ya dawo dashi inda yake,, aikuwa bai gama ajiye shi ba,, ta d'auka tayi wurgi dashi waje,, takaici yasa Iliya kai mata duka, itama ta kai masa,, kafin kace kwabo fad'a ya rincab'e a tsakaninsu,, wata yarinya ce ta futo hannunta d'auke da kwano Wanda yake cike da koko sai turiri yake,an sallame ta,, babu zato Ladidi ta ingiji ta kokon ya kife a jikinta, yarinyar ta kurma ihu!!!"Wayyo Allah na""" Iya ta saki ludayin hannunta da sauri ta nufi soro,, Me zata gani, Ladidi da Iliya ne suke kokawa katitir! Duk da Iliya yake namiji wanda ya girmi Ladidi da shekaru kusan biyar, ya kasa yin galaba a kanta, duka take kai masa ta ko ina tana k'okarin tad'o k'afarsa da tata k'afar, in ka kalleta a lokaci sai ka rantse da Allah ba Ita bace, duk kamaninta sun sauya,sai naushi take kai masa tana cakumar sa,, Mai koko ta rasa gurin wanda zata nufa,, ga Aminoni tana Ihu!!! Koko ya k'ona ta,, ga Ladidiya can tana d'aban albarka. *COMMENT VOTE AND SHARE* [9/27, 5:17 PM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* *NA* _BINTA UMAR ABBALE_ ~*®BINTUBATULA👄*~ *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` _*LOODING:*_ _*{LADIDI K'WADAGA🌚}*_ _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain aur reades``` _______________________ _*DEDIGATED*_ *TO* _RAHAMA ALIYU_ _ALHERIN ALLAH YAZO INDA KIKE_ *NANA AISHATU KADUNA* _Hak'ika ina jin dadin comment dinki ubangiji Allah ya bar kauna,Aishatu inai miku fatan alkairi a rayuwar ki🥰_ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿10* Da k'yar Iya ta taimaka wa Aminoni ta cire rigarta ta goge mata jikinta tana ta faman yi mata sannu, ita ko sai sosa inda yake mata zafi take tana kuka,, baki na rawa Mai koko tace"ina ne yake miki zafi" ? Aminoni ta nuna mata k'irjinta da gefen hannun ta,aikuwa tana dubawa taga gurin yayi jajazur har ya soma tashi, cikin gida ta shige da sauri tana salati,,,,, zuwa yanzu mazan dake waje sunji abunda yake faruwa nan suka shigo suna aikin raba fad'a inda Ladidi ta dunga Kai musu duka tana zaginsu duk girman su kuwa, da yake duk sun san halinta,suka k'yaleta k'okarin su fuzge Iliya da tayi masa rik'on tsauri,, Iliya da ya samu ta sake shi sai yayi waje yana maida nuffashi,, ita ko Ladidi gefe ta koma tana haki! Bakin ta bai mutu ba, tana ta zagin Iliya da masu roban fad'a,, futa sukayi suna mamakin rashin kunyar ta,, bakin kofar ta tsare tana kallon Iliya tace"Wallahi baza a siyar maka da kokon ba, don haka kasan inda dare yayi maka,, bai ce mata komai ba d'auki kofunsa ya tafi,,, cikin takaicin na bata lokacin sa da yayi gashi gidansu duk sun fi son kokon Iya saboda ta iya ga gard'i da tsabta fari tass dashi yana k'amshin citta da kaninfari. Mai koko ta dawo hannunta dauke da wata roba ta kad'o omo a ciki tazo tana shafawa Aminoni a jiki tana mata sannu, Aminoni kad'a kai kurum take tayiwa Ladidi Allah ya isa babu a dadi domin babu damar ta fada a fili,, rigar Ladidi ta sanya mata, ta dauki kwanon kokon ta zubo mata wani,, har waje ta rakata tana mata sannu,, mutanan dake waje ta tsaya tana bawa hakuri, sannan ta koma ciki, ko takan Ladidi bata bi ba, ta cigaba da sallamr mutane,, haka suka hak'ura da hukuncin da Ladidi tayi musu na farko ya koma k'arshe na k'arshe ya koma baya ********** Hajiya Asiya na zaune kan kujera tana jiran isowar su,, tayi kwalliya tsab da ita ta shiryawa shalelen ta daining shi kadai kawai ake jira,,, tana jin shigowar mota gidan ta furta Kalmar "Alhamdulilahi, idonta a kofa har suka shigo,, da sauri ya cire hannunsa daga na Salima ya rungumeta yana fad'in" Mamana I miss you!!" Shafa kansa tayi tana murmushi tace"Nima haka my Son nayi kewar ka, sati biyu kacal sai suka zama kamar shekara a gurina" lumshe idonsa yayi yana jin d'umin mahaifiyar sa mai so da kaunar sa,, G.Abbas yace"Idan ya koma can da zama kuma yaya zakiyi gwara ma ki sawa zuciyar ki sauk'i" Hakkim ya zauna hannusa rik'e da nata yana kallon Dady din yace"Wallahi Dady saboda Mama zan iya hak'ura nifa da man bai wani dame ni ba,gwara in zauna a k'asata" Dady yace"Aikin gama ya Riga ya gama tunda kaje ka saka hannu lokaci kawai ake jira"" Hajiya Asiya tace"Tashi muje kaci abunci na mussaman" cike da farin ciki suka nufi gurin cin abunci dukan su.. Bayan ya gama cin abunci part d'insa ya nufa a gajiye ya fad'a toilet yayi Wanka ya futo daure da towol a jikinsa, ko mai bai shafa ba,ya zauna gefan gado yana latse-latse a wayar sa,, kira ne ya shigo yana dubawa yaga babban abokinsa Yusuf d'aga wayar yayi tare da fad'in "Ya akaiyi ne yaro"? D'ayan b'angaran Yusuf yace" Ganin kan hanya nasan dai yanzu all ready kana gida" Hakkim yace"Ina gida hutawa kuma zanyi karkazo ka dame ni da surutun ka na ala tsine" Yusuf na k'okarin kashe wayar yace"Idan nazo kar ka bude min kofa" Kitty!ya kashe wayarsa, Hakkim yasa Dariya yana fad'in"Lallai wannan bai da mutumci ni ya kashewa waya, anyway zai zo ya same ni""" mik'ewa yayi ya d'auko boxer da singlet Cikin kayansa ya saka ya fesa turare ya koma ya zauna inda ya tashi, latse-latse ya cigaba dayi da wayarsa.. Bugun kofa Yusuf yake yana jinsa ya share shi,, kiran wayarsa yayi ya kashe,wato ya rama kenan, Yusuf ya fi minti goma a tsaye sannan yaje ya bude masa kofa,, ya shigo cikin jin haushi yace"Wallahi mugun Dan wulakanci ne kai fa" kai tsaye yace"Waye yace ka kashe min waya, abunda na tsana a rayuwa ta" Yusuf yace"An kashe d'in, dallah kai kowa sai ka gwadawa iko da mulki to ni baka isa ba""Dariya Hakkim yake masa ya bashi hannu suka tafa,, Yusuf ya zauna yana fad'in"To yane akwai labari ne"? Tab'e baki yayi yace"Ni da na dawo ni za'a bawa labari ai" Gyara zama yayi yace"Aiko akwai labari fa""""" kallonsa yayi yana kanne masa ido,, doka ya kai masa yana fad'in"Bana son iskanci fa" Sosai Hakkim yake dariya yana fad'in "Ai nasan zance gizo baya wuce na k'oki labarin ka kullum akan abu d'aya ne,, kan wannan bak'yauyiyar budurwar taka da komai bata Iya shafawa ba"" Yusuf ya b'ata fuska yana fad'in"Bana son iya shege gwara ni ina da budurwa kai kuwa fa,ka tsaya tsoron mata dube ka don Allah gemai-geman da kai to wai in kayi auran ya zakayi da ita"" ? Ya k'arashe maganar yana dariya ta shak'iyan ci,, a kufule Hakkim yace"Uwar ka zanyi da ita d'an iska" dariya Yusuf yake har da kwanciya yace"Kullum sai sweet heart d'ina ta tambaye ka,,wai kazo ta baka kanwar ta" Duka ya kaima sa,, da sauri ya goce yana cigaba da masa dariya"" cikin jin haushi yace"Idan kaje kafad'a mata ni nafi k'arfin k'azamar kanwar ta"" Yusuf yace"Aikuwa zan fada mata wallahi,, kullum in muna hira ko a wayane ina bata labarin ka da yanda kake tsoron mace sai tai ta mamaki ita tana ganin kamar k'arya nake, a wannan zamanin akwai namiji me tsoron mace kuwa,nace ta kwantar da hankalin ta zan kawo mata kai har gida"" hararasa yayi yace"Taje tayi ta mamaki, kuma Wallahi idan baka daina bata labari na,, na rantse maka da Allah har a d'aura auranku bazan jebe". Yusuf ya mike zaune yana fad'in "Na daina ni da da nake so gobe ma ka rakani gurin ta""" tab'e baki yayi yana fad'in"Sai dai ka bari sai na dawo domin zan tafi Hutu ne"? "Ina zakaje Hutu kaji d'an iska"" Hakkim yayi wani k'ayattacen murmushi yana fad'in "Kano zani Dady yayi gidan gona wani k'auye shine nake ta zumud'i""" Yusuf yace"A'a kace zamu huta yaushe zamu tafi"? Kallonsa yayi yana fad'in "Zakaje ne"? Gyad'a kai yayi yace" K'warai kuwa""" kashewa sukayi suna dariya yace"Gobe nake so mu tafi"" Yusuf yace "Yayi Allah ya kaimu". *COMMENT VOTE AND SHARE* [9/28, 10:16 AM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* *NA* _BINTA UMAR ABBALE_ ~*®BINTUBATULA👄*~ *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` _*LOODING:*_ _*{LADIDI K'WADAGA🌚}*_ _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain aur reades``` _______________________ _*DEDIGATED*_ *TO* _RAHAMA ALIYU_ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *Ayi hakuri errow⚠⚠* *🅿11* Cikin kyakyawan shiri ya futo daga part dinsa , kai tsaye part d'in Mama ya nufa cikin nutsuwa yayi sallama, Mama da mai aikin ta Jummai suna tsaye suna shirya daining ta amsa fuska a sake take fad'in "Har ka shirya kenan"? K'araso wa yayi inda suke, da murmushi a fuskarsa yace" Tuntuni na shirya yanzu ma Yusuf nake jira,banason tafiyar rana" Mama tace"Yusuf ma zashi ne"? Zama yayi kan daya daga cikin kujerun cin abunci yana fad'in"Jiya daga ji ina zancan yace shima zashi" Salima dake zaune can falo tace"Babban yaya nima zani don Allah" hararata yayi yace"Babu inda zani dake" Mama tace."Kai kuwa kaje da ita mana dama sunyi Hutu". Yace. "Mama kin san ko kwana zamuyi kuwa"? Girgiza kai tayi tana fad'in" Sai ka fad'a". "Sati biyu zamuyi fa" Mama tace"To meye a ciki ka tafi da ita kawai" shiru yayi baya son musu da Maman shi, Gen.Abbas ne yake saukowa daga bene yana sanye da jallabiyya ruwan toka hannunsa rike da Jarida ta Daily trus, idonsa farin galashi ne, zama yayi suna gaisawa Mama ta fara had'a musu Kalaci, bayan sun kammala Hakkim yace."Dady na fa shirya" Gen. Yace. Na gani ai daga dawo wa zaka k'ara tafiya jiya munyi waya da masu aikin komai ya kammala, mybe yau zasu bar gurin amma dai na fada musu su zauna sai kazo". Yace. "Dady yanzu ma Yusuf nake jira tare zamu tafi". Salima ce ta futo cikin shiri sai murna take hannuta rike da trolly d'inta ya loda uban kaya, Dady yace." Ke kuma fa"? Narai-narai tayi da ido, Mama tayi saurin cewa"Tare zasu tafi" ."Shine ta lodo kaya Cikin jaka kamar wacce zata bar gari" tsuro-tsuru tayi, Hakkim ya buga mata tsawa! Tare da fad'in"Maza je ki rage kayan nan idan ba haka ba wallahi inki zuwa dake". Da gudu ta koma dakinta ******** Ihun!! Ladidi ne ya cika gidan,inda har daga waje ma ana jinta, sai zageye tsargidan take tana buga tsalle Mai koko na bin ta sai ta kamata,hannuta rike da sabuwar reza cikin takardar ta,fad'i take" Baki tsaya ba ko Ladidi ki daina wahalar dani, gwara ki tsaya a aske miki gashin kema kya huta da wannan azababbiyar kwarkwatar da ta dame ki". Ladidi tace"Wallahi ba zaki min aski ba,haka kurum sai kice sai kin aske min gashi ne,ina ruwanki da kwarkwatata ki bar min kayata mana, Mai koko tayi kanta da sauri zata damk'e ta, ta buga wani uban tsalle! Sai gata ta tsallake rijiya da baya!! A gigice Mai koko take salati, babu shiri taje ta aje rezar tana fad'in"Kinga na aje rezar futo daga bayan rijiyar Ladidi"mak'e kafad'a tayi tana fad'in"Wato in futo ki kamani,wallahi na gadama sai in fada rijayar ma" Sanin rashin hankali da gab'unta na Ladidi yasa Mai koko ta fara rarrashin ta da dadad'an kalamai, tace."Kinga d'azu munyi magana da Mairo mai dashi cewar zata bani d'auka ta uku shine nace da ta bani zan shiga kasuwar burni na siyo miki kayan kallo" Ladidi tasa dariya tana fad'in"Nagane wayo zakiyi min, ni sai na fad'a a rijayar ma" tayi taga-taga!! Kamar zata fad'a!Mai koko ta rafka salati zaninta na k'okarin fad'uwa tayi waje da sauri ko ina zata oho"! Dariya Ladidi take mata, ta buga tsalle ta futo daga bayan rijiyar, can wani guri da ya rushe Cikin gidan taje ta b'oya dake tunda gurin ya rushe babu mai zuwa gurin,Mai koko ta dawo ciki tare da wasu mutane biyu ita a nufinta su taya ta bawa Ladidi hakuri, wayam! Babu ita a gurin, Wani irin salati Mai koko ta kurma tayi bakin rijiyar gadan-gadan tana fad'in"Shikkenan ta fad'a cikin rijiya dama nasan Halin ladidi kome tace zatayi sai tayi, kuka ta farayi tana kara zura kanta cikin rijiyar, sai akayi sa'a tarwad'ar dake cikin rijiyar suka dunga motsi a ciki, kuka sosai Mai koko take tana fyace majina tace"Kunyi tsaye meye amfanin ku, kuzo Ku shiga Ku d'auko ta,Idan ma mutuwa zatayi ta mutu a gabana" Kallon juna sukayi suka kama hanya futa suna fad'in"A'a Mai koko bari dai mu garzaya mu kira miki sarkin ruwa, wannan yarinyar me k'wamk'wamai watak'ila ma su suka jata ta fad'a ciki, haka kawai mu shiga su kama mu, domin ita suna iya sakin ta, tunda tasu CE"Mai koko ta saki baki har suka fuce. Suna futa d'aya yace."Allah yasa ma su kaita bakin ruwa su d'auke kayan su kowa ya huta da masifa". Mai koko ta lek'a rijayar tana fad'in"Mai yasa zakiyi min haka Aminatu mai yasa zakiyi min ke kad'ai nake kallo a matsayin Aminu shine zaki fad'a rijiya Haba Ladidiya kiyi hakuri da halina da halin Kawun ki, majina ta fyace! da gefen zaninta sai zura kanta take cikin rijar tana sambatu! Ladidi ta lek'o daga kanta ta wata 'yar kafa sai dariya take yiwa Mai koko ganin yadda take kuka tana fyace majina dariya har sai da ta kwanta. Kafin kace kwabo labari ya bazu a cikin unguwar Ladidi ta fad'a rijiya wasu suyi jaje wasu suyi ko murna suke cewar an rage mugun iri, D'alha na gurin sana'ar sa labari ya riske shi, babu shiri ya tawo gida ko kayan sana'ar bai d'auko ba, Mai koko kuwa ganin kamar tana son fad'awa cikin rijiyar yasa mak'otan ta suka nufi gudansu da ita sai sambatu take, hakan ya bawa Ladidi damar futowa daga mab'oyar ta tayi waje a guje! Kanta ko d'ankwali babu,wani abun mamaki da al'ajabi idan ka kalli gashin nata sai ya baka tsoro domin Duk ya dunk'ule ya cure guri guda yayi wata muguwar dauda ga tsakin kwarkwata da amosani man burjiki! Wani gurin sal-sal babu d'igon Gashi wani gurin da akwai, ita kanta idan tana sosawa ciro gashin take da hannunta ta yar. *Ni kaina sai da nace Ladidi da kin sani kin bari anyi miki aski domin shine mafuta a gare ki* Can hanyar titi ta nufa tana fafara gudu kamar mahaukaciya, ko da wasa babu wanda ya ga gilmawar ta. Sarkin ruwa tare da jama'ar gari suka shiga cikin gidan, jin ance ga Sarkin ruwa nan yazo yasa Mai koko futowa daga gidan da take da sauri duk tayi wujuga-wujuga, suka had'u da D'alha sai gumi yake zabgawa babu wanda yace da Dan uwa sa komai suka afka cikin gidan, To duk iya lalube Sarkin ruwa yayi amma bai ga Ladidi ba kusan awarsa guda a cikin ruwa ya futo yana fad'in"Da Ladidi tana cikin rijiyar nan to ko da na ganta domin na baje basira ta sak'o da loko, kogo da kogona babu inda ban duba bata ciki". Guri yayi Tsitt!! D'ai-d'ai jama'a suka fara futa suna surutu cewar "dama tuntuni suna zargin yarinyar " yar ruwa ce to gwara da suka d'auke kayansu kowa ya huta. *********** Tafiya suke suna hira irin ta abokai sai dariya suke ma junansu Salima na bayan mota da waya a hannunta tana chat fa friends d'inta, sam bata jin abunda suke cewa to suma k'asa-k'asa suke hirar su, har suka shigo Kano suka d'auki hanyar K'auyan d'an kunkuru Yusuf yace"Har na fara jin wata iska me dad'i wallahi" Dariya Hakkim yayi yace." Sai ma ka shiga garin sosai zakaji dad'insa shiru babu hayaniya sai manya bishiyu masu bada iska mai dad'i". Wani dank'areran get nake hangowa tunda nesa nan naga Hakkim ya nufa da mota, wasu mutane dake tsaye bakin gurin suka bud'e masa get d'in ya shiga da motar ciki, sai da yayi tafiya sosai sannan ya samu guri yayi parking Yusuf ya futo daga motar yana fad'in"Wow kaga guri sai kace a k'asar waje Yaro" ? Murmushi Hakkim yayi ya kashe motar futowa yayi yana mik'a ta gajiya gurin kawai yake bi da kallo cike da sha'awa irin bokokin nan na k'asar waje hudu ne sai part biyu da gurin kiwo an kewaye shi na kaji daban na kifi daban na talo talo daban ko wanne an kewaye shi, gefan hannunsa kuma wasu manya-manya lambu ne a kewaye da raga k'ofar da mutum zai shiga tana can baya, da sauri yaja hannun Yusuf suka nufi gurin shiga Salima na binsu a baya tana tsalle da dariya fad'i take"Zanci d'ata in more abuna dama a abuja babu sai mutum ya sha wahala kafin ya samu. Suna shiga kowa ya kama gabansa domin kashe kwarkwatar idonsa , Hakkim ya nutsa sosai ciki, yaji motsi saman bishiya d'aga kai yayi da sauri, wata halitta ya gani ita ba mutum ba ita ba aljana ba, gabansa ya fad'i, dake namijin duniya ne sai ya dake yana hirji cikin zuciyarsa cikin jarumta yace"Ke wacece ke mutum ko aljana"? Ladidi ta tsura masa ido tana kallonsa,a zuciyar ta tace"Dube shi kyakyawa d'an burni yasa fararan kaya gaskiya yayi kyau"!! Buga mata tsawa! yayi a karo na biyu ya sake fad'in"Mutum ko aljan nace kun tsura min ido babu kyawun gani kuna kallo" Soso kanta tayi ta ciro kwarkwata har biyu, ta kalle shi ya kalle ta daga saman bishiyan ta sako masa kwarkwartar ta fad'o jikinsa, abunka da fararan kaya, aikuwa nan take suka nuna kwarkwata ga tanan tana bin gefen kafad'ar shi har guda biyu, tsalle! Ya buga ganin k'awaro baki na bin jikinsa ya bugeta cike da k'yamkyami ya tsartar da miyau! Ya d'ago kansa a fusace! Ganinta yayi mak'ale jikin bishiyar tana k'okarin sakkowa kamar me sufa, dura k'asa tayi yayi sauri matsawa baya gaban shi na bugawa! Amma idan ka kalli fuskarsa baza ka gane razanar sa ba,, cikin minti biyu ya gama k'are mata kallo, k'anjamammiyar yarinya mai k'irar muciya kanta wani gurin da gashi wani garin babu fuskarta a rame sai uban dogon hanci irin na aljani ga hannuta da k'afar ta k'ananu duk jijiya" hirji yake Cikin zuciyar sa, yace."Ke aljana ce ko mutum"? Kai tsaye tace"Aljana ce" Cikin tsawa yace"Bar nan yanzu don ubanki ko na zane ki, dagani ke ba aljana bace ibilishiya ce,me ya kawo nan har da hawa kan bishiya" ? "kar ka k'ara zagina" tafad'a idonta a kansa, a zabure! Yace"Ubanki uwarki kajini da shegiyar yarinya k'azama zo ki fuce daga gurin nan ko in karya miki k'afafu" ya k'arashe maganar yana zuwa kanta, wani tsalle ta buga! Ta d'ane jikin bishiyar mangwaro can kololowa, cikin mamaki ya d'aga kai yana kallonta, itama shi take kallo tace." Idan ka isa kazo ka Kore ni, bayan ma gonar ta kakana ce kuka sace mana" Hakkim ya saki baki galala! Yana kallonta ,wasu mangwaro ta Ciro sun gaji da nuna ta mulmulasu sukayi ruwa tafasa da bakin ta ta saita shi, ta jefo masa a jiki kafin kace me yayi fallatsi ya b'ata masa duk gaban rigar sa da fuskar sa. *COMMENT VOTE AND SHARE* [9/29, 6:51 PM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* *NA* _BINTA UMAR ABBALE_ ~*®BINTUBATULA👄*~ *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` _*LOODING:*_ _*{LADIDI K'WADAGA🌚}*_ _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain aur reades``` _______________________ *DEDIGATED* *TO* *RAHAMA ALIYU* _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *Ayi hak'uri da errow⚠* _Yau pege d'in babu yawa saboda ina fama da zazzab'i, ina b'ukatar addu'ar ku😓👏🏻_ *🅿12* Cikin tsantsar b'acin rai! Ya d'aga kansa sama yana kallonta, tana k'okarin saukowa sai dariya take k'yalk'yala masa, tana dura k'asa ya cafki hannunta wanda yaji tamkar ya rik'e bushashan ice dan tauri, k'okarin fuzge hannunta take tana zabga masa harara tamkar idonta zai fad'o k'asa!. A fusace! ya kai mata wani wawan mari! ta kauce da sauri! amma duk da haka sai da ya samu gefan fuskar ta, zagi ta hau d'ura masa tana tsalle, kamar zata kai masa duka take fad'in "Sakar min hannuna ni ba " yar iska bace". Hakkim ya buge mata baki da d'aya hannun nasa, kafin kace kwabo jini ya fara zuba, ihu! ta kurma wanda yasa su Yusuf suka runtumo da gudu gurin. Hakkim na tsaye hannunsa tam! da na Ladidi sai buge-buge take tana kwanciya a k'asa dole sai ta k'wace daga hannunsa, wawan hauri ya kai mata da k'afar shi guda, ta k'ara k'wala k'ara tana kuza masa ashariya! Yusuf ya k'araso gurin, hankali a tashe yake fad'in"Wai meye yake faruwa ne? wannan yarinyar fa, daga ina".? Bak'in ciki da b'acin ya hana shi cewa uffan,sai cije baki yake yana dukanta da k'afar sa, Salima ta k'araso gurin jikinta a sanyaye take fad'in"Broth waye ya b'ata maka jiki da wannan k'azantar " Yusuf ya Kai dubansa gurin shi sam bai lura ba, hankalin sa na kan Ladidi, har hanzu hannuta na rike a nashi yana dukanta da k'afafunsa ita kuma bakin ta bai bar zaginsa ba, tana deb'o k'asar gurin tana watsa masa a jiki. Yusuf ya fara k'okarin kwace daga hannunsa, ya fuzge da k'arfin yayi wani mugun boll da ita ta gangara can gurin k'ofar futa kanta ya bugu da wani dutse, da sauri ta mike tamkar ba ita akai wa wannan dukan ba, wani mugun tsalle tayi sai gata a gabansa, dama ya tsammaci zuwan ta, k'afar sa ya sanya ya tad'eta! Ta fad'in a gurin a sume!! Yusuf ya saka salati yana fad'in"Shikkenan kaga ka kashe yarinyar mutane ko, innalilahi wa'inna ilahi raji'un"!! Salima ta fashe da kuka tayi kan Ladidi tana tattab'a jikinta, Yusuf ya futa daga gurin da sauri, gabansa sai fad'uwa yake, ashe k'addara ce ta kawo shi, shi ko Hakkim ko a jikinsa, karkad'e rigar sa yayi cike da bak'in ciki da b'acin rai! Yake k'okarin barin gurin,Salima ta rik'e hannunsa tana kuka take fad'in"Broth ina zakaje LA tsaya ka duba wannan yarinyar ko suma tayi don girman Allah, ni kam Wallahi da nasan haka zata faru da ban biyo ka ba" . Fuzge hannunsa yayi cikin b'acin rai! Yace"Yanzu ma kina iya komawa gida babu Wanda ya rike miki k'afafu ga hanya nan" yana gama fad'in maganar shi ya futa daga gurin. Karo suka ci da Yusuf ya tawo da sauri hannunsa rike da robar ruwa na faro, ko kallonsa bai yi ba yayi fucewar sa. *COMMENT VOTE AND SHARE* [9/30, 10:08 AM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* *NA* _BINTA UMAR ABBALE_ ~*®BINTUBATULA👄*~ *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` _*LOODING:*_ _*{LADIDI K'WADAGA🌚}*_ _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain aur reades``` _______________________ _Alhmdullahi jiki yayi sauk'i_ *Gaskiya naji dad'i sosai da kularwar ku akaina nagode masu kirana a waya kuna yimin ya jiki da fatan samu lafiya,masu min sannu ta pravite wanda na sani da wanda ban sani ba nagode sosai da sosai ina muku fatan alkairi* *Jan kunne⚠* _Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin book d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ ki siyar min da littafi ba da sanina ba, Wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan haka, hattara dai!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje yaci gumin sa, kane mi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka_ *DEDIGATED* *TO* *RAHAMA ALIYU* _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿13* Cikin sauri Yusuf ya k'araso gurin da Ladidi take kwance, ya bud'e ruwan,ya fara zuba mata a fuskar ta furgice! ta mik'e zaune ta k'wala k'ara! Waige-waige take tana neman Hakkim a gurin, Salima ta rik'e hannunta tana son tayi mata magana. Fuzge hannunta tayi da sauri ta mik'e tsaye tana fad'in" Yana ina."? Duk suka mik'e suna kallonta, Yusuf yace." Ke yarinya me ya shigo dake gurin nan?,da har kika jawo wa kanki suma." Banza kallo tayi masa ta murgud'a bakinta, bata ce masa komai ba, ta bar gurin bagazan-bagazan! kallo suka bita dashi, Yusuf ya kalli Salima yace." Anya kuwa yarinyar nan me lafiya ce"? Salima ta k'unshe dariya tace." Lafiyan ta lau. Kamar ka manta da a k'auye kake dole kaga haka." Yusuf ya girgiza kai yace." Ni abunda ya bani mamaki da ita shine yadda ta shigo gurin nan wallahi". "Gaskiya nima nayi mamaki." Salima tafad'a yayin da suke k'okarin futa dafa gurin. ******** Ta inda ta shiga gurin tanan ta haura ta futa Hakkim na kallonta tun futowar ta har lokacin da take haure katangar yana gani, zuciyar sa yana mamakin ibilicin yarinyar, yau d'in nan zai sanya a kewaye katangar gurin, da waya mai k'ayoyi, duk saboda ita dole kuma a zuba masu gadi a gurin. tuni ya cire kayan da ta b'ata masa ya watsar dasu harabar gurin, domin mugun k'yamk'yami ne dashi, idan ya tuno halittar yarinyar sai yaji zuciyarsa tana wani irin tashi! sosai zuciyar sa take masa zafi, tunda yake a rayuwarsa babu wanda ya tab'ai masa irin abunda yarinyar tayi masa dole ne ya d'auki mataki akanta mutukar ya kara ganin k'afarta a gidan, karya ta zaiyi kawai kowa ya huta. Su Yusuf suka k'araso gurinshi ya sha kunnu domin baya son ma yayi masa maganar, Simi-simi Salima ta shiga ciki, Yusuf ya samu kujera ya zauna yana kallon Hakkim d'in, da yake k'ara yin kicin-kicin da fuska, yace." Zauna zamuyi magana da kai". A fusace! Ya juyo yana fad'in"Ubana ne kai zaka bani umarni". Yusuf ya kalleshi , da alama zuciyar sa har yanzu batayi sanyi ba. Yace." A'a ba ubanka bane". "To ka fad'i duk abunda zaka fad'a kunne na yana ji". Ya k'arashe maganar yana juya masa baya. Yusuf ya mik'e ya k'arasa inda yake, kafad'arsa ya dafa cikin taushin murya yace." Aboki wai me ya faru tsakanin ka da yarinyar nan? Wallahi hankalina ya tashi sosai domin ta dad'e kafin ta farfad'o,haka kurum daga zuwanmu guri zakayi kisan kai saboda zafin zuciya". Hakkim ya juyo yana fuskantar sa, cikin kaushin murya ya fara fad'a masa abunda ya faru. Yusuf ya sauke ajiyar zuciya yace." Gaskiya kam yarinyar ba tayi maka dai-dai ba,amma kai ma bai kamata kayi mata irin wannan dukan ba,saboda yadda na lura da ita kamar irin yaran nan masu lalurar k'wak'walwa kasan k'auye ko d'ansu na cuta basa mai da hankali sai abu yayi tsanani, sannan zaka gansu sun nufi asibiti hankali a tashe." Zuciyarsa ce fara sanyi ya zauna kan kujera guda Yusuf ma ya zauna kusa dashi, yace." Ka bari kawai Yaro wallahi zuciyata a lokacin ji nake tamkar na kashe ta na huta da b'akin ciki." "Kayi hakuri don Allah ka rage zafin zuciya." Yusuf yafad'a yana dukan kafad'unsa. Salima ya k'walawa kira, tana can ta shagala da kallon yadda aka tsara falo da kayan jin dad'i da more rayuwa, har ta kunna kallo tanayi taji kiran big broth amsawa tayi ta mik'e da sauri, tana zuwa yace." Ki shiga kchin kiyi mana abunci." "Angama big broth" tafad'a cike da bin umarni, kai tsaye kichin d'in ta nufa, gashinan komai akwai na amfani nan take ta fara aikinta. ********** To can gidan su Ladidiya kuwa Mai koko ta saddak'ar ta fawwala wa Allah cewar Ladidi ta mutu cikin rijiyar don haka mutane sun cika gidan ana yi mata ta'aziyya, Jama'a sun kewaye ta, tana zaune da carbi a hannu ga idonta yayi jajazur! taci kuka ta k'oshi, D'alha na waje da mutane zazzaune kan tabarma, sam yak'i yadda cewar Ladidiya ta mutu cikin rijiya k'wak'walwar sa tafi tunanin yarinyar tana can gurin gantalin ta, shiyasa ya kasa zaune ya kasa tsaye sai zurga-zurga yake a gurin. Duk Wanda yazo gurin sai ya hau yi masa gaisuwa, ko kallon su baya yi ********* Tafiya take fakam-fakam!! sak'e-sak'e kawai take a zuciyarta da tunanin d'aukar fansa kan, d'an burni,sunan da ta sama sa kenan, wallahi bai dake ta a banza,sai ta rama duk hanyar da zata bi ta sani, leb'anta ta tab'a da hannunta, cire hannuta tayi tana girgiza kai! a fili tace."Wallahi he na rama idan ubanka ne shugaban k'asa he na rama, nima sai na fasa maka baki,hummm!! Zaka san ka tab'o Ladidi jikar Mai koko, bana barin takwana kuma bana manta ranar d'aukar fansa." Da tafiyar ta ya gane i tace jiki na rawa ya k'wala mata kira,"Ladidi" da sauri ta juyo tana waigen idan taji ana kiranta. Kakanta ne D'an fulani, yake tawo wa inda take, yana can gurin kiwo labari ya same shi na mutuwar ta,shine ya tawo cikin tashin hankali! Abun mamaki kuma sai gashi ya ganta a hanya, yana k'arasowa inda take ya damk'i hannuta, bai ce mata komai ba suka fara tafiya, zub'uro baki tayi tace." Ni ka sake ni ka rik'e min hannu da k'arfi ai gida zani ba wani guri ba." D'an Fulani yayi mata shiru, shi dai k'okarin shi kawai yaga ya danganata da gida,hankalin kowa ya kwanta. Tun daga nesa jama'ar dake gurin suka hango tawowar su, sai aka fara kallon-kallo tsakanin su, da suka tabbatar da cewar itace sai kowa ya fara zura silafas d'insa yana guduwa, D'alha ya juya yaga wayam! babu kowa a gurin, girgiza kai kurum yayi yana jin wani d'aci cikin zuciyarsa wato Ladidi ta zama abun tsoro kenan? D'an Fulani ya d'amk'ata a hannunsa yana fad'in"Gatanan can wajejan titi na gano ta tana tafiya ita kad'ai." D'alha ya sauke ajiyar zuciya yace."Alhamdullahi, dama ni jiki na bani yarinyar nan tana raye,amma jama'ar gari suna ta fad'in ta mutu a cikin ruwa,Allah nagode maka daka bayyana mana ita ko hankalin Mai koko ya kwanta." Sai sanan Ladidi ta tuna da abunda ya faru d'azu tsakaninta da Mai koko, dariya ta kece dashi,hahahaha! D'alha ya gaura mata mari! Yana fad'in"Rufe miki don buhun ubanki, shashasha, shakatafe, naga ranar da zakiyi hankali dai" D'an Fulani kuwa a'lamarin Ladidi ya fara bashi tsoro,don haka yace."D'alha mu shiga cikin gidan sai mu San abun yi." Kai tsaye cikin gidan suka shiga. *Tofaa ko ya zata kasance idan jama'ar gidan sukaga Ladidi Wanda suka dauka ta mutu cikin rijiya,ko yaya Mai koko zatayi in taga Ladidi? To Ku cigaba da bina dai cikin labarin domin in warware muku* *COMMENT VOTE AND SHARE* [10/2, 5:54 AM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` *LOADING:* *{LADIDI K'WADAGA🌚}* _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain our reades``` _______________________ *ALHAMDULLAHI* *HAUWA S ZARI'A* _Maman Usuwan_ *Ina taya ki murnar kammala littafin ki HAKA ALLAH YA NUFA _KADDARA TACE_ ALLAH YA KARA BASIRA YASA SAKON KI YA ISA INDA KIKE SO* ____________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_ *DEDIGATED* *TO* *RAHAMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM* *🅿14* Suna k'okarin shiga da ita cikin gidan tana turjewa D'alha ya kwad'e mata k'eya yana fad'in "Zaki wuce muje ko kuwa,? Kin tayar wa da mutane hankali, gidan buhun ubanki zaki je ne" Ihu! Ta kurma, wanda yasa Mai koko da sauran jama'ar gidan mik'ewa tsaye da sauri sukayo waje suna salati! Kafin su rufe bakinsu, sai ga Ladidi an shigo da ita tana turjewa! Mai koko ta bude baki zatayi magana D'alha ya katse ta hanyar cewa." Don Allah kar Ku tsorata da ganin ta, dama na fada muku tana raye bata mutu ba, ga shi a can bakin titi d'an Fulani ya gano ta,wanda shima labari ne ya riske har inda yake kiwo cewar ta mutu." Mai koko ta k'araso gurin da jiki a sanyaye zuwa yanzu itama ta fara tsorata da al'amarin Ladidi, da muryar ta wacce tasha kuka ta gaji tace. " Ladidiya dama baki fad'a rijiya ba, me yasa kika yi min haka Ladidi"? Turo baki tayi tace." Nifa ban fad'a rijiya ba, kinga gurin dana b'uyar miki fa" Mai koko tabi hannuta da kallo, cike da mamaki da al'ajabi Matan da suke tsatstsaye a gurin, duk suka tsure sai zare ido suke burin su kawai su bar gidan, Mai koko tace." Me yasa to duk aka duba ba a ganki ba"? Shiru tayi mata, D'alha ya dubi matan dake tsatstsaye, yace." Ko wacce tana iya tafiya" aikuwa kafin kace kwabo duk sun zura takalman su, suna bangazar juna suka futa daga gidan, ko wacce cikin ta ya d'uri ruwa. D'an Fulani yace." Ku zauna zamuyi magana ta fahimta" Mai koko taja hannun Ladidi suka zauna kan tabarma. D'alha suka zauna gan benci, D'an Fulani ya kalli Mai koko a nutse yace." Al'amarin yarinyar nan ya soma bani tsoro saboda haka na yanke wata shawara." Mai koko tace." Ai kana da iko akanta tunda kai ka haifi mahaifiyar ta." Yace." NA yanke shawarar cewa gobe insha Allahu zan kawo malamin ruk'iya zai yi mata idan da makarai a jikinta sai a sulhun ta dasu" Shiru tayi na minti biyu, ta d'ago kai tana kallonsa, tace." Ba wai nak'i taka bane, gaskiya ka janye maganar ruk'iyar nan,domin su wad'annan mutane ba a haka dasu, idan kuma basu suka rab'e ta b,kaga sai a jawo mata su da hujja, abar maganar ruk'iya mu cigaba da yi mata addu'a" Dan Fulani da D'alha suka kalli juna, girgiza kai kurum D'alha yake yasan dama Mai koko baza ta yarda ba, shi ko D'an Fulani saboda tsabar haushi da takaici bai sake cewa komai ba. Ya mik'e yana musu sallama, sama-sama Mai koko ta amsa masa, D'alha ya mik'e domin ya raka shi. Mai koko ta dinga rarrashin Ladidi, da lallab'ata tamkar ba wacce tayi mata laifi ba, tace." Tashi ga ruwan zafi can muje kiyi Wanka ko"? Mak'ale kafad'a tayi. Tace." Akwai miyar kifi nan a fulas na aje miki sai ki siyo buredi" Mik'ewa tayi zaune tana Sosa kai tace." Amma ni zanyi wanka na gaskiya" tace." E amma zan cud'a miki baya." Mik'ewa tayi tana tube kayan jikinta ita kuma ta nufi kicin din, bakin rijiya ta tsuguna tana wasa da ruwan Wanka, Mai koko ta k'araso da abun sabulu a hannuta tace."Ladidi waye ya fasa miki leb'e haka? Ko garin tsalle-tsallen ki ne"? Hannuta tasa ta shafo gurin, girgiza kai tayi tace." Wani d'an burni ne, kawai babu abunda nayi masa don zalin ci." "A'a Ladidi nasan halin ki fa"? Iya tafad'a tana murza sabulu jikin soso. " Kawai don na shiga gonarmu shine ya doke ni" "Wace gona kuke da ita Ladidi'? Iya. Ta fada cike da mamaki! " Ranan da zamu wuce Kawu ya nuna min gonar tun kafin a gina gurin yace."Tasu ce da babana." "To yanzu na gane inda kika dosa" Iya tafad'a tana durzar jikinta da soso, ta cigaba da cewa " Ladidi kin cika futuna me ya kai ki gurin nan, yanzu bs gonar su bace, domin sun siyar da ita dalilin haihuwar ki, ranar bakiji Kawun ki yana fad'in wani mai kud'i ya siya har da tasu Malam Tanimu da Manu ba" girgiza kai tayi tace." Ni babu ruwana ko sun siyar ko basu siyar ba, in naga dama zanje ne" Mai koko tace." To sai ki kiyaye domin mutanan burni ba dai-dai suke da na k'auye ba." Zumb'ura baki tayi tace." Aiko sai na rama abunda yayi min ko shugaban k'asa ne ya haife shi." Mai koko dai shiru tayi domin bata so ta tsanan ta mata kar ta sake guduwa. Kawu D'alha kuwa akwai abunda ya k'udura a ransa kan Ladidi. Sai da ya tabbatar da sunyi bacci sannan ya shigo gidan, kai tsaye dakin Mai koko ya nufa, dama duk ranar da tayi ibilincin ta. To in ta kwanta bacci bata motsawa sai gari ya waye, Mai koko ma bacci take sosai ansha fargaba an gaji, reza ya futo da ita daga cikin aljinunsa ya kwance d'aurin d'ankwalin Ladidi a nutse a shafa sabulu da ruwa ya soma yi mata aski babu abunda ya dame shi. Har D'alha ya gama aske mata kai bata motsa ba, ya mayar mata da dankwalin ta ya daure mata kanta kamar yanda tayi, ya sunkuya ya tattare gashin da zube k'asa ya zuba cikin leda shara ya zuba yasa omo ya wanke hannunsa tass!!! . Ladidi bacci tayi sosai da sosai sam bata san inda kanta yake ba, sai wajan shiga da rabi na safe ta tashi lokacin Mai koko ta Dade da tashi tana can tana hidimar huta huta domin ta d'ora ruwan kuka. D'ankwalin ta take laluba kan shinfid'ar ta d'auka zata d'aura akanta tana tab'awa taji sumul tamkar gwiwa hannuwa biyu tasa tana shafawa, Ihu!! Ta kurma tana fad'in "Wayyo!! Mai koko wani ya aske min kai na" Mai koko ta aje icen dake hannunta da sauri ta nufi dakin. Tana shiga taga Ladidi ta d'ora hannu aka tana kurma ihu! Ga kanta sumul! Babu k'wallin gashi ko d'aya, cikin mamaki tace."Ladidi waye yayi miki k'wal kwabo hak..... Kafin ta k'arasa muryar D'alha ta katse ta inda yake cewa." Iya nine nayi mata aski saboda in cika rantsuwa bayan haka kuma da wahalar da ta bamu jiya, shiyasa na yanke wannan hukuncin a kanta." *COMMENT VOTE AND SHARE* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` *LOADING:* *{LADIDI K'WADAGA🌚}* _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain our reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_ *DEDIGATED* *TO* *RAHAMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿15* Mai koko tace." To kinji inda maganar take, don haka sai kiyi hak'uri kinji da kunnen ki,wanda ya aske miki kanki." D'alha ya kalle ta cikin taikaci ya buga mata tsawa tare da fad'in."Rufe min baki ko inzo k'ara fasa miki shi,shashasha kawai!! Gum! tayi da bakin ta dama kukan babu hawaye sai dai ihu! Sai dai kana kallon idonta kasan tana cikin b'acin rai! Yarinya 'yar shekara goma sha biyu ta san d'aukar fansa, abunda take ta raya wa kenan cikin zuciyar ta Kawunta da d'an burni sai ta rama abunda sukayi mata. Mai koko ta kalleta ganin yadda take ta sauke ajiyar zuciya yasa ta sassauta murya tace." Yanzu ke kanki zaki ji dad'i kuma iska zata shiga kanki sosai kinga kin rabu da kwarkwata har abada,domin wani sabon gashi ne zai futo miki." Banza tayi mata. Kawu D'alha ya futa ya barsu a d'akin, Mai koko dai da taga tak'i kulata sai ta futa ta k'yaleta tana addu'ar kat Allah yasa ta b'ullo da wani abun kuma. Aikuwa futowa tayi babu d'ankwali a kanta nufi gidin rijiya, 'yan siyan koko suka bita da kallo, tuni wasu daga cikinsu suka fara futa waje cikin tsoro ganin kan Ladidi a cikin rana sai k'yalli yake, Mai koko tace." Ya kuke futa kuma kowa ya tsaya a sallame shi." Wani Yaro yace." Iya wacece wacan kamar Ladidiya ko." Iya ta kalli inda Yaron yake nunawa Ladidi ta gani da buta a hannu tana durzar bakin ta da dakakkaken gawayi kanta sai k'yalli yake cikin hasken ranar da ya fara futowa, cikin takaici tace." Ladidi ke ko kika futo babu Dan kwali ko kunyar k'awayen ki baza kyaji, ki koma ki dauro dan kwalin ki." Kuskure bakinta tayi tace." Daga yau na bar d'aura d'ankwali wallahi haka zan dinga yawo da kai na, kuma duk yaron da ya tsokane ni, inci Ubansa." Jiki a sanyaye Mai koko ta juya ta cigaba da abunda take cikin zuciyar ta take fad'in"Ba a rabu da bukar ba an haifi Habu,dama ni nasan wata futunar zata k'ara b'ullo da ita." Tana gama Alwalar ta bar gurin. Wani tsohon buhu ta kwance nan kayan ta na sawa suke ta ciro wata doguwar riga irin ta kanti duk taji jiki dan wani gurin ma d'inkin ya soma zarewa gashi ta tattare sosai ta d'angale mata duk k'waurinta a waje ta saka, ta zura hijabin da take sallah ta tayar da sallah.Bayan ta idar ta tub'e hijab d'in ta aje shi kan gado, haka ta futo babu d'ankwali kai tsaye hanyar futa ta nufa, tunda ta doso gurin suka fara matsawa kowa na k'okarin ya bata hanya kar ta make shi, ball tayi da kofin Alawiyya dake bisa layi, Iya ta juyo da sauri tana fad'in." Kar Ku har gitsa layin fa.' Ladidi ta gani tana k'okarin futa,da sauri tace." Ina zakije a haka sai da nace ki d'aure kanki ke ku kunya ba kya ji." Ko kallonta ba tayi ba ta fuce abunta,girgiza kai kurum tayi ta cigaba da aikin ta tan addu'ar Allah yasa Kawunta na waje ya koro ta, aikuwa D'alha na tsaye da kayan sana'arshi suna gaisawa da mak'ocin su Yahaya,suka had'a ido dashi, sam bata tsorata ba. Ta fara k'okarin wuce shi,tsawa ya buga mata yana fad'in"Koma ki d'auro d'an kwallinki" Ido jazur! Ta koma ta cikin gidan, D'alha yayi sallama da Yahaya ya kama hanya ya tafi, lab'ewa tayi bayan k'yaure sai da ta tabbatar da yayi nisa sannan ta futo, tana ganin Yahaya yana gyara kwatar gidansa, ta galla masa harara, yana sunkuye bai sai abunda take ba, sai saukar Abu yaji a jikinsa, da sauri ya dago yana karkad'ewa sai ga tarkacan da ya kwaso daga kwata suna fad'owa k'asa, bayan rigarsa duk ya b'aci da kwata, waige-waige yake yana neman yaron da yayi masa wannan sha'ani, ido hud'u sukayi da ita, zabura! Yayi ya matsa gefe guda baki na rawa yace." Lad..ladid..katsaye shi tayi ta hanyar fad'in" Jiya har da kai gurin cewa na mutu har kuna shimfid'a tabarma da zama, to ban mutu, kuma duk sai na kashe Ku." Cikin Yahaya ya bada sautin kulululu!! Bakin sa sai motsi yake, zare masa manyan idonta tayi, ganin yanda yake gumi! ne yasa ta k'yalk'ale da dariya "hahahahahaaaa! fyallawa tayi da gudu ta barshi tsaye a gurin,saura kad'an ya saki futsari. Cikin mutuwar jiki ya zauna kan dakalin gidansa yana sauke ajiyar zuciya,sai zare ido yake. Babu inda tayiwa tsinke sai gidan gonar su Hakkim, tana isa ta tarar da an kewaye katangar da waya mai fasa k'afafu dan wani gurin ma har da k'ananun k'walabe, b'uya tayi wani gurin tana tunanin ya za'ayi ta shiga gurin. Can taji motsi an bude kofa, lek'awa tayi kad'an , d'an burni ta hango ya futo daga ciki jikinsa sanye da singlet da wando iya gwiwa 3quetar, suna magana da wani me wanki takalmi, tsura masa Ido tayi tana girgiza kai, a fili tace." Wannan girman jikin naka da wannan k'wanjin naka da wannan murd'ewar taka, duk baza su hanani in d'auki fansa akanka ba, hummm! Ko Kaine Singam gurin k'arfi sai na rama fasa min bakina da kayi." Tana kallonshi suka gama magana da me gyaran takalman ya koma ciki ba tare da kulle k'aramar kofar ba. Da sauri ta futo daga gurin b'uyan ta, kamar walkiya tazo ta shige ciki, Mai gadi nacan na fama da redi'o a hannu, wata bukka ta shiga ta b'uya Kansan kujerun hutawar dake ciki, tana kallonshi ya futo daga wani d'aki hannunsa ruk'e da takalma biyu ya kara futa waje, wuf! Ta futo daga farko inda take, ta afka inda taga ya futo, Sam had'uwar falon ba ya gabanta burinta kawai ta d'auki fansa, ba ta tsaya kalle kalle ba ta afka wani d'aki da tagani a bude, tana shiga ta fara zare ido motsin ruwa taji a band'aki, da sauri ta matse jikinta ta b'uya bayan gado. dama kar ku manta Ladidi bata da k'iba siririya ce sosai, Yusuf ya futo daga toilet yana goge jikinsa da towol, sauri sauri ya sanya kayansa. Ya tsaya gaban mirror yana shafa mai ajikinsa, Hakkim ya shigo d'akin hannunsa rike da takalman su an wanke su tas sai kyalli suke, Yusuf yace." Ka dame ni na tashi na shirya gashinan dai na shirya sai kayi sauri kaima." Zube takalman yayi a gefe guda, toilet ya nufa yana fad'in" Yanda kake da nauyin bacci idan ba haka nayi maka ba ai baza ka tashi ba." Yusuf yace.'' Son bacci da nauyin bacci har na kai ka." Shiru yayi masa ya shiga toilet din, shi kuma yana gama abunda yake ya futa farlor, Ladidi duk tana jinsu, tasan Hakkim ne ya shiga band'aki, futowa tayi daga inda take, ta zauna gefan gadon gami da tsurawa kofar band'ankin ido tana dakon futowar sa. Jikinsa d'aure da guntun towol ya futo cin yoyinsa duk a waje domin babu gajeran wando,a jikinsa dama da k'yar towol d'in ya ratsa masa jiki, yana futowa idonsa ya sauka a nata, tana zaune ta d'ora kafa d'aya kan d'aya, kanta sai k'yalli yake, sam! Bai gane ta ba, domin duk hattun ta sun sauya. Da k'arfi! Yace." Auzibillahi minashaid'anirrajim"!!!! Nan take ya fara karantun ayatul kursiyo, har yanzu idonsa na kallonta itama ta k'ura masa ido k'urrrr!! *COMMENT VOTE AND SHARE* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` *LOADING:* *{LADIDI K'WADAGA🌚}* _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain our reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_ *DEDIGATED* *TO* *RAHAMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿16* Cikin abunda bai fi second guda ba ya ganta a tsaye kan allon gado,kafin yace me ta buga wani tsallen ta sauka kan dressing mirror, tuni kayan shafa suka fara fad'owa k'asa suna fashewa,ta sanya k'afarta guda ta fara ball da sauran suna fad'owa kan 'yan uwansu, d'aya k'afarta tasa ta baya ta daki! mirror d'in ya tarwatse! Dura k'asa tayi ta tsaya gami da rik'e k'ugu! tana kallon sa. Hakkim kuwa jikinsa duk ya jik'e da gumi! Tamkar ba daga wanka ya futo ba, zuwa yanzu yasan mutum yake tare dashi ba aljan ba,saboda lokacin da take ball da kayan shafar sa ya kalli k'afarta,sosai ya tsorata da ibilicin wannan hallitan mace ko namiji domin dai ya kasa gane wani jinsi ne, k'aramin towol d'in dake rataye a wuyansa ya ciro ya goge gumin goshin sa, ya jefar dashi k'asa,rai a b'ace ya durfafi inda take. Tana tsaye turmin danya tana sauraron isowar sa, sam ya manta da kwalaben da ta fasha,kwalba ta caki k'afarsa me mugun tsini kafin kace kwabo jini ya fara zuba yana bin tayal cije baki yayi cikin azaba! Ladidi ta kwashe da dariya "Hahahahaha" tana nuna shi da hannu,d'ago kansa yayi yana kallonta,shan kunu tayi tace." Ni ce wannan yarinyar ta jiya daka doka na fad'a maka dama sai na rama,ko shugaban k'asa ne ubanka. Hehehhaaha." Ta k'arasa maganar tana mahaukaciyar dariya. Cikin tsananin fushi ya cire d'aya k'afar tashi da niyar d'amk'ota, k'afar ta caki! Wata kwalbar turare me tsini! K'ara! ya saki yayi taga-taga zai fad'i, da sauri ya dafe towol d'in jikinsa da yake barazanar fad'uwa k'asa, saboda sanin halin da yake ciki shi kadai ne a jikinsa, gwiwar sa ya sanya a gurin ya sanya hannunwa ya dafe k'asa sai cije baki yake, idonsa ya kad'a yayi ja, jini kuwa duk ya b'ata gurin. Kan gadon ta hau tayi tsaye tana kallonsa, Tace." Naji dad'i na rama abunda kayi min gaba ma sai ka k'ara dukana kaga abunda zanyi maka." Tana gama maganar ta ta dura k'asa, bude kofa tayi ta futa daga d'akin, Salima da Yusuf na tsaye harabar gurin suna jiran futowarsa kawai sai suka ganta ta futo,bagaz-bagan! ta wuce fuuuuu! tamkar zata tashi sama! Cike da tsoro Yusuf ya shiga ciki,Salima kuwa kin shiga tayi,domin ba k"aramin tsorata tayi ba, ita kam da tasan wannan masifar zata gani da bata biyo su, ba k'afafunta sai rawa suke ta nemi guri ta zauna,cikin zuciyarta take cewa gaskiya gurin nan akwai aljanu insha wata k'ila Dady bai sa anyi saukar alk'urani me girma a gidan ba. Cikin jarumta ya mik'e tsaye da sauri ya bi bayanta,yana jin in ya kama yarinyar nan to sai dai idan uwarta ta haifi wata domin har in bai kashe ta ba to sai yayi mata muguwar illah a rayuwarta, wani irin suka da azaba! Tafin k'afafun shi suke yana jin shigar kwalbar jikin jikinshi bai damu ba, bud'e kofa yayi a fusace! Suka ci karo da Yusuf ya shigo a razane! ganin fuskar Hakkim d'in babu rahama ko kad'an, yasa ya duburburce yace." Yaro wai meke faruwa ne,waye ya futa yanzu mace ko namiji? naga yaro ya futa yanzu, ina cikin rud'u fa,anya gurin nan babu aljanu kuwa." Shiru yayi masa cikin k'arfin hali ya nufi kofa da niyyar futa. Yusuf ya bishi da kallo yana kallo yadda yake Jan k'afa ga jini duk ya b'ata gurin, da sauri ya bishi ya dafa kafad'ar shi,yana fad'in." Wai ina zaka ne cikin wannan halin."? A hasale yace." K'yaleni malam." Yusuf yaje ya rufe kofar futa da key ya zura a aljihun sa, yace." Babu inda zakaje sai ka fada min abunda yake faruwa, yanzu fa na futo daga d'akin lafiya Lou amma dubi wani abun al'ajabi. " yace." Zo ka bude min kofa." Yusuf yace." Bazan bude ba wallahi." Wani uban naushi! ya kaiwa kofar da hannuwansa yana fad'in." Yusuf wallahi suma tallahi idan idona ya k'ara ganin yarinyar nan, to ina me tabbatar maka da cewar sai dai uwarta ta haifi wata,wallahi duk shad'aicin ta,sai naci ubanta sai na ragargaza ta, ni zatayi hakaaaaa."!!!!!! Salima na daga waje ta ji ihun Dan uwanta a tsorace ta fara buga kofar tana kuka, Yusuf ya bud'e mata ta shigo yayi saurin mai da kofar ya rufe, cikin mawuyacin hali taganshi tace." Babban yaya waye ya zubar maka da jini? Innalillahi wa inna ilahi raji'un." Sai ta kara rurucewa da kuka. Yusuf ya rasa ma abunyi yace." Yanzu dai muje hospital ayi maka dressing d'in ciwon nan,in yaso ko ma meye sai ya faru, ni wallahi kaina ya kulle ma." Salima tace." Ya Yusuf fada sukayi ne." ? D'aga mata kai yayi ya nufi bedroom domin dauko masa kaya, to duk irin tambayoyin da Salima take masa yak'i tanka mata, yana durkushe sai sakin ajiyar zuciya yake ta b'acin rai! Da cin alwashi kan Ladidi. Wata razananniyar tsawa! ya buga mata tare da fad'in "Tashi ki bani gurin idan na fada miki waye me zakiyi, ne kin dame ni." Salima ta mike da sauri taja gefe cike da tsoro take kallonsa ganin yanda duk hallitunsa suka sauya. *COMMENT VOTE AND SHARE* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` *LOADING:* *{LADIDI K'WADAGA🌚}* _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain our reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_ *DEDIGATED* *TO* *RAHAMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿17* Yusuf ne ya katse masa tunanin da take. Yace."Ka tashi ka saka muje hospital, ko sai na taimaka maka ne."? Da k'arfi ya fuzge! kayan da ya ke mik'o masa, ya mik'e da kuzari ya fara sanyawa zuciyarsa nayi masa zafi da radadin gami da takaicin abunda Ladidi tayi shuka masa. Yusuf yayi gaba yana fad'in." Bari in matso da mota kusa." Ko kallonsa baiyi ya fara d'ingisawa Salima tabi bayansa simi-simi. Cikin gari suka futa suka nemi wani pravite hospital, nan akai masa dressing sosai suka had'a masa magunguna masu kyau da tsada, Wanda in yayi amfani dasu insha'Allah zai samu sassauci. Hanyar su ta dawowa suka tsaya suka siyi abubuwan da basu dashi, Salima ta kalli Yusuf a tsorace tace." Ya Yusuf nifa ina jin kwana biyu ko uku zanyi in koma gida wallahi tsoro nake ji." Yusuf ya fashe da dariya har da dukan kan mota yace." Nima ai munyi d'aya dake gaskiya tafiya zamuyi tsakanin jiya da yau mun sha fargaba mu da muka zo Hutu mun b'ige da jinya, ga tashin hankalin wannan yarinyar." Hakkim ya ja tsaki! yace." Wallahi babu inda zaku je,ni kadai na shirya tafiya ta,saboda gulma da munafurci kuka ce dole sai kunzo, mussaman ke." Ya fada yana kallon Salima da ta sunkuyar da kanta ya cigaba da cewa "har da kuka sai kinzo saboda haka dole ku zauna sai sanda naga damar tafiya sannan." Yusuf yace." Ni indai tani ne babu matsala Salima ce abun ji." Aikuwa ta marairaice fuska, Yusuf ya dinga mata dariya yana tsokanar ta da daddare zata ga Ladidi a kusa da ita tazo taya ta kwana aikuwa duk ta gigice. da wannan suka Isa, Hakkim ya futo daga mota yana kalle-kalle wai ko zai ga Ladidi,duk suka shige suka barshi a gurin, daga bisani ya bi bayansu yana d'in gisa k'afafu. ********* Ladidi kuwa tunda ta samu ta d'auki fansar abunda Dan burni yayi mata sai kawai ta manta dashi da al'amuran shi ta cigaba da sabgarta. Tafe take fakam-fakam da allo a hannunta ta cire d'ankwalin ta taci Uwar d'ammara dashi, tana sane ta cire ko wani zai tsokane ta ta samu na duka, bayan haka kuma tana so ta b'akantawa Kawun ta D'alha rai tunda ta lura baya so ya ga tana yawo babu d'ankwali, shi kanshi hijab dinta na hannuta, karo suka ci da Iliya dai-dai wani lungu, Tun daga nesa yake k'unshe dariya, har ya k'araso daf da ita, taki kaucewa tamkar zasu bangaji juna, Iliya ya sha kunu ya d'an kauce mata tazo ta wuce, shima kamar zai wuce sai ya tsaya ya mik'a hannusa ya daki! kanta sosai yace.' Woooo k'waryar malo dama a namiji aka hallice ki domin kin fi kyau da maza!yana gama fad'ar haka ya runtuma da gudu yana dariya, aikuwa a sittin! Ta bishi da wani irin mugun gudu kamar zata tashi sama, yana gudu yana waiwayen ta,ganin ta kusa cimma sa yasa ya kara k'aimi!wani irin tsalle me had'e da gudu ta buga sai gata a gabansa,ba tayi wata-wata ba ta zura k'afarta k'arkashin tasa ta tad'o shi ya fad'i wanwar a gurin, ya yunk'ura zai mik'e, da sauri ta d'ebi k'asar gurin ta watsa masa a fuska, aikuwa ya saka ihu! Yana rintse idonsa, kamar walkiya ta bar gurin. Iliya ya dinga lalube yana ihu gami da mutsika idanunwansa k'asa sai gurin-gurin take masa a ciki ruwa ne kawai yake shatata da k'yar ya mike ya fara tafiya, aikuwa ya jishi cikin kwata tsumbul, yayi zaman 'yan bori, ya dinga salati yana neman d'auki. ********* Yau kwanan so biyar a garin d'an kunkuru Hakkim ya warke tsaf, kullum cikin zuba ido yake yaga ko Ladidi zata kara dawo wa, shiru safe da yamma sai sun futa ganin gari cikin mota, ya dinga kalle-kalle kenan ko zai ganta babu alamunta, cikin zuciyarsa shi kadai yasan irin tanadin da yayi mata, Labarin abunda ya faru kuwa har su Dady sun sani domin Salima ta fada musu komai, Dady ya kira shi a waya tare masa fad'a kan ya kula kar ya k'ara dukan yarinyar kowa a garin shi kam baya son tashin hankali, amma ya Dade da sanin halin dashi mafad'aci ne sosai idan aka tab'o shi, tun yana yaro haka yake,amma fa in baka tab'o shi ba zaka jima dashi kuna mu'amula domin yana da saukin kai. Duk wannan gargad'in da Dady yayi masa yaji ne kawai amma yanda yaci alwashi kan yarinyar yana gani in bai dauki fansa a kanta ba ma kamar ya aikata zunubi ne. ********** Yau Juma'a tun sassafe Mai koko ta tsaya kan Ladidi sai da taga tayi Wanka tas sannan ta k'yaleta ta shiga sabgogina, tana zaune tsakar gida, sanye da atamfa nicham jajazur da ita,ta sallahr ta ce ta bara,dinkin riga da zani ne da d'ankwali, tayi kwaliyya rabazau a fuskarta da d'ige-d'ige inda ta labta Jan jan baki a leb'anta da kan hancin ta saman idonta da girar ta, Mai koko ta k'araso gurin da Murmushi a fuskarta tace." Ko kefa Jikar Mai koko Ladidiya matar gwamna da shugaban k'asa,Ladidiya matar sarakai da Alhazai Ladidi matar masu mulki, kinyi kyau sosai, ki dinga tsafta kina wanka ki nutsu kinga kin fara girma wai baki ga kirjin ki bane har kin fara k'irgan dangi."? ta k'arashe maganar tana 'yar dariya. K'irjinta ta kalla jin abunda Iya tace zumb'ura baki tayi ta cigaba da goga jar hodar ta,a fuska.Mai koko tace." Hodar ta isa haka ai kar tayi miki yawa." Aje abun shafar tayi tace." Dandali zamu je yau akwai gad'a kuma kin san nice shugaba." Mai koko tace." To babu laifi, amma idan kin je don Allah ki nutsu kar ki shirme banda fad'a da maza ki kama kanki kinji ko." Tab'e baki tayi tace." Nifa Iya kin san duk wanda ya takale ni mace ko namiji babba ko yaro sai na rama ehee." Iya tace." To naji ai duk Wanda bai kula ki ba babu ruwan ki dashi." Gyad'a Kai tayi ta mike tsaye tana warware wani mayafin ta me kama da abun tata, sai uban k'yalli yake wani har yana zuba a k'asa, k'okarin d'aura k'ugunta take dashi, Mai koko tace." A'a ke da zaki yafa kuma kyayi d'amara dashi." " Ni dai k'yale ni nafi son haka." Tafad'a tana zura silifas dinta sabo dal dashi,da alama yau zata fara sawa. Mai koko tace." To sai an dawo kar kiyi dare." Uffan bata ce ba takama hanyar futa fakam-fakam zanin jikinta sai harde ta yake, tana futa waje ta kwance shi ta jashi sama sosai duk k'waurin ta a waje, ta fi jin dadin tafiya a haka. Har ta nufi hanyar Dandali sai ta fasa ta nufi hanyar titi. ********** Cikin kyakyawan shiri suka futo duk su ukun Salima sai washe baki take yau zata koma gida, shima Yusuf murna yake saboda yayi kewar sweetyn shi kullum suna mak'ale a waye tana masa mita. Shi ko gogon naku cikin b'acin rai yake,gashi har sun gama hutun su zasu koma bai ga al'janar yarinyar nan, balle ya dauki fansar abunda tayi masa,motsi kad'an zai buga musu tsawa kamar wani ubansu Yusuf har ya gaji ya fara mayar masa da martani,sai da suka kusa yin fada da juna, yana huci ya bude mota ya shiga suka shiga suma,da gudu ya figeta suka futa daga gidan, kasancewar hanyar babu kyau kafin a futa titi yasa tayar su tayi faci, cikin jin haushi Yusuf yace." Gashi nan garin zagin zuciya ka satar mana da taya sai ka futa ka d'aura mana wata." Yace." Sai dai in kai ka futa ka d'aura wallahi." Sanin halinsa na taurin kai yasa ya bude motar ya futa. Yana dubawa yaga babu wata spire yace." Babu wata fa." Gabansa ne ya fad'i jin abunda Yusuf yace futowa yayi yana tunanin yaya za'ayi, Yusuf yace " Dole a futa bakin titi a siyo wata bari inje da kaina. ". Daga masa kai kurum yayi, Yusuf ya kama hanya tafi. Bayan tafiyar Yusuf da kamar minti goma Ladidi ta bayyana a gurin. *COMMENT VOTE AND SHARE* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` *LOADING:* *{LADIDI K'WADAGA🌚}* _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain our reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_ *DEDIGATED* *TO* *RAHAMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿18* Kanshi a k'asa ya dinga jin alamun tafiya, a nutse ya d'ago kanshi, suka had'a ido da ita ta kusa k'arasowa inda yake tsaye, wannan karon ma bai gane taba saboda kwalliyar da tayiwa fuskarta, kauda kansa kurum yayi, ita kam Ladidi ta gane shi sosai, wuce shi tayi, sai kuma ta dawo da baya, ta d'an tsaya nesa dashi, tace." Kai d'an burni." Da sauri ya d'ago kansa jin muryar yarinyar da yake nema ruwa a jallo. aikuwa k'wayar idonta ya kalla ya gane itace, fuskarsa ta rikid'e tayi murtuk kam bai tab'a dariya ba tunda Allah ya hallice shi, kanta yayi da sauri! tana tsaye tana jiran isowarsa tana dariya kamar mahaukaciya, tana ganin ya kusa k'arasowa gurin ta sunkuya ta d'ibi k'asar gurin ta watsa masa a fuska tana shek'a dariya fad'i take" Zo ka kamani ka gani in zaka iya, hahahahaha." Hakkim yaji shigar yashi idonsa sosai bai damu ba, cikin wata irin zuciya ya kai hannunsa zai mare ta ta sunkuya tana dariya,ya mari iska! cikin rashin imani! Ya kwarfo k'afafunta duk biyun, ta zube a gurin,yunk'urin mik'ewa take ranta a b'ace yayi saurin take mata k'afa guda ya dinga murzata da takalmin shi sawu ciki, ihu!! Ta kurma tafa d'ura masa ashar! ya daki! Bakinta da gwiwar hannusa, kafin kwace kwabo bakin ya fashe, hannunsa guda ya sa ya d'ago ta, ta rike hannunsa tana cizo,ko a jikinsa, ya shak'e mata wuya sosai! Suka fara kallon-kallon ita dashi, idonta yayi bala'in ja na azaba! Shims nasa idon sunyi jajazur! Ko da yake dama tunda suka futo haka nasa yake, a zafafe! Yace." Ke dan ubanki ya sunanki."? Cikin shak'ewar nuffashi tace." Ba dai Ubana wallahi meye ruwanka da sanin sunana,kuma zaka san ni ka Mara." Yace." Sai dai uban wa.". Ko nuffasa bata bari yayi ba tace." Sai dai ubanka." Murmushi yayi kana ganinsa kasan zaiyi mugunta, sakin ta yayi ta fad'i gurin tana mai da nuffashi, ta zabura zata mike yq maida kafarsa kan tata, blet din jikin shi ya Ciro, ya fara lafta mata, Ladidi ta fara ihu tana neman d'auki. Salima na cikin mota tana kukan tashin hankali tana jin tsoran kar yayan ta yayi kisan kai! Dukan Ladidi yake ko ta ina tana ihu! Wanda babu hawaye, da wuya tayi wuya sai ta fara sharb'en kuka tana cigaba da zaginsa,Salima ta bude mota a tsorace tazo ta rike shi tana bashi hakuri ya bangaje ta tafad'i a gurin,ya cigaba da laftar Ladidi har sai da yaga bakin ta yayi shiru, duk da haka bai saurara mata ba sai da yaga ta daina nuffashi sannan ya k'yaleta! Ya maida belt d'insa gami da matsawa gefe guda yana mai da nuffashi. Yusuf ya k'araso gurin hankali a tashe, Ladidi kawai yake bi da kallo cikin tsantsar tashin hankali ya jefar da tayar yayi kanta yana salati. Salima ya kalla bakinsa sai motsi yake, ita kam kuka kawai take, Hakkim kuwa tayar ya d'auka ya fara sanyawa babu abunda ya dame shi. Suna can durk'ushe kan Ladidi sukaji karar mota a Kansu,da sauri suka mike Hakkim ya kunna mota yana k'okarin tafiya ya barsu, jiki a sanyaye suka bude motar suka shiga cike da tausayin Ladidi da bata san a wace duniyar take ciki ba. Sai da suka hau titi sosai Yusuf ya samu bakin magana yace." Yanzu sai da ka aikata abunda kayi niyya kan yarinyar nan, wato duk irin maganar da Dady yayi maka baka d'auka ba ko."? Hakkim yayi masa banza fuskarsa a had'e take har yanzu, wani gefen kuma ya dan samu sassauci tunda ya hukunta yarinyar yana ganin gaba idan ance mata gashi a guri baza ta zo gurin ba. Yusuf ya sauke ajiyar zuciya yace." To wallahi ka sani kamar Dady yaji wannan labarin, kome zakayi sai na fada masa." D'aga kafad'u yayi alamun bai dame shi ba. Cikin b'acin rai suka isa Abuja. Mai gadi ya bude musu get yana musu bar ka zuwa, Yusuf ne kawai ya amsa, Hakkim ya shige da mota ya gyara parking, futowa yayi ya nufi part d'insa, Yusuf da Salima suka nufi cikin gidan. Mama na zaune a falo tana kallo taji sallamar su ta dago kanta cike da walwala da farin ciki ta amsa, Salima ta tawo da gudu gurinta, rungume ta tayi ta fashe da kuka! Mama ta kalli ya Yusuf ta ganshi duk a furgice tace." Yusuf me ya faru ina Abdul yake." ?Ajiyar zuciya ya sauke ya zauna kan kujera yana goge gomin dake tsatstsafo masa, yace." Lafiya ba lafiya ba Mama." Salati Mama tasa tace." To ai sai kayi min bayani. Salima ta bude baki zatayi magana Mama tace." A'a bake na tambaya ba." Shiru tayi tana ajiyar zuciya. Yusuf ya warware wa Mama duk abunda ya faru tunda ranar da sukaje har yau da zasu dawo. Mama ta dinga salati tana sallallami, tace."Wai wannan zuciya ta Abdul ina zata kaishi yanzu idan ya kashe musu yarinya fa." ? Yusuf yace." Wallahi Mama na tsorata da al'amarin domin ni gani nake ma kamar ta mutu." Salima tace." Wallahi nima haka." Mama ta mik'e tsaye da sauri! Jikinta sai rawa yake wayar ta ta d'auko ta kira mijinta yana dagawa tace." Kazo gida babu lafiya." Ba ta jira abunda zai ce ba ta kashe wayar. Tace." Yusuf je ka kira min shi yanzu.' Yusuf ya mike da jiki a sanyaye ya nufi part d'insa. *COMMENT VOTE AND SHARE* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` *LOADING:* *{LADIDI K'WADAGA🌚}* _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain our reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_ *DEDIGATED* *TO* *RAHAMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿19* Lokacin da Yusuf ya shiga d'akin samun sa yayi zaune gefen gado d'aure da towol a jikinsa da alama daga Wanka ya futo, yana zaune yana danne-danne a waya babu abunda ya dame shi. Cikin takaici Yusuf yace." Sai kazo Mama na kira,wato kai kanan kana danne-danne a waya babu abunda ya dame ka ko." Dago kansa yayi yana kallonsa yace." E babu abunda ya dame ni, d'in, so kake in tada hankalina kamar yanda ka tada naka ko me."? Yusuf yace." Zakayi bayani ne wallahi ni kaga tafiya ta, idan kaga dama kaje kiran da ake maka." Tsaki! Yaja ya d'auke kansa Yusuf ya futa cike da jin haushin sa. K'ananun kaya ya sanya a jikinsa Wanda suka masa kyau sosai ya fesa turare, me sanyin kamshi wayarshi ya d'auka tare da eirpix d'insa ya futa. Mama na tsaye a farlo tana kai kawo hankalinta duk ya tashi, yayi sallama ya shiga, Salima ce kawai ta amsa masa yana kallon fuskar Maman shi yasan tana cikin tashin hankali da damuwa, k'okarin zama yake ta dakatar dashi ta hanyar fad'in." Kar ka zauna domin zama bai kama ka ba." Tsayawa yayi yana sunkuyar da kai kasa, tace." Ka kyauta Abdul nace ka kyauta da abunda kayi." Shuru farlon yayi, tace." Kullum ina gargadin ka da ka rage zafin zuciyar nan taka kana mai da abun wasa, duk naji abunda kaje ka aikata a garin mutane ka sumar da yarinyar mutane har sau biyu kan abunda bai taka kara ya karya ba ko."? Dago kansa yayi yana kallon Maman yace." Mama kin San abunda yarinyar nan tayi min kuwa? Nasan Yusuf ne zai ce miki babu abunda tayi min domin ya kareta, idan da tsautsayi lokacin da ta fasa kwalabe na taka da narasa k'afafu me za kuce ko kuma in kwanta jinya me tsayi kinga ta cuce nu, wallahi Mama ibilicin yarinyar nan ya wuce tunanin me tunani shiyasa na hora ta yadda gaba baza ta kara yiwa wani Abu makamancin nawa ba." Mama tace." Kaine kake ganin haka, Abdul kasan halin mahaifin ku dai ba kai kadai abun zai tsaya ba har dani, babban abunda ya tada min hankali yanda Yusuf yace ka hana ya tsaya ya ceci rayuwar ta kayi mata dukan mutuwa tana kwance bata san inda kanta yake ba." Sunkuyar da kansa tayi har yanzu baya nadamar abunda ya aikata ga Ladidi. General. Ne yayi sallama ya shigo cikin sauri, duk ya gansu a tsaye, hankalin sa ya kara tashi, wata irin tsawa! ya buga musu har da Maman yace." Ku fada min abunda yake faruwa kinyi cirko!Cirko".! Jiki a sanyaye Mama tace." Gashinan a tsaye ya janyo mana tashin hankali nan ta warware masa duk abunda ya faru. Wani irin bahagon mari! Ya kaiwa Hakkim jikinsa na tsuma! Yace." Abunda ka je kayi kenan shiya dama ka takura dole Kaine zaka fara zuwa."? Hakkim ya dafe kuncinsa ransa a mugun b'ace! Yau shi mahaifinsa ya Mara kan wata "yar iskar yarinya 'yar kauyen k'auyau! Nan take yaji wata muguwar tsanar Ladidi cikin zuciyarsa. General ya cigaba da cewa." Duk irin jan kunnen da nayi maka kan yarinyar ashe baka ji ba, kanan da muguwar zuciyar ka, OK shikkenan ka sani mutukar yarinyar mutane ta mutu ko ta nakasa ta dalilin ka babu shakka! Zan barka da Matsalar ka ne domin ni ba abunda ya shafe ni bane ko me hukuma zatayi maka tayi maka, ni zan bada tawa gudumawar." Salim ne ya shigo ya tarar da tashin hankali Mama na kuka Salima na kuka gogan na tsaye idonsa yayi jazur General sai surfa masa bala'i yake, nan Salim ya tambayi abunda yake faruwa Yusuf ne ya warware masa komai. Shima ya kad'u sosai kuma ya rausayawa Dan uwansa saboda yasan b'acin ran mahaifin su bashi da kyau mugun mafada ci ne. General ya kalli Mama cike da bada umarni yace." Ku shirya muna yin sallahr La'asar zamu dauki hanyar Kano dole ne muje mu ga halin da yarinyar ke ciki, duk inda take za binciko min ita." Mama tace." To Allah ya kaimu." Sama ya hau ya barsu suna tunanin abunda zai faru a gaba addu'a kawai suke Allah yasa yarinyar bata mutu ba. Hakkim yq mike ba tare da ya kalli kowa ba ya zura takalmin shi ya futa ransa a dugunzu me, ya lura da Dady ya dauki serious kan al'amarin, wato Sam!shi ba'a duba irin b'arnar da yarinyar tayi masa abun ya kai har da duka abunda bai tab'a faruwa ba tsakanin shi da mahaifinsa tunani yake wane irin hukunci ya kamata ya yanke kan yarinyar. ******** Ladidi kwance cikin jini gefen kunne ta ya fashe yana digar da jini gashi ya kumbura leb'anta ya kumbura had'e da saman idon ta,duk hallitun fuskar ta sun jirkita tana kwance bata san in da take ba, hanya ce da ba kowa ne yake bi ba sai masu kiwo sune suka bi tare da dabbobinsu shiyasa har yanzu babu Wanda ya kawo mata dauki. D'an Fulani ne ya shigo gurin tare da d'anshi Mati da dabbobin su, sai da suka zo dabda ita sannan suka fahimci mutum ne a kwance ,Mati yayi saurin birkitoto kawai sai yaga Ladidi d'iyar yayarsa Amina, me rasuwa, cike da tsoro ya kira mahaifin nasa yana fad'in "Baffa zo ka ga Ladidiyar Mai koko ce....... *COMMENT VOTE AND SHARE* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` *LOADING:* *{LADIDI K'WADAGA🌚}* _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain our reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_ *DEDIGATED* *TO* *RAHAMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿20* Da sauri d'an Fulani ya k'araso gurin, hankalinsa a tashe yace." Maza d'auke ta muje gida nasan ana can ana neman ta." Mati ya sab'ata a kafad'a bata san inda kanta yake ba, suka nufi gida. Mai koko na aikace-aikacen ta na gida kawai taga an shigo da Ladidi a kafad'a, da sauri ya yar da tsintsiyar hannunta tana salati, Mati ya shimfid'eta a tabarma da sauri ya nufi gidin rijiya ya jawo ruwa cikin wata roba ba tare da b'ata lokaci ba yazo ya kwara mata a fuskar. Minti biyar tsakani ta saki wata wawar ajiyar zuciya, nuffashin ta ya dawo amma kuma bata bude ido ba. Mai koko ta dinga share hawaye cike da tausayin ta tace." A'ina kuka ganta kuma waye ya fasa mata baki har ya zubar mata da jini."? Dan Fulani yace." Inda kika ganta muma haka muka ganta kwance hanyar titi bata san inda kanta yake ba. Amma nafi tunanin wani tayiwa rashin kunya ya gwada mata rashin imani." "Shiyasa kullum nake gargad'inta da rage haikewa manya domin nasan watarana dole ta had'u da wanda zai hukuntata." tafad'a tana goge hawayen ta da gefan zanin ta. D'an Fulani yace." Ai tun farko an fada miki abunda za'ayi mata a huta kink'iji, ni kinga tafiya na Dade da sanin duk lalatar da yarinyar take kece kike daure mata gindi,ni babu abunda zance sai dai ince Allah shi kyauta." Yana gama maganar shi ya kad'a kansa ya futa, Mati ya rufa masa baya Mai koko tabisu da kallo cike da takaici ya share hawaye tace." Duk dan kunga marainiya ce shiyasa kuke mata haka, wallahi idona idon wanda yayi wa jikata wannan b'arnar sai na rotsa masa kansa shima." Ta fada cike da jin haushi da takaici, Ladidi ta fara motsa idonta a hankali -a hankali ta bude tana kallon Iya, tayi saurin dafe kanta tana rumtse ido! Da sauri Mai koko ta rike hannun tana yi mata sannu, da k'yar tace." Iya bani ruwa insha wayyo kaina!!!! Iya ta mike da sauri ta d'ebo mata ruwa. Ta tashe ta zaune tare da karata a jikinta ta fara bata ruwan. Kad'an tasha ta kauda kanta. Mai koko tace." LADIDI ina kikaje waye yayi miki wannan dukan. "? Kamar da dutse take magana. ta kara maimaita maganar tata. Ladidi batasan ma tanayi ba hannunta ta tab'a tare da fad'in ." magana nake miki fa." Da k'arfi tace." Iya me kika CE." Itama Iya sai ta bud'e murya sosai tace." Cewa nayi waye ya doke ki haka har ya kumbura miki fuska tare da zubar miki da jini."? Kuka ta fashe dashi tace." Wani d'an burni ne ya doke ni babu abunda nayi masa kawai don na zo wucewa Iya Allah kuwa sai narama bazan barshi ba." Cike da takaici da jin zafi tace." Ai nima bazan barshi ba,sai nabi miki hakkin ki, domin bazai shigo garinmu yaci albarkaci na kuma ya doke ki har da zubar miki da jini kowa daga ya tashi muguntarsa sai yace ke,to sai nabi miki hakkin ki, ko dame yake tak'ama kuwa.". Kuka sosai Ladidi take, hankali Mai koko ya kara tashi, tunda taga Ladidi na kuka tabbas tana jin jiki. ********* K'arfe biyar shaura kwata sun shirya tsaf! suna tsatsaye a harabar gidan suna jiran futowar general, kana kallon fuskokinsu kasan suna cikin damuwa, mussaman Hajiya Asiya. General ya futo cikin sauri yana d'aura agogo hannunshi, duk ya bisu da kallo, yace." Ina Hakkim d'in yake." Yusuf ya sunkyar da kanshi yace." Bai futo ba." Cikin b'acin rai! General yace." Maza jeka kira shi,Hakkim yana so mu sanya k'afar wando guda dashi wallahi." Salim yace." Dady kayi hakuri " ko kallonsa baiyi ba ya shiga mota Mama da Salima suka bude suka shiga. Minti biyar tsakani sai gasu nan sun futo Hakkim sai cin magani yake, Dady yayi k'wafa yana girgiza Kai cikin zuciyarsa yace." Zakaci malafar ubanka ne yaro." Yace." Ka shiga kayi driving domin babu wani direba da zan d'auka. " zuciyarsa babu dad'i ya shiga motar gami da kunna ta, suka futa daga gidan. ******** Hankali Mai koko bai k'ara tashi ba sai da taga tana yiwa Ladidi magana tana shiru tamkar bata ji ba,sai ta d'aga murya sosai sannan take amsa mata, tace." Oh! ni 'yarnan Allah yasa wannan mugun mutumin bai lahanta miki kunne ba." Jira kawai take D'alha ya dawo domin tafad'a masa hankalin ta yayi mugun tashi, duk da ta gaggasa mata jiki tare da shafe mata jiki da Robb hakan bai hana ta cize baki ba,daga an tab'ata zata kurma ihu!! Jikinta duk ciwo yake. D'alha ya dawo a gajiye ya Tatar da wannan tashin hankalin ,Iya ta kwashe komai ta fada masa hankali sa ya tashi shima ya kwatanta kiran Ladidi shiru sai da ya d'aga murya sannan taji shi, nan ya k'ara tambayar ta abunda ya faru, tana kuka ta warware masa komai. Shikam bai yadda ba yafi yadda da cewar wani abun tayi masa shine shi kuma ya mata wannan dukan, tunanin mafuta kawai yake, d'an jarinsa bai taka kara ya k'arya ba shi zai rusa dole ya kaita asibitin burni a duba mata kunnuwan ta, tun kafin Abu yayi tsanani, dama asibitoci suna kuka dasu mutanan k'auye cewa basa tashi zuwa asibiti sai sunga cuta tayi tsanani, shikam baya fatan haka. ****** Gudu yake shararawa General ya buga masa tsawa! tare da fad'in." Ka jamu a hankali ka kaimu ko muma za ka gwada mana zafin zuciyar ne, sai faman gudu kake damu a mota kamar Wanda zai bar gari." Hakkim ya rage gudun da yake, yana jin wani daci a zuciyarsa wai yau shi Dady yakewa tsawa kan wata bare yarinyar da bai sani ba, kwata-kwata ya kasa fahimtar shi, fad'a sosai General ya dinga yi masa har suka Isa Kano bakinsa baiyi shiru ba, Hakkim duk ya koma kalar tausayi saboda abunda bai saba ne, Yusuf ne dinga bawa Dady Hakuri,shima Yusuf din ya samu rabonsa, sai yaja bakinsa yayi shiru cikin zuciyarsa yake cewa" da alama allurar soja ce ta motsawa Dady. *COMMENT VOTE AND SHARE* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` *LOADING:* *{LADIDI K'WADAGA🌚}* _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain our reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_ *DEDIGATED* *TO* *RAHAMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿21* Sai bayan sallahr magariba suka isa K'auyan D'an kunkuru, Dady ya futo daga mota yana hamdala ga Allah, gurin yake bi da kallo sosai yayi kyau ya k'ayatu haske fitila ko ina,nan ya jagoran ce su suka shiga ciki domin su samu nutsuwa suyi sallah, in yaso ko meye sai ya biyo baya. Sallolinsu sukayi suka ci abinci, Dady ya kalli agogon dake manne a bangon farlon takwas da rabi na dare, ya kalli Hakkim da fuska a turb'une yace.'" Yanzu dai ka huta sai ka tashi ka fara laluben inda yarinyar mutane take domin inyi abunda ya kawo ni garin." Ya d'ago kanshi dake sunkuya yace." Dady dare yayi yanzu ga hanya babu kyau ga yanayi na damuna gari duk ya jike kayi hakuri sai Gabe." Tsawa! Ya buga masa tare da fad'in." Bana son wata banzar magana ka tashi ka fara laluben yarinyar nan da halin da take ciki." Mik'ewa yayi da sauri Yusuf ya mike shima suka futa tare. Dady yace." Ai ka jawowa kanka tunda kai kace me kunnen k'ashi ne." Cikin d'ari-d'ari Hajiya Asiya tace." Ayi hakuri Yallab'ai." Ko kallonta baiyi ba ya cigaba da girgiza k'afarsa guda. Tsaye suke a harabar gurin suna shawarwarin me za suyi. Hakkim ya nufi gurin masu gadi jikinsa duk yayi sanyi fad'an Dady ta soma damunshi, Sam! bai saba ba. Suna ganinshi ne suka nutsu nan ya k'arasa gami da mik'a musu hannu suka gaisa a mutunce. Sai ya rasa me zai ce. D'aya daga cikinsu yace." Akwai abunda za'ayi ne Oga."? Girgiza kai yayi alamun a'a yace." Tambayar ku kawai zanyi." Sukace Allah yasa mun sani. "Wata yarinya siririya nake tambaya zaku ganta fara 'yar fulani k'azama yarinyar bata da kintsi tana tafiya kamar mahaukaciya ko kun santa." Shuru sukayi na minti biyu daga bisani suka had'a baki gurin fad'in." Gaskiya ba mu gane yarinyar ba domin kasan yaran K'auyan nan suna da yawa kuma dai duk haka d'abin ansu yake na rashin kintsi." Yusuf yace." Ko d'azu ma ta wuce ta nan wajejen k'arfe goma na Safiya, ko gilmawarta baku gani ba." ? Nan suka ce Sam basu gane taba. Cike da jin haushin su Hakkim ya futa waje yana kalle-kalle Yusuf yace." Bari in d'auko mota mu nausa ciki ko za'a dace." Shiru yayi masa kawai ya soka hannuwansa duk biyun cikin aljuhu. Yusuf ya futo da mota ya shiga suka kama nausa cikin karkarar ba tare da sun san ina zasu je ba. Ganin mota tana shigowa ne yasa matasa da suke zaune Suna shan rake tsakiyar su futalar aci bal-bal ce sai hayaki take suna ta hira da shewa duk suka bi motar da kallo. Yusuf yace." Ina ganin mu tsaya mu tambayi matasan can." Parking yayi suka futo a tare matasan suka bisu da kallo. Cikin nutsuwa suka k'arasa kusa dasu duk suka basu hannu sukayi musabaha. Yusuf yace." Muna tambaya ne." Sukaje Allah yasa mun sani." Shiru yayi domin ya rasa da yaya zaiyi kwatan Ladidi. Hakkim yaja tsaki yace.' Ka fara magana kuma kayi shiru, muna tambayar wata ibilishiyar yarinya a garin nan, ita ba mutum ba ita ba'ajana ba siririya tamkar tsolan rake, zaku ganta k'azama tana da manyan idanu." Shiru sukayi na minti biyu daga bisani sukace ."Gaskiya bamu gane taba, sai da Ku k'ara shiga cikin k'auyen ko za'a dace." Ko gama sauraransu baiyi ba yayi gaba ya bud'e mota ya shiga Yusuf ya biyo bayanshi shima duk ya sare da al'amarin. Har ya kunna mota zasu tafi, d'aya daga cikinsu ya taso da sauri yana fad'in." Ku tsaya Ku tsaya." Hakkim yace." Dallah ja mota mu tafi ya Wani taso yana mu tsaya mybe ma yayi mana shirme." Yusuf ya share shi kawai ya kashe mota, saurayin ya k'araso yana fad'in." Ina kyautata zaton yarinyar da kuke magana akanta baza ta wuce Ladidi ba, domin duk siffofin daka fada ita take dasu." Yana daga cikin mota tace." Shigo ka kaimu gidansu." Da sauri yaja baya cike da tsoro, chaiiiii! Akan me zai shiga motarsu ya sani ko 'yan yankan kai ne, Karin abun damuwar ma Ladidi suke nema, tabbas yasan abun babbane. Ina-inda ya fara da k'yar yace." Yanzu dare yayi zani gurin iyalina,amma bari in yi muku kwatance." Yusuf yace." Ok muna jinka." "Idan kuka mike wannan hanyar zata kaiku har *Dausara* sai ku tsaya dai-dai majalisar Yahaya kuce ina ne gidan Iya Mai koko insha Allahu za a nuna muku nan ne gidansu Ladidi." Yusuf ya zura hannu a aljuhu ya Ciro gudar dubu daya ya mik'a masa, yana godiya, Da sauri ya karb'a yana zabga masa godiya Motar yaja suka k'ara gaba. ****** D'alha da Yahaya na zaune a kan dakali suna hira Duk 'yan majalisar sun tashi, nan D'alha ya samu damar fad'awa mak'ocinsa Yahaya abunda ya faru da Ladidi Sosai Yahaya ya jimanta al'amarin yace." Yanzu kana nufin jarin ka zaka rusa kan yarinyar nan D'alha ka k'yaleta kawai tunda tana ji kad'an kad'an sai nake ganin kamar wahalar da kanka zakayi kan hakan.' Ajiyar zuciya D'alha ya sauke yace." Wallahi Yahaya ina mutukar tausayin rayuwar Ladidi marainiya ce bata da uwa babu uba sam bata san su ba bata da gatan kowa sai ni sai Ubangiji kaga kuwa dole in tsaya kan lafiyarta domin nasan amana ce a hannuna." Yahaya yace." Da ina da wasu kudi a aje dana ranta maka gaskiya bana so ka taba jarinka." "To yaya za'ayi insha Allahu zai farfad'o." Haske mota suka hango tun daga nesa yana haske su. Yahaya yace." Baki mukayi daga burni kenan.'? D'alha yace." Da'alama dai." Ido suka zubawa motar har ta k'araso inda suke. Yusuf yayi parking suka futo a tare. Suna isa kusa dasu suka mik'a musu hannu suka gaisa, Hakkim yace." Da Allah muna neman majalisar Yahaya ne." D'alha yace." Gatanan ga Yahaya nan yana jin ka." Yace." Gidan Iya mai koko muke nema." Da hannu Yahaya ya nuna musu kofar gidan. Hamdala Yusuf yayi yana jin farin ciki, yace." Nan wata yarinya Ladidi take." Yahaya yace." K'warai kuwa ince ko lafiya."? Hakkim ya juya ya da niyyar shiga mota a cikin zuciyarsa yace." Tunda anga gidan kome me sauki ne, gwara inje in kwanta in huta ko na samu Dady ya k'yaleni." Bayani Yusuf ya tsaya yana musu Hakkim ya kunna Mota da k'arfi yake masa hon!!! Yusuf yace." Kuyi hakuri Insha Allahu gobe zamu zo da safe kome ye sai ayi." Yana gama maganar yaje ya bud'e mota ya shiga, Yusuf ya fige ta suka bar gurin. Cikin takaici yace." Duk wannan abun bazai kai maka ba, don ma ka samu ina taimaka maka na tabbata da kai kadai ne sai dai ka kwana a kauyen nan kana tambaya baka samu ba, shine kake k'okarin tafiya ka barni. " Shiru yayi masa yana draving, Yusuf ya dunga masa mita hat suka Isa masaukinsu. *COMMENT VOTE AND SHARE* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` *LOADING:* *{LADIDI K'WADAGA🌚}* _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain our reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_ *DEDIGATED* *TO* *RAHAMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿22* Motar su na barin gurin. D'alha ya mik'a da niyar shiga gida yana mik'awa Yahaya hannu sukayi sallama kowa ya shiga gida. Cikin bacci taji kamar murya D'alha yana tashin ta, ta mike zauna tana gyara d'aurin dankwalinta. Hasken Fitilar kwai ta karo tace." Lafiya kake tashina bacci na yayi nisa wallahi." D'alha ya zauna gefen katifar da take zaune yace." Wasu mutane ne suka zo yanzu, wai suna Neman Ladidi." Bude ido tayi sosai gabanta na fad'uwa tace." Wace Ladidi kuma,wacce yinin yau bata futa ba balle ace tayi Wani Abu." Kwantar da hankalin ki Iya suma basu ce tayi komai ba, sun dai ga gidan sun ce gobe zasu dawo da safe." Iya tayi jigum! Tana kallon Ladidi dake shararar baccinta tace." Kaganta nan ta sha wahala kafin bacci ya d'auke ta, motsi kad'an sai tace kunnenta." D'alha yace." Da'alama ai kunnen ba k'aramin bugu akayi masa ba." Iya ta share hawaye cike da tausayin jikar tata tace." Ko waye wannan ba k'aramin azzalimi bane wallahi. " Shiru D'alha yayi domin baya so ya tanka maganar yasan laifin Ladidin ne. Mik'ewa yayi yana mata sallama, har zai futa ta tsayar dashi tana cewa." Kace gobe babu koko ko."? "Eh kin san zamu futa da safe sosai domin mu kama layi,sai dai hanzari ba gudu ba, mutanan da zasu zo." Iya tace." Hakane kuma dole mu jirasu domin muji da abunda zasu dashi." ****** Lokacin dasu Hakkim suka koma gida babu kowa a farlo sai General kawai duk sun je sun kwanta, yana zaune yana jiran dawowar su Ko zama bai bari sunyi ba yace." Kun samu inda take.? Yusuf yace." Eh Dady mun samu saboda dare yasa muka ce mu bari gobe da safe sai mu koma." Dady ya mike tsaye yana kallonsu yace." Allah ya kaimu gobe nima dani za'aje domin inga inda yarinyar take." Shiru sukayi kai a kasa sai da ya wuce tukkuna suka dago Kansu, Hakkim ya zube. Cikin kujera yana shafa kansa yayi wata muguwar gajiyq Yusuf kuwa tv ya kuna ya zauna yana fadin ." duk yanda kake ganin ga gaji ni nafi ka gajiya wallahi." Hakkim yayi masa shiru yana lumshe ido, mik'ewa yayi ya nufi firji domin d'auko Lemo ko ya samu ya samu sassauci a zuciyarsa. ****** Da safe da k'yar Iya ta taimakwa Ladidi tayi wanka domin jikin nata ya kara d'aukar zafi mussaman gefen wuyanta wanda da k'yar take iya motsa shi, har dan kumbura yayi. Tana zaune cikin wani leshi wanda ya gaji da kodewa yayi haske sosai dinki riga da zani ne da d'ankwali Iya ma ta shirya tsaf hijab dinta na aje a gefe D'alha ya shigo ya tarar dasu suna karyawa iya na lallaba ta tasha koko, tana kin sha, saboda zafi da take ji gurin hadiyar abu shiyasa ma ko kosai ba ta Ciba. Iya tace." Har yanzu basu zo ba ko." Daga kai D'alha yayi Yace. " gashi yanzu k'arfe takwas ba." Tace." To ai sai muta fi domin ba zamu tsaya su katse mana abunda mukayi NIyya ba." Yace." Hakane kuwa hankali na ya kara tashi da yanda naga yarinyar ta tashi da jiki yau." Iya tace." Yanzu da k'yar take hadiyar koko dan taki cin k'osai ma." Kallonta D'alha yake cike da tausayi..... Sallama suka ji daga waje D'alha ya mike da sauri ya futa ***** Gaban shi ne ya fad'i ganin hamshakin mutum jingine da mota, fuskokin su Hakkim yake karewa kallo yana so ya fahimci ko sune mutanan na jiya. A hankali ya k'arasa kusa dasu ya dan rankwafa gami da fadin." Barka da zuwa ranka ya Dade." General ya mik'a masa hannu fuskar sa a sake yace." Barka kadai samari fatan mun same Ku lafiya. " D'alha yace." Lafiya lau Alhaji." Hannu ya mik'awa su Hakkim sukayi musabaha ga juna yace." Hala kune bakinmu na jiya da daddare ko."? Yusuf yace." Mune wallahi." D'alha yace." To bari in shiga gida in sanar da mahaifiyata dama yanzu muke shirin futa." General yace." Babu laifi samari." D'alha ya shiga gida cikin sauri. Gogon ku na tsaye jikin mota ya harde hannuwansa a k'irji jira kawai su shiga gidan ya kara yin ido hudu da marakaunyar yarinyar nan yaga tayi ladaf ko kuwa. Minti biyar D'alha yayi ya dawo da sauri yace." Bisimillah Alhaji ku shigo daga ciki." Bayan sa suka bi. Yaran unguwar dake tsaye na kallonsu suka biyo su yuuuuuuu! D'alha ya buga musu tsawa, suka koma gefe,wasu na cewa Ladidi ce taje ta jawo futuna. Mai koko na zaune gefan tabarma ta lullub'e jikinta da mayafi. Sukayi sallama suka shiga gurin zama ta nuna musu tana musu Barka da zuwa cike da mamakinsu Suka zauna babu kyankyamin komai domin gidan tsaf yake tun safe tayi shara da wanke wanke ko ina tas iskar Safiya na kadawa Gaisawa suke cike da mutumchi, General yace." Ina fata nan ne gidan su wata yarinya Ladidi." Mai koko tace." K'warai kuwa nan Alhaji ina fatan ba wani abun tayi muku ba." Cike fa tausayi yake kallonta yace." Mine dai mukayi mata laif............ Kafin ya gama maganar shi Ladidi ta bayyana a gurin, ta tsaya tsakinyar ta barmar idonta kan Hakkim! suka kurawa juna ido. Ihu!!! Ta kurma tana nuna shi da hannunta tace." Iya!!! Gashinan shine ya dinga dukana kamar zai kashe ni wallahi Iya shine, Allah ya kawo shi gidanmu mu dauki fansa domin bazan barshi ba." *COMMENT VOTE AND SHARE* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` *LOADING:* *{LADIDI K'WADAGA🌚}* _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain our reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_ *DEDIGATED* *TO* *RAHAMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿23* Cike da mamaki General yake kallon Ladidi. dake tsaye Kansu D'alha mata tsawa ta matsa daka kan mutane amma kamar kara ingizata ake tanayi kamar zata kaiwa Hakkim duka. General ya kalli Yusuf da alamun tambaya. Yusuf yace." Itace yarinyar Dady." Sosai General yayi mamakin kankantar ta ya kalli Hakkim cike da takaici yace." Meye abun duka jikin wannan k'aramar yarinyar."? Sunkuyar da kansa kasa yayi. Yana jin tsoron kar dady ya tsinkashi a gaban mutane. Ladidi ta ruga kicin da gudu! Duk suka bita da kallo. D'alha kamar yasan abunda zatayi ya mike da sauri zai bita.sai gata ta futo hannunta rike da doguwar muciyar da Iya take dama koko tayi kan Hakkim da gudu. Hakkim yasan gurinsa ta nufo sai ya shirya tsaff ta d'aga muciyar da k'arfi zata maka masa.ya rike ta da sauri yw fuzgota sai gata ta fad'o jikinsa,cike da mugunta ya wurgar da ita gurin kanta ya bugu da bango ihu!! Ta kurma tana fadin." Wayyo kaina."!! D'alha yazo ya daga ta cike da jin haushi ya kwarfa mata mari yana fad'in." Ashe rashin lafiyar naki na k'arya ne." General yace." Yi mata a hankali samari." D'alha yace."Alhaji baka San halin yarinyar nan ba ne." General yace." Koma meye dai ni ta burge ni tunda take k'okarin k'watar 'yan cinta ga Wanda ya cuce ta, saboda rashin imani kamar Hakkim da shekarunsa da komai ya zage k'arfin shi kan yarinya k'arama kamar wannan." Mai koko tace." Alhaji bamu game me kake nufi ba."? General yace." Wannan da yake zaune shine ya sumar muku da ita jiya nine kuma mahaifinsa Nazo domin in nemi afuwar Ku." Iya ta mike tsaye da sauri ta gyara d'aurin zaninta tace." Ko dana ji ahwo!!! Shiyasa naga yana sinne kai tamkar b'arawo a hannun mata,wato dama kaine kake k'okarin kurman tamin da jikita. ? Babu shakka Ladidi ta kurmance sai munyi sha'ra'a dakai." Wani mugun haushin Matar yaji a zuciyarsa yace." Da zata kurman ce ma ai da kowa ya huta da alak'ak'ai." Ladidi ta taso da sauri tana rike Iya tana kuka take fad'in." Iya kar ki barshi nima bazan barshi ba." General yace." Innalillahi wa'inna ilahi rajinu. Ashe abun yayi tsanani haka,shiyasa zuciya ta kasa amunta nace dole sai Nazo naga halin da take ciki. Tabbas dole ki dauki hukunci Iya amma ki zauna muyi mgn dake ta fahimta. " Mai koko ta koma ta zauna tana maida nuffashi Ladidi ta jawo jikinta ta rungume ta tana rarrashin ta. Haushi duk ya tuk'e D'alha ya kalli General a nutse yace." Alhaji ka kwantar da hankalin ka don Allah ni nasan duk abunda ya faru da dalili haka kurum shi bazai kamata ya doke ta ba." General yace." Haka kake gani samari inace gashinan a gabanka ya wurgar da ita da mugunta ta buga kanta a hango ko baka gani bane."? D'alha yace." Nagaji Alhaji ai kana ganin abunda tayi masa ko."? Shiru General yayi yana girgiza kansa. D'alha ya bugawa ladidi tsawa tare da fad'in" yimana shiru shashasha kawai kin bude baki kina kukan banza da wofi." Iya tace." K'yaleta tayi kukan ta to kaji."!!!!. General yace."ina me bawa zuciyoyin Ku hakuri sosai domin narasa dame zan fara a halin yanzu amma kafin wani hukunci ya biyo baya ina rokon Ku da muje mu kai yarinyar nan asibiti a duba ta, domin hankalina ya tashi da jin maganar da kikayi." D'alha yace." Dama yanzu zamu tafi asibitin cikin gari." Mik'ewa General yayi yace." Maza Ku futo muje Allah ya kiyaye gaba." Mai koko ta zura mata hijabinta tana goge mata fuska suka futa To gurin shiga motar ma Ladidi ki tayi ta dinga turjewa wai bata yarda ba gurin yankan kai za'a kaisu a siyar musu da kai. Da k'yar Dady ya rarrashe ta ta shiga motar. Hakkim kamar ya Dora hannu aka Dan takaicin ta. *Comment vote and share* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` *LOADING:* *{LADIDI K'WADAGA🌚}* _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain our reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_ *DEDIGATED* *TO* *RAHAMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿24* Cikin gari suka futa General yace." Zamu samu pravite hospital anan kurkusa sai mu tsaya kawai ba sai mun je babban asibiti na Murtala ba." D'alha yace." Za'a samu Alhaji." Yace." Sai mu tsaya anan kawai a duba ta." Cikin birget suka samu hospital.Hakkim ya kashe mota duk suka futo suka shiga ciki. Idan da kud'in ka babu wahala da kaskantar da kai da zakayi,D'alha yayi mamakin yanda ma'aikatan asubitin suke karrama Alhaji sai rawar jiki suke.nan ka yanki kati likita na ofis General yace." Da Ladidi tazo su shiga tare. Mak'ale kafad'a tayi tana b'uya bayan Mai koko, murmushi yayi yace." Zo muje ciki dactor ya duba ki kinji ko." Ladidi ta zumb'uro baki gaba. Yace." Dawa-dawa kike so mu shiga tare." ? Shiru tayi masa. Haushi yasa D'alha ya buga mata tsawa tare da fad'in." Idan baki sake ta wallahi sai Nazo nan na gaura miki mari." Mai koko tace." Kaga D'alha rabu da ita don Allah.Ina dalili nifa wannan asibitin be kwanta min a rai ba,asibiti ko ina sanyi hatta k'afar ka in ka aje ta a kasa sanyi ga wasu abubuwa a bango naji fa ana cewa wasu asubitin duk barna suke aikata wa. Gwara muje na Murtala kawai." Takaici ya hana D'alha cewa komai. General yace." Iya wannan hospital din ana biyan kudi sab'anin sa dana gwamnati kenan kinga ai baza mu bi wannan dogon layin ba, kiyi hakuri mu shiga tare dake babu abunda za'ayi mata." Mai koko ta kalli Ladidi tana yi mata magana k'asa-k'asa sannan ta sake ta suka mike General yayu gaba suka bishi a baya. D'alha ya nemi guri ya zauna yana sauke ajiyar zuciya. Hakkim kuwa takaici ya hanashi cewa komai yarasa me yasa Dady ya damu da al'amarin yarinyar nan wallahi. Shiko Yusuf Dariya yakewa Ladidi ganin yanda take ta kalle-kalle kauyacinta kawai take. Dactor suka gaisa da General cikin mutum ci yana tsokanar Ladidi bata San ma yanayi ba domin tana can tana kallon tv mak'ale a bango na wani India film na fad'a, amma ba fassarar hausa bace. Dariya ta kyalkyale dashi tace." Iya kalli wannan film din ki gani don Allah, na fada miki afton nan Dan bala'in ne hinefa singam da nake fada miki,hahahahahaha." General da Dactor suka saki baki suna kallon mara lafiya tayi tsalle gaban tv tana kallo tamkar zata rikito da ita daga sama. Wannan karon kunya ce ta kama Iya ganin abunda Ladidi take babu kamun kai,kokari kawai take tayi tsalle ta tab'o tv in da jarumi Ajay devgan yake ragargaza 'yan gidan boss da bundigar sa,Ihu!! Kawai ta kurmawa tana buga tsalle. Sosai dariya take cin General yana k'okarin dannewa sai da ta subuce. Ganin yana dariya yasa Dactor ya fara yi shima Suna kallon juna. Iya tana k'okarin kamo ta tana fuzgewa duk kunya ta ishe ta gashi tun farko dama bata iya sarrafa Ladidi. Dactor ne da ya gaji da abunda take ga jama'a a na jiran shi a waje yasa ya buga mata tsawa! Tare da fad'in." Ki nutsu yanzu ko in sa a zo a zuk'i jinin ki kuma inyi miki allura goma.'' Firgigit ta dawo nutsuwar ta jin zan can Allura sai taji kallon ya fuce mata daga rai mugun tsoran dactor ya shiga zuciyar ta simi-simi ta dawo kusa da Iya tana zare ido.! Iya tace." Ke kam anyi mara wayo wallahi ke da baki da lafiya kike tsalle-tsalle." Da sauri tace." Nifa lafiya na lau ni dai kice kar ayi min allura bana so." General yace." Ai dama ba allura za'ayi miki ba, dawo nan kusa dani dactor ya duba ki kaman matsalar kunnen ki,sai ya baki magani bazan bari yayi miki allura ba." A d'arare taje ta zauna inda yake nuna mata sai harara Dactor take yi, bai lura ba yana can yana aikin sa. Ya d'ago kansa a nutse yace Alhaji meye Matsalar ta ne." Iya da ba'a tambaya ta fara zayya no masa abunda ya faru." A hankali ya ambaci sunan Ladidi Wanda ya gani jikin kati wato Amina sai yaga bata dago kai ta kalle shi ba, da Ladidi ya kira ta da k'arfi sai ta dago kanta tana kallonsa. Mik'ewa yayi hannunsa rike da wani Abu,ganin yana zuwa inda suke ne yasa ta tsora ta ga wani Abu a hannunsa. Kafin General ya ankara ta buga tsalle, wajan kofar futa suka tsince ta tana kici-kicin budewa ta futa. General ya mike da sauri yana kiranta ko sauraron sa ba tayi ba Allah ya bata sa'a ta bude tayi waje da gudu.! Su Hakkim na zaune reception suka ga futowar ta kamar walkiya tayi kofar futa. D'alha gyangyad'i yake bai ganta ba, kasan cewar jiya baccinsa ragagge ne. General suka gani ya futo hankali a tashe yake fadin "Tana ina ne." Kofa ya kalla yaga gilmawar ta ta futa, ya bugawa Hakkim tsawa tare da fad'in" Maza tashi kaje ka dauko ta.wato kana kallo ta futa baka yi wani Abu akai ba ko."? Hakkim ya mike da sauri ya futa yana kunshe dariya yaji dad'i da Ladidi ta nunawa Dady wacece ita. General ya jin gina da hango yana sauke ajiyar zuciya gefe guda kuma yana mamakin halin yarinyar kamar aljana, yanzu ya fara sarewa da lamarinta. Hakkim na futa ya hango ta bakin get tana rigima da masu gadi, dole sai sun barta ta futa su kuma sun hanata saboda ganin yanda ta futo daga ciki tana fella guda sai kace me tab'in hankali. Kuma sunga lokacin da suka zo cikin mota sosai asibiti yake da tsaro. A hankali ya Isa inda suke dama tun kafin ya k'arasa yayi shiri ya tattate hannun rigarsa, yana isa ya sunkuce ta, sosai ya rike tamau! Ya had'e k'afafun ta da hannaye ta ya sab'a a kafad'arsa. Ladidi ta dinga ihu! Tana zandare masa a baya Hakkim ya rik'e hannuwan balle ta doke shi, sai ta kafa kanta a wuyansa ta gartsa masa cizo. Ko a jikinsa, bai sauke ta ba sai ya kaita har ofis din dactoe. Iya tace."Sannu na yaba da k'okarin ka samari da baka d'auko ta ba wallahi futa waje zatayi k'arshe mu rasa inda take, Maza danne ta likita ya duba ta." Hakkim ya b'ata fuska bai mata komai ba ya fara k'okarin futa sai suka ci karo da General da D'alha suna k'okarin shigowa, Dady yace." Koma muje ka riketa a duba kunnen nata. Babu yadda ya iya ya koma ya zauna kan wata kujera Ya jawo Ladidi tana turjewa ya rike tamau! A jikinsa Dactor yazo da Abu a hannunsa ya kunna hasken sa, ya kafa kunnen Ladidi yana dubawa. Ihu!!!!! Take kurmawa tun k'arfin ta,tana haure-haure da hannuwata da k'afafun ta tare da ya kushin Hakkim ko ta Ina.ganin hakane yasa D'alha zuwa gurin ya rike hannunwan nata tamau! Dactor ya cigaba da aikinsa. *COMMENT VOTE AND SHARE* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` *LOADING:* *{LADIDI K'WADAGA🌚}* _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain our reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_ *DEDIGATED* *TO* *RAHIMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿25* Hakkim zuciyar sa zafi take masa yana jin kamar ya saki Ladidi ta fad'i kasa saboda yanda take ta faman duk k'irjinsa duk ta ya kushe masa fatar hannunsa ga majinarta da miyau duk sun b'ata masa jikinsa, lokaci guda yaji zuciyarsa na tashi kyamkyamin Ladidi yake sosai.ya dinga kauda fuskarsa har dactor ya gama dube-duben sa ya matsa daga gurin. Da sauri ya sake ta ta fad'i kasan gurin ya mik'e da sauri yana duba jikinsa. Saboda fargabar da suke ciki babu Wanda ya damu da fad'uwarta a gurin itama bata damuba ta mik'e zumbur tana sharb'e hawayen fuskar ta. General ya k'araso kusa da ita cikin taushin harshe yace." Yi hakuri kinji Aminatu kinga ni ai na fada miki ba allura za ai miki ba kin tashi hankalin ki da namu kiyi shiru ki fada min me kike so in siya miki." Ya k'arashe maganar sa lokacin da suke zama kujerar dake fuskantar ta dactor. Tsabar takaici da b'acin rai yasa Hakkim kasa cewa komai ya bude kofa ya futa a fusace.!! Dactor ya gama rubuce-rubucen sa ya d'ago yana kallon General yace." Alhaji gaskiya ta samu matsala daga kunnen ta na hagu, Wanda ya dumd'e ba taji sosai ta bangaran sa,amma insha Allahu in an bi doka zai dawo dai-dai yanzu zan dorata kan magani kuma kullum za'a dunga kawo ta ana mata wankin kunnen tsahon sati uku, insha Allahu idan akayi haka za'a samu maslaha." General ya d'aga kansa cike da takaici yake Neman Hakkim a gurin sai ga babu shi girgiza kai yayi ya maida kallonsa gurin Dactor yace." Babu damuwa dactor INA so ka tsaya min kan yarinyar nan domin bana so ta rasa wani Abu me muhimmamci a rayuwar ta mussaman ma kunne domin jikin dan Adam yana da muhimamci duk abunda ake buk'ata zan biya insha Allahu a kula min da ita." Dactor yace." Insha Allahu za muyi iya iyawar mu Matsalar daga yarinyar ne Allah yasa ta bamu hadin kai." General yace." Insha Allahu babu Matsala." Dactor ya mik'e tsaye yace." Muje pharmacy zan had'a mata magani gobe misalin takwas na safe sai a kawo ta domi fara yi mata wankin kunne." Duk suka mik'e suka futa a reception suka zauna Dactor shi da wata nurse suka nufi dakin magana. General ya dinga laluben inda Hakkim yake bai ganshi ba Yusuf ya kalla da fuska a daure yace." Ina Hakkim yake.? Kai a sunkuye Yusuf yace." Ya tafi sanjo kaya." Cike da mamaki General yace." Kamar yaya ya tafi sanjo kaya wato yana nufin mu tsaya jiran shi ya tafi da mota sai sanda ya ga damar dawowa ko me.? K'asa da kai Yusuf yayi cike da girmamawa. General yace." Ya kyauta ai." Suna zaune Dactor ya dawo hannunsa rike da Leda me tambari da sunan hospital din nasu cike da mugunguna nasha dana digawa a kunne dactor ya mik'awa General yana fad'a masa yanda za'ayi amfani dasu. Nan General ya karb'i numbar account ni dactor din domin ya turo musu da hakkin su sukayi sallama suka futa. Hakkim ne ya shigo asibitin cikin mota General ya sauke ajiyar zuciya a fili yace." Kayiwa kanka k'iyamun laili wallahi da ka bari mun bi motar haya sai na b'ata maka rai." Shiru yayi yana sunkuyar da kai kasa ya sanjo kaya yanzu yana sanye da wata lafiyyyare shadda geznar sai maiko take brown ce babu hula kanshi sai sumar shi tasha gyara da alamu sai da ya sake sabon Wanka kafin ya dawo. General da kansa ya budewa Ladidi kofar ta shiga su Iya da D'alha suka shiga sannan ya shiga, Yusuf ya zauna kusa da Hakkim ya ja motar Dady na d'agawa Dactor hannu. General ya zurfafa a tunanin yaya za'ayi wannan bayin Allah su yarda da shawarar da ya yanke kan Ladidi, zuciyarsa a dake ya kalli Mai koko da tayi tsumu! Cikin hijabi tana shan Ac mota sai zare ido take yace." Iya akwai shawarar da na yanke kan Aminatu. " Mai koko ta kalle shi tace." To Alaji ai babu komai ka fada min naji ai kana da kirki kai kam ko ajikin masu kud'in samun kamar ka sai an tona lallai albasa batayi halin ruwa ba wancan yaron naka me zuciyar kafurai da rashin imani." Tafad'a tana hararar Hakkim dake driving Takaici kamar ya kashe D'alha Ji Iya da wata magana don Allah ya juyo yana kifta mata ido Iya ko ganewa ba tayi ba ta cigaba da surutun ta daga ni tana cike da jin haushin Hakkim din. Sai da General ya Bari ta gama surutun nata sannan yace." Dama cewa nayi me zai hana Aminatu ta dawo hannuna saboda shan maganin ta kan k'aida idan yaso idan lokacin da dactor din ya d'iba ya cika sai ta dawo gurin ki ko yaya kike CE." General ya karashe maganar a tausashe domin ya lura tsohuwar yar taratsatsi ce. Mai koko ta kalli General baki na rawa tace." Me kake cewa Alhaji."!!!!!!? *Inga ruwan comment da dogon sharhi kan book din nan idan ba haka ba tammm! Zan mai dashi........ Ba sai na fada ba kun San sauran ehe, ko ta ina ina ga ruwan comment na zuba Lol😄* *COMMENT VOTE AND SHARE* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` *LOADING:* *{LADIDI K'WADAGA🌚}* _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain our reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_ *DEDIGATED* *TO* *RAHIMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿26* General yace." Iya cewa nayi ki bar min Aminatu a hannuna domin tafi jin dadin karb'ar magani cikin nutsuwa kinga lalurar tata tana buk'atar hakan ,zamu zauna da ita a gidana na nan garin tsawon lokacin da dactor din ya fad'a insha Allahu komai zai yi dai-dai." Girgiza kai Mai koko tayi tace." Ayyo! yanzu na fahimci inda ka dosa Alaji, ni kam ban amunce ba domin bazan iya baku ladidi ba ta zauna tare da wanda yayi yunk'urin nakasta ta." General yace." Maganar ki haka take Iya amma wannan karon ina me tabbatar miki da cewar idan Hakkim ya kuskura hannunsa ya sauka kan Aminatu da sunan duka to babu shakka zan dauki k'wak'warar mataki kansa." Girgiza kai Iya tayi tace." Oh!-oh! Ni kam ban yarda ba Alaji kawai ka bamu magani ai naga lokacin da likita ya ke nuna maka yanda za'ayi amfani dashi sai in dinga bata." Shiru motor tayi kowa na tunani a zuciyarsa hak'ika General bai ji dadin rashin amincewar Iya ba. D'alha ya juyu a nutse yana kallon General yace." Allah kada ranka ya b'aci kan hakan hak'ika nasan zuciyarka daya ka fad'i haka za mu baka Ladidi kamar yanda ka buk'ata tunda ba nisa zakuyi da ita ba kuna cikin garin nan sai in dinga kawo Iya tana ganinta kullum ina ganin haka yayi ko."? General yace." Haka yayi samari naji dad'i kuma daka fahimce ni sosai da sosai." Iya ta kalli D'alha cike da takaici gani tayi fuskarsa a murtuke sai tayi shiru bata kara cewa komai ba sam bata son b'acin ransa kasamcewar shi kadai ne da ita a halin yanzu. Cike da mamaki suka ga motar ta tsaya gidan gonar dasu ke hira a kwanaki, da sauri Iya tace." Alaji nan ne gidan naka. " ? Da murmushi a fuskarsa yace." Eh nan ne amma ba'anan muke da zama ba ni da iyalina muna abuja, kwanaki na siyi gurin nan nayi gidan gona domin mu dinga zuwa hutu ni da iyalina." Caraf! Ladidi tace." Dama bana fada miki ba Nace gonarmu ce suka sace, mana shine daga zuwa zan tsinko mangwaro ya kamani yayi ta duka ni da gonarmu Allah ya isa ban yafe ba kuma sai na rama." Hakkim tun sanda ta fara magana yake kallonta ta mirror yana jin wani kuttun bakin cikin da takaici ji yake kamar ya tsayar da mota ya futar da yarinyar waje, amma babu hali yin haka. Yanzu tunanin da yake yaya za'ayi ya bar garin domin dai bazai iya had'a guri da ita yana jin zai iya kasheta saboda yanda yake jin zafinta a cikin zuciyarsa. Dariya General yayi jin abunda Ladidi take fada ya kalli D'alha dake sunkuyar da kai cike da kunya yace." Hakane abunda ta fad'a 'yan samari."? D'alha ya sunkuyar da kansa kasa sosai yace." Hakane Alhaji mun siyar da gurin ne ni da mahaifina kafin rasuwar sa shekaru goma sha biyu da suka wuce,sai dai ba duka ne gurinmu ba." General yace." Ayya! Allah ya jikansa da rahama, ya kyauta makwancin mazan jiya hak'ika nasan babbar matsala ce tasa ya daga gonarsa ya siyar haka." D'alha yace." Hakane Alhaji. " General yace." Ku futo mu shiga ciki ai duk Iyalina na ciki sai Ku gaisa." Futowa sukayi dukaninsu, banda Hakkim shi tunda yayi parking gurin da aka tanada domin aje mota yayi fucewarsa ya barsu cikin motar. Kai tsaye sharararn farlo suka nufa dukansu, Iya sai kalle-kalle take na k'auyanci ita ko Ladidi dama ba wannan ne zuwanta na farko ba. Hajiya Asiya na hakimce kan kujera da romot control a hannunta tana neman tashar kallo, Salima ta Dora kanta a cinyarta suna hira, suka ji sallama. Hajiya Asiya ta amsa a nutse tana yi musu sannu da zuwa, Salima ta mike da sauri tana kallon Ladidi cikin tsoro. General yace." Bisimilh Ku zauna mana." D'alha ya zauna yana satar kallon farlo. Iya ma haka suka zauna guri guda da Ladidin ta. Cike da farin ciki Hajiya Asiya tace." Alhaji da alama waccan CE yarinyar."? Yace." Itace Momy kin ganta k'arama ko." Tace." Wallahi kuwa, zo nan kinji mu gaisa." Tafad'a tana mik'awa Ladidi hannu." Kin zuwa tayi sai da D'alha ya buga mata tsawa sannan ta tashi tana zumb'ura baki. Mama tace. " kayi mata a hankali mana." Ladidi ta k'arasa kusa da ita, da sauri Salima ta mike ta bar gurin jikinta na b'ari! Kusa da Dady dinta ta koma tana zare ido! Ya kalleta yana fadin." Ga 'yar uwa na kawo miki zata zauna damu sati uku ta karb'i magani Dan uwanki yayi mata lahani ke shaida CE kin gani da idon ki." Hajiya Asiya tace." Alhaji ban fahimci abunda kake nufi ba." Nan General ya warware mata duk abunda ya faru da abunda dector yace . salati kawai takeyi tana duba kunnen Ladidi tace." Oh ni Asiya yaro na nema ya jawo mana masifa." Mai koko ta kalla tace." Kuyi hakuri don Allah tsautsayi ne." Mai koko tace." A'a babu komai ai ya wuce. Sai dai ga Ladidi nan amana Ku kula da ita domin marainiya CE, zan dinga zuwa kullum ina dubata" Hajiya Asiya tace." Ai kar ki damu Iya insha Allah za kula da ita yanda ya kamata Allah ya bawa zuciyoyinku hakuri dai." D'alha yace." Ai magana ta wuce mu zamu tafi gida." Mik'ewa sukayi suna shirin tafiya. Abun mamaki sai naga Ladidi ko a jikinta ta nemi guri ta zauna gami da tsurawa TV ido fuskarta d'auke da murmushi sai motsu-mutsun dad'i take, TV din D'alha ya kalla sai yaga jarumi Salman khan da kayan 'yan sanda a jikinsa yana suburbud'an 'yan gidan boss! D'auke kansa yayi cike da takaici. Iya ta kalleta tare da fad'in."Ladidi mun tafi babu rakiya ne."? Inaa!! Ladidi na can ta na kallo tama manta dasu a gurin. *COMMENT* *VOTE AND* *SHARE* *16/October/2009* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` *LOADING:* *{LADIDI K'WADAGA🌚}* _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain our reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_ *DEDIGATED* *TO* *RAHAMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿27* General yace." Iya Aminatu ta samu kallo ai ba zata saurare ku ba." Murmushi Mai koko tayi tace." Aikam gashinan naga alama Humm Ladidi da son kallon talabijin ai sai addu'a." Dariya sukayi dukaninsu Hajiya Asiya ta mike domin tayi musu rakiya, tare suka futa harabar gidan Wanda yayi dai-dai da shigowar Salim cikin mota yana k'okarin gyara parking General yace." Ya bari tukkuna ga bak'i nan ya mai dasu gida, cike da mamaki Salim yake kallonsu suka gaisa sama-sama ganin kallon da yakewa su D'alha na rashin sani yasa ya fara yi masa bayaninsu, sai ya saki fuskarsa sosai suka shiga mota General na daga musu hannu suka futa daga gidan. Salima kuwa da aka futa aka barta ita da Ladidi cike da tsoro take kallonta, sai taga Ladidi kwata-kwata hankalinta baya kanta tana can tana kallo abunta. Muryar ta na rawa tace." Ya sunan ki na gaskiya."? Ladidi ta juyo fuskarta d'auke da murmushi tace." Amina kefa."? Tace." Salima sunana." Dariya Ladidi tasa tace." Sunan 'yan gayu 'yan burni da dad'i Wallahi. " Salima tasa dariya wanda yayi dai-dai da shigowar su General yace." Yawwa Salima kuje da ita ki nuna mata komai tayi wanka sosai sai kuzo muje cikin gari a siya mata kayan kwalliya irin naki domin so nake Aminatu ta dawo 'yar burni.' Ladidi ta buga tsalle ta koma kusa da General tana washe baki tace." Ni so nima wallahi baba daga yanzu ka zama Ubana zan zauna daku ina sha'awar Ku." Tausayin ta yaji sosai yace." Muma muna sonki Aminatu zan nemi alfarma gurin Kawun ki ya bani aronki in sanya ki a makaranta.". Murna sosai ta dinga yi, Hajiya Asiya taji tausayin ta da so da kaunarta. Nan Salima ta jata d'akinta suka shiga toilet ta nuna mata komai. Dake Ladidi akwai saurin fahimta bata sha wahalar hada ruwan Wanka ba tayi tsaf ta wanke bakin ta da miskilin kamar yarda Salima ta nuna mata ta futo daure da towol Wanda ta aje mata. Salima ta kalleta tana b'oye dariya ganin yanda kanta yake babu gashi duk yayi cibiri-birici gashi nan ya fara futowa ta wanke shi tas! Tace." Yanzu in muka shiga cikin gari za siya miki man gashi me kyau daka gani kina da kufan gashi ganin ya fara daga farko sinkif dashi." Ladidi ta zauna kusa da ita tace." Kwarkwata ce ta dame ni shine Kawuna yasa aka aske min amma duk cikin k'awayena babu wacce ta fini gashi." Salima tace." Aikuwa naga alama gashinan ai.yanzu ungo wannan kayan ki sanya a jikin ki sai kizo muje farlo." Ladidi ta kalli kayan da Salima ta mik'a mata, ta sanya hannu ta karb'a da fuskarta da murmushi tace." Ina son mai sona nagode sosai wallahi ina son babanku." Salima tace." Dady ya gode, ai mu 'yan gidanan haka muke ba yabon kai ba duk Wanda ya zauna damu sai yaji yana son mu." Ladidi ta mike tsaye tana k'okarin saka kaya tace." Amma banda mutum daya a cikinku na tsane shi wallahi." Salima tace." Wai kina nufi Yaya Hakkim."? D'aga kai tayi tana saka riga a jikinta, Salima tasan dalilin da yasa tace haka sai ta basar da maganar kawai. Tace "baki saka vest a ciki ba." "K'yaleni haka wannan shimin takura min take." Ladidi ta fada tana zura siket a jikinta sosai Riga da siket na atamfa Ghana suka yi mata kyau tamkar an gwada jikinta kasan cewar Salima itama bata da wani jikin kirki bayan haka kuma bata da tsayi sosai ga yanayin dinkin 'yan matan abuja a matse shiyasa kayanta suka yiwa Ladidi cif. Tare suka futa farlo Ladidi sai hardewa takeyi na rashin sabo saboda siket din ya dame mata cinye sosai yanayin rigar yasa k'irgar danginta suka futo currr! Kamar gobar da bata gama nuna ba. Lokacin da suka futo Hakkim ya shigo yana zaune cikin kujera yana cin magani duk yak'i kula kowa. Ladidi na gano shi ta zabga masa harara tana zumb'ura baki sosai ta tsane shi.Hajiya Asiya ta d'an d'aga muryar ta yanda Ladidi zata ji sosai tace." Iyee! Aminatu ashe haka kike da kyau bafulatana dake, kin ga yanda kikayi kyau kuwa zo nan 'yata." Ladidi ta washe bakinta ba tun yau ba take son taga ana cewa tana da kyau da sauri ta je gurin Hajiya Asiya sai wata dariya take ta shashanci. Salim da Yusuf sai b'oye dariya suke kar suyi ransu ya b'aci gurin Dady Dan ma baya gurin. Ta zauna kusa da ita tace." Hajiya da gaske kike ni me kyau ce hehehehe."! Ta kyalkyale da dariya. Hajiya Asiya tace." Sosai kuwa wallahi son kowa kin wanda ya rasa." Dariya su Yusuf ce ta dawo da hankalinta Kansu ta daina dariyar haukan da takeyi ta kalli Hajiya cike da b'acin rai tace " kin ga sunayi min dariya ko.'' Rai a bace Hajiya Asiya tace." Wallahi duk Wanda ya kara yi mata dariya nan gurin ransa zai b'aci." Shiru sukayi dukaninsu Ladidi ta b'ata rai sosai tana tabkawa Hakkim harara shida bai ko kalli inda take ba A Karaf! Suka had'a ido dashi yana kishingid'e cikin kujera da airpic a kunne shi,zare mata ido yayi sosai wai taji tsoran shi,aikuwa itama ta zare masa nata tana zabga masa k'atuwar harara tare da murgud'a bakinta. Cike da mamaki ya yunk'ura ya tashi sosai yana kallonta itama ta kafe shi da idonta kwala-kwala, tsaki! Yaja me sauti k'asa-k'asa yace." Yarinya ita ba mutum ba ba aljan ba ba mayya ba dubi wasu ido kamar daffafiyar gurjiya." Babu Wanda yaji abunda yace a farlo saboda surutun da suke yi Hajiya Asiya ma nacan tana saka musu baki. Ladidi duk taji abunda yace da ita. Tayi k'wafa had'e da girgiza kanta itama a hankali tace." Dube shi wai shi Dan burni da hanci sai kace na butorami. Hahahahahahaha"!!! Ta shek'e da mahaukaciyar dariya. Duk suka juyo suna kallonta cike da mamaki sosai Hajiya Asiya tace." Aminatu Lafiyar ki k'alau kike dariya haka."? Bata fasa dariyar ba ta nuna mata tv da hannunta Hajiya Asiya ta kalli TV sai ga mage da b'era suna gudu sun sato nama a kicin din wata mata." Dariya tayi kawai tace." Aminatu kenan. Salim da Yusuf kuwa kus-kus suke DOMIN suna ganin al'amarin yarinyar kamar da almutsutsai a ciki. Gogan Ku kuwa, cikin zafin zuciya ya mik'e tsaye yana wani irin huci yayi ball da k'afafunta dake kan hanya y ma fuce yana Jan wani mutsiyacin tsaki!! Mtssssssss!! Kallo suka bishi dashi cike da mamaki.Ladidi ta cigaba da sheka dariyar ta har ya futa waje yana jinta. Zama yayi cikin wata rumfa yana sak'e-sak'e yau d'in nan zai bar garin nan. Domin zuciyarsa zata iya bundiga in yana kallon mummunar fuskar yarinyar nan me kama da Aljanu. *17/October/2009* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` *LOADING:* *{LADIDI K'WADAGA🌚}* _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain our reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_ *DEDIGATED* *TO* *RAHIMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿28* *Saturday* *19/October/ 2009* ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^ Girgiza kai kurum Hajiya Asiya tayi saboda tasan halin bak'ar zuciyar yaron nata, shiyasa basa shiri da Dadynsu wani lokacin saboda baud'ad'an ra'ayinsa, wanda shima General din ba baya bane gurin baud'ewa kusan ma shi Hakkim din ya gado. Ladidi kuwa gyara zama tayi tana kallon ta sai dariya take shekewa tun abun na basu mamaki yazo ya daina basu suka cigaba da hirarrsu nan General din ya sauko daga sama ya same su,ya shirya tsaf da shi cikin manya kaya ya kalli Ladidi yana murmushi yace." Aminatu kallo kike ne."? Cike da farin ciki tace." Eh Baba." Yace." Da kyau yanzu abunda za'ayi shine ki aje kallon muje mu dawo kin jiko." Ladidi tace." To Baba" Mik'ewa tayi idonta akan tv ta kasa daukewa." Hjy Asiya tace." Kuje Ku dawo ai yananan yana jiran ki." Dariya tayi kamar wata shashasha ta bi bayansu General tana waiwayen tv Su Yusuf kallonta kawai suke cike da mamaki.! Buge kanta tayi garin waige ta dafe gushin tana sakin ihu!! Duk suka maida hankalinsu kanta Hjy Asiya tace." Aminatu ho!! ki rage wannan k'auyancin naki don Allah." Ladidi ta fuce tana zumb'ura baki. Tana futa Yusuf da Salim suka kwashe da dariya dama saboda kar suyi a gabanta ne ta fadawa Dady Hjy Asiya itama tasa dariyar tana ta yasu. Yana zaune gurin hutarwar ya hangi futowar su, tun daga nesa yake k'arewa yarinyar kallo zuciyarsa na sak'a masa abubuwa da yawa a kanta, sosai yake jin zafin abunda tayi mishi farkon zuwan shi gidan. Yana jin wani irin haushin ta gami da k'yamarta domin shi ramar ta ma tsoro take bashi yarinya sai kace muciya sai kai da uban ido kwala-kwala jiki duk jijiya. Saurin d'auke kansa yayi da yaga Dady ya d'ago kansa yana dube-dube aikuwa karaf ya hango shi zaune. Daga murya yayi tare da kiran sunan shi. Ya amsa cike da ladabi ya taso. Ladidi na tsaye hannuta rike da murfin mota ta dinga banka masa harara tana ya mutse fuska duk cikin'yayan General shi kadai ta tsana tunda baya kaunar ta. Cike da bada umarni General yace." Ka shiga ka tuk'a mu zamu shiga kasuwa yanzu." Sunkyar da kansa kasa yayi yana sosa kai kamar munafuki yace." Dady da ina so in koma abuja ne yanzu shirin da nake kenan wallahi." Wani kallo General din yayi masa yace." Ka koma abuja kayi me."? Kansa ya Sosa yana shirin kirkiro k'aryar da za shirga. General din yace." Kaga Malam bama son rashin abunyi kawai ka shiga mota kamar yanda nace.ai na gano abunda zai sanya ka koma abuja yau din." Cike da takaici Hakkim ya bud'e kofar mota mazaunin dravar ya shiga yana jin wani kunci da takaici a zuciyarsa Wato shi ya zama dravar kenan ? Shi da yazo Hutu an mai she shi dravar saboda tsabar bashi da galihu dravar ma na kucakar yarinya 'yar k'auye me kwarkwata gami da karzuwa, ya zame masa dole ya bar garin nan.domin ya fuskanci Dady ya shirya tsaf! Gurin ganin ya kuntata masa. Suka hau titi sosai sai gudu yake Ladidi ta tsira da k'arfi tace." Baba kace dashi ya daina gudu nan da yake tsoro nake wallahi." General yayi saurin kallon Hakkim yace." Ka kula mana ka rage gudu sai shilla mu kake kamar zamu tashi sama." Hakkim bai san sanda ya daki kan motar ba saboda tsabar takaici wato yanzu Dady shima umarni Yarinyar take bashi. General yace." Kai meye haka kuma? Kai da aka ce ka rage gudu zaka daki kan mota ." Hankalinsa ya dawo cikin wayancewa ya Sosa kansa bai ce komai ba ya rage gudun da yake yi. Shi ko General ya juya ya cigaba da hirarasa dasu Ladidi wacce Salima take ta zolayarta ita kuma sai zantuka take mata irin na shashanci. A hankali yace." Dady mun futo cikin gari wace kasuwa zamu shiga ne." ? General yace. " anya kuwa zamu shiga kasuwa yanzu dubi lokaci 1:00 na rana muje Sahad stor kawai duk abunda ake bukata za'a samu." Bai ce komai ba ya juya kan motar zuwa Shahad Sto zuciyarsa na masa zafi DOMIN ya fuskanci Ladidi za'ayiwa siyayya. Parking yayi inda aka tanada suka futo shi kuma ya gyara zama cikin motar bashi da niyyar futowa.General yace." Ka futo mu shiga tare mana." Girgiza kansa yayi tare da fad'in "Dady Ku shiga kawai bana bukatar komai." General yace." Sai ka futo fa domin ni banga amfanin zamanka cikin motar ba." Hakkim bai iya musu ba bare ga mahaifinsa sai ya bude mota ya futo kawai yana jin taikacin takura sa da Dady yayi abunda ba halinsa ba. Suna shiga ya samu kujera ya zaune fuskar nan a murtuke,wayarsa ya Ciro yana latsawa . Dady suka wuce ciki shida su Salima.Ladidi sai K'auyan ci take zubawa sosai jama'ar da suke ciki suka dinga kallonta kamar sun samu TV Dady sunyi gaba shi da Sallma bai San ta tsaya a baya ba, tana hauka ganin wani takalmi me mugun tsini da jakarsa cikin wani glass sai d'aukar ido yake kokari kawai take ta bude glass din ta Ciro takalmin fad'i take." Yeeeeeh kan uban can kunga wani hegen takalmi kamar jirgin sama wallahi sai na d'auko hi." Hannunwanta biyu ta sanya tana k'okarin zuge glass din sai wata mahaukaciyar dariya take. Aikuwa kan kice kwabo jama'a sun fara Ciro wayoyinsu suna mata video suna dariya, wata mata tazo ta riketa tana fadin "Ki tsaya mana a zo a bude miki." Bangaje ta tayi ta fad'i a gurin.daya daga cikin ma'aikatan gurin ya k'araso da sauri yana mata magana, ko kallonsa ba tayi ba ta cigaba da abunda takeyi. Cikin zafin rai ya k'araso gurin ya juyo da ita a zafafe ya shimfid'a mata wani bahagon mari! Ji kake Tass! Tass! Har sau biyu. https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` *LOADING:* *{LADIDI K'WADAGA🌚}* _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain our reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_ *DEDIGATED* *TO* *RAHIMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *23/October/2019* *29* Wani uban ihu! Ta kurma Wanda ya jawo hankalin mutane da dama dake cikin gurin ciki kuwa harda General da Salima dake can b'ngaran kayan tea Salima na had'awa, da sauri General ya aje kwalin Milo dake hannunsa domun ya fahimci Ladidi ce take kurma ihu!! Yana zuwa yaga dandazon mutane sun kewaye ta, ga Hakkim a tsaye a kanta yana zazzaga mata masifa tare da zaginta da fada mata munanan maganganu. Cike da b'acin rai ya k'arasa gurin yace." Wai me yake faruwa ne? Take wani ma'aikacin gurin ya fara fad'a masa duk abunda ya faru, ya kalli Hakkim ransa a b'ace yace" kan ta aikata haka ka dake ta.? Shiru yayi yana kauda kansa yaso Dady bai zo gurin ba ya wulakanta ta cikin jama'a. Genaral ya kalli jama'ar gurin yace" kowa ya tafiyar sa" aikuwa suka watse daga gurin. Ya kalli ma'aikacin dake tsaye a gurin yace." Ka ciro mata takalmin da jakar tunda tana so." Yace." Angama Alhaji." Hakkim tsantsar takaici da b'acin rai yasa ya bar gurin a fusace! Dady ya bishi da kallo yana girgiza kansa. Ladidi ya kalla dake zaune a kasan gurin hannunta dafe da kuncinta sai zumb'ure-zumb'uran baki take yace."gashi nan za'a d'auko miki takalmi ai kina so ko"? Daga kanta tayi ta mik'e tsaye tana buge jikinta General yace." Duk abunda kika gani kina so anan ki fad'a a d'auko miki kar ki kara saka hannu saboda kar kiyi musu b'arna" d'aga kanta tayi, zuwa yanzu itama ta fahimci wautar da ta. tafka, Bayansu ta bi simi-simi duk jikinta yayi sanyi da ganin yanda jama'a suke kallonta wasu na ta b'oye dariyar su wasu kuwa tana kallonsu suna bude wayoyinsu tasan abunda tayi suke dubawa suna dariya kunya duk ta ishe ta taji takaicin zagin da Hakkim yayi mata cikin mutane. Salima ce ta dinga zab'ar mata kaya masu kyau da dogayen riguna gami da undis kayan kwalliya mayafai masu kyau da tsada, tsaf suka kammala Dady ya biya kudi Salima ta fara yunk'urin d'aukar kayan General ya dakatar da ita tare da fad'in" ta kira Abudul a waje." Jiki a sanyaye ta tafi yana zaune cikin mota tace Broth Dady na kiran ka" fuskarsa a murtuke yace." Me zanyi masa dallah Malama kauce ki bani guri" da sauri Salima ta bar gurin, tana komawa tace" Dady gashinan" wani ma'aikacin gurin ya k'araso tare da fadin " Alhaji wannan aikin mu ne" ya fara d'aukar kayan yana futa dasu wajan mota suka biyo bayansa Boot ya bud'e masa yana zubawa General ya kalli Hakkim dake faman d'auke kansa yace." Kaje ka taya shi d'ebo kayan mana" Wani iri yaji a zuciyarsa wai me Dady yake nufi ne? Shi ko General yana sane yake masa haka domin ya k'untata masa ne. A hankali ya futo daga motar ya shiga ciki, su kuma suka shiga motar Hakkim ya dinga futo da kayan yana zubawa a boot zuciyarsa na masa zafi da rad'adi. Sai da sukayi saura sannan ya bar masa ya k'arasa General ya futo da kudi ya bashi, yayi ta godiya ya tafi. Motar ya shiga ya kunna suka bar gurin, General da 'yayansa hira suke sosai babu me saka sunan Hakkim a ciki to shima nashi b'angaran yaji dadin haka, sauri-sauri yake suje gida ko ya daina ganin mummunar fuskar yarinyar duk sanda zasu hada ido da ita ta mirror mugun kallone yake raba su da ita. Suna Isa gida ana kiran sallahr la'asar da sauri ya futo daga motar domin baya so ma wata magana ta had'a shi da Dady din don kar yace ya d'ibi kayan ya shiga dasu ciki. Yana shiga parlor dircat bedroom d'insa ya shiga babu wanda ya kula a cikinsu Salim ne yake masa magana da cewar "broth kun dawo kenan"? Uffan be ce masa ba ya wuce ciki." Hjy Asiya tace" butsu kenan mybe sun tafka rigimar shida Dady shiyasa ya shigo yana bugun iska" Yusuf yace." Aikuwa kuma nasan duk akan Ladidiya ne" Salim yace." Aikuwa na lura yarinyar ta shiga ran Dady wallahi ". Hjy Asiya tace." Ni kaina yarinyar tana bani tausayi sosai na lura shima Dadyn Ku tausayin ta yake ji kasan shi da tausayin tsiya" Yusuf yace "hakane Mama." General na shigowa ya umarci su Yusuf da Salim suje su kwaso kaya cikin mota, suka mike domun cika umarni, daining ya nufa yana fad'in" Zo ki had'a mana abunci mu kwaso yunwa sosai." Hjy Asiya ta mike tana fad'in "ai naga alama gashi wancan sarkin zuciyar ya shigo a fusace kamar zai duke mu." K'wafa general yayi yace." Rabu dashi kinji! Na rasa me ke damun Hakkim wallahi zafin zuciyarsa yayi yawa, Aminatu ya samu Sahad sto ya k'ara duka jama'a suka taro a Kansu." Hjy Asiya ta saka salati tana fad'in " Me tayi masa kuma"? Girgiza kai yayi yace." Ta nuna tana son takalmi to kinsan halin mutuniyar taki da k'auyanci tana k'okarin yi musu barna shine ya yanke wannan hukunci a kanta." Hjy Asiya ta kalli LADIDI dake tsaye tana kumbura kamar zata fashe tace." Zo Amina ke Salima Zo Ku ci abunci." Suka k'araso gurin tare da zama kan kujera. Nan ta hadawa kowa nashi cikin hikima take wa Ladidi Fad'a sosai jikinta yayi sanyi da abunda ta aikata Hjiy Asiya ta kalli Salima tace." Ki nuna mata yadda zata yi amfani da komai ki dinga koya mata abubuwa burni ta fara girma kinga ko zaki girme ta da k'adab ne ki dauketa a matsayin k'anwar ki". Salima tace." Insha Allah Mama na dauki alk'awarin yin haka, sai naji ina ma kakarta zata barma na ita." General yace." Ba ke kadai kike wannan tunanin ba Salima." Haka dai suka ci abunci suna hira , bayan sun gama General ya mike ya shiga bedroom domin yin wanka da sallar la'asar Salima da Ladidi suma suka shiga cikin wani bedroom Sukayi Wanka tare da Sallah nan Salima ta baje kayan tana nunawa Ladidi yanda ake amfani da komai. Magariba kowa ya shiga domin yin sallah Ladidi ta futo parlor taga babu kowa da sauri ta nufi kofar futa, harabar gurin shiru duhu ya fara kawo wa masu gadi duk sun juya baya suna sallah tazo ta bud'e k'aramar k'ofa ta futa, ko ina zata oho!!!! *BINTA U ABBALE* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` *LOADING:* *{LADIDI K'WADAGA🌚}* _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain our reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_ *DEDIGATED* *TO* *RAHIMA ALIYU* ~*ABUJA*~ *26/October/2019* _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿30* Waige-wage take yi babu kowa a layin tsitt!! Kawai ta sai ci hanyar zuwa gidan su tana yi tana waiwayen bayan ta, Hakkim ya futo daga wani massalaci dake bayan layin ya hango ta tana tafiya kamar wata mahaukaciya, bayan ta ya bi da sauri domin ya tsorata mutuk'a yana jin tsoran kar ta gudu Dady ya sirfa masa bala'i yasan cewa zai yi shine ya kore ta, jin ana bin ta a baya yasa ta wai wayo da sauri suka hada ido da Hakkim din a guje!!! Ta falle, siket din jikinta na harde ta, shima gudun ya sanya da k'arfi yana tattare hannun rigar shi saboda ya lura sai yayi da gaske domin yasan halin taurin kan yarinyar. Garin waiwaye taji tun tub'e da wani k'aton dutse ta fad'i a gurin tare da rik'e k'afar ta guda tana kurma ihu!!! Ya k'arasa gurin yana watsa mata wani banza kallo. Cikin wata razananniyar tsawa! Yace." Don ubanki ina zakije? Kurrr!!! Tayi masa da ido tana cije bakinta. Ya k'ara buga mata tsawa a karo na biyu tare da fadin "ba magana nake dake ba ne shashasha mahaukaciya kawai." Da sauri ta mike tsaye tare da fad'in." Kaine mahaukaci bani ba." Cike da mamaki yake kallonta. K'irjinsa ya nuna da hannunsa yace." Ni." Gyad'a kanta tayi babu tsoro a idonta. Wani bahagon mari ya kwarfa mata a fusace! Yace." Wuce muje gida ko yanzu in karasa toshe miki d'aya kunnen naki." Ido jazur tace." Ank'i a wuce din." Janta ya fara yi a k'asa ita kuma tana d'ebo k'asar gurin tana watsa masa a jiki tana zaginsa." Hakkim yaji kamar zuciyarsa zatayi bundiga wai wannan yarinyar wace irin ibilishiya CE ne? Yake fada cikin zuciyarsa. Wayarsa ya Ciro da sauri ya fara Neman numbar Dadyn nasu.General ya dauki wayar da sallama Hakkim din yace." Dady ka futo yanzu ga yarinyar nan a bayan layi na ganta zata gudu." General ya aje wayar da sauri! Ya mik'e Hjy Asiya tace." Wani abun ne ya faru."? Cikin fada yace." Garin yaya kika bari Aminatu ta futa amanar da kika d'auka kenan." ? Hjy Asiya ta mike tsaye da sauri tace." Yarinyar da suke daki ita da Salima Yallab'ai. " futa yayi ba tare da ya tsaya ya saurari sauran zan can ba. Ita kuma ta nufi dakin Salima hankali a tashe! General yana futa ya hango Hakkim na janta kamar Wanda yake Jan ice ranshi ya b'aci da sauri ya karasa gurin yace." Hakkim mutum fa kake ja a kasa ba dabbah ba." Cike da jin haushi yace." Dady kasan halin kaurin kan yarinyar fa, yanzu ma bakaga yanda take zagina ba. Aikuwa kafin ya rufe bakinsa Ladidi ta dibi kasa ta watsa masa k'asa tare da fadin "Allah ya isa mugu azzalimi sai na rama duk abunda kamin kuma na fasa zama a gidan NAKU." Ta k'arashe maganar muryar ta na karkarwa. Hakkim ya sake ta ta fad'i a gurin aikuwa da sauri ta mike zata zunduma da gudu General yayi saurin rike hannunta tamau!! Sai ta soma lauyewa zata fad'i kasa Hakkim ya kalla dake k'okarin shiga gida yace." Zo ka d'auke ta ka shiga da ita ciki Aminatu fitinar ki tayi yawa." Ya fada cike da kosawa. Kukan da take boyewa ne ya kwace mata,kafin kaga Abu yasa ta kuka zaka dad'e. Sosai take kuka General ya tsuguna yana rarashinta ta tubure ita baza ta koma cikin gidan ba kawai ya barta ta tafi gidansu. Umarni ya bawa Hakkim ya d'auke ta ya shiga da ita, babu yadda ya iya ya tattare hannun rigar sa ya fara kokari d'aukar ta ta dinga kawo masa duka da ya kushi yana ji ya naga ni ya sab'ata a kafad'a suka nufi cikin gidan. Ladidi ta dunga dukansa bayansa da gwiwar hannunta tana cizo da ya kushi gami da yi masa Allah ya Isa, shi ko duk yana jinta yana jin kamar ya jefar da ita a gurin amma babu halin yin haka tunda umarnin dady ne. Shi kansa General ya ji haushin abunda yarinyar take yana ji kamar ya kaude ta da mari yarinya me baud'ad'an hali in ka taro ta can sai ta baud'e ta tafi wani guri. Lallai yanzu ya soma ganin halinta. Tsakiyar parlor ya aje ta ya juya ba tare da yace da kowa komai ba ya fuce daga parlor. Hjy Asiya ta k'araso inda Ladidi take tana rarrashinta tare da tambayar ta abunda aka yi mata, kuka kawai take taki cewa komai. General ya kalli Hjy Asiya tare da fad'in" kunna mata kallo ki sanya mata film na fad'a." Aikuwa da sauri ta kunna tv India film ta d'auko ta sanya a DVD film din fassarar Hausa ne na jarumi akshey kumar,,, kafin mintu goma film ya fara d'aukar zafi can na hango ladidi ta warware ta kamar ba itace take kuka da turje-turje ba ta zubawa TV ido tana kallo fuskar ta a sake har ta manta da guduwa gidan mai koko. Hjy Asiya ta kalli mijin NATA tare da girgiza kanta tace." Anya kuwa yarinyar nan bata da matsala a kwakwalar ta."? Numfashi ya sauke ya zauna gefan ta yace." Lafiyan ta lau wallahi kin San wasu yaran haka k'uruciyar su take sai sun girma sannan hankali yake zuwa Kansu kuma kin San dama dab'iun mutanan k'auye dana birni ba d'aya suke ba." Tace." Ko dana ji iya sanina dai babu abunda akayi mata Wanda zai tunzura zuciyarta da har zata ce zata gudu gida, domin shi Hakkim ma tunda ya futa d'azu be shigo parlor ba balle in ce ko shine tunda da shine basa shiri." *BINTA U ABBALE* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` *LOADING:* *{LADIDI K'WADAGA🌚}* _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain our reades``` _______________________ *30/October/2019* ________________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_ *DEDIGATED* *TO* *RAHAMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿31* General yace." Dole ki dinga saka ido a kanta saboda amana aka bamu har sanda zata gama shan magani ta koma gurin iyayen ta." Hjy Asiya tace." Insha Allahu zan kula wallahi yanzu ma ban San ta futa ba." Nan kusa cigaba da hirar da ta shafe su, Ladidi kuwa nacan tana kallon tv yayin da Salima take kwance kan kujera tana chat babu ruwanta da wani kallo tunda bai dame ta ba. Goma shaura general ya kalli ladidi yace." Aminatu ya kamata ki kwanta haka saboda gobe ki tashi da wuri zamu je kiga dector ko."? Zumb'ura baki tayi tace." Sai na gama kallona." Salima ta kalli tv din tace." Film din nan fa da saura Dan sai kin kai kusan sha d'aya da rabi na dare a zaune a gurin nan sannan zai kare." General ya mik'e yana fadin "Rabu da ita Salima ta gama kallonta ke dai ki bar dakin a bude kar ki rufe kofa." Yana gama maganar shi ya wuce bedroom Hjy Asiya ta bishi, to Salima ma minti ashirin ta kara ta mike ta shiga bedroom domin kwanciya, aka bar Ladidi ita kadai a parlor.... Sha d'aya saura Yusuf da Salim suka shigo, cike da mamaki suke kallonta, ganin irin kallon da suke matane ya bata haushi tace." Meye! Kuka zuba min ido." Shiru sukayi kawai domin suna iya magana ta sanya ihu ransu ne zai b'aci in Dady ya ji, wani daki suka shige dukaninsu suna mamakin rashin kunyar yarinyar gami da k'arfin halinta Sha daya da kwata ya shigo shima ya gaji mutuka bacci kawai yake so yayi, yana shiga parlor yaga Ladidi tsaye gaban Tv tana dariya kamar mahaukaciya tv ya kalla da sauri sai yaga jarumi Akshey kumar yana dukan boss da alama film din yazo k'arshe. Ladidi sai ihu! Take tana fad'in"Yawwa! Kashe shi! Hege! Mugu dama bashi da wani amfani"!! Takaici ya hana shi cewa komai kawai ya nufi gaban tv romt ya d'auka ya kashe TV ya zare wayoyin daga jikin soket din. A zabure!!! Ta kalle shi! Sai kuma ta ja da baya ganin Hakkim din ne. Bude baki tayi zata yi magana yace." Wuce! Kije ki kwanta mahaukaciya kawai." Ladidi takaici kamar ta Dora hannu aka gashi ana fad'an k'arshe wannan Dan rainin hankali yazo ya kashe TV kamar zata yi kuka tace" ka kunna min in karasa gani,." A fusace! Yace." An ki a kunna miki Dan uwarki ibilishi dak'ikiya wacce bata sa komai a gaba ba sai dakikanci da jahilici." Tunda take a rayuwa babu Wanda ya tab'a yi mata zagin cin mutum fi irin na yau. Ta fara sanin ciwon kanta tana a matsayin shekaru goma sha uku.yanzu idonta ya ciko da kwallah sosai. Tsawa! Ya buga mata akaro na uku yace." Kin bar nan gurin ko kuwa sai nayi kulikulin kubura dake yanzu." Da gudu ta shige dakin da Salima take tana wani irin kukan taki. Shiko wani sanyi yaji cikin zuciyarsa ganin ya sata kuka dama abunda yake so kenan, duk irin b'acin ran da ya kunsa daga gurin Dadyn sa, sai ya fanshe a kanta, d'akinsa ya nufa zuciyarsa babu dad'i. Misalin k'arfe bakwai da rabi kowa ya hallara a parlor ana shirin karyawa, ya futo cikin shiru fuskar nan a had'e General ya kalle shi tare da fadin "yawwa dama yanzu nake cewa Salim ya shiga ya kira min kai mu tafi hospital din nan da wuri." Zama yayi kujerar daining yace." Dady wane irin hospital ? Ni da zan wuce Abuja yanzu." Wani irin kallo general din yayi masa yace." Yanda muka zo tare to haka zamu koma. tare babu inda zakaje." Ganin Dady din fuskarsa babu wasa yasa ya kwantar da murya cikin laluma yace." Dady kasan sati biyu zanyi in koma America kaga yau nayi kwana Tara da zuwa, ya zama dole yanzu inje in fara shirye-shiryen tafiya ko." Shiru general din yayi masa ya cigaba da karyar warshi hankali kwance. Hjiy Asiya ta kalle shi tare da fadin "ko a had'a maka breakfast din ne." Gyad'a kansa yayi. Had'a masa tayi ta tura masa gabansa, tsatstsakura yayi a je fork din, ya cigaba da kurb'ar tea din ranshi babu dad'i. Salima da Ladidi ne suka futo tare sun shirya tsaf!! Ladidi an sha kwalliyar fuska leb'anta jazur da Jan janbaki babu yanda Salima bata yi da ita ba kan kar ta sanya sai da ta saka, ta zabga jar hoda fuskarta tayi fururu!! Kauda kansa yayi yana Jan tsaki! Salim ya sunkuyar da kansa yana kunshe dariya. General yace. " Aminatu wannan kwalliyar fa." Washe baki tayi tace." Yanzu nayi tayi kyau ko." Yace." Kinyi kyau mutuka amma ke Salima gyara mata hodar fuskar tata zata fi kyau." Salima ta fara goge mata fuskar nuna wa tayi bata so don sai kauda fuskarta take. Hjy Asiya tace." Rabu da ita kawai tunda bata so." Suna zama kan kujearar daining din ya mik'e hannunsa rike da cup din tea ya wuce can parlor had'e da zama kan kujera yana ya mutse fuskarsa kamar Wanda yaga kashi. gurguje Salima ta had'a musu breakfast suka karya General ya mik'e yana duba agogon hannusa yace." Ku tashi mu tafi. Salima da Ladidi suka mik'e da sauri suka futa waje Salim ya mik'e Yana fadin "Dady bari inzo inyi draving d'inku tunda big broth zai tafi.. General ya kalli Yusuf da ya futo daga daki cikin shiri yace." Kai yau zaka koma ne."? Yusuf yace." Eh Dady." Gyda kai kurrum general yayi yace." Wato ya sauya maka ra'ayi kenan.". Murmushi yayi tare da fadin "ba haka bane Dady" wuce wa yayi yana fadin" Nayi karya kenan, Ku sauka lafiya." Yana gama maganar shi ya futa Salim ya rufa masa baya. Hajy Asiya nayi masa adawo lafiya. *30/October/2019* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` *LOADING:* *{LADIDI K'WADAGA🌚}* _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain our reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_ ________________________ *1/NOVEMBER/2019* ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^ *DEDIGATED* *TO* *RAHIMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿32* Wannan karon Ladidi ba tayi hauka a hospital ba tsaf ta tsaya dector ya duba ta sosai yayi mata wankin kunne kamar yanda ya fad'a jiya, nan sukayi sallama da general, cikin mutum ci da mutuntawa suka dawo gida, lokacin Hakkim da Yusuf sun Dade da barin garin, general yace." Gwara da ya tafi domin ina ganin zaman sa a gidan zai iya sanya wa Aminatu ta gudu kamar yanda ta fara yunk'uri guduwa da farko." Ita dai Hjy Asiya lallaba Ladidi kawai take kamar yanda mijinta ya umarce ta, bayan sallahr la'asar ne Mai koko ta iso gidan cikin walwala da sakin fuska Hjy Asiya ta karb'e ta lokacin general ya shiga cikin gari domin gaisawa da tsoffin abokansa, Ladidi ta dinga ihu!! Tana murna ta rungume mai koko tana fad'in"Iya kin ganni ko dubi kayan jikina Iya wallahi ina son zama da mutanan suna da kirki, don Allah ki barni a gurin su." Mai koko tace" Ai kya bari mu gaisa tukkuna kafin ki fara yi min wannan sangar ta taki ko." Ladidi ta zauna kusa da ita sai washe baki take ta fara gaishe ta. Mai koko ta amsa fuska a sake tace"Dole ne ki so zaman gidan nan tunda kin samu tv da vedio amma ni kam babu Wanda zan iya barwa ke Ladidi ." Ladidi ta b'ata fuskarta kamar ta kurma ihu!! Hjy Asiya tace" Tunda tana son zama damu Iya muna Neman alfarma ki bamu ita don Allah mu tafi da ita can abuja mana." Mai koko ta bude baki cike da mamaki tace." Habuja fa kika ce Hjy? Kina nufin in baku Ladidi Ku tafi da ita yaron ku ya k'arasa ta, shi da naga bashi da imani, ba da ban Allah ya kiyaye ba da tuni ya kurmantar da ita, Hjy kuyi hakuri bazan iya ba." Ta k'arashe maganar ta tsakanin ta da Allah. Girgiza Kai Mai koko tayi alamun bata amunce ba, Hjy Asiya ta kalli Salima dake zaune kan kujera da waya a hannu tace"Salima kawo wa Iya ruwa da abunci." Da sauri Mai koko tace"Alhamdullahi Hjy a koshe nake wallahi." Hjy tace"A'a Iya dole ki ci wani abun kam ai ko ruwa kyasha." Shiru mai koko tayi tana addu'ar kar Allah yasa Ladidi ta tubure mata kan abunda ta fad'a, jiya ma kwana sukayi suna Abu guda ita da Dalha domin ya fad'a mata yanda suka yi da General, tace masa bata amince ba, ko da wasa kar ya kuskura ya amsa masa. Ganin take taken Ladidi ne yasa Mai koko mik'ewa tana niyyar tafiya Ladidi tak'i kallon inda take sai zumb'ura baki take." Mai koko ta rik'e hab'arta cike da takaici take fadin". 'Yar nan kar dai da gaske take." Bata da me bata amsa, don haka sai ta nufi hanya futa Hjy Asiya ta mik'e da sauri tayi mata rakiya har waje. Salima ta kalli Ladidi a tsanake tace"Idan fa kina so ki shiga birni dole ne duk wannan shashanci ki daina ki nutsu ki daina k'auyanci da rawar kai shima na tabbatar da cewa rashin kamun kan da kike yi ne yasa bakwa shiri da big brother, idan kika kama kanki zaki ga kowa yana son yin mu'amula dake." Ladidi ta kalleta a nutse tace"kina nufin idan na daina magana yayan ki zai dai na hantara gami da ce min aljana." ? Salima tace"K'warai kuwa Big brother ya tsani k'azanta da rashin kamun kai, ki nutsu zaki ga ya daina hantarar ki." Shiru Ladidi tayi tana sak'e-sak'e cikin zuciyarta. ******* Yau kwanan Ladidi biyar a gidan gona kullum ta wanke goma ta tsoma biyar ta ci abunda ranta yake so ta sha abunda ranta yake so, dodon ta baya gidan shiyasa take sakewa tayi kallonta son ranta, duk sai a tashi a barta a parlor ita kadai.domin kar ranta ya b'aci yasa general yake k'yaleta, ta more saboda ya fuskanci yarinyar dole sai da siyasa. Yau ne Ladidi ta gama shanye magungunan ta kuma Alhmdullahi jin ta ya dawo rad'au! DOMIN har har yaso yafi da. A yau ne kuma Mai koko ta dira a gidan da niyyar tafiya da ita. *BINTA U ABBALE* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` *LOADING:* *{LADIDI K'WADAGA🌚}* _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain our reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_ ^^^^^^^^°^^^^^^^^^^^^ *3/November/2019* ^^^°^^^^^^^^^^^^^^^^^ *DEDIGATED* *TO* *RAHIMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *WANNAN PEGE D'IN NAKA NE ABUE SALEH ZAMANI WRITARS, ALLAH YA K'ARA MAKA HIKIMA DA AZANCI* *33* General yana ganin Mai koko yasan da abunda tazo, shi tun jiya sun gama magana da D'alha ya yardar masa ya tafi da Ladidi abuja, domin yana kwad'ayin tayi karatu kuma ta nutsu tabbas hankalin sa ya kwanta da mutumin yasan bazai cuce shi na. Sosai general ya karb'i mai koko fuska a sake yake gaishe ta ta amsa babu yabu babu fallasa tace"Naga kun shirya dama ina addu'ar Allah yasa na tadda daku domin tun jiya jikina yake bani da akwai wata a k'asa." General yace." Hak'ika Iya kina da gaskiya kuma maganar cewa za'a b'oye miki sam! bata taso ba, jiya mun Dade da D'alha a waje muna tattsunar maganar . Nan duk ya kwashe komai ya fada mata. Mai koko tace" Kun munafur ce ni Alhaji, ina ganin mutumncin ka, Wallahi wato dama da biyu kace dole sai ta zauna a gidan ka ko domin Ku cusa mata k'in zama cikinmu ai babu komai, Alhaji ga amanar Ladidi nan a hannuku marainiya ce,duk Wanda ya cuceta shi da Allah." Ta k'arashe maganar muryar ta na rawa. General bai ji dadin kalaman da Mai koko tayi amfani dasu ba gurin fada masa magana amma domin a zauna lafiya yasa ya dinga lallab'ata hade da rarrashin ta, cewar ta kwantar da hankalinta yayi mata alk'awarin duk wata zai dinga sanyawa ana kawo ta suna gaisawa. Ba tace komai ba ta mik'e ta fuce daga parlor zuciyar ta babu dad'i, Hjy Asiya ta biyo bayan ta tana yi mata magana mai koko ko juyo wa ba tayi ba, babban abunda ya bata shaushi ganin yanda Ladidi taki kallon inda take balle ma tayi mata magana. Tana komawa gida ta Tarar da D'alha ya futo zai tafi gurin sana'ar sa, nan ta rufe shi da fada tana share hawaye tana fadin"me yarinyar nan ta tsare maka ne ? Ka dauke ta ka bada ita hannun mutanan da baka sani ba." D'alha ya tsaya yana fahimtar da ita, kin sauraron sa tayi ta shige cikin gidan ranta a bace.! Futa yayi kawai yasan duk maganar da zai fada mata yanzu ba sauraransa zata yi ba, dole ya bari ta huce tukkuna sai yayi mata bayani yadda zata fuskarta. ******* *LADIDI A ABUJA* Tunda suka isa birnin tarraya take kalle-kalle cike da k'auyanci gine-gine take kallo iri-iri Salima ta tab'o da hannunta tace"Salima kuma wannan dogwayen gine-ginen basa fad'owa kan mutane." Salima tayi murmushi tare da fad'in"Amanatu kenan, duk haka ginin garin yake, babu kuma Wanda zai fad'o." Ladidi tayi shiru cikin motar zuciyar ta fara zugata da tasani bata biyo su ba tabi Iya wata kila ma zasu siyar da ita ne, hawaye ta fara sharewa cike da tausayin kanta, Salima tace"Kuka kike Amina." Fuskarta ta b'oye tsakanin k'afafun ta,General ya juyo da sauri tare da fadin"Kukan me takeyi Salima." Tace" Wallahi ban sani ba Dady." Salim ne yasa dariya tare da fadin "ko ta tuno gida ne"? Hjy Asiya tace" Salim kar ka kara yi mata dariya " gumtse bakinsa yayi yace." Toum, Hjy ASIYA ya juyo tana rarrashinta da kyar tayi shiru, suka Isa gida. Ganin mai gadi na bude wani wangameman get yasa Ladidi ta tsorata ganin doguwar kanta kewaye da kayoyi lokaci guda zuciyarta ya fara sak'a cewar in tayi sha'awar futa wasa ta ina za ta futa, bata k'ara tsinkewa da al'amarin na sai da taga wasu manya-manyan sojoji guda uku ko wanne hannunsa rike da budinga sun taso daga gurin zaman su, suna wa General barka da zuwa. B'uya tayi bayan Hjy Asiya tana zare idonta, nan Salima taja hannunta suka shige ciki. Tunda suka shiga parlor take bin ko ina da kallo gaskiya haduwa lparlor ya kai ya kawo wasu tafka-tafkan hotona ne kafe a hango uku general ne da iyalinsa, sai kuma nashi shi kadai yana sanye da kayan sojoji Jikinta yayi sanyi ta kalli Salima tare da fadin"Dama Baba soja ne."? Salima tace" Eh amma ritaya shekaru biyar da suka wuce. " shiru tayi tana kara bin parlor da kallo can ta hango wani tafkeken hoton Hakkim jikin bango Yana sanye da wasu suit Wanda suka yi masa mugun kyau dariya yake yi lokacin da aka dauki hoton tsantsar kyawun shi gami da haibar shi ya sun futo da alama ma hoton na anan aka dauke shi ba, kamar a k'asar waje ne................ *BINTA U ABBALE* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` *LOADING:* *{LADIDI K'WADAGA🌚}* _*ZAMANI WRITES ASSOCIATION🤝🏻*_ _______________________ ```We are here to educate motivate and entertain our reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a d'aukar min d'aya daga cikin books d'ina a siyar min ba, duk mai buk'atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d'inka shi yafi amfani a gare ka.*_ ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^ *5/November/2019* ^^^°^^^^^^^^^^^^^^^^^^ *DEDIGATED* *TO* *RAHIMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿34* Jikinta a sanyaye ta zauna kusa da Salima, a lokacin idan ka ganta baza ka tab'a cewa Ladidi ta Mai koko bace saboda yanda ta koma kalar tausayi duk babu wannan rawar kan da ta saba. General da Hjy Asiya suka shigo palo bakin su dauke da sallama, mai aikin gidan ce ta futo daga kicin da sauri tana yi musu barka da zuwa. Hjy Asiya ce kawai ta saurare ta tuni general ya hau sama, jikinshi duk babu dad'i wanka kawai yake son ya yi. Baito mai aiki ta kalli Ladidi tana washe bakinta tace"Hjy bak'uwa muka samu ne." ? Hjy Asiya dake kokarin hawa sama tace"E gatanan bak'uwa ce kuma 'yar gida." Baito tace"Masha Allah yarinya kyakyawa da ita gata 'yar Fulani, ya sunan ki."? Baki na rawa tace." Sunana Ladidi." Salima tace"Daga yau ba sunan ki Ladidi ba, sunan ki Aminatu." Baito tace"Suna me daraja sunan mahaifiyar Annabi MUHAMMADU (Slw)." Ita dai Ladidi shiru tayi kawai tana satar kallon hoton Hakkim dake mak'ale a bango.. Take wani irin fargaba da tsoro suka shige ta, Sai hawaye sharrrr! Suka fara biyo kumatun ta. Salima tace"Kuka kike yi Aminatu." ? Mik'ewa tayi zumbur!! Ta kama hanya zata futa." Baito ta matsa gefe ganin tana k'okarin buge ta. Salima ta mike da sauri tana k'okarin rike hannunta LADIDI ta fuzge hannunta tana kokarin futa.. Cikin sauri Salima ta kara rike hannunta, wata irin bangaza tayi mata sai ga Salima a k'asa, Ladidi ta bude kofa ta fuce da gudu. "Momy"!!! Salima ta kwalawa Hjy Asiya kira, da sauri Hjy Asiya ta sauko jin irin kiran da Salima ta kurma mata fad'i take " Lafiya kike kurma min uban kira haka."? Baki na rawa tace" Amin.... Kafin ta karasa Hjy Asiya ta katse ta da fad'in",Tana ina."!? Da hannunta ta nuna kofa tana fad'in"Ta futa da gudu." Cikin sauri Hjy ta bude kofar parlor ta futa tana salati. Can ta hango Ladidi bakin gate suna rigima da masu gadi, sai kuka take tana burgima a kasa wai dole sai sun bud'e mata k'ofa. Tun daga nesa Hjy Asiya take fad'in"Kar Ku Bari ta futa duk Wanda ya bar ta ta futa a bakin aikin shi." Jin abunda Hjy take cewa ne yasa Ladidi zabura! Ta buga wani uban tsalle! Sai gata ta d'are gatangar dake kewaye da gidan, duk da cewa akwai k'ananun k'usoshi saboda tsaro (Security) Hjy Baito masu gadi sakin baki suka yi suna kallon hatsabiban cin yarinyar. Cikin rarrashi Hjy tace"Aminatu ki rufa min asiri ki sauko don girman Allah kar ki kashe min aure na." Ko kallonta Ladidi ba tayi ba, k'okarin dirga k'asa take k'afafunta har sun fara fidda jini. Hjy ta kalli Salima dake tsaye tsoro ya cika mata ciki tace"Maza je ki kira Dadynku nasan dai yau sai ta Allah, bazai tab'a karb'ar uzirina ba." Salima ta wuce cikin gidan da sauri. Rarrashin ta suke sosai kan ta sauko kar ta jiwa kanta ciwo Ladidi ko sauraran su bata yi, kokari kawai take ta sauka k'asa. Hawaye Hjy Asiya ta fara sharewa tana fad'in"Ashe tsautsayi ne yasa muka d'auko ki muka kawo ki anan Amina ki rufa mana asiri idan kika fad'o daga wannan ginin ai idan baki mutu ba, to babu shakka sai kin kakkarye." Ganin tana k'okarin zura k'afar ta k'asa yasa d'aya daga cikin masu gadin gidan ya futa da gudu, domin ya tare ta ko da zata fad'o. Raba k'afafunta tayi d'aya cikin gidan d'aya a wajan gidan, ta kalli Hjy Asiya tare da turb'u ne fuskarta tace'Wato kun kawo ni nan gidan domin Ku yanka min kai ko? Hahahahaha na gane ku ai." Hjy Asiya ta fara rantse-rantse muryar ta na rawa! General na hango ya tawo a sukwane! Tun daga nesa yake hango abunda yake faruwa, wani irin zufa ne ya tsinke a jikinshi kamar ba daga wanka ya futo ba. Ya k'arasa gurin da sauri yake fad'in"Aminatu me akai miki? Sauko kinji ki fad'a min me kike so in siya miki kar ki fad'a kasa Aminatu."! Dariya tayi tana kallonsa tace"Baba duk na gane Ku wato kun kawo ni kuyi cinikin kaina ko hahaha to kafin Ku siyar dani ni zan siyar da kaina, domin fecewa zanyi sai inga Wanda zaku siyar." General ya sharce gumin dake tsatstsafo mishi a goshi duk ya rasa me zaiyi, Salima ya kalla da sauri yace." Kira min Hakkim a waya kice masa duk inda yake yazo yanzu-yanzu." Da sauri ta koma Cikin gidan domin ta dauko wayar ta. Har yanzu Ladidi na tsaye kan Katanga tana kallonsu suna kallonta Da wayar a hannunta ta futo tana laluben numbar Bigbrth kamar yanda suke kiran shi, "Dady wayar tak'i shiga." Tafad'a bakinta na rawa.General ya karb'i wayar da sauri yana k'ara gwada kiran. Cikin sa'a ta shiga,Hakkim ya dauka had'e da Sallama, Dady yace"Kana ina ne."? "Dady muna tare da Salmanu muna k'arasa shirye-shirye mybe ma, ba a gida Zan kwana ba." General yace."Kwana a gida ya kama ko domin mun shigo garin yanzu haka ma muna gida, maza! Ka bar Abunda kake yi kazo, yarinyar nan tana kokarin jawo min bala'i." Yace." Wace yarinya Dady." ? Kashe wayar general yayi ba tare da ya amsa masa ba. Da sauri ya mike hade da d'aukar key d'insa sukayi sallama da Salmanu ya futo cikin sauri ya shiga motar sa, hade da fuzgarta da gudu. Tunani yake a mota me Salima take kokarin ta aikata Wanda har ta tayar da hankalin Dady haka, shi Sam! Bai kawo cewar Ladidi ba ce. *BINTA. U ABBALE* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *ZAMANI WRITES* *ASSOCIATION🤝🏻* ___________________ ```We are here to educate motivate and entertain our readas``` ____________________ *10/November/2019* ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^ ```Shirafa'u 'yayan Nana kusa ni cikin masoya``` _________________________ *DEDIGATED* *TO* *RAHIMA ALIYU* *ABUJA* ```BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM ``` *🅿35* Tun da ya shigo da motar layin nasu hango abunda yake faruwa. Cikin mamaki ya k'araso da motar tare da yin parking ya futo da sauri idanunsa a sama yana so ya gazgata abunda idonsa yake nuna masa. Tabbas Wannan aljanar yarinyar ce,kenan Dady da ita ya tawo garin abuja. Tambayar kanshi yake babu amsa. Haladu mai gadi ya k'araso kusa dashi bakinsa na rawa yace." Allah ya taimake ka ka taimaka mana ka sauko mana da wannan hatsabibiyar yarinyar daga sama ga Hajiya can tana zubar da hawaye... Hakkim bai karasa jin abunda Haladu yake fad'a ba ya wuce da sauri! Cikin gidan ya shiga. Dady ns tsaye sai magiya yake zabgawa LADIDI kan ta sauko daga saman gurin, Momy da Salima na gefe suna matsar hawaye. Daga kansa yayi yana kallon Ladidi dake tsaye tsakanin wayoyin dake kewaye da gurin ta raba k'afafun ta gida biyu d'aya a cikin gidan d'aya a waje. Sosai yake mamakin yanda a kayi ta hau gurin tunanin yake ya za'ayi ya fuzgota daga gurin, futa yayi waje da sauri, Haladu na tsaye hankalinsa na sama yana gadin LADIDI ko da zata fad'o sai ya tare ta. Cikin ikon Allah hankalinta na cikin gidan General ya dauke mata hankali gurin magana, Hakkim yace da Haladu yayi masa dokin wuya aikuwa haka aka yi dokin wuya yayi masa jikin duguwar gatan gar akwai guraran rodi da a had'a dasu ba gurin gini nan Hakkim ya kama cikin dubara ya haure katangar hannunsa suka cake da k'ananun k'usosi jini ya fara zuba! K'afar ta guda ya fuzgo da k'arfi ta kifo jikinsa suka fad'o k'asa tare. General da sauran mutanan gidan suka runtumo da gudu suna salati domin su duk a tunanin su ta fad'a ne kamar yanda take fad'a musu. Sai suka gan ta kwance saman ruwan cikin Hakkim, Wanda yake mata wani irin mugun kallo na tsana idonsa yayi jawur!! Ga hannunsa yana d'igar da jini. Ladidi idanunta a k'ek'ashe take kallonsa, babu alamun risina a tare da ita,Hakkim ya mike a zafafe! Ya watsar da ita a gurin. Ta mike da sauri hade da d'ibar k'asar gurin kamar yanda ta saba ta watsa masa a jikinsa ta runtuma da wani irin gudu ta dauki hanya ...... Da gudu ya bi bayan ta, General ya zube a gurin hade da dafe kansa Cikin tsantsar tashin hankali. Salima tace"Dady dama na fada maka wannan yarinyar zata iya d'ora wa mutum hawan jini Dady tun kafin ta jawo mana wani bal'in gwara gobe a mayar da ita gudansu. Hajiya Asiya kuwa ta daina matsayar hawayen yanzu abun tsoro yake bata sosai take zargin yarinyar da motsuwar k'wak'walwa idan ba haka ba kuma to tabbas da akwai aljanu a kanta. Gudu take kamar wata filfilwa, Hakkim ya k'ure gudunsa domi ya tadda ita Sam baya son ta futa titi a haka yasan ba k'aramin kunya bane a ganshi yana falfala gudu kamar wani zararre. Duk iya gudu irin na Hakkim kasa cin mata yayi, ya sare mutuka yanzu ya kara tabbatar wa da cewar yarinyar annoba ce a gare su. Cak!!!! Ta tsaya jin haushin karnuka wan! Wan! Wan!wan! Haushin ya cika gurin. Tana haki! Ta waiwaya bayanta ta hango Hakkim ya kusa cimma ta, ta kalli gabas kudu a rewa babu gurin b'uya ga karnuka sun taso mata, ihu!! Ta kurma hade da d'ora hannunta a kanta tana fad'in"Wayyo Allah Mai koko Wayyo na Iya shikkenan mun rabu da juna sun kawo ni gidan yankan kai, Dama sai da kika ce kar na zo nace sai Nazo shikkke....... Bata karasa ba ya k'araso gurin yana wani irin huci! Ya sanya hannunsa ya kwad'e mata bakinta da. Mugun k'arfi Bakin ya fashe da sauri! Ta sanya hannunta ta Dan gwalo jini daga bakinta. Wani razanannan ihu! Ta kurma Wanda har sai da gurin ya amsa! Dan dai unguwar ma ta masu hannu da shuni ce ko wane gate a gark'ame da irin unguwar yaku bayi ne da tuni ai gurin ya cika da 'yan kallo. Blet din jikinsa ya cire ya fara zabga mata a jikinta kamar Wanda Allah ya aikoshi, dukan ta yake babu sassauci ita Kuma tana ihu! Hade da zaginsa tana yi masa Allah ya Isa. Bai fasa dukan ta ba har sai da yaji bakinta ya mutu ta kwanta a gurin tana nishi hade da ne kare kanta sannan ya mai da blet din jikinsa, ya bar gurin a fusace. Motar su Dady ya ci karo da ita tsananin b'acin ran da ya ke ciki bai sa ya tsaya ya saurare su ba ya wuce abunsa. Tun daga nesa suka hangota kwance hasken Fitilar motar ne ya nuna musu General ya kara sauri har suka Isa inda take kwance nuffashin ta na futa sama-sama a gigice general ya dauke ta ya shiga motar da ita. Hajiya Asiya ta dawo mazaunin dravar ta kunna motar, da sauri General Yace. " Maza mu tafi babban asibiti yarinyar ta suma."!!! Hajiya Asiya ta k'ara k'arfin motar tana fad'in *"Innalillahi wa'inna ilahi raj'inun* *BINTA U ABBALE* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *ZAMANI WRITES* *ASSOCIATION🤝🏻* ___________________ ```We are here to educate motivate and entertain our readas``` ____________________ *Fadima Ummul hasnaini ya tsokar jikin Habibi* ____________________ *DEDIGATED* *TO* *RAHIMA ALIYU* *ABUJA* ```BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM ``` *🅿37* D'aya daga cikin likitocin dake duba LADIDI ne ya futo yana goge gumin fuskar sa, General ya mike da sauri tare da tarar gabansa hankali a tashi yace." Dr ya jikin yarinyar ne."? Cikin yanayin damuwa Dr ya kalli General yace." Gaskiya yarinyar tayi dogon suma sosai duk iya bakin kokarin munyi domin ta dawo hakan bai yi wu ba, but kwantar da hankalin Ku, zata dawo normal insha Allahu daga nan zuwa gobe." General ya share gumin dake tsatstsafo masa a goshinsa hankalin sa a tashe yake fadin"Innalillahi wa inna ilahi raji'un." Dr ya gyada kansa cike da jimami yace." Yarinyar ta furgita ne kuma anyi mata dukan mutuwa sosai ta jikkata gaskiya duk Wanda yayi mata wannan duk bashi da imani, yarinya k'arama anyi mata duka irin na masu laifi." General Yayi shiru domin bashi da ta cewa Dr ya girgiza kansa kawai ya bude ofis d'insa ya shige. General zubewa yayi a gurin hankalinsa ya tashi mutuka yanzu yake da ya sanin dauko yarinyar ganin tsautsayi yana nema ya haushi. Hajiya Asiya tazo ta zauna kusa dashi tare da dafa kafad'ar shi muryar ta a sanyaye tace." Dady ka kwantar da hankalin ka insha Allahu komai zai zo da sauki na lura yarinyar bata da cikkakiyar lafiya, sai futuna da ibilici ina ganin Idan komai ya dai-dai ta mai zai hana ka kirawo Liman ya duba ta sosai nasan Idan akwai wani jinnu da suke damunta to zai fada kaga sai mu san ta inda zamu fara." General ya dago kansa yana kallon matar tasa Yace. " Babu babban Mara hankali irin Hakkim da zai kama d'iyar mutane ya dinga jibga kamar Wanda Allah ya aiko shi, yanzu idan wani Abu ya samu yarinyar ba fata nake ba, in je in ce da iyayen ta me."? Hajiya Asiya tace." Dady ka manta Halin yarinyar ko? Ni a ganina abunda Hakkim yayi mata shine dai-dai in ba haka ba baxa ta tsaya ba, yanzu idan ta gudu ta ina za mu fara neman ta cikin wannan gari mai girman gaske." General girgiza kansa kawai yake tabbas shawarar da matar shi ta bashi itace abun dubawa tunda ya Riga ya dauki amanar rike yarinyar tsakani da Allah kuma ya dauko ta daga gurin iyayen ta Dole yanzu duk wani nauyi ta yana kansa. Hakkim kuwa ranshi a masifar b'ace ya koma gida diract part d'insa ya wuce Salima ta biyo shi a baya tana tambayar sa ladidi wata irin shegiyar tsawa ya buga mata, wacce ta sanya ta rugawa da gudu part dinsu. Ya ja tsaki ya wuce part dinsa . takalmin shi bai cire ba ya kwanta rigingine kan bed dinshi yana sakin ajiyar zuciya kana ganinshi kasan a cikin b'acin rai yake, ya rasa wane irin mutum ne Dady dinshi daka ganin sarki fawa sai zak'i, haka kurrum ya d'ako musu alak'ak'ai cikin gida, Ladidi Annabo ce,domin shi kwata-kwata baya yi mata kallo mai hankali ta yaya zasu yi rayuwa da mahaukaciya, dole ma ya bar garinan. Domin bazai iya zama inuwa guda da yarinyar ba, yana jin wata irin tsanar ta cikin zuciyar sa. Kusan awar shi guda a kwance yana sak'e-sak'e daga bisani ya mike jikinshi duk babu dad'i ya fada toilet dinshi ruwa ya hada mai dumi yayi wanka, ya futo daure da towol mai girma wani rataye a wuyan shi, ko mai bai shafa ba, ya zura boxer hade da singilet yayi kwanciyar shi kan bed yana lumshe idon sa, wayar sa ce ta fara ringing yana dubawa yaga Dady ne , gyada kansa yayi yace." Dady kai ka jawo wa kanka wannan masifar wallahi babu ruwana, gobe iwar haka ma ni na bar garin." Har wayar ta tsinke ba dauka ba, wani kiran ya k'ara shigowa hararar wayar yayi, yace." Nasan kan yarinyar zai yi min magana yanda na kwanta ina hutawa ta,wallahi bazan tashi ba." Juyawa yayi hade da gyara kwanciyar sa. General ya kira wayar yafi sau biyar Hakkim bai dauka ba, kuma yana ji, Dan ma kar ya kashe wayar ne General din ya fuskanci wani Abu shiyasa ya k'yale ta, gobe yana tambayar sa yasan k'aryar da zai shirga masa, amma shi babu yadda za'ayi ya tada hankalin sa, kan wata banzar yarinya kidahuma 'yar kauyen k'ayau. General da Hjy Asiya haka suka kwana cikin tashin hankali da damuwa, b'angaran Hakkim kuwa baccin sa ya shirga babu abunda ya dame shi, a subar fari ya tashi, yayi wanka kamar yadda ya saba ya wuce masjid, k'arfe shida shaura ya shigo gidan, ya fara shirinsa domin Sam baya so Dady ya dawo ya tadda shi gidan, yasan wata masifar ce, cikin wasu suit ya futo black and White sunyi mishi kyau sosai ya matse wuyan shi da necktie lafiyayar sumar shi tasha gyara sai kyalli take, kafarshi sanye da helf cover black sai shaining yake yi yayi kyau sosai kalar fatar shi ta futo kamar wani black america haka ya futo hannunsa rike da wata k'aramar jaka. Salima da Baito mai aiki suna Palo Baito na gurin daining tana gyarawa Salima kuwa na zaune kan kujera cikin damuwa kana kallonta kasan bata yi baccin kirki ba, ta na ganshi ta sauke ajiyar zuciya hade da fadin "Broth barka da Safiya ." Nazarinta yake ganin yanda tayi figai-firgai yace." Barka kadai, ni zan wuce idan sun dawo ki Sanar musu, bakinta na rawa tace"Bro ladidi fa har yanzu bata farfad'o ba." Wata irin muguwar tsawa ya buga mata tare da fadin"Don Ubanki ni ina ruwana! Da zaki wani dame ni ki damu kanki, ko wa ya siyi rariya yasan zata zubda ruwa kuje Ku k'arata da ita tunda kune kuka dauko ta ni nayi tafiya, wallahi ko da wasa kika kara yimin maganar mahaukaciyar yarinyar nan sai na ballaki! Wallahi Idoit kawai !.""" Yana gama maganar shi ya fuce a fusace! Salima tayi tsuru-tsuru tana bin hanyar da wuce da kallo ita kanta tana jin tsoron masifar yayan nasu hade da b'acin ransa, lallai yau zuciyar sa a tunzure ta, tana ganin ko Dady ne yayi masa magana zai iya fada masa magana me zafi indai akan LADIDI ne. *BINTA U ABBALE* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *ZAMANI WRITES* *ASSOCIATION🤝🏻* ___________________ ```We are here to educate motivate and entertain our readas``` ____________________ ```Shugabar mataye Binta taga mala'ika da idonta, ba shamaki ba tafinta, har ya aike ta gun Habibi``` *Fad'ima Umul Hasnaini ya tsokar jikin Habibi* ______________________ *DEDIGATED* *TO* *RAHIMA ALIYU* *ABUJA* *BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM* *🅿39* Cike da rashin tsoro general ya tsuguna kusa da Ladidi dake wani irin Abu da idonta, yace." Kuji tsoron Allah da manzo sa ku rabu da wannan 'yarinyar marainiyar Allah me tayi muku? Kuka yi aure kuka tare a kanta, shine me zaku cewa ubangji ranar alkiyama."? "Hahahahaha!! Suka ji wata mahaukaciyar dariya, Ladidi nayi, tafi minti uku tana yi daga bisani tayi d'if!! Gurin yayi shiru Lokacin Salima sai da ta saki futsari a wando. Tsoro duk ya cika zuciyoyin su daga ita har Momyn ta Hjy Asiya..... General ya fara tofa mata dukanin addu'ar da tazo bakin sa. Ya kai Kusan 30minutes tsugune gaban Ladidi yana tofe jikinta da addu'a, sannan ta bude idon ta, gami da yin wata irin mik'a! Ta mike zaune zumbur! Kuka ta fashe dashi tana waige-waige a gurin. Su din dai ta gani a tsaitsaye sun zuba mata ido. Take kukan ta ya kara k'arfi tana nuna kafarta duk bakinta yayi mata nauyi so take tayi magana amma ta kasa. General ya fahimci ta dawo dai-dai sai ya fara kokarin daukar ta cike da tausayin ta, domin ya lura aljanun da suke kanta manya ne sosai Dole ta kasa motsa jikinta. Jiki babu k'wari su Hjy da Salima suka bi bayan general Wanda ke rungume da Ladidi a jikinsa ya nufi cikin gidan da ita. Hjy da Salima Dan babu yanda zasu yi da sun hana general shigar musu da Ladidi gida saboda tsaro , Salima tsoron mutum me aljanu take. Kan kujera ya aje ta ya kara k'arfin AC ya kalli Hjy Asiya tare da fad'in ki hada mata ruwan ka tayi sai taci abunci." Hajiya Asiya ta wuce kicin jikinta duk babu k'wari, ita kuwa Salima zama tayi ta k'urawa Ladidi ido babu abunda take tsoro da fargaba sai dare domin tasan Dady zai ce Dole sai ta kwana d'aki daya da Ladidi. Kamar me k koyon magana tace"Zan sha ruwa." General da kansa ya nufi furji ya dauko mata ruwan gora mai sanyi bayan ya bude murfin ya mik'a mata. Tunda ta kafa kanta kan robar ruwan bata d'ago ba sai da ta shanye shi tas! Sannan ta jefar da robar hade da yin wata shegiyar gyasa lumshe idonta ta fara yi, tuni ta b'ingire a gurin nannayaun bacci yayi gaba da ita. General ya saki ajiyar zuciya ganin bacci ya dauke Ladidi ya mike yana niyyar barin gurun, da sauri! Salima ta mike hade da rike rigar shi ta baya tana tafiya tana waiwayen Ladidi. General ya juyo yana kallonta da murmushi a fuskar sa yace." Na lura dake da Momy taki tsoron Aminta kuke yi tun d'azu naga sai zare ido kuke yi." Salima tace."Wallahi Dady da gaske tsoran ta nake ji, yanzu haka jikina a jike yake ban San sanda futsarin tsoro ya kuffe min ba." Dariya general yasa yace." Ho Salima sarki tsoro ki daina jin tsoron Aljan babu abunda ya Isa yayi miki Wanda Allah bai miki shi ba, ke kike da makamai a hannun ki, kina fara karatun ayatul kursiyo sai gudu." Salima tace"Duk da haka dai Dady wallahi tsoro nake ji, mu kam Big broth ya jawo mana, Dady kana jin abunda fa aljanun suke cewa zasu masa, wai sai sun dauki fansar abunda yayi mata." Murmushi general yayi a lokacin da suke taka steps yace." Duk abunda suka yi masa shi ya jawo kanshi babu ruwana. " cikin Salima ya karta!!! Cike da tsoro tace"Please Dady ka basu hakuri don Allah kar su tab'a mana bro." Salima iya Gaskiyar ta take magana. General kam dariya yake mata sosai har suka hau sama, ko wanne ya shige dakin shi. Hajiya Asiya na futowa daga kicin taga parlor babu kowa Sai Ladidi a kwance kan 3sitar wata irin fad'uwar gaba taji, da sauri ta fara hawa step ta waiwayen Ladidi dake kwance General ta samu zai shiga bathroom tace"Yallab'ai gashi ruwa har yayi zafi kuma naga tana bacci a k'asa. " Yana kokarin shiga toilet din yace." Ai bacci shine samun nutsuwar ta, ki k'yaleta tayi kar Wanda ya tashe ta, sai ta tashi Dan kanta. " Hajiya Asiya ta zauna bakin gado tana al'ajabin wannan Abu. ****** Hakkim kam ya manta da wata Ladidi don Ku da suka gama waya da Dadyn sha. Ya fada masa tayi dogon suma bai damu ba, shi tunda ya bar k'asar shikkenan, suje su k'arata su da suka daukota. Wasu had'andun gidaje ne company da suke wa aiki ya raba musu kyauta, plate uku ne shi d'aya Salmanu d'aya Bash d'aya, gidane me girman gaske babu abunda babu na more rayuwa swimming shi kanshi uku ne da gurin motsa jiki uku gurin wassanin yara iri-iri a gurin. Yanda company ya basu gurin zasu iya yin aure su tare da iyalinsu zaman america har a bada su da iyalinsu. Tofa Bash tun da suka je ya samu sake wa ya fara sha'anin shi da 'yan mata kala-kala, shi kuwa Salmanu baya Neman mata amma fa shaye-shaye babu irin Wanda baya yayi, Bash kullum da daddare yana night club, sai dare ya raba yake dawo wa gida, wataran Salmanu yana binsa yaje yayi kallo ya dawo gida a buge. Hakkim ya rasa yanda zaiyi musu kullum Cikin yi musu masifa yake sai dai suyi masa dariya kawai suna fadin "Har yanzu kanshi a tukunya yake bai san yaya duniya take ciki ba. Tunda suka Isa garin na america yau kwanaki takwas kenan wayoyin sa suke kashe, yau ta kama Sunday babu aiki duk suna gida yace bari ya kunna wayar tasa, dama saboda fad'an Dadyn d'insa ya kashe wayar ya San dai yanzu ya huce fushin sa. *24/11/2019* *BINTA U ABBALE* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *ZAMANI WRITES* *ASSOCIATION🤝🏻* ___________________ ```We are here to educate motivate and entertain our readas``` ____________________ *DEDIGATED* *TO* *RAHIMA ALIYU* *ABUJA* *BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM* *🅿40* Ko da General yaga kiran wayar Hakkim kin dauka yayi. Hajiya Asiya ta shigo ta same shi zaune ga waya nayi tace"Dady kana ganin kiran waya fa." Yace." Ki dauka in zaki dauka yaron ki ne sai Yau ya ga damar tunawa damu. " Hajiya Asiya ta dauki wayar tana fad'in "Ni kam zan dauka mu gaisa dashi." Hararata general yayi tare da fadin" Ke akan 'yaya bakya jin kunya ai." Dariya tayi ta d'aga wayar, b'angaran hakkim kuwa jin muryar Maman shi sai ya saki fuska cikin shagwaba yace." Mama Duk kun manta dani ko? Sai da na gaji don kaina na kira wayarku babu Wanda ya kirani yaji ya na sauka lafiya." Hjy Asiya tayi 'yar dariya tare da fad'in"Nasan kana cikin koshin lafiya my son, duk laifin ka ne, kaje ka sumar da yarinyar mutane ka gudu yanzu inda bata dawo nutsuwar ta ba me zaka ce umm? Don Allah ka rage zafin zuciya myson." Yace." Momy daga taimako sai ace na sumar da ita, ni wallahi da zaku bi tawa da Ku mai da yarinyar nan domin Zata jawo muku masifa." Hjy ta kalli gen dake kallon TV tana jin tsoron kar yaji abunda hakkim din yake cewa, da sauri ta katseshi ta hanyar fadin"Kai ka fiye Abu myson babu wani Abu insha Allah." Yace." Shikkenan tom ni dai babu ruwana inanan." Dariya Momy tayi tana tambayar sa aikinsa yace." Alhmdullahi Momy komai ya kammala muna aiki har sun bamu gurin zama. " Momy tace"Tom Allah ya taimaka yayi jagora ." yace." Dady ne."? Gashinan zaune." Yace." Yawwa bashi wayar mu gaisa. " general ta mik'awa wayar ya karba a nutse suka gaisa dashi ya tambaye shi aiki kamar yanda Momyn shi ta tambaye nan yayi masa fatan alkairi sannan suka yi sallama. **** *K'auyan d'an kunkuru* Tunda Ladidi tq bar K'auyan Dan kunkuru hankulan jama'ar garin ya kwanta kowa ya sake yana rayuwar su nan suka k'ara tabbatar wa da cewar Ladidi annoba Ce a garin, wasu kuwa fad'i suke ai Mai koko ta tura Ladidi birni domin tayi iskanci ne wasu kuwa saboda jahilci cewa suke yi ai Mai koko da D'alha sun siyar da Ladidi saboda su hutawa da masifa kowa da abunda yake cewa. D'alha ya samu aiki a cikin birni sai ya daina sana'ar sai da d'ata da gobe yana zuwa cikin gari yayi sati d'aya biyu uku ya dawo gida, Mai koko kuwa har yanzu tanan tana sana'ar kokon ta, tayi kewar Ladidi ta gaji wani lokacin in ta tuna da ita har hawaye take yi tana tunanin ko a wane hali take ciki oho, gashi D'alha baya zama amma tayi alk'awarin wannan dawowar in yayi dole zata turasashi ya kai ta inda Ladidi take ta ganta. **** Yau watan Ladidi biyar a abuja za kuso kiga yanda ta sanja tayi wata kiba mai ban sha'awa farar fatar ta ta murje, duk wannan ramar babu ita sumar kanta ta futo sosai domin har tafi ta da, sai dai ko da wasa bata bari a tab'a mata kanta da sunan kitso duk ranar da akayi tsautsayin tab'a kan kuwa aljanunta sai sun buge ta yini suke yi Abu d'aya dole sai an kira malamin dake tsaye a kanta yazo yayi mata addu'oi sannan suke gusawa ta kwana tana bacci sai don kanta ta tashi. [11/28, 9:34 AM] BintuUmarAbbale Shiyasa suke taka tsantsan da abunda zai bata mata rai indai tace bata son Abu to Dady zaiyi ta fada kar ayi mata shi, lokacin general ya sanya Yusuf dake gari ya nemo mata makaranta mai tsada akayi komai da komai general da kanshi yake kai ta ya dauko ta duk da cewa akawai direbobin sa kusan uku, shi dai bukatar sa Aminatu ta samu nutsuwa, cikin ikon Allah da taimakon Liman Ladidi ta samu ta nutsu ta daina shirme da shiririta yanzu kallo ma bai dame ta ba kullum in ta dawo daga makaranta suna tare sa Salima tana nuna mata abunda bata gane ba. Yusuf dake shirin kai kud'in aure yaji duk duniya babu yarinyar da yake so kamar Ladidi yana mamakin asitaccan kyawun ta don a k'auye ta ke ne shiyasa komai ya b'uya, sai ya zamana bashi da gidan zuwa sai gidan su Hakkim yana fakewa da cewa yazo gaishe da General ne, nan kuwa Ladidi yake karewa kallo dukaninsu basu gane ba, lokacin suka yi wata irin sha kuwa da Ladidi itama in bata ganshi ba ta dinga cigiyar sa kenan..... Yusuf ba kullum suke waya da Hakkim sai jefi-jefi domin wani lokacin shi hakkim din bashi da time kullum suna aiki yafi samun sakewa Duk weak end sai su sha hirarsu a waya yayi ta tsokanar sa cewar ina bagidajiyar budurwar sa, shi kam Yusuf dariya yake yana fadin "Na wuce babinta yanzu na sanja wata zukekiya zan turo maka hotonta ma ka gani." Hakkim mamaki yake sosai yace."Yanzu duk irin son da kake wa Naja'atu ka daina kalli ka cika mayaudari." Yusuf dariya yayi yace." Na samu wata wacce ta fita komai da komai akan me bazan rabu da ita ba." Tsiya Hakkim yake masa yace ." ka turo min inga hoton yarinyar da ta rusa gwamantin Hafsa a zuciyar ka." Yusuf Yace. " zan turo maka amma ba yanzu ba." Haka suka yi sallama cike da barkwanci da kaunar juna. *28/11/2019* *BINTA U ABBALE* *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *ZAMANI WRITES* *ASSOCIATION🤝🏻* ___________________ ```We are here to educate motivate and entertain our readas``` ____________________ *DEDIGATED* *TO* *RAHIMA ALIYU* *ABUJA* ```BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM ``` *🅿41* A takaice dai sai da Hakkim yayi shekara guda sannan ya dauki Hutu ya fara shirye-shiryen zuwa gida Lokacin ya kara wani kyau da waye wa.... Ya fara soyayya da wata Aboki yar aikinsa 'yar Ghana Sarah kenan tun da taga Hakkim ta kwallafawa ranta shi. Tun Yana share ta har dai yaji ta kwanta masa da ya fuskanci tana da nutsuwa da kamun Kai sam bata iya shirme irin na 'yan matan ZAMANI ba. Yaji zai iya auranta ko don kyawawan haleyen ta. Ganin ya dauki Hutu yasa Sarah itama ta dauki Hutu a rana daya suka tafi filin jirgi sukayi sallama da juna kowa ya nufi kasarshi cike da kewar juna. Labarin zuwan Hakkim gidan yayi mugun d'agawa Ladidi hankali domin mata mance dashi ba s gidan sosai yanzu ta tsani abunda zai sake hada ta dashi ko da can ma rashin hankali ne amma yanzu ji take bata da babban makiyi kamar shi.... Duk taki sakewa a gidan Sai nukufurci take yi, Cikin su babu Wanda ya fahimci abunda take wa fushi Hjy Asiya dai hankakin ta ya tashi tana jin tsoron kar aljanu su buge ta domin duk ranar da ta tashi da fushi da nukufurci yini take tana tayar da aljanu sai an dauki malamin ta sannan suke gusawa, sai ta samu mijinta tayi masa maganar. General yace." Na fiki damuwa da zuwan Abdul saboda nasan abunda zuwansa zai haifar tunda kina gani tunda aka fara zancan zai zo take fushi ki duba ki gani tafi wata biyar iskar ta bata tashi ba, nasan idan ba'ayi wasa ba zuwan sa zai haifar da matsala." Hjiy Asiya cikinta ya d'uri ruwa domin tana masifar jin tsoron iskokin Ladidi kala-kala suke hawa suke sauka kuma ko wanne idan yazo da budirin sa yake zuwa domin akwai ranar da ta fara tun k'arfe goma na safe basu sake ta ba sai goma na dare akwai wani Wanda ya hau yace a cikin daran nan aje a samo masa k'adangare mai kala hudu har da fad'ar irin kalolin kamar haka *1 bulu* *2 shanshanbale* *2Yalo* *3 Orange* Take Hjy Asiya ta fahimci ko wane k'adangare yake nufi guduwa tayi d'akinta ta bar general yana ar tabu dasu... Cikin daran ya kira Malamin dake mata tofi yazo sannan fa suka gusa tayi ta bacci kamar mattaciya ta tashi a jeme duk tayi rama abun tausayi. General yana bala'in tausayawa rayuwar yarinyar marainiyar gaba da baya tarin almutsutsai sunyi kaka gida a jikinta fatan shi ma Allah yasa su barta tayi aure. Kwantar mata da hankali yayi yace." Duk wani Abu da kika San zata gani hankalin ta ya tashi sai ki guje shi kuma shima Hakkim din ki ja masa kunne sosai ni kaina sai na gargade shi kan yarinyar babu ruwan shi da ita." Hjy Asiya ta mike jikinta duk babu kuzari Salima kuwa tafi kowa rud'ewa a gidan. **** Shi Hakkim da ake abun domun shi Sam ya manta da wata Ladidi soyayyar Sarah ta mantar dashi wata 'ya mace don haka da kuzarin sa ya sauka a k'asar tashi ta gado, fuskarsa cike da fara'a ya rungume Dan uwansa Salim da yazo daukar shi. B'ata fuska yayi yace." Bro me ya hana Dady zuwa daukana ne kamar yanda ya saba."? Salim yace." Wallahi kwana biyu yayi zazzab'i shine fa jikin NASA bai yi kwari ba har yanzu... Suna kokarin shiga mota Hakkim din yace." Shine ni saboda an raina ni aka ki fada min." Salim na driving yace." Am sorry bro laifina ne."! Kafadar sa ya buga yace." Zan hukunta ka kuwa." Salim yasa dariya yana bashi hakuri yace." Bro ka kara girma da kyau ba kamata yayi ka kawo mana big aunt. "!!! Hakkim yayi murmushi hade da fadin" kar ka damu tanan zuwa insha Allah." Salim yace."Alhmdullahi dama dady yana ta so yaga baby's a gaban shi." Cikin barkwanci Hakkim din yace. "Kai ka fara kawo masa baby's din mana." Salim yace." UmUm!!! Ai Kaine babbana." Dariya suka sa a tare cike da nishadi to a haka suka isa gida Cikin farin ciki da kaunar junan su irin na 'yan uwanta ka. *5/12/2018* *BintuUm@rAbb@le* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *ZAMANI WRITES* *ASSOCIATION🤝🏻* ___________________ ```We are here to educate motivate and entertain our readas``` ____________________ *DEDIGATED* *TO* *RAHIMA ALIYU* *ABUJA* ```BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM ``` *🅿42* Hajiya Asiya ta tari Hakkim cikin kulawa da 'kauna irin ta uwa da d'anta, a parlor suka zauna ta cika gaban shi da kayan ciye-ciye birjik yace." Momy wannan delicious din duk ni kad'ai lallai kinyi kewa ta da yawa." Cikin jin dad'i tace"Dole my son nayi kewar ka sosai shekara guda ai dole in tar'be ka da muhimanci." Dariya yayi yace." Momy nazo miki da labari mai dad'i fa." Tace"Masha Allah gama cin abincin ka bani na sha." Murmushi yayi ya fara cin abincin sa cikin nutsuwa. Salim yace." Momy ni kin manta dani kenan." ? Tace" Ka bari tukkuna ya kammala sai kaci sauran." Cikin shagwa'ba yace." Momy ni bazan fi sauran ba sai kace wani al'majiri." Dariya suka yi masa dukanin su. Hakkim ya kammala cin abuncin ya dauki tissue ya goge bakinsa ya kalli Momyn sa yace." Wai ina dady ne."? Tace"Yanzu zai shigo yaje d'auko Aminatu a makaranta. " Cike da mamaki yace." Momy wacece Amina da har dady zai je d'auko ta a makaranta."? Ganin yanda ya 'bata fuska yasa Momy gyara Fuskar ya tace"Ladidi nake nufi ba ka dawo gidan ba tom babu ruwan Ka da ita don ba cikkakiyar lafiya ne da ita ba, don Allah kar ka shiga harkan ta." Jin ta ambaci sunan yarinyar da ya tsana duk duniya yace." Momy har yanzu baku maida yarinyar gida ba."? Tace"Wane gida kuma? Karma ka sake Dadyn Ku yaji wannan maganar daga bakin ka zai 'bata maka rai! Nima kaina abun sai ya shafe ni." Babu walwala a tare dashi yace." Momy kan yarinyar nan wallahi zan iya koma wa inda na futo nifa kallonta bana son yi wallahi." Salim yace." Aikuwa zaku yi fad'a da Yusuf domin budurwar sace Wallahi ka iya bakin ka." Hakkim ya kawo hannu ya gwa'be bakin Salim d'in ya goce da sauri yana dariya. Tsaki yaja cikin 'bacin rai yace." Yusuf bai da hankali wallahi ko meye abun so jikin 'kanjamammiyar irin wannan mtssss." Salim Yace. " sanin da kayi mata a da kenan, amma Yanzu indan ka ganta zaka sha mamaki." Mi'kewa yayi yana fad'in"Momy ni zan je in kwanta in huta zuwa anjima." Tace"To my son sai ka futo." 'Kokarin futa yake yi General ya shigo parlor Ladidi na bayan sa tana sanye da kayan makaranta. Baya ya matsa yana fadin "Dady barka da shigowa." Hannu general din ya mik'a masa suka yi musabaha kana yace." Dady na same Ku lafiya."? General yace." Lafiya Lou Alhmdullahi ya aiki? Ka samu lafiya kaje ka samu guri kayi Uwar 'kiba mu kuma nan ka barmu da zan can Ka." Dariya yasa yana Sosa kansa yace."Dady ban in na kira wayar ka baka d'auka ." General d'in yace." Kai kasan dalilina ai kuma ka kiyaye babu ruwan ka da yarinyar mutane." Yafadi maganar babu alamun wasa a tare dashi. Yace." Dady ka kwantar da hankalin ka ni da wuri zan koma ma." Ciki general d'in ya shiga yana fad'in"Wannan kuma Matsalar ka ce ni dai na fad'a maka." Ladidi ta 'kura masa ido kurr! Tana mamakin irin Uwar 'kibar da yayi ya 'kara haske abunshi. Had'a ido suka yi shi da ita, yaji gabansa ya fad'i! Ta maza yayi ya maze yana danne zuciyar sa yace." Kauce ki bani hanya." Harara ta watsa masa kana ta matsa daga bakin 'kofar. Futa yayi niyyar yi ya sanya 'kafarshi dake cikin takalmi sahu ciki ya take mata 'kafa cike da mugunta.! Aiko tsigar jikinta ta fara mi'kewa ta fara jin wani irin jiri 'kara ta 'kwala!! Ta zube a gurin tana fuzge-fuzge! Ihun 'karar ta ne ya dawo da shi parlor sai ya tadda ita a kwance 'kasan tayel su General sun rufu a kanta suna yi mata tofi ita kuma sai fuzge-fuzge take wata irin kumfa na futowa daga bakinsa. Dariya abun ya bashi amma ya dake ya 'karaso gurin yana le'kenta aikuwa ta zaburo! Da sauri tayo kansa.! Cikin jarumta ya tsaya a gurin Hajiya Asiya cikin tsoro take fad'in"Ka futa da sauri! Maza! Ka futa Kaine basa son su gani." Cike da mamaki! Yace." Momy su waye."? *10/12/2019* *BintuUm@rAbb@le* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *ZAMANI WRITES* *ASSOCIATION🤝🏻* ___________________ ```We are here to educate motivate and entertain our readas``` ____________________ *DEDIGATED* *TO* *RAHIMA ALIYU* *ABUJA* ```BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM ``` *🅿43* Kafin ya rufe bakinsa Ladidi tayi wani yun'kuri inda ta buge General da yake tsaye a kanta yana tofa mata addu'a duk da tazo bakinsa, kan Hakkim tayi gadan-gadan! Ganin da gaske take tayo kansa zata d'afe jikinsa da sauri ya buga tsalle yayi gefe guda cike da al'ajabi abunda yake faruwa tabbas Yarinyar aljanu take yi domin dai duk lafiyayan mutum ba zai dinga wannan buge-bugen ba. General yaje ya dauki wayarsa da sauri! Ya kira wayar Malam yace." Maza yazo babu Lafiya to da yake gidan malam din babu nisa dasu minti goma ya shigo cikin parlor yasan tunda aka kirashi abun ya ci tura, kan Ladidi yayi dake kwance tsakiyar parlor tana wani irin matagugu kumfa na futa daga bakinta ga idonta duk ya jirkice gashin kanta ya ya mutse! Duk me imani a lokacin sai ya tausaya mata, Hakkim dake tsaye bakin 'kofa yaji ta bashi tausayi babu shakka aljanu iri-iri ne akwai masu taimako akwai kuma mugwaye ya lura wadanda suke kan Yarinyar mugwaye ne sosai ta bashi tausayi ganin yanda duk hallitun ta suka jirkice Malam na rike hannun ta guda ta nitsu ta daina abunda take yi. Addu'a ya fara tofa mata a jikinta da fuskarta tsawon minti ashirin suka ji wata irin murya na magana. "Ka bari! Bama so kana takura mana damu da jaririyar muuuuu."! Malam yayi gyaran murya ya fara magana kamar haka. "Kunce bakwa so ayi muku addu'a kuma kun'ki ku rabuda yarinyar nan ta samu Lafiya yanzu me ya kawo Ku ko kuma kun manta da al'kawarin da kuka daukar min na cewar zaku k'yale Yarinyar nan tayi rayuwar ta kamar yanda kowa yake yi." Cikin sha'kakkiyar murya suka ji ance "Mu ba laifin mu bane ga mai laifi can."! Duk suka juya suna kallo Hakkim dake tsaye bakin 'kofa yana cike da mamaki ana magana da Aljani a cikin gidansu lallai dady ya dauko wa kanshi masifa. Malam yace." Dole kuyi hakuri dashi tunda yayanta ne kuma Dan gida ne don dai baya gari ne kwana biyu Idan kuma kunki hak'ura tom ni zan 'kona Ku komai yawan Ku baku fi k'arfin ayar Allah ba." Wani irin siririn kuka suka ji ladidi tana yi tana sha'kewa sannan suka ji wata irin murya ba irin ta d'azu ba tana magana kamar haka "Kada ko 'kona mu domin mune garkuwa a jikinta mu musulmi ne kuma muna tsare ta daga sharrin jinshi mu masu cutarwa muna so kujawa Jariri kunne ya futa daga sabgarmu da ta jariryarmu domin kullum muna kusa da ita muna bibiyar lamuranta shiga hankalin sa damu babu ruwan sa damu."!!! Malam yace." Kuma babu ruwan Ku dashi kuma kar Wanda ya sake ya ya kulla masa wani sharrin a cikin wallahi sai na 'kone shi kurmus! Shiru na tsawon minti biyar babu Wanda yace komai Ladidi suka gani ta fad'i a gurin rigib! Bacci mai nauyi ya dauke ta! Malam ya mike tsaye yana kallon general da yake kallon Ladidi cike da tsananin kauna da tausayin ta, hak'ika da yana da yanda zai yi da ya cire mata wad'annan kafuran aljanun da suka dame ta suke wahalar da ita gami da hanata sakewa sosai yake tausayawa Yarinyar a rayuwar sa. Malam yace." Yana da kyau Ku kula kuma ku kiyaye abunda zai bata mata rai mussaman kai." Yafad'a yana kallon Hakkim dake tsaye bakin kofa yana mamakin al'amarin. Ya cigaba da cewa"Kaji 'korafin su akanka yake don haka ka kiyaye abunda zai sa su kusanto jikin yarinyar har ta kaisu ga bata wahala irin wannan domin ni daku Duk mun san cewa Jinnu ba karya bane kuma wadanda suke jikin yarinyar manya ne yana da kyau a kiyaye 'bata mata rai ko kuma ayi mata abunda bata so insha Allah ni nayi alk'awarin duk sai na rabata da mugwayen cikinsu da izinin Allah." General yace." Insha Allah za'a kiyaye kuma dama ta kwana biyu basu matsoba wannan ma tsautsayi ubangiji Allah yayi mana tsari dafa sharrin su." Malam yace." Ameen yana kokarin tafiya ne general ya Ciro kudi masu yawa ya bashi da kyar ya karba yana fadin"Shi ba don kudi yake taimakon yarinyar ba kwai yanayi ne don Allah. General din yace." Shima ya sani kyauta akwai ya bashi, cike da girmama juna suka yi sallama. Sosai general yayi wa Hakkim fada kan ya futa daga sabgar Ladidi ko don gudun abunda ka iya zuwa ya dawo, to shima Hakkim din nashi 'bangaran ya fahimci komai kuma yanzu ya gane cewar duk abunda Ladidi take yi ba yin kanta bane junnu ke sata yayi alk'awarin futa sabgar ta har abada tunda dai shi dady din yaji ya gani zai riketa a haka Shikkenan Allah ya taya shi rik'o. Ladidi bata farka daga bacci ba sai kusan daf da magariba sannan ta farka jikinta duk ya mutu ko ina nayi mata tsami tunda taji ta farka da mugun ciwon kai tasan tayi iska!!! Tana share hawaye ta mike ya shige d'akinta Wanda aka mallaka mata a gidan, zama tayi gefan gado tana kuka domin itama har ga Allah ta tsani wannam abunda take yi don dai babu yanda zata yi ne addu'a take cikin ranta Akan Allah ya yaye mata. Ko da Hjy Asiya ta futo daga daki taga babu ladidi a parlor nan ta fahimci ta farka daga bacci kicin ta shihe kawai tana girgiza kanta gefe guda Kuma tana tausayawa yarinyar da irin tata kaddarar. Ladidi kuwa ruwa ta hada mai zafi tayi wanka duk Dan taji dadin jikinta ta fito daure da alwala ta shirya tsaf ta futo parlor lokacin babu kowa sai ta zauna kan kujera tana jiran kira sallah magariba Salim ne ya shigo parlor ya ganta ita kadai yace"Menna 'yan mata ta gidan Yusuf bada kanki a sare." Hararasa tayi ta dauke kanta shi kuma yasa dariya yana fadi'n komai abunki Yusuf zaki aura." Ita dai shiru tayi masa shi kuma ya shigeta yana cigaba da tsokanar ta har Hjy Asiya ta futo daga kicin. Tace"Sarki tsokana kazo zaka dame ta ko."? Yace." Shigowa ta. kenan wallahi Mama yau ina Salima take ne tun safe ban ganta ba." Hjy Asiya tace"Ta yini gidansu kawarta amma dai yanzu tace min tana kan hanya." Hakkim ne ya shigo parlor yana sanye da JS a jikinsa sunyi masa kyau sosai ya taje Lafiya yar suman kansa Salim yace"Yauwa broh zo ka bani tsaraba ta da kayi min alk'awari." Hararasa Hakkim Yayi har ya 'karaso tsakiyar parlor ganin Ladidi a zaune sai juya daining ya nufa yana ya mutse fuska. *16/12/2019* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *ZAMANI WRITES* *ASSOCIATION🤝🏻* ___________________ ```We are here to educate motivate and entertain our readas``` ____________________ *DEDIGATED* *TO* *RAHIMA ALIYU* *ABUJA* ```BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM ``` *🅿44* Zama yayi kan kujerar daining Hjy Asiya ta futo daga kicin ta ganshi fuska ta saki a nutse tace "Dama yanzu nake shirin aikawa a kira ka domin d'azu naga ba wani abincin kirki kaci ba." Murmushi yayi a hankali yace."Ni kam na koshi mama kar ki ce sai naci wani abunci yanzu cikina zai fashe." A shagwabe ya fad'i maganar. Ladidi dake zaune a can parlor tana jinsu tab'e bakinta tayi tana mamakin sa gotai gotai dashi yana shagwaba a ganinta shirme ne. Hajiya Asiya tace"To Shikkenan bazan matsaba maka ba ai cikin Kane yanzu dai bani labarin domin dai tun d'azu nake tsumayin ka." Hakkim ya lumshe idonsa da ya tuno da Sarah yace." Mama nayi budurwa fa kuma insha Allah ita zan aura domin na yaba da d'abi'unta." General ne ya karaso gurin Hajiya Asiya tace"Yawwa ga dady nan ayi maganar dashi amma dai gaskiya naji dadin wannan al'amari.' General yaji duk abunda suke tattaunawa amma bai ce musu komai ba cin abincin sa kurrum yake. Hajiya Asiya tace"Dady kanajin mu fa da Hakkim ka'ki cewa komai." A nutse yace." Allah ya sanya alkairi Abdul girma yazo." Dariya hakkim yayi yace."Dady da wuri fa nake so ayi komai a gama." General yace." Ai babu matsala ni Zan sanya ayi min bunkice kan Yarinyar Allah ya kaimu lokacin." Hakkim yaji dadin hadin kan da ya samu gurin mahaifin nasa ya San kuma ko da yayi bunkice ya samu labarin cewar Sarah tubabbiya ce bazai hana auran ba sanin halin dady nasa Yana da saukin kai da bawa kowa damar za'bar abunda yake so. ****** Yau kwanan Hakkim uku da dawowa kuma tun ranar da abun ya faru bai kara shiga harkar Ladidi ba wani sa'in ko parlor ya shigo ya tadda ita a zaune a futa yake yi saboda Sam baya bukatar abunda zai hadashi da ita, To itama Ladidin nata 'bangaran hakane kwata-kwata idan yana guri bata sake wa a gidan shiyasa duk sanda taji motsinsa a parlor bata futowa har sai ya futa. Yusuf ya dage fa da gaske yake yi shi son Ladidi yake general yasan da maganar haka ma mahaifinsa duk sun San da maganar shi dai general har yanzu bai ce komai ba yana dai kallon yanda Yusuf din yake shige da fuce a gidan da yanda yakewa Ladidi hidima suttura iri-iri wani ma ba na 'kasar bane ga k'atuwar waya ya siya mata. Hakkim kam kallonsa yake yana mamakin sa da irin ibtila'in da yake so ya d'aukowa kansa yarinyar da take da tawagar aljanu a kanta itace zai aura lallai Yusuf yaci kai. Shi kam Yusuf ya matsawa dadynsa dole yazo ya nema masa aure gurin general hakanan yazo a lokacin ne kuma general din yace." Ya bari tukkuna zai je ya nemi izini daga gurin iyayenta domin shima ba a bashi damar ya aurar da ita ba, Mahaifin Yusuf yace." To hakan yayi idan ka tashi tafiya sai muje tare." To da wannan suka rufe maganar. Hakkim yaso ya zuga Yusuf kan ya fasa auran Ladidi a cewar sa tana da girka girkan jinnu watarana yana ji yana gani zasu dame shi. Yusuf Yayi nisa a kaunar Ladidi yace ko bishiyar kuka ce a kanta shi yaji ya gani. Hakkim dariya yake masa yanayi masa kallon Mara hankali. Tunda mahaifin Yusuf yazo wa da dady wannan maganar yasa kansa cikin damuwa tabbas tsakanin Hakkim da Yusuf a gurunsa daya ne amma idan San samu ne shi kam yafi so Hakkim ya auri Ladidi saboda yanda Allah ya zuba masa kaunarta cikin zuciyarsa dole yayi wani abu akan lamarin. *18/12/2019* _BintuUm@rAbb@le_ https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation *🌚🌚🌚LADIDI🌚🌚🌚* *🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀K'WADAGA🧟‍♀🧟‍♀🧟‍♀* ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *ZAMANI WRITES* *ASSOCIATION🤝🏻* ___________________ ```We are here to educate motivate and entertain our readas``` ____________________ *DEDIGATED* *TO* *RAHIMA ALIYU* *ABUJA* ```BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM ``` *🅿45* Salima da Ladidi ne zaune a parlor suna hira lokacin Hjy Asiya tana kicin ita da mai aikinta Hjy Asiya Lemo ta had'a na zob'o tsaf ta kammala ta sanya a frji baito mai aiki ta hau gyara gurin ita kuma ta futo daga kicin din. Ladidi duk jinta take yi a takure a gurin sakamakon shigowar dodon ta Hakkim Wanda yake magana da Salima. Ganin zaman da take gurin bashi da amfani yasa ta mike da sauri zata bar gurin. Cikin bada umarni yace." Ki koma kiyi zaman ki ni futa zanyi ban ga dalilin da zai sanya idan kin ganni a guri sai ki ke damun kanki wannan zai nuna wa mutane cewar kamar wani abun nai miki." Ladidi ta wuce shi kawai ba tare da ta koma ta zauna ba, Salima ya kalla yace." Kin gani ko Yanzu idan dady zai gani zaice nine nake takura mata. Salima tace"Nima fad'an da nake mata kenan cewar ta dinga sakewa da kowa kai din ma yanzu ka gane bata da lafiya duk abunda take yi" Hakkim yace." Ni tuntuni dama na fahimci yarinyar tana da matsala ni kam yanzu babu ruwana da ita bare aljanunta su tashi ace nine." Salima tasa dariya tana fadin"Ni kaina yanzu na daina jin tsoro Wallahi da ne dai nake jin tsuro idan suka tashi." Ta'be bakinsa yayi ya zauna kan kujera tare da fafine"Je ki kawo min abunci yunwa nake ji." Salima ta mike da sauri ta nufi kicin. Ladidi kuwa na cikin dakin zugum tayi kan gado tana tuno fuskar Hakkim yanzu take ganin kyawunsa sosai taji zuciyarta na masa wani irin so cikin zuciyarta tace"Allah yasa dady yace ya aure ni da naji dad'i." Ita kadai take zancan zuci kafin ta kwanta kan bed din tana lumshe ido cike da soyyayr Hakkim din. **** Daddare bayan sun gama dinnar General ya kallesu a nutse yace." Zamuje kano 'kauyan d'an kunkuru zamu je mu dubo su Mai koko bayan haka kuma zan mu nemi izinin daga gurin waliyyin Aminatu." Hakkim yace." Dady Allah ya sanya alkairi ni kam bazan samu zuwa ba." General yace." Dole sai kaje baka da wani uziri da zaka kawo min na yarda dashi." Sunkuyar da kansa yayi yana sakin dariya,Salima da Salim kam murna suke yi zasu je gidan gona, Ladidi kam babu Wanda ya kaita farin ciki sunkuyar da kanta tayi cikin jin dad'i. Hakkim ya dinga mamakin ta sau kusan hudu suna hada ido dashi sai tayi saurin kauda kanta tana sakar masa murmushi abun ya daure masa kai sosai daga k'arshe sai ya fara tunanin ko aljanunta ne zasu motsa tashi yayi daga gurin yana tsaki a zuciyarsa yace." Haka kurrum ki dinga dariya kamar wata shashasha, waje ya futa ya zauna kan wata irin kujera ta huta waya ya futo da ita ya kira Rabin ransa Sarah, Ladidi kuwa haushi taji da ya tashi daga gurin tana jin dadin kallon kyakyawar surarar shi da muryarsa mai dadin sauraro ikon Allah ita kanta mamaki take yi lokaci guda Allah ya Dora mata sonshi da kaunar sa. **** Washe garin ranar suka shirya tsaf harda Yusuf suka tafi *Kano ta dabo timbin giwa kano ko dame kazo an fika!* Tun mota Ladidi take murna da dariya Hakkim nayi mata kallon Mara hankali lokaci lokaci yana jan tsaki mussaman Idan yaga irin rawar jikin da Yusuf yake yi a kanta. Shifa dan dady ya matsa masa ne da babu abunda zai sanya ya hada tafiya da Mara hankali sunan da ya sata mata kenan. Mai koko na zaune a tsakar gida tana sauraron redio kawai Ladidi ta fad'o gidan babu sallama tayi kan Mai koko tana ihu! Iya ta mike zaune da sauri tana murna da farin ciki sai shafa jikinta take tana mutsika idonta fad'i take "Yau wa nake gani a gabana Ladidi na ce ta zama babbar mace kai Alhmdullahi Allah nagode maka Ashe dai zan sake ganin ki Ladidi ta Mai kok...... Kafin Iya ta rufe bakin ta Ladidi ta fad'i a gurin tana turje-turje! sai burgima take yi a tsakar gida wata farar kumfa na futowa daga bakinta, hakan yayi dai-dai da shigowar su Hakkim gidan general yayi kanta da sauri hat suna buga karo da Mai koko wace take ta faman salati da sallalami! Hakkim Yusuf Hajiya Asiya Salima da salim duk suna tsaye suna kallon ikon Allah. *22/12/2019* _BintuUm@rAbb@le_ An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels