An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels *💣💣DIJE K'ARANGIGIYA💣💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *ALHMDLLH ALLAH DA YA NUNA MANI WANNAN RANA HAKA MA NA GODEWA ALLAH DA HAR YA ARA MANI LOKACI YA BANI RAI DA LAFIYAR DA ZAN SAKE DORA ALKALAMINA DA SABON LITTAFINA MAI SUNA DIJE K'ARANGIYA, SAI DAI GAJEREN LABARI NE MAI CIKE DA BARKWANCI DA NISHADANTARWA HADI DA ILMANTARWA DUKA, MASOYANA A DUK INDA KUKE INA ALFAKHARI DA KU HAR MA DA MAKIYAN DUKA D/AUTA TANA GODIYA👍🏻* *LITTAFIN DIJE K'ARANGIYA SADAUKARWA NE GA MAHAIFIYATA UWA MA BA DA MAMA BAYA GOYA MARAYUN ALLAH, UBANGIJI YA K'ARA MAKI LAFIYA YA JA MANA DA NISAN KWANANKI INA SONKI SOSAI MUMMYTA ALLAH YA KAREKI DA SHARRIN MUTUM DA SHARRIN SHEDAN ALLAH YA SAKA MAKI DA GIDAN ALJANNAH KO ALJANNAR TA CEN CEN KOLOLUWA I LOVE YOU SO SO MUCH MUMMYTA💋💋💋👍🏻* *Lamba ta 1* Tafe suke su biyar kowacensu kanta d'auke da daurin ciyawar da suka debowa dabbobinsu, kowace karkashin ciyawar da ganwo a kanta sunyi d'ana tafe suke akan siririyar hanyar da ta ratsa ciyayi suna tafe suna ta firarsu suna dariya, sai dai wadda ke gabansu duka wadda tana tafe da Yar bulalarta a hannu tana dukan ciyawar da ke gefe gefen hanya tayi wata kuwwa ta fara waka tana cewa. "ku saura ku ji Yau fa in naga dama" Dukansu Suka had'a baki da kalar wakar da tayi wajen fad'in cewa "Dije k'arangiya yau kuma wacce kika k'ullo?" Wadda aka kira da Dijen ta yi tsalle har sai da ciyawarta ta so fad'uwa ta tare da sauri cikin wakar tace,. "Rumfar mai gari yau nike so mu je mu tarwatsa" Hansai ta zaro Ido waje bakinta yana rawa tace,. "WALLAHI nikam Dije babu ruwana haka kawai mu je mu d'auki alhakin mutane a banz......" Dije cikin zafin nama ta kaiwa bakinta faka tace, "ware anan tun kafin yau Inna Meramu ta yi maki tuwon k'asa, kuma WALLAHI kika kuskura na ji kin fad'i maganarnan sai na darje maki baki yayi jini" Sanin halin yasa Hansai ta yi saurin yanke hanyar ta barsu anan tana yi tana waigen Dije don kar ta biyota ta jibgeta a banza, don ta santa sarai wannan k'aramin aikinta ne, Dijen ta kalli sauran abokan nata ta ajiye ciyawarta ganin haka yasa dukansu suka ajiye tasu, Dije ta saka bulalar dake hannunta ta daki d'aya daga cikin kawayen nata tace, "Ke kuma Lanti in kinsan cewa bak'in halinki zaki nuna har kisa a gano Shirinmu ba gaske bane ba to ki tafi gida kawai zamu k'araso" Lanti jikinta yana rawa ta marairece tace,. "A yi dani kawai ba Zan bari a gano ba" Dije ta kalli sauran ta kyalkyale da dariya sannan ta janyo kansu ta had'e waje d'aya ta fara rada masu kus kus a kunne, gaba d'aya suka tuntsure da dariya Mune tana dariya ta ce,. "Har na hango yanda maigari zai ....." Dije ta yi saurin buge mata baki tace,. "To tonanna tonamu aji tun kafin muje cikin garin" Aiko ba shiri Mune ta yi gum tana fiki fiki da ido daga nan Dijen tace da kowa ya shirya da sunje bakin garin zasu fara shirinsu, aiko Suka k'ara d'aukar ciyawarsu Suka dora akai suna tafe suna dariya har daf da shiga cikin garin Suka fara koyon K'ugin kukan Kura sannan dukansu suka ciccire talkaminsu suka sagala a hannuwa Dije ta fara dafe ciyawarta ta zankara aguje tana K'ugin kura tana kuwwa tana fad'in "wayyoo Kura! kura a garinmu ku yo agaji gata nan shigowa garin daf take damu ta kusa k'araso" Aiko sauran kawayenta suma Suka dafe mata baya suna K'ugin suna ihun ga kura nan ta shigo gari, Mutane tun da suka fahimci abunda suke fad'a Suka fara gudun ceton Rai Dije da kawayenta aguje har fadar Mai Garin don tun daga nesa da Suka jiyo sautin kukan Kuran suka natsu musamman da suka ji abunda take fad'a sai ga dandalin ya fara watsewa, saboda ganin yanda suke gudu a bala'e suna haki suka Fara gasgata lamarin, sai mutum biyu aka bari a wajen sai ko ga su sun k'araso tana haki tace da su "Mai Gari Mahaukaciyar Kura a garinmu yau gata cen har ta fara cin wasu a farkon gari da alama ma tana gaf da karasowa nan muma dakyar mukasha" Maigarin ya zaro Ido waje yace,. "Ke Dije kinsan nasan halinki ko? To Wallahi......" Kafin ya k'arasa sai ga wani aguje ya nufosu Yana fad'in "Kura! kura! Maigari" Aiko Mai Gari ya zabura ya zankara aguje dafe da rawaninshi sai dai Yana gaf da shiga gidanshi ne wani kwatami ya jashi yayi luuu sai jinshi kake Tim! A k'asa rawani yayi gabas hula tayi yamma, sai ga Maigari da fasa wata arniyar k'ara ya mike cikin zafin nama ya fad'a gidanshi ko kallon rawanin da hular bai yi ba sai ihu yake yi yana fad'in,. "Kowa yayi ta kanshi Rana ta b'aci yau maza bisa kanmu". Dije da sauran kawayenta da suke labe jikin k'aton iccen da ke k'ofar gidan Wanda anan Maigarin da mutaneshi suke Shan iska, sai k'ugin kukan kurar suke yi ganin kowa ya shige yasa suka fito suna ta tuntsura dariya musamman da suka hango wani dattijo aguje ya dafe keya sai gudun ceton Rai yake yi ya shige gidanshi kudum ya dantse k'ofa. Daga nan bakin Gidan Maigarin Dije tace kowa tayi gida aiko kowacensu ta nufi gidansu Dije tana tafe tana dariyar keta idan ta hango wasu da gudu ta sake yin k'ugin kurar itama ta dafe ciyawarta aguje tana cewa "Gatanan WALLAHI taci mutum biyar a farkon gari" Aiko Mutane sai su k'ara d'aga k'afa da haka har ta kai gida sai dai tana Kai k'ofar gidan ta ga gidan a rufe gam! Wata dariya ta sake zubo mata, ta Kai kallonta ga wani gida da su ke makota da juna nan ma rufe yake gam sai da tayi dariyarta mai lasisi sannan ta fara buga kyauren Gidansu tana sake koyon kugin kurar a haukace tana fad'in "Baffah ka bud'e Kura zata cenyeni a arha" Sai gashi ko taji an bude k'ofar da sauri ya fisgota da k'arfi har sai da ciyawar ta fad'i ya turata ciki ya sake dantse k'ofar yana haki ya janyota har cikin Gidan yace, "Maza shiga d'akin innarki ku b'oye Ni idan har ta shigo gidan ta canyeni ku sai ku tsira illah iyaka ku bini da addu'a" Dije ta tuntsure da dariya saboda ganin yanda Baffan yake ta zaro Ido yana dubin k'ofar hanyar fita Gidan, aiko sai ga Kukan akuya a k'ofar gidan tana meeh! meeh! A guje Baffa ya zankara da gudu yayi hanyar d'akinshi yana fad'in "Salamun k'aulan min rabbir'rahim shikenan tamu ta k'are yau shahada zallah a garin K'IRIU" Har ya fad'a d'akinshi zai rufo ya waigo ganin Dije tsaye tana k'unshe dariyarta, cikin d'aga murya yace "Uban me kike anan da ba zaki b'oye ba ke?......" Jin sautin kuwwa a makotansu yasa Baffa ya kullo k'ofar garam ya Fara salati iya karfinshi, Dije ta k'araso jikin k'ofar tace "WALLAHI Baffa ba wata kura ka kwantar da hankalinka" Ganin yaki budewa ne kuma bai daina Salatin ba yasa ta nufi k'ofar gidan ta bud'e kyauren aiko sai ga Yar akuyarta a k'ofar gidan ta dawo kiyo ashe itace take kuka, ta rik'o igiyarta ta janyota har cikin Gidan ta je bakin k'ofar d'akin Innarta tace "Inna ki bud'e ba wata kura WALLAHI duk k'arya ne" Jin sautin kukan akuyar yasa Innar zaro Ido daga cen d'akin tace "Dije kina Nan ko ta fara cenyeki" Dije dafe cikinta tana dariyar fitar hankali cikin dariyar tace,. "Akuyata ce Inna ki fito ma ki gani da idonki" Innar ta d'aga murya tace,. "WALLAHI in har kin ganni Lahira to kaini aka yi amman ba dai ace inje da kafafuna ba" Baffa jin dariyarta ta yi yawa yasa ya zaci ko kukane take yi ya d'an bud'e k'ofar d'akinshi kad'an ya dan lek'o da idonshi d'aya jikinshi sai rawa yake yi yana makyarkyatar tsoro, aiko sai ga Dije ya hango kwance dafe da ciki tana dariyar keta. Ya bud'e d'akin duka ya lek'o kanshi yace,. "Wai ke me yasa kike ja'ira yanzu ke duk wannan tashin hankali da kowa yake ciki ke dariya ma kika samu damar yi? To WALLAHI ki sani da ta shigo gidan da ke zata fara cin karo don Ni kafin ma infito cetonki kin zama Jan nama" Dije ta rufe bakinta da dariyar da ta sub'uce mata tace, "WALLAHI Baffah k'arya ce kawai ake yi ba wata kura su Mune ne kawai Suka shirya komi" Baffah ya zaro Ido ya fito d'akin duka yace "Su Mune ? Ko dai su ke? To WALLAHI in dai har da gaske karya ce kuka shirya wannan karon ba ruwana da rigimar da kika janyowa kanki don ki sani ......" Kafin ya k'arasa maganar sai gashi ko ya jiyo sautin haushin mutane a k'ofar gidan anata hayaniya, ana dad'i "Yau Kam ya zama Dole a garemu mu d'auki mataki akan yarinyar nan" Dije ta zabura da sauri tana rabon Ido ta Kai kallonta ga bishiyar itaciyar da ke tsakiyar gidan nasu, ta yi wurin aguje ta yi tsul ta haye saman itaciyar sai gata da kaiwa cen koli ta lafe luf tana sauraren jin irin matakin da za'a d'auka akanta yau kuma, don ita kanta tasan yau Kam ta tarowa kanta aradu da fad'i. Dandano daga labarin Dije k'arangiya labarin barkwanci ne Mai cike da nishantarwa hadi da ilimantarwa a fakaice. Akafta🤾🏻‍♂️ D/AUTA CE✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *Rangadi lalle Dije k'arangiya ta cafko jama'a Alhmdllh Ina godiya sosai Wallahi naji dad'in ruwan comments dinku akan book d'ina Alkhairin ALLAH ya Kai maku a ko'ina kuke fad'in duniyar nan luv u all💋* *Lamba ta 2* Baffah ya bi bishiyar da kallo cike takaicin ka haifi mutum baka haifi halinshi ba ya nufi k'ofar Gidan, sai dai ganin cincirindon mutane fal a k'ofar Gidan nashi kowane da abun dukanshi sai muzurai suke yi yasa shi dawowa da sauri yana sauke numfashin mai cike da tsantsar tashin hankali, aiko suka fara cewa "Malam Buba ka fito da ita tun kafin mu shigo da kanmu mu janyota don kuwa Maigarin ne da kanshi yake nemanka tare da tijararriyar d'iyar taku" Malam Buba ya fara had'a hannu waje d'aya yana fad'in,. "Don girman Allah ayi hak'uri da halin Dije yanzu haka Ni har yanzu ma ban ganta ba don ko Gida bata dawo ba" Wani katoton bafaden Maigari ranshi a b'ace yace,. "Zaka fito da ita taje ta karb'i hukunci Koko sai mun shiga da kanmu mun fito da ita?" Malam Buba ya marairece yace, "Ku yi hakuri don ALLAH duk da dai ni har yanzu ma bansan laifin da ta yi maku ba" Bafaden ya zabura Kamar ya daki Baffah yace, "Yanzu duk guje gujen zuwan Kura da ake yi a garin nan kana nufin baka sani ba? To Bari kaji yanzu haka Uwardakin Maigari ta karye Kuma duk a sanadin yarka Dije, don haka Maigari ya bada umurnin a d'auko masa ita ko a raye ko a mace domin a ladaftar da ita" Yana k'are maganar Baffah ya zaro Ido yace, "Don girman ALLAH kuyi hakuri amman Dije bata dawo gidan nan ba, idan kuma baku amince da maganata ba ku shiga na baku dama ku fito da ita" Aiko kafin ma ya karasa maganar suka tureshi suka fad'a Gidan, Kai tsaye suka dinga neman Dije lungu da sak'o na gidan ganin d'akin Inna a rufe yasa suka zaci tana ciki, Aiko k'aton bafaden ya saka k'afa ya buge kyauren Inna da ke rakub'e tana salati don ta zaci ko Kurar ce ta shigo Gidan mutane suka biyota ana neman hanyar kamata, jin an bugo k'ofar yasa Inna rafka salati tace "Wayyo Uwata wayyo Ubana zan biku ba tare da guzurina ba, wayyo ALLAHna ka taimakeni Kura zata yi man tsiya" Inna ta make cen karkashin gadon bononta inda ta b'oye sai ihu take kwarmawa, jin motsin shigowar mutum yasa ta k'ara sautinta tana fad'in "Yihhuuu Jama'a ku yo agaji tun kafin ta k'araso ta Kai mani wawa" Baffah ya duk'o da kanshi ta karkashin Gadon inda yake jin sautinta, Inna tana had'a ido da kanshi ta zaci Kan kurar ne ta saka k'afa ta halbo wata fanteka dake ke karkashin gadon sai a fuskar Baffah, a zabure ya d'ago ranshi a b'ace yace "Ke Mahaukaciya fito haka nan ba wata kura yarki ce ta janyo masifar don haka ga Maigari nan ya aiko a kamota" INNA cikin wani sabon firgici tace "Da gaske???" A kufule Baffah yace, "Karyar da na saba yi maki ce yau na k'ara kwatawa" INNA cikin rawar jiki ta lallaba tana ture kwanukan da ta shige cikinsu ta samu ta fito, da kyar ganin Baffan baya d'akin yasa ta fito tsakar gidan, aiko sai gata da yin arba da mutane cike da gidan nasu Mata da Maza, cike da tsananin rudu tace "Na shigesu jama'a Lafiya?" Wata Yar tsohuwa tace,. "Ina fa Lafiya Dije ta janyo anyita jin raunuka a gari duk a sanadin rashin mutuncinta, ki je ki fito da ita tun kafin Maigari ya sa a d'auki hukunci akanku, daman ance d'ankuka Mai jawa Uwarshi jifa, to yau dai ta sake janyo maku abunda yafi na kullum" Baffah cikin takaici yace, Na gaya maku bata gidan amman kunki amincewa" Aiko daga cen saman itaciyar Dije ta kai iya wuya sai jin suka yi tace,. "Barsu Baffahna idan ma sunki amincewa su kasheni idan na sauko" Aiko gaba d'aya suka d'aga Kai suna kallon bishiyar cike da tanbabar a'ina maganar take fitowa, Dije ta kurawa tsohuwar Ido tana maka mata harara tace,. "WALLAHI da kin cikani ta kanki zan diro Uwar tsugudidin tsiya" Aiko a lokacin suka tabbatar da ashe ma saman itaciyar ta b'oye, Bafaden ya zo gaban bishiyar yace "Ki sauko salun alun tun kafin a sare itaciyar duka ki fado ki kakkarye" Dije ta yi saurin fad'in "Yasin ba zan sauko ba duk Mai son in sauko ya hawo ya sauko dani, amman kusani duk Wanda yayi wautar hawa bishiyar nan to ina maku albishir ba zai sauko da Ido d'aya ba, don kuwa sai nasa aljanina ya zuke idon muga ta tsiya" Aiko jikin kowa yayi sanyi saboda sanin halin wacece Dijen da hatsabibancinta, daga nan aka fara shawarar wa zai hau ya sauko da ita? Aka Kai karshe akan Baffahnta ya hau ya sauko da ita, ganin gidan sai k'ara dinkewa yake yi da mutane yasa shi yanke shawarar hawa ya sauko da ita ko don a samu rangwamen hukuncin da za'a yanke mata. Aiko ya kama bishiyar zai hau kenan Dije tace,. "Jira in sauko Baffah ai dai Raina a hannun ALLAH yake duk cikinsu Babu mai ikon kasheni" Baffah yace,. "Sauko a hankali to ai duk ke kika jawo komi muna zaman zamanmu kika d'auko muna abun magana" Dije ta fara saukowa a hankali har ta kawo kusa ta diro k'asa aiko caraf Bafaden ya riketa gam! Ya janyota tana tirjiya har suka fito gidan, sai fad'in take yi "ka jira in tafi da kaina ai ko? Tunda dai ba Kai ka cire man kafafun ba" Amman Ina janta kawai yake yi da k'arfin tsiya cikin zafin nama tana tirjiya da gangan don kawai ta wahalar dashi, mutane ko suka biyosu buuu! Har k'ofar Gidan Maigarin inda nan ma mutane sun cika ana jiran zuwan Dijen. Aiko sai gashi ana ganinta wuri ya fara dinkewa da zage zage da surutai, Bafaden cikin matuk'ar gajiya ya Kai Dije gaban Maigarin inda a kallo d'aya zaka gano kumburewar da Bakinshi yayi suntum! Saboda garin gudun tsoron kura ya buge Bakinshi. Dije ta ki zama tayi tsaye ta rik'e k'ugu tana k'arewa su Hansai da Lanti da Mune da kuma jummala da Ladiyo, zuciyarta cike tsantsar fushi wanda k'iris take jira ta tada wata sabuwar fitina. Aiko Maigarin yace da ita ta zauna ta yi Kamar bata jishi ba, Bafaden ya katsa mata tsawa yace "Don kaniyarki ba da ke ake magana ba? ko sai na zaunar da ke da kaina?" Dije ta galla masa wata uwar harara tace,. "Laisal matsi bi gairi haza takura ka barni inyi ijlis da duwawuna" Aiko ya zabura ya Kai mata wani lafiyayyen mari har sai da tayi zaman yan bori, rik'e da gefen da ya maretan nan take idonta suka canza zuwa ja cikin zafin nama ta zabura ta mike tsaye ta heta kuwwa iya k'arfinta tace "Yihuuuuuuhuu kurunkus kan dan bera" Ta yi tsalle ta haye jikin Bafaden ta cafko wuyanshi ta rik'e gam! sai surutai take yi kamar wata mai aljanun gaske tana fad'in "Sai mun cire wuyan nan dole ai yasin wanga kai dashi zamu yi kalacin dare yau makogoron nan kuwa dashi zamu yi busa, idanuwan nan kuma zamu saka a bindin jakinmu mulkutus barakus rik'e man hancin nan" Aiko jama'a kowa ya mike sai turin juna ake yi wajen leken Dije da Bafade, shi kam da yaji wuya ta Kai karo zuciyarshi ta tabbatar masa da aljanu ne yake fad'a da su ba Dije ba, don ya kasa kwatar kanshi ga hannun Dije duk ko da take Yar firit ba wani jiki gareta ba ko kad'an, aiko ya fara kwarantin Kiran "Innahu min Sulaimanu lak'ada kawas da bak'in Aljanin, don inji dad'in narkar da shegiya k'asa" Aiko dakyar da jib'in goshi aka banbari Dije daga wuyan Bafaden, kafin kace me wuyanshi yasuntume suntum idonshi sun yi jawur duk ta yakushe masa fuska da akaifarta. Ita Kam ana banbareta jikinshi ta fadi ta sheme sai surutai take yi sai kace daman cen aljanun gaske ne gareta. Akafta😂 D/AUTA CE✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *INA GODIYA SOSAI DA COMMENTS DINKU💃🏻💃🏻💃🏻 K'arangiya tana gaisheku🤣* *Lamba ta 3* Bafade rik'e da wuyanshi yake fad'in,. "Akwai kan bisa wuyan ko ta yi sa'ar rabashi da gangar jikin??" Gaba d'aya wurin yayi shiru wasu Kam basu daina yin dariya k'asa k'asa ba, Baffah jikinshi yana rawa ya k'araso wurin Dije zai tab'ata ta yi saurin fad'in "Aljani danduna rik'e man hannunshi kar ka bari ya tabamu idan ya tabamu hannunshi zai k'one zai k'one kurmus tamkar yanda wuta take cenye kara" Aiko da sauri Baffah ya ja baya Maigari yace da Liman ya matso ya yi mata addu'a da nufin a samu aljanun su kwanta ta karb'i hukuncinta, Aiko Liman yana matsowa kusa da ita ta yi wata zabura ba mutanen da ke wurin suna kallo ba har shi kanshi Liman sai da yaji tsoro, hannunshi yana rawa ya d'ora hannunshi akan goshin Dije ya fara tofa mata addu'a, Aiko Dije ta kurma kuwwa ta fara surutai tana cewa "Ba zamu fita ba kama daina addu'ar nan ko'ina ba zamu je ba muna nan har sai Maigari ya janye kudurinshi na son d'aukar hukunci akan god'iyarmu, akanta zamu tada garin nan akanta zamu mayar da garin nan toka" Liman dai sai zuba addu'a yake yi sai cen Dije tace "Ayi hak'uri zamu yi magana za muyi magana nace" Maigarin ya yi Liman alamu da Ido akan ya dakata aiko Dije ta fara fad'in "Mune muka zama kura mune muka fito a siffar kura muka biyosu, kuma a gaban idonta muka kashe mutum biyar a farkon gari amman ba mutanenku bane mutanenmu ne, tunda ta take muna 'ya'ya muka biyosu ita da kawayenta, don yanzu haka abokan fadan nawa ya jiman raunuka saboda fad'an da muka yi da junanmu Ni da yan uwana aljanu don haka Bari in fito a siffata ku gani nasan zaku tausaya man" Kowa na wajen yace "A'a kar ka fito" Wasu suka ce "ALLAH ya baka lafiya ka ja Yan uwanka ku tafi kawai mun yafe mata" Dije ta sake cewa "Idan na tafi kuka daketa fa ko kuka d'auki wani mataki kanta fa zan gayyato Yan uwana mu sake zama kuraye mu zo garin nan sai mun kashe kowa don kowa ma ba zai tsira ba" Aiko cikinsu ya duri ruwa Maigari yace, "Ba za'a tab'ata ba amman don ALLAH in kuna wa ALLAH ku yi nesa da garin nan, Kuma ku yi alk'awali akan ba zaku sake shiga shirginmu ba" Dije tace "zamu tafi amman har sai mun mayarwa da sarkin fadawa kanshi da muka tsige" Bafaden ya shafo kanshi da yasha mola sol! sol! yace, "Ranka ya dad'e ai ya koma da kanshi ma gashi a saman wuyan ina jinshi" DIJE ta mike tsaye cikin zabura ta katsa masa wata uwar harara da idanuwanta da suka jajawur! Tace "Wa ya Gaya maka kanka ne a sama to bari ka ji ku kuke ganinshi kamar Kai irin naku to wannan Yar karamar dabbarmu ce dake bacci a saman kanka, naka kan yana cen bangon duniya bakin kogin zumburbur an fara had'a kayan dafuwarshi da ka yi sake nan da safiya zaka rasa ranka da an jefashi cikin tunkunyar dafuwar" Bafaden ya zabura dafe kan yace "A cire man dabbar a maidoman kaina don ALLAH ka taimakeni" Dije ta kyalkyale da wata mahaukaciyar dariya sannan ta yi shiru tana tare da Kara kunnenta a iska kamar mai sauraren wani abu sai cen tace,. "Ranka ya dad'e Sarki gani nan zuwa yanzu a yi man afuwa yanzu zan kawo maka" Tana k'are surutan tace, "Babana Sarkin aljanu yace da Ni in tattaroku yanzun nan dukanku mu had'u a bakin Ruwa ayi shari'ar a cen" Kowa ya gwalalo Ido waje Aiko cikin sauri ta fara fad'in "Ya zajisu ya zurmukus banbaradusa ya zamburkusadduna ya......." Kafin kace me duk wuri ya hautsine da k'ura saboda dan neman gudun famfalakin da mutane suke yi, Bafade dafe da kanshi yana gudu yana fad'in "Ki tashi daga baccin nan don girman ALLAH ki dauko mani kaina, tun kafin a fara dafuwarshi a bangon duniya" Ganin mutane da yawa sun watse sai Yan gani kasheni ciki kuwa har da Maigari da Liman sannan da Baffanta da ke nesa da su yana haki, ta k'ara keta kuwwa tace "Ku saurareni zamu tafi amman ko harara aka yiwa god'iyarmu Dije sai mun dawo tare da gayyar rundunar Yan uwana aljanu, mun tafi Sarkin fadawa ga kanka Nan gobe ka k'ara dan gidan marasa tausayi amman ka sani za mu zo mu tafi da kai da ka kuskura ka fito fitsarin dare, mun tafi zo muje ke kuma sarkin bacci" Sai kawai aka ga Dije ta fad'i yaraf tana fisge fisge tana wani Abu da kai ta gwalo Ido sai cen ta yi luf kamar Mai bacci. Liman ya sake tofa mata addu'ar ya fara Kiran sunanta, Dije ta yi wukil da Ido d'aya suna had'a Ido da Liman ta zabura ta mike zaune tace "Don Allah ka yi hak'uri WALLAHI da gaske naga Kura Ni da su Ladiyo, a tambayesu aji ai ko su zasu fadi gaskiya don ba Ni kad'ai na ganta ba har dasu, a gaban idona taci mutum biyar a farkon gari" Maigarin yayi shiru yana nazari sannan yace,. "Ai kinci sa'a komi ya wuce tunda an wankeki tashi kije gida amman kar ki sake zuwa daji debo ciyawa" Dije ta zaro Ido tace "Na shiga Uku ita akuyar tawa me zata ci idan na daina fita daji?" Maigarin ya yi Yar dariya yace "Ni Zan sa akawo maki Ciyawar kullum ki dinga bata saboda baki da isashiyar lafiya tashi kije gida ki kwanta ki huta ALLAH ya baki lafiya" Dije ta washe baki tace,. " Harda dussa?" Yace "har da ita tafi gidan kawai" Dije ta Mik'e tana tsallen jin dad'i tace "Na gode Maigari ALLAH ya ja da nisan bacci kuma ya baka lafiya ya tsare gaba kuma yasa kar ka mance watarana kaki aikowa" Maigari sai Ameeen yake fad'i don a matse yake da ta bar wurin tun kafin shima yayi sanadin abunda zai janyo ta k'ara kassarashi. Dije ta nufi wajen Baffahnta tana dariya tace, "Na huta da zuwa Daji akuyata zata sami ciyawa kullum" Baffah ya fisgo hannunta suka nufi gida, Mutane da sun hangota su yi ta darewa suna gudu Dije kam sai tsallen cin nasara take yi, Liman kam binta yayi da kallo yayi dariya don shi tsaf ya gano ba wani aljani da ke kanta tsabar iya shege ne ke damunta, amman ko ba komi ya jinjina mata tunda har ta samowa kanta hanyar kwatar kai, daga wannan gangamin jidalin data hadowa mutane a cikin gari. Akafta😅 D/AUTA CE✍🏻 *💣DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *WAI! WAI! WAI RIGIJI GABJI WANI KAYA SAI AMALI LALLE DIJE K'ARANGIYA TAYI FARIN JINI BA KAD'AN BA INA GODIYA SOSAI MASOYA BOOK D'IN ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU A DUK INDA KUKE👍🏻* *Lamba ta 4* Ko da suka je gida suka taradda Inna tana tankaden garin masara tana yi tana sharar hawaye, Dije da gudu ta isa wurinta ta fad'a jikinta har sai da tiren garin yayi tsalle rabi ya zube rabi ciki, Inna ta saka hannu ta Kai mata wani mugun dunku a baya har sai da ta gantsara, a zabure Dije ta mike tana sosa wajen tana zunburo Baki alamar taji haushin dukan, Inna ta nunata da dan yatsa tace "WALLAHI ki fita idona in rufe Dije na fara gajiya da rashin hankalinki, ke kenan kullum janyowa kanki abunda za'a saka ki a bakin duniya muma ki ja muna zagi a gari, to bari kiji WALLAHI kwanan nan zan sa Delu ta tafi dake birni kamar yanda kullum take rokata akan in bata ke ta kaiki aikatau, kije cen ki had'u da masu horaki da kyau tunda Ni kin renani" Dije ta fara dire diren kafa tana kuka tana fadin, "ai WALLAHI Inna ko an kaini sai na dawo don ban zuwa birni a yanke mani Kai, Ni dai kiyi hak'uri don ALLAH na yi maki rantsuwa idan na sake ki dakeni" Inna ta yi banza da ita ta makure jikin gina tana zunburar Baki tana mui mui da Baki tana sharar hawaye, sai ga Baffah ya fito bayi yana fad'in "Wai ke Hasiya me yasa kullum kike tsangwamar yarinyar nan, to WALLAHI ahir dinki wannan karon don kuwa Dije dan sarkin aljanu ne a saman kanta, yanzu haka shi ya zo ya hana a d'auki mataki kanta Kan abunda ta aikata, kuma yayi gargadin ko harara wani yayi mata za su dawo su sake hargitsa garin nan, idan ke kinga ke zaki iya taron aradu da ka to karki fasa" Ya kalli Dije yace "Tafi ki dibi ruwa ki yi wanka ko da zakiji dad'in jikinki akan wannan sukuwar hawan dokin da aljanu suka yi akanki" INNA Hasiya ta rik'e baki tace, "yanzu Kai Malam har ka yarda da shirmen Dije? Lalle kam, to Ni dai ina baka shawara WALLAHI ka daina goya mata baya tana k'ara zama girtsatstsa, don wannan shirmen nata ba zai hanani jibgarta ba idan tayi laifi ko da ko tsamiya ce akanta Ni babu ruwana" Baffah zai shiga dakinshi ya waigo yace, "Kurar da kike tsoron zuwanta garin nan to ko nan gidan ma zata dira idan ta zo wannan karon, sai ki je kiyi gaggawar yin rame a karkashin gadonki kinga idan ta zo sai ki shige kawai, don kuwa ba fashi zaki janyo fushin Dan Sarkin aljanu" Yana K'are maganar ya shige d'aki abunshi domin a matse yake da yada hakarkarinshi ya huta ya samu natsuwarshi ta dawo. Dije ta dibi ruwa cike fam da farin bokin fenti ta kinkimeshi tana nishi ta yi bayi tana ta gunguni, don taci alwashin sai ta debe haushinta da ruwan gidan don kuwa sai ta yi wacakarta son ranta dasu tunda Innar ta yi mata fad'a. Gashi sai sun zagaya bayan gidan suka debo ruwan ga wata rijiyar k'ofar gidansu Ladiyo kawarta, ta yi wankanta mai cike da barna sannan ta fito tana rawar sanyi daga ita sai siket a k'irji tana tsallen sanyi, Inna ta kalleta tace "In dai takamarki mugunta kanki zaki yiwa in mura ta kamaki sai ki bidi mai ce maki sannu, sannan ruwa ma idan sun k'are ai kece zaki debosu don kinfi kowa sanin halin yayanki" Dije ta zunburo Baki tace,. "WALLAHI Inna kar ki janyo fushin murkustus barakus bn muruddika, yanzu ya sanar dani in fad'a maki suna jin nauyinki don ke kika haifeni sunce in sanar dake daga yau kar ki koma yiman fad'a, da kyar na basu hakuri suka ce sun yafe amman kar a k'ara " INNA ta rik'e baki tace "Au abun har ya kai cen? To ki fad'a masu ba k'ari ba har da k'are k'are sai na yi idan sun tashi su yi kuli kulin kubura dani" Kafin Dije ta yi magana sai ga Usmanu ya shigo Dije tana ganinshi ta yi sum sum ta sassada ta shige dakin Inna kudum, Usmanu ya bita da harara yace "Wai Inna yaushe yarinyar zata yi hankali ne? Yanzu abunda ta janyo kenan a garin nan? WALLAHI taci sa'a bani nan da sai na kakkaryata bak'ar jidalalla, sannan wannan siket d'in da na hanata sakawa ta fito tsakar gida dashi hakanan shi kad'ai bata bari, to duk abunda na yi wa yarinyar cen Inna kar ki ga laifina tunda ta nuna cewa ban isa ba, to Ni sai na nuna mata na fita kangarewa" INNA tace "Halin Dije sai ita abita da addu'a kawai ko za'a ci nasarar abun, amman duka yau aka Saba?" Baffah ya fito yana saka talkaminshi yace "Ka dai yi a hankali in har ba so kake yi garin nan ya dawo toka ba, don kuwa Dije ba ita kad'ai bace idan ka janyo aka maidaka dan duk'usurun bak'in jakki ko bunsuru shikenan Kai ka janyowa kanka" Ya fice abinshi Usmanu yaso yayi dariya ya mazge ya nufi randar ruwa Yana lek'awa ya hango ba komi duka tukanen duk ta kwashe ta yi wanka, aiko ya fara kwalla mata kira sai gata da kwandon kayan kwalliyarta tana shafa jar hodarta, cike da bacin ran da ke kwance akan fuskarshi yace "Uban mi kike cikin Gidan da ba zaki je ki debo ruwa ba?" Dije ta zunburo Baki tace,. "Yanzu na fito wanka fa Yaya sannan ace inje in debo ruwa? lalle ma!" Usmanu yayo kanta zai daketa ta yi bayan Inna ta b'oye, cikin gargadi yace da ita WALLAHI muddin bata debo ruwan nan ba sai jikinta ya gaya mata yau. A gurguje ta gama dige digen bak'in kwallinta ta danbara janbakinta ja fam da Baki sannan ta fisgi bokitin karfensu ta fita tana gunguni. Ko da taje rijiyar makil take da mutane wad'anda wasu da yawa duka tsararta ne, tun daga nesa suna hangota wata ta yafito wata da ke kusa da ita tace "Ga fa K'arangiya Nan Wai ashe aljanu ne da ita shiyasa ma masifarta kullum take gaba gaba" Kafin Yar uwar ta bada amsa Dije ta k'araso ta ajiye bokitinta ta rik'e kugu, Kai tsaye ta matsa jikin rijiyar ta ce da wata mai suna Bintalo ta bata guga ta cika bokitinta, Bintalo ta yi mata kallon banza tace "Kina so ki cika da wuri me ya hana ki zo da taki gugar?" Dije tace,. "Taki nike ra'ayin dibar ruwan da ita zaki bani ko sai na janyo maki asara?" Bintalo ta dafe gugarta da k'afa ta rik'e kugu tace,. "Me zaki iya yi ko an Gaya maki Ni ina tsoronki ne kamar kowa? To WALLAHI kika kawon wasa sai na maki danbanzan duka a wurinn...." Kafin ta Kai k'arshe sai ko taji saukar mari akan fuskarta, Bintalo ta zabura zata rama gugarta ta sub'uce ta fad'a rijiyar, cike da takaici taci kwalar Dije ta shaketa saboda tafi Dije girma nesa, kafin kace me idon DIJE sun yi ja cikin tsananin fushi tace "Sakeni Bintalo" Bintalo ta zakalkalo tace,. "Anki a sakeki ba za'a sake kin ba kiyi abunda zaki iya" Dije tace "nace ki sakeni Bintalo" Bintalo ta k'ara shaketa cikin masifa tace, "Sai kin fiddo man gugata da kika sa ta fad'a ko ina sakinki, WALLAHI yau sai na ga k'arshen rashin kunyarki ba aljanu ba ko iccen kuka ne akanki sai na ci Ubanki..... " Karaf! Sai jin k'arar saukar bokitin k'arfe aka yi a goshin Bintalo Dije ta kwad'a mata kasan bokitin, Aiko Bintalo ta fasa k'ara kafin kace me jini ya fara wanke mata fuska. 😳na yi nan🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️wlh Babu ruwana kar ace Ina nan aka yi 🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️ Akafta🤣🙌🏻 D/AUTA ce✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *COMMENTERS INA MAKU JINJINAR BAN GIRMA🤣👍🏻* *Lamba ta 5* Bintalo tana shafo goshinta ta ga jini ta fad'i k'asa tana kururuwa, gaba d'aya mutanen da ke wurin hankali a tashe suka fara salati, a cikin matasan 'yanmatan da ke wurin wata ta zo da gudu ta cire dankwalin Bintalon ta d'aure mata goshin jabau! Bintalo Kam sai ihu take wasu suka rikata zuwa gidansu. DIJE kam ganin an bar gugunan d'ibar ruwa an nufi wajen Bintalo ana sallallami yasa ta cika bokitinta dam! Ta d'ora akai har ta fara tafiya, hankalin mutanen da ke wajen ya dawo kanta aiko wasu da yawa suka fara jifarta da miyagun kalamai suna aibatata, ita kam ko juyowa bata yi ba ta ci gaba da tafiyarta don ita kanta ganin jinin da ke fita a goshin Bintalon ya tsoratata, sai dai ta mazge kawai don kada a gano taji tsoro ace za'a ci zarafinta a banza. Ko da ta shigo gidan da sanyin jiki ta juye ruwan ta ajiye bokitin zata shige d'aki, Inna Hasiya ta bita da kallo tace "Ke lafiyarki na ganki wata sukuku haka? Ko karyar ciyon ne ya tashi don ba kyason komawa debo ruwan?" Dije ta zumburo Baki tace,. "Ba Bintalo ba ce ta jani muka yi fad'a, kuma WALLAHI sai da nace ta kyaleni ta kyaleni taki to ai gashi nan yanzu ta janyo goshinta ya fashe jini sai tsiyaya yake yi" INNA ta zaro Ido waje dafe da kirji tace,. "Goshinta ya fashe ko dai kin fasa mata? Na shiga Ukuna Ni Hasiya wai Dije kasheni kike so kiyi ne? kulluma da sabuwar masifar da zaki jajibo muna kisa mutane su yi ta ganin kamar bama tsawatar maki, to bari kiji WALLAHI Wannan karon sai dai in kasheki za'ayi a kasheki amman Ni Kam ba hannuna ba k'afata tunda ke kunnuwan Kashi ne da ke" Tana k'are maganar cikin k'unar Rai tayi madafi inda taci gaba da tuka tuwon masararta, tana yi tana fad'a Dije ta shige d'aki sum sum tana matsar kwallah. Aiko minti biyar a tsakani sai ga tashin muryar Iya Mero Uwar Bintalo, tun daga farkon shigowa Gidan take zazzaga ruwan bala'i har ta shigo Gidan rik'e da hannun Bintalo tare da wasu Yan bani na'iya masu zuwa ganin k'wam. Iya Mero tana shigowa ta fara fad'in, "Ina Hasiya fito kiga abunda tsinanniyar 'yarki ta yiwa Bintalo, WALLAHI Ni Kam bazan tab'a lamunta da rashin mutuncin da take yiwa mutane ba, don in kowa ya kyaleta Ni bazan kyaleta ba Dole ne sai na ramawa Bintalo itama in fasa mata goshin ta ji inda dad'i" INNA ta fito daga madafi tana sharce majina saboda hayakin da ya turnuke d'akin madafin yasa idonta sunyi jawur, ta goge fuskarta da gefen zanenta ta k'araso wajen tace "Don ALLAH Mero kiyi hakuri WALLAHI d'a ne ka haifeshi baka haifi halinshi ba, don da ta Ni Dije take bi to ko hannu aka saka mata a baki bazata ciza ba" Ta nufo wurin Bintalo ta rik'ota da nufin taga yanayin raunin, aiko Iya Mero ta tureta da k'arfi ta shiga gaban Bintalo tare da cire mayafinta ta sha d'amara a masifance tace "Ba wani dad'in bakinki da zai yi tasiri a wurina don yau dole ne sai na ramawa Bintalo abunda 'yarki ta yi mata don d'a baifi d'a ba da zaki wani kalallameni da dad'in baki to bazan hak'ura din ba sai na rama mata" INNA cikin b'acin Rai ta shiga d'aki ta janyo Dije da ke makure Kan gadon bonon Innar suka fito d'akin, Inna janye da ita har sai da ta Kai Dije gaban Iya Meron ta saketa, sannan ta d'auko bokitin karfen ta ajiye gabanta tace, "Ga ki gata nan Mero don ALLAH ki kasheta kar ki barta da ranta" Cikin borin kunya Mero ta d'aga hannu ta zabgawa Dije wani Uban mari har sai da ta hantsila, aiko dukawar da Dije zata yi bata taso ba sai da kafafuwan Iya Mero sai gata ko tim! A k'asa tana salati zane ya wancakale gefe, sai fad'in take yi "Ku ke ganinmu ba mu muke ganinKu ba...." DIJE sai harararta take tana wani ciccika tana kumbura saboda tsananin b'acin Rai. Yara kam da ke tsaye suna kallo sai ihu suke yi suna dariyar wallen da Iya Mero ta yi, aiko suka fara fad'in " Ku zo ku ga Dije ta yasar da Innar Bintalo k'asa" Bintalo tana ganin abunda Dije ta yiwa Innarta ta yo kan DIJE cikin zafin nama ta fara kai mata duka, Dije ta yi tsalle kamar wata zakanya ta sakarwa Bintalo duka a saman goshin, aiko Bintalon ta fasa wata arniyar k'ara ta durk'ushe tana ihu dafe da goshinta da ya sake fashewa da jini daga kanikancin da aka yi mata a shagon sai da maganin da ke kauyen, Iya Mero ta mik'e cike da jin kunyar abunda Dije ta yi mata gaban yara ta rik'o Bintalo da ke ihun wayyo goshinta tace "Zo muje wurin Maigari tunda ita Uwarta ta kasa ALLAH wadaran wata haifuwa, WALLAHI Allah ya'isa tsakaninmu da ku Hasiya, kin haifo muna jaraba kin kawo muna cikin gari ta zame muna karfen k'afa" Aiko ta ja Bintalon tana kuka tana ihu suka fita yaran suka bi su buuu! A baya suna dariya, Inna da ke kitchen tana ta sabgarta suna fita ya fito ta rufe Dije da duka ta ko'ina saboda haushinta da ya rufeta, sai ga Baffah ya shigo cikin tashin hankali saboda labari ya je masa irin aika aikar da Dije ta yiwa Bintalo, Yana kan hanyar zuwa gidansu Iya Meron ne aka ce dashi sunyi gidanshi takakka, shine ya nufo gidan da sauri don tsoron abunda zai je ya dawo don yasan halin Dije sarai ba za'a kwashe da ita ta dad'i ba. Sai ko gashi ya taradda INNA Hasiya tana dukanta, aiko dakyar ya kwaceta a hannunta saboda zuciyar INNA ta Kai wuya da halin Dijen shiyasa ta yi ta jibgarta kamar ba gobe. Dije Kam sai ihu take yi tana Kiran sunan Baffa tana fad'in "Wayyo ALLAH ta karyani ta karya man hannu Baffa" Baffah ya jata ya zaunar da ita akan tabarmar da Inna ta shinfida masa wadda ta zama ka'ida kullum sai an shimfidata saboda cin abincin dare. Ya Fara lallashinta yana bata baki da kyar ya ciyo kanta ta daina kukan sai dai kam bata daina sauke ajiyar zuciya ba tana ciccika, don kam ta jibgu iya jibga a hannun INNA. Har sai da aka kira sallahr Magrib sannan ya daina lallashin da yake yi mata, yace taje ta yi sallah kafin ya dawo ya siyo mata tsiren da take so mai shegen dad'i, Dije ta mik'e tana gunguni ta yi arwallah ko d'akin Innar kin shiga tayi anan waje ta shinfida tabarmarta ta yi sallahr tana kumbure kumburen fuska. Baffah ya dawo rik'e da bak'ar ledar ya zo har gabanta ya ajiye yace, "gashi kici ko tsoka bance ki baiwa kowa ba, kici ke kad'ai abunki gobe ma zan siyo maki wani in har naga kin saki fuskarki kin daina fushi" Dije ta karb'i ledar ta ajiye gabanta ciki ciki tayi godiya ta dunk'ule cikin kafafuwanta tana turo Baki, ko da ma aka gama abinci kin ci ta yi don daman wannan halinta ne duk lokacin da take fushi bata cin abinci sai kowa yayi kwana, in taji yunwa ta matsa mata sannan ne take fitowa a sace ta ci ta koma. To haka abun yake ko yau don kuwa ko Naman da Baffah ya siyo matan bata ci ba har sai da taga kowa yayi bacci, sannan ta canyeshi tas amman bata daina jin yunwa ba don rabonta da abinci tun safe kafin su je daji yin ciyawa, aiko ta fito Sadaf Sadaf ta nufi madafi, ta debo abincin tana ci tana tunanin abunda zata yi ta soshe dukan da Inna ta yi mata, aiko tana gama cin abincin ta sha ruwa ta yi gyatsa sanna fara d'auko tabarya ta bud'e turmin da ke kife ta fara daka iya k'arfinta tana lugude tana tana kad'a turmin tana waka sama sama. Aiko cikin Bacci INNA ta jiyo sautin daka tsakar dare ta waiga taga Baffa kwananshi kawai yake har da minshari, ta yi saurin dunkulewa cikin tsoro sai dai ta kasa kunne tana jiyo sautin kad'a turmin da wakar da ake yi sama sama, kafin kace me INNA ta fara jib'i don ko numfashi dakyar take bari ya fito don tsoro, sai cen ta ji an koma dukan langa langar da aka yi rufin madafinsu da shi, sai waka ake yi inda cikin wakar taji muryar Dije tana fad'in " Gamu yau munzo a gidan nan!, zamu tsolale idon matar gidan nan!, don nasan tana saurarenmu a gidan nan!, gamu nan gamu nan zuwa wajenki ki fito Nan! ko mu zo da kanmu a nan wurin nan!, murkutus barakus matso nan! d'an jugumuna matso nan!, ku matso ku matso ku kamota a cen din!, don mu had'u mu tsigale idon nan!" INNA ta zabura da k'arfi sai gata k'asa ta fad'o tim!, Har ta fasa k'ara ta yi saurin toshe bakinta, saboda har izuwa lokacin ba'a daina wakar ba sai ma maimaitawa da ake yi, INNA cikin rawar jiki da kyarmar tsoro ta fara bubbuga filon Baffah, har ta yi nasarar tashinshi cikin rufe baki alamun tsoro tana zaro Ido tana yi masa nuni da k'ofar d'aki, Baffah cikin firgici yace "lafiya? Me aka yi ne na ganki haka" Inna ta yi mashi alamu da ya sassafta murya cikin tsananin tsoro bakinta yana rawa tace,. "Saurara ka ji" Aiko Baffah ya taso ya tsaya jikin k'ofar ya kasa kunne yana sauraren wakar da Dije take yi, cikin fad'uwar gaba yace "Innahu min Sulaimanu......" Ya dawo cikin tsoro ya fara tofe Inna da addu'a shima ya tofe kanshi sannan ya nufi k'ofar da nufin ya bud'e, INNA ta zaro Ido tace "Don girman Allah Kar ka bud'e" Baffah ya juyo cikin rada yace,. "Ke a ganinKi don mun rufe d'aki bazasu iya zuwa su cire maki idon ba? To kinyi kuskure don haka Ni fita zanyi in basu hakuri in kuma Ni sun cire nawa idon a madadinki shikenan, sai da nace maki kar ki matsawa yarinyar nan ai gashi kin janyo muna jangwam!" Ya nufi k'ofar cikin fushi ya fara kiciniyar bud'e d'akin aiko sai jin Suka yi garam! A guje dukansu suka nufi karkashin gado kowa yana turin Dan uwanshi domin ya samu ma b'oya. Dije Kam jin muryarsu da ta yi ne ta shige d'akin Innar ta rufo k'ofar da sauri har sautin yace garam! d'in, don tsabar sauri ko sakatar bata saka ba ta dunkule gado tana minsharin k'arya, don nufinta ko da sun zo su taradda ita tana bacci don su gasgata abun da gaske ne ba shirinta ba. Akafta🤣 D/AUTA CE✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *BAK'ON YANAYI BOOK NE MAI ZAFI HAR KUNA YAKE YI A HANNU SABODA TSABAR TSANANIN ZAK'INSHI BOOK D'IN BAK'ON YANAYI SALONSHI DABAN NE DA KOWANE BOOK DA KA TAB'A KARANTAWA A DUNIYAR LITTAFAI, ZAKU SAMESHI A ARHA DA FARASHIN NERA D'ARI UKU KACAL KUMA ZAKU SAMESHI A COMPLETE DINSHI CIKAKKE MAI B'UKATA TA NEMENI TA WANNAN NUMBER 09032685442 SAYEN NA GARI MAYAR DA KUD'I GIDA SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI👍🏻 DOMIN KUWA BAK'ON YANAYI DAUKE YAKE DA NASHI KALAR SALO KALA KALA KUMA MABANBANTA MASU BURGE MAI KARATU DA SAKASHI SHIGA CIKIN SHAUKI YAYIN KARANTAWA💃🏻* *Lamba ta 6* Aiko mai makon taji shigowar su Inna sai taji saukar duka a jikinta, da sauri ta zabura ta fara sosa inda dukan ya sauka tana muzurai saboda ganin Yaya Usman a tsaye da bulalarshi a hannu, cikin fushi ya fara magana yana cewa "Don Ubanki buge bugen Uban mi kike yi muna cikin dare?" Dije ta zaro Ido waje tace,. "Buge buge kuma? Yaushe?" Ya d'aga bulalar ya sake kai mata wani dukan aiko ta fasa Kara, Inna da baffa da tunda Suka jiyo sautin tafiyar Usman suka sha jinin jikinsu suna addu'a k'asa k'asa tamkar wasu sababbin larabawa, ihun Dije yasa Suka kalli Juna ba shiri Inna ta dafe k'irji tace "Wayyo Ni Uwata wayyo Ubana Dije ALLAH ya kawo maki d'auki" Baffah ya yi saurin kallonta yace,. " Mi kike nufi? Ai dole muje mu dubo mu ga meke faruwa" INNA ta zaro Ido tace "Wa? Ni! WALLAHI ka je dai nikam ba inda zanje kana jin tana zuba irin wannan ihun haka kawai ace tarko ne suka had'a man inje su tsigale man idanuwa su barni da kwarmin ido wayam ba komi" Baffah ya maka mata wata jar harara ya fara gungurowa yana fitowa karkashin gadon, musamman kuwwar da yaji Dije tana zubawa yasashi k'ara kid'imewa ya nufi k'ofar d'akin a sukwane zai bud'e, daga cen karkashin gadon Inna tace "Ka rufeni ta baya da kwad'o Don Allah kar ka barni a bud'e" Baffah yayi saurin bud'e d'akin yana tofa addu'a a gaggauce saboda ihun Dijen da yak'i k'arewa, Aiko yana fitowa ya fara jiyo sautin Dije tana magiya har ya Kai bakin k'ofar ya dawo da sauri saboda sautin saukar dukan da yaji ana yiwa Dije, sai murzar hannu yake yi yana muzurai yana sake tofa wata addu'ar, sannan yayi kundunbalar fad'awa d'akin aguje kamar an jefoshi sai gashi karaf ya hango Usman da bulalar dokinshi yanata laftar Dije, cikin tsananin b'acin Rai ya d'auke Usman da wani bahagon mari sannan ya fisge bulalar cikin fushi ya fara fad'in "Wane rashin Imani ne ya sakaka dukanta cikin wannan talatainin dare? Me ta yi maka da bazaka bari har safiya ta waye ba ka horatan?" Usman cikin k'unar zuciya yace,. "Yanzu Baffah duk wannan iya shegen da take yi a cikin gidannan baka ji ba?" Baffah ya yi saurin fad'in,. " Don naji sai Kuma aka ce maka itace mai yin abun? WALLAHI Usman ahir dinka ka kiyayi janyowa kanka abunda zai hanaka bacci mai dad'i" Usman ya nufi hanyar fita yana fad'in,. "Duk buge bugen iskancin da tayi ta hana mutane bacci baka gani ba sai ma Ni laifina aka gani" Cikin d'aga murya Baffah yace,. "Tunda ifrituwa ce ai dole ta fito cikin dare tana Wasa, WALLAHI in banda muke dare da yanzu sai na rama mata dukan da ka yi mata na d'aukar alhaki" Ya dubi Dije cikin d'aure fuska yace,. "Me ya kaiki fitowa cikin daren nan kina buge buge?" Dije ta fara matsar kwallah tace,. "Ba fa inda naje ina tsaka da baccina mai dad'i na ji saukar duka" Baffah ya janyo hannunta ya zaunar da ita akan Gadon Innar yace,. "Kwanta kiyi baccinki ki barni dashi da safe zamu gauraya" Dije ta share hawayenta da gefen dankwalinta ta lallaba ta kwanta, sai ajiyar zuciyar take yi cikin tausayinta Baffah yace "Barni da shi da safe sai ya yi man bayanin dalilin da yasashi dukanki cikin dare, amman ke tsakaninki da ALLAH Dije ba ke bace? har da muryarki fa na jiyo kina rangad'a waka mai dad'i" Dije ta Sha jinin jikinta tace,. "Nima na jiyo ana wakar Baffah amman wata murya daban ce na jiyo Ni, sai dai ban gano me ake cewa cikin wakar ba" Baffah ya kalli k'ofar d'akin ya hadiyi miyon tsoron da ya sake diro masa yace,. "To dai yanzu ki yi addu'a ki koma kiyi baccinki kinji?" Dije ta d'aga masa Kai ya fara tofeta da addu'o'i sannan ya zo zai fita ya juyo yace,. "Tashi ki rufe d'akin kada ya zo ya sake dukanki a banza" Dije ta tashi zauna tana sharar kwallah tace,. "WALLAHI Baffah tsoro nike ji in kwana ni kad'ai sai inji anata kiran sunana wai in zo mu tafi bakin teku muyi wasa" Baffah ya dawo da sauri jikinshi ya d'auki rawa yace,. "Ku tafi Ina?" Ta turo baki tace,. "Wai bakin teku" Baffah ya fara fad'in, "K'alu Innalilahi wa'Inna ilairraji'una teku? Lalle akwai gurmi a gaba muddin ba'a daina jangwalo fushin dan Sarkin ba, jirani bari in zo yanzun nan" Ya fice da sauri har yana tuntube ya nufi dakinshi Inna da ta ji fad'an Baffan da muryar Usman ta lallaba ta fito karkashin gadon, tana so ta fita tana jin tsoro sai ko gashi Baffahn ya shigo d'akin ranshi a b'ace yace,. "To tashi kije cen ki kwanta tun kafin safiya ta waye ki shafa kiga an d'auketa an tafi da ita, tunda ke Kika janyo komi to ki san hanyar da zaki gyara" INNA ta zaro Ido tace,. "A d'auketa kamar ya?" Kai tsaye Baffah yace,. "Kamar yanda kika saki kwanji kika lakad'a mata duka, haka su ma za suyi wuf da ita sama su je wasa da ita bakin teku, watak'ila ma shikenan ba zaki sake ganinta ba kinga sai ki sake haifo wata tunda ita kin janyo munyi asararta" INNA ta mike jikinta yana rawa tace,. "Muje ka rakani in ganota Don Allah" Baffah yayi kwanciyarshi yace,. "Ni da na je ke kika rakani ki je cen ku kwana da ita sai da safe ALLAH ya tashemu lafiya" INNA ta dad'e tana kallonshi gano da gaske yake yi yasa ta ja kafafuwanta ta fice, tafe take tana addu'a har ta isa d'akin, sai dai ganin Dije da tayi a zaune tana sharar hawaye yasa ta k'arasa wurinta da sauri tace,. "Ke lafiya kike kuka?" Dije wasu hawaye Suka zubo mata tace, "ba Yaya Usman ba ne ya zo yayi ta dukana bayan ban yi mashi komi ba" Inna ta yi saurin zaunawa tace, "au! Shine yake dukanki kike ihu?" Dije ta saka bayan hannu ta share hawayen da suke sauko mata tace, "Shine" Inna ta yi saurin fad'in "to me kika yi masa cikin daren nan?" Dije ta zumburo Baki tace,. "Wai cewa yayi na fita inata buge buge bayan Ni tuwo kawai naci na dawo d'aki ina cikin Bacci naji yana dukana" INNA ta zaro mata Ido tace "Kin dai fitan ko?" Dije ta gyad'a Kai, Inna ta maka mata wata jar harara tace,. "Aiko naji dad'in da ya jibgeki don dama ace bai dake kin ba to da Ni yanzu sai na yi maki nawa dukan, don ina da tabbacin kece kike ta daka kina dukan rufin madafinmu kina waka" Dije ta yi saurin ja da baya tace,. "Nasha aradu ba Ni bace nima Ina Bacci naji ana ta yi" INNA ta saka hannu ta dungure mata Kai tace,. "Zaki yi man shiru ko sai na kasheki da mari yanzu?, Ai WALLAHI ba wasu aljanu kece kuma na sake jin kin sake kwata irin wannan rashin mutuncin cikin dare WALLAHI sai jikinki ya gaya maki, ki godewa ALLAH da har aljanun gasken basu kawo maki farmaki ba, don muddin Baki daina kokwayonsu ba WALLAHI wani ya shige jikinki kin boni don ko sai dai ki wayi safiya watarana aga kin mutu, saboda ganinsu za ki yi a gabanki sun fito da siffarsu, kuma kinji ana cewa duk wanda yaga aljanu Ido da Ido da siffarshi ta gaskiya to mutuwa zai yi, amman in har ke kin shirya zuwa Lahira yanzu to kici gaba da koyonsu in kin aza wasa ake" Dije jikinta ya d'auki rawar tsoro ta makure gefe ta dunkule waje d'aya tana addua, Inna ta maka mata wata hararar ta rab'a gefenta ta yi kwanciyarta hankalinta a kwance don ta gano cewa duk iya shegen Dije ne ba wasu aljanu. Akafta🤾🏻‍♂️ D/AUTA CE✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *BAK'ON YANAYI BOOK NE MAI ZAFI HAR KUNA YAKE YI A HANNU SABODA TSABAR TSANANIN ZAK'INSHI BOOK D'IN BAK'ON YANAYI SALONSHI DABAN NE DA KOWANE BOOK DA KA TAB'A KARANTAWA A DUNIYAR LITTAFAI, ZAKU SAMESHI A ARHA DA FARASHIN NERA D'ARI UKU KACAL KUMA ZAKU SAMESHI A COMPLETE DINSHI CIKAKKE MAI B'UKATA TA NEMENI TA WANNAN NUMBER 09032685442 SAYEN NA GARI MAYAR DA KUD'I GIDA SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI👍🏻 DOMIN KUWA BAK'ON YANAYI DAUKE YAKE DA NASHI KALAR SALO KALA KALA KUMA MABANBANTA MASU BURGE MAI KARATU DA SAKASHI SHIGA CIKIN SHAUKI YAYIN KARANTAWA💃🏻* *Lamba ta 7* Aiko Dije har safe ko motsin kirki bata sake yi ba saboda ta tsorata da jan kunnen da Inna ta yi mata, don hasali ma har mafalki ta yi wai gasunan sun bayyana da siffarsu sun zo wurinta zasu kasheta, cikin firgici ta falka a zabure tana fad'in "Don ALLAH kuyi hakuri bazan sake ba na tuba nabi ALLAH da manzonshi, amman in har kunga na sake to ku d'auki mataki" Inna da ke shigowa d'akin ta d'auro arwallar sallahr Asuba da nufin ta tada ita sai gashi ta taradda ita zaune tsakiyar gado tana sambatu, Inna ta kalleta da kyau tace "Lafiyarki tun da safe kike yiwa mutane soki burutsun zance?" Dije ta waiga gefe da gefenta sannan ta fara saukowa gadon tace,. 'ba komi" INNA ta bita da kallo har ta fice d'akin ta girgiza kai sannan ta shimfida wata sabuwar tabarmar kaba da suke sallah akai ta tada sallahrta. Dije kam har ta k'are arwallar ta dawo d'akin tunanin mafalkin take yi, jikinta a sanyaye ta yi sallah ta gayar da Inna sannan ta fara bitar karatunta na allo, Inna cikin jin dad'in ganin sauyin Dije ta bita da addu'ar ALLAH yasa abun ya dore a haka, don dai ita jikinta yana bata ko dai da gaske Dijen akwai wasu k'wank'wammai akanta masu sakata jidali da yawan fad'ace fad'ace kullum?, Ta fice zuciyarta cike da jin dad'i ta yi madafi domin ta d'ind'ima masu tuwon da zasu karyawa dashi. Dije Kam tana k'are bitar karatunta ta jingine allonta ta nufi d'akin Baffah domin ta yi mashi Ina kwana, aiko sai gashi sunyi kicib'is da Usman ta ja baya ya shige d'akin sannan ta bi bayanshi da harara ta shige d'akin itama, Baffah yana kishingide da carbi a hannunshi yana ja yana gyangyadi, jin sallamar Usman yasa ya yi saurin tashi zaune yana amsa masa sallamar fuska a d'aure, ganin Dije a bayanshi yasa ya saki fuskarshi da fara'a tana shirin zama nesa dashi yayi saurin fad'in,. "Matso nan kusa da ni Dijengalata ya jikin naki?" Dije ta zunburo Baki tace,. "Naji sauk'i sai dai dukan da Yaya Usman yayi mani ashe duk ya farfasa man jikina kallo ka gani Baffah" Ta k'are maganar tare da zubowar wasu kwallah tana nuna masa tsintsiyar hannunta inda shatin bulalar ya fito rad'am. Baffah ranshi ya K'ara b'aci cikin d'aure fuska yace da Usman da ke k'ok'arin gayar dashi yace,. "Ajiye gaisuwarka bana so tunda har baka ji kunyar saka bulala ka yiwa Dije irin wannan dukan ba, don tsabar rashin imani Innarku ta daketa da dare ace wai kaima ka bita tsakar dare da dukan kawo wuk'a, to bari kaji muddin ka sake yi mata irin wannan dukan WALLAHI sai na sab'a maka, don nafi son Ni in illataka da hannuna da dai ace Yariman Aljanu ya kawo maka farmaki, don ko Hasiya ALLAH ne ya tsareta da yau bata tashi da idanuwanta ba, duk kuma akan dukan da tayiwa Dijen, Kai ma ka kiyayi kanka da tsokano fushin d'an Gidan mai martaba" Usman yayi saurin toshe dariyarshi yace,. "WALLAHI Baffah k'arya take yi ba wasu aljanu don da idona na ganta jiya tana rera waka tana dukan rufin madafinmu" Baffah ya galla masa wata jar harara yace,. "To ka godewa ALLAH da har siffarta ka gani a jiki ba siffarsu ba, to bari kaji Kai kanka zasu iya yin siffarka suje inda suke so bale ta Dijen" Usman ya yunkura zai tashi yace,. "Ni zan tafi gona Baffah kafin ka shigo" Saboda ganin da yayi idan ya tsaya musu ne zasu ci gaba da yi da shi don gano da Baffah Kam yayi amanna da karyar aljanun Dije. Baffah ya ce "ba zaka bari ka ci tuwo ba?" Usman zai yi magana Inna ta shigo da kwanon abincin Baffah ta ajiye, ta kalli Dije dake rakub'e kusa da Baffah'n tace,. "Tashi ki d'auki abincin yayanki ki kai masa dakinshi, kema ki d'auki naki kici ki tafi Makaranta" Dije ta yunkura ta tashi ranta a bace tana fitowa ta bi hanyar d'akin Usman da kallo ta yi kwafa, saboda d'akin ya nufa ya shige abunshi ko waigota bai yi ba, ta nufi madafin ta bud'a kwanon abincinshi da kullum dashi ake zuba masa abinci ciki, ta bud'a langar ta damko gishiri cike da hannunta ta nutse dashi cikin miyar, ta maida murfin ta rufe ta d'auko tana tafe tana had'e fuska har ta kai dakinshi ta yi sallama ciki ciki ta ajiye kwanon bakin k'ofar shiga d'akin zata wuce, ya yi saurin fad'in "Ki kawoshi nan a gabana ki ajiye" Ta fisgi kwanon ta je gabanshi ta ajiye tana wani cin magani har ta zo fita yace,. "Ki kawo man ruwan sha to" Dije ta fice ko waigoshi bata yi ba sai ko gata da ruwa cike da kofi kamar arzik'i ta ajiye cikin ladabi sannan ta fita da sauri jikinta yana rawa ta nufi wurin Baffah da ke cin tuwonshi har lokacin, ta wani marairecewa tace "Don Allah Baffah ka rantsewa Yaya Usman akan kada ya sake dukana, don yanzu haka hararata kawai yake yi nasan k'iris yake jira ya kamani yayi ta jibga kamar jaka" "Baffah yace kyaleshi je kici abincinki ki tafi Makaranta kar kiyi latti yaran da kike karantarwa su yi ta jira" Dije tuno irin cin zalin d'in da take yiwa yaran makatantar yasa ta kyalkyale da dariya tace,. "Bari in d'auko tuwon nan inci Baffah a gabanka" Ta nufi madafin da saurinta don tsoron Usman ya cafketa aiko fitowarta ke da wuya taji ya shako wuyanta, Aiko ta fasa k'ara tare da kiran sunan Baffah akan ya kawo mata agaji, sai ko gashi ya fito Usman yana d'aga hannu da nufin ya saukeshi a fuskarta Baffah ya rik'e hannunshi cikin fushi Yace "Wai kai shikenan ita bazaka barta ta sakata ta wala ba cikin gidan nan? To WALLAHI wannan karon ko kallon banza naga ka sake yi mata sai na rama mata" Ya fisge hannun Dije daga rikon da Usman yayi mata suka shige dakinshi, Usman ranshi a b'ace ya kalli Inna yace "Gishiri fa ta saka man a tuwon da kikace ta kai mani, ruwa ma da nace ta debo man duk sai da ta zuba gishirin ciki ina kurbawa ba shiri na furzar saboda bala'in zartsinsu, amman Kinga Baffah laifina ya gani to WALLAHI idan ta cikani sai na karyata cikin Gidan nan" Baffah ya lek'o kanshi Usman yana gaf da fita yace, "Wanda ya fasa karyata ban gode masa ba, Kai ko ka zuba ido ka ga irin kalar hukuncin da zan dauka kanka" INNA dai ranta a b'ace tace ,. "Haba Malam ka dubi abun nan fa da idon basira, gishiri fa ta zabga masa a abinci da ruwan sha ina ko Dije taga gaskiya anan?" Baffah ya yi mata wani kallo yace,. "Anji bata da gaskiyar ku had'u ke da shi ku kasheta" INNA tace,. "ALLAH ya baka hak'uri ni dai fadar gaskiya ce tawa" Baffah cikin d'aga murya yace,. "To ba'a so ki rik'e gaskiyarki ku bar Yarinya ta sarara" Dije dai sai guma lomomin tuwonta take yi tana kammalawa ta wanke hannunta ta ja allonta ta fice, tana tafe tana wakarta har ta kusa kaiwa Makarantar ta hango Hansai da itama tun daga nesa da ta hangota tafe ta k'ara d'aga kafafuwanta da sauri don bata son Dije ta cimmata, aiko Dijen tana hangota ta kwalla mata kira ganin taki tsayawa yasa ta d'aga murya tace,. "WALLAHI in baki tsaya ba na kamaki sai na canza maki kamannu" Hansai ta tsaya jikinta yana rawa tace,. "Aikena aka yi akace in yi sauri in dawo" Dije ta k'araso hannunta rik'e da k'ugu tana yiwa Hansai wani kallo tace, "Aikenki aka yi Kuma na ganki da Allo?" Hansai ta Kai kallonta ga allon cikin rawar Baki tace,. "Allon zan ajiye sai in tafi aiken" Dije ta dungure mata Kai tace,. "Ke dai kinji haushi WALLAHI bak'ar makaryaciya, na ganoki ai don kinsan kin tonani ne shiyasa kike tsoron mu had'u, amman kinsan kina tsorona Ubanwa yace kije ki sanarwa Maigari Wai k'arya nake yi ba wata Kura?" Hansai ta zaro Ido tace,. "Ni d'in WALLAHI Ni k'arya ake yi man bani na fad'a ba" Dije ta ajiye allonta ta rik'e k'ugu tace,. "To wa ya fad'a??" Hansai hawayen da take makalewa suka zubo tace,. "WALLAHI in har nice na fad'a ALLAH kada ya dagar dani anan wurin" Dije ganin hawaye ga fuskar Hansai yasa ta d'auki allonta ta lakamo kafad'ar Hansai din tace,. "To Zo muje na yafe maki amman don ALLAH ke baki san wacce ta fad'a ba cikinmu?" Hansai ta share hawayenta cikin jin dad'in yafe matan da Dije tayi tace,. "WALLAHI bansani ba nikam Dije" Dije tace,. "To yi shiru shikenan zaki zo Wasa Gidanmu ai anjima ko?" Tace,. "Eh in Innata ta barni" Dije tace,. "Zata ma barki ki zo nayi maki d'iyar kare mai shegen kyau" Tace,. "To" Sannan suka rankaya har cikin Makarantar inda Suka taradda ta cika fam! Sai karatu ake tayi, Dije taje ta bita karatunta ga Babban malaminsu, sannan ta d'auki bulalarta ta fara koyawa yara karatu, aiko suna ganinta kowa yasha jinin jikinshi sai d'aga murya suke yi suna ta karatu da k'arfin gaske, saboda sun san irin bala'in kashin da take basu wanda abu kad'an ne zai janyo yasa ta ci uban yaro, musamman wad'anda basu gane karatun su Kam ba k'aramar azaba take basu ba. Don wani zubin ma Kan yaro take hayewa ta taushe masa kai tana muntsilarshi, wani zubin ma har cizo take had'awa mutum da shi in ta kama, don Iyayen yara da yawa sun Sha kawo kararta wurin Malamin musamman idan sunga shatin bulalar ko na muntsilar ko cizon da take yiwa 'ya'yansu, Malamin yana toshe kunnuwanshi ne kawai saboda bala'in k'ok'arin da take da shi gashi kuma yaran suna gane karatunta kuma tana natsar da Makaranta su daina rashin ji in tana wurin, sai dai yayi mata fad'a cikin hikima baya ma nuna mata wai k'ararta aka kawo don tsoron kada ta yi abunda zai fi wanda ta aikata . Saboda ko baffanta ba'a kwana biyu ba'a Kai masa k'ararta ba akan ta daki wani ko taci zalin wani, iyakaci dai ya bada hak'uri idan ya shiga yayi ta nusar da ita akan ta rage tsaurara horon da take yiwa yaran. Aiko bayan an tashi Makarantar ne suna tafe su biyar dinsu kamar kullum,har sai da suka kai wani lungu sannan Dije tace "Yawwa daman Ina son in gano a cikinku wacece taje ta fad'i cewa Wai k'arya ce nake yi ba wata Kura??" Kowa ya fara rantse rantsen ba shi bane Dije ta kalli Mune da kyau tace,. "Ke nasan duk cikinmu kinfi kowa bak'in surutun tsiya da fad'i ba'a tambayeki ba, don haka kece kika fad'a ai na ganoki yarinya" Mune ta zaro Ido waje tana muzurai tace,. "WALLAHI Nima banso fad'a ba ai Babanmu naga garin gudu yaji ciyo a k'afa shine fa na fad'a masu gaskiya don su kwantar da hankalinsu" Dije ta yi wani tsalle ta ciyo kwalar Mune tace,. "Yau ko za'a yi watandarki a bakin tekun zurmukus banbaradusa, ai daman nasan kece kika fad'a to kisani sai na yi kuli kulin rakkiya dake a garin nan yau" Dije ta mik'awa Hansai allonta ta saki Mune tasha d'amara da gyalenta Mune tana ganin haka ta ce k'afa mi naci ban baki ba, aiko ta zunduma da gudunta Dije ta bita itama sauran kawayen nasu da wasu Yan kallo suka bisu a baya, sai ko gashi Mune taci karo da yayanta tayi saurin yin bayanshi ta b'oye, Dije tana kawowa ta yi tsalle ta dako Mune ta bayanshi, cikin fushi ya rik'e hannun Dijen yace "Me tayi maki da zaki daketa?" Dije ta fisge hannunta ta murgud'a masa baki tace,. "Ai Kaima kasan idan bata yi man komi ba haka kawai bazan biyota ba" Yayan Mune ya kalleta cikin fushi yace,. "Waike me yasa kullum baki rabuwa da fad'a da anjaki da ba'a jaki ba ke duk sai kinyi?" Dije ta hade fuska tana wani girgizar jiki tace,. "Ni dai ka matsa babu ruwanka kada Kuma in zo in yi maka wani abu aga laifina" Yayan Munen ya rik'e Baki yace,. "Au ko Nima fasa man Kan zaki yi kamar yanda kika fasawa Bintalo goshi, don Kinga Maigari yace ayi maki hakuri a kyaleki shine kike ganin kamar tsoronki ake yi ko??, To bari kiji ni WALLAHI idan kika yarda kika shiga sabgata sai na lakad'a maki shegen duka a garin nan Inga mai d'aure maki gindi" Dije ta ja baya da k'arfi ta ce. "He! he! he! daman shi abun dai ai shi abun fad'i yin kanshi yake yi don kuwa kanku aka farashi, ko ka manta duk garin nan kowa yasan cewa Iya Zulai barauniya c......." Kafin ta k'arasa yayan Mune mai suna Tanbari ya Kai mata wani mahaukacin mari, Dije tace la.la.la. Ni ka mara?" Cikin tsananin fushi yace,. "An mareki ke d'iyar Gidan Uban w.........." Kafin ya k'arasa Dije ta duka cikin zafin nama ta debo k'asa ta watsa masa a cikin idanuwa, aiko tambari ya yi saurin kai mata wani uban naushi ta kauce da sauri. Idonshi cike taf da k'asa ya fara Kaiwa iska naushi iya k'arfinshi yana fad'in, "Yau sai na kassaraki na kamaki sai na kakkaryaki a garin nan" Dije ma bakinta bai yi shiru ba sai ramawa take yi, Aiko yana fad'a Yana kaiwa iska naushi ta inda yake jiyo muryarta, har ya Kai wurin wani icce ya bugoshi da k'arfi sai gashi da fasa k'ara don kuwa kanshi yaci karo da iccen ya bugu da k'arfi ga hannunshi da ya naushi iccen, zafi biyu da biyu ya durk'ushe a k'asa yana murkususun wayyo hannunshi. Akafta🤾🏻‍♂️🏃🏻‍♀️ D/AUTA CE✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *MUTANEN DIJE K'ARANGIYA INA GAIDA KOWA ALL ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU👍🏻* *Lamba ta 8* Mune ganin yayanta yana kuwwa yasa ta sake zundumawa da gudu ta yi gida da nufin taje ta fadowa Innarsu, Dije kam karbar Allonta ta yi ta kalli su Hansai tace "Ku muje in kuma anan zaku tsaya sai in tafiyata" Yayan Mune sai tsine mata yake yi Dije ta waigo tace,. "Ni bani da lokacinka tunda ALLAH ya saka man akanka, saura kuma idan ka tashi fad'i kace nice na ji maka ciyon a hannu" Yanata surfa mata zagi tana masa dariya taja kawayenta suka tafi suka barshi anan, kowa idan aka kai gidansu ya shige masu ratsewa su yi hanyar da zata sadasu gidajensu kuma su ratse su tafi, suka bar Dije ita kad'ai tana tafe tana Yar wakarta zuciyarta cike da jin dad'in abunda ta yiwa Tambari, aiko sai gashi ta had'u da Bala wanda tun daga nesa da ya hangota fuskarshi a washe ya k'araso idonshi akanta yace,. "A'ah su Dije Makaranta aka fito ne??" Ta Kai kallonta gareshi ta bata fuska tace,. "Eh cen na fito" Tana maganar tana ci gaba da tafiya abunta, Bala ya biyota a baya yace,. "Dije ki tsaya akwai maganar da nike son muyi Ni da ke" Dije ta waigo ta rik'e kugunta tana yi masa wani kallon reni tace,. "Magana kuma? Bayan wadda muke yi da Kai yanzu?" Ya gyara tsayuwarshi yana fesheta da wani arnen murmushi yace,. "Wannan ta musamman ce ai don WALLAHI na dad'e da abun cikin Raina sai dai tsoro yasa na yi ta b'oye abuta a cikin zuciyata" Dije tana yi masa kallon Ido cikin Ido tace,. "Toh kace abun babba ne Bala? ALLAH yasa dai ba cewa za'a yi nayi wani abun ba kuma?" Bala ya yi saurin fad'in,. "Ba kiyi komi ba na aibi Dije illah ni da kika sakani shiga damuwa da zullumi kullum safiya" Dije cikin k'ulle kai da rashin gano inda zantukan Bala Suka nufa tace,. "To ai sai ka fad'a Kai tsaye basai ka tsaya zagaye zagaye ba" Bala ya kafeta da kallo cikin tsananin kaunarta da ta cika masa zuciya yace,. "WALLAHI Dije sonki dai Nikeyi tun da dad'ewa, ammman na kasa furta maki ina jin tsoro" Dije ta yi saurin dafe k'irji tace,. "Yanzu Kai Bala duk mutuncin da nake ganinka dashi ashe daman cen dan iska ne Kai ban sani ba??" Balan ya zaro Ido waje yace,. "Iskanci kamar yaya Dije don nace Ina sonki shine nayi iskancin??" Dije ta maka masa wata jar harara tace,. "Yo in ba iskanci ba me ya kawo zancen kana Sona? Ko ka d'auka Ni Yar iska ce kamar kai to WALLAHI wurin Duduwa zan kaika in sanar da ita don ta ja maka kunne tun kafin ka janyo Baffahna ya kasheni a garin nan" Aiko ta juya ta nufi gidansu Bala, Bala ya bita yana magiya akan kar ta Fado ta rufa masa asiri ba zai sake yi mata maganar ba, amman Dije ta Kai wuya shiyasa bata fasa nufar gidan ba cikin fushi kamar wata zakanya, aiko tana shiga ta fara kwallawa Duduwa kira waton Kakar Bala ta wajen Uba da bayan rasuwar Mahaifiyarshi ya dawo hannunta. Sai ko ga Duduwa ta fito d'aki tana gyara daurin zanenta tace, "lafiya kike kirana? injin dai ba bashinki naci ba?" Dije ta k'araso ta kantare k'ugu tana wani cije Baki tana murgudashi tace,. "Aiko dole ki ganni tunda har Bala yake so ya maidani Yar iska kamarshi" Tsohuwa Duduwa ta zaro Ido waje tace, "ke dakata Dije ki fita idona in rufe kada ki kuskura ki yiwa Balana sharri" Dije ta yi mata wani kallo ta waiga bayanta inda Balan yake shigowa Gidan tace,. "Ai gashinan ki tambayeshi in har zai fadi tsakaninshi da ALLAH me ya fad'a mani yanzu?" Bala ya k'araso yana dariya yace,. "WALLAHI Duduwa ba fa wani Abu nace da ita mai girma ba, cewa kawai fa nayi da ita Ina sonta shine fa ta ce sai ta kawoni k'ara wurinki" Duduwa ta kalli Dije ta yi wani mere tace,. "Ke daga ma kin samu yace yana sonki shine zaki biyoshi Gida da kullin sharrinki? To don yace yana sonki miye abun iskanci a ciki?" Dije ta galla mata harara tace,. "Au yanzu na gano Ashe da had'in bakinki yake so ya lalatani, to WALLAHI sai dai yaje ya bidi Yar iska dai dai shi don ni ba Yar iska bace bale yace yana sona" Ta k'are maganar tare da murgud'awa Duduwa Baki, Duduwa ta zaro Ido tace "Yo in dai har haka kawai don yace da ke yana sonki shine iskancin to Innarki Hasiya da Baffanki sun dad'e da iskancewa" Dije ta dafe kirji Bakinta a bud'e ta ce,. "WALLAHI ALLAH ya sakawa su INNA don kinci da zalinsu Kuma akan mummunar fahimtar da kika yi masu idan Baki rokesu suka yafe maki ba da wuya in hakkinsu zai barki ki shiga aljanna" Duduwa ta ce,. "Ki je ki sanar dasu idan suna da abun Kare kansu su Kare kansu in gani in har su d'in ba Yan iskan bane kamar yanda kike tunani, to ma wai ke tayaya aka sameki in ba ta hanyar abunda kike kira iskanci ba?, To bari kiji hanyar da aka sameki itace Bala yake so yabi shima ya yi auren ya samo nashi rabon 'ya'yan, shima in banda rashin hankali irin nashi me zai yi dake masifaffiya bak'ar mafadaciya dake, shiyasa ma in bandashi kaf garin nan babu wanda na tab'a jin yace yana sonki to me za'a tsinta jikinki in banda jidali" Dije ta zumburo Baki tace,. "WALLAHI kinci sa'a Ina ganin kimarki a idona da tuni na shikka maki rashin mutunci akan wannan k'azafin da kika yi man Ni da su Baffah, to Ni ALLAH na tuba ma wani tsautsayi zai sa har in yarda wani yace yana sona? Ai duk Wanda kika ga yana soyayya WALLAHI mugun ma dan iska ne na fad'a na k'ara fad'a Duduwa Bala Dan iska ne tunda har baiji kunyar kallon tsabar idanuwana ba ya bud'a Bakinshi yace wai yana sona ba" Ta kalli Balan ta murgud'a Baki ta buga masa wata jar harara tace,. " kuma Bari kaji narantse da ALLAH duk kasa nayi ciki da kai zan kuka tunda kai baka da imani" Tana k'are maganar ta fashe da kuka saboda tuno labarin da Inna ta Bata akan cewa duk ta yarda wani ya tab'a hannunta ko kuma yace yana sonta ta amince ciki zai fito jikinta yayi katoto ta haifo macizai. Tana k'are maganar ta fita rangai rangai ta bare Baki iya k'arfinta tana ta kuka tana fad'in wayyo ita yau ta shiga uku tsautsayi ya hau kanta, kowa ya ganta tana kukan sai dai ya bita da kallo yana tunanin yau me yasa Dije kuka haka, saboda kowa yasan takadirancinta don abunda duk zai sakata irin wannan kukan ba abune kad'an ba, wasu ko dad'i kawai suke ji don tunaninsu ko wani ta samu wanda yafi k'arfinta ya darza mata shegen kashi. Dije kam ko gabanta bata gani saboda tashin hankalin da ta fad'a, don ita a ganinta tata ta k'are shikenan tunda bala yace yana sonta cikinta zai yi katoto ta haifo macizai. Aiko tun daga nesa Inna ta fara jiyo sautin kukanta cike da mamakin abunda ya saka Dije kuka yasa ta yi kasake tana jiran shigowarta, sai ko gata buguzum buguzum ta fad'o Gidan sai da ta yi tsalle ta fad'i k'asa tana ta kururuwar wayyo ita cikinta macizai sun fara taruwa, Inna ta bita da kallo cike da mamaki tace da ita, "Wai ke lafiyarki kike cikawa mutane kunnuwa da kuka haka?" Dije ta tsagaita da kukanta tace,. "Ba Balan Duduwa bane yace wai yana sona ba, Kinga fa har macizan sun fara taruwa cikin cikina suna cizar mani hanjina" Inna ta so ta yi dariya amman ta mazge tace,. "Ni dad'ina dake hauka to bari kiji idan dai kika yarda ya tab'a hannunki ne macizan zasu fara taruwa ko kin manta labarin da na baki?" Dije ta yi girgiza Kai, Inna tace "ya tab'a maki hannun ne?" Tayi saurin girgiza Kai tace, "A'a" Inna tace, "to kwantar da hankalinki ba abunda zai sameki ai tunda ke baki ce kina sonshi ba har hakan ya janyo ki bashi fuskar da zai tab'a maki hannu, amman da ace kin bari ya tab'a maki hannun kam to da yau macizan zasu fara taruwa a cikin naki, amman yanzu tunda har kin tabbata bai tab'aki ba to Alhmdllh tashi kije ki ajiye allonki ki zo kiji wani labarin" Dije ta share hawayenta hankalinta ya dan kwanta ta je ta ajiye allon ta dawo Inna ta shimfida masu tabarma ta ci gaba da bata labarai masu sakata tsantseni da halayen maza marasa mutunci masu lalata yara, Aiko daram darasin Inna ya shige kwanyarta don daman cen ita rayuwar maza ba damunta ta yi ba, don in banda Bala ma kaf garin ba Wanda ya tab'a taronta da wannan mummunar maganar. Suna cikin firar ne aka fara buga masu sallama a k'ofar Gida, Inna ta kalli Dije tace "Je ki gani wa yake sallama idan Baffanku ake nema ki sanar bai dawo ba" Dije ta tashi tana yar wakarta ta nufi k'ofar Gidan, aiko sai gashi taga wani yaron Maigari ta kalleshi da kyau ta yatsina fuska tace,. ,"Baya gida kaje ka sanar" Yaron ya kalleta kamar ya shaketa yace, "ai tunda ke kina nan muje Maigari yana nemanki daman dake da Baffan aka ce ku zo to tunda shi baya nan ke ki zo ki wakilceshi" Dije ta murgud'a masa Baki tace, ,"wani munafukin ne ya Kai karata kuma? Ni me ma nayi da za'a nemeni?" Yaron ya juya ya fara tafiya yace, "Wannan kuma sai ki baiwa kanki amsa Ni Kinga tafiyata sai kin k'araso" Dije ta bi bayanshi da harara aiko sai ga Kira Inna ta kwala mata, ta amsa da k'arfi ta koma cikin gidan tace "Inna Maigari ne ya aiko yace inje in karb'o dussata da ciyawar da yayi alk'awali zai dinga baiwa Akuyata" Inna ta yi mata wani kallo tace, "wace dusa bayan waccen wadda ya aiko maki?" Dije ta Sosa kai tace, "To ko dai ciyawarce yake nufi Dan sak'on ne bai ji sak'on dai dai ba? Bari inje in karb'o in dawo INNA kar yaga na dad'e" Ta fice da sauri Inna ta bita da kallo tace, "ALLAH ya shirya" Dije kam tana fita ta nufi gidansu Hansai da sauran kawayenta sannan suka rankaya Gidan Maigarin, don zuciyarta ta tabbatar mata cewa Tambari ne ya kaita k'ara wajen Maigarin. Aikuwa sai ko gashi tana zuwa ta ga Tambari da Mahaifinshi, sai dai kuma bakin fuskokin da ta gani da bakuwar motar da ke ajiye k'ofar Gidan Maigarin, wadda ko Babu tambaya zaa gano tasu ce duba da yanda ta hangosu yan gayu da wasu tufafi da suke sanye dasu iri d'aya da hula wadda a tashi d'aya za'a banbancesu da wayayyun yan boko, saboda kayan bautar K'asar da ke sanye a jikinsu dukansu su biyun da d'aya ya kasance fari yayin da d'ayan kuma yake baki-baki don ba za'a kirashi da wulik ba. Tofa ga wata sabuwar cakwakiya🤣 Akafta😅 D/Auta CE✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *BAK'ON YANAYI BOOK NE MAI ZAFI HAR KUNA YAKE YI A HANNU SABODA TSABAR TSANANIN ZAK'INSHI BOOK D'IN BAK'ON YANAYI SALONSHI DABAN NE DA KOWANE BOOK DA KA TAB'A KARANTAWA A DUNIYAR LITTAFAI, ZAKU SAMESHI A ARHA DA FARASHIN NERA D'ARI UKU KACAL KUMA ZAKU SAMESHI A COMPLETE DINSHI CIKAKKE MAI B'UKATA TA NEMENI TA WANNAN NUMBER 09032685442 SAYEN NA GARI MAYAR DA KUD'I GIDA SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI👍🏻 DOMIN KUWA BAK'ON YANAYI DAUKE YAKE DA NASHI KALAR SALO KALA KALA KUMA MABANBANTA MASU BURGE MAI KARATU DA SAKASHI SHIGA CIKIN SHAUKI YAYIN KARANTAWA💃🏻* *Lamba ta 9* Dije garin kallonsu har da su tuntub'e sannan ta sami gefe ta rakub'e kamar wata ta ALLAH tana yafito su Hansai da suka saki Baki suna kallon bak'in Yan bokon, Maigarin ya karb'i wata farar takarda daga hannun wannan farin mutumen, sannan ya bud'a takardar sai kace daman cen shi d'in wani jan wuya ne a bokon, gano ko harafi d'aya bai gano maanarshi ba yasa ya mik'awa Liman takardar, shima ya duba yaga bai san komi a ciki ba ya kalli Dije yayi wata dariya yace "Karb'i takardar nan karanta muna ita Yar gidan Baffahnta" Dije ta ji k'irjinta ya buga dam! da shiri cikin sanyin jiki ta karb'i takardar ta Kura mata Ido kurum!tana so ta gano abunda ke ciki, don ALLAH ya taimaka da harshen hausa aka yi rubutun sai dai kasancewar ba kullum ake zuwa Makaranta a garin ba yasa ba duka hausar ta sani ba, aiko kai tsaye wani tunani ya zo mata ta d'ago kanta ta kalli Yan bokon da suma ita suke kallo, sannan ta mayar da kanta tana k'ara tantance takardar ta mik'e cikin fara'a da wata jarumta ta kalli mai garin tace, "Sak'o ne aka aiko daga birni akan a had'a duk wasu matasa na garin nan za'a daukesu aikin Soja a turasu Maiduguri domin a kwantar da tarzoma" Maigarin da sauran masu ruwa da tsaki da ke garin har ma da su kansu bak'in suka zaro Ido, cikin firgici Tambari ya mike jikinshi yana rawa ya kalli Babanshi yace "Muje Baba kasan bana jin k'arfin jikina idanuwana ma ko gani basuyi sosai, watakila ma shikenan Ni da lafiyar Ido haihata haihata" Ba shiri dayan bakon wanda ba fari ba ya kumshe dariyarshi yayi saurin cewa,. "A'a ba haka bane mu an turo mu ne daga birnin akan zamu yiwa k'asa aiki mu zauna da ku anan Garin mu dinga koyawa yara karatu har na tsawon shekara d'aya, fatanmu kawai ku bamu had'in kai don ku sani tab'amu tamkar tab'a k'asa ne, don kuwa akanmu mutum zai iya k'are rayuwarshi gaba d'aya a prison in har ya kawowa hukuma ganganci" Maigarin da sauran mutanen da ke garin suka zaro Ido alamun tsoro, Maigarin kam sai gyad'a kanshi yake yi alamun gamsuwa da zancenshi, Dije kam tana jin haka ta fara hararar dan farin saboda ganin yanda yake ta wani cin magani yana binsu da kallon kyama, Maigarin da kowa aka yi ta yi masu sannu da zuwa da fatar nasara akan aikinsu da suka baro gidajensu suka zo kauyen da nufin su tallafa masu. Daga nan Maigarin yasa aka je aka gyara masu masaukin da zasu zauna sannan aka yi masu iso suka fito da jakunkunansu da suka zo da su aka shigar masu da su. Dije ta bi dan farin da wata jar harara aranta tace,. _"jishi don ALLAH sai kace baya tsugunnin Kashi, mu za'a nunawa fari?? farin banza da wani janbaki da ya gogawa lebenshi don kitifirin bala'i"_ Shi dai Kam bai ma san tana yi ba don hasali ma shi kwata kwata hankalinshi baya wurinsu yana cen tunanin ta yaya zai iya zama kauyen har ma yayi rayuwa a cikinta?. Bayan sun shige ne Maigarin ya dawo da hankalinshi garesu ya Kai kallonshi ga Dijen yace,. "Wai ke me yasa ba kya jin kunyar yin k'arya? Idan baki gane abunda takardar ta kunsa ba ai sai ki bari wad'anda suka sani suyi bayani yafi da ki tayarwa da mutane hankali a banza" Dije ta muskuta ta kalli Tambari ta mere masa baki tace,. "Ai Ni na zaci sak'on da ke ciki kenan don na gansu da kayan sojoji" Maigari zai sake yin magana Liman yayi saurin fad'in,. "ALLAH ya kyauta yanzu ayi abunda yasa aka taraku dai ba wani zakale zakalen magana aka ce ki zo wa mutane ba da su ba" Ya katse abun ne don gudun kuma wata b'araka ta kunno Kai ganin sababbin bak'in da suka zo kar su fara cin karo da abunda zai saka su fara jin dama basu zo kauyen ba. Maigarin ya gyara zamanshi yayi gyaran murya yace,. ,"Miye hadinki da Tambari har kika watsa masa k'asa a Ido kikasa yaji ciyo a hannu ya buge goshinshi?" Dije ta makawa Tambari harara tace,. "WALLAHI Ni ba dashi nike fad'ana ba don Ni har ma muka gama fad'an ban ma ganshi a wurin ba, sai zan bar wajen ne ma na hangoshi yana mukususu" Liman yakalli Dije da kyau yace,. "Kiji tsoron ALLAH ki fad'i me ya hadaki da shi?" Dije ta Sosa kanta tace, "Eh to tunda kace tsakanina da ALLAH WALLAHI ba dashi nike fad'a ba shine ya shigarwa Kanwarshi ya zo zai dakeni Ni Kuma na watsa masa k'asa a ido yaje ya buge da icce ya jiwa kanshi ciyo, idan kuma ba'a yarda ba a tambayi su Hansai gasu nan ai" Maigarin ya kurawa Dije Ido yana karantar yanayinta sannan yace,. "To munji wannan shi kuma Kiran Mahaifiyarshi da kika yi barauniya fa wa ta tab'a yiwa sata a gabanki" Dije ta zabura tsaye tace,. "Ai WALLAHI ko a gabanta zan fad'a don tasan naganta lokacin da ta yiwa Innarsu Ladiyo sata har ma na fad'awa Innar Ladiyon sai ko gashi da aka binciketa anga kud'in saboda cikin dankwalinta ta b'oyesu, har ma ........." Sunne Kan da Babansu Tambari yayi yana girgizar kai yasa Maigarin saurin dakatar da ita yace,. "To munji baki abun magana amman kisani ko da wasa kika sake cewa da ita barauniya sai kin karb'i hukunci, don Kinga wad'annan bak'in to su zan baiwa ke su kaiki birni asakaki gidan kaso a rufe ayi ta gana maki azaba, kinga shikenan bazaki sake ganin Innarki da Baffahnki ba, muma mu huta da bari barin da kike sakamu kullum safiya, haka fa kika fasawa yarinyar cen Bintalo goshi suka kawo kararki anan na basu hakuri dakyar suka hak'ura, yanzu haka ma Uwar d'akina tana cen tana fama da k'afa tun lokacin da kika zo muna da zancen Kura, to kiji ki k'ara ji kika yarda kika sake wani laifi a wannan karon ba zaki sha ta dad'i ba" Dije ta yi fiki fiki da Ido alamun tsoro ya shigeta fuskarta a kumbure tace,. "To ai sune suke tsokalo fad'an ko banso muyi fad'a ba sai sun janyo anyi, suma a ja masu kunne su daina shiga sabgata" Maigari yayiwa Tambari da Dijen iyaka haka ma su Hansai duka sai da ya ja masu kunne sosai akan kada su koma janyo abunda zai had'asu fad'a da kowa a garin bale ita kanta Dijen. Haka aka gama aka baiwa Mahaifinsu Tambari hak'uri aka aje akan za'a ga Baffann Dije idan ya dawo shima a sanar dashi ya ja kunnuwan 'yarshi. Har sun tashi zasu bar wajen Dije ta koma ta zauna tace,. "Nace ciyawar ita Kam har yanzu ba'a Kai ba" Maigarin ya kawar da kanshi gefe yace,. "Kije Gida idan baki ganta ba ki dawo ki karb'a" Dije ta mike cikin sanyin jiki tace,. "WALLAHI fa yau ban tafi Daji ba idan akuyata bata ci ciyawar ba hanamu baccin dare zata yi" Maigarin ya waigo cikin b'acin Rai yace,. "To kunatau! Kije tana cen nace akai maki idan an yo" Sannan Dije ta washe Baki tace,. "Yawwa Nagode ALLAH yasa kafi haka dussar ma ankai nagode duka amman har da gobe zaka aiko man ko?" A kufule ya d'aga murya yace,. "Har jibi ma kije Gida shikenan" Dije ta lak'ama kafad'ar su Ladiyo suka tafi suna ta firarsu suna dariya, har sunyi nisa Dije ta dafe Baki tace dasu "Wai kun ga abunda na gani kuwa?" Lanti Jummala da Ladiyo Hansai suka had'a baki wajen fad'in "Bamu kanun labaran mu sha?" Dije ta sassafta murya tace,. "Kunga wani fi'ili wai Namiji da shafa janbaki?" Ladiyo ta kyakyalkyale da dariya tace,. "Ashe ba Ni kad'ai nagani ba?" Hansai tace,. "Kuka sani ko haka Bakinshi yake?" Lanti tace,. "Injiwa? Baki ganin yanda yake fari tass! Ai irinsu ance cikin injin ake sakasu ana wankesu, garin wankin nasu ne ma bakinsu yake yin ja irin haka" Dije ta yi wani mere tace,. "Tirr ALLAH ya rabani da canza halittar da Ubangiji ya bani haka kawai garin wankan injin d'in a wanke da zuciyata ta fashe in mutu" Hansai tace "Ameen to amman naji ance zasu dinga karantar da mu to me zasu karanta muna?" Lanti tace,. "Wai Boko mu da ko Makarantar ma ba wani zuwanta ake yi ba za'a yi wahalar d'aukosu a kawosu garin nan" Dije ta harareta tace,. "Kece dai bakya zuwa nikam duk ranar da nasan malamai zasu zo ai kinsan ina zuwa, ku ne dai ba kwa son karatun Shiyasa duk cikinku babu wadda ta iya abacada" Hansai zata yi magana Ladiyo ta rufe mata Baki tace,. "Ni dai ku zo muje gida kar aga mun dad'e tunda an kashe rigimar" Hansai tayi gaba Ladiyo tabi bayanta Suka tafi, Dije ta kalli Lanti da Jummala tace,. "Ni fa kunsan me?" Suka ce "sai kin fad'a" Dije ta janyo kansu ta yi masu kus kus d'in cewa,. "So nike muje mu ga wadancen bak'in Yan bokon muji shi wancen Mai wankan injin d'in ko ya iya hausar shi" Lanti ta zaro Ido tace, "Bakiji kashedin da aka yi muna ba halan? Ni dai WALLAHI ban zuwa babu ruwana kunga tafiyata" Dije ta kalli Jummala tace,. "Kema jeki abunki amman ku sani WALLAHI sai kunsan Ni kuka yiwa rashin nasiha" Jummala ta kalli Lanti da ke ta sauri ta bar waen ta dawo da kallonta ga fuskar Dije take ta ciccika tana harararta cikin tsoron hukuncin da zata yi masu tace,. "Ni dai muje in raka kin" Dije ta washe baki tace,. "Ko ke fa zo muje su Kuma ki barni da su zamu had'u ai" Jummala cikin tsoro da kashedin da Maigarin yayi masu ta bi Dije Suka zagaya ta bayan gidan Maigarin har suka kai bakin k'ofar d'akin da aka ajiye bak'in cikin sanda Dije itace a gaba ta saka hannu ta yaye labulen kad'an ta leka kanta, aiko ta hango dan farin yana sauya tufafi ya zura dogon wandonshi kenan idonshi suka yi caraf da na Dije, aiko ba shiri ta saki labulen aguje ta falfala da gudunta saboda tsoron ganinshi da tayi daga shi sai guntun wando, saboda a rayuwarta kaf bata tab'a cin karo da wani a hakan ba sai ranar. Mutumin kam cikin sauri ya saka wandon ya mayar da rigar ya fito d'akin da sauri sai dai ko kurar Dije bai hango ba sai Jummala da ke gudu itama a k'ok'arinta na son ganin ta taradda Dijen da ta samu tasha kwana sai balbala gudu take yi kamar wacce zata tashi sama. Yayi kwafa ranshi a b'ace ya yi tsaye Yana nazarin mafita sannan ya koma d'akin inda ya taradda abokin tafiyarshi ya dawo da kwanon abincin da Maigarin ya Aiko masu. Cikin tsananin b'acin Rai ya zauna yana huci cikin harshen turanci yace,. "Bazan iya zama a garin nan ba gaskiya , sai da na fad'awa Mama bazan zo ba ta matsa man in zo to ai gashi nan na fara cin karo da takaicin babbak'un kauyawan" Abokin tafiyarshi yace ,. "Plss Safwan ka fahimci abunda ake so ka gane mana, yanzu miye aibin garin nan ne? gashi Maigarin da mutaneshi sai ina zasu sakamu suke yi sun karbemu hannu bibbiyu fa" Wanda aka Kira da safwan d'in ya wani mere baki ya gallawa abokin tafiyar tashi harara ya buga wani uban tsaki yace,. "WALLAHI da naga abunda bazan iya ba Ni fecewata zanyi in barka kaji da su, don bazan zauna takaicinsu ya kar ni ba a banza, yanzun nan fa ina k'ok'arin canza kayana ne na hango idon wata bak'ar mage ta zuro Kai tana kallona" Abokin tafiyarshi ya kyalkyale da wata arniyar dariya yace,. "Anan din ma ka sake had'uwa da wata magen kenan? To kasani ko ita wannan d'in itace Matar ba magen da ka baro a cen ba" Safwan saboda tsabar takaici ko kallonshi bai sake yi ba yana kammala saka kayan yayi kwanciyarshi, tare da janyo wayarshi da nufin ya yi kira aiko sai gashi yaga gaba d'aya kaf layukanshi babu d'aya mai network duk sun d'auke. Ba shiri ya Mik'e zaune cikin harshen turanci yace. "Oh sheet! Wannan wane irin bak'in gari ne haka? gaba d'aya basu da service fa ko d'aya" 🤣🤣🤣🤣wasa farin girki shin su waye su Kuma bak'in Yan bokon????. Akafta😛 D/AUTA CE✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *Jinjinar ban girma gareki masoyiyata ta asali mai Sona da zuciya d'aya Yar kanawa d'iyar mutan Yola Alkharin ALLAH ya Kai maki har gadon baccinki, Ina alfakhari da samunki gareni AISHA YOLA kisani sonki cikin jinina yake ALLAH ya bar mu tare har aljannah gaba dai gaba dai tawajena makiyanki fadawanki😛* *BAK'ON YANAYI COMPLETE ga Mai b'ukata 300 kacal Mai so ta tuntubeni ta wannan number 09032685442* *Lamba ta 10* Dije kam tana gudu tana haki har takai gindin wata bishiya ta fadi zaune k'asa tana sauke nishi a wahalce saboda Uban gudun da ta kwaso, Jummala ta k'araso itama tana haki ta fad'i kusa da ita tana hakin tana fad'in "Haba Dije shine kika ki tsaya man in fa an kamani kice me?" Dije ta kalleta Kai tsaye tace, "Zan ce Sabida kinje ganin Yan birni ne sun kamaki kina lekonsu" Jummala ta zaro ido waje tace,. "To ai kece kika leka ba Ni ba don ni ban ma hangosu ba" Dije tuno abunda ta gani yasa ta yi saurin rufe fuskarta tace,. "Ai nikam na ganowa kaina shiyasa Inna tace leke baya da amfani don garin leken sai ka ganowa kanka abunda ba shi ba ashe da gaskiyar Innata" Jummala ta bi ta kallo mai cike da son karin bayani tace,. "Me kika gano halan?" Dije ta runtse idonta da sauri cikin jin kunyar kanta tace,. "Kinga Jummala bazan iya tuna komi ba tashi muje gida tun kafin a gano mu ne muka lekasu idan har ya sanarwa da Maigari" Jummala ta Mik'e jikinta yana rawa tace,. ,"Hakane fa to Ni dai Kinga na tafi ko banza tallah zan je ma yanzu" Jummala ta yi hanyar Gidansu Dije ta yi Gida zuciyarta sai wassafa mata Yanayin da taga Safwan d'in take yi, inda take jin kunyar kanta da kanta saboda mugun ganin da idanuwanta suka yi. Aiko haka ta kwana duk wani motsinta sai taga fuskar Safwan tana yi mata gizo yana harararta tare da yi mata kashedi da gargadi kala kala, don har Inna sai da ta gano akwai abunda yake damunta, amman da ta tambayeta tace, "wasu bak'in Yan boko suka zo garin nan zasu koya muna karatun Boko, shine na matsu Litinin ta zo mu fara zuwa Makarantar". Inna kam sanin wacece Dije dangane da son karatun yasa ta amince, sai ko gashi ko da safiya ta waye aka yi gangami akan kowa ya taru k'ofar Gidan Maigari ana nemansu babba da yaro, aiko cikin kankanin lokaci aka hallara k'ofar gidan inda kai tsaye Maigarin yayi masu bayanin zuwansu Safwan da Lawi da dalilin da ya kawosu garin, inda yayi masu gargadi da jan kunne sosai akan tabasu da abunda zai biyo bayan hakan. Aiko kowa jikinshi yayi sanyi duk da wasu da yawa cikin garin bokon ba damunsu yayi ba bale har su damu da wani zuwansu, don da yawa cikinsu yaransu ko Makarantar basu tab'a lek'awa ba, masu k'ok'arin zuwan ma irinsu Dije kasancewar Malamman daga wani babban garin da suke a karkashinshi ne ake turosu, saboda sun fahimci daliban kalilan ne yasa suke yin tsalle akan zuwan nasu garin kullum, don wani zubin ma sau biyu ko sau uku ne suke zuwa a sati har ta kai yaranma kansu basu zuwa Makarantar sai ranar da suka san malamman zasu zo,Dije ma tana cikin masu k'ok'arin zuwa Makarantar na sahun farko, don wani zubin ma a sanadinta wasu yara da yawa suke zuwa Makarantar don habaici da take yi masu tana yi masu gorin cewa su jahilai ne tunda har basu iya abacada ba, amman duk da hakan a class d'aya duka ba zasu wuce mutum biyar zuwa shida ba, yanzu haka aji biyar Dije take a Makarantar tare da su Jummala da su Hansai, yan ajin shida mata duka anyi masu aure mazan kuma daman cen karatun bai wani damunsu ba. Haka Maigarin ya Kare yi masu bayanin ya gabatar da su Safwan garesu, Lawi dai kam ya saki jiki yayi masu bayani dai dai da saninsu amman Safwan kam iyakacinshi gyad'a kai yana dariyar yake, saboda shi warinsu ma yakeji yana damunshi a gundure yake da akai k'arshe ya bar wajen. Da ma aka zo kanshi akan ya tofa albarkacin bakinshi don tsabar renin hankali irin nashi da harshen turanci yayi magana, dukansu ko sai zarar Ido sukeyi suna kallon Bakinshi don su ko zo in kasheka da turancin basu sani ba, bayan ya k'are bayanin ne Abokinshi Lawi ya fassara masu abunda ya fad'a tare da yi masu bayanin cewa Safwan bai iya hausa ba baya jin yaren sam, Dije kam tana jin haka tace "Tab! Kace dai shi d'in katon kafuri ne ya zo muna cikin gari? To sai ka barshi ta k'arfin tsiya tunda mu babu irinka marar sallah cikinmu" Lawi yayi saurin Kai kallonshi ga Dije don yaga yanda take murgud'a Baki sai makawa Safwan harara take yi tana mui mui duk da baisan me take fad'a ba amman ya gano bakinta ba alkhairi yake fad'a ba, cikin wayancewa ya d'aga murya yace "Magana kike yi ne?" Dije ta yi saurin Shan jinin jikinta tace,. "Me kaji nace?" Lawi yayi Yar dariya yace, "na zaci akwai wata tambaya dangane da abunda ya shige maki duhu akanmu ne" Dije ta wani mere tace "Ba komi wancen din ne kawai nake ta ganinshi Kamar ba musulmi ba" Safwan yayi saurin Kai kallonshi gareta Aiko sai gashi ya gano fuskarta da idanuwanta da ya kasa mantasu tun lokacin da ta zuro kanta wajen lekenshi sukayi four eyes, aiko sai gashi da jin wani sabon b'acin Rai ya ziyartoshi, saboda daman cen da takaicinta da garin nasu duka ya kwana yana tsinewa wanda yayi tsanin postoshi garin, inda abokinshi Lawi yayi ta yi masa dariya don waya ma har sai da suka tambayi Maigarin yasa aka kaisu wani wuri nesa kad'an da cikin garin inda ake samun service, sannan ya yi waya da Yan gidansu ya sanar dasu halin da garin yake ciki don kada su kirashi suji basu sameshi ba su d'aga hankalinsu. Shima Lawi yayi waya gidan nasu da abokan arzik'i sannan suka dawo zuciyar Safwan kamar ta fashe saboda takaicin garinsu Dije, da yake yiwa 'yan garin kallon bagidajai tamkar wasu mahaukata saboda kyankyaminsu da yake yi, don ko abincin da aka basu baici ba fiddo rishonsu yayi ya kunna ya dafa indomin da suka yo guzurinta kwali kwali, sannan ya kwankwadi ruwan gorarshi da ya zo dasu catoon catoon yasha ya jefar da gora sannan yaji hankalinshi ya dan kwanta. Lawi kam sakin jikinshi yayi ya ci abincinshi kuma cikin dace yaji dad'in abincin don ba laifi basu da wata shahararriyar kazanta sukam. Idonshi akanta yana jin tamkar ya shaketa a wurin, inda itama shi d'in take kallo tana yi tana harararshi tana murgud'a masa Baki tana mui mui. Ranshi a matuk'ar bace ya mike ya koma d'akin da aka basu zuciyarshi cike da kuna tamkar yasa bindiga ya bindige kowa ma na garin yake ji saboda takaicinsu da abunda Dije ta yi masa yanzu. Dije kam binshi ta yi da kallo tana yi masa hararar gefen Ido har ya bar wajen, sannan ta cije lebe tana wassafa irin matakin da zata d'auka a kanshi don ta ga kanshi yana rawa. Har aka gama jawaban aka watse tunaninta baya wajensu tafe take zuwa hanyar Gidansu tana tunanin abunyi har taje Gida, aiko tun da sassafe Dije ta shirya cikin uniform d'inta da sukasha wanki tun jiya da marece, ta linkesu ta saka a karkashin filonta suka kwanta luf tamkar anyi guga, sannan ta baje ta zuba kwalliyarta da digo digon kwalli a fuska ta ranbada janbakinta ram a Baki taja Jakarta tana yiwa Inna da Baffah sallama. Inna ta bita da kallo tace,. "Lalle wad'annan bak'in turawa da Sa'a suke, irin wannan kwalliya haka sai kace ranar JUMU'A??" Dije ta rufe fuskarta tace,. "So nike yi abani shugabar Makarantar Inna naji wani Malami ranar yana cewa duk wadda kayanta suka fi haske itace za'a baiwa, don naji ma ranar yana magana da wani Malamin wai Ni yakeso a saka" Inna ta rik'e baki tace "To kenan ba ta k'ok'ari ake bi ba??" Dije ta yi saurin fad'in "To ai nafi kowa k'ok'ari ke Inna shiyasa ma da bak'in suka zo Ni aka baiwa takarda na karanta, baki ga yanda na burge kowa ba saboda turancin da nayi ta karantawa kamar ba Ni ba" Sai jin Suka yi ance "Kika iya karanta shirme dai, ai an fad'a mani komi bale ki zo ki dinga yiwa mutane bak'ar k'arya" Usman da ke shigowa cikin Gidan ya katse masu firar, Dije ta zunburo Baki ta yi d'akin Baffah tace "Baffah na tafi sai na dawo kayi man addu'a" Baffah ya fito yana yi mata adawo lafiya ta fice cikin sauri don gudun Usman ya ci gaba da fallasa gaskiyar karyar da ta yiwa Innar. Tun daga nesa ta hango Mutanenta da ke zaune bakin doguwar barandar ajijuwan hudu da ke Makarantar, wad'anda su kadai ne a duk fad'in Makarantar saboda rashin Muhimmancin da basa baiwa bokon bale har su nemi gudunmuwar gwamnati akan ta k'ara masu wasu ajujuwan domin k'ara fadada Makarantar. Dije kam tana hangosu ta had'e Rai fuska murtuk'e alamun ba wasa tana tafe tana wasa da Karen da ke hannunta har ta zo ta gabansu zata wuce ko kallo basu isheta ba, Lawi ya bita da kallo yana dariya Safwan kam a hasale ya ce "Hey you come here" Dije ta waigo ta murgud'a masa Baki taci gaba da tafiyarta, aiko ya kara d'aga murya yace "Stupid girl I say come here" Dije ta waigo ta sake murgud'a Baki ta yi gaba, Lawi da dariyar da yake makalewa taso fitowa yayi saurin fad'in "Da ke ake magana fa ko baki ji bane??" Dije ta waigo cikin dan guntun ladabinta tace,. "Ai ni to bansan me yake cewa ba" Lawi ya had'e fuska yace,. "Ki zo aka ce" Dije ta dawo tana cin magani tace,. "Ai Naga banyi latti ba shiyasa" Ta zo ta tsaya kansu kikam tare da rik'e kugu tana yiwa Safwan wani mugun kallo sannan ta kalli Lawi tace,. "Gani Malam" Lawi yana kumshe dariyarshi yace,. "Kinga wanda ya kiraki nan ko shi ba Malamin bane?" Dije ta kawar da kanta a gefe ba tare da tace kanzil ba, cikin fushi Safwan ya ce da ita "Stupid girl kneel down!" Cikin tsawa yayi maganar ya taso Kamar zai daketa, Dije ta yi saurin durkusawa k'asa cikin gunguni tana fad'in, "Kaci sa'a nasan wannan da WALLAHI bazan durk'usa ba" Aiko cikin fushi Safwan ya cira hannu ya gaura mata wani azababben mari, tare da nunata da yatsa cikin harshen turanci yace "Zaki fad'i abunda kika ce ko sai na kifar da ke a k'asa??" Dije dafe da gefen da tasha marin ta fara zubar da hawayen takaicin tozarcin da yayi mata a gaban sauran yaran garinsu masu jin tsoronta, aiko cikin takaicinta Safwan ya sake katsa matavwatw tsawar cikin turancin yace "Ba zaki fad'a ba??" Dije kam ganin zai sake dukanta ne yasa ta tashi ta yi tsalle ta fad'i k'asa dabas tare da kwallah wata Uwar k'ara tace "Ayihuhu maza bisa kanku" Akafta😛 D/AUTA CE *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *Jinjinar ban girma gareki HAJIYA DUDUWA mai abun mamaki🤣* *BAK'ON YANAYI littafine mai tafe da nashi kalar salo Wanda yasha banbam da sauran littafan da kuka tab'a karantawa a duniyar littafai, kar ku Bari ayi babu ku Naira 300 kacal zata baku damar tantance gaskiyar abunda na fad'a ma ku, mai bukatar littafin ta tuntubeni ta wannan number 09032685442 sai kun zo sayen nagari mayar da kud'i gida👍🏻* *Lamba ta 11* Ido sama ta fara sambatunta da ta saba kullum tana fad'in,. "Ya kai dan Sarkin aljanun yankin barakutusa, ya kai yariman sunbulowa ya kai dan gidan wargaza gumurzun jadduniya, ku garzayo duka anan yau ga ranarku ta zo mu taka rawa mu juyawa bikin cin dafuwar kan mai wankan injin, ku had'a wuta ku zuba ruwa a tukunya yanzu zan tsige maku Kan in baku kuje dashi bakin ruwan tekun bangon duniya, acen zamu yi shagalinmu na yau" Tana k'are surutan ta mik'e tsaye tana wani juya idanuwa ta zo gaban Safwan tana wani kyarmar jiki tana dalalo da miyau tana wassafa irin shakar da zata yi masa tana shakku, aikuwa dai ta yi jarumtar yin kundunbalar keta wata arniyar kuwwar tace "Gareeeeeeeki Lugudaniya" Aikuwa ta cafko wuyanshi iya k'arfinta ta fara yakuce masa wuyan da fuskar duka, cikin azama ya saka hannu d'aya ya fisgota ta fad'i k'asa Tim! Kai tsaya ya d'aga hannu ya kara sharara mata wani marin, Dije ta mik'e ta sake yin cikinshi da yakushi ganin zata ji masa rauni ne yasa ya nufi wani iccen dalbejiya yayi tsalle ya katso wata k'atuwar bulala, Dije kam bata daina biyarshi tana yakucinshi ba don ma da abun yayi mata dad'i har da su cizonta take Kai masa hari dashi, yana samun sa'ar saita bulalar ya ware iya karfinshi ya dinga lafta mata bulalar, tun tana juriya itama tana yin cikinshi da yakushin da cizon har ta Kai ta fasa wata k'arar dole saboda zafin bulolin da ya ke sauke mata a jiki, ba shiri ta fara fad'in cewa "Sai mun kasheka sai mun tsige maka idanuwa, sai mun nakasa maka k'afafuwa sai mun cire maka halshe" Safwan kam bai daina dukanta ba har sai da yaji ta fara fad'in "Nice Dije su sun wuce ni ce na iso yanzu WALLAHI nice Dijengalar Baffah da Inna Hasiya, kanwar Usmanu mijin Hansai, abokiyar Ladiyo da jummala" Gano da gaske ita d'in ce ba aljanun ba yasa ya daina dukanta ko shi sai da Lawi ya zo ya rik'e bulalar, tare da wasu malamai biyu da suka zo suna bashi hak'uri, saboda zafin kan Safwan ba mai sauk'i bane don da ace Dije tasan koshi d'in wanene da bata yi wannan wautar gareshi ba, don kam iya gaskiya Dije ta daku iya dakuwa a hannunshi, don haka ta baje k'asa tana ta tumurmusau tana kuwwar wayyo ita ALLAH ya cire mata zuciya ya karya mata hannu da k'afa saboda tsananin azabar da tasha. Lawi ya kalleshi ganin yanda yake ta wani sauke numfashi mai cike da tsagwaron fushi da b'acin ran da ya bayyana akan fuskarshi cikin harshen turanci yace dashi,. "Cool Dawn my man wannan fa ba Sury bace bale ka yi ta dukanta haka, idan wani abin ya sami Yar mutane zaka sakamu shiga Uku fa" Cikin fushi tare da d'aga murya Safwan ya yi magana cikin turancinshi da ya zame masa jiki yace,. "WALLAHI I can't tolerate any stupid nonsense from this villagers people, more especially that black cat, WALLAHI I will teach her lessons" yana k'are fadar maganar ya bar wajen cikin k'unar rai ya nufi wani office d'in da yake da tabbacin nan ne d'akin Malamai, Lawi ya bishi da kallo ya girgiza kai sannan ya nufi inda Dije take ya ce da kawayenta su Mune su rikata ta tashi, sai dai kowacensu tsoro ya hana su yi abunda ya sakasu saboda sanin wacecen Dijen, Lanti ce ta yi jarumtar zuwa ta rik'o hannunta tace "Yi hakuri Dije ALLAH zai saka maki tashi muje aji za'a fara yimuna karatun" Dije da ke kuka har lokacin iya k'arfinta ta yi banza da ita, Lawi ya k'araso wurinta yace "Ki yi hakuri ki tashi kije class dinku za'a fara yi maku karatu" Dije ta yi wata zabura Lanti da su Mune duka suka yi baya da sauri cikin tsoronta, ita kam tana tashi ko ta kan talkaminta bata bi ba ta nufi hanyar gida tana tafe tanata rera kukanta har ta isa Gida, tana zuwa ta fad'a d'akin Inna ta dunkule saman gado sai gurzar kuka take yi, cike da mamaki Inna take ta tambayarta lafiya? Me aka yi mata? Amman kuka yaci k'arfinta, dakyar Inna ta samu ta yi shiru sai ajiyar zuciya take yi wata bayan wata tana ciccika, Inna tabi jikinta da kallo da duk shatin bulalar ya fito rad'am a jikinta duk da kasancewarta bak'a, cikin sanyin jiki tace da ita "Wa kika jangalo yau wanda yafi karfinki yayi maki irin wannan dukan hakan?" Dije kam tambayar Inna tasata fashewa da wani sabon kuka tana sauke ajiyar zuciya cikin kukan tace,. "WALLAHI Inna sai na kasheshi" Inna ta zaro Ido waje tace, "ke Dije ki kiyayeni kar ki janyo in k'ara yi maki wani dukan a yanzu, WALLAHI ahir dinki kada in sake jin irin wannan kalami ya fito a bakinki, ke da wa halan? me kika yi masa ya yi maki wannan dukan gashi duk ya farfasa maki jiki haka?" Dije ta saka bayan hannu ta share hawayenta tace, "Wani bak'in kafuri ne cikin malaman da aka kawo Garin nan" INNA ta zaro Ido waje tace, " cikin bak'in Yan birnin??" Dije ta d'aga kai tare da saukowar wasu hawayen, Inna tace "Me kika yi masa" Dije tace "banyi masa komi ba don kawai zan wuce naga Yana hararata na rama shikenan ya kamani yanata jibga kamar ya samu jaka, har da cewa wai Kuma har ku zai had'e ya daka yaga uban da zai hanashi a garin nan" Inna ta yi mata wani kallon rashin yarda tace, "ki fadi gaskiya Dije don nasan da Baffanki ya dawo sai ya nemi jin ba'asin mafarin abun, kada kije ki sakashi jin kunya a gaban mutane" Dije ta Fara rantsuwa tace, "WALLAHI ALLAH har cewa yayi sai ya turo mota daga birni an rushe gidanmu, kuma ni yasa a saceni a tafi Dani birni a sayar da kaina yayi kud'i" Inna ta zabura cikin tsoro tace,. "To gashi Kuma kince baki yi masa komi ba, to haka kawai don kinfi kowa bak'in jini zai ce ya dakeki ke kad'ai? Akwai dai bari Baffanku ya dawo shi zai je yaji komi ai tunda ke kink'i fad'in gaskiya" Inna ta fita ranta a b'ace da ganin dukan da aka yiwa yarta duk da zuciyarta ta bata cewa da walakin goro cikin miya, don kuwa tabbas banza bazata kai zomo kasuwa ba, dole dai akwai abunda tayi masa ya daketan. Aiko sai gashi kafin kace me zazzab'i ya rufe Dije saboda kukan da tasha da zugin da bulolin suke yi mata, Koda lokacin tashi Makarantar yayi Lawi dakanshi yasa su Mune suka kawoshi gidansu Dijen, domin ya zo ya baiwa Iyayenta hak'uri duk da yasan itama bata da gaskiya, amman don a Sami zaman lafiya ya zo sai dai Baffah da Usman duk basu gidan Dole sak'o ya baiwa su Lanti su fad'awa Inna Hasiya, Ladiyo da su Jummala sunata yi masa godiya da kirkinshi da ya nuna masu a cen Makarantar, cike da jin dad'i suka shiga Gidan sai dai ganin Dije lullube tana rawar d'ari yasa duka jikinsu yayi sanyi k'alau, Inna ta washe baki tace dasu "Yawwa Jummala ku fad'a mani me ya had'a Dije da Bakon dan birni??" Lanti ta bayyanawa Inna komi da ya faru, sannan suka bada Jakarta da talkaminta da ta baro a aje mata, suka dubo Dijen da ke ta ta bacci sharkaf tana nishin ciyo, kowacensu cikin tausayi ta nufi gida, Inna kam sai cisgar fad'a take yi ita kad'ai saboda ganin ashe ma Dijen ce ta janyo aka lakad'a mata irin Wannan shegen dukan gashi ta janyowa kanta ciyo. An fara wasar fa😹 Akafta🤾🏻‍♂️ D/AUTA CE✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *MUTANEN DIJE K'ARANGIYA INA GAIDA KOWA Team Dije da team Safwan ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU DUKA👍🏻* *Lamba ta 12* Ko da Baffah ya dawo shiru shiru bai ji duriyar Dije ba tun yana zura idon ganin ta inda zata bullo har ya gaji dai ya tambaya, don ita kanta Innar ganinta da yayi sai a hankali yasa ya zargi ko sun k'ara kwatawa ne da Dijen shiyasa yaji Gidan shiru alamun bata nan, Inna kam bata so sanar dashi ba har sai ya ci abinci don tasan muddin yaji ba k'aramin d'aga hankalinshi zai yi ba, sai dai dole ba yanda ta iya saboda yanda ya matsa mata da tambayar ina Dijen taje har lokacin bata dawo Gidan ba?. Kai tsaye ta ce dashi tana ciki bata da lafiya, hankalin Baffah a tashe ya garzaya d'akin Innar inda Dije take kwance cikin zazzab'i sharkaf sai nishin marasa lafiya takeyi, aiko tana ganinshi ta fashe da sabon kuka gwanin ban tausayi, cike da fad'uwar gaba Baffah ya zauna bakin gadon ya rik'o hannunta yace "Meke maki ciyo?" Dije ta share hawayenta cikin rawar murya tace, "jikina gaba d'aya ciyo yake yi man ga raunukan sai zafi suke yi man Baffah, WALLAHI saura kad'an a kashe maka ni yau da baka zo ka sameni ba" Baffahn ya zaro Ido waje yace,. "Wanene da wannan danyen aikin gareki halan?, Ashe ko yau ba zan saurarawa kowa a gidan nan ba tunda har abun ya zo da cin zarafi irin haka, ki yi gaggawar sanar dani wa ya dake? tashi zaune ki fad'a man don in san irin matakin da zan d'auka kan mutum ko ma wanene" Dije ta yunkura dakyar ya rikata ta tashi zaune cikin kuka ta fara nuna masa raunukan da Safwan ya ji mata ciyo, Baffah kam ganin jikin Dije duk shatin bulalar yasa ya fara zuba ruwan fad'a bakinshi har kumfa yake yi saboda tsabar b'acin rai, Inna kam ganin yanda ya hau da yawa yasa ta fayyaace masa komi da aka fad'a mata ta sanar dashi, akan wanda ya dake tan tare da dalilin da ya janyo ya yi mata dukan. Baffah cikin tsananin b'acin Rai ya ja talkamanshi sai Gidan Maigarin, inda kai tsaye ya fara nuna rashin dacewar abunda BAK'ON Malamin yayi wa 'yarshi, Maigari da sauran mutanen da ke wurin Suka dinga bashi hak'uri sannan cikin tattausan kalami Suka nuna masa aibun abunda Dijen ta yi masa wanda Sam Sam bai dace da tarbiyyar dalibi ga malaminshi ba, tun yana ganin laifin Safwan har ya kai ya gano ashe rabin laifin duk na Dijenshi ne, sannan Maigarin da mutanen Suka fahimtar dashi sosai akan ya tsawatarwa Dije akan sake faruwar wata hatsaniya tsakaninsu, daga k'arshe suka bashi hak'uri akan abunda aka yiwa Dijen , sannan ya baro wurin ya koma gida inda dakyar da jib'in goshi ya samu tasha yan farau faraun fura sannan tasha pracetamol ta koma ta kwanta, cikin dabara Baffah yayi ta kwantar mata da hankali akan muddin Safwan d'in ya sake dukanta ta zo ta sanar dashi don wannan karon shi da kanshi zai rama mata, ba ko Malami yake ba ko hukumar ce da kanta sai dai idan an rufeshi mabudin ya b'ace. Sannan Dije ta rage bak'in cikin da ke cin zuciyarta, amman fa tasha alwashin sai yasan da ita yake zancen, haka ta kwana tanata wassafa irin muguntar da zata yi masa, cikin ikon ALLAH kwananta biyu ta warke Masha ALLAH,a rana ta uku da komawa Makaranta ne ta ci alwashin sai taje school d'in ko don labarin da su Jummala suke ta bata kullum akan yanda suke gane karatunsu, duk da dai shi Safwan d'in ba hausa yake yi masu ba amman dai ba laifi suna dan fahimta sama sama. Aiko ranar Alhamis tun da sassafe ta shirya cikin uniform d'inta, ta yi sallama da su Baffah cikin natsuwa ta nufi Makarantar, don shi Baffah har so yayi ta daina zuwa Makarantar a cewarshi tunda ba ta ALLAH ba ce, don dai ita Dijen ta nace tana son karatun ne yasa ya amince amman ya ja kunnuwanta da kyau akan ko kallon Safwan d'in kada ta sake yi don gudun wata sabuwar fitinar, sai da ta yi masa alk'awali sannan ya barta akan zata koma d'in, don tun lokacin da tasha dukan ta zama wata so silent da ita ko rashin jin cikin Gida duk ta daina yi, saboda kwata kwata ko walwala daina yi ta yi a gidan kullum tana d'akin Inna dunkule kan gado, don duk masifar da take yiwa akuyarta idan ta zubar da abinci ko abinsha, a lokacin duk ta daina don acen baya har bulala take sakawa ta yi ta dukan akuyar tana yi mata fad'a da kashedi kala kala, har wani zubin sai Inna ta yi mata fad'a akan zalin d'in akuyar da take ci sannan take kyaleta, amman sai gashi Safwan yasata zama kurum kurum dolenta. Aiko tafe take kanta a duk'e tun da ta hangosu daga nesa ta Sha mur tare da saita natsuwarta, don ko da ta zo ta gabansu sai da ta dan rankwafa sannan ta gayar dasu sai dai bata jira sun amsa ba tayi gaba abinta, Safwan ya bita da wata jar harara yayi kwafa yace "Mumu kawai black cat" Lawi ya kyalkyale da dariya yana dafe bakinshi don kada Dijen ta jiyo dariyarshi, amman duk da hakan bai hanawa kunnuwanta ji ba sai dai ko kad'an bata waigo ba har ta shige cikin class dinsu. Dan lokaci a tsakani sai gashi ya shigo ajin yana wani cin magani ya jefa mata chalk tare da nunata yace ta goge allo, ta mik'e ba tare da ta yi gardama ba ta goge black board d'in tass ta koma ta zauna, daga nan ya fara karatunshi mai cike da zallar turanci tsintsa don mugunta duk ya zo tambaya sai ya tambayeta saboda kawai ya kureta, Wani lokaci ta bashi amsa dai dai wani kuma idan bata iya ba ya kirata jahila, haka ya k'are darasin nashi cikin isa da gadara ya koma tambayoyin cikin tambayoyin ne kawai sai ga wani bera tun daga cen saman rufin ajin ya fado tsakiyar class d'in saboda rufin ajin gaba d'aya duk ruwa sun canye rabin, aiko ba shiri yayi wani tsalle cikin tsoro yace "Oh my gosh" Bera ko kamar ya san tsoronshi yake yi garin gudun neman mafaka ne ya nufi wurinshi, aiko sai ga Malam Safwan da yin wani uban tsalle ya dale window yana sambatu irin na tsoro, ganin hakan yasa duka Yan ajin suka fara dariya k'asa k'asa, Dije kam fuskarta a had'e tamau tamau ba alamun ma zata yi dariya, bayan beran ya wuce ne a gurguje ya kammala karatun ya fice, Dije ta kalli Yar paper'r da ke hannunta ta fara karanto abubuwan da duk yayi ta fad'a mata kalmomi kanana na turanci kamar haka Illiterate. Black cat. Urgly girl. Village girl Sai maimaitasu take yi amman ta kasa tantance fassararsu bale tasan ma'anarsu, a ranta ta kudurta zata tambayi abokinshi domin ya fassara mata su fillah fillah, Aiko kai tsaye ta fito ajin aka yi dace ta hangoshi cikin wani class yana karantarwa, aiko taje da sallamarta cikin ladabi tace dashi wurinshi ta zo, ya yi Yar guntuwar dariya ya d'auki excuse wurin Yan class d'in ya fito, cikin sakin fuska tace dashi don ALLAH wata tambaya take son yi masa in da Kai tsaye ta fara zayyano sunayen a kanta da ta samu ta hardace su cikin kanta. Lawi yayi shiru yana tunanin amsar da zai Bata wadda ranta ba zai b'aci ba, don zuciyarshi ta bashi cewa duka kalmomin daga bakin Safwan suka fito zuwa gareta don yasan k'aramin aikin abokinshi ne wannan, aiko dai ya koma class ya dauko wani littafin kalmomin turanci da fassararsu cikin harshen hausa ya mika mata yace taje ta duba da kyau zata gano fassarar kalmomin duka a ciki, cike da jin dadi Dije ta karb'a tana murna har ta juya zata tafi ta waigo tace "Don ALLAH ka ara man shi nan da kwana Uku zan maido maka" Yana dariya yace, "Na baki sati d'aya ma amman ki sani akwai tambayoyin da zanyi maki idan lokacin ya cika kin kawo" Cike da jin dad'i tace ta amince ta koma class dinsu zuciyarta cike fal da murna, tare da tunanin hanya mafi sauk'i da ta gano wadda zata rama abunda Safwan d'in yayi mata cikin dan kankanin lokaci. Har aka tashi Makarantar Dije bin littafin take yi d'aya bayan d'aya shafi bayan shafi har ta gano abunda duk yake nufi da miyagun kalmomin da ya yi ta jifarta da su kala kala. Tsawon kwana biyu Dije tana kamun beraye tana sakawa kwali tana b'oyewa don har da abinci da ruwa take ajiye masu, don kuwa ta kama bera yafi ashirin irin bakake d'in nan manya manyan, kullum Inna da Baffah sai dariya suke yi mata suna fad'in "Dije Kuma aikin kiyon beraye kika koma yi ??" Sai dai tayi dariya amman bata nuna masu cewa wani nufi ne a ranta ba, sai ko gashi tun da sassafe zata je Makarantar Allo ta yi dubarar fita da k'aton kwalin berayen, bata zame ko'ina ba sai Gidan Maigarin cikin nasara ba kowa a wajen ta yi dubarar ajiye kwalin ta je k'ofar d'akinsu Safwan ta leka, sai ko gashi shi kad'ai a d'akin yanata baccinshi hankali kwance. Dije ta d'auko kwalin ta shigo bakin d'akin a hankali ta kwantar da kwalin ta budeshi Aiko sai ga Beraye suna ta fitowa daga ciki suna shigewa cikin d'akin sai da ta juyesu duka sannan ta fito da kwalinta ta janyo k'ofar ta rufe ruf da kwadon da ke makale jikin k'ofar, sannan ta tafi da key din ta cillashi cikin ciyayi cikin sauri ta tafiyarta zuwa Makaranta zuciyarta cike da tsantsar farin cikin rama abunda ya yi mata . Ku taimaka kar ta yi kisan Kai😳🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️ Akafta🤣 D/AUTA CE✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *BAKINA YA YI KAD'AN YA NUNA DINBIN GODIYATA ZUWA GAREKU BA MASOYA BOOK D'IN DIJE K'ARANGIYA, AMMAN KU SANI INA YINKU SOSAI INA MAKU GASKIYAR SO FISABILILLAH💃🏻* *Lamba ta 13* SAFWAN kam cikin Bacci ya fara jin abu yana hawa jikinshi, wani jarumin beran ma cikin k'warewa da mugunta ya cafko masa farcen k'afa da k'arfi sai ga Malam Safwan a zabure tare da kwallah k'ara, idonshi suna kaiwa kan berayen ya fasa wata arniyar k'ara ya nufi k'ofar fita, sai dai mamakinshi rufe take gam gam ba alamun zata iya budewa, SAFWAN kam ya fara tsalle yana ihu Berayen suka firgice suma su ka dinga gudu suna neman maboya, wurin gudun ne wasu Suka yo kanshi aka yi sa'a wani zai hau sama ya kuskure sai gashi ya fado jikinshi, cikin firgici ya fasa wata arniyar k'ara tare da yin tsalle sai ga bera ya shige cikin rigarshi, Safwan ya ci gaba da ihu yanata tsalle har ya samu ya fito rigar da k'yar, amman duk da hakan bai daina zuba ihun ba don kafin kace me k'ofar d'akin nasu ta cika fam da dan Adam, don kuwwar da yake yi iya karfinshi ta janyo hankulan Mutane da yawa ciki kuwa har da Lawi da ke dawowa daga wajen kiran wayar da yayi da mutanen gidansu, kai tsaye aka fara k'ok'arin buge kwadon don a samu k'ofar d'akin ta bud'e, sai dai kafin ma a sami sa'ar budewa tuni Malam Safwan ya some saboda tsabar tashin hankali da firgici da tsoron da ya kamashi, don daman cen shi babu abunda yake tsoro a duniya face b'eraye, akan bera guda d'aya sai ya hargitsa d'aki kaf wajen nemanshi don kuwa muddin akwai bera a d'aki to kam sam shi bashi ba bacci a ranar har sai ya kasheshi sannan ne hankalinshi ke kwanci, to gashi yanzu ya janyo Dije ta yi masa gudunmuwa da manyan zaratan lukutayen kosashin Berayen kauyensu. Aikuwa ko da aka samu sa'ar bud'e d'akin kwance yake a sheme tsakiyar d'akin tsilla tsillan berayen sai hawa suke yi kanshi suna ta wasa, ganin Berayen yasa Lawi firgicewa saboda yasan yanda Abokinshi yake tsananin tsoronsu, cikin zafin nama ya dauko ruwa ya kandama masa, sai gashi da sauke k'atuwar ajiyar zuciya ya mike a zabure ya fito d'akin yana ihun kiran wayyo a taimakeshi beraye zasu kasheshi. Mutane kam sai kumshe dariyarsu suke yi ganin wai shi duk akan bera ne yake wannan firgici da tashin hankali har da su suma, Lawi kam sanin wanene abokin nashi da beran ya nufi wajenshi yana ta bashi Baki, sai dai ganin babban farcenshi na k'afa yana zubar jini yasa ya gano ba k'aramar barna Berayen suka yi masa ba, uwa uba fuskarshi da wuyanshi da ya yi jawur ga sawun yagar beran nan ya fito a jikinshi kasancewarshi farin mutum wurin yayi jawur, da kyar ya ciyo kanshi ya daina haukar da yake yi ya samu natsuwa ta ziyartoshi, ya jashi ya kaishi gindin iccen da ke k'ofar gidan Maigarin ya zaunar dashi, maigarin da sauran mutanen kowa sai yi masa sannu suke yi. Maigarin yasa aka fito da Berayen d'aya bayan d'aya anata kashesu, amman duk da hakan Safwan kafewa yayi akan shi ba zai sake shiga d'akin ba, don ko wunin ranar ma duk a waje yayi komi saboda tsoron shiga d'akin da yake yi, lokacin da dare yayi ma Dole sai d'akin wasu samarin yaran Maigarin aka kai shi ya yi bacci, amman duk da hakan motsi kad'an zai sa ya zabura haka ya kwana zuciya ba natsuwa. Ko da safiya ta waye tun da sassafe ya nufi Makarantarsu Dije don ko karyawa bai jira ya yi ba saboda gaba d'aya zama gidan ya gundureshi, aka yi dace itama Dijen ta yi sammakon fitowa don kusan ma itace ta biyu ko uku da zuwa Makarantar duka, tana hangoshi saman baranda kanshi duke yanata tunani ta fara kumshe dariyarta, ta yi k'ok'arin saita kanta ta isa wurinshi ta tsaya gabanshi cikin jarumta tace "Toch me toch fire live me live dengerous your cross the bala'i kaddara your business for nown you tunani in kwakwalwarka" Tana kare maganar ta gyara zaman Jakar fatar da ke rataye a kafad'arta ta yi masa wani kallo ta wuce fuuu abinta zuwa class dinsu, don tsoron ya sake yi mata irin dukan da yayi mata ranar, Safwan kam binta yayi da wani kallon tafi cen sakarai yana wani mere sai cen Kuma ya tuntsure da wata arniyar dariya, don a iya zamanshi garin ko Murmushi bai tab'a yi ba amman sai gashi yau da kyakyatawa kuma duk a sanadin abokiyar fadan nashi Dije, yarinyar da yake jin tsanarta har cikin zuciyarshi tsana irin wadda bai tab'a yiwa kowa irinta ba. Yabi bayanta da kallo yana dariyar takaici yace, "crazy girl" Dije kam murna kawai take yi shima yau ta wankeshi da turanci don ya gano cewa ita d'in ba jahila bace kamar yanda yake kallonta, taji matuk'ar dad'in samun aron littafin da Lawi ya bata don kuwa dashi ta ke kwana a saman kanta tana hardar kalamai tana had'a wannan da wancen ta yi magana cikin turancin duk da ba dai dai take yi ba amman ba laifi tana kamo hanya. Har aka tashi school Safwan bai da wata natsuwa Dije kam sai jinta take yi cikin nishadi, don tasa a ranta duk ya kuskura ya sake yi mata wani abun abunda zata yi masa a gaba sai yafi wanda ta yi masa a yanzu. Safwan kam kalamanta sun saka ya zargi cewa ko itace ta yi masa wannan horon da Berayen?, Sai dai ya sa a ranshi zai binciki kawarta d'aya idan har da gaske ita din ce to shi ko sai ta yabawa aya zakinta, aiko safiya tana wayewa ya yi sammako kamar yanda ya yi jiyan sai gashi ko Mune da su jummalo sun zo zasu wuce ya kira mune ta k'araso wurinshi cikin ladabi ta gayar dashi, sannan ya yi mata tambayar cewa "Kawarki ta gaya maku cewa ta saka man beraye a d'aki ko?" Mune ta fara waige waige tace, "A'a ba Ni ta fad'awa ba su Jummala ne ta fad'awa" Safwan ya had'e fuska yace,. "Au da gaske kenan itace ta saka man?" Mune ta rufe bakinta da sauri tace,. "Ni ma ban sani ba na dai ji tana fad'awa su jummalar don ni yanzu ko magana na yi mata bata amsa man gaba take yi dani" Ta k'are maganar cikin taruwar kwallah a idonta, Safwan ya bita da kallon mamakin ashe zarginshi ya zama gaskiya ita din ce amman Lawi ya tsaya Kai da fata yanata kareta tare da wanketa tas da soso da sabulu, cikin k'ara tsuke fuska yace "Me ya had'aku da har take gaba da ke?" Mune tana shirin bashi amsa ne ta hango Dije tafe tana tsallen jin dad'i tana yan wakokinta, ta yi saurin dafe k'irjinta tace "Na shiga Uku don ALLAH kar kace Ni na fad'a maka WALLAHI dukana zata yi in taji" Cikin rawar jiki Mune ta bar wajen da sauri har da su gudunta ta shige ajinsu, Dije Kam duk da ta hangosu amman ko kallo bai isheta ba ta dage kanta sama ta shige aji, sai ko gashi ya shigo class d'in yayi masu karatu saboda takaicin Dijen ko tambaya d'aya bai tambayeta ba, don ko ta d'aga hannu da nufin bada wata amsar sai ya basar da ita ya zab'i wata, haka yayi ta yi tun Dije bata damu ba har ta zo wuya itama ta daina d'aga hannun. Ko da aka tashi ya sakata kamun kunne cikin rana tsoron ya daketa yasa ta kama kunnen, tun tana juriya har ta kai ta fara kuka tana fad'in jininta zai dawo ta kai zubowa zai yi k'asa idan taci gaba, ya ce ta koma yin kneel down ta d'aga kanta sama ta kalli rana hannuwanta duka biyu ya d'ora mata duwatsu masu dan girma yace kuma ta yarda suka fad'i jikinta ya gaya mata. Dije tsawon minti sha biyar tana kallon ranar da taji azaba ta Kai mata karo ta fad'i sheme alamun aljanun sun zo, Safwan ya dauko bulala zai daketa ta yi saurin tashi tana fad'in "Don girman ALLAH Malam ka yi hakuri yunwa nike ji ka bari in je gida" Yace da ita suna nan har marece sai ta fad'i uban da yasa ta saka masa beraye a d'aki, Dije ta fara rantsuwar ba ita bace Mune ce amman duk da hakan sai da yayi mata bulala goma tare da gargadin ko kallonshi ta sake yi sai ya nakasata bale har ta sake shirya masa wata mugunta. Dije ta dawo gida sai kumbure kumburen fuska take yi sai dai taki fad'in abunda yayi mata don kada Baffah yace bazata sake zuwa Makarantar ba. Marece sakaliya ta tanadi kuka da toshshi ta k'ulle a leda, tana ta harkokinta har zuwa dare sannan ta sassada ta debi garwashin wuta cikin wani mataccen kwano ta rufe ta fita, Kai tsaye Gidan Maigarin ta nufa tamkar wacce aka aika tana shiga sashen d'akinsu Safwan d'in, ta ajiye kwanon ta fiddo tosshi da kukar da ta makale jikinta ta leka d'akin ta hangoshi yanata danne dannen wayarshi, ta dawo ta watsa tosshin da kukar ta yi saurin zuwa ta ajiye masa a bakin k'ofar ta janyo d'akin da sauri ta sake rufewa da wani k'aton iccen katako ta dantseshi ta tafiyarta" Safwan kam ko da ya ji sautin rufe d'akin yayi saurin Kai kallonshi ga k'ofar, abun mamaki sai ga hayaki ya hango yana fitowa cikin kwanon mikewar da zai yi bala'in azabar da ke cikin hayakin ta fara kaiwa idonshi da hancinshi ziyara, aiko nan take ya fara atishaya ya yi ta dukan k'ofar akan a bud'e masa ba kowa wajen don Lawi ma yana wurin Maigarin sunata firarsu, aiko tun yana iya gane gabanshi har hayakin ya turnuke d'akin ko hannunshi baya gani ga kuma tsananin azabar da ke cikin hayakin, ko da Lawi da sauran Yan Gidan suka zo kawo masa agaji tuni Safwan ya galabaita sai sauke numfashin yake yi a wahalce yana nishi sama sama. Ganin halin da yake ciki ne yasa Maigarin yaji tsoro yasa Lawi ya d'auki motarsu aka saka Safwan da wasu mutum biyu suka nufi Asibitin babban garin da suke karkashinshi, cikin gaggawa aka shiga dashi emergency room, Lawi da sauran mutanen duka sun yi jugum jugum saboda sun ji tsoron halin da Suka ga Safwan d'in ya shiga cikin kankanin lokaci. Team Safwan ku garzayo ni kam nayi nan🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️ Akafta🤾🏻‍♂️ D/AUTA CE✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *ALHMDLLH Lalle dole ne in godewa ALLAH saboda Littafin Dije k'arangiya ya Kai in da Ni din ban isa in je ba, Na gode sosai mutanen Dije Ina yinku all dinku wallah💃🏻💃🏻💃🏻* *Jinjinar ban girma gareki Kanwata ta gefen awazar damata waton HAJIYA DUDUWA Ina godiya da soyayyarki ga Littafin K'arangiya ALLAH ya bar zumunci tawan🥰🤝🏻* *Lamba ta 14* An d'auki lokaci kafin ayi nasarar dawo da numfashin Safwan dai dai, sannan aka kaishi d'akin hutu tare da makala masa ruwa in da shi yake ta barcinshi sharkaf yana ta sauke numfashi a hankali. Daga Lawi har mutanen da suka zo da su sai a lokaciin hankalinsu ya kwanta, ganin ya dawo cikin natsuwarshi duk da har lokacin bai farfado ba, amman alamun nasarar da suka bayyana ne yasa suka ji natsuwa ta zo masu, a k'arshe dai Lawi ne ya kwana da shi su kuma suka juya suka koma kauyensu domin su sanarwa da Maigarin halin da ake ciki. *** Dije kam ko da ta saka turaren ba gida ta yi ba lab'ewa tayi tana jiran taga ta ya abun zai kasance, aiko sai gashi tana jikin gini mak'e ta sha jinin jikinta ta fara jin yana ta dukan k'ofa, ta rufe bakinta saboda dariyar da ta sub'uce mata cike da jin dad'i ta k'ara bud'e kunnuwa domin ta ji me yake fad'a, jin yanata atishaya yasa ta fara tsallen jin dad'i ta nufi k'ofar da nufin ta bud'e katakon da ta rufe d'akin dashi ne ta jiyo takun talkami za'a zo, cikin firgici ta koma maboyarta cikin duhu ta lafe luf jikin ginin, sai dai abunda ya firgitata shine ganin an fito da Safwan rangai rangai yana wani numfashi sama sama, nan take jikinta ya d'auki rawa tare da gwalalo ido cikin tsananin tsoro ta biyo bayansu Lawi da sauran mutanen, ganin an sakashi a mota ana shawarar a kaishi Asibiti yasa ta zunduma aguje cikin tashin hankali ta nufi gidansu. Aiko shigarta ke da wuya Inna ta fara balbaleta da fad'a akan ina ta fito cikin daren? kuma me ya fitar da ita?. Dije ta yi tsuru tsuru tana warar idanuwa cikin tsoron abunda zai je ya dawo in har wani abin ya sami Safwan d'in, aiko ba shiri ta fashe da wani irin kukan tausayin su Innar, don tasan muddin ya mutu to daga ita har su sun shiga Uku don zaman duniyar ma sai ya gagaresu bale garin nadu, cikin Kuka ta fara fad'in "WALLAHI Ni ban yi komi ba Inna don ALLAH ki yafe mani" INNA Hasiya ta bita da kallo cikin duhun daren ta cafko hannunta cike da rud'ewa da jin tsoron in ba wani abu miyagun garin suka yi wa Dijenta ba, sai da ta d'auki wuk'a a kitchen sannan ta jata har kuryar d'akinta ta jefar da ita a tsakiyar d'akin, fuskarta a had'e ta nuna mata wuk'ar tace "Zaki fad'a man abunda ya fitar da ke gidan nan ko ba zaki fad'a ba sai na kasheki an huta?" Dije ta zaro ido tare da ja da baya tana kumshe kukanta Inna ma tana biyarta da wuk'ar zare da idanuwa kamar da gaske yankatan zata yi, Dije ta kai jikin bango ta fara kyarma tana fad'in "WALLAHI Inna ban yi komi ba ki yarda dani" Cikin b'acin rai Inna tace,. "Baki yi komi ba kika fita? Bayan kin San cewa Baffahnki ya hanaki fitar daren?yanzu haka ga Abincin Inna Gambo nan ajiye ina jiran Usman ya dawo ya kai mata, in da ina b'ukatar ki fitan ai sai a baki kije ki kai mata, zaki fad'a ko sai na yankaki d'in?? " Inna ta nufota da wuk'ar saitin wuyanta Dije ta zaro Ido tare da fasa k'ara tace "Wayyo Inna ki yi hak'uri wajen Dan birni naje na yi masa turaren hayakin toshhi da kuka" INNA ta dafe kirji tace "La'ilaha illallahu Muhammadur'rasulullahi Dije kashemu zaki sa ayi a garin nan ne?me yayi maki kuma ya zu da zaki yi masa turaren mayu?" Dije ta Sha jinin jikinta tana ajiyar zuciyar kuka tace,. "To Inna ba shi bane ya dakeni ranar" Inna cikin fushi ta kai mata wani mangari tare da wata muguwar faka a baya tana fad'in,. "Ba sai da nace ki kyaleshi kar ki yi masa komi ba? Ashe duk nasihar da nayi maki ta bayan kunnuwanki ta bi ta wuce?, To ai kin kyauta kije ki yi abunda duk kika ga yafi maki tunda Ni kin maida maganata ba komi" Tana k'are maganar ta fice ranta a matuk'ar bace tana fyace majinar kukan da ya zo mata ba shiri, Dije ta dunkule itama sai kukan take yi saboda har ga ALLAH taji tsoron halin da taga Safwan a ciki. Ko da Baffah da Usman suka dawo Inna bata yi k'asa a gwiwa ba wajen zayyane masu komi, hankalin Baffah a tashe ya garzaya gidan Maigarin, in da ya taradda k'ofar gidan dank'am! Ana ta bi da zancen abunda ya faru, sai dai duk kashe kunnuwan da yayi bai ji ance Dije ce silar abun ba, hakan yasa shi sakin jiki ya baje anata cecekuce akan binciko wanene mai hannu akan faruwar lamarin, don har kwanon da Dije ta debo garwashin da shi sai da ya gani anata tuhumar inda kwanon ya fito, tare da zayyana irin abunda aka yi masa kwana biyu da suka wuce da Beraye, Wanda a iya bincike duk an bincika an tabbatar d'akin babu wani bera ko d'aya kafin faruwar hakan, ALLAH ya taimaka Safwan da Lawi basu fad'i cewa Dije ce ta aikata ba, to sai gashi yanzu ma ta sake kwatawa don kawai k'ok'arinta na rama abunda aka yi mata, don bata yafiya kuma bata manta ranar d'aukar fansa. Baffah dai haka ya baje k'ofar Gidan Maigarin har wad'anda suka je kai Safwan Asibiti suka dawo, jin ba'asin samun nasara akan matsalar yasa ya yi sallama da su ya mamayi idanuwan Mutane ya dauke kwanon ya nufo gida da shi , Ko da ya shigo ranshi a b'ace ya wurgar da kwanon ya kalli Inna da ke cika tulunta da ruwan da Usman ya debo mata, yayi kwafa sannan yace "Ki gaggauta jefa kwanon cen masai tun kafin bincike ya sa a gano Dije ce ta aikata wannan bak'in halin, don WALLAHI wannan karon kam ta jangwalo muna k'aton jidali, saboda yanzu haka fa yaron yana Asibiti sai da naji yanayin jikin nashi sannan na baro wajen" Inna ta daina zuba ruwan ta yi tagumi tace,. "Ni WALLAHI na fara tunanin ko dai ayi wa Dije aure ne a huta?" Baffah ya maka mata wata harara yace, "WALLAHI ba wani aure da zan yi wa Dije yanzu tana yar shekara sha Uku, addu'ar nan dai da muke yi mata kullum to ita za mu ci gaba da yi ko yanzu, ina da tabbacin komi yayi tsanani to maganinshi ALLAH sarki, don haka yanzu ki yi gaggawar jefa kwanon cen a Masai mu huta da fad'uwar gaba" Har ya fara tafiya ya waigo ya kalli Inna da tayi tagumi ta yi shiru tana nazarin mafita, cikin damuwa yace "Ina ita Dijen?" Inna ta yi masa nuni da hannunta akan cewa tana d'aki, Baffah ya nufi d'akin, Inna ta ja kafafuwanta ta d'auki kwanon ta nufi bayi ta jefashi sannan ta dawo cikin sanyin jiki ta k'arasa zuba ruwan ta nufo d'akinta, in da ta taradda Baffah ya ke ta balbale Dijen da ruwan fad'a kamar ya daketa, Dije kam sai kukanta take ta sharba tana ajiyar zuciya wata bayan wata. Ranar dai haka mutanen gidan suka kwana kowane da abunda yake damunshi, Inna kam kwana ta yi tana rokarwa Dije shiriya tare da rokon ALLAH akan ya bata Miji nagari. *** Malam Safwan kam sai da ya kwashi awanni sannan ya dawo cikin hankalinshi, in da ya kurawa Abokinshi Lawi idanuwa yana son ya gano tantagaryar abunda ya faru dashi, aiko sai gashi take yanke ya dinga kallon abun a cikin idanuwanshi in da Kai tsaye bayan k'are tunanin nashi zuciyarshi ta tabbatar masa da cewa Dije ce ta yi masa wanna aikin, cikin k'unar zuciya ya gyara kwanciyarshi ya kalli Lawi yace "Yarinyar nan ko kad'an bata da imani kasheni take so ta yi abokina" Lawi ya gyara zamanshi yace,. "Me yasa kake son d'orawa yarinyar nan laifin da ba ita ce ta aikata ba?" Safwan ya k'ara b'ata fuskarshi yace,. "Yarinyar nan ko da ace kanwarka ce iya abunda zaka yi akanta kenan, ban san me yasa kake son kare yarinyar cen ba wai ko dai sonta kake yi ne Abokina?" Lawi ya yi saurin girgiza kai yace,. "Ko d'aya Ni dai bana son ka dinga zarginta akan abunda ba ita ce ta yi ba, don takamar kaji cewa ta saka maka Beraye to ai wannan baka ji ta fad'a a bakin kowa ba, don haka ka daina zarginta kuma ka ajiye zaton cewa ita ce ka bi a hankali in har ita d'in ce zaka gano ai idan mun koma" Safwan ya zaro Ido waje yace,. "Mu koma ina? Ai ni kam daga nan sai Gida don kam bazan koma bak'in kauyen nan ba, don na tsani ganin fuskar bak'ar shegiyar yarinyar nan, na tsaneta na tsaneta WALLAHI muddin ina ganinta to ko nine Nan zan yi ajalinta" Lawi ya zaro ida cikin tsoron lafazin Safwan d'in, sannan ya kyalkyale da wata arniyar dariya yace "Lalle ashe ko gaba da gabanta waton dai da gaske tsoronta kake ji Abokina, tunda har akanta zaka ajiye aikinka mai Muhimmanci" Safwan yayi masa wani kallo yace,. "Tsoro??? Duk in rasa wa zan yi tsoro sai wannan bak'ar magen? Cabd'i aiko kayi kuskure Abokina amman tunda har kace haka Zan koma Makarantar inci gaba da karantarwar amman anan garin zan sami wurin zama sai in dinga zuwa ina dawowa" Lawi ya k'umshe dariyarshi yace,. ,"Har yanzu da tsoron dai to ALLAh yasa hakan shine alkhairi amman Ni kam ina cen kauyen don a gaskiya naji dad'inshi" Safwan ya yi masa wani mere yace,. "Kaji da rashin hankalinka amman Ni kam na k'are kwana garin daga yau" 🤣🤣🤣🤣🤣 Akafta😹 D/AUTA CE✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *BAK'ON YANAYI LITTAFI NE MAI ZAFI 300 KACAL ZA TA MALLAKA MAKI SHI MAI BUKATA TA TUNTUB'E NI TA WANNAN NUMBER 09032685442* *Lamba ta 15* Tun daga Ranar Dije ta yi sukuku da ita don daga Baffah har Inna sun daina sakewa da ita, daman cen shi Usman ba wani shiri suke yi da ita Sosai ba, Dije cikin dabara ta dinga makalewa gidan Inna Gambo, don wani zubin ma dawowarta Makarantar bokon ke da wuya take tafiyarta gidanta ko Makarantar allonsu daga cen ta ke zuwa, INNA kanta ta fi sha'awar zuwanta Gidan da dai ace taje ta yi ta janyo masu abun magana, duk da ko ita Inna Gambon ana nuna mata halin watarana, saboda muddin ta kawo mata Abinci bata bata nera biyar d'in da take bata kullum ta kawo mata tuwon ba, to ko ko da ta ajiye tuwon sai ta dawo tace "Inna Gambo kinji Innata tace in babu biyar d'in to a bada tuwon" Wani zubin ta hanata d'aukar tuwon watarana kuma tace da ita,. "D'auki tuwonku ki kaiwa duk wanda kike so tunda daman cen ba don ALLAH kike kawo man ba" Watarana kuma ta jefa mata nera biyar d'in tace,. " D'auki gata nan amman ki sani gobe kar ma ki kawo man tuwon don bana so " Dije sai ta d'auke biyar d'in sannan ta dawo tana kalailameta da dad'in baki, Sabida gyaran hanya har shara da wanke wanke sai ta yi mata, sannan ta dinga debo mata ruwa tana cika mata tukanenta da tulunanta na ruwa. Inna Gambo da Dije in sun had'u wajibi ne ma sai ka yi dariya saboda yanda suke tsarguwar junansu, musamman dai ita Gambo da kullum ta ke yiwa Dije kirari da cewa "Alhudahuda Sarkin karatu sillen kara ta Ummaru Sanda, sarka mai rikicin gan gan, in kin so ayi ta morarki in kuma kin k'i ki fad'i ki rikice a rasa gano kanki, Dijengala ta megari Dije ba auren talaka ba talaka noma da sassabe, ALLAH ya kai mu inga aurenki ko don in baiwa Mijinki gudunmuwar bulala" Dije kam in Gambo tana yi mata kirarin har wani tsallen jin dad'i take yi tana rufe ido wai ita kunya, to dai kam wannan karon ko ita Gambon ta gano damuwar da Dijen take ciki, saboda zaunenta ta ke yi ta yi ta karatunta duk wata kiriniya ajiyeta ta yi ta koma sukuku da ita. Hankalinta bai kwanta ba sai ranar da ta je Makarantar ta hango Malam Safwan, cikin sanyin jiki ta isa wurinshi ta gayar da shi ta wuce ajinsu, duk da bai amsa ba amman ta ji dad'in ganin ya mirmije daga ciyon dolen da ta sakashi. SAFWAN kam binta yayi da kallon tsana tamkar ya janyota yayi ta jibga yake ji, amman tsoron sharrin da zata sake kulla masa yasashi yin alk'awalin ba zai sake biyeta ba, ballantana har watarana ta janyo masa bala'in da bai san ta inda zai taroshi ba, karatu dai ne ya zama dole to zai yi masu amman kam yasa a ranshi ba zai sake shiga shirginta ba. Ta bangarenta ne da kawayenta suka yanke shawarar kai kararshi wajen shugaban Makarantar, saboda basu fahimtar karatunshi sabida tsagwaron turancin da yake ta zuba masu, har za su fita Dije wani tunani ya zo mata a rai tace da su "Ku tsaya kuji wata shawara in kun amince mu ma mu dinga buga masa turancinmu na hauka ko da ba dai dai muka yi ba, ya fi dai da ace mu kai kararshi ya zo ya kara renamu" Ladiyo ta rik'e hab'a tace,. "Ke Dije to in ke kin iya turancin mu ai bamu iya komi ba" Dijen ta kyalkyale da wata dariya sannan tace,. "In kun amince Littafin da nake dubawa ina hardace sunayen abubuwa zan fara koya maku shi ku ma, ko don mu dinga haukatashi da turancinmu saboda if you had'a turanci da Hausa to no body kan k'ureka da shi" Mune da ke cen rakub'e tana kallonsu ta yi wani tsalle tace,. "Yee! Su Dije anji dad'i an kware da turanci" Dije ta galla mata harara tace,. "Ba nace kar ki sake shiga shirgina ba?? Ai Ni WALLAHI tun da kike da baki irin na aku kuturu bazan sake huldata da ke ba, ke kenan yawon gulma da tsegumi ko kin d'auka bansan kece kika fad'awa Malam nice na saka masa Beraye ba?, To bari kiji ko kusa dani na sake ganinki sai na shikka maki rashin mutunci mai matsayin monita a Makarantar nan" Mune ta yi rau rau da Ido ta dunkule tana kuka, Dije ta ja su Ladiyo suka fita sunata shawarwarinsu akan baturen Malamin nasu. Ai kuwa sai gashi cikin kwana biyu Dije ta fara koyawa su Ladiyo Littafin, cikin ikon ALLAH har sun fara ganewa suka watsar da karatun don daman cen ba wani son bokon suke yi ba, Dije Kam ta fita iskansu tana ta ci gaba da nacin bin kalmomin tana tantance su, don shi kanshi ganin ta fara catching d'in abubuwa ya fara rage nauyin tsanar da yake yi mata, wasa wasa sai gashi har lesson yake yi mata na daban ita kad'ai duk da a cikin class yake yi gaban sauran Yan ajin, amma kamar ita kadaice yake yiwa karatun, Sabida su iya kacinsu ido don basu fahimtar komi a darasin nashi. Cikin ikon ALLAH sai ga Safwan da sakarwa Dije fuska wani zubin ma har da su murmushi idan ta buga masa wani kalar turancinta mai had'e da Hausa. Lawi kam ganin yanda suke d'asawa ya fara jinshi yana kishin hakan, duk da dai bai tab'a nuna wani Abu da zai nuna matsayin da ya dauki Dijen ba, amman a zahirin gaskiya ba k'aramin so yake yiwa Dijen ba, yak'i furtawa ne don ya fahimci ita ba wannan ne a gabanta ba, don sai da ya bincika sosai ya tabbatar da Dije bata kula kowa sannan hankalinshi ya kwanta, to amman sai ga shi ya fara ganin canji a wurin Abokin nashi dangane da ita Dijen, cikin dabara ya shirya bugun cikinshi domin yaji gaskiyar lamarin. Aiko ranar suna d'akinsu na gidan Maigarin don tuni Safwan d'in ya baro cen garin ya dawo nan d'in saboda wahalar go and come d'in da yake yi kullum tsakanin garin da kauyensu Dijen. Lawi ya kalleshi yaga yanda yake ta marking d'in papers d'in Test d'in da yayiwa yaran Makarantar, ya yi gyaran murya yace "Abokina wai fa kwanan nan naga sai wani kawance kuke yi da mutuniyar taka, ko dai ka rufta ne kai ma kamar Ni?" Safwan bai daina marking papers d'in ba yace,. "Wace mutunniyar?" Lawi ya yi masa hararar gefe yace,. "Wace fa bayan Dije abokiyar rigimarka" Safwan ya d'aga kafada yace,. "No ba wani abun kawai dai don naga tana da jajircewa akan karatun ne shiyasa" Lawi ya k'ura masa Ido saboda son tabbatar da gaskiyar zancen, sannan ya sauke ajiyar zuciya yace, "Da dai ka sanar dani gaskiya Abokina don bana son mu zo mu mato a soyayyarta daga Ni har kai" Ba shiri Safwan ya d'ago kanshi ya kai kallonshi ga Lawin baki a bud'e zuciyarshi sai bugawa take yi da sauri da sauri, cikin b'acin Rai yace "Kai ko ance maka zan so black cat zaka amince? Me Zan yi da karamar Yarinya irinta kuma don rashin mafadi Yar k'auye" Lawi ya yi saurin fad'in "Me zai hana ita din ba mace bace halan?" Safwan cikin zafin Rai ya ajiye takardun ya mike ranshi a b'ace yace,. "Kai dai da kaga zaka iya to ka je ka yi ta yi, amman Ni kam matsayina ya girmi in lalace Kan duk wata ''ya da ke Cikin kauyen nan, musamman dai ita d'in da baka banbance komi a fuskarta sai hak'oranta da kwayar idanuwanta saboda tsabar bak'in da take dashi, cab! ALLAH ya rabani WALLAHI ku je cen ku k'arata" Cike da jin dad'i Lawi ya bi bayan abokin na shi da kallo har ya fice, sannan ya mike tsaye cikin wani tsantsar farin ciki yace "Gareka Lawi lokaci yayi da zaka fara farauto soyayyarka" Aiko a gurguje ya shirya ya nufi wurin Maigari bayan sun gaisa ne ya dan sosa kanshi yana so yayi magana yana tunanin ta ina ma zai fara?, Maigarin ya kalli yanda bakinshi yake rawa alamun akwai maganar da yake so su yi amman nauyi ya hanashi fad'a, shiyasa ya sallami sauran mutanen da ke wajen sannan ya kalli Lawi yana murmushi yace, "Lafiya yarona na ganka haka? Ga dukkan alamu dai akwai zancen da ka zo man da shi, to kar ka ji komi nasha gaya maka ka d'auka tamkar cewa Ni din Mahaifinka ne, don haka kar ka ji shakkun tunkarata da kowace irin magana ce " Lawi ya kara sunne kanshi yace,. "Wata yarinya ce na gani Ina so a garin nan, to shine nike jin tsoron bayyana kaina gareta gashi bansan al'adar garin ba" Maigarin ya washe bakinshi yace "A'ah to Masha ALLAHU ita ko wace mai sa'a ce wannan ???" Lawi cikin zumudinshi yace,. "Wata yarinya ce naji ana kiranta Dije" Ba Maigarin ba harta Liman da ke zaune da carbinshi yana ja sai da ya zaro Ido, cikin fargaba Maigarin yace "Wace Dijen ba dai ta gidan Malam Sanda ba?" Lawi cikin jin nauyi yace "Eh ita ranka ya dad'e" Maigarin ya sauke ajiyar zuciya yace,. "To dai lamarin aure bincike ake so a fara yi kafin a tsunduma kan lamarin, yana da kyau ka fara binciken halinta kafin ka fito da bukatarka gareta" Lawi ya yi shiru sannan yace, "To Baba a matsayinka na mahaifinmu anan garin na baka wuk'a da nama akan lamarin" Maigarin kam sai faman girgiza Kai yake yi cikin damuwa yace,. "Kana da masaniyar itace ta yi wa Abokinka turaren mayu har ya yi kwanciya Asibiti a sanadin hakan?, To bari in sanar da kai gaskiya tun wuri ka canza neman aurenka zuwa wani Gida, don wannan yarinyar mai Ido a tsakiyar kai ta shiga birni to ba'a san iya abunda zata aikata ba don......" Liman yayi saurin katseshi ta hanyar fad'in,. "Ayi mata fatan shiriya watak'ila ma sanadin shigarta birnin a samu matsalolinta su kau" Hmmmm😕 Akafta😅 D/AUTA CE✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *MUTANEN DIJE K'ARANGIYA INA GAIDA KOWA A KOWACE NAHIYA KUKE CIKIN DUNIYA ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU, HADIZA D/AUTA TANA GODIYA SOSAI👍🏻* *Lamba ta 16* Maigari ya yi wani mere ya mayar da kai gefe alamun rashin gamsuwa da zancen Liman, ganin haka yasa Liman d'in ya gyara zamanshi yace "Ni a tawa shawara abunda naga yafi a kira MALAM Sanda a sanar dashi zancen, ka ga duk abunda ya fad'a shikenan da shi za muyi aiki" Maigarin ya yi shiru na d'an lokaci sannan yace,. "To za mu kirashin duk yanda muka yi zaka ji yarona, amman ina son ka yi nazarin maganata kafin ka yi nutso cikin abunda zaka zo daga baya kana cizon yatsa, Sabida a zahirin gaskiya yarinyar nan kirin jijiya ce, bata jin magana ko kad'an ina ji maka tsoron ka je da ita cikin danginka ta wargaza maka zumunci da Yan uwanka" Lawi ya kara sunne kanshi cikin sanyi murya yace,. "Ai yanzu kurciya ce Baba jikina yana bani zata natsu matuk'ar ta ga bata gaban Iyayenta" Maigarin ya d'age kanshi a sama yace,. "Uhm lalle kam akwai k'urciya to ALLAh ya baka k'arfin gwiwar tunkarar matsalolinta" Lawi ya washe Baki fuska a sake yace,. "Ameen Baba na gode ALLAH ya rufa asiri kuma ya ja da nisan kwana" Maigarin da Liman suka ce "Ameen" Lawi ya mike tsaye yace "Ni zan dan fita babban birni in yo muna siyayya" Maigarin yace "a dawo lafiya ALLAH ya tsare" Suka yi sallama Lawi ya tafi zuciyarshi cike da farin cikin ganin cewa tamkar ma Dijen ta zamo Matarshi, bayan tafiyarshi ne Liman ya yi ta fahimtar da Maigarin akan fa'idar auren Dije birni, amman Maigarin kam sanin wacece Dijen yasa sam yak'i gano abunda Liman yake son nusar dashi, sai dai ya aika a Kira masa Baffahn Dijen don ya ji ta bakinshi saboda shi ya sa a ranshi ba zai tab'a yarda ya yi tsanin abunda za'a zo daga baya ayi kuka dashi ba. Aiko dan sak'on yana sanar da Baffah'n Dije bai yi k'asa a gwiwa ba ya garzayo cikin fad'uwar gaba domin ya ji kiran me ne Maigarin ya ke masa kuma yanzu, duk da wani gefe na zuciyarshi yana sanar dashi cewa Dijen ce ta sake aikata wani abin bayan sakawa D'anbirni turaren mayu da ta yi, don duk iya b'oyon da yayi akan kada a gano Dijen ce sai da Maigarin ya gano itace, don kai tsaye ya kira Baffah'n ya yi masa Kamar daman cen ya san itace d'in, ta sigar bugun ciki yace da shi, "Sanda mai yasa 'yarka bata bari a zauna lafiya ne wai? abun ya wuce kanmu ga shi yanzu har ta fara tab'a bak'inmu, to WALLAHI wannan karon za ta janyo maka zama gidan kaso matuk'ar baka tsawatar da ita ta ajiye shirmenta da rashin hankalin da take yi a garin nan ba" Baffah jikinshi ya d'auki rawa ya fara cewa,. "Don ALLAH ayi hak'uri WALLAHI na yi mata fad'a sosai akan wannan abun da ta aikata, kuma yanzu haka ma an samu ta rage duk wani k'irin ji da take yi, insha ALLAHu hakan ba zata sake faruwa ba" Maigarin ya yi shiru sannan yace, "au! Ashe dai da gaske itace d'in ce ta aikata? Um lalle rashin mutuncinta sai hauhawa yake yi, to WALLAHI bari kaji ta sake kwatanta wannan shirmen a gaban kowa zan saka Bafade ya yi mata d"an banzan duka a garin nan sai ya farfasa mata jikinta duka WALLAHI ka ji na rantse kuwa " Cikin fushi ya mike ya shige cikin gida sai Liman ne ya dinga fahimtar da Baffah'n akan abun da Dijen ta yi bata kyauta ba, Baffah sai hak'uri kawai yake ta badawa cikin sanyin jiki ya baro k'ofar Gidan Maigarin. To shiyasa yanzu ya ji tsoron wannan kiran kuma da Maigarin ya sake yi masa, a sukwane ya isa ya zauna cikin d'ar d'ar ya fara mik'a masu hannu suka gaisa, sannan cike fargaba ya ce "Gani ranka ya dad'e ALLAH dai yasa lafiya??" Maigarin ya gyara zamanshi ya yi shiru na d'an lokaci sannan yace, "to Sanda wannan kiran daban ya ke da sauran kiran da aka sha yi maka a baya, saboda haka ka natsu ka fahimci abun da zai fishsheka ya sama maka zaman lafiya Kai da 'yarka da iyalan gidanka duka" Baffah ya gyara zamanshi ya ce "Ina sauraronka ranka ya dad'e" Maigarin ya fesar da iska a bakinshi kai tsaye ya ce "D'aya daga cikin bak'in yan birnin nan to mai wankan darzar ne ya ga 'yarka Dije yana sonta da aure, kai me ka gani zaka iya surukuta da mutanen birni ko kuwa?don shi dai wannan yaron dan Gombe ne, abokin tafiyarshi ne dan YOLA" Baffah kam dirim! dum! yaji a cikin zuciyarshi don kuwa maimakon ya ji dad'in maganar amman sai dakan lugude zuciyarshi take yi, ya yi shiru na yan mintuna Maigarin yana ta yi masa kallon gefe yana girgiza k'afafuwa, sai cen Baffah'n ya yi jarumtar fad'in "ALLAH ya taimake ka ni dai gaskiya bazan tab'a yin nisa da Dije ba, nafi son ALLAh ya bata Mijinta a garin nan in auradda ita kusa da ni, don haka Ina mai baku hak'uri akan ya samu wata kawai su daidaita amman Ni kam ba zan yi wa Dije aure a birni ba" Maigarin ya gyad'a Kai yace, "kayi kyaun kai Malam Sanda Ni ma dai abunda na hango kenan tun kafin ka zo da naji maganar, insha ALLAHu zan sanar dashi sakonka ALLAH ya zab'a musu abunda ya fi alkhairi dukansu da mu gaba d'aya" Baffahn ya ce "Ameen" har zai mike Liman ya yi saurin dakatar da shi yace,. "Malam Sanda ka je dai ka yi shawara kafin akai karshen maganar saboda shi fa aure nufin ALLAH ne, Kuma duk inda ya nufa cen za'a Kai Yarinya to mutum bai isa ya canza tsarin ALLAH ba don lamarin ALLAH ba'a yi masa shishigi, don haka ka da ka yi jayayya da hukuncin Ubangiji a cikin lamarin aure, ka je ka nemi zabin ALLAH kafin ka yanke hukuncinka na k'arshe akan maganar" Baffah ya dan yi Murmushin yak'e yace,. "Na gode liman amman Ni Kam iya gaskiyata ce na sanar da ku, don kam Ni bazan yi wa Dije aure a birni ba, musamman ma dai gari irin wannan na nesa ka ga tafiyata na barku lafiya" Baffah sai fad'a yake yi cikin zuciyarshi har ya isa gida in da kai tsaye ya zayyanawa Inna duk abunda ke faruwa Inna ta zaro ido waje tace "Oh ni d'iyar mutum biyu yanzu ita Dije me ya had'ata da wad'annan Yan gayu da har zasu ce suna sonta? Ko dai basu dube yanayinta da kyau bane?" Baffah ya galla mata wata jar harara yace,. "Fad'a man aibin da ke jikinta da har wani ba zai ganta yace yana sonta ba??" Inna ta mik'e cikin sanyin jiki tace,. "Na ga dai ko Yan garin nan namu har yanzu babu Wanda ya tab'a cewa yana son Dije sai Bala,ko shi kuma har yanzu bai tab'a zuwa Gidan nan yace ya zo zance wajenta ba" Baffah cike da fushi yace,. "Eh kam da yake tafi kowa muni kaf! kafatanin mutanen garin ba ai ko dole a k'ita kam, to ke Hasiya in tone tone kike so ayi sai in ce mace nawa aka aurar a garin nan wadda ko kafar Dije bata kamo ba? Ke kanki kinsan cewa rashin jinta ne kawai ya janyo ake jin shakkun zuwa neman aurenta, kuma insha ALLAHu da ta mallaki hankalinta zata dena ai" Inna ta yi saurin fad'in "Da zaka bi shawarata Ni dai Malam da ka yi bincike akan asalin yaron, idan ka gamsu dashi shikenan sai a auradda ita a huta kaga ita hankalinta a kwance namu a kwance" Baffah yayi saurin fad'in " nasha aradun ALLAH in za'a mayar da gabana gabas a yankani ba zan bashi auren Dije ba, kiji ki k'ara fad'a in dai har nine nake da ikon auradda ita to bazan kaita nesa da mu ba, auren nesa ko auren jaraba haka kawai in bada 'yata ayi ta cin zalinta bata da kowa a gari bale taje ta Kai masa kuka taji dad'i, Ina ai bazata sabu ba wai bindiga a ruwa" Ya mike ya fice fuuu sai zabgar fad'a yake ta yi, mintuna kad'an da fitarshi sai ga Dije ta shigo da Yan wak'e wak'enta tana tsalle, Inna ta yafitota ta ce "Ke zo nan" Dije ta k'araso ta zauna nesa da ita cikin tsoron kada Inna tace ta yi wani abin kuma, Inna ta maka mata harara tace "Ki matso nace" Dije ta gurguso ta zauna tare da zunb'uro baki ta kumbure fuska, cikin k'ara had'e fuska Inna tace "Miye hadinki da Abokin wanda kika yiwa turaren mayu??" Dije ta washe Baki tace,. "ALLAH sarki ai yana da kirki Inna kinsan na ce maki shine ya aramani Littafin nan na koyon turanci, kuma WALLAHI kullum sai yaba kokarina yake yi har litrafan rubutu ya bani Inna ai na nuna maki su ko?" Inna ta maka mata wata hararar tace,. "Au ashe ya dad'e yana sonki shine baki fad'a man ba??" Dije ta zabura tare da zaro Ido waje tace,. "Kambala'innan Ni yake so?? Inna wa ya fad'a maki wannan bak'in kazafin? Haka kawai Ina zaman zamana a janyo man jarfa" Aiko Dije ta fashe da wani mugun kuka tace,. "ai na rantse da ALLAH ban yafe wa duk wanda yayi man wannan bak'in sharrin ba, ALLAH yasa cikin mutum ya kumbura ya fashe kafin safiya ta waye " Inna ta kume dariyarta tace,. "To mara hankali Baffahnki ne ya fad'a Kinga shikenan da adduarki ta karbu ko da safiya ke yi sai dai aga hanjinshi a watse cikinshi ya fashe" Dije ta zaro Ido waje tace,. "Na shigesu WALLAHI na goge addu'ar kuma na yafe masa amman shi kuma sai na ji dadilin da yake son jangwalo man jangwam" Tana k'are maganar ta yi hanyar fita, Inna tace,. "Dawo ina zaki je?" Dije bata fasa fitar ba tace,. "Inna don girman ALLAH ki yi hak'uri inje in dawo" Ta fice da saurinta sai ciccika take yi ta nufi gidan Maigarin, aiko sai gashi tana kaiwa tana hango Lawi ya dawo yana ta d'auko ledodin siyayyar da ya yi masu Safwan yana taimaka masa da wasu, Dije tana zuwa ta tsaya gaban Maigarin ta rik'e k'ugu tace, "Maigari na kawo k'arar bak'onka da yake son ya lalatani ya ci amanata ya yi man ciki don bashi da Imani" 😳🙆🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️ Akafta🤣 D/AUTA CE✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *MUTANEN DIJE K'ARANGIYA INA GAIDA KOWA ALL ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU👍🏻* *Lamba ta 17* Ba Lawi kawai ba harta Maigarin da sauran mutanen da ke wajen sai da suka furta "Innalilahi wa'Inna ilairraji'un raji'un" Cikin rud'ewa Maigarin yace,. "Subhanllah! garin yaya hakan ta faru?" Dije ta mayar da kallonta ga Lawi tace,. "Gashi nan ka tambayeshi ka ji ai Wanda ya mutu a ke yi wa k'arya" Lawi ya k'araso gabanta cikin rud'ewa tare da kid'imewa bakinshi yana rawa yace,. "Dije ki fad'i tsakaninki da ALLAH yaushe muka yi haka da ke?" Dije ta galla masa harara tace, "kai ma ka fad'i tsakani da ALLAH in ba cewa ka yi ka yi kana sona ba?" Ta k'are maganar tare da murgud'a masa Baki tana yi masa wani kallon up and dawn, Safwan da ke tsaye yana kallonsu ba shiri ya tuntsure da wata arniyar dariya, sannan ya koma jikin motarsu ya jingina yana toshe dariyarshi da taki tsayawa. Maigari yayi saurin fad'in, "Ina Dije" Dije ta waigo da kallonta gareshi tace "gani" Yace "zauna inji shin shi Lawi ta wace hanya ya bi domin ya lalataki kamar yanda kika fad'a yanzu??" Dije ta zauna tare da lankwashe k'afafuwa tace,. "Cewa fa ya yi yana sona to Ni kuma WALLAHI billahillazi ban sonshi ku shaida don ni ban shiryawa yin ciki ba yanzu, to haka kawai ya janyo man bala'i ina zaman zamana yasa in haifo macizai su zo su kasheni a banza, to WALLAHI ban sonshi Ni kam ya ma sani tun yanzu" Cikin k'umshe dariya Maigarin ya kalli Lawi da ke tsaye sororo ya kasa d'auke idonshi akanta saboda tsagwaron tsantsar mamakin da ta bashi, yace,. "Yarona ka zauna don inji ta yaya har hakan ta faru bayan tun farko sai da na sanar da kai gaskiya??" Lawi ya janyo kafafunshi tamkar Wanda kwai ya fashewa a ciki ya zauna tare da sunne kanshi cikin jin nauyin su Maigarin, maigarin ya sake cewa "Me ya hadaka da Dije?" Lawi ya sauke ajiyar zuciya yace, "WALLAHI Ni ba abunda ya hadani da ita, hasali ma Ni ko maganar da na sanar da kai har yanzu ban tab'a yinta da ita ba, kawai dai ta jahilci abun ne shiyasa" Dije ta maka masa wata harara tace, "Ai billahillazi ka yi kad'an da ka kirani jahila ko don ka bani littafai to ai ka jira ka ga in ban maido maka da kayanka ba" Maigarin ya dake cikin bata fuska yace,. "Ke Dije ki fad'i tsakaninki da ALLAH ya tab'a cewa da ke yana sonki bakinshi da naki? Ko kuma ya tab'a nuna maki wani halin rashin da'a Wanda ya danganci k'ok'arinshi na son yi maki cikin kamar yanda kika fad'a??" Dije ta yi shiru tana nazari sannan tace,. "Eh to tsakanina da ALLAH bai tab'a cewa dani yana sona ba, don ni WALLAHI ma mutuncinshi nike gani saboda naga yana da kirki, ba kamar Abokinshi da muka fara fad'a ba duk da ko shi d'in yanzu mun shirya har karatu yake koya man" Lawi sai lokacin ya ji wani sanyi ya ratsa zuciyarshi, cikin tanbaba yace "To ya aka yi kika ce Ina son in lalataki in yi maki ciki??" Dije ta ce,. "To wa ya ce ka ce kana Sona??" Yayi saurin fad'in "au! Don nace ina sonki shine zan yi maki ciki?" Tace "Eh ai Kai ma kasan da na ce nima ina sonka dole ne inyi cikin, Ni ko don a shawo kan matsalar tun kafin faruwar hakan shine na kawoka kararka" Cikin k'umshe dariya yace,. "Au yanzu da kince kina sona shikenan sai ki yi ciki.?" Dije tace "Eh in ma baka sani ba to ka sani yanzu don Ni na dad'e da sanin hakan" Ta k'are maganar tare da murgud'a masa Baki ta kalli Maigarin tace,. "Don Allah ka yi man iyaka da shi tun kafin ya kassarani" Maigarin gano inda ta dosa yace,. "Ai kuma tunda kince baki sonshi shikenan zance ya wuce, amman ki sani don yace yana sonki kin amince masa ba shi zai sa ki yi ciki ba, don haka kai yarona ka bata hakuri kuma a kiyaye faruwar hakan a gaba tunda dai ita tace bata sonka" Lawi ya mike Dije ta yi saurin kallonshi tace,. "Ina zaka je kuma bayan baka bani hak'urin ba?" Ya fuske yana saka talkamanshi yace,. "To ki taso mu je daga cen sai in baki hakurin in kina so" Dije ta mike ta bi bayanshi har zuwa wani k'aton kututturen icce da ke gefen k'ofar gidan Maigarin ya zauna, Safwan ya bisu da kallo ya yi mere ya shige d'akinsu sai dariya yake kyakyatawa. Dije ta yi tsaye kikam tana girgizar jiki tace,. "Bani hak'urin Ni dai in tafi inda zan je kar aga na dad'e" Lawi ya kai kallonshi ga su Maigarin ganin basu kallonshi ya washe fuskarshi yace,. "Ai dai nasan kina son kije Makarantar gaba da primary ko?" Dije ta saki baki sake tace, "Eh kai zaka kaini?" Ya yi saurin fad'in "Tabbas in har kin amince kin aureni to Ni na yi maki alk'awali Ni zan kaiki kiyi Makarantarki har ki yi degree ki zama likita kina yi wa marasa lafiya allura" Dije ta zaro Ido cikin jin dad'i ta yi saurin zaunawa kan iccen tace, "Don Allah da gaske kake yi zaka kaini in yi likita ???" Yace "me zai hana in har zaki aureni" Dije ta yi shiru sannan ta ce "Ni ba Wai aurenka ne matsalata ba bana son ne ince ina sonka don WALLAHI na tsani in haifi macizai saboda tsoronsu nike ji sosai, akwai ranar da muka je daji muka ganshi WALLAHI har suma sai da na yi acen aka kwasoni aka kawoni gida" Ta k'are maganar cikin zubowar wasu yanmatan kwallah, Lawi ya yi saurin fad'in "To ya isa daina kuka Ni na hak'ura ko baki ce kina sona ba in dai har kin yarda zaki aureni shikenan Ni kin gama mani komi, Ni ko zan kaiki ki yi karatu har ki fito matsayin babbar likitar Mata" Dije ta washe Baki cikin tsananin jin dad'i tace,. "Aiko WALLAHI na amince kai Ni gobe ma ayi auren muje in fara karatun Likitancin" Lawi ya zaro Ido waje yana dariya yace,. "Masha ALLAh lalle Ni Lawi dangata ne" Dije ta rufe fuska tace,. "WALLAHI ina son inga ina yiwa mutane allura nasan sai sunyi ta kuka" Lawi ya tuntsure da dariya yace,. "Au to mugunta ma za ki yi ashe ba taimako ba??" Dije tace "duka biyun ai Ni ina da tausayi wani zubin fa in naga ana kuka nima sai inji ina yi" Lawi bakinshi a washe yace,. "ALLAHu Akbar ashe haka Dijen take da imani ban sani ba?" Dije ta rufe fuska tace,. "Ni dai yaushe za'a yi auren in fara zuwa karatun likitar?" Lawi ya sassauta murya yace, "to ai ke sai kin gama wannan da kike yi sai kije ta gaba sannan ki fara ta Likitar" Dije ta zaro Ido tace,. "Cabd'i ashe abun da wahala? To yanzu ita ta gaban wannan da muke yi mi ye sunanta??" Lawi yace,. "Secondary". Dije ta yi saurin maimatawa tace,. "Sakandari?" Ya ce,. "Eh". Tace "shekara nawa ake yi a gama to?" Yace "shekara shida ce itama kamar primary" Dije ta zaro Ido cikin sanyin jiki tace,. "Anya ko Baffahnah zai barni in yi karatun kuwa??" Lawi cikin farin ciki yace,. "Me zai hana ke dai kawai kice masa kina son akai ki idan har ya amince ko kina cikin karatun sai a yi muna aurenmu ki je kici gaba a gidana" Dije ta rufe fuskarta cike da jin kunya ta tashi ta zank'ara da gudu aguje ta nufi gida cikin tsananin farin ciki, Lawi ya bita da kallo yana dariyar shirmenta musamman da ya tuno da zancen zai lalatata ya yi mata ciki don ba ya da imani. Dijelawis asha luv lfy🤣 Akafta😛 D/AUTA CE✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *MUTANEN K'ARANGIYA GA JINJINAR BAN GIRMA👍🏻😝* *Lamba ta 18* Da tsallen jin dad'i ta shiga gidansu sai wasar Baki take yi, Inna ta bita da kallon mamaki wadda ta fita tana kuka yanzu kuma itace ta dawo tana wasar Baki, aiko sai da ta zauna daf da Inna sannan ta kwanta saman cinyarta tana rufe ido da tafukan hannayenta, Inna ta shafo dunbujen tulin gashinta da kullum ba'a wuce yi mata tsoro hudu a saman Kan nata, saboda bala'in jin zafin kitso ne da ita gashi gashin a cikenshi yake da kuma tsawonshi tubarakallah, don ko shartar gashin za'a yi mata idan an kwance sai duk makota sun sheda, saboda kururuwar da zata dinga yi tana kukan wayyo ita zafi, shiyasa kullum kitsonta tsoro hudu ne don ko shi d'in sai Inna ta ajiye bulala a gefe sannan ake yinshi tana kuka har da su majina shabe shabe, saboda in ta kawo mata reni kai tsaye ta ke mazgarta da bulalar, shiyasa in dai har ranar kitson ta zagayo to ko Baffah dole ne sai ya siyo mata wani Abu a matsayin cin hanci don kawai a samu ta natsu a yi kitson lami lafiya, amman da ta canye abun sai a koma tarxomar da aka saba kullum. Tana shafar gashin kan nata tace,. "Yau kuma me ya saka 'yar Baffah farin ciki irin haka??, Ke da kika fita da kuka to me ya sakaki wannan murmushi da kike ta yi?" Dije ta tashi daga kwancen ta rufe fuskarta tace,. "Inna mun shirya da D'anbirni har ma ya yi man alk'awali zai sakani Makarantar Likitoci in dinga yiwa mutane allura" Inna ta zaro ido waje tace,. "Au kin amince zaki aureshin yanzu??" Dije ta rufe fuskarta alamun jin kunya tare da d'aga kanta, Inna ta bita da wani kallon yaron man kaza tace "Kina sonshi kenan?" Dije ta mik'e da sauri zata shige d'aki tace,. "Ni WALLAHI fa bana sonshi amman zan aureshi saboda ya kaini Makarantar koyon Likitanci" Har zata shige ta dawo baya tace,. "Kin ga shikenan Ni sai in dinga yiwa mutane allura ba har sai an tafi zuwa birni ba" Inna ta maka mata harara tace,. "To sai aka ce da ke in har kin aureshi a nan garin zai zauna da ke ko?, to bari kiji garinsu nisa ne dashi ke asali ma sai anyi kwana biyu ana tafiya kafin aje cen d'in, kin ko ga Baffahnki ba zai tab'a bari ki yi auren ba saboda nisan da ke tsakaninmu da su" Dije ta dawo tare da kumbure fuska tana dire diren kafa tana fad'in,. "Ni WALLAHI Inna ina son in zama Likita don ALLAH ki ce da Baffah ya barni in aureshi don ALLAH" Aikuwa caraf sai ga kunnen Baffah da ke shigowa tare da Usman, cike da mamakin abunda ya jiyowa kunnenshi ya k'araso idonshi akanta yace,. "Me naji kina fad'a ne???" Dije ta isa wurinshi da sauri ta rik'o hannunshi tana share yan guntayen kwallar da suka zubo mata tace,. "Baffah D'anbirni yace dani idan na aureshi zai sakani Makarantar likitoci in zama babbar Likitar Mata don ALLAH ka barni in aureshi WALLAHI ina son zama liktanya Baffah don ALLAH kaji?" Ta k'are maganar tare da d'aga kanta ta kalleshi cikin marairecewa, Baffah ya k'wace hannunshi da ta rik'e ya tureta gefe ya wuce yana fad'in "Ke wace irin yarinya ce da kullum shirmenki k'aruwa yake yi? Sai ana murna anga sauyi sai kuma ki k'ara tsunduma ruwa? To bari kiji ni zan ganshi da kaina in sanar dashi cewa ba Zan bashi ke ba, tunda har baiji kunyar zaunar dake ya sharara maki wannan k'arya ba, ke kuma da yake ba wayau ne da ke ba kika amince da zancenshi na yaudara, to WALLAHI na sake jin ma kin tsaya da shi kunyi magana sai kinsan d'anjaki dukiya ne, tunda ke kwakwalwarrki bata hasko komi sai shirme mara tushe bale makama, ke Makarantar ma kin daina zuwa daga yau sai nagani in akwai wanda ya isa yasa ki koma" Haka ya yi ta sababin fad'a Dije kam ta rabe jikin gini sai kukanta take sharba, Usman ya maka mata wata jar harara yace "Wawuya kawai mara hankali ke in banda wauta irin taki ma me 'yanbirni irinsu zasu yi dake ne? Da har zaki yarda da karyar da ya shinfida maki??ke da ko wanka har yanzu baki iya ba sai bak'ar jik'a jik'ar daud'ar da kike yi kullum, har sai Inna ta gaji da kazantarki ta yi maki a hakan za ki je birnin?? ALLAH yasa ma Baffah ya hanaki sake zuwa Makarantar da gaske muga ta iyayin bacci da Littafin Boko a karkashin filo" Ya buga mata wani uban tsaki ya shige d'akinshi, Dije ta bishi da harara tare da murgud'a Baki tace,. "Ai billahillazi in na zama likita ko zaka mutu bazan yi maka allura ba" Usman har zai shige d'akinshi ya waigo yace,. "ALLAH ma ya tsareni da allurarki WALLAHI, kuma yarinya ta jira idan har taga ta zama Likitar sannan" Dije ta bi k'ofar da kallo tana harare harare sannan ta yi tsugunne tana wasa da kare tana zane k'asa tana rubuta, _WALLAHI Ni sai na zama likitar nan_ Ta goge ta sake rubuta _Idan ba haka ba daji Zan koma da zamana acen kuraye da sauran namun daji su cenyeni tunda har ba'a sona._ Haka ta lalace a wurin ta yi ta shirmenta har sai da Inna ta fito ta korata ta shiga d'aki. ***** A bangaren Lawi kuwa tana tafiya ya nufi wurinsu Maigarin Baki har kunne yake sanar da su cewa Dijen ta amince, Maigarin ya yi masa wani kallo yace "Yaro man kaza to bari kaji gaskiyar lamarin Mahaifinta ya tabbatar man da cewa ba zai baka aurenta ba, don haka kaje ka nemo wata in har sha'awar aure a cikin garin namu kake yi, ka duba da kyau Akwai sa'o'inta da yawa a garin har ma da wad'anda suka fita, duk Yar da kake so ka nemota Ni zan shige maka gaba har sai ka sameta, matuk'ar ba wannan masifaffiyar yarinyar bace" Lawi murnarshi ta koma ciki, cikin sanyin jiki yace "Idan har ba zan sameta ba a bar zancen wata kawai Baba" Yana kare fad'ar maganar ya mike ya nufi d'akinsu zuciyarshi sai hasko masa fuskar Dije take yi lokacin da take rufe fuskarshi alamun jin kunyarshi, don kuwa saura k'iris ya rage ya ci k'asa saboda wani uban tuntuben da yayi, cikin yamutse fuska ya shiga d'akin ya fad'a kan katifarshi ya baje tare da d'ora hannu a saman goshinshi yace "Hasbunallahu wa ni'imal wakil!" Safwan da ke ta game a wayarshi da ko caji har sai sun kaita babban garin sun samo sannan su yi ta maneji har lokacin da ya sake cenyewa, shiyasa suka fara shawarar saka Generator su huta da zirga zirgar kai cajin da suke yi. Ya yi saurin kai kallonshi gareshi ganin yanayin da ya ganshi yasa ya ajiye wayar ya tashi zaune yana kumshe dariyarshi yace "Yanzu Kai don baka da imani shine kake so ta yi ciki?? To WALLAHI Ni babu ruwana idan ka janyo ta haifi macizai" Ya k'are maganar cikin shekewa da wata arniyar dariya tamkar ba Safwan ba, saboda ba k'aramin dad'i ya ji ba akan wannan wasar kwaikwayon da Lawi ya yi da Dijen, Lawi ya mike zaune cikin damuwa yace " Seriously WALLAHI ina son yarinyar sosai, bansan ta ya zanyi in shawo kan Mahaifinta ba, har in samu ya amince ya bani aurenta" Safwan kam sai kallonshi yake yi da gabanshi da ke ta fad'uwa da sauri da sauri, cikin dakiya yace dashi "To ita yarinyar ta amince da kai ne halan?" Lawi ya dafe kanshi yace, "bana jin yarinyar yanzu saboda na fahimci ta inda zan shawo kanta cikin sauk'i in janyo ra'ayinta a kaina, don ko yanzu na gano tana sona k'urciya ce kawai tak'i bari ta gano hakan, amman Mahaifinta ne matsalata don yanzu Maigari yake sanar dani wai yace shi ba zai auradda d'iyatai gareni ba saboda munyi nisa, to Ni WALLAHI idan zai amince sai in dawo nan garin da suke karkashinshi in nemi aikina a nan, idan na samu sai in zauna nan din mu shimfida rayuwar aurenmu Ni da Matata" Safwan ya yi masa wani kallo yace,. "Su Kuma iyayenka da sauran danginka sai ka yi ya ya dasu??" Lawi ya yi saurin fad'in, "Zan dinga zuwa Ina dubosu ai WALLAHI ya fi man da dai ace in rasata gaba d'aya" Safwan ya buga wani uban tsaki yace "Lalle akwai alamun tabin hankali a Kwakwalwarka tunda har zuciyarka take hasko maka hakan shine dai dai, yanzu akan mace macen ma wannan kucakar yarinyar ace zaka rabu da kowa naka akanta?? WALLAHI ka yi kuskure don tun wuri ka ajiye wannan shirmen banzar, ko ka manta cewa Kaine fitilar da Mahaifinka da mahaifiyarka da kannenka suke haskawa su ji sanyi?? Ka yi nesa da su ta ya ya kake ganin zasu dauki hakan a matsayinka na mai taimakonsu???" Lawi ya furzar da iska a bakinshi yace, "ba zaka gane ba ne Abokina WALLAHI ina mugun son yarinyar, nima bansan ya aka yi har ta sami irin wannan mazauni a zuciyata ba kada ka ga laifina plss!" SAFWAN zuciyarshi sai dakan lugude take yi muryarshi a sarke yace,. "Yanzu kai duk matayen da ke duniyar nan ka rasa wadda zaka so sai wannan bagidajiyar??" Lawi ya maka masa harara yace,. "Plss abar zancen na godewa ALLAH da har ya b'oye maka abunda ni na hango, wanda a birnin ma ire irenta ne suke d'aga kai suna hurar hanci suna tak'ama, don WALLAHI wannan yarinyar da ka ke renawa ta shiga birni ruwan birnin suka wanketa tas tasha jar miya to WALLAHI ba k'aramar mace za'a yi ba" SAFWAN cikin fushi yace,. "Da bak'in??" Lawi yace,. "Ni bakinta bai dameni ba don asali ma bak'inta mai kyau ne idan fatarta ta sami man shafa pure wanda zai gyarata sosai WALLAHI sai ka sha mamaki idan ka ganta wata rana" Safwan cikin sanyin jiki yace ,. "Shi kuma kauyancin fa ka yi ya ya da shi haka kawai ka sakata Mutane ta dinga kwafsawa???" Lawi ya sauke nannauyar ajiyar zuciya yace,. "A tsarina tun fil'azal kai ka sani bana son wayayyiyar mace, nafi son macen da komi sai na d'orata akan hanya, wadda duk tarbiyyar da na bata akanta zata hau ta yi tafiya har a cimma nasara a gaba" SAFWAN ya maka masa wata jar harara kamar ya dakeshi yace,. "To dai ita wannan yarinyar bazata tab'a yi maka abunda kake so kuma kake ta hasashe ba" Lawi ya yi saurin fad'in "Saboda mi?" Kai tsaye SAFWAN yace,. "Saboda ba zaka aureta ba" Lawi ya zaro Ido waje yace,. "Au! don kai kake so ka aureta kenan ko ya ya??" SAFWAN ya yunkura kamar zai dakeshi yace,. "ALLAH ya rabani da wahala WALLAHI, Kai din ma bazan barka ka aureta ba" Tofa🤔 Kai ko MALAM SAFWAN banda hana ruwa gudu fa😕 Akafta😊 D/AUTA CE✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *Masu comments da masu share bani da bakin godiya gareku sai dai ince ALLAH ya biyaku ya saka maku da alkhairi, naga comments dinku all kuma na gode sosai dukanku I love you gabza gabza😉* *Special gift for you my..... HAJIYA DUDUWA Ina yinki sosai wlh💋* *Lamba ta 19* Lawi ya bishi da kallo har ya fice sannan yace,. "WALLAHI ka yi kad'an ka hanani abunda nike so, don son Dije cikin jinina yake kuma aurenta kamar nayi na gama don haka ka zura ido ka yi kallo" SAFWAN ya dawo da kanshi yace,. "Ka rok'i ALLAH ma akan ka bar garin nan lami lafiya ba tare da ka janyo anyi cikin macizai ba" Lawi ya mike ya fito shima tare da dafa kafadarshi yace,. "Stof jocking my man WALLAHI da gaske nike son yarinyar, don ALLAH ta wace hanya ka ga zanbi in shawo kan matsalar??" Safwan da kanshi yake duk'e ya d'ago da jajayen idanuwanshi ya d'orasu kan Lawi yace,. "To be sincere Abokina wannan yarinyar ba ajinka bace, kuma kasancewar iyayenta gidadawa ne zaka sha matuk'ar wuya idan kace ala dole itace zaka aura, shawara d'aya zan baka akan ka bi komi a hankali in matarka ce zaka aureta komi tsanani kuwa, amman idan ka tsaurara to garin neman gira zaka fa rasa Ido, baka ga auren baka ga Mutuncinka da mutane suke gani a garin nan, don yanzu kafin aje ko'ina ma shi kanshi Maigarin zai ga kamar baka ji maganarshi ba, tunda har ya fad'a maka gaskiyar abunda Mahaifin yarinyar yace, tare da guje maka aibin da ke tattare da auren yarinyar" Lawi ya yi shiru sannan yace,. "Wai Abokina ko dai sace yarinyar nan zan yi ne?, Idan muka yi aure na dirko mata ciki acen sannan in dawo masu da ita, nasan izuwa lokacin dole ne ma su hak'ura su janye tsattsauran ra'ayinsu akan kin aurena" SAFWAN ya bishi da wani kallo baki sake yace,. "Lalle baka cikin hayyacinka to bari kaji kasan ALLAH WALLAHI duk inda ka kaita ka b'oye Ni sai na zakulota na dawowa da iyayenta 'yarsu, don tun wuri ma ka ajiye wannan bak'in kudurin naka tun kafin zuciya ta debeka ka aikata abunda daga baya zaka zo kana danasani, Ni in bancin k'ulafuci irin naka ma me aka yi aka yi wannan bak'ar magen?? Wadda ita kanta har yanzu bata san me ye duniyar ba, to kaje ka aikata duk abunda kake so tunda har ni baka d'aukeni Abokin kwarai Mai baka shawarar gari ba" Yana kare fad'ar maganar ya tafi abunshi ya bar Lawi da tunanin zuci mai cike da neman mafita akan matsalar auren Dijen Baffah da Inna Hasiya kanwar Usmanu Mijin Hansai. *** A bangaren Dije kuwa tsawon kwana biyu ta daina kula kowa a gidan, don Baffah yace da ita bazata sake zuwa Makarantar bokon ba, shiyasa ta k'ara shiga kunci kullum ta shige d'aki tanata kukanta har sai INNA ta fara balbalin fad'a sannan ta yi shiru, don tun tana yin banza da ita har ta fara shiga damuwa akan kuncin na Dije, don Baffah in ya fita gonarshi sai gaf da magriba yake dawowa, kuma da ya dawo yake yin arwallah ya nufi masallaci sai isha yake dawowa, sannan shigowarshi gidan ke da wuya zai fad'a wanka don ko da zai kammala sauran abubuwan tuni Dije ta yi bacci, shiyasa baya sanin halin damuwar da take yini da shi ganin hakan yasa Inna ta fara yi masa korafi akan sabon sauyin da Dijen ta shiga, cikin tashin hankali ya nufi d'akin Innar inda take ta baccinta tana sauke ajiyar zuciya, cikin tausayi Baffah ya kalli Inna yace "Gobe idan ALLAH ya kaimu na amince ta koma Makarantarta amman da sharadin bata ba wannan yaron, idan ta amince shikenan don shima zan je in fad'awa Maigari ya ja masa kunne sosai akan 'yata, don kada in zo in saki baki ya yi mani sakiyar da babu ruwa don Yan birnin nan ba kunya ce da su ba" Yana kare maganar ya juya zai fita cikin damuwa yace,. "Ni dai WALLAHI ALLAH banji dad'in zuwan bak'in nan garinmu ba, haka kawai muna zamanmu lafiya su zo muna da wani tsirfin tsiya" Inna ta bishi baya cikin sanyin jiki tana k'ara zayyana masa irin kuncin da Dijen ta saka kanta akan rashin zuwanta Makarantar. Aiko tun Asuba Inna ta yiwa Dije albishir da zuwanta Makaranta, cike da d'oki Dije ta je ta d'ora ruwan zafin wanka ta sullo wankanta tas, ta shirya cikin uniform d'inta da suke cikin rigar filonta da kullum take matashin kai da su, sunsha karin guga fess da su sai wasar Baki take yi ta nufi d'akin Baffah da ke zaune yanata laziminshi da ya zame masa jiki kullum, ta durk'usa har k'asa cikin wani sabon ladabi tace "Ina kwana baffah" Ya kalleta cikin jin dad'in ganin yanayinta yace,. "Lafiya Lau Makarantar za'a je ne?" Dije ta washe baki tace,. "Eh nagode Baffah da ka yafe man WALLAHI baka ji yanda naji ba kwana biyu da bana zuwa, har mafalkin Makarantar nake ta yi" Baffah ya tashi daga kishingidar da yake ya zauna da kyau yace,. "Idan har kina son in barki kici gaba da zuwa to ki yi man alk'awali ba ki ba sake kula Yaron nan, idan kuma kika kuskura na ji ance an ganki da shi to ko ki sani ba ki ba sake zuwa ko k'ofar Makarantar nan, in kin amince shikenan ki tashi kije idan kuma kinga ba zaki yarda da hakan ba to ki je ki cire tufafin ki yi zamanki gida tunda ba da karatun za'a tambayemu cikin kabari ba" Dije ta yi saurin fad'in "Na yi maka alk'awali Baffah in kuma na sab'a ka ce man shegiya" Baffah ya yi saurin runtse idonshi yace,. "Kinga haukarki ko to kar in sake jin kin Kira kanki da suna shegiya kinji ko??" Ta d'aga kanta alamun gamsuwa . Akafta😝 D/AUTA CE✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *COMMENTERS GA JINJINAR BAN GIRMA👍🏻* *Lamba ta 20* Sai da ta yi masa alk'awali sannan Suka yi sallama ta fito ta nufi Makaranta, tana tafe tana wasar baki musamman idan ta tuno watarana ita Likita ce, sai wassafa yanda zata dinga soke Mutane take yi suna ihu, ita kad'ai sai faman murmushi take yi bisa hanya har ta isa makatantar, inda ta taradda Malam Safwan zaune bakin barandar ya duk'e kanshi ya lula zuzzurfan tunani mai zurfi,don har ta kawo wurinshi ta gayar dashi bai ma san ta yi ba, ganin ya kyaleta yasa ta murgud'a masa Baki ta wuce abunta, tana gaf da shigewa class ne ya ankara da ita aiko cikin sauri ya d'aga murya yace "Hey!" Taso ta share amman dai ta waigo don tana da tabbacin da ita yake, amman duk da haka sai da ta nuna kanta tace "Ni?" Ya d'aga mata kai sannan ta dawo zuciyarta cike da tsoron laifin me ta yi masa kuma?, Aiko tana zuwa gabanshi zata yi kneel down ya yi saurin girgiza kai yace,. "No! no!" Dije ta mik'e cike da mamakin sauyawarshi ta kura masa kallo sai da ya yi shiru sannan cikin yaren hausa yace,. "Me ya hanaki zuwa Makaranta kwana biyu" Dije ta zaro ido waje saboda tsananin mamakin da ya bata bakinta yana rawa tace,. "Malam ashe daman cen ka iya hausa?" Hararar da ya maka mata ce yasa ta yi saurin rufe Bakinta tace,. "Sorry ser" Ya sake maimaita tambayarshi Dije kam nan take ta bata fuska tace, "Baffahna ne ya hanani zuwa" Cike da mamaki Safwan ya yi saurin cewa,. "Saboda mi?" Dije wasu hawaye suka gangaro mata tace,. "Saboda Abokinka yace yana so ya aureni shine ya hanani zuwa Makarantar, yanzu haka ma sai da na yi masa alk'awalin bazan sake kulashi ba sannan ya barni na tafo, don ALLAH Malam ka ce dashi ya yi hak'uri ya daina yiman magana har sai na kare Makaranta, don WALLAHI ina son karatun bana son a hanani zuwa kuma gashi ma ina son ya kaini Makarantar Likitancin da yace zai kaini" Ta k'are maganar cikin zubowar wasu ruwan hawayen, Safwan ya yi shiru yana nazarin maganganunta sannan cen ya d'ago da kanshi ya kalleta cikin sanyin jiki ya ce "kina so ki yi karatu mai zurfi bayan kuma kinsan hakan ba al'adar garinku bace, ko akwai wadda ta tab'a zuwa Makarantar gaba da primary a garin nan?" Dije ta girgiza masa kai tace,. "Ko d'aya duka aure ake masu, yanzu haka ma cikin kawayena Hansai da Ladiyo da Jummala duk suna da Miji da an tashi aure kawai za'a yi masu" Safwan ya yi saurin zaro ido yace,. "Cabd'i jam! To ke ba'a yi maki Mijin bane?" Ta rufe fuskarta tace,. "Ai Ni ba wanda ma ya tab'a cewa yana sona sai mutum biyu" Cikin kureta da kallo tare da had'e fuska yace,. "Su waye Mutum biyu din?" Dije ta rufe fuskarta tace,. "Kunyar fad'a nake ji WALLAHI" Shi kanshi gano wannan firar bata dace da Malami da dalibi ba yasa yace,. "Ok to je ki shiga class amman Kika kuskura naji kince da wata na iya Hausa I will purnish you" Dije ta dafe bakinta tana k'umshe dariyar da ta zo mata tace,. "Ba zan fad'a ba ai" Safwan yana shirin sake yi mata magana ne ya hango Lawi zai shigo Makarantar ya yi saurin fad'in,. "Oya go to your class" Dije ta tafi tana ta k'umshe dariyarta saboda gargadin da yayi mata ya bata dariya, don ganin renin wayon nashi ma ya yi yawa ashe ma ya iya hausa amman kullum yake ta zuba masu zallar turanci, sannan zagin da tasha yi mashi da Hausa ita da su Lanti ashe duk yana ji amman yake yi kamar bai san me suke fad'a ba, sai dai laifi kad'an zai sa ya yi ta harararsu yana muzurai, k'arshe ma haka zai k'are karatun ba tare da sun fahimci komi ba. Lawi kam tun daga nesa da ya hango Dije yake ta sauri sai gashi kafin ya k'araso har ta wuce, cikin damuwa ya isa wurin Safwan ya zauna ya na bin class d'in su Dijen da kallo, Safwan ya yi masa wani kallo ya yi wani mere yace "To yarinyar nan dai ka d'aga mata k'afa don yanzu ta ke sanar dani Mahaifinta ya hanata zuwa Makaranta ne saboda kai, idan har da gaske kana sonta to ka barta ta yi karatunta, don an gargad'eta a gida duk ranar da aka sake ganinta da kai za'a cireta daga school d'in gaba d'aya" Lawi ya yi saurin fad'in "Innalilahi wa'Inna ilairraji'un kai wannan bala'i da me yayi Kama?? WALLAHI kwana biyun nan da ban ganta ba jinsu nayi tamkar shekara biyu, Abokina ka taimaki rayuwata WALLAHI mutuwa zanyi idan har ban auri yarinyar nan ba" Safwan ya yi saurin mik'ewa tare da buga wani uban tsaki ya barshi a nan ya shige Ofishin Malammai, Lawi ya bishi da kallon mamaki sannan ya yu shiru yana nazarin mood d'in abokin nashi akan matsalar, da kullum baya bashi goyon baya akan soyayyarshi da Dijen, asali ma sai Kara dakushe masa karsashi yake yi kullum safiya, a ranshi yace _"shin wai shi baya da imani ne da har ba zai taimakeni na samu abunda yafi soyuwa agareni ba?, Ko don shi har yanzu bai San zafin son bane?"_. Ya furzar da iska mai zafi a bakinshi ya mike ya nufi office d'in ranshi a b'ace, saboda damuwowin da suka yi masa yawa ga rashin goyon bayan Safwan akan masoyiyarshi Dije, ga kuma wata bakuwar matsalar da aka kunno masa da ita, don rashin magana da Dije a wurin ba k'aramin purnishmen ne aka bashi ba, yarinyar da har gizo take masa a ido baya da wani mafalki a Yan kwanakin nan sai nata, lokaci d'aya a rabashi da ita irin haka ai an ci da zalinshi. Ranar har aka tashi ba wata walwala ko wata huld'a mai k'arfi da ta shiga tsakanin Abokan biyu, abun takaicinma lokacin da aka tashin k'iri K'iri Dije ta ki tsayawa ta ji uzurin Lawi da ke son yin magana da ita, saboda tsoron a ganta aje a fad'awa Baffanta Safwan kam ba k'aramin dad'i hakan ya yi masa ba, ya sake girmama lamarinta saboda ganin ashe rashin kunyarta da sauk'i tunda har tana jin maganar iyayenta. Lawi kam ko dakinsu bai nufa ba ya isa wurin Maigarin cikin damuwar da ta kasa boyuwa akan fuskarshi, Maigarin ya kalleshi cikin tausayawa don yasan labarin gizo baya wuce na koki, amman duk da hakan sai da ya wayance yace dashi "Yarona lafiya Na ganka haka? ko wani abun ne ya faru cen Gida? " Lawi ya kara sunne kai yace,. "A'a Baba akan dai matsalar nan ne" Maigarin ya ce,. "Wace matsala Kuma? Ko ta Yar Gidan Malam Sanda?" Lawi ya d'aga kanshi yace,. "Eh ita to yanzu abun ya Kara rikicewa saboda ko magana ma an hanata tsayawa ta yi dani" Maigarin ya yi shiru sannan yace,. "Ka yi hak'uri yarona Ni zan ga Malam Sanda duk yanda muka yi zan neme ka" Lawi ya mike tare da yi masa godiya ya yi d'akinsu, zuciyarshi cike da takaicin bala'in da ya janyowa kanshi yana zaman zamanshi. Maigarin kam bai yi k'asa a gwiwa ba dakanshi bayan magrib ya yi tattaki tare da mukarrabanshi suka nufi gidansu Dije, cike da mamaki Baffah'n ya shimfida masu tabarma suka zauna tare da yi masu sannu da zuwa. Bayan an k'are gaggaisawa ne Maigarin ya yi gyaran murya yace,. "Malam Sanda nasan zaka yi mamakin abunda yasa na yo tattaki zuwa wajenka?, To ba komi ba ne akan matsalar Bakon yaron cen ne da Yar wajenka Dije, a zahirin gaskiya yaron nan dai na gano ba k'aramin so yake yi mata ba, shiyasa nace bari in zo in jaddada maka zancenshi da muka yi a kwanakin baya, shin har yanzu kana kan bakanka akan bazaka baiwa mutumen nesa yarka ba Koko ya abun yake?" Baffah kam Nan take wani sabon b'acin Rai ya ziyartoshi amman cikin dariyar yake yace,. "Ranka shi dad'e ina mai jin kunyar sanar da Kai cewa na yiwa Dije Miji, kuma insha ALLAHu wata mai kamawa Zan auradda Dije ga Bala dan Gidan Mariganyi Mamman jikan Inna Duduwa" To fa rigiji Gabji😳 lalle akwai kwacagiya😝 Akafta🤣 D/AUTA CE✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *MUTANEN DIJE K'ARANGIYA INA GAIDA KOWA ALL ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU👍🏻* *Lamba ta 21* Gaba d'aya jikin kowa na wurin ya yi sanyi sai cen Maigarin ya yi jarumtar fad'in,. "A komi ALLAH Ubangiji yasa hakan shine alkhairin" Ya yunkura ya mike tsaye yana saka talkaminshi yace da abokan tafiyarshi,. "Ki tashi muje sai mu yi masa bayani idan har ALLAH zai sa ya fahimcemu" Haka suka bar k'ofar gidan kowa jiki ba kuzari saboda ganin duk girman Maigarin ya zo neman abu wajen Baffah amman ya rufe idonshi ya kasa yi masa wannan alfarma, shi Kam Baffah ko a jikinshi hasali ma hankalinshi kwance ya nad'e tabamar ya shige cikin gida, inda kai tsaye ya kira Usman ya ce ya je ya kira masa Balan Duduwar, sannan ya shige d'aki abunshi Inna ta bishi da kallon mamaki jin aiken da ya yi na neman Bala, cikin sanyin jiki ta bishi d'akin tace "Malam ALLAH dai yasa lafiya?? Naga Maigari ya zo wajenka kuma ga shi na ji yanzu ka ce a kira Bala" Baffah ya yi saurin fadada fuskarshi da murmushin yace,. "Abunda kike so ne za'a yi maki tunda na hango hakan shine mafita akan matsalolin da suke son kunno man kai cikin gida" Inna ta bishi da kallo Baki sake tace,. "Ka yi man bayani yanda Zan gane Malam" Baffah ya fito d'akin tare da d'auko buta ya fara sabuwar arwallah har ya k'are ba tare da yace kanzil ba, sannan ya mike ya kalleta yace "Wata mai kamawa Zan yiwa Dije aure da Balan Duduwa tunda har yana sonta" Inna ta zaro ido waje tace,. "A'a Malam gaggawa fa aikin shedan ce, ka bari abi komi a hankali kar a zo ayi abu don neman mafita wata sabuwar matsalar ta bullo" Baffah ya kalli Inna shekeke sannan ya nufi hanyar fita yace,. "Alkhairi muke fata kuma shi zamu gani" Ya fice ranshi a b'ace Dije da ke k'ofar Inna ta k'araso wajen da Innar take tsaye cikin kokwanto tace,. "INNA naji Baffah yana zancen aurena da Balan Duduwa da gaske yake yi ko wasa???" Inna ta maka mata wata Uwar harara ta nufi madafi tace,. "Ki jira idan har ya dawo sai ya amsa maki tambayar da bakinshi tunda ai ba Ni kika ji na fad'a ba" Dije ta ja buta ta yi bayi tana gungunin cewa,. "Ai na rantse da ALLAH ni Malam Danbirni zan aura cabd'i! Haka kawai in aureshi ya hanani zuwa Makarantar koyon Likitanci hum! lalle ma ko" ** Baffah Kam tare da Bala da Usman suka yi sallahr Isha sannan suka garzayo gida, Baffah yasa Usman ya shimfida masu tabarma a zauren gidan, sannan yasa aka kawo masa tuwonshi ya yi wa Bala tayi Bala cike da jin nauyin surukuta yace,. "Alhmdllh" Baffah ya kalli Balan yace,. "Naji labarin cewa kana son Dije ko?" Bala ya sunne kai cike da jin kunyarshi, Baffah ya ce "Magana zamu yi mai Muhimmanci saboda auradda ita nike son yi idan har kashirya aurenta to ka fito da karfinka Ni zan aura maka Dije duk lokacin da ka shirya" Cike da tsananin farin ciki yace "Na gode Baffah" Balan kam bakinshi ya kasa rufuwa saboda tsabar murnar ganin nesa ta zo masa kusa, cikin jin nauyi ya nunawa Baffah amincewarshi tare da godiya akan wannan karamci da ya yi masa, sannan ya yi masa alk'awalin zai turo iyayenshi kurkusa ayi komi a gama cikin kankanin lokaci. Haka suka rabu zuciyarshi cike da farin ciki uwa uba ma da Baffah'n ya bashi damar ya fara zuwa zance wajen Dijen don su fahimci juna kafin lokacin auren ya zo. Baffah kam bai shigo Gida ba har sai da ya tabbatar Dije ta yi bacci don ba ya son ta janyo abunda zai sa ya jibgeta a banza, don tunda ya dawo masallacin ya ga yanda ta makure jikin gini tana sharar hawaye yasan akwai magana, don baya raba d'aya biyu yasan taji zancen aurenta Balan shiyasa, sai dai a mamakinshi ko da ya shiga cikin Gidan ya taradda ita idonta biyu jikin ginin har lokacin tana gyangyadi, jin shigowarshi yasa ta yi saurin mik'ewa ta nufoshi tana fad'in "WALLAHI Ni Baffah ban son Bala ba zan aureshi ba" Baffahn ya yi mata wani kallo yace,. "Baki sonshi wa kike so??" Dije ta yi saurin kamo gefen dankwalinta tana wasa dashi tace,. "Ni Baffah ba wanda nike so WALLAHI Ni gurina kawai inje Makarantar gaba in zama likita" Baffah ya zaro Ido waje yace,. "Au shirmen ya kitsa maki kenan ko? To ai kwanan nan zanyi maganin abun, ai WALLAHI ko bani so dole ne in auradda ke cikin gaggawa tun kafin su kaini ga maganar banza" Yana kare maganar ya shige d'akinshi zuciyarshi cike da jin tsoron sharrin wad'annan bak'in Yan bokon ga Yar guda gudar yarshi Dije, wadda ko kuda baya so ya tab'a masa ita matuk'ar yana da ikon hakan. Dije kam ranar kwana ta yi tana sharbar hawayenta saboda sam sam ita bata son auren kacakam ballantana auren Balan, idan son damunta ne ace ta yi karatu mai zurfi ta zamo abar alfakhari cikin kauyensu, amman ina kash tasan gurint sam bazai tab'a cika ba muddin ta auri Bala, don dama ace Lawi ne da zata sakawa ranta cewa gurinta zai cika komi daren dad'ewa. Ko da Safiya ta waye da d'ar d'ar ta shirya don ta zaci Baffah'n ya hanata zuwa Makaranta, amman sai gashi bai hanata ba har da yi mata ALLAH ya kiyaye, saboda yasan Shirin da yake yi akan auradda ita d'in cikin kankanin lokaci. Dije sukuku ta zo Makarantar Lawi ya so ya yi mata magana amman tuno irin gargadin da Maigarin ya yi masa akanta yasa ya yi k'ok'arin kawar da kanshi gareta, don ko da aka tashi ma sai da kowa ya watse Makarantar sannan shi ya nufo masaukinsu, don gaba d'aya ma shi zaman garin ya gundureshi jin yake yi kamar a saman kaya yake, Alla Alla yake yi su kammala service dinsu su bar Garin, don akan hakan ma har abokin nashi ma sun fara zaman doya da manja dashi, gashi shi ma Maigarin yace ya zame hannunshi idan shi zai iya ga fili ga mai doki. ** Cikin wata d'aya aka kammala neman auren Bala da Dije inda aka kawo komi na auren Rana kawai ake jira ta zo a sha shagali, izuwa lokacin Dije ta saduda dolenta saboda ba tirjiyar da bata yi ba akan auren amman Baffah'n kam ya kafe ba gudu ba ja da baya, don ita kanta Innar ganin akan auren Dije zasu samu matsala da Baffah'n shiyasa ta zubar da makamanta ta fara shirye shiryen auren Dijenta. Ana saura sati d'aya bikin Dije suka zana jarabawar kammala primary, kowa sai murna yake yi inda shi Kuma Lawi yake cike da bak'in cikin rasa Dijen da yayi, Safwan kam ko kad'an bazaka gano yanayin da yake ciki ba, asali ma shi hankalinshi kwance yake ta d'aukar photuna da su Dije da sauran yaran Makarantar, Dijen ma ba wata walwala akan fuskarta don kuwa a kallo d'aya zaka gano sauyawar da ta yi, don kuwa gaba d'aya ra zabge sai Ido da karan hanci don izuwa lokacin har wata natsuwar dole ta ziyartota, duk nacin da Lawi ya yi akan yana so ya yi sallama da Dije bai sami wannan damar ba, saboda ganin yanda Safwan ya keta hidimar d'aukar pic's d'inshi da su Dijen. Sai da aka gama ne ya samu ya yi wa Dije sallama tare da mika mata wata envelope idonshi jawur tamkar ya yi kuka, don shi ya kuduri aniyar ba zai jira ayi auren Dijen da shi ba, da nufin tun da sassafe ya had'a inashi inashi ya bar garin, don shi Safwan ya ce ba ranar zai tafi ba ya yi gaba shi zai biyoshi ta baya. Dije tana kuka suka yi sallama da Lawi ta tura envelope d'in da ya bata a jaka ta nufi gida,. Kai tsaye ta shige toilet ta bud'a envelope d'in saboda ta matsu taga me ke ciki gashi bata son Inna ta gani. Aiko sai gashi tana budawa taga wasu Yan hannu da zobe masu bala'in kyau sannan da bandur d'in kud'i sababbi kal yan d'ari bibbiyu, Dije ta zaro ido tare da goge hawayenta cikin sauri ta rungume kud'in da sauran kayan ta fashe da kuka gwanin ban tausayi, sai dai ita bata san duk abunda take yi Inna tana hankalce da ita, shiyasa lokacin da taga ta dad'e bayin ta biyo sawunta sai ko gashi ta ganta durk'ushe kasan bayin tana ta kuka, cikin tausayawa ta isa wurinta ta tadata Dije ta yi saurin yunkurin b'oye kud'in sai ga takardar kud'in ta yage kud'in sun zubo shaaaa! A k'asa. Ku yi hakuri da kuskuren da kuka gani yau ban yi editing ba🤦🏻‍♀️ Akafta😉 D/AUTA CE✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *MUTANEN DIJE K'ARANGIYA INA GAIDA KOWA ALL ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU👍🏻* *Lamba ta 22* Daga Inna har Dijen gaba d'aya zaro Ido suka yi suna kallon kud'in, cikin firgici inna ta yi saurin fad'in "Dije me nake Shirin gani yau Ni Hasiya?" Dije ta yi saurin duk'atawa tana ta tattara kud'in har ta kammala sannan ta mik'awa Inna tace,. "Karb'i kyauta ce aka bani" Inna ta tak'i karb'ar kud'in ta tsuke fuska tace,. "Gaya man duk fad'in garin nan waye mai arzik'in da har zai iya baki wad'annan mak'udan kud'in sababbi k'al da su haka?" Dije ta saka hannu ta share hawayen da har lokacin basu daina zubo mata ba tace,. "Malaminmu D'anbirni ne ya bani wai tashi gudunmuwa ce yace ko Daddawa a siya man" Inna ta maka mata wata jar harara tace,. "To WALLAHI Ni ba ruwana in har Baffah'nki ya ji wannan magana,sawunki a likkafa ki tattara kayanshi da kud'inshi ki je ki Kai masa salun alun ba wanda ya ji ba wanda ya gani" Dije ta sake fashewa da wani sabon kuka tace,. "Ni dai Inna ina son awarwaron da zoben, don ALLAH ki bari in mayar masa da kud'in kawai don ALLAH Inna" Ta k'are maganar cikin marairecewa gwanin ban tausayi, Inna ta karbe kud'in da awarwaron da zoben ta janyo hannunta suka fito tana janye da hannun Dijen har d'akinta, sannan ta samo wata leda baka ta zuba kud'in da kayan ta k'ulle jabau! Ta mika mata tare da had'e fuska alamun ba wasa tace,. "Karb'i kije ki mayar masa da kayanshi yanzun ba sai anjima ba" Dije ta karb'a har ta fito ta dawo tace,. "To Inna ki bari in cire kayan Makarantar in saka na Gida" Inna ta taso mata kamar zata daketa tace,. "Bazan bari ba nace ba za'a bari ba zaki je ko sai na sab'a maki ne yanzu Nan??" Dije ta fice tana tafe tana gunguni har ta kai wani lungu ta bud'e ledar ta cire awarwaron da zoben ta k'ulle ledar ta nufi gidan Inna Gambo, sai da ta samu wani waje cikin dabara ta b'oyesu d'akin Gambon sannan ta fito ta nufi gidan Maigarin, sai dai rashin sa'ar da ta taka tun kafin ta isa daga nesa Maigarin da ya hangota ya bada umurnin a hanata zuwa wurinshi, saboda yaci alwashin daga Dijen har Baffah'n ba zai sake shiga cikin shirginsu ba, sai dai ita kam ta nace akan ita bazata koma ba don wurin Malaminsu ta zo ba wurinshi ba, Maigari kam ganin rigima zata b'alle ne a tsakanin Dijen da wani yaronshi yasa yace a kyaleta, kai tsaye ta nufi k'ofar d'akinsu Safwan ta fara rafka sallama sai dai ta yi har ta gaji ko sau d'aya bata ji an amsa mata ba, cike da k'unar rai ta fad'a d'akin da k'arfinta sai dai wayam ba kowa d'akin, tana k'ok'arin fitowa ne ta ji ta yi karo da mutum da sauri ta ja baya tana sosa goshinta da kan Safwan ya buge, Cikin tsoro ta rab'a ta gefenshi ta fito jikinta yana rawa ta fara fad'in "Don ALLAH ka yi hak'uri wajen Malam na zo na yita sallama banji an amsa ba shiyasa na shigo in ga ko lafiya" Safwan ya maka mata wata Uwar harara sannan ya rungume hannu a K'irji ya ce,. "Lafiya kike nemansa? ba naga kunyi sallama ba ko Mahaifin naki ne ya amince zai bashi aurenki ne shiyasa kika zo yi masa albishir? " Dije yanayin fuskarshi da tambayoyinshi sun sakata daburcewa, cikin rawar murya tace "Kyautar da ya bani ce na zo kawo masa kayanshi sabida gidanmu ance bazan karb'a ba" SAFWAN ya yi wani mere yace,. "Sai Kuma aka yi rashin sa'a shi ya bar garin gaba d'aya ya koma gida, cen zaki bishi garinsu ki kai masa ko yaya?" Dije ta zaro ido tace,. "WALLAHI na koma da su sai sun janyo man gagarumar matsala, don ALLAH ka karb'a ka ajiye masa idan ka koma sai ka bashi abunshi kace na gode sosai ALLAH ya had'a fuskokinmu a aljannah, kuma ka yi masa albishir insha ALLAHu nice Matarshi a Lahira idan munje cen" SAFWAN ya galla mata wata jar harara da jajayen idonshi da suka rine lokaci d'aya yace,. "Zaki bar wajen nan ko sai kin janyo na karairayaki a kaiwa kwad'ayayyen angonki sauran k'asusuwan???" Dije ta yi saurin ja da baya tace,. "Don girman ALLAH ka karb'a WALLAHI dukana za'a yi gidanmu idan na koma da su" Safwan ya buga mata wani uban tsaki ya shige d'akinsu tare da fad'in,. "Idiot!!!" Dije kam sanin idan ta koma da su gida akwai matsala ta lallaba ta jefa ledar kud'in cikin d'akin ta zank'ara da gudun tsiya, Maigarin da mutanenshi suna ganin fitowarta da gudu suka bita da kallo, Maigari ya mike tsaye jikinshi yana rawa yace "Bari in je in dubo yaron Mutane kada ta kasheshi mu shiga uku, tunda shi har yanzu bai tashi barin garin ba duk da kyamar garin da yake yi" Sauran mutanen su ka biyoshi baya har zuwa d'akin sai dai ganinshi da suka yi kwance yana latsar waya ne yasa hankalinsu ya kwanta, sannan suka koma suna ci gaba da yi da Dije da Baffah'nta, inda wasu suke ganin laifinshi akan abunda ya yi wa Maigarin yayin da wasu suke ganin hakan da ya yi shine dai dai. Bikin yana saura kwana Uku aka gyarewa Dije d'akinta ram! gidan Inna Duduwa,Wanda Balan ya ci gado ga Mahaifinshi da ya mutu, don asalima d'akin Mahaifiyarshi ne da ta yi zama ciki lokacin da Mahaifinshi yana raye, don yanzu haka tana wani k'auye tana aurenta da yaranta biyar bayan Balan. Biki sai kankama yake yi Bala da abokanshi da kawayen Dije Su Jummala sai shagalin bikinsu suke ta yi, don ana saura kwana biyu ne aka shirya wani bikin tauri a k'ofar gidansu Balan, inda yan tauri suka baje sai nuna k'warewarsu suke yi, sun burge iya burgewa in da bikin wasar taurin ya d'auki lokaci har cikin dare anata fafatawa da zaratan jaruman Yan taurin. Ko da safiyar JUMU'A ta waye aka shiga hada hadar hidimar d'aurin auren a k'ofar gidansu Dijen, don tun kafin aje masallacin JUMU'A aka fara shimfida sabbin tabarmomi da ledar buhu manya manya aka malale k'ofar gidan ko'ina, ko da aka ta so mutane ta ko'ina sai b'arkowa suke yi zuwa k'ofar gidan Baffah'n Dije Malam Sanda, Baki na nesa da na kusa Kai har na manyan biranen da Baffah yake abun arzik'i da su sai da ya gayyatosu zuwa daurin auren shalelenshi Dijengala. Cikin bak'in da ake zuwa daurin auren har da wasu fararen dattijai na hango tare da motocinsu na alfarma, inda kai tsaye hankulan mutanen k'auyen ya karkata kansu saboda alamun hutun da ya bayyana a jikinsu, nan take za'a banbancesu da mutanen garin saboda kamarsu daban da take ko da ko a cikin duhu. Wani Dan'uwan Baffah'n shine zai yi waliccin Dije, yayin da wani kanen Baban Bala zai karb'arwa Bala auren Dije, soron Gidansu Dije nan ne aka yiwa wad'annan bak'in alfarmar masauki akan saman sababbin tabarmin da Baffah'n ya tanada don kawai wannan Rana. Kai tsaye Liman ya nemi ganin waliyyin Ango da waliyyin Amarya duk suka hallara, Baffah kam bakinshi kamar gonar auduga saboda tsabar farin cikin ganin wannan Rana mai d'inbin tarihi a wajenshi da Dijenshi, saboda auren Dijen yana daga cikin abubuwa masu muhimmanci a rayuwarshi, don yasa a ranshi ko yau ya kwanta dama shi gurinshi ya cika tunda har ya auradda 'yarshi guda mace da ALLAH ya albarkaceshi da ita a doron duniya. Kafin kace me sai ga Liman ya fara hud'ubar aure cikin ikon ALLAH sai jin aka yi mai sanarwa fad'in auren ya fara shelar shewa an d'aura auren NANA HADIZA wadda aka fi sani da suna DIJE tare da Angonta MUHAMMADU SAFWANU JABB'I YOLA. Durum! dum! dam! dum! dum! Haka naji gaban Baffah yana ta luguden fad'uwa tare da sauran mutanen da ke wajen da ma ita kanta Dijen da ke bayi tana ta gurzar kuka na tashin hankali. Oh! oh! rigiji Gabji 😳 Ni kam taya aka haifu a ragaya😱🤔 HAJIYA DUDUWA kar ki zargeni don ni ma bansan komi ba🙌🏻🏃🏻‍♀️ Akafta👻 D/AUTA CE✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *LUV U SO MUCH ALL MY FAN'S💋Ina jin dad'in yanda ku ke kaunar book din Dije K'arangiya yawanku ya kai bazan iya lissafoku ba amman ku sani ina yinku sosai all my guys👍🏻* *Lamba ta 23* A zabure Baffah'n ya mik'e cikin sabon tashin hankali marar misaltuwa ya nufi wurin k'anen Mahaifin Bala yana fad'in,. "Daman shi haka sunan Balan na gaskiya yake?" K'anen Mahaifin Bala yayi d'an murmushin yak'e yace,. "An samu akasi ne Malam Sanda don ba da Bala aka d'aura auren ba" Baffah'n yana jin haka ya rud'e tashin hankalinshi ya k'ara k'aruwa cikin zaro Ido waje ya nufi wurin Liman ya shak'o wuyanshi yace,. "Da wa ka d'aurawa 'yata aure ne?? mugu azzalumi ai WALLAHI sai na yi shari'a da kai matuk'ar baka yi gaggawar kwance wannan mugun auren ba" Cikin masifa Baffah'n Dije ya shak'e Liman tare da kai masa wani azababben naushi mutane suka rirrik'eshi, kafin ka ce me wuri ya hautsine hargitsi tare da gutsuri tsoman jama'a, saboda ruwan bala'in da Baffah yake ta zubawa cikin d'aga murya yana hargowar cewa,. "Ai WALLAHI in duk garin nan za su taru a kaina bazan lamunta ba sai an kwance wannan bak'in auren da aka k'ullawa 'yata, Ni na haifeta kuma nace ba zan bada ba shin auren dole ne ko ita kad'ai ce 'ya mace a garin nan" Kai rigima fa tun ana ganinta a wasa sai ga abu tana shirin zama Babba, don kuwa Baffah sai zillo yake yi akan sai an barshi ya daki Liman, ana cikin rigimar ne sai ga sak'o daga Maigarin ya aiko duk kowa ya hallara a k'ofar gidanshi, Baffah'n kam har kowa ya tsiyaye aka barshi shi kad'ai k'ofar gidan yanata sauke ruwan sababi, Inna da sauran matan da ke cikin Gidan suka fito sunata bashi baki. Maigarin ya yi ta aikowa da sak'on neman Baffah'n ya kai sau uku sannan ya nufi gidan Maigarin har lokacin bai daina sambatun fad'anshi ba tamkar wani tabab'b'e sabon kamu. Abun mamaki k'ofar gidan Maigarin cike dank'am da d'an'adam maza da mata yara da mayan, sai dai kuma idan aka yi la'akari da yanda kowa yake son ya ji k'waf to hakan ba abun mamaki ba ne ba saboda ba Baffah'n kad'ai ba wasu da yawa suna son su san shin ta yaya aka haifu a ragaya?, Baffah'n da idanuwanshi da ba abunda ke cikinsu a lokacin face tsagwaron tashin hankalin da yake ciki jin yake yi gaba d'aya kowa haushi yake ba shi, yana muzurai zuciyarshi awa garwashin wuta saboda tsabar k'unar da take yi masa, ba tare da ya zauna ba ya tsaya k'ik'am yana huci tamkar wanda ke shirin kai naushi. Maigarin ya kalleshi da kyau yace,. "Malam Sanda ka zauna wannan taron ba don kowa aka yi shi ba face donka da kuma 'yarka Dije" Baffahn ya makawa Maigarin wata jar harara yace,. "Me kuma zan zauna a fad'a man yanzu? wanda ya wuce muguwar kullalliyar da kuka k'ulla kuka rufeni kuka baiwa 'yata Mijin da ba Ni na zab'a mata ba???, Sai na gani da Ni da ku wa ye yake da ikon auradda ita??don ku ma sani wannan auren k'addara mai cike da bak'ar manufar tamkar an kwanceshi an gama" Ya k'are maganar cikin huci tare da zabgawa Liman wata muguwar harara sannan ya yi kyafci, Maigarin ya k'ara cewa da shi "Da kasan irin ta'adin da 'yarka ta shirya idan anyi auren da wanda kake son ta aura d'in,to da baka tsaya gaban Mutane kana wannn shirmen ba, Kai godiya ya dace ace ka yi wa Mutane ba wai ka tsaya kana yi wa mutane karatun hauka ba" Aiko cikin nasara maganganun Maigarin sun saka Baffah cikin shakku da tsoron abunda zai fito akan wani aikin ashsha da Dije ta aikata ko take Shirin aikatawa, saboda yasani sarai ba son auren take yi ba haka ma yasan wacece ita da ayukanta, shiyasa cikin sanyin jiki ya ja k'afafuwanshi zuwa kusa da wad'annan manyan alhazawan bak'in fuskar ya zauna. Maigarin ya kalli Safwan da ke cikin manyan kayanshi da suka fito da zallar kyawunshi na Bafillacen usali, ya yi shiru na d'an lokaci sannan Maigarin yace da shi "Yi masa bayani da bakinka don ya san cewa muma ba ma cikin mutanen da zasu cutar da wasu ma bale shi" Safwan ya gyara zama tare da yin gyaran murya yace,. "To a zahirin gaskiya yau kwana shida da 'yarka ta iskeni har d'akina tana sanar da ni cewa muddin ba'a aura mata Abokina ba to ko ita duk ranar da aka kaita gidan Mijin da ka zab'a mata zata kashe kanta shi ma ta kasheshi, ta hanyar saka masa shinkafar b'era su ci dukansu su mutu murus daga shi har ita" Aiko ba Baffah'n ba har ta mutanen da ke wajen sai da suka fara salatin fad'in "Innalilahi wa'Inna ilairraji'un" Cike da fad'uwar gaba Baffah'n yace,. "Wannan k'azafi ne aka yiwa Dijeta don kuwa sam k'wak'walwarta bazata yi wannan tunanin marar amfani ba, dududu duka Dijen guda nawa ta ke? da har za'a ce tasan da wannan mugun tunani kai ina da sake WALLAHI" Ya mike tsam! da nufin barin wajen Safwan ya yiwa Bala wani kallo k'asa k'asa aiko sai ga Bala da mik'ewa tsaye yana fad'in,. "Baffah ka tsaya ka ji gaskiya ce ake fad'a don Nima bakina da nata tace dani duk ban janye aurenta da Ni ba sai ta kasheni ta kashe kanta, shine na zo wajen wannan Abokin wanda take so d'in na nemi alfarmarshi akan ya aureta Ni na hak'ura ko don mu shawo Kan matsalar, to Abokin ya tafi kuma an yi ta nemanshi a waya amman ba'a sameshi ba, shine sai shi wannan bawan ALLAHn ya karb'i tayin aurenta ga waliyyanshi anan su ne suka karb'i aurenta wajen Baba Buba" Cewa da D'an uwan Baffah'n Wanda shine ya bada auren Dijen ga Safwan, cike da tsananin firgici Baffah'n ya koma ya zauna dab'as yanata jero salati, tare da godewa ALLAH da har hakan bata kasance ba. Cikin zubowar wasu hawayen takaici ya kalli SAFWAN yace,. "A matsayina na Mahaifin Dije na rok'i alfarmar ka sauwake mata, don ko auren da Balan yanzu na janyeshi ba za'a sake zancenshi ba har duniya ta nad'e, ina yi maka godiya sosai na gode da taimakonka amman don girman ka taimaki rayuwata da ta 'yata ka sauwak'e mata yanzu ba sai anjima ba" SAFWAN cikin sauri ya duk'e kanshi tare da yin nazari na d'an lokaci, sannan ya d'ago da jajayen idanuwanshi da a take suka sauya zuwa tashin hankali, ya shafo dan k'aramin gemunshi sannan yace "Ka yi hak'uri Baba wasiyyar da Mahaifina ya bar man kenan lokacin da zai rasuwa, akan cewa duk runtsi kada in zamo mutum mai auri saki, ballantana irin wannan auren da ko ina ba'a je ba ya haneni da yin irinshi tun lokacin da yana ray...." Zancenshi ya katse ne saboda ji yo sautin Dije da aka yi tana fad'in,. "Ai billahillazi daga kai har Balan sai kun san da ni kuke zancen, Ni za ku ci wa amana ku yi man k'azafi da raina ban mutu ba??????" SAFWAN da Balan suka yi saurin kai kallonsu gareta, cikin sabon b'acin rai Safwan ya mik'e ya kalleta ido cikin ido yace "Ni zan yi maki k'arya?? Yanzu kina nufin kin manta lokacin da kika zo kina fad'a man maganar?" Dije ta fashe da kuka tace,. "Ai WALLAHI sai dai in aljanuna ne amman Ni kam bansan ma na yi ba" Safwan ya kalli Maigarin yace,. "Baba ai kasan lokacin da kuka je ganin ya nake bayan ta fita wurina aguje ko?" Maigarin yace,. "Tabbas hak'ik'atul amri ba ma Ni kad'ai ba har ma da su Malam Tsalha duk mun ganta da idanuwanmu lokacin da ta zo" Safwan ya ce "to ai a ranar ne take sanar dani wannan magana, har ma ta rok'eni ta ce da Ni don ALLAH ka da in fad'a har sai bayan sun mutun ita da Angonta, Ni kuma ganin zata je ta yi aika aika yasa lokacin da shi Balan ya zo neman Abokina ban ja da tsauri ba na amince a d'aura da Ni, saboda haka ina b'ukatar a bani Matata yanzu mu kama hanyar garinmu saboda mu yi saurin isa gida tare da Iyayena da suka yo tattaki tun daga Yola har wannan Gari domin kawai su karb'a mani aurenta" Baffah ya mike cikin wata sabuwar rud'ewa yace,. "Ni fa kam ba fa zan lamunta da aje man da 'ya ko'ina ba, shiyasa tun farko naki amincewa da auren Abokinka, ashe ban tsira ba na yi gudun gara ne na fad'awa zago" Ya k'are maganar cikin share wasu hawayen tashin hankalin rabuwa Dijenshi, cikin sanyin jiki Safwan ya kalli Dije da ke tsaye gaba d'aya ta rasa ma abun cewa saboda tsabar gaskiyar da ta yi mata yawa, sai canke canke ta ke yi wai ko dai da gaske tana da aljanun bata sani ba??don ita daga Balan har Safwan d'in bata san ta yi makamanciyar magana irin haka da su ba. Cikin d'aga murya Safwan yace,. ,"Ke!!" Ta yi saurin dawowa daga tunanin da ta lula tare da Kai kallonta gareshi, ba kunya Safwan ya rik'o hannunta suka yi nesa kad'an da mutane, sannan ya ja ya tsaya yana k'are mata kallo cikin mere yace "To bari kiji ni taimakonki zan yi idan munje in sakaki Makarantar secondary har ki zama babbar Likita, idan kuma ba zaki so ba ki fad'a yanzu sai in barki tare da Mahaifinki ya aura maki duk wanda yake so, tunda ke kin kasa hango irin taimakon da zan yi maki bale har ki shawo Kan Mahaifinki ya aminta da auren, bale har ki nuna masa ke zaki aureni kuma za ki bini garinmu duk in da nake ko don cikar burinki na zama babbar Likita" Dije ta washe baki tace,. "Da gaske Kai ma zaka sakani Makarantar likitocin???" Safwan ya ce "Eh amman idan har kin amince da aljanunki sun fad'i cewa sai sun kasheki sai sun kashe Bala, sannan kuma idan kin amince za ki bini garinmu" Dije ta yi saurin kallon hannunta da ya rik'a tace,. "Zan bika amman ya Zan yi da cikin da ka yi mani yanzun nan?" 🤣🤣🤣sai kunzo suna Dije ta samu ciki🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️ Akafta😝 D/AUTA CE🤝🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *MUTANEN DIJE K'ARANGIYA INA GAIDA KOWA ALL ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU👍🏻* *Lamba ta 24* Safwan ya zaro ido waje yace,. "Ci me...??" Dije ta bata fuska ta bar wajen tana ta yarfa hannun alamun k'yama ta nufi wurin Baffanta tace,. "Ka kwantar da hankalinka Baffah duk bayan kwana biyu Ni zan dinga zuwa ina dubaku kaji?" Ta k'are maganar tare da langab'e kai, Baffahn ya yi mata wani kallo sannan yace,. "Za ki yi man shiru ko sai na mazgeki?? k'iri k'iri kin sa komi ya lalace muna saboda bak'in sakarcinki, to ni Kinga tafiyata idan kin tashi ki bisu ku je bangon duniya ma in kina so" Yana kare fad'ar maganar ya mike fuuu! Yana kakkab'e riga ya nufi hanyar Gida, Maigarin ya kalli Dijen yace "Kin amince zaki bi Mijinki?" Dije ta d'aga kai tana yarfa hannunta da Safwan ya rik'e fuskarta a yamutse hawaye suna sauka tana saka d'ayan hannu tana sharewa, Maigarin yace "Alhmdllh" Sannan ya kalli IYAYEN Safwan yace,. "Ku yi hakuri bayin ALLAH daga yanzu zuwa gobe za mu shawo kan matsalar, insha ALLAHu tun da sassafe sai ku kama hanya,saboda haka na wakilici MALAM Sanda na amice idan kun tashi ku je da Dije amman da rakiyar mutum Uku zuwa hudu ta gefenmu, saboda mu ga muhallinku kuma mu san inda za'a kai 'yarmu Dije" Gaba d'aya suka amince da hakan, Maigarin ya kalli Bala ya ce, "Kai kuma sai ka nemi matar da duk kake so a garin nan ka aura tunda har hakan ta riga da ta kasance" K'anen Mahaifin Bala ya fito da kud'i ya nufi wurin Baban Ladiyo ya ajiye kud'i tare da rusunawa yace,. "A matsayina na k'anen Mahaifin Bala ina nemarwa Bala auren yarka Ladiyo, idan ka amince yanzun nan sai a shafa fatiha kowa ya shaida" Baban Ladiyo ya daburce ya kalli sauran d'inbin jama'ar da ke wajen yace, "Ni Malam Shehu na amince da na baiwa Bala auren 'yata Ladiyo jama'a ku sheda" Ladiyo ta zaro ido tare da barin wajen aguje ta nufi gida Mutane sai dariya suke yi mata, daga nan ba b'ata lokaci aka rarraba goro cikin dan kankanin lokaci aka d'aura auren Ladiyo da Bala, Baffah Kuma aka kai k'arshe akan za'a kwaso masa kayan d'akin Dije da aka jera gidan Bala a dawo masa da abunshi. Sannan cikin mutuntawa Maigarin ya sa aka shigar da Iyayen Safwan d'akinsu Safwaan d'in, tare da yi masu tarba da abinci mai rai da lafiya wanda Safwan ya sa aka tanadar masu tun kafin su shigo garin. Bayan sun kimtsa ne Safwan ya yi masu jagora har babban birnin garin ya sama masu masauki sannan ya juyo ya dawo k'auyen. Dije kam cikin firgici ta koma gida tana yarfa hannu saboda ganin take yi ta hakan ne macizan zasu zube ba za su yi nasarar shiga jikinta su taru ba balle cikinta ya yi k'ato, su Jummala suka biyota d'ii! a baya sunata jin ina ma su ne suka sami irin wannan damar, ta auren mutum d'anboko irin Safwan ga shi fari mai kyau da shi. Shigarta Gidan ke da wuya ta fara jiyo sautin Baffanta da ya ke ta zuba fad'a cikin d'aga murya, jiki a sanyaye ta isa d'akin nashi tare da rakubewa gefe tace "Baffahna don ALLAH ka yi hak'uri ka barni in je birnin nan, ka ga idan na yi kud'i na zama likita shikenan zan zo in ta fi da kai mu zauna da ku kai da Inna inda nake" Baffah ya maka mata wata Uwar harara da jajayen idanuwanshi yace,. "Ke dad'ina da ke sakarci shikenan tunda ya jaki gefe ya karanta Maki k'arya tare da yi maki wayon ya cusa maki ra'ayin biyarshi Ni ma hakan za ki yi man kenan ko?, To bari kiji aure dai an riga da d'aura ba kuma yanda Zan yi in kwanceshi da hannuna amman ki sani ba zaki tab'a biyarshi ba, na fi son abarman ke da igiyar auren saman kanki a gabana har k'arshe duniya aga in.........." "Da ko baka ji dad'i ba WALLAHI don wannan abin kunya ne ka ke so ka janyowa zuri'armu, saboda haka matuk'ar ina raye Ni ba za'a yi haka ina kallo ba" Maganar tsohuwa Inna Gambo ce ta katsewa Baffah zancen da yake yi, ta k'araso cikin d'akin tare da dogara sandarta Inna ta yi saurin shimfida mata tabarma ta zauna, Dije ta ja jiki ta isa wurinta ta fad'a jikinta ta fashe da kuka wiwi, Inna Gambo ta shafo kanta tace "Daina kuka ke ma zaki je ki yi aurenki kamar yanda kowace mace take yi a gidan Mijinta" Sannan ta d'ago da kanta ta kalli Inna da ke ajiye mata ruwa a sabon kwanon sha tace,. "Ku bar ruwanku bana sha tunda har kuke so ku hana abunda ALLAH ya k'addara, idan ba shirme ba wa ya isa ya ja da hukuncin ALLAH?? Yanzu ku ba ku gano cewa shi ALLAH ba'a yi masa dabara ba?? Kun hanata auren wancen sai gashi ba zato Wannan d'in kuma ya zama ashe shine Mijin, to gargadi na k'arshe gareka Sanda ka kiyayi yin ganganci da abunda ALLAH ya riga da ya tsara a rayuwar 'yarku, don daga Kai har ita Hasiya babu wanda yasan hikimar abunda ALLAH yake nufi da hakan, saboda haka ka bar Dije ta bi Mijinta ku bita da addu'ar fatan zaman lafiya, don sau da yawa abunda baka so shine alkhairinka abunda Kuma kake so sai ka ga ba'a cen alkhairin yake ba, don ba zaka gano hakan ba har sai ka bi diddigi ka sami abun ta k'arfin tsiya sannan ne daga baya zaka gano kuskuren da ka tafka, yo in banda rashin hankali irin naka Sanda ka dubi fad'in garin nan kaf! amman ace 'yarka d'aya ta tab'a samun wannan nasarar auren mutanen birni, ba ka ganin hakan ma wata baiwa ce???, To ka ajiye komi ka fuskanci gaskiya ka gano alkhairin da ke gabanka da sannu a hankali zaka gano manufar yin hakan" Baffah ya yi saurin share guntayen hawayenshi da suka cika masa ido yace,. "Ki yi hak'uri Inna na amince ALLAH yasa shine alkhairin kamar yanda kika fad'a, amman kam Dole ne in je inga inda za'a kaiman 'yata ko a ina ne ko" Dije ta mik'e daga jikin Inna Gambo tace,. "WALLAHI Baffah shi ma ya ce zai sakani Makaranta a cen birnin har in zama likitar" Baffah ya mike tsaye zuciyarshi cike da k'una ya fice don baya son ya furta wani abun da yayar Mahaifiyarshi da ta rage kaf cikin dangin iyayenshi taga ya yi mata rashin kunya, Dije ta bishi da kallo ta sake komawa jikin Gambo tace "Ni dai Gambo na fasa zuwa birnin tunda Baffahna baya so" Gambon tace,. "Ko shi ba so ne ba ya yi ba rabuwa da ke ne baya so, musamman da aka ce garin Mijin naki nesa ne sosai" Dije ta yi saurin fad'in cewa,. "To ai duk bayan sati biyu Sai in dinga zuwa ganinKu ke Gambo" Inna Gambon ta yi dariya tace,. "Ai ko shekara shekara kike zuwa kin yi sauri ballantana sati biyu" Dije ta yi saurin mik'ewa tace,. "Ai Ni kam ko wata bazan bari ayi ba Gambo, kuka zan ta yi masu sai an kawoni na ganku WALLAHI " Gambo ta yi mere tace, "yaro man kaza ke dai ki rik'e abunda na yi ta fad'a maki saboda aure yana da dad'i amman Kuma yana da wahala, don haka ba za'a ci ribarshi ba har sai an had'a da hak'uri, kiji ki ki sauraro ki gani ki yi Kamar baki gani ba, ki rufe kunnuwanki ruf ki raba idanuwanki da ganin abunda bai shafeki ba" Haka Inna Gambo ta dauki lokacin tana ta baiwa Dije shawarwarin da ita sam bata san ma'anarsu ba. Ko da dare ya yi Maigarin ya zo da kanshi ya yiwa Baffah bayanin abunda ake ciki, ba jayayya ya amince amman yace k'afarshi kafarsu sai yaga inda za'a kai masa Dijenshi. Inna da Baffah'n kwana suka yi sunata ja mata kunne tare da nasihohin da Suka sakata jin bata son tafiya ta barsu, Baffah ya k'arfafa mata gwiwa akan cewa ai tare za su, sannan hankalinta ya kwanta. Aiko Asubar farin ta nufi gidan Gambo ta d'auko ajiyarta tare da yi mata sallama, haka ta bi gidan kawayenta duk tana yi masu bankwana kamar ba Amarya ba, alhali cen gidan sai nemanta ake yi akan ta shirya kar su makara a tafiyar tasu kasancewar tafiya ce sosai a gabansu. Tare da rakiyarsu Hansai da su Jummala da Lanti har da Mune ta dawo gidan zuciyarta cike da tunanin jin wai Bala ya auri Ladiyo kawarta. Bayan sun shirya ne Safwan da Iyayenshi suka zo sake gaisawa da Baffah, ba k'aramin dad'i Suka ji ba da ganin sauyin da aka samu, don har cikin Gidan Baffah ya yi masu jagora Safwan ya gayar da Inna bayan sun gaisa da Iyayen nashi, sannan suka yi masu alkhairi mai tsoka don har gidan Gambo aka kaisu suka gaisa itama suka yi mata alkhairin. Inna Kam cikin sanyin jiki ta jinjina maganganun da Inna Gambo tayi, saboda ganin Safwan da Iyayenshi yasa ta gano ba k'aramar baiwace Allah ya yiwa Dijensu ba, mutanen unguwa da abokan arzik'i suka cika k'ofar gidan dank'am ana yi masu sallama, bayan duk wad'anda aka zab'a za'a je da su kowa ya shiga motane amman ba'a ga Dije ta fito gidan ba, ana k'ok'arin a shiga a fito da ita ne sai gata ta fito janye da akuyarta tana fad'in "Zo muje ke ma ba zan ci amanarki ba don zan zama Likita, don haka dole ne kema in kin fara zawo in yi maki allura" Cike da mamaki kowa ya saki baki yana kallonta, Safwan kam mere ya yi ya d'auke Kai yana k'umshe dariyarshi, Inna ce ta karb'e akuyar tana cewa da ita ta bari idan ta sake dawowa ta tafi da ita, Dije Kam ta fashe da kuka cikin fushi Usman ya fisgo hannunta ya sakata motar Safwan a seat d'in gaba ya zaunar da ita sannan ya rufe k'ofar. Haka Suka bar k'ofar gidan sai bye bye ake yi masu tare da yi masu addu'ar ALLAH ya tsare hanya. Maza bisa Kan Yan birni😝 Akafta🤣 D/AUTA CE🤝🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *GA KIRA DA BABBAR MURYA BAN YARDA BA KUMA BAN AMINCE BA BAN LAMUNTA BA DA A SAKE CANZA KO A SAKE SARRAFA MANI LITTAFAINA BA TA KOWACE SIGA* *TARTSATSI.* *RUWA DA. KANKARA.* *DIJE K'ARANGIYA* *NI HADIZA D/AUTA BAN LAMUNTA BA AKAN KOWA DA YA SAKE SARRAFA MANI LITTAFAINA BA TA KO WACE HANYA DA KO WANE YANAYI BA TARE DA IZININA BA AKASIN HAKAN KUWA WALLAHIL'AZIM ZAMU GAURAYA DA KOMA WACEE DON SAI NA JA HAKKINA AKAN KOMA WA YE A BI DOKA A ZAUNA LAFIYA🤝🏻* BAN AMINTA BA! BAN AMINTA BA! KAR A SAKE! KAR A SAKE! *Lamba ta 25* DIJE kam duk Wanda ta sani sai ta tashi tsaye ta fito da kanta tana d'agawa mutane hannu, tun Safwan yana jin takaicin abun a ranshi har sai da ya kai ya katsa mata wata arniyar tsawa yace "Wai ke wace irin bak'auya ce ke? Wannan abu da kike yi tamkar wata zararra fa?" Dije kam bata daina gaisawa da mutanen k'auyensu ba, cike da jin haushin abin ya ciyo kugunta ya janyo zanenta da k'arfi ta dawo dab'as ta zauna, kanta ya bugu da bayan seat d'in tace "Wash! ALLAH kaina" Cikin masifa yace,. ,"Ya dad'e bai cire ba shi kan naki tunda ke ba kya ji WALLAHI ba zan lamunci hakan ba" Dije ta makure ta sha jinin jikinta tana yi masa hararar gefe tana mui mui, mata biyu yan rakiyar Dijen da suke tare da su cikin motar suka had'a baki wajen fad'in cewa "Don ALLAH ka yi hak'uri k'urciya ce" Safwan ya yi banza da su tamkar ma bai ji su ba, ba shiri su ma suka yi gum motar ta yi shiru na d'an lokaci aikuwa cen Dije ta hango wata 'yar Makarantarsu ta Allo ta yi saurin yin wani zillo tamkar biranya ta dale saman seat d'in da kafafunta ta tashi tsaye ta fito da jikinta suka tana fad'in "Ladidi kin ganni nan cikin mota anyi mani aure birni zan je, me kike so idan zan dawo in kawo maki?" Ladidin ta washe Baki tace,. "Burodi nike so Dije don ALLAH fa kar ki mance kinji??" Dije tace, "bazan mance ba Ladidi Sha kuruminki kinji ai kud'i zan yi idan naje, ke karatun Likitancin fa zan yo a cen fa ki ce da Malam Mainasara ya ci gaba da yi man addu'a sai na dawo" Haka Dije ta yi ta zuba shirmenta da Ladidi har suka daina ganin juna, sannan ta dawo ta zauna tana washe Baki tace "ALLAH sarki garinmu shikenan zan barka kar ka yi kuka ka ji sai na dawo" Safwan dai zuciyarshi ta kai wuya ya k'ufula sosai Shiyasa bai biyeta ba don matuk'ar ya kulata ba k'aramar jibga zai yi mata ba, gashi tare yake da Baffah'nta da yan uwanta yasan dole ne sai sunji ba dad'i, shiyasa ya yi kwafa kawai ya yi sannan ya ci gaba da tuk'inshi sannu a hankali har suka shiga babban birnin k'auyen su Dijen, aiko tana hango wani mai shayi da biredi motar tana gudu ta fara yunkurin tsallakewa ta tagar da nufin ta fita, Safwan ya yi nisa da tunani sai gashi ya dawo hankalinshi ba shiri saboda fahimtar abunda take so ta yi, aiko ba shiri ya fisgota ta dawo ciki tare da yin sauri ya zuge glass d'in ya rufe ruf, ta yi saurin kallonshi tace "Don girman ALLAH ka barni in sha shayi da burodin cen WALLAHI raina ya biya sosai, ka ga yawuna ma har sun tsinke gaba d'aya WALLAHI" Ta k'are maganar tare da had'iye wasu yawun suka wuce a makoshinta kutt! Safwan ya yi banza da ita, Dije ta tashi ta fara dukan gilas d'in tana fad'in "Wayyo ALLAH ga wani kifi cen za'a gasa daga ganinshi zai yi dad'i WALLAHI" Cen kuma ta sake cewa "ji matar cen tana soya kosai gaskiya daga ji zai yi dad'i WALLAHI, har da wani Abu gashi cen ina ma zan samu in ci shi inji?" Ta k'are maganar cikin marairecewa Safwan ya yi k'ok'arin yin parking a gefen titin ya fito ranshi a b'ace ya nufi wurin mai suyar k'osan, mintuna a tsakani sai gashi ya dawo da ledodi himili guda sai ga motar bayansu ta Iyayen Safwan, wadda Baffahn Dije yake ciki suma sun tsaya suka ce da shi lafiya?, Kai tsaye ya sanar da su cewa Dije ya yiwa siyayyar abun kari tace bata karya ba, cike da jin dad'in hakan Baffahn ya washe Baki ganin himilin ledodin, sannan ya ce da su su tafi abunsu kawai shi zai biyosu daga baya, Baffahn ganin Dijen da Mata biyu yan garinsu yasa bai ji komi ba ya koma motar suka tafi, shi ko ya bud'e murfin gefen Dijen ya zuba mata ledodin a cinya duka ya karb'i wata da wani yaro ya rik'o masa itama duk ya tula mata a jiki sannan ya rufe k'ofar garam! Da k'arfi ya zagaya ya shiga ya tada motar suka bar wajen. Sai ga Dije da kwallah k'ara tana fad'in wayyo ALLAH zafi kunama tana cizona a cinya WALLAHI" Ya yi banza da ita cikin sauri ta ture ledodin da ke saman cinyarta sai ga Ledar ruwan zafin shayin da yasa aka k'ullo mata ta fado k'afarta har sun zuba kad'an ta yi saurin d'age k'afar tana fad'in "Wayyo ALLAH zafi" Ta saka hannu ta shafo k'afar ganin abu fari yasa ta lasa aikuwa ta yi saurin dukawa ta d'auko ledar tana wash! zafi tana lasar bayan ledar inda shayin ya zubo ya b'ata bayan ledar. Sannan ta ajiye ledar gefen sitarin motar ta duka ta d'auko wata ledar sai ga kosai yana tiririn zafi, ta yi saurin budewa ta d'auko guda ta kai baki sai gata da yin saurin fad'in "Wayyo!" Ta fara hura bakin da hannu tana fad'in,. "Wai wai gaskiya wannan yafi na garinmu dad'i" Sai da taci sosai sannan ta waigo ta mikowa su Inna Kandala rabi tace "Ku ci kuma ku ji yafi na garinmu dad'i" Sai da taci kosan sosai sannan ta bud'a wata ledar sai ga soyayyar doya da kwai ta yi saurin zaro ido tace,. "WALLAHI shine na hango kai honi Dije yau ina ta shan dad'ina WALLAHI cabd'i" Ta sake rabawa biyu ta mik'awa na baya ta fara cin doyar tana fad'in,. "Shi Kuma wannan abun ko da mi ake had'ashi shi kuma? Kai Yan birni suna jin dad'insu WALLAHi" Haka ta tasa doyar a gaba ta ci mai isarta sannan ta fara sauke nishi tana fad'in,. "Cikina zai fashe yasin" Sannan ta ajiye ledar doyar itama ta bud'e wata ledar sai ga waina da miya k'ulle a leda sai kamshin manshanu ke tashi, Dije ta zaro Ido tace "Kai kai ho! ni Dije ho! Ni Dije gashi na koshi bansan ya zanyi da wainar nan ba?" Safwan ya yi saurin fad'in,. "Ki zubar kawai a wuce wajen" Ta k'ara damke ledar tace,. "Cabd'i ai WALLAHI Ni kam sai na cita inji ya take itama, don nasan dole ma ta yi dad'i don ba zata yi kamshin banza ba" Sannan ta ajiye ledar wainar ta d'auko wata leda sai ga k'aton Biredi ta zaro ido tace,. "Idona idonka WALLAHI wayyo ALLAH dad'i na gode sosai ka ji in akuyata ta haifu na yi maka alk'awali zan baka abunda ta haifa kyauta ai kana so ko?" Safwan ya shafa gemunshi yace,. "A yi ta kaya Ni kam na yafe" Dije ta zunburo Baki tace,. "Don ma ka samu zan baka?" Tana k'are fad'ar maganar ta ciro ledar shayin ta huda ta fara gutsuro biredi katoto guda ta kurbi shayin, tace "A'a'a'ah haka shima nasu shayin yake da dad'i haka? Wayyo har wani k'amshin dad'i yake yi yasin, Kai garin dad'i na nesa Kai! Kai! Kai!" Haka ta dinga sambatu tana Shan shayin da biredin har ta kusa canye rabin ledar biredin sannan ta yi gyatsa tace,. "Alkur'an yau na yi cin haram ALLAH ya jikanki Dije ina Innata tana kusa ta ci itama ta ji" Ta mik'awa matan biredin da ledar shayin ta shafa cikinta tace,. "Sai ka sacce in sake cin wainar itama inji ya take" Kafin ka ce me sai ga Dije da langabewa tana bacci sai ajiyar zuciya take saukewa a hankali, Safwan ya kai kallonshi gareta ya girgiza Kai a ranshi yace,. _"Dole ki yi bacci wannan ci da kika yi kam acicin banza wa'kazuba"_ Sannan ya mayar da hankalinshi akan tuk'inshi yana yi yana murmushin da shi kad'ai yasan ma'anarshi. Tafiya ta mika Safwan da sauran abokan tafiyar sai shillawa suke yi Kan titi suna k'ara nausawa Kan hanyarsu, Dije kam har lokacin baccinta take yi har sai da lokacin sallah yayi Suka tsaya suka yi suka ci abinci Suka k'ara mikar titi tun suna jin dad'in tafiyar har dukansu suka fara jigata musamman su Baffah da Basu tab'a irin tafiyar ba, Dije kam duk sai da ta canye komi sannan ta ji natsuwa ta zo mata, shiyasa ba wuya ta sake komawa bacci har duhun dare ya sauka. K'arfe d'aya saura Suka isa garin Gombe inda suka yada masauki a wani hotel da nufin tun da sassafe su kama hanyarsu ta zuwa Yola. Akafta👍🏻 D/AUTA CE🤝🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *GA KIRA DA BABBAR MURYA BAN YARDA BA KUMA BAN AMINCE BA BAN LAMUNTA A CANZA A SARRAFA MANI LITTAFAINA BA TA KOWACE SIGA* *TARTSATSI.* *RUWA DA KANKARA.* *DIJE K'ARANGIYA* *NI HADIZA D/AUTA BAN LAMUNTA BA AKAN KOWA YA SARRAFA MANI LITTAFAINA BA BA TARE DA IZININA BA AKASIN HAKA KUWA WALLAHIL'AZIM ZAMU GAURAYA DA KOMA WACE DON SAI NA JA HAKKINA AKAN KOMA WA YE A BI DOKA A ZAUNA LAFIYA🤝🏻* *Lamba ta 26* Hak'ik'a ba k'aramin k'auyanci Dije da Baffah'nta da 'yan rakiyarta suka yi a Hotel d'in ba, sai dai kasancewar su Safwan d'in sun san daga ina suka fito shiyasa ba su yi mamakin hakan ba, don Dije A.c'n da ta zuk'a ya sata bajewa tana bacci har da su minshari, daga ita har abokan tafiyarta don dak'yar aka tashesu suka yi wanka mai cike da k'auyanci shi ma, sannan suka yi breakfast suka shirya suna jiran Safwan ya dawo daga fitar da yayi cikin gari su tafi. Aikuwa Safwan fitarshi ke da wuya bai zame ko'ina ba kai tsaye sai Gidansu Lawi, inda ya taradda shi kwance yana bacci kasancewar d'akinshi lik'e yake da gidansu k'ofarshi tana kallon hanya. Ba k'aramin mamaki Lawi ya yi ba da ya ganshi, cike da d'okin son jin wani labari daga Dijenshi ya yi saurin wartsakewa yace "Abokina wannan tafiya babu sanarwa fa? Ko dai bazata ka zo ka yi man akan ka sanar dani cewa an amince in zo in auri Dijena? WALLAHI yanzu haka da ka ganni mafalkinta nake yi" Safwan ya b'ata fuska tare da mik'ewa tsaye ya fito da kud'inshi da Dije ta bada a bashi ya ajiye masa a gefen katifarshi, sannan ya soka hannunshi duka a aljihu yace "Ga kud'inka nan inji Khadija ta ce in kawo maka, saboda gidansu ance bazata karb'a ba don Ni ma ban so na rabata da kud'in ba shine ta wurgosu d'akinmu ban sani ba ta tsere abinta". Lawi cikin tsananin firgici tare da fad'uwar da gabanshi yake ta yi da sauri da sauri yace "Yanzu shi kenan ana nufin an rabani da ita da gaske an aurawa wani ita wanda bai san darajarta ba?, D'ankauye irinta wanda ba zai taimaketa ta cika gurinta a rayuwa ba?" Ya k'are maganar tare da zubowar wasu hawaye masu zafi akan fuskarshi, Safwan ya yi taku d'aya biyu tare da juyawa Lawi baya sannan ya furzar da iska mai k'arfi a bakinshi yace "Gurinta zai cika Insha ALLAHu kamar yanda kake yi mata fata don ni zan rik'eta da zuciya d'aya har sai na tabbatar da ta cika gurinta na zama likitar kamar yanda take gurin zama" Lawi cikin k'ullewar kai da maganganun Abokin nashi ya yi saurin mik'ewa tsaye ya fuskanceshi idonshi fes akan fuskarshi zuciyarshi cike da wasi wasi yace "Fashe man bak'i akan abunda kake nufi Abokina, don zuciyata ta fara hasasoman abunda nake hangowa kamar ba gaskiya bane" SAFWAN ya saka hannu ya dafa kafad'ar Lawi yace,. "Ka d'auka cewa komi rubuce yake a Littafin kundin k'addararmu mai kyau ko akasin hakan, kuma ka d'auka cewa matar mutum kabarinshi wani ba zai tab'a auren matar da ba tashi ba" Lawi cikin matsananciyar damuwa yace,. "A tak'aice kana son ka sanar dani cewa anyiwa Dije aure kuma ba da d'ankauyensu ba to da wa aka d'aura da har zaka d'auki nauyin cikar burinta??" Ya k'are maganar cikin yi masa kallon tuhuma, cikin sanyin jiki tare da daburcewa Safwan yace,. "A lokacin da ka baro k'auyen KHADIJA ta tub'ure akan ba zata auri wanda aka zab'a mata ba, ganin hakan Mahaifinta ya ce ta je ta auri wanda take so amman a rana da lokacin da aka saka da wancen d'in, idan ba haka ba shi ba zai fasa auradda ita ba kuma ba zai d'aga lokaci ba, shine da ta zo ta sanar dani na yi ta neman layinka ban sameka ba gashi lokacin ana saura kwana biyu, hankalina ya tashi sosai ga Yarinyar ta d'aga hankalinta akan rashin samunka da ba'ayi ba, shine ta rok'eni akan don ALLAH ni in amince in aureta" Rassssss! Gaban Lawi ya buga ba shiri hawayen da yake mak'alewa suka gangaro masa cikin muryar kuka yace,. "Ba sai ka k'arasa dogon labarinka na k'arya da ka shiryo man ba wanda ko kad'an k'arya bata kamaceka ba don ba halinka ba ce, na fahimci inda duk ka dosa don daman cen na dad'e da gano kana sonta, na kyaleka ne don kawai inga iya gudun ruwanka ka je kawai ALLAH ya baku zaman lafiya, kuma Ni na yafe maka duk abunda ka yi mani saboda kawai nasan cewa kula mata ba d'abi'arka bane, Kuma na godewa ALLAH da ya jarrabeka da son abunda ka rena ko don ka fahimci cewa wulak'ancin da ka ke yiwa Mutane ALLAH ya nuna maka cewa su d'in ba abun reni ba ne, ka je kawai ALLAH ya baku zaman lafiya amman ka sani naji haushin da tun farko ka b'oye mani cewa kana sonta, ka barni sai da na zurma da yawa sannan ka dawo ka kwaye mani baya ka sani amincinmu bai ci haka ba" Yana k'are maganar ya fice d'akin cikin sauri, Safwan ya bishi da kallo zuciyarshi cike da takaicin abunda ya aikatawa abokinshi, jiki a sanyaye ya janyo k'afafuwanshi ya shiga gidansu Lawin, kasancewar sun sanshi sosai Shiyasa suna jin sallamarshi k'anwar Lawi ta lek'o tana ganinshi ta koma da sauri ta yi cikin Gidan, sai gata ta dawo tace da shi ya shigo Safwan ya shiga zuciyarshi cike da jin kunyar abunda ya yiwa Lawi, ya isa wurin Mahaifinshi da ke zaune yana fama da jiki ya gayar da shi, sannan Mahaifiyar Lawin ta zo itama suka gaisa, suna yi masa ya Hanya. Banyan sun gama gaosuwar ne Mamar Lawin tace,. "Aiko ina jin yana d'akinshi ko kun had'u?" Safwan ya duk'e kanshi yace,. "Eh mun had'u daman wucewa zan yi nace bari in zo in ga jikin Baba, ALHAMDULILLAH ma naga lafiya ta samu" Mamar tace,. "Eh ai kwanan nan Masha ALLAH jikin sauk'i sai samuwa yake yi" Safwan ya zura hannu aljihu ya fiddo kud'i masu d'an kauri ya ajiye a saman shimfid'ar Baban yace, "Ga shi Baba ni zan wuce ALLAH ya bida lafiya" Mahaifin Lawin yace "Masha ALLAH Safwanu ALLAH ya tsare ya kaika lafiya ka gayar da mutanen gidan duka" Haka suka yi sallama ya fito sai dai kam ba Lawi ba samatarshi, haka aka yi ta bulayin nemanshi akan su yi sallama da Safwan amman ba'a ganshi ba, dole ya lallab'o ya baro unguwar cikin jin haushin kanshi akan me yasa bai hak'ura ya barwa Abokin nashi ba, wata zuciyar tace da shi _"To Kai fa ko ka manta halin da ka shiga ne akan ganin zata sub'uce maka?Shareshi kawai zai hak'ura ne daga baya"_ Haka ya nufo Hotel d'in suka d'uru motocinsu suka kama hanyarsu ta zuwa Yola, har suka isa zuciyarshi bata daina yi masa canki in canka ba, a k'arshe dai ya tsayu akan magana d'aya wadda yake ganin itace mafitar da zai wanke laifin da ya yiwa Abokinshi. Kasancewar an san da zuwansu shiyasa kai tsaye aka wuce da su ainahin gidansu Safwan d'in, aikuwa sai ga Mahaifiyarshi da k'annenshi biyu sun fito tarbarsu cike da d'okin ganinshi, Mama Hajiya waton Mahaifyar Safwan kai tsaye wajen Dije ta nufa inda zuciyarta ta tabbatar mata da itace Matar Safwan d'in, duk da zuciyarta ba k'aramin bugawa ta yi ba lokacin da ta yi arba da Dijen ba, sai dai ta mazge ta rik'o hannunta tace "Oyoyo 'yata sannu da zuwa" Dije ta bita da kallo Baki washe tace,. "Laaah! Ashe kin sanni??" Safwan ya yi saurin fad'in "to maganatu ke bakinki ba zai yi shiru ba? Ko gaisawa ba'a yi ba sai surutu" Dije ta sunne kai tare da maka masa hararar gefen ido ta kalli Mama Hajiyar ta rusuna k'asa tace,. "Barka da yini Inna" Mama Hajiyar ta d'agota tana dariyar yak'e tace,. "Barka dai 'yata sannunki da zuwa to mu shiga daga ciki" Ta janyo hannunta tare da yiwa 'yan rakiyar Dije maraba da Baffah'nta da yake ta kallon k'aton gidan yana jinjina girmamshi a ranshi, har suka shiga ciki inda su Baffanta da sauran mutum biyu da suka rakoshi aka kaisu babban sit room d'in Gidan tare da Iyayen Safwan d'in biyu da suke tare. Dije kam cikin Gidan Hajiya Mama ta ja ta K'annen Safwan biyu suna biye da su suna k'umshe dariya, musamman dai d'aya k'anwar tashi da har dafe ciki take yi saboda waige waigen da Dijen da 'yan rakiyarta suke ta yi, don suna ta kalle kallensu har suka shiga ciki, in da aka yiwa matan biyu masauki a wani d'aki Dije kam kai tsaye ta nufi d'akinta da ita ta zaunar da ita falonta, su Sury da ke biye da su suna shigowa ta korasu suka fita saboda ganin yanda su ke ta faman yi wa Dijen dariya. Sannan ta kira wata 'yar aikinsu ta kawowa Dijen Abinci da wad'ancen matan sannan ta yi k'uryar d'akinta zuciyarta cike da tunane tunane, Dije kam ba wani jin nauyi ko jin kunya ta saki jiki ta kwashi abincinta tana santi har da su lashe filet d'in tas da halshenta, sannan da ta k'oshi ma ta saka hannunta cikin miyar ta dinga tsamo tsokokin naman tana cinyewa tana fad'in "Wannan Abinci sai kace a aljannah?? Cabd'i jam, ai Ni kam gaba ta yi da ni wai zak'wai yasin ai Ni kam ba mai fiddani cikin gidan nan" Surayya da fiddo kam da suke lab'e jikin k'ofar d'akin sunata turereniyar lek'enta, sai uwar dariya suke ci har sai da Hajiya Mama ta fito ta gansu suka yi saurin barin wajen tare da k'umshe dariyar da take son kashesu, saboda ganin duk felek'en Yaya Safwan d'in ace wai wannan Bagidajiyar ce Matarshi. Hajiya Mama ta yi zaune tana kallon Dijen yanda bakinta ya nashe da maik'o gashi sai faman lashe hannunta take yi tana fad'in,. "Hannuna Kai ma yau ka san ka shigo gidan Yan gayu munci dad'i abunmu ALLAH yasa in mutu a gidan nan Ni kam, dole in koma in zo da Innata da Gambo su ma su sha dad'insu, ta sake d'auko wani k'aton k'ashi tace wohoho ina ma Gambo ta sami wannan k'ashin nasan da hak'oranta da suka zube duka sai sun dawo" A cen gefen su Baffah kuwa an tarbesu da manyan kulolin abinci na alfarma, sannan aka nuna masu toilet da komi suka fara gabatar da sallolinsu sannan suka ci abinci suka yi k'at! Sannan aka had'u duka akan a tattauna muhimmiyar maganar da ta had'asu dukansu.. Akafta D/AUTA CE😅 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *BAN LAMUNTA BA AKAN KOWA YA SARRAFA MANI LITTAFAINA BA BA TARE DA IZININA BA AKASIN HAKA KUWA WALLAHIL'AZIM ZAMU GAURAYA DA KOMA WACE DON SAI NA JA HAKKINA AKAN KOMA WA YE A BI DOKA A ZAUNA LAFIYA🤝🏻* *Kukan Kurciya......😉* *Lamba ta 27* Safwan kam ko da ya je sanarwa da Hajiya Mama ya taradda ita zaune falonta ta yi tagumi tana nazarin abunda ya ja Safwan ga Dije har ya zab'eta a matsayin matar aurenshi, saboda saninshi da ta yi ciki da bayanshi akan mugun k'yank'yami tare da wofintar da sha'anin Mata, cikin sanyin jiki ya isa wurinta saboda yanayinta ya nuna k'arara damuwar da take ciki, ya sami d'aya daga cikin kujerun ya zauna sannan yace "Maaah!" Ta d'ago kanta da sauri tana murmushin yak'e tace,. "Ya dai? Sun kammala cin abincin ne?" Ya sosa kanshi ya ce "Eh ina ita yarinyar?" Hajiya Mama ta yi masa nuni da k'uryar d'akinta tace,. "Tana ciki tana SALLAH" Sannan ya ce "Ok to ki je su Baba Ali suna so su tafi gida shine aka ce ki zo ku yi sallama" Hajiya Mama ta mike ta janyo hijabinta ta saka tace,. "Ok to mu je" Ya sosa kanshi yace,. "Itama ta zo ai zaman har da ita ne" Hajiya Mama tace,. "Ok to ku sameni a cen d'in" Ta fice zuciyarta bata daina mamakin Safwan ba, Safwan kam kai tsaye d'akin ya nufa in da ya taradda ita tsaye a gaban standing mirror tana kallon kanta tana wasar Baki, tana yi tana rufe fuskarta cen ta bud'e tana dariya saboda ganin kanta jikin k'aton madubin yasata jinta cikin wani nishad'i. A hankali ya ja ya tsaya bayanta tare da rungume hannu a K'irji yana kallonta, cikin Madubin Dije ta hangoshi tsaye ta yi saurin waigawa sai ko gashi yana yi mata wani kallon reni yace "Ke Wai shikenan ba zaki yi hankali ba?" Dije ta sha jinin jikinta tace,. "Ai kasan cewa Ni ba mahaukaciya ba ce ba ko?" Ta k'are maganar tare da murgud'a masa Baki, ya tako a hankali ya tsaya gaf da ita tare da rik'e mata kunne ya jawo cikin sigar k'eta Dije ta yage baki tace "Wayyo! Baffahna" Safwan ya yi saurin sakinta ya ce " ke fa wata b'aro ce to ki zo muje ana nemanki kuma saura idan kika je don ALLAH ki zuba shirmenki da kika saba, WALLAHI in saki jiki in jibegeki a banza kin ga nan ba k'auyenku bane bale har ki sami damar yi man turaren mayu ko ki saka man b'eraye" Yana k'are maganar ya nufi k'ofar fita yace,. "Ki zo mu je na ce" Dije ta sha jinin jikinta sosai saboda tuno abunda ta yi masa sannan ta bishi a baya tana fad'in "Don Allah Ni dai ai ba wani laifi nayi ba kuma yanzu ko? Don Ni dai WALLAHI ALLAH bana son a ce in bar gidan nan, ashe haka kuke cin dad'inku ku kam? Cab! Gaskiya Wallahi kun zo duniyar a sa'a ashe ku ma kuna cikin mutanen da na ji Malaminmu ya fad'a muna ana baiwa Aljannah tun nan duniya ku canye mu Kuma sai a bamu ta Lahira" Ya yi banza da ita yana gaba tana biyarshi tana zuba masa surutu har suka kai Babban falon Gidan, in da su Fiddo su ke zaune suna kallo suna labarin shirmen Dije suna dariya, suna hangoshi suka yi muk'us dukansu saboda bala'in tsoronshi da suke ji kamar me, ya wuce abinshi ba tare da ko kallonsu ya yi ba, Dije kam tana k'arasowa tana kalle kallenta ta hango t.v ana wani wrestling, dai dai in da wani k'aton mutum ya d'aga wani sama ya jefoshi k'asa ya bishi ya danne ana kidanyar d'aya biyu uku, Dije ta yi wani tsalle tace "Tashi ka rama WALLAHI kada ka yarda cabd'i jam haka kawai ka zuba masa Ido ya jibgi banza?" Sai Kuma gashi Kuma wanda ya danne d'in ya hanashi ci ta hanyar yin wani zillo cikin jin haushin hakan mai son ya ci d'in ya saki kwanji ya yi ta kaiwa na k'asan naushi, Dije ta zabura ta gyara tsayuwar dambe ta sha fili tace "Ai billahillazi kar ka yarda tashi ka rama nace ko baka jini ba? kutuma lalle Kai yanzu zaune zaka yi yanata jibgarka a banza lalle ma kai wawan banza ne kai cabd'i!" Surry da Fiddo ko me za su yi ba dariya ba don kuwa daina kallon suka yi suka koma kallonta suna cin uban dariya, Safwan kam jin kamar bata biyarshi yasa ya waiga ganin bai ganta ba ya dawo sai dai tsayin da ya ga ta yi ne shi ma kanshi ya so ya bashi dariya, amman ya mazge ya katsa mata wata uwar tsawa yace "Ke Uban mi kike yi a wurin ba za ki zo mu tafi ba??" Dije ta yi saurin waigawa sannan ta b'ata fuska tace, "wani abun takaici na gani yanzu wai wani k'atoton banza ne ya yi kwance anata jibgarshi a wofi WALLAHI ya ji haushi shi kam" Safwan hararar da ya danna mata ce tasa ta yi muk'us ba shiri ta nufo wajen tare da rab'awa ta gefenshi ta wuce, su Surry kansu tuni suka yi gum! har sai da suka ga ya wuce sannan suka sake fashewa da wata sabuwar dariya saboda abinda Dijen ta yi ba k'aramin dariya ya basu ba. Bayan sun bar wajen ne Safwan d'in ya fisgota da k'arfi ya had'ata da gini tare da d'aga hannu kamar zai daketa cikin b'acin rai ya nunata da yatsa yace "WALLAHI kada ki kuskura ki janyo in karairayaki cikin Gidan nan, ke shikenan ba zaki natsu ba sai abu kike yi tamkar wata mahaukaciya to bari kiji na sake ganin kin sake irin wannan shirmen jikinki ne zai gaya maki wawuyar banza,, matsa daga nan kina wani kallona da wasu idanuwanki guru guru tamkar idanuwan mota" Dije ta zunb'uro baki Kai tsaye ya fisgo hannunta cike da jin haushin kwafsawar da take yi masa suka nufi d'akin, sannan ya saketa da sauri suka shiga tare da sallama a bakunansu. Dije kam sage da hannu ta shiga ta Sami gefe ta rakub'e tana yarfa hannunta,a zuciyarta tana fad'in _"Shi Kam wannan mugun mutumen har ciki nawa ya ke so ya yi man ne? "_ Tunaninta ya katse ne saboda jin muryar wani d'aya daga cikin Iyayen Safwan d'in da ta jii yana cewa,. "Matso daga ciki ki zauna kinji 'yata" Dije ta mik'e ta dawo ciki kad'an ta zauna k'asan carpet kamar yanda taga Safwan d'in ya yi, duk da wata zuciyar ta so ace ta hau Kan kujerar ko don ta ji ya laushinta ya ke, don tunda ta k'yalla Ido ta hangosu tasan ba k'aramin dad'in zama za su yi ba, amman firgicin cikin da Safwan ya sake yi mata yasa ta ji duniyar gaba d'aya ma ta fice mata a Rai. Baba Ali ya sake cewa "Masha ALLAHU kamar yanda kowa ya sani ne wannan zama mun yishi ne saboda Safwan da Khadija, saboda auren da Ubangiji ya nufa aka yi a tsakaninsu, to Masha ALLAH yanzu Malam Sanda ga gidansu Mijin 'yarka yanda idan ka tashi nemanta kasan ta inda zaka nemeta, Hajiya Balkisu kinga Mahaifin Khadija Malam Sanda wad'annan kuma abokan tafiyarshi ne, Khadija kin ga Mahaifiyar Mijinki Safwan Mahaifinshi kuma tuni ALLAH ya yi masa rasuwa,m sai dai Ni yayanshi tare da wannan k'anenshi tare da sauran 'yan uwanmu Mata da maza da suka rage, shi kam sai dai mu bishi da addu'ar ALLAH Ubangiji ya dad'a masa Rahama a cikin k'abarinshi tare da musulmin duniya gaba d'aya, mu ma idan ta mu ta zo yasa mu cika da imani" Dukansu suka ce "Ameen Ameen" sannan d'aya bayan d'aya kowa ya yi jawabi tare da neman ma zaman auren nasu albarka, sannan aka ja hankalinsu duka daga shi har ita akan zaman auren tare da nuna masu muhimmancin auren tare da hak'uri a zamantakewar auren duka. ALHMDLLH shi kanshi Baffahn na Dije yanzu hankalinshi ya kwanta sosai saboda ganin yanda suke Mutane masu karamci, daga nan shi ma ya damk'awa Safwan da Mahaifiyarshi har ma da Iyayen Maza amanar Dijenshi, tare da rok'onsu akan duk abunda ta yi wanda bai dace ba don ALLAH ayi hak'uri da ita da sannu zata dawo dai dai da yanda ake son kowace d'iyar ta kasance, don a fakaice ya yi masu nuni da su yi hak'uri da halayenta don ba ya son ya bayyana k'arara cewa ga laifin 'yarshi, ya fi son idan sun gani a matsayinsu na masu ilimi su fahimtar da ita abunda ya dace su d'orata kan hanya har ta fahimci rayuwar da yanda ake zama cikinta. Taro ya watse akan cewa gobe tun da sassafe su Baffah'n za su kama hanyarsu ta komawa gida, sannan su Iyaye mazan suka yi sallama da su akan sai goben za su zo su yi sallama da su Baffah'n, Safwan da Hajiyarshi har gindin mota suka rakasu suna yi masu godiya har suka bar Gidan. Dije kam suna fita ta tashi ta nufi Baffah'nta tana washe baki tace,. "Baffah Kai ma ka ci naman mai yawa ko? WALLAHI baka ga Wanda na ci ba ga abincinsu mai shegen dad'in tsiya" Baffah ya washe Bakinshi ya ce, "kin samu gidan Aure Dije don ALLAH ki yi biyayya kinji?" Dije ta d'aga Kai, tana matsa 'yan yatsunta tace,. "Ai ni duk ma aikin da suke so in yi masu zan yi WALLAHI ko don su dinga bani abincina mai dad'i ina ci" Baffah ya ce,. "Duk abunda Mijinki ya sakaki ki yi masa kinji? haka ma Mahaifiyarshi kin ga dai suna da kirki don ALLAH kada ki yi abunda zai janyo har ace baki kyauta ba" Dije tace,. ,"Insha ALLAHu Baffah ba Zan yi rashin ji ba ko cen garinmu ai ka ga su ke ja na ai" Baffah ya ce "Nan ma ai dole su ja ki amman don ALLAH kar ki biyesu ki ce ke dole sai kin rama ki kyalesu da halinsu da sannu zaki ci ribar hak'urinki" Dije tace "to Baffah amman don ALLAH ka ce da shi ya daina rik'e man hannu WALLAHI Ni bana son inyi ciki gashi yanzu har ciki biyu ya yi mani d'aya nan d'aya a k'auyenmu" Ta k'are maganar cikin zubowar wasu 'yanmatan hawaye, Baffah zai yi magana kenan sai ga su Safwan d'in sun shigo, dole ya wayance yana fad'in "Ki yi hak'uri ai ko nan gida ne kamar cen d'in saboda nan da cen duk d'aya ne a wajenki Babu banbanci" Akafta😛 D/AUTA CE✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *Masu buk'atar Littafaina ga su kamar haka:* *TARTSATSI* *RUWA DA K'ANK'ARA* *BAKAN GIZO* *DIJE K'ARANGIYA* *BAK'ON YANAYI sai dai shi na kud'i ne da d'ari uku kacal zaki sameshi a complete d'inshi😇* *Lamba ta 28* Haka Baffah ya shashantar da zancen aka yi ta fira har aka yi magrib suna tare da Safwan sunata fira duk da ba wani sabawa ya yi da su ba amman ba laifi sun d'an tab'a fira, kiran sallah'r yasa Dije ta yi cikin Gidan tare da matan biyu domin su yi SALLAH, su Baffah kuwa suka yi masallacin da ke k'ofar gidan. Ko da dare ya yi Hajiya Mama ta saka Dije ta yi wanka da kanta ta nuna mata yanda zata yi kwalliya ba irinta haukarta da ta saba ba, ta d'auko wasu sababbin kayan bacci masu shegen kyau tace ta saka, Dije kam saboda hud'ubar da Baffah'nta ya yi mata sannan da kashedin da Safwan d'in ya yi mata shi yasa ta rage shirme in taga wani abu da bata sani ba sai ta yi shiru ba zata yi ta surutu ba, bakinta alekum ta saka kayan tare da fessesa mata turaren da Hajiya Mama ta yi sannan ta kira Surry tace da ita ta je ta Kai Dije d'akin Safwan, Dije ta zaro Ido waje tace "Hajiya me zanyi wajenshi Sabida ALLAH Ni kam cikin daren nan yanzu??" Hajiya ta dafe goshinta tace,. "Ki je ki yi kwanciyarki a cen kafin da safe sai a kaiki gidanki in da zaku zauna da Mijin naki" Dije ta zaro Ido waje tace,. "Kina nufin gidan nan zan bari???, WALLAHI idan na barshi an cuceni wa zai bani irin abincin da na ci d'azu mai d'an karen dad'i?" Hajiya Mama ta dafa kafad'arta tace,. "Ki kwantar da hankalinki insha ALLAHu abincin da zaki ci a cen har sai ya fi na wannan Gidan dad'i, yanzu dai ki je da safe idan kika zo zan yi maki bayanin komi" Dije ta marairece cikin kuka tace,. "Yanzu tsakaninki da ALLAH d'akin Namiji zaki kaini inje in kwana???bayan nasan ke ma kanki kinsan cewa hakan bai dace ba amman kike k'ok'arin turani???" Hajiya Mama ta dafe goshinta ba shiri ta kai zaune tace da Surry da ke sunne kai tana k'umshe dariya da ta je, sannan ta janyo hannun Dijen ta zaunar da ita kan gadon ta yi shiru na d'an lokaci sannan tace "Ai dai kinsan cewa an yi maki aure da shi ko?" Dije ta d'aga kanta, Hajiya Mama tace "Masha ALLAH to ai kinga shi baya cikin jerin mazan da aka haramta ki je d'akinsu ko?" Dije ta yi shiru na d'an lokaci tana tunani tace,. "To Ni dai tsakani da ALLAH Innata ta hanani ko magana in dinga tsayawa ina yi da maza sosai, kuma yanzu idan Baffahna ya ji ai WALLAHI dole ma ne ya dakeni, Ni dai don hasken da ALLAH ya yi wa Qur'ani kada ki bari ya sake yi man ciki na uku" Hajiya Mama ta zaro ido waje tace,. "Ciki na Uku?????" Dije tace, "Eh ya yi man d'aya a k'auyenmu yanzu gashi d'azu lokacin da ya zo kirana muje wurinku sai da ya yi man d'aya yanzu haka Ina jin macizai sun fara taruwa a cikina kin gani WALLAHI cikina ya k'ara yin k'ato" Hajiya Mama ta yi shiru tana nazarin maganganun Dijen sai cen ta nisa tace,. "To ta yaya yake yi maki cikin halan don inji in yi masa fad'a ya daina kada ya sake??" Dije ta b'ata fuska tare da ciro hannunta duka biyu ta nunawa Hajiya Mamar tace,. "Duba ki gani kowane hannu nawa da kike gani akwai cikinshi d'auke a ciki, gashi ina jin tsoron macizai da yawa idan na haifosu bansan ya zanyi da su ba" Hajiya Mama ta yi murmushi irin nasu na manya tace "waton hannun naki ya rik'a ko ko ya abun yake ne?" Dije ta goge hawayenta tace,. "Eh rik'e man ya yi har sau biyu shiyasa Nike jin tsoron ya sake yiman cikin, idan ba haka ba WALLAHI zan yi addu'a in mutu kafin lokacin sai ya san yanda zai yi da macizan idan sun fasa cikina sun fito" Hajiya Mama ta rik'o hannunta tace,. "Wa ya sanar da ke hakan halan??" Dije ta goge hawayenta tace,. "Innata" Hajiya Mama ta yi Yar dariya sannan tace,. "Alhmdllh Innarki ta yi gaskiya sai dai ita baki gano abunda take nufi ba shiyasa, abunda take nufi shine idan har wani daban wanda ba Mjinki ba ya rik'a hannunki to anan ne za ki yi cikin macizan, amman kuma in dai har Mijinki ne ya tab'a hannun anan kam ba wani cikin macizai da zaki yi sai ma lada da zaki samu, ki yi tunani shin lokacin da ya rik'a hannun naki anyi maku aure ne ko kuma kafin ayi?" Dije cikin sanyin jiki ta ce,. "Bayan anyi addu'ar d'aurin auren ne" Hajiya Mama tace "Alhmdllh to kinga yanzu gaskiya ta fito saboda haka tashi mu je in rakaki da kaina ki yi kwanciyarki a cen da safe ki zo in baki wani labari" Dije ta marairece Hajiya Mama ta rik'o hannunta suka nufi d'akin Safwan, Safwan kam yana kwance Kan gadonshi ya zurfafa dogon tunanin abunda yake so ya aiwatar saboda cikar muradin Abokinshi, yana cikin nazarin ne sai gashi ya ji k'wank'wasar d'akin cikin sanyin jiki yace "Come in!" Dije ta shigo kanta a duk'e tana zunb'urar baki, ba shiri ya yi zumbur ya mike tare da nunata da d'an yatsa yana fad'in "Wa ya kawoki d'akin......." Maganarshi ta mak'ale ne saboda ganin Hajiya Mama a bayanta, cikin sage hannu ya sosa kanshi ya sami gefen gadon ya zauna tare da duk'e kanshi yana feso iska a bakinshi, Hajiya Mama ta zaunar da ita a Kan gadon tace "Ga Matarka nan sai da safe Ubangiji ALLAH ya baka ikon rik'e 'yar Mutane amana" Tana k'are maganar ta d'ago fuskar Dije da hawaye suka wanke mata fuska shab'e shab'e tace "Sai da safe 'yata ALLAH ya baku hak'urin zama da junanku" Sannan ta fice daga Safwan har Dijen ba wanda ya yi dogon motsi har aka kwashi tsawon lokaci, sannan Dije ta mik'e tsaye zata fita ya yi saurin rik'o hannunta aiko ba shiri jikinta ya d'auki rawa tare da kallon hannun tana k'ok'arin k'wacewa, sai dai kasancewar ba rik'on wasa ya yi mata ba shiyasa bata sami damar k'wace hannun ba, cikin fushi tace "Wai me yasa kai kake jin dad'in rik'e man hannu ne WALLAHI ka ci sa'a ance ba wani cikin su macizai da zanyi da WALLAHI duk na haifosu kaine na farkon wanda zan sa su ciccije yasin" Safwan ya mike tsaye tare da sakin hannunta ya d'auko filo ya d'ora akan doguwar kujerar da ke d'akin, sannan ya je ya rufo d'akin ya dawo ya ce da ita "Kinga wajen kwanciyarki a nan ki kwanta kuma kada ki kuskura inji minsharinki don ba abunda zai hana ni in fiddaki ki kwana waje matuk'ar kika dameni" Dije ta kalli kujerar ta fisgo filon ta ajiye k'asan carpet d'in ta yi kwanciyarta tana murgud'a Baki, Safwan ya yi saurin kawar da kanshi gefe tare da dafe goshinshi ya yi jarumtar jan k'afafuwanshi ya hau gadonshi ya kwanta, ya d'auki lokaci yana nazari sannan ya yi saurin tashi zaune tare da kiran sunanta a hankali yace "Khadija!!!" Dije kam tuni Bacci ya yi awon gaba da ita, ya kirata ya fi sau uku amman bata san ma ya yi ba, jiki a mace ya sauko a hankali ya tallabota tamkar Yar yarinya ya d'orata akan gadon, yana gyara mata kwanciyar ne hular kanta ta sub'uce aiko sai ga himilin gashinta ya hango, don kuwa duk da zirin kitson duka suke a dunkule amman sunyi mata ganwo a baya, don a kallo d'aya za'a gano baiwar gashin da Ubangiji ya wadaceta da shi gashi baki k'irin. Cike da mamakin ganin gashin nata ya sauko gadon ya kwanta kan kujerar tare da sauke wata ajiyar zuciya, haka ya kwana yanata juye juye saboda tunanin da ya dameshi wanda yasa shi kasa natsuwa. Dije kam lami lafiya ta yi baccinta duk da zuciyarta cike take da tsoron had'a d'akin da ta yi da shi a matsayinshi na Namiji. Shiyasa ko da Asuba ta yi ta rigashi tashi ta nufi k'ofar d'akin da nufin ta koma d'akin Hajiya Mama, sai dai ganin d'akin rufe duk da akwai key a jikin k'ofar amman ta kasa yanda zata yi ta bud'e d'akin, don kuwa jawoshi take yi iya k'arfinta amman ko gezau bai yi ba, ganin hakan yasa ta fara bubbuga k'ofar sai ga shi ya tashi firgigit tare da kai kallonshi gareta, cikin d'aga murya yace "Wai ke me yasa kika cika rashin hankali ne? Me kike son yi ne?" Ba tare da ta waigo ba tace, "fita zanyi" Cikin sanyin jiki yace "Kinyi SALLAH?" tace "a'a itace zan je inyi" Ya mike tsaye ya zo bayanta ya tsaya yace, "Ki jira ki yi SALLAH kafin ki tafin" Yana kare maganar ya nufi toilet d'inshi ya d'oro arwallah ya fito ya bata umurnin ta je ta yi arwallah a bayin ta yi SALLAH kafin ya dawo masallaci. Dije kam yana fita itama ta fece zuwa d'akin Hajiya Mama, inda ta taradda ita tana sallahr itama, Kai tsaye ta wuce toilet d'inta ta yi arwallah ta fito ta saka hijabin da Hajiya Mama ta bata ta yi SALLAH da shi jiyan, sannan ta tayar da sallah'rta ba tare da ta tsaya shimfid'a komi ba, tana k'arewa ta fara jero adduointa a bayyane kamar yanda ta saba kullum kamar haka "ALLAH ka sani Aljannah ka sa Innata da Baffahna da Gambo, Allah ka bani Miji nagari wanda zai dinga siyoman tsiren da Baffah yake siyoman, ALLAH ka sa in zama Likita in dinga yiwa Yaya Usmanu Allura, ALLAH ka sa nice Matar Malam Lawi a Aljannah" Hajiya Mama da ke zaune tana lazimi ba shiri ta waigo tana kallonta zuciyarta cike da fad'uwar gaba saboda sunan Lawi da ta ji ta ambata. Akafta😆 D/AUTA CE✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *Masha ALLAH Mutanen Dije sannunku da k'ok'arin comments all musamman wad'annan groups d'in:* *Mata Rahama group* *D/Auta Novel Fan's* *Dijen K'arangiya fan's* *TAURARI fan's 1&2* *Fadar Ummun fareesa fan's* *Fatima ce ko zarah fan's* *Aseela fans group* *Salmancy fan's group* *Tamegari Novel fan's* *K'aramar bazawara fan's* *Daular Billyn Abdul* *Kwai cikin k'aya fan's* *Novels Arena group* *Maman Maleek group* *Zauren Uom Mumtaz & Zaratan Mata group* *Dukanku all ina godiya sosai da dad'ad'an comments dinku kai har ma da wad'anda ban lissafo ba ku sani duk inda kuke HADIZA D/AUTA tana yinku all💋* *Lamba ta 29* Cike da mamakin abun Hajiya Mama ta dinga jan carbon tana kallonta har ta kammala jaye sauran 'ya'yan carbin da suka rage ta yi addu'a a gajarce ta shafa ta kalli Dije da har lokacin sai maimaita addu'ar take yi kanta a sama idonta suna kallon rufin d'akin, sai da ta bari ta kammala don kanta sannan tana k'ok'arin yi mata magana Dijen ta janyo jikinta ta k'araso gabanta ta duk'a tare da sunkuyar da kanta k'asa tace "Ina kwana Hajiya ALLAH ya biya ya saka da gidan Aljannah ALLAH karo maku kud'i ku yi ta cin dad'inku" Hajiya Mama da ke ta fad'in "Ameen Ameen" addu'ar Dije ta k'arshe tasa ta yi guntun murmushi sannan tace,. "Naji kin fad'i sunan Abokin Safwan Lawi shi miye dangantakarki da shi ne??" Dije ta yi saurin gyara zamanta ta rufe ido tace,. "Shine ya so ya aureni Babana ya hana kuma bayan yace zai sakani Makaranta har in zama Likita" Hajiya Mama ta yi shiru sannan tace,. "to ya aka yi shi Safwan aka amince ya aureki??" Dije ta b'ata fuska tace "Wai cewa ya yi nace Zan kashe Balan Duduwa bayan Ni WALLAHI ban tab'a cewa haka ba" Ta k'are maganar cikin zubowar hawaye sannan caraf ta tuno da alk'awalin da Safwan ya yi mata akan cewa in tace itace ta fad'a zai sakata Makaranta, aiko ba shiri ta washe Baki tace "Laah! Kinga na manta ashe aljanuna ne Suka fad'a ba Ni ba" Mama ta sake zaro Ido tace,. "Aljanu gareki???" Dije ta rufe Baki tace "In fad'a maki gaskiya?" Mama ta d'aga Kai ba tare da ta sami damar magana ba, Dije ta washe bakinta tace "Tsakani da ALLAH Ni kam bani da komi amman fa ke kad'ai na fad'awa don ALLAH kar ki fad'awa kowa kinji?" Hajiya Mama ta yi Yar dariya tace "idan har kina son kar in fad'a to sai kinyi man alk'awali ba zaki sake k'aryar aljanu ba kin amince?" Ta yi saurin d'aga kai tare da cewa "ai dai ke Zaki sakani Makarantar Likitar ko?" Hajiya Mama tace "in dai kina so Kuma Mijinki ya amince to Ni zan sakaki da kaina, amman sai in kin daina yawan surutu sannan duk abunda kika gani wanda Baki sani ba ki zo ki tambayeni" Dije ta ce "WALLAHI Ni nama bari daga yau idan ma kina so ki lissafaman da me da me zan dinga fad'a kullum don bana son inyi abunda zai sa ki fasa sakani Makarantar, bayan kuma ga shi Ni nike son in dinga yiwa Usmanu allura saboda kullum sai ya dakeni ya yi ta man fad'a sai kace shi ya haifeni" HAJIYA Mama tace "ya kike da shi?" Tace "yayana ne fa Baki ganshi ba WALLAHI mugu ne Abu kad'an sai ya dakeni don ma Baffah baya bari ya dakeni wani lokaci, amman kinga Innata WALLAHI itama baki ga dukan da take yi man ba ko tausayina bata ji, amman ai ke nasan ba zaki dakeni ba ko???" Hajiya Mama ta sauke tagumin da ta yi tare sauke wata nannuyar ajiyar zuciya tace "Ba zan dakeki ba amman idan kin daina rashin jin da kike fa, don ko ita Innar taki don baki barin rashin jin ne yasa ta ke dukanki" Dije zata yi magana sai ga wata Yar aiki ta k'wank'wasa d'akin da sallamarta, Hajiyar tace ta shigo ta shigo tana yi mata Ina kwana tare da sanar da ita an kammala komi na break fast d'in, ta bata umurnin da zata bata ta fice sai ga su Surry sun shigo kowacensu da Hijabinta har k'asa suna gaidata, fiddo ta zauna tana sunne dariyarta saboda ganin Dijen ya sa ta tuno shirmen da ta yi ta bugawa jiyan, Hajiya Mama tace da su su gayar da Matar yayansu Fiddo ta zaro Ido tace "Haba Hajiya ita wannan yarinyar na fa girmeta WALLAHI" Surayya ta rik'o hannun Dijen tace,. "Matar yayanmu ina kwananki dafatar dai kin tashi lafiya?" Dije ta washe Baki tace,. "ke kam kina da kirkinki don kinfi wannan mai ido mitsi mitsin" Fiddo ta maka mata harara zata yi magana sai ga Safwan ya yi sallama, aiko ba shiri suka mik'e dukansu za su fita cikin rawar jiki Hajiya Mama tace "A'ah fiddo ki k'arasa maganar ai ko don......." Fiddo ta yi saurin d'ora hannunta a baki tana yiwa Hajiya nuni da hannunta alamun ta yi shiru, yana shigowa suka gayar da shi suka fice da saurinsu ya k'araso ya zauna tare da gayar da Hajiyar. Dije ta kalleshi tace "Ina kwana Malam?" Safwan ya yi banza da ita Hajiya Mama ta yi kamar bata lura ba ta k'wallawa Surry kira sai gata ta shigo cikin fargaba, Hajiyar tace da ita taje da Dije d'akinsu ta yi wanka ta nuna mata duk abunda batasani ba, sannan ta ce ta je ta d'auko mata doguwar rigar da zata saka cikin kayan da tun kafin su zo aka siyo mata su na wuccin gadi, kafin ta zo aga girmanta da yanayinta a siyo mata wasu a d'inka mata dai dai ita. Surayya ta d'auko rigar ta ja Dijen suka fice Hajiya Mama ta kalli Safwan d'in ta sauke ajiyar zuciya tace,. "Ya tashin bak'in??" "Lafiya k'alau yanzu na dubosu har ma naga an Kai masu abun breakfast ai" Ta yi shiru sannan tace,. "to sai ka yi k'ok'ari cikin kwanan nan a k'arasa gyara abunda ke b'ukatar gyara a gidanka ka kai Matarka a cen ku zauna" Safwan ya shafa kanshi yace,. "Ta yi zamanta a nan kawai Hajiya Mama in da hali ma ta shiga cikinsu delu mai'aiki kawai su ci gaba da aikin gidan" Hajiyar ba shiri ta zaro Ido tace,. "Me kake nufi da hakan?" Ya yi saurin dafe kanshi yace,. "ta zama 'yar aikinki kawai Hajiya don gaskiya Ni ba Zan iya zaman aure da wannan tatsitsiyar yarinyar ba, musamman ma dai a yanda take d'in nan Tiphical Yar k'auyen nan?, Kai ina bazan iya ba gaskiya ai sai ta janyo ayi man dariya, ALLAH na tuba Hajiya me zan tsinta a jikinta Ni Kam!? astagfirullah ALLAH ya rabani da kayan takaici WALLAHI" Not edited😕 Ayi manage plss 😍😍 Akafta🤣 D/AUTA CE✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *Wannan page kyauta ce gareki sukutum Kanwata ta hannun damata, wadda nije jinki har cikin b'argona, ke ta daban ce a wajena HANNAH MAHMUD SUHANA ina yinki har abadan abade😍* *Lamba ta 30* Yana k'are fad'ar maganar ya mik'e tsaye zai fita har ya kai bakin k'ofa zai fita, Hajiya Mama ta kira sunanshi cikin wata muryar da shi kanshi sai da ya ji kiran ya fad'ar masa da gaba, cikin sanyin jiki ya dawo ya zauna tare da b'ata fuska tamkar wanda aka daka yace "Nasan tambayar da kike son ki yi man Hajiya Mama plss ki yi hak'uri WALLAHI ni ma bansan me ya ja ni na kasa barinta ta auri D'ankauye irinta ba, ni dai abunda kawai na sani taimakonta na yi niyyar yi saboda naga tana son karatu sosai,kuma matuk'ar ta yi aure wannan bak'in k'auyen na su to gurinta ba zai tab'a cika ba, kinji abunda ya sa na aureta Hajiya Mama don nasan Mahaifinta ba zai bani ita haka kawai ba in zo da ita" HAJIYA Mama tun daga kallon da ya ga tana yi masa ya gano cewa maganarshi bata yi tasiri a wajenta ba, shiyasa ya yi shiru dolenshi zuciyarshi cike da takaicin me ma yasa bai barta ta yi aurenta ba?. Hajiya Mama ta sauke wata nannuyar ajiyar zuciya sannan tace,. "Baka sonta ka hana Abokinka Lawi ya aureta??? Bayan kasan cewa shi ma ai taimakonta yake son ya yi akan buk'atarta me ya hana ka taimakeshi ya sameta????" Safwan ya sosa kanshi yace "ai baya garin ne shiyasa da ni ba abunda zai sakani wannan aikin, saboda haka ki barta a nan kawai ta shiga cikin ma'aikatan, su ci gaba da aikinsu kud'inta na wata idan an tara zan dinga aikawa iyayenta" Hajiya Mama ranta a b'ace tace,. "Safwan ka fita idona in rufe yarinya dai ko kana so ko baka so yanzu ta zama matarka, kuma ko kai baka isa ka kunce shi ba matuk'ar ina raye, kai ko bayan raina ban amince da ka saki yarinyar cen ba matuk'ar ba wani k'wak'k'waran dalili ba" Safwan ya yi saurin fad'in "haba Mama WALLAHI ni bana son zama da ita da sunan aure ki bari kawai a taimaketa ta yi karatun shikenan kin ga zamu sami ladar, amman a ajiye zancen auren kawai Hajiya Mama yafi gaskiya, don ni Makaranta ma zan koma in k'aro karatu har zuwa lokacin da zan sami wadda nike so in aura" Ranta ya kai iya k'ololuwar b'aci tace,. "Tashi daga gabana Safwan bana son in sake jin wata magana daga bakinka, ka je kawai akwai ranar da gaskiya zata yi halinta, amman ina son ka fara cukucukun nema mata Makarantar saboda ka samu ka cika alk'awalin da ka d'auka tun wuri" Safwan ya marairece yace,. "Don Allah Hajiya Mama kiyi hak'uri naga kamar ranki ya b'aci WALLAHI bana son ganin fushinki ke ma kin sani, kada ki bari wannan 'yark'auyen ta shiga tsakanina da ke don ALLAH" Ta yunk'ura ta mik'e fuskarta a sake tace,. "Ka je ka ji da bak'in in sun kammala in zo mu gaisa amman ina son kafin su tafi ka kai Mahaifinta Gidanka ya ga muhallin 'yarshi" Safwan ganin yanda yanayinta yake ya sa bai musa ba ya mike ya fice, zuciyarshi cike da tunanin yanda zai yi ya kunce auren cikin ruwan sanyi ba tare da ya b'ata ran Hajiya Mama ba. Dije kam tana cen Surry tanata shiryata cikin tsanaki duk da taso ta zuba d'ige d'igen kwalliyarta da ta saba amman Surryn ta hanata, sai ko ga Dije ta fito Masha ALLAH da ita saboda daman cen ita mai kyau ce duk da ta kasance bak'ar Mace, amman bak'inta mai kyau ne don bai b'oyewa kyawunta fitowa ba, Dije sai wasar baki take yi tana kallon kanta cikin madubi ta makawa Fiddo harara tace da Surry "Ashe haka nike da kyau ni ma ban sani ba? Ji rigar nan WALLAHI ta yi man kyau sosai amman ta Makkah ce ko?" Surry tana 'yar dariya tace, "a'ah a nan garin aka siyeta ba ma ita kad'ai ba ce da wasu ma suna d'akin Hajiya Mama kuma donki kawai aka siyo su, ki yi ta sakawa ke ma ki zama 'yar gayu irin Fiddo" Dije ta waiga ta kalli Fiddon da ke ta dariyarta tace, "A'ah bana son in zama irinta irinki na ke son zama har da farinki ma don ALLAH ki sani a injinin da ake maku wanka da shi ni ma ya wankeni tas! in zama fara irinku in na koma garinmu su Ladiyo su kasa gane ni" Fiddo me zata yi ba fashewa da wata arniyar dariya ba tace, "to ai ke bak'in da shi aka haifeki mu ko farare ne na asali ta ya zaki had'a kanki da mu? Cab! Ki dai ciji bulo 'yanci tara sai kuma idan har farin shago kike so sai a siyo maki mayukan bleaching da allurori ki yi fess har ma ki fi mu farin tunda ke bak'ar gasar tsiya ce da ke, daga ganin Sarkin fawa sai miya ta yi zak'i to WALLAHI ki sake tunani don mu in banda k'addara ma mi yaya Safwan zai had'ashi da ke har ya kwasoki ya kawo muna cikin gida??" Dije ta mik'e tsaye tace,. "Kan uban nan amman ina ganin baki san Dijen Baffah ba ne d'iyar Inna Hasiya kanwar Usmanu Mijin Hansai? Cabd'i jam ai billahillazi kada ki bari mu gauraya ni da ke, kin ganni yar tsiton nan ko ta tsaf zan had'a maki jini da majina in sauya maki kamannu cikin k'ank'anin lokaci, don ki gano cewa wacece asalin Dijen Baffah?ke garinmu kaf tsorona ake ji daga abokanaina har yaran garinmu duka, don haka ki daina shiga sabgata idan har kina son ki tsira a wajena" Fiddo ta taso ta zo gabanta ta tsaya Surry ta yi saurin fad'in,. "WALLAHI kika tab'a 'yar Mutane ba ruwana sai na fad'awa Yaya Safwan" Dije ta yi mata wani kallon tace,. "Ke wai a nufinki dukana zaki yi? Cabd'i jam to WALLAHI kar ma ki soma tun wuri na baki shawarar gari, idan kuma kinki ji ai ko ba zaki k'i gani ba don ko shi yayan naku yasan halina ku tambayeshi zai gaya maku don bai sha ta dad'i wajena ba shi ma." Fiddo ta turata baya tace,. "Wai ke me kike tak'ama da shi ne bak'auyiyar banza d'iyar talakawa me kuke da shi a gidanku halan da Yaya Safwan zai k'yaleki ki rena masa wayo bai jibgeki ba??" Dije ta kalli Surry tace "Kin dai gani ko? kuma ke ce sheda ko? To duk abunda na yi mata WALLAHI kar ma ace za'a ga laifina, don ko yanzu sai da Baffahna ya yi man wa'azi yace kada in ce zan rama abu in yi hak'uri amman duk da hakan ta koma ba fa zan k'yaleta ba WALLAHI" Fiddo ta fad'a gado tana cin uban dariya saboda ganin take yi Dijen ba wata ba ce a duka d'aya zata bugeta saboda ganin yanda take 'yar firit gata siririya ba wani kumarin kirki, Surry kam janyo hannunta ta yi suka fito zuwa diny suna karyawa abunsu tana cin dariyar Dije idan ta yi wani abun. A gefen bak'i matan kuwa Hajiya Mama ta je sunyi Ina kwana sannan suka yi mata godiyar dawainiyar da aka yi da su, ta kawo alkhairi mai yawa ta Basu ta bangaren atamfofi da kud'i, sannan ta nufi inda su Baffah'n suma ta gaisa da su suma ta yi masu alkhairi sosai, Baffahn ya d'auko dunk'ulallin kud'i da zasu Kai dubu d'ari biyu ya mik'awa Hajiyar ya ce a yiwa Dije kayan d'aki da su, saboda ganinta da ya yi mace Mai nagarta da kamalar mutanen kirki a fuskarta. Hajiya Mama tace ya barsu kawai ya je da su ya kara a kasuwarshi ita zata d'auki nauyin komi, Baffah ya dage shi kam ba zai koma da su ba a matsayinshi na Mahaifinta dole ne ya sauke nauyinta da ALLAH ya d'ora masa nata, sannan Hajiya Mama ta karb'i kud'in ta fito da nufin ta kira Dijen su yi sallama da Mahaifinta. Aiko ba k'aramin dad'i Baffah ya ji ba da ya ganta ta sha wankanta masha ALLAH a lokaci d'aya ta fara canzawa, cikin jin dad'i ya dinga murmushi yana cewa "Anya Dijengalata nan gaba ko zan ganeki kuwa? Wannan gayu haka ai sai in za ci canza man Dijen tawa aka yi" Dije ta rufe fuskarta tana dariya tace,. "Ai Baffah ni ma naji dad'in zuwa gidan nan WALLAHI baka ga yanda Matar gidan take sona ba, sai dai kanwar Malaminmu fa WALLAHI Baffah ta cikani dukan tsiya zan mata sai dai a maidani garinmu" Baffah ya zaro ido yace,. "Kar ki soma Dije Kar inji kar in gani ki barta ta ci albarkacin Hajiyar tunda kince tana sonki ko?" Dijen ta d'aga kai tace, "Kuma ma ta ce zata sakani Makaranta fa" Ya ce "to kin gani don ALLAH kar ki tab'a kowa gidan nan kinji ko Dijeta?, In har kina son in na tafi in siyo maki wata sabuwar akuya ki had'a biyu" Dije ta washe baki ta ce "ina so Baffah ka siyo man ba zan biyeta ba ka ji?" Haka suka dinga firarsu yanata d'orata akan hanya a fakaice har su Baba Ali su ka zo da tashar motar da aka d'auko masu har gida, sannan suka yi sallama cikin mutunta juna kowa yana ganin girman d'an uwanshi, Dije kam da k'yar aka rabata da Baffah'nta saboda Uban kukan da take ci tana fad'in ta fasa karatun ita gida zata koma, don shi ma kanshi Baffahn sai da yayi guntayen hawayen rabuwa da Dijenshi. Safwan ya yi masu jagora har katafaren gidanshi Baffah sai hamdala ya ke yi ga Ubangiji tare da jinjinawa hikimar Inna Gambo da ta fahimtar da hakan tun kafin ya zo ya ganewa idonshi. Abokan tafiyarshi ma da matan sai jinjina kai suke yi suna fad'in "ALLAH mai hikima yanzu wannan shi ne gidan Dije uwar tsiwa to ALLAh ya bada hak'urin zaman" Safwan ya yi masu sha tara ta arzik'i sannan suka yi sallama da juna ya dawo gida su kuma Direba ya kwaahesu suka miki hanyar komawa gida. Sauka lafiya😅 Akafta😊 D/AUTA CE✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *Masha ALLAH Mutanen Dije sannunku da k'ok'arin comments all musamman wad'annan groups d'in:* *Ina farin cikin tayaki murnar cenye gasar da kika yi Ƙanwata waton Balkisu Muhammad Garkuwa (Ummi) ALLAH ya ƙara basira da ɗaukaka kuma ya ƙara dafa maki ga dukkan al'amurranki na yau da kullum tare da mu gaba ɗaya🤲🏻* *Lamba ta 31* Mai motar har ƙofar gidan Maigarin ya ajiyesu, kowane zuciyarshi cike da farin cikin nasarar dawowa gida lafiyar da suka yi, kafin kace me ƙofar gidan ta cika maƙil da yara da manya tare da wasu sauran matasan garin da suka rako motar tun daga farkon shigowa har zuwa ƙofar gidan Maigarin, sai kuwwa ake yi ana ta yi masu sannu da zuwa saboda uwar tafiyar da suka shawo. Ba ƙaramin daɗi Maigarin ya ji ba saboda ganin karamcin da Safwan ya yi masu, don saƙonshi daban na musamman Safwan ya bada akawo mashi, don manyan riguna ne na alfarma waɗanda suka sha aiki tun daga sama har ƙasa kala biyu ya bada akawo mashi tare da turaruka masu kyau. Shiyasa mai motar bai bar garin ba har sai da aka ciyar da shi da abinci yaci ya ƙoshi sannan ya kama hanyar komawa gida, Baffah da sauran waɗanda suka tafi kowa ya nufi gida zuciyarshi cike da farin cikin wannan tafiyar arziƙi da suka yi. Inna Hasiya zaune ta yi ta tasa saƙon da Hajiya Mama ta bada akawo mata a gaba tana kallo, zuciyarta cike fal! da farin cikin ganin Dijenta ta yi sa'ar aure har ma da dace da suruka tagari da tayi, ba tare da ta tantance ba sai jin ta yi hawayen farin ciki suna sauka a kan fuskarta, cikin farin ciki Baffah ya ce "Ba kuka zaki yi ba godiya ya kamata ki yi don kam tabbas Dije ta yi sa'ar aure, don ina tabbatar maki da cewa kaf faɗin garin nan namu ba wanda ya isa ya nunawa Dijeta Miji ke har ma da mutanen birnin duka, saboda ALLAH cikin hikimar ya jefo muna yaran nan don kawai su haska rayuwar Dijenmu, na yarda da maganar Inna Gambo da tace shi bawa bai san ta inda alkhairinshi yake ba, fatanmu kawai yanzu ALLAH Ubangiji ya basu zaman lafiya kuma ya ƙara masu haƙurin zama da Dijen" Inna ta saka gefen zane ta share hawayenta cikin sanyin jiki tace,. ,"Ameen Malam amman ina jin tsoron Dije ta je ta yi abunda zai janyo girmanmu ya zube a idanunsu ka fa san halinta sarai, ko mu ya muka ƙare da ita balai Mutanen da basu san halinta ba?" Baffah ya maka mata wata ƙatuwar harara ya ce,. "Idan kin san bakinki ba zai faɗi alkhairi akanta ba to ki yi haƙuri bana son maganar don ALLAH" Inna ta miƙe tsaye tana ƙoƙarin kwashe kayan tace "ALLAH ya baka haƙuri ita kuma ya sa ta canza ta zama dai dai da yanda ake son kowace macen kirki ta kasance gidan Mijinta" Ya yi saurin sakin fuskarshi yace, "Ameen ko ke fa? Haka ya dace ki ce tun farko, ba ki wai ki zauna kina ta janyo maganganun da idan aka aunasu dai dai suke da muguwar fata ba" Inna za ta yi magana kenan sai ga Usmanu ya shigo bakinshi har kunne ya ƙaraso wurinsu yana faɗin , "Sannu da zuwa Baffah ya hanya?" Baffah ya washe baki yace, "Alhamdulillahi Usmanu ALLAH ya nufa mun dawo lafiya tare da abun alkhairin da aka cikomu da su" Inna ta ajiye ledar da ke hannunta tana murmushin jin daɗi, Usman sai duba kayan yake yi yana faɗin "Kai! Kai! Kai! Lalle Baffah Dijenka ta zama hamshaƙiya waɗannan kaya haka?" Baffah ya janyo wata ledar ya fiddo shadda da turare yace,. "Kai ma ga naka sai ka ji daɗin yi wa ƴar uwarka addu'ar zaman lafiya gidan aurenta" Usmanu cike da jin daɗi ya karɓa tare da rufe Bakinshi ya ce, "cabɗi ashe muma za mu shana? to ALLAH ya ba su zaman lafiya Baffah, kuma ya sa ta rage rashin jin nata don kar ta je ta janyo muna abun magana" Baffah ya tsuke fuska yace,. "Alkhairi zaku gani daga kai har Uwarka, tunda ta bar maku filin gidan ai sai ku wataya yanzu" Yana ƙare faɗar maganar ya miƙe ya nufi waje saboda sallamar da ya jiyo ana yi masa a ƙofar gida. Inna da Usmanu suka bishi da kallo cikin sanyin jiki Inna tace, "Ni na rasa gano inda Malam ya nufa da mu da kullum yake ganin kamar mu bama son Dijen" Usmanu ya yi saurin faɗin , "ya san sarai duk muna sonta Inna kawai dai don tana ƴar gaban goshinshi ne yake ƙin son a faɗi aibinta, bayan kuma mu gaskiya ce muke kai kuma ita muke faɗa, saboda gudun a barta ba kwaɓa ba hantara ta ƙara sangarcewa aje a shiga uku, yanzu dai tunda komi ya wuce fatan da za mu yi mata shine ALLAH yasa wannan auren ya zamo silar shiryuwarta, don kin ga mu fa in mun juri halinta WALLAHI su cen ba jura za su yi ba" Inna ta sauke ajiyar zuciya tace, "ALLAH dai ya sa ta gyara mu ma ai farin cikinmu ne Usmanu" Muryar Baffah da suka ji yo a bayansu yana faɗin "Ameen" shi yasa duk suka miƙe kowa ya nufi sabgoginshi, Baffah ya yi guntun murmushi yace "Kuna nan zaune kuna gulmar Dije zaku ganinta ta zamo Babbar Hajiya ba tare da kun tantance ba" Usman ya ƙumshe dariyarshi ya shige ɗakinshi zuciyarshi wasai saboda ganin bakinsu zai huta da bari barin Dije. Kafin ka ce me gari ya ɗauka Dije ta auri ɗan gidan masu kuɗi a birni mutane sai shigowa yiwa Inna da Baffah sam barka ake yi,su Jummala da Lanti sun ji ina ma ace su ne suka sami wannan damar, don ko Balan Duduwa ma da ya ji labarin abun alkhairin da aka yi wasu Baffah kai tsaye ya nufi ɗakin Duduwa Bakinshi a washe yana faɗin "Kin gani ko Duduwa ke da ke yi man faɗa kan abunda na yi yanzu ga shi ko Mahaifinta ya ji daɗin abun har wasu ma sun sheda" Inna Duduwa ta maka masa wata ƙatuwar harara ta ce "Kai tafi cen sakaran banza ashe daman cen son da kace kana yiwa Dijen na ƙarya ne tunda har ka karɓi kuɗi a matsayin fansar son da kake yi mata" Balan ya turo baki irin na sangarta yace,. Haba Duduwa yanzu don ALLAH duk wannan tsiren da nake siyo maki kullum baki gode ba?, Yanzu ga shi naci riba biyu ga Matata kuma ga kuɗina ina mora, Ni dai WALLAHI kam banyi nadama ba don ni da ma zai sake ganin Ladiyo ya ce in bar masa ita ya biyani wasu kuɗin tsaf zan bar masa ita, ai da arziƙi gidan wasu gara gidanmu WALLAHI cab! Ai ni....." Sai jin ya yi muryar Ladiyo a bayanshi da ke ƙoƙarin shigowa tana faɗin, "ai ni ma WALLAHI da ashe zai ganni ya ce yana so da sai nafi kowa murna, ko da zan huta da tusoshin da kake buga mani duk daren ALLAH kafin safiya ta waye ka yi ashirin" Bala ya zabura ya ce, "Don Ubanki ba tare da ke muke cin ƙuli ƙulin tsiren ba? Ko ba ke ma kina tusar ba? Shikenan ni na haƙura banyi ƙorafi ba ke zaki zo kina tona man asiri gaban Duduwa, to ba zaki sake cin tsiren da ƙulin ba baƙar munafuka" Ladiyo ta riƙe ƙugu tana maka masa harara sama da ƙasa tana murguɗar masa baki, Duduwa ta yi sakato tana kallonsu cike da takaici tace,. "Kun dai ji haushi ku kam! Amman ko da yake kai ne babban mai laifin ba ita ba, ALLAH ya shiryeka da baƙin halin da ka tsirowa kanka daga jin ɗimin kuɗi a hannunka ka rikice saboda zalama, to tsiren ma idan ka sake kawo man sai na ci mutuncinka sakaran banza" Tana ƙare faɗar maganar ta ɗauki zanenta ta yafa ta bar masu gidan tana tafe tana faɗa har gidan Inna Gambo, kasancewar ƙawarta ce ta ƙud da ƙud tun ƙurciya har yanzu da suka manyanta. Sai dai faɗanta ya tsaya ne saboda ganin Gambo rungume da atamfofi biyu tana murna bakinta yaƙi rufuwa sai zubawa Dije ruwan addu'a take yi, Duduwa ta janyo kujera ƴar zuƙunno ta zauna tana faɗin "Gambo wannan farin cikin daga ina haka?" Gambo ta ɗaga Atamfofin sama tana kallonsu ido cikin ido tace,. "Daga hannun Jikata Dijen Sanda saƙo ne tun daga gidan mijinta ta çe akawo mani in saka in ji daɗin yi mata addu'ar nasarar zaman lafiya da Mijinta" Gambo ta yi shiru sannan ta ce "Ah lalle dole ki yi farin ciki sosai to ALLAH ya haɗa hankulansu kafin nan da shekaru mu ga ƴan dugadugai suna yawo a tsakiyar gidan nan naki" Gambo ta yi saurin faɗin, "Allahumma Ameen Duduwa karɓi goro ki tamna don mu ji daɗin yin firar" Duwawa ta karɓi goron ta kai bakinta ta ramtsa tace, "Lalle wani hani ga ALLAH baiwa ne ya hanata Bala ya baiwa ɗanbirni, to ALLAH ya basu zaman lafiya daga ita har Balan tare da Matarshi Ladiyo" Inna Gambo tace "Ameen ya rabbil'alamina Aminiyata" Dije kam............😛 Ku yi manage insha ALLAHu maybe anjima ku jini matuƙar na samu yanda nike so😁 Akafta🤗 D/AUTA CE✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *BAƘON YANAYI ne sunan Book ɗin don haka idan kin san baki karantashi ba to ki garzayo da gudunki don kar ayi babu ke, da 300 kacal zaki sameshi a complete ɗinshi ki yi yanda kike so, don ke da kanki zaki banbance tsakanin tea da shayi kada ki bari a yi babu ke salonshi daban ya ke da saura don tun daga sunan zaku gane cewa fa shi ɗin na daban ne, ga mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09032685442 sai na ji ku👍🏻😅* *Lamba ta 32* Dije kam kwana biyu da zuwanta Yola Hajiya Mama ta sa Safwan ya fara yi mata lesson, saboda a cewarta don ta sami ƙarfin gwiwar tunkarar makarantar da za'a sakata da kyau, aiko sai ga shi duk da kyarar da yake yi mata hakan bai hanata fahimtar karatun da yake koya mata ba, don wannan karon ma ta ci Sa'a da Hausa ya ke fahimtar da ita duk wani abund bata gane ba, don wani zubin ma Hajiya Mama a gabanta ake karatun saboda cin zalin Dije da yake yi, duk da aranta wani lokaci sai ta ƙudurta ramawa sau kuma ta tuno huɗubar da Baffah'nta ya yi mata sai ta fasa, sai dai ta yi ta binshi da harara tana cizon yatsa saboda kullum cikin dare sai ta yi kukan rashin ganinsu. Sai dai ta samu Surry da Hajiya Mama suna ina ka aza da ita komi take buƙata ko da bata faɗa ba yi mata ake yi, abinci ma kala kala ake baje mata ta ci wanda take so, Fiddo kam yanzu tsakaninta da Dije sai harara da murguɗar baki saboda faɗan da Hajiya Mama ta yi mata sosai akan Dijen, tare da gargaɗi mai tsanani akan duk ta sake yi wa Dije gori ko ta ci zarafinta sai ta saɓa mata. A yau ma sati ɗaya da zuwan Dije gidan Garin suna babban falon gidan ne suna karatun kamar kullum, Safwan yana koya mata karatun tana gyangyaɗin Bacci don daman cen Dije ba gwanar firar dare ba ce, jin haushin baccin da take so ta yi bayan Hajiyar ta hana shi fita zuwa inda ya so ya je yasa ya fakaici idon Hajiya Mamar, ya janyo mata dogon tsoronta da ya fito cikin hular da ke saman kanta, cikin ƙeta ya janyo tsoron da ƙarfi ba shiri Dije ta ƙwallah ƙara tare da dunƙulewa tana kuka mai cike da takaicin hanata baccin da yake yi da muguntarshi kala kala. Hajiya Mama ta yi saurin faɗin,. "Ka kiyayeni Sawan me ta yi maka yanzu kuma?" Safwan ya sosa kanshi cikin sauri yace,. "Bacci fa take yi Hajiya Mama don ta renani ga shi ƙiri ƙiri ta sa an hanani fita kuma ta zo tana yi wa mutane baccin renin wayo" Hajiya Mama ta tashi cikin sauri ta riƙo hannunta tace,. "Tashi mu je ki yi baccinki tunda karatun na mugunta ne ake yi" Dije ta miƙe tsaye sai ga zobenta da Lawi ya bata ya faɗo ƙasa don ana karatun ta cire shi tana wasa da shi, bayan wucewarsu ne ya miƙe da nufin barin wajen sai ga shi ya hango Zoben, cikin ko in kula ya duƙa ya ɗauki Zoben ya saka aljihunshi ya nufi ɗakinshi, zuciyarshi cike da tunanin ina ta samo zobe mai kyau haka? Wata zuciyar tace da shi maybe Hajiya Mama ce ta bata shi, sai kuma cen ya tuno da zasu zo garin ya hango Zoben a hannunta, to wa ya bata? Haka ya yi ta yiwa kanshi tambayar da babu mai amsa masa, amman ya ci alwashin sai ya tambayeta ya ji ina ta samo zoben don yasan da sanin cewa kaf garinsu babu mai wayewar da zai iya bata kyautar Zoben. Haka kawai ya ji zuciyarshi ta kasa natsuwa don wata zuciyar tana sanar da shi cewa ƙila Lawi ne ya bata shi, haka ya kwana cike da takaicin da shi kanshi baisan mafarinshi ba. Shiyasa ko da safiya ma ta waye ƙin fitowa ya yi ayi break da shi kamar yanda aka saba kullum, sau biyu ana turo kiranshi yana faɗin zai zo amman yaƙi fitowa, dole Hajiya Mama bayan sun ƙare ta ce da Dije ta ɗauki nashi ta je ta kai masa,amman idan ta ga zai daketa ta dawo abunta kar ta zure ya yi mata dukan banza. Aiko cike da Sa'a tana ƙwanƙwasa ɗakin ya ce a shigo, ta tura ƙofar ta shiga tana ƙoƙarin ajiye wa ne ya galla mata harara ta ja baya kaɗan cikin tsoro ta ajiye zata fita ya yi saurin fisgota da ƙarfi sai gata ko ta faɗo jikinshi saboda kasancewarta lange lange ba wani kumarin kirki, cikin masifa ya yi saurin tureta ta faɗi ƙasa sai ga ta da saurin faɗin "Wayyo hannuna" Ya wurga mata harara sannan ya fito da zoben yace,. "Uban wa ya baki wannan Zoben???" Dije ta yi saurin kai kallonta ga zoben ta washe baki ta ce "Laaa ina ka ganshi?? Tun dazu nike ta nemanshi WALLAHI" Cike da takaicin rashin amsa masa tambayar da bata yi ba yace,. "Ina kika samo shi ko sata kika fara yi a gidan namu bamu sani ba??" Dije ta zaro Ido tare da rufe bakinta alamun firgici ta ce,. "Sata????" Ya ɗaga mata kai ya ce "Eh sata saboda wannan Zoben kaf ƙauyenku babu wanda ya isa ya yi maki kyautarshi" Dije ta miƙe tsaye cikin fushi ta riƙe ƙugu tace,. "Kam balasi me kake nufi da hakan? Ai billahillazi Ni ba ɓarauniya ba ce ka je ka tambayi Hajiyar taka idan na taɓa ɗaukar maku wani abu ka ji, kuma WALLAHI idan har ta rufeni kace da ita ban yafe ba......." Karaf ta ji saukar mari akan fuskarta ta yi saurin dafe kumatu cike da mamaki tace,. "Laaa! Laaa! Laaa! Ni ka mara? Me na yi maka da zaka mareni?" Safwan yana wani muzurai ya taso mata a harzuƙe yace,. "An mareki ke ɗin ɗiyar waye da ba za'a mareki ba WALLAHI idan baki faɗa man inda kika samo zoben nan ba dukan tsiya ne zan yi maki, ƙaramar mara kunya ko an faɗa maki ke wata tsiya ce da har za'a ji shayin sakin ƙwanji a jibgi abun banza?, Kwaɗayayyun banza kawai don masifa irinta baƙin ƙauyen naku ace wai mijin da zai aureki a siyeshi da kuɗi don bala'i kuma ya amince, to ki sani ni ba wai don ina sonki na auroki ba kar ki zargi hakan ki zo wa mutane da renin hankali, zaki faɗa ko ba zaki faɗa ba sai na kakkaryaki a gun yanzun nan?" Dije ta kawo iya wuya saboda baƙaƙen maganganun da yake ta jifarta da su, cikin fushi ta nunashi da yatsa tace "Ka daina gangancin sukar garinmu don Ni ma ba sonka nake yi ba tun farko da Malam Lawi ka nemo ya aureni da nafi farin ciki sau dubu da wannan cin zarafin da kake yi mani a cikin gidanku, Zobe kuma mai sona tsakani da ALLAH ya bani wanda nake hango da ace shine tsaye a gabana yanzu ba zai taɓa yi man gori ba, kai ma ɗin ka je kai da ALLAH don ba yafe maka ƙazafin satar da ka yi man na yi ba" Tana ƙare maganar ta zo zata fita saboda kukan da ya zo mata, Safwan ya riƙo hannunta da sauri ya dawo da ita gabanshi ido cikin ido suke kallon juna ya zare mata idanuwa tare faɗar "Uban wa ya baki Zoben na ce ko ba zaki faɗa ba??" Dije ta fisge hannunta cikin fushi da hayagaga tace,. "Masoyi na na gaskiya Abokinka Malam Lawi shine ya bani, idan kuma kana tamtama ka je ka tambayeshi ka ji kuma WALLAHI idan har baka bani abuna ba akan shi zaka janyo in in yi maka abunda kaf garin nan sai an tsine mani" Tana ƙare maganar ta fice tana wani irin kuka gwanin ban tausayi, saboda ba ƙaramin zafi ta ji ba akan ƙazafin satar da ya yi mata, uwa uba da cin zarafin mutanen ƙauyensu da ya yi. Safwan kam ba shiri ya dafe kai saboda abunda ya ji ta faɗa akan Zoben da wanda ya bata shi ya sa ya ji duniyar tana juyawa da shi, ya yi shiru na ɗan lokaci sannan ya furzar da iska a bakinshi yace "Lawi hmmmmm!" Yana cikin nazarin abun yi ne sai ga Hajiya Mama ta zo tana rufeshi da faɗa kamar zata dakeshi ba tare da ma ta jira taji ba'asin maganar daga Bakinshi ba, ta ce ya bata Zoben dole ba yanda ya iya ya fiddoshi aljihu ya miƙa mata, sai dai kam damuwar da yake ciki ta janyo ƙanzil ya kasa cewa bale har ya yi yunƙurin kare kanshi, har ta yi faɗanta ta gama ta fita bai ce da ita komi ba, cikin tsananin fushi yace "Dole ma ne in tattara inawa inawa in bar mata gidan don WALLAHI ba zan zauna takaicin Black Cat ya janyo in mussure ba, ina ba zai yiwu ba WALLAHI zan bar maki ita Hajiya tunda kinfi sonta da ni" A gurguje ya shirya ya fice gidan yanata cuku cukun barin garin zuwa makarantar da yake son yin applying zuwa U.S sai ko ga shi cikin nasara ya harhaɗa komi da ya dace sati biyu a tsakani ya ɗage ya bar ƙasar gaba ɗaya. Daga Dijen har su Surry sun ji daɗin tafiyar tashi saboda takurasun da yake yi kullum, amman yanzu ko za su sakata su wala yanda suke so, Dijen ma itama Hajiya Mama da kanta ta ɗauketa ta kaita wata bording school ta kuɗi da ke cikin babban garin Yolar, cikin nasara ana yi mata interview aka yi nasarar samun abunda ake so ba laifi aka ajiye ta J.a.s.s 1 da nufin idan ta shiga 2 idan an auna ƙwaƙwalwarta sai ayi mata jumping zuwa 3 ta zana J.l.c, Dije ta sha kukan rabuwa da Hajiya Mama saboda a ɗan zaman da suka yi ta gano cewa ba ƙaramin kirki take da shi ba, kuma tana sonta sosai don komi da ake buƙata na ɗan makaranta sai da ta siya mata har ma da kayan da ba wani muhimmanci ne da su, da waɗanda ita kanta Dijen bata sansu ba bale amfaninsu. Sannan Hajiya Mama da kanta ta sanarwa da principal d'in Makarantar cewa Dije matar aure ce kada a daketa kamar yanda ake yiwa sauran ɗalibai, duk da Dijen ta ji haushin kiranta da matar auren da ta yi saboda gargaɗin da Safwan ya yi mata kafin ya tafi akan cewa ko da wasa ta faɗawa wani cewa shine Mijinta sai ya fasa mata baki. ***** Cikin sati ɗaya Dije ta fahimci kan makarantar saboda wata yarinya da wata prefet ta haɗata da ita mai suna Hannatu. Hannatu ɗiyar masu kuɗin gaske ce ga ta da son mutane sosai kowa faram faram take da shi tun gida babu ruwanta da ƙyama irinta ɗiyan masu kuɗi, haɗuwarta da Dijen yasa ta ji daɗi sosai shiyasa ta dinga fahimtar da ita duk wani abu da bata sani ba, cikin ƙanƙanin lokaci shaƙuwa ta shiga tsakaninsu saboda bala'in kirkin da Hannatun take da shi. ALLAH ya yi taimako Dijen Baffah, Safwanunmu kuma a dawo lafiya da guzurin baturiya💃🏻😛🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️ Akafta😁 D/AUTA Ce✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *BAƘON YANAYI ne sunan Book ɗin don haka idan kin san baki karantashi ba to ki garzayo da gudunki don kar ayi babu ke, da 300 kacal zaki sameshi a complete ɗinshi ki yi yanda kike so, don ke da kanki zaki banbance tsakanin tea da shayi kada ki bari a yi babu ke salonshi daban ya ke da saura don tun daga sunan zaku gane cewa fa shi ɗin na daban ne, ga mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09032685442 sai na ji ku👍🏻😅* *Lamba ta 33* Cikin wata ɗaya da zuwan Dije makarantar da yawa mutane sun fara saninta, saboda halin nata da a ko'ina baya b'oyuwa don kuwa watarana tana zaune kan barandar da hostel ɗinsu, taga wata house captain ɗinsu ta saka wata yarinya kneel down tanata dukanta, kuma ga shi ita yarinyar har ta fi Captain ɗin tsawo da girma saboda jin haushin zaunen da ta yi anata dukanta tana ihu yasa Dijen ta nufi wurunsu ta tsaya, cike da fushi ta fisge bulalar hannun Captain ɗin ta zubawa yarinyar bulala ɗaya iya k'arfinta tace "Kinga yanda na yi maki ko to haka nike so ki karɓi bulalar ke ma ki rama ko in haɗa maki jini da majina yanzu" Ba Captain ɗin ba harta ita kanta yarinyar da sauran mutanen da ke wajen sai da suka zaro ido, saboda mamakin ƙarfin halin Dije a matsayinta na junio a house ɗin, ganin yarinyar ta ƙi karɓa cike da tashin hankali da tausayin Dijen yasa ta rufe bakinta alamun firgici. Captain ɗin ta riƙe ƙugu tana ƙarewa Dije kallo sama da ƙasa tace,. "Ashe ko yau zan ci Uban Matar aure a makarantar nan sai naga uban da ya ɗauke maki gindin da zaki tunkarata da wannan baƙin gangancin" Ta yi wata arniyar dariya ta fisge bulalar a hannun Dijen ta yi ta zabga mata bulolin ta duk inda ta samu, Dije kam jin zafin dukan yana ratsata yasa ta yi wani ihu ta yi tsalle ya haye kan Captain, kafin kace me wurin ya cika maƙil da yan makaranta, tsakanin prefet da senios har ma da juneos ɗin ba'a bari ba, don kuwa Dije ta zage damtse sai artabun doke doke take yi tsakaninta da Hause Captain ɗin, in da da ƙyar aka ɓanɓari Captain ɗin a hannun Dijen, don kowa ƙasa ta murƙusheta tanata kai mata naushi aiko gaba ɗaya prefet suka taru kan Dijen sunata jibga saboda takaicin abunda ta yiwa ƴar uwarsu a gaban junios ɗinsu masu ganin girmansu da kuma jin tsoronsu. Hannatu a gefe sai uban kuka take ci saboda ganin dukan da ake yiwa Dijen, ganin za su kassarata ne yasa ta bazama aguje sai gidan principal ɗinsu tana sanar da ita, aiko a firgice principal ɗin ta nufo Hostel ɗin don zuwa lokacin makarantar gaba ɗaya ta taru wajen ɗauki ba daɗin dukan da prefet ɗin suke yiwa Dijen, don kowa ya kasa karɓarta a hannasu hasali ma wata ɗaya daga cikinsu da ta so a ƙyaleta itama aka hayayyaƙo mata dole ta yi shiru. Ko da principal ɗin ta zo tuni sun jigatar da Dijen Baffah don kuwa gaba ɗaya sun ji mata raunuka don ko motsin kirki bata iya yi, cike da tashin hankali principal ɗin ta sa aka ɗauketa aka nufi clinic da ita cikin sauri aka fara treatment ɗinta, sannan ta sa aka haɗa assembly na gaggawa ba tare da ɓata lokaci ba kowa ya hallara prefets ɗin da suka yi aikin kam gaba ɗaya cikinsu ya ɗuri ruwa, don kuwa sai a lokacin ne wasu da yawa suka ji labarin cewa wai matar aure ce, duk da cewa wasu sam basu yarda da cewa matar auren ba ce duba da yanayin karancin shekarunta, don kwata kwata a lokacin Dijen shekararta goma sha huɗu. Cikin tsananin ɓacin rai principal ɗin ta yi ta faɗa cikin firgici da jin tsoron abunda zai biyo baya, saboda jan kunnen Da Hajiya Mama ta yi tun farkon kawo Dijen akan kada a daketa ko a sakata wani aikin wahala saboda matar aure ce, sannan ta yi hani ga kowace prefet da ta sake dukan juneos ba tare da ƙwƙƙwaran dalili ba, sannan ta tsawatar sosai akan kada a sake yiwa kowa irin wannan dukan da ake yiwa yaran mutane. Bayan an sallami sauran ɗaliban ne aka bar prefets ɗin inda aka yi bincike aka fitar da waɗanda suka daki Dijen aka yi masu horo mai tsanani sannan aka karɓe ɗankwalayensu sannan aka basu suspension na kwana uku zuwa gidajensu. Sannan sauran ta tsoratar da su sosai akan kada su sake dukan ƴar kowa uwa uba kuma ita Dijen da ta kasance matar aure inda gaba ɗaya dukansu sunyi mamakin jin cewa wai ita Dijen matar aure. Hakan da aka yi shi ya janyowa Dije suna a cikin makarantar, sai dai kuma waɗanda abun ya shafa tuni sun k'ulla gaba da sabuwar ƙiyayya a tsakaninsu da ita, inda wasu da yawa sun ci alwashin cewa sai sun ja mata abun da za'a koreta makarantar. Not editing😻 😝😝😝😝 Akafta😝 D/AUTA Ce✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *BAƘON YANAYI ne sunan Book ɗin don haka idan kin san baki karantashi ba to ki garzayo da gudunki don kar ayi babu ke, da 300 kacal zaki sameshi a complete ɗinshi ki yi yanda kike so, don ke da kanki zaki banbance tsakanin tea da shayi kada ki bari a yi babu ke salonshi daban ya ke da saura don tun daga sunan zaku gane cewa fa shi ɗin na daban ne, ga mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09032685442 sai na ji ku👍🏻😅* *Lamba ta 34* Dije kam bayan kwana biyu ta ji sauƙi sai dai shatin bulolin da suka rage su ƙarasa warkewa kawai, inda ƙawarta Hannatu da sauran wasu da principal ɗin tasa su kula da ita sosai, sun bata kulawa tamkar ƴar uwarsu ta jini don ba ƙaramar gata tasha a hanunnsu ba, don wata prefet ma mai suna Zee Baby takanas ta maidata wurinta tana tarairayarta tamkar ƙanwarta ciki ɗaya, saboda shagwaɓar Dijen da yanayin barkwancinta yasa ta shaƙu da ita aɗan zaman jinyar da tayi clinic na kwana biyu. Dije kam tana jin ta samu kanta ta fara komawa kan harkokinta kamar kullum, saboda yanzu ɗaurin gindin da ta samu wajen principal ɗin da sauran wasu prefet ɗin yasa take jinta ita wata ce. A ɓangaren Malamai ma Dijen Baffah ba ɓoyayya bace, don duk malamin da ya shiga ajinsu tabbas sai yasan da zamanta, don kuwa ba laifi tana catching ɗin karatun yanda ake ɓukata. Akwai wata rana ma wata malamar Hausa ta rubuta masu test cikin ɗoki Dijen Baffah itace ta farkon wadda ta fara gamawa ta miƙa, Malamar sai jinjina mata take yi saboda daman cen akwai jituwa tsakaninsu sosai, don saboda saurin gane karatunta da take yi kafin kowa ya gane. Bayan an kammala ne aka haɗawa Malamar takardun ta fice wani malami ya shigo, bayan kwana biyu da rubuta test ɗin sai gashi hissar Malamar ta zagayo ta dawo, cike da ɗoki kowa yake murna saboda test ɗinsu da ta fara raba masu, wadda kusan kowa ma na ajin ya canye amman Dije cike da mamaki ta ƙurawa takardar kallo, cen dai ta kasa haƙuri saboda jin Malamar tace duk wanda yake da wani ƙorafi ya faɗa, aiko cikin sauri tace "Malama naga nan ƙasan tambaya ta biyu kin zagaye mani baki bani marking ko ɗaya ba, gashi kuma na bada amsar karin maganar da kika ce a kawo guda biyar" Malamar ta zo gaban desk ɗin Dijen ta tsaya ido cikin ido tace da Dijen, "Karanto karin maganar muji me kika rubuta?" Dije ta fara kwantawa kamar haka "ALLAH ya kashe Uwar Ubana lafiya" Malamar ta ce da ita "Ƙara dubawa dai ki ga" Dije ta sake karantawa kamar farko, Malamar tace ta dai sake dubawa da kyau aiko Dije ta ƙara ƙurawa takardar kallo tana karantawa fillah fillah tace "ALLAH ya kashe Uwar.... Uban......ki lafiya" Aiko ba sauran Yan ajin ba har ta ita kanta Dujen sai da ta zaro ido saboda ita har ga ALLAH ba haka taso ta rubuta ba, Malamar ranta a ɓace tace Da sauran abokan zaman Dije wa zai riƙe mata ita?,kusan mutum huɗu ya fito yace "shi, shi," aiko cikin tsananin ɓacin rai Malamar ta kalli Dijen tace "Daman jira nike yi ki kawo kanki Khadijah yau sai na wulaƙantaki" Aiko jikin yan ajin yayi sanyi ƙalau saboda ganin yanda take ɗasawa da Dijen amman yau take faɗar haka, aiko Malamar ta sa aka kira sergent ya zo ta karɓi bulalarshi tace da Dije ta kwanta, cikin tsananin tsoro Dijen ta fara roƙonta akan ta yi haƙuri WALLAHI ita ba abunda ta je rubutawa ba kenan kuskure ne, aiko Malamar ta kasa sauraren magiyar da Dijen take ta kwantar da ita ƙasa flat ta dinga zuba mata buloli tun yaran class ɗin suna lissafi har suka gaji suka daina, don kuwa dukan Dijen take yi ba na wasa ba duka irin na fitar hankali har sai da Dijen Baffah ta yi suman ƙarya sannan ne ta ƙyaleta ta daina dukanta ta kwashi tarkacen kayanta ta tsallaketa ta fice. Hannatu da sauran abokan Dijen suka taso suka talalllabeta suka yi store ɗinsu da ita, aka fara yayyafa mata ruwa ana yi mata fifita, Dijen ta fashe da wani azababben kuka gwanin ban tausayi abokan sai lallashinta suke yi, Hannatu kam itama kukan take yi saboda tsananin tausayin Dijen don ba ƙaramin duka ta ci ba a hannun Malama Ubaidah ba, amman duk da hakan baisa ta kasa turo wata prefet waton sabuwar Captain ɗin House ɗinsu Dijen, akan ta baiwa Dije aiki mai tsanani kullum safiya tare da rakiyar wasu buloli goma kullum ba fashi har na tsawon sati biyu. Aiko Dije cikin jinyar raunukan ta fara yin aikin kamar gaske sai ko gashi rana ta uku tun Asuba ta saka Uniform ɗinta daga Masallaci bata dawo House ɗin ba ta bi wata ƙofa tayi area classes abunta, akaci nemanta har aka gaji amman ba'a ganta ba dole akasa wasu suka yi aikin tunda ba'a ganta ba. Sai bayan an dawo school ne prefet ɗin ta ganta ta yi mata faɗa sosai tare da jan kunnenta akan gobe ta sake tserewa linka mata aikin za'ayi, amman duk da hakan bai hanawa Dijen sake fecewa ba wata safiyar haka suka ci gaba da yi har prefet ɗin ta haƙura don kanta, amman kam Dije taci alwashin sai ta rama abunda Malamar ta yi mata komi daren daɗewa. Aiko sai gashi wata rana Malamar tana yi masu karatu ta ce da Dijen taje Office ɗinsu ta ɗauko mata jakarta da zata ɗauki wani abu, aiko Dije tun daga cen ta yi sa'ar cafke wani ƙadangare ta jefa mata a jakar ta kawo mata, cikin Sa'a aka kirata ga waya da saurinta ta zura hannu da nufin ɗauko wayar aiko ta cafko ƙadangaren, ba shiri ta fasa wata uwar kuwwa ta saki jakar ƙasa, cikin sa'a ƙadangaren ya yo tsul ya fito ya haye ƙafafunta ya yo saman jikinta aguje, ba shiri Malamar ta fara ihu tana cilli da kayan jikinta tsakanin gyalen da dankwalinta har ma da yunƙurin cire doguwar rigar da ke jikinta, sai gashi anyi Sa'a ya fito jikinta da sauri ya fice don shima neman hanyar tserewa yake yi. Aiko cikin tsananin firgici ta kwashi kayanta jikinta sai rawa yake yi ta zo zata fice taci tuntuɓe ta faɗi sai ga Malama ƙasa ta baje dafe da ƙugu tana yamutsar fuska, cikin jin kunya ta yunƙura da ƙyar riƙe da ƙugunta da ya bugu ta fisgi gyalenta a hannu tamkar wata zararra ta yi waje, inda fitarta ya baiwa ƴan ajin damar fito da dariyarsu da suke ta ɓoyewa, Dije Kam har ƙasa ta kai dafe da cikinta tana wata irin arniyar dariyar muguntar da ta yi, cikin ranta tace.. _"Gobe ma ki sake dukana da wani ƙaramin kai naki sai kace Ladingo ta baki aro😝"_ Yaran ajin ma kowa sai uban dariya yake ci musamman idan sun tuno ihu da kururuwar da Malamar ta yi, musamman dai faɗuwar da ta yi ta baje ƙasa tare da yin zaman yan bori. Sai bayan sun koma Hostel ne take sanarwa da Hannatu cewa itace ta saka mata ƙadangaren, Hannatu ta rufe baki tace "Don Allah Ni dai to kar ki bari wani ya ji aje a sanar da ita ki sake shiga uku" Dije ta yi saurin faɗin "Tab! Ai WALLAHI duk ta kuskura ta sake dukana sai na yi mata abunda sai ta yi kuka" Hannatu ta zaro ido waje tace,. "Ni dai Ƙawata ki rage tsokano abunda zai saka ayi ta dukanki a banza don ALLAH" Dijen ta yi shiru tace "Ke Ni fa in banda nike son Karatun nan ko to yasin da na jangwalo abunda makarantar nan zata hautsine gaba ɗaya" Hannatu ta yi shiru sannan tace,. "Wai ni kam Khadijah ke bakya gajiya da janyo abin magana ne??" Dije ta ƙyalƙyale da dariya tace,. "Cabd'i ai ni idan banyi ba bana jin kaina dai dai yanzu dai mu je ki rakani inyi fitsari" Suka rankaya gefen wani Pampo Dije ta tsugguna tana fitsarin tace da Hannatu ta je wajen wasu yara da ke cikon ruwa a bokitansu tace da su ita senior ce su bata ruwan tayi tsalki ko taci Ubansu. Aiko Hannatu ta nufi wurinsu ta sanar da su saƙon Dijen suka bada ruwan jikinsu yana rawa ta kai mata, Dije kam bayan tayi tsalkin ne ta yunƙura kenan zata tashi ta hango wata prefet cikin waɗanda ta janyo aka karɓewa ɗankwali, ta zo da wasu yara da bokitai cike zata ɗibi ruwa aiko ba shiri Dijen ta koma tsugunnen tamkar fitsarin take yi da gaske don bata son ta ganta, aiko Dije tana zuƙunne wajen har ƙafafuwanta suka yi sanyi, kasancewar prefet ɗin cin layi ta yiwa yaran bayan ta cika bokitanta ne idonta ya kai kan Dije da ke tsugunne tace "Ke don Ubanki zo ki ɗauki ruwan nan mu je" Dije ta yi kamar bata ji ba ta ƙara shan jinin jikinta, prefet ɗin ta ƙara ɗaga murya tace "Ke wai don Ubanki ba da ke nake magana ba wai? Zaki taso ki zo ki sai na ci Ubanki" Yaran suka zaro ido suka ce "laaaah! Ashe ba senior bace ita shine tace in bamu bata ruwa ba zata ci Ubanmu???" Prefet ɗin ta zaro ido tace "haka tace da ku??" Suka tabbatar mata aiko cikin sauri ta je ta cafko ƙugun Dije ta janyota har gindin pampon tace "Yau sai na koya maki hankali don Ubanki ɗauki ruwan mu je" Dije ta ɓata fuska tace "Bana ɗibar ruwa ko a gidanmu saboda aljanuna basa bari in ɗora Abu saman kaina". Prefet ɗin ta yi wata shewa tace,. "Ashe ko yau zanyi bikin cin Ubanki don ko ɗiyar wa ce ke a garin nan sai na cakwaɗaki sai dai a koreni gaba ɗaya in bar makarantar" Cikin tsoro Dijen ta ɗauki bokitin ta ɗora a kanta sauran yaran suka ɗauko wasu su ma, prefet ɗin tana gaba suna biyarta sai kawai Dije taci tuntuɓe sai ga bokitin ya yi sama ya faɗo ƙasa gaba ɗaya ruwan suka zube ƙasa itama suka jiƙata. Ba shiri prefet ɗin ta waigo tana ƙarewa Dijen kallo sama da ƙasa tana wassafa irin abunda zata yiwa Dijen ta soshe haushinta da take ji. Ni dai kam ba da ni ba yasin nayi nan🏃🏻‍♀️don kar ace nasan mafarin faɗan😛 Akafta😅 D/AUTA Ce✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *Duniya Rawar ƴanmata na gaba sai ya yo baya zamani adon tafiya ne baya ɓoye baiwata aha💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻* *Sonki a jinin jikina yake my Hannah ina yinki sosai har cikin ɓargona alkhairin ALLAH ya kai maki har gadon baccinki my besty💋* *Lamba ta 35* Cikin zafin nama ta kaiwa Dije wani bahagon mari, Dije ta dafe gefen fuskar tare buɗe baki tana faɗin "Laaa! Laaa! Laaa! Mu kika mara? Ashe ko yau zamu yi luguden dafuwar kanki a kogin burunduƙusuru zunbukur, ayyihuhu kibiyarmu zama daram iso ta hannun damana" Ta ɗaga hannunta sama kanta ƙasa tana wani surutai kafin kace me sai ga Dije ta yi tsalle ta ɗale prefect d'in tare da cafko gashin kanta da ƙarfi cikin ikon Allah sai ga tsoron prefect ɗaya a hannun Dijen ta raboshi daga cikin ƴan'uwanshi ta jefar, ta sake komawa ta cafko fuskarta iya ƙarfinta ta fara yakuceta ta ko'ina cikin wasu irin surutai da ita kaɗai tasan ma'anarsu, cikin ƙanƙanin lokaci sai ga jini ya fara saukowa tun daga cikin kan prefect d'in yana gangarowa zuwa jikinta, saboda tsoro ɗaya da Dije ta cire mata aiko jini ta ko'ina sai zubowa yakeyi, azabar hakan tasa prefect ɗin ƙwacewa ta arce da gudun bala'i tana faɗin a taimaketa saboda ganin ya firgitata gashi bai daina saukowa ba, Dijen ma haka bata daina biyarta ba aguje itama tana faɗin "Ai billahillazi yau sai mun kasheki dole ne ma sai mun sha romon kanki a cikin daren yau" Prefect kam tana gudun ceton rai tana faɗin,. "Ku rabani da ita tun kafin takasheni jini jini ku taimakeni zata kasheni" Mutane kam kowa ya hango Dije sai ya dare shi ma ya nemi maɓoya saboda ganin abunda ta yiwa Prefect ɗin wanda a duba ɗaya za'a ce aikin baƙaƙen aljanu ne, duba da yanda Dijen take ƴar firit da ita amman ta ci galabar Prefect ɗin da take ƙatotuwa. Aiko saboda ganin kowa yaƙi yarda ya tunkari Dijen a riƙeta yasa Prefect ta ƙara ƙarfin gudunta ta nufi bakin Gate wurin Baba maigadin Hostel ɗinsu, tana kaiwa ta yi Bayan maigadin tana kururuwar ya taimaketa, Dijen ma itama tana isa ta yi wata irin arniyar ƙara cikin ƙaraji tace "Murkutus riƙe muna ita a cire shegen kan nan!!!!" Tayi cikin Baba maigadin da nufin ta cafkota aiko ba shiri Prefect ta some saboda tsananin tsabar tsoron da taji, Maigadin cike da jin haushi ya cira wata ƙatuwar bulalarshi ta doki ya sakarwa Dije har sau biyu, Dije jin azabar saukar bulalar yasa itama ta yi wani tsalle ta faɗi ƙasa tana surutan faɗin "Ku tafi da ruhinta ga mu nan zuwa ku je ku je fa yanzu a fara dafuwar tarugu da tattasai duka a saka kar a saka gishiri a saka sugar ihu wayyo ALLAHna WALLAHI sai mun kashe duk wanda ya sake taɓa muna goɗiya" Tana ƙare faɗar haka ta yi ɗif sai yawu take fitowa a bakinta tana furzarwa suna sauka kan fuskarta tana gurnani, ganin haka yasa wasu Prefect suka nufi ƴar'uwarsu suna zuba mata ruwa ta farfaɗo amman duk da hakan jinin da ke fita cikin kanta yasa ya sake bugeta ta tafi luuuu suka rirriƙeta suna kiran sunanta, inda wasu kuma suka nufi Dijen anata ƙoƙarin talallabarta tana ihu tana botsarewa. Kai tsaye wasu da yawa suma aljanunsu suka fara tashi kafin ka ce me Makarantar ta hautsine da tashe tashen aljanu, sai yarinya tana tsaye sai dai aga ta heta kuwwa ta faɗi ƙasa tana sambatu aiko makaranta ta rikice ko ta ina sai ihu ake yi. Ana cikin hakan sai ga wani Malami da vice principal sun shigo bakin Gate ɗin Hostel ɗinsu saboda labari yaje garesu cewa makarantar ba lafiya, sai ko gashi sun taradda abunda ya firgitasu agurguje aka ɗauki Prefect ɗin mai suna Rukayya aka nufi clinic da ita don har lokacin cikin mayen bugun jinin take sai mashalo take yi, Dije kam malamin yasa aka kawo masa ruwa a kofi yayi mata addu'a ya tofa mata ta yi firgigit ta miƙe kamar wata mahaukaciya sabon kamu tana waige waigen faɗin "A ina nake? me ya kawoni nan? don Allah Aunty kiyi haƙuri WALLAHI ba da gangan na zubar da ruwan ba, don ALLAH ki yi haƙuri kar ki dakeni" Wasu daga cikin Ɗaliban da ke tsaitsaye suna kallonta suka fara faɗin "Ai na faɗa maku baƙaƙen aljanune da ita kuka ƙi yarda ai to yanzu dai gaskiya ta fito" Hannatu tana kuka ta ratso students ɗin ta zo gaban Dijen ta tsaya tace "Khadijah sannu" Dije ta waiga ta kalli Hannatu tace,. "Me ya kawoni nan Hannatu??" Malamin ya ƙura mata kallo yana nazarinta, sannan ya sa aka ta yiwa sauran masu aljanun addu'a suna tashi ɗaya bayan ɗaya, bayan komi ya lafa ya dawo wurin Dijen ya tambayeta minene asalin abunda ya haɗata da Ruƙayya, Dije ta zaro ido tace "Wace Ruƙayya?? Ni fa banyi faɗa da kowa ba". Yace ba kiyi faɗa ba kika ji mata rauni har kika tsige mata tsoro ɗaya? Gashi a sanadin hakan kin janyo ta suma zaki faɗa ko sai na saitaki yanzu?" Dije ta fashe da kuka tace,. "Ni fa WALLAHI Malam ba wanda nayi faɗa da shi ka tambayi Hannatu ka ji" Malamin ya kalli Hannatu yace, "Au kenan da ke aka haɗu aka jiwa yarinyar mutane ciyo ko?" Hannatu ta fara rantsuwar ita kam bada ita ba a tambayi kowa zai faɗa, daga nan ta yi bayanin yanda duk abun ya faru, Malamin yasa wasu Prefects ɗin su rubuto masa sunan Dijen da duk wanda aka yi abun gabanshi tun farko, yace da su su kawo masa su gobe idan an tashi assembly, sannan aka kori kowa ya watse Dije ta miƙe da ƙyar suka nufi Hostel ɗinsu, don ranar kam gaba ɗaya labarin ake ta yi duk faɗin school ɗin inda wasu da yawa sunji daɗin abunda aka yiwa Rukayya saboda muguntarta, sai tsiraru ne suka ji tausayinta tare da jin haushin abunda Dijen ta yi mata cikin bainar nasi, yayin da wasu da yawa suka fara jin tsoron Dijen don gudun kada su ma ta yi masu abunda ta yiwa senior Ruƙayya. Dije dai kam duk da ta yi mugunta amman hakan bai hanata jin tsoron makarantar ba, saboda tashe tashen aljanun da ta ga ana ta yi ranar ya firgitata sosai, musamman da dare ya yi ta kasa bacci har kowa yayi bacci ita ido ƙyamas zuciyarta cike da jin tsoro, aiko tana kwanarsu kwance kan gado ta ji takun tafiya ƙwass! Ƙwass! Ana tafiya da talkami ƴan'tsini ana karkaɗa awarwaro suna ƙara kuma direct wajen gadon da take kwance aka nufo, cikin tsananin firgici da tashin hankali ta sha jinin jikinta sai kawai ta ji an fisgi gadon da take an jijjigashi da ƙarfin tsiya, ana walili da gadon kamar fanka tare da ita anata zagaye ana faɗin "Ba ke bace kike ƙarya da mu ba to gamu munzo me kike soooooo! me zamu yi makiiiiiii!" Dije saboda tsabar tashin hankali sai addu'a take zubawa fili, sai dai kam in ta kamo wannan ta suɓuce ta saketa ta sake kamo wata haka ta dinga yi har ta ji anyi jifa da ita tun daga kan gadon har tsakiyar dogon ɗakin nasu, ba shiri ta ƙwallah wata arniyar ƙara tana faɗin "Wallahi na daina bazan sake ba na tuba ku yafe mani wayyo Baffahna" Tana cikin surutan ne ta ji an dafata ta zabura da sauri za ta zuba da gudu taji muryar Hannatu tana faɗin "Ni ce Khadijah lafiya kike wannan uban ihun cikin daren nan?" Dije ta tsurawa Hannatu kallo tuno abunda taji da kunnuwanta yasa ta ruƙunƙumeta tana faɗin "WALLAHI mu bar makarantar nan aljanu ne da ita kasheni zasu yi Ni dai gida za'a kaini bazan zauna ba wayyo ALLAHna WALLAHI na daina bazan sake ba, an kashe kowa mu ne kawai muka yi saura" Hannatu ta riƙo hannunta tace,. "Kalli ki ga? ga kowa nan lafiya ba abunda ya samemu kema tsoro ne kika ji tashi muje mu kwanta" Wata senior ta zo ta riƙata ta tashi tsaye ta kaita kwanarta suka kwanta tare tana ta tofeta da addu'o'i saboda ba ƙaramin tausayi ta bata ba. Aiko tun daga ranar Dije tasha jinin jikinta da lamarin duniya don ko malamin da ya tarasu don yiwa kowa hukunci bata ɓoye ba ta sanar da shi ba wasu aljanu ƙarya ce itace,. Amman kasancewar ganin irin ta'adin da ta yiwa Prefect ɗin yasa ba'a yarda da zancenta ba, an dai yi mata gargaɗi sosai akan kada ta sake in kuma ta sake za'a koreta makarantar bayan anyi mata horo mai tsanani, tsoron hakan yasa Dije ta sha jinin jikinta da kowa. Ranar da aka yi visiting Hajiya Mama da Surry suka zo mata Visiting tare da uwar siyayya da abinci mai rai da lafiya da suka kawo mata, bayan zuƙa zuƙan namomin da aka soyo mata daban tare da wanda aka tsatstsago mata cikin miyar tumaturin da aka ciko mata wani ƙaton ƙaramin bokiti. Sun sha fira sosai inda har ta gabatar masu da Hannatu Hajiya Mama ta yi ta murnar ganin Dijen ta fara rage ƙiriniyar da take yi, shiyasa ta yiwa Hannatu kyauta tare da ƙara nuna mata ta dinga fahimtar da Dijen abunda ya dace, da kuka suka rabu Dijen tana ta faɗin ita dai a kaita wurin Baffah'nta ta fasa karatun, da ƙyar Hajiya Mama ta zille mata suka tafi suka barta tana ta kukan ita garinsu take so ta koma ta fasa karatun bata son zama likitar. Dije a hankali ta fara rage rashin jin nata saboda ita kullum dare da tsoro take kwana matuƙar ba tare da Prefect ɗin nan take ba, shiyasa kacokam ma ta koma kwanarta don tafi jin natsuwa idan tana tare da ita, saboda Senior Aysha ba dai addini ba sannan uwa uba tana da tausayin na ƙasa da ita sosai gata da natsuwa, don kuwa ita ko shirgin sauran ɗalibai bata shiga, iyakacinta karatu tare da zuwa masallaci da kullum jam'i baya wuceta saboda addini ya ratsa jikinta sosai. Sannu a hankali shaƙuwa ta shiga tsakaninsu har itama Hannatun ta dawo wurinta suka yi zamansu hankali a kwance, idan zata je masallaci tare suke zuwa haka ma abinci bata jin ita senior ce da su take bajewa su ci abinsu, wanki ma itace take yi masu su iyakacinsu ɗaurayewa su shanya, ta kamasu ta kwance masu kansu ta tsantsara masu kitso mai kyau don tana jinsu tamkar ƙannenta na jini, musammam ma dai Dijen da yawan gashinta yasa take ƙara sonta saboda duk ta yi mata kitso sai an dinga zuwa kallonshi. Gata iya gata Senior Aysha tana nuna masu hakan yasa Dije ta kwantar da hankalinta ta fara jin daɗin zaman makarantar, duk da wasu da yawa ma akan abinda ta yiwa Senior Ruƙayya Yusuf yasa suka daina shige mata da nufin cin zarafinta ko su sakata wani mugun aiki. Don ko da aka yi hutu Dije ƙaguwa ta yi da ta dawo makaranta saboda mutuncin Senior Aysha da kuma ƙawarta Hannatu. Watan Dije biyar a Yola da aka yi wani hutun second term Hajiya Mama ta shirya ta da uwayen tsaraba suka nufi ƘIRIU waton garinsu Dijen Baffah ɗiyar Inna Hasiya kanwar Usmanu mijin Hansai. Ina yinku sosai mutanena😅🤝🏻 Akafta😛 D/AUTA Ce😊 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *Ɗaukaka da baiwa ALLAH sai ya baka in ya so, babu Malami ba boka zaka zamo mafifici ko da maƙiyanka basa so, ilimi nagarta ke saka ɗan'adam sahun farko, babba ko ko yaro adalci ke saka ka yo ƙarko, daina hanzari magana jari salonta na ɗauko aha😉duniya rawar ƴanmata na gaba sai ya yo baya, inda lokaci zamani ba shi ɓoye baiwata🥴* *Lamba ta 36* Tun daga farkon shiga garin Dije ta fara hango mutanen da ta sani, aiko sai faman murna take yi tana ɗaga masu hannu, kafin kace me yara da abokan Dijen da ƴan makarantar allonsu duka sun biyo motar suna kuwwar faɗin "Ga Dije, ga Dije, Dijen Baffah ta dawo ƘIRIU" Direba da ƙyar ya samu wajen da ya raɓa ya yi parking saboda cincirindon yara da matasan ƴanmata har ma da wasu samarin duka, kowa fatanshi ya fara yin ido biyu da Dijen, saboda labarin da suka ji cewa Dijen ta yi aure gidan masu kuɗi. Aikam itama Dijen cikin ƙaguwa ta ɓalle murfin motar ta fito bakinta a washe tana faɗin,. "Wayyo daɗi gani na dawo garinmu" Aguje ta zanƙara da gudu ta yi cikin gidansu inda taci karo da Inna rik'e da zane tana ƙoƙarin yafawa yana zarmewa, saboda tsabar saurin taje ta ga Dijenta da taji anata ihun faɗin gata ta zo. Suna cin karo Inna ta zaro ido cike da mamakin ganin Dijen tare da buɗe baki saboda tsabar farin ciki ta ma rasa me zata faɗa, Dije kam tsalle ta yi ta ruƙunƙumeta tana faɗin "Wayyo ALLAHna daɗi kasheni gani ga Innata, yi huhu ina Baffahna ALLAH yasa yana gida" Ta saki Inna ta yi cikin gidan aguje sai dai dole ta ci ƙaton birki saboda ganin ɗakin Baffahn a rufe, cike da jin haushi ta ɓata fuska ta nufo Inna da ke ƙoƙarin dawowa cikin gidan tana faɗin "Bari inje in dubo Baffahna Inna idan mutanen sun shigo ki basu ruwa kafin ina dawo" Inna ta yi saurin faɗin "Au! Ki ce ba tare da mijin kaɗai kuka zo ba? To ki jira mana yana ƙofar gidan Maigari yanzu a je a kirashi ai tunda......" Maganar ta maƙale ne saboda ganin yara sunata shigowa da buhuhunan shinkafa tare da sauran kwalaye, Inna ta bi yaran da kallo riƙe da baki zuciyarta cike da tsantsar farin ciki, sai ga sallamar su Hajiya Mama da su surry, da sauri Inna ta juya tare da washe baki cikin rawar jiki ta nufi ɗaki ta ɗauko sabuwar tabarmar ta shimfiɗa masu a kofar ɗakinta da yake share fess! Da shi, tana tambayarsu ya hanya tare da yi masu barka da zuwa, cikin sauri ta je ta ɗebo masu ruwa ga tulunta mai shegen sanyi cikin babban kwanon sha sabo dal, tayi masu farau faraun fura ta miƙa masu sannan ta dinga taimakawa yaran da har lokacin basu daina shigowa da kayan tsarabarba. Dije kam tana samu ta fice ta nufi ƙofar gidan Maigarin ƙawayenta su Lanti da Hansai da Mune suka biyota kowa yana ƙoƙarin ya dai samu ya riƙa hannunta, ita ko sai wasar baki takeyi tana faɗin "Hansai da Lanti kuna nan ku har yanzu baku yi auren ba ashe? Ina Jummala ko anyi mata auren?" Mune tayi caraf tace, "Ko sati biyu ba'ayi ba da aurenta ai, sai dai kam ko jiya da naje na isketa sai kuka take yi, ke baki ma sani ba tun ranar da aka kaita ta gudo cikin dare ta dawo gida, wai ita bazata kwana da Garbati ba tunda ɗan'iska ne" Dije ta yi saurin faɗin "To faɗi ba'a tambayeki ba, wai ke Mune har yanzu baki daina gulmar taki ba?, To ke yaushe za'ayi maki auren ne?, Amman dai Ni dai WALLAHI ina baki shawara ki daina yawan gulma nan kada watarana ki janyowa kanki a lakaɗa maki shegen dukan tsiya" Mune ta yi shiru zuciyarta a cunkushe tace, "Ai gaskiya ce na faɗa WALLAHI ki ma tambayi su Hansai ki ji in nayi ƙarya" Dije tace "Ni dai fa bance kinyi ƙarya ba amman na ce ki rage yawan surutunki na tsiya da baƙar gulmarki da kika saba, don Ni dai WALLAHI banga laifin Jummala ba haka kawai a kaika wajen Namiji ace ku kwana ɗaki ɗaya, don kawai salon ya lalataka azo daga baya ana faɗin ka zama ɗan'iska" Hansai ta ƙyalƙyale da dariya tace,. "Cafɗi Ni ma fa wai an kusa aurena da Usmanu, amman Ni dai yasin har na matsu ayi a ƙare saboda nasan shi Usmanu ba ɗan'iska bane, Jummala dai kam sai haƙuri tunda Garbatin ya riga da ya tanbaɗe sai neman shiriya" Lanti kam da tunda ake ta surutun bata ce komi ba, cikin sanyin jiki ta sauke ajiyar zuciya tace "Ni WALLAHI har ma tsoro auren yake bani musamman yanda Jummala take ta kuka duk dare sai ta gudo Gidansu ana maidata, ni na rasa me ma Garbatin yake yi mata da har take jin tsoronshi" Cikin tsananin tsusayin Jummalar Dije tace "wai ina Ladiyo ita dai ai suna zaman lafiyarsu ko?" Mune ta yi saurin faɗin "cabɗi ai billahillazi ko jiya sai da na taraddasu suna ta kokawa Duduwa tana rabasu suka ƙi bari, Bala sai zagin Ladiyo yake yi wai sai ta biyashi kuɗinshi da ta sata" Dije da suke tafiyar a hankali suna firar ba shiri ta ja ta tsaya, cikin sabon ɓacin rai ta ce "Wai kunsan wani abu kuwa??" Dukansu suka ce "A'a" Ta dafa kafaɗar mune tace,. "Na dafeki da alkhairi yau halinki zai yi man rana ko da ko ban biya kwandala ba, karkaɗe kunnenki da kyau kiji Mune Bala dai ashe kuɗi Malaminmu ya bashi shiyasa ya janye zancen aurenmu da shi aka ɗaura da Malam Safwan, ashe daman cen ba son ALLAh da Manzonsa ya ke yi man ba, don haka ki je ki yi ta yamaɗiɗi da wannan zance Mune na baki kyauta, kar ki yi sanya ina son kafatanin wannan garin kowa ma ya san da wannan sirrin da Balan Duduwa ya rufe lokacin aurena dashi, ki bankaɗe komi ƙawata kinji? Tunda har shi ya zama baƙin zalamammen banza kwaɗayayye" Ba Mune da Dijen ta ke baiwa labarin ba har su Lanti sai da suka jinjina irin abunda Bala ya aikata, Dije zata sake yin magana kenan ta hango Baffah'nta da yake ta sauri tun daga nesa Bakinshi a washe, wanda ko tantama babu akan cewa labarin zuwan Dijen ne ya kai gareshi, aiko aguje ta zanƙara da gudu ta nufeshi tana faɗin "Wayyo Baffahna Oyoyo Oyoyo wallahi nayi missing ɗinka" Tana zuwa ta faɗa jikinshi, shi ma cike da tsananin jin daɗin ganinta yace "Baƙin birni sannunku da zuwa yanzu nake ji ashe ko da gaske Dijengalata ce ta zo ganina" Ya riƙo hannunta suka nufi gidan sai tsalle take yi tana wasar baki tana murna, su Lanti suka bi su a baya Hansai kam ta doje ta yi gida saboda kunyar surukuta da take yi da Inna Hasiya. Ko da suka shiga sun taradda Hajiya Mama da su Surry cikin ɗakin Inna sun gama SALLAH, Inna ko sai haɗa wuta take yi tana jefa masu ɗanwaken da ta gama kwaɓashi a gaggauce, don kawai ta sami abun tarbar baƙinsu da shi saboda ita dambun gero ne ta yi tana ganin idan ta basu ƙila ba za su iya ci ba. Baffah ya isa ƙofar ɗakin cikin farin ciki yayi masu sallama, sai da suka amsa sannan ya shiga yana yi masu sannu da zuwa tare da tambayarsu ya hanya?. Cikin mutunta juna suka gaggaisa sannan ya fito Dije ta biyoshi a baya tana faɗin "Baffah banga yaya Usmanu ba" Ya waigo zuciyarshi fess yace "Tun da safe ya je birni cin kasuwa kinsan yanzu a cen yake kasa kayan koli yana sai dawa tun lokacin da muka dawo garin Mijinki" Dije ta washe baki tace,. "ALLAH sarki yaya Usman ashe an kara sanin ciyon kai" Inna da take dakan toshshi ta goge fuskarta da jiɓin da feso mata tace,. "Saura k'iris ma ya rage ayi aurenshi kinga shikenan kun zama ɗaya ba zancen wani gori bale har nan gaba ki ɗauka cewa ke ce yayarshi tunda kina ganin kin rigashi aure" Baffah ya maka mata harara yace, "ko yau aka yi auren ai dai na Dije ne aka fara yi, don haka a daina yi muna wani feleƙe tunda har mu mun riga da mun yi ɗin ai kuma mun wuce wurin" Dije ta washe baki tace,. "Shiyasa kullum sai nayi mafalkinka Baffahna saboda duk garin nan kafi kowa sona" Mama Hajiya da ke ɗaki tana ji yo su ta yi murmushinsu na manya zuciyarta cike da sha'awar ahalin sabida barkwancinsu da kusan rabi duk Dijen garesu ta gado, uwa uba ma sun burgeta saboda ganin yanda suke nagartattun ma'aurata masu son farantawa junansu cikin barkwanci. Fiddo kam sai yatsine yatsine take yi tana ƙarewa ɗakin Inna kallo, Hajiya Mama tana yi tana yi mata kashedi da ido amman duk da haka sai ta fakaici idonta ta yi guntun tsaki. Baffah ya koma waje inda aka shimfiɗawa Direban tabarma gindin wani iccen dake ƙofar gidan, yana shan iska, ya zauna suka sake gaisawa a tsanake. Dije ta nufi wurin Inna ta karɓi taɓaryar tana daka toshshin su Lanti suka karɓe suna daka mata, suna ci gaba firarsu ta yaushe gamo. Bayan Inna ta kammala ɗan'waken ta zubawa Hajiya Mama ga sabon kwanon Samira, su Surry ma kowace da sabon kwanonta haka ma Direban da suka zo da shi, Dije kam dambun geron ta ɗauko ta fara ci Surry ta ce ta zo su ci ta ji don k'amshin dambun sai kai mata yakeyi a hanci, duk da ko shi kanshi ɗan'waken ba ƙaramin daɗi ya yi mata ba, aiko tana guma lomar dambun ta yi saurin faɗin "Uh! uh! uhm!" Sai data haɗye sannan ta ce "cabɗi ashe Khadijah da wayo kika so ki yi man wannan abu da daɗin gaske yake yasin" Sai ci take yi abunta babu ƙyama cikinsu Dijen da Lanti da Mune da suka fara ci tare, Inna da su ko sai faman dariya suke yi mata da ma suka cenye Inna ta ƙaro masu sannan Baffah ya shigo da ledar ruwan sanyi har suraci suke yi, tare da lemuka irin na ƴan'birni da ya bada aka siyo masu babban garin da ke kusa da su. Fiddo kam zurum ta yi tana kallon kwanon abincin ta kasa ci, Hajiya Mama da ke ɗakin Inna tana cin abincinta hankalin kwance, ta kalleta tace "Ke ba zaki ci abincin ba ne?? Fiddo ta turo baki ta ce "Gaskiya Ni bazan iya cinshi ba ku dai ku ci idan mun fita wannan ƙauyen sai a siyo man wani abu sai in ci" Hajiya Mama ta wulla mata wata ƙatuwar harara ta ce "WALLAHI muddin baki ci ba to har mu koma gida bazaki ci komi ba" Fiddo cikin tsananin ɓacin rai ta ɗauki cokali ta ɗauko ɗan'waken cikin ƙyama ta kai bakinta, sai gashi yayi mata bazata don kuwa wani daɗi ne ya ziyarci halshenta, ta haɗiye ta ƙara kai wata loma Hajiya Mama tana kallonta ta gefen ido, aiko kafin ka ce me har ta kusa tayar da kwanon ɗan'waken, don kuwa har da su cire ɗankwali tana ƴar waƙa tana rawa da kai. Ni dai kar ki cenye ki raga man fiddo☹️ Kuyi hkr dani kwana biyu na shiga rububi ne😆 Akafta🧐 D/AUTA CE✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *Soyayya da tasiri in har an saka tarbiyya,idan zaka yo komi farko ka fara yin niyya, duk mai ƙinka in ya biyo hanyarka za ya sha kunya, fasahar gwani matsayi nai ya fi inda zai zauna, hanci kan ji ƙamshi baki sa ƙashi ka ɗan tauna, ido kan ga haske linzami kace da ni suna ahaaa😉* *Lamba ta 37* Kafin ka ce me sai ga fiddo ta tada kwanon ɗan'waken tare da ɓalle murfin lemun da Baffah ya siyo masu, ta kafa kai ta kwankwaɗe tass ta jefar da gorar ta buga wata uwar gyatsa tare da shafa cikinta ta kalli Hajiya Mama da itama ɗin ita take kallo tana yi mata dariya, Fiddo ta wayancewa da faɗin "WALLAHI ashe dai naji yunwa sosai Hajiyarmu" Hajiya ta yi mata wani mere tace, "Naga alama kam tunda gashi har kin tada kwanon ɗan'waken duka, bayan ko daɗinshi ma baki ji ba" Fiddo ta yi saurin ƙyalƙyalewa da dariya tace,. "yunwa ce naji ai" Hajiya Mama tana dariya tace "Ga wani ki ƙara ko da ALLAH zai sa ki ji yunwar ta yi nesa da ke" Fiddo ta yi saurin faɗin,. "A'a naƙoshi fa amman da ace wannan yarinyar zata iya irinshi idan mun koma gida ai da sai ta dinga yi man kawai" Hajiya Mama ta yi saurin ɓata fuska tace,. "Eh kam tunda zamanki take yi me zai hana ta yi maki WALLAHI ki kiyayeni tun kafin ki janyo in barki garin nan tare da Khadijah har sai kinyi sati biyun da zata yi, kinga shikenan sai ki tayata ganin gidan" Fiddo ta zaro ido waje tace,. ,"Don ALLAH kiyi haƙuri WALLAHI na daina" Suna cikin firar ne Surry da Dije da su Lanti suka shigo Dije ta gabatar da su ga Hajiya Mama, cike da jin daɗi take amsa gaisuwarsu saboda ganin yanda suka durƙusa har ƙasa suna gaidata cikin ladabi cikin farin ciki ta yi masu kyautar kuɗi sunata godiya cike da murna. Bayan komi ya lafa ne aka sake sabuwar gaisawa tsakanin Hajiya Mama da su Inna Hasiya, inda take sanar da su Safwan baya ƙasar ya je ƙaro karatu na tsawon shekara uku, amman ta sanar da su Dijen zata ci gaba da zama a hannunta har ALLAH ya dawo da shi lafiya, sannan ta sanar da su zancen makarantar da Dijen take yi, cikin jin daɗi su Baffahn suka yi masa fatar dawowa lafiya, tare da yiwa Hajiya Mama godiya da irin kayan arzukkan da ta cikasu da su, tsakanin kayan abinci da kayan masarufi, sannan ta kawo jimillar kuɗi har dubu ashirin ta basu tace su yi cefane, Baffah da Inna saboda tsabar jin daɗi har kukan murna suka yi sai zuba godiya suke yi. Dije ta ja Surry suka yi gidan Inna Gambo domin su gayar da ita, suna cen ne su Hajiya Mama suka taraddasu aka sake aza sabuwar gaisuwa da Inna Gambon inda take ta yi wa Dije sharrin ta je birni tasha jar miya ta fara manyan kumatu, Hajiya Mama ta saki jiki ta dinga kare Dijen cike da barkwancin suka baro gidan bayan ta cikata da kyautar bajinta, sannan suka dawo gidansu Dije inda suka taradda Maigari ya aiko masu da kwano fam da naman kajin hausa da yasa aka yi masu dafuwar ruwa sun dafu lunguɓus sai ƙamshin daddawa da kayan yaji ke tashi, aiko cike da zumuɗi Surry ta fara ɗanɗanawa tana rawar kai ta zuzzuba masu har da Direbansu sannan ta ɗauki sauran ta kaiwa Inna Hasiya tace suma su ci, Inna cike da jin nauyi ta nuna mata ai ba komi su na gida ne su ci abunsu kawai, amman duk da haka atafau ta ce dole suma sai sun ci tunda suma ɗin ai ba baƙi bane. Haka suka yi ta harƙallarsu cikin mutunta juna har zuwa marece, sannan suka shirya tsaf da nufin tafiya sai ga Usmanu ya dawo kan Babur ɗinshi da Baffah ya siya masa don zirga zirgar kasuwancinshi da ya fara cikin babban birnin, cike da jin daɗin ganinsu ya gayar da su a mutunce Dije sai farin ciki takeyi saboda ganin ɗan'uwanta. Sun kimtsa tsaf da nufin tafiya saboda akwai inda zasu je su kwana da safe su kama hanyarsu ta zuwa Yola direct, sannan aka yi masu rakiya har gidan Maigarin suka je suka kai masa gaisuwa tare da godiya akan ɗawainiyar da aka yi da su, Mama Hajiya ta yi masa alkhairi tare da matanshi sannan ta fito aka rakosu har bakin motarsu ana yi masu ALLAH ya kiyaye. Dijen ma sai wasar baki take yi tana yi masu bye bye sai dai suna haɗa ido da Fiddo ta galla mata ƙatuwar harara tare da murguɗa mata baki, Fiddo ta taɓe baki tare da yi mata wani mere tana yatsinar fuska, Hajiya Mama kam haka suka rabu cikin aminci tare da kewar juna, zuciyar Hajiyar fes saboda jin daɗin karamcin da aka yi masu, uwa uba sauƙin kan da Baffah'n Dije ya nuna akan rashin zaman Safwan gida tare da 'yarsu. Bayan sun tafi ne Dije da su Baffah suka koma cikin gidan zuciyarsu cike da girmama irin mutuncinsu Safwan, Baffah sai jinjina lamarin Ubangiji yake yi tare godiya gareshi akan haɗasu da yayi da surkai nagari, waɗanda suka san mutunci tare da girmama ɗan'adam k ko da ko sun san cewa sun fisu nesa ba kusa. Sauka lafiya su Hajiya Mama😆 Not edited😓 Akafta 😉 D/AUTA CE✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *Alhmdllh Alhmdllh lalle dole ne in fara godiya ga Ubangiji kafin in ce komi, saboda jin daɗin yanda kuka nuna man ƙauna ta zahiri tare da ɗinbin karamcinku gareni ni D/AUTA, ku sani naji matuƙar daɗin ganin irin ruwan addu'o'inku gareni masu ɗauke da fatan alkhairi iri-iri, haƙiƙa duk wanda ALLAH ya baiwa masoya ya ji daɗi a rayuwarshi ta duniya, kamar yanda ni ma a yanzu naji mugun daɗi marar misaltuwa akan zallar ƙaunar da kuka nuna mani tare da littafina na DIJE ƘARANGIYA, naji daɗi na gode sosai wallahi ALLAH ya bar zumuncinmu da ku har aljannah, ni ma ina sonku all my FAN'S son so fisabilillah💋* *Lamba ta 38* Baffah saboda tsabar farin ciki nan take ya ce da inna, "idan ALLAH ya kaimu gobe ki ɗibi gero ki yi wainar sadaka a raba ko don mu nunawa Allah jin daɗin baiwar da ya yi muna, don WALLAHI sai yanzu nake jin nauyin abunda na aikata lokacin da na ke son hanawa Dije auren Malaminsu, musamman wancen yaron da shine tun farko ya fara yi wa Dije so na tsakani da ALLAH, ashe alkhairin nata wajensu yake ina ta ƙoƙarin hanata kaiwa wajenshi, Dije ki ci gaba da yi wa mutanen nan biyayya don ALLAH saboda ba ƙaramin mutunci ne da su ba, don ko a cikin masu kuɗin su nasu mutuncin daban ne, yanzu ki duba ki ga yanda suka saki jiki da mu tamkar cewa daman cen mun saba da su, Wallahi Ni dai kai bakina ba zai gaji da zunduma masu addu'ar fatan alkhairi tare da gamawa lafiya ba. Dije tana wasa da gefen gyalenta tana ta wasar bakin jin daɗin yabonsu da yake yi, sai ko SAFWAN ya faɗo mata a rai ta saurin ɓata fuska tace "To ai kai Baffah ita da surry ne masu mutuncin amman shi kanshi malamin namu fa ba halin kirki ne da shi ba, tare da wannan ƙanwar ta shi ƙarama WALLAHI in banda na ke tuna cewa kace kada in biyeta da tuni na aikata mata mara daɗi, don fa kusan kullum da sai ta tsokaneni da faɗa" Baffah ya yi murmushinsu na manya ya ce,. "Ai shiyasa nake ta saka maki albarka saboda kawai biyayyar da kike mani ko da baki ganina kusa da ke, amman kada ki in sake jin kin faɗi cewa Mijinki ba shi da kirki tunda har ya nunawa duniya matsayinki ya aureki ai ya gama maki komi Dije" Dije ta ɓata fuska tace "Wallahi fa ba sona yake yi ba Baffah har kuɗi fa ya baiwa Balan Duduwa ya toshe masa baki akan ya bar masa ni, to mai sonka ne zai yi maka irin wannan kutunguilar?" Baffah ya yi dariya mai sauti yace,. "Yaro man kaza to ai sonki ne da yake yi ma yasa ya bada kuɗin don kawai ya sami damar aurenki, don idan har da gaske baya sonki ai ba abunda zai sa ya damu don kawai wani zai aureki, amman kin ga yanzu sonki ne ya janyo ya yi amfani da damar da ALLAH ya bashi ya yi nasarar aureki, don haka ko da wani kika ji ya faɗi hakan to kada ki yi shayin ce wa da shi ni Baffahnki Ummaru Sanda nace ƙarya yake yi, ko da ko shi mijin naki ne kika ji ya faɗa to bance ki amince da zancen ba, don kuwa so mai suna so yake yi maki ko da ko bai faɗa ba" Dije ta share guntayen hawayenta tace,. "To Baffah me yasa kullum yake ta yiman mugunta??, WALLAHI fa Hajiya kamar zata dake shi watarana idan taga yana cin zalina" Baffah daɗi ya sa bakinshi yaƙi rufuwa yace,. "Ki godewa ALLAH Dijengalata saboda ya yi maki baiwar da ba kowa yake yi wa irinta ba, ki ce Alhmdllh kawai sai ya ƙaro maki wata ɗaukakar" Dije ta washe baki tace,. "Alhmdllh na godewa ALLAH Baffahna WALLAHI na ji daɗin bokon da Hajiyar ta sakani, saboda na haɗu da mutane masu mutunci Baffah, WALLAHI baka ga yanda suke sona ba don ɗaya ma har karatu take ƙarani duk da su nasu karatun ba irin namu na nan garin bane, amman na fara ganeshi har ma na Kai hizif talatin wurinta Baffah, duk da fa cewa ta yi dole sai na dawo baya tun farko amman na yi nisa wallahi" Baffah ya faɗaɗa fuskarshi da fara'a yace,. "Ai duk inda kike albarkar da muke saka maki tana tare da ke, ke dai ki ci gaba da haƙuri kawai da sannu zaki zamo abar kwatance a wannan garin namu, tashi ki je ki yi SALLAH idan na dawo masallaci mu ci gaba da firarmu kawai" Yana ƙare maganar ya miƙe tsaye ya karɓi butar da Inna take miƙo masa ya fice ƙofar gida zuciyarshi cike fal da farin ciki. Bayan fitarshi ne Inna ta jawo hannunta da sauri suka yi ɗaki, ta maka mata wata uwar harara tace "Na sake jin kin faɗi sirrin dake tsakaninki da Mijinki ko na gidan aurenki ga kowa sai na saɓa maki, ko da ko Baffah'n ne naji kin sake tona wata magana ba mai daɗi ba to ni kaɗai nasan abunda zan yi maki, tunda har na gano ke har yanzu baki da wayo, in kuma har kina son ya hanaki komawa ki daina makarantar da kike son zama likitan shikenan, kije ki yi ta faɗa har ya ji zafi ya ce ba zaki ci gaba da karatun ba" Inna tana gama faɗar maganganun cike da jin haushi ta fice, Dije ta biyota tace "na Bari Inna ni yanzu ma ko da wani ya tambayeni cewa zan yi ina jin daɗin zama da shi har ma da ƙanwarshi Fiddausi, ai ya yi haka ko Inna?" Innar ta juyo tace,. "Da kin taimaki kanki don muddin kika sake faɗar wani aibin da ya shafi aurenki to tsaf zai ce ba zaki koma birnin ba, shikenan sai ki dawo nan ki ci gaba da zaman tunda haka kike so" Dije ta rufe bakinta tace,. "Laa! Kin ko ga sai yanzu na tuno Inna itama da Hajiyar sai da tace da ni kar in faɗa maku yana cin zalina" Inna tace ",kinji ba tunda kin janyo ta fahimci baƙin surutunki naki ko?, To yanzu dai ki ko yi ɓoye sirrin Mijinki da na gidan aurenki ga kowa ma, ke har ni kaina nan bance ki faɗa man ba" Dije ta toshe dariyar da ta zo mata tace,. "Har da ke Inna to ke wani zaki je ki faɗawa ne halan?" Inna ta fice ɗakin tana faɗin "Maba zan baiwa kuɗi ya yi ta sanarwa yana shela ko'ina a garin nan sai kowa ma ya sani" Dije ta tuntsure da dariya tace,. ,"ALLAH ya bar man ke Innata" Inna ta ɗauki butarta ta yi bayi tana faɗin "ke kuma ya shirya man ke ba" Da dare ko da Baffah ya dawo gidan da ledar tsirenshi da ya siyowa Dijen tuni har ta yi bacci, dole ya ajiye mata sai da safe sannan ya bata ta cenye tana yi wa Usmanu dariyar an bashi tsoka biyu. Bayan ta yi wanka ne tace da Inna zata je gidansu Gambo su ƙara gaisawa, Inna ta ce da ita to ta jira a bata kayan tsarabar da aka kawo masu ta kai mata nata kaso, Baffah ya ce ta raba kayan a kaiwa duk wanda ALLAH yasa da rabonshi a ciki, ta fidda na Gambon Usmanu ya karɓa zai wuce mata da kayan a babur ɗinshi, sannan shi ya wuce birni wajen harkar kasuwancinshi. Sauran na mutanen garin kuma ya kira yara da kanshi anata lissafa gida gida da wanda za'a kaiwa sabulu da Omon, ita kuma Dijen ya bata na Maigari ya ce ta fara zuwa gidanshi ta kai masa kafin ta je gidan Gambon. Lanti da Mune sune suka riƙa kayan suka taka mata har gidan Maigarin, cikin natsuwa Dijen ta gayar da shi tare da Matanshi sannan ta karɓi kayan tsarabar ta bashi tare da yi wa uwargidan Maigarin ya jikinta akan kariyar da ta janyo mata lokacin gudun kura, duk da har lokacin bata koma dai-dai ba amman sunji daɗin kular da ta nuna masu, suna saka mata albarka ta fito gidan tare da jinjina yanda Dijen ta fara shiryuwa, saboda ganin yanda ta yi masu komi cikin ladabi ba kamar cen baya ba da ko gidan bata shigowa bale su sami arziƙin ta zo gayar da su. Suna fitowa Dije tace da su Lanti gidan Gambo nik son in je amman zuciyata tana bani in fara zuwa wurin Jummala in ganota, saboda jiya da tausayinta na kwana Lanti musamman labarin gudowar da kuka ce tana yi, ina son inje inji dalilinta don gaskiya bana son a cutar da rayuwarta WALLAHi" Mune ta sauke ajiyar zuciya tace,. "Hu'umm to ALLAH yasa Garbatin baya gida" Suka haɗa baki wajen cewa "Ameen" Dije ta ƙara da cewa "ko ma yana gidan ai sai ya fito ya barmu mun gaisa da ƙawarmu" Suka rankaya zuwa gidan Jummala sai dai tun kafin su isa suka fara jiyo kururuwar Jummala, cikin sauri suka ƙarasa cikin gidan abun mamaki ɗakin Jummalar a rufe amman sai kuwwa take zubawa tana magiya akan ya yi haƙuri, cikin faɗuwar gaba Dijen ta je bakin ƙofar ɗakin ta fara bubbugawa tana faɗin "Jummala ki buɗe ɗakin me ya faru da ke ne? Buɗe nice Dije na zo ganinki" Bubbugar ɗakin da Dijen take yi shi ya dawo da Garbatin daga duniyar ma'aurata da ya lula, cike da tsanani jin haushi ya sauko gadon yana gyara zaman kayanshi ya nufi Kofar ya buɗe, yana ƙarewa Dije kallo da jajayen idanuwanshi da suka so su baiwa Dijen tsoro, cikin dakiya tace "Matsa daga nan ni ka bani hanya inga Jummalar tun kafin ka kasheta ka raba ganawar tamu" Garbati ya yi maka mata wata harara tare da riƙe ƙofar yace,. "Sannu uwar Jummala to bari kiji WALLAHI da kin kawo iskanci har ki bar garin nan bazan taɓa barinki ki ga matata ba, don na sanki sarai da baƙin halinki tsaf zaki hure mata kunne ta bijire mani, bayan namijin ƙoƙarin da aka yi akan shawo kan matsalarta, don haka ki sani kika kuskura naji wani abu daga baya to ki sani duk garin nan ba mai hanani yin ƙasa ƙasa da ke idan na tashi gwada maki haukata" Dije ta riƙe ƙugu tana maka masa wata harara sama da ƙasa tace,. "A tsammaninka share shayen da ka fara zai tsoratani ne?? To ka yi kuskure don kuwa Dijen Baffah tana nan yanda ka santa har ma da ƙarin wani ilimin baƙin halin da na ƙaro, zaka bani hanya in gano Ƙawata ko sai na fara nuna maka kalar baƙaƙen halayen nawa??" Garbati ba shiri ya tuntsure da wata arniyar dariya yace,. "Ana iya shege a duniya yasin to ke Dije halan ance maki ni lusari ne kamar Tambari da kika renawa hankali?, To ni......" Fitowar Jummalar ne ya sa shi yin shiru saboda turenshi da tayi da hannu biyu ta fito tana share hawaye ta janyo hannun Dijen suka shiga cikin ɗakin, Garbati ya bita da kallo yace "Yanzu Jummala ni kika yi wa haka akan Dije?? Lalle kam yau sai kin nemi mai ƙwatarki hannuna" Dije ta ɗaga murya tace, "ALLAH ya fika Garbati" Jummala kam juyowa ta yi ta murguɗa masa baki wanda hakan da ta yi ba ƙaramar dariya ta bashi ba, ya sosa kanshi ya fice sannan su Mune suka shigo ɗakin su ma kowane da abunda zuciyarshi take ƙissima mashi. Dije ta zauna kan gadon Jummala tana ƙare mata kallon mamakin yanda duk ta bi ta firgice ta rame saboda zalamar Garbati, ta riƙo hannunta tace "Ƙawata baki da lafiya ne halan? Naga duk kin canza ba yanda na sanki ba" Jummala ta kalli Mune da Lanti ta share hawayenta sannab tace,. "Ba komi" Dije fahimtar tana son ta sanar da ita amman bata son su Mune su sani yasa ta ce da su Munen, "Don Allah Lanti ku jirani a waje zamu yi magana da Jummala kunji?, Kar fa kuji haushi kunsan komi yana buƙatar sirri" Lanti kasancewar tasan saboda Mune ne yasa Jummala bata son fayyace sirrinta yasa ta miƙe ta fice, Mune ta taɓe baki ta miƙe ta fice tana gungunin faɗin "To ALLAH na tuba mu miye ma ne bamu sani ba?" Suna fita Jummala ta fashe da kuka Dije ta fara lallashinta tana faɗin,. "Ki yi haƙuri Jummala ki sanar dani matsalarki da kaina zan je wajen Maigari in sanar da shi aka maki haƙƙinki" Jummala ta share hawayenta tace,. "Ai ba abunda za'a iya yi akan matsalata Dije saboda Garbati ya riga da ya sami ɗaurin gindinsu Babana, don asali ma sune suka bashi damar da har ya dinga yi man abunda yake man" Kan Dije ya ƙulle da zancen Jummala cikin rashin fahimtar inda ta dosa tace,. "Wace dama ce suka bashi halan?? Gaske dai naga yana wata gadara ashe wuri ya samu" Jummala ta saka gefen ɗankwalinta ta shafe fuskarta ta ce,. "Tun ranar da aka kawoni gidan nan ya fara bijiro mani da wani sabon iskanci, ganin da gaske yake yi yasa na ƙwaci kaina da ƙarfin tsiya na gudu gidanmu, amman tun cikin daren aka dawo masa dani, ke in taƙaice maki labari na jera sati ɗaya ina guduwa cikin dare ana dawo dani, a ranar da na cika kwana takwas a gidan nan ne Baba Ɗanliti ya zo da ƙatuwar igiyar ya ɗaureni kan gadon nan ta ko'ina, yanda ko motsin kirki bana iya yi bayan ya gama dukana yanata zagina, haka ya fice ya ce da Garbati duk abunda yake so ya yi dani kar ya ji tausayina, Garbati ganin wannan damar da ya samu yasa bai ji kunyar ALLAH ba ya yi ta cin zalina, ina kuka ina ihu amman bai ji tausayina ba ko kaɗan asali ma haka na kwana ɗauren, sai da safe ya kwance ni haka kullum dare Baba Ɗanliti yake zuwa yana ɗaureni har tsawon kwana uku sannan aka daina ɗaureni, shi kuma Garbati baya jin kunyar ALLAH baya tsoron aradu ta faɗo masa har yanzu bai fasa abunda ya ke yi ba" Dije tace "Ni Jummala har kinsa jikina ya yi sanyi WALLAHi, saboda nasan Baba Ɗanliti mutum ne shi mai kirki banyi tsammanin haka daga wajenshi ba, amman ki yi haƙuri tunda har kika ga anata dawo dake idan kin gudu to ana son ki zauna ne, don haka don Allah ki daina ihun da kike yi kina tonawa Mijinki asiri tunda har baya barin cin zalinki, insha ALLAHu watarana ko ance ya yi ma ba zai yi ba tunda har nasan yana sonki Jummala, ki ɗauka cewa ko yanzu sharrin sheɗan ne da kuma shaye shayen da ya fara" Jummala ta yi saurin kallonta tace,. "Wa ya gaya maki yana shaye shaye ne?!" Dije tace,. "Ke baki ga idonshi bane yanda suka koma jajjaye??" Jummala ta yi saurin faɗin,. "WALLAHI Garbati baya shaye shaye don ko taba ma ban taɓa ganin yana busawa ba, wani lokaci dai ne nake ganin idanuwan suna komawa hakan ɗin, amman kuma daga baya sai su koma dai dai" Dije tace "to ki yi haƙuri ni dai don ALLAH Jummala tunda dai ke ma fa kina son Garbati" Jummala ta ce "in don so kam ina sonshi Dije amman abunda yake yi man ne bana so, sai inga kamar da mun mutu wuta ALLAH zai jefamu" Dije ta miƙe tsaye tace,. "Ni dai haƙuri nike baki kuma ina baki shawarar ki daina ihu da kuwwar da kike yi ki barshi da ALLAH shi zai saka maki, don WALLAHI har an fara gulmarki a garin nan namu akan gudun da kike yi kina iface iface" Jummala ta zaro ido waje tace,. "Na shiga uku Dije da gaske kike yi? Ashe ana jina wai ni ALLAH, gaske naga watarana yara suna zuwa gidan nan da sun kalleni suyi ta dariya" Dije tace,. "Kaɗan ma kenan idan baki daina ba har sai kin fita kinji ana faɗin ga Jummala mai ihu cikin dare" Jummala ta rufe baki tace,. "Aiko idan zai kasheni a gidan nan ba zan sake ihu har ajiyoni ba" Dije tana saka talkaminta tace,. "Yafi maki dai ko don gudun gori watarana, tare da ƙananan gulmar masu yawan surutu" Su Lanti da Mune suka taso ran Mune a jagule saboda ranta ya bata cewa da ita Dijen take, shiyasa ta yi saurin nufar hanyar fita tana faɗin "Ni dai kunga tafiyata daman aikena aka yi na biyeku" Dije tace,. "ALLAH ya kiyaye Mune sai mun haɗu gidanmu ko? ko shikenan daga nan munyi sallamar har in bar garin" Mune ta washe baki tace,. "Rufani ki saya anjima kaɗan ma zan sameki gidan Gambon, bari dai in je inda aka aikeni in dawo" Ta fice Jummala da Lanti suka ƙyalƙyale da dariya, Dije ma tana dariyar tace "Mune mutunniyata ALLAH ya nuna mani ta daina halinta da naji daɗi" Sannan Jummala ta rakosu har bakin gidan tana ƙarewa Dije kallo tace,. "Ashe gani duhu na yi maki ƙawallita, kinga yanda kika yi kyawonki masha ALLAH har da wasu kumatu kika fara yi, lalle birni ta karɓeki WALLAHi watarana ma ko ganeki nasan ba zamu yi ba" Ke kika ce haka Jummala balle ni Dijen😝😂 Akafta🤣 D/AUTA Ce✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *AM BACK MY FAN'S albishirinku Littafina na BAƘON YANAYI na sakeshi free ga kowa, duk mai buƙata ya nemeni insha ALLAHu zan bashi kyauta ba sai ka biya ƙwandala ba, fatana kawai ku bini da ruwan addu'oinku kamar yanda kuka saba, ina yinku sosai alkhairin ALLAH ya kai maku duk inda kuke masoyana👍🏻* *Lamba ta 39* Dije ta ƙyalƙyale da dariya tace,. "Haba Jummala ai duk inda na shiga ba zaki ce ki kasa ganeni ba, ballantana ma ai fuskata ba canzawa zata yi ba, ita ɗin dai ce wadda kika sani don haka ki ma daina wannan zancen, insha ALLAHu ni da ku mutu ka raba ƙawayena don kar ku ga wai don na je birni ku zaci watarana zan manta da ku, saboda komi na zama ai bazan taɓa mance Asalina ba, kuma muddin na tuno gida dole ne ku ma in tuno da ku, ni dai yanzu fatana kawai ki riƙe abunda na faɗa maki duk runtsi kada ki bari wani ya ji sirrin Mijinki, ALLAH ya baku zaman lafiya" Jummala da Lanti suka ce "Ameen" ta rakosu har ƙofar gida tana ɗagawa Dije hannu tace "Amman dai zaki dawo kafin ki koma ko?" Dije tana shirin yin magana kenan suka jiyo muryar Garbati yana faɗin,. "Ta dawo ina? Ai ko wannan don kawai na so ne da WALLAHi ba zatan bata damar yin magana da ke ba, wannan ziyarar ma da aka kawo mun gode da ita, ina fatar ALLAH ya sa ba'a jangwalo man abunda zai fi ƙarfina ba" Dije ta kalleshi sama da ƙasa tace,,,, "ka ma godewa ALLAH da har na zo na gyara abunda ka kasa gyarawa da kanka, idan ka ji tsoron Allah ka rage cin zalinta shikenan ka taimaki kanka, ni ka ga tafiyata don nasan darajar aurena bazan biyeka muna sa'insa ba" Tana ƙare faɗar haka ta buga masa tsaki ta wuce abinta,Jummala ta ɗaga murya tace, "Na gode Dije ALLAH ya biya sai kin dawo ai mun yi sallama ko?" Dije ta ci gaba da tafiyarta ba tare da ta juyo ba ta ɗago mata hannu tace, "Eh" Lanti ce kawai ta ce,, "to ya yi sai mun dawo jummala" Suna tafe Lanti tana bata haƙuri akan abinda Garbatin ya yi mata, Dije saboda haushinshi ƙanzil ma kasa cewa ta yi har suka isa gidan Inna Gambo. Yanayin yanda Gambon ta ganta yasa ta yi saurin faɗin,. "Wa ya taɓo mani Dijengalata ne? Daga zuwanta za'a fara ɗaga mata hankali" Dije ta janyo tabarma ta zauna ta ce da Lanti itama ta zauna, bayan sun gaisa ne tace "Wai ni kam Gambo yaushe Garbati ya koma haka ne??" Gambo ta ce "tooh! Ke kuma Dije me ya haɗaki da Garbati ne?, Ko kin manta cewa da da yanzu ba ɗaya bane?" Dije ta taɓe baki tace, "Ai ni Gambo ba ruwana da sabgarshi shine dai yake son shige mani hanci, don Ni WALLAHI in Banda Jummala da ba abunda zai sa ma in ganshi in yi masa magana, saboda baƙar muguntar da yake yi wa Jummala don ya ga ita ba zata iya ramawa ba, don WALLAHI ALLAH in nice a dare ɗaya zan ji masa rauni" Ta ƙare maganar tare da bubbuga hannunta tana dukan tabarma alamun da gaske take zancenta, Gambo ta yi mata wani kallo tana mere Baki tace " To ko ke ɗin ce me zaki iya yi? Ballantana ma ni ina maki addu'ar ALLAH ya rabaki da wannan mugun hali irin na Jummala, Ai babu sakaryar yarinya irin wannan yarinya da bata da aiki sai tonawa kai asiri, saboda a garin nan ma mu yaushe rabonmu da wannan abun kunyar da haukar da take yi ne?, Ai ni WALLAHi ya biyani ma da ya ke koya mata hankali tunda har ita ta zama mara rufin asiri" Dije ta bi Gambo da kallon baki san dawan garin ba ne, duk da wani gefe na zuciyarta kuma tana son ƙarin bayani akan zancen nata, ta sauke ajiyar zuciya tace,. "Ke dai Gambo don baki san irin cutar da yake yi mata bane, don ke kanki kinsan Jummala ba ruwanta abun ne ya yi mata yawa shiyasa ta kasa haƙuri" Gambo ta yi mata wani kallo tace, "To karkaɗe kunnuwanki da kyau kiji Jummala sam bata kyautawa kanta ba, saboda halinta na rashin haƙuri ne ya janyo komi, ina laifin Garbati don ya nemi yin kwanan aure da ita?, Mitssss! Ni bari inje in kawo maku fura ku sha ya fi man wannan magana mai cike da abun haushi" Dije ta yi tagumi tanata nanata kalmar kwanan Aure a ranta don kawai ta gano ma'anarshi, amman ta kasa cikin zuciyarta tace _"To ni kam wane kwanan Aure ne haka wanda har ake cin zalin mutum a kanshi?, wai ko dai Gambo bata gano abinda nake nufi ba ne shiyasa....."_ Hushin numfashin Gambon ne da taji a kusa da ita yasa ta yi saurin cire tagumin da tayi tana faɗin,. "Ni fa Gambo bana shan furar nan a ƙoshe nake" Gambo ta maka mata harara tace,. "Ita furar ce yau bazaki sha ba Dije? Tab! Lalle birni ya sa kin fara canzawa, yanzu furar da har kokawa muke yi da ke akan sai kinsha ina ba zaki sha ba itace yau na baki a arha kike gwasaleni? To ai in ke ba zaki sha ba ke Lanti karɓi ki sha tunda dai nasan ba zaki ƙi cimarmu ba ke" Gambo tana ƙoƙarin miƙawa Lanti furar Dije ta yi saurin riƙe kwanon tana turo baki tace,. "Ni dai bani in sha don naga kina ƙoƙarin ki canza man manufata" Gambo ta buge hannunta Dije ta sake riƙe kwanon tana dariya tace,. "Sai fa na sha Gambo kafin ki bata tunda har ni kika fara yi wa tayi tun farko" Gambo ta sakar mata tana faɗin,. "In banda ina tsoron ki janyo man asarar furar da ko lasata ba zaki yi ba, wai ma me ya janyo shi mijin naki da zai tafi ƙasar wajen bai je da ke ba??" Dije ta kai ludayin fura bakinta tana faɗin, "sha kuruminki ko yanzu idan ya dawo tare zamu koma sai kinyi shekara biyar baki ganni ba, balle har ki yi man kora da hali, don haka ki rubuta ki ajiye sai kin nemi ganina da kuɗinki baki ganni ba, don ma ko da zan dawo na koma baturiya bazaki gane ni ba" Gambo da Lanti suka fashe da dariya, cikin dariyar Gambo tace,. "sannu turawa masu jajayen kunnuwa sai dai kuma ke gashi naki baƙaƙe ne, to ko ya za'a zamo baturiyar da kunne baƙi Oho!?" Haka suka ci gaba da firarsu mai cike da barkwanci suna dariya har aka aiko kiran Lanti daga gidansu, bayan tafiyarta ne Dije tana wasa da kare tana zane a ƙasa tace da Gambo,. "Wai ni kam Gambo in tambayeki? minene kwanan Aure da naji ɗazu kin faɗa?" Gambo ta yi shiru na ɗan lokaci sannan tace,. "Yanzu ke baki san kwanan auren ba??" Dije ta na dariya tace,. "Da na sani Gambo me zai sa in tambayeki? Ko yanzu abunda yasa na tambaya don bana son ya fito a jarabawarmu ta hausa ne ko wata rana wani ya tambayeni ya gano ban sani ba??" Gambo tace,. "Hu'umm yanzu ke baki taɓa yin kwanan auren ba kike nufi ko yaya?" Dije ta yi shiru sannan tace, "To ba bama sai in na sanshi ba sannan zanyi" Gambo ta yi saurin cewa,. "Baki taɓa kwana ɗaki ɗaya da Mijinki ba?" Ta yi shiru tana nazari sannan tace "eh to na taɓa sau ɗaya lokacin da Hajiya ta matsa naje ɗakin Malaminmu na kwana, amman ni bansan me hakan yake nufi ba" Gambo tace "To yanzu ki adana tambayarki kar ki yi ta da kowa sai Mijinki idan har ALLAH ya dawo da shi lafiya, kar ki mance ki tambayeshi ki ji menene kwanan Auren?, Insha ALLAHu da kanshi zai warware maki zare da abawa, don na tabbata shi yasan me hakan yake nufi, amman fa kar ki sake ki tambayi kowa sai shi kin ji ko?" Dije ta ɗaga kai cikin rashin fahimtar inda ta dosa, amman har dare bata daina tunanin kalmar kwanan Auren ba, in ta canko wannan ta canko wancen har ta gaji ta jefar duka, duk da ta so ace ta tambayi Inna Hasiya amman da ta tuno da gargaɗin da Gambo ta yi mata sai ta fasa. Tun cikin daren ranar Inna ta fara haɗa wainar farar shinkafar da Usmanu ya siyo daga birni, madadin Geron da Baffah ya ce ayi da shi. Aiko tun da sassafe ta fara tuyar wainar Dije tana tayata har suka gama, aka bi gida gida da wainar ana rabawa mutane sai sambarka suke yi, don ko Maigarin sai da aka cika masa ƙaton kwano da waina da miya har da manshanu aka kai masa gida yana ta godiya. Mutane sai shigowa suke yi ana yi wa Dije Barka da zuwa ana yi wa su Inna godiyar tsaraba, duk da wasu da yawa ma gulma ce take kawosu don su ganewa idonsu yanda Dijen ta koma, sai dai yanda take ta gayar da su ne a mutunce yasa suka fara ajiye gulmarsu, don mafi akasarin masu shigowar sun jinjina yanda Dijen take gayar da su cikin ladabin da basu santa da shi ba, uwa uba yanda suka ga jikinta ya murje kyawonta ya ƙara fitowa duk da take baƙar fata. Kwanan Dije biyar a garin sai ga Abinci Garbati da kanshi ya yi sallama har ƙofar gidansu Dijen ya kawowa Dije inji Jummala, mamaki fal ranta daga ita har Inna saboda ta bata labarin abunda ya faru tsakaninsu, don ma tsabar renin hankali har da cewa wai don ALLAH ta je Jummala tana son ganinta, Dije tana ganin Inna ta shige bayi ta yi ficewa ta kira yaron da Garbati ya baiwa ya kawo mata abincin har ya yi nisa, ta miƙa masa tace ya je yace da shi bata so ai ita ba mayunwaciya ba ce. Yaron ya karɓa ya tafi ta tsaya soron tana jiran dawowarshi don kada ma Inna ta ji ta yi faɗan me yasa ta mayar, aiko madadin ta ga yaron sai ga shi ta ji sallamar Garbati, ta yi saurin fitowa ta tsaya gaban Garbatin ta riƙe ƙugu tana girgiza ƙafa tace "Yawwa daman ai kai nike jira abincin me ne ka kawo man? ance maka ina da yunwa ne ko kuwa??" Garbati ya marairece fuska ya ce,. "Nasan nayi maki abunda bai kamata ba amman don ALLAH ki yi haƙuri, WALLAHi naji daɗin zuwanki wurin Jummala kin ga yanzu zamanmu muke yi lami lafiya, WALLAHi na gode sosai da ƙoƙarinki ALLAH ya biyaki da gidan Aljannah" Dije dole ta ajiye makaman rashin kunyar da ta tanadar masa tace,. ,"Na yafe amman ku bar abincinku na gode" Tana ƙare faɗar haka ta koma gida abunta, Garbati bai yi ƙasa a gwiwa ba wajen sake nemo yaro ya ƙara aika mata da abincin sannan ya tafiyarshi, zuciyarshi cike da jin haushin mummunar fassarar da ya yi mata. Dama ka bani idan bata so ni ina ci😔 Akafta😆 D/AUTA Ce✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *AM BACK MY FAN'S😉* *Lamba ta 40* Shigar yaron ya yi dai dai da fitowar Inna daga bayi, cike da mamaki ta bi Dije da kallo har yaron ya ajiye kwanon abincin ya fice, Inna zata yi magana Dije ta yi saurin faɗin "Mayar masa da abincinsu na yi shine ya dawo da shi" Inna ta ɓata fuska tace,. "Ba'a mayar da hannun kyauta baya ko baza ki ciki ba sai ki kyautar ya fi da ace ki maida" Dije ta miƙe tsaye tana dariya tace,. "Bale ma zan ci ai abincin Jummala ne don haka zan ci inji in ta iya girkin" Inna ta maka mata harara tace,. "Au kina ma so amman shine kika mayar? to ALLAH ya kyauta amman ko ba yanzu ki daina mayar da hannun kyauta don wannan yana daga cikin aikin sheɗan" Dije tana wanke hannunta tace "insha ALLAHU Inna bazan sake ba, yanzun ma don ya gano naji haushin abunda ya yi mani ne" Dije ta zauna ta fara cin abincin tana yi tana rawa da kai tace "Inna ko ashe da gaske Jummala ta iya girkin" Inna ta yi banza da ita kamar bata ji ta ba har sai da ta gama sannan tace da ita, "Shin wai ke kin fara koyon abincin ƴan'birnin ko kuwa har yanzu irin namu ne kawai kika iya? " Dije tana lashe hannunta tace, "Ni fa Inna Makaranta nike zuwa kuma a cen ma muke kwana har sai anyi hutu nake dawowa gidan, kuma idan na dawo Hajiya bata bari in yi wani aikin wahala, cewa take yi wai in huta kafin in ƙara girma sai a fara koya man girkin" Inna ta yi shiru sannan tace,. "Idan kin koma ki dinga shiga cikin masu dafuwar abincin gidan kina kallon yanda suke girkinsu, ko da tace ki zauna ki huta ki ce da ita ke kina son ki iya kinji ko? Sannan ita kanta ki dinga share mata ɗakinta kina gyarashi tsaf tsaf yanda kika ga ana yi mata" Dije ta ɓata fuska tace, "To ai tana da mai yi mata gyaran ɗaki, har ma da bayinta duk akwai masu wankewa kullum" Inna tace,. "To idan kin koma ki karɓi komi ki dinga yi mata da kanki, girkin ma ki shiga cikin masu girkawa kuna yi tare don ki ga yanda ake yi" Dije ta turo baki tace "Don Allah Inna ki bari kawai Surry ta koya man, tunda naga itama watarana tana shiga ta yi girkin idan saurayinta zai zo fira, sai dai kuma su fa da wata ƙatuwar akwati suke sanwa a kai, baki ganshi ba da murhun ɗora girki ya kai shida ko bakwai fa, to ni har yanzu ban ma san ta yanda ake kunna abun ba, saboda da wutar lantarki ma naga ana aiki da shi" Inna tace "To ki dinga koya kinji kinga abincinsu daban da namu, idan baki iya ba sam ba zaki ji daɗin zama cikinsu ba, kuma kinga Mijinki ɗan gayu ne yana buƙatar ace komi kin iya irin nasu, idan kuma ya ga baki iya komi ba sai ya auro wata matar wadda ta iya abubuwa irin nasu, kin ga shikenan sai ta karɓe mijin ta barki sake da baki tunda baki iya komi ba" Dije ta yi shiru sannan tace,. "Ai ni Inna ko don renin hankalinshi ma dole in koya kafin ya dawo, amman fa gaskiya in yace zai auro wata bayan ni yasin sai naci Uban ko ma wacece inna" Inna ta zaro ido waje tace, "saboda mi? Ko ance maki ke kaɗai ce ALLAH ya halastawa ya zauna da ke? To kul kar in fara jin wannan shirmen gareki, don jikina yana bani yanda yake ɗan birnin nan ba zai zauna da ke ke kaɗai ba matuƙar ba kin iya komi na yan birnin ba, don haka idan har baki son ya ga wata ya sake aurowa to ki natsu da kyau ke ma ki zama yar gayu kamar su, ki dinga wanka kamar yanda suke yi, ki iya girki irin nasu, ki iya kwalliya irin ta su ke tafiya ma idan kin so zaki iya maidata irin tasu, saboda kawai ki zamo dai dai da mutanensu don kawai ki ƙwatowa kanki ƴanci, ki rage yawan surutu da faɗi ba'a tambayeki ba, ki zamo shiru shiru sannan ki dinga komi cikin natsuwa ba rawar jiki ko ƙiriniyar da kika saba yi anan ba, sannan kar ki yi wasa da ibada kamar yanda kika koya tun nan gidan, idan ma da hali ki dinga yin azuminki na Litinin da Alhamis don samun nutsuwar zuciya" Dije ta yi shiru tana ta wassafa duk abubuwan da Inna ta faɗa a ranta, sai cen ta yi ajiyar zuciya tace "Ai Inna na fara koyar wasu abubuwa, kinga ko kwalliyar garinmu da nake yi acen yanzu duk na daina yi, saboda Surry tace in ina yi mutane zasu gano cewa wai daga ƙauye na fito su rena ni" Inna tace,. ,"To ki yi ƙoƙari ki yi ta koyar abubuwa irin nasu kafin Mijinki ya dawo, saboda kawai idan ya zo ki yi masa bazata don na tabbata ba ƙaramin so yake yi maki ba, tunda har ya aureki a yanda ya ganki bayan akwai ƴanmata da yawa a cen birnin, amman duk ya tsallake kowa ya aureki" Dije ta cire tagumin da ta yi tace, "Ni WALLAHI sai in ga shi baya sona ma kamar Malam Lawi, don yafi sona da shi nesa ba kusa ba, don dai shi baki ga yanda yake ta hantarata ba komi na yi ya yi ta gwasaleni yana katsa man tsawa, watarana ma har dukana yake yi fa" Inna ta yi saurin faɗin,"Ni kaina da na haifeki ai idan kika kaini bango watarana ina dukanki ko kin manta ne?, To shikenan don kinyi laifi na dokeki sai ace ban sonki? Saboda haka idan kina son ki ƙwato ƴancinki gareshi to ki zama mace kamar sauran matan garinsu kafin ya dawo, in da hali ma har ki fisu natsuwa da kamun kai har ma da gayun gaba ɗaya, ke ko ki ga yanda zai dawo yana lallaɓaki don gaban kowa baya shayin nunaki matuƙar kika zama yanda yake so, sannan kika zamo dai dai da yanda na lissafo maki, amman idan kina wannan shirmen me zai hana ya jibgeki ko?, tunda ke kanki kinsan kunnuwanki ba jin magana suke yi ba" Haka Inna ta yi ta cusawa Dije ra'ayin son abunda zai sa ta ƙwato yancinta wajen Safwan, saboda a matsayinta na Uwa ta fahimci cewa har yanzu ba wani abu da ya shiga tsakaninsu na auratayya, kuma har ga ALLAH tana son su Hajiyar su ji daɗin zama da Dijen, kamar yanda ta ga ita Dijen hankalinta ya fara kwantawa da su, saboda kyawawan dabi'unta da zata nuna masu su zai sa ta samu matsayi fiye da yanda ta samu yanzu garesu, musamman shi uban tafiyar wanda take so ta zamo tauraruwa a wajenshi fiye da duk wasu mata da zai aura bayanta. Suna cikin firar ne suka jiyo sallamar Ladiyo, Dije ta yi saurin washe fuskarta da fara'a tace "Ladiyooo!" Ladiyo ta zauna kusa da Dijen tana gayar da Inna, sannan ta kalli Dije ta ɓata fuska tace "Yanzu Dije ki zo garin nan ki kasa zuwa wurina?" Dije tana dariya tace, "na so zuwa fa Inna ce ta hanani wai......" Kallon da taga Inna tana yi mata ne yasa ta yi shiru ba shiri, Ladiyo ta zubo da wasu hawayen takaici tace,. "Banga laifin Inna ba tunda har Bala bai ji kunyar karɓar kuɗi a madadinki ba, WALLAHI ki godewa ALLAH ma da bai zamo Mijinki ba, don yanzu haka ba yanda banyi da shi ba akan ya barni in zo in ganki yaƙi baki, yanzu haka ma bai san na fito ba saboda Duduwa bata gidan yana fita nima ta fito abuna" To fa🙀🤣🤣😂 Akafta😝 D/AUTA Ce✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *Ku yi haƙuri da rashin mayar da reply akan comments ɗinku wani lkc amman duk wanda ya yi ina group ɗin na gani duka kuma na gode sosai ALLAH ya bar ƙauna.* *Lamba ta 41* Inna ta yi saurin faɗin "Haba Ladiyo wannan hali ba halin macen da tasan haƙƙin aure bane, don na tabbata ke ma kin san cewa abunda kika yi ba kyautawa bace, saboda haka sawunki a likkafa ki tashi ki koma gidan Mijinki, kuma ki yi haƙuri tunda har bai amince da ki zo ba, insha ALLAHu Dije zata zo har gidan naku sai ku gaisa" Ladiyo ta miƙe tana matsar ƙwallah tace, "Don Allah Inna ki barta ta zo taje gidan kowa fa ni kaɗai ce bata zo wurina ba" Inna tace,. "Yi sauri ki je kada ya dawo ya taradda baki nan insha ALLAHu zata zo tunda nace maki zata zo" Ladiyo ta fice da sauri tana faɗin,. "Sai kin zo Dije ina jiranki kinji?" Dije ta ce "kar kiji komi tunda har Inna ta bari ai zaki ganni, daman cen don ta ce kada in je ne shiyasa......" Inna ta yi saurin buge mata baki da bayan hannunta tace,. "Shikenan ke ba za'a yi sirri da ke ba? To ni ba wai bana son ki je bane don wata manufa, tsoron nike ki je ki ɓallo muna wani aikin azo kuma ace ke ce mafari, amman yanzun ma ko da zaki je ban lamunta da inji wata mummunar maganar Bala ta shiga kunnuwan Ladiyo ba, ke shi kanshi ma ban amince da ki tankashi ba idan kin ganshi matuƙar ba gaidashi zaki yi ba" Dije ta turo baki tace,. "Cabɗi ai WALLAHi Inna ban iya gaidashi lalle ma kam yaji daɗi nai" Inna ta yi saurin kai mata wani mangari Dije ta miƙe cikin sauri ta bar wajen tana dariya tana faɗin,. "Wai ke Inna yanzu duk abunda Bala ya yi man baki ga laifinshi ba?" Inna ta ce "ai mu godiya ma ya kamata mu yi masa ba muji haushinshi ba, don ke ma da kina da hankali da kin fahimci cewa hakan da ya yi taimakonki ne ya yi, don in banda shi da yanzu baki je makarantar da kike da gurin zama likitar ba" Dije ta yi saurin faɗin "Haka ne kuma Inna in don wannan kuma da wannan gaskiya, shege Bala shine ya ƙi yi man bayani tun farko in zo inyi masa godiya?" Inna ta maka mata harara tace,. "Ke tafi cen sakarya sai aka ce dole shine zai yi maki bayani ba kece zaki hankalta da abun alkhairin da ya yi maki ba?, To yanzu dai gobe idan ALLAH ya kaimu kije gidan ki gayar da Duduwa har shi ma Balan ki gaisheshi ki yi masa godiya" Dije ta washe baki tace, "aiko WALLAHi zan yi masa godiyar don na fahimci ba ƙaramin taimakona ya yi ba, yanzu ga shi ta sanadinshi na je birni na shiga makaranta idan ALLAH ya cika mani gurina shikenan sai in zama babbar Likita, kai Balan Duduwa dole ne inyi maka godiya yasin, Inna ko ma in je yanzu in dawo da wuri kafin ayi magriba?" Inna tace,. "A'a ki dai bari sai goben yafi" Haka ko aka yi goben tana yi bayan ta yi wankanta Inna ta ce ya saka tufafinta waɗanda suka fi kowane kyau cikin kayanta, sannan ta ɗauko kuɗi sababbi yan ɗari bibbiyu cikin waɗanda Hajiya Mama ta baiwa Dije wai ko da zata kasa idan ta buƙata, tace da ita ta je da su ta baiwa Inna Duduwa ɗari huɗu ta baiwa Jummala ɗari shida, ta ɗauko dubu ɗaya guda biyar ta ce idan ta ga Balan ta bashi ta ce ya yi cefane, sannan ta yi masa godiya, cikin hikima Inna ta dinga koya mata yanda zata yi da abunda zata faɗa, aiko Dije ta riƙe komi a kanta tana harda. Sai ko ga Lanti da Mune sun zo suka taka mata suna ta yaba irin kyawon da ta yi, sai taɓa lesin da ke jikin Dijen suke yi suna jinjina kyawonshi, Mune ta kasa haƙuri sai da ta ce "Lalle Dije ke kam kinji daɗi kin tako arziƙi wannan gayun haka ai ko birnin ma iyaka kenan" Dije ta washe baki ta ce,. "Ai wannan ba komi bane idan kuka ga waɗanda aka saka man cikin kayan lefena" Lanti da ta yi tagumi ta ce,. "Kinji daɗinki ke kam amman ko wannan ai ba ƙaramin kyau ne da shi ba" Haka suka yi ta zuzuta Dije suna ƙara koɗata tana jin kanta a sama har da wani canza tafiya tana yanga kamar bata son taka ƙasa, har suka je gidan basu daina wasata ba. Shigarsu gidan kai tsaye ɗakin Duduwa ta nufa, cike da fara'a Inna Duduwa ta fara tarbonta tana faɗin "Lale marhabin da mutanen birni sannunku da zuwa, ashe muma zaki zo ganinmu? da har na fara yiwa Gambo ƙorafin rashin zuwanki ashe kina hanya?" Dije ta yi ɗan murmushi tace, "eh daman ina da ƙudurin zuwa mu gaisa, yanzu kuma ga shi na zo na wanke laifina" Duduwa zata yi magana sai ga Ladiyo aguje ta shigo tana wasar baki tana faɗin "Sannu da zuwa Dije ashe da gaske kece kika zo?" Dije tana dariya ta ce "Nice kuwa ba wata ba to ya kika ganni" Ta yi wani rawa da ido tana kallon kanta Ladiyo tace,. "Ai Dije ko kamshinki kawai aka ji ai ansan ke ɗin mai tsada ce balantana anyi arba da kyakkyawar fuskarki, ke ma da kanki kinsan kinyi kyau masha ALLAH da ke, ki godewa ALLAH birni ya karɓeki WALLAHi" Duduwa ta miƙowa Dije kwanon faraufaraun da ta haɗo mata tace,. "Karɓi ki jiƙa maƙoshinki kar ki biye wannan uwar surutun" Dije ta karɓa tana dariya ta ɗan kurɓa kaɗan ta miƙawa Lanti kwanon, tana goge bakinta da hankacif ta buɗe zif ɗin jakarta ta ciro ɗari biyu guda biyun ta miƙawa Duduwa tace, "Gashi a siye goro Duduwa" Duduwa jikinta yana rawa saboda tsabar farin ciki ta karɓa, sai zubawa Dije godiya take yi tare addu'a ba ƙaƙƙautawa, ƙarshe ma sai gata da ɓugewa da yiwa Dije kirari sai kace wata mabanya. Dije ta riƙo hannun Ladiyo da ke ta wasar baki tace, "muje ke kuma inga ɗakin naki Ƙawata" Ladiyo cike tsakanin jin daɗi ta ƙanƙame Dijen tana tsalle suka shiga sashen nata da aka keɓe da katangar da ta raba tsakaninta da Duduwar. Dije tana zama Ladiyo ta fara jero mata kayan ƙurasa kala kala waɗanda suka haɗa da danginsu, Fara, kwai da kwai, ƙamƙam, ɗantamatsitsi, hanjinligidi, da soyayyiyar aya, saboda su ne sana'arta da take saidawa, Dije kam duk da kwaɗayinta gaba ɗaya ba abunda ta ci saboda jan kunnen da Inna ta yi mata, ganin haka yasa Ladiyon ta zuzzuba mata kowane a leda ta baiwa Lanti ta riƙa mata, sannan suka ci gaba da fira na ɗan lokaci kafin ta fiddo kuɗinta itama ta bata, Ladiyo cike da jin daɗi take ta yi mata godiya, sannan ta miƙe tana yi mata sallama Ladiyon ta rakota bakinta bai daina yi mata godiyar ba, Duduwa ma ta biyota sai godiya take yi mata sai gashi ko suka yi kiciɓis da Balan, yana ƙoƙarin zagayeta ya wuce don yi yayi kamar ma bai ganeta ba, Dije ta faɗaɗa fuskarta da fara'a tace "A'a Malam Bala abun ba ko magana?, Ai sai ka tsaya mu gaisa ko?" Bala ya fara sosa kai yana faɗin, "a'ah Dije ce? ai ban ganeki ba naga kin zama wata babbar Hajiya shi yasa" Dije ta yi masa wani kallo tace, "ai dole in zama Hajiya Bala saboda ina tare da alhazawan, nan gaba kaɗan ma zan zo yi maku sallama idan zamu ta fi Saudiyya, ai dole ne in yi maka godiya akan abun alkhairin da ka yi mani, na gode sosai ALLAH ya ƙara lafiyar aljihu" Ta saka hannu ta ciro kuɗin a jaka tace,. "Ga wannan ba yawa a ƙara ayi cefane" Bala da gaba ɗaya kunya ta kasheshi cikin muzanta yace, "Da kin barsu kawai ai don har yanzu da sauran na cefanen" Duduwa ta yi masa wani mere tace, "da dai ka karɓa don kada ta tafi ka dawo kana cizon yatsa" Bala ya sosa ƙeya yace, "Ayi haka? " Dije ta mazge tace "Karɓi kawai ai an zama ɗaya Bala idan basu isa ba ka faɗa kawai sai a ƙaro maka ai, don insha ALLAHu zakkar da za'a badawa idan an tashi ka tsimayi zuwanta, ko don saboda Ladiyo ai ba'a rabu ba ana tare" Bala ya zura hannu cike da jin nauyi ya karɓe kuɗin, ya fara godiya Dije ta ce "Ai Ni ce da godiya WALLAHi na gode sosai ALLAH ya biyaka ya saka maka dai dai da taimakon da ka yi" Duka suka rakota har bakin gida sai godiya suke zubawa, har ta yi nisa Bala ya biyota cike da ladabi ya rusuna yace "Afuwa nake nema nasan nayi maki laifi ki yi haƙuri ki yafe man don ALLAH" Dije ta waigo tace da shi "Zan yafe maka kuma zan ci gaba da kyautata maka matuƙar ka riƙe Ladiyo amana, ka kyautata zamanka tare da ita kuma ka gyara halayyarka ta son kuɗi ka daina kiranta ɓarauniya, sannan ka gyara duk wata mu'amalarka da ita, to da ka yi hakan ka ɗauka cewa tamkar ka sami alkhairina da na Maigidana ne, amman muddin na ji cewa baka zama da ita yanda ya da ce to ka ɗauka tamkar ka datse igiyar alkhairanka garemu ne, saboda haka idan ka gyara ka ga da kyau a aljihunka, idan kuma ka ɓata to shikenan ka lalace komi, ni ka ga tafiyata kuma ka sani zan saka masu kula da komi, don kada ka ga bana nan to ina da idanuwa ta ko'ina a garin nan" Bala baki washe ya ce "Ai Insha ALLAHu alkhairi ma zaki ji amman itama zan turo ta wajenki ki ja kunnenta akan abubuwan da take yi mani, da ta gyara shikenan matsala ta kau gareni da yardar Allah" Dije tace, "tace wannan ba damuwa bace sai ta zo kawai ALLAH ya sa mu dace dai gaba ɗayanmu ya bamu zaman lafiya" Yace "Ameen Ameen ranki ya daɗe ai ke kin haye saura mu kawai" Dije ta so ta yi dariya ta mazge tace, "kai m ka kusa hayewar matuƙar na dawo garin nan na ji labari mai daɗi" Bala sai duƙe ɗuke yake yi yan faɗin, "kar ki ji komi insha ALLAHu komi zai daidaita" Haka suka rabu Dije sai ƙumshe dariyar da take cinta take yi, su Lantin ma sai da ta basu ɗari biyu tace su raba, suka tafi gida suna ta jin daɗi. Hannuna ya yi sanyi yasin😩 Akafta😆 D/AUTA Ce✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *INA YINKU ALL MY FAN'S INA GODIYA🙏🏻 DA ADDU'ARKU GARENI KU DAƊE KU YI LASTING MUTANENA👍🏻* *Lamba ta 42* Dije kam tana cin kayan ƙwalam ɗin tana kyalkyatar dariya, tana baiwa Inna labarin abunda ya faru don ko da su Baffah suka dawo gidan ranar labarin ne kawai take ta basu ana dariya. Haka Dijen ta ci gaba da ziyarar yan uwa da abokan arziƙi don har wani ƙauye suka je da Inna inda ainahin tushen iyayenta suke, kowa ya yi sambarka da auren Dijen don kuwa su ma sun sheda ta sanadiyyar tsarabar Dijen da Inna ta kai masu. Satinta biyu dam a ƙiriu Direban da ya kawota ya zo ɗaukarta da uwar tsarabar ƙauyensu niƙi niƙi suka lula yola, bayan tasha kukan rabuwa da Inna da sauran ƙawayenta da yan uwa da abokan arziƙi, kowa da kalar tsarabar da ya bata ta kaiwa surukarta Hajiya Mama, don Maigarin kanshi galan ɗin manshanu lafiyayyen suya ya bada akai masu, Baffah da Inna kam babu ce kawai basu bayar ba don tsakanin tsintsiyar laushi, kuka, daddawa, guro, kayan yaji maburki, busasshiyar rama, gero, dawa, wake, niƙaƙƙen garin waken na ɗanwake lafiyayye, manja, manƙuli, soyayyar gyaɗa, kai kayan ƙwalam na Ladiyo ma ba'a barsu a baya ba, don kuwa kaf maƙulashenta sai da ta yo wa Dije tsarabarsu saboda takanas Bala ya bada kuɗi aka haɗa mata kayan. Tafiyar wuni biyu ce ta kai Dije Yola cikin tsananin galabaita saboda rashin sabo da tafiyar, Ba Surry da Hajiya Mama ba har Fiddo kanta sai da ta nuna jin daɗin dawowar Dijen, saboda himilin kayan tsarabar da ta zo masu da su, Hajiya Mama baki har kunne sai godiya take zubawa saboda tsananin jin daɗin karamcin da su Baffah'n suka yi masu. Kasancewar hutunsu Dijen ya ƙare kwananta biyu a gidan aka yi mata provision ta koma makaranta, ita kanta cike take da ɗokin ganin mutanenta sis Aysha da kuma ƙawarta Hannatu, saboda sunyi kewar juna ba kaɗan ba. Kwanci tashi asarar mai rai sai ga Dijen Baffah ta shiga jerin sahun kowace mace a duniya, don kuwa ranar farko da ta fara ganin baƙon watanta duk house ɗinsu sai da kowa ya sani, saboda uban kuka da ta ci akan ita bata taɓa iskanci ba amman jini sai fitowa yake yi a jikinta, Wayyo ita ALLAH a taimaketa wani yaci amanarta ya iskanceta bata sani ba, Sis Aysha itace ta janyota zuwa toilet saboda uwar dariyar da taga anael yi mata, cikin natsuwa ta fahimtar da ita komi ta nuna mata ga yanda zata yi ta kimtsa kanta, sannan hankalin Dije ya kwanta amman fa tasha tsokana a wajen mutane ba kaɗan ba, lokacin da ta gama kwanakinta ma Sis Aysha itace ta yi mata gwari gwari akan yanda zata tsallake jikinta. *Shin wai ina baƙin Turai ne?* Malam Safwan kam tunda ya tafi Ƙasar ya yi ƙoƙarin danne damuwar da ya tafi da ita domin ya fuskanci karatunshi, sai dai wani gefe na zuciyarshi yana tunano masa Dijen Baffah da shirmenta, wani zubin ya yi dariya wani lokaci kuma ya ɓata fuska musamman idan ya tuno abunda Hajiya Mama take yi masa akanta. Masha ALLAH kasancewarshi mutum mai tsattsauran ra'ayi yasa baya da wasu abokan kirki sai tsirara ko su just for mutunci kawai don shi miskili ne na gasken sosai, baya shiga shirgin kowa sai wanda ya dace ace ya shiga. Wannan halin na shi ne ya janyo mata da yawa suka mato a kanshi, inda ko wace ƙoƙarin take yi ace itace ta yi sa'ar ƙulla alaƙa da shi, musamman ma da ya kasance gifted akan karatunshi ko kaɗan baya wasa, don daman cen shi tun asali yana baiwa karatu muhimmanci ko lokacin da ya yi karatun a gida Nigeria bale yanzu da ya shigo cikin fararen fata. Matan turawan ma da yawa wasu sun ƙyasa ballantana na mu matan na baƙar fata masu zuwa cen karatu, sai dai rashin fuskarshi yasa kowace take ɗar ɗar da shiga sabgarshi don tsoron kada ya yanƙwanasu su ji kunya, amman a hakan sai da wasu turawa suka sami kanshi suka fara mutunci da shi, a cikin baƙaƙen fatarmu namu ma akwai mace ɗaya Zainab wacce ake kira da Zee bab da Namiji ɗaya Auwal da suka sami sa'ar shiga rayuwarshi, waɗanda su kansu yan asalin Nigeria ne sai dai kowane daga cikinsu suna garuruwa mabanbanta, zee Bab yar Gombe ce yayin da Auwal yake ɗan asalin Kano, wasa wasa sai gasu sun zamo aminanshi waɗanda komi zasu yi dole ne sai sun nemi junansu. Zee Bab kam gurinta na shiga rayuwar Safwan ya cika don kuwa sannu a hankali ta fara nuna masa irin yanda ta damu da shi, kasancewar ba directly ta fito masa ba shiyasa bai hantareta kamar yanda ya saba yiwa sauran mata ba, cikin dabara ta ƙulla alaƙar soyayya da shi mai ƙarfi, wadda ta kai basa shayin nunawa duniya irin yanda suke son junansu ko a gaban ma waye, har suna iƙirarin zasu auri junansu duk runtsi duk da cewa itama Zee ɗin tana da mijinta da zata aura acen gida Nigeria. Sai dai akasin da aka samu shine ranar da Safwan ya sanarwa da Hajiya Mama labarinta rufe ido ta yi fata fata da shi, akan cewa bata lamunta da ya auri kowace mace ba har sai ya mutunta auren Dije tukunna, shi ko ya nuna mata shi fa ba sonta yake yi ba yanzu ya sami matar aure kuma ita yake so ya aura, don hasali ma ita kanta Zee ɗin bai sanar da ita cewa yana da wata mata ba, saboda rena auren Dijen da ya yi a tunaninshi da ya auri Zee zai korata ta koma ƙauyensu, idan kuma Hajiya ta bashi dama zai cikawa amininshi Lawi alƙawalin da ya yi wa kanshi na duk runtsi sai ya mayar masa da ita ya aureta tunda har ya fishi sonta. Sai dai kuma gashi Hajiya Mama tana son dakushe masa karsashi, don shi kam sun riga da sun daidaita da Zee akan da ya kammala karatunshi zasu dawo gida Nigeria ayi aurensu kawai. Akan haka ne ma rashin fahimta ya shiga tsakaninshi da Hajiyar, idan ya kira wayarta ta ƙi ɗauka ya galabaita sosai da mugun fushin ta yi da shi sosai, saboda duk Iyayenshi maza ya yayunshi biyu mata da suke aure duk sunyi ta bata haƙuri akan ta barshi ya yi auren amman ta yi biris da kowa, tace in dai har akan ta goya masa baya ne ya yi wani auren ya ci amanar yarinyar mutane to bazata taɓa lamuncewa da auren ba, jin wannan kalaman nata masu tsauri yasa ya ajiye komi ya nufo Nigeria ba shiri, sai dai yanayin da ya taradda ita ya sa ya ƙara gasgata zancenta dole marairecewa akan neman biyan buƙatarshi, tare yi mata bayanin cewa shi ba zai ci amanar Dijen ba, asali ma so yake yi ya haɗata da masoyinta na asali tunda har ya sami matar da yake so. ganin ta ƙi amince cewa ne yasa ya kwaso mata mutane suka zo suna bata baki kowa da abunda yake cewa dangane da ALLAH ya ce Annabi yace, ana roƙonta akan ta barshi ya yi aurenshi kafin ita Dijen ta mallaki hankalinta tasan minene auren, da ƙyar aka shawo kanta amman da sharaɗin duk ranar da Amaryar ta tare itama Dijen a ranar za'a kaita gidanshi a matsayinta na uwargida, hankalinshi ya ƙara tashi ya ruɗe gaba ɗaya saboda tsoron Zee taga kamar ya munafunceta tunda bai ce da ita yana da wata matar ba, aikam ba kalar magiyar da bai yi mata ba akan ta janye zancen tariyar Dijen sai daga baya idan Zee ta zo, amman Hajiya Mama tace sam! Bata san da wannan zance ba, dole ba kuzari ya harhaɗa kayanshi da nufin komawa, saboda yanda ita Zee ɗin ta dameshi akan ya dawo ya dawo. Hajiya ta ce da shi kafin ya bar ƙasar ya je makarantarsu Dije ya ganota, amman don kada ma ta gano ba zuwan zai yi ba ya nuna mata cewa zai je har da cewa ta kawo saƙo, aikam sai ga shi saƙon ma da ta bada akaiwa Dijen aika mata ya yi shi ya fece, zuciyarshi cike da mugun jin haushinta saboda shiga rayuwarshi da ta yi, uwa uba yanzu da ta sanadinta aka hanashi yin abunda yake so, don shi bai ma san da wane kalar idon zai kalli Zee ya sanar da ita cewa wai yana da mata, kuma matar ma irin Dije ai wannan ma shi idan ta sani ya zubarwa da kanshi aji, shiyasa ya ci alwashin ba zai taɓa bari tasan da wannan mummunar maganar ba, har sai idan an ɗaura masu auren da ita idan ta zo ta gani da kanta ta ji da kunnuwanta, akan haka ya tsayu suka ci gaba da zuƙar soyayyarsu hankali kwance, duk da kuma wani gefen na zuciyarshi cike yake da fargabar Zee ta san da labarin kafin aurensu. *** A cen ƙauyensu Dijen kuma anyi auren Usmanu da Hansai, Dijen ma ta je amman kwananta biyu ta dawo Yola saboda a lokaci ana cikin karatu ne excuse ne aka ɗaukar mata, ƙawayenta kuma su Jummala da Ladiyo ma masha ALLAH zamansu lafiya, sun ajiye shirmen yarinya sun fuskanci zaman aurensu, sai dai Balan Duduwa da kullum tsimayi yake yi zuwan ranar da Dijen zata aiko masa da zakkar, shiyasa lokacin da ma ta zo bikin Usmanu yake ta rawar jiki akan bata wani girma na musamman, ganin hakan yasa ta sake yi masa wata kyautar duk da cewa a lokacin itama buƙace take da kuɗin saboda guntayen matsalolin hidamar auren Usmanun, don ba ƙaramar hidima aka yi ba saboda ko ɗakin Hansai shafe yake fess da broking tyles, Mutane sai zuwa gani ake yi ana sontin sulɓinshi, don kaf garin ɗakinta ne kaɗai da tyles ɗin don Inna cewa ta yi ta haƙura bata so ita kam ta yafe. ***** Kwanaki suna tafiya makonni su zo su wuce, wata ya wuce shekara ta zo wasa wasa sai ga shekara biyu an laƙumeta ba tare da an tantance ba, bikin Surayya ya zo sai hada hadar bikin ake yi bangaroran biyu, waton gidan ango da na Amarya saboda daman cen angon ne ake jira ya kammala ginin gidanshi, Alhmdllh kuma ya kammala masha ALLAH yanzu haka saura sati biyu ayi auren nasu, Safwan ma kanshi saura shekararshi ɗaya ya kammala karatun da ya je yi ya dawo gida, ayi aurenshi da masoyiyarshi Zainab wadda a yanzu yake jin akan sonta ba gudu ba ja da baya. Dijen Baffah ma a lokacin tana J.a.s.s 3 zasu yi j.l.c su wuce s.s 1, a lokacin idan kika ga Dijen Baffah ba zaki ce itace ba, saboda yanda maƙerin ƴanmata ya fara ƙereta ta ko'ina ta cike masha ALLAH, kwanciyar hankalin da ta samu ya fito jikinta ya haskaka mata fatarta, don a duba ɗaya zaka gano tsantsar kyawon halittar da ALLAH ya yi mata, uwa uba ga kyawon fuskarta da ya fito ɗas cikin doguwar fuskarta, ga gashinta ya ƙara cika da tsawo saboda gyaran da yake samu sosai, Hajiya Mama kanta idan ta kalli Dije sai ta ji takaicin rashin sanin ciyon kan da Safwan ya nuna akan Dijen, saboda ganin yanda komai da ake so mace ta mallaka na siffar jikin Dije ALLAH ya wadata da abunta, sai dai kawai don ita ɗin tana baƙa amman kuma yanzu baƙin ba ƙaramin kyau ya yi mata ba, asali ma shine ya ƙara banbantata da sauran mata, don fatarta ta murje luwai luwai ta washe gwanin burgewa, ga ƙirjinta cike fam da dukiyar Fulani kuma a tsaye suke ƙyam! ba alamun zasu ranƙwafa a gaba, saboda girkin kwarya ne da su sun cika fam kuma sun baje a ƙirjinta, duk da ba wai sun gama girman bane amman a hakan ma sai sambarka. Ana saura kwana takwas bikin Surayya ne su Dije suka kammala zana jarabawar j.l.cn tasu, cike da farin ciki da jin daɗi suka baro makarantar tana ɗokin zuwanta gidan saboda shagalin bikin Surayyar da zasu yi. Aiko tana dawowa suka ci gaba da shirye shiryensu tare da abokan Surryn yan jami'a, don Surry ta kammala degree ɗinta na farko cikin nasara ba tare da samun matsala ba, Fiddo ce ta yi candy a lokacin. Ana cikin hidimar ne gaba ɗaya suna babban falo sunata tsare tsarensu ne Safwan ya kira Fiddo, cike da tsananin jin daɗi ta cire wayar daga caji ta ɗauka tana faɗin "Oyoyo big bros don ALLAH ka zo cikin lokaci plss kasan fa kai ne idonmu" A cen gefenshi ya ce "Kada ki ji komi zan zo har ma da Auntynki itama zata zo bikin kuma wajenki zata sauka" Fiddo ta yi wani tsallen jin daɗi sai dai suna haɗa ido da Dije ta maka mata harara tace,. "Kada ka ji komi big bros bani ita mu gaisa idan kuna kusa" Zee ta karɓa cike da jin daɗin ganin yanda ƙanwarshi ke sonta tace, "Sannu Sis ki tanadi masaukina insha ALLAHu da ni za'a sha shagalin bikin Surry ki zuba idon ganina kinji" Fiddo ta yi saurin faɗin "kina da babban masauki big Aunty fatana kawai ALLAH ya kawoku lafiya" Safwan ya karɓa yace "Ina Surryn?" Fiddo ta yi wajen Surry ta miƙa mata wayar cike da jin daɗi ta ce "Amaryar Yaya Safwan ma zata zo bikin wayyo daɗi" Diirim! dum! Ba shiri kirjin Dije ya buga, cikin son jin gaskiyar abunda kunnuwanta suka jiye mata aranta tace _"Amarya? Wace Amarya kuma?..."_ Tunaninta ya katse ne lokacin da Surry ta kara mata wayar a kunne cikin sassauta murya tace, "Yaya Safwan ne" Gaban Dije ya ƙire ya faɗi ba shiri cikin ɗimaucewa ta ji wani kuka ya zo mata ba tare da ta tantance ba, saboda maimakon ta ji muryar Safwan ɗin sai jin ta yi Zee tana cewa "Ina fatar zaku tarybeni a matsayin Matar yayanku, kuma ku ɗauki cewa tamkar ma an ɗaura na shigo familynku" Cikin sauri Dije ta saki wayar ta miƙe da gudu ta nufi ɗakinsu, saboda zuwan wani dunƙulallen abu a ƙirjinta, wanda ya janyo ta kasa juriya bale ta haƙura da kukan bazatan da ya zo mata. Gareku reader's shin minene wannan abun da ya ziyarci zuciyar Dijen Baffah????????😢 Akafta🤞🏻 D/AUTA Ce✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *Domin farin cikinku kawai mutanena😅* *Lamba ta 43* Dije dunƙule kan gado tana kuka ta ji an dafa kanta cikin sauri ta goge hawayenta ta ɗago fuskata, aiko caraf ta yi ido huɗu da Hajiya Mama fuskarta ƙumshe da damuwa, ta yi jarumtar washe bakinta guntayen hawayenta da suka maƙale suka faɗo, cikin basarwa tace "Me aka yi maki Hajiyata?" Hajiya ta sake dafa kanta ta shafo dogon gashinta tace,. "Naji komi Surayya ta faɗa man ki yi haƙuri ki barni da shi ai zai zo garin ya sameni ina jiranshi" Dije ta yi saurin faɗin "Ki ƙyaleshi kawai Hajiya Ni na haƙura da duk abunda ALLAH ya ƙaddaro man, haka kuma ma zan yi biyayya ga duk abunda kika umurceni" Hajiya Mama cike da jin daɗin canjin da Dijen ta samu a wurinsu tace,. "Ki yi ƙoƙari ki nuna masa cewa fa ke ma mace ce duk runtsi kada ki bada wata ƙofa da shi ko yarinyar zasu renaki" Dije ta ɗaga kanta alamun gamsuwa Hajiyar ta riƙo hannunta tace, " saki jikinki ki koma ku je kuci gaba da shirye shiryenku, ki yi kamar daman cen komai bai faru ba" Sai da tasata ta je toilet ta wanko fuskarta sannan suka fito tare. Haka aka ci gaba da hada hadar tare da Dijen duk da zuciyarta ba daɗi amman hakan bai hanata nuna annushuwa kan fuskarta ba, sai dai kuma Fiddo tasha jinin jikinta saboda faɗan da Hajiya Mama ta yi mata akan abinda ta yi a gaban Dijen, duk da ta ci alwashin bazata fasa nuna ƙaunar budurwar Safwan ba ko don Dijen ta ji haushi. Ana saura kwana huɗu bikin ne Safwan ya diro Nageria tare da budurwarshi, sai dai ita ta yi garinsu sai taga gida sannan ta zo bikin daga baya, a ranar da ya diro gidan da marece za'a je yin wani event mai suna tea party, duka Amarya da ƙawayenta da ma ita kanta Dijen da Fiddo duka sunyi shigar wani yadi milk da kalar cofee, kowacensu ta sha makeup irin na classic ladys masha ALLAH gwanin burgewa, har sun shishiga motoci ne aka manta da agogon Amarya akan stool ɗakinsu, shine Dijen ta fito ta koma cikin sauri da nufin ta ɗauko ta dawo ana jiranta su tafi. Ta ɗauko agogon ta fito kenan a tsakiyar babban falon suka yi karo har tana ƙoƙarin faɗuwa, cikin sauri ya riƙota ta faɗo jikinshi tare da riƙeta ƙam ƙam don kar ta faɗin, jikinta yana ɓari ta yi saurin kai kallonta gareshi saboda turaren da ta ji ya tabbatar mata da cewa shi ne, ido cikin ido suka kalli juna dukansu a lokaci ɗaya gabansu ya faɗi ras! ras!, Cikin sauri ya saketa duk da bai tabbatar da cewa ita ɗin ce ko ba ita ba, itama kanta ta aro wata jarumta ta yi kamar ma bata taɓa ganinshi ba ta duƙa ta ɗauki agogon da faɗi ta fara taku a hankali cikin wani salon da ita kanta batasan ta iya irinshi ba ta fice, Safwan ya bi bayanta da kallo har ta ɓacewa ganinshi amman bai daina kallon ƙofar ba, cikin wani hargitsatstsen yanayi ya ja jakarshi ya nufi ɗakin Hajiya Mama, don gidan shiru saboda mutane da yawa sun tafi partyn. Dije kam har ta shiga motar suka tafi ƙirjinta bai daina bugawa ba, saboda ganin bazatan da ta yi masa duk da daman cen tasan da zuwan nashi a ranar. Sun gudanar da bikinsu masha ALLAH ansha rawa Amarya da Angonta sun gwangwaje tare da abokan ta da yan uwa da abokan arziƙi, Dije ma ba'a barta a baya baya bayan photunan da aka sha kala kala kowace da kalar nata salo ba ƙarya. Bayan an watse taron ne wani ya biyo Dije har gida saboda tun a cen wajen ta ɗauki hankalinshi sosai, yana biye da komi nata har suka dawo gidan, suna ƙoƙarin kwasar wasu kaya ne a bayan boot ya yi mata sallama. Ba shiri ta ɗago tana ƙare masa kallo sama da ƙasa sannan ta amsa masa sallamar a yangance, cike da jin daɗi ya yi wani tsadadden murmushi yace "Khadijah ko?" tayi saurin zaro ido waje tace "Ni? ko dai wata Khadijar?" Matashin saurayin yace, "ke dai tawa khadijar" Dije ta zaro Ido waje ta kinkimi kayan da zata ɗauka ta yi cikin gida don ita sam ma bata kula da Safwan da ke zaune harabar gidan yana chat da Zee ba, Amman shi tun daga nesa ya ƙura mata kallo har ta shige, sai dai kuma ganin wannan matashin saurayin ya bita da kallo ne yasa ya yi saurin miƙewa ya soka wayar aljihu ya nufo wurinshi, wanda kafin ma ya isa sai ga Dije da Fiddo sun zo kwasar wasu kayan, Saurayin ya sake nufar Dijen yana faɗin "Haba Khadijah ki tsaya ki saurareni mana, WALLAHi takanas wannan zuwan da na yi a nan donki kawai na zo" Ganin Safwan a wurin yasa ta yi saurin washe baki tace, "ALLAH sarki ka yi haƙuri daman na je ne in ajiye kayan in dawo, to ya kake dafatar ka zo lafiya?" Cike da mamaki Safwan da Fiddo suka bita da kallo, Fiddo ta yi saurin faɗin "Malam ina zaka kai zunubin fira da matar aure?" Saurayin ya zaro ido waje zai yi magana Dije ta yi saurin faɗin, "No! no! Share da ita wasa ce take yi maka dubanni da kyau, kai kanka ai kasan banyi kama da matan aure ba ko?" Fiddo zata sake yin magana Safwan ya yi mata alamu da ta yi shiru, dole tayi gum ba shiri saboda bala'in tsoronshi da take yi , Dan Saurayin kam ya bi Dije da wani shu'umin kallo sama da ƙasa ita ko sai wani girgizar jiki take yi tana fesa masa wani murmushin da ita kaɗai tasan ma'anarshi, sai dai ɗagowar da zai yi a ƙoƙarinshi na son mayar mata da martanin kallonta Karaf yaji saukar naushi a fuskarshi, kafin ka ce me ya fara lallasuwa a hannun Malam Safwan, don kuwa sai da ya ci nasarar haɗa masa jini da majina, da ƙyar aka ƙwaceshi a hannunshi don saboda baƙar zuciya irin tashi duk tambayar da ake yi akan me ya yi masa ƙanzil bai iya furtawa ba, hasali ma shigewa ya yi ɗakinshi ya dantse yana kuncinshi shi kaɗai. Dije kam zuciyarta fes ta kwashi sauran kayan ta yi cikin gida,inda ta taradda Fiddo tana gayawa Hajiya abinda Dijen ta yi wanda har ta janyo aka yi faɗan. Hajiya ta yi murmushinta mai cike da ma'anoni tace da Dijen kawai ta daina yin irin wannan wautar saboda shi aure ba'a wasa da shi, amman bayan haka ba wani faɗa ko jan kunne da ta sake yi mata, Fiddo kam ganin ba wani mummunan matakin da Hajiyar ta ɗauka akanta yasa ta ci alwashi a ranta na cewa _"sai na zuga Yaya Safwan ya jibgi shegiya kafin ya koma tunda ita Hajiyar mutanen ƙauyen sun shanyeta bata ganin laifin wannan munafukar ƴar tasu"_ Haka Safwan ya kwana cikin kuncin Dije kam ko a jikinta asali ma yi ta yi kamar ma batasan ta yi wani laifi ba, ko da safiya ta waye aka fara hidimar yin kamun Amarya wanda mutane da yawa sun ci buri a kanshi ciki kuwa har da Dijen Baffah, don kuwa tun da sassafe suka je gidan lalle tare da Amarya, bayan an ƙare ne suka halarci wajen gyaran gashi sai ga Dijen Baffah ta fito shar tamkar wata sabuwar Amaryar, masha ALLAH da ita gwanin burgewa bayan sun dawo gida ne saboda ɗakinsu mutane sun yi yawa ta yi ɗakin Hajiya domin ta shirya, saboda lokaci yana so ya ƙure masu saboda daɗewar da suka yi a wajen saloon ɗin. Cikin sauri ta tuɓe ta shige wanka a gaggauce ta fito da guntun towel ɗinta iya cinya amman a hakan da shi take yin tsalle tana goge dumbujen gashinta da ya sami ruwa ta gefe ɗaya, ba tare da ta damu da gudun shigowar wani ba saboda baƙar wautarta, sai ko gashi ta yi wani tsalle ta saka gefen towel ɗin tana goge bayan kunnuwanta, wanda hakan ya yi dai dai da shigowar Safwan, cikin rawar jikin ta gyara sai ga guntun towel ɗin ya suɓuce ya faɗi ƙasa. Ba shiri ya dafe kai tare da zaro ido waje saboda abunda ya gani ya janyo masa wani abu a zuciya tamkar bugun guduma, cikin sauri ta yi wata kuwwa tare da kwasar towel ɗin ta koma toilet aguje ta dantse tana rufe fuska alamun jin nauyin abunda ya faru, makyarkyatar tsoron hukuncin da zai yanke mata, tare da tsananin jin haushin kanta akan abinda ya faru don kada ya ce zai faɗawa wani ko ya rena mata hankali, daman cen ba da wata ƙima yake kallonta ba bale yanzu da ya ganta irin ganin da kowa na duniya bai taɓa yi mata irinshi ba sai shi. SAFWAN kam wani sabon tashin hankali ne ya ziyarceshi, dafe da goshi ya fice ya nufi ɗakinshi inda yake jin wani masifar ciyon kai tamkar ya rabe masa biyu saboda tsabar saran da yake yi masa. Cikin zafin nama ya jawo jakarshi ta tafiya da ya zo da ita ya fiddo wasu tablets ya afa a baki ya kora da ruwa sannan ya kwanta shiru yana nazari, tare da ƙoƙarin kawar da gizon da halittar Dijen take yi masa a ido, sai duk wani motsi nashi abun ya ke kallo a ido ya kasa goguwa akan hasken gilashin idonshi, cike da jin haushi ya ɗauko wayarshi ya fito harabar gidan ya zauna yana waya da Zee, inda take sanar da shi cewa gobe Alhamis zata zo insha ALLAHu. Suna cikin wayar ne ya fara hango mata suna fitowa kowace da shirinta har ma an fara kwasar wasu ana kaisu inda za'a yi taron kamun. Ya ci gaba da wayarshi yana yi yana kallon ta ina zai hango Dijen, sai dai duk iya nacinshi bai hango ko mai kama da ita ba, ya kasa haƙuri ya mike ya nufi cikin gidan sai dai tun kafin ya isa cikin babban falon ya hango bayanta wata ƙawar Surry tana ɗaura mata ɗankwali, wanda ba tantama zuciyarshi ta bashi cewa itace don izuwa yanzu ya fara hardace tsarin surar jikinta. Fiddo fito da shirinta tana hangoshi ta nufo wurinshi tana gayar da shi cikin ladabi tace "Big bros yaushe Auntyn zata zo ne?" Idonshi akan Dijen yana kallon bayanta yace,. "sai gobe zata zo amman ki ce da waccen yarinyar kada ta kuskura ta fita gidan nan bada izinana ba" Yana gama faɗar maganar ya fice ya faɗa Motarshi ya fisgeta cikin zafin nama ya bar gidan aguje, cike da jin daɗi Fiddo ta nufi wurin Dijen tana wata yatsina tace "To ke kinji ya ce kada ki kuskura ki fita gidan nan ba tare da izininshi ba" Cikin tsananin faɗuwar gaba Dije ta zaro ido waje tace "Inji waye?" Fiddo ta yi mata wani kallon uku saura kwabo tace "Wanda yake da ikon hanaki fitar idan kuma bai isa da ke ba ki je ƙofa a buɗe take" Tana ƙare maganar ta fice abunta fuuu tare da wasu ƙawayenta tana yatsine yaysinen ƙara turawa Dije haushi, Dije kam cike da tashin hankali ta fisge kanta daga ɗaurin ɗankwalin da ake yi mata ta nufi wurin Hajiya Mama, inda ta taradda ɗakin a cike fam da wasu yan uwansu, cikin sauri ta dawo ta makure tana sharar ƙwallah a gabanta mutane suke ta ficewa zuwa Kamun, har abokan ango suka zo ɗaukar Surayya ganin tana kuka ne yasa tace da ita ta daina kuka bari ta je ta faɗowa Hajiyarsu, sai dai Surayya abokanta suka matsa mata ba shiri ta bisu saboda jiranta da ake yi. Duk mai niyyar zuwa wurin kamun ya tafi amman Dije tana makure tana kuka ba tare da Hajiya ma ta sani ba, har sai da wata ta ganta ta je ta sanar da Hajiyar sannan ta zo tana tambayar abunda ya gabata zuwa kamun. Ba ɓata lokaci Dije ta sanar da ita saƙon da da barwa Fiddo ta faɗa mata, aiko take ran Hajiyar ya ɓace ta fara faɗa tare da danna masa kira, tace da shi duk inda yake ya yi gaggawar dawowa gida ya ɗauki Dije ya kaita wajen kamun da kanshi, sannan ta jaddada masa cewa minti biyar ta bashi ya zo ya tafi da ita, tace da ita ta je ta sake gyara fuskarta kafin ya zo. Jinjina ga Hajiyarmu ta mutunci👍🏻 Akafta😍 D/AUTA Ce✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *SPECIAL THANKS FOR YOU MY OMEESHER, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKI HAR GADON BACCINKI, HAƘIƘA MARYAM OMEE KE ƊIN TA DABAN CE A WURINA,KI SANI INA YINKI HAR ABADAN ABADE, ALLAH YA BAR ZUMUNCINMU HAR ALJANNAH, ALLAH YA KAREKI DA SHARRIN MUTUM DA NA ALJAN DA DUK WANI ABU MAI CUTARWA A DORON DUNIYA, UBANGIJI YA ƘARA DAFA LAMURRANKI YA ƘARA KAWO MAKI HASKE CIKIN RAYUWARKI, TABBAS NI DA KE AKWAI ƘAUNA IRINTA FISABILILLAH.* *Lamba ta 44* Cike da jin daɗi Dije ta koma ɗakinsu ta wanke fuskarta sama sama a gurguje, saboda kwalliyar da aka yi mata tana nan raɗam, ƙara gyarata kawai ta yi tare da sassaita ɗaurin ɗankwalin sai gata ta fito shar! da ita masha ALLAH, idonta kawai zaka kalla ka gano kukan da ta sha saboda jan da suka yi, amman a hakan ma ta fito ɗagwas ɗagwas abunta, ta ƙara feshe jikinta da turaruka ta ɗauki jakarta ta fito falo, zamanta bai kai na minti huɗu ba sai ga sallamarshi ya shigo yana wani ɓata fuska yana cin magani, ba tare da ya ma kalli inda take ba ya nufi ɗakin Hajiya Mama, daga nan inda take tana jiyo shi yana faɗin "Don Allah Hajiyarmu ki bar yarinyar nan renani take so ta yi fa, kuma ke kin zo kina goya mata baya ta je ta yi abunda bai dace acen, ki barni da ita don ALLAH ɗazu fa a gaban kowa ta nuna cewa ita bata da aure to a hakan za'a dinga barinta tana shiga ko'ina duk inda taso?" Hajiya Mama ta maka masa wata jar harara tace, "to Ina ruwanka don tace bata da aure? Auren ne da ita to? ka ga Safwan kar fa ka nemi takura man yarinya, ka barta ta yi abunda take so don kai ma an barka ka je ka yi abunda kake so ko?, To itama tana da ƴanci abarta ta sakata ta wala tunda kai baka so ALLAH zai bata rabonta a gaba, kuma umurni na baka ka ɗauketa yanzu ka je ka kaita cikin ƴan uwanta" Tana ƙare faɗar haka ta koma ɗaki abunta ta barshi a tsaye zuciyarshi kamar ta tarwatse saboda baƙin cikin da kalaman Hajiya suka sakashi, ya fito fuu yayi waje Dije ta bishi da kallo ganin bai ce da ita ta taso ba yasa ta ƙi binshi, amman sai ga ƙarar tada Motarshi tare da uban horn da ta ji ya fara bugawa iya karfinshi wani bayan wani, cikin sauri ta miƙe ta fito ba tare da ma ta damu da yawan horn ɗin ba ta fara tafiyarta a yangace tana wani basarwa itama fuskarta a haɗe, cike da masifar jin haushinta ya yo kanta da motar kamar zai kaɗeta, amman kasancewar itama zuciyarta a wuya take ko ɗar bata ji ba, asalima tsaye ta yi tana kallon gefe tare da riƙe ƙugu tana girgizar ƙafa, a zuciye ya fito cikin masifa ya ɗaga hannu da nufin sharara mata mari, kallon da ta yi masa yasa ya yi saurin dunƙule hannunshi, sai dai ya yi jarumtar nunata da yatsa yace "Don kin ga Hajiya tana ɗauke maki shine zaki kawo man ƙananan iskanci ko?, To WALLAHi da kin cikani ɗaukarki zan yi in mayar da ke garinku, don ni aure zanyi bazan juri zama gwauro ba akanki baƙar baƙauyiyar banza, wawuya kawai wadda bata san darajar aure ba in banda ƙaddara ma ni me zai sa in rasa matar da zan aura sai ke?" Ya nunata a wulaƙance sama da ƙasa sannan ya buga wani uban tsaki ya juya ya shige motarshi tare da rufo ƙofar da ƙarfin bala'i, ganin ko motsi ta kasa yi illa kallonshi da take yi fuskarta a haɗe tana wassafa irin abunda zata yi masa ta huce, yasa ya leƙo da kanshi yace "WALLAHI idan baki zo ba tafiyata zan yi sai dai aga laifina" Dije ta yi masa wani mugun kallo sannan ta tako ta buɗe bayan motar ta zauna itama ta jawo Kofar da ƙarfi har sai da tayi ƙara tace garam!, Ba shiri ya waigo baya yace "Uban wa kika ajiye ya zamo direbanki?" Ta yi banza da shi ya sake maimaita maganar nan ma ta sake yin banza da shi illa gefe da take kallo tana wani cin magani, aiko a zafafe ya fito ya buɗe murfin ya fisgota iya karfinshi sai gata da faɗowa jikinshi, ba kunya ya saka hannu ya rungumota gaba ɗaya tsantsan don ya kasa controlling ɗin kanshi, cikin zafin nama ta tureshi tare da nunashi da hannu tace "Babban gangancin da zaka yi kenan a rayuwa ka ce zaka taɓa jikina, don WALLAHi sai na nuna maka cewa Dijen ce dai wadda ka sani ba wata ba, haka ma zan banbance maka tsakanin Khadijah da Dije, idan kuma kana musu ka sake taɓa wani sashe na jikina ka gani, ko an gaya maka cewa ni ƴar iska ce kamar matsiyaciyar budurwar da zaka aura?" Ta buga masa wani uban tsaki ta buɗe gaban seat ta zauna ta wani hakimce tana wani faɗi tana bajewa,, madadin ya ji ta ɓata masa rai sai kawai ya tuntsure da wata dariyar mugunta, ba tare da ya ce da ita ƙanzil ba ya faɗa motar ya ja da ƙarfi yana tafiya yana shafa gemunshi yana murmushi, kasancewar Dije ba wani sanin garin ta yi ba shiyasa bata gane inda yake bi da ita ba, har sai da suka kai wani katafaren gida wanda tun daga bakin Gate ɗin gidan zaka gano ba ƙaramar nera aka kasa wajen haɗashi ba, maigadi ya yi saurin wangale masa Gate ɗin yana faɗin "Sannu da zuwa ranka ya daɗe" Safwan yana amsawa cikin isa kamar ba shi bane ya ke ta faman murmushi ba, cikin faɗuwar gaba Dije ta yi saurin kai kallonta gareshi ta kalli gidan tace "Ba fa nan ake kamun ba, me ya kawomu nan kuma??" Ya yi banza da ita ya fice ya karɓi key hannun Maigadin ya leƙo da kanshi saitinta yace, "Zaki fito ko sai na fito da ke?" Dije ta ɓoye firgicinta da take ciki tace "Idan ka ga na fito to ka kaini inda Hajiyarmu ta ce ka kaini ne" Ya ce "ok to jirani Bari in zo minti biyu" Ta murguɗa masa baki tare da bin bayanshi da kallo har ya buɗe wata ƙofa da ta kasance gefe ɗaya na farkon shigowa gidan, ya shiga minti biyu zuwa uku sai gashi ya fito tana ganinshi ta wani juya kanta gefe tana cin magani, yana zuwa ya buɗe motar ya riƙo hannunta ta fisge ya sake janyo hannunta da ƙarfi ta riƙe kujera tana faɗin "Ba nace kada ka koma taɓani ba? Zaka sakeni ko sai na janyo abunda gaba ɗaya unguwar nan zata taru akanka?" Ba tare da ya damu da zancenta ba ya janyota gaba ɗaya jikinshi tana tureshi yana ƙara maƙaleta ya janyota iya ƙarfinshi tana tirjiya amman sai da ya shiga da ita cikin gidan, cikin tsoro Dije tace "Ni dai tsaya mu fahimci juna WALLAHi ba a nan ake bukin ba don ALLAH ka kaini inda ake yi" Ta ƙare maganar cikin kuka saboda ganinta da ta yi har ƙuryar wani ɗaki ya yada ita akan ƙatuwar katifar da ke shimfiɗe cikin ɗakin, tsoronta ya ƙaru ne lokacin da taga yana rufe ɗakin da key, cikin firgici tace "Don girman ALLAH ka yi haƙuri WALLAHi ni ba ƴar iska ba ce" Safwan ya waigo yana wata dariya yace "To Ni da ke waye ɗan'isakan a cikinmu?" Ta yi saurin faɗin "Ni ce, Ni ce WALLAHi" Ya ƙumshe dariyarshi yace,. "To ai ko yanzu zamu gwada ƙwanji irin na ƴan'iskan ai kin iya ko?" Ta yi saurin girgiza kai tana matsar ƙwallah ganin ya fara cire riga ne ya sa Dije shiga cikin wani mugun tsoro ta zaro ido waje cikin kuka tace "Ni Dije yau me nake shirin gani ne?" Safwan ya mazge ya fisgota ta faɗo jikinshi ya fara yunƙurin zuge mata zif ta yi saurin riƙe hannunshi tana kuka tace "Ka ji tsoron Allah kada ka ci amanar iyayena don kaga basu garin nan" Safwan ya fisge hannunshi cikin jajayen idanuwanshi ya kalleta ido cikin ido yace,. "Kika kuskura na sake jin wata magana ta fito bakinki sai kinyi danasanin furta ta" Dije ta yi saurin rufe bakinta tana toshe kukan da zai fito saboda tsabar tsoron da ya bata amman bata daina zubar hawayen kukanta ba, saboda tana ji tana gani ya zuge zif ɗin rigarta tare da zura hannunshi ta ciki, tashin hankalinta bai ƙaru ba har sai da ta ji inda hannunshi ya sauka, ta yi wata zabura tana ƙanƙame jiki tana faɗin "Ka tausaya man don ALLAH wallahi Ni ba ƴar iska bace kai ma sheda ne don ALLAH kada lalaceni" Safwan kam laushin dukiyar fulaninta da yaji a hannunshi yasa shi ɗimaucewa, cikin wata siriryar murya yace "Ba wani abu zanyi maki ba amman WALLAHi idan kika sake yiman gardama sai kin nemi mai ƙwatarki hannuna" Dije tana kuka tace "Ka ceci rayuwata WALLAHi Baffahna ya ji wannan labari kasheni kawai zai yi ba zai barni da raina ba, kada ka janyo abunda zai sa Inna ta tsine man in bi duniya don ALLAH" Cike da jin haushin magiyar da take yi ya mayar da rigarshi ya buɗe ɗakin a fusace ya fice, cikin sauri ta mayar da zif ɗinta ta ɗauki gyalenta ta fice jikinta sai rawa yake yi, sai dai ganinshi duƙe jikin motar ya dafe kai yasa ta ji jikinta ya yi sanyi, amman a hakan ta buɗe seat ɗin gaba ta zauna tana share hawayenta, sai da ya ɗauki lokaci sannan ya shiga ya tada motar suka fice gidan Maigadin yana yi masa ALLAH ya tsare amman ko kallonshi bai yi ba. Kai tsaye wajen kamun ya nufa da ita yana ajiyeta bakin Gate ɗin ya juya abunshi ko kallonta bai sake yi ba, Dije ta bi motar da kallo cike da mamakin abunda ya sauyashi lokaci ɗaya, cikin sanyin jiki ta ja ƙafafuwanta ta shiga wurin kamun. Har aka gama kamun bata da wata natsuwa yaƙe kawai take yi saboda abunda Safwan ya yi mata yasa taji zama garin gaba ɗaya ya fita kanta, don ko ƙudin da ta tanada don ta yi liƙi haka ta koma da su gida ko nera bata liƙa ba, asali ma gaba ɗaya komi ta ji ya fita ranta har sai da Surayya ta fahimci halin da take ciki, cikin damuwa ta ke tambayarta me aka yi taganta so silent haka? me Yaya Safwan ɗin ya yi mata? Dije kam iyakaci tace ba komi ƙarshe ma sai kuka ta fashe da shi, Surayya ta yi ta bata haƙuri don jikinta ya bata cewa wataƙila ko dukanta ya yi saboda ta gaya mata cewa Hajiya ta matsa masa dole shiyasa ya kawotan. Fiddo kam daɗi kawai take ji saboda ganin Safwan ya fara koya mata hankali, don yanayin Dijen ya nuna ƙarara akwai abun takaicin da ya ƙumsa mata, Hajiya ma kanta ganin yanayin Dijen yasa ta jata gefe tana yi mata faɗa akan ta daina yi masa kuka idan ya yi mata wani abu, ta nuna masa bata ji zafi ba ta hakan ne zai gano kuskurenshi har ya fahimci bai kyauta ba, cikin kwantar da murya ta samu ta shawo kan Dijen, duk da Dijen taso ta sanar da ita abunda ya yi mata amman tana jin kunyar ace ta faɗi wannan abun kunyar wani ya ji, sai dai tasha alwashin duk ya sake kwatsnta mata wannan iskancin ita ko sai ta faɗawa Hajiyar komi. Safwan kam ALLAH ne kawai ya kawoshi gida saboda rikitaccen yanayin da ya faɗa, wanda shi kanshi ya yi danasanin biye wa son zuciyarshi da ya yi, gashi zai janyowa kanshi baƙauyiyar yarinyar ta ga damarshi a banza a wofi, yaci alwashin ba zai sake kulata ba kuma zai yi ƙoƙarin auren Zainab kafin ma ya kammala karatun, sai suyi zamansu a cen kawai har sai sun gama karatunsu sun huta sannan ya dawo gida. 😝😝😝😝😝uhum Akafta😍 D/AUTA Ce✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *COMMENTERS ina matuƙar alfakhari da ku, saboda jajircewarku wajen daɗaɗan Comments naku ba dare ba rana,, Mmn Irfaan taki gaisuwa ta musamman ce,, ƴargata mmn Sultan ina yabawa ƙoƙarinki a kullum,, Hauwa Zubair ina yinki sosai tawajena,, Mun Sayyid sannu da ƙoƙari, Sa'ar Bukar Allah ja da kwananki,, Daughter Rufaida siffanta matsayinki a wurina abu ne mai girma, Maryam Omee bakina ba zai gaji wajen gode maki ba, saboda comments ɗinki yana ƙara mani ƙarfin gwiwa sosai, Ummu Afrah (Goribatyna) zumuncinmu daban ne,,,wai wai abun da da yawa fa aka ce mutuwa ta shigo kasuwa, Mutanen Dije idan nace zan ta lissafoku tabbas zan ƙare wannan page kaf ba tare da na gama zayyanoku ba, saboda haka mu haɗu a next Page's sannu a hnkl zamu game😉.* *Lamba ta 45* A ranar haka ya kwana yana ta murƙususunshi shi kaɗai cikin ɗaki ba wanda ma yasan me yake ciki, don kuwa yanda yaga dare haka ya ga safiya ko da safiya ta waye gaba ɗaya ya rafke ido sun faɗa sai karen hancishi da ya ƙara tsawo. Ranar Alhamis ɗin itace ranar da ta kama za'a yi mother's day wanda za'a yi a wani katafaren hall da aka Ƙawata, don Hajiya Mama ma da ita za'a je wannan bikin, shiyasa shiri ake ta ko'ina su Dije sai kaiwa da komowa ake yi anata zirga zirga, Safwan da ke ɗaki yanata kuncinshi ganin Hajiya Mama tana ta sabgar bikinta ko damuwa da ta jishi ma bata yi ba, duk da kuma ta ji shiru bata ganshi ba tun safe har azahar, ko abun break ɗin da aka kai masa ko taɓawa bai yi ba yana nan yanda aka kawo shi ajiye, cike da takaici ya fito ɗakinshi yana wani muzurai ya yafito Fiddo zata wuce, cikin sauri ta ƙaraso wajenshi tana faɗin "Big bros me ke damunka naga kamar ma baka da lafiya?" Ya wani basar da zancen yace "kice da yarinyar nan ta kawo mani tea zan fita yanzu kafin in dawo, sannan kayan break ɗin da ke ɗakina a kwashe su duka a fito da su" Yana ƙare faɗa ya juya Fiddo ta yi saurin faɗin "Big bros ko dai in haɗo maka da kaina ne? WALLAHi wannan yarinyar ba abunda ta iya sai shirme" Ba tare da ya juyo ba yace, "ki je ki sanar da ita" Fiddo ta yi wani yatsine ta ce, "Ni na rasa me ma ya janyo ka kwasowa kanka wannan ƴar dajin, haka kawai ta zo ta janyo maka hawan jini da ƙurciyarka, duk matan duniyar nan ka rasa macen aure sai ita don bala'i, da class ɗinka ka lalace a kanta wannan abun kunyar da me ya yi kama?, Mitssss!" Ta buga wani uban tsaki ta yi cikin gidan ranta a ɓace, maimakon ta sanarwa da Dijen saƙonshi ta yi wajen Hajiya Mama ta ce "Yau fa bros baya jin daɗi Hajiyarmu, yanzu haka break ɗin safe da aka kai masa yace a fito da shi bai taɓa ba, yanzu haka tea kawai yace a haɗo masa kafin ya dawo" Hajiya ta yi shiru sannan tace "to ki je ki cewa Khadijah ta haɗa masa ta kai masa ALLAH ya bashi lafiya" Tana ƙare faɗar hakan ta ci gaba da sabgoginta Fiddo ta fito cike da jin haushi ta nufi wurin Dijen tana sanar da ita, wai don ta cusa mata haushi ta ce da Surayya "Aunty Surry yau fa muna da babbar baƙuwa daga Gombe Amaryar yaya Safwan zata zo" Surayya ta kalli Dije da ke ƙoƙarin fita ɗakin ta janyo kunnen Fiddo tace,. "WALLAHi Hajiya Mama ta ji ki sai kin san baki ragawa kanki ba, ko ranar ba naji tana yi maki kashedi akan hakan ba?" Fiddo ta ɓata fuska tace, "to ni miye laifina a ciki don na taya yayana son abunda yake so?, Shikenan sai ace kowa baya son zaɓinshi sai wannan bagidajiyar?, Ku kanku ai kunsan cewa ba ajinshi bace amman kuka rufe gaskiya kuna goya mata baya" Surayya ta yi mata wani mere tace, "Ni rashin hankalinki Fiddo mamaki yake bani WALLAHi, shin da mu da shi wa ya kawo Khadijah gidan nan? Hajiya ko Ni? To ki buɗe kunnuwanki da kyau kiji da ace yaya Safwan baya sonta WALLAHi da ba zai taɓa amincewa ya aureta ba, saboda haka ki ajiye haukarki a gefe ki bar Mata da Mijinta su huta, saboda ke da kanki watarana zaki bada labarin irin son da yake yi mata WALLAHi, don ko wannan auren da yace zai yi, zai yi shi ne kawai amman ba wai don baya son khadija ba, kuma ma yanzu idan ba makiyin ALLAH ba wa zai ga khadija a yanzu yace bata dace da shi ba?" Fiddo ta yi saurin faɗin, "sai kuma ni nan don WALLAHi ko kaɗan ma ba mahaɗa don kinsan ya yi mata zarra sosai" Surry ta watsa mata wata harara tace, "to ai ki je kiyi ta yi kar ki fasa" Haka suka yi ta sa'insa a tsakaninsu har abun ya so ya zamar masu faɗa sai da ƴanmatan da ke ɗakin suka shiga tsakaninsu, Dije kam cike da faɗuwar gaba ta kammala haɗa masa komi a wani ƙaramin tire, ta nufi ɗakinshi gabanta sai faɗuwa yake yi sai dai ganin ɗakin ba kowa ne yasa hankalinta ya kwanta, ta yi saurin ajiyewa ta zo zata fita kenan ta ji ƙarar buɗewar toilet ɗinshi, ta yi saurin ficewa ya ɗaga murya a hankali yace "wannan kayan fa wa kika barwa su?" Dije ta dawo jikinta yana rawa ta ɗauki ƙaton tiren ta zo zata fita yace "Ki je ki dawo ina jiranki" Ta fice ko waigowa bata yi ba saboda tsananin tsoronshi da take ji, ya bi bayanta da kallo jiki a mace ya zauna ya yi tagumi yana nazarin abubuwan da suka sha masa kai a zuciya, yana nan zaune har ta dawo ya yi saurin cire tagumin ya kalleta sama da ƙasa ya maka mata harara tare da zaro ido yace "Ni kike so in zuba da kaina ko kuwa?" Dije da ke tsaye tana wasa da yatsunta ta yi saurin duƙawa ta ɗauki ƙaramin flaks ɗin ta fara tsiyaya masa tea ɗin cikin cup, ta miƙo masa ba tare da ta kalleshi ba jin shiru bai karɓa ba yasa ta ɗago kanta ta kalleshi, sai ko caraf ta yi arba da kallon da yake yiwa ƙirjinta da ya fito cikin wuyan rigarta ba tare da ta sani ba wajen ƙoƙarin zuba masa tea ɗin, ta yi saurin ajiye tean cikin firgici ta miƙe tsaye tana gyara zaman rigarta zata fice, caraf ya riƙo hannunta da jajayen idanuwanshi ya yi jarumtar faɗin "Magana zan yi da ke fa" Dije ta waigo cike da mamakin jin muryarshi a tausashe ta ƙwace hannunta tare da gyara tsayuwarta ta rungume hannuwa tana wani cin magani, cikin ko in kula ya ɗauki kofin tean ya kurɓa sannan ya ajiye ya kalleta yace "Zama zaki yi ba tsaye zaki yi man a kai ba" Dije ta zauna kan kujerar nesa kaɗan da shi ba tare da tace ƙanzil ba, ya maka mata wata harara yace "Au tsaranki ne ni kenan da zan zauna kan kujera ke ma ki zauna?" Dije ta yi kamar ba zata sauka ba cikin fushi ya ce "ba da ke nake magana ba ne?" Ta sauko da sauri tana gunguni ƙasa ƙasa ya bi bakinta da kallo tare da ƙara haɗe fuska yace,. "Ni kike zagi?" Ta yi saurin kallonshi ta murguɗa masa baki tace,. "Idan ba zaka faɗi maganarka ba ni tafiya zanyi" Ya yi mata wani kallo yace, "Ok to ko zaki gwada tafiyar ne?" Dije ta yi masa wani kallon reni duk da tana jin tsoronshi haka ta miƙe da nufin fitar, ya yi saurin miƙewa ya sawa ɗakin key ya zare ya ƙaraso gabanta ya tsaya yana zuƙar shayin yana kallonta har ya gama ya miƙa mata kofin ta ƙi karɓa, ya saka ƙafarshi ya take ƙafarta da ƙarfi tare da rungumota da hannu ɗaya ya matse mata gefen ciki da ƙarfi, sai gata da fasa wata ƙara saboda azabar da ta ziyarceta ba shiri, ta yi saurin karɓar kofin amman yaƙi bata damar ta ajiye kamar yanda yake so, cikin sigar mugunta ya saka ɗayan hannunshi ya ɗago fuskarta daf da tashi, yana ƙare mata kallon ido cikin ido sannan ya yi wani shu'umin murmushi yace "Ni zaki kawowa ƙananun rashin kunyar da kika saba yi ko? To wannan karon da kanki zaki gano cewa ni ba sa'ar wasarki bane, idan kin ajiye rashin mutuncin kin tsira don zaki taimaki kanki, idan kuma kika ce zaki yi jayayya da ni to ke ce a wahale" Dije ta yi saurin fisge kanta tana yi masa wani kallo ranta a matuƙar ɓace tace, "ba nace kada ka sake taɓa jikina ba ne? to WALLAHi wannan karon sai na faɗawa Hajiya duk abunda kake yi man" Safwan ya bita da wani guntun mere sannan ya fashe da wata munafukar dariya ya ce "to bari in baki saƙon idan kin je sai ki sanar da ita" Cikin mugunta ya fisgo kanta har ɗankwalinta ya faɗi gashinta da ke cikin ribom ya fito saboda faɗuwar da ribom ɗin ya yi, Safwan cikin fitar hayyaci ya damƙo gashin ya ɗago fuskarta tare da kai bakinshi cikin nata kamar wani maye, haka ya dinga tsotse leɓenta yana wata irin tsotsar fitar hankali tamkar wanda aka baiwa umurnin ya rabata da leɓunan duka, Dije tana zubar hawayen azaba tana dukanshi iya ƙarfinta amman hakan bai hanashi yin abunda yake yi ba, tun tana ɗaukar abun wasa har ta fara sarewa da lamarinshi,cikin zafin nana ta yi jarumtar turashi baya kasancewar gaba ɗaya a kasalance yake, hakan ya bata damar ƙwatar kanta tana kuka tana shafa leben da take tsammanin ma ya yi jini. Ganin babu jinin yasa ta kalleshi kallo mai cike da tsana tace, "WALLAHi wannan karon sai kasan ni kake ciwa amana" Cikin fushi ta nufi ƙofar ɗakin da nufin buɗewa ta tuno da cewa rufe yake, ta dawo gabanshi ta tsaya tana faɗin "ka buɗe man in fita tun kafin in tara maka jama'a WALLAHi" Safwan ya ɗago da jajayen idanuwanshi da suka so baiwa Dije tsoro cikin dakiya tace "Zaka buɗe ko kuwa har sai na yi maka abunda za'a kaika asibiti yanzun nan?" Ya yi guntun murmushi cikin wata siriryar murya yace "To ki jira inyi abunda ko da kin yi nasarar kaini Asibitin ba zan ji haushin jinyar ba saboda na fanshe haushina" Ya nufo kanta ta yi baya cikin tsananin tsoro amman bai fasa nufota ba ganin da gaske yake yi wata cutar zai sake yi mata yasa ta maƙe jikin bango tana faɗin "Don Allah Malam ka yi haƙuri WALLAHi bana son abunda kake yi man ka ji tsoron ALLAh kada ya kamaka da laifin cin amanar iyayena da kake son yi" Safwan bai fasa zuwa wurinta ba asali ma hannunshi duka biyu ya saka ya rungumota tare da shafo dukiyar fulaninta, a ɗimauce ya zuge mata zif ya dinga wasa da su son ranshi, Dije kam gaba ɗaya wani masifar tsoro ne ya sake ziyartarta tare da azabar da take ji, Malam Safwanu kam ganin tsoro akan fuskarta yasa ya daina ƙawata son zuciyarshi da laushin fatarta, ya shafo himilin gashinta ya ɗora kanshi saman kanta ya shaƙo ƙamshin mayukan da aka shafe gashin da shi, ba shiri ya lumshe idonshi tare da ƙara ƙankameta jikinshi ya sauke wata ajiyar zuciya, Dije kam saboda kukan da ya ci ƙarfinta kasa ƙwatar kanta ta yi, ƙarshe ma sulalewa ta yi ƙasa ta durƙushe tana wani irin kuka gwanin ban tausayi, saboda ganin take yi ba ƙaramin saɓon Allah bane Safwan yake aikatawa, ya yi saurin durƙusowa gabanta yana ƙare mata kallo zuciyarshi cike da jin haushin kanshi, amman cikin dakiya ya haɗe fuska yace "Zaki yi wa mutane shiru ko kuwa sai kin janyo na lallasaki yanzun nan?, To bari kiji kinga wannan abun da na yi maki WALLAHI ubanshi zanyi matuƙar Matar da zan aure ta zo gidan nan kika yi mata rashin kunya, ko kuma kika nuna cewa ma wai kin sanni a gabanta, don ko da wasa kika nuna cewa akwai wata alaƙa tsakanina da ke sai kinsan kin aikata hakan, ke ko da ma ace kinji an faɗa a gabanki to kiyi gaggawar ƙaryata hakan gareta, idan ba haka ba WALLAHi abunda zan yi maki sai ya fi wannan muni, idan kuma kina ganin zancena faɗa ne kawai to ki fallasa wannan sirrin ina jiranki" Yana ƙare faɗar maganar ya buɗe ɗakin ya fice zuciyarshi fes yake ji tamkar an sauke masa wani ƙaton ɗutsi a saman kai, don yasan tsoron da ya baiwa Dijen ba zai bari ta yi masa wani shirme ba idan Zee ta zo, don daman fargabarshi ɗaya ita don yasanta sarai da salon rashin kunyarta tsaf zata yanyo kwaɓarshi ta yi ruwa. Tsabar takaicin abunda ya yi mata ne yasa ta kasa barin ɗakin, ta ci gaba da kukanta sannan daga baya ta lallashi kanta ta yi ƙoƙarin saita kanta ta kimtsa jikinta ta fito ɗakin, tamkar wadda ƙwai ya fashewa a ciki ta yi sashen masu aiki don bata so Hajiya ko wani ya tambayeta me ta yi wa kuka, don bata san da wane ido zata kallesu ta sanar da su irin cin mutuncin da Safwan ɗin ya yi wa addini ba. Ko da ƙarfe huɗu tayi mutane da yawa sun fara shirin zuwa mother's day, don Safwan kanshi ma ya shirye tsaf sai tashin ƙamshi yake yi saboda murnar zuwan Zee da ke kan hanyar gidan ita da ƙawarta Ruma, da kanshi ya je ya sanarwa Hajiya zai je ya taro su Zee kada ta fita zai je ya kawosu gidan su gaisa kafin su wuce wajen event ɗin, cike da walwala ta nuna masa farin cikinta don ta nuna masa bata da mu ba, duk da cikin zuciyarta cike take fam da takaicin rashin sanin ciyon kanshi da bai yi ba, sai dai kuma idan ta tuna yanda yanzu yake ta nuna kulawarshi akan Dijen sai ta gode wa ALLAH saboda ganin addu'arta ta fara karɓuwa. Dije kam ta shirya tsaf cikin ƴanmata sai tashin ƙamshi take yi duk da kasancewar zuciyarta ba daɗi, amman hakan bai hanata tsara shigarta irinta wayayyun ƴan boko ba, don kuwa takanas Surayya ta ce da mai mata kwalliya ta gyara Dijen tamkar yanda zata gyarata, saboda tana son Zee ɗin ta gano itama Dijen ba baya ba ce don kar ta Renata, cikin ikon Allah ko sai ga Dije ta fito ras da ita tamkar ka saceta ka tsere don kyau, ga doguwar rigar fitted gawn ce ta Kama jikinta sosai ko'ina ya fito tsantsan, musamman hips ɗinta da ƙirjinta da suka fito raɗam a cikin rigar, idan baka sani ba zaka ɗauka cewa ma itace Amaryar, don komi irin na Amare aka yi mata har ɗaurin head ɗin da aka yi mata ma wani style ne a saman kanta, aiko Dije sai jinta take yi wata higher class tamkar ba ƴar secondary ba, saboda a lokacin tana da shekara sha shida amman yanayinta zai sa ka ga tamkar tafi hakan saboda tsabar kauɗinta. Hajiya Mama kanta da ta ganta ba ƙaramin daɗi ta ji ba a ranta ku ta yaba kwalliyar sosai. Motocin suka fara kwasar mutane zuwa wajen da za'a yi bikin, manyan mata hamshaƙai haka suka yi ta shigowa gidan da motocinsu suna gaisawa da Hajiyar suna wucewa wajen da za'a yi taron, gidan ya rage ba wasu mutane da yawa sai Amarya da ƙawayenta a falo sunata shirinsu ana ƙara gyara amaryar. Sai ga Safwan da Zee'nshi tare da ƙawarta sun yi sallama sun shigo, Fiddo ta yi wani tsallen jin daɗi ta nufesu tana faɗin "Oyoyo Auntynmu" Kasancewar tasanta a hoto yasa ta je wajenta ta rungumeta, Dije tana ganinsu wani faɗuwar gaba ya ziyarceta, kai tsaye wata dubara ta zo mata don ta tabbatar da lalle itace budurwarshi da yake yi mata kashedi akanta baya son tasan tsakaninsu, ta yi wani murmushin mai cike da ma'anoni ta taso tana wani taku cikin wani salo ta sha gabansu duka ta tsaya, tana yi wa Safwan wani shu'umin kallon cikin shagwaɓa tace "Haba Husby Ina ta jiranka ka zo ka ga kwalliyata tun kafin ta goge shine sai yanzu ka dawo gidan" Ta jujjuya gaba da baya sannan ta tako gabanshi ta ɗora hannunta ɗaya a kafaɗarshi duk da ya fita tsawo sosai, ta shafo fuskarshi da ɗaya hannun ta yi fari da ido tace,. "To yanzu ya ka ganni na yi kyau ko kuwa da wani gyara in je in gyara?" Cikin tashin hankali Zee ta kalleshi cikin hargitsewar tunani, nan take wani jiri ya kwasheta ta yi baya ba shiri ƙawarta ta yi saurin riƙota tare da yi mata kashedi da ido, amman duk da hakan ta kasa natsuwar da ƙawarta take so ta yi saboda masifar kishinshi da ya rufeta, don son Safwan da kishinshi a jininta yake ko da basu tare bale yanzu da aka janyo zuwanshi ta ƙarfin tsiya. Ina team Zee ku zo ku riƙe Zee don kar ta faɗi yasin ni dai na yi nan babu ruwana🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️😝 *Hmmmm! Rashin COMMENTS zai janyo fushin Alƙalamina, da ya ɗauke yasin zaku jini ɗif kamar an ɗauke wuta😚, idan banga sauyi ba daga yau zan shiga hutun sabuwar Shekara😼* Akafta🤣 D/AUTA Ce✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *Lalle yau kwalliya ta biya kuɗin sabulu💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 yasin yau kun faranta man fiye da tunaninku🥰 don haka ga nawa tukuici nan gareku masoya Dije Ƙarangiya all, ku ma ku ji daɗi kamar yanda na ji, ku daɗe ku yi lasting mutanena gaba ɗayanku ina yinku sosai ba shakka👍🏻* *Lamba ta 46* Safwan mamaki da al'ajabin da ta bashi ne yasashi daskarewa ko motsi ya kasa yi bale ya yi wani yunƙurin kare kanshi, illah kallon Zee da yake yi yana girgiza kai, ganin hakan yasa Fiddo ta yi saurin riƙo hannun Zee tace "Zo mu je ciki ku gaisa da Hajiyarmu Aunty, wannan da kike gani ba kowa ba ce face ƙaskantacciyar ƴar aikinmu, dubarta da kyau ki gani bagidajiya ce usuli ƴar ƙauyen ƙayau, ta nace akan dole sai yaya Safwan ya aureta bayan kuma shi ko kaɗan baya sonta" Ta janyo hannun Zee ta yi wa Dije wani kallo ta buga mata ƙaton tsaki tace, " mtsss! Mayya kawai" Zee tana yi tana waigenshi zuciyarta cike da ƙunar baƙin cikin da Dije ta sakar mata, sai wassafa yanda zata shaƙe Dijen take yi a ranta har sai ta ɗauke numfashi sannan ta saketa, har suka isa ɗakin Hajiyar suka zauna bata san ma sun je ba, sai da ta ji Fiddo tana gabatar da ita ga wata Auntynsu sannan ta dawo hankalinta ta fara sunne kai tana gayar da su. Safwan kam shigewar su Zee ciki yayi dai dai da dawowar natsuwarshi, ya kai kallonshi ga inda yake tsammanin ganin Dijen sai dai kuma wayam bata nan, ya wara idanuwanshi a masifance domin ya hango ta ina zai ganta ya sauke fushinshi akanta, sai dai kuma bata ba dalilinta a falon duka, a harzuƙe ya yi wurin Surayya yace "Ina magen yarinyar cen ta tafi???" Sury cikin firgici tace "WALLAHi Ni ma bansan inda ta je ba yayanmu" Safwan ya kaiwa iska duka sannan ya bar wajen ya sake dawowa ya ce da ita, "to ki yi gaggawar dubo man ita yanzun nan idan ba haka ba WALLAHi yau daga ke har ita sai kun san dani kuke zance" Cikin rawar jiki Surry ta miƙe ta yi ɗakinsu domin ta gani Dijen tana cen ko kuwa, sai dai ta duba ko'ina Dijen bata gidan take ta sanar da shi yana huci ya yi wurin Hajiya, sai dai tuno ɗakin da mutane yasa ya ja ribas dole tare da furzo iska mai zafi a bakinshi yana wani bubbuga kanshi alamun ta saka shi a tension da yawa. Yana nan tsaye sai ga Fiddo ta fito tare da su Zee tana ganinshi ta yi saurin zuwa wurinshi tace, "big bros WALLAHi yau idan ka kama yarinyar nan ka ci ubanta da kyau da kyau, don ni kaina yau sai na tayaka mun ci uban shegiya......" Kallon da Safwan ɗin ya yi mata ne yasa ta yi saurin cewa da su Zee "Aunty ku zo mu je ku ci abincin kafin mu je wajen da za'a yi event ɗin" Zee ta yatsina fuska ta kalli Safwan tace, "Barshi kawai Ƙanwata ni yanzu ma zamu koma gida" Safwan ya yi saurin zaro ido cikin wani sabon tashin hankali ya marairece fuska yace, "Sorry Unique ke ma kinsan ke ce dream ɗina safe da rana, ke ce wadda nike mafalkin aure a kowane lokaci, wannan yarinyar ba kowa ba ce a wurinmu face ƴar aiki kamar yanda kika ji Fiddo ta sanar da ke tun farko" Zee ta yi masa wani arnen kallo mai cike da ma'anoni sannan ta nufi hanyar fita ƙawarta ta riƙo hannunta, cikin wayancewa ta ce da Fiddo mu je ki kaimu wajen da za'a yi bikin, Fiddo cike da damuwa ta ce "to ku yi haƙuri ku ci abincin mana kunga kun kwaso tafiya ga shi ko ruwa ma baku sha ba" Ƙawarta Ruma ta yi murmushi ta ce "ok to mu je mu ɗin ai sai mu yi sauri mu kammala" Fiddo cike da jin daɗi ta kai su ɗakinsu da ta riga da ta shirya shi tsaf saboda tarbonsu, ta nuna masu toilet sannan ta fito zuwa kwaso masu kayan abincin, Safwan da ke tsaye jiki ba kuzari damuwa fal ranshi yace "Zo nan ki ji" Fiddo ta ƙaraso wajenshi cikin sassauta murya yace,. "Don Allah ki yi duk yanda zaki yi ki nuna mata cewa ba wani abu tsakaninmu da yarinyar cen, don WALLAHi idan bata amince ba yau sai na ci uban yarinyar nan a gidan nan" Hajiya da ke bayansu cikin shirinta na fita zuwa bikin ta ce, "Wa za'a ci wa Uba kuma a gidan nan yau?" Safwan ya gyara tsayuwarshi tare da sosai kai yace, "Wata ce Hajiyarmu" Hajiya ta ce "ALLAH ya taimakeka to tunda ba Khadijah kake nufi ba don WALLAHi idan har da ita kake ka kuskura naji ka daketa akan wata sai na baka mamaki" Tana ƙare faɗar haka ta sa kai ta tafiyarta, Safwan da Fiddo suka bita da kallo har ta wuce, sannan ya nufi ɗakinsu Fiddon ranshi a matuƙar ɓace saboda jin haushin taka masa burkin da Hajiya Mama take yi akan Dije. Yana shiga ya taradda Zee dunƙule tana kuka ƙawarta tana lallashinta tana bata baki, tana ganinshi ta yi saurin zuwa ta cakumo rigarshi cikin kuka tace "Daman abunda ka shirya man kenan Shiyasa ka matsa akan in zo bikin ƙanwarka??, To na zo na gani tabbas kana da matar da zaka aura ƴar Uwarka ALLAH ya baku zaman lafiya Ni na haƙura na bar mata ALLAH ya bani dangana, amman ka sani sonka shine ajalina idan ka ji saƙon mutuwa to shine sila" Safwan ya dafe goshinshi cike da wani takaici da ruɗewa yace, "ki yi haƙuri my fiance na gaya maki yar aikin gidan nan ce, tukunna ma ina wadda na taɓa sanar da ke an so a haɗamu aure da ita to ai itace wannan" Ta yi masa wani kallo mai cike da tuhuma tace, "eh kam lalle yar uwar taku ce yanzu ta zama yar aikin naku ko? Hmm! To bari ka ji bazan ja abun da tsauri ba na haƙura na bar mata kai kawai" Tana ƙare faɗar maganar ta fisgo gyalenta da ƙarfi zata fita ya yi saurin riƙo hannunta cikin damuwa yace "plsss Zee ki fahimceni mana, wallahil'azim a shirye nike da in aureki a kowane lokaci, ki bani dama domin in tabbatar maki da hakan idan kin aminta yanzu ma kafin mu koma ayi auren kawai mu tafi abun mu cen mu zauna idan kinsan hakan zai kwantar maki da hankali" Zee ta kalleshi zuciyarta cike da jin daɗi tace, "promise?".. Yace "promise" Sannan ta rufe fuskarta tana dariyar jin daɗi, Safwan ma ba shiri ya mayar mata da martanin dariyarta zuciyarshi fess saboda ganin ya tufke abunda Dije ta warware masa. Fiddo ta shigo ta ajiye kayan abincin tana wasar bakin jin daɗin ganin Zee ta washe tace, "masha ALLAH Auntynmu har naji daɗi da kika saki fuskarki, yayanmu ba shi da wata matar da zai aura a yanzu face ke, don wannan munafukar yarinyar da kika gani itace take sonshi sai dai shi ko kaɗan ba ya sonta, ta yi masa haka ne a gabanki don kawai ta haɗaku faɗa, daman gurinta bai wuce ki yi zuciya ki bar mata big bros, to don ALLAh Auntynmu ki bata kunya kada ki bari ta rabaki da yayanmu kinji" Zee ta washe baki tace, "na gode ƙanwata ina jin daɗin yanda kike sona ke da yayanki, kuma insha ALLAHu bazan taɓa nuna damuwata akan wani abu da zata sake yi ba, matuƙar ba my soul ne ya nuna kulawarshi akanta ba, to agaskiya anan kam bazan taɓa jura ba don Ina kishin inga wata mace ta raɓeshi bayan ni WALLAHi" Fiddo ta fara zuba masu abincin tace, ",kwantar da hankalinki don ba ma zai kulatan ba saboda daman cen itace kawai da baƙin nacinta" Haka dai Fiddo ta yi ta basu kulawa tana wanke zuciyar Zee daga tsatsar da Dije ta sakawa ruhinta, har suka ƙare komi cikin kulawar Fiddo sannan suka ajiye motarta da suka zo da ita Safwan ya ɗaukesu suka tafi bikin. Shigarsu hall ɗin ke da wuya Safwan ya hango Dije tsakiyar fili tana ta cashewa abunta, zuciyarshi a take ta zo wuya saboda ganin yanda ƙaton hall ɗin ya cika ya batse tsakanin maza da mata. Fiddo ta wuce da su Zee tana ta gabatar da ita ga ƴan'uwa da abokan arziƙi, sai dai abinda bata sani ba mutanen da yawa wadañda basu san da zancen auren ba sunyi mamakin auren da Safwan ɗin zai sake yi, bayan ga Dije dake hannun Hajiya kuma itama tana amsa sunan Matarshi. Safwan kam cikin dubara ya fice ya sa wata ƙawar Surayya ta kira masa Dijen, sai dai cikin rashin Sa'a Dijen ta ƙi biyo ƙawar Surryn saboda gargaɗin da Hajiya ta yi mata akan kada ta biyewa Safwan ɗin ya daketa a banza, ƙiri ƙiri tace da ƙawar Surryn Hajiya tace kada ta fita ko'ina, dole haka ƙawar taje ta sanar da shi, aiko ya ƙara hawa akan fushin da Dijen ta saka shi, ya yi ƙwafa ya koma hall ɗin Sai dai rawar da ya ga tana ta cisga ne yasa shi dafe goshinshi ba shiri, ranshi a ɓace ya kasa haƙuri ya nufi wurinta gadan gadan da nufin kai mata wani bahagon mari, tana hangoshi ta yi saurin ficewa filin ta nufi wurin Hajiyar tana haki, ya wayance ya fara zubawa Surry likin kuɗi daga nan ƴan'uwa suka cika filin suna yi masa liƙi yana yi masu shi ma, ta ko'ina sai zubo kuɗi ake yi har sai da mc ya bada umurnin kowa ya koma ya zauna abar Amarya kawai a tsakar fili. Ganin hakan ya baiwa Zee damar fitowa ita da ƙawarta suka fara watsawa Surry farfaru bugun Abuja, Hajiya Mama ta ciro kuɗi a jakarta ta miƙa wa Dije tace itama ta je ta watsa, cikin jin daɗi ta karɓa ta isa wurin ta fara mannawa Surryn kuɗin sannan ta dawo tana mannawa Zee cikin murya ƙasa ƙasa tace "Da kin daina wannan zaƙewa tunda dai har yanzu baki riga da kin shigo familyn ba, amman kuma ba komi a hakan ma muna godiya, sai dai kuma ga shawara ki adana sauran kuɗinki don rabawa malamai su ji daɗin yi maki addu'ar ƙwato zuciyar wanda ake yi dominshi" Saboda salon yaudara irin na Dije tana liƙa mata kuɗin fuskarta a sake take maganar, wanda bai ji ba ba zai taɓa fahimtar cewa wai wata baƙar magana ce take faɗa mata ba, don shi kanshi Safwan ɗin ya yi mamakin ganin Dijen tana wasar baki ga Zee, uwa uba ma har da su watsa kuɗi don a ɗauka cewa bata san zafin kishi ba. Har aka watse taron Zee maganganun Dije suna yawo cikin kwanyar kanta, sai dai idan ta tuno da zancen aurensu da Safwan ɗin da ya zo mata da shi sai ta ji wani sassafci a ranta, duk da tasan cewa itama za'a sha fama da ita kafin a janye zancen auren wani da ke kanta. Dije kam har aka shiga bacci bata bari sun haɗu da Safwan ba, saboda ma tunda ya fita raka Zee gidan ƴan'uwasu da suka sauka a cen, bai dawo gidan ba har sai da dare ya tsala sannan ya dawo ya shige zuciyarshi cike da jin daɗin shima ya kusa angwancewa, sai dai wani sashe na zuciyarshi yana ingizashi akan ya koyawa Dije hankali kafin ya bar garin, amman yana jin tsoron abunda zai janyowa kanshi wajen Hajiya Mama. Ranar juma'a ranar ce ta kama ta ɗaurin aure kuma ayi walima, haka ranar ce kuma Malam Lawi ya diro garin tare da wani abokinsu da ke cen Gomben, saboda gayyatar da Safwan ɗin ya yi masu, cike da jin daɗin gani junansu kowa yake ta ɗokin ɗan'uwanshi, sai firar yaushe gamo ta ɓarke a tsakaninsu ihunsu kawai ke tashi a ƙofar gidan bayan sun dawo ɗaurin auren. Kasancewar a harabar filin gidan ne za'a yi walima shiyasa aka kafa rumfuna manya manya aka ƙawataa wurin sosai. Dije ta fito zata je cen wajen ne idonta ya kai kan malam Lawi, cikin sauri ta zaro ido cike da jin daɗin ganinshi ta nufi wajensu fuskarta a washe take faɗin "Rai kan ga rai Malam? ashe ina da rabon sake ganinka a duniya?" Lawi cike da mamaki ya bi ta da kallo tun daga sama har ƙasa saboda ganin yanda gaba ɗaya ta sauya kamannu kamar ba Dijen da ya sani ba, wadda ko a mafalki da siffarta ta ƙauye yake hangota, sai dai kasancewar yasan cewa da da yanzu ba ɗaya ba ne, saboda yanzu igiyoyin aure sun yi masa shamaki da ita, auren ma na Abokinshi Safwan, shiyasa ya wani basar ba tare da wani sakin jiki ba ya ce "Amarya kinsha ƙamshi ya garin? da fatar kina lafiya?" Dije ta washe baki cike da jin nauyinshi tace, "Malam saukar yaushe haka babu sanarwa?" Lawi ya kalli Safwan ya ga yanda gaba ɗaya yanayinshi ya canza ya yi gajeren murmushi yace, "wannan kuma laifin angonki ne tunda shine bai sanar da ke ba" Dije ta kai kallonta gareshi ta yi ɗan murmushin yaƙe sannan ta ce "Bari in je in dawo Malam ai da nasan kana nan da tun ɗazu ka sha tarbata" Lawi ya bita da kallo yana wani murmushi cen kuma me ya tuna ya yi saurin kawar da kanshi a gefe yana wassafa siffarta cikin bular doguwar rigar da ke jikinta, ta yi mata kyau ɗagwasgwas ta zauna a jikinta, ga ɗankwalin rigar da ta yafo gaban kanta gaba ɗaya a buɗe yake har ana hango kwantaccen gashin kanta da yasha gyara ya kwana, ga sajen gashin ma ya kwanta luf luf a gefe da gefen fuskarta, girarta ma cike tafi da gashi gazar gazar da ta ƙara Ƙawata mata fuskar, duk da bata yi wata doguwar kwalliya ba amman yanayin tsarin shigarta ta burgeta sosai. Daga shi har Safwan sun faɗa tunanin da su kaɗai suka san me suke tunawa, tunaninsu ya katse ne lokacin da Dijen ta dawo tana murmushi tace "Malam zo mu je falon baƙi ka ci abinci ko?" Abokinsu da suka zo tare da Lawin ya kalli Dije cikin murmushi yace, "Au Wai abun ƴar wariya ce daman?" Dije ta waigo tana dariya tace, "yi haƙuri idona ne suka rufe ruf WALLAHi a duk wurin bana hangen kowa sai malamina kawai" Ba Safwan da maganar ta daka a ƙirji ba har shi kanshi Lawin ba shiri ya waigo, saboda maganarta ba ƙaramin dukan zuciyarshi ta yi ba. To fa wata sabuwa 😝 Akafta😅 D/AUTA Ce✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *My fans bakina ba zai iya misalta farin cikin da kuka sakani ba, naso in zayyano sunayenku to amman yawanku ya kai ba zan iya lissafoku duka ba, amman na gode 🙏🏻na gode🙏🏻 sosai Alkhairin ALLAH ya kai maku duk inda kuke💃🏻ku daɗe ku yi ƙarko mutanena👍🏻* *Lamba ta 47* A harzuƙe ya taso da nufin kai mata duka sai ga motarsu Zee ta kunno kai harabar gidan, cikin sauri ya nufi motar yana washe baki saboda jin daɗin ganinta, Dije ta kai kallonta gareta take wani ɓacin rai ya ziyartota, amman a hakan ta kalli Lawi ta yi wani murumushi tace "Zo mu je Malam" Lawi ya yi shiru sannan yace da abokin nasu mai suna Kamal yace, "zo mu je Abokina don wannan tafiyar dole ne a buƙaci rakiyarka" Kamal kam sai kallon motarsu Zee yake yi mamaki fal ranshi yace da Lawi, "Abokina baka gane wannan yarinyar ba ne?" Lawi ya kai kallonshi ga motar inda Safwan da Zee suke tsaye jikin motar suna fira kowanensu cikin farin cikin ganin ɗan'uwanshi, Lawi yace "Kai ne idon gari Abokina ban gane su ba gaskiya" Kamal ya ce, "budurwar Aminu ce fa wadda ya susuce kanta kullum yana dakon ta kammala karatun da take yi ayi auren amman Mahaifinta sai ja masa rai yake yi, ko kallon zumuncin da ke tsakaninsu ba ya yi, ya fifita son zuciyar ƴarshi akan na kowa" Lawi yace, "Eh kam sai yanzu na tuna amman kasan ni daman bansan yarinyar ba ai labarinta kawai nake ji" Dije tana tsaye tana saurarensu ba tare da ta ma nuna tasan wani abu da ke faruwa ba, cikin dariyar yaƙe tace "Ai kam dai yanzu sai dai Aminu ya yi haƙuri saboda ita ce matar da Malam Safwan zai aura tare suke karatu a cen ƙasar wajen" Daga Lawi har Kamal suka zaro ido cike da mamakin jin wannan zance a bakin Dije, haka kawai Lawi ya tsinci kanshi da cewa "To ke har kin amince kenan?" Dije ta yi shiru tana yar dariya mai cike da takaicin da ke cin zuciyarta tace, "ku zo mu je mu barshi ya ji daɗin firar don kada mu takurashi" Suka wuce Safwan da hankalinshi gaba ɗaya yana kansu saboda tsabar kishin da ke cin zuciyarshi, ya bisu da kallo ranshi a matuƙar ɓace yace da Zee "Zo mu shiga ciki ku gaisa da Hajiya" Zee ta bishi da kallon mamakin me ke damunshi tace, "my man what's wrong with you?? Ko na yi maka wani abu ne?" Safwan cike da ƙunar rai ya shafo kanshi ya ce "No! no! kada kiji komi mu je kawai" Yayi gaba Zee ta bishi da kallo ƙawarta ta riƙo hannunta suka shiga cikin gidan, suna shiga suka yi kiciɓis da Fiddo ya ce da ita ta kaisu wajen Hajiyar idan sun gaisa abasu muhalli a wajen walimar, sannan ya barosu ya nufi ɗakin baƙin da zuciyarshi take ta azalzalarsa akan ya je ya ga wace irin wainar ce ake toyawa, ai kuwa sai ko ya taradda Dijen ta gama zuzzuba masu abincin tana miƙawa Lawi lemun da ta zuba masa a cup, daga ita har shi murmushi ne kwance a kan fuskarsu, idonshi a rufe yana zuwa bai wata wata ba ya fella mata wani wahalallen mari har sai da ta saki cup ɗin saboda tsabar tsoronshi da kuma azabar da ta ziyarceta, cikin wani masifar ƙarfi ya fisgo hannunta suka fice Kamal da Lawi suka bisu da kallo, cikin tsananin ɓacin rai Lawi ya dafe kanshi zuciyarshi sai tafasa take yi saboda zafin marin da Safwan ya yiwa Dije ya ji shi har cikin ranshi. Kamal ya kalli Lawi yace, "wai wannan guy ɗin mi ke damun ƙwaƙwalwarshi ne?, Ko da yake banga laifinshi ba fa don ko ni nan ina da irin wannan mata WALLAHi dole ne na yi kishinta, amman kuma yasan yana sonta zai tsirowa kanshi auren Zee da rana tsaka?" Lawi ya yi shiru saboda ɓacin ran da yake ji yasa ya ma kasa furta wata kalma a bakinshi, sai shafa ɗan ƙaramin gemunshi da yake yi yana nazari. Safwan kam bai zame ko'ina ba sai ɗakinshi da Dijen, yana shiga ya saka key tare da wurgar da ita a tsakiyar falon yana ƙare mata kallo yana nazarin ma wane hukunci zai yanke mata don ya ji sauƙin abunda ke azalzalar zuciyarshi, cikin takaici ya cakumo gashinta da ƙarfi ya miƙar da ita tsaye, cikin jin zafin da ke ratsa kanta tace "Don Allah ka yi haƙuri WALLAHi bazan sake ba" Safwan ya turata baya da ƙarfi ta yi taga taga zata faɗi kuma ya yi saurin riƙota cikin fushi yace "Kasheni kike so ki yi ne ko kuwa?, Me na yi maki Kika zaɓi ki tozartani cikin mutane?, To WALLAHi tunda har ke baki san darajar aure ba zaki janyo in fiddaki Makarantar da kike kwaɗayi gaba ɗaya, don na fahimci duk wannan rawar kan naki don kin ga an baki damar yin karatun ne, to daga yanzu ba zaki sake zuwa wata makaranta ba da sunan karatu idan ba islamiya, ita ɗin ma anan gidan za'a zo a dinga koyar dake saboda kawai ki san muhimmancin auren da ke kanki" Dije ta kalleshi ido cikin ido tace,. "Wane aure naji kana faɗa ne? Auren da kai da bakinka ka ce da ni kada in yarda cewa wani yasan kai ne mijina? To Ni yanzu WALLAHi na gaji da wannan wahalallen auren, tunda mai sona tsakani da ALLAH ya bayyana ka barni kawai in auri wanda ya soni tun kafin ka aureni, don ni shi Nike so........." Wani marin da ya kaiwa bakinta ne yasa ta yi saurin dafe bakinta tana zubar ƙwallah tace, "ko zaka kasheni ba zan fasa faɗar cewa ina son Malam Lawi ba tunda har kai bakasan darajata ba, shi nake so kuma shi nake da gurin zaman aure da shi idan ba haka ba kuma WALLAHi zan koma garinmu gaba ɗaya na haƙura da makarantar bana so" Ta ƙare faɗar maganar cikin kuka ta durƙushe tana gunjin i kukanta gwanin ban tausayi, cikin wani sabon tashin hankali ya yi durƙuso gabanta har ya so ya shafo kanta, me ya tuna kuma ya yi saurin miƙewa tsaye yace "Da ace zai amince ya karɓekin da nafi kowa farin ciki, to amman yanzu haka ko da kuɗi aka bashi ke bazai taɓa karɓar ki ba, ko ni nan don Allah ya ƙaddaro da zaki zama matata da ke kinsan baki kai matsayin wadda zan iya rayuwar aure da ita ba, nasan ba abinda ke damun zuciyarki a yanzu face kishi ko? to ki kwantar da hankalinki da anyi aurenmu da Matata Zee zamu bar maki ƙasar gaba ɗaya sai ki ji daɗin karatun naki" Dije ta miƙe tsaye hawaye shaɓe shaɓe akan fuskarta tace "Ai Ni ma kasan ba roƙarka na yi nace sai ka aureni dole ba, saboda haka ka barni da shi ka ga idan har bai aurenin ba.." . Ya kaiwa bakinta duka yace, "WALLAHi na ji kin sake zancen wani da aurena akanki sai kin gano baki da wayo, wai me kike taƙama da shi ne ba budurci ba? to zan karɓe shi yanzun nan inga ta yiwa mutane wata firiritar tsiya" Ya fisgota da ƙarfi ta faɗa jikinshi ta fara tirjiya amman hakan bai hanashi cire doguwar rigar da ke jikinta ba, surar jikinta tasa ya ƙara ɗimaucewa a HAUKACE ya fara yamutsata son ranshi, Dije ta na ƙoƙarin kare kanta wajen kai masa duka shi ko yana cen duniyar tsimuwa da muguwar guguwar sha'awarta,don kuwa gaba ɗaya ya susuce sai wasa yake yi da jikinta ta ko'ina yana sauke wani nishin mai bayyana tsantsar kiɗimewarshi akanta, ganin da gaske yake yi zai ci amanarta ta dinga rarumo abubuwa tana kai masa duka da shi, ya yi nasarar rabata da komi na jikinta sannan ya wurgata kan gadonshi, Dije ta firgice iya firgici ta fara ihun neman taimako amman bai ji kunyar rufe bakinshi da nata ba cikin mayen bala'in wutar sha'awarta da ke fisgarshi, cikin dubara ya fara aika mata saƙon da ya fara cin galabarta, ganin haka yasa ya dinga yamutsata iya son ranshi yana wani gurnani tamkar wani ƙaton rago. Dije ta kasa jurewa ta firgice masa da kalar tata haukar, cikin nasara ta kai hannunta ga laptop ɗinshi dake gefen gadon ta ɗaga ta kwaɗa masa ita a kai, ba shiri ya saketa dafe da kanshi yana faɗin "La la la ni zaki yi wa rotse?" Dije ta sauko jikinta yana rawa ta mayar da doguwar rigarta ta buɗe ɗakin ta fice aguje, Safwan ya bita da kallon mugunta yana dariya a ranshi yace "Komi wayon Amarya....." Da ƙyar ya samu ya yi control ɗin kanshi ta hanyar kora kwayuj magungunanshi da ruwa sannan ya dinga sakarwa kanshi ruwa har da ya ji zuciyarshi ta yi sassauci sosai akan damuwar da take ciki, sannan ya yi wanka a gurguje ya fito ya nufi inda su Lawi, don lokacin ma har an fara walimar sautin wa'azin malamar da ke yi wa Amarya huɗuba duk ya karaɗe gidan. Yanayin da ya taradda Lawin ne yasashi saurin washe baki yace, "Abokina ya dai ko har ka fara kewar gida ne?" Lawi ya yi masa wani kallo sannan ya gyara zamanshi yace, "banji daɗin dukan khadija da ka yi ba gaskiya, yakamata ka fahimci cewa mata suna da wata darajar da duk namijin kirki ba zai taɓa iya ɗaya hannu ya dakesu ba, ka tuna kar garin nan bata da kowa sai kai shin kasan ba zaka riƙe ƴar mutane amana ba me yasa ka aurota??" Baki sake Safwan yake kallon Lawin cikin mamakin titsiyen da yake son yi masa yace "ka ga malam wannan kuma ba abinda ya shafe ka bane, Khadija Matata ce ina da ikon da zan yi mata koma mine don haka don ALLAH ka daina saka man ido akan duk wani abu da aka ga nayi" Lawi ya sauke ajiyar zuciya yace, "idan kasan ba zaka riƙe masu ƴa tsakani da ALLAH to ka mayar da ita gaban iyayenta yafi da ka kawota nan ka ajiye kana dukanta, don WALLAHi matuƙar baka daina ba da kaina zan je garinsu in sanarwa iyayenta irin abinda kake yi mata, sannan wannan auren da naji wai zaka sake yi to idan baka ajiye wannan shirme ba tabbas Ni kuma a shirye nike karɓar Khadija a hannunka ko ta halin ƙaƙa" To fa tsugunne bata ƙare ba kenan🙀😢shin Lawi ko Safwan ina team Dije ku fito ku afafata🤪 Akafta😍 D/AUTA Ce✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *Ina yabawa ƙoƙarinku COMMENTERS😉* *Lamba ta 48* Safwan ya bishi da wani malalacin kallo yace, "idan har ka ga ka sami damar auren khadija a dai nan wannan duniyar da muke ciki to ka ɗauka cewa bana numfashi ne a doron duniyar, sai ka jira idan har na mutun sai ka yi murna ka garzayo ka auretan, amman yanzu kam WALLAHi bazan taɓa baka damar mallakar macen da na fi so fiye da kowace mace da zan aura ba duniya, kar ka ɗauka cewa wai ka fini sonta to WALLAHi kashi ɗaya cikin goman da nake mata to ko rabi ba zaka kwasa ba, amman bazan taɓa ɗaga mata ƙafa ba matuƙar ta yi man abunda bai gamsheni ba, saboda haka ka kawar da kanka akan matata ka yi gaggawar fito da taka matar don wannan kam ta yi maka nisa, saboda na fahimci cewa idan ban fito na yi maka gwari gwari ba to zaka janyo man abunda zai saka jinina ya hawa, yanzu ga shi daga zuwanka ka firgice mani mata na kasa gano kanta" Ya kalli Kamal yace, "Aboki ka yi masa wa'azi don ya gano kallon matar aure ma haramun ne balle ya tsaya mayar da yawu da ita yana jin daɗin zancenta, to ka zama sheda WALLAHi ya sake tsaf zan yi masa ALLAH ya isa akan matata" Kamal yana dariya yace, "banga laifinka ba abokina saboda haka kai Malam ka tsaya iya matsayinka na malam kawai, don kaji a gabanka mijin ɗalibar taka ya kawo ƙararka" Lawi da ke saurarensu zuciyarshi fess da jin kalaman Safwan, ba shiri wata dariya ta suɓuce masa ya kalli Safwan ɗin yace "To kai mijin ɗalibata ka ji tsoron Allah ka riƙe man ita amana kada ka bari ɗalibata ta yi kuka matuƙar kana son inci gaba da koya mata dabarun biyayya gareka" Safwan ya maka masa wata jar harara yace, "kar ma kasa ranka zan bari ka sake ganinta, don ba zaka sake janyo man kwaɓata yin ruwa ba" Lawi yana dariya yace "Kwantar da hankalinka nima na kusa angwancewa yanzu haka saura wata biyu masu zuwa insha ALLAHu" Safwan ya yi saurin washe baki yace "ko kai fa? Ai da ka taimaki kanka gaskiya, zaman tuzururantaka ai ba daɗi ne da shi ba, ka ga ni naji daɗin daushen farko har wani sabon lambun nike son in ƙara ninƙaya a ciki" Kamal ya yi saurin faɗin, "wai da gaske ne kai zaka auri Zee" Safwan ya washe baki yace "Insha ALLAHu kwanan nan ma kuwa don bazan koma school ba har sai an shafa fatiha in kwashi matata mu bar maku ƙasarku" Lawi ya yi shiru na ɗan lokaci sannan ya ce, "Abokina gaskiya zan sanar da kai wannan yarinyar da kake gani yanzu haka da mijinta da za'a haɗasu aure a gida, me zai hana ka riƙe matarka ka barta ta je ta auri zaɓin gidansu? WALLAHi ina jin tsoron haƙƙinshi ya kamaku kai da ita, don abinda ka yi mani ba kowa ne yake da sauƙin zuciyar yafiya ba, ka janye jikinka ka barta ta yiwa iyayenta biyayya ko don dakon jiranta shekara da shekaru da Aminu ya yi saboda kawai yana son aureta" Safwan ya yi saurin faɗin, "Eh nasan da zancen amman tunda ita bata sonshi ai sai a barta ta auri wanda take so" Lawi yace "ka dai sowa ɗan uwanka abunda kake sowa kanka yafi abokina, hadisi ne ingantacce kuma ina da tabbacin kasan da shi, saboda haka Ni ina baka shawara ne a matsayina na Abokinka idan kaji ka taimaki kanka, idan kuma ka rufe ido ka ka kasa hango gaskiya to shikenan Ni dai na fita haƙƙinka" Safwan ya yi wata dariyar gefen baki yace, "idan ka ga ban auri Zee ba to sai in itace da kanta ta ce ta fasa aurena, saboda na riga da na yi mata alƙawari akan zan auretan duk runtsi" Kamal yace "ALLAH sarki Aminu WALLAHi na tausaya masa" Safwan ya ɗaga kafaɗa yace, "ka ji da shi ni dai ba gudu ba ja da baya saboda nasan tana sona" Haka suka yi ta fafatawa har aka gama walimar Safwan ya fito don ya yi sallama da su Zee, Kamal ya biyoshi saboda yana son ta ganshi don tasan yasan komi, aiko sai gata tsaye da Safwan ɗin suna sallama Fiddo ta riƙo masu kayan walimarsu da aka basu ta saka masu a mota, Zee tana yi wa Fiddo godiya suka yi ido biyu da Kamal, ta yi saurin riƙo ƙawarta tace "Ruma kin ga Mituminki fa" Ruma ta washe baki tace "laa! Kamal Rai kan ga rai?" Kamar yana ɗan murmushin yace "Rumasa'u kwana da yawa" Tace "sai Alkhairi" ta ƙara da cewa "kai ma ka zo bikin kenan" Yana dariya yace "Eh gamu munzo ta ya su Zee murna ALLAH ya sanya alkhairi" Zee ta yi masa wani kallon tambaya sannan tace "Ameen" saboda mamakin ya aka yi yasan tsakaninta da Safwan ɗin, shi ko don ya tabbatar mata da yasan komi yace,. "Ashe haka aka yi kenan Abokina ya yi wa wani Abokina ƙwace?" Zee ta yi saurin kallon Safwan tace, "Abokin yaya Aminu ne fa" Safwan ya ɗaga kafaɗa alamun ko a jikinshi yace, "ALLAH ya baiwa mai rabo sa'a idan Abokin nashi ne mijin ai sai ku daidaita kawai" Zee ta zaro ido tare da ɓata fuska ta ce "Haka ma zaka ce?" Yace "eh to ai addu'a ce nayi ko?" Ta turo baki tace, "to in fa Kuma addu'ar ta faɗa kanshi fa?" Ya yi saurin faɗin "sai in ɗauki na annabawa ALLAH ya bani wata madadinki" Kamal ya yi saurin faɗin, "ALLAH ai ya baka kuma sai dai in bazaka gode wa irin baiwar da ya yi maka ba" Zee ta yi saurin kallonshi tace, "wa ya ba shi ɗin ?" Kai tsaye kamal yace, " kyakkyawar Matarshi mana ko baki ganta ba" Zee cikin firgici tace "Tsaya Kamal don kana taya Aminu kishi kada ka ce zaka ɓata man rai, wace mata ka aura masa bayan ni da zai aura kwanan nan? A gaskiya bani son muguwar fata" Ta ƙare maganar tana harararshi, Kamal ya yi yar dariya ya kalli Safwan da duk ya diririce alamun rashin gaskiya suka bayyana akan fuskarshi yace "Kai Abokina to ka yi mata bayani da bakinka mana don naga kamar na shiga hurumin da ba nawa ba" Safwan cike da jin haushinshi yace, "kai da ka yi mani waliccin auren ai sai ka yi mata bayani da bakinka don sai tafi saurin gamsuwa dai dai" Zee ta washe baki ta ce "ƙyaleshi my cuddle bear nasan kishi ne yake taya Abokinshi bayan ni na riga da na yi masu nisa sai dai haƙuri" Kamal ya yi mata wani kallo cike da jin haushin irin cin amanar da zata yi wa Abokinshi yace, "ita dai gaskiya idan ta tashi fita tafin hannu ya yi kaɗan da ya kareta, haka duk wanda ya ci amana to ya sani akwai lokacin da ranar sakamako zata ziyartoshi, ni kinga tafiyata fatana kawai ita Uwargidan ALLAH ya bata haƙurin sammakon da za'a yi mata" Yana ƙare faɗar haka ya wuce abinshi, daga Safwan har ita Zee suka bishi da wani kallo mai ƙumshe da harara, ran Zee a jagule ta kalli Safwan ta ce" "My hero Wai me yasa a ko'ina sai an samu yan adawa ne?, Ji don ALLAH yanda yake wani zaƙewa sai kace shine Aminun?" Safwan ranshi a ɓace yace, "shareshi kawai hassada ce zo muje ki yi sallama da Hajiya mu je in raka ku gida tun kafin wannan magulmacin ya ɓata muna tsari" Ya yi gaba Zee tare da janyo hannun ƙawarta amman sai Ruma ta ce da ita su je kawai ita zata jirasu, suna shigewa Ruma ta yi wurin Kamal zuciyarta cike da son jin gaskiyar abunda yake son sanar da Zee, ta nemi izinin ganinshi na ɗan lokaci suka keɓe gefe, Ruma ta zama serious bayan sun ƙare ɗan barkwancin da suka saba tace "Kamal don ALLAH ka sanar da ni gaskiyar zance shin da gaske Man ɗin Zee yana da aure?" Kamal ya yi yar gajeruwar dariya yace, "tunda kince ALLAH to ba wani kwana da zan tsaya yi maki, tabbas Safwan yana da Mata asali ma yanzu haka shekararshi biyu cikin ta uku da aurensu" Ruma ta zaro ido waje tace, "Kamal kasan dai bamu irin wannan wasar da kai ko?, tsakaninka da ALLAH na roƙeka ka faɗa mani gaskiyar lamarin, saboda WALLAHi Zee ta mato sosai akan wannan guy ɗin idan har ta ji wannan magana nasan ba ƙaramin tashin hankali zata shiga ba" Kamal ya karkace baki yana dariyar gefe idonshi suka kai ga Surayya da ke ta ɗaukar hotuna da Ƙawayenta ya yafitota da hannu, ta nufoshi tana dariya kasancewar tasanshi sosai saboda tare suka yi karatu da Safwan a garin, asali ma kamar gidan suke dukansu har da Lawi a lokacin da suka yi karatun jami'arsu. Tana zuwa ta gayar da shi a mutunce bayan sun gaisa ya ce da ita, "Surayya ki yi mata bayanin gaskiya saboda ta ji da kunnuwanta, shin da gaske Safwan yana da aure ko kuwa?" Surayya ta washe baki tace, "ALLAH sarki ƴar uwa da gaske kuwa Yayanmu yana da aure kuma yana bala'in son Matarshi, haka itama kuma tana sonshi sosai" Diirim! dum! Shine abunda zuciyar Ruma ta yi saboda maganar ba ƙaramin bugun zuciyarta ta yi ba, nan take ta fara tausayin ƙawarta cikin canzawar yanayinta da ya koma kalar damuwa ta ce "ALLAH sarki ko zaki iya nuna mani matar in ganta don ALLAH" Surry tace, "bari in dubota don tun ɗazu ma ban ganta ba" Surry ta yi cikin gidan zuciyarta cike da fatar ALLAH yasa ma auren ya wargaje kowa ma ya huta, sai dai duk bulayin neman Dijen da ta yi bata ganta ba, dole ta dawo da nufin sanar da ita cewa bata ganta ba, sai ga shi ma ta taradda su duka har da Safwan ɗin suna sallama da juna, saboda Ruma bata nuna komi ba nufinta sai sun je masaukinsu ta sanar wa da ƙawarta gaskiyar zancen. Cikin tsoro Surry ta yi saurin komawa cikin gidan ta laɓe, har suka fita Gate ɗin gida Safwan ya bi su a baya sannan ta fito tana sauke ajiyar zuciya. To sai dai abu kamar wasa har dare anata neman Dijen Baffah ammsn ba'a ganta ba, tun ana ɗaukar abun wasa har kowa hankalinshi ya fara tashi don kuwa anyi nemanta ko'ina gidan kaf ba'a ganta ba, Hajiya ta firgice sosai sai kiran Safwan take yi akan ta ji shin yana tare da Dijen ko kuwa, amman bai ɗauka ba saboda bai ma san ta kirashi ba don wayar a silen take, sai bayan ya gama firarshi da Zee ne Suka yi sallama yana kan hanya ya ga tarin miss calls na Hajiyar da su Surry da wasu ƴan uwansu duka, cikin tashin hankali ya dannawa Hajiyar kira sai ko ta yi caraf ta ɗauka, ba tare da ta jira jin abinda zai faɗa ba ta ce "Ina khadija kuna tare da ita ne?" Safwan a firgice yace "A'a WALLAHi Ni tun ɗazu rabon da na ganta" Hajiyar ta yi saurin faɗin ka yi gaggawar nemota duk inda take, saboda an duba kaf gidan nan ba'a ganta ba, kuma jikina yana bani kai ne ka yi mata abunda ya janyo ta bar gidan, WALLAHi ka ji na rantse matuƙar baka nemo man ita ba to ko kada ka kuskura ka tako ƙafarka cikin gidan nan". Kitt! Ta kashe wayar zuciyarshi cike da tashin hankali ya furta "Innalilahi wa'Inna ilairraji'un" Cikin ruɗewa ya nufi tasha saboda cen zuciyarshi ta hasko masa zata nufa, saboda cewar da ta yi masa bata son karatun ita garinsu zata koma, sai dai kuma duk iya binciken da aka yi tashar babu sunan Khadija Umar a cikin jerin list ɗin mutanen da Motarsu ta tashi ranar a tashar, ya fito a gigice ya nufi wata ƙaramar tashar da ake shiga Mota nan ma ba wani alamun ta je cen, haka ya yi ta zagayen wuri wuri amman ko mai kama da ita bai gani ba, dole ya yi parking ya fito dafe da kanshi da ke yi masa mugun sara gashi dare ya fara yi da ke yi, saboda tsabar tashin hankalin da yake ciki sai waige waige yake yi a tunaninshi ko zai hangota, yana cikin hakan ne ya ji wayarshi ta yi Virbration cikin sauri ya ɗaukota tsammanin Hajiya ce zata sanar da shi cewa ya dawo an ganta, sai kawai ya ji Muryar Zee tana kuka tana faɗin "Munafukin banza baƙin mayaudari ashe daman kai maƙaryaci ne ban sani ba? To asirinka ya tonu yau gaskiya ta fito labarin aurenka ya zo kunnuwana, ashe daman cen kana da Mata shine ka ɓoye man, to ka sani na tsaneka na tsaneka tsana mafi muni a rayuwata" Ƙitttt ta kashe wayar, cikin wani sabon tashin hankalin da ya ƙara ziyartoshi ba shiri ya kai zaune daɓas ƙasa dafe da kai yace "Kai wannan bala'in da me ya yi kama wayyo ALLAHna khadija ina zan ganki WALLAHi ina sonki don ALLAH ki dawo gareni plss!" Ni ma dai tashin hankalin yasa alkalamina ya faɗi ba shiri🙀 Akafta🤪 D/AUTA Ce✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *Kar kuji komai allurar ƙarfi aka yi man😂😂😂😂😂shiyasa na zauce hannuna ya HAUKACE yana ta suburbuɗo maku typing, ku sha sha'aninku kawai kafin Nima in sha nawa idan allurar ta sakeni yasin😝* *Lamba ta 49* Dijen Baffah kam tunda ta fito ɗakinshi ta nufi ɗakinsu cikin dubarar rufe fuskarta da ɗankwalin doguwar rigar da ke jikinta, ta ɗauko jakarta da kuɗin liƙinta suke ciki ta rataya, ta fito kamar wacce zata shiga wurin walimar ta fice gidan cikin sauri ta tare Napep ta haye sai babbar tasha, ta ce motar garinsu take nema aka ce da ita sai dai ta Gombe idan taje sai ta shiga motar Kano, daga cen sai ta shiga motar da zata kaita babban birnin garinsu, cikin rashin tsoro ta faɗa motar jikinta yana rawa ta tambayi kuɗin motar aka faɗa mata ta biya, da aka zo wajen rubuta suna da numbar waya kamar tasan za'a nemeta ta rubuta sunan ƙarya da numbobin banza, tunda ita ko wayar ma bata da bale ta yi number, zuwanta bai wuce minti goma ba motar ta cika suka tafi don ko da tara na dare ta buga tana garin Gombe, sai da aka je cen ne wani tsoro ya shigeta saboda batasan inda zata je ta kwana ba, ta rakuɓe gefen wata mota tana ta sharar ƙwallah saboda motar da taga za'a hau a lokacin kuma a ce wai tafiya za'a yi cikin daren, tana nan tsaye sai ga wani ɗan union ya zo yana faɗin "Ina zaki je ne Kano ko Kaduna ko Bauchi Sokoto ko Zamfara?" Dije ta yi saurin goge ƙwallarta tace "kano" Yace "to zo mu je ga motocin Kano cen ina kayanki?" Tace "babu" Ya yi saurin waigowa yace, "bangane babu ba an sace kayan ne ko yaya?" Ta ce "bani da kaya" Ya ce ",to ai sai ki yi bayani yanda zan gane zo mu je kar motar ta tashi don ta kusa cika" Dije ta bi bayanshi har inda motar take aka yi mata mazauni ta yi tsalle ta shige saboda ƙatuwar mota ce, ta sami wuri ta rakuɓe tana muzurai saboda tsoron yanda za'a bi hanyar zuwa wani gari cikin daren, zamanta ba wuya aka tada motar suka kama hanya, tafe take tana addu'ar ALLAH ya kaisu lafiya har bacci ya yi awon gaba da ita, ga masifar yunwar da ta addabeta don rabonta da abinci tun Yola. Cikin ikon Allah Asubar farin suna isa Kano, bayan an saukesu mutane da yawa suka fara arwallah domin su yi SALLAH, itama ta bi sahun mutanen ta siyi ruwan ta yi arwallah ta yi SALLAH duk da masifar ciyon da kanta take ji, sannan ta tambayi wani ina ake shiga motar Katsina, ya yi mata jagora har zuwa inda motocin suke ta ƙara ce da shi "don ALLAH Malam ina zan samu abinci inci WALLAHi yunwa nike ji sosai" ya ce ta zo su je ya nuna mata wani shagon sayar da abinci, aiko ta bishi har zuwa wani ƙaramin shagon, yace da ita ta shiga ta zauna ta jirashi ya kawo mata abincin, ba wani tunani ta shige shagon ta zauna tana kallon mutanen da ke wulgawa ta Kofar shagon, ƴan mintuna a sai gashi ya dawo yana wata dariyar rashin gaskiya, yana zuwa ba wani jinkiri ya rufe shagon, cikin tsoro Dije ta ce "Ina abincin ?" Ya sosa kanshi yace "Ki fara bani naki abincin sannan sai in je in kawo maki nawa kafin lokacin ma mai abincin ta kammala" Dije cikin mamaki tace "Ni ina naga abincin da zan baka?da ina da shi ai bazan tambayeka ba" Ya yi sake yin wata dariyar shakiyanci yace "Ke ko kike da abincin ci ki natsu kawai mu gama komi cikin lokaci kafin mutane su fara cika tashar" Dije ta zaro ido cikin tsoro tace, "WALLAHi ko ka bani hanya in fita ko yanzun nan in yi maka sanadin barin duniya" Cikin dariya ya nufota zai cafkota ta zille ya sake yunkurin kamota ta ɗaga jakarta ta buga masa ita iya ƙarfinta, aiko cike da jin haushi ya damƙota ta fasa wata uwar ƙara, shi ko ba kunya sai ƙoƙarin mannata da jikinshi yake yi, ganin da gaske keta mata haddi yake so ya yi ta fasa wata uwar kuwwa bakinta a sake sai ihu take yi, suna cikin kokawar ne aka banko Ƙofar shagon da ƙarfi ta buɗe ya yi saurin kallon ƙofar yana muzurai, Dije ta yi waje da gudu a firgice ko ɗankwali babu bale takalmi, jikinta sai rawa yake yi tana faɗin "WALLAHi sai na kasheka azzalumi shegen banza ɗan'iska" Mutane suka taru a kanta saboda ganin yanda take ta kuka tana tsine masa, sai tambayarta ake ba ɓata lokaci ta yi bayanin duk abunda ya haɗa su, aiko nan take mutane suka yi ta tsine masa suna aibatashi, wani ya shiga ya ɗauko mata jakarta da talkami da ɗankwalinta ya bata ta saka, sannan wasu matasa suka rufeshi da duka, cikin tausayinta wani bawan ALLAH ya je ya siyo mata tea da biredi ya kaita wani waje ta raɓa ta sha, sai dai tana gama sha amai ya biyo baya ba shiri ta fara rawar sanyi, mutumin ya siyo mata magani ta sha sannan ya sakata motar katsina sai da motar ta tashi sannan ya tafi yana jinjina halin wasu iyaye masu yiwa ƴaƴa riƙon sakainar kashi, su yi ta sakin ƴaƴansu duk inda suka ga dama. A galabaice Dije ta isa babban birnin garinsu ta shiga motar da zata kaita ƙauyensu, har ƙofar gida Direban ya kaita saboda babu ko sisi a hannunta duk mota ta cenye kuɗin, asalima ko kuɗin zuwa katsinar ma sai da wata mata ta cika mata da nata basu kai ba, cikin tsananin galabaita ta faɗa gidansu yaran da suka biyo motar suka bita suna ihun ga Dije ga Dije amman ko ta kansu bata bi ba. Tana shiga kai tsaye ɗakin Inna ta faɗa ta haye gado ta dunƙule cikin zane tana rawar sanyi, Inna daga bayi ta jiyo muryar yara suna ta kuwwar zuwan Dijen, jikinta yana rawa ta nufi ƙofar gidan inda suka ci karo da Hansai da itama ta fito daga sashenta aguje cikin murna da ɗokin ganin Dijen. Amman basu ganta ba sai Direban da ya kawota kawai da ke ƙofar gidan yana bada saƙon a karɓo masa kuɗinshi tafiya zai yi, Inna ta tambayi yaran ina Dijen suka ce tana cikin gidan ta shige ɗaki, gaban Inna ya ƙire ya faɗi saboda jikinta ya bata cewa ba zuwan lafiya ne Dijen ta yo ba, cikin sauri ta kwance ƙullin da ke haɓar zanenta ta re da tambayar nawa ne kuɗin? Direban ya faɗa ta bashi ta yi masa godiya cike da rawar jiki ta koma cikin gidan gabanta sai faɗuwa yake yi, sai dai tun kafin ta isa gadon ta jiyo sautin nishin Dijen, da ke ta rawar sanyi haƙoranta suna haɗuwa suna karkarwa, cikin sauri Inna ta zauna ta re da yaye rufar da ta yi ta taɓa wuyanta ta ji zafi zau!, Cikin faɗuwar gaba tace "Dije lafiyarki ku wa?ina Hajiyar? Ya aka yi kika zo ke kaɗai bayan kuma nasan buki kuke yi?" Dije cikin rawar baki hawaye suna zuba gefen idonta tace,. "Ni kaɗai nake ai" Hansai ta shigo jiki a sanyaye ta zauna gefen Dijen tace, "Sannu Dije baki da lafiya ne?" Dije ta ɗaya Kai Inna ta miƙe ta je ta ɗauko mata magunguna ta matsa mata sai da ta sha sannan ta koma ta dunƙule, Inna ta kalli Hansai tace "A sami yaro a aikashi gidan Maigari ki ce ya zo gida ana nemanshi" Hansai ta fita Inna ta dawo ta sassafta murya tace, "Dije faɗa man gaskiya kafin malam ya zo shin Mijinki rabuwa ya yi dake ne ko yaya?" Dije ta yi saurin girgiza kai tace, "A'ah Inna ba ma wanda yasan na tafo" Inna ta sake jin wani sabon fargaba, ta tada ita zaune tace "Kallanni da kyau Dije bana son Baffahnki ya shigo baki sanar da Ni gaskiyar abunda yake faruwa ba" Dije ta ja jikinta ta jingina da bango tace, "Ba rabuwa ya yi dani ba Inna amman WALLAHi ni na gaji da aurenshi tunda yake son ya lalace mani rayuwa" Inna ta zaro ido waje tace "bangane ya lalace maki rayuwa ba? ki yi man bayani dalla dalla yanda zan gane" Dije ta share hawayenta tace "Inna jikina yake taɓawa WALLAHi har kayana ya tuɓe yanata yi man wani iskanci a jiki........" Ba shiri Inna ta kai mata wani bahagon mari a baki cikin fushi ta nunata da hannu tace, "au Wai daman akan wannan dalilin ne kika gudo tun daga Yola har zuwa garin nan? To buɗe kunnuwanki da kyau kiji WALLAHI matuƙar kika ce bazaki iya yiwa Mijinki biyayya akan duk abunda ya zo maki da shi ba, to Ni Ko ko kaɗan ba zamu shirya da ke ba" Dije dafe da gefen da ta sha marin cike da mamaki tace, "Inna WALLAHi har ƙirjina yake taɓawa yana ƙoƙarin cire mani ɗan kamfai, kuma ma har dukana yake yi fa" Inna ta wurga mata wata ƙatuwar harara tace, "abunda ya fi duka ma idan ya yi maki kin cancanta ai, to bari kiji duk abunda kika ga ya yi maki ko yana ƙoƙarin yi dake to tuni Baffahnki yayi hakan dani, kuma gani daram har yanzu kin ganni ba abunda ya sameni, don haka tun wuri WALLAHi ki shiga taitayinki miye amfanin karatun da kike yi?, Saboda haka tun kafin ki janyo wa kanki abun gori cikin mutane, sannan ki tsallake Hajiya ki nufo gidan nan ke kaɗai ko tsoron abunda zai sameki a hanyar baki ji ba, yanzu da wane ido kike so mu kalleta ace kin tsallaketa akan wannan guntuwar matsala kin nufo gida?. " Dije ta zumɓuro Baki tace, "kedai Inna don baki san me yake yi mani bane shiyasa" Inna ta buge mata baki tace "ina ko zan sani tunda ban taɓa yin auren ba, to bari kiji in baki sani ba ki sani shekarun baya akan wannan dalilin ne aka ɗaure Jummala, ke ma idan kina son ayi maki haka to WALLAHi ko a cikin ɗakin nan zamu iya ɗaure masa ke, ya yi duk abunda yake so da ke tunda ba zunubi ne zai aikata ba" Dije ta zaro ido tace "Inna yanzu daman akan haka ne aka ɗaure Jummalar? Cabɗi to WALLAHi gaskiya kam ba'a kyautawa rayuwarta ba, to ni dai WALLAHI bazan taɓa bari wani ƙaton banza ya yi iskanci da Ni ba ina kallo in ƙyaleshi ba" Inna ta sake Kai mata wani marin wanda ya yi dai dai da shigowar Baffah tana faɗin "Mu zaki tonawa asiri Dije?" "Wane asiri zata tona bayan yanzun nan muka gama waya da Uwar mijinta an sanar da ita Dijen tana nan saboda ta ɗaga hankalinta sosai akan rashin ganinta, don haka ki bar yarinya ta huta da wahalar motar da ta kwaso sannan ki fara dukan nata tunda ke hannunki bai girma da bugunta" Ya ƙaraso wajen Dijen ya shafo kanta yace, "Dijengalata me yasa kika baro cen ba tare da sanin Mijinki ba" Dije ta fashe da wani sabon kuka, Inna ta ce da Baffahn ya zo ya ji suka fita tare har zuwa ɗakinshi, cikin ɓacin rai ta sanar da shi dalilin da ya dawo da Dijen, Baffah ya yi shiru yana nazari saboda shi tsammaninshi ma tuni an wuce wannan babin, ashe yanzu ake matsalar ya sauke ƙatuwar ajiyar zuciya yace "A gaskiya yaron nan ya yi haƙuri da yawa WALLAHi, amman ita kuma a hankali zaki fahimtar da ita ba da duka ko faɗa ba, saboda yanzu haka mijinta yana kan hanyar zuwa garin nan, kuma da ya zo nike son ta bishi su koma don banga amfanin zaman da zata yi muna anan ba" Inna ta sauke ajiyar zuciya tace, "ALLAH ya kawoshi lafiya amman kasan dai ko kaɗan bata kyautawa Hajiya ba ko?, Ace duk dawainiyar da take yi da ita amman ta tsallaketa ta zo wurinmu akan wannan guntuwar matsala" Baffah yace "Haƙuri za'a yi kuma yanzu tunda dai mai afkuwa ta riga da ta afku, sai a kira ita Hajiyar a bata haƙuri shi kuma idan yazo mu bashi haƙuri ya tafi da matarshi" Inna sauke wata ajiyar zuciya tace "ALLAH ya kawoshi lafiya sai dai ni naso ace a barta ta yi kwana biyu anan, saboda in fahimtar da ita abubuwan da suka shige mata duhu" Baffah ya ce "aganinki ba za'a ga munyi ƙaranta ba?" Inna tace "izininshi zamu nema ai saboda duk abunda zai sa ta kamo hanya tun daga cen har nan to abun ba ƙarami bane, saboda haka don ALLAH idan ya zo ka nuna masa kana son a bar Dijen nan ta ɗan kwana biyu" Baffah cike da mamakinta yace, "ke fa kika ce da ni ga dalilin da yasa ta gudo to kuma yanzu sai ya zo tafiya da ita kuma muce a barta ta yi kwana biyu?, Ni fa bana son abunda zai sa mutanen nan su ga rashin kyautawarmu, ko dai akwai wani abu bayan wannan ne?" Cikin damuwa Inna tace, "babu wani abu amman kasani ko yanzu tsugunne bata ƙare ba, matuƙar ta koma ba tare da an fahimtar da ita minene auren ba da abunda ya ƙumsa, saboda ina jin tsoron tace zata sake biyo doguwar hanyar nan ita kaɗai ko don gudun wani abu mara kyau ya sameta" Baffah ya yi shiru yana nazari sannan yace, "to kuma Hasiya kin yi nazari anan, to ALLAH yasa shi ma idan ya zo ya amince ya bar muna ita ɗin" Inna tace "ai nuna masa ɓacin ranka zaka yi akan sakacin da ya yi har ta biyo wannan uwar hanyar ita kaɗai" Baffah ya yi saurin faɗin, "kar fa ki janyo inji kunya wajen surukina?" Inna tace "ba wani jin kunya hakan da zaka yi shine zai ƙwatowa Dije ƴancinta, saboda gobe ya ji tsoron ƙara yin sakaci da ita har ta biyo hanya ba tare da sananinshi ba" Tofa Inna uhum da kinsan halin da mijin Dijen yake ciki da ba ki ce haka ba😔 Akafta😉 D/AUTA Ce✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *DOMIN JIN DAƊINKU MASOYANA ku natsu tsaf ku ci gaba da kwasar ganima😂😝* *Lamba ta 50* Safwan kam firgicin da yake ciki ne yasa ya baje ƙasa cikin kiɗimewa yana ta sambatun kiran sunan Dijen, tare da faɗin "Ina kika shiga ne don ALLAH ki dawo wallahi ina sonki ke ma kinsani ai" Har dare ya raba yana ta abu ɗaya zuwa lokacin mutane sun fara taruwa kanshi ana tambayarshi mafari, da dai ya fahimci ya tarawa kanshi ƴan kallo ne ya tashi ya faɗa Motarshi ya nufi gidansu wani ɗan uwansu kuma abokinshi, cike da tsantsar tashin hankali yake yi masa bayanin duk abunda yake faruwa, Abokin nashi ya jinjina abun a ranshi sannan ya ce "A gaskiya Abokina ka yi kuskure babba yanzu mafita ɗaya ce ka je ka baiwa Hajiyar Haƙuri kafin ka kama hanyar zuwa garinsu yarinyar, saboda jikina yana bani ta yi gida don ta gaji da abunda kake yi mata ne shiyasa ta gudu" Sannan Safwan ya tuno da wayarshi ya ɗaukota da nufin kiran Hajiyar sai ga kiran Lawi da Kamal ya fi ashirin a wayar, cikin sauri ya kira Lawin da rawar baki yake faɗin "An ganta?" Lawi murya mai cike da damuwa yace "WALLAHi ba'a ganta ba ni na fara zargin ko ta yi garinsu" Safwan ya dafe kanshi cikin wani sabon firgici yace,. "Don Allah Abokina ka roƙar mani Hajiya in dawo gidan in bata haƙuri WALLAHi gobe tun da sassafe zan kama hanyar garinsu Khadija in dawo da ita" Lawi yace "kayi haƙuri Abokina WALLAHi Hajiya ta shiga damuwa sosai akan ɓatan khadija yanzu haka ma da ƙyar na lallasheta ta daina kuka, ga gidan gaba ɗaya hankalinsu ya tashi madadin farin ciki gida ya koma na jimami" Safwan a kiɗime ya kashe wayar tare da furta "Innalilahi wa'Inna ilairraji'un Allahumma la sahla illa maja'altahu sahla, ALLAH ka tsare yarinyar nan a duk inda take, Ubangiji ka bani ƙarfin gwiwar tunkarar wannan mummunar ƙaddara da ta faɗowa rayuwata" Ya kalli Abokin nashi da jajayen idanuwanshi yace, "bari inje Mubarak banga ta zama ba tunda har nine na janyo komi" Mubarak cike da tausayinshi yace, "ba dai yanzu kake nufin zaka bi bayanta ba?" A zafafe ya faɗa motarshi yana faɗin "banga ta zama ba ai kuma matuƙar ba ganin yarinyar nan nayi ba....." Kiran wayarshi ne ya katse maganar da yake yi cikin sauri ya ɗaga saboda ganin numbar Hajiyarshi ce, kafin ma yayi magana yaji muryarta cikin muryar kuka tace "WALLAHi matuƙar baka dawo man da yarinyata ba to kada ka kuskura ka tako ƙafarka cikin gidan nan" Cikin rawar murya yace, "ki bini da addu'ar tsari kawai Hajiyata, nayi maki alkƙawali bazaki ganni ba sai tare da Khadija insha ALLAHu" Kittt! Hajiyar ta kashe wayar saboda wani kukan tausayin kansu da ya kamata, Surayya dake ta bata haƙuri ta yi saurin faɗin "Don girman ALLAH Hajiyarmu ki yi haƙuri Insha ALLAHu ba abunda zai sami Khadijah ALLAH zai kareta a duk inda take" Hajiya ta miƙe ta nufi toilet Surayya da Fiddo da yayyensu biyu mata da wasu ƴanuwasu da ke ɗakin suka bita da kallon tausayi, saboda yanda ta ɗaga hankalinta sosai akan rashin ganin Dijen, kowa sai faɗin albarkacin bakinshi yake yi akan lamarin. Wannan shine abunda ya faru kafin Hajiya ta kira garinsu Dijen ta ji labarin cewa tana cen, don ko shi Safwan ɗin yana kan hanyarshi ne ya sami labarin cewa tana garinsu a bakin Surayya, saboda ƙoƙarinta na son rage masa damuwar da yake ciki. Ranar yinin bikin Surayyar ma bikin ba wani armashi saboda damuwar da uwar bikin take ciki, haka aka tattara aka kai Surayya ɗakin Mijinta ita kanta zuciyarta ba daɗi saboda halin damuwar da ta baro Hajiyarsu a ciki. Safwan kam sai da ya ganshi a babban birnin su Dijen sannan hankalinshi ya fara daidaito, ya yi masauki anan sannan ya kimtsa sosai cikin shiga ta alfarma ya buga Motarshi ya nufi ƙauyensu Dijen, zuciyarshi cike da jin daɗin matsalarshi ta zo ƙarshe, saboda fushin da Hajiyar take yi da shi ya fi komi ɗaga masa hankali fiye da duk wani hali da yake ciki. Dije kam kasancewar daga ita sai kayan jikinta ta shigo garin, Inna ta ɗauki turminta biyu ta baiwa Usmanu tace ya kai babban birninsu inda aka yi wa Hansai ɗinkinta na aure ayowa Dijen ɗinkin Express saboda mijinta yana kan hanya, ya karɓa ya tafi yana dariyar yanda Inna take son farantawa surukinta. Da marece sakaliya Usmanu ya dawo da ɗinkunan Inna ta karɓa tana ta murna Dije kam iyakacinta ido, don gaba ɗaya jin take yi zama gidan ya gundureta saboda jin da ta yi ance Safwan yana kan hanyar zuwa garin. Kasancewar shagar dare ya yiwa garinsu Dijen shiyasa da yawa mutane basu san da zuwan nashi ba, cike da jin daɗi ya yi parking ƙofar gidan ya fito yana baza babbar riga sai tashin ƙamshi yake yi. Jin ƙarar ajiye motar yasa Usmanu saurin fitowa saboda daman cen kowa da tsumayin zuwan nashi yake a gidan, bayan sun yi musabaha ne Usmanu ya ce da shi ya shigo, Safwan ya biyo bayanshi zuciyarshi sai dakan lugude take yi saboda tsoron kada Dijen ta bashi kunya a gaban surukan nashi, da sallamarshi a baki ya shiga Baffah da Inna baki har kunne suke amsa masa sallamar, Dije da ke ɗaki tana gunguni tun daga cen ta ji yo ƙamshin turarenshi, ta yi saurin duƙunkunewa kan gadon har da su lulluɓewa duk da gayun da Inna tasata ta yi na tarbon Safwan ɗin. Safwan cikin ladabi da jin nauyinsu ya rusuna yana gayar dasu, inda suma ɗin suke amsawa cikin mutunta juna da karamci irin na surukantaka, bayan an ƙare gaishe gaishen ne Safwan ya ɗan muskuta tare da ƙara sunne kanshi yace "Don ALLAH ayi haƙuri da zuwan da Khadija ta yi WALLAHi bansan da zuwan na ta ba a yafe mani don ALLAH" Dije daga cen ɗaki jin abinda ya faɗa yasa ta yi zumbur ta fito tana huci tace "Ba kai kace......." "Kul!" Katon kashedin da Inna ta yi mata kenan wanda ya sata yin shiru ba shiri, ta yi saurin komawa ɗakin tare da fashewa da kuka tana faɗin "Shikenan Ni komi na yi bani da gaskiya ai" Baffah ya kalli Safwan da kyau yace, "ka yi haƙuri da halinta don ALLAH don alamu duk sun nuna ba ƙaramin surutu take sakaku ba, don ko wannan zuwan da ta yi hakan ya tabbatar mani da cewa har yanzu bata san minene auren ba, ina mai ƙara baka haƙuri akan shirmen da take yi maku don ALLAH ku ƙara haƙuri da ita, insha ALLAHu da sannu komi zai daidaita har ma ku yi alfahari da zamanta cikinku" Safwan ya duƙe kai yana murmushi yace, "ba komi Baffah insha ALLAHU ma komi ya wuce daga yanzu, saboda gobe idan ALLAH ya kaimu lafiya nike son mu koma tare da ita" Baffah ya yi shiru sannan ya ce, "ina neman alfarmarka Muhammadu akan ka yi haƙuri ka bar muna ita anan zuwa wani ɗan lokaci, Insha ALLAHu zamu fahimtar da ita komi saboda gudun irin wannan matsalar da ta faru ta sake faruwa" Kirjin Safwan ya buga dirim! dim! Cikin firgici yace, "don ALLAH ka yi haƙuri in tafi da ita Baffah, saboda WALLAHi idan ban koma da ita ba akwai matsala, saboda yanzu haka Hajiya fushi take yi da ni sosai akan zuwan da Khadija ta yi, kuma ta sanar da ni cewa muddin ban dawo ƙafata ƙafarta ba to kada ma in koma gidan, gashi ina son in koma makaranta saboda saura shekara ɗaya in kammala karatuna" Baffah ya yiwa Inna wani kallon neman shawara ta ɗaga masa kai a fakaice, cikin sauki ya ɗauko hannu sannan ya ce "To ya yi ai ba komi ALLAH ya nuna muna goben lafiya kuma ya tsare hanya ku je lafiya" Cike da jin daɗi Safwan ya washe baki ya ce, "Ameen Baffah" Inna ta ce da shi 'ka yi haƙuri ko ruwa bamu baka ba" "Dije!!" Inna ta ƙwallawa Dijen kira tace ta je ta kaishi ɗakin samartakar Usmanu ya ci abinci, Dije ta fito tana tunzure tunzure ta nufi ɗakin da ke cikin zauren gidan, wanda tun da safe Inna ta gyarashi tsaf aka malala ƙatuwar tabarma sabuwa dal, tare da wata babbar carpet a samanta, ga wani turaren wuta da aka ƙamsasa ɗakin da shi, kasancewar Abincin da komi da aka tanadar masa yana ɗakin an ajiye, Dije tana shiga ɗakin ta ja ta tsaya tana wani cin magani tana gunguni, Safwan cike tsantsar farin ciki ya nufi inda take tsaye ya tsaya tare da rungume hannuwa a ƙirji yana ƙare mata kallo cikin hasken ƙatuwar fitilar cajin da ke haskaka ɗakin, wadda takanas Usmanu ya siyowa su Inna ita har da Baffah da tashi ta zama torch light a babban birnin garinsu, idan zai je da safe ya fita da su a cikosu da caji ya kawo masu, shiyasa basu rabo da caji kullum gasu da ɗan karen haske tamkar nefa. Kallon da Safwan ɗin yake yi mata ne yasa ta ɗago fuskarta tana yi masa hararar sama da ƙasa, sannan tace "Ka daina murna don kaji ance zan koma WALLAHi muddin ka sake taɓani idan na baro garin to ko gidan nan bazan dawo ba, tunda na gano suma ɗin ba sona suke yi ba komi nayi sai anga laifina" Safwan ya sauke wata ajiyar zuciya tare da ƙara matsowa daf da ita ya dafa bango da hannunshi ɗaya yayi mata rumfa, cikin tsoro ta yi saurin kallonshi tace "A gidan namu ma bazaka barni ba kenan?" Yayi wani murmushin gefen baki yace, "Ni ba a namu gidan kika so ki kasheni da soyayyarki ba? Ko kin manta abunda kika yi mani a gaban kowa wanda har yanzu gashi kin janyo budurwata ta gujeni?" Dije ta yi saurin rufe fuska tace, "Surayya ce tace dani inyi hakan idan naganka tare da budurwar, to ma ni ina ruwana da ita da har zansa ta gujeka?, Ka je cen ku sasanta abunku don ni yanzu gaba ɗaya ma daga kai har ita baku gabana" Ba shiri ya ɗora hannunshi saman leɓunan bakinta, cikin wata siririyar murya yace, "shiiiiiii! Bana son doguwar magana anan gidan, ki zo kawai ki bani abincin da aka ce ki bani yunwa nake ji" Ya ƙare maganar tare da langaɓe mata kai kamar wani yaro, Dije ta kalleshi cike da mamakinshi ta ce "Ka je gashi cen ka ci ni bana son salon yaudara don an ganni cikin gidanmu" Safwan ya yi saurin haɗe fuska ya ce "To shikenan bari inje in sanarwa da Inna kince in zuba da kaina" Yana gama faɗar maganar ya nufi ƙofa da nufin fita ta yi saurin shan gabanshi tace, "To Ni dai ka tsaya ai ba cewa na yi bazan zuba ba ko?" Ya yi saurin bushewa da dariya yace, "to muje ki bani kuma ga baki nake so idan ba haka ba yanzu inje in sanarwa da su Baffah" Dije ta yi saurin zuwa wajen kayan abincin tana zuba masa ta ce "shi dai mutum duk muguntarshi to ya kiyayi haɗa ɗiya da Uwayenta" Cikin dariya ya ce "Wannan kuma ai sai ki yiwa kanki wa'azi don ke kullum aikinki kenan haɗa ɗa da Uwatai, yanzu haka akanki ance kada ya kuskura ya sake taka gidan Ubanshi matuƙar ba tare da ke ya dawo ba, sai ki auna da tawa muguntar da taki wacece ta fi muni???" To reader's ku bashi amsa in Dijen taku ta kasa🤪 Akafta🤣 D/AUTA Ce✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *Ina baku haƙuri akan rashin mayar da reply ɗin da banyi ba na comments ɗinku😍amman ku sani na gani all kuma ngd gaba ɗayanku🙏🏻* *Lamba ta 51* Dije tace "taka muguntar ce mana, saboda miye ma Ni baka yi man ba?, Ai WALLAHi ka ci sa'ar Inna ta ce kada in koma yi maka wani abun da bai dace ba, da bazaka bar garin nan ba har sai na bar maka shaidar da zaka nuna a matsayin tarbar da nayi maka, wadda a kullum ka kalleta sai ka tuno da ni don kuwa tambon ba zai taɓa goguwa a jikinka ba" Safwan ya tako a hankali ya ƙaraso inda take zuƙunne tana zuba abincin, shima ya yi durƙuso ido cikin ido yake kallonta na tsawon mintuna, sannan cikin wata murya mai kama da raɗa ya ce "Ko yanzu mi ye marabar dambe da faɗa?, Ai tuni kin barni da taɓon da ya fi wanda kike da gurin yi mani a yanzu, tambon da nike da tabbacin har abada ba zai taɓa goguwa a cikin zuciyata ba, kin riga da kin sakar mani dafin da ya bi jikina ya mamaye ko'ina lungu da sak'o, a ganinki wannan tambon bai fi wanda kike ikirarin ki yi man ba a yanzu?" Dije ta turo baki ta ce, "Ai fa yanzu kam tunda an ganni gidanmu komi ma cewa za'a yi, amma da na yi sakacin da na bika kuma sai ka nunawa duniya cewa ni ɗin ba kowa ba ce bayan ƙaskantacciyar ƴar ƙauye, ka sani a shekarun baya ka yi nasara akaina wajen biyarka da na yi saboda daɗin bakin da ka yi mani, amman ka sani wannan karon daban da wancen cen, saboda cikin alƙawullan da ka ɗaukar mani ko ɗaya baka cika mani ba" Cike da mutuwar jikin da kalaman nata suka haifar masa ya yi jarumtar faɗin "Kamar wane da wane fa don ina son yanzu in tabbatar maki da gaskiyar duk abunda kika ji ya fito bakina" Dije ta jawo abincin gabanshi ta ce "Ka zauna da kyau ka ci abincin ni dai kada ƙafafuwanka su yi sanyi ace garinmu aka samu ciyon" Tana ƙare faɗar maganar ta miƙe ya yi saurin riƙo hannunta yace, "ina zaki je kuma muna firarmu mai daɗi?" Dije ta wurga masa wata harara tace, "abinci aka ce in baka Kuma gashi na baka to kuma ni yanzu zaman me kake so in yi anan?" Safwan yana rike da hannunta ya yunƙura ya miƙe tsaye, cikin mayen sonta da ke fisgarshi ya saka hannu biyu ya rungumota duka jikinshi, ta yi saurin zillewa amman sai da ya sake rungumotan har ƙamshin turarenshi mai daɗi ya daki hancinta, cikin wata murya da ita kanta batasan ya aka yi ta canza ba tace "Haba Malam ka daina abunda kake yi ba kyau fa, saboda akan wannan halin naka na dawo gida amman kuma gashi anan ɗin ma ban tsira ba, kai wai halan baka jin kunyar wani ya ganmu da wannan zunubin da kake ƙoƙarin aikatawa gareni kullum?" Safwan ya kai bakinshi saiti da nata ya sakar mata wani guntun kiss, ta yi saurin kaucewa tana goge bakin da hannunta ta ce "WALLAHi Malam kaji tsoron Allah Ni dai gaskiya nike faɗa maka" Ya yi saurin damƙe hannunta yace "tsoron ALLAHn kenan tunda ba wani waje naje nayi hakan ba, kuma mallakina ce ke ina da ikon yin duk abunda nake so da ke, saboda Allah ya bani damar in zo maki a duk lokacin da na so kuma inyi abunda naga dama" Dije ta zaro ido tare da rufe baki alamun firgici tace, "har da irin wannan abun duka?" Ya ɗaga mata kai tare da lumshe ido sannan ya buɗesu fes akanta yace, "har da shi har da ma kuma abunda yafi hakan ɗin duka" Dije ta yi saurin ƙwace jikinta ta ce, "Ni dai WALLAHI Allah ban son irin wannan lalacewar, don wannan ma idan wani ya ji ai sai kasa ayi mani kallon ƴar'iska, haka fa wani a tasha ya so ya lalaceni ALLAH ya taimakeni asirinshi ya tonu" Dirim! dum! dam! Haka ƙirjinshi ya buga ba shiri tare zuwan wani aringizon tashin hankalin da ya ziyartoshi, yanayin da ta ganshi yasa ta yi saurin shan jinin jikinta saboda tsoron kada ya kai mata duka, amman duk da hakan sai da ya damƙo gashinta iya ƙarfinshi yace "Me kika aikata man bayan idona? Wanene shi? Wa ya baki izinin fitowa gida ba tare da izinana ba? WALLAHi kinji na rantse kika yarda wani abu ya faru WALLAHi dake ki sani bazan taɓa yafe maki ba" Ya yi wurgi da ita har sai da kanta ya daku da gini ba shiri ta fasa wata uwar ƙara, amman ko takanta bai bi ba ya fice ɗakin fuuu ko da su Baffah suka fito sai jin ƙarar tashin Motarshi suka yi, cike da mamaki suke tambayarta me ya faru Cikin kuka take sanar da su cewa "Wai fa daga na faɗa masa abunda wani ɗan iska yaso ya yi mani a cikin tasha shine fa ya jawo mani gashi iya ƙarfinshi har sai da na bugu da gini, ya yi fushi ya tafiyarshi gashi ko abincin ma bai tsaya ya ci ba" Baffah da Inna da shi kanshi Usmanu suka ƙumshe dariyarsu, saboda kai tsaye sun gano cewa kishinta ne ya janyo yayi abunda yayi, Inna ta fara yi mata faɗan rashin dalili tace "Ai in dai baki bar baƙin surutunki ba to sai ya janyo maki watarana ya yi maki ɗan karen duka, ai gara da ya yi maki hakan sai gobe ki ƙara tunda ke bakinki sam baya da sirri kwata kwata" Dije ta yi fuuu ta wuce ɗakin Innar tana kuka saboda takaicin tafiyar da ya yi bai ci abincin ba, Usmanu ya yi sashenshi yana dariya a ranshi yace "Wannan yarinya ko yaushe zata yi hankali Oho?" Baffah da Inna Kam tsakar gida suka yada zango suna ta firar Dijen da shi Safwan ɗin, zuciyar inna cike da jin daɗin ganin Safwan ɗin yana mugun son Dijen tasu, saboda abunda ya yi yasa dukansu sun gano cewa ba ƙaramin so yake yi mata ba, haka ma yasan darajarta zai riƙeta amana ya bata kulawar da kowace mace take buƙata a wurin mijinta. Hankalinsu a kwance suka kwana saɓanin ita Dijen da ta kwana tana juye juye saboda haushinshi da take ji, uwa uba kuma ɓacin ran da ya nuna ba ƙaramin tsaya masa a rai ya yi ba, har sai da Inna ta tashi zaune tare da yadata da fitila ta kira sunanta, Dije ta yi saurin share hawayenta ta amsa tana sharɓar kukanta, cikin tausayinta Inna tace "Tashi ki zauna magana zamu yi" Dije ta yunƙura ta tashi tana ci gaba da goge hawayenta da hularta da ke hannunta, Inna tace "Ki natsu da kyau ki saurareni Dije, saboda ina son ki fahimci halin Mijinki ku daina samun saɓani da shi,Mijinki ba wai sonki ne baya yi ba halinshi ne hakan saboda ALLAH ya yoshi mutum mai zafi,ki yi ƙoƙari ki karanceshi ki kiyayi abunda kika san zai ɓata masa rai, haka ma ki so abunda kika fahimci yana so ko da ko ke bakya son abun a ranki, kuma ki sani Mijinki yana da ikon taɓa ko'ina na jikinki ba tare da ya yi laifi ba, asali ma har lada ALLAH zai bashi idan yayi abunda kike ganin kamar bai dace ba, ki tallafi kanki da Mijinki Dije ko da ko bayan bamu duniya ki yi ƙoƙari ki samarwa kanki wata daraja mau girma a wurinshi, yanda ko da ya auro wata ba zata fiki da komi a wurinshi ba, don WALLAHi wannan mijin naki da kike gani to kowace mace tana fatar ace ta samu irinshi, amman ke gaki ALLAH ya baki kyauta kina so ki yi wasa damarki" Dije ta share hawayenta tace, "Inna me yasa kullum baki ganin laifinshi sai nawa? Ko don ban sanar da ke cewa yanzu haka aure zai yi ba da wata abokiyar karatunshi" Inna ta zaro ido waje Tace. " aure??" Dije tace "Aure inna kuma har kashedi yayi mani akan idan na sanar da ita cewa Ni Matarshi ce sai ya yi man mugunta, kuma baki ganta ba ƴargayu da ita harda mota take tuƙawa" Inna ta yi shiru tana nazari sannan ta ce, "to ke ina ruwanki da motarta tunda dai dake da ita duk ɗaya kuke a wurinshi,don har ma kin fita saboda ke yanzu Matarshi ce ita kuwa budurwarshi ai ko a hakan ma ke matsayinki yafi nata nesa ba kusa ba, saboda haka ki yi ƙoƙari ki danƙe Mijinki a hannu ko da zata shigo daga baya to ke kin riga da kin fita matsayi a wurinshi, saboda haka ki ajiye shirme Dije ki kama Mijinki WALLAHi tun kafin wata mace ta yi maki sakiyar da babu ruwa akanshi, don haka ki bi abunki sau da ƙafa duk abunda yace ki yi idan yace ki bari ki bari sai ki ga a hankali ma ya daina wannan zafin kan da yake yi" Dije ta yi shiru tana nazari sannan tace, "to ai Ni Inna bama zama yake yi ba ai saboda yanzu haka da an ƙare bikin Surayya zai tafiyarshi to wace biyayya zan yi masa bayan bamu ma tare?" Inna tace "ko bangon duniya ya je ai dai Mijinki ne ko? Kuma kuma zai dawo kuma zaki yi masa biyayya ko bayan idonshi, saboda haka ki yi ƙoƙari kafin ya koma ya ji daɗin ɗan zaman da zai yi da ke, saboda ko da ya tafi ki barshi da kewarki a zuciyarshi yanda kullum zai yi ta fatar yayi sauri ya kammala karatun nashi ya dawo wajenki, amman idan kika yi sake har ya yi auren baki canza wannan halin naki ba to idan ya je mantawa ma zai yi dake ya yi ta Amaryarshi, ya barki sake da baki anan kina lissafin lokacin dawowarshi, wataƙila ma idan ya ji daɗi sai dai kiji ya ƙara wasu shekaru yace ba yanzu zai dawo ba" Dije ta yi shiru sannan ta ce "to yanzu idan nayi masa duk abunda yake son zai fasa auren ko kuwa??? " Inna ta yi saurin faɗin "Ina ruwanki da aurenshi ya auri matan duniya ma idan zai iya kedai ki bi hanyoyin da duk na sanar da ke ki samu ki samo kanshi, da kinyi haka shikenan kin gama da matsalar wasu mata cen, don shi da kanshi zai bayyanawa matan matsayin da kike da shi a wurinshi, kuma dole ma suma su shiga taitayinsu idan har suna son zaman lafiya tare da shi" Dije tace "aiko inna sai na ba ki mamaki don kuwa bazan taɓa bari wani ya sake jin tsakanina da shi ba, in dai har hakan shi zai kankaro mani darajata a wurin ƴanmatanshi" Inna tace "yawwa Dijeta ki gwada hakan da na sanar da ke ke da kanki zaki gano irin nasarar da za'a yi" Haka Inna ta yi ta ɗorata a hanya har taga Dijen ta fara gyangyaɗi sannan tace su kwanta sai da safe a ci gaba, Dije ta baje tana ta sharar baccinta mai cike da mafalkai iri iri na Safwan da budurwarshi Zee. Ko da safiya ta waye tun asuba Inna ta ci gaba da bata wasu darussan, Dije kam ta naɗe komi cikin ƙwaƙwalwarta har ALLAH Allah take yi ta fara aiwatar da su idan sun koma cen, fatanta kawai Safwan ɗin ya nunawa Zee irin yanda take da matsayi a wurinshi. Hhhhhh wasar zata fara kenan😅 Akafta🤪 D/AUTA CE *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *ALHMDLLH MUTANEN ƘARANGIYA BA ABUN DA ZAN CE DA KU SAI GODIYA, SABODA KUN NUNAWA LITTAFIN ƘAUNA FIYE DA YANDA NAYI TUNANI, TSAKANINA DA KU SAI SAMBARKA DA SON SO IRIN NA FISABILILLAH😍 ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU* *Lamba ta 52* Ko kafin Safwan ɗin ya zo tuni Dije ta yi wankanta tsaf ta shirya, cikin zuciyarta cike take da ɗokin zuwan na shi saboda ta bashi haƙuri akan abunda ta yi masa, duk da kuma wani sashen na zuciyarta cike yake da jin nauyin haɗuwarta da Hajiya Mama, saboda yanda ta kamo hanya abinta ba tare da ta yi sallama da ita ba, bayan ta gama kammala duk abunda zata yi ne tace da Inna tana so ta je ta yi sallama da Inna Gambo, Inna tace ba inda zata je har sai Mijinta ya zo, ta ɓata fuska tace "Inna fa sauri zan yi inje in dawo don kada ya zo yace sauri yake yi ba zai bari inje ba" Inna tace "sai ki lallasheshi ai tunda kina son ya barkin" Suna cikin wannan diramar ne suka jiyo ihun yara da saukar mota a ƙofar gidan, Dije ta diririce tace "Kinji ko Inna gashi nan ma har ya zo ban tafi ba" Inna ta maka mata wata uwar harara ta ce, "da kin je ai da zai ɗaukemu mutanen banza in ya zo bai taradda ke ba.." Sallamar Usmanu da shi Safwan ɗin ne ya katse maganar Inna ta yi saurin faɗawa ɗaki ta sako hijabi ta fito suna gaisawa, Dije Usmanu yana baza masa tabarma da nufin ya zauna yace "Ai da ka barta tafiya zamu yi saboda kada mu yi dare sosai kafin mu isa Gombe" Usmanu ya kalli Inna yace "Ina Baffah su yi sallama to don naga baya gidan??" Inna tace "yanzu nan zaka ganshi don bai daɗe da fita ba" Usmanu ya baza tabarmar Safwan ya zauna yana kallon Dije dake zaune saman turmi tana yankan akaifa, don tun da ta gayar da shi ta sha jinin jikinta. Baffah ya shigo cikin sauri yana yi wa Safwan Barka da zuwa bayan sun gaisa ne Baffah ya yafito Dijen ta taso jiki a sanyaye saboda yanda take jin gabanta yana faɗuwa tun lokacin da ta yi ido biyu da Safwan ɗin, saboda wani sihirtaccen kallon da ya jefeta da shi, ba shiri ta yi saurin kawar da idonta, shiyasa ko da ta zo wurin Baffan bata bari sun haɗa ido ba ta zauna gefen Baffan, Baffah ya kalli Safwan yace "Bakina ba zai gaji ba wajen baka haƙuri akan ƙurciyar Dije, don ALLAH ka ƙara lurar da ita akan duk abunda ka ga ta yi na rashin kyautawa, kai kuma ka ji tsoron Allah ka riƙe matarka Amana, sannan ka yi mata uzuri akan abunda ta aikata a bisa kuskure" Safwan ya sunkuyar da kanshi yace, "ba komi Baffah insha ALLAHu komi ya wuce kuma ma hakan bazata sake faruwa ba, adai ci gaba da yi muna addu'a kawai saboda addu'arku tana da tasiri sosai garemu" Cike da jin daɗin zancenshi Baffah ya kalli Dijen yace "ke kuma ki yiwa Mijinki biyayya duk abunda ya ce dake ki yi kar kiyi masa musu ki amince, saboda in yasan abun nan ba mai kyau bane kema kinsan ba zai ce ki aikata ba, don haka yi nayi bari na bari shine halin matayen kirki, saboda haka kiyi ƙoƙari kiyi koyi da halin mahaifiyarki don kin fi kowa sanin yanda take zama dani, saboda haka kema ki koya ki zauna da Mijinki cikin girmamawa, ALLAH ya yi maku albarka ya baku zaman lafiya a cikin zaman aureku" Daga Dijen har Inna har shi Safwan ɗin da Usmanu da ke tsaye sai "Ameen Ameen" suke faɗi, Inna tace ta je ta ɗauko Hijabinta sabo da ta bar mata, Safwan ya ciro kuɗi a masu dama ya ajiye gaban Baffah sannan ya miƙe, cike da jin daɗi Baffah yace "Haba haba ai kuma hidimar tayi yawa gaskiya, ka barshi kawai ALLAH ya sa albarka" Safwan ya nuna sam bazai karɓa ba dole Baffah ya dawo godiya tare da sanya alkhairi, Dije ta shiga ɗaki ta ɗauko Hijabin Innar da ta bata sabo fil,, Usmanu ya ɗauki manshanun da Baffah ya shigo da shi cike da galam ya je ya saka masu a mota tare da taimakon Safwan ɗin da ya bi bayanshi ya buɗe masa Boot ɗin, Dije ta sako hijabin tana ɓata fuska ta nufi sashen Hansai suka yi sallama, sannan ta fito ta kalli Inna tana matsar ƙwallah tace "Inna yanzu shikenan bazan je inyiwa Gambo sallama ba? Ga shi ma gidan kowa ma baki barni na je ba" Inna ta ce "ki tambayeshi idan ya amince ku je tare da shi ma sai ya gaisheta" Dije ta fito Inna da Hansai da Baffah suka biyo bayanta suna yi mata ALLAH ya kiyaye hanya, sai da Baffah da kanshi yace da shi don ALLAH ya biya da ita ta yi sallama da Inna Gambon, cike da jin daɗi ta shige motar tana yi masu bye bye suna yi mata har suka bar ƙofar gidan, kai tsaye Safwan ya nufi gidan Maigari bayan sun gaisa sama sama ya yi masu alkhairi suka nufi gidan Duduwa tana nuna masa hanya, yara suka biyosu buuuu! A baya suna yi masu Allah ya tsare. Bayan sun gaggaisa da Gambon ne itama ya yi mata alkhairi sannan ya fita, cikin barkwanci ta dinga tsokanar Dijen, sannan ta shiga ɗaki ta ɗauko wani abu a gorar lacasera tace ta sha rabi ta ajiye rabi daga baya ta shanye, Dije tana dariya ta kwankwaɗe abun duka ta yasar da gorar tana goge baki tace "Haka kawai ki saka man wata doka cen marar tushe?, To yanzu dai na shanye sai inga kuma wani fi'ilin da za'a yi man" Ta ƙare maganar tana dariya, Gambo riƙe da baki tace "Ni ai tausayinki nake ji shiyasa kika ji nace ki raba biyu, saboda takanas na dafa maki shi da hannuna dalilin da yasa na yi ta aiken ki zo mu yi sallama, amman tunda ke jaruma ce ALLAH ya baki ikon jurewa" Dije tana dariya tace "Na shiga uku Gambo me yake sakawa ne???" Gambo ta ce "idan kun zo kwanciyar auren zaki gane da kanki" Dije ta ƙyalƙyale da dariya tace "Oh Ni Dije ai ke Gambo ni ba wata kwanciyar aure da nike tsoro, tunda asali ma Ni ba a ɗaki ɗaya muke kwana ba balle har ayi kwanciyar" Gambo ta maka mata wata uwar harara ta ce, "to wannan karon WALLAHi kika gudo sai munyi maki bankaɗa a garin nan" Dije zata yi magana taji horn ɗin motar da ƙarfi, ta fito tana dariya Gambo ta biyota a baya har wurin motar, in da suka taradda Balan Duduwa tsaye da Safwan suna magana, sai zuba fadanci yake yi yana godiya, wanda ba'a raba ɗaya biyu akan kamar ma kyauta ce Safwan ɗin ya yi masa yake godiya, Gambo tace da Dijen "Kada dai ki mance ki tambayeshi abunda kika taɓa tambayata ko kin mance in tuna maki?" Dije ta bud'e motar ta shiga ta zauna tana dariya tace,, "ai kuma yanzu wannan ya wuce Gambo tunda wadda ma aka yi abun kanta yanzu har ta mance da ma an taɓa yimata laifin, to ni kuma miye nawa na bin diddigi yanzu? ALLAH dai ya bamu haƙuri dukanmu" Gambo tace "Ameen amman ya kamata kema ki tambayeshi saboda akwai ƙaruwa a ciki idan kin sani" Dije tace "Tom naji Ni dai matsa kada mu tureki ki yi kuka" Gambo ta dungure mata kai tace "kece dai wadda zaki yi kukan amman nikam me zai haɗani da kuka yanzu?? Sai dai kuma in na farin ciki idan ina da rabon ganin yaran da zaki haifowa" Haka suka rabu Dije tana ta ƙyalƙyala dariya suka baro ƙofar gidan suka kama hanyar fitowa garin, Safwan yana kallonta sai dariya take yi ita kaɗai, sai cen kuma ta fara matsar ƙwallah cike da mamaki yace "Kukan fa?" Tace "WALLAHi kamar kada in baro garinmu gashi ma kowa banje gidanshi ba tunda na zo" Safwan ya yi murmushi yace, "to ai gara da baki je ba saboda kada zunubin ya yi maki yawa, kin zo ba izinin miji kuma ki kwashi ƙafafuwa ki fara bin gidaje, ai sai ki janyo Mala'iku su yi ta aikin rubuta yawan zunubinki" Dije ta share hawayenta tace, "ai dai yanzu ka yafe man ko?" Ya yi yar dariya yace, "na yafe amman Ni ma zan fanshe wahalar da aka sakani, sannan Ni ma in nemi yafiyarki idan na fahimci abun zai janyo man aljanun tekun banbaradusa" Dije ta yi saurin kallonshi tare da rufe bakinta tana dariya tace, "WALLAHi ba ruwana in har su mulƙutus baraƙus suka jiyoka, don tsaf zasu iya yin langaɓu da kanka a bakin tekun bangon duniya" Ba shiri Safwan ya yi dariya saboda ba ƙaramar dariya ta bashi ba, amman ya waske yana yi a hankali don maganar da ta yi ce tasa ya tuno da labarin da wani ɗan Maigarin ya bashi nata, lokacin da ta yi ƙaryar aljanu a ƙofar gidan Maigari, musamman abunda ta yi wa Bafade ba ƙaramar dariya yake bashi ba idan ya tuna. Ganin kamar dariyar taƙi ƙarewa ne saboda murmushin kawai yake yi yana dariyar a hankali, shi yasa ta ɓata fuska tace "Wai yau kai ne kake dariya haka? Daman kana da fara'a shine kullum kake faman haɗe fuska??" Safwan ya ci gaba da dariyarshi ba tare da yace da ita komi ba, itama ta yi shiru tana kallon gefen titi har suka shiga babban birnin garinsu Dijen, har sun wuce wani wuri ya dawo baya yana kallon bakin titin yace "Ga mutuniyarki cen ta fito ko yau bazaki ci ƙosan ba? Ga wani abu cen ma tana suya da alamu shima zai yi daɗi" Dije ta kai kallonta ga mai soya ƙosan dake bakin titi tace, "me ye abun da take soyawar? ba doya da ƙwai ba ce nake hangowa?? " Safwan ya gimtse dariyarshi yace, "itace jirani bari in zo" Ya fice Dije ta bishi da kallo tace, "Ni da ma ka barsu don ko ka saya ba ci zanyi ba ma" Tana kallonshi har ya dawo da ledodin ya buɗe gefen da take ya ɗora a saman cinyarta, ta yi saurin zabura saboda ruwan team ɗin da suka zubar mata a jiki, sannan ya rufe ya zagayo ya shiga ya tada motar, ta bishi da kallo tare da ɓata fuska tace "Me nayi maka da zaka ƙonani da tea??" Yana kallon gabashi yace, "ke fa na siyowa duka ko baki so?" Dije ta ɗauki kayan ta ajiye a bayan seat tace , "Ni bana sha'awar cin komi a ƙoshe nake" Yace "ok to tunda kin ƙoshi Ni ki bani zan ci ai" Ta yi saurin kallonshi tace, "da gaske kake yi zaka iya ci?" Ya waigo ya kalleta yace, "to me zai hana yana da wani abun ne?" Ta yi saurin faɗin "a'a" Yace "to oya a fara bani ga bakin nawa yana jira" Dije cike da mamakinshi ta ce "me zaka fara ci a ciki" Ya ce "abunda kika san kin fara ci farkon lokacin da muka fara siyen irinsu" Dije ta yi saurin kallonshi tace "ƙosai shi za'a baka?" Ya ce "Yes! In jira ko rowa za'a yimani ne in haƙura?" Ta sauke tagumin da ta yi tace, "ALLAH ya baka haƙuri ai abun bai kai cen ba, don kare da kuɗinshi ba za'a hana shi shan rubutun malam ba" Ya yi saurin kallonta yace "au haka ne?" Tace "eh kam yanda kowa ya siya ya sha haka shima za'a bashi tunda har da kuɗinshi a aljihu" Ya yi shiru sannan yace, "nyc! Kice haka abun yake? to in fa shi malamin yaki siyar masa fa kuma bayan ya karɓe masa kuɗin?" Ta yi saurin faɗin "Bama zai ƙi siyarwa ba tunda dai ba kyauta aka ce ya bayar ba, sai da aka bashi kuɗi ya karɓa aiko ya zama dole ya bada ko yana so ko baya so" Ya yi saurin faɗin "woww! Ki ce Ni nawa shan rubutun zai zo man cikin ruwan sanyi" Tace "tabbas amman ka gwada ka ga in har kana shakku a maganata" Ya yi saurin kallonta tare da yin wata siririyar dariya yace, "hmmm! ALLAH ya bani sa'a to" Tace "Ameen" Hmmmm nima dai nace Ameen ɗin don tsuntsun da ya ja ruwa ..............😝ku ƙarasa mata ni dai na yi nan🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️ Not edited Akafta😹 D/AUTA Ce✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *Sai kun yi haƙuri dani kwana biyun nan saboda uzurora da suka sha kaina, amman insha ALLAHu zan ƙoƙarta in yi maku ko ba yawa, sai dai ina son ku yi man uzuri idan kuka jini shiru ba ba daga gareni bane kamawa ta yi* *Lamba ta 53* Haka ya buɗe baki tana ta bashi ƙosan yana ci yana tuƙinshi hankali kwance yana jin kanshi cikin wani sabon nishaɗi, don ko tea ɗin ba ƙyama ba wata damuwa ya karɓa ya dinga shan abunshi, ƙarshe ma itama sai da ya tilasta mata ta ci kaɗan sannan ta buge tana ta bacci abunta, don kuwa tun tana kallon gefen titin tana ta wassfa kunya zata ji idan ta je wurin Hajiya Mama, don sai yanzu take hango rashin dacewar abunda ta aikata, saboda ƙiri ƙiri ta haramtawa kanta tsayawa ayi bikin Surayya da ita, tana cikin tunanin ne taji wata muguwar kasala ta sauko mata a jiki, sai gata da jera hamma kala kala Safwan dai sai tuƙinshi yake yi yana kallonta ta gefen ido har baccin ya yi awon gaba da ita. Tun daga babban birnin garinsu take ta sharara bacci mai shegen nauyi har ta kwashi kusan awa biyar bata falka ba, shima tun yana ganin baccin gajiya ne take yi har ya fara tsarguwa da baccin nata, dole da suka je wani gari ya sauka ya tada ita cikin mayen baccin suka ci abinci suka yi salloli sannan suka sake ɗibar hanya. Tafiya tana miƙawa ta ci gaba da baccinta har suka kai Gombe bata san sun kai ba, saboda misalin sha biyun dare ne har da wasu mintuna sama suka shiga garin, daman yasa anyi masu booking ɗin wani hotel suka sauka da nufin da safe su kama hanyarsu ta zuwa Yola. Shigarsu masaukin ke da wuya ya faɗa toilet ya yo wanka ya fito daga shi sai trouser yana goge ruwan da ke jikinshi da towel, ya kalleta a rakuɓe bakin gadon tana ta baccinta, cike da mamakin wannan bacci da take yawan yi ya duƙo ya sumbaci ƙwayar idonta da karan hancinta, amman ko motsi bata yi ba bale tasan me yake yi, ya saka hannu biyu ya tallafota jikinshi ta faɗo masa yaraf kuma still har lokacin baccin take yi, cikin fargaba ya ɗago fuskarta yana ƙare mata kallo sannan ya kai bakinshi cikin nata tare da jarumtar tsotso halshenta, sai gata da saurin buɗe idonta da suka yi jawur saboda baccin da ta sha ta saukesu duka a kanshi, ba shiri ta ƙwace daga gareshi tana ƙarewa ɗakin kallon sannan ta dawo da kallonta gareshi tace "Safiya ta waye ne?" Ya yi ƴar dariya ya ce "Zata waye dai yanzu insha ALLAH, ki je kiyi wanka kiyo arwallah ga toilet cen ki zo mu yi sallah mu ci abinci" Dije ta dafe goshinta saboda juyawar da taji kanta yana yi sannan ta nufi inda ya nuna mata ɗin, tsawon minti sha biyar tana toilet ɗin har sai da ya gaji da jiranta ya leƙo sai gata cikin bahon wanka tana bacci, da alama ma ko wankan ma bata fara yi ba, ya tako a hankali zuciyarshi sai nazarin dalilin wannan baccin nata yake yi amman ya kasa gano mafarinshi, ya ɗauki tsawon minti biyar tsaye a kanta yana ƙarewa cikar ƙirjinta kallo, ya lumshe ido tare da sauke ajiyar zuciya ya ranƙwafo ya saka hannu ya shafosu duka biyu ta zabura ba shiri, tare da saurin buɗe idonta cikin firgici da tsoron ganinshi a kanta, ta yi saurin ƙanƙame jikinta tana ɓata fuska, da wata murya mai cike da kasala tace "Don Allah ka je ni dai yanzu zan yi wankan in fito?" Ba shiri ya yi guntun murmushi ya yi kamar bai jita ba ya fara ƙoƙarin yi mata wankan tana zillewa, saboda inda yake son ya taɓo ta rufe da hannunta ta dunƙulewa waje ɗaya, ganin zata ɓata masa lokaci ne ya sake yin wata arwallah ya fice yana faɗin, idan bata yi sauri ta fito ba har ya dawo to shi zai yi mata wankan da kanshi, ai kuwa jin haka yasa a gurguje ta yi wankan ta fito ɗaure da towel iya cinya ta kwaso kayanta tana raɓe raɓe jikin gini. Fitowarta yasa ya yi saurin ɗauke kanshi saboda baya son sake wata arwallah bayan wadda ya yi a yanzu, saboda yanayin da yake ji game da ita abu kaɗan ne zai janyo masa shiga wata sabuwar duniyar, ta mayar da kayanta suka yi sallolin da basu yi ba, bayan sun ƙare ne ya sata suka yi nafilar godiyar ALLAH, tare da zubawa kansu da aurensu addu'o'i kala kala, Dije iyakacinta cewa "Ameen" saboda haka kawai ta tsinci kanta cikin wani tsoron da bata san ko na minene ba, uwa uba yanayin da take jin jikinta yasa bata da wani kuzarin kirki, don ko abincin da abun shan da aka kawo masu ma da ƙyar taci har sai da taga zai yi mata ɗuren dole sannan ta ware ta tsakura, bayan sun kammala ne Dije ta je ta wanko bakinta ta haye gado tare da duƙunƙunewa cikin dogon hijabinta. Shima cikin ɗoki ya kimtsa sannan ya hawo gadon shima ya tura kanshi cikin hijabin nata ta ƙarfi, dole ta yi saurin miƙewa zaune tana kallonshi ta ɓata fuska tace "Bacci nike ji fa?" Ya yi saurin cire mata hijabin yace "to cire wannan kayan zafin nima shi nike ji, saboda haka ki kwanta mu yi abunmu kawai" Dije ta yunƙura zata sauko ya yi saurin riƙo hannunta yace, "ina zaki je kuma?" Tace "ƙasa zan sauka nafi jin daɗin kwanciya a ƙasan" yace "Ok to mu je ɗin nima daman na yi niyyar kwanan a ƙasan" Dije ta zumɓuro baki tace, "to ka je cen Ni in kwanta a nan ɗin" Ya yi murmushin gefen baki yace, "ai kuma na gama kwanan tuzurantaka tunda har ina tare da ke" Dije ta yi saurin kallonshi ta ce "Ban gane ba me kake nufi?" Yace "ina nufin a yau zan san wacece matar da na aura? Kuma wacece Dijen Baffah?don naga idan ban yi da gaske ba so kike yi ki sakani shiga uku" Ta yi saurin faɗin "shiga uku kamar ya?" Ya janyo hannunta ya ɗora a kan jarumarshi da ta ke miƙe samɓal yana faɗin, "kin jita ko? To a haka zata kwana matuƙar ba'a bata abincinta ba" cike da firgici tayi saurin janye hannunta tare da saukowa gadon da ƙarfi,tana yi masa kallon mai cike da mamakinshi tace "Ashe haka kake daman??" Ya sauko ya nufota yana faɗin "ai har na wuce haka ɗin in kuma kina shakku to yanzu zan tabbatar maki da gaskiyar komi" Dije tana ja da baya yana biyota sai ga wasu hawaye ƴanmatan hawaye suna kwaranya akan fuskarta tana faɗin, "yanzu don ALLAH ni ina nasan inda zan samo abincinta?" Safwan cikin wani tsauƙin wutar sha'awarta da ke fisgarshi ya yi saurin damƙota ya haɗata da jikinshi, cikin marairece ya ce, "ke fa kika ce kare da kuɗinshi dole ne a bashi rubutunshi ya sha, ko kin manta kince ko malami yana so ko baya so dole ne sai ya bada tunda ya karɓe kuɗin??" Dije ta zaro Ido jikinta yana rawa tace, "to kai karen ne da zaka kawo wannan maganar yanzu?" Ya yi guntun murmushi yace, "idan dai akanki ne to ki ɗauka na ma fi ƙaren matsala, saboda haka ki taimaki kanki kada ki baiwa kanki wahala a banza, don wannan karon bazan taɓa ɗaga maki ƙafa ba haka kawai in kwana ina haɗiyar ƙwayun Bature, tunda dai har ina da maganin da yafi shan ƙwayar a kusa dani to ba shakka dole in mori aurena" Hawaye suna zuba akan fuskarta tace, "mi kake nufi? WALLAHi ka san dai ni ban san komi ba akan hakan" Ya fisgota jikinshi da ƙarfi ya fara cire mata kayan jikinta duk da tirjiyar da take yi, cikin kuka ta ce "Tace don ALLAH kada ka cutar da ni" Cikin wata maƙalalliyar muryar da ta sha jaraba ta ƙoshi ya ce, "to ki taimaki kanki kawai idan bakya son in wahalar da ke" Sai da ya cire komi nata tass! sannan ya fara aika mata da saƙo tun a tsayen, Dije ta fara ruɗewa tana roƙonshi ya yi haƙuri duk abunda yake so zata yi masa, jin hakan yasa ya janyota zuwa kan gadon shima ya yi tik! cike da jin wani masifar tsoronshi ta rufe ido tace "Na shiga ukuna ni kam yau naga bala'i" Ya kanne dariyar da ta so bashi ya janyota jikinshi tana tirjiya ya fara mamayeta da kalolin soyayyarshi, tun tana kuka har ta yi shiru tana sauraren saƙon da yake aikawa zuciyarta da sassan jikinta, jikinta ko'ina sai rawa yake yi gogan kam wani kalar nishi kawai yake fitarwa saboda yanda yake bi da salo salo, cikin ƙwarewa yake ta aikin lashe ko'ina na jikinta tamkar wane maye. A kiɗimewa ya ke tsotse twins ɗinshi da yake masifar so a jikinta, Dije tsoron Allah ya kamata sai faɗin take yi "Wayyo Uwata wayyo Ubana wayyo ALLAHna Ni Dije yau ina ganin abunda ya fi ƙarfina, wayyo don ......." Bakinta da ya cafke ne yasa ta yi shiru dolenta cikin wannan salon ya mamayeta ya nufi ƙofar babban birni fadarta, sai dai jin wajen a rufe ruf! ba hanya yasa shi ƙara yin ƙaimi wajen samun hanyar ɓullewa ta ƙarfin tsiya, saboda yanda yake ji a tattare da ita ko da bindiga aka ce ya barta a wannan lokacin to sai dai a kasheshi amman ba zai iya ɗaga mata ƙafa ba,, cikin nasarar cin yaƙin ne ya fasa bututun maji daɗinta ya afka iya ƙarfinshi, Dije kam ziyartar wata uwar azabar da ta sauka cikin ƙwaƙwalwarta tasata kurma wani uban ihu, ya yi saurin toshe bakinta da nashi cikin kiɗimewa da gushewar hankali a jikinshi, sannan ya fara kai da komo cikin natsuwa kafin ya fara HAUKACE mata, don kuwa zaƙin ɗanɗanon ni'imarta da yake ji yana ratsa jikinshi da ƙwaƙwalwarshi yasa ya ruɗe mata ya gigice, ya rasa tunaninshi kwata kwata ya dinga haƙar gonarta ba ji ba gani. Bata da damar yin ihu ko wata doguwar magana ya riga da ya toshe bakinta da nashi, amman dole da azaba ta kai mata geji ta fisge bakin ta ƙarfin tsiya ta dinga ihu da kururuwar neman agaji, shima kanshi ihun yake yi yana surutai marasa kan gado, waɗanda idan za'a titsiyeshi bai san ma me yake faɗa ba. Safwan kam ya haukace iya haukacewa akan sabon lambun Dijengalar Baffah sai kwasar ni'imarta yake yi yana sambatu, don kuwa ya ɗauki tsowon lokaci yana abu ɗaya har sai da yaga ta some masa ne sannan ya saurara mata dole ba don ya so ba, jikinshi yana rawa ya ɗebo ruwa ya zuba mata sannan ta dawo hayyacinta tare da fasa wata uwar ƙara, saboda zabura da tayi yasa ta ji wani masifar zafi ya ziyarci ƙasanta, dole ya koma aikin lallashi amman ita kam kukanta kawai take yi iya ƙarfinta tana kiran Baffahnta da Innarta akan su taimaketa, sai dai ya kasa controlling kanshi akanta ya sake mamayarta ya koma faɗawa fadar gwamnatinta, ai ko ta ƙara fasa wata ƙarar saboda azabar da ta sake ziyartarta, haka suka cenye wannan daren yanata abu ɗaya, tun tana da ƙarfin yin kukan har ta kai ma ko muryarta bata iya fitowa, sai zubar hawayen kawai take yi murya ta disashe, bai fahimci irin ɓarnar da ya yi ba har sai da ya gama shan shagalinshi ne ya ga jini malale akan gadon tamkar an saka wuƙa an yankata. Sannan hankalinshi ya tashi cikin rawar jiki ya zo zai tallabeta ta buge masa hannu da sauran ƙarfin da ya rage mats, ta kalleshi da kumburarrun idanuwanta tace "Ka zo ka ƙarasa kasheni kawai tunda daman cen gurinka ka rabani da rayuwata ne" Safwan ya diririce ya ruɗe ya rasa ya zai yi ya taimaketa, cikin sauri ya je ya yi wanka ya yi sallah agurguje sannan ya ja key ɗin Motarshi ya fice, Dije kam sai uban kuka take yi tana ALLAH wadai da hali irin na Safwan ɗin, a zuciyarta ta ce _"Daman irin wannan biyayyar ce Inna kike cewa in yi?? Ashe haka aka yiwa Jummala bayan zaluncin har da su ɗauri da igiya?? cabɗi to WALLAHi da nasan haka ne WALLAHi ALLAH in za'a kasheni bazan biyoshi ba, ashe Gambo wannan shine kwanan auren da kike faɗa? WALLAHi baku yi man adalci ba dukanku, yanzu da ya kasheni ai da shikenan kowa sai ya ji daɗi"_ Haka ta yi ta zancen zucinta tana kuka har taji buɗewar ƙofa an shigo, sallamar wata mata ne da ta jiyo yasa ta yi saurin zabura da nufin ta ɓoye, sai dai dole ta koma ta kwanta tare da fasa ƙara saboda wata azabar da ta yi mata sallama, cikin sauri matar ta ƙaraso tana faɗin "Sannu kinji sannunki" Dije ta rufe idonta ruf saboda tsabar kunyar da ta kamata, tare da jinjinawa rashin kunyar Safwan ɗin da ya iya bari har wani yasan da wannan abun kunyar da ya aikata mata, da ƙyar matar ta shawo kan Dije ta bari ta fara dubata, nan take ran matar ya ɓaci amman ta yi ƙoƙarin ɓoye komi ta lallaɓi Dijen ta samu ta kaita toilet da ƙyar, ta gasa mata jikin Dije tana ihu tana kuka sannan ta yi mata ɗinki kamu ɗaya, saboda DAGARGAZAR da Safwan ɗin ya yi wa matuccinta, sannan ta taimaka mata ta yi wanka ta yi arwallah ta riƙota suka fito, Safwan ɗin ya shigo da ƙatuwar leda ya ajiye yana faɗin "Sannu ya jikin?" Dije ta yi banza da shi matar ta karɓi ledar ta fito mata da doguwar riga ta saka sannan ta bata hijabi, a zaune Dije ta yi SALLAH duk da ko a hakan ba ƙaramar azaba take ji ba, tana ƙarewa matar ta bata tea mai zafi ta sha tare da magunguna ta taimaka mata ta kwanta sai bacci. Matar ta kalli Safwan ɗin tace, "A gaskiya Oga ka ɗagawa yarinyar nan ƙafa WALLAHi ta ji rauni sosai" Safwan ya shafa kanshi yace, "ba komi za'a kiyaye yanzu dai ba wata matsala ko?" Ta kalli Dijen cike da tausayi tace, "Eh Babu amman tana buƙatar kulawa sosai" Yace "wannan ba damuwa bane insha ALLAHu na gode sosai da taimakonki" Suka fita tare ya biyata kuɗinta ya dawo zuciyarshi fes cike da wani masifar sonta da yake ji yana ƙara nutso ta ko'ina cikin jikinshi da zuciyarshi, uwa uba ganimar da ya kwasa a jikinta ya janyo mata wani girma da ƙima a idonshi, cike da ɗokinta ya zauna kusa da ita yana shafo gashinta da fuskarta yace "can't wait loving you fruits loops forever and ever, you are key to my lyf my popster " Ya kaiwa bakinta wani ƙaramin kiss ya sake cewa, "sugar lipsy, I love you so much sweet bab life partner, your star shine in my heart chocolatynah, you are my final choice Khadija, saboda bazan taɓa iya haɗa soyayyarki da kowace mace a zuciyata ba, kece farin cikina sanyin idaniyata mai sakani natsuwar da a tara mata dubu ba zasu kama ƙafarki wajen tarin ni'imomin da ALLAH ya tattara ya baki ke kaɗai ba" Haka ya susuce yana ta suburbudo zantukka, Dije kam sai sauke ajiyar zuciya take yi saboda kukan da tasha, cikin jin daɗi ya raɓa gefenta ya rungumota a hankali shima sai baccin. Ƙarar wayarshi ce da ta fara ɓurari ta janyo suka farka dukansu, cikin sauri ya sauko ya ɗauki wayar jin muryar Lawi yasa ya fara faɗin "Abokina ya dai?" Lawin ya ce, "zaka shigo in jiraka mu je Asibitin dubo Zee ko ko? Don fita nike son yi"" Safwan ya zaro ido waje yace, "me ya sameta?" Lawi yace "kana nufin ba ka san an yi admitting ɗinta Asibiti ba?" Safwan ya dafe kai ya ce "subhanllah yaushe?" Lawi yace "Oho ni ma Kamal ne ya sanar dani" Safwan ya yi shiru sannan yace, "ALLAH dai yasa ba nine sila ba? don ta sanar dani idan naji mutuwarta to son da take yi man ne ya janyo ajalinta, kuma Ni a yanzu hankalina yafi natsuwa da matata, ka gayar da ita kawai Abokina gaskiya ba zan je ba ALLAH dai ya bata lafiya" Lawi ya ce "ina alƙawarin auren har ya watse kenan?" Safwan ya kalli Dije da ta yi kamar bacci take yi yace, "matata ta isheni Abokina itama ta yiwa iyayenta biyayya kawai, na so in zo in kawo Khadijah wurinsu Mama to bata da lafiya ne, amman insha ALLAHu kafin in koma school zan kawota su gaisa" Yana ƙare maganar ne ya kashe wayar zuciyarshi cike da tunanin halin da Zee take ciki, wani sashe na zuciyarshi yana Ƙawata masa son zuwa ya dubota, wani sashen kuma yana nusar da shi ya barta kawai ta yiwa iyayenta biyayya, don ko da ya aurota ba wani kulawarshi zata samu ba matuƙar Dijen Baffah tana kusa da shi. Yana cikin nazarin ne Hajiya ta kirashi,ganin sunanta yasa gabanshi ya faɗi ba shiri, ya gayyato natsuwar dole sannan ya ɗaga wayar cikin ɗar ɗar sai ko ya ji tana cewa "Kuna ina ne yanzu?" Safwan ya yi saurin kallon Dije yace, "muna Gombe Hajiya mun kusa ƙarasowa" Tace "to ka yi gaggawar kawo man yarinya tun kafin ka sake ɓat man rai, umurni nike baka ka kawota da sauri ita ake jira" Tana ƙare Maganar cikin kausasa murya sannan ta kashe wayar, kafin ya tantance abin yi ya ji muryar Dije tana faɗin, "don ALLAH ka kaini gida na fasa zuwa Yolar ni dai" Safwan ya yi saurin kallonta ya ce "Ita Yolar me ta yi maki?" Ta maka masa harara tace, "Ni dai gidanmu nike son komawa kawai, na amince ka je ka auri budurwarka WALLAHi ba zan zauna ka kasheni ba" 😍😍😍 Akafta😅 D/AUTA Ce✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *Naga comments ɗinku all kuma na gode🙏🏻* *Lamba ta 54* Safwan ya zaro ido waje yace, "kashewa??, To in na kasheki ni in shiga ina?" Dije ta murguɗa masa baki tace, ,"so kake yi in zauna ka kassarani kenan? ai WALLAHi ni kam bana iya biyayya a wannan baƙin lalacin da ka iya, ƙatoto da kai ko kunya baka ji ka rufe ido ka yi wannan muguwar ta'asa dani, WALLAHi itama innarmu don bata san halinka bane shiyasa ta matsa mani akan in yi maka biyayya" Safwan ya yana dariya ya dawo kan gadon ya kwanta suna facing ɗin juna tare da ƙura mata idanuwa yana murmushi, Dije kam sai harararshi take yi sama da ƙasa tana murguɗar baki, hakan da take yi ba ƙaramar dariya ta ba shi ba, cikin ƙumshe dariyar yace "Wai duk wannan hararar ni ake yiwa ita?" Dije ta ce "to da dawa nake halan?" Ya ɓata fuska tare da cewa, "kenan har yanzu da sauran renin tsakaninmu kenan? Bayan kuma Baffah da kanshi kinji yana faɗin ki yi man biyayya" Ta zumɓuro baki tace "to ai kai ka janyo renin? Tunda har baka ji kunyar yi man abunda ka yi man ba " Yace "ok haka ne ko? To bari in cire tausayinki da nake ji tun da bakin tsiwar taki har yanzu bai mutu ba" Ya janyota jikinshi ta fasa ƙara saboda zafin da take ji, amman duk da hakan bai hana ya fara yamutsata ba cikin wani sabon salo, Dije tana tureshi tare da kai masa duka amman bai hanashi komawa cikin jikinta ba, tana ihu tana kururuwar neman agaji saboda uwar azabar da take ji tana ratsa ko'ina na jikinta, shi kam ya riga da ya lula cikin hazon gajimare ko gabanshi baya gani bale bayanshi, banda ihun daɗin da yake yi da surutai ba abunda yake fitowa bakinshi sai saka mata albarka kala kala da yake yi, tare da zuba mata ruwan kalaman da ko da wasa bata taɓa tsammanin za su iya fitowa a bakinshi ba. Sai da ya tabbatar da gamsuwarshi tare da samun nutsuwa a jikinta sannan ya koma lallashinta tare da kalamai masu daɗi na ban haƙuri, Dije kam banda kuka ba abunda take yi cikin kukan ta yunƙura ta miƙe da ƙyar tana faɗin "WALLAHi ba zan ƙara minti goma cikin garin nan ba sai ka mayar da ni gidanmu ko kuma ni inje da kaina, tunda har kai baka da ɗigon imani a zuciyarka, daman ai son ƙarya ne kake yi man ba wani sona da kake yi sai baƙar yaudarar kalaman da ka saba yi man kullum" Ta nufi ƙofar fita ya yi saurin biyota yana faɗin "haba khadija wai tona man asiri kike son yi wurin mutane?,kada fa ki sa jama'a su zargi cewa ba muharramata ba ce ke" Dije ta fashe da kuka cikin takaicinshi da ya cika mata ciki tare da faɗin, "Ni kam WALLAHi babu wanda ya janyo man wannan abun face su Inna" Safwan yana dariya ya lallaɓata suka yi wanka a gurguje duk da ita ko kaɗan ba da son ranta ba, sannan suka haɗa ƴan komatsansu suka fito, ganin yanayin yanda take tafiya ne yasa gabanshi ƙirewa ya faɗi, saboda tsoron Hajiya Mama ta gano abunda ya faru bayan ya gama cika bakin cewa me zai yi da ita. Cikin rashin kuzari ya riƙeta gam a jikinshi tana cije leɓe suka shiga motar, sai da ya biya ya sissiyo mata abubuwan maƙulashe da nufin toshiyar baki sannan suka bar Gombe suka kama hanyarsu ta zuwa Yola. Kasancewar da yunwa a cikinta ta saki jiki ta ci abubuwan da ya siyo mata sannan ta langaɓe sai bacci, ko da suka isa garin ma baccinta take sha ƙa har sai da suka kusa kaiwa unguwarsu sannan ta falka tana ƙarewa gidajen unguwar kallo tace "Don Allah ka kaini wani wuri inda bazan ga Hajiyarmu ba" Cikin ranshi yace _"Ni ma da zan sami hakan da nafi kowa murna"_ Amman a fili ya ce, "kin san kina jin kunyar haɗuwa da ita kika tafi ba da saninta ba?" Dije ta matso ƙwallar da ta maƙale a idonta tace, "Ni ba ma wannan ba da wane idon zan kalleta idan ta gano abunda ka yi mani?" Ya sosa kanshi yace "To ni me ma na yi maki? Salon ki je ki haɗani da ita ko?" Ta yi saurin kallonshi tace "au kana nufin ka manta abunda ka yi kenan lalle, to ko WALLAHi in baka bini a hankali ba tsaf zan fayyace mata komi" Ba shiri ya fashe da dariya yace "to na biki a hankalin don ALLAH kar ki fallasani don nasan ƙaramin aikinki ne, idan kuma ke baki san yanda ake rufe sirrin miji ba to ki tona ɗin sai inga da ni da ke waye zai jiyo kunya?" Wasu hawaye suka zubo mata akan fuska tace, "WALLAHi ALLAH baka kyauta man ba, yanzu shikenan zata gano na iskance" Ya yi shiru yana saurarenta tana kuka tana soki burutsun zantukkanta, har suka je bakin gate ɗin gidan sannan ta sake fashewa da wani sabon kukan, cike da mamakinta da fargabar da ta cika masa zuciya ya yi parking ya fito suna gaisawa da ma'aikatan gidan, Dije kam kasa motsi ta yi har sai da ta ji yo muryar Fiddo tana yi wa Safwan Oyoyo. Sannan ta muskuta da ƙyar ta fito tana goge hawayen da suka ɓata mata fuska, ganin yaran wata yayarsu Safwan ɗin sun nufota suna faɗin "Oyoyo sannu da zuwa" yasa ta washe ta taryesu da murnarta ta ɗauki ƙaramin yaron, ko kallon Fiddo da shi bata yi ba ta fara taku a hankali cikin ƙarfin hali ta shiga cikin gidan, Safwan ya bi bayanta da kallo cikin tausayawa halin da take ciki a zuciyarshi, Fiddo ma shi ta bi da kallo tana faɗin "Ai WALLAHi yayanmu duk abunda Hajiya ta yi maka ka fanshe akanta, kana ga fa tunda ta bar gidan nan bamu sake ganin fuskar Hajiya ba, kullum zancenta ɗaya ne ALLAH ya dawo da wannan ƴar ƙauyen lafiya, ita bata ko ta jin taka sai ta ɗiyar wasu haka kawai ta zo ta ƙwace muna fada a wurin Hajiya, yawwa ina zancen da ta ji muna yi da kai....? shikenan fa ta hau akan cewa wai ni da kai ne muka haɗa kai muka sa ƴar ƙauyen ta bar gidan, duk rantsuwar da nasha yi mata fa bata yarda da ba hannunmu ba" Safwan ya bita da kallo mai cike da harara yace, "to wai ke wa ma ya tambayeki wannan uban surutun da kike yi? Yarinya dai gata na dawo da ita to kuma yanzu me yayi saura?" Fiddo cikin tsoron yanayinshi da taga ya canza a lokaci ɗaya yasa ta sha jinin jikinta ta ce "ka yi haƙuri big bros Bari in shiga ciki kafin ka ƙaraso" Da sauri ta shige ta barshi yana tunanin ya shiga ko ya bari sai dare ya sulalo ya shige ɗakinshi?, Wata zuciya tace da shi ya shiga kawai ya roƙeta yafiya ya sauke nauyin, ya mazge ya ja ƙafafuwanshi ya shiga gidan cikin fargaba, yana ta rokon ALLAH a zuciyarshi akan kada yasa Hajiya ta ja abun da tsauri. Sai dai yanayin da yaga ta tarbeshi ne yasashi shan jinin jikinshi amman a hakan ya ƙoƙarta yace, "Don Allah Hajiyarmu ki yi haƙuri WALLAHi......." Ta yi saurin ɗaga masa hannu tace, "ajiye ban haƙurinka ni ba shi nake buƙata ba, yarinya dai gata ta dawo hannuna to kaji da kanka kawai don ALLAH" Safwan zai fara yi mata magiya ta katsa masa tsawa tare da bashi umurnin fita ɗakin, ya miƙe ba shiri ya fice cikin ƙunar zuciya, Hajiyar ta bugawa Fiddo da ke tsaye wata uwar harara itama ta fice sum sum, ta kalli Dije da ke zaune tana sharar ƙwallah ta ce "Ke kuma jeki ɗaki ki jirani kafin in zo" Dije ta miƙe a hankali ta fara ɗingisa ƙafa Hajiya ta bi ta da kallo har ta shige, cikin tausayawa ta dawo da kallonta ga Yayarsu Safwan ɗin tace "Ummi ki kirashi kawai yanzu tunda har mun samu ta dawo lafiya, gobe idan ALLAH ya kaimu tun da sassafe sai ku kama hanya, saboda bana son ma yasan ke ce kika tafi da ita, don nasan halinshi bana don ya dameki akan sai an bashi ita" Aunty Ummi ta yi shiru sannan tace, "Hajiyarmu naga kamar yanzu yana son Matarshi fa ki yi haƙuri ki yafe mashi don ALLAH Hajiyarmu" Cikin tsananin ɓacin rai tace "eh nasani Kuma a sanadiyar hakan ma ne nike son nuna masa cewa ko shege yana da ranar shi, saboda haka ki yi abunda nace da ke kawai umurni na baki ba shawararki na nema ba" Cikin sanyin jiki Ummi ta ɗaga waya ta kira wani mai suna Garba, bayan ya ɗauka tace da shi gobe tun da sassafe ya zo ya ɗaukesu ya yi driving ɗinsu ita da yaranta zuwa Abuja. SAFWAN kam yana fitowa kiran Ruma yana shigowa wayarshi, ganin mai kiran har yaso kar ya ɗauka ganin ta dameshi da kiran ne yasa ya ɗaga, cikin Muryar kuka Ruma tace "Don Allah ka zo Zee tana cikin mawuyacin hali kuma ba wanda take kira sai sunanka, plss ka zo WALLAHI tana unconscious we need your help seriously kuma urgent plss and plss" Wata sabuwa🤦🏻‍♀️ Akafta😉 D/AUTA Ce✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *Ku yi haƙuri ku yi haƙuri ni ma ba haka na so ba😢* *Lamba ta 55* Cikin wani sabon tashin hankali tare da kiɗimewa ya koma wurin Hajiyar, yana sanar da ita halin da Zee take ciki tare neman izininta akan komawar da yake son yi Gomben, ba tare da wata damuwa ba ta ce da shi ALLAH ya tsare, har ya fito ya dawo yana sosa kai yace "Khadija fa? Don Allah zan bata saƙo kafin in tafi" Hajiyar tace da shi tana ciki ya yi saurin shigewa ɗakin zuciyarshi cike da tunanin abubuwa da yawa a ranshi, sai dai yanayin da ya taradda ita ne yasa gwiwowinsa suka yi sanyi, cikin mutuwar jiki ya ja ƙafafuwanshi ya isa wurin da take kwance tana ta cisgar kuka, ya yi saurin duƙawa gaban gadon tare da ƙoƙarin ɗago fuskarta amman ta ƙi ba shi damar hakan, cikin damuwa ya ce "Haba khadija yanzu kuma me aka yi maki?don ALLAH ki yi haƙuri ki yafe mani abunda na yi maki, Ni ma ba da son raina ba na kasa controlling kaina ne shiyasa, ban san me yasa na sake aikata maki abunda na yi ba duk da nasan zan cutar da ke, plss ki yafe mani don ALLAH, plss ki ɗago fuskarki ki ce dani kin yafe mani don ALLAH" Dije taƙi ɗago fuskar haka ma ta ƙi daina kukanta, yana cikin magiyar ne kira ya sake shigowa wayarshi, cikin sauri ya fiddo wayar ya duba ganin Daddyn Zee ne da kanshi yasa ya yi saurin ɗagawa, cikin muryar kuka mai haɗe da tashin hankali Daddyn Zee ya ce da shi "Don Allah ka zo ƴata zata rasa ranta a sanadinka, plss ka bi yo jirgi urgently ake buƙatar ganinka, don ALLAH ka taimaki rayuwar ƴata ka zo" Ya ce "insha ALLAHu zan zo soon" sannan ya kashe wayar ya miƙe jkinshi yana rawa ya kalli Dije da ke ta kukanta, cikin damuwa ya ce "Ni zan je Gombe yanzu Khadija ki yi man addu'ar dawo wa lafiya kinji?" Yana ƙare maganar ya duƙo da kanshi saitin fuskarta ya sakar mata da wani kiss a kumata sannan ya fice da saurinshi, daga nan inda take tana ji yo shi yana yin sallama da su Hajiyar, haka kawai ta ji kamar ta tashi ta bishi ta sanar da shi ta yafe masa, amman wata zuciyar ta gargaɗeta akan kada ta yi hakan saboda kunyar idonsu Hajiya da Aunty Ummin da ke falon, sai dai a zuciyarta ta yi masa fatar ALLAH ya dawo da shi lafiya, saboda bata fahimci ko wanene ya yi kiran nashi ba, ammsn taji rashin son tafiyar har cikin ranta. Tana kwance ɗakin ne Hajiyar ta shigo ta yi toilet minti biyar a tsakani sai gata ta fito ta ce da ita ta biyota toilet ɗin, cikin fargaba Dije ta miƙe ta tako a hankali saboda zafin da take ji yana ratsata, sai dai ganin fuskar Hajiyar a haɗe ya sa ta yi saurin gyara tafiyar cikin ƙarfin hali, Hajiyar ta maka mata wata uwar harara ta ce "Ki cire komi naki ki shiga cikin ruwan nan ki buɗa ƙafafuwanki da kyau su ratsa jikinki, ki yi haka har sau uku duk kika tara ruwan kinga wannan maganin ki zuba a cikin sannan ki sake shiga, idan kuma baki yi yanda na ce da ke ba to ni zan zo da kaina in yi maki, tunda ke Kika janyo wa kanki duk abunda ya yi maki, to ai ga shi nan ya barki da jinyar jiki shi ko a jikinshi" Cikin fushi ta fice toilet ɗin tana ta ƙananan faɗa, Dije ta bi ruwan da ke cike da bahon wankan har turirin ɗimi suke yi, amman saboda gudun ta zo ta yi matan kamar yanda ta faɗa ya sa ta yi saurin cire kayanta ta shige ruwan zafin ta zauna, ruwan suna shiga jikinta tana yarfa hannu tare da cije leɓe har suka dallashe, sannan ta fara jin ƙarfi a jikinta ta yi hakan sau uku kamar yanda Hajiya ta ce sannan ta yi wanka ta fito, sai gata tana takawa da kyau duk wani zafi da take ji ya rage sosai, bayan ta shirya ta ci abinci ne Hajiyar ta zaunar da ita ta ce "Gobe idan ALLAH ya kaimu Ummi zata je da ke Abuja, zaki zauna a cen ki ci gaba da karatunki a cen, insha ALLAHu zata riƙeki kamar yanda na yi maki a nan, fatana kawai ke ma ki ɗauke ta tamkar yanda kika ɗaukeni, don duk da kinsani amman dole in ƙara sanar da ke cewa itace gaba da Safwan shi yake bi mata, ki yi haƙuri da duk abunda ya yi maki da sannu zai hankalta har ya dawo ya baki matsayin da nike ta yi maki fata a wurinshi, sai dai ki iya mu'amala da kowa saboda yanzu da da cen inda aka fito ba ɗaya ba, kina da aure kuma Mijinki yana sonki ko da ko bai faɗa ba, saboda ki riƙe masa amanar kanki kuma ki riƙe mutuncin aurenki, ALLAH ya baku haƙurin zama ki dage ki yi karatunki don shine gatanki ko don ke ma ki tallafi iyayenki da hannunki" Dije ta yi shiru tana sharar ƙwallah tace "ALLAH ya bamu haƙurin zama" Ummi da Hajiya ta ce "Ameen" Tun cikin daren ranar Hajiya ta haɗa mata kayanta tsaf! Asubar farin Garba ya zo ya ɗaukesu suka kama hanya sai fatan sauka lafiya ake ta yi masu, bayan tafiyarsu ne Hajiya Mama ta riƙo kunnen Fiddo ta ce "Ke kuma WALLAHi ko da wasa na ji kin sanar da shi cewa ga inda Matarshi ta ke, to ki sani daga ranar kin bar gidan nan, don kuwa ƙauyensu Baabah Kulu zan kai ki cen ki zauna har sai an tashi aurenki a dawo da ke nan" Fiddo ta zaro ido waje tace "Haba Hajiya wannan mugun ƙauyen? Ai WALLAHi ni ko yini ɗaya ba zan iya yi a cen ba bale har in yi rayuwa a cen tab! Mutuwa, Hajiya garin da ko toilet ba bu daji ake kashi kike so in je inyi rayuwa a cen?" Hajiyar ta sunne dariyarta tace, "to idan ba kya so ki ceci kanki kawai a wuce wurin, amman WALLAHi duk ranar da naji kin faɗa masa inda take to a ranar zaki bar garin nan ki je cen" Fiddo ta yi saurin shigewa ɗakinsu tana zancen zucinta tana faɗin, "to ni me ma zai sa in faɗi inda take tunda har ma ba wani damuwa ya yi da ita ba, kuma ma ni daga ALLAH ya rabamu da ƙaya ai godiya yakamata inyi wa ALLAH ba wai faɗa masa ba, don ni har kuɗi ma zan iya badawa akan kada ya gano inda take" Ta faɗa gadonsu cike da jin daɗi tace"ALLAH ya raka taki gona WALLAHi Ummu ta gayar da Aysha" *** Safwan kam a kiɗime ya isa Gomben kai tsaye Asibitin ya nufa don ko Lawi bai nemi rakiyarshi ba, sai kuwa ga shi zuwan ya yi rana don kuwa ko da ya je numfashinta sama tana kiran sunanshi cikin dusashiyar muryar da ta sha ciyo na faraɗ ɗaya, mahaifiyarta da Daddynta da sauran Yan uwanta da Aminu da ƙawarta Ruma duk kuka suke yi, ganin Safwan ɗin da ta yi ne yasa ta yi saurin kiran sunanshi da ƙarfi ta some, ai kuwa ɗakin ya ɗauki kuka saboda tsammaninsu ko ta rasu, shi kanshi Safwan ɗin kwatanta tashin hankalin da ya shiga abu ne babba, saboda ganin yanda ta rame lokaci ɗaya sai karen hanci da ya fito idanuwanta duk sun zurma, hankalinshi bai kwanta ba har sai da likitoci suka rufu a kanta tare da yin nasarar zuƙo numfashinta, cikin dawowar numfashin ne ta fara nishi sama sama tare da sauke numfashin da sauri da sauri, Mahaifin Zee ya zo gabanshi ya duƙa hawaye suna kwaranya akan fuskarshi ya ce "Ka taimaki ƴata ta dawo cikin natsuwarta" Aminu da ke tsaye ranshi a ɓace ya fice ɗakin, Safwan ya ɗago Mahaifin Zee ɗin ya miƙe cikin kwantar da murya yace "Ka yi haƙuri Alhaji Insha ALLAHu ALLAH zai bata lafiya" Muryarshi da ta ji yo yasa ta yi saurin faɗin sunanshi, Likitan ya ce ya matso kusa da ita ya bashi wuri ya matsa jikin gadon, Zee ta yi saurin riƙe hannunshi ƙam ƙam tana zubar da wasu hawayen takaicin kanta ta ce "Me yasa ka yi man ƙarya? Me yasa ka amince da ni bayan kasan kana da matarka wadda ka fi so fiye da ko wace mace?, a hakan ka so in aureka in je inyi auren boranci? Ina sonka my man amman ka sani ko da zan mutu ba zan aureka ba, na yafe maka abunda duk ka yi mani ALLAH ya haɗa fuskokinmu a al..ja..n...n...ah" Sarƙewar da numfashinta ya yi ne yasa ta sake somewa, Mahaifiyarta ta fashe da wani uban kuka, Ruma da ƙawarta da sauran matan da ke ɗakin suma suka kwantsama kukan, da ƙyar likitoci shawo kansu wajen fitar da su ɗakin suka dawo kan Zee ɗin suna ta aikin neman ceton rayuwarta. Wayyo Zee Baby😢 Akafta🥰 D/AUTA CE✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *Addu'o'inku da kullum kuke bina da su ba ƙaramin faranta man zuciya suke yi ba🥰, na gode 🙏🏻sosai Mutanena Alkhairin ALLAH ya kai maku a ko ina kuke👍🏻 muna kyawon tare🤝🏻* *Lamba ta 56* Likitoci sun yi iya ƙoƙarinsu amman numfashinta sai sama da ƙasa yake yi, wani likita ya ce da Safwan ɗin ya yi mata magana cikin daɗaɗan kalamai, ko da ALLAH zai sa ayi nasarar ceto ranta cikin mawuyacin halin da take ciki, saboda tana sonshi idan ta ji muryarshi kuma ALLAH ya shiga cikin lamarinta aka yi dace za'a yi nasara. Safwan riƙe da hannun Zee ɗin da har lokacin take riƙe da shi jabau!, yana hawayen tausayinta ya ce "Plss my precious ki tashi gani a kusa da ke, ke ma kinsan ina sonki kuma bazan iya rayuwa babu ke ba, plss and plss for give me i apologies for you and everything else, ki tashi ki kalleni ido cikin ido in sanar da ke a shirye nike da aurenki a kowane lokaci, kinsan na yi maki alk'awali kuma insha ALLAHu bazan saɓa ba, ki tashi ki kalli Man ɗinki ki ido cikin ido ki ce kin yafe masa plss my dream" Ya ƙare maganar cikin wata muryar kuka saboda yanda yaga har lokacin numfashinta ya ƙi daidaita, saboda yana jin tsoron ace ƴar mutane ta mutu ta sanadinshi, ganin anƙi samun abinda ake buƙata ne yace da likitocin su bashi minti biyu, saboda sun san kan aikinsu yasa suka bashi haɗin kai wajen ficewa dukansu, Safwan ya miƙe ya yi sunkuyo saiti da fuskarta ya buɗa bakinta ya saka nashi ciki, cikin wani salo ya fara zuƙo numfashinta a hankali tare da yi mata kalamai masu sanyi tare da kiran sunayen da suke faɗawa junansu cikin wata murya mai tsada, cikin nasara Zee ta dawo hayyacinta tare da fara zubar da hawaye gefe da gefen fuskarta, sannan ta ƙura masa ido ko ƙiftawa bata yi saboda ganin take yi abun kamar almara ko a mafalki, Safwan ɗin da ko hannunta bai son taɓawa ko acen ƙasar Turai wai shine yau da tsotsar bakinta, cikin mayen sonshi da ke fisgarta ta riƙe hannunshi gam ta ce "My man me yasa ka yaudareni?" Ya yi saurin ɗora hannunshi akan lebenta yace, "ki bar zancen plss a shirye nike da aurenki a duk lokacin da kika tashi" Zee ta washe baki cikin farin furucinshi ta ce, "duk da ka yaudareni amman still har yanzu ban daina sonka ba, me yasa so yake makaho ne? me yasa zuciyata ta ƙi karɓar ƙiyayyarka da na yi ta cusa mata?, Haƙiƙa ka yi nasarar samun sarautar zuciyata You are my prince chrmn and my everything shonah" Safwan cike da tausayinta yace "na yi kuskure ki yafe mani albarkacin son da kike mani ko don ceto lafiyarki, saboda ko da ina son a yi muna auren yanzu kin ga sai an jira kinji sauƙi tukunna, don kin san ba za'a yi aure kina cikin ciwo ba" Zee ta yi saurin share hawayenta ta yunƙura da nufin ta shi zaune amman ta kasa, dole ya riƙata ta tashi zaunen tare da taimaka mata ta jingina jikinta da filo tana binshi da kallon ƙauna, cike da jin daɗin ganin nasarar da aka samu ne Safwan ɗin ya leƙa ya kira likitocin, abun mamaki sai ga Zee sun taradda ita zaune tana share hawayenta jefi jefi. Cikin sauri wani likita ya kira Iyayenta suka shigo cike da jin daɗin albishirin ɗin da ya yi masu, mamaki fal zuciyoyinsu saboda ganin yanda ta ke zaune har da su dariyar ƙarfin hali, dukansu har likitocin sun gasgata ba ƙaramin so Zee take yi wa Safwan ba, Aminu kanshi da ya dawo ya taradda ita zaune ana bata tea tana sha ya jinjina lamarin, take yanke ya sallamawa kanshi barin Zee ko don ta samu abinda take so, saboda a yanzu ya tabbatar da cewa babu wanda ya isa ya yi abunda ALLAH bai tsara a cikin rayuwarshi ba, haka wani bai isa ya auri matar da ba ta shi ba, don da tuni ya aureta saboda dakon sonta da ya yi ta yi a zuciyarshi tun tana ƙarama. Kowa sai murna yake yi kan haka ne ma mahaifin Zee ya ja hannun Safwan ɗin suka fita, cike da jin daɗin ganin ƴarshi ta fara dawowa hayyacinshi yace "Duk da bansan me ya haɗaka da Zainab ba amman jikina ya bani cewa kai ka janyo mata shiga halin da take ciki, a matsayina na Mahaifinta ina roƙonka da ka taimaki rayuwar ƴata ka aureta, tunda har kai take so ni ba zan takura rayuwarta ba saboda haka ba zan taɓa aura mata wanda bata yi na'am da shi ba, idan ka shirya ka turo iyayenka ni zan aura maka ita da hannuna ko da kowa baya so, tunda tana sonka ni ma kai nake so na aurawa ƴata" Safwan ya yi shiru yana nazarin mafita saboda ya rasa ta wace hanya zai nunawa Baban Zee shi ba zai aureta ba, amman cikin zuwan wata dubara ya buɗa baki zai yi magana Baban Zee ya dafa kafaɗarshi ya ce "Kada ka ji komi ni zan baka ita da hannuna fatana kawai ALLAH ya sa ka riƙe mani ita Amana kuma ka dubi son da take yi maka ka riƙeta tsakani da ALLAH" Safwan ya dafe goshinshi cikin rikicewa yace "na gode Alhaji" Alhajin ya sake dafa kafaɗarshi cikin murna ya ce"ALLAH ya albarkaci aurenku" Sannan ya koma cikin ɗakin cike da jin daɗin samarwa ƴarshi abunda take so, Safwan ya riƙe ƙarfen baranda ya yi shiru tare da juya zancen cikin ranshi, ya nutsa sosai cikin zurfin tunani sai jin magana ya yi ana ce wa da shi "Ko wane Mutum tafe yake da kundin ƙaddararshi na yarda da tawa ƙaddarar na amince na rasa Zainab ALLAH Ubangiji ya baku zaman lafiya" Zancen Aminu kenan da ke tsaye soke da hannunshi duka biyu a aljihu, yana ƙare faɗar hakan ya juya zai tafi Safwan ya yi saurin dafo kafaɗarshi ta baya Aminu ya tsaya cak! Kamar an masa dole, Safwan ya yi ƙarfin halin faɗin "Kada ka yi fushi akan abunda kake so ka yi haƙuri ku daidaita da Zee ku yi aurenku kawai, Ni na haƙura na bar maka ita ka je ku yi aurenku plss" Aminu ya juyo ya sauke hannun Safwan da ke kafaɗarshi ya sake mayar da hannunshi aljihu yace "Kada ka ji komi ka ji da kanka ni na barwa ALLAH kuma ina da tabbacin zai yi man mafita" Yana ƙare faɗar maganar ya bar wajen tare da jan Motarshi ya fice asibitin gaba ɗaya, Safwan cikin tashin hankali ya ciro wayarshi ya kira Lawi domin ya ji a ina zai sameshi, Lawi ya yi masa kwatance sannan ya fice Asibitin ko sallama bai yi da su ba ya nufi wurin Lawin. Cikin guntun bayani mai gamsarwa Safwan ya yi masa bayanin duk halin da ake ciki, Lawi ya yi shiru yana nazari sannan ya ce "To ka aureta kawai tunda ƙaddarar aurenta ne ya haɗaku tun farko" Safwan ya goge jiɓin da ya jiƙa masa fuska yace, "Ni ban san da wane idon zan kalli Khadija in ce da ita zan yi aure ba, WALLAHi ni yanzu auren Zee ya fita kaina, na fi son in mayar da hankalina kan matata in gyara abunda na ɓata a baya, in nuna mata irin gatan da kowace mace take nema a wurin Mijinta, ka sanar da ni Abokina ta ya zan saukewa kaina auren Zee??" Lawi ya ce "ba wata mafita gaskiya saboda kai kasan irin son da take yi maka, kuma nasan kai ma kana sonta to tunda har anyi hakan mafita ɗaya ce ka sami Aminun har gida ka sanar da shi da gaske kake yi ka bar masa Zee, idan ya amince shikenan idan kuma ya ƙi sai ka aureta kawai tunda ALLAH bai haramta maka ita ba" Safwan ya yi shiru yana nazari sannan ya nemi Lawin ya rakashi su je gidansu Aminun ba musu suka nufi gidan, sai dai iya daɗin bakinsu da nuna masa su ma sun san fiqhu da Tauhidi bai sa Aminu ya karɓi buƙatarsa ba, don ya yi biris akan buƙatarsu sosai ya rufe ido ya nuna baya ra'ayin aurenta, sannan ya nuna masu cewa shi fa ya haƙura ya yi imani akan duk abunda ALLAH ya tsara masa, kuma insha ALLAHu shi ma kwanan nan zai fito da mata ya yi aurenshi, dole ba don sun so ba suka haƙura suka bar gidan cikin sanyin jiki. Tare suka koma Asibitin da Lawi sun ɗan jima a cen sannan suka yi masu sallama suka dawo gidan Lawin, gidanshi da yake ta gyara saboda lokacin aurenshi da yake ta matsowa. Da safe ma ko da suka koma sun taradda ita da sauƙi sosai don kuwa sai samuwa yake yi a hankali, ganin hakan yasa ƴan'uwan Zee suka ta yi masa godiya tare da yi masu fatar alkhairi a auren nasu, cike da jin nauyi yake amsa masu ba yabo ba fallasa. Kasancewar Zee ta ji albishiri ɗin aurenta da Safwan a bakin mahaifinta yasa ta saki jiki sai wasar baki take yi, zuciyarta cike da jin daɗin mallakar mutumen da tafi so fiye da kowa ne ɗa Namiji a duniya. Bayan kowa ya fice ne aka barta da Safwan ɗin don ko Lawi fitowarshi ya yi ya barosu, cike da jin daɗin ganinshi cikin muryar ciyo ta ce "My hero ya zaka yi da mata biyu da kake ƙoƙarin haɗawa a zuciyarka?" Safwan ya yi dariyar yaƙe ya ce "ALLAH zan roƙa ya bani ikon yin adalci tsakaninku" Cikin jin kishin matar tashi ta ce, "to yanzu idan mun yi auren da ita zamu koma school ko kuwa?" Ya yi shiru sannan ya ce, "sai abunda Hajiyata ta ce sannan duk hukuncin da ta yanke muna to ni banda ja akanshi" Cikin sauri aranta ta ce _"ALLAH yasa ma ta ce a barta anan ɗin mu mu tafiyarmu abunmu"_ Amman a fili tace "ALLAH ya sa mu dace all, amman plss ka nuna mani wacece Uwargidana ko da a hoto ne, don ina son na nasan wacece ta yi saurin sace zuciyar Realitynah?" Safwan ya yi ƴar dariya saboda tuno Dijen Baffah sannan ya ce "saurin me kike yi zaki santa soon Insha ALLAH " Haka Zee ta yi ta shige masa suna ta firarsu cikin natsuwa har Safwan ɗin ya yi sallama da ita akan zai koma Yola ya turo Iyayenshi ayi zancen auren nasu. Cike da tsantsar farin ciki ta yi ta jera masa kalaman soyayya tare da yi masa fatan ALLAH ya tsare hanya, da ma zai ta fi har son ta yi ta sauko ta rakashi sai da ya hanata sannan ta haƙura, tana yi masa bye bye yana yi mata suka rabu. Mahaifinta ya karɓi account ɗin Safwan a take yanke ya yi masa transfer ta 2million ya ce da shi ya je ya fara shirye shiryen aurenshi da Zee, saboda komi cikin gaggawa yake son ayi saboda buƙatar su koma makaranta cikin lokaci. Safwan ya tafi zuciyarshi ba yabo ba fallasa don har cikin ranshi bai yi wata murna akan auren ba bale kuɗin da Daddyn Zee ya ba shi, don a ganinshi tamkar ma ya renashi ne, saboda tambayar kanshi da ya yi akan cewa, shin ya ɗauki kuɗin ya bashi ne don ya siyeshi da kuɗin ya auri ƴarshi? ko ku wa don ya nuna masa cewa su ma masu kuɗi ne fiye da su?. Oho Safwan🙄 ni dai in baka so ko 5ok ka yi man transfer a nawa bank account na yi maka alƙawari zan tayaka addu'ar neman zaɓin ALLAH😝 Akafta🤣 D/AUTA Ce *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *Because of you ƙanwata Leemart pinkey MHiss purple ALLAHU ya bar zumunci ta hannun damata🖐🏻* *Lamba ta 57* Jiki ba kuzari yake driving har ya isa Yola cikin amincin ALLAH, sai dai yawan faɗuwar da gabanshi yake yi yasa ya ji baya sha'awar zuwa gida, sai da ya biya wajen Mubarak suka tattauna sosai akan matsalar sannan ya nufo gidan. Jiki a sanyaye ya yi parking ya daɗe zaune cikin motar yana nazarin ta ina zai fara?, wurin Hajiya Mama ko wurin Khadijarshi?, a ƙarshe dai ya yanke shawarar fara tunkarar Hajiyar saboda ta fi khadija matsala a wurinshi, don ita da ya kanainayeta da daɗin baki zata bi ba tare da yasha wahala ba, cikin ƙarfin gwiwar da zuciyarshi take ba shi ne ya fito ya nufi cikin gidan, sai ko ya taki sa'a ya taradda Hajiyar da Fiddo a babban falo suna kallo, ya shigo da sallamarshi ya ƙaraso ya zauna tare da faɗin "Wash! ALLAH Hajiyarmu gani na dawo lafiya" Idonta akan tv tace "masha Allah sannu da dawowa" Fiddo ta gayar da shi cikin ladabi sannan ta ce, ,"big bros ya jikin Aunty Zee ɗin? da fatar taji sauƙi sosai?" Ya shafo sumar kanshi da take cike da gashi kwance baƙi ƙirin a saman kan nashi, sannan ya ce "Ta sami lafiya khadija fa?" Fiddo ta yi saurin kallon Hajiya Mama sannan ta ce "Tana ɗaki maybe bacci take yi" Cikin jin nauyin idon Hajiyar ya ce "je ki ce ta kawo man abinci" Fiddo ta daburce ta miƙe tana sosa kai tace "tun ɗazu fa kamar bata gidan nan don ban ga ko wulgawarta ba" Cikin faɗuwar gaba ya zaro ido waje "me kike nufin sanar da ni? Ba ta nan to ina ta je ne ba tare da izinina ba??, Hajiyarmu ko ke kika aiketa ne don nasan Khadija ko ƙawa bata da a cikin garin nan bale ace ta je cen, ko dai tana gidan Surayya ne?" Hajiya Mama cikin ko in kula ta ce, "mi ye damuwarka da ita ne? Ni fa bana son takura, saboda haka ka bar yarinya ta sha iska" Safwan ya marairece fuska yace , "matata ce fa Hajiya ko ba komi akwai haƙƙin aurena a kanta" Hajiya ta maka masa harara ta ce "don kana aurenta ai har yanzu bata zama kamar sauran matan aure ba, don cikin haƙƙoƙanta da Allah ya rataya a wuyanka nawa ka sauke faɗa man cinka? ko shanka? Ko kuma suturarka?, To bana son zaƙewa da yawa don ni nake da ikonta tunda kai da kanka ka saka muna ita cikin ƴan aikinmu, to yanzu kuma ka ke son zuwa ka kawo mani wani zancen banza cen" Safwan ya yi saurin faɗin "to na tuba a gafarceni Hajiya yanzu ina ta je in je in ɗaukota", Cikin basarwa Hajiyar ta ce "to Khadija dai bata gidan nan na turata aikatau wani gari, saboda naga mu nan ƴan aikin ma sun yi muna yawa, shine na ga da a barta haka kawai zaune ba wani moruwarta da muke yi, shine na ga gara kawai na turata cen ɗin, insha ALLAHu duk kuɗinta na wata wata idan an aiko mani zan je da kaina har ƙauyensu in kai wa iyayenta" Firgici tashin hankali tare da ruɗewa duka suka ziyarto wa Safwan ba tare da ya shiryawa zuwansu ba, cike da wani tsantsar tsagwaron tashin hankalin da ya bayyana a kan fuskarshi ya ce "WALLAHI ina sonta Hajiya don ALLAH ki dawo man da matata hannuna, na yi maki alk'awali zan riƙeta in mata gata fiye da kowace mace mai gata a gidan Mijinta" Ya ƙare maganar cikin muryar kuka tare da zuwa gaban Hajiyar ya durƙusa gwiwa bibbiyu ya haɗa hannu biyu waje ɗaya alamun roƙo ya sake cewa "Na tuba Hajiyarmu ki yafe mani WALLAHIL'AZIM yanzu da gaske ina sonta, kuma a shirye nike da in zauna da ita a inuwa ɗaya a matsayin matar aurena" Fiddo ta bi shi cike da kallon mamaki baki a sake tace, "Dijen kake so big Bros??" Wani hargitsatstsen kallon da ya bi ta da shi da jajayen idanuwanshi yasa ta yi saurin rufe bakinta da hannu ta bar falon, Hajiya Mama ta ƙi kallonshi sai kallon tv'n take yi kamar kallon take yi da gaske, don bata son Kallonshi saboda gudun tausayinshi ya karya mata zuciya, Safwan ya riƙo ƙafarta tare da duƙewa ƙasa cikin wata murya mai cike da ban tausayi ya ce "Ki gafarceni Hajiyarmu nasan na yi kuskure a baya plss ki dawo man da khadija don ALLAH Hajiyarmu" Hajiya ta miƙe tsaye ta yi taku ɗaya biyu kamar zata bar falon sannan ta tsaya ta waigo ta ce "Yanzu ba wurin budurwarka ka fito ba? Kuma ba aurenta ka ke so ka yi ba? To ka je na baka dama tuni ka yi aurenka ai, amman ka sani yanzu na fasa amincewa da tariyar khadija gidanka, zan barta cen wajen aikatau ɗin sai ka rubuta mata takardar sakinta idan ta sami mijinta a cen sai ta yi aurenta" Tana ƙare faɗar maganar ta wuce abinta ta nufi ɗakinta, cikin sauri ya biyota cike da wani sabon tashin hankali yana faɗin "Don girman ALLAH Hajiyarmu ki yi haƙuri ki yafe mani laifukana" Sai dai yana kawowa bakin ƙofar ɗakin ta rufo ƙofar ɗakin da ƙarfi har saura ƙiris ta haɗa da kanshi, Safwan ya dawo baya cikin hanzari sannan ya durƙushe bakin ƙofar yana faɗin "Zan mutu Hajiya idan har ba'a kawo man matata ba" Daga cen cikin ɗakin Hajiyar ta ce "ka yi sauri ka mutun don ALLAH, kana da rai ma wani aure zata yi bale ka tafi ka bar duniyar?" Safwan ya dafe saitin zuciyarshi yace "Wayyo Hajiyarmu kada ki yi man irin wannan horon wallahil'azim ina sonta ke ma zaki sheda hakan" Haka ya yi ta surutanshi har ya gaji Hajiyar bata sake tankashi ba, dole ya gaji ya miƙe ya nufi ɗaikinshi ya faɗa gado cikin ƙunar zuciya tare da yin nadama akan abunda ya aikatawa Dijen Baffah a farko, yanzu ga shi Hajiyar tana son horashi da laifin da har ya mance da ya aikata, saboda yanzu giyar sonta da ke walagigi da rayuwarshi yasa ya manta baya, haka ya yi ta kukan zucinshi cikin ɗaki cike baƙin cikin da ya mamaye masa zuciya, saboda Zee sai damunshi da kira take yi wani bayan wani ko gajiya bata yi amman yaƙi ɗaukar ko ɗaya, saboda damuwar da yake ciki a ganinshi ta shi ta shalle tunanin ta ta damuwar. Haka ya yi ta yiwa Hajiya magiya akan ta dawo masa da Khadijarshi, da ya ga ma ta ƙi saurararsa ne ya kira Fiddo cikin sirri yana tambayarta inda aka kai khadijar, amman itama cike da jin haushinshi ta ce ita bata ma san Dijen bata gidan ba, dole ya koma tambayar ma'aikatan gidan sai dai su ma duka bakinsu ɗaya ne babu wanda yasan inda aka kaita, sai ga Safwan da biyar gidajen ƴan'uwa lungu da saƙo yana binciken ina aka kawo sabuwar ƴar'aiki, amman dai iya bincikenshi babu Dije babu mafarinta, dole ya dawo gida a jigace yana yi wa Hajiya kuka da hawayen da suke ta sauka a kan fuskarshi ba tare da sautin kukan ya fito ba, amman a hakan Hajiyar ta bushe fitilarta ta ce ba zata dawo da ita ba kuma sai ya bata takardar sakin Dijen dolenshi. Damuwa goma da ashirin suka yi masa yawa a kai saboda izuwa lokacin Mahaifin Zee ma ya shiga cikin jerin sahun masu kiran nashi akan ya turo Iyayenshi, saboda danginsu sun yo masa caa! Akan rashin kyautawar da zai yi wa Aminu, shi kuma ya kafe akan cewa duk abunda ƴarshi take so shi ma cen yake so, don har meeting aka yi akan matsalar ƙarshe kuma aka watse baram baram, saboda wasu da yawa sun ga laifinshi ya yin da wasu kuma suka goyi bayan Daddyn Zee ɗin saboda illolin auren dolen da ake hangowa, a ƙarshe dai Aminu da kanshi yake baiwa masu goyon bayanshi haƙuri akan lamarin, tare da sare masu gwiwa wajen sanar da su cewa shi fa ya janye, dole kowa ya haƙura aka zubawa Daddyn Zee ido aga iya gudun ruwansu shi da ƴarshi. Kan haka ne ya yi ta samun Safwan ɗin da kira sai dai zance ɗaya ne yake yi masa na cewa wanda zai zo nema masa auren ya yi tafiya, da ma ya fahimci kamar zillewa yake son yi yasa su ji kunya ga ƴan'uwansu ya ce ya ce da shi "Ya bashi number'r wakilin nashi shi zai kirashi ya yi masa bayanin abunda ke faruwa" Dole Safwan ya saka masu ranar da zasu zo shi da Iyayenshi akai ƙarshe akan lamarin, sannan hankalin Daddyn Zee ya kwanta tare da kwantar na ƴarshi da ta ƙi ci ta ƙi sha akan damuwar rashin ɗaukar wayarta da Safwan ɗin baya yi. Safwan ya je wa da Hajiya Mama da maganar tare da fayyace mata komi akan halin da ake ciki, sai dai duk da ta ji zafin abun aranta amman hakan bai sa ta hanashi auren ba, asali ma ta amince masa kamar farko yanda yasa mutane suka tursasata kan zancen auren, saboda tausayin yanda ya firgice cikin lokaci ɗaya saboda rashin Dijen, ya bi ya rame saboda damuwar da ya sakawa zuciyarshi akan rashin Matarshi, sannan ta san muddin ta hanashi auren bayan ta ɗauke masa Dijen ta cutar da rayuwar ɗanta, sai dai bata amince da auren ba ne sai da ta yi nazarinshi sosai akan damuwar rashin Dijen bazai barshi ya ji daɗin auren da zai yi ba, kuma ta hakan ne zata ƙara samun wata damar da babu wata ƴa mace da zata samu a wurinshi. Safwan kam cike da tausayin kanshi da ita kan Zee ɗin ya tura Iyayenshi suka neme masa aurenta inda aka saka rana da lokaci sati biyu kacal masu zuwa, saboda su koma school su ci gaba da harƙallar karatunsu. **** Biki sai ƙaratowa yake yi duk da ango kam ba wani jin daɗin auren ko zumuɗi irin na ango da yake yi, don a kullum dare ya kwanta baya baccin kirki saboda mafalkin Dijen da yake yi cikin yanayi kala kala, ta ɓangaren Zee Kam sai shirye shiryensu suke yi cike da alfahari, saboda su cusawa waɗanda basu son auren haushi, inda su kuma suka koma gefe suna kallon ta yanda za'a yi auren cin amana ya yi daɗi. ***** Dijen Baffah kam duk da ta ji daɗin garin amman zuciyarta cike take da kewar Mijinta, bata da wani aiki sai na tunaninshi da kalamanshi waɗanda ada take hangosu a matsayin na yaudara, sai ga su a lokacin tana jinsu har cikin ruhinta, saboda ba ƙaramin daɗi suke yi mata a kunnuwa da gangar jikinta ba, waɗanda wani zubin bata san lokacin da wasu hawwyen kuka yake zuwar mata ba, don ita a son samunta a barta ta koma wurin Mijinta ta yi masa biyayyar da Inna take ta yi mata jan kunne akan ta yi masa, yanzu ta amince wa zuciyarta cewa itama fa tana son MALAM Safwan, ga shi ko waya babu a hannunta ba le ta kirashi ta ji daɗi, kuma kunyar idon Auntyn da kashedin Hajiyar yake sa ta ƙi tambayar a wane hali yake. Ganin halin da take ciki ne yasa Aunty Ummi ta fara shiga damuwa duk da tana iya ƙoƙarinta wajen sakata nishaɗi saboda gurinta na son cire mata damuwa, shiyasa ko auren da ta ji ƙin nuna mata wani abu da zata gano ta yi, saboda jan kunnen da Hajiyar ta yi mata akan kada ta bari ta san da zancen, da ma lokacin auren ya matso ne ta yi mata ƙaryar wani biki ne daban zata je, da ma Dijen ta nuna tana son zuwan itama sai ta ce da ita ta yi haƙuri ba zata daɗe ba, don ma ta kwantar mata da hankali ta bar yaranta mata manya ta tafi da ƙananun saboda Maigidanta daman cen ba mazauni bane ba. **** Biki bidiri bireɗe amfanin soyayya aure Zee ta angwance da masoyinta Safwan, zuciyarta cike da tsantsar farin ciki saɓaninshi da yake cikin ƙunci don duk wasu events ma ba da shi aka yi ba, an ɗauki Amarya daga Gombe zuwa Yola mahaifar Mijinta, inda aka wuce da ita gidan Hajiya Mama kai tsaye saboda ta kwashi tubarrakin uwar mijinta ta sawa aurensu albarka kafin akaita gidan angonta. Sorry team Dije 🙇🏻‍♀️ku sani babu ruwana nidai 🙌🏻🏃🏻‍♀️ Akafta🙌🏻 D/AUTA Ce✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *Mutanen Dije ina baku haƙuri🙏🏻dangane da auren Zee da Safwan ya yi, amman ina son ku sani ana yin book ne don faɗakarwa tare da wa'azantarwa sannan da kwatanta abunda ke faruwa a cikin al'ummarmu, saboda haka ku natsu tsaf ku bini sannu a hankali zan warware maku komi cikin tsarinshi😉* *Lamba ta 58* Har ƙuryar ɗakin Hajiya Mama aka kai Zee da ke ta rufe fuska tana ta wasar baki saboda daɗin da ya kasa ɓoyuwa a kan fuskarta, gaban kowa da mutanen da suka yi mata rakiya Hajiya Mama ta ce da Zee "ALLAH ya baku haƙurin zama, kuma albarkaci aurenku tare da zuri'a ɗayyaba gaba ɗaya, sannan da fatar zaman lafiya ke da abokiyar zamanki" Dirim! dum! Shine bugun da zuciyar da Zee ta yi amman ta wayance tare da noƙe fuskarta tace "Ameen" Hajiya Mama ta ƙara da cewa "Ki yi haƙuri nasan zaki ga abokiyar zamanki bata sami halarta bikin ba, to hakan ya faru ne a sanadin hidimar karatun da ya sha kanta, amman ina fatar a duk lokacin da zama ya haɗaku ki yi ƙoƙari ki baiwa Mijinki haɗin kai wajen yi maku adalci a tsakaninku, ALLAH ya baku zaman lafiya a tsakaninku duka ya kawar da sheɗan cikin gidanku gaba ɗaya" Kowa sai "Ameen Ameen" yake faɗa sannan ta kawo dunƙulalliyar kyauta ta bata, aka fito da Zee mutane da yawa sai yaba kirkin Hajiyar yake yi, inda kai tsaye aka wuce da Zee katafaren gidan Safwan wanda ya laƙume maƙudan kuɗi wajen haɗashi ta ko'ina, inda itama kanta Zee iyayenta suka zuba ta su bajintar wajen ƙawatashi da kayan ƙarau lungu da saƙo, abun dai masha ALLAH sai wanda ya gani don tsayawa misalta haɗuwarshi ma ɓata baki ne, saboda haka masu karatu na baku wannan aikin wajen misalta gidan da kanku. Har ɗakinta aka kaita iyaye da ƴan uwa da ƙawayenta sai addu'ar zaman lafiya su ke yi mata, saboda ganin yanda ta haye wajen samun kyakkyawan Miji da kyakkyawan muhallinta gwani burgewa, uwa uba itama gata kyakkyawar farar mace kuma ga su da hannu da shuni ta ko'ina suka motsa nera kukan wahala ta ke yi, saboda akwai kuma an tara babu abunda zai gagaresu nema matuƙar da kuɗi ake sakawa a nemi abun. Abokan Safwan sun shirya dinner wadda za'a yi a wani katafaren hall, sai dai shi ango ya ce sam shi kam ba wata dinner da zai je, shagugulan da aka yi ma sun wadatar ALLAH ya sawa aure albarka, ba magiyar da Zee ba ta yi masa ba akan ya yi haƙuri su je ko da rage lokacin da aka ɗiba ne za'a yi sai ayi komi cikin lokuta ƙalilan, amman ya buga kanshi a ƙasa ya ce shi bai san da wannan zance ba, cike da jin haushi Zee ta fashe masa da kuka dole ya koma aikin lallashinta, ganin yanda ta dami kanta akan son zuwan ne ya shirya suka je, amman har cikin zuciyarshi ba ya wani murna da duk wani shagali, aure dai ne anyi to tsirfin na mi ne kuma?. Har aka yi dinner aka watse Safwan fuskarshi ba yabo ba fallasa sai dariyar yaƙe da yake yi wa mutane, Amarya da ango sun fito sun yi rawa sun sha liƙi ta ko'ina kuɗi ne ake zuba masu, bayan sun ƙare ne suka yanka cake tare da ciyar da junansu mutane sai ɗaukarsu photuna da videos ake yi, saboda shagalin ya ƙayatar da rai sosai ba tare da jan lokaci ba aka watse koma ya kama gabanshi, inda Ango ya ɗauko Amaryarshi zuwa gida tare da rakiyar abokai da ƙawayen Zee ɗin da za su kwana da safe su kama gabansu. Kasancewar part ɗinshi daban shiyasa kai tsaye ya nufi sashenshi ya barta tare da zugar ƙawayenta suka nufi sashenta, cike da tsananin gajiya ya faɗa kan gadonshi tare da dafe kanshi idonshi a sama yana kallon seilling yana hasko Dijen Baffah cikin idanuwanshi, musamman lokacin da ya sami sa'ar rabata da abunda har lokacin idan ya tuna sai ya ji shi cikin wani yanayin buƙatuwa da son komawa cikin tafkinta mai ɓulɓulo da ruwan kogin ni'ima, waɗanda ko a misali ba zai taɓa kwatanta irin abunda ya ji a jikinta ba, don duk abunda zai faɗa ganin yake yi kamar ya fi hakan, saboda shi kanshi ya yi matuƙar mamakin yarinya kamarta ace itace da wannan tarin albarkatun ni'imar a jikinta, sai dai idan ya yi nazarin cewa ance ko wace mace da kalar ni'imarta sai ya ajiye mamakin don yasan ALLAHn da ya raba ya baiwa kowa ce mace haka itama ya raba ya bata tata, don ikon ALLAH ya fi gaban a yi mamakinshi illah kawai mu ce Alhmdllh a kowane hali a kuma kowane yanayi. ZEE kam kasancewar abokan nata su ma kansu a fashe yake, shiyasa suka sakata ta sheƙo wanka tare da tsara mata dress cikin wata arniyar night gown fara ta yi kyau iya kyau sai dai komi na jikinta babu wanda ya ɓuya don har pant ɗin da ke jikinta ana hangowa, bra ma cewa suka yi kada ta saka kasancewarta daman cen breasts ɗin nata ba wani yawa ne da su ba, don bafulatana ce ta usuli mai ƙananan nonuwa, amman a hakan ma ba laifi sun ɗan fito a cikin rigar kuma shigar ta karɓe ta sosai, sannan suka fesheta da tsadaddun turaruka masu ɗan karen ƙamshi, suka zaunar da ita suna yi mata bitar abubuwan da ta yi, tana daɗe tana zaman jiran shigowar angon domin ya tafi da ita, sai dai shiru shirun da suka ji ya yi yawa ne suka bata shawarar kawai ta je ta sameshi da kanta, cikin zumuɗi ta miƙe don daman cen kawaici ne kawai take yi saboda kar aga zalamarta, aikuwa ta zumbula dogon hijabi wata ƙawarta ta rakata har sashenshi sannan ta dawo, Zee ta daɗe a ƙofar tana wassafa irin kallon da zata yi masa wanda zai sa ta sace zuciyarshi a lokaci ɗaya ya faɗa tarkonta. Da guntuwar sallama ta shiga inda sallamar ta katse ba shiri saboda ganinshi da ta yi kwance takalman da ke ƙafarshi ma bai samu cirewa ba, suna nan sanye a ƙafar ta shi har lokacin, hular kanshi kawai ya cire saboda damuwar rashin sanin takamaiman inda Dijen take, damuwar hakan ne ta cika masa ziciya, Zee ta tako a hankali cikin faɗuwar gaba ta zauna gefen gadon tare da ɗora hannunta akan jikinshi ta ce "My Man wai meke damunka ne? Na fahimci akwai damuwa a tattare da kai musamman yau ɗin nan, me yasa zaka taryi wannan daren na mu mai tarihi a garemu da wannan sabon yanayin??" Safwan ya yi saurin riƙo hannunta daga kwancen tare da sauke wata nannauyar ajiyar zuciya ya ce "Sorry ni ma ban san me ke damuna ba, haka kawai na tsinci kaina cikin wannan yanayin, ki yi haƙuri kinji?" Zee ta sauko ƙasa ta fara cire masa takalmin da Safar duka sannan ta haɗasu ta kai muhallinsu ta ajiye, ta dawo ta kwanta gefenshi ta shafo fuskarshi tana yi masa wani kallo ta ce "Plss Honeybee ka daina wannan damuwar ka tattara sabon yanayin nan ka a jiyeshi a gefe ka kalli sabuwar Amaryarka gata a kusa da kai tana buƙatar kulawarka" Safwan ya saka hannunshi ya janyota kusa da shi sosai ido cikin ido suke kallon juna, yana yi mata wani kallon tausayi saboda yasan ba ƙaramin so take yi masa ba, cikin mairairece fuska da alamun son yin kuka ta ce "Plsss! my man!" Safwan ya janyota jikinshi all kasancewar ba wani kumari ne da ita ba ya sakar mata kiss a goshi sannan ya miƙe zaune ya ce "Bari in je in yi wanka ko da zan ɗan ji ƙarfin jikina, sannan mu zo mu yi sallahr godiyar ALLAH ga Ubangijinmu" Cike da jin daɗin maganarshi ta lumshe ido daga kwancen ba tare da ta ce ƙanzil ba, ya miƙe yana cire kayanshi ta bishi da kallon ƙauna har ya shige toilet sannan ta sauke ajiyar zuciya a ranta ta ce _"ALLAH ka bani ƴa ko ɗa mai kama da kai sak! my Bunny"_ Har ya fito bata san ya fito ba saboda ta lula sosai wajen tunanin zazzafar soyayyar da take yi masa, sai da ya saka ƙafa ya soso sililin ƙafarta sannan ta yi saurin ta shi zaune tana murmushi, ya ce ta je ta yi arwallah ta zo su yi sallar, ta miƙe tsaye ta yi wata miƙa ta cire hijabin da ke jikinta ta nufi toilet ɗin cikin wani takun jan hankali, ya bi bayanta da kallo ya yi wani gajeren murmushi sannan ya saka doguwar jallabiya fara ya shimfiɗa ƙatuwar carpet yana jiran fitowarta. Bayan sun ƙare sallahr ne ya yi ta jera masu addu'o'in neman zaman lafiya sannan ya fara latsa amaryarshi tun a nan, don ko kazar amarcin da ake ci su ba su sami damar ci ba, saboda angon ba wani sukunin zuciya ne da shi ba shiyasa komi ma ya fita a ranshi, ita kuma murnar ganin yanda ya fara nuna mata zallar ƙaunarshi ne yasa ta ƙi cin komi, a hakan suka baje suna ta farantawa junansu ta hanyar musayar abubuwa da yawa, saɓanin Dije da shi ya yi kiɗan kuma ya yi rawar har ma ya sami guzurin kukan da ta rufeshi da shi wanda ya zama tamkar taki wajen haukace mata, Zee kam jiki ta saki itama ta nuna masa ba fa shi kaɗai ya iya tarairayar ba, cikin salon ƙaunar da ta baibayeshi da ita ne ta ci galabar samunshi yanda take buƙata, don kuwa ya baje sosai ya karɓi budurcin Amaryarshi, ba tare da ya sha wata wahala ba, duk ko da yanda take jin azaba amman hakan bai sa ta nuna masa gajiyarta ba, sai dai sunan Khadija da bakinshi ya ƙi daina ambata ya sa ta shiga tunanin wace khadija ce yake faɗa a yayin kwanciyar aurensu na farko?, amman ta bar abun aranta don bata son ta ɓata masa rai cikin wannan yanayin da suke ciki, sai da ya tabbatar da ya jigatar da ita sannan ya saurara mata don kanshi, ya koma saka mata albarka tare da jinjina mata akan budurcinta da ta adana masa. Haka suka kwana cikin damuwa dukansu kowa da tunanin da yake yi cikin zuciyarshi, inda shi ya kwana yana tunanin ƙira da cikar ƙirjin Dijen Baffah, yayin da ita kuma ta kwana tana tambayar kanta wacece khadijar da ya yi ta kira lokacin da suke faranta junansu?. Bayan sun yi SALLAHr asuba ne Zee ta kasa haƙuri ta ce da shi "My man Ina son inyi maka wata tambaya da fatar baza ka ga laifina ba?" Ya shafo fuskarta tare da riƙo hannunta ya sakar mata kiss a bayan hannun sannan ya ce "Idan har kin san tambayar ba mai laifin ba ce ki yi kawai a shirye nike da in baki amsarta" Zee ta yi saurin riƙo hannunshi ta saka nata sama da ƙasa ta riƙe gam gam wasu hawaye suka fara zarya cikin idonta ta ce "Wacece khadijar da na ji kana ta kira a jiya? Don Allah ka sanar da ni saboda ina jin tsoron ace sunan Uwargidanka ne ka ke ta ambata" Safwan ya yi saurin kawar da kanshi gefe tare da jin nauyin abunda ya aikata mata cikin rashin sani, sannan ya ce "Ki yafeni Matata nasan ban kyauta ba amman Insha ALLAHu hakan ba zata sake faruwa ba in dai har daga gareni ne matsalar ta fito " ZEE ta share hawayenta da suke ta sauka akan fuskarta ta ce "Ina jin tsoron ace akwai wadda ta fini samun muhalli a cikin zuciyarka, don WALLAhi matuƙar hakan ta faru to bazan taɓa yafe wa kaina ba" Safwan ya rungumota jikinshi tare da ɗora kanshi saman kanta yana wassafo Dijen Baffah a ranshi da ruhinshi sannan ya sauke ajiyar zuciya yace "So shu'umi ne my unique ki yafewa Man ɗinki albarkacin son da kike yi masa kin ji?" Ta riƙo hannunshi sannan ta shafo fuskarshi ido cikin ido ta ce "Ina sonka sosai My Man don ALLAH ka riƙeni amana ka ji?" Ya lumshe idanuwanshi ya sake rufewa sai ga fuskar Dijen Baffah ta zo masa a cikin gilashin idonshi, cikin sauri ya yi saurin buɗe idanuwan yana kallonta fuskarta ƙur sai ga fuskar Dijen Baffah ta bayyana cikin ta ta, ya yi saurin duƙowa cike da zalama ya cafki leɓenta yana wata irin tsotsa tamkar zai rabata da bakin duka, cikin fitar hayyaci tare da rasa tunaninshi na wuccin gadi ya ɗago fuskarta idonshi a rufe ya ce "Me yasa kika bari aka rabani da ke ne? Me yasa kika tafi kika barni? Kinsan iya adadin damuwar da kika sanyani kuwa? Plss ki dawo gareni khadija, plss ki dawo wurina na ce!!!!" Ya ƙare maganar cikin zubowar wasu hawaye masu zafi waɗanda tunda ya shiga cikin damuwar bai sami damar yin ƙwallah ko ɗaya ba bayan kukan da ya yi wa Hajiya sai wannan, shiyasa hawayen suka kasa tsayawa sai sauka suke yi a fuskar Zee, saboda ta kasa ɗauke idanuwanta akanshi sabida mamakin da ya game jikinta da zuciyarta. Zee cikin wani fushi mai cike da zallar tsagwaron kishinshi ta yunƙura cikin zafin nama ta yi saurin tureshi ta miƙe tsaye, idonta akanshi hawaye suna zuba masu zafi ta nunashi da hannu ta ce "Ka yi gaggawar sanar da ni wacece khadija tun kafin ka janyo zuciyata ta buga" To fa🙀Ke ko amarya kar ki yi fatar bugawar zuciya a ranar farko gidan aurenki😢 Akafta😝 D/AUTA Ce✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *special thanks to you all my FANS😉* *Lamba 59* Cikin sanyin jiki ya miƙe tare da janyo ƙafafuwanshi zuwa inda take sannan ya yi ƙarfin halin riƙo hannunta, cikin fushi ta ƙwace hannun tare da matsawa baya tana yi masa wani kallon mai cike da fushi tace "Wacece wannan baƙar yarinyar da kake ambata a gabana?? Don na ce ina sonka laifi na yi da har kake ƙoƙarin baƙanta man cikin lokutana da Allah ya bani daga gareka??, Sakayyar da zaka yi man.. ke....nan?" Ta ƙare maganar cikin sarƙewar murya tare da zuwan wani masifaffen kuka, cikin tsananin damuwa Safwan ya isa wurinta ya rungumota jikinshi, ba shiri ta faɗa ta narke masa tana wani irin kuka gwanin ban tausayi, cikin dakusasshiyar muryarshi da ta sha kuka ya shafo gashinta ya ce "Don ALLAH ki yi haƙuri kinji? Insha ALLAHu hakan ba zata sake faruwa ba" Zee ta share hawayenta sannan ta ɗago tana kallonshi tace "Matuƙar kana son mu yi zama na jin daɗi da farantawa juna ni da kai, to ya zama dole ka nisanci duk wani abunda zai janyo muna matsala, saboda akanka wallahil'azim zan iya aikata koma menene saboda haka ka kiyayi faɗin sunan kowace shegiya a gabana, that's the first and last idan har kana son farin ciki a gidanka" Safwan ya yi shiru yana nazarin rashin dacewar abunda ya aikata, amman duk da haka wani sashe na zuciyarshi cike yake da jin zafin baƙar da ta kira Khadijarshi, sai dai saboda sanin shine mai laifin yasa ya zare jikinshi daga nata ya nufi kan gadon ya kwanta, tare da dafe kanshi yana nazarin mafita akan matsalolin da suke son ruftowa rayuwarshi. Cikin damuwa Zee ta bishi da kallo sannan ta ƙaraso ta zauna gefen gadon tare da riƙo hannunshi ta ce "Baka sanar da ni matsayin wannan suna da naji kake ta ambata ba tun jiya har yau, wacece ita? Saboda jikina yana bani cewa tabbas itace silar shigarka cikin wannan sabon yanayin da ka ke ciki" Safwan ya janyo hannunta saman ƙirjinshi sannan ya ce, "ki yi haƙuri khadija matata ce asali ma itace matar da kika ji an ce da ke ina da, kuma ita ce Uwargidana a yanzu haka, amman duk da haka nan ina baki haƙuri akan laifin da na aikata kuma insha ALLAHu bazan sake ba" A hankali ta zare hannunta cikin na shi saboda wani kuka da ya zo mata, sannan ta miƙe cikin jarumta ta ce "bari in je wajen su Ruma kada su ga na barsu" Ƙanzil bai ce da ita ba har ta fice zuciyarta cike da tsantsar baƙin ciki, tafiya take yi idonta a rufe saboda zallar tsagwaron kishin Dijen da ya rufe mata idanuwa, har ta isa sashenta bata san ma ta kai ba har sai da ta jiyo shewarsu Ruma sannan ta yi saurin share hawayenta tare da saita kanta ta shiga tana wasar baki, aiko suka yo mata caa da tsokana ko wa da abinda ya ke faɗa akanta, da kyar ta sulle ta faɗa toilet inda ta ɗauki lokaci tana ta kukanta sannan ta baiwa kanta haƙuri ta yi wankan ta fito. Da taimakon ƙawayenta ta fesa wata arniyar kwalliya ta ci wani danƙareren less black colour tare da ɗigon pinck a jikinshi, an mata ɗinkin half bubu ta ji aiki sosai a gaban rigar, sannan ga ɗaurin ɗankwalin da suka yi mata irin na wayayyun ƴanmata, sai gata da fitowa sharri! Masha ALLAH sai pics ake yi mata tana jin kanta wata shegiya, sannan su ka ta yi tare da ƙawayenta suna iya shegensu, duk da ita kam ƙarfin hali ne kawai ta ke yi tana wayancewa cikinsu ana ta sharholiya. Bayan sun yi break ne Safwan ya zo suka gaggaisa tare da yi masu godiya akan ɗawainiyar da suka yi, sai dai da yawa wasu daga cikin ƙawayen nata sun ƙyasa sosai akanshi, wasu ma har kwatantawa suke yi ina ma ace sune suka sameshi, wasu kuma suka ga gaskiyar Zee da ta nace sai shi duk cewa shi kanshi Aminun ba abun kushewa bane, amman ko kaɗan ba za'a haɗashi da Man ɗin Zee ba, saboda Safwan ƙosasshshen ingarman namiji ne cikakke mai cikar haiba ta ko'ina, saɓanin Aminu da yake siriri sosai sai dai daga ganinshi zaka gano cewa shima jarumin gaske ne. Bayan fitarshi ne Zee ta samu keɓewa da wasu amintattun ƙawayenta biyu Ruma da wata Sadiya, inda ta sanar da su irin abunda Safwan ɗin ya yi mata, Ruma ta yi shiru sannan ta ce "Ke fa mace ce don haka ki bi shi da taki kalar salon kissa don ki samo kan Mijinki, saboda irin wannan renin hankalin WALLAHI ba kowa ce mace ce zata iya jura ba gaskiya, don ance yana son Matarshi ai ba sai ya nuna maki ba tunda dai ke ma ɗin yanzu Matarshi ce, don ko an ƙi ko an so ke da ita duk matsayinku ɗaya a wurinshi, to cin zarafin kiran sunanta a gabanki na minene?" Sadiya ta yi saurin faɗin "Wa ya ce matsayinsu ɗaya? Don Allah ki daina ragewa Zee martaba Rumasa'u, ai ko makaho ya shafa Zee ya shafa waccen matsiyaciyar Uwargidan tashi duk da bamu santa ba WALLAhi kinsan Zee ta fita nesa ba kusa ba" Ta dafa kafaɗar Zee da ta yi tagumi tana saurarensu ta ce, "ke mrs Man buɗa kunnuwanki da kyau ki ji Ni, WALLAhi ki zage damtse ki fatattaketa da kyau a zuciyarshi don ke ma ki sami matsugunnin da ya fi na kowa a wurinshi, in ba haka ba WALLAhi kina ji kina gani zata ƙwace maki mijin ta barki da cizon yatsa, kallarki da kyau mace har mace son kowa ƙin wanda bai samu ba, don haka ta ƙarfin tsiya ke ma ki mamaye ko'ina na zuciyarshi, ke in da hali ma kada ki bari ko kaɗan ta raɓeshi ki kama abunki ki riƙe gam gam tunda dai ba wani abu aka fiki da shi ba, kyau kuɗi iya soyayya da hali mai kyau kowane ALLAH ya baki ai, saboda haka ya rage naki ki ƙwaci Mijinki tun kafin kwaɗo ya yi maki ƙafa kina ji kina gani, don WANNAan tsadadden mijin naki ko wace mace a duniya tana son irinshi idan zata samu" Ruma ta yi ƙarfin halin cewa "Haƙiƙa kam tun kafin ki aureshi ƙanwarshi da kanta ta sanar da ni yana bala'in son Matarshi, saboda haka Ni ina ganin tunda har karatu aka ce tana yi me zai hana ku tattara ku bar ƙasar ku koma school abunku ke da shi, kin ga daga cen sai ki cusa masa kanki ta yanda ko sunan wata mace ma ba zai so a faɗa ba bayan ke, kin ga duk lokacin da ku ka dawo ba wani power da ita waccen matar tashi zata fi ki a wajenshi, saboda kin riga da kin mallake komi dole ta yi haƙuri don kin fita a wurinshi, tsorona ɗaya ne kada ace itama sai ta biku kun je tare, don a gaskiya idan aka yi maki hakan za'a wargaza komi" ZEE ta yi saurin faɗin "Ba ma za'a je da ita ba WALLAhi, haka kawai in dai ba salon mugunta ba ai tun cen tare aka ganmu ita kuma tana nan, To yanzu kuma akan me za'a ce ta bimu? lalle ma ai WALLAHI da taga rashin mutuncina kuwa don sai nasa ta dawo gidan ubanta ba shiri, saboda sai na nuna mata cewa ita ƙaryar asirin farauto zuciyar miji take yi, da salon Soyayyata zan sakashi ya manta uwar da ta haifeshi ma ballantana ita ƙaramar ƴar iska" Ta ƙare maganar cikin huci, Sadiya ta dafa kafaɗarta ta ce "Cool down Zee Sani wannan faɗan fa duk mai sauƙi ne idan kin so ki sauƙaƙawa kanki shi, yanzu dai miji a hannunki yake to ki yi iya ƙoƙariinki wajen ƙwamuso abunki ya dawo hannunki, Saboda ke ce amarya mai sabon muhallin shiga har ana ihu musamman idan kina gyara jikinki, to ko uwarshi kika ce kada ya kalla bai isa ya kalleta ba bale wata aba kishiya cen, wadda idan kika so cikin ƙanƙanin lokaci zaki saita mata hanyar zuwa gidan ubanta ba tare da ta shiryawa zuwan ranar ba" Daga Zee har Ruma suka ƙyalkyale da dariya har da su shewa, ZEE tana dariya tace "Daɗina da ke ƙawata baki da sanya, WALLAhi tunda har ya tsiro da wannan renin hankalin to Ni kuma sai na nuna masu cewa ba a banza aka haifoni duniya ba" Haka suka yi ta zuga Zee tana hawa tare da sanar da ita wasu salon kissoshi da bata san da su ba, sannan aka yi masu sha tara ta arziƙi suka tattara yanasu yanasu suka koma Gombe, tare da yi mata fatar zaman lafiya da mijinta. **** Amarya Zee kam sannu a hankali ta dinga nutse Angonta cikin tafkin kogin ƙaunarta, saboda ko kaɗan bata gajiya da buƙatarshi akan hakan ta sami matsayin da ko kaɗan bata yi tsammani ba, saboda salon kissar da ta mamayeshi da ita wadda ko kaɗan bata nuna masa jin haushinta akan damuwar rashin Dijen da yake yi, illa ma haƙurin da take ba shi duk da har lokacin bata san asalin labarin ba, saboda ta tafi ne kawai a zuwan makarantar da take yi ne baya so a sanadin hakan ta haifar masu da matsala, shiyasa ya shiga irin wannan damuwar ta yi amfani da damarta ta saka shi nanuƙe mata kullum, saboda ba laifi ta tsayu da kyau wajen gyara jikinta a ƙokarinta na son fin kowa a wurinshi. Bayan sati biyu da aurensu ne suka yi sallama da kowa suka kama hanyarsu ta zuwa London, zuciyar Zee cike da jin daɗin ganin Safwan ɗin ya zama nata ita kaɗai kuma mallakinta, saboda ko kaɗan Hajiya Mama bata nuna cewa sai an tafi da Dijen ba, don ganin yanda Zee take ta rawar kai da Safwan ɗin, kuma ta fi son duk lokacin da Dijen zata dawo gareshi ya zamto itama ta zamo mace dai dai da kowace mace mai ji da kanta, wanda a lokacin ita da kanta zata ƙwaci ƴancinta a hannunshi ba tare da ta nemi taimakon kowa ba. ***** Dije kam tun tana damuwar rabuwa da su Hajiyar tare da kewar Mijinta har ya zamo ta saki jikinta ta fara zuwa Makarantar da aka sakata ta fara daga class five waton ss 2 wadda ta zamo jeka ka dawo ce kullum da mota ake kaita a dawo da ita, babu inda take zuwa daga gida sai makarantar sai kuma idan zasu je yawon buɗa idanuwa wurin shaƙatawa kala kala ko kuma idan zasu shiga shaguna siyayyarsu ko ta gida, sannu a hankali idon Dijen Baffah ya fara buɗewa ta fara jin kanta itama wata aba ce mai daraja, musamman idan ta ga ta yi wanka ta sade cikin ƴaƴan Aunty Ummin ba wani banbanci sai fari da zasu nuna mata, don idan ma aka ce za'a tantance take yanke za'a ce ta fisu, saboda cikar ƙirjinta da suka ƙara fitowa ɓul ɓul ga kuma hips ɗinta da ya buɗe tare da tudun duwawunta masu gantsarwa da suka turo, don ko hijabi ta saka dole ne ma sai sun fito ballantana tana cikin shigar ƙananan kaya, fatarta ta murje sosai sai sheƙi take yi haka ma jikinta ya mulmule ta ko'ina ba rama. Ga cima irin ta yangayu da take ci ga zama wuri ɗaya da hutun ya ratsa jikinta, tubarakallah masha ALLAH Dijen Baffah kam, don kuwa duk mai son mace ya ganta ya zo ƙarshen nema. Duk da jin daɗin da take yi hakan bai hanata yin kewar Mijinta ba, don kuwa lokaci zuwa lokaci tana tsintar kanta cikin wani sabon yanayin buƙatuwa da mijinta, amman dole take ɓoyewa don bata son Aunty Ummi ta ganota, sai ga shi watarana tana dawo wa daga school ta taradda wayar Aunty Ummi tana ta ɓurari soke da caji, ta ɗauka ta nufi ɗakinta bata nan ta dawo ɗakinsu Husnah babbar ƴar Aunty Ummin da nufin ta tambayesu ita, suka sanar da ita ai ta fita wataƙila mantawa ta yi da wayar ta fita ta barta, sai ga kiran ya katse aka sake bugowa Husnah ta karɓi wayar tana ganin numbar ta gano Safwan ne, cikin dariya ta miƙa mata wayar ta ce "Aunty Khady ki ɗauka mana maybe uzurin babba ne shiyasa ake ta kira" Kasancewar number ce kawai ba suna shi yasa ta yi saurin ɗauka ba tare da ta ce ƙanzil ba ta ji ya ce "Plss Aunty Ummi don ALLAH ki tayani roƙon Hajiyarmu ta dawo man da matata WALLAhi a takure nake sosai da rashin sanin inda take, don ALLAH Aunty ki ce ta bani matata WALLAhi buƙace nike da ita kamar in kuwata" Dije ta yi saurin cire wayar a kunnenta ta goge kwallar da ta sauko mata ta miƙawa Husnah wayar cikin sanyin jiki ta fice ɗakin ta nufi ɗakinta da aka ware mata ita kaɗai, Husnah ta bita da kallon tausayi ta kara wayar a kunnenta saboda maganar da yake ta yi yana kiran sunan Aunty Ummin cikin magiya, cikin wata muryar tausayawa dukansu ta ce "Auncle Mummy bata nan ta fita idan ta dawo za'a sanar da ita ka kira" Cike da jin haushinta ya ce, "uban wa ya ce ki ɗauki wayar kin san bata nan?" Ta yi saurin faɗin "Sorry Auncle....." Kittt ya kashe wayar cike da jin haushinta, Husnah ta sauke wayar ta yi shiru tana nazari sannan ta miƙe ta nufi ɗakin Dijen, sai dai kukan da ta ji tana yi ne yasa ta yi saurin isa wurinta tana faɗin "Plss Aunty Khady ki yi haƙuri ki yi shiru ki sanar da ni abunda kike wa kuka, Ni kuma insha ALLAHu zan taimakeki ko don ki sami farin ciki" Da ƙyar ta shawo kanta ta yi shiru sannan Dijen ta miƙe zaune tare da share hawayenta ta ce, "kin yi alƙawalin ba zaki faɗawa kowa ba?" Husnah ta yi mata kallon tausayi ta ce, "ki faɗa kawai Auntynmu ni nace da ke zan taimakeki in dai hakan zai sakaki farin ciki" Dije ta ce "Ya zanyi in dinga communicate da Auncle ɗinku ba tare da ya gano ni ce ba?" Husnah ta yi shiru sannan tace, "ki bani yau zuwa gobe zan samo maki number'rshi da yake using da ita yanzu, ke kuma sai a buɗa maki whassapp ki dinga yi masa magana a ɓoye amman fa plss kada ki bayyana masa inda kike, har sai lokacin da Hajiya Mama ta sanar da shi da kanta, don WALLAhi Mummy tasan da Ni a wannan lamarin kinsan zan ci Ubana ne a hannunta" Dije cike da jin daɗi tace "na amince My Husny don ALLAH ki taimakeni WALLAHI da kinyi man haka kin gama man komi don sai naji daɗi sosai, kuma kin ga ke ma ai zaki sami lada" Husnah tana dariya ta ce "ai naji haushin da wayar Mummy take da security na fingerprint WALLAhi da yanzun nan zamu samota" Dije ta dafe goshi tace "Ai shiyasa ma kika ga bana taɓa wayar Aunty saboda ba abunda zaka iya yi da ita idan ma ka ɗauka" Haka suka yi ta shawarwarinsu har dare lokacin da Aunty Ummi ta yi bacci, sannan Husnah ta je ta lallaɓa ta saka yatsanta da ta yi lock ɗin da shi ta cire securityn, sannan ta yi saurin shiga wayar ta ɗauki number'r Safwan a wayarta ta ajiye wayar ta fito cikin sanɗa, sannan ta dawo wurin Dijen da ke ta tsumayin jiran fitowarta, kai tsaye ta bata numbar ta yi saving a wayarta, sannan ta nuna mata duk yanda zata yi da yanda zata shiga da fice cikin whassapp ɗin, sannan ta yi mata sai da safe ta shige ɗakinsu. Dije kam cike da tsananin farin ciki ta shige nata ɗakin ta dantse, sannan ta haye gado cike da murna ta fara shiga contacts list ɗinta sai ga number'r Safwan ta fito raɗam tare da hotonshi da ke dp, inda ya sha ƙananun kaya sun fito da kyaunshi sosai sai dai ƴar ramar da ya yi, amman duk da hakan sajenshi da ɗan ƙaramin gemunshi sun ƙawata fuskarshi gwanin burgewa, ya fito bafulataninshi na usuli mai cikar zati tare da tarin kamala da ke tattare da fuskarshi. Dije ta yi zooming hoton sosai tana shafo fuskar sannan ta kai bakinta ga hoton ta yi mai kiss ba shiri ta rufe fuskarta tana dariya alamun jin kunya, sannan ta shiga ta fara yi masa sallama, aka yi dace yana online amman bai kula da ita ba ma balai ya duba yaga ko wace ce, saboda ganin baƙuwar number Kuma daga Nigeria, don in da sabo ya Saba da gayyar mata da maza masu son cuso kansu gareshi ta ƙarfin tsiya, shiyasa bai cika damuwa ma da ire irensu idan ya gani ba, Dije kam ganin bai amsa ba yasa ta sake turo masa emoji na kuka mai ɗauke da ƙwalla kamar haka😢ta sake ce wa _Salam!_ Amman nan ma shiru cike da jin haushi ta shiga gallery ta Ciro wani pic ɗinta Wanda daga ita sai guntuwar t.shirt baƙa ba ɗankwali sai dai ta yi cropping ɗinshi ta cire fuskarta ta bar ƙirjinta kawai tare da jelar gashinta da ta sauko a kafaɗunta har gaban ƙirjinta, sai da ta tabbatar da hoton ya shiga sannan ta yi offline zuciyarta cike da jin daɗin ganin photonshi. Dijen Baffah banda jan rai hwa🙄 Akafta😝 D/AUTA Ce✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *Na gode sosai da addu'o'inku gareni i luv u all my guys💋* *Lamba ta 60* Sai dai ƴan mintuna a tsakani ta kasa haƙuri ta dawo abun haushi har lokacin bai duba ba, cike da takaici ta kashe datar ta kwanta abunta tare da ƙarewa pic ɗinshi da ta ɗauka kallo, haka ta kwana cikin begen Mijinta tare da mafalkinshi kala kala. ***** Malam Safwan kam sai da ya kammala uzurin da ke gabanshi zuciyarshi ta ƙawata masa duba sauran text's ɗin da ake turo masa da numbers mabanbanta, cikin nasara ya kawo kan na Dijen Baffah cike da mamaki ya bi massages ɗin da kallo _Salam_ _😢_ _Salam_ Sai hoton da ta turo wanda idonshi a kan dukiyar fulaninta da suka cika ƙirjim fam kamar za su fasa rigar su fito, ba shiri ya haɗiyi wasu yawu da suka tsinke masa, sannan ya sake yin zooming ɗin pic ɗin haka kawai ya tsinci kanshi da faɗin "I like it" Amman a zuciyarshi ya ce _ita kuma wannan wacece take son janyo hankalina da abunda na fi so a jikin mace??._ Haka kawai ya ji ya kasa ɗauke kanshi daga pic ɗin sai ga shi da tsintar kanshi cikin wani yanayi marar misaltuwa, cikin wata kasala da ta sauko masa ya mayar mata da reply kamar haka _wslm plss wace ce?_ Sannan ya kashe wayar yana ta ƙarewa pic ɗin kallo duk da wani sashe na zuciyarshi yana yi masa kashedi da kallon pic ɗin, kuma ta shawarceshi akan ya goge hoton sai dai kuma ya kasa baiwa zuciyarshi haɗin kai, saboda ba ƙaramin kyau suka yi masa a ido ba. Dije kam ko da safiya ta waye tana gama SALLAHr asuba ta janyo waya ta duba cike da zumuɗi tare da fatar ya ga massages ɗinta, ai kuwa sai ga shi ta ga ya duba har da su reply, cikin rawar jiki ta mayar masa da amsa kamar haka _"Am the one how was the day??"_ Sannan ta sake ɗauko wani pic ɗin wanda daga ita sai rigar bacci mai siririn hannun vest, ga shi ko bra babu a jikinta sun fito sosai masha ALLAH ta yi crop ɗinshi ta cire fuskarta, sannan a ƙasan photon ta rubuta _Good morning my life partner._ Sannan ta sauka ta nufi kitchen ita da su Husnah da wasu ma'aikatan gidan biyu suna shirya abun break fast, Bayan sun ƙare ne ta dawo ɗakinta da nufin yin wanka, amman zuciyarta ta ƙawata mata ta duba ta ga in ya ga saƙonta, sai dai ganin bai hau online ɗin ba yasa ta yi saurin shigewa toilet domin ta yi shirin zuwa school. Dije har ta je makarantar ta dawo tunaninta yana kan wayarta, saboda son ganin wane saƙo ne ya turo mata, aikuwa cike da ɗoki ta duba wayar sai ga reply ta gani kamar haka _"Idan ba zaki buɗe fuskarki ba kada ki sake yi man magana"_ Cikin daburcewa Dijen ta yi shiru tana nazari sannan ta yanke wata shawara ta sake ciro wani photon wanda ta yi daga ita sai wata doguwar riga half gown ta kanti da wani wando skin tight baƙi, inda ta juya gefen fuskarta kawai ya fito don gaba ɗaya ma bayanta kawai aka ɗauka sai gefen fuskarta ga gashinta ya zubo har gadon bayanta, sannan a ƙasanshi ta rubuta "Good bye" Aka yi da ce shima yana online saboda ya kasa natsuwa zuciyarshi sai hasko masa fuskar Dije take yi a matsayin mamallakiyar photon, shiyasa ya ce idan ba za'a turo fuska ba kada a sake yi masa magana saboda kawai ko wacece ta bayyana kanta, sai ko ga shi wannan photon da ta sake turo masa na ƙarshe ya tabbatar masa da lalle Khadijarshi ce, saboda ko a mafalki ya ga gefen fuskarta sai gano ita ce bale a ido biyu, sai dai kuma kokwanton da ya ke yi akan anya zata iya aikata hakan gareshi,sai ga shi da tsintar kanshi cikin wani tsantsar farin ciki marar misaltuwa, cike da zumuɗi ya yi saurin mayar da reply da cewa _"wow! wonderful babe! plss Ina buƙatar wasu pic's ɗin amman masu ɗauke da kyakkyawar fuskar da ke jikin wannan tsadadden body"_ Cike da jin daɗin yabon da ta ji ya yi mata ta yi saurin rufe furkarta Kamar a gabanshi, kasancewar itama a matse take da son Mijinta na ta cikin sauri ta mayar masa da reply ɗin cewa _"Thanks my angel"_ Safwan ya bi text ɗin da kallo zuciyarshi cike da tsanani ƙaunar Dijenshi, duk da bai tabbatar da ita ɗin ce ba amma jikinshi ya ba shi ita ɗin ce shiyasa ya sake cewa da ita _"More pictures plss"_ Ta mayar masa da reply ɗin _" No bye"_ Ya yi saurin rubuta _" wait! wait! plss my precious what's your name?"_ Dije zata mayar masa da amsa kenan ta ji muryar Aunty Ummin zata shigo ɗakin, cikin sauri ta ajiye wayar ta faɗa toilet, ko da ta zo taga bata ɗakin ta ce "Ki fito ki ci abinci Ni bana son yi wa kai horon yunwa" Daga cen toilet ta yi gyaran murya alamun ta ji ta sannan Aunty Ummin ta fice ɗakin, cikin sauri Dijen ta tuɓe Uniform ɗinta daga cen toilet ɗin ta yi wanka a gurguje ta fito, sai ga kira ya shigo wayarta tana duba sunan mai kiran ta ji ƙirjinta ya buga dam! Amman ta yi jarumtar ɗauka sannan ta ajiye wayar akan gadon ba tare da sanin cewa Video call ne Safwan ya kirata ba, ta ƙurawa wayar kallo ta kasa ɗauka bale ta saka a kunnenta sai ganin fuskarshi ta yi cikin screen ɗin wayar ta yi saurin zaro ido waje tare da dafe ƙirji, inda shi ma ɗin ita yake kallo cikin mamakin yanda ta koma saboda daga ita sai guntun towel iya cinya, ga abubuwan da yake so cike fal a ƙirjinta ba shiri ya tsinci kanshi cikin wata kasala tare da faɗin "Khadijah me yasa kika tafi kika barni? Me na yi maki da ......." Fisge wayar da aka yi a hannunshi ne yasa maganar da yake yi ta katse, saboda ZEE cike tsantsar kishin kiran sunan Dijen da ta ji ya ambata yasa ta ƙaraso wurinshi ba tare da ya kula da ita ba, hango yanayin da Dijen ta ke ne duk da bata ga fuskarta da kyau ba yasa ta ji wani bala'in kishi ya rufeta, wanda ya janyo ta fisge wayar da ƙarfi tare da dokata ga ƙasa ta tarwatse, ya bita da kallon takaici ranshi a matuƙar ɓace ya ɗaga hannu ya watsa mata wani wahalallen mari har sau biyu, sannan ya zare belt ɗin jikinshi ya yi ta mazgarta tana ihun neman taimako babu mai cetonta, sai da ta lallasu da kyau sannan ya saurara mata cikin fushi ya ce "Akan wannan rashin hankalin naki WALLAhi zaki janyowa kanki wahala a hannuna, ko an ce maki ina cikin mazajen da mata suke juyawa ne?, Ke har kin isa ina tare da matata ki hanani yin abunda nake so?, To bari ki ji akan wannan haukar ta ki zaki janyo wa kanki komawa Nigeria WALLAhi, saboda ina da ikon da zan datse karatun naki gaba ɗaya idan kuma akwai wanda ya isa ya ce sai kin ƙarasa to sai ya dawo da ke in gani" Yana ƙare maganar ya wuce fuuu ya fice ya barta tana ta kuka tare da mamakin wai ita ce yau Man ɗinta ya daka akan matsiyaciyar Matarshi. To fa su Zee an Fara sanin wanene Safwanu😊 Akafta😝 D/AUTA Ce✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *Ina alfakhari da ku my fans saboda ku ne ƙashin goyon bayan duk wata ɗaukaka da zan samu, ina yinku all a ko'ina kuke kuma a duk inda kuka kasance, tsakanina da ku sai son so fisabilillah😅* *Lamba ta 61* Sai da ta ci kukanta ta ƙoshi sannan ta baiwa kanta haƙuri dolenta, don bai dawo gidan ba har sai da ya tabbatar da ta yi bacci sannan ya shigo, saboda baya son haɗa ido da ita akan nauyin dukan da ta janyo ya yi mata, duk da wani sashe na zuciyarshi yana ba shi cewa ko kaɗan bai yi laifi, don yanda ya ƙagu da yasan inda Khadijarshi take komi zai iya aikatawa akan wanda ya ke so ya toshe masa ƙofofin da da zasu sadashi da farin cikinshi. Sannu a hankali ya ƙaraso wajen wayarshi da ke tarwatse har lokacin, ya duƙa ya ɗauki kangalwar wayar ya zare sim cards ɗinshi sannan ya saka cikin wata sabuwar wayar da ya siyo, sai dai baƙin cikin rashin saving ɗin numbar Dijen da bai yi ba tun farko yasa ya dannawa Hajiyarshi kira, bayan sun gaisa ya marairece murya ya ce "Haba Hajiyarmu plss don ALLAH ki sanar da ni inda aka kai Khadija, saboda jikina yana bani cewa ba aikatau Khadija ta je ba, don ALLAH ki tausaya man Hajiyarmu ki bani matata WALLAhi ina sonta sosai" Hajiya Mama ta yi shiru sannan ta ce "Ka kwantar da hankalinka duk lokacin da ka dawo ƙasar nan insha ALLAHu zaka taradda kHadija a gidanka zaune tana jiran dawowarka" Cike da tsananin jin daɗi ya ce "in dai haka ne to ni ai sai in tattaro kayana kawai in dawo gida Hajiyarmu" Ta ɓata fuska kamar tana ganinshi ta ce "shi karatun na ka idan ka dawo wa zai ƙarasa maka shi ne?bayan saura lokaci kaɗan ka kammala" Safwan ya sosa kanshi yana murmushin jin daɗi ya ce "to Hajiyarmu me zai hana ayi mata viza kawai ta samemu anan ɗin ta tayamu zaman, kin ga in mun kammala sai mu dawo gida tare gaba ɗayanmu?" Hajiyar ta yi ƴar dariya sannan ta ce "ita kuma karatun nata fa? Sai ta ajiye ta zo ta tayaku naku karatun kenan? to bari ka ji idan ka kawo wasa ko ka dawo bazan bari ka ganta ba, matuƙar baka natsu ka ƙare karatunka da ya rage saura ɗan lokaci ba" Safwan ya durƙusa ƙasa kamar a gabanta ya ce "plss Hajiyarmu don ALLAH ko numbar da zan sameta ne a bani plss sai mu dinga gaisawa, don wallahi rashin jinta zai iya janyo inyi asarar duka shekarun da na ɓata a baya wajen karatun" Hajiya ta yi shiru sannan ta ce "zan baka numbar khadija amman da sharaɗin bazaka tambayeta inda take ba har sai ka jira na sanar da kai da kaina, kuma ko da ka gano daga baya ba zaka ga laifin wadda take wurinta ba don Ni na bata khadija da hannuna" Cikin zumuɗi ya ce "bani numbar kawai Hajiyarmu wannan duk mai sauƙi ne in dai har na sami number'rta" Ba ɓata lokaci Hajiyar ta saka Fiddo ta yi masa sending number'r ta whassapp cike da zumuɗi ya yi Saving ɗinta a cikin wayarshi sannan ya danna mata kira. Dije kam kasancewar bata nan tana school saboda lokaci ba ɗaya ba, kuma ga wayar ma a kashe take shiyasa ya yi kira ya kai hamsin amman bai sameta ba, cike da jin zafin hakan da takaici ya yi kwanciyarshi akan kujera ya ƙi zuwa wurin Zee da tunda suka yi aure basu taɓa raba wurin kwanciya ba sai ranar, haka wanibacci mara daɗi ya fisgeshi mai ɗauke da mafalkin khadijar saboda tunaninta ne a zuciyarshi har baccin ya yi awon gaba da shi. Zee cikin bacci ta shafo gadon ta ji wayam ba kamar kullum yanda ta saba shigewa jikinshi tana shagwaɓa ba, ta yi saurin buɗe idonta tare da kaiwa kan gadon kallo sai gata da miƙewa zaune ba shiri, cikin mamakin sababbin halayen da ya tsiro mata ta sauko gadon ta fito falon, in da ta hangoshi kwance da alamu ma baccin yake yi, nan take wani kuka ya zo mata ta janyo ƙafafuwanta ta ƙaraso bakin kujerar ta yi duƙuso, sannan ta ɗora kanta saman ƙirjinshi ta fara kuka ƙasa ƙasa, cikin bacci ya jiyo sautin kukanta ba shiri ya buɗe ido tare da shafo kanta da ke saman jikinshi, ya yi shiru yana sauraren kukan nata ba tare da ya ce da ita ƙanzil ba, ganin ta ƙi daina kukan ne ya yi dubarar cire kanta ya miƙe zai bar wajen ta yi saurin riƙo ƙafarshi ta ce "Ka kasheni kawai tunda har ba zaka iya cewa da ni in yi haƙuri in daina kukan ba" Safwan ya fisge ƙafarshi ya koma ɗakinsu ya yi kwanciyarshi, Zee ta biyoshi cikin fushi ta hau gadon tare da ciyo kwalarshi daga kwancen ta ce "WALLAHI tun da ba wukaƙantatta ka ganni ba ka yi kaɗan ka wulaƙantani akan wata matsiyaciya" Kalmarta ta ƙarshe ba ƙaramin baƙanta masa rai ta yi ba, amman ya yi mata shiru tana ta surutanta na cin zarafi gareshi ga kuma Dijenshi, sai da ya ga renin hankalin nata zai yi yawa ne ya yi saurin miƙewa zaune da nufin kai mata wani wawan mari, cikin tsoro ta kwarma ihu tare da sakinshi ta maƙe jikin gadon tana kyarmar tsoro, cike da takaici ya kalleta ya tabbatarwa kanshi idan ya biyewa zuciyarshi ba ƙaramin duka zai yi mata ba, kuma a yanayin jikinta ba ƙaramar illah zai yi mata ba idan har ya ce kullum ya saki ƙwanji ya yi ta jibgarta, shiyasa ya nunata da hannu ya ce "Ki kiyayi kawo man ƙananan rashin kunya matuƙar kina son jikinki ya tsira da dukana, idan kuma kin fi son in yi ta jibgarki a banza to ki ci gaba da nuna man kalar taki rashin kunya" Yana ƙare faɗar maganar ya gyara kwanciyarshi ya kwanta abunshi zuciyarshi cike da ƙuncin rashin samun Dijen da kuma takaicin rashin kunyar da Zee take son yi masa,wadda ko kaɗan ba ya jin zai iya ɗaukar mata wannan halin renin da take son kawo masa. Ganin ya yi fushi da yawa ne ta janyo jiki ta faɗa jikinshi tana share hawayenta ta ce "To ni dai ka yi haƙuri ai kai ne ka janyo komi muna zamanmu lafiya" Ya saka hannu ya tureta ta sake maƙaleshi tana yi masa wani salon da ta san zata samo kanshi, amman duk da ya ji abun har cikin jikinshi a hakan ya mazge ya nuna bai ma san me take yi ba, ganin haka yasa ta marairece tana ba shi haƙuri cikin muryar kuka tare da yi masa kalamai masu nuna karayarta a zahiri, sannan ta samo kanshi amman tare da alƙawalin ba zata sake yi masa irin hakan ba, itama ta roƙeshi duk abunda zai yi da Dijen ya yi a waje amman da ya dawo gida lokacinta ne, akan hakan suka shirya yarjejeniya har ta ciyo kanshi suka lula duniyar ma'aurata, duk da cikinsu kowane zuciyarshi ba daɗi amman hakan bai hanasu gamsar da juna ba. **** Dije kam itama a ƙagauce ta dawo saboda tunanin sahibul ƙalbinta don ba kiran da bata yi masa ba amman wayarshi ta ƙi shiga, ta hau online ta yi ta bulayin jiranshi nan ma bai hau ba, ta yi ta ajiye masa saƙo ya fi goma na damuwa da rashin jinshi amman bata ga ya duba ba, dole ta haƙura ta kwanta, da safe ma cikin sanyin jiki ta yi komi ta nufi makaranta ba kuzari saboda rashin jinshi da bata yi ba, shiyasa yanzun tana dawowa ko Uniform bata cire ba ta ɗauko wayar ta kunna, abun haushi har lokacin bata ga ya duba massages ɗin da ta tura masa ba, dole ta ajiye wayar ta cire kayanta ta shiga wanka. Da marece sakaliya suna harabar gidan ita da su Husnah da sauran yaran gidan suna shan iska ne kiranshi ya shigo wayar, ta yi saurin komawa ɗakinta ta rufe sannan ta ɗauki kiran da ya zama na uku zuwa huɗu bata ɗauka ba, cike da jin daɗin ɗaukar da ya ji ta yi yace "Plss! Khadijah me na yi ake son horani da wannan babban horon?" Cikin ƙasa da murya ta ce "wane horo?" Ya ce "ga shi nan mana ana ta yi man kala kala, plss ki daina kashe waya bana son in kiraki in ji ta a kashe kin ji??" Ta ce "tom". Ya sauke ajiyar zuciya ya ce "kina a ina yanzu haka kuma ke kaɗai ce ko kuwa??" Cikin daburcewa ta ce "A'inah nake?" Ya ce "Eh ina nufin a ɗaki ko falo ko kuma kitchen Ko karatu ki ke yi ne?" Ta ce "a'a ina ɗaki kwance kawai na ke kuma ni kaɗai ba kowa" Ya yi saurin faɗin "We'll idan na ce ki yi man wani abu zaki iya yi?" Ta yi shiru sannan ta ce "eh" Ya ce "ok tom Ina son ki tuɓe all ki ɗaukar mani pic's ɗinki Kamar guda goma ko fi haka, amman da sharaɗin duk kika zo cire wani abun sai kiñyi man pic a hakan kafin ki cire wani, tukunna ma menene a jikinki?" Dije da jikinta ya ɗauki rawa ta yi shiru sai da ya yi tambayar sau uku sannan ta ce "riga da siket ne na atamfa" Ya ce "ok tom oya fara ɗaukar pic ɗin a haka sannan ki cire ɗankwali shima ki ɗauki pic haka zaki yi ta yi har sai kin gama cirewa all sannan ki yi man na ƙarshen wanda shi ne nafi buƙata akan kowane, na baki minti goma kacal idan kin kammala zan kiraki" Dije ta yi shiru tare da sauke wayar a kunnenta, jikinta sai rawa yake yi saboda tsoro da kunyar wannan abun da yake son ta aikata, har minti goman ta cika ya sake kira bata ko motsa daga inda take ba, shiyasa ya yi ta kira bata ɗauka ba wani bayan wani haka ya yi ta kira tana kallon wayar amman ta kasa taɓa ta, ƙarshe ma kashe wayar ta yi all zuciyarta cike da jin haushin me ma yasa ta bashi fuskar da har zai zo mata da irin wannan fetsara, ta yi kwance tana ta nazarin huɗubar da Inna ta yi mata akan duk abunda ya nema wajenta ta yi masa matuƙar ba saɓon Allah a ciki, cikin sanyin jiki ta buɗa wayar ta kira Sis Aysha da ta ke hardace da numbarta da ta ba su tun makaranta, lokacin da ta taɓa zuwar masu Visiting ita da Hannatu bayan ta ƙare makarantar. Kasancewar suna communication da juna ne yasa ta kirata tana shiga kira ɗaya biyu ta ɗauka, bayan sun gaisa cike da jin nauyi ta ce da ita zata turo mata text sai ta duba don ALLAH ta bata amsar da ya dace, minti biyu a tsakani ta gama rubuta text ɗin ta tura mata, sai ga reply ya shigo mata akan ta yi masa duk abunda yake buƙata tunda mijinta ne ba wani cen daban ba. Cike da jin nauyi ta yi duk abunda ya umurceta sannan ta gama ta tura masa su ta whassapp duks sannan tura masa text kamar haka "Ga saƙon cen na tura idan ka hau online zaka gani" Tana ƙare tura masa ta kashe wayar all sannan ta sake kimtsa jikinta ta fito suka ci gaba da sha'aninsu ita da yaran gidan, har dare bata kunna wayar ba sai da ta zo kwanciya ne ta buɗa saboda ta ga Ni Ko ya duba, aikuwa buɗe wayar ke da wuya sai ga kiranshi yana shigowa a wayar, ba shiri ta dafe goshi sannan ta ɗaga wayar zuciyarta cike da jin nauyinshi, amman sai ga shi dole yasa ta ware saboda kalaman ƙaunar da yake ta zazzage mata a cikin kunne suna sauka cikin gangar jikinta, inda cikin lokaci ƙanƙani suka tsintsi kansu cikin wani sabon yanayin buƙatuwa da junansu, akan hakan ya kirata video call suka ci gaba da shan soyayyarsu hankali kwance duk da Dijen ba wani sakin jiki take yi da shi ba. Wasa wasa sai ga Dije zaman ɗaki ya fara aurarta don kuwa yawan kiranta da yake yi yasa bata zama cikinsu Husnah, don yanzu ita kanta Aunty Ummin har ta fara yi mata tsarguwa akan soyayyar da suke kwasa, saboda yanda suke baje kolinsu ita da Malaminta abun ba kama hannun yaro, saboda da an taso school baya dawowa wurin Zee sai dare ya tsala sannan ya dawo ya lallaɓa ya kwanta, tun bata kulawa har ta zo ta fara damuwa tana yi masa ƙorafin rashin zama gidan da baya son yi, ba wani rufe rufe ya sanar da ita saboda baya son ranta ya ɓaci shiyasa ya ke zamanshi a cen wajen don kada ya shigo ya yi wani abun da zata ga kamar ya ci mata fuska, Zee ta fashe da kuka ta ce da shi ita sam bata yarda ba dole ne itama ya bata haƙƙinta itama tana buƙatar kulawarshi kuma ya bata lokacinshi su yi fira tunda ba ta da wani wanda zai ɗebe mata kewa a gidan bale su yi firar. Ganin ta ɗaga hankalinta ne akan dole sai ya zauna gidan ya fara rage lokacin da yake yi a wajen, cikin haka ne watarana yana chatt da Dijen wani uzuri yasa ya ajiye wayar ya fita, jikin Zee yana rawa ta ɗauki wayar ta fara yi masa bincike saboda ko kaɗan baya bari ta taɓa masa waya, sunan da ta ga Ni saman contact chat ɗinshi ne ya ja ra'ayinta da shiga kundin ma'adanar, sai gata da zaro ido waje saboda mugun ganin da idanuwanta suka yi mata don kuwa photon Dijen ne daga ita sai wata vest shara shara ko hannu bata da kuma gaba ɗaya shafin dukiyar fulaninta duk a waje don har kan nipple ɗinta ana hangowa cikin yar rigar, ba shiri ta kai zaune dafe da zuciya hawaye suna zuba akan fuskarta tamkar famfo, fige wayarshi da ya yi ne a hannunta yasa ta yi saurin kallo inda yake idonta a kanshi ta ce "Eh kam naga abunda kake ta aikatawa kullum shiyasa baka bari in tab'a wayar, wanda akanshi ne ma ka ke ɗaukar lokaci a waje baka dawowa gida sai dare ya tsala, to ita kuma wannan yar aikin taku da ka ce wa aikatau aka kawota gidanku yanzu kuma akanta ka lalace??, To billahillazi wannan karon sai dai ayi abunda za'a yi ko ni ko ita WALLAhi, don kuwa akanka wallahil'azim ko kasheta zan iya yi matuƙar ta sake shiga sabgarka, na fi son idan har na kasheta ni ma a zo a kasheni" To fa wata sabuwa na yi nan WALLAh🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️ tun kafin Zee ta gano ina masu leƙe ta shaƙo wuyana😅 Ina baran adduarku akan ALLAH ya baiwa Mahaifiyata lafiya mai ɗorewa😢saboda kwana biyun nan jikin sai a hankali😭 Akafta😝 D/AUTA Ce✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *Alhmdllh jikin Mummy ya yi sauƙi masha ALLAH, naji daɗin addu'o'inku sosai da sosai, hakan ya tabbatar man da cewa ni ma ɗin ashe kuna yi na😉, don da har na fara kishi da Dijen Baffah saboda yanda naga kuke sonta da yawa, shine na yi zaton kamar ta fini matsayi😅 ashe dai Ni ma ɗin ta ku ce ba algus tom Alhmdllh na gode sosai🙏🏻* *Lamba ta 62* Safwan ya bi ta da kallo baki a sake ya ce "wai ke me yasa ko kaɗan ba ki da hankali ne?, Yanzu ke ashe zaki iya kashe mutum da hannunki saboda kishi?" Ta murguɗa masa baki tare da riƙe ƙugu tace, "kai da bakinka ka sanar da ni cewa ƴar aikinku ce, kuma daga kai har munafukar ƙanwar ta ka kun nuna man cewa ita ce ke sonka kai baka sonta, to yanzu kuma akan mi take bibiyarka? kuma sannan har ka bata damar da Ni ma da kake aure baka bani irinta ba? Ga shi ka janyo ta yi nasarar shiga tsakanina da kai, don na tabbata akanta ne kake raba daren da kake yi a waje, to WALLAHI ka ji da kyau ka ƙara ji matuƙar baka sanar da ita ta fita sha'aninka ba WALLAhi ka ji na rantse sai na watsa mata fetur na ƙoneta ƙurmus kowa ma ya huta da mugun halinta na bin Mazajen mutane, yar iskar banza baƙar karuwa ALLAH ya tsinewa iyayen da suka kawota duniya ma balle it.......... " Saukar marin da ta ji ne a kumatunta yasa ta yi saurin haɗiye sauran maganar, cike da mamaki ta ke kallonshii hawaye suna sauka akan idonta ta ce "My man ni ce na zama jaka a hannunka saboda matarka?, Yanzun ma kuma saboda da tsananin lalacewar akan wata ƙaramar karuwa ka ɗaga hannu ka mareni?" Safwan ya yi saurin ɗaga hannun da nufin ya ƙara kai mata wani marin, me ya tuna kuma ya dunƙule hannun ya naushi iska sannan ya nunata da yatsa kamar zai tsole mata ido, jikinshi sai tsuma ya ke yi saboda tsabar ɓacin ran da ta cusa masa, ya ce "Duk ranar da kika sake kiran Matata da sunan karuwa to WALLAHIL'AZIM kin ji na rantse a ranar zaki gano ainahin wanene Safwan, don kuwa sai na yi maki dukan da a RAYUWARKI kaf ba'a taɓa yi maki irinshi ba" Sannan ya cisgo gashinta da ƙarfin gaske ta yi ƙara fuskarshi daf da tata suna kallon juna ido cikin ido ya ce "Wannan da kike gani ita ce Matata Khadija kuma Uwargidana wadda kike da labarin na aureta tun kafin ke, zancen Ƴar aiki ya riga da ya wuce tuni don daman cen kawaici ne na yi maki na ƙi sanar da ke gaskiyar wacece, saboda kawai bana son ranki ya ɓaci idan kin ji ina da aure, to amman yanzu tunda har kin gano komi to kenan ɓoyon da nake maki ma ba shi amfani, saboda haka ki kwantar da hankalinki zan baki wata dama" Ya fidda wayar da key ɗin da take ya damƙa mata wayat a hannu cikin fusata ya ce "karɓi ki shiga chat ɗina da ita da kike son ganin abunda ake yi maki ɓoyo kullum, to yanzu ki shiga duk inda kike so na baki wannan damar ki karanta komi kuma ki ga komi da idonki, kin ga kin hutar da ni akan duk wani labari da zan sake ba ki a yanzu kuma da gaba ma idan ta kama, na ba ki awa biyu ki yi duk abunda kike so saboda kawai idan kin ta shi kashetan sai ki haɗa da Ni, ke in ma da hali ki fara ta kaina kafin zuwan lokacin da za ki haɗu da ita itama ki kashetan" Yana ƙare maganar ya fice ya barta da waya a hannu baki a sake kamar wata sakarya, idonta akanshi suna zubar da hawaye wasu bayan wasu, saboda tsabar baƙin ciki da takaicin da ya cika mata ciki, cikin sauri ta jefar da wayar kan kujera itama ta durƙushe ƙasa tana wani irin kuka gwanin ban tausayi. Saboda izuwa lokacin ta fara yin nadamar biyewa son zuciyarta da ta yi ta aureshi, yanzu ga shi ba'a je ko'ina ba ta fara cin karo da takaicin auren mijin wata da ta yi, don ta tabbata inda Aminu ta aura to da babu yanda za'a ya yi mata irin wannan wulaƙancin akan wata mace, tuno irin renin hankalin da ta yi wa Aminun yasa ta ƙara sautin kukanta, don har awa biyun suka cika ya dawo bata daina kukan ba. Ganin hakan ya ji jikinshi ya yi sanyi ya zo inda take ya ɗagota daga durƙushen ya zauna kan kujerar da ita a jikinshi yana bubbuga bayanta alamun ta yi shiru, saboda shi kanshi zuciyarshi cike take da ƙuncin da ya fi nata, saboda har ga ALLAH ba da son ranshi ya ke yi mata abunda ya ke yi ba, kawai dai don ya kasa controlling ɗin kanshi ne akan Dijen Baffah, shiyasa ya ke jin komi ma zai iya aikatawa in dai hakan zai farantawa Dijenshi, don izuwa lokacin ya fara fahimtar irin yanda take sonshi itama, kawai dai tana ɓoyewa ne don bata son ya fahimci itama ta yi kewarshi don wata manufa ta ta da shi bai gano nufinta ba, haka ya danne ta shi damuwar ya koma lallashinta har ya samu ta yi shiru sai dai ta ƙi cewa da shi ƙanzil har suka shiga bacci. **** Haka rayuwar auren nasu ya ci gaba da zama yau fari gobe baƙi, duk da ya rage wasu abubuwa da yawa don kawai su sami zaman lafiya, amman kishinshi da Zee ta ke yi abu kaɗan ne zai janyo masu matsala sai an hau sama a dawo a shirya, don izuwa lokacin ita kanta ta matsu da su gama karatun su dawo gida, saboda tunanin da take yi yawan yi akan ita fa muddin bai canza hali ba idan suka dawo gidansu zata koma, ta sa Mahaifinta ya karɓar mata takardarta, don ba zata zauna ciyon zuciya ya kasheta da ƙurciyarta ba akan wata ɗiya macen da bata fita da komi ba. Haka rayuwa ta yi ta shurawa sati ya zo ya wuce wata ya zo ya wuce shekara ta gangaro itama har ma ta nemi wucewa, sannu a hankali sai ga su Safwan sun kammala karatunsu, sun ƙara wasu watanni ne saboda su harhaɗa komi sannan su dawo, duk da turawa sun so su riƙesu su yi aiki da su ko na shekara ne, amman fafur Safwan ya buga kanshi akan cewa ƙasarsu za su koma itama ta moresu. *** Dije kam a lokacin tana Ss 3 har ana cukucukun fara jarabawar candy, ga shi Hajiya Mama ta yi wa Safwan alƙawarin duk lokacin da zai dawo zai taradda ita cikin gidanshi, sai dai karatun da take yi yana so ya wargaza alƙawarin, don bata son ta dawo ba tare da ta kammala karatunta ba, amman duk da hakan da lokacin dawowarshi ya ƙaraso dole ba don dukansu sun so ba Aunty Ummin ta tattaro khadija ta dawo da ita Yola. Hajiya ta zaunar da ita ta fayyace mata komi dalla dalla akan auren da Safwan ya yi ba tare da saninta ba, sannan ta sanar da ita alfanun kaita Abujar da ta sa aka yi don kawai itama ta san minene rayuwa, Dije tasha kuka saboda kishin auren da ta ji ya yi, amman sannu a hankali Hajiya tana ta tausarta tare da nuna mata cewa ita ɗin tana da damar dawo da Mijinta hannunta don ba'a fita da komi ba, sannan ne hankalinta ya ɗan kwanta ta ji sanyi a ranta ta saki jikinta, sai dai duk lokacin da ta tuna da wata mace a tare da shi sai ta yi kuka a ɓoye. Hajiya Mama ta saki jiki ta gyarewa Dijen Baffah ɗakinta tamkar kowace yarinya mai gata a wurin iyayenta, itama kanta ta fara gyarata ciki da bayanta lungu da saƙonta, don takanas ta nemo wata Mata ta dinka tsima Dijen tun tana jin daɗin karamcin har ta kai ta fara nuna gajiyawarta, dole Hajiya ta ce a dakatar da komi sannan aka koma gyara mata jiki Dilka halawa duka ba wanda ba'a yi mata ba, jikinta ya dawo smuth har wani sheƙi yake yi, ga fatarta hutu yasa ta murje ta cire baƙin ta zama chocolate color, ga gashinta Kuma da kullum yake ƙara cika masha ALLAH, shi ma ba ƙaramin gyara ya ke sha ba a hannun Matar, Fiddo kanta ba Dijen ta burgeta saboda ganin yanda gaba ɗaya ta sauya tamkar ba ƴar ƙauyen da ta sani ba, saboda ta zanzare ta zama wayayyi ƴar boko musamman yanzu da Safwan ya ƙara buɗe mata idanuwa da salon Soyayyarshi, amman duk da hakan ba wata magana mai tsawo da ke haɗasu, saboda ita kanta a yanzu jinta take yi dai dai da kowa, musamman idan ta tuno da ita ɓangaren Amarya take shiyasa ma ko kaɗan bata shiga shirgin Fiddon matuƙar ba dolen dole ce ta janyo ba. Ana gobe su Safwan za su da wo ne Hajiya ta saka Aunty Ummi da su Surayya da sauran wasu ƴan uwa suka yi wa Dijen rakiya gidan angonta Safwan, zuciyarta cike da farin cikin ganin wannan rana mai cike da ɗinbin tarihi a rayuwarta, saboda tsabar murnar ganin muhallinta har da kukan farin ciki Dijen ta yi, musamman da ta kalli ko'ina sama da ƙasa gabas da yamma Kudu da Arewa taga uwar dukiyar da aka narka mata, ta yi sha'awar ina ma ace Inna da Baffah'nta da ƙawayenta su ma su zo su ga muhallinta, ta ruƙunkume Aunty Ummi sai kuka take cisga, Fiddo kam sai wani yatsine yatsine take yi zuciyarta cike da jin haushin kwashe masu dukiya da Hajiyar ta yi ta zube a ɗakin Dijen, a ranta ta ƙara tabbatar da cewa lalle ba ƙaramin asiri su Baffah su ka yi masu ba musamman ita da SAFWAN ɗin. Surayya tana dariya zuciyarta cike da jin daɗi ta yi mata raɗa a kunne sai ga Dije ta sunne kai cike da kunya tana dariya, saboda cewar da ta yi "Ba wani kuka yarinya gobe iwar haka har kin mance da mu kina ta Mijinki" Haka suka tasata da wasa har ta ware tana mayarwa Surayya suna gidan har dare sannan aka barta da Husnah da wata dattijuwar da zata riƙa yi mata hidima, haka ta kwana cikin farin cikin dawowar Angonta masoyinta kuma Malaminta Muhammad Safwanu JABB'I YOLA. Ayyururui Amarya ta ango🥳 Akafta😝 D/AUTA Ce✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *Ruwan sharhin da kuke ta bugawa akan book ɗin nan ba ƙaramin daɗi yake sakani ba, saboda haka ku ci gaba da fafatawa ni ma in ci gaba da sambaɗo maku labarai😉😂* *Lamba ta 63* Tunda sassafe Surayya ta zo suka shiga kitchen sunata hidimar ɗora abincin tarbon baƙi kala kala, ko da sha biyu na rana ta yi duk sun kammala abunda ake buƙata, Dije ta je ta sullo wankan da sai da ta ɓata lokaci sosai wajen wanke ko'ina lungu da saƙo na jikinta, tare da ɗimama kanta da turarukan wanka masu daɗin ƙamshi, waɗanda a hankali har sun fara bin jikinta saboda yanda take yawan amfani da su akai akai tun dawowarta Abuja. Bayan ta yi SALLAHr azahar ne Surayya ta zauna ta tsara mata kwalliya cikin tsari irin na wayayyun yan birni, kafin ka ce me sai ga Dijen Baffah ta fito sharr! Abunta cikin wata rantsattsiyar shadda golden color har sheƙin maiƙo take yi, ga ɗinkin da aka watsawa shaddar na stone work shuwari stone sai walwalniya suke yi ta ko'ina idan ta motsa, sannan ga danƙareriyar sarƙarta ta gold da ta ƙara ƙawata kwalliyar, wadda Hajiya ta bata a matsayin kyautar suruka lokacin da za ta zuwa gidan mijinta, ta sha manyan awarwaro da agogo tare da Zoben azurfan da ke maƙale a yatsanta na biyu, wanda ya ƙara fito mata da zarazaran dogayen yatsunta da suka sha ƙunshin jan lalle masha ALLAH. Dijen Baffah ta yi kyau iya kyau kamar ka saceta ka tsere saboda wankan ya hau jikinta sosai ya zauna, suka fito harabar gidan sai ɗaukar photuna suke yi ita da su Surayya da Husnah, Fiddo kam latsar wayarta kawai take yi saboda fushin da take yi na tilastata da Hajiya Mama ta yi akan sai ta zo gidan, don ta so ta yi zamanta acen gida tunda dole a cen ne zasu fara zuwa su ga Hajiyar sannan su yo nan gidan. Shiyasa tunda ta zo ba wanda ta shiga sha'aninshi sai sabgoginta ta ke ita kaɗai, yanda ta share kowa haka duk cikinsu kowa ya shareta suna ta harkokinsu. **** Malam Safwanu kam suna fitowa jirgi ya ja numfashi ya shaƙi iskan ƙasarshi ta Nageria da ƙarfi tare da lumshe ido ya kallo Amaryarshi da ke gefenshi cike da wani salon da shi kaɗai yasan ma'anar kallon, ganin haka ta ƙara maƙale hannunshi da take riƙe da shi tare da ɗora kanta a kafaɗarshi tana murmushin itama, don on ready ko da suka sauko direba yana airport ɗin yana jiran saukarsu, shiyasa ba tare da ɓata lokaci ba ya kwasosu suka nufo unguwarsu Hajiya Mama domin su fara gaisawa kafin su je cen gidan nasu, Zee haka kawai ta tsinci kanta da faɗuwar gaba tare da jin kwatakwata bata son zuwa gidansu Hajiya Mamar, saboda tunaninta ya tafi ne akan cewa Dijen tana gidan, sai dai har aka gama gaisawa da juna cikin farin ciki da ɗoki tare da murnar ganin juna bata hango ko mai kama da Dijen Baffahn ba, taji daɗi sosai a ranta saboda tunaninta har lokacin tana cen Makarantar da aka ce tana yi, shiyasa ta saki jiki sai wasar baki take yi anata gaggaisawa kafin su yi sallama da juna su fito gidan, tare da rakiyarsu Hajiyar da Aunty Ummi da yaranta da wasu ma'aikata mata da suka biyosu suna yi masu addu'ar sauka lafiya, Safwan ya kalli Hajiyar bakinshi yana rawa saboda son tambayarta da ya ke yi akan alƙawarin da ta yi masa, cikin dariya Aunty Ummi da ta fahimceshi ta yi saurin faɗin "Mun kai maka tana cen kai take jira" Zee da ke mota tana wasar baki ba shiri ta ji ƙirjinta ya buga, duk da ce wa bata gano ma'anar inda maganar ta dosa ba amman ta yi wasiwasin cewa _"Anya ba wannan mayyar yarinyar ba ce ake magana a kanta ba kuwa?"_ Sai gata da haɗe fuska tana dariyar yaƙe har suka bar gidan, cike da tsananin farin da jin daɗi Safwan ya riƙo hannunta ya ce "Hajjaju ayi murna mun dawo ƙasarmu ta gado, sai hankali ya kwanta ga ki kusa da Daddynki da kullum kike ta faɗin kin matsu ki ganshi, tsorona ɗaya shine kada ace gulmata ce ake zumuɗin kai wa?" ZEE ta yi dariyar yaƙe ba tare da ta ce komi ba, saboda faɗuwar gabanta da ya tsananta bugawa cikin sauri da sauri, har suka je bakin kantamin Gate ɗin gidan nasu bata ji natsuwa ta zo mata ba, hankalinta ya fara ta shi ne lokacin da Direban da ya ɗaukosu ya ke ta buga horn wani bayan wani alamun sanarwar zuwansu. Ai kuwa kafin ma su je parking space ya ajiye motar sai ga su Surayya da su Husnah tare da Ruma ƙawar zee da wasu ƴan'uwanta biyu aguje sun fito, su Surayya daga sashen Khadijar suna ihun murnar dawowarsu, yayin da su Ruma suka fito daga nata sashen cike farin ciki, gaban Zee ya ƙire ya faɗi ba shiri ta yi saurin fitowa tana ƙarewa gidan kallon yanda aka ƙawatashi da sabon fenti, sannan ta dawo da kallonta ga su Surayya da suka maƙalkale Safwan suna murnar ganinshi, su Ruma suka ƙaraso wurinta cike da murna suna yi masu sannu da zuwa, Fiddo ta saki Safwan ta nufo Zee inda ta wani haɗe rai tana yi mata wani mugun kallo, ba shiri Fiddo ta sha jinin jikinta tare da wayancewa da dannar wayar da ke hannunta. Cen sai ga wani taku da ya ja hankalinsu duka tare da shaƙo wani daddaɗan ƙamshin da iska ya kwaso ya shaƙawa Zee cikin hanci tamkar da gayya cikin lamarin, ta yi saurin kallon inda take jin sautin takun takalmin sai gata da dafe ƙirji ba shiri, cikin matsanancin faɗuwar gaba tare da dakan luguden da zuciyarta ta ke yi ne ta yi mutuwar tsaye, Dukansu suka ƙurawa Dijen kallo musamman ita da ta kafeta da ido ƙur har ta ƙaraso wurinta, cikin sigar duniyanci Dijen ta rungume Zee fuskarta ɗauke da fara'a ta ce "Oyoyo Ƙanwata sannunku da zuwa da fatar kun iso lafiya" Ta ƙare maganar tare da fesheta da wani sabon murmushin da Zee ta kasa gano ko na minene, sannan Dijen ta saketa ta nufi Safwan ɗin da tunda ya ƙyalla idonshi akanta gaba ɗaya ya susuce, yanda ya ke kallonta cikin shauƙin sonta da ke fisgarshi haka ita ma Zee ta bi ta da kallon mamaki, tare da su Ruma da suma ta zamo masu tv saboda kallo. Dije kam tana zuwa ta yi saurin maƙaloshi tare da yin tsalle ta kai masa kiss a kumatu sannan ta faɗa jikinshi ta ruƙunƙumeshi sosai cikin wani tsantsar farin cikin ganinshi tana faɗin "Am happy to see you my Husby, your welcome key to my life" Daga Safwan ɗin har su Zee kasa ɗauke idonsu suka yi gareta saboda tsabar mamakin da ta ba su, duk da wani sashe na zuciyarshi yasan fiye da hakan ma zata iya aikatawa tunda har yasan kalar koyarwar da ya yi mata, sai dai ita Zee mamakinta ya Sha bambam da na shi don kuwa ita ƙarfin halin yarinyar take mamaki musamman da ta kirata ƙanwarta, amman kasancewar itama ɗin ba baya ba wajen kishi shiyasa ta yi saurin ɓoye kukan da ya zo mata ta nufi sashenta su Ruma suka dafe mata baya suka barsu anan ko waiwayensu bata sake yi ba. Ganin hakan ya sa Safwan ɗin sakin jikin ya mayar mata da martanin sumbar da ta yi masa a leɓenta, sannan ya ɗora kanshi saman wuyanta ya kai mata wani zazzafan kiss ta yi saurin zullewa tare da riƙo hannunshi tana dariya ta ce "Oya mu je daga ciki kada ka janyo muna abun magana gaban mutane" Saboda yanda ma'aikatan suke ta satar kallonsu a fakaice ga kuma fiddo da ke tsaye itama, lura da hakan yasa ta hilatoshi suka shige sashenta, wanda shi biye da ita kawai yake amman sam gaba ɗaya ya manta kowa da komi sai ita, yana jin wani daɗi yana huda ko'ina na jikinshi saboda farin cikin ganinta, yau ga shi ga ma'ul hayatynshi Dijengalar Baffah kuma Black cat ɗin shi ada, wadda yanzu ta zamo masa fitilar da yake amfani da haskenta matuƙar yana son ya gane gabanshi. Surayya da su Husnah da sauran wasu ma'aikatan gidan tuni suka kwashi kayan da Direba yake fitowa suka fara shigarwa sashen Zee, sannan suka koma sashen Dijen inda ita kam tuni ta shige da Mijinta ɗakin da yake mallakinshi a cikin sashen nata ta fara ɗorashi a saiti, don tun shigarsu ya janyota jikinshi ya fara yamutsata tare da aika mata da saƙunan kisses tamkar wani zautaccen mayen ƙarfe, ganin in ta biyeshi za su ɓata lokuta masu yawa yasa ta yi dubarar riƙe hannunshi cikin wani kallo ta ce "Plss mu je ka yi wanka ku ci abinci kai da Amaryarka kada ta ɗaukeni mai rowa, don na tabbata dukanku kuna buƙatar abincin" Ta mairaire fuska har da riƙe kunne alamun ban haƙuri sannan ya miƙe tare da dafe goshi yana yi mata kallon mamakin irin wayewar da ta yi masa ta bazata, sannan ya riƙo hannunta ya ce "Wayo ko? To ai mu je ɗin sai ki tayani wankan don na fahimci so kike ma ki nuna kin fini girma" Dije ta yi yar dariya sannan ta rufe fuska da hannu ɗaya ta ce "Ni dai mu je ɗin kada ta ga an ƙyaleta" Sannan suka je toilet ta haɗa masa komai zata fito ya ce ta jirashi amman daga nesa don baya son ta ɓata masa kwalliyar, ita ko ganin hakan yasa ta yi nazarin kawai ta taimaka masa tunda Surayya ta sanar da ita hakan ma yana ƙara shaƙuwa tsakanin ma'aurata, aiko ta saki jiki ta ajiye kunyar ta taimaka masa sai gata itama ya janyota suka faɗa ruwan ya yi nasarar cire mata kayan ya dinga mammatsewa tare da tanɗewa da lashe abubuwan da ya fi so a rayuwarshi, duk da take jin zafin zafin abunda ya ke yi amman ta nuna masa lalle itama ɗin yanzu ba da bace, da ƙyar ta lallaboshi suka fito toilet ɗin bayan dukansu sun tsalkake jikinsu. Yana rama sallolin da suka kubce masa ne ta sulale ta wata ƙofar da ke sadata da ɗakinta ta sake yin wani sabon shiri cikin wani danƙareren less bulue black, Wanda aka yi wa ɗinkin riga da siket ya hau jikinta sosai, saboda ɗinkunan takanas Aunty Ummi ta ɗinka mata su Abuja don kawai ta ji daɗin tarbon Angonta, bayan ta kimtsa fess abunta sannan ta sake feshe jiki da turarukanta masu daɗin ƙamshin sannan ta koma wurinshi, yanda ya lalace da kallonta ne yasa ta ƙaraso wurinshi tare da hure masa ido da iskan bakinta ta ce "It's time for lunch my dear" Ya rungumota jikinshi yana lakuce mata dogon hancinta ya ce "Ki godewa ALLAH idan har kinsa Malaminki ya zauce a kanki" Ta yi wani yarr da ido ta ce "rufani ka saya ai sai ka janyo ace wannan ɗaliba ta wuce gona da iri idan har ta zarta sanin malaminta" Ya sauke mata wani kiss a goshi sannan ya shirya cikin wasu kayanshi da aka ajiye a ɗakin, sannan ya riƙo hannunta suka fito suka nufi sashenshi da yake tsakiyar na su ita da Zee, inda acen ne ma suka kai komi da suka dafa saboda kawai a nunawa Zee cewa su sun san me suke yi, kuma wannan duk yana cikin shawarar Aunty Ummin da take ta baiwa Dijen akan neman zaman lafiyarta ita da abokiyar zamsnta, har zasu zauna kan diny ɗin Dije ta yi saurin ce wa "Malam plss ka fito da Amarya ta zo mu haɗu ayi lunch don cikina har ya fara kiran ciroma" Safwan yana ƴar dariya ya ce "sannu acici to jirani in zo minti ɗaya" Sannan ya bi wata ƙofa ya yi sashen Zee inda ya taradda ita tare da ƴan uwanta biyun da ƙawarta Ruma da suka zo tarbarta, bayan sun sake gaisa ne ya ke cewa da ita ta zo su je aci abincin, ta nuna cewa ita sam bazata je ba ta riga da ta ci wanda su Ruma suka dafa mata, Ruma ta yi mata signal da ido sannan ta miƙe ta biyoshi ranta a haɗe saboda takaicinshi da take ji a zuciyarta tare da munafukar Matarshi a cewarta, wadda ta sha alwashin ko da bala'i sai ta fiddata gidan ta ƙarfin tsiya, tunda har ita zata nunawa kissa da kitifiri don salon kawo mata reni har da kiranta ƙanwarta wai, haka ta yi ta saƙe saƙen zucinta har suka shiga falon nashi, sai dai hango Dijen da ta yi tana ta Saving abinci a plates kala kala yasa ta ji wani bala'a'en kishi ya taso mata, musamman yanda ta ga har da wani sabon wankan ta sake yi don ta nuna mata cewa sunyi wani abu da Safwan ɗin, tunanin hakan yasa ta ja ta tsaya ta ƙi ƙarasawa wajen diny ɗin, ta rungume hannu tana yi mata wani kallo sai wani girgizar jiki take yi saboda a wuya take ƙiris take jira ayi wadda za'a yi. Safwan ya ja kujera ya zauna Dijen ta janyo masa abinci a gabanshi tana dariya ta kalli Zee ta ce "Ƙamshin girkina zai yi maki illa Amarya matuƙar baki yi gaggawar ƙarasowa ki ka fara cinshi ba" Zee ta yi mata wani kallo sama da ƙasa mai cike da reni sannan ta buga wani uban tsaki tace "Wahainiyarki ta kiyayi ramata tun wuri WALLAhi, ke ce matsiyaciya wadda abinci ya dama saboda haka ki je ki tambayo wacece Zee kafun ki fara yiwa mutane iyayin tsiya, baƙar munafukar banza annamimiya mai shiga tsakanin mata da mijinta, WALLAhi tun kafin in nuna maki wacece Ni ki kama kanki da ni" Tana ƙare faɗar maganar ta yi masu wani mugun kallo sannan ta buga wani uban tsaki ta juya cikin fushi ta koma inda ta fito, Safwan kam sai cin abincinshi yake yi ba tare da ma ya nuna damuwarshi akan duk abunda ta faɗa ba, ya ɗago fuskarshi ya kalli Dijen ya wayance tare da faɗar "Sakin bakin na minene? Ko zaki bita ki bata haƙuri ne? Saki jiki ki ci abincinki in har kina son farin cikina, to ki tattara komi ki ajiye a gefe ki fuskanci gabanki tare da Mijinki da ke kusa da ke, saboda haka dawo nan kusa da ni sai mun fi jin daɗin cin abincinmu" Dije ta yi shiru sannan ta goge guntuwar ƙwallah da ta cika mata ido ta dawo kujerar da ya ce, yana dariyar da iyakacinta fuska ya ciko spoon da abincin ya nufo bakinta, ta yi masa wani kallo zuciyarta cike da takaici ya girgiza mata kai ta yi saurin haɗiye kukanta. Haka suka ci abincin kowane zuciya ba daɗi sai dai ba laifi sun ciyar da junansu sosai, sannan ya ja abarshi suka yi ɗakinshi inda ba ɓata lokaci ya fara saitata a hanya, kafin ka ce me shima ya fara rikicewa tare da zaucewa akan Dijenshi, don kuwa tun haɗuwar fatar jikinsu ya gano akwai banbanci tsakaninta da Zee sosai haka ma akwai tazara mai yawa a tsakaninsu, to balle da ya sami sa'ar shigewa fadar gwamnatinta sai ga shi da fasa wani ihun daɗi yana kuwwa, saboda gaba ɗaya ya zauce mata ni'imarta tasa ya kiɗime babu abunda ke fita bakinshi sai ihu da sambatun daɗi. Zee kam tana cen su Ruma suna lallashinta ne ta jiyo ihunshi, cike da mamaki ta yi saurin dawowa falon sai dai fahimtar abinda yakewa ihun ne yasa ta dafe ƙirji ba shiri, tare da zuwa ƙofar ɗakin tana dukan ƙofar a haukace tana tsine masu dukansu. Ganin kamar ba su ma san tana yi ba yasa ta bazama aguje ta yi ɗakin ajiyar fetur ta kinkimo jarkar ta fito da gudu kamar wata mahaukaciya, ma'aikatan gidan suka bita da kallo cike da mamaki duk da duhun magriba ya kawo jiki a lokacin. Tana zuwa ta fara watsa fetur ɗin ta ko'ina cikin falon da ƙofar ɗakin tana surutan faɗin "Sai na kasheku dukanku yau yan bura'uba azzulumai macuta, ALLAH ya tsine maku gaba ɗayanku WALLAHI yau sai na kasheku" Ta yi sashenta aguje gudu ta ɗauko ashana su Ruma suka biyota da gudunsu don su ga abunda yake faruwa, tana zuwa ta kunna ashanar cikin bushewar zuciya ta cillata ƙofar ɗakin. Wayyo ALLAHna😳🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️wuta 🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️wuta ku yo agaji🏃🏻‍♀️. Akafta😝 D/AUTA Ce✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *Rigiji Gabji wani kaya sai Amalii ina gwanayen wasu ga nawa 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻har ga ALLAH ruwan sharhinku akan book ɗin Ƙarangiya yana faranta man rai ba kaɗan ba, haƙiƙa dole inyi alfakhari da ku saboda ku ɗin nawa ne ba ƙarya,ina miƙa ɗinbin godiyata gareki ƴargata Maman Sultan, irin godiyar da baki ba zai taɓa iya zayyanowa ba, alkhairin ALLAH ya kai maki har ƙasar Niger cikin gidan Baban Sultan akan gadonki wanda kike bacci a kuma gefen da kike kwanciya😝😜* *Lamba ta 64* A zafafe Ruma ta yi wani tsalle ta cafke ashanar cikin wani firgici da tashin hankalin da ya ziyarceta, don garin cafke ashanar fetur ɗin da ke malale ƙasa tyles ɗin ya jata ta faɗi tim! A ƙasa, amman duk da hakan sai dai ta yiwa ashanar murzar bala'i duk da zafin ƙunar da ya ratsa hannun nata, cikin fushi ta miƙe ta yo kan Zee zata ƙwace ashanar, Zee ta ƙara yin baya cikin bushewar zuciya da ta yi dacen aka janye mata imani a zuciyar don babu abunda take so irin ta ƙonesu da kowa ma da ke gidan har itama kanta, saboda a ganinta hakan ne kawai zata yi ta cire zafin abunda take ji a zuciyarta, Ruma tana girgiza kai cikin ruɗewa tace "Kar ki aikata abunda zaki zo ki yi danasani daga baya" Hawaye suna zuba akan fuskar Zee da idonta suka rikiɗe zuwa jajaye saboda tsallar tsagwaron bushewar da zuciyarta ta yi, ta sake kunna wata ashanar hawaye suna zuba akan fuskarta tace "Matuƙar na barsu da rai bazan taɓa yafewa kaina ba, ya zama dole su ɗanɗani azabar mutuwa dai dai da cin amanar da suka aikata ma....." Wani mari ne da ya sauka akan fuskarta ne yasa ta yi saurin sakin guntuwar ashanar da ta kusa cenyewa a hannunta, Ruma ta yi saurin taketa da ƙafa ta murje, a zafafe Zee ta waiga domin taga wace mai ƙarfin halin ce ta mareta, yanda ta ga fuskar Surayya da ke tsaye gefenta tana huci yasa ta yi wata gajerar dariya ta ce "Wow sannu fa ki ce masu mutuwar yau yawa ne da su? To ki jira ke ma saura kaɗan naki ajalin ya iso ku sa da ke" Tana ƙare maganar ta fiddo wata ƙwarar ashana kafin ta kyasta ta sake jin wani uban naushi da Surayya ta sauke mata a gefen fuskarta, ba shiri ta saki ashanar ƙasa Ruma ta ɗauke ta fice da ashanar cikin sauri, Zee ko ta yi cikin Surayya suka fara kaiwa juna duka, kafin ka ce damben bala'i ya kacame a tsakaninsu ƴan'uwan Zee ɗin su biyu da ke tsaye suna kallon abunda ke faruwa suna rabon faɗan, sai ga Husnah aguje itama kamar wata zakanya ta rufarwa Zee suka yi ta mazgarta ita da Surayya, sai dukanta suke yi kamar ALLAH ya aikosu tun tana ƙoƙarin kare kanta har ta koma laƙwas Husnah ta kwashe mata ƙafafuwa ta faɗi ƙasa ba shiri, Surayya ta yi saurin haye ruwan cikinta suna ta duka duk da ƙoƙarin hanasu da ƴan'uwan Zee suke yi, amman hakan bai hanasu yi mata dukan kawo wuƙa ba. Safwan da Dijenshi kam basu ma san me ke faruwa ba har sai da Surayya ta kirasu a waya ne take sanarwa da Safwan ɗin abunda Zee take yi don a lokacin itama suna sashen Dijen ne wani ma'aikaci ya zo aguje yake sanar da su abunda ke faruwa, shiyasa hankalin Surayya a tashe ta kira Safwan ɗin saboda zuciyarta ta bata cewa Zee ba alkhairi zata shuka ba, tun yanayin da ta ganta lokacin da suka dawo ta yi sashenta cikin fushi, bayan ta gama kiran Safwan ɗin ta sanar da shi abunda aka faɗa masu ne ta ce da su Husnah su kira Aunty Ummi su sanar da ita kafin ta je ta ga abunda ke faruwa, aiko sai gashi tana zuwa ta ji kalaman da Zee take faɗa Shiyasa bata yi ƙasa a gwiwa ba wajen kai mata hannu. Ko da Safwan ɗin da Dije suka fito cike da firgici akan fuskarsu, sai ga wani sabon firgicin da ya sake sakasu ruɗewa saboda ganin gaba ɗaya falon warin fetur ne da wani wanda bai ƙasara bin iska ba malale a ƙasa, Safwan ya kai kallonshi inda su Surayya da ke ta jibgar Zee har lokacin, ya yi saurin katsa masu wata uwar tsawa suka zabura cikin firgici daga su har ita Zee ɗin da ke kwance ligya ligya don ta daku ba ƙarya. Ya ƙasaro wajensu ya kallesu ɗaya bayan ɗaya ya ɗaga murya a fusace ya ce "Wai me ke faruwa ne wai??" Zee ta miƙe da ƙyar ta kalleshi cikin wani kallon reni da kumburarren bakinta da suka fashe ta ce "Ni zaka tambaya don ni ce zan yi ajalinku dukanku ka sani ka ƙara sani dukanku sai na kasheku" Tana ƙare maganar ta yi sashenta aguje ko wa ya bita da kallo, cikin fushi Safwan ya bita ƴan'uwan Zee ɗin da Ruma suka biyoshi a baya suna bashi haƙuri, Dije ko ta yi wurinsu Surayya tana tambayarsu mafarin abun. Safwan yana kaiwa sashen nata sai ga ta sun ci karo da ita da sharɓeɓiyar wuƙarta ta nufoshi gadan gadan da nufin ta soka masa ita, ya yi jarumtar riƙe tsinin wuƙar ya fisgeta da ƙarfi wuƙar ta yankeshi sosai amman duk da hakan bai yi ƙasa a gwiwa ba wajen kai mata wani wahalallen mari har sai da taga taurari, sannan ya dinga kai mata duka ta ko'ina kamar wani zaki, itama har da su ƙarfin halin kuwar faɗin sai ta kasheshi duk da uban kashin da take sha, don kuwa da ya yi wani ball da ita har sai da ta kai bango, sannan ya damƙo gashinta ya janyota ƙiii ya fito da ita har gindin Motarshi, sannan ya jefata motar ya saka lock sannan ya faɗa cikin zafin nama ya tada motar ya yi wani uban ribas sannan ya fisgeta da ƙarfin tsiya ya fice, bai zame ko'ina da ita ba sai headquarter'r ƴansanda, kai tsaye ya nemi ganin D.p.o ya damƙa masu ita da hannunshi tare da sanar da su cewa Matarshi ce take son kasheshi, su riƙe ta a hannunsu su yanke mata hukunci dai dai da laifinta, suka karɓeta suka jefata ɗakin ajiya suka kulle sannan suka sanar da shi zasu yi ƙwaƙƙwaran bincike akan case ɗin idan har komi ya kammala ta aikata abunda ake tuhumarta da shi to zasu yanke mata hukunci dai dai da laifinta. Sannan ya baro wurinsu tare da wasu ƴansanda da za su zo yin bincike akan abunda ya faru, shima ya nufo gida saboda damunshi da kiran da ake ta yi, don yaso zuwa ayi masa kanikancin hannun da ya yanke da shi, amman yanda yake jin zuciyarshi ne yasa ko kiran da ake ta yi masa ɗaya bai ɗaga ba, sai na Hajiyarshi ko shi don baya iya ganin kiran yaƙi ɗauka, sai dai bai iya furta ko kalma ɗaya ba sai "to" kawai da ya faɗa, saboda tsananin ɓaci ran da ya cunkushe masa zuciya. Ko da suka shiga gidan suka taradda kowa a harabar gidan ana jiran zuwanshi, cike da ruɗewa Aunty Ummi ta nufoshi tana faɗin "Ba abunda ya sameka ko to Alhmdllh mun godewa ALLAH Hajiyarmu ba abunda ya sameshi" Ya baiwa ƴansandan dama suka shiga ciki suna ta bincikensu, har wuƙar da galam ɗin fetur duk sai da suka fito da su duka, sannan suka fara yiwa mutane tambaya ɗaya bayan ɗaya, don har su kansu ma'aikatan gidan ba'a barsu ba sai da aka tambayesu suka faɗi abunda suka sani, sannan ƴansandan suka bar gidan tare da rahotannin da suka naɗa a wayoyinsu. Safwan da ke jikin Motarshi tsaye ya ƙaraso wajen Hajiya Mama yana dafe kai ya zauna kan wani ɗan dakalin da aka zagaye wasu flowers, hannunshi da suka hango da ya yi bala'in walshewa da wuƙa kowa hankalinshi ya tashi, Hajiyarmu ta ƙaraso wajenshi ta ce "Garin ya ya haka ta faru??" Ya yi shiru sannan ya yarfa hannu saboda jinin da ke ɗiga har lokacin ya ce "Ni ma bansan abunda yake faruwa ba har sai da Surayya ta sanar da ni" Hajiya Mama cikin damuwa ta ce "Ina ita Zainab ɗin?" Ya yi shiru sannan ya ce, "tana hannun ƴansandan" Ko wa ya yi shiru yana nazarin abun a ranshi sannan Hajiyar ta ce "To ka je a yi maka dressing ɗin hannun sannan ka dawo muna jiranka" Safwan ya miƙe zuciyarshi kamar zata fashe ya kalli su Ruma da ke tsaye dukansu sun sha jinin jikinsu ya ce "Kada in dawo in taradda ku cikin gidana" Sannan ya ja Motarshi ya fice aguje, su Hajiya Mama suka yi sashen Dijen suka zauna, inda su ke ta lallahin Dijen da ke ta kuka saboda tunda ta ji abunda Zee ta ce a bakin Surayya hankalinta ya tashi ta fara kuka, sai ga shi kuma ta hango Safwan ɗin yana jan Zee a ƙasa hannunshi sai zubar jini yake yi, akan hakan ta sake ruɗewa tana ta kuka don jin take yi kamar ma ta bar masu gidansu ta koma garinsu tun kafin a kasheta ga banza, don ganin ƴansandan ma yasa ta ji wani tsoro ya sake kamata. Ko da Safwan ya dawo an ɗaure masa hannu da bandeji bayan an ɗinke masa ƙatuwar yankuwar da ya yi, ya shigo ya zauna idonshi akan Dijenshi da ke sharar ƙwallah idonta sun yi ja saboda kukan da ta sha, cikin sanyin jiki ya ce "To ke me kike wa kuka kuma yanzu?" Aunty Ummi ta ce "dole ta yi kuka tunda bata taɓa ganin irin wannan bala'i ba a rayuwarta, wannan matar ƙaddara ai babu mai fatar ALLAH ya haɗashi da ita bale ta zowa mutum a matsayin kishiya" Ta ƙare maganar cikin yin wani kalar mere kamar wata yarinya, Hajiya Mama ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce "Yanzu dai abunda ya faru ya riga da ya faru fatanmu kawai ALLAH ya taƙaita wahala kuma ya tsare gaba" Safwan ya dafe kanshi da ke ta sara masa ya ce, "ai kuma yanzu sai dai ta bi wasu shanun don nikam WALLAhi saki uku ringis zan dannawa shegiya, don bana fatar ko a hanya in sake haɗuwa da ita bale ta sake zama gidana" Surayya ta yi saurin faɗin, "hukuncin da ya dace ita kenan baƙar arniya mai zuciyar kafuran farko" Hajiya Mama ta maka mata wata harara Surayya ta ce,. "Haba Hajiyarmu yanzu da ace ta kashe muna su ai da mu ta bari da shiga uku, don duk hukuncin da za'a yi mata ba lalle ne ya zama dai dai da abunda ta aikata ba" A harzuƙe Husnah tace "Ni WALLAHI na ma so mun illata shegiya kafin Auncle ya zo" Aunty Ummi ta ce "ai WALLAHI da ace ina kusa sai na ja shegiya na damalmala kanta cikin fetur ɗin sannan in fito da ita tsakar gidan nan in ƙyasta mata ashanar sai ta ci wutar ƴar shegiya" Hajiyarmu ta yi saurin faɗin "to kenan da ke da ita duk hukuncinku ɗaya in har kika aika wannan shirmen, yanzu dai abu ɗaya ya rage ka kira Mahaifinta ka sanar da shi abunda ke faruwa" Safwan ya ɓata fuska ya ce "Ƴan'uwanta da aka yi a gabansu miye amfaninsu da ba zasu sanar da su abunda yake faruwa ba?" Hajiyarmu ta ɓata fuska ta ce, "kaine ke da haƙƙin sanar da su ba wasu ba, saboda haka ka kirasu yanzu ka sanar da su abunda ke faruwa" Safwan cike da jin haushi ya ɗaga waya ya kira Daddyn Zee ba tare da jiran komi ba ya ce "Na saki Zee saki biyu a bisa sunnah da in ana yin ɗari duk sai nayi mata, don haka ayi gaggawar zuwa a kwashe mani tarkacen kayanta cikin gidana" To fa 😳😳😳kai ko Malam Safwanu saki haka da sauri 😔 Akafta🙌🏻 D/AUTA Ce✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *Am sorry fo you my FANS😊 jiya kun ji Ni shiru ko? To ku yi haƙuri yanzu gani tare da ku😸fatana kawai ku biyoni mu je🏃🏻‍♀️* *Lamba ta 65* Yana ƙare maganar ya kashe wayar cikin fushi ya miƙe zai bar falon Hajiya Mama ta kira sunanshi a hankali cikin wata murya mai cike da alhini, ba shiri ya waigo ta ce da shi ya dawo ya zauna, sannan ya dawo ya zauna sai wani cika yake yi alamun a wuya ya ke sosai, Hajiya Mama ta sake kiran sunanshi ta ce "Abunda na ce ka aikata kenan? Me yasa kai a koda yaushe baka iya dafa mutum cikin ruwan sanyi ba?, Nasan Zainab bata kyauta ba amman shi mahaifinta laifin me ya yi da har zaka yi masa wannan cin fuskar?, Yanzu idan kai ne a matsayinshi wani ya kiraka ya saki ƴarka irin haka wane irin hali kake tsammanin zaka shiga?, To bari ka ji banji daɗin abunda ka aikata ba, don Mahaifinta komi lalacewarshi ya gama maka komi tunda har ya ɗauki ɗiyarshi ya baka, don haka ka sani laifin wani baya shafuwar wani, saboda shi mutum daraja gareshi mussaman wanda ya ke sama da kai irin haka, saboda haka ka dinga kwatanta adalci akan duk wanda mu'amala ta haɗaka da shi, don da ace ka yi cuta gara ace kai ne aka cuta, don yanzu wannan abun da ka yi masa har abada ba zai taɓa mantawa ba, tabbas kam ƴarshi bata yi abunda ya dace ba amman ka sani kai ka yi abunda ya fi wanda ta aikata muni" Safwan da su Aunty Ummi Suka kallota cikin mamaki ta ce "Eh tabbas haka ne don ita da makami ta yi niyya kasheka cikin fushi, kai kuka ka yi amfani da dafin harshe ka caki ubanta da mummunar maganar da dole ne ta daki zuciyarshi, ko baki ji ance dafin harshe ya fi na takobi zafi ba?, to bari ka ji yanzu wannan raunin da ta ji maka a hannu zai iya warkewa har wurin ya koma tamkar ma ba'a yi, amman dafin abunda ka yi wa mahaifinta ka sani har abada ba zai taɓa goguwa a cikin zuciyarshi ba, saboda haka ka daina yanke hukunci cikin fushi a koda yaushe idan har kasan abunda zaka faɗa ba mai kyau bane, to ka yi ƙoƙarin danne zuciyarka ka yi shiru saboda faɗar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama da ya ce(falyaƙul khairan auliyasmut, ka faɗi alkhairi ko ka yi shiru) saboda shi baki dafi ne da shi wanda idan aka yi maka wata mummunar magana har abada ba zaka taɓa mantawa da ita ba" Safwan ya shafo kanshi da hannunshi mai lafiya ya ce "na yi kuskure Hajiyarmu kuma Insha ALLAH bazan sake maimaita kwatankwacin hakan ba...." Kiran wayar Safwan ce ta katse maganar da yake yi, cikin sauri ya duba mai kiran sai ga shi da kallo Hajiyar cikin sauri ya ce "Mahaifinta ne" Hajiyarmu ta ce "Ka ɗauka ka ji to" Ya ɗaga ba tare da ya ce ƙanzil ba ya saka hands free, sai ga muryar Mahaifiyar Zee cikin wayar tar! tar! tana kuka tana faɗin "Me ke faruwa ne? Me ya sami Zainab ɗin ne? ga Daddynta nan ya faɗi rai a hannun ALLAH sai sunanta ya ke kira, me ke faruwa ne na ce?" Ta ƙare maganar cikin kuka tare da ɗaga murya Hajiya Mama ta yi masa nuni da hannu alamun ya sanar da ita, cikin sanyin jiki ya fayyace mata abunda ya faru a dunƙule, mahaifiyarta ta fasa wata uwar ƙara tare da cewa "Innalilahi wa'Inna ilairraji'un, Allahumma ajirni fi musibati wa alkhalifni khairun minha" Sannan ta kashe wayar gaba ɗaya jikin kowa ya yi sanyi, ran Hajiyar a matuƙar ɓace cikin tagumi ta ce "ka ga abunda nike sanar da kai ko? To idan har ka yi sanadin mutuwarshi sai kasan abunda zaka faɗawa ALLAH idan kun je lahira" Hajiyar Mama ta miƙe cikin fushi zata fita ya yi saurin shan gabanta yana bata haƙuri tare da su Aunty Ummi, Dije ta duƙa ƙasa ta riƙo leɓen zanenta cikin kuka ta ce "Ki yi haƙuri Hajiyarmu kada ki fushi da Malam don ALLAH ki yafe masa" Hajiyar ta duƙa ta ɗagota tare da share mata hawayen da suke ta zuba a idonta ta ce, "komi ya wuce na haƙura insha ALLAHu amman matuƙar yana son in yafe masa to sai ya furta ya mayar da Zainab a matsayin matarshi" Dije da su Aunty Ummi da shi kanshi suka zaro ido waje saboda bugawar da zuciyoyinsu suka yi, cikin tabbatarwa ta sake ce wa "haka na ce kuma haka ni ke son ayi don hakan kawai zai rage raɗadin baƙin cikin abunda zai faru ga mahaifinta, wanda ko kaɗan bani fatar ace kai ne ka yi silar mutuwarshi da hannunka, duk da bana fatar hakan amman ka sani duk ya mutu a sanadin wautarka to baka yi wa kanka adalci ba" Safwan da su Aunty Suka yi shiru kowa da nazarin da yake yi a zuciyarshi, Dije ta je gabanshi tare da haɗa hannuwa biyu alamun roƙo ta ce "Don Allah Malam ka dawo da ita a matsayin matarka plss" Cikin tsananin ɓacin rai ya ce "na dawo da ita da sauran igiya ɗayar da ta rage a tsakaninmu, amman WALLAhi bazan taɓa yafe mata abunda ta aikata man ba" Yana ƙare faɗar hakan ya bar wajen cikin ƙunar zuciya, Hajiyar ma ta ce da su Aunty Ummi su zo su tafi gida, kasancewar isha ma ta wuce kuma ga shi wasu cikinsu ko SALLAHr magrib ma ba su yi ba, har bakin motar da ta kawosu Surayya da Dije suka rakasu, bayan sun tafi ne itama Surayya ta kira Mijinta ya zo ya ɗauketa, Dije ta nufi ɗakinta ta yi sallolinta sannan ta nufo ɗakinshi da ke sashenta, inda ta taraddashi zaune akan carpet fuskar haɗe ya yi shiru alamun ya faɗa cikin dogon nazari, ta sami gefenshi ta zauna tare da riƙo hannunshi mai yankuwa ta ɗora saman jikinta, cikin sanyin murya ta ce "Don Allah ka daina wannan damuwar komi da ka ganshi daman cen rubuce yake mune ba mu sani ba, sai abun ya faru ne mu ke ganinshi tamkar sabon abu, don ALLAH Malam ka daina wannan damuwar WALLAhi bana son ganinta a fuskarka ni dai" Safwan ya kallota da jajayen idonshi da suka rine saboda tsabar ɓacin rai ya ce "Ta ya bazan yi damuwa ba? Bayan Hajiyarmu ta sani mayar da wannan matar bala'i cikin rayuwarmu,yanzu ta sami damar yin haka ina ga abunda zata aikata a gaba? Hajiyarmu me yasa ta kasa gano Zainab ba alkhairi ce ga rayuwarmu ba? To Wallahi ko da ace zata dawo ɗin to ni kuma bazata taɓa jin daɗin zama da ni ba, sai ta bar gidan nan da ƙafafuwanta ba tare da ta shirya ba" Dije ta yi saurin kwantawa saman kafaɗarshi cikin muryar kuka ta ce "Ni dai ka yi haƙuri don ALLAH Malam saboda Hajiyarmu bazata taɓa cewa ka yi abunda bai dace ba kai ma ka sani?" Safwan ya shafo kanta cikin tausayinta ya ce "wai waye malamin? Ni fa bana son wannan sunan na fara gajiya da shi, don bazan yarda ki mayar da ni tamkar wani tsoho ba, amman ki daina kukan nan bana sonshi" Ya ƙare maganar tare da goge mata hawayen da ke ta kwaranya akan fuskarta, saboda zafin dawo da Zee ɗin da ya yi har cikin zuciyarta bata ji daɗin hakan ba, amman bata son ta nuna ne don kada aga rashin kyautawarta, amman ta ci alwashin duk ranar da ta dawo ita kuma a ranar zata bar gidan don bazata zauna ba ta kasheta a banza ba, Dijen ta ɗago fuskarta tare da saka hannu ta share hawayenta sannan ta ce "Mu je mu ci abinci" Ya bita da kallon mamaki ya ce " Ke kina jin yunwa ne?" Ta ɗaga masa kai, ya ce "magana za ki yi" cikin siriryar murya ta ce "Eh" sannan ya miƙe suka fito ɗakin har zata cire hijabin da ke jikinta ya ce ta barshi fita za su yi, ta biyoshi a baya suka shiga Mota kai tsaye ya ja suka fice. Basu zame ko'ina ba sai wata haɗɗaɗiyar Restaurant yasa aka yi mata odar abinci kala kala, Dije ta ƙi ci ta ce dole sai dai su ci tare, ba don ya so ba ta dinga ciyar da shi yana ci itama yana bata tana ci har suka yi ƙat! Sannan ya biya Bill suka nufi wata plazar suka sissiyo kayan tanɗe tanɗensu da maƙulashe sannan suka dawo gidan, duk da a ƙoshe su ke amman hakan bai hanasu sake cin gasashiyar kazar da suka siyo ba, tare da korawa da abun sanyaya maƙoshi, bayan sun kammale ne suka je suka yi wanka suka kwanta, duk da hannunshi da ke ciyo bai hanashi sakin jiki ya sake angwancewa da matarshi ba, saboda a yanda yake ji ko kaɗan ba zai iya haƙura da ita ba a wannan lokacin, haka suka raba dare suna farantawa juna har sai da ita kanta ta ji tausayinshi saboda yanda yake ta shan shagalinshi ba tare da ya yi duba da ciyon da ke hannunshi ba. Ko da safiya ta waye Dukansu cikin farin ciki da ƙarin ƙaunar junansu suka ta shi, bayan sun yi break ma haka suka sake komawa cikin duniyar ma'auratan sannan dukansu bacci mai ƙarfi ya yi awon gaba da su. Kiran wayar da ake ta yi masa wani bayan wani ne yasa ya yi saurin falkawa daga nannauyan baccin da ya ke yi, cikin yin wani uban tsaki tare da jin haushin da bai sakata a silent ba, ya miƙe ya ɗauko wayar ganin baƙin numbobi barkatai yasa ya yi saurin zaunawa, sai ga wani kiran ya sake shigowa da sauri ya ɗaga, sai ga wani ƙanen mahaifin Zee yana sanar da shi gasu cikin gidanshi sun zo suna son yin magana da shi. Cikin jin haushi ya kalli Dijen da ke ta baccinta hankali kwance, ya yi wani murmushin jin daɗi saboda ni'imar da ya kwasa a jikinta, ya yi mata wani kiss a iska ya hura mata sannan ya miƙe ya je ya yi wanka ya saka doguwar jallabiya baƙa ya ja talkamanshi plat ya fice tare da janyo ƙafa a hankali don kar ta tashi. Ganin baƙin motoci biyu tare da dattijan mutanen yasa ya shiga cikin natsuwarshi, ya isa wurinsu suka gaisa sannan ya yi masu jagora har sashenshi inda babban falon tarbar baƙinshi ya ke, bayan sun zazzauna ne aka sake gaisawa sannan suka sanar da shi sun zo akan su ji ba'asin abunda ke faruwa, don yanzu haka Mahaifin Zee yana kwance asibiti hawan jininshi ya ta shi, saboda abunda ya ji da kunnenshi da wanda ya saurara a gidan Tv.. Saboda ƙarin jawabin da su Ruma suka zo masu da shi na cewa Zee tana hannun ƴansanda, sannan da labaran da aka gabatar a gidan TV dangane da case ɗin masu ɗauke da rahotannin tabbatar da faruwar hakan daga bakin Safwan ɗin da kuma su Surayya da Ruma da sauran ƴan'uwanta duka da aka ɗauka, a daren jiya wanda kuma a ranar aka watsashi a gidan television, wanda ya watsu cikin mintuna ƙalilan tamkar tashin bom ta ko'ina labarin ake yi, sai dai ba'a nuna fuskokin kowa ba don Safwan ne da kanshi ya ce kada a bari fuskokinsu su bayyana saboda tsaro, amman duk da hakan labarin ba ƙaramin shiga zuciyar mutane ya yi ba, musamman wanda yasan ita Zee ɗin da su Safwan ɗin su ma, shiyasa mutane suke ta kiranshi don kawai su ji tabbaci wasu kuma don su jajanta masa. Ba tare da jan wata doguwar magana ba Safwan ya bayyana masu abunda ya sani da wanda ya ji a bakin Surayya da kuma Ruma, sannan ya yi masu jagora har falonshi na ciki inda aka yi abun wanda har lokacin akwai warin fetur ɗin duk da ya bi iska sosai, cikin sanyin jiki suka dinga bashi haƙuri don sanin da suka yi tabbas Zee bata da gaskiya, sannan suka nemi alfarmar a basu Zee su koma da ita gida saboda Mahaifinta da ke unconscious, ya ce sai dai aje gun Hajiyarshi duk abunda ta ce shikenan, dole suka ɗuru mota suka nufi gidansu Hajiyarmu, bayan an gaisa ne suka fara bata haƙuri kan abunda ya faru sannan suka nemi alfarmar inda hali suna son a janye wannan case don ALLAH kada a bari ya je kotu, ganin girmansu yasa ta ce da su ba komi insha ALLAHu ba za'a je kotu ba indai har itace ta haifi Safwan, cike da jin daɗi suka baro gidan suka nufi Police station ɗin sai dai duk yanda suka so a basu belin Zee hakan bai samu ba, don shi kanshi Safwan ɗin sun nuna masa tunda aiki ya zo hannunsu ko ya janye su bazasu janye ba, don case ɗinta ba ƙaramin case bane bale har a yi gaggawar kasheshi cikin ƙanƙanin lokaci, dole suka haƙura suka koma ba tare da ko ganinta sun sami damar yi ba, don a zahirin gaskiya Zee tana cikin mawuyacin hali saboda yanzu haka tana Asibiti maƙale da oxcegyn saboda azabar da ta sha a hannu ƴansandan. Tsawon sati biyu dangin Zee suna ta sintiri tsakanin Gombe da Yola akan su samu a kashe case ɗin, da ƙyar suka yi nasarar karɓota a hannunsu bayan uwayen miliyoyin kuɗin da suka narka saboda kawai a kashe case ɗin ba sai ya je kotu ba, don shi Safwan kallonsu kawai ya ke yi saboda shima kanshi da kalar na shi takun a ciki, don gurinshi na son ta gane kuskuren da ta aikata, don har lokacin bai cire takaicin dawo da itan da Hajiya Mama tasa aka yi ba, shiyasa ya nemi alfarmar Hajiyar akan a barta ta je gida har sai ya nemeta, haka ko aka yi sun karɓota aka kaita wurin Hajiyarmu ta bata haƙuri sannan ta baiwa Safwan da Dijen haƙuri suka kwasheta aka nufi Gombe da ita, inda ita kanta ta ji ina ma ace akwai wani garin da zata je ba cen Gomben ba, don tasan muddin ta je cen dole ne ta fuskanci ƙalubale ba kaɗan ba wajen ƴan'uwanta musamman masu goyon bayan Aminu. To fa sai hkr Zee😊 Akafta🙌🏻 D/AUTA CE✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *Don Allah masu neman book ɗin Ƙarangiya daga farko ku yi haƙuri idan an kammala za ku sameshi a complete ɗinshi, plss ku yi haƙuri kunji😢saboda anyi nisa sosai kuma bana son kuna tambaya baku samu ba😆* *Lamba 66* Zee durƙushe ƙasa tana kukan fitar hankali gaban gadon da Mahaifinta yake kwance gorar ruwa saƙale a hannunshi, ya yi shiru yana sauraren sautin kukan nata, zuciyarshi cike fal da wata sabuwar damuwa don abunda ta aikata da saƙon da Safwan ya isar masa ba ƙaramin dukan zuciyarshi suka yi ba, duk da ko an sanar da shi cewa ya mayar da ita a matsayin matarshi, amman har wannan lokacin bai dawo cikin natsuwarshi ba, wata ƙanwar Mahaifinta ce mai suna Baabaah Asabe ta katsa mata wata uwar tsawa ta ce "Zaki ta shi ki bar ɗakin nan ko sai kin iyar da kashe muna ɗan'uwa ne?" Zee ta miƙe jikinta yana rawa dafe da bakinta tana toshe kukan da yake fitowa tana kallon Daddynta bata son fita, cikin wata sabuwar tsawar Baabah Asabe ta sake cewa "Ki fita na ce ko sai na fiddaki da ƙarfi ne?" Zee ta dinga ja da baya tana gunjin kuka za ta fice Daddyn ya ɗaga hannu ya yafitota alamun ta zo wurinshi, da sauri ta dawo jikin gadon ta tsaya tare da riƙe kan gadon tana toshe kukan da ke ta fitowa a bakinta ta ce "Don Allah Daddy ka yafe mani nasan na yi kuskure ka yafe man......." Ya riƙo hannunta hawaye suna zuba akan fuskarshi ya ce, "me yasa kika aikata abinda zai janyo muna surutu a bakin mutane?" Zee ta riƙe hannunshi gam ta durƙushe ƙasa ta ce "plss Daddy ka yafe mani abun kunyar da na janyo maku don ALLAH" Baabaah Asabe ta fisgota da ƙarfi ta fiddata ɗakin sai da ta yi nesa da ɗakin Daddyn sannan ta wurgar da ita cikin fushi ta ce "Na ƙara ganinki a ɗakin nan sai na baki mamaki WALLAHI, abun kunya kuma da kike so ayi haƙuri kanshi ke me ya hana ki yi haƙurin a lokacin da kika ji ɓacin ran da ya janyo kika yi wannan rashin hankalin?, Yanzu in Banda ALLAH ya taƙaita wahala kinsan iya adadin rayuka nawa zaki saka cikin ƙunci?? Bayan waɗanda zaki yi sanadin barinsu duniya? Ko ko an faɗa maki cewa idan kin kashesu ke ƙyaleki za'a yi?, To buɗe kunnuwanki da kyau ki ji gidana zaki dawo da zama daga yau har zuwa lokacin da Mijin naki ya ga dama ya nemeki, tunda don kinga Yaya Mani ya sake maki da yawa ne shiyasa kike ganin dai dai kike da kowa, to har abada na gaba yana gaban kuma ba zai taɓa dawowa baya ba, don gashi cen yanzu kin baro mata gidan tana jin daɗinta da mijinta ke kuma ga ki nan kunci zai kasheki tare da Iyayenki, to Ni dai WALLAHI wannan karon bazan zuba mako ido kina yin abunda kika ga dama ba, dole ne a nuna maki cewa ƴa ce ke kuma haifarki aka yi akwai na gaba da ke har gobe" Tana ƙare faɗar maganar ta koma ɗakin Daddyn inda ta taraddashi sai shar ƙwallah yake yi, da ban baki da lallami ta samu ta shawo kanshi da ƙyar ya yi shiru, cikin nadamar irin damar da ya baiwa Zee a farko yake ta baiwa yar uwarshi haƙuri akan abunda ya aika akan Aminu, don itama tana cikin mutanen da suka yi fushi da shi akan auren sai dai don ance hannunka baya ruɓewa ka yanke ka cire inji hausawa fa, don kam a wannan zamani da muke ciki sau nawa aka yanke hannun aka jefar? ALLAH dai yasa mu fi ƙarfin zuciyarmu. Zee ta daɗe durƙushe anan tana kuka har sai da Ruma ta zo ta ɗagata suka shiga ciki, inda suka taradda mahaifiyarta itama sai kukan take cisga gwanin ban tausayi, saboda takaicin abinda Zee ta aikata wanda tuntuni take nusar da Daddynta akan sangarcin da ya yi mata don ko kaɗan baya so a kyareta bale a nuna mata laifin da ta aikata ta gyara, to ga irinta nan yanzu ta janyo masu abun gori wurin mutane, Zee ta je ta rungume Mahaifiyarta tana wani irin kuka mai cike da ban tausayi, Mahaifiyar ta tureta har sai da ta faɗi ƙasa, sannan ta miƙe tsaye tare da nunata da yatsa ta ce "Babban kuskuren da zaki aikata shine ki sake zuwa kusa da ni, don haka ki je tunda kin isa da kanki ki aikata duk abunda kike so, duniya ce wanda bai zo ba ma jiranshi take yi, kuma ta ishi kowa riga da wando har da zanen ɗaurawa" Tana ƙare faɗar haka ta shige ɗaki abunta har da su dantse ƙofa, Zee ta sake fashewa da wani sabon kuka Ruma ta dinga bata haƙuri, amman ina yanayin da take ciki yafi ƙarfin ban haƙurinta, dole ta zura mata ido tana kallo zuciyarta cike da jimamin abun a ranta, tare da godewa ALLAH akan ƙoƙarin da ta yi wajen hana Zee cika burinta akansu Safwan da abunda zai faru ALLAH kaɗai yasan iyakacinshi akan matsalar. **** Dijen Baffah kam ita da Malaminta sai cin amarcinsu suke yi hankali kwance, don ma masu zuwa jaje suna takurasu amman duk da hakan bai hanasu baiwa juna kulawa ba, cikin ɗan lokacin daga shi har ita sun sauya saboda natsuwar da suke samu da junansu, don shi Safwan ko tuno Zee baya son yi a ranshi, saboda ya riga da ya shafe babinta a rayuwarshi duka kuma yasa a ranshi duk runtsi ba zai sake zaman aure da ita ba, igiyar auren ce dai ta yi ta sha zamanta lafiya ko ita don ba ya iya saɓa umurnin Hajiyarshi ne da tuni ya cikasa mata ukunta ta huta. Safwan kwance a falon Dije yana mayar da reply ga masu yi masa jaje ne ta fito ɗakinta cikin sanɗa ta zo bayanshi ta tsaya, sannan ta yi saurin duƙowa saitin kunnenshi cikin ɗaga murya ta ce "Habiby!!!!!!" Ba shiri ya zabura tare da jefar da wayar cikin firgicin da ta sakashi, Dije ta dafe ciki tana ƙyalƙyala dariya tana nunashi da hannu, cikin dariyar shi ma ya miƙe da nufin kamota ganin haka yasa ta fara gudu tana dariya, shi ma ya biyota yana faɗin "Babyluv ki tsaya tun baki janyowa kanki aiki ba" Dije ta dinga gudu sunata zagayen falon har ya ci nasarar cafketa suka faɗa kan kujera tare suna mayar da numfashi, Dije tana kyalƙyala dariya tace "Don Allah Malam ka yi haƙuri ba zan sake ba" Safwan ya cusa kanshi cikin wuyanta yana shinshino ƙamshinta idonshi a rufe ya ce "Tunda baki tausayin kanki ai nima bana gajiya" Dije ta yi sauri zaro ido tare da marairece fuska ta riƙe kunnuwanta duka biyu ta ce "Am sorry my luv" Idonshi a lumshe ya fara yamutsata tana zillewa tare da bashi haƙuri amman duk da hakan bai hanashi yin abunda yake so ba, bayan ya kammala ne ya koma faɗin "Ke kika janyoni don haka dole ne ki yi haƙuri da halin Mijinki, faɗa man me kike so in yu maki ni ma wanda zan faranta maki tukuicin farin cikin da kike sakani?" Dije ta zumɓuro baki wa je ta ce "Baffah'na nike son in je in gano kwanan nan sai mafalkinshi nike yi" Safwan ya zaro ido waje ya ce "canza wani don bazan lamunci doguwar tafiya da ke ba a yanzu, don ban sani ba ko na yi ajiya a jikinki ki zo ki jaza man jinya ba" Dije ta ɓata fuska tace "To Ni dai shi kaɗai nike so tunda na riga da na zana jarabawata da sai in ce ita, sai kuma in zaka kaini in fara karatun nursing ɗin tun yanzu" Ya miƙe ya nufi ɗakinshi yana faɗin "in dai karatu ne har sai kin ce kin gaji amman tafiyar da kike so ce nake tantama, amman idan na yi shawara zan sanar da ke abunda na yanke" Dije ta yi saurin miƙewa ta biyoshi tana faɗin "Don Allah ka barni inje WALLAhi na yi kewarsu Inna raboda da cen tun lokacin da Hansai ta haifu fa" Ya yi saurin juyowa ya ce "to ke ma idan kin haifun ai sai ki je ba wani abu bane ba" Dije ta fara kumbura fuska tare da rufe ido ta ce ",to Ni ina na isa yin cikin ma?" Ba shiri ya fashe da dariya tare da dawowa inda take tsaye ya rungumota yana kallonta ya ce "Baki isa ba ko?" Ta ɗaga masa kai tana rufe ido, ya sake yin wani murmushi ya ce "Ok tom ya yi mu je in aunaki in gani in har da gsk baki isan ba" Dije ta zare jikinta ta ce "A kaini Asibiti dai likita ya aunoni ai shi zai gano ban isa ba" Ya ƙara janyota jikinshi ya sakar mata wani kiss a wuya ta zabura tare da kai masa wata kalar harara, ya yi dariya sannan ya ɗago fuskarta ido cikin ido ya ce "A ganinki akwai wani likitanki bayan Ni Malaminki? To buɗe kunnuwanki ki ji, kinga waɗannan abubuwan sun ƙara cikowa" Ya ƙare maganar tare da damƙo dukiyar fulaninta ta yi saurin lumshe ido, ya bita da kallo cike zallar ƙaunarta da sha'awarta da kullum take ɗibarsa, ya sake matso hips ɗinta ya ce "Shi ma wannan ya ƙara buɗewa alamu sun nuna ni ɗin ba ƙaramin jarumi bane, don haka daga yanzu ki ɗauki kanki dai dai da matsayin mace mai ciki, saboda haka ba inda zaki je amman in har su ɗin kike son gani zasu zo har gidan nan ki gansu insha ALLAHu" Dije ta yi saurin buɗe idonta tare da yin wani tsalle ta maƙalƙaleshi cike da tsantsar farin ciki ta ce "Wayyo Habibyna shiyasa nike bala'in sonka" Baki sake ya ce "To bi a hankali kafin ki sanar da ni irin bala'in sona da kike yi don bazan lamunci a yi man asara ba" Dije ta rufe idonta tace "Wai da gaske cikin ne da Ni?" Yana dariya ya ce "idan kina tantama ki bani nan da sati biyu zaki gasgatani" Ta yi saurin barin wurin ta shige ɗakinta tana dariya wai ita kunya, ya bita da kallon ƙauna sannan ya shafo kanshi ya shige nashi shima saboda magriba ta kawo jiki kuma yana so ya sami jam'in SALLAH a Masallacin da ke manne da gidanshi, wanda bai wuce sati ɗaya da buɗashi ana sallah a ciki ba. Tsuntsayen soyayya ayi a hankali kar ƙone wajen cinta da zafinta😝 Akafta👩🏻‍🦯 D/AUTA Ce ✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *Don Allah masu neman book ɗin Ƙarangiya daga farko ku yi haƙuri idan an kammala za ku sameshi a complete ɗinshi, plss ku yi haƙuri kunji😢saboda anyi nisa sosai kuma bana son kuna tambaya baku samu ba😆* *Lamba 67* Zancen Safwan ya tabbata don kuwa sati biyu bai cika ba Dije ta fara laulayi mai ɗan karen zafi, don kuwa ruwa ma idan ta sha sai ta amayesu, ga shi a lokacin Safwan ya fara zirga zirgar neman aikinshi, inda aka yi dace aka nemeshi Abuja interview, shiyasa ya mayar da ita wurin Hajiya amman ko da yaushe suna maƙale a waya har ALLAH ya dawo da shi, sannan ya kwashi Matarshi suka koma gida yana ci gaba da renon abarshi, don kuwa duk abunda take so baya jin nauyin dattijuwar da ke taya Dijen aiki yake zagewa kitchen ya yi mata, ko ba daɗi ta cinye tana santi daga baya kuma ta amaye tass!, Haka suke abu ƙaɗan ya ce sai sun je Asibiti an dubata don baya son ta zauna cikin gida da wata matsala a tattare jikinta, shiyasa duk wani abu sai ya nemi sani tare da shawarwarin ƴan Asibitin, duk da wani zubin yana biyewa son zuciyarta ya yi mata duk abunda ta ke so saboda kawai ta yi farin ciki, don ba ƙaramin jin jiki take yi ba, cikin haka ne Safwan ya tura direba ba tare da ta sani ba ya ɗauko su Baffah da Inna da Hansai da Usmanu don Gambo ta ce ita ta yi tsufa ba zata iya yin wannan doguwar tafiyar ba, duk da har a ranta ta so ace ta je ta dubo jikallenta, amman yanayin jikinta na tsufa yau lafiya gobe ciyo yasa ta haƙura ba don tana so ba. Dije cike da mamakin ganin gidan wasu ƴan'uwansu Safwan da su Surayya a kitchen sai hidimar dafe dafe da soye soye suke yi, in sun sauke wannan su ɗora wancen gida ya runtume sai zuba ƙamshin garar da ake ta haɗawa su Inna ake yi, duk abunda aka yi sai an kawo mata ace ta ɗanɗana ta ji in ya yi, cike da mamaki take tambayarshi wai halan wasu baƙi ne zai yi masu muhimmanci shiyasa ake ta wannan hadahadar?, Yana dariya ya ce "Ke dai ki ci ki ƙoshi ki sha maganin amanki ki je ki yi wanka ki tsalo kwalliyarki cikin sababbin ɗinkunanki" Cike da jin daɗi ta fara cin wani dambun nama tana ci tana kaɗa kai alamun ya yi daɗi sosai, hannunshi riƙe da plate ɗin tana ci yana yi mata dariya, bayan ta ci abunda zata iya ci ne ya bata magani ta sha sannan ya je ya taimaka mata ta yi wanka, wanda ko shi ɗin sai da suka ɓata lokaci sosai sunata wasarsu ta ma'aurata, tare suka yi wankan suka fito sannan suka shirya cikin taimakekeniyar juna, kafin ka ce me sai ga su dukansu sun fito shar! Abunsu kowane sai tashin ƙamshi yake yi, duk da ta yi rama amman hakan bai hana kwalliyar ta yi kyau ba, don kuwa fatarta ta washe sosai ta yi haske dai dai jikinta, haka ma ta ƙara yin kyau masha ALLAH dukiyar fulaninta sun ƙara cikowa sosai a ƙirjinta, waɗanda a kullum baya gajiya da lalacewa akansu yana santin yanda suke ta ƙara hawa tamkar an hura masu iska ga taushi tamkar balombalom, dole ba don ta so ba take sakin jiki ta barshi ya yi abunda yake so don duk da ciyon ta wannan ɓangaren baya ɗaga ƙafa, a cewarshi wai duk wani maganin da zata sha bai kai wannan tasiri a jikinta ba, da wayo da lallami yake samun abunnda yake ƙulafuci, don idan ma ta ce zata yi tirjiya ma ba haƙura zai yi ba shiyasa take ta danne zuciyarta tana faranta masa, amman ita sam bata son damuwa a wannan lokacin da zai barta na tsawon watanni da tafi sha'awar hakan fiye da yanda yake manne mata akan biyan buƙatarshi. Bayan sun gama kimtsa komi da ko'ina ne Safwan ya kawo falo ya ce ta zauna ta jirashi minti biyar kacal zai je ya tarbo baƙinshi ya dawo, aikuwa cike da mamakin da son ganin waɗanni baƙi ne haka?, Ta zauna tare da su Surayya suna kallo a falo suna fira jefi jefi, don ko ita ya ja kunnenta sosai akan kada ta sanarwa da Dijen zuwansu Baffahn ya fi so ta gansu unexpected, ai kuwa suna nan suka ji saukar motoci, Surayya ta yi tsalle ta kalleta ta ce "Yau fa manyan baƙi ne da mu a garin namu" Dije ta yi wata dariya tare da cewa "ai kam ga shi na ga alama don ko mu mun sheda da waɗannan manyan baƙi" Surayya ta nufi hanyar fitq falon da sauri tana murna duk da itama cikin ne a jikinta, Dije ta bi ta da kallo ta ce "Aunty Surayya dai ba'a girma ba har yanzu, da cikinki kike wannan uban rawar jikin ki je ki janyo muna jidali muna zaman zamanmu" Surayya ta ɗaga murya kafin ta ƙarasa ficewa ta ce "ai sawun Giwa ya take na raƙumi wannan abun murnar dole ne mu nuna farin cikinmu" Dije haka kawai ta ji ta kasa ɗauke idonta a ƙofar da ake shigowa falon, saboda jinta da take yi cikin ɗokin ganin su wanene waɗannan baƙin, ai kuwa sai ga Surayya riƙe da Abba yaron Usmanu wanda aka yiwa Baffah takwara da shi, cike da mamaki ta zaro ido cen sai ga Hansai bayan Surry, a zabure ta miƙe Baki a sake zata yi magana kenan ta hango Inna a bayan Hansai, aiko ba shiri ta fasa wata uwar kuwwa ta nufosu aguje tana kururuwa sai ga Baffah ta hango da Usmanu tare da Habibynta, cike da tsantsar mamaki ta dinga rufe ido tana budewa tare da murzasu tana faɗin "Wayyo ALLAHna shin mafalki nike yi ko gaske?" Hansai ta riƙo hannunta cike da jin daɗin ganinta ta ce "Ido buɗe ne mune muka kawo maku ziyara" Dije ta ruƙunƙumeta tana murna ta saketa ta nufi Inna ta faɗa jikinta tana ihun jin daɗi, ta saki Inna ta zo gaban Baffahnta ta riƙo hannunshi tana faɗin "Ashe ko da gaske kai ne Baffahnah wayyo daɗi kasheni Ni Dije" Usmanu ya hararota ya ce "ashe dai har yanzu da sauran hankalin?" Tana dariya ta saki Baffah ta ce "Yaya Usmanu ya zu fa na girma kai ma ka sani ai" Surayya ta kai su Inna har falon sannan ta dawo ta ce da su Baffahn su shigo a gaisa kafin a kaisu muhallin da aka tanadar masu, Safwan dai tsaye kawai yake hannunshi a aljihu yana kallon Matarshi wadda ita har kullum bata gajiya da abun dariya, haka ma shagwaɓarta da wautarta suke ƙara dulmiyashi cikin ƙaunarta, waɗanda a cen inda aka fito yake ganin shirmenta amman sai ga shi yanzu sun yi masa rana, don kuwa salon ba ƙaramin burgeshi yake yi ba. Bayan sun zazzauna ne aka sake sabuwar gaisuwa Dije baki yaƙi rufuwa saboda murna, Hansai kam sai yi take yi tana satar kallon falon saboda ganin tamkar ba a duniya take ba, don ko ita kanta Inna ta jinjina irin wannan daula da Dijenta ta ke ciki, shi kam Baffah ba ma maganarshi ake yi ba don sai hamdala yake yi cikin zucinshi akan wannan ni'ima da Allah ya wadata Dijenshi da ita. Bayan an ƙare gaiigasawa ne Dukansu aka kaishi masaukinshi, Inna da Hansai aka kaisu wani ɗakin baki da ke cikin sashen Dijen, Baffah da Usmanu kam takanas Safwan ya yi masu jagora zuwa ɓangarenshi, inda aka kaisu wani ɗakin alfarma da aka haɗashi tamkar ɗakin wasu sarakuna don kuwa ya sha ado ta ko'ina sai ƙamari ke ta shi. Sannan aka kawo masu abincinsu da aka tanadar masu kala kala, bayan sunyi Sallah ne suka fara lodawa cikinsu suna jinjina irin wannan uwar gara da aka tanada donsu kawai, Usmanu ya buɗe ƙafafuwa sai jan girki yake yi yana faɗin "Ashe Baffah shiyasa kake ta farin ciki saboda kasan inda ka kawo ƴarka?, To Wallahi a ja kunnenta duk tsanani ta ci gaba da yi masa biyayya, don ko watarana ta yi masa shirme ya kaita ƙofar gida ya ce ya ce ta fi gida, to ta ce masa ita ba inda zata je don taga wurin zama, yana kaita tana dawowa har sai ya gaji don kanshi ya haƙura ya ƙyaleta" Baffah nama cike da bakinshi ya ce "ba ma zata aika shirmen ba bale har akaita ƙofar gidan, don haka ka godewa ALLAH ka godewa Dijengalata don sanadinta ne kake cin wannan naman" Haka suka dinga firarsu da suka saba cikin raha da tsantsar farin ciki da jin daɗin ganin Dijensu ta yi dacen aure. Inna Kam da Hansai su ma suna inda aka saukesu Hansai tare da yaronta sai jan gara suke yi Inna kam cike da jin nauyi take tsakura abincin, Dije tana kallonta cike da jin daɗi ta ce "Inna ki saki jikinki don ALLAH ki ci abincinki, ba fa kowa daga Ni sai ku ko Surayya ta barku ku ji daɗin cin abincinku cikin nutsuwa" Inna ta maka mata harara tace "don ma kin ci sa'a na zo? Ba yanda banyi da Baffah'nki da Mijinki ba akan a barni ba sai na zo ba suka ce dole da ni za'a yi tafiyar, Ni ban saba da wannan rashin kunyar ba ta ƴan zamani, zuwa gidan Suruki har da zube ɗuwawu a cenye abincin Suruki, kai Ni Hasiya wannan zamani ina zaka da mu? Kin ga Inna Tumba har ALLAH ya yi mata rasuwa bata taɓa tako ƙafarta ɗakina ba" cewa da Mahaifiyarta da ta haifeta ma'ana kakar Dijen. Dije tana dariya ta ce "Cabɗi to ai Ni Inna duk wanda ma zai auri ɗiyana dole ne ma ya yi man nawa ɗakin a gidanshi yanda ya yiwa Mahaifiyarshi" Inna da Hansai suka zaro ido, Dije ta ƙyalƙyale da dariya ta ce "ALLAH kuwa zama zan yi yanda ta zauna idan aka muzgunawa ƴata in fito mu raba gari Ni da Uwarshi WALLAhi" Inna ta ce "laaa! Na ga aya ashe Dijen har yanzu ba ta yi hankali ba, to ai sai ki janyo a tattaroki tare da ƴar a watsoku waje da kayanku kusan na yi WALLAhi" Dije da Hansai suka dinga dariya Surayya ta shigo da wasu sauran kulolin itama ta zauna aka ci gaba da firar da ita anata dariya. Da ƙyar suka ciyo kan Inna ta ci abincin sai dai ta ƙi cin sauran abubuwan a gaban Surayya da Hansai, saboda surukutar da ke tsakaninsu, ganin haka yasa Dijen ta ja Hansai ɗakinta suka bar Inna nan ita kaɗai sannan ta cisgi garar itama cikin ɗar! ɗar! don kada a risketa bata sani ba. **** Zee kam a ranar bata kwana gidansu ba don kuwa Baaba Asabe ta kwasheta da kayanta suka nufi gidanta, suna shiga tashin farko ta ce da ita "Bani wayarki" Zee ta ce "ai Ni tun ranar da na bar gidan ban sake ganinta da idona ba, tana cen Yola a falona ban sani ba ko ya ɗauke mani ko kuma ma an sace oho" Baabaah Asabe haɗe da fuska ta ce "to je ki kai kayanki ɗakinsu Inna Dela ki dawo ki ji" ZEE ta zaro Ido waje ta ce "Inna Dela fa kika ce Gwaggo?" Kai tsaye ta ce "eh ita nace ko a cikin halittar jikinki akwai abunda su babu irinsu jikinsu?? " Zee ta girgiza kai tare da sosa kai murya ƙasa ƙasa ta ce "ƴan aiki ne fa Gwaggo, Ni dai don ALLAH ki barni ko ɗakin waje ne zan zauna amman ba ɗakinsu Dela ba" Baabaah Asabe ta katsa mata wata arniyar tsawa ta ce "za ki je ki kai kayan ko sai na haɗaki da buloli yanzu?" Zee ta zabura aguje ta nufi inda ɗakin na ma'aikatan gidan yake saboda tsabar tsoron Baabaah Asaben da take yi, tana tafe tana gunguni Baabaah Asabe ta ɗaga murya ta ce "Ai da kin tsaya ki nuna man banbancinki da ƴar aikin, to ai gara su basu shuka tsiyar da kika shuka a gidan mazajensu ba amman ga su a matsayin yan aikin, to ke in Baki yi a hankali ba yan aikin ma sai su fiki daraja a idon duniya, don ko wannan bankaɗa da kika janyo aka yi wa zuri'armu kawai hakkinmu ya isheki ballantana haƙƙin ɗaukar rai da kika so ki yi, in banda ALLAH ya tarfawa garinki nono da yanzu kin janyo muna bala'in da bamu san inda zamu jefa kanmu ba, don haka WALLAhi Ni banu wani ragi tsakanina da ke a gidan nan don yan aikin ma sai sun fiki daraja a wurina" Har Zee ta ajiye kayan ta fito bata daina sababin faɗa ba, haka ta zaunar da ita tana ta tsara mata abunda zata yi a gidan tun daga safiya har dare, hankalin Zee bai ta shi ba har sai da ta ji wai har da wanki zata dinga yi kullum, wankin ma kuma na samarin ƴaƴanta da suka balaga wasu ma har suna zancen aure amman ace har da su zata dinga yiwa wanki,cike da ƙuncin zuciya ta kwana tare da cin alwashin muddin ta ji za'a kasheta WALLAhi dole ta tsere ta bar mata gidanta, don bazata zura ido aiki ya kassarata ba tunda daman cen ita ko undies ɗinta wanke mata ake yi, ba abunda ta iya in banda dafa indomie ko shi don watarana in an dafo mata tace bata yi mata daɗi ba, Mahaifiyarta tace ba mai sake dafo mata wata in tana so ta je ta dafa da kanta, to da hakan ne ta iya dafata saboda Daddynta ya ajiye mata masu aikin da suke yi mata duk abunda take so, to yanzu ga shi Baabaah Asabe zata sakata shiga uku. Don kuwa tun da sassafe ta tadota daga baccin da ta koma na bayan asuba, ta fito ta kaita wajen tulin kayan wanke wanke ta ce ta fara idan ta gama ta je ta share gidan lungu da saƙo, cike da fargaba da tsananin tashin hankali ta ke ƙarewa ƙaton gidan kallo, tana nazarin ko rabinshi aka sakata sharewa ai an so kasheta bale duka, sai ga muryarta a saman kanta tana faɗin "Zaki fara wanke wanken ko sai na fara sauke maki bulalata a jikinki?" Zee jiki yana rawa ta fara harhaɗa kwanonin Baabaah Asaben ta ce da wata matashiyar ƴar aikinta ta nunnuna mata yanda zata yi, tana tsaye har aka nunawa Zee komi ta fara m wankewa tana hawaye sannan ta bar wajen, ta dawo falo ta zauna zuciyarta cike da jin daɗin yanda ta yi nasarar da Daddyn Zee ɗin ya gano kuskuren da ya tafka akan tarbiyyar ɗiyarshi, tare da jin daɗin amincewar da ya yi akan ta zo da ita hannunta ta zauna don bai san ƙudurinta akan Zee ɗin ba, da wataƙila ba zai yi saurin amincewa ba duk da kuma yasan ba zata yi mata ta daɗi ba, amman bai taba tunanin irin wannan azabtarwa zata yi mata ba. Zee Kam haka aka yini ana aiki wankin samarin ma sai da ta yi sai dai su ma kansu ba da son ransu ba don dai Mahaifiyarsu ta yi masu jan kunne da kashedi sosai akan duk abunda suka ga ta saka Zee iyakacinsu Ido, Dole Suka zura ido suna kallon yanda take ta yi masu wankin, cikin ƙankanin lokaci hannunta ya yi ja ya saluɓe aiko ta fara yarfa hannu tana kuka, ganin haka yasa aka canza mata wani aikin ko da dare ya yi ta kwanta ko'ina nata ciwo yake yi, da ciwon jiki ta kwana kan tabarma tana haki tana juye juyen wahala. Sorry Zee😢 Wai ko dai in zo in gudu dake ne🙊 gidan mum Irfaan ko gidan Daughter Rufaida ko wurin ƙanwata Asiya? Ki yi shawarar inda kike son zuwa kafin in dawo🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🤣 Akafta😊 D/AUTA CE✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *Don Allah masu neman book ɗin Ƙarangiya daga farko ku yi haƙuri idan an kammala za ku sameshi a complete ɗinshi, plss ku yi haƙuri kunji😢saboda anyi nisa sosai kuma bana son kuna tambaya baku samu ba😆* *Lamba 68* Daren ranar Dije da Inna sai hira suke ta zubawa, don ita Hansai tun da ta ji cikinta ya ɗauka ta baje abunta sai sharar baccinta take yi ita da yaronta, ganin dare ya miƙa ne Inna ta ce da Dijen ta tashi ta je wurin Mijinta, Dije tana zumɓuro baki ta ce "Anan zan kwana Inna mu yi ta firarmu Ni da ke Inna, sabida ALLAH yaushe rabon da mu ga juna an daɗe fa? Ni dai don girman ALLAH Inna ki barni in kwana abuna anan ɗakin" Ta ƙare maganar tare da zubowar wasu ƙwallah, Inna ta gyara ta yi kwanciyarta tana faɗin "To Ni dai bacci nike ji idan ke baki gaji da firar ba ki ci gaba ai akwai aljanun dare suna saurarenki zasu tayaki yin firar" Dije ta zaro ido tuno abunda ya taɓa faruwa a school ta yi saurin kwanciya bayanta ta ƙudundune tana faɗin "Inna ki yi man addu'a kar su kamani don ALLAH" Inna ta miƙe zaune cike da mamaki ta ce "zaki ta shi ki je wurin Mijinki ko ko so kike yi ya ɗaukemu waɗanda basu san abunda suke yi ba?" Dije ta miƙe tana kallon ƙofa tace "To mu je ki rakani WALLAHI tsoro nike ji" Inna ta riƙe baki cike da mamaki ta ce "Tunda kike gidan baki ji tsoro ba sai yanzu da kika ga mun zo ko? To ya yi insha ALLAHu gobe tun da sassafe mu zamu bar maki gidanki tunda so kike yi ya ɗaukemu mutanen banza" Dije ta miƙe ta fito Inna ta rufo ɗakin zuciyarta cike da nauyin kada Safwan ɗin ya ga sun riƙeta, aikuwa Dije cikin sanɗa ta ke tafiya tana waige sai jin ta yi anyi caraf da ita, ba shiri ta yage baki da nufin fasa ƙara taji bakin Malaminta cikin nata, gano shine yasa ta ƙara ruƙunƙumeshi jikinshi tana faɗin "Mu je ɗaki tsoro nike ji" Cike da jin daɗi ya sake manneta jikinshi suka yi ɗakinshi, ganin da gaske tsoron take ji yasa ya fara tambayarta abunda ya tsoratata, cikin murya ƙasa ƙasa ta yi masa bayanin yanda suka yi da Inna, cikin dariya ya ce "ALLAH ya biya Inna da gidan Aljannah don Ni ta kyauta man, saboda tun ɗazu da na dawo wurinsu Baffah nike ta juye juye Ni kaɗai akan gado, dole na fito falo na zauna ina kallo nan ma na ji ba daɗi na kashe ina tunanin yanda zan yi in ce ki zo, ashe Inna tasan ƙishina shiyasa ta koro man ke waje" Dije ta tureshi cikin fushi ta ce "tunda haɗe man kai kuke son yi ai ku je ni ma gobe wurin Hajiyarmu zan kwana " Safwan ya janyota jikinshi ya ce "ai Hajiyarmu ma ba zata so ki bar Mijinki shi kaɗai ba yana kewa ba" Haka ya hilaceta ya gwangwaje abunshi tare da sassafta murya wurin sambatun da ya saba, don gudun ya tafka abun kunya gaban surukai. Tun da Sassafe aka kammala masu komi na breakfast ɗinsu tare da taimakon wasu yan aiki biyu da Hajiyar ta ƙaro masu, bayan sun karya ne aka sake wata sabuwar gaisawa sannan Safwan ya kwaahesu zuwa gidansu su gayar da Hajiyar, tarba ta mutumci Hajiya Mama ta yi masu fuska cike da fara'a tamkar cewa da man cen ƴan'uwanta ne, Inna da Baffah suka yi godiya sosai akan yanda take kulawa da Dije tamkar itace ɗiyarta ba Safwan ba, Inna da Hansai da Dijen sun daɗe gidan tare da Hajiya Mama sannan Safwan ya dawo da su Baffah da ya je kaisu yawon ganin gari, marece sakaliya ya ɗaukesu ya kaisu gidan Mijin Surayyy, inda itama ta yi masu tarba mai kyau tamkar kar su rabu saboda kirkin Surry ba ƙaramin burge su Inna yake yi ba, sai gaf da magriba suka dawo gidan inda suka taradda an haɗa masu abincin dare mai rai da lafiya, tuwon farar shinkafa da miyar agusi ta ji zuƙa zuƙan namomi tare da lafiyayye ferfesun kajin turawa masu manyan tsokoki, bayan sun ci abincin ne aka koma yin firar bankwana saboda tun da sassafe zasu juyawa inda suka fito, tun cikin daren Safwan ya tanadar masu duk abunda zai ba su ya basu, Hajiya Mama ma da nata kalar tsarabar Surayya ma da tata, haka suka yi ta godiya kamar ba gobe, don kuwa su kansu sun san ba ƙaramin arziƙi suka yi ba,saboda bancin sutura kuɗi tsabarsu dubu ɗari Safwan ya baiwa Baffah, Inna dubu Hamsin Usmanu da talatin Hansai ashirin yaronta goma, bayan suturar da aka cikasu da ita da turaruka da sabulai kala kala, yaron Hansai kanshi ledar kayanshi daban aka siyo mashi masu ɗan karen kyau. Tun cikin daren Dukansu suka saka Dije tsakiya suna yi mata nasihohi tare da jan kunne akan ta ninka wa mijinta da Mahaifiyarshi biyayyar da take yi masu, haka ma ƴan'uwaanshi ta riƙesu tamkar yanda zata riƙe nata, in ma da hali su fi natan don kawai ta sami zaman lafiya da kwanciyar hankali a gidan aurenta, anan ne take sanar da su gumurzun da aka yi da Zee akan kashe sun da ta so yi tare da ƙudurinta da ta yanke akan muddin Zee ta dawo to ita zata bar mata gidan, cikin fushi Usmanu ya ce "WALLAHI kika kuskura kika bar wannan gidan akan baƙin shirmenki sai na saki jiki na lakaɗa maki shegen duka" Inna tana harararta ta ce "to bari ki ji da kyau muddin kika taka ƙafarki kika bar gidan nan bada izinin Mijinki ba to ki sani ban yafe maki ba" Baffah ya yafito Dijen ta zo gabanshi ta zauna tana zimɓoro baki yana dariya ya ce "Shin Ina Dijengalata?? " Hawaye suka zubo mata ta ce "Gani Baffah". Yace "to ki ajiye komi ki yi zaman aurenki tsakani da ALLAH, ki sa a ranki duk duniya babu wanda ya isa ya yi maki abunda ALLAH bai yi maki ba, haka ma kaf mutanen duniyar nan idan ymza su taru akan sai sun kasheki to basu isa su kasheki ba har sai kwananki ya ƙare, don haka ki ɗauka cewa duk abunda kika ga ya sameki daga ALLAH ne, abunda ma ya kuskure maki shi ma daga ALLAH ne da kin yi hakan shikenan kin ci maganin matsalarki, ALLAH ya saukeki lafiya ke da ƴar uwarki kuma ya baku zaman lafiya a gidajen aurenku" Dije ta rufe fuska cike da jin kunya ta ce "Ameen" cikin maƙoshi, haka suka dinga nusar da ita abubuwa da yawa masu amfanarwa sannan ta saki jiki ta dawo dai dai aka ci gaba da fira cikin raha da annushuwa. Dije ta ce su gayar mata da Gambo da su Ladiyo, ta ɗauko sako ta bayar ta ce akai masu ace in jita, don kuwa su Ladiyo kowa dubu bibbiyu ta bada akai masu Balan duduwa dubu biyar tare da Duduwar itama dubu biyu, sannan saƙon Maigari da Matanshi na shadda da atamfofi, Malaminta na makarantar allo ma da saƙonshi tare da ɗalibanta na makarantar da ta baiwa sababbin goma goma ta ce a raba masu su yi mata addu'a, abun dai masha ALLAH gwanin burgewa Dukansu kowane zuciya cike da tsantsar farin ciki da jin daɗi, tare da yi wa ALLAH godiya da ya baiwa Dije miji ɗaya tamkar da goma kuma ya haɗasu da mutanen kirki. Tun cikin daren su Hajiya Mama suka zo suka yi sallama da juna shiyasa tun da sassafe suka fara shirin barin garin, Dije sai kuka take ci ana lallashinta har motarsu ta ɗaga ta faɗi ƙasa tana ta kuka gwanin ban tausayi, sai da Malaminta ya yi mata jan ido sannan ta fara shiga taitayinta, don ya yi mata alƙawarin in dai har ta bar kukan to itama zai kaita idan cikinta ya yi ƙwari ta je ta ganosu, sannan ne ya samo kanta ya koma aikin ban baki tare da daɗin baki kala kala. Sati ɗaya a tsakani takardar samun aikinshi ta fito inda kai tsaye aka postershi Abuja, tare da zunzurutun albashi mai tsoka da kyautar sabuwar mota da gida a garin Abuja, mutane da yan uwa sai murna ake yi masu don Lawi kanshi sai da ya zo ta ya murna tun daga Gombe har Yola tare da Amaryarshi da tuni itama ta kusa zama Mama, don kuwa ɗauke take da cikinta ɗan wata biyar itama kyakkyawar bafulatana da ita masha ALLAH, kwanansu ɗaya a gidan suka koma cikin kewar juna, saboda jinin matar Lawin mai suna Maryam da ya haɗu cikin lokaci ƙanƙani da na Dijen Baffahn, saboda itama ba laifi akwai barkwanci da son wasa da dariya gata da saurin sabo. Lokacin da aka ɗibar masa da ya cika ya fara zuwa aiki, fiddo da wasu dattijai biyu suka dawo gidan suna taya Dijen Baffah zama, atakure ya yi sati ɗaya ya dawo Yola cike da ɗokin Matarshi, don ba ƙaramin sabo ya yiwa kanshi da ita ba, shiyasa ya ji gaba ɗaya zama garin bai masa daɗi ba, dole ya kwashi Matarshi suka nufi garin Abuja a gidansu da aka basu, don ya so har sai ta haifu sannan su dawo nan ɗin , to amman ya ga hakan bazata samu ba don sabon da ta yi masa kanta, ga shi kuma shi matan banza basu gabanshi don ko na kwarai ɗin baya kula shirginsu bale har na banzan. Aunty Ummi da su Husnah sai murna suke yi Dijen ta dawo kusa da su, shiyasa kullum suna tare basu wannan wurin shaƙatawa basu wurin ciye ciye da tanɗe tanɗe da lashe lashe, kafin ka ce me idon Dijen sun ƙara buɗewa cikin garin Abuja, don kuwa ita kanta tasan wurare da yawa. Da zama ma ya yi daɗi sai ga shi da koya mata driving, tana jin tsoro tana fargaba haka yake koya mata ita duk da bata so, saboda bala'in tsoron da ta ke ji amman a hankali ko wata biyu basu rufa ba a garin ta fara iyawa, don ya ce da ta iya zai siya mata tata idan ALLAH ya sauke ta lfy, ko don ta fara zuwa makarantar da take kwaɗayi ba tare da takura ba, don saboda busyn da yake yi a wurin aikin nashi kullum, gashi kuma yana son ta yi karatun don shine babban gatan da zai mata a rayuwa, saboda akwai rayuwa akwai mutuwa in mune yau ba mune gobe ba, Yana da kyau mace ta dogara da kanta ko don ranar da kika rasa mai tallafa maki ki kula da kanki da yaranki da iyaye da ƴan uwanki duka. **** ZEE Kam tun bata saba da aikin wahala ba har yanzu ya fara zame mata jiki, don ta yi ta tserewa tana zuwa gidajen yan uwa ana dawo da ita wurin Baabaah Asaben, don kowa cike yake da haushinta ba kaɗan ba musamman ƙin Aminu da ta yi tare da abun kunyar da ta janyo masu, Mahaifiyarta kanta da ta je gidan take korota ta fito tare da yi mata kashedi da gargadin cewa duk ta yarda Daddynta yasan halin da take ciki a gidan gwaggonta sai ta tsine mata, tana kuka take komawa yanzu har ta haƙura don kanta ta daina gudun, ganin hakan yasa Gwaggon ta fara sassafta mata daga matsin lambar da take yi mata, don kuwa ta ladaftu sosai kuma ta gano irin kuskuren da ta so aikatawa, ta yiwa ALLAH godiya da yasa Ruma bata bari ta aikata mugun abun da ta yi niyya ba, ga shi ta rasa Safwan ɗin kuma Aminun ma ta rasa shi don kuwa yanzu haka ƙawarta Sadiya yake aure, don Ruma ya so aura ta nuna masa amincinta da Zee bazata iya aurenshi ba, Sadiya kam hannu biyu ta karɓeshi yanzu haka da ƴarsu tana nan mai sunan Mahaifiyarshi. Zee ta shiga damuwar rashin jin Safwan ɗin da kullum take tsumayin zuwanshi gareta ya ce ta dawo, amman shirun da ta jini yayi yawa ne ta fara tunanin binshi da kanta, don laifin da ta aikata masa ko ma wanene dole ne ya sallamata, kasancewar tasan numbarshi akanta yasa da Ruma ta zo ta ari wayarta ta kirashi, kasancewar baya da layin Rumar a lokacin shiyasa daga baya ya bi miss call ɗin da ya gani kusan goma sha bai ma san an kira ba, sai dai jin murya Ruma yasa ya yi saurin faɗin "Wacece ??" Jikinta yana rawa ta ce "Rumasa'u ce ƙawar Zee don ALLAH ka yi haƙuri da abunda ta aikata ita ce ta kiraka ɗazu da naje wurinta ta ari wayar ta kiraka baka ɗaga ba, saboda WALLAhi yanzu Zee ta canza sosai kuma ta yi nadamar abunda ta aikata" Cike da mamaki ya ce "Daga ke har ita kada ku sake nemana matuƙar kuna son kanku zaman lafiya" Ƙittt! Ya kashe wayarshi gaba ɗaya cike da jin haushinsu duka, Dije da ke shigowa ɗakin da tiren coffee'nshi ta ajiye tiren akan stool ta ɗauki cup ɗin ta zauna tana kallonshi tare da nazarin yanayi shi, sannan ya zura hannu da nufin ya karɓi kofin ta riƙe gam idonta a kanshi ta ce "Wa ya taɓo man Habibyna? Don haka na fita na barshi ba plss ka yi haƙuri ko ma mene saboda zama cikin mutane sai da kai zuciya nesa Mijina" Cike da jin daɗin kalamanta ya duƙo ya kurɓi coffee'n sannan ya ce, "waɗannan ba irin mutanen da kike tunani bane, ki share da su kawai don na riga da na shafe babinsu a rayuwata" Dije ta miƙa masa cup ɗin ya karɓa ya dinga sha a hankali har ya shanye, sannan ta karɓi cup ɗin ta ajiye ta kalle da kyau ta riƙo hannunshi ta haɗe da nata ta dunƙule waje ɗaya ta ce "Wacece ta kiraka?" Cikin diriricewa ya ce "Ruma ce ƙawar Zee take rokona akan inyi haƙuri in yafe wa Zee wai ta yi nadamar abunda ta aikata" Dije ta ji wani ɓacin rai ya ziyarci zuciyarta, amman ta yi dubarar ɓoye damuwarta ta ce "To kai kuma me ka ce?" Ya ɓata fuska tamkar a lokacin sannan ya sanar da ita abinda ya ce da ita, Dije ta ɗauko hannunshi ta ɗora a saman cikinta da ya fara turowa kaɗan, ya bita da kallon ƙarin ba'asi sannan ta kashe masa ido ɗaya ta ce "Nasan kana sonshi ko?" Ya maka mata wata harara, ta zunɓuro baki ta ce "Ni dai ka daina hararata amsa nake nema" Ya yi saurin faɗin "Yo idan ma ba don kina son kawo man reni ba ta ya zaki kalli tsabar idona ki tambayeni ina son abunda Ni da kaina sai da na zuba ƙarfi kafin in sameshi?, Kin fi kowa sani kaf duniya babu wanda zai fini son abunda ke cikinki ko da ko ke ɗin ce da zaki haifo man shi" Dije ta ƙumshe dariyarta ta ce "au abun har ya kai cen?" Yana dariya ya ce "ya ma wuce ai" tace "well yanzu idan na ce ka yi mani wata alfarma saboda son da kake masa zaka yi?" Cikin sauri ya ce ",Me zai hana in dai har hakan zai faranta ranki da unborn ɗina" Ta ce "to in ko haka ne bari in zube ƙasa in rok'i alfarmar don ina son ayi saurin amsa mani" Ta sauko ƙasa zata durƙusa ya riƙo hannunta tare da dawo da ita kan gadon ta zauna ya ce "Faɗi buƙatarki kawai ba sai kin cutar man da abun ciki ba" Dije ta yi dariya cike da jin daɗi sannan ta riƙo hannunshi ta matse gam ido cikin ido ta ce "Daga Ni har babynka Muna so ka dawo muna da Aunty Zee ko don mu sami abokiyar shawara tunda har an ce ta yi nadamar abunda ta aikata" Cike da ƙunar zuciya ya ƙwace hannunshi tare da miƙewa tsaye ya kalleta ranshi a ɓace ya ce "Wannan rana da wannan lokaci su zamo na ƙarshe da zaki sake tunkarata da wannan zance" Yana ƙare faɗar hakan ya fice ɗakin fuuu ya barta zaune sake da baki, zuciyarta cike da tabbacin abunda Inna ta nusar da ita wanda ita ta kasa gano hakan sai yanzu da ta tabbatar da hangen nesan Innarta, cikin tsananin farin ciki tace "ALLAH ya ƙara maki tsawon rai innata" To Ameen Dijen Safwan tare da namu Innonin duka kuma ya ƙaro masu lafiya mai ɗorewa Amee🤲🏻. Akafta🥰 D/AUTA Ce✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *Don Allah masu neman book ɗin Ƙarangiya daga farko ku yi haƙuri idan an kammala za ku sameshi a complete ɗinshi, plss ku yi haƙuri kunji😢saboda anyi nisa sosai kuma bana son kuna tambaya baku samu ba😆* *Lamba 69* Duk da take cikin farin ciki haka ta fito ɗakin haɗe da fuska ta zo ta zauna tana shan ƙamshi tare da mayar da hankalinta ga kallon tv'n da ke ta aiki shi kaɗai, don shi kwance yake tare da rufe fuskarshi da hannu alamun yana cikin damuwa a zahiri, jin motsin shigowarta yasa ya buɗe ido yana kallonta, ganin yanayinta kuma ta ƙi kulashi yasa ya ji ba daɗi, ya miƙe zaune yana kallon yanda ta haɗe fuska tamau ba alamun wasa, cikin danne dariya ya taso ya zo gabanta ya yi tsugunno tare da riƙo hannunta yace "Wai ke wace irin mace ce ke? Ni dai nasan kowace mace tana kishin mijinta amman ke har ingizashi kike yi akan ya yo maki kishiya" Dije ta zare hannunta a hankali zata miƙe tsaye ya yi saurin dafeta ya ta shi ya zauna kan kujerar ya rungumota jikinshi ya ce "Ki ji tsoron Allah kar ki jefa Mijinki a damuwa saboda macen da bata san muhimmancin kanta ba ma bale tasan na wani, kina kallo gaban idonki ta so kashemu da ma bata sami sa'a ba wuƙa ta ɗauko da nufin ta soka man, yanzu irin wannan matar kike so in sake dawo da ita cikinmu?" Dije ta riƙo hannunshi ta ce "ba laifi bane don an yi maka laifi ka yafewa wanda ya cutar da kai, don ALLAH da kanshi haƙuri yake yi da mu da halayenmu saboda darajar fiyayyen halitta Annabinmu Muhammadu s.a.w da muke cin albarkacin shi, kuma a shirye yake da ya yafe muna a duk lokacin da mu ka yi tuba zuwa gareshi, tunda haka ne mu me zai hana mu yafe mata akan abunda ta aikata muna a baya?, Don ALLAH ka yafe don ni tuni na yafe mata ka sake bata wata dama matuƙar ka tabbatar da ingancin nadamar da ta yi " Safwan ya sauke ajiyar zuciya yace "zan dawo da ita kamar yanda kika nema in har na tabbatar da gaske ta yi nadamar, amman da sharaɗin bata zo nan Abujar ba sai dai idan har ta amince zata zauna Yola, don bazan haɗaku waje ɗaya ba ta je ta koya maki mugun hali" Dije ta ji wani sanyin daɗi ya ratsa zuciyarta cike da tsantsar farin ciki tace " ina sonka Mijina ALLAH ya baka ikon yin adalci a tsakaninmu" Ya lakuce mata hanci "Ya ce Ameen Matata ke ma ina sonki son da Ni kaina ban san iya adadinshi ba, na godewa ALLAH da ya azurtani da samun mace irinki, wadda take da wankakkiyar zuciya mai sowa wata abunda ta sowa kanta, don ba kowa ce mace zata iya yin abunda kika yi ba, ALLAH Ubangiji ya yi maki albarka ya kuma saukeki man ke lafiya tare da Babyna" Cike da jin daɗi take ta faɗin "Ameen Ameen Habibyna, tom kirata yanzu ka sanar da ita ta dawo ka yafe mata" Ya maka mata wata uwar harara ya ce "su kenan ba sai an tantance ba? Ai WALLAHI sai na tabbatar da lalle ta gyaru sannan in ce ta dawo, don bazan taɓa yarda in siyowa kaina rariyar da zata yi man asarar ruwa ba" Dije ta ƙyalƙyale da dariya ta ce "uhummm har na tuna lokacin da ake yi man kashedi akanta, daɗin abun da dai komi yake wucewa don yanzu ga shi kai da kanka ka bayyana mata matsayina bayan ka gama yi mata ɓoyo, ai WALLAHI kai ma da naka laifi Malamina don da tun farko ka sanar da ita da abun bai yi tsananin irin wannan ba, don da ace ta kashemu da shikenan mun tafi bamu bar masu yi muna addu'a ba" Ya sosa kanshi cike da jin nauyin maganar tata ya ce "Ni dai bana son tone tone idan abu ya wuce a dinga barinshi a matsayin ya wuce, ki ta so mu je dai ki ji wata magana dare ya fara tsalawa" Ta bishi da wani kallo tana ƙumshe dariyarta tace "Ni yau anan ma zan yi baccina na gaji da kwanciya akan gadon nan" Ba shiri ya waigo ya ce "Ashe ko da ke ce zaki wahala don WALLAhi in Banda tausayin abun cikina da kinsha mamakina, amman tunda hakan kike so bari in zo daga baya na baiwa abun cikina haƙuri" Sanin halinshi yasa ta yi saurin tashi tana dariya ta ce "mu je Ni dai yasin idan na koma haifuwa garinmu sai na yi kusan shekara ban dawo ba" Ya riƙo hannunta yana dariya ya ce "ki ce kawai in rubuta takardar barin aiki don kin san ƙafata ƙafarki kuma idan sun gaji da halina sai su korani in koma Yola dolena" Ta yi masa wani mintsina a gefen ciki tana dariya ta yi ɗakinta da sauri tana faɗin "banji bakinka ba WALLAhi, Ni da nake shirin zama student kake so ka yi man ciki baƙi?" Ya bita yana dariya ya ce " to Alhudahuda ai dai kya bari ki haife man abun cikina ko?" Haka suka dinga wasarsu cikin raha har suka kwanta bacci bayan sun gama farantawa juna cikin tsantsar ƙaunar juna. **** Ruma kam jikinta yana rawa tun da sassafe ta je ta sanarwa Zee abunda ya faru bayan barinta wurinta, cikin sanyin jiki da zubowar hawayen tausayin kanta ta karɓi wayar ta sake kiranshi, sai dai ta yi rashin sa'a wayarshi a kashe lokacin suna gudanar da wani meeting, ganin ta ƙi samunshi ne yasa ta rubuta masa saƙo ta tura masa kamar haka _Aslm_ _Plss my Man Ni ce Zee don girman ALLAH ka yafe mani abunda na yi maka WALLAhi na yi nadama kuma na yi godiya ga Allah da ban ci nasarar abunda na so aikatawa ba, don yanzu haka Daddyna yana kwance har yanzu bai koma dai dai ba, kuma Mummy ta tsaneni ko kusa da ita bata bari inje, gani gidan ƙasar Daddy sai azabtar da ni take yi da ayyuka kala kala don ALLAH ka taimaki rayuwata ka ce in dawo ɗakina, WALLAhi na yi alƙawarin ba zan sake_ yin abunda bai da ce ba, plss ka yafe mani mu cuddle bear wallahi sonka ne ya rufe mani ido ya janyo na so aikata duk abunda ka gani, don ALLAH ka ce ka yafe mani in dawo don ALLAH my Bobbie. Tana kuka take rubuta text ɗin bayan ta tura kuma ta sake bi da kira amman kuma bata shiga ba, saboda bai buɗe wayarshi ba har sai ya dawo gida ne bayan ya gama komi sannan ya buɗe, aiko buɗewar ke da wuya sai ga saƙon Zee ya danno kai, ba ɓata lokaci ya duba duk da ya tausaya mata amman hakan bai sa ya mayar mata da amsa ko ɗaya ba, asali ma goge text ɗin ya yi gaba ɗaya a wayar, sannan ya mayar da hankalinshi akan sauran saƙonnin da suke ta shigowa. Zee ta gaji da jira ta sake gwada kiran sai ko ta yi dace ta shiga cike da tsananin jin daɗi ta yi wani ihu saboda murna, yana ɗauka ta daburce tana ta kame kame ganin bata da abun faɗa ne ya sa ya katse kiran, cikin sauri ta sake binshi da wani kiran har sai da ta tsinke bai ɗauka ba, bata gaji ba ta sake kira ganin zata dameshi ne yasa ya ɗauka, cikin rikicewa ta fara rawar murya tana faɗin "Don Allah ka yi haƙuri ka yafe mani my Bonnie plss" Cikin ko in kula ya ce "Ni fa yanzu matata ta isheni bana fatar haɗata da kowace mace a matsayin kishiya ballantana mai som ta kashe mu Ni da ita, don haka ki ƙara haƙuri sai na yi shawara in ta amince tukunna" Yana kare faɗar maganar ya kashe wayar, Zee ta fashe da kuka cikin tsananin takaicin kanta da har ta yi abunda ya janyo mata faɗuwar daraja warwas, don daman cen ya lafiyar kura ballantana yanzu ta ci sarauta?, Dole sai haƙuri cikin kukan ta sake kiranshi caraf ya ɗauka cike da Muryar kuka ta ce "Ko a ƴar aikinta ka ce in zo Zan zo idan har zaka yafe man abunda na yi maka" Safwan ya ɓata fuska kamar yana ganinta ya ce "kina da labarin ina Abuja yanzu ko?" Ta ce "a'a bani da labari" ya ce "Ok tom yanzu haka ina Abuja Ni da Matata nasami aiki ne a cen, idan kin shiryawa zaman Yola to ki tattaro kayanki ki koma, amman ki sani weekend kawai zai dawo da ni Yola idan kin amince shikenan fine, idan kuma kin ji ba zaji iyawa ba Tom sai mu sahalewa juna" Cike da jin daɗi bakinta yana rawa ta ce "Na amince My Man amman don ALLAH ka ce ka yafe man, itama ka nemar mani tafiyarta kafin ku haɗu" To kawai ya ce ya kashe wayar, Zee ta yo sororo da waya a hannu tana kallon Ruma ta ce "Ya ce in koma amman har yanzu bai ce ya yafe mani ba" Ruma cike da tausayinta ta ce "kada ki damu a hankali yafiyar zata biyo baya in har ya fahimci kin canza ba Zee ɗin da ya sani ba ce a cen baya, fatana kawai ki san yanda zaki taushi zuciyarki saboda tsoron aikata abinda za'a azo ana da ansani daga baya" Zee ta share hawayenta ta ce "Ai Ni tuni na gano cewa zafin nema baya kawo samu, don da banda ke da yanzu Ni kaina bana duniyar an riga da an kasheni, wanda ta sanadin haka ina da tabbacin Daddyna ma zai mutu itama kanta Mummy zata shiga muwuyacin hali, saboda gorin mutane ƙarshe itama ta bimu, Nagode sosai Ƙawata lalle ke ƙawar amana ce ALLAH ya bar zumunci kuma ya baki miji nagari ke ma ki je ki yi aurenki ki huta" Ruma ta ce "Ameen" Tare suka je suka samarwa Baabaah Asaben abunda ke faruwa cike da jin daɗi ta nufi gidamsu Zee ta sanarwa Mahaifin Zee saboda murna sai gashi da tashi zaune ba shiri zuciyarshi cike da jin daɗin jin wannan abun farin ciki, Mahaifiyarta ma ba ƙaramin daɗi ta ji ba da jin maganar, shiyasa ta nemi alfarmar ganinta ba ɓata lokaci Baabaah Asaben ta kira wani yaronta ta ce ya ɗauko Zee ya kawota. Satinta ɗaya gidansu Mahaifiyarta tana nusar da ita tare da nasihohi kala kala da misalan abubuwa da yawa wadañda suka faru a duniya masu daɗi da akasinsu, sannan aka fara gyarata na tsawon kwana uku sannan Mahaifinta ya yi mata huɗuba sosai da kanshi ya ɗauketa ya kaita gidansu Safwan wurin Hajiya Mama ya bada haƙuri sosai sannan ya ɗauketa ya kaita gidan Safwan da hannunshi tare da yi masu addu'ar zaman lafiya. Satinta biyu a gidanshi ba tare da ya waiwayota ba, har sai da Hajiya Mama ta nuna masa rashin kyautawarshi sannan ya baro Abuja ya nufo Yola ranshi ba daɗi, don in ta shi ake bi abarshi da Dijenshi ta isheshi rayuwa a duniya. Ko da ya shigo garin sai da ya je wajen Hajiyarshi suka gaisa ya bata tsarabarsu sannan ya ɗan taɓa fira da fiddo da Surayya da aka dawo da ita haifuwa saboda Mijinta da baya nan, bayan sun gama tambayar juna bayan rabuwa ne ya miƙe zai tafi Hajiyarmu ta ce "Ka kula da matarka don na hango shiriya a idanuwanta, kuma ka yi haƙuri da ni don nasan ba da son ranka ba biyayya ce kawai kake yi man, to ka sani duk lokacin da wani ya sami shiriya ta sanadinka ba ƙaramar lada zaka samu a wurin Ubangiji ba, shiyasa duk da nasan ta aikata mummunan laifi amman hakan bai sa na barka ka yi abunda ka so ba, don ina jin tsoron ka sake auro wadda zata aikata abinda yafi wanda ya yi muni, don gara ita da kishinta yake a fili yake kowa zai gani, saɓanin wasu da suke ɓoyewa a fili su nuna ba komi kuma su bi ta ƙarƙashin ƙasa su wargazaka daga kai har matar taka, to ko a hakan ma ka godewa ALLAH da baiwar da ya yi maka tunda bai haɗaka da mace mashurika ba mai biyar bokaye, wadda ba matarka ba har Ni da na haifeka da ƴan'uwanka duka zata iya rabaka gaba ɗaya" Cikin sanyin jiki ya ce "Na gode Hajiyarmu ai nasan daman ke baki ɗora wani ma a hanyar da bata dace ba bale ɗanki da kika haifa, Ubangiji ya ƙara bar muna ke ya karo lafiya da nisan kwana Hajiyarmu, na gode sosai kinga na manta da tsarabar da ɗiyarki ta bada in kawo maki" Ya kalli fiddo ya ce "ke zo mu je ki karɓo na tafi Hajiyarmu sai na dawo" Fiddo ta biyoshi zuciyarta cike shakkun abinda zata faɗa cen dai ta danne ta ce "big bros yaushe zaka je da Ni Abuja wurin Khadija?" Ya waigo Yana yi mata wani kallo ya ce "Ba ma maraba da gulma idan har itace zata kaiki don nasan Zee ce taki don haka ki tattara kayanki ki je ki tayata zama idan na koma, ko ko karatu na ki ya zaki yi da shi idan kin je cen?" Ranta a ɓace ta ce "Ni dai yayanmu cen nike son zuwa don ALLAH ka je da Ni in zaka koma yanzu, sai ka sakani makarantar a cen don nafi son inyi karatuna a cen" Ya miƙo mata ledar saƙon da Dijen ta aikowa Hajiyar yana faɗin "lalle baki da hankali kina year 2 ki nemi barin makaranta saboda daɗin da ya yi maki yawa ko? To ki jira idan kin fara aiki sai ki koma cen da karatun kina biyawa kanki, Ni matsa ki bani gu tun ban hanɓarar da ke ba" Fiddo ta yi cikin gidan tana gunguni don ita zaman garin ne ya gundureta, saboda in suna chatt da Husnah tana turo mata pictures ɗinsu in suna shaguna ko wuraren shaƙatawar da suke yawan zuwa, abun yana burgeta sosai shiyasa tasawa ranta itama zata koma cen a fantama da ita, amman dai ga shi ya gwasaleta a tashin farko. Ya fisgi Motarshi ya nufi gidanshi, haka kawai yake jin baya son shiga gidan don ya daɗe zaune a parking space yana firarshi da ma'aikatan gidan, don ko jakarshi tuni aka shige da ita ciki sannan ya fito ya nufi sashen Zee ɗin zuciyarshi a cunkushe, sai dai yanayin da ga Zee ɗin yasa ya yi saurin sakin fuskarshi saboda ba ƙaramin bugawa zuciyarshi ta yi ba, ganin yanda ta yi baƙi ta rame sosai amman a hakan har da fara'a kwance a fuskarta da ta rame sosai tana yi masa sannu da zuwa. Ya zauna tare da bin falon da kallo kamar mai neman wani abu sannan ya dawo da kallonshi gareta ya ce "Ke fa? me ya sameki kika rame irin haka??" Ta duƙe hawaye suna zuba ta fara wasa da yan yatsunta, cike da tausayinta ya ce "Zo zo inji me ke faruwa ne?" Zee ta durƙushe ƙasa tare da riƙo ƙafafuwanshi tana wani irin kuka take faɗin "Plss ka yafe mani don ALLAH nasan ban yiwa kaina adalci ba, don ALLAH ka ce ka yafe mani ko da zuciyata zata yi sanyi" Safwan ya ɗagota ya zaunar da ita kan kujerar da yake yana share mata hawayen ya ce "komi ya wuce ki daina wannan kukan yanzu ba gamu tare ba?" Zee ta sake fashewa da kuka tana faɗin "na cutar da kaina da hannuna don ALLAH ka yi haƙuri" Dole Safwan ya ajiye komi ya fara lallashinta, sannan ta kaishi ya yi wanka ta rakoshi diny inda ta shirya masa abinci mai kyau, yana ci yana janta da fira saboda ganin har lokacin bata daina hawaye ba. Cikin dauriya ya bata kulawa ba yabo ba fallasa haka suka kwana kowa da tunanin da ke cike cikin zuciyoyinsu, ita tana ganin kamar yana riƙe da ita shi kuma yana tunanin irin lalacewar da ta yi. To mu dai sai dai muyi maku fatar ALLAH ya bada zaman lafiya da hkr😝 Akafta😊 D/AUTA Ce✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *Aski ya zo gaban gashi Mutanena💃🏻* *Lamba 70 * Haka dai suka kwana ba natsuwar zuciyoyi, bayan SALLAHr Asuba Safwan ko da ya dawo masallaci ya taradda Zee tana ta karatun Qur'ani, abun ya buregeshi kuma haka ya ba shi mamaki sosai, saboda sanin da ya yi mata ada da ƙyar ma take tashi yin SALLAHr a lokacin, sannan idan ma ya matsa mata ta yi tana kammalawa take yin kwanciyarta ko addu'ar kirki bata tsayawa yi, amman yanzu ita ce har da su karatun Qur'ani, cike da jin daɗin sauyin da aka samu ne ya zauna kan gadon yana ƙarasa addu'o'inshi na azkar, har bacci ya fara janshi ya kwanta ba shiri saboda baccin da ya fiegeshi ba tare da ya shiryawa hakan ba. Misalin ƙarfe takwas ya falka saboda ƙamshij abun break ɗin da take haɗa masu, mamaki ya sake kamashi ya fito ɗakin ya nufi kitchen yana kallon yanda take ta hadadarta, cikin shigar wata doguwar riga ƴar kanti, tana ganinshi ta diririce tana gayar da shi cikin ladabi, bayan ya amsa ne zuciyarshi cike da jin daɗin sauyin da ta samu, ya fice kitchen ɗin zuwa sashenshi saboda zuciyarshi da ke ta kwaɗayin son jin muryar Uwargidanshi, don tun yana kan hanyar shigowa garin da suka yi waya ta ji ya sauka lafiya ta kashe wayarta, saboda kishin da ke cin zuciyarta game da zuwanshi wurin Zee, da abun ya kwana a ranshi saboda ya yi ta kiran wayoyinta a kashe ta Husnah ma a kashe, cikin takaici ya kira Aunty Ummi ya ce ta haɗashi da ɗaya daga cikinsu yana son yin magana da Dijenshi, Aunty Ummi ta nuna masa dare ya yi sosai ya dai haƙura sai da safe, saboda a lokacin ƙarfe sha biyu da mintuna dole ba don ya so ba ya haƙura amman zuciyarshi cike fal da son jin dalilin da Dijen ta aikata hakan. Shiyasa ko da ya shiga sashenshi ko wanka bai yi ba ya fara nemanta a waya, aka yi da ce ta shiga itama caraf ta ɗaga sai dai shirun da ya ji ta yi masa ne yasa shi saurin faɗin "Me na yi maki kika horani da rashin jin muryarki?" Sheshshekar kukan da ya ji ne a kunnenshi yasa ya yi saurin sake wata maganar a rikice ya ce "Subhanllah me ke faruwa ne? Me aka yi maki? Wa ya taɓa man ke don ya ga bana nan?" Dije ta sake fashewa da kukan gaba ɗaya cike da ruɗewa ya ce "Plss babyluv don ALLAH ki daina kukan nan ki sanar da ni abunda ya faru idan har kina son ganin natsuwata" Cikin kukan Dije ta ce "Ka gaisheta" Tana ƙare faɗar hakan ta datse kiran, cikin wani sabon tashin hankali ya sake bi da wani kiran amman har ta tsinke bata ɗauka ba, ganin hakan ya sa ya dinga kiran Husnah kira bayan kira, tana bacci dole ta miƙe ta ɗauka ya ce da ita ta kaiwa Dijen, ta miƙe cike da jin haushin katse mata bacci da aka yi, sai dai kukan da ta tarar tana yi ne yasa jikinta ya yi sanyi, ta miƙa mata wayar ta fito zuciyarta cike da jin zafin kukan da ta ga Auntynta tana yi, don tun jiya take lallashinta akan ta yi haƙuri ta daina kukan da ta ke yi na rashin Auncle ɗinsu, ta yi kamar ta haƙura ashe bata haƙura da kukan ba. Dije ta kara wayar a kunne tana share hawayenta ta ce "Ba wani abu fa kaina ne yake ciyo" Daga cen ɓangaren ya sauke ajiyar zuciya yace, "haba haba My luv to meyasa ba zaki sanar da ni ba kike wahalar man da kanki da Babyna? Yanzu ki shirya Aunty Ummi zata zo ta kaiki Asibiti sannu kin ji? ALLAH ya baki lafiya" Ta ce "Ameen" cen cikin maƙoshi sannan ya sake cewa "ya kwananki da na Babyna?" Ta ce "ƙalau" Cike da mamakin yanda take ta ba shi amsa a taƙaice ya ce "Babyluv ko na yi maki wani abun ne ban sani ba?" Ta ce "A'a" yace 'to wacece kike cewa da ni in gayar?" Ta murguɗa baki kamar yana gabanta ta ce "wadda ka je wajenta ko ba'a buƙatar gaisuwar tawa ne?" Ba shiri ya rufe bakinshi saboda fahimtar inda ta dosa, cikin dariyar da ta so kufce masa ne ya ce "Ana buƙata kuma an karɓa hannu bibbiyu ALLAH ya saka da aljannah, amman fushin na minene? ko kin manta Umurninki na bi? To yanzu kuma tunda an yi maki abunda kike buƙata kuma ta dawo kamar yanda kika roƙar mata alfarma Ni kuma mi ye laifina a ciki?" Ta ce "ba ko ɗaya hasali ma ka yi abunda ya dace" zai sake yin magana ne Zee ta turo ƙofar ɗakin ta shigo da nufin sanar da shi komi ya yi ready, ganin yana waya ya sa ta yi saurin juyawa da nufin komawa, ya yi gyaran murya ta waigo ya yafitota ta ƙaraso wurinshi, ya miƙa mata wayar cikin jarumta ya ce "kHadija ce ku gaisa" ZEE ta karɓi wayar cikin sanyin jiki tana shirin yin magana ta ji Dijen tana faɗin "Dawo da itan ai abu ne wanda ya dace, kuma kai kanka zaka gano alfanun yafiya ga wanda ya yi maka laifi, saboda ladarka tana wurin Allah Kuma insha ALLAHu za ka ga sakamakon abun alkhairin da ka yi, fatana kawai ALLAH ya baka ikon yi muna adalci, kada don an sami ta ƙarfen a juyawa ƴar ƙauye baya" Zee ta yi saurin faɗin "Insha ALLAHu in dai ta ɓangarena ne matsala ta ƙare, da ni da ke yanzu mun zama abu ɗaya babu wani gorin asali ko wani fifiko, a zahirance ma kin sha gabana don kin riga da kin yi man fintinkau tunda har kike da zuciyar imani, kika ɗora Mijinki akan hanyar dawo da ni cikinku duk da abunda na aikata maku a baya, don ALLAH ki yafe mani kinji insha ALLAHu zan yi ko yi da kyakkyawar zuciya irin taki, saboda yanzu na gano cewa ko wane mutum da kalar baiwar da Allah ya yi masa, sau da yawa wanda ka ke renawa sai ya zo ya fi ka ta hanyoyin da kai ko da kuɗi ba zaka iya binsu ba, matuƙar sheɗan yana buga ganganunshi saman kanka, na gode sosai da taimakon da kika yi mani aka dawo da ni, kuma ki sa a ranki cewa kina da ƴar'uwa saboda yanzu Zee ta ɗaukeki tamkar ƴar'uwarta ta ciki ɗaya tunda har na gano ke ɗin alkhairi ce garemu ni da shi" Tana ƙare faɗar maganar ta miƙa masa wayar ta fice da sauri tana kuka, ya bita da kallo sannan ya sauke ajiyar zuciya yace "Babyluv sannu da namijin ƙoƙarinki, lalle ke alkhairi ce ga rayuwata, ina ta ya ƴaƴana farin cikin samun uwa ta gari irinki, fatana kawai a yanzu ALLAH ya sauke man ke lafiya ki bani Babyna a hannu in ɗauka" Dije ta goge ƙwallarta ta saita natsuwarta ta ce "Insha ALLAHu ƴaƴa har sai ka ce in tsaya haka nan in huta , don in na Fara watso maku su sai ka rasa da hannun da zaka riƙe sauran" Safwan ya fashe da dariya cikin dariyar ya ce "au watsosu ma zaki yi don salon mugunta?, To bari ki ji ko da jefosu zaki yi ta yi duk bayan minti biyar Habibynki ba zai taɓa rasa hannun da zai karɓesu ba, ke dai kawai ki natsu ki sako man su sannu a hankali ina karɓewa cikin farin ciki ba tare da gajiyawa ba ko ƙosawa" Haka suka yi ta firarsu mai cike da barkwanci da raha har dukansu suka daina jin damuwar rashin ganin juna, sannan Dije ta daƙile firar dolenta don bata son ta shiga haƙƙin Zee, ba don ya so ba suka yi sallama cikin kewar juna tare da kwaɗayin ganin junansu, saboda mugun sabon da suka yi wa juna da kawunansu. Har ga ALLAH Safwan ya ji daɗin yanda Zee ta dawo macen kirki, shiyasa cikin dauriya da kai zuciya nesa ya mu'amalanceta har lokacin barin garin ya yi ya tattara kayanshi ya koma Abuja, wurin Matarshi da ya ke jin a duniya kaf ba ya da matar da zata kamo ƙafarta ma bale ta kamota, ko da ko akwai ɗiyan lu'ulu'u da murjani a cikin. **** Haka rayuwa ta yi ta shurawa sannu a hankali har cikin Surayya ya isa haifuwa ta haifo ƴarta mace masha ALLAH da ita. Cikin zumuɗi Dijen ta yi ta murnar zuwa Yolar sai dai idan ta tuna da zata ga Zee sai jikinta ya yi sanyi, dole dai haka ta daure ta matsa masa ya barta ta biyo su Aunty Ummi suka nufo Yola, saboda a lokacin shi ana tsaka da aiki don during working hours ne, cike da jin daɗin yarinyar Dije ta fara santi tamkar ta sace yarinyar take ji saboda sonta da take yi, Hajiya Mama da su Surayya sai dariya suke yi mata ganin yanda ta maƙake yarinyar bata son kowa ya ɗauketa, don har goyeta take yi sai Hajiya ta yi faɗa take sauketa, Zee ma kullum tana zuwa da ita ake komi shiyasa Dijen ta rage kishinta da take ji aranta, saboda ganin yanda ta ke ta haba haba da ita tamkar cewa babu abunda ya taɓa shiga a tsakaninsu, haka ma da yanda take ta janta a jiki tana nuna mata cewa ai an zama ɗaya babu zancen wata kishiya shiyasa itama ta ajiye komi suka fara ɗasawa, wanda hakan ba ƙaramin daɗi ya yi wa Hajiya Mama ba, ta ƙara godewa ALLAH da har ta jajirce Safwan ya dawo da aurenta, don tasan dole ne sai ya nemi wani auren tunda har ya saba da mace biyun, kuma da wacce ba'a san halinta ba gwara wadda daman cen an san halinta sai a ci maganin matsalar. Aka yi taron suna lafiya cike da ƙayatarwa yarinya ta ci sunan uwar Mijin Surry ana yi mata laƙabi da ilham, bayan suna Safwan ɗin ya zo ya yi kwana biyu sannan ya kwashi Matarshi suka koma Abuja. kawosu ita da Sannu a hankali itama Dijen cikinta yana ta miƙawa har ya kai watannin haifuwa, Hajiya Mama ta matsa masa akan dole ya dawo da ita wurinta ta haifu, amman ya nuna shi dai ya fi son idan ta haifu sai su dawo yolar, saboda cen ɗin tana samun kulawar manyan likitoci a Asibitin da take awo, sai da Hajiya Mama ta yi masa jan ido sannan ya kwasota da himilin uwar siyayarta da ta jaririn da za'a haifo masa, don daman cen shi rabuwa da ita ne ba ya so saboda ko da take da titsetsen cikinta idan jarabarshi ta motsa tasan ta yanda zata faranta masa har ta gamsar da Habibynta. Shi yasa ko da suka zo Yolar ya kasa ya tsare gidan Hajiya Mamar ya ƙi barin garin har sai da korashi saboda yanda ake ta nemanshi a ma'aikatar ta su, saboda muhimmancin da yake da shi dole ne wani abun sai da shi. Satinta ɗaya a Yola ta fara jin sign na naƙuda, Hajiya Mama tana bata kula sosai da sosai don itama ɗin har nurse's ta samo mata masu duba mata ita har gida ba sai anje Asibiti ba, Zee kanta kullum tana gidan ana renon cikin da dakon zuwan haifuwar, sai ko ga shi cikin ikon ALLAH wata ranar juma'a Asubar farin ta fara naƙuda, jikin Hajiya Mama yana rawa ta saka direba ya kwasheta da kayan da duk za'a buƙata suka nufi wata babbar Asibin da ke garin yolar, cikin nasara kwata kwata bata yi minti goma da shigarta labour room ba ta haifo santalelen yaronta Mai kama da Ubanshi sak, fari jajir har wani yalo yalo yake yi saboda tsabar farinshi, ga shi ƙatoto da shi masha ALLAH tamkar ba haifuwar Dijen Baffah ba. Farin ciki wajensu Hajiya Mama da fiddo da ma Zee ɗin abun ba'a magana, saboda har rige rigen ɗauka ake yi tsakaninsu su biyu, Surayya ma rufe ido ta yi tace tunda da ita yaron yake kama itace zata riƙeshi, Hajiya Mama dai sai dariya take yi masu idonta akan ɗakin da Dijen take tana ta baccin sauke gajiyar naƙudar da ta sha. Ango ƙarni kam daman yana kan hanyar zuwa Yolar sai ga kiran Fiddo ya shigo wayarshi cikin kuwwa da ihun murna take sanar da shi an samu Baby boy, ba shiri shi ma ya buga wata ƙatuwar kabbara ya ce "ALLAHU Akbar? Alhmdllh! Shikenan na zama Baba, Little sis kina da tukuici mai tsoka a wurina, to ya ita Mamar boy ɗin lafiyarta ƙalau dai ko?" Cikin murnar albishir ɗin da ya yi mata na tukuici ta ce "fine take big bros bacci ma ta ke yi yanzu haka" Baki a washe ya ce "Ok Ina Kan hanya daman ganin na kusa ƙarasowa garin ki shafa man kan babyna" Cike da jin daɗi fiddo ta koma ɗakin tana dariya ta ce "Wayyo daɗi Ni ce na yiwa yayanmu albishir ya ce in tsumayi tukuicina" Surayya da ke ta faman murnar ta sameshi a wayar da nufin ta riga kowa sanar da shi ba shiri ta kashe wayar tana harararta ta ce "Ai WALLAHI kin ƙware da mugunta yanzu don salon yaudara shine kika fice waje kika rigani to ai dole mu raba koma minene" Zee sai dariya take masu Hajiya Mama ta kira cen garinsu Dijen ta sanarwa da su Baffah, sannan ta dinga kiran mutane yan'uwa da abokan arziƙi tana ta sanarwar haifuwar, kafin ka ce me Asibitin ta cika da yan taya murna kowa baki har kunne. Angon ƙarni ma ko da ya zo ya taradda mutane ciccike sai tayashi murna ake yi, sai washe baki yake yi amman idonshi suna cen wajen dubo ta ina zai hango kyautar da ALLAH ya yi masa?, Aiko sai ga shi ya hango babyn hannu wata dattijuwa tana tofeshi da addu'o'i. Cikin sauri ya nufeta ba kunya ya saka hannu ya karɓe yaron tamkar ya yi ihu saboda daɗin ganin yaron a hannunshi, ba tare da tuna da inda yake ba ya kaiwa yaron kiss a goshi da baki, sannan ya hankalta da mutane bakinshi ya ki rufuwa saboda dariyar kanshi da jin daɗin ganin ɗan shi,sannan ya miƙa yaron yana tambayar Hajiya Mama Dijen ta yi masa nuni da ɗakin da take hutawar, ya nufi ɗakin zuciyarshi fess da farin cikin hangota kwance har a lokacin tana ta baccinta, ya tsaya jikin gadon ya shafo kanta tare da duƙowa ya yi mata kiss sannan ya riƙo hannunta, cikin sauri ta buɗe idonta ta saukesu a kanshi ba shiri ta washe baki da murmushi akan fuskarta ta ce "Habiby" Ya riƙe hannunta duka biyu ya ce "sannu da ƙoƙari kin ji? ALLAH ya biyaki da gidan Aljannah, naga yarona Masha ALLAH har ya fiki kyau" Ta ɓata fuska tare da turo baki ta ce "Saura ƙiris in fara kishi da shi yasin" Yana dariya mai cewa cike da zallar ƙaunarta tare da shauƙin sonta da ke ɗibarshi, ya duƙa ya tsotso leɓenta sannan ya ce "I love You so much my heart desire, ke mahaɗina ce idan ina kusa da ke kina sakani susucewa, don haka kada ki janyo in yi abunda za'a ga na yi rashin kunya" Dije ta yi masa wani fari da ido ta rausayasu sannan ta ce "ina sonka Habiby" Cikin zurmawa da salonta ya ce "ina son matata kuma ina son kasancewa da abuta a kullum a koda yaushe kuma a kowane lokaci, amman yanzu sai na yi zaman jira kenan ko? Kwana nawa ne ma ake yi wai?" Dije ta rufe fuska cike da jin nauyin maganar ta ce "kwana dubu uku ne ake yi ai nasan Habibyna jarumin gaske ne zai iya yin fiye da kwanakin ma " Ya zaro ido waje baki buɗe ya ce "A wannan karon kam dole ne kowa sai ya gano ragwantakata, cabɗi ki ce in mutu kawai kafin zuwan lokacin" Dije zata yi magana wata Nurse ta shigo tana dariya musamman ganin yanda suke riƙe da hannun juna gam gam tace "To luv bird's zaku iya tafiya gida tunda har ta gama hutun, sai ku je cen ku ƙarasa soyayyar" Dukansu suka kalli juna suna dariya Safwan ya saka hannu aljihu ya fiddo kuɗi bai ma tsaya lissafi ba ya miƙa mata yana faɗin "To ga goro a tayamu da du'a'in dawwama cikin farantawa juna" Ta karɓe tana jin daɗi ta fice bayan ta gama zuba masu addu'o'in. Haka aka tattaro da maijego da jinjirinta da masu zuwa ta ya murna aka nufo gidan Safwan, saboda Hajiya Mama ta ce akai Dijen ɗakinta saboda danginta idan sun zo ta ji daɗin tarbarsu, kuma duk wanda bai san muhallinta ba ya gani, amman ta saka wasu dattijai masu kula da ita waɗanda za su yi mata komi kamar a gabanta, cike da jin daɗi Safwan ya fice bayan ya saukesu ya faɗa shaguna yanata lodo kaya har na hauka, bayan waɗanda suka sissiyo a Abuja sai da ya yiwa Dijenshi set biyu na jakunkuna masu samfurin akwati tsadaddu masu shegen kyau, kowace jaka maƙare da kaya na alfarma sannan ya yi wa boy na shi set guda shi ma tsadaddun kaya, Zee ma da nata set sannann ya yi wa su Hajiya Mama da su fiddo su ma, ya sa aka kwaso masa kayan suka nufi gidan Hajiya Mama ya zubesu gabanta, duk da ta ji daɗi amman ta yi masa faɗan almubazzaranci ba kyau, yana dariya ya ce "Duk abunda na yi maku Hajiya ai kun fi ƙarfinshi wajena, amman insha ALLAHU zan kiyaye a gaba, don ko wannan don naga khadija ko lefe ban yi mata a lokacin aurenmu ba" Ta sauke ajiyar zuciya ta ce To ALLAH ya rufa asiri ya ƙara buɗa maka kuma ya baka ikon sauke ɗawainiyar gidanka gaba ɗaya " Ya ce '"Ameen" Sannan ta ce idan duhun dare ya shigo ya zo ya kwashi kayanshi ya kaiwa Matanshi, sannan ta yi masa godiyar na su da ya siyo masu tare da saka masa albarka, da addu'ar kariya daga sharrin ko mi ƙankantarshi. Dije kam tana cen ita jaririnta sun sha wanka sai ƙamshi suke yi, Surayya ta haɗa mata tea mai shegen kauri ta shanye saboda saukowar ruwan nono da wuri, sannan dattijan suka baje wajen da aka keɓe don kawai irin wannan lokacin, anata hidimar dafe dafe da dama mata kunun jegon da Hajiya Mama tasa aka dako tun lokacin da aka yi haifuwar. Ko da ya dawo gidan ya taradda Zee da su Surayya ɗakin sunata firarsu suna shewar jin daɗi, Dije riƙe da kofin kunun tana sha a hankali saboda zafinshi, ya ƙaraso cikin ɗakin ya kalli Zee da ke goye da yaron ya ce "Naman boy Daman cen kin iya goyon ne?" Tana dariya ta juya kanta baya ta kallo yaron ta ce "Ka ga alama don kuwa ga yarona nan yanata baccinshi don shi ma yasan Uwa ba wasa ba ce" Gaba ɗaya suka fashe da dariya wajen dariya har Dijen ta ƙware da kunun da ta cika bakinta, sai ga shi da kaiwa wurinta ba shiri yana bubbuga bayanta yana hura mata kai tare da faɗin "Sannu baby sannu" Hankalinshi bai kwanta ba har sai da ya ga ta dawo normal sannan ya fara dungure mata kai ya ce ,. "Idan kin san ba zaki natsu ba to ki koma wani gu sai kin shanye kunun ki dawo don bana son wasa da lafiya" Dije ta yi masa wani kallo cikin marairece fuska sannan ta riƙe kunnenta ta ce "Am sorry habi....." Ta kallo Zee ta yi saurin datse cikon maganar, Zee tana dariya ta ce "biby" Surayya da fiddo suka fashe da dariya saboda yanayin da Zee ta yi maganar tana marairece fuska tana lanƙwashe wuya tare da murguɗa baki, sannan ta kalli su Surry ta ce "Ku zo mu basu waje tunda a gabanmu ma ba za'a yi muna kawaici ba" Su Surry Suka fice ɗakin suka barsu sunata kallon Zee cike da dariyar da ta suƙesu, Safwan ya kalli Dijen ya ce "To Ni yanzu ya zaku yi da ni? Babyna na zo gani na taradda an wani duƙunƙuneshi a baya, ƙarshe ma ga yanzu kin janyo an fice da shi bamu gaisai ba" Dije ta ɗauki kunun ta kurɓa sannan ta haɗiye ta ce "kun fi kusa ka je ka karɓo tunda baka godewa kulawar da yake samu ba" Ya kalleta da kyau ya ce "haka ma zaki faɗa?" Ta sake kurɓa kununta sai da ta cika bakinta sannan matso jikinshi ta janyoshi ta riƙo kanshi ta tallafo ido cikin ido ta goga hancinta da na shi sannan ta nufi bakinshi kamar wani sakarai ya buɗe bakin ta juye masa kunun sannan suka fara zuƙe kunun tare har suka shanye, sai ga shi sun buge da dulmiya cikin wata sabuwar duniya sun manta shaf da cewa ba su kaɗai suke ba har sai da suka ji kukan yaron sannan suka dawo hayyacinsu. Sai ga fiddo ta zo rungume da shi ta ce tsohuwa ɗaya daga cikin dattijan ta ce ta ba shi nononshi ya tsotsa, Dije ta zaro ido waje ta ce "To Ni ina nasan yanda zan bashi ??" Safwan ya karɓi yaron Fiddo ta fice ya sakarwa yaron kiss sannan ya kalleta ya ce "Oyo bari Abban boy ya koya maki riƙe man shi anan" Ta karɓa ta rungumeshi ya ɗaga rigarta ta ƙasa ya fito da nonuwan, cike da zallar maitarsu a fili ya shafosu duka ta yi saurin lumshe ido, sannan ya ɗago kan yaron ya saita bakinshi ga ɗaya aiko yaron ya fara tsotsa zumui zumui tsut! tsut! Ta cije baki tana faɗin "Da zafi Habiby kuma ma WALLAhi ba komi a ciki don ALLAH ka bari har ruwan ya zo a hakan zafi kawai zan sha" Yana ƙumshe dariyarshi ya cire nonon a bakin yaron ya karɓeshi ya ajiye sannan ya je ya rufo ƙofar ɗakin, ya dawo yana wata dariya ya yi durƙuso a gabanta ya sunkuya ya kai nonon a bakinshi ya fara tsotso cikin mugunta, ta fara tureshi amman hakan bai hanashi tsotse ɗaya tas ya saki ya kama ɗayan ba, sai da ya ɗauki lokaci yana zuƙo nonon sannan ya saki, Dije tana hawaye wahala ta ce "Shi dai mutum ya kamata yasan ya fara girma, a gaban yaro ko kunya baka ji ba kake wannan halin?" Yana dariya ya sake ɗauko yaron ya ajiye a gabanta ya saita bakinshi ya saka masa nonon, yaro ya ci gaba da tsotsa har da su sauke ajiyar zuciya, Dije ta bi shi da harara ta ce "Yasin zaka janyo in horashi tunda akanshi ne ake yi man mugunta" Yana dariya ya ce "wuta bal bal cin zalin yarona ko a bayana ne ku wa" Ta murguɗa masa baki tana cije leɓe saboda zafin da take ji yana ratsata, haka yaron kam ya sha iya son ranshi sannan ya koma bacci, Safwan ya karɓeshi ya kwantar da shi ya zauna suna firarsu mai cike da nasu salon son, har sai da suka ji ana ƙwanƙwsa ƙofar ne ya buɗe ya fice su Surry suka shigo suna yi mata tsiya. Ko da dare ya yi Safwan ya kawo masu kayansu Dukansu sunyi farin ciki ba kaɗan ba, musamman Dije da har sai da ta yi kukan daɗi saboda ganin himilin kaya kuma wai duk nata ita da yaronta, ba shiri ta rungumeshi tana kuka tana yi masa godiya. Mai jego muma dai kam mun tayaki murna😊 Akafta🤪 D/AUTA Ce✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *ALHAMDULILLAH!!!!* *Lamba 71* Dije da yaronta suna samun kulawa sosai tamkar a gaban iyayenta ko ma fi, don ta ɓangaren cima mai daɗi bata da wani aiki sai na cin daɗi, saboda har rago biyu ya sa aka yanke aka soye mata wani bayan an sarrafa sauran kala kala aka tasata gaba ta yi ta kwasar gararta, kwana biyar da haifuwarta ne ƴan'uwanta suka diro Yola ƙatuwar Bus cike da mutane har da masu zuwa ganin ƙwam, don kuwa izuwa lokacin Dije ta yi wata daraja da ƙima a idanuwan yan garin nasu, saboda mutumci da Safwan ya siya mata a wurinsu ba tare da ma ta sani ba, wanda ya janyo har su kansu Inna da Baffah yanzu sun zamo wasu mutane masu daraja a cikin garin na su ta sanadin hakan. Dije murna baki har kunne saboda jin daɗin ganin ƴan'uwanta da abokan arziki a cikin gidan aurenta, sai haba haba take yi da su cikin mutuntawa tare da girmama matsayinsu a wurinta, wuri na musamman aka keɓe masu ana ta basu kulawa ta ɓangaren abinci da abinsha sai sambarka suke ta yi da sa albarka, Dije kam farin cikin fal ranta bakinta ya ƙi rufuwa saboda ganin Abokanta na ƙurciya, waton Ladiyo Jummala da Lanti da Mune sai Hansai da ta zame mata tamkar ƴar uwa tuni, saboda auren Usmanu da ta ke yi sannan kuma ga shi tana kyautawawa Innarta shiyasa ta ke jinta ta daban a wurinta. Mutanen garinsu Dije kam sai mamakin ganin yanda ta koma ƴargayu suke yi, don tuni ta sade da su ba zaka taɓa ganinta ka gano cewa wai tashin ƙauye ba ce, ta burgesu sosai musamman yanda ta ke nuna masu kulawa babu ƙyama bale nuna wariyar launin fata, ganin haka ne su Surayya da Zee da ita kanta Fiddon suke ta Nam nan da su su ma. Tun ana gobe suna aka watsawa aka fara hidimar bikin don kuwa gidan cike yake fam da mutane ana ta hada hadar bikin, tsakanin soye soye da dafe dafe bayan wanda aka kai wani guri ayo ammsn duk da hakan mutane sai ɓarkowa suke yi. Ranar suna maijego da yaronta da ya ci sunan Mahaifin Safwan ana kiranshi da Sayyid shi ma kanshi ya sha gayu bayan an ɓata lokaci wajen tofeshi da addu'o'in kariya daga sharrin mutum da na aljan, don farinshi yasa ko wa ya ganshi dole ne ma sai ya maganta, musamman yan ƙauyensu Dijen da suke ganinshi tamkar ba Dijen ce ta haifoshi ba, saboda ganin yanda yake tamkar ɗan indiyawa saboda kyau da fari. Dije tare da su Surry da sauran mutane sai ɗaukar photuna ake yi cen na hango wata tawagar mutane ta doso Dijen ko da na duba da kyau na hango Shaharrun marubutan nan masu ji da kansu da amfani da lokacinsu wajen farantawa al'umma irinsu Hannah Suhana (Hajiya Duduwa)da Billy s fari Ayusher Muhammad, tare da Ummi Garkuwa, Nimcyluv, Maizafafa, Oum Mumtaz, Ummu Najma, Salaha Muhammad, sai Mmn Musaddiq, Firdausi mrs shugaba, Ameera Adam, Mmn Shaheed, Mmn Maleek, Autar manya, tare da Ummu Ja'afar. Ganin yanayin takunsu yasa ta gano su ɗin ba ƙananun mutane ne bay yasa ta sa aka tanadar masu wurin zama na musamman, sannan ta je rungume da Sayyid tana gaisawa da su ɗaya bayan ɗaya sannan kowacensu ta gabatar mata da kanta cikin raha da wayewar kai irinta Marubutan, sannan suka dinga ɗaukar photuna da ita tare da Baby, sai ga shi na hango ana rigimar karɓar Sayyid tsakanin ƙannena biyu Billy s fari da Hajiya Duduwa, ko wace ta na faɗin ita ce zata ɗauka sannan dai Ƙanwata Ummi Garkuwa ta raba gardamar wajen shiga tsakiyarsu ta riƙe yaron aka fara ɗaukar photuna. Tana cikin marubutan ne Fiddo ta zo tana haki ta ce ta zo ga wasu gungun mata cen su zo suna nemanta, Surry ta ce ta je ita zata ji da su aiko ta saki jiki ta dinga lodo masu abinci da abinsha da maƙulashe ko wace ta ci ta sha sannan ta cika mas ledodinsu na kayan bikin kala kala. Dije ta je ta sauyo wasu kayan cikin wani arnen tsadadden less wanda yaji shuwari stone ta ko'ina sai walwalniya suke yi, ta fito tana takun ƙamshi ta nufi inda ake nemanta, sai ko ga Maryam Omee ta yi saurin zuwa wurinta ta rungumeta tana faɗin "Oyoyo Dijeta Barka da arziƙi" Dije ta saki baki tana dariya tace "yawwa Barka dai Auntyna" duk da bata ganota ba amman ganin zallar ƙaunar da ta nuna mata yasa ta ji itama ta kwanta mata a rai, Omee ta waigo bayanta tana kallonsu Mmn irfaan da ke tsaye suna kallonsu ta ce "mun yo tattaki ne takanas daga group mabanbanta saboda kawai mu tayaki murnar zuwan wannan rana mai cike da farin ciki a garemu duka, saboda haka yanzu zan yi maki bayaninsu filla filla" Ta nuna Mmn irfaan da ke tsaye tana wara idon ta ina zata hango Zee ta ce "Wannan itace Mmn irfaan sai wannan Mmn ss, Ummu Afrah, Fati Ghana, Oum Suhail, Hauwa Zubair, Deejerlee, Mum Sayyid, Sa'ar Bukar, Faeexe, Najida Aliyu, Daughter Ummi Khatsina, Rufaida idris, Hamida Ƙaura, Jamila Haidara, Mmn Ra'ees, A'isha Yola, " gano hakan yasanMmn Heedaya, Zainab Garba, Aunty Sady,Rahina, Glam By hajia sumy,Ummu Rauda, A'isha kishoor, Amrah barrister, Mmn Beaty, Mum of 3full H, Ummu Muhammad, Aisha S yamm, Subai'a Hussaini Gwandu, Hannatu Umar, Saratu Nakura, Zee MD, Hannatu Ahmed, Ummu deedat, Firdausi Muhammad sani, Rukynamango, A'isha Muhammad, azrarrfa8, Fatima sani mmn Masoyi, Princess N, Nakura, Ummin Sadiq, Ummi Sajida, Mmn meenat, mmn Yusuf, Hannatu Garba, mmn inty&Anwar, Shafaatu Aminu, Halima Gwani, Mmn Moh'd, Tamasu, mmn basma, mmn Hafsa, mrs Kamal, Aisha mada, Ummu Aisha, Ummu Haidar, Fatima Bello maimaita, mmn Abdu, Nasmie mafara, i lv u mum,Mummyn Nasrin, Jamila Isa, Aunty Islam,mmn Husnah,Mummyn annur, mmn shuraim, Ummul adnan,Amina Abdullahi. Cikin sauke numfashin wahala Omee ta dafe goshi ta ce "wai ALLAH yasin muna da yawa in nace in ta zayyanosu zamu kwana anan bamu tantance ba,don haka don ALLAH ku yi haƙuri saura abun ne da yawa...." Tana cikin maganar ne maganar ta tsaya saboda hango Asiya Umar A ya yarda, da tayi ta shigo gidan cikin gayunta tana wara idon ta ina zata hango idon sani, Omee ta washe baki tare ta dafe goshi ta ce "Wayyo rimatyna ta ƙasaro" Dije ta yi dariya ta ce dasu gaba ɗaya tana yi masu sannu da zuwa sannan ta jasu suka yi ciki inda ta yi masu masauki a ƙaton falon nata, Dukansu suka shishigo kowace tana samun wurin zama inda wasu ma har ƙasa suka zube abunsu saboda yawa su yasa falon yana so ya yi masu kaɗan. Nan fa aka shiga yi masu tarba ta musamman, don su yawansu bai hana kowacensu ta yi ƙat ta yi hani'an ba saboda anyi komi a wadace. Ana cikin cin abincin ne naga ɗiyar ɗakina Mmn irfaan da Daughter Rufaida da ƙanwata Asiya Umar sun haɗa kai suna ƙusƙus, sai ga shi naga suna ta zarmewa da ɗaya ɗaya suka fice falon, aiko na biyo bayansu sai naga sun nufi sashen Zee, na bisu cike da mamaki a raina nace "Lalle so duk so ne amman son kai ya fi yau ko ga shi na gani da idona" Ina biye da su har falon Zee inda na hangota cikin shiga ta alfarma tana ta hidima da ƴan'uwanta da suka zo daga Gombe, abun mamaki Asiya naga ta manna da gudu ta rungumeta tana ihun faɗin "wayyo Aunty Zee Ina yinki WALLAhi" ZEE tana dariya ta bi Asiya da kallo ta ce "Ni ma haka ƙanwata saukar yaushe?'" Asiya ta washe baki ta ce "mun jima munata neman inda zamu ganki tare Ni ke da ƴan'uwana suma masoyanki ne na haƙika kamar Ni, don lokacin da wannan ƙaddarar ta sameki mune muka yi ruwa kuka yi tsaki akan kare maki martabarki agun abokan adawa" Zee ta sake rungume Asiya cike da jin daɗin maganar tata ta janyo hannunta ta ce "Oya ku zo mu je masaukinku na daban ne ai" Ɗiyar ɗakina da Daughter Rufaida Suka biyo bayansu suna dariya, aiko sunga tarba kuma sun ga gata don kuwa Zee komi nata na tarbon baƙint ta yi abunta daban bayan na gidan. Shiyasa suka baje suka kwashi Gara abunsu ina yi ina haɗiyar yawu saboda ina jin tsoron in fito su gano leƙen asirinsu na zo yi. Haka aka yi taro cikin farin ciki da annushuwa kowa ya tafi yana murna saboda anyi masu komi a wadace babu ƙwange hannu a cikin lamarin ko kaɗan. Taro ya watse lafiya kowa ya nufi gidajenshi anata yabawa sannan da yi wa jariri da Mahaifiyarshi addu'a, da yi masu fatar ƙarin buɗi mai alkhairi ko don wasu su amfana. Don yan garinsu Dije daren da zasu koma gida ne Safwan ya cikasu da abun alkhairinshi, suka ruɗe sai zuba godiya suke yi, haka ma ZEE ta yi masu alkhairi dai dai iyawarta suna ta godiya da yi masu addu'ar zaman lafiya ga junansu. Dije da su Ladiyo suna ɗakinta ana firar bankwana Ladiyo ta kalli Dije cike da urgewa ta ce "Ai ke Dije yanzu ba abunda ya rage maki a duniyar nan illah ki cika da imani ki je lahira ki sami aljannah, don WALLAhi duk abunda ake yi ALLAH ya yi maki saboda haka ki godewa ALLAH" Dije ta yi dariya ta riƙo hannunta ta ce "Alhmdllh K'awata wannan kalmar itace kalmar da kullum nake yawan faɗa a bakina, saboda Ni kaina sanan ya yi man baiwar da ba kowa ya yi wa irinta ba" Jummala ta ce ", TABBAS ke ƴar baiwa ce a cikin mata don ga shi ko mu yanzu ta sanadinki mun fara zama ƴaƴan baiwar, don kuɗin da kika aiko muna kwanaki wallahi Ni dai sun yi man tsanin alkhairi Ni da Garbatina, don kuwa yanzu haka birni yake zuwa yana siyar da fitullu kala kala na zamani masu batur da masu aiki da zuƙar nefa, kamar da wasa ya fara kasuwancin sai ga shi yanzu kullum abu sai haɓaka ya ke yi, WALLAhi mun gode sosai mukam" Lanti da ta yi tagumi ta ce "ai Ni bance komi ba Dije don WALLAhi har zaucewa na so yi lokacin da Usmanu ya kawo man su har gida ya ce in jiki wai mu ja jari, haka naga abun kamar almara WALLAHI" Dije cike da mamaki ta kalli Hansai saboda neman ƙarin bayani don ita bata ma san kan zancen ba, kuma bata da masaniyar komi akai, Hansai ta yi dariya ta ce "Habibynki ne ya turowa wani saƙon ya baiwa Baban yaron nan ya kawo muna ya ce in ji ki abamu mu abokanki" Dije ta ji wata ƙwallah ta sauko mata cike da jin ƙara ƙaunar mijin nata, saboda ita ko kaɗan bai sanar da ita anyi hakan ba sai yanzu da ta ji a bakunansu, Mune ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Dole ki yi kuka don farin ciki ya yi a rayuwa, ALLAH ya ƙara buɗe maku hanyoyin samu ta ko'ina ko don mu na kusa da ku mu amfana" Gaba ɗaya aka ce "Ameen" Dije ta share hawayenta tana dariya ta ce "Mune naga yanzu kin rage surutu mi ye sirrin halan?" Mune ta yi dariya ta ce "Hmmmmmmmm ai ke dai in ana SALLAH ba'a magana, don kuwa akan halin har sakina ma Ummaru ya yi na dawo gida, saboda wani faɗa da na haɗa tsakanin matan yayan Ummaru, duk da a zahiri Ni iya gaskiyata ce na faɗi, amman duk wanda ya ji zai ɗauka cewa munafucci ne" Lanti tana dariya ta ce "To da gaskiya ta bayyana ai ALLAH ya wankeki ko? Kuma ki godewa ALLAH tunda har hakan ya zamo sanadin shiriyarki kika daina yawan faɗi ba'a tambayeki ba" Dije ta kalli Jummala ta ce "me ya faru halan" Ladiyo ta fashe da dariya ta ce "ki tambayi ƴar gidan taki mana sai ta fi iya bada labarin yanda ake so" Mune ta cire taguminta ta ce "Matan yayan Ummaru ne suke ta faɗan kishi kullum a tsakaninsu, shine ranar na ji ɗaya tana faɗawa wata abokiyarta cewa zata sakawa abokiyar zaman shinkafar ɓera a abinci ta mutu, to shine Ni kuma na ji tsoro na je na sanarwa wadda ake so akashen, aiko ta sanarwa da mijinsu sai ko ga shi wadda ta ci alwashin ta kawo mata abinci ta ce bazata ci ita sai ta ci ta ƙi ci, daman an shirya hakan mijin ma ya kafe akan dole sai taci abincin ta ƙi ci, rigima ta rikice gida ya cika da mutane ƙarshe dai abu har gaban Maigari, aka baiwa kyanwa ta ci bata yi komi ba itama aka tilastata dole sai da ta ci, abun mamaki ba abunda ta yi shine aka fara kuka ta ce daman na ce sai na ƙalla mata sharri, nan mutane suka yi ta tsine mani ana cewa da ni daman cen Ni Munafuka ce, gashi yanzu zan haɗa rigima don kawai na tsani ɗayar, ke a taƙaice dai akan hakan Ummaru ya sakeni na koma gida sai daga baya da gaskiya ta fito aka gano makirci ne ta ƙulla ashe ta ji lokacin da nike faɗawa waccen ɗin, shine ta liƙaman sharri sai cikin ikon ALLAH bayan bana gidan faɗa ya haɗasu ta ɗauko taɓarya ta ce sai ta kashe kishiyar, da komi ya lafa aka gano gaskiya don ta yi iƙirari da bakinta akan cewa itace ta faɗa na ji a lokacin, shine fa ya dawo da ni gidanshi bayan an ja kunnena da faɗi ba'a tambayeka ba, to tun daga haka na kame bakina ba ruwana da faɗin abunda bai shafeni ba, kinji mafarin shiriyata, yanzu ko a gabana aka yi abu WALLAhi ba abunda ya dameni bale in fad'a" Dije tana dariya ta ce "Alhmdllh ƙawata baki dadi wallahi yanzu ki ce ko a gabanki mu yi kashinmu ba zaki faɗa ba? " Mune tana dariya ta ce "tabbas Ni ce ma zan sakayaku in yi maku labule don kar a ganku" Gaba ɗaya aka saka dariya, haka suka yi ta tuno baya suna mayar da zance suna dariya, sun ɗauki lokaci sunata firarsu har dare ya raba sannan suka je suka kwanta. Tunda sassafe suka yi sallama da kowa suka kama hanyar zuwa inda suka fito, da nufin sati yana zagayowa itama zata bi su ta je wankan gida a garinsu . Haka ko aka yi Satin yana zuwa Fiddo da Zee da wata dattijuwaar da zata dinga taimakonta suka rakata zuwa garinsu ta jirgin sama da zai rage masu hanya zuwa sannan su ci gaba da motar, saboda kawai Yaron Safwan da ko ƙuda baya son su hau kanshi bale wahalar doguwar tafiya irin wannan. Ko da Jirgin ya saukesu motar tana jiransu saboda tuni ta taso sannan su daga baya suka biyo hanya, kasancewar an samu ci gaba sosai a babban birninsu Dijen har cikin ƙauyensu, shi yasa basu sha wata wahala ba suka isa ƙauyen ƙiriu garinsu Dijen Baffah. Mamaki bai kashe Dijen ba har sai da suka isa ƙofar gidan nasu taga kamar ma ba nan ne ba, don kuwa gida ne na alfarma Safwan ya ƙyanƙyara masu saboda kawai ya basu tukuicin faranta masan da ƴarsu take yi a kullum, ga kuma hasken solar ta ko'ina tun daga ƙofar gidan har cikin gidan fes yake masha ALLAH tare da sabon fentiin da ya ƙara fito da kyawon gidan. Baki sake Dije take kallon gidan don ko kula da masu yi mata sannu da zuwa bata yi ba har suka isa cikin gidan ita da su Zee, Baki bud'e ta ƙura wa inna ido cikin shiga mai kyau ta buɗe wata doguwar freezer tana fito da wasu gorunan ruwa tana saka wasu, bakinta washe ta ke faɗin "Sannunku da zuwa mutanen Yola sannu da zuwa" Fiddo kanta mamaki abun ya bata saboda tasan yanda gidan ya ke acen baya, Zee kam wasar bakinta kawai ta ke yi har suka shiga falon Inna da ya ƙawatu da kujeru irin na ƴan gayu, Suka zazzauna Dije kam ƙurya ta shige saboda kukan da ya zo mata kuma ba zata iya danneshi ba, haka ma bata son ta yi shi a gaban Zee ta fahimci wani abu. Inna ta fara jera masu abinci kala kala da ruwa da lemuka tana faɗin "ku sha ruwa kun kwaso hanya kam" Fiddo ta karɓi Sayyid hannun Zee ta ce "Inna ba zan baki yarona ba tunda har baki yi murna da zuwanshi ba" Inna ta rufe Baki tana dariya ta ce "ku yi ta kaya Ni mai Malam me zan yi da wannan mijin cikin zane komai sai anyi masa?" ZEE ta ɗauki ruwa tana tsiyayawa a kofi tace "ai dai inna shi sabon miji daban yake tsoho, idan kuma kika bari ya yi fushi ya ce ya fasa kuma shikenan sai mu nemo masa wasu matan" Shigowar Hansai cikin tsantsar farin ciki yasa Inna Bata Sami damar mayar masu da amsa ba, Hansai ta karɓe yaron tana ihun faɗin "Wayyo daɗi ɗanmu ya zama ɗan turawa Inna duba ki gani" Inna ta ƙarɓeshi da bisimillah tana faɗin "Waɗannan uwayen dai akwai kuri, to ALLAH yasa kafin ku haifu wasu sun rigaku haifuwar" Ta ƙare maganar tare da zaunawa tana gyara masa hannun rigarshi ta kayan sanyin da ke jikinshi ya sauko ƙasa ya rufe tafinshi, Zee tana dariya ta ce "Mu dai na mu muka sani Inna don zamu iya bugun ƙirji mu ce namu ya fi na kowa" Inna tana dariya ta ɗagashi sama tana yin miƙa yana wani botsarewa alamun ya ji daɗin hakan, Inna ta kalli Fiddo ta ce "Ku ne da yaron amman baku iya renon ba, to ku biya kawai a tayaku renonshi kawai" Dattijuwaar da suka zo da ita tana dariya ta ce "Mutum da Matarshi har sai an biya? To a biyosu bashi idan ya girma sai ya biya da kanshi" Sai ga sallamar Baffah ya shigo Dije da ke ƙuryar ɗaki tana kuka Hansai na lallashinta Muryar Baffah ta sa ta fito da saurinta ta taryeshi cike da jin daɗin ganinshi ta durƙusa tana gayar da shi, cike tsantsan farin ciki ya ke amsawa sannan ya tsaya bakin ƙofar falon ya gaisa da su Zee, sannan ya yi masu sannu da zuwa tare da tambayar mutanen gida, bayan sun ƙare gaisawar ne ya yi ɗakinshi Dije ta biyoshi zuciyarta cike tsantsan farin cikin ganin yanda yayi ƙiba hankalinshi a kwance, ta zauna tana wasa da yan yatsunta suka sake gaisawa a tsanake sannan ya kalleta yana ƴar dariya ya ce "Wa ya taɓa man Dijeta daga zuwanta?" Dije ta share hawayenta tana dariya ta ce "naga gida ya yi kyau Baffah ashe haka ka gyara gidan?" Yana dariyarsu ta manya ya ce "na gyara ko aka gyara man? ki yi haƙuri shi ya ce kada a sanar da ke sai in kin zo kin gani da idonki, don yanzu haka bamu fi wata uku da tarewa ba, saboda cikin ƴan watanni aka yi komi aka gama, mutane da yawa sunyi mamakin yanda aka kammala ginin cikin lokaci kaɗan, Alhmdllh kam mun godewa ALLAH da ya had'amu da mutanen kirki masu mutunci da sanin Yakamata, da ace duk sauran mutane haka su ke da ina tabbatar maki mabuƙata ba zasu taɓa yin kuka ba, to matsalar da aka samu irinsu ƙaɗan ne a cikin al'umma" Dije ta share hawayenta ta ce "Ni ban ma san mi zan ce ba Baffah saboda tun da naga wannan gyaran nasab aikinshi ne, haka fa ya aikowa da su Ladiyo kuɗi Ni banma sani ba ya ce in jini su ja jari" Baffah ya yi murmushi mai cike da jin daɗi ya ce "daman ita addu'ar a kullum mutum ya yi bata faɗuwa ƙasa banza, don haka muka roƙa kuma ga shi ALLAH ya cika muna gurunmu fiye da yanda muka yi tsammani, da ina da iko da na tara mutane na sanar da su cewa kada su gaji da yiwa ƴaƴansu addu'a, duk halin da suke a kullum su ci gaba da yi masu addu'ar shiriya saɓanin faɗin aibinsu a bakinsu, saboda addu'ar iyaye bata da shamaki wajen Ubangiji, da sunyi take tafiya sai dai ayi jinkiri wajen ganin sakamakon addu'ar, yanzu ga ki kamar ba ke ba kin natsu kin ajiye shirme da tsokana, kin ajiye jan faɗa da abun maganar da kike ta janyo muna a cen baya, ga shi Sakamakon haƙurin da muka yi ALLAH ya mayar muna da alkhairin da bamu zato ba bale tsammani" Dije ta ce "hakane Baffah ALLAH ya ƙara shirya maka Ni" Ameenn 🙏🏻 Akafta🤪 D/AUTA Ce✍🏻 *💣 DIJE K'ARANGIYA💣* *NA HADIZA D/AUTA* *TAURARI WRITER'S ASSOCIATION* *ALHAMDULILLAH!!!! ALHMDLLH!!! ALHMDLLH!! GIDAN AURE shine sunan book ɗina da zanyi a gaba, wadda take buƙata zata biya kuɗinta 300 kacal ta hanyar transfer ta wannan account ɗin HADIZA D AUTA 1230094555 access Bank, idan kuma kati ne zaki turo aritel ko mtn na ɗari uku to za'a turo ta wannan numbar 09032685442* *Ƴargata Maman Sultan Ubangiji ya baki lafiya yasa kaffara, Mrs Naseer ina miƙo gaisuwata zuwa gareki akan namijin ƙoƙarinki ga book ɗina, my Ambash ALLAH ya saukeki lafiya mu zo mu ci rangyem, Asma'u Umar ki yi haƙuri na goge laifina🤗* *Lamba 72 last page* 🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚 Baffah yana murmushin jin daɗi ya ce "Ameen Dijengalata amman fa ko haka aka tsaya Alhamdulillahi, don ba abunda za mu ce wa ALLAH sai godiya ALLAH ya sawa aurenmki albarka ya baku zaman lafiya ke da Mijinki da abokiyar zamanki duka, kuma ya baki ƴaƴa nagari masu albarka waɗanda zasu yi maki fiye da abunda kinka yi muna na alkhairi" Dije sai "Ameen Ameen" take faɗi zuciyarta cike da jin daɗin samun iyaye nagari, sai da suka ɗan taɓa fira sannan ta dawo falon Inna suna cin abincin ana ci gaba da fira cikin raha da barkwanci. Kwanansu Zee ɗaya direba ya kwashesu suka suka koma suka bar su Inna da kewarsu tare da jinjina lamarin Ubangiji, ganin yanda dukansu daga Zee har ita Fiddon sun saki jiki da su kamar cewa daman cen ƴan'uwan juna ne. Bayan su Inna sun dawo daga rakiyarsu ne Hansai ta goye Sayyid ta yi ɓangarenta, Dije ta faɗa kujera tace "Wash ALLAHna WALLAHI Inna gaba ɗaya jikina ciyo yake yi" Inna ta zauna tana ƴar dariya ta ce "sai kin yi haƙuri kam don yanzu jikinki yake haɗewa daga ɗaukar ciki da haifuwar da kika yi, wani zubin ma har zazzaɓi wasu su ke yi a wannan lokacin" Dije ta dafe goshinta ta ce "ai kam dai nima ina jin abinda nike ji a jikina" Inna ta kalleta da kyau sannan ta ce "Naji daɗin yanda yarinyar nan ta sauko kuka fahimci juna ga shi yanzu zamanku gwanin burgewa" Dije ta yunƙura ta ta shi zaune sannan ta kalli Inna ta ce "kin dai gani Inna ga shi yanzu kamar ba'a yi ba ashe da kirkinta sharrin sheɗan ne da kuma mugun kishin Abban Sayyid da take yi" Inna ta sauke ajiyar zuciya ta ce "duk macen duniya dole zata yi kishin mijinta, ke ba mijinta kawai ba duk abunda kake so a rayuwa dole ka yi kishin ganin wani ya raɓeshi, sai dai na wani ya fi wani don kowa da kalar dauriyarshi, shiyasa kika ji na ce da ke duk runtsi ki sa ya dawo da ita a matsayin matarshi, saboda ko da ta fita dole ne ya auri wata, kuma ita zata iya shigowa gidan da shirinta ƙarshe ma ta janye maki Mijin ya koma gareta a barki da cizon yatsa, amman in ita ce sanadiyyar wannan abun da ta aikata zai dakushe mata karsashi akan ko ma aikata wani mummunan abu saboda ganin igiya ɗaya ce ta rage a tsakaninsu, saɓanin wacce zai auro ba ita, don ba lalle bane ba ace ku fahimci juna, bale kuma ta barki ki ji daɗin zama gidan aurenki ko zama da Mijinki lafiya, don wata mace sharrinta ko sheɗan ya sarawa bala'in da ke tattare da ita, amman yanzu kin ga komi ya zama tarihi kuna zaman lafiyarku Masha Allah, wanda hakan da kuke shi zai ƙara farantawa mijinku rai ya ji daɗin kyautata maku" Dije ta cire tagumin da ta yi ta ce "Lalle Inna na yarda da aka ce abunda babba ya hango yaro ko da ya hau sama bazai iya hangowa, kuma naji daɗin biyayyar da na yi wajen sakashi dawo da ita, yanzu ga shi abun Ni ma ya zamo mani alkhairi don baki ga yanda ta ke son Sayyid ba, bata bari ya zauna hannuna matukar ba abincinshi zai sha ba, kuma ina bashi take sake karɓeshi su tafi, shi kanshi Abbanshi sanadin wannan halin kirkin da take yi ne yasa ya sake mata sosai suna ɗasawa, sai dai wani lokacin ina jin ba daɗi idan naga yana kulata Inna, Amman idan na tuno da cewa itama fa Matarshi ce kamar Ni sai in baiwa zuciyata haƙuri don bana son ta fahimci ina jin zafinta" Inna ta yi shiru sannan ta ce "hakan da kike yi ya yi kuma shine abunda ya dace ki yi, don yanda kike ji haka itama take ji amman ta ke haƙura saboda neman zaman lafiyarku, ALLAH ya baku haƙurin zama da junanku itama kuma ya bata nata rabo" Dije ƙirjinta ya buga amman ta daure ta ce "Ameen inna Bari in je in kwanta Wallahi wani bacci nike ji a idona" Inna ta bita da kallo cike da jin daɗin ganin yanda hankali ya shige Dijenta, sannan ta ce "Duk baccin da ki ke son yi ai wannan baturen baya barinki sai dai in bai rikice ba" Daga cen cikin ɗakin Dije ta ce "WALLAhi sai in tafiyata gidan Gambo in sha baccina in barku da shi ku yi ta fama" Inna tana dariya ta ce "Ai duk inda zaki je ki ɓoye sai an kai maki shi acen tunda mu bamu da abunda zamu ba shi" Dije ta yi saurin faɗin "Gaskiya Inna uwaye suna shan wahalar renon ƴaƴa a rayuwa" Inna ta fashe da dariya ta ce "Kamar yanda aka sha taki ba ai duk uwar da kika gani da ɗanta to ita kaɗai tasan wahalar da ta sha da abunta lokacin da yana ƙarami har girmanshi, ALLAH dai ya jiƙan iyayenmu da rahamomi Wallahi" Dije ta ce "Ameen" sannan ta yi kwanciyarta aranta tana jinjina irin yanda iyaye mata suke shan wahalar reno musamman farkon haifuwa, wanda ita sai yanzu ta gano cewa ashe ba ƙaramin haƙuri Inna ta yi da ita ba, cikin zuciyarta sai addu'a take zubawa Innar saboda tuno irin abun maganar da ta yi ta janyo masu a baya, tana cikin tunanin ne wani ta yi dariya wani ta ɓata fuska har bacci ya yi awon gaba da ita. **** Rayuwa mai daɗi Dije ta yi a gidansu saboda komi yi mata ake yi aikinta bacci da cin abinci sai kuma baiwa Sayyid nono, sannan da baiwa Malaminta dama wajen ƙara macewa kanta, don kuwa suna maƙale a waya ko wane lokaci yana nuna mata irin kewarta da ya yi, tare da sanar da ita da ta cika wata ɗaya a garin zai zo ya kwashesu su koma, cikin dubara take ta hilatarshi har ya bar zancen don bata son ya gano bata son komawar a lokacin, kada ya ga kamar ita bata yi kewarshi ba kamar yanda kullum yake sanar da ita irin damuwar da yake ciki, don Zee ta so binshi acen Abujar ya ce ta jira anan Yolar zai dinga zuwa akai akai wurinta, dole ta haƙura amman ba don ranta ya so ba sai don samun zaman lafiyar da ko kaɗan bata son abunda zai janyo wata fitina a tsakaninsu. Satin Dije Uku a garin ta yi ɓul ɓul daga ita har yaronta gwani sha'awa saboda kulawar da suke samu wurin Inna da dattijuwar matar, a gefe ɗaya kuma Gambo da bata gajiya da dafa mata abubuwa tana shanyewa, don wani zubin acen ma take kwanciyarta daga ita yaronta da dattijuwar, ga Yan garin na su kowa sai nan nan ake yi da ita da kuma yaronta, don ma Gambo bata son ana yawan fita da shi don ƙa'ida ne kullum sai ta tofeshi da addu'o'in tsari, sannan ta ce dole itama Dijen sai ta tosheshi da addu'o'in saboda kariya daga sharrin mutum ko aljan da wasu masu kambun baki, saboda farin yaron da yanda yake kyakkyawa ga shi ɓul ɓul dole ne mutane su yi shaawarshi, sannan uwa uba ga shi fes fes kullum cikin shiga ta alfarma kuma irinta wayayyun ƴan birni. **** Wasa wasa Dijen Baffah sai da ta yi wata biyu a garinsu sannan Angonta ya garzayo ya kwashi Matarshi da yaronshi suka koma Yola, suka bar su Inna da Baffah da mutanen garin da kewar Dijen da ɗan baturen yaronta mai kama da indiyawa samfurin larabawa kalar yan Ethiopia. Hajiya Mama ba ƙaramin daɗi ta ji ba da ta ga yanda yaron da mamarshi suka yi sharr abunsu, cike da tsananin farin ciki ta karɓe shi tana ta yi masa wasa yana wasar baki, Fiddo ta karɓeshi tana faɗin "Coming to your mama my beautiful boy" Hajiya Mama ta kalleta tana dariya ta ce "in dai ɗanku ne ga shi nan don ma na yi maku kara na ɗauka?" Fiddo tana dariya ta ce "WALLAhi Hajiyarmu son yaron nan Nike yi, don ALLAH ki ce da Yayanmu su tafi da Ni Abuja don bana son a rabani da shi ALLAH" Hajiyar tana dariya ta ce "ki jira idan kunyi jarabawar ƙarshe sai ki tattara inaki inaki ki koma cen duka tunda ke baki fatar ki je naki gidan mijin sai taya wasu zaman aure" Dije dai dariya kawai ta ke yi cikin dariyar ta ce "ai Insha ALLAHu acen ma zamu yi mata aure don bama fatar a raba uwa da ɗanta" Safwan da ke shigowa ɗakin ya ce "ba inda zata je don tana kammala karatunta zamu auradda ita" Fiddo ta zumɓuro baki ta ce "to ai Ni bani da miji" Dije ta dafe baki ta ce "Mukhtar ɗin fa? Ko an ɓata?" Ta miƙe tana dariya ta ce "yarona zo mu je tunda yau haɗe man kai ake yi a gidan" Ta fice suka bita da kallo Safwan ya ƙaraso ya zauna suna ci gaba da firarsu kafin lokacin tafiyarsu ya yi suka tafi duka har Fiddon cen gidan nashi, inda Surayya da wasu yan'uwa suke acen suna tsumayin zuwansu. Aiko shigarsu gidan mutane suka zo tarbarsu cikin farin ciki ana yi mata Barka da dawowa, Zee ta karɓe yaron tana ta juyi da shi Safwan ya riƙo hannunta ya yi mata raɗa ta yi saurin rufe ido, Dije ta bisu da kallo cikin gefen ido sannan ta shige sashenta tare da mutane tana dariyar yaƙe, Zee tayi sashenta da Sayyid tana ta murnar dawowarshi. Dije kam tana shiga ta faɗa toilet tana share ƙwallar kishin da ya turnuƙota, sannan ta watsa ruwa ta ɗauro arwallah, bayan ta fito ne Surry ta ce "haba Hajiya daga zuwa ba wani jira sai shige abunki ki barmu a falo muna jiranki?" Dije ta washe baki cikin ƙarfin hali ta ce "Tom bari in shirya in zo inji me da me aka tanadarwa baƙuwar?" Surry ta riƙo hannunta ta ce "ki daina ɓoyo nasan me ke damunki to Aunty zee dai ciki. E da ita shiyasa kika ga yayanmu ya hanata wannan tsallen da take yi don kada ta janyo muna aiki, saboda haka plss a yafewa yayanmu don ALLAH, kada a lalace masa wannan dare da yake ta tsimayin zuwanshi" Dije ta rufe baki cike da jin kunyar ganotan da surry ta yi ta ce "Bafa wani abu Ni daman cen ban ji komi ba Aunty Surrynmu" Surry ta fice tana dariya tace "ki dai zo ga delicious cen mun haɗa ma ku yana jiranku ke da Big bros" Dije ta bita da kallo tana dariya sannan ta fara shiryawa tana jin daɗin cikin da aka ce ZEE tana da itama, don ƙaunar Sayyid da take yi yasa ko kaɗan bata kishin abunda zata haifo itama, Shiyasa ta yi mata fatan alkhairi a zucinta. Bayan ta yi sallah ne tashirya cikin wani voil da yaji aiki tun daga sama har ƙasa sannan fara fesa turare sai ga Safwan ɗin ya shigo ɗakin, yana hangota ya ƙaraso ta bayanta ya rungumota a jikinshi, sannan ya sunsuno dogon wuyanta tare da sauke masa wani wawan kiss, ba shiri ta zabura tare da ɗauke wuta na wuccin gadi, sannan ta kai kallonta jikin madubin tana ƙare masa kallo cikin wani sihirtaccen kallon da shi kanshi baisan ta iya shi ba, ba shiri ya ji yar ya jikinshi tsikarshi ta miƙe, ya yi saurin kwantowa bayanta yana sauke hannunshi akan dukiyar fulaninta da suke cike fam, ta yi saurin runtse ido tace "Da zafi fa" Ya juyota a zafafe ya dinga tsotse mata baki tamkar zai cire mata shi, da kyar ta samu ya ta ƙwaci leɓenta sannan ta ɗago tana kallonshi ido cikin ido da wasu jajayen idanuwanshi da suka rine a lokaci daya, sannan ta ce "Mu je mu ci abinci yana jiranmu" Tana gama faɗar hakan ta zille ta fice ta bar masa ɗakin ya bi bayanta da kallo tare da dafe jarumarshi da ta miƙe tana kallon gabanta, ya nufi toilet minti biyar a tsakani sannan ya fito ya fice cikin wata kasala da ta diro masa. Har suka ci abincin suka ƙare ba wata walwala a fuskarshi, yana ƙarewa ya shige ɗakinshi na sashen Zee sai dare sosai ya dawo sashen Dijen, inda ko da ya taradda ita har ta yi bacci ita da yaronta, cikin dabara ya ɗauke yaron ya kaishi cikin gadonshi ya ajiye sannan ya dawo kan gadon ya janyota jikinshi sai rawa yake yi, Cikin bacci ta jiyo saƙonshi yana sauka ta ko'ina cikin jikinta, dole ta wartsake ta karɓi mijinta hannu bibbiyu suka dinga farantawa juna cikin farin ciki da ɗokin juna, ALLAH ya taimakesu yaron ya basu haɗin kai domin shi ma kanshi a gajiya yake shiyasa yake ta baccinshi su kuma suna ta shan soyayyarsu kan kari, don Safwan ya susuce akanta sosai sai zuba santin daɗi yake yi yana nishi saboda irin bala'in daɗin da yake ji yana ratsa koina na jikinshi, sun daɗe suna abu ɗaya har sai da Sayyid ya falka sannan suka haƙura ba don sun so ba. Da safe ma ba ƙaramin rawar jiki ya yi akanta ba don ma yana kawaici baya don Zee ta ganoshi, gudun janyo wata sabuwar fitinar yasa kwanansu biyu a Yola ya tattara Matarshi da ɗan shi suka koma Abuja, inda suka ci gaba da jiyar da junansu daɗi tare da tarairayar juna kamar yanzu ne suka yi sabon auren, a gefe ɗaya kuma suna renon yaronsu da ko kaɗan basu son ganin kukanshi don inda hali ma ƙuda basa son ya hau kanshi. Watan Sayyid huɗu Dije ta fara zuwa school saboda ƙulafucinta akan makarantar, dole aka nemo mata wadda zata dinga kula da Sayyid saboda hidimar karatun ba wasa ba. ***** Bayan shekara biyar Dijen Baffah ta yi karatunta ta ƙare har ta sami aiki a wata babbar Asibitin da ke Abuja, sannan ALLAH ya sake bata wata haifuwar inda ta sami ƴa mace aka saka mata sunan Hajiya Mama ta ci sunan Sayyada, Zee ma ta yarinyarta ɗaya mai suna Ummusalmah itama tana aikinta acen Yolar cikin amincin ALLAH, Fiddo ma anyi mata aure har ya haifi ɗanta masha ALLAH, Surayya ma yaranta uku Husnah ma ta yi aure da ƴarta mai sunan Nasiba. Zamansu lafiya har lokacin saboda akwai fahimtar juna sosai a tsakaninsu, shi ma kanshi Uban gayyar ya zama ƙaton Alhaji don kuwa daga shi har Matanshi duka sun sauke farali, Inna da Baffah ma da Gambo da Maigari duka sun je, a gefe ɗaya kuma Dije daga lokacin da ta fara karbar salary ne ta fara asusun gina makarantar boko da islamiya garin na su, ga alkhairin da take yi wa yan garin da guminta bayan na Maigidanta, izuwa lokacin su Ladiyo kansu sun zama wata tsiya a sanadin Ƙawarsu Dijen Baffah, sai dai kwatsam ALLAH ya aikowa Gambo rasuwa bayan gajeruwar jinyar da ta sha, Dije ta yi kukan rashin Gambo saboda wani jigo ce ta rayuwarta, akan hakane ta yi ƙudurin gina masallaci a ƙauyen hadiyya zuwa gareta, ALLAH ya taimaketa Alhaji Safwan ya dafa mata ta cika gurinta, mutanen garin sai sambarka suke yi tare da godiya ga Ubangiji da ya sanya Dijen da suke aibatawa a baya itace yanzu ta zamo silar jin daɗinsu, Usmanu ma ya zama babban ɗan kasuwa yana samu daidai gwargwado don ya riki kanshi da Iyayenshi har ma wasu suna jin dadi ta sanadinshi. Dije ma Cikin ƙashin kanta da shekaru suka ja ta biyawa Usmanu da Hansai Hajji, bayan sun dawo ne wata shekara suka yi haɗaka da Malaminta suka biyawa ƙawayen Dijen, Ladiyo Jummala Lanti da Mune tare suka je da su ma ɗin kansu suka sake komawa tare da su. Wata shekara ma da kanta ta biyawa uwargidan Maigarin hajjin ta je don har abada bata mance karayar da ta janyo mata ta yi a lokacin gudun kura da suka yi. Hajiya Dije da ALHAJI Safwan a ƙauyensu Dijen mutane sai turuwar zuwa gayar da su ake yi a ƙofar gidan Maigarin da suka fara zuwa domin su gayar da shi, sai ga wasu yan bautar ƙasa an turo tare da doguwar takardar da aka ce akawowa Maigarin, Maigarin ya karɓa yana kallon Dijen da ke dariya cikin ƙasaita saboda tuno abunda ya faru a baya, Dije ta karɓa ta dinga karantawa cikin harshen turancinta irin na ƴan America, bayan ta kare ta fassara masu duk abunda takardar ta ƙunsa, gaba ɗaya wurin manya da yara samari da ƴanmata aka dinga yi mata tafi ana yi mata kirari irin na mutuntawa da zayyano irin halayen kirkinta ita da Mijinta, zuciyarta cike fess da farin ciki ta tashi ta fara nuna jin daɗinta a fili sannan ta yi kira sosai ga mutanen garin akan su jajirce su dinga saka ƴaƴansu a makarantar boko da islamiya, saboda su ma su waye su zamo dai dai da kowa adaina yi masu kallon ƙauyawa, ta yi masu nuni da kanta da irin nasarar da ta samu duk a sanadin bokon wanda su kansu shaida ne ba sai an sanar da su ba, sannan ta yi kira ga iyaye sosai akan su dinga haƙuri da halayen ƴaƴansu musamman marasa ji, Baffah'nta ma ya tashi ya yi dogon jawabi akan alfanun yi wa ya'ya addu'a kuma kada a gaji da yi madu addu'a aduk wani rashin ji ko wani abu mara kyau da suka aikata, don ALLAH maji roƙon bawanshi ne kuma aduk lokacin da aka roƙa zai amsa sai dai jinkirin sakamakon a wani lokaci, mutane da dama sunyi alwashin jajircewa sosai akan karatun ƴaƴansu, kuma sunyi godiya da abun alkhairin Dije da Mijinta garesu, nan suka fito da kuɗi suka rarraba wa mutane duk wanda Allah ya sa da rabonshi ya samu, don ko yan bautar ƙasar ma sai da Suka wankesu da alkharinsu da suka saba. Tammat bi hamdullah anan na kawo karshen littafin na *Dije ƙarangiya* masu comments masu masu yiman addu'a da masu yiman sharing book din a groups Kuma na gode sosai sai mun hadu a littafin na kuɗi mai suna *GIDAN AURE* littafi ne wanda ya kunshi rigingumun gidajen aurenmu a yau da kuma ma wasu abubuwa da baki bazai iya faɗa ba, masoyana masu son bin books ɗina a Koda yaushe idan kuna buƙata zaku sameni ta wannan numbar sai mu yi magana 09032685442 sai kuma na Free da zanyi don ku masoyana shi ma mai suna *SHAGALLIYA* wanda shi ma ɗin cike yake da barkwanci da nishaɗi ba kaɗan ba kusan ince fiye ma da Dijen Ƙarangiya, don haka ku ci gaba da bibiyata Ni *HADIZA IBRAHIM D/AUTA wadda wasu suka fi sani da PRINCESS DIJA* zaku iya nemana ta wattpad kamar haka *Princessdija246* INA SONKU SOSAI MASOYANA ADUK INDA KUKE KUMA A DUK INDA KUKA KASANCE🤝🏻 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels