An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels *LADIDIN KAUYE* _funny & love story._ *Labari mai ban dariya haɗi da faɗa karwa* *NA* *MOM ISLAM* *ZAINAB HABIB* *MARUBUCIYAR:* *ZAINABU ABU*_ *AND NOW* *LADIDIN K'AUYE* ~MALLAKAR~ ZAINAB HABIB (mom Islam ). *GODIYA* ina ƙara miƙa godiya ta ga Allah maɗaukakin sarki Wanda yabani ikon sake rubuto muku wanan ƙayatacen labarin cikin hikimar sa da iyawarsa Allah nagode maka. *GARGƊi*_wanan labarin ƙir ƙirane ban yishi dan wani ko wata ba nayi shine dan ni shaɗii da ban dariya in yazo dai dai da rayuwarki /ratuwarka to hasa shene kawai._ 🤏ban yarda wani ko wata su juyamin labari ba duk Wanda yayi yinkurin yin hakan to shida rabil izzati🤙. 08141799224 *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *EPISODE 1&2.* 📖____Yarinya ce ƴar kimanin shekara goma sha biyu da aihuwa sanye take da rigar atamfa da wandon yadi. Tafiya takeyi tana waƙa da zabgegiyar bulala a hannun ta me rake ta hango da gudu ta ƙarasa gurinshi yana ganin ta ya washe jajayen haƙoransa kana yace "LADIDI daga ina kika fito haka"¿. Ɗaukar rake ƴan hamsin tayi kana ta ce "daga gida mana". Ganin LADIDI ta kusa shanye rakeb hannunta tana shirin ɗaukar wani ido ya zare mata kana yace "ke baki da hankali ne kin ɗauki raken hamsin banyi miki magana ba yanzu kuma zaki kuma ɗaukar wani". LADIDI dake ta shan raken ta yawu nazuba a bakinta tace "wlh ko kabani raken in daɗa ko kuwa yanzu kaci najaki". mai raken da aƙalla yayi sa,an baban ta dubanta yayi kana yace "yarinya ki wuce kitafi sabgar ki , LADIDI daketa juya bulala tana dariya tana kallonsa. mai rake ne yace "yarinya ni natafi kiyimun addu,a yau inyi ciniki LADIDI ce tadubi mai rake tace "karka damu". Mai rake ya juya zeja baron rakenshi yaji saukar bulala dur ƙusawa yayi yana ihu yana sosawa juyawa yayi yaga babu LADIDI babu samatan ta . Gudu takeyi har ta isa gidansu , gidane ma dai daici kewaye yake da katangar kara. YADIKKO na surfen dawa ko sallama batayi ba tashige ɗakin data ke kwana tarufe ƙofa YADIKKO tarasa abinda zatace ta girgiza kai ta ɗaga hanu tana rokon Allah yashir yamata LADIDI. Kayan wasanta ta ɗibo kai tsaye gurin bishiyar kukar data mamayi filin tsakar gidan tanufa YADIKKO tana wanke dawar data surfa ta dubi Ladidi kana tace "bana ce ki dena zuwa gurin bishiyar nan ba¿. LADIDI ce ta turo baki tana ƙananun maganganu YADIKKO ce ta riƙe haɓa kana tace "to kodai kin kwaso aljanu ne tunda kin nace da zuwa gindin kuka ita dai LADIDI bata kula YADIKKON ba taci gaba da wasanta . YADIKKO ce take ta ƙwalawa Ladidi kira tasowa tayi tana bubuga kafa nera goma ta miƙawa LADIDI kana tace "ki ɗauki waccan dawar ki kai ingin Shafi,u kice ya miki yanzu . Ɗauko mayafinta tayi ta ɗaure a kwan kwasonta kana ta ɗora markaɗen a kai . Tana cikin tafiya taci karo da me awara ajiye nikan tayi kana ta kirashi tunda yaron ya tabbatar LADIDI ce me kiran har ze kwasa da gudu ta riƙoshi kana tace "ina zaka dan uwarka kasanni kuwa¿". Dur ƙusawa yaron yayi kana yace "LADIDI kiyi hakuri talle mai ƙeya tayi kana tace "nawa nawa awaran¿ "Biyu biyar yaron yace saboda a tsorace yake Ladidi ce ta haɗa guda huɗu a guri ɗaya tacewa yaron naci biyu ƙara ɗibo huɗu takumayi tace naci na kuɗina saura ala koro nan yaron yadu beta yace "wlh LADIDI goggo na ta hanani LADIDI ce ta buge mai baki ta ɗiibi biyu. Seda yaron yayi nisa sanan yace LADIDI bogaza Allah ya isa LADIDI tayi ƙwafa tasan ko ba komai taci awarar goma a talatin. Nikan ta ɗauka tana zuwa dai dai ingin ɗin Shafi,u tace nakawo niƙa Shafi,u daketa nikan shi be kulata ba magana taƙarayi amma yaƙi kulata ramin cinnaka tagani kusada ƙafar shi ɗaya ta ɗauka tasamai a takalmin ƙafarshi takuma ɗaukar ɗaya tasamai a gefen rigarshi ragowar ɗayan tasa mai gurin da taga ya yage a rigar komawa gefe tayi kana tahau waƙe waƙenta . Shafi,u ne yafara jin cizo ta kafa ze sosa yaji cizo ta kanshi yakai hannu ze Sosa kan yakuma ji ta jikinshi a she cinnaka har cikin wandon shi ya shige da gudu ya fice a ɗakin niƙan yana ihu LADIDI babu abin da takeyi in banda dariya shafi,u ne yayi hanyar gidansu yaje tsallaka murhun girkin gidan yataka tsakiyar murhun a she da wuta kwanciya yayi yana birgima an rasa meke damunshi sedai yasosa nan ya Sosa can LADIDI kuwa tunda Shafi,u yafice take gurin ingin niƙan dama ta iya tana gama niƙan ta daura a kanta tana tafiya tana dariya tana faɗin "dama nakashe goman YADIKKO gashi nasami niƙa a sabill. Tana tafiya taci karo da wani me rogo dafaffe tsareshi tayi kana tasauke nikan ta dubeshi tace "mai rogo akwai ala koro¿." mai rogon nne ya galla mata harara yace "dan uwarki wanne kora dazan baki ala koro LADIDI ce tazaro ido kana tace "uwata fa kazaga mai rogo ne yace me kika isa kiyi jibeki kamar buhun alabo . Be Ankara ba LADIDI ta ɓarar da tiran rogon kasa takwashi wanda zata kwasa tazo guduwa mai rogo ya riƙota faɗawa tayi kanshi tahau ruwan cikin shi tadinga kai mai duka baji ba gan. Hakuri yashiga bata ɗagashi tayi kana ta ce "baka ganni yar ƙarama ba shine kakeson cin uwata a banza me rogo ne ya miƙowa LADIDI na ashirin ya zura da gudu . Cigaba tayi da tafiyar ta har ta isa gida YADIKKO ce tace "LADIDI baky ajin faɗan da nake yi miki ko ¿. sauke nikan tayi kana tace "YADIKKO zansha ruwa. YADIKKO dake ɓarar gyaɗa tace "wlh ke da yar kishi yace kin shiga uku LADIDI ce kamar an tsikareta ta zabura a guje tafice waje. Ƙarar mota , taji gurin masu motar tanufa ɗaya daga cikin su ne yadubi Ladidi kana yace "baiwar Allah tambaya muke yi" Murguɗa musu baki tayi kana tace "nifa banason kinin bibi zakayi magana kana wani tsari ɗaya daga cikin motar ne yace kiyi hakuri yammata dama muna neman mallam Adamu ne. ta6e baki tayi kana tace "nasan gidan amma saidai inzaku sani acikin wanan akori kurar. Wani daga cikin motar da tunda ɗayan yafara magana shi beyi ba leƙowa yayi ta cikin motar kana ya ce "ubanwa kika gani a akori kura¿. Murguɗa mai baki tayi kana tace "karka ƙara zagina na kusa da shine yace Humaid mu lallaɓata ta raka mu . Buɗe mata murfin motar Humaid ɗin yayi shigowarta keda wuya sukaji motar ta game da wari kamar anyi tusa Jalal ne yace "Humaid bakaji wani wari ba dede lokacin da warin ya iso hancin Humaid sun rasa meke wari a motar LADIDI ce ta dube su tace sewani toshe toshen hanci kukeyi sekace wasu malaman. Duban tsafta Humaid ne ya ce wlh ga meyin warin nan hatta bakin ta wari yakeyi LADIDI data tabbatar da ita akeyi ciro alurar ɗinkin hannu tayi kana ta waiga taga Humaid ɗin yadena kallonta murmushi tayi kana tayi gefe da hannun ta sokawa Humaid alurar ihu Humaid yakeyi ba k'a kau tawa Jalal ne yafaka motar kana yazo gurin Humaid ɗin dake faman ihu LADIDI ce ta dubeshi kana tace "meyasa meka ne ɗan gayu¿ cikin su babu wanda ya kulata bare su waigo ta Humaid ne yace ja motar Jalal muyi sauri mu isa gidan . Sun zo dai dai k'ofar gidan LADIDI tace "to munzo seku fito Humaid dake ɗin gisa ƙafarsa yace "to ai seki koma tun da kin rako mu. Zaro ido waje tayi kana a zuciyarta tace lallai wannan besan ko wacece LADIDI ba . Duban ƙafar Humaid ɗin LADIDI tayi kana ta fashe da dariya Humaid da babu halin gudu ya dura mata zagi Jalal ne yace "tunda ta nuna mana ƙofar gidan to muje ka kyale yarinyar nan . Hango wata zabge giyar sanda tayi ta ɗauka kana ta gyara bakinta seda tabari Humaid yazo dede saitin shiga gidan ta zula mai a kafar da tayimai allura zubewa yayi a ƙasa yana ihu da gudu ta ƙasa... Malam adamu ne yaj ihu kuma na babban mutum da sauri ya ƙaraso Jalal ne yace "barka malam , malam adamu ne yace a,a wana ke gani kamar yan birni¿ Jalal ne yace "malam mune wata yarinya ce tara komu gidanka gashi ta bugawa Humaid sanda a ƙafa ta gudu ,malam yajin jina zancen kana yace "nasan ba wata bace illa LADIDI wannan aikin seita . Humaid ne yayi ƙarfin halin magana yace "Jalal kaje kane momin yarin yar nan senaga waye ubananta. Malam adamu ne yace "wlh gara ka hakura saboda wanan yarinyar ana tunanin tana da aljanu ......✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽. *_~MOM ISLAM CE✍🏽.~_* *LADIDIN ƘAUYE.* _funny & love story._ *Labari mai ban dariya haɗi da faɗa karwa* *NA* *MOM ISLAM* *ZAINAB HABIB* *MARUBUCIYAR:ZAINABU ABU* *_AND NOW *_ *LADIDIN ƘAUYE.* *BIMILLAHEER RAHMANIR RAHEEM.* *EPISODE 3&4.* ___malam adamu ne yayi musu nuni dasu ƙarasa cikin gidan inna Hauwa matar malam Adamu ta na ganin su ta shiga yi musu sanu da zuwa d'akin malam Adamu suka wuce kai tsaye Humaid ne yayi rau rau da ido kamar me shirin yin kuka yace "Jalal please help me jalal da shima hanka linshi ya fara tashi yace "sorry brother anjima ka d'an zakaji jikin naka ya koma normal Humaid ne a ts,wace ,ya dubi Jalal kana yace "baka san azabar da nake ji bane shi yasa . Jalal ne ya mik'e jiki babu k'wari yanufi gurin da inna hauwa take tambayar ta yashiga yi akwai asibiti anan kusa¿ inna hauwa dake dama fura da nono ta ce "eh akwai amma fa akwai tafiya sosai Jalal ne yace indai akwai barin yiwa Humaid magana mutafi inna hauwa ce ta kwala wa malam adamu kira shigowa yayi d'auke da ledar lemu da ayaba da kankana ajiye ledar yayi ganin yanayin Jalal malam Adamu ne ya ce har yazu jikin humidun ne eh Jalal ya ce asibiti nakeso mu kaishi ko aliura ayi mai . Shiga d'akin sukayi suka temaka mai ya mike suka sa shi a mota seda suka yi tafiya me nisa kana suka shiga asbitin . Wani likita ne yazo gurin malam Adamu hannu ya mik'awa malam Adamu suka gaisa kana likitan yace "baba waye babu lpy ¿. malam Adamu ne ya nuna Humaid da zazza6i yarufeshi ri rik'eshi sukayi yanuna musu d'akin kwantar da marasa lpy ruwa aka fara samai kana aka yimai allurori bacci ne ya d'auke shi me nauyi Jalal ne yaji cikin shi na kukan yunwa mik'ewa tsaye ,yayi kana yace mala barin d'an fita yanzu zan dawo. Malam Adamu ne yace ina kuma zaka¿ Jalal ne ya ce wlh am feeling Hungary malam Adamu ne ya zaro ido kana yace naji kamar kace kwan giri Jalal ne ya tun tsure da ,dariya kana yace . "Cewa nayi ina jin yunwa malam Adamu ne ya ce au to ko in koma gida ne in taho muku da fura da nono ¿". Jalal ne yace a,a ai dazamu taho naga masu saida abinci malam Adamu ne yayi mai Allah ya tsare Humaid ne ya farka d'auke da salati a bakin shi. Malam Adamu ne yace sanu Humaidu,, humai ne ya dubi malam Adamu kana "yace yauwa sannu ina Jalal yayi ?". Malam Adamu ne yace Jalal yaje siyo abinci yanzu ze dawo . Likitan d'azu ne yashi go d'auke ta ,takaddar salama mik'awa malam Adamu yayi kana ya tambayi Humaid ya,,ya kejin jikin nashi Humaid ne ya ce wlh yanzu babu inda yake ciwo hamdala malam Adamu yayi . Jalal ne yashigo da ba bbar leda a hannun shi kifi yasiyo soyayye da kuma kaza guda biyu gasassu malam Adamu ne yace duk wanan kayan ina za,a kai su lemun kewalba ya mik'awa Humaid da kifi domin Humaid d'in ma,abocin son kifi ne jalal ne ya d'auke kaza guda daya ,ya mik'awa malam Adamu . Malam Adamu ne ya e a a ni bazan ci ba ,dole dai seda ya kar6a tukun ya d'an sha lemun ya barsu a gurin ya nufi masalaci. Suma bayan sun gama sallah sukayi kana suka biya likita kud'in shi ,suka hau mota suna cikin tafiya suka hango Ladidi tana jifan mangoro abishiya Humaid ne ya dubi jalal yace tsaya ga mahau kaciyar ,yarin yar nan . Malam adamu ne yace kufa kiyayi Ladidi kotayi lefi babu me d'aukar mataki Humaid ne a zuciye ,yace wai malam wanan yar gidan waye ¿malam adamu ne ya ce yar gidan amini na ne malam musa. Humaid ne ya ce dan Allah malam kabari ,inkoya mata hankali malam adamu ne ya ce jalal kawuce mutafi na gaya maka kar katsaya . Humaid ne ya lek'a ta window yace ke Ladidi wlh kinci bashi zanga uban daya tsaya miki a fad'in a kurkin k'auyen nan . Ladidi ,da kamar jira takeyi ta sami abokin fad'a dagudu tayi ,yo gurin motar amma ina jalal ya k'ara gudun motar duwatsu tasamu tanata kai jifa amma babu sa,a jifan data kai na k'arshe se a bayan wani bafula tani yana tsugune a wata gona yana kashi yaji ,jifa a bayan sa dasauri yaja wandon sa ya rik'e yana ihu Ladidi data lura tayi mugunta tazo guduwa bafula tani yace yau k'aryar ki takare kamota yayi kana ya dunga dukan ta . Yana saketa ,ta mul mulo zagi shikuwa bafula tani dayaga Ladidi tafi k'ar fin shi ya shemeta da sanda ko motsi bata yi . *_FARKON LABARI*_ Malam musa shine ma haifin Ladidi ita kad'ai Allah ya basu tun tana k'arama bata ji ko,kad'an bare duka shima be dame taba abota ce me k'arfi ta shiga tsakanin malam musa da malam adamu mutanen kirki . Malam Adamu shine k'anin mahaifin su Humaid da jalal ma haifin su Humaid wato alhaji abdullahi tun bayan rasuwar mahai finsu wato kakan su Humaid kenan da mahai fiyar shi. ya had'a kayan shi yatafi neman ilimi shi kuwa malam adamu be bi d'an uwan ,nasa ba ya zauna ,yana koyar da almajirai . Shigar dadyn su Humaid garin jos ya had'u da wani bawon Allah ya d'aukeshi zaman shagon atamfofi suna samun alkairi sosai saboda alhaji abdullahi akwai amana baya cin kayan da bana shiba shiyasa yake zaune lpy da mutane. K'watsam wata rana uban gidan shi yabashi kyautar wani katafaren shagon da yagina had'i da bashi kaya masu yawa acikin lokaci k'alilan kud'i suka bunk'asa uban gidan nashi ne ya cire kud'in shi kana yabawa alhaji abdullahi ribar halak d'inshi ne yana juyawa yana karatun boko kan kace me arziki ya hau hawa . Daga nan yafara neman aure Alhajin da ya bud'e mai shago shine yazama uba a garezhi yabashi kyautar gida a ranar alhaji abdullahi yayi ,kuka sosai ,yana fad'in inama iyayenshi na raye da sunga gatan da wadatar dayake ciki . Bayan auran, ne malam adamu ya zo jos ganin ,gidan alhaji abdullahi gidane. Gidane me kyan gaske sedai ba shida girma sosai amaryar tashi me suna Aisha tayiwa malam adamu tar ba me kyau. Bayan y'an watanni Allah ya albar kace su ,da samun cikin Humaid cikin Aisha yasami gata sosai bayan wata ,tara da kwana goma Allah ya albar kacesu da samun k'aruwa kya'kyawan yaro me farin jini ya taso cikin gata da nuna kulawa ,kwatsam tana yaye Humaid se cikin jalal Allah yara bata da cikin lpy anyi hidima sosai tundaga lokacin aihuwa ta,tsaya mata . *_BACK TO STORY*_ Bafula tanin ne ya d'auko jar, kar ,ruwan shi ya shek'a mata duka a jiki ware idanu tayi kana tace ,wai shin idan mutum ya mutu yana dawowa ne bafula tanin ne ya dube ta kana yace tunda kinga yanzu kindawo ba. Shirin muguntar da zata yiwa bafula tanin takeyi sandar ,da ya buga mata ,ta d'auke ta ruga a guje . Shikuwa bafula tani basan gidan su Ladidi ba yaro ne yazo wu cewa kiran shi yayi kana yace kasan gidan su Ladidi¿" yaron ,ne ya d'aga kai ,kana yace babu nisa ai bafula cewa ya yi to don Allah zoka ,rakani . Barin shanun yayi suka nufi gidan su Ldidi yaron,ne ya shige cikin gidan ya diko ya samu tana shara gai sheta yayi kana yace ana sallama da Ladidi yadiko saboda jin dad'in yar tata zata fara zuwa hira ta ce kace gatanan fitowa . Yaron ,ne Yakoma ya gayawa bafula tanin wai gatanan zuwa . Ladidi ce ta fito daga d'akin yadiko tasha kwaliya in kagan,ta kace sabuwar aljana washe hak'ora tayi kana tace yadiko nayi kyau ¿" Yadiko ce ta jin ,jina mata ,kana tafara yimata kira ,ri. Kaga yar gidan yadiko ,washe bakin ta kumayi tana dariya. Lek'awa tayi dan taga me sallamar hango shi tayi ,yana ta dunk'ule hannu kamar me shirin kai naushi . K'ara mai da hanka linta tayi gurin sauraran abin dayake cewa jitayi ya na fad'in wlh tana fitowa zan ,zuba mata naushi . Itako Ladidi jin haka yasa ta koma gida yadiko ce ,tace har kin dawo ¿". A, a Ladidi tace kana ta shige d'an k'aramin d'akin ta ,,ta d'auko sandar bafula tanin ta dawo ta la6e kusa da inda yake zaune seda ta dede,ci ya juya baya ai kuwa ta d'aga sandar ta sheme shi fad'uwa k'asa yayi ita kwa Ladidi gaba ta k'ara ta barshi ,shida sandar shi a gurin yakasa tashi yana ta ihu. Tana cikin tafiya ta ci karo da wasu samari su biyu . Tana ganin su ta ,tuno inda ta, ta6a ganin su Humaid ne shi,da Jalal sun fito kewaye . *LADIDIN ƘAUYE.* _funny & love story._ *_Labari mai ban dariya haɗi da faɗa karwa_* *NA* *ZAINAB HABIB* _{MOM ISLAM}._ *MARUBUCIYAR* *ZAINABU ABU* *AND NOW* *LADIDIN K'AUYE* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *Episode: 5_6.* ____Humaid yasa shadda fara shi kuma jalal k'ana nan kaya ne a jikin shi Ladidi ce ta rik'e baki shagon da take kusa dashi ta shiga kana tace "dan Allah me manja samin a hannuna me manja ne ya dubeta kana yace "ke baki da hankali ko¿ LADIDI ce ta dubi me manjan kana tace "zaka ga aikin masu hankali roba ta hango a can waje zuwa ta yi ta d'auko robar shidai me manja yana kallon ta be ankara ba ta dumbula robar cikin manja . Me manja da yaga barnar da LADIDI tayi mai mik'ewa yai kana ya nufo ta da niyar kai mata mari. Ya d'aga hanu ze mare ta yaji an wanke mai fuska da manja sakinta yai kana ya nemi gurin zama . LADIDI kuwa ganin haka ta kuma dum bular manjan tayi gaba . Hango su Humaid tayi a gindin wata bishiyar mangoro suna hutawa . A hankali ta tako kana ta zagaya ta bayan su inda bazasu ganta ba saboda bishiyar k'atuwa ce . Juye manjan tayi a rigar Humaid ta baya sunata hira basusan abinda ke faruwa ba a jiye robar tayi a gefe . Hango cinnaku tayi da yawa d'auko biyu tayi tasawa Humaid a dede gurin zaman shi kuma d'auko biyu tayi kana tasawa Jalal a daidai saitin da ya zauna. Tashi tayi taje wani shagon da ake siyarda yar bebi jitayi anata ihu Humaid ta hango yanata tsalle shima jallal d'in tsalle yakeyi a tak'ai ce dai babu me temakon d'an uwansa. Sun rasa inda za suyi aikuwa suka zuba a guje . Kamar mahaukata Jalal ne yace "Humaid wlh bayanka manja . Zaro ido Humaid yayi kana yace "kai k'yaleni bata manja nakeyi ba. Mutane sa kallon su suke ta famanyi, ita kuwa LADIDI barin gurin tayi dan karsu ganeta da k'yar suka gane hanyar gidan malam Adamu saboda zuwansu na biyu kenan . Da gudu su ka shige cikin gidan inna hauwa tanajin an shigo gidan da gudu bata tsaya ganin kosu waye ba itama ta ruga d'akinta da gudu. Su Humaid ne suka shige d'akin da malam ya basu wanan na ihu wancan na ihu se zuwa can anjima ya lafa musu . Humaid ne ya hau tattaro kayansu yana had'awa guri d'aya jalal ne yace "Humaid me zakayi da kayannan . Humaid ne ya kalli jalal kana yace "insha Allah gobe zamu bar wanan k'auyen . Jalal ne ya tuna da gudu da suka dinga kwasa ya kyalkyle da dariya . LADIDI ce ta fito d'auke da tiren tuwo da miya malam adamu ne da malam musa suna zaune suna hira kasa kunne tayi taji suna cewa ai bak'in gidana gobe zasu tafi . Tsalle LADIDI ta buga kana ta je gurin kayan wasan ta kusa da bishiyar kuka . Dakin YADIKKO ta nufa samun YADIKKON tayi tana sallahr isha I . Fitilar d'akin ta d'auko kana ta koma gurin kayan wasan . Farar k'asa ta d'auko taje kan dutse ta dan dak'ashi seda yayi laushi. Ta kwashe shi a leda d'akinta ta nufa mudubi ta samu . Ta lakato mai me yawa ta shafa a fuskarta ta d'auko farar k'asar da tadaka shima ta goga a fuskarta, tunawa tayi ai batasa kwallin ba d'auko kwalkin tayi ta zana baki a bakinta takuma zazzana a duka fuskarta kayanta da suka yayyage ta d'auko . Riga tasa me yagaggen hannu se wandon atamfa shima ta gwuiwa ya yage . Dan k'aramin gyalenta ta d'auko ta kuma nan nad'ashi a kanta . Duk wanda yaga Ladidi to ze d'auka aljana ce saboda ba lallai ka gane taba . YADIKKO ce keta k'wala mata kira amma tana ji taki kulata . Kuma lek'awa kofar gidan nasu ta yi hango su baban ta da malam adamu suna tsaye da alamu baban nata gida ze shigo shikuma malam adamu zashi masallaci ya kwana . Wurga sandar ta tayi kana ta dura ta katanga . Tunda tafara tafiya bata had'u da kowa ba ta kusa isa gidan malam adamu ta had'u da wani mutumi me tallan tsire yana ganin ta . Ze ruga da gudu kenan Ladidi ta nunashi da sanda tace "wlh ko ka tsaya ko kuma yanzu inkaika gurin baba ifiritu me tsire yaji za,a kaishi gurin aljani ya dur k'usa har kasa ya ce ku kuke ganin mu ba mu muke ganin kuba dan girman Allah kuyi hakuri LADIDI ce ta zaro jajayen idanuwan ta kana tace "Zamu kyaleka amma da sharad'i me tsire ne yace "kome kukeso zan Baku indai zaku barni da raina da lpy . LADIDI jin hakan ta dubeshi kana tace "tashi ka bud'emin wannan kwanon . Me tsire na rawar jiki yaje ya bude kwanon ya mik'owa LADIDI tsire ne aciki tsinke biyar . Kwashewa ta yi duka ta had'esu guri guda tana tafiya tana ci shikuwa me tsire tunda yaga tayi nisa ya ruga da gudu yabar kwanon a gurin. Kafin ta k'arasa gidan su malam adamu k'arfe 9 tayi kowa ya kwanta suma su jalal sun gaji saboda gudun da suka kwasa d'azu. Taci sa,ar gidan a bud'e yake tunawa tayi da malam adamu a masallaci ze kwana kai tsaye d'akin nashi ta nufa lek'awa tayi ta windown d'akin suna kwnce suna danna waya. Basu ankara ba sukaji durowar mutum da farko hankalinsu be tashi ba seda suka hango farar fuska kamarta aljanu . Dakin nasu babu haske sosai . LADIDI ce taje bakin k'ofar d'akin tasa sak'ata tanata zaro jajayen idanuwan ta . Humaid tunda ya firgita ya koma kusada jakar kayan su ya 6uya shiko jalal dur k'usawa yayi yana bata hakuri . LADIDI ce ta dubi Humaid kana tace "kai bakan manya bako to yau karyarku ta kare . Rik'e hanun juna sukayi suna matsawa da baya da baya Humaid ganin abin yakeyi kamar a mafarki d'ago kan daza suyi suka hango nama a hanunta kurma ihu suka dingayi . Humaid tsabar tsorata fitsari yayi a wando shi kuma jalal yaje yin tusa ya had'o da kashi . Ladidi ce ta lura da abinda sukayi tace "kowannen ku ze kar6i wanan naman yaci Humaid ne yace "Ai Allah yayi kune dan Ku temaki mutane amma kunzo zaku cutar damu . LADIDI ce ta daka musu tsawa kana tace "tunda bazakuci naman ba to Ku cire wandunan Ku kai da kayi fitsari ka tsotse kai kuma me k'aton kai dakayi kashi kaci kad'an . Zaro ido sukayi kana suka fara "dan Allah kuyi hak'uri tsawa takuma daka musu tace Ku za6a yaji ta hango a gefen ta a kulle a leda ajiye musu a gaban su tayi ta finciko nama a tsinken tsiren tace to sekun shanye yajin nan duka . Humaid yana kuka yace Jalal gara musha yajin. Dukufa shan yajin da da d'an guntun naman sukayi idanunsu yayi jajur ga kuka ga shan yaji . Suna tsayawa zata daka musu tsawa inna hauwa ce tajiyo tsawar. Fitowa tsakar gidan tayi bata gane ta ina akeyin tsawar ba seda ta jiyo k'arar bud'e k'ofar d'akin malam adamu wanda su Humaid suke ciki . Kafin ta ankara taji an turo ta d'akin su Humaid juyowar da zatayi suka had'a ido da LADIDI . Inna hauwa ce ta kurma ihu tana salati tana fad'in dama ashe aljana ce tashigo mana gida shine bata k'arasa maganar ba taji LADIDI na rawa . LADIDI ce ta zaro musu ido kana tace rawa zakuyi ina hauwa ce ta zaro ido kana tace "kuyi hakuri kusan mu bil adama bamu da k'arfi . LADIDI ce ta d'aga sandar ta zata buga musu sukasa ihu rawa sukeyi kamar mahaukata inna hauwa ta dage se rawa take kwasa. LADIDI ce tace "jibeku dame k'aton kai dame k'aton hanci. Kekuma yar tsohuwa me k'aton goshi ki k'ara shiga abinda babu ruwanki . Inna hauwa ce ta had'a hanuwan ta biyu tace "kiyi hakuri bazan sake ba . LADIDI ce tace musu "kowa ya rife idanu kuma karku bud'e har senace inkuma ba haka ba to zaku tsinceku a duniyar aljanu . Kafin ta gama ,magana har sun rife ido . Ficewa tayi a d'akin ta nufi d'akin inna hauwa ......✍🏽✍🏽✍🏽. *Mom Islam✍🏽.* *LADIDIN K'AUYE* _Funny & love story._ *_Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa_* *NA* *MOM ISLAM* *ZAINAB HABIB*. *MARUBUCIYR :* *ZAINABU ABU* *AND* *LADIDIN K'AUYE* *BISMILLAHIR RAHMANIR _RAHIM* *Episode: 7_8* _____kwanuka tagani wanda akaci abinci wani kwano ta hango a rufe bud'ewa tayi abinda idanunta suka hango ya bata mamaki sosai. K'ara bude ido tayi nama ne soyayye cike a kwanon leda ta hango ta d'ibi iya san ranta ta fice a gidan . Tana fita suka bude ido sunata mamakin aljanar da suka gani . Inna hauwa ce tace "jalal zoka rakani d'aki jalal ne ya zaro ido ya dubi inna hauwa yace "walh inma zaki tafi ki tafi babu inda zani. Inna Hauwa ce tayi a uzubillahi ta ruga d'akinta da gudu . LADIDI ce ta koma gida duk mutanen gidan sunyi bacci lalla6awa tayi ta shige d'akinta ta kwanta babu maganar sallah . Washe gari bayan sallar asbah Humaid ya fito da jakar kayan su ko wanka basu yi ba malam Adamu ne ya dube su kana yace "badai tafiya zakuyi ba da wanan duku dukun safiyar gari be gama haske ba. Jalal ne yace "wlh mun shirya inna hauwa ce ta fito da carbi a hannun ta ,tana lazimi ta ce "malam ai dole suce zasu tafi, malam Adamu ne ya nemi guri ya zauna kana yace "meke faruwa.¿ Humaid ne ya nisa kana yace "wlh malam aljana ce tashigo gidannan jiya da daddare tadin ga yimana mugunta. malam Adamu ne ya jinjina lamarin ya ce to shine dalilin tafiyar Ku da wanan safiyar . Jalal yana gyara takal minshi yace "insha Allah yanzu zamu wuce jos . Ina hauwa ce taje d'auko kwanon da ta zuba soyayyen nama ganin naman ciki befi biyar ba yasa ta rafka salati har su jalal suna rugawa da gudu . Malam Adamu ne ya lek'a d'akin kana yace "meke faruwa ne¿ inna hauwa ce ta dubi malam da alamun damuwa tace "kaga naman da kasiyo wlh ragowarshi kenan malam be nuna dumuwar komai ba yace "karki damu kawo a kai musu . Barinje in siyo musu lemon kwalba ficewa yai . Ba dad'e ba se gashi ya dawo da lemon kwalba guda hud'u . Inna Hauwa ce ta kai musu d'aki suna zaune suna jiran lokacin tafiyar su yayi . Inna Hauwa ce ta mik'a musu had'e " da nama kar6a sukayi ci sukeyi da sauri sauri nan danan suka gama . Fitowa sukayi rataye da jaka a kafad'ar su inna Hauwa ce tayi musu Allah ya tsare. Humaid tsabar ya matsu su tafi harya shige mota Mallam Adamu ne ya fito d'auke da tsaraba a hannun shi bud'e bayan motar Jalal yayi ya shige motar suka d'auki hanya se jos. Washe gari Malam musa ya tashi babu lpy duk iya gigiwar LADIDI seda tayi sanyi ganin jikin mahaifin nata kwance yake se nishi yakeyi kamar me ciwon zuciya YADIKKO da jikinta yagama yin sanyi . Tanaji kamar Malam musa baze tashi ba tari ne ya sark'e mai wuya . Yafara k'ok'arin magana sunan YADIKKO ya kirawo wato Aisha amsawa tayi da na,am Malam yunk'urawa yayi . Kana yace dan Allah ki kula da LADIDI kinga y'a mace ce tunda Malam musa yafara magana YADIKKO ta fara hawaye . Tari ne yakuma sark'eshi YADIKKO ce ta umarci LADIDI ta kawowa mahaifin ta ruwa bayan ta kawo yasha . Yak'ara da cewa na bawa Malam Adamu LADIDI YADIKKO ce ta rushe da kuka ta aika LADIDI ta kirawo Malam Adamu ba,a jima ba se gashi sun dawo tare da gudu Malam Adamu ya k'araso ya rik'e hannun Malam musa jiki a sanyaye yace "sannu Malam . Amsawa yayi da yauwa ga amanar LADIDI nan nabaka jikin Malam Adamu yakuma yin sanyi sosai ya daure yace "insha Allah zakaji sauki . Murmushin yak'e Malam musa yayi daga nan ya kirawo LADIDI matsowa tayi kusa dashi ya kamo hannunta ya rik'e gam daganan yafara shak'uwa . Kulli nafsin za,ikatul mauti .. Allah yayiwa Malam musa rasuwa kowa ya jimama mutuwar Malam musa . YADIKKO inta kalli k'ofar Malam musa setaji hawaye ya zubo mata . LADIDI kuwa takoma kamar mutuniyar kirki bata fad'a bare neman tsokana duk wanda ya tsokaneta bata kulashi. Bayan anyi sadakar bakwai kowa ya watse YADIKKO ta kwanta rashin lafiya har asibiti Malam Adamu ya kaita amma an rasa gane ciwon dake damun YADIKKO . Kulum cikin ciwo take LADIDI kuwa tunda taga YADIKKO na ciwo shikenan ta karaya tana ganin kamar itama zatabi mahaifinta ne a kulum YADIKKO in suka zauna da LADIDI basayin wata magana kamar tadinga cemata ki rik'e mutuncinki a matsayinki na y'a mace, LADIDI na kuka tana jin YADIKKO. Ciwon YADIKKO ne yatashi sosai da gudu Ladidi ta tafi domin kiran Malam Adamu YADIKKO na d'agawa LADIDI hannu akan tadawo ina LADIDI ta kid'ime bata ankara ba tafice da gudu Malam Adamu tasamu a zaune shida inna Hauwa suna hira ganin ta cikin wanan yanayin yasa su mik'ewa a zabure LADIDI tana kuka tana cewa su Malam Adamu YADIKKO na zata mutu kuzo duk wanda yaga LADIDI a lokacin komi rashin imanin shi seya tausaya mata . Kafin inna Hauwa ta d'auko gyale ta fito har Malam Adamu ya isa gidan su LADIDI salati yahau yi ganin YADIKKO rai yayi halinsa . Inna Hauwa ce suka k'araso itada LADIDI Malam Adamu na ganin su ya juya fuska yana sharar kwallah . Tunda LADIDI taga haka itama ta zauna ta rafka uban ihu tareda birgima a k'asa babu wanda yayi yunk'urin hanata kukan mutane ne suka fara shigowa masu kuka nayi masu salati nayi masu adu,a nayi hak'ik'a mutuwar YADIKKO ta girgiza mutane sosai . Tsakaninsu da mijinta Malam musa wata d'aya bayan anyi sadakar uku inna Hauwa tasa LADIDI ta kwaso kayanta ta dawo gidanta da zama duniya tayiwa LADIDI kunci kwata,kwata batajin dad'in zaman duniyar. Bayan sadakar bakwai aka rufo gidan da kwad'o tunda LADIDI ta dawo gidan inna Hauwa takoma shiru shiru ko abinci takeso bata magana sedai in and'auko anbata. JOS tunda su Humaid da Jalal suka koma garinsu kowa ya koma bakin aikin shi Humaid aiki yakeyi a hospital d'in dadynshi daya bud'e mai , shikuma Jalal aiki yakeyi a ma,aikatar mahai finshi. Wato saida kayayyakin mata na sawa dana maza da sauransu sun maida hankali akan sana,ar sosai . Dady ne zaune a dining suna breakfast shida su momy da Humaid da Jalal kirane ya shigo wayar dady d'auka yayi kana ya kara a kunnenshi jinayi yace innalilahi yaushe ¿"dady ne ya ajiye wayar yana jimama rasuwar Malam musa da Aisha wato YADIKKO. Jalal ne yakalli dadyn nashi kana yace "badai iyayen LADIDI bane suka rasu¿ daday ne ya amsa da cewa dama sunada y'a LADIDI ne ? Jalal ne yace inadai kauyen da muka jene to tabbas iyayenta ne abokin Malam ne dadyne yace tabbas sune momy ce ta fara tambayar dady kwatance yayi mata inda zata gane adu,a sukayi musu daganan kowa ya wuce gurin aikin shi. ★ ★★ ★ ★ ★ Bayan shekara uku LADIDI tana da shekara 14 years tayi tsayi tayi k'iba farinta ya k'ara fitowa ga k'irjinta yafara cika tafiya takeyi tana waka ta hango me tallar k'uli,k'ulli tana zaune a gindin bishiyar kukar dake k'ofar gidan Malam Adamu da tazamo gurin zamanta tun ana hanata har anzo ana barinta. Me k'uli _k'uli ne ya kawowa Ladidi ,'d'agawa tahauyi tana cewa nawa nawa yaro me tallan k'uli yace "ashirin,ne Ladidi ce tace "za6omin d'auri d'aya kuma k'atoto mik'o mata yaron yayi kunce ledar tayi tanaci tana jefa k'afa yaro ne yagaji da zama yace ba bani kud'in kafin ya k'arasa Ladidi ta buge bakin yaron tace tunda har katambayeni wlh bazan bada kud'in ba kuka ya hauyi yaron tasowa tayi ta kama kunnenshi ta murd'a seda ya kwala k'ara ta sakeshi kana tace daga yau ka karayimin rashin kunya kagani.....✍🏽✍🏽✍🏽 *MOM ISLAM✍🏽✍🏽✍🏽.* *LADIDIN K'AUYE* Funny & love story. *Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa* *NA* *MOM ISLAM* *ZAINAB HABIB* *MARUBUCIYAR:* *ZAINABU ABU* *AND NOW* *LADIDIN K'AUYE* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *Episode:* 9_10 ______malam Adamu ne yakira dadyn su Humaid a waya akan cewar Ladidi zata dawo gurinshi saboda tasami ,ilimi sosai"beyi musuba yace ranar lahadi se su Humaid suzo su d'auketa malam adamu ne yace da muna shirin kawota gobe nida Hauwa dady ne yace to ai babu damuwa duk d'aya ne sekun so Allah yakawoku lpy daganan sukayi sallama". Inna hauwa ce ta ,tattaro wa Ladidi kayanta had'i da bata kud'in sabulu akan tayi wanki gobe zasu wuce birni aikuwa Ladidi jin haka ta fara murna tana tsalle ta kar6i kudin tafice siyo sabulu tana cikin tafiya ,ta had'u da k'awarta tana siyarda d'anwake gashi Ladidi najin yunwa k'awar ce tace Ladidi barin zuba miki d'an waken saboda tasan inta wuce Ladidi zata iya 6aro da robar d'an waken". Fara zubawa tayi Ladidi tace ke barshi haka yarinya gobe zamu tafi birni mushi kayan d'ad'i kawar Ladidi ce ,tace nima inason zuwa birni sedai bamuda y'an uwa a birni . Bayan ta siyo sabulun tafara wanki seda tagama duka sannan ta zauna tana jira su bushe ta ninke ". Washe gari bayan sunyi sallahr asbh malam adamu yashigo yace su shirya da wuri saboda wuyar mota. K'arfe goma suka tafi tasha sunyi sa,a wata mota bata cikaba suka shige malam adamu yabiya kud'in motar suka d'auki hanya zuwa jos". Tunda suka shiga mota Ladidi ta hango wani k'aton arne yana cin Apple lek'enshi takeyi tana lashe baki had'a ido sukayi ta sunkuyar da kai a karo na biyu takuma d'ago kai tayi sa,a shima yad'go suka had'a ido ita kuma Ladidi ganin yanata kallon ta mugud'a mai baki shikuwa yana ganin haka ya bige bakin inna Hauwa ce ta ce kaikuma metayi maka dazaka bigi yar marainiyar Allah . Da hausar da bata game bakinshi ba yace wanna yariya batada hakali Ladidi ce ta ,tuntsire da ,dariya shikuwa yaji haushin wanan dariya ana zuwa gurin sojoji ya bawa Ladidi 6awon gyad'a yace tazubar mai Ladidi bata ta6a shiga motar da zatayi tafiya me nisaba aikuwa ta watsa 6awon gyd'ar kusada wani k'aton soja suna ganin haka suka tare motar su Ladidi suka ce kowa ya fito da kuma wacce ta watso 6awon gyad'a ". Ladidi ce tahau zaro ido saboda tana tsoron masu bakin kaya malam Adamu ne yace mekuma mukayi arnen ne yace daughtern kuce ta zubo bawon gyada malam Adamu ya bud'e baki yace ba ita bace". Koda zamu fito bataci gyad'a ba kuma babu komai a hannun ta Ladidi ce ta nuna arnen tace wlh shine yabani yace in wurgar sukuwa sojoji sun rasa wazasu kama sukace Ladidi itada Arnen su fito suyi tsalen kwad'o . Sojanne ya k'araso kusada su kana yace ku za6a ko tsallen kwad'o ko ayi muku bulala Ladidi ce ,tace wlh gara ayimin bulala tunda wanan k'aton arnen yajamin bulala biyar sukayi mata lafiyayyu malam Adamu bashida ta cewa kar a had'a dashi yaja baki yayi shiru direban motar sune yaketa masifa . Ladidi ce tashige mota tanata kuka shikuwa arnen yak'i zuwa ayimai d'ayan sojan ne ya nuno arnen da bindiga da gudu yazo ganin sun saita kanshi. Tunda aka fara bulalar yafara kuka yana basu hakuri ,ita kuwa Ladidi se dariya takeyi. Malam Adamu ne yace wlh da tuni mun isa bayan an gama bulalar suka shige mota kowane fasinja yana fad'ar albarkacin bakinci har suka iso well come to plateau . Kowa ya sauka a mota Ladidi tak'i fitowa seda ta ciro wata allura a kanta lokacin su malam Adamu sun tari adaidaita sahu zasu shiga ta sokawa arnen ta shige da gudu ". Sun isa 6ukur park G.R.A anan ne anguwar su dadyn Humaid take wato alhaji abdullahi tsaya sukayi a bakin get d'in megadi ne ya lek'o kana yace daga ina kuke malam Adamu ne yace daga kano muke ni yayan mai gidannan ne seda megadi yakira a waya tukun yabarsu suka shige". Tun daga k'ofar gidan Ladidi ke kallon tsarin gidan tunda tazo duniya bata ta6a kallon kyau da tsarin gida irin wanan ba sekace baza,a mutu ba inna Hauwa ce ta janyo mata hannu suka shige domin malam Adamu yarigasu shigewa. Da sallama suka shigo itada inna Hauwa k'asa Ladidi ta zauna ina Hauwa a kujera malam Adamu shima yana kujera suna jiran mutanen gidan wata wata mata ce fara sol da ak'alla zatakai shekara arba,in a duniya sanye take da wani dakakken leshi me duwatsu tafiya takeyi kamar wata sarauniya ta iso gurin su inna Hauwa ta nemi kujera ta zauna . Inna Hauwa ce ta fara gaida hajiya amina hajiya amina batasan inna Hauwa ba amma ganin malam Adamu yasa tagane matar shice bayan sun gaisa hajiya amina ta gaida malam Adamu Ladidi kuwa ta ,tafi a kallon palon dan batasan me akeyi ba seda inna Hauwa tace Ladidi baki iya gaisuwa bane ¿". Ladidi ce,tace ina wuni hajiya amina tace lpy daughter ya kike shiru Ladidi tayi taci gaba da kalle kallen ta . Hajiya amina ce ta k'walawa yar aikinta me suna ummi kira dagudu ummi ta k'araso ta durk'usa a gaban hajiya amina. Cewa tayi kikawowa su malam abinci amsawa tayi da to hajiya ta mik'e ta nufi kitchen jollof d'in taliya ce wace taji kayan lambu sai k'amshi take zubawa da hollondia yogurt me sanyi ta d'oro akan turai ta kawo musu mik'awa malam Adamu tayi takuma mik'awa inna Hauwa nata ta d'auko wani ta mik'awa Ladidi nata da rawar jiki Ladidi ta k'ar6e abincin ta cire cokalin hajiya amina ce ,tace daughter kisa cokalin mana Ladidi ce tace a a wlh da hannu ma ya nak'are bare nasa cokalin. Bayan dare yayi suyi sallah hajiya amina ta nunawa inna Hauwa d'akin da zasu kwanta suna shiga d'akin Ladidi ta d'are gado tanata tsalle tana cewa wanan aba kamar burodi mu agarinmu babu wanan aba me laushi haka inna Hauwa tana jinta bata kulataba. Inna Hauwa ce takira sunan Ladidi tsayawa tayi da tsallen tace na,am inna kinsan me nakeso dake Ladidi tace a a". Kinga kindawo birni da zama tsalle Ladidi tayi tana murna inna Hauwa ce ,tace kirik'e mutuncin ki dan Allah kinga ke marainiya ce kar ,rud'in duniya yasa ki zubda tarbiyarki to Ladidi tace". Washe gari su Humaid sun shigo part d'in momy take gaya musu suje su gaida matar malam Adamu jalal ne yace ai tun jiya muka gaisa da malam Adamu sedai ,inna bari muje momy ce tace musu amma zaku shigo kafin kutafi ko Humaid ne yace eh insha Allah momy. Direct dakin da momy tace musu inna Hauwa na can suka nufa sallama sukayi ,inna tana kan sallahya tana lazimi suka shigo gyaran murya tayi musu ,bayan ta shafa adu,ar ne suka fara gaisawa inna tace jiya tunda mukazo bamu had'u dakuba Humaid ne yace wlh inna aiyuka ne sukayimana yawa shiyasa inna ce ta sanya musu albarka suna cikin hira sega Ladidi nan tafito daga toilet da gudu batama lura dasu Jalal ba tahau jikin inna tana ihu Humaid ne yace inna a ina kika samo wanan yarinyar Jalal ne ya zaro ido ganin kamar yarinyar da tabige k'afar Humaid ce ,a zabure Jalal ya mik'e yadubi Humaid kana yace wlh brother wanan yarinyar ce da ta addabi mutanen k'auyen su d'ago kai Ladidi tayi suka had'a ido da Humaid . Humaid ne yazaro ido yace yaushe zaku tafi ne inna¿" inna Hauwa ce ta washe baki ,kana tace ni da malam yau zamu wuce ita kuma Ladidi anan zamu barta . Kwata ,kwata Ladidi batasan gidan su Humaid suka zoba sai yanzu , Humaid ne ce munshiga uku "inna Hauwa ce ta dubi Jalal da yakasa cewa komai se Humaid ne da keta salati duban su tayi kana tace wanan yarinyar yar uwar kuce dan Allah ku, kula da ita sosai duk cikin su babu me magana suka mik'e suka wuce d'akinsu . Dayake d'akinnasu a had'e yake Jalal ne yadubi Humaid yace wlh brother ankawo mana bala,i cikin gidan mu.....✍️✍️✍️ Mom Islam ce ✍️✍️✍️ *LADIDIN K'AUYE* Funny & love story. *Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa* *NA* *MOM ISLAM* *ZAINAB HABIB* *MARUBUCIYAR:* *ZAINABU ABU* *AND NOW* *LADIDIN K'AUYE* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *Episode:* 11_12 _____washe gari ,inna Hauwa ta shirya malam Adamu ya aiko jalal ya kirawo ta dan bayason suyi tafiyar dare shigowa inna Hauwa tayi ta sami guri ta zauna dady ne shida malam Adamu suna hira dady ne yace ina Ladidin inna Hauwa ce ta kwalawa Ladidi kira segatanan da gudu ta k'araso dady ne yace sannu baiwar Allah ina kwana tace bayan ya amsa ne malam Adamu yadubi Ladidi kana yace yanzu ,zamu tafi amma inna tagaya miki anan zaki sauna ko ¿"Ladidi tana murna tace eh ta gayamin malam Adamu ne yafara yimata nasiha da fad'a akan tarbiya dakuma tayiwa su dady biyayya to tace musu daganan suka mik'e Humaid ne da Jalal suka shigo suka durk'usa suka gaida malam Adamu shida dadyn su ". Mik'ewa sukayi sega momy nan d'auke da wata leda mekyau ta mik'awa inna Hauwa godiya inna Hauwa tayi mata daganan suka fito waje" Ladidi ce ,tace inna yaushe zaku dawo"ina Hauwa ce tadube ta da alamun tausayawa tace karki damu zamuzo dubaki Ladidi bata nuna 6acin raiba saboda tana son zaman birni "Humaid ne yatada mota suka shiga dady ,yaciro dubu goma yabawa malam Adamu godiya malam Adamu yadinga yiwa dady daga nan suka fice daga gidan suka zarce tasha suna zuwa suka shige mota se kano. Ladidi ganin babu wanda tasani acikin gidan yasata yin sanyi gashi yunwa takeji tarasa inda zatasa kanta tagumi tayi seta fara tuno inna Hauwa da acan k'auyen,nne da ko tuwo ne taci sau biyu su nan idan aka bawa mutum shayi da burodi abincin rana se k'arfe d'aya na rana" dady ne yazo wucewa yaga Ladidi a kan dakalin wucewa palon tazuba uban tagumi "dadyne yadube ta kana yace Ladidi meke faruwa ne Ladidi da tarasa abinda satace seta k'ak'alo karya tace dama narasa d'akin dazan shiga ne dady ne yarik'e hannunta ya nuna mata d'akin da suka kwana jiya yace nanne d'akin ki ,kinji to tace mai shikuma yafice daga part d'in ,nata. Tunda tashiga taji kamar an karo yunwar ne juyi tadingayi a katifa yar aikin gidan ce wato ummi tashigo da tiren abinci doya ce da miyar k'awai se lemon gora fanta da sauri Ladidi ta diro daga kan gadon ta kar6i abincin ita ko ummi mamakin ci ,irinna Ladidi takeyi " ko wanke hannu batayi ba tadinga tura doyar tana kur6ar ruwa seda taciye duka sanan takoma kan miyar kwan tana ta lasa tarasa miyar menene amma dai koba komai tayi dad'i tak'yar ta mik'e tanufi bayi kashine ya matseta seda tashiga ta tuna tunda suka zo batayi kashi ba seyau lek'a bayan gidan tadingayi kozataga masai "ina sewata kwalba fara mekamada kujera sekuma baho a gefe shima na kwalba . Ihu ta kurma saboda kashi na neman zubo mata da gudu momy tashigo d'akinnanta taduba bata ganta ba k'wala mata kira tayi momy ce taji Ladidi takuma kurma ihu k'ofar toilet d'in ta ,tura ganin Ladidi a zaune tana ihu tayi" k'arasawa kusada ita tayi kana tace Ladidi meke faruwa tundaga room d'ina najiyo ihunki Ladidi batasan room ba sedai cewa tayi kashine ya matseni wlh na kusa yi a wando momy ce ta rik'o mata hannu ta mik'e nuna mata inda zata zauna tayi Ladidi gani takeyi kamar zata fad'a ciki se zaro ido takeyi kamar an tare kwarto. Yau watan Ladidi daya a yaune dady ,ya samowa Ladidi makarantar primary a class 5 aka sata kasancewar sunje anyi mata interview tanada basira bazatayi wuyar d'aukar karatu ba "tunda tafara zuwa makarantar bata shiga sabgar kowa ,wata rana suna zaune a class teacher yashigo yace a fad'a mai masu ,surutu kowa a class d'in Ladidi yanuna kasancewar tunda tashigo school d'in ba,a ta6a kawo k'ararta ba ai kuwa malamin ya kamata yayimata duka sosai seda yafasa mata farcen baban dan yatsa" kuma tasha alwashi seta rama tunda yanaso tadawo Ladidin k'auye . K'arfe hud'u na yamma dady ,yakirawo Humaid yana gurin aiki akan yaje ya d'auko Ladidi a school ranshi ba k'aramin 6aci yayi ba amma babu inda ya iya dole ya ajiye abinda yakeyi yaje d'aukarta babu kowa a school d'in kowa yatafi gida se teachers dasuke office suna ta ttaunawa tana hango motar Humaid gabata yashiga bugawa shigewa baya tayi seda yatada motar ya daka mata tsawa yace ubanwaye drivernki fitowa tayi saboda yunwa takeji dukda anbata kudin break amma ,a banza. Tun kafin takoma gida take ciwon ciki sosai tarasa inda zatasa rayuwarta Humaid ,da yalura da halin da take ciki seya rud'e ko magana bata iya yi hospital d'inshi ya wuce da ita wani d'aki ya kaita da babu kowa aciki se karar Ac daketa bada iska yaje siyo mata abincin turo k'ofa yayi yaga jini yana zuba zaro,ido yayi yadubi Ladidi da ko motsi batayi seda ya,yayyafa mata ruwa kana ya murd'e bakin ,nata ko kulashi batayi ba dan ita kad'ai tasan wahalar da takesha alura yayi mata daganan yafice d'auko mata magani wayarshi ce take ringing dady yagani d'agawa yayi dadyne yace ina Ladidi Humaid cikin jin nauyin maganar da zegayawa dady yace gatanan a hospital zaro ido dady ,yayi kana yace meke faruwa da ita Humaid ne yakasa yiwa dady bayani yace am dady in momy na kusa please kabata wayar dady ne yahau banbamin fad'a kana yace ubanme kayi mata dabazaka fad'amin ba itako Ladidi hatta jinin da yazuba a jikinta duk bata sani ba tunda tana farfad'owa daga suman datayi yayi mata allurar bacci . Dadyne rai a 6ace yamik'awa momy Humaid ne yace momy zakizo hospital d'innne¿" eh momy tace gamunan nida dadynka"hijab momy ta d'auko zuka nufi hospital d'in Humaid itada dady da isarsu direct office d'inshi suka wuce dady ne ya nannad'e malun malun din'shi yace to gamu maunzo nace uban me kayiwa yar mutane momy ce ,tace katsaya a tambayeshi mana kanata fad'a Humaid dai yakasa magana dan yana ganin kamar inya cewa iyayenshi Ladidi tafara period zasuce bashida kunya" sunkuyar da kai k'asa yayi kana yace 6atan wata tafara kuma yau d'inan momy ce tadubi Humaid tace to wanan shine abin 6oyewa dady ne yanemi guri ya zauna yace to yanzu tana ina Humaid ne ya mik'e yace kuzo muje d'akin "suna zuwa suka samu haryanzu tana bacci momy ce takalli fuskarta hak'ik'a tayi rama sosai Allah sarki. Momy ce ta ,tambayi Humaid kasiyo mata pad kuwa eh yace kana yabawa momy ledar harda sababin pants yasiyo mata dady bece komai ba yana tsaye yazuba hannu cikin aljihu. Farkawa tayi taga su momy a kanta tuno ciwon cikin datayi ne a mota sekuma taga jini a zaninta zaro ido tayi tafara kuka dady ne suka fice shida Humaid momy ta k'arasa gurinta tayi mata bayani dakuma inda zatayi ta gyara kanta momy tayi mata fad'an sallah akan lokaci " bayan ta gama shiryawa ne momy takira Humaid a waya tace yasiyowa ladidi riga ko doguwa ce "be jima ba segashi da rigar "dayake basuda nisa da masu saida kayayyaki". Ruwan zafi yasa akawomata bayan tafito daga wankan ta kintsa kanta suka nufi gida momy a motar dady suka tafi shikuma Humaid da Ladidi suka tafi tunda suka fara tafiya talura da kallon da humaid yake yimata amma seta basar". *BAYAN SHEKARA DAYA* Ladidi na hango takuma kyau tayi haske tayi k'iba sosai gashi tafara jin turanci kuma tadena wauta irinta yan k'auye " samarine da ita sunkai biyar amma Humaid na ganinsu seyace anyi mata miji "itadai Ladidi batasan hujjar yin hakanba " tagama primary yanzu tana jss 2 komai nata yak'ara baiyana ". Batada abokin shawara inba jalal ba duk wata damuwa tata yasani basa shiri da jalal " wata rana tana cikin tafiya zataje gidan wata k'awarta ta had'u da wani saurayi kya kyawa yana cikin mota ita kuma tana tafiya a k'afa"baya yayi da motarshi yace ya ,yammata ina magana kink'i kulani cigaba tayi da tafiya jitayi ya rik'o hannunta a zabure ta juye dan tunda take babu namijin da yata6a gigin rik'e koda gefen mayafinta ne........✍️✍️✍ ✍️Mom Islam ce *LADIDIN K'AUYE* Funny & love story. *Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa* *NA* *MOM ISLAM* *ZAINAB HABIB* *MARUBUCIYAR:* *ZAINABU ABU* *AND NOW* *LADIDIN K'AUYE* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *Episode:* 13_14 ___durk'usawa yayi a gabanta yace please beautiful ki saurareni wlh tunda naganki naji nasami matar aure ko banyi miki bane Ladidi ce ta yamutsa fuska kana tace bancema haka ba"mik'ewa yayi yace sunanan Amar jitayi sunan yayi mata d'adi sosai Ladidi ce ta fad'amai asalin sunanta wato khadija wow Amar yace daganan yace kozan iya d'aukar ki a mota ,ta eh tace babu damuwa daganan ya maidata gida sunyi musayar number tashige gida mom ce take tambayarta daga ina take cewa tayi daga gidansu yar ajinmu ne naje dubota babu lpy momy ce ,tace to kiyi sallah kici abinci semu shiga kitchen ". Bayan tayi sallah taci abinci ta d'auko wayarta tana duba massage number Amar tagani ya rubuto mata sak'on" kin budewa tayi saboda batason seta fara karantawa momy ta kirata kuma taga sak'on da yawa tana shirin tashi tajiyo kiran momy amsawa tayi ta jona wayar tata a charge ta,tafi kiran direct kitchen tawuce tasami momy tana had'a kayan buk'ata na girki saboda yanzu tare sukeyin girki ummi tayi aure kuma bata nemi yar, aiki ba". Bayan sun gama girkin ta nufi d'akinta ta gyara dan sam batason k'azanta shiyasa komai nata tsaf ,tsaf bayan sallahr isha,I tana shirin karanta massage d'in Ammar sega kiranshi nan yashigo muryarshi me sanyi ce tadaki dodon kunnenta kirari yafara yimata yana wasata godiya tayi mai daganan suka gaisa "rungume fillow yayi ,yace kinsan me khadija ¿a,a tace yaci gaba dacewa wlh jinakeyi ,inama kena rungume ba fillow ba murmushi tayi kana tace to mekakeci naba na zuba ". Dambu yace suka suka sa dariya" tambayarta yayi kinayin whtsapp ne ¿"a,a tace mai Amar ne yace to meyasa¿Ladidi ce ,tace ra,ayina ne hakan shiru yayi kana yace inason zuwa hira yaushe kikeso inzo shiru tayi nad'an wani lokaci kana tace zanyi shawara"Amar ,ranshi ya 6aci amma be nuna mata ba sukayi sallama "bacci ya gagara d'aukar shi se tunanin Khadija yakeyi wato Ladidi yarasa wane irin so yake yimata sona sha,awa ne kokuma so na zuciya se juyi yakeyi "jiyayi mararshi tashiga ciwo yarasa ina zesa kansa yaji dad'i wata babyn shi yakirawo da sukeyin masha,arsu ". *WAYE AMAR* Amar d'a ne ga Alhaji atiku dollars yataso cikin gata da kulawa sam bashida tarbiyar kuma baya tare da iyayenshi a London suke da zama tun mahaifan Alhaji Atiku suna London har aka haifi Alhaji Atiku shikad''ai Allah yabasu shiyasa basa,son lefin Alhajin shiyasa gatan da iyayen Alhaji Atiku suka bashi,shi yabawa d'anshi a ganinshi ,shine birgewa" Amar yaza6i yayi karatu a Nigeria shiyasa yabar iyayenshi yazo Nigeria yana karatu bashida kowa a Nigeria shiyasa yake abinda yaga dama y'an matanshi sunfi a k'irga "yanzu gashi Allah ya had'ashi da Ladidi kuma indai yaso abu to seya mallakeshi yake samun nutsuwa" gashi Allah yad'ora mai yawan sha,awa baya sati beyi sex da mata ba' gashi kya kyawa "wanan kenan. Washe gari bayan Amar yaji sauk'i yakira Ladidi a waya ringin d'aya ta d'aga wayar jin muryarshi tayi wata " iri"cewa tayi lpy Amar najika haka¿lpy yace mata ya nisa,yace beauty kin hanani barci"zaro ido Ladidi tayi 'kamar yana ganinta". Tace nikuma "eh yace kinsani wanka zeci gaba tace momy na kira na bari,inje in dawo katse wayar tayi'ta dafe k'irjinta tunda take Allah beta,6a had'ata da mara kunyar saurayi kamar Amar ba". Yau kwanansu hud'u da had'uwa ,yaune Amar yakira Ladidi a waya ,yake gaya mata, bashi,da lpy " hankalin,ta yayi mutuk'ar tashi tarasa yanda zatayi ta fad'awa momy saboda tanason zuwa gaishe,shi".ganin shiru,shiru "bata zoba yasa,shi neman number ta" wayar nata ringin amma tak'i d'agawa saboda yau Humaid na gida shikuma Jalal yatafi gurin sana,arsa. Ranshi ya 6aci sosai"amma ya,d'au alwashin,shirin dayakeyi a kanta , momy ce ta,k'awala mata, kira amsawa tayi "da,sauri ta'amsa' bayan ta gyara fuskar,ta " tana ganin kamar momy zata gano damuwa shimfid'e a fuskar ta,da sallama tashigo palon momy,samun guri tayi ta zauna"kana tace momy gani . Momy ce ta dubeta ,tace khadija meyasa bakyason fad'amin damuwar,ki "murmushin yak'e tayi kana tace momy wlh bani'da wata damuwa kawai tunanin karatu nakeyi" momy badan ta yarda'ba tace to shikenan kinci abinci kuwa eh tace suna cikin magana tajiyo wayar momy na ruri"tashi tayi taje ta'd'aukowa momy wayar,ta momy ce tace waye yake kira¿"Humaid ne Ladidi taba momy amsa to ki d'aga mana jiki na rawa ta d'aga wayar da sallama jin muryar mai maganar yasa'shi daka mata tsawa ,cewa yayi ubanwa yabaki ,ikon d'aga waya momy na "nakira ba keba rau'rau tayi da idanu momy taga yanayin'ta amma bata ce komai ba yak'ara da kicewa Ummi ta,kawomin abinci to 'tace ta ajiye wayar momy ce tadubi ladidi tace meya,ce miki ¿"Ladidi ce tace wai Ummi ta kaimai abinci momy ce tayi murmushi kana tace to meyasa baki cemai Ummi takoma garin su Ladidi da idan ta yakawo k'awllah tace bakomai momy barin je in kaimai ,momy ce tayi'mata Allah ya shi albarka Ladidi tanajin dad'in wanan kalmar sosai shiyasa takeson momy bata'son 6acin ran'ta . Kitchen ta wuce tazubo mai abincin ta had'o da juice me sanyi ta nufi hanyar da zata sadata da ,d'akinsu Humaid kasancewar da nisa a tsakanin'su da isar'ta " tayi nocking batayi magana ba" k'ara buga k'ofar tayi Humaid ne yace ubanwaye'yake damuna "shiru tayi bata'ce komai tura k'ofar tayi da sallama tashiga d'akin ganin halin da,yake ciki'ne ya sata sake kular abincin da kofin da'ta d'auko juice d'in zata gudu ya kamo ta ya k'ulle k'ofar. Munafuka waya baki,izinin shigo'min d'aki " tayi mamakin sosai amma tasan ba acikin hayya'cinsa yaje ba "kwalbar giya ce 'a gaban shi se kwalin taba ya birki'ta d'akin " Ladidi ce takuma rugawa da ,gudu k'ofar d'akin tanufa"amma ina taji a kulle duban ta "takai ga Humaid da idanuwan shi sukayi ja kamar gauta tace please brother kabud'e,min k'ofa wlh nomy zata neme,ni shiru yayi yakuma duban 'ta mik'ewa yayi jiki na rawa yace baby kinzo a lokacin da nakeda buk'atar ki Ladidi ce ta mai'maita sunan da yakira ta wai baby tafiya yakeyi yana layi alamun yasha ya bugu ya matso kusada ita sunajin 'numfashin juna matsawa tadingayi shikuma yana binta kamar k'aramin yaro saida ya kaita bango tukun ya rungume'ta runtse idanun tayi wasu hawaye masu zafi na zubo mata jin alamun tudun breast d'inta yasa,shi rud'ewa " je'fata kan makeken gadon,shi yayi yafara had'e fuskar su guri d'aya"Ladidi kuka takeyi kamar,ranta ze fita tuno nasihar Yadikon,ta "tayi tashiga ture Humaid daga jikinta amma ko turuwa bayayi dake ingar'man ,namiji ne k'arfin ta ,ta had'a da cizo ta yak'ushi ta tureshi tana mikewa ta hango key, tabud'e k'ofar zata fice ya kamo'ta baya tayi da k'afarta ,ta tokare,shi ya fad'i a bakin k'ofar " ta fito da hawaye sha6e,sha6e a fuskar ta duk wanda yaganta yasan tana cikin damuwa Allah yatema keta tunda ta fito daga part d'in Humaid babu wanda ya ganta . {K'ALU BALE GAREKU Y'AN MATA BA WAYON'KIBA BA DABARAR,KIBA ADU,A ITACE TAKI ALLAH YABAKU MIJI NAGARI DUK MACEN DA TABI DUNIYA TO TABBAS DANA SANI SHINE KARATUNTA ,KAR SOYAYYA TA RUFE MUKU IDO KUCE AI ZE AUREKI INA WLH BA AURANKI ZEYI BA .}..✍️✍️✍️ Mom Islam ce ✍️✍️ *LADIDIN K'AUYE* Funny & love story. *Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa* *NA* *MOM ISLAM* *ZAINAB HABIB* *MARUBUCIYAR:* *ZAINABU ABU* *AND NOW* *LADIDIN K'AUYE* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *Episode:* 15_16 _____gado tafad'a taci gaba da rera kukanta a yanzu ko san taga Humaid batayi "misalin k'arfe shida na yamma tafito zuwa ,kitchen tasamu momy tagama komai sedai jera abinci a dining, temaka mata Ladidi tayi suka k'arasa. "Washe gari ammar yakirata a waya, yake gaya mata tazo tarakashi gidan su k'anwar momyn'shi " cewa tayi zatazo amma seta tambayi momyn ta ,cikin farinciki ammar ya sa aka ,gyara gidanshi aka feshe gidan da turaruka masu tsada. Washe gari Ladidi takira Ammar a waya tacemai yazo ,misalin k'arfe sha biyu na rana yazo ya d'auketa ,jin haka ya buga tsalle yana murna" suna cikin haka ne yake tambayar ta ,wane colorn abinci tafiso?dariya tayi kana tace indomie "cikin jin dad'i yace to karki damu drinks fa ?kowanne tace ,sukayi sallama . Washe gari misalin k'arfe sha d'aya na rana Ladidi tagama komai tasami momy take gaya mata zataje gurin wankin kai " momy ce tace kije ki tambayo dadynki tunda yana gida. Da sallama tashiga parlour n dady ,samunshi tayi yana waya bayan yagama ne ta gaishe'shi cikin ladabi ya amsa "sekuma ta sunkuyar da kanta k'asa dady ne yace Khadija meyafaru?cikin jin nauyi tace dama inason zuwa gurin kitso ne" dady ne yace to gashi su Humaid basanan ,amma kisa driver ya kaiki" to tacewa kana tamik'e zata fita. Kiranta yayi ,yabata kud'i ,godiya tayimai ta fice ." Zuwa tayi parlourn momy tagaya mata dady 'ya barta kuma yabata kud'in kitson"nasiha momy tayi mata daganan ta d'auko hijab d'inta ta fice, taje tayiwa driver magana tafad'a mai 'inda ze kaita " Bayan sunje suna hanyar dawowa suka ,hango motoci bak'ak'e sun zagaye su ,babu hanyar da zasu ,wuce " Bude murfin motar tayi , baba driver ne yace"wallahi Khadija karki fita, Ladidi 'da hankalin ta ya tashi tace karka damu yanzu zan dawo ficewa tayi a motar, ta nufi gurin masu bak'ak'en motocin'nan bata hango kowaba acikin motar ,zata juya ta koma ,tasu motar "taji an janyota an turata mota,baba driver ne ya fito yana salati kafin yakai gurin masu motocin ,tuni suka wuce da gudu ,Baba megadi yara yazeyi ,mezeje ya fad'awa su Alhaji " driving yakeyi amma hankalin shi baya jikin shi ,haka ya iso gidan . Momy ce dake shirin fita anguwa taji Horn d'in baba driver ,bayan yafito daga motar ne ya durk'usa kana yagaida momy'mom daketa lek'en ta ina Ladidi zata fito "baba driver ne yace hajiya wlh tsau'tsayine yafaru da Khadijan " momy da bata,gane inda yadosa ba tace mekake nufi "koba tare kuka fita da khadija ba ¿" shiru yayi cankuma yace wlhi Allah hajiya muna cikin tafiya mukaga wasu a wata bak'ar mota ,yabata labarin inda akayi har cemata da yayi karta fita. "Cikin tashin hankali momy ta ,kalli baba driver tace kuma ka iya dawowa saboda ragon azanci baka bisu ba ko" "Kana ganin kai rayuwar ka tafi ta kowa muhummanci . Shiru drivern yayi kana yafara da ayi hak'uri hajiya ,momy cikin fushi tace ai wlh zakayi dana sani bari alhaji yadawo . Waya sani ma koda sa hannunka a tafiyar da 'akayi da ita". " cikin rud'ani driver yace ,wlhi hajiya babu sa hannun' na momy ce cikin fusata da 6acin rai tace shot up your mouth . "Tace wlh idan kasake magana senayi report d'inka gurin police "zaro ido driver yayi kana yabar gurin ,momy da hankalin ta yagama tashi tarasa wace kalama zata ,fad'awa dady idan yadawo". Shigewa part d'inta 'tayi ganin Humaid a ,zaune yasata ware ido tace" wato kai bakaji tashin' hankalin dake faruwa ba"Humaid da hankalin shi yatafi gurin TV a tsorace ya d'auki remote ya ,kashe kallon kana yamaida hankalinshi,gurin momy 'yace momy meke faruwa?" Momy da idanuwan'ta suka ciko da hawaye ,tashare tadubi Humaid tace "tunda Khadija ta fita wlh ba,a gantaba a tsorace Humaid yace" bangane ba momy . Momy na kuka tabashi labarin da 'driver yabata, a zabure Humaid ya mik'e ya'yi hanyar fita waje ,momy da keta kiranshi yak'i juyowa bare ya saurareta. Kai tsaye gurin baba driver yanufa ,tunda baban ya hango shi ya fara salati,saboda dama basa shiri da Humaid ." Cikin azama Humaid ya ,nufi gurinshi yana zuwa ya cakumo wuyar 'rigar baba driver yace gidan uban wa kakai marainiyar Allah "baba driver daya gama tsorata yace yaro " karka manta shekarata goma ina aiki a gidannan kuma ba,a ta6a samun matsala ba, seyanzu ne zance zan cutar da wani". Humaid da bayajin ko mai da baba driver yake cewa yadinga ball dashi ,har seda momy tajiyo hayaniyar su tazo tana yiwa Humaid fad'a" "Hak'uri tabawa drivern,ta ruk'o hannun Humaid suka shige ciki , tana cikin yimai fad'a sega Jalal nan ya k'araso ,ganin fuskar momy da Humaid babu fara'a yasashi k'arasowa da sauri yana momy meys faru " Humaid cikin k'unar zuciya yace Khadija cefa driver ya 6atar da ita "a zabure Jalal ya mik'e yace shine bro ka barshi? "Momy ce tadubi Jalal tabashi labarin da driver yabata Jalal yace wlh k'arya yakeyi" momy cikin d'aga murya tace zan sa6a muku "kubari dadynku yadawo ." "Da daddare dady 'yashigo da fara,arsa ,rungumo momy ,yayi seyaga tak'i yin dariya alhalin ba haka tasaba yimai ba" duba fuskarta yayi kana yace hajiya meke faruwa naga kin sauya cikin tashin hankali da muryar da taci kuka ,tace Khadija . Dady ne yace meyafaru da Khadijan¿ momy tace barin kirayo maka driver "mik'ewa tayi ,dady ganin momy tayi waje yasa'shi mik'ewa tare suka fita . Tunda suka isa parking space d'in momy take ta k'awalawa driver kira ". A hanzarce ya fito cikin ladabi ya gaida dady ' dady ne yace meyafaru ne da Khadija ?" Cikin fad'uwar gaba driver yabawa dady labarin abinda yafaru dasu . Kid'imewa dady 'yayi yahau fad'a ,yana cewa wlh baku kyauta minba meyasa ba'a kirani a wayaba "momy da kuka ya ku6uce mata ,takasa magana ,dady ne ya d'auki motarshi ya nufi police station yayi musu bayani ". Tare dakawo photon Ladidin dakuma kalar kayan da tasa . Bayan su momy sun dawo gida,suna zaune da safe ,suna kallo a TV sukaji ana cigiyr Ladidi momy jitayi hawaye sun zubo mata,dady kuwa hak'uri yake bata amma shima yanajin cikin zuciyarshi babu dad'i". Tunda Ladidi ta 6ata momy tadena jin dad'in aiki sosai ,seda tasa aka d'auko mata yar aiki . *WAYE YA SACE LADIDI* Tunda suka sata a mota suka rufe mata fuska da bak'in wani abu, ihu takeyi 'iya k'arfinta amma babu wanda ya kulata, jitayi an d'auketa ana tafiya da ita ,daganan taji an sauketa an zaunar da ita an wurgo mata Jakarta . Takai minti talatin a haka can kuma taji an bude mata ido,ganin ta a wani k'ayataccen parlor yasata sakin kuka tana, kiran momy " Ammar ne yafito d'auke da plate na abinci a wani farin trai me adon flowers masu kyau. Ajiye mata yayi a gabanta ,nunashi tashiga yi da 'dasha shiyar muryar ta 'tace Ammar wanan ce soyayya ? ta k'ara dacewa wlh ka cuci kanka kuma tayarwa da iyayena hankali da kayi se Allah, yayimin sakayya .✍️✍️✍️ Mom Islam ce✍️✍️✍️ *LADIDIN K'AUYE* Funny & love story. *Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa* *NA* *MOM ISLAM* *ZAINAB HABIB* *MARUBUCIYAR:* *ZAINABU ABU* *AND NOW* *LADIDIN K'AUYE* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *Episode:* 17_18 _____Dariya ma tabashi ,seda yayi mai 'isarshi kana yace "kin mance da masoyinki ko ?kin kulashi tayi,sekuma taji hawaye na zubo mata . Ammar ne yaturo mata abincin kana yace kici abinci " dama kince kinfison indomie ,kuma ita na dafa miki . Kici kiji girkin Ammar d'inki "cikin masifa tace tirr !da hali 'irin 'naka ,tuno halinta na da lokacin da take k'auye tayi ,shirin mugunta take yimai . " Tace to yanzu ka maidani gida" wani 'irin kallo yayi mata, ina wanan brother naki mara mutunci "cikin fusata tace bangane ba ¿" dariya yayi mata irin 'na y'an duniya yace manta. Jiyo k'arar wayarta tayi dake hand bag d'inta ,zata d'auka Ammar ya kwace wayar ,cikin masifa tace wlh koka bani wayata kokuma kayi nadama"yayi receive din kiran kenan , zeyi magana da alamu han,kalinshi na kan wayar yana shirya iskancin daze fad'a musu . Ficewa yayi a parlor yana tunanin ai bazata fice ba". Bud'e k'ofar tayi a hankali tayi waje babu hijab a jikinta babu takalmi, lek'awa tayi taga babu megadi ,ta bud'e k'ofar da gudu ta ruga tanata gudu ,tarasa inda zata nufa . A wata anguwa mesuna rikos ta tsaya tana jiran mutane ,hango wani yaro tayi ze shiga wani gida." Azama tayi ta isa gurin yaron kana tafara tambayar shi ,dan Allah yaro daga nan zuwa 6ukur park G.R.A dan Allah nawa ne ? yaron yace" masu napep zasu kaiki a d'ari biyu ,godiya tayi mai tacigaba da tafiya. Tana cikin tafiya ne ta hango wani me adai,daita yace hajiya ina zuwa "anguwar ta fad'amai, yace " tashiga su tafi ." Sunyi tafiya me nisa sanan suka iso anguwar ,a lokacinne tafara gane anguwar tasu,nuni tayi mai da ga'gidan can "barinje in kar6o maka kud'inka ." Me napep ne yashiga yimata masifa yana cewa dama kinsan bakida kud'i kika shiga to wlh inan a nan kishiga ki fito ". Tana shiga taci karo da Jalal ,yana ganinta yahau tuhumarta" Ladidi cikin jin tsoron abinda ze biyo baya tace dan Allah brother dari biyu zaka bani 'inbawa me napep "Jalal ne yace gashi mik'a mai ". Fita tayi tabashi ya tafi,tadawo cikin gidan. Bata sami Jalal din waje ba ,tashige cikin gidan ,tana shiga tayi sallama ta hango momy da Humaid da Jalal da ,dady saboda baije aiki ba. Tunda dady'ya hangota yafara yimata wani kallo tana shigowa ,Humaid ya mik'e ya wanka mata tagwayen maruka har biyu,babu wanda yayi 'yink'urin hanashi . Cikin 6acin rai Humaid yace gidan ubanwa kikaje" banza mara tunani" Ladidi da tarasa mai zatace tadubi dady da tun shigowar'ta yake kallon ta 'taje har gabanshi tana kuka tace wlh dady ba wani guri naje ba "ya d'aga hannu zekai mata mari momy ta rik'e hannun tace katsaya muji abinda zatace" ai alamun mai gaskiya ya fita da ban . Dady ne ya saurara,yana jiran mezatace cikin murya mai ban tausayi Ladidi tace wlh dady dama cemaka nayi zani gurin kitso ,to bayan an yimin muna cikin dawowa da driver mukaga wasu ,bak'ak'en motoci sun zagayemu "shine na fita inyi musu magana ,naji anturani cikin mota an rufemin fuskata ,an kawoni wani gida kuma bansan inda jakata take ba " momy ce tadubi Ladidi tace to d'azu da Jalal yakira a wayarki waye ya d'auka? cikin she' shek'ar kuka Ladidi tace lokacin da aka shigo dani cikin wani gidan shine naga babu kowa a gidan ,cankuma naji motsin,fitowar mutum. Bayan mutumin ya fito shine , naji alamun ana kira a wayata ,ashe wayar na gefena "nazo d'auka naji an kwace wayar" da mutumin yashige ciki nikuma na gudo ". Dady ne ya jinjina lamarin yace " amma kinsman shine ?atsorace tace wlh dady bansan shiba ,su Jalal da Hunaid 'da suka zuba mata ido suna kallon ta ,momy tace Allah sarki daughter Allah yadad'a tsareki "kowa ya amsa da amin. Washe gari dady 'yakira nalam Adamu ,suna cikin wayar ne naji dady yace" yaya so, nakeyi muhad'a Khadija da Humaid aure ,cikin farinciki malam Adamu yace" wanan ai abin murna ne, amma naji dad'i sosai . Dady ne yace"abinda yasa nakawo wanan shawarar saboda muk'ara k'arfafa zumunci ,malam Adamu yace"karfa kadamu ,sukayi sallama. "Bayan dady 'yakoma gida yasamu momy da maganar ,itama tayi farinciki sosai sedai tana ganin ,anya Humaid baze wulak'anta Khadija ba ? ". Saurin kawarda tunanin tayi ,dady da yalura momy tunani takeyi yace" tunanin mekuma kikeyi ,fara'ar dole momy ta k'ir' k'iro tace" duk acikin farinciki ne ". Yau kawanansu dady biyu da yin maganar auran su Humaid, dady ne yatarasu a parlor'nshi saboda ya gaya musu,halin da 'ake ciki ". Tunda Humaid yaji wanan kyakyawan albishir ,yadinga farinciki . Ladidi dajin hakan taji tsoro ya shigeta, saboda tana tunanin,halin da zata shiga ". Washe gari dady ,yace" ansa biki sati biyu,momy ce tazaro ido tace"sati biyu fa alhaji? dady cikin tuhuma yace "kina nufin yayi kad'an ko¿" eh momy tace. Dady ne yace"muyi fatan Allah ya kaimu kawai , Ladidi ce kwance a d'aki tana tunanin halin da tashiga, Allah ma yatemaketa Ammar d'in beyi mata komai ba,tunowa da wayarta tayi kukane ya k'wace mata ,tadinga cewa"wlh nayi nadamar saninka Ammar ". Bayan sati d'aya ,yau biki saura sati biyu ,momy ce take ta shirya Ladidi musamman takira wata k'awarta daga Maiduguri". Tunda tazo aka fara yiwa Ladidi dilka dasu magunguna ,tun Ladidi nashan 'na marmari har tadawo k'in maganin,se momy tayi da gaske take sha . Tadena fita ko da harabar gidan'ne , daga d'aki se sallah ,wani haske Ladidi tayi ,dama fara ce gashi kuma ankuma gyarata. Tunda akasa biki ango Humaid ya dena zama ,shikuwa Jalal kulum cikin siyayya yake". Yau biki saura sati d'aya, bak'i ne suka fara zuwa na kusa dana nesa ,Inna hauwa ma ta iso itada malam Adamu ,se dangin momy da suka iso saboda shirye shiryen biki". A yaune lahadi wata k'awar Ladidi tazo tayi mata make up saboda tanada shago, kwaliyar hausa day akayi mata ,duka k'awayen sunsa" farar riga dakuma zanin atamfa da suka fitar anko ,DJ' Jalal ya d'auko musu ,kasancewa gidan yanada fili ". Bayan Amarya da ango sun fito ne DJ yace " ga Amarya nan itada angon ta ,please kutafa musu "bayan angama tafinne D J ,ya sake wakar da akayi musu ,Humaid 'da baki yak'i rufuwa ya ruk'o hannun Ladidi suna rawa ,sauya wak'ar akayi suka nemi guri suka zauna . DJ ne yace munason muga nera biyar a gurinnan Jalal yaje yasa dubu d'aya, ana cikin haka ne momy ta fito taja Ladidi tace asa musu wak'ar da 'akayi musu ,Ladidi kanta a sunkuye suke rawa da momy ba k'aramin kud'i momy ta zuba ba. Ana cikin rawa y'an uwan momy suka fitoda ,su goruba magarya taura aduwa se fate wanda yaji kashi a takeaway dakuma dambu ,kai kowa ya yaba wanan shiri da akayi ,anyi taro lpy an tashi . Washe gari kuma za,ayi ,kumbo day fans kuzo kuga k'ayatuwa da gurin yayi ,tunda aka fara kumbo ake jiran amarya ,tana can anayimata kwaliya material ne a jikinta me tsada sekuma head d'in data d'aura kasancewar milk ne material d'in ,ta d'aura pink head sekuma takalmi shima pink and milk ,woo gaskiya 'amarya tafito sosai ga k'afar tasha lalle ". Humaid ne yashigo yasa shadda pink hula milk wow shimafa 'angon ya had'u . Momy da takejin farinciki tashigo da turare a hannunta ta fesawa Ladidi takuma fesawa Humaid sega y'an uwan momy nan sun shigo suna gud'a.....✍️✍️ Mom Islam ce✍️✍️✍️ *LADIDIN K'AUYE* Funny & love story. *Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa* *NA* *MOM ISLAM* *ZAINAB HABIB* *MARUBUCIYAR:* *ZAINABU ABU* *AND NOW* *LADIDIN K'AUYE* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *Episode:* 19_20 _____wata kakar su Humaid ce ta shigo tana sanye da wata tsaleliyar atamfa, daka ganta kasan nera tayi kuka sawa tayi aka kirawo Ladidi ,Ladidi tana kuka 'aka shigo da ita ,lokacin ta canza kaya 'atamfa ce Holland me tsadar gaske ,riga da skirt ne mai adon stone a jiki ,tunda 'aka fito da ita take kuka mai cin rai y'an uwan momy ne suka rik'ota suka wuce da ita part d'in momy, lulu6eta naga 'anyi daganan kuma 'aka d'auko turaruka masu k'amshi aka fara fesa mata sosai take jin zafin rabuwar ta da iyayen ta gashi kuma yanzu wanda sha'awar ta yakeyi shi za'a 'aura mata kuma tsanan ta kukan tayi saboda zuciyar ta d'aci take yimata , jiyo muryar mutane suna rangad'a gud'a yasata dawowa daga duniyar tunanin da ta tafi, momy ce ta janyo ta jikin ta kana tace" Khadija duk abinda zance na fad'a miki tun jiya , sai dai zan kuma yimiki tuni da ki rik'e mijinki da 'amana kuma kiyi biyayya 'a gareshi kibi duk wani abu da yakeso inhar bai sa6awa shari'a ba ,wani kukan 'ne yakuma ku6uce mata saboda wanan nasihar ba k'aramin shigar ta sukayi ba ." Bayan momy ta share hawayen da suka zubo mata tace"wa wasu mata da 'alamu k'annen ta ne tace"musu su raka Khadija d'akin dadyn su , k'afar momy Ladidi ta rik'e tana kuka mai tsuma zuciya ,kowa na gurin saida ya zubda hawaye saboda tausayi, bayan sun kaita d'akin dady ne yafara yimata nasiha bayan wa inda suka rakota sun kauce yafara sanya mata 'albarka daganan yafara da ina 'alfahari dake Khadija kibi mijinki karkiyi k'ok'arin sa6a mai kuma yakamata kisani karki kasance mai d'aga murya 'akan ta mijinki kibi umarnin mijinki , karki sa6a masa indai umarnin bai sa6awa addinin musulunci ba ,kanta 'a k'asa tace Dady nagode ,wani small box Dady 'ya d'auko wasu keys ne na mota ,mik'awa Khadija yayi duk da 6acin ran datake ciki saida ta dara saboda tsabar farinciki har k'yal k'yalewa da dariya take,hak'ik'a dady 'yaji matuk'ar farinciki tare dakuma sanya mata 'albarka,kira yayi akan azo a tafi da Khadija ba'adau wani long time ba saiga wasu mata nan suka d'agota kiran sunan dady takeyi amma inna shima baiyi magana ba ,hawayen da suka zubo mai yashere batare da kowa yagani ba ." Humaid ne zaune a d'akin abokanan shi yana hutawa ,wani abokin shine yace "abokina wallahi ka huta saboda wanan babyn taka tagama had'a maka komai ,Humaid ne ya gyara zama yana kallon abokin 'nashi yace" banason irin wanan wasan, daga nan ya gyara zama ,jiyo k'arar wayar shi ne yasa shi duba gurin da ya 'ajiye wayar ,ganin 'number babu suna yasa shi jinkirta d'aukar wayar ,saida 'akayi 6 miss call sanan ya d'auka ,jin muryar wani yasa shi gyara zama k'irjinshi na dukan uku_ uku,ji nayi yace"what!!!. " Wata razana nniyar k'ara yasa yana cewa no_no wlh ba ita bace kana ya mik'e yana layi ,abokin 'nashi yace "Humaid akwai problem ne ?" idan Humaid da ya sauya launi ya juyo yace"babu komai zan dawo anjima,abokin baiji dad'in jin hakan ba 'amma sanin halin Humaid yasa shi yin shiru da bakinshi. Bayan Humaid ya isa gida ne ya hango Khadija ita da k'anwar momy suna magana ,wata muguwar tsanar ta yakeji acikin ranshi, wucewa part d'inshi yayi ba tare da k'ara kallon gurin da 'amaryar tashi take ba?"direct parlorn dady 'ya nufa kafin ya shiga saida ya tsaya sosai yana tunanin kalmar dazai fad'awa dady ,ganin bashiga mafita yasa shi, shigrwa kai tsaye ,bayan yayi sallama ne yasami dady zaune da laptop a hannun shi ,dady ne ya cire farin glass d'in da yake manne a idonshi kana ya juya ya kalli d'an 'nashi ,kan Humaid na k'asa saboda bayason su had'a ido da dady ,bayan sun gaisa ne dady 'yake cemai lafiya ko naga kayi shiru ?"dady ne ya d'ago kai ganin mood d'in Humaid ya sauya sosai yasashi cewa to me kuma ya faru ?idanun Humaid sunk'ara kad'awa ya d'ago kai yana duban dady 'yace"dady dan Allah dan darajar manzon Allah ka fahimceni ,dady dai baisan inda Humaid ya dosa ba saboda babu abinda ya fahimta ,Humaid ne yace"dady nafasa auran Khadija!!!,sauran kalmar ta mak'ale a bakin shi ganin wani mugun kallo da ,dady ke jifanshi dashi." Dady da yakejin ranshi yana yimai d'aci ya dubi Humaid 'da jikin shi ke rawa yace"wallahi wallahi ko bayan raina ban yarda 'ace ka fasa 'auran Khadija ba ,da ubanwa yasa kace" kana sonta, kodan kanaso ka wulak'anta mu ?"girgiza kai Humaid yayi saboda yana ganin dady bazai fahimceshi ba ,dady ne yace"tashi ka ficemin marar kunya da bakasan mutunci ba ni zakazo kacewa wai kafasa 'auran Khadija to dama gobe juma'a 'aure babu fashi wallahi sai anyi ,Humaid ne yayi saurin ficewa daga part d'in dady saboda kar momy tasan halin da 'ake ciki ,komawa bedroom d'inshi yayi ya hau makeken gadonshi juyi yakeyi saboda zuciyar shi ji yakeyi kamar zata fashe , yafara tuno kalar tanadin da yace"zai yiwa Khadija 'amma yanzu gashi komai ya rushe ,yafara kuka kamar k'aramin yaro ,sai kuma ya tuno cewa gobe nefa d'aurin aure dafe kanshi da yake faman ciwo yayi yana salati ,akwatin shi da yacika shi da d'inkuna ya kalla saboda kayak shiki zasukai kala talatin amma gashi komai ya rruguje." Khadija ce zaune kusa da umma tana k'ara tunatar da ita 'akan zaman lafiya dakuma ibada da hak'uri ,wata gora babba momy ta d'auko tabawa Khadija tace"kinga wanan daga saudiya 'aka kawo min kuma dan ke nasa'aka taho dashi saboda ba ,a ko ina 'ake samunshi ba , ita dai Ladidi ta kasa gane me momy take nufi ,momy ce ta dubi Ladidi kana tace"zuma ce ta mata kullum zakidinga sha 'amma fa yanada k'arfi,2 small spoon zaki dinga sha ,Ladidi ce take mamakin momy da take zayyane mata maganin mata." 💍 *WEEDING*💍 Yau juma'a yaune dubban jama'a suka shaida daura auran *KHADIJA MUSA DA HUMAID ADAM* Akan sadaki dubu d'ari lakadan ba 'ajalan ba 'abokanan su Humaid basu ji dad'in ganin yanayin angon ba kasan cewar baya cikin 'nutsuwar shi saboda 'a inda yake basu labarin shagalin da zasuyi a gun bikin dakuma garar daze kwasa 'amma sunga yanzu ko sunan amaryar baya son ji ." Kowa ka gan yana cikin farinciki a yau saboda biki yayi biki amma banda mutum biyu wato Khadija da Humaid , wata k'awar Khadija ce tace yakamata mu tambayi Humaid saboda musan a inda za 'ayi dinner Khadija ce tace"hmm kuna iya zuwa bazan hanaku ba ,babbar k'awar ce mai suna ramsy ta d'aga waya tana lalubar number Humaid 'dan kab k'awayen sunfi shiri sosai ,jin takira wayar tanata ringing ba'a d'aga ba yasata dad'a gwa dawa cikin k'araji yace" wai waye ne please banason takura ,Ramsy ce tace"Humaid baka ganin 'number tane nice fa ,Humaid ne yace"to inna gani sai me yanzu mezan miki hak'ik'a Ramsy taji zafin hakan amma sai ta daure tace"dama maganar dinner ne shine nace kafin a tafi ne za'ayi kokuma sai ankai amarya, jin ya daka mata tsawa yasata zabura tace"daga tambaya saika nemi firgita ni ,to kasani ko a gidan mu babu mai yimin tsawa ka kiyaye ,ko kulata baiyi ba yaja waya ya kashe ,Khadija ko kuka takeyi dama tasan za'ayi hakan ,tafara magana da k'arfi tana cewa"daman wlhi na kawo wanan ranan saboda yaga 'an d'aura 'aure nazama mallakin shi shine ya keson wulak'anta ni."✍️✍️✍️. *MOM ISLAM CE*✍️✍️✍️.. *LADIDIN K'AUYE* Funny & love story. *Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa* *NA* *MOM ISLAM* *ZAINAB HABIB* *MARUBUCIYAR:* *ZAINABU ABU* *AND NOW* *LADIDIN K'AUYE* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *Episode:* 21_22 ____Kashe wayar yayi gaba d'aya dan bayason jin duk wani abu daya shafi Khadija saboda 'a halin yanzu wutar k'iyayyar ta ce take ruruwa 'acikin zuciyar shi, da misalin k'arfe tara na dare saiga motocin angwaye sun zo d'aukar amarya ,bayan angama yimata makeup dasu nasiha 'aka ce tafito su tafi , tunda taji haka ta k'ank'ame momy sosai tanajin zafin tafiyar da za'ayi da ita saboda tayi nadamar auran Humaid amma babu inda zatayi dole ta yarda kodan soyayyar da su momy suka nuna mata gashi dady harda bata mukullin mota,tana cikin tunani ne taji muryar momy na cewa , ina Khadija tayi share hawayen ta tayi kana ta gyara yafa gyalen ta ,jin alamun shigowar umma yasata dai_daita nutsuwar ta , bayan momy ta shigo ta ganta 'a zaune ta takure gefe d'aya , cikin azama tace"taso taso muje kiyi wanka kinga masu mota sun iso." Jiki babu k'wari Khadija ta tashi ta rufawa momy baya , bayan sun wuce toilet d'in momy ne momy tace "zonan suna shiga momy ta had'a mata wasu turaruka dakuma magun guna ta shige wanka , bayan ta fito ne momy tasa 'ayi mata makeup aka fito mata da kayan dazata sa , fans kuzo kuga Khadija kamar tauraruwa kowa sai mararin ganinta yakeyi, bayan sungama ne aka fito da ita tana sanye da swiss lace mai ruwan ganye ,fito da ita sukayi aka fara rangad'a gud'a Khadija kuka takeyi sosai kamar 'ranta zai fita, momy juyawa tayi saboda bazata iya ganin Khadija 'a yanayin kukan da takeyi ba ,wata kakar su Humaid ce tace" zo yarinya kiyi bismillah ki shiga ,haka Khadija tashige mota tana kuka mai tsuma zuciyar mai saurare , tunda suka tafi momy ta koma bedroom d'inta tana ta sharar hawaye , ganin ai yau ranar farinciki ce a gurinta yasata murmushi da yau Humaid ya auri wacce take so adu'a tayi musu kana ta haura sama gurin dady ,samunshi tayi kwance yana duba wani file na business d'inshi yana ganinta yafara sakin murmushi k'arasawa tayi ta fad'a saman k'irjin shi tana shafa mai kai ,cikin jin d'ad'i dady yace ,lovely na menene ?"🤭momy ce tafashe da kuka tana cewa shikenan yanzu zan dena ganin Khadija 'a kusa dani." Gyara musu kwanciya dady 'yayi kana yafara share mata hawayen fuskar ta daganan'na rufo musu k'ofa ." *GIDAN AMARYA KHADIJA*👰. Zaune take tana ta gurshek'en kuka babbar k'awar ta Ramsy ce tazo kusa da ita tana cewa habba Khady maiyasa saikace ba 'auran soyayya ba ,share hawayen ta tayi batace komai ba ,dan a halin yanzu batajin zata iya wata magana tunda babu mai fahimtar ta, wanka ta sake yi ,kana suka k'ara yi mata make-up wanda yafi na d'azu aka sauya mata kaya zuwa wani material mai laushi suka feshe ta da turaruka masu k'amshi wow koni danaga Khady saida na yarda 'alk'alami na , shirin tafiya suka farayi ai kuwa Khadija na ganin hakan tafara gurshek'en kuka mai tsuma zuciya mai saurare ,zuciyar ta bata gama tsinkewa ba sai lokacin da taga sun yafa mayafi suna shirin fita ,durk'usawa tayi tana cewa kuyi hak'uri ku tafi dani ,nikuwa nace aure fa kikayi hhh yarinya ki gane aure yafi gaban wasa ." Haka tanaji tana gani suka wuce suka barta ,komawa tayi ta haye makeken gadon ta daya k'awata d'akin, kwanciya tayi can kuma tafara jin tsoro na shigar ta ,misalin 10:pm taji alamun shigowar mota, wani tsoron takuma ji tana 'adu'a 'a cikin zuciyar ta mik'ewa tayi ta lek'a ta window hango shi tayi shi kad'ai yana shirin fitowa daga mota, sanye yake da shadda mai kalar brown wace ta k'ara fito da ainihin kyan shi ,bayan ya rufe motar ne ya d'auko wata leda ya yi hanyar shigowa parlon ,Khadija ce ta koma ta gyara rufe fuskarta da mayafin jikin ta 'takoma tsakiyar gado ta zauna ,da sallama 'a bakinshi ya shigo zama yayi a d'aya daga cikin kujerar d'akin kasancewar bedroom d'in 'nata kujeru biyu ne ammafa sun k'awata d'akin ,bayan ya zauna ne yace"inkinyi ra'ayi zaki iya bud'e fuskarki ,wanan maganar ba k'aramin dukan Khadija tayi ba ,amma batace komai ba ,kuma d'ago kai yayi yakuma cewa to mekuma zaki 6oyemin bayan angama tallarsu a titi ,a firgice ta mik'e tana nuna Humaid 'da yatsa abinda bata ta6a yiba kenan ko musu dasu batayi amma yaukan ya kaita mak'ura ". Cewa tayi duk abinda ka fad'a 'a kaina nayi shiru ban kulaka ba yanzu kuma ka sake jifana da wanan mumunanr kalmar ?" to wallahi bazan lamunta ba ,kafin ta k'arasa ya wanketa da mari jiki na rawa tace"kozaka kasheni wallahi sai Allah ya sakamin ,wurga mata ledar yayi ya fice a fusace , kwanciya tayi tafara gurshek'en kuka gashi babu mai rarrashin ta. Misalin k'arfe 11:pm ta mik'e ta daddafa bango saboda mugun ciwon da kanta yakeyi bata gani sosai,toilet 'ta shiga ta wanko bakinta tazo ta zauna tana son cin abinci gashi matsanancin ciwon kai na damunta ,ba'a fushi da 'abinci ,janyo ledar daya wurgo mata tayi tana bud'ewa taga mutuniyar tace wato kaza gasashiya da yogurt aiko tafara yagowa tanaci tana shan yogurt d'in ,duk girman kazar saida tayi rabi ,alokacin'ne taji ciwon kan ya ragu ba kamar da ba ,mik'ewa tayi ta cire kayan jikinta ta sauya izuwa sleeping dress sosai kayan sukayi mata kyau ,bayan tayi adu'ar kwanciya bacci ,tana kwanciya bacci mai nauyi ya tasheta tare da mugayen mafarkai masu firgitar wa, washe gari tunda tayi sallahar asbha ta koma bacci ba ita ta farka ba sai misalin karfe 9:am lokacin ma jin alamun 'nocking d'in k'ofa ne ya tayar da ita". Zumbulelen hijab d'inta tasa kana ta nufi k'ofa ,tana fita parlor takuma ji ana nocking cikin azama ta isa k'ofar ta bud'e ,ganin yar aikin momy ce yasa Khadija washe baki tace"yaushe kika dawo ne Ummi?"Ummi cikin jin dad'i da tarbar da Khadija tayi mata tace"yau kwanana d'aya ,Khadija ce tace"to kishiga mana kamar bak'uwa ,shiga Ummi tayi bayan ta mik'awa Khadija abincin da momy tabayar akawo musu tuwon shinkafa ne miyar shuwaka wacce taji nama kamar zasuyi magana kai dakaga tuwon kasan zaiyi dad'i ,jere kulolin tayi a dining ta dawo ta zauna ,kusada Ummi ,tambayar ta tashiga yi 'inasu momy da yaya Jalal 'lafiya Lou tace"daganan Khadija ta kunna musu kallo ,Khadija ce ta mik'e tace Ummi ki jirani yanzu zanyi wanka in fito ,Ummi data tuna da kashedin da Momy tayi mata yasata cewa to nimafa tafiya zanyi dan momy na jirana ,badan Khadija taso tafiyar Ummi ba 'amma tayi mata godiya sukayi sallama . Humaid ne yafito parlor lokacin 11:am na safe sanye yake da wani lallausan yadi mai ruwan coffee kasancewar shi farine ba k'aramin kyau yayi ba ,shafa bak'ar sumar datayi luf a kanshi yayi can kuma ya ciro waya kamar mai jiran wani abu ,Khadija ce tafito tana sanye da doguwar 'riga pink mai adon ston black tayi rolling kanta da mayafin rigar ,tana fitowa Humaid yakai dubanshi gareta cikin zuciyar shi kuwa ji yakeyi kamar yaje yai hugging d'inta tunda matsayin da 'a gurinshi yayi kawai sai ya had'e rai ,ya dubeta tana neman gurin zama yace"keee!!saida gabata ya fad'i tashi ki gyaramin d'akina baki iya gaisuwa bane ?"na iya tace"a tak'aice ,Humaid ne yace "to kullum zaki dinga zuwa gaisheni ko sau goma zan fita kuma in dawo ,to kawai tace" ganin yayi hanyar dining ne yasata k'arawa da gudu ta kwashe kulolin tayi d'akinta dasu ,key tasa ta rufe k'ofar.....✍️✍️✍️. *~MOM ISLAM CE~* *LADIDIN K'AUYE* Funny & love story. *Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa* *NA* *MOM ISLAM* *ZAINAB HABIB* *MARUBUCIYAR:* *ZAINABU ABU* *AND NOW* *LADIDIN K'AUYE* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *Episode:* 23_24 _____Saida ta tsince naman kaff tukun ta ci tuwon bayan tagama cine ta fito da ragowar parlor, bata lura da mutum a parlorn ba direct ta wuce dining ,saida ta 'ajiye kular ta hango shi yana kan doguwar kujera maicin mutun uku ,zata ruga da gudu ya daka mata tsawa yace"kee!!zonan zataci gaba da tafiya ya mik'e da gudu ya janyota ya wurgata gefe kana yace "wuce ki dafamin dambu,zaro ido tayi kana tace"me kuma mai suna haka?". " Cewa yayi ubanwa zaki rainawa hankali ¿"cikin jin tsoro da fargaba tace"ni ba rainama hankali zanyi ba ,gani 'nayi ban iya ba shiyasa nake tambayar ka, tsawa yakuma daka mata saida ta tsorata yace"kin zo bariki kin manta da shan garin kwaki ko ?"to kitashi ki goge gidannan kuma kar in dawo insami akasin hakan, haka ta shiga bedroom d'inshi tafara wanke toilet sanan ta dawo gyara bed d'inshi tayo kan TV da sauran kayan kallon ta gogesu kana ta dawo tafara shara tana gamawa tayi mopping, bayan ta gama ne kawai tad'an kishingid'e a gefen bed' d'inshi saboda wata gajiya da tayimata sallama ,bacci ne mai nauyi ya kwasheta 🤭nikuwa nace"anci an k'oshi zaki gane, jin shiru har tayi 1 hour bata fito ba yasashi kashe kallon daya kunna kana ya wuce bedroom, samunta yayi kwance tayi d'ai_ d'ai ,zaro ido yayi kana yafara tunanin irin muguntar da zaiyi mata." D'auko alurar malaria yayi wacce yake ajiyewa 'a gida saboda koda wata matsalar zata taso, bayan yagama zuba magungunan dayasan Khadija zata bada labari ,komawa yayi kusa da ita yana k'are mata kallo can kuma yaji muguwar tsanarta tana kuma baiyyana cikin zuciyar shi. Tunda 'akayi bikin Humaid 'da Khadija babu wanda yayi k'ok'arin kiran su momy gashi yau har kwana biyu da wuni saidai momy na 'aiko da 'abinci kullum ,amma hakan bai sata kwanciyar hankali ba , kiran Jalal tayi a waya yana d'auka tace" dan Allah kazo inason ganinka . "Cewa yayi momy lafiya dai ko ?"lafiya tace masa daganan ta kashe wayar ba'adau lokaci mai tsayi ba saiga Horn d'in motar Jalal nan kasan cewar baya gida ,yana shigowa tun daga parlor yafara k'walawa momy kira yana cewa momy gani na iso, sako tayi daga matatrakar dake tsakiyar d'akin tace"gidan Humaid nakeson kaje inasan kadubo su ko lafiya ,itadai Khadija nasan batada waya , dariya ce taso ku6ucewa Jalal ganin damuwa k'arara 'a fuskar momy sun kuyar da kansa k'asa yayi kana yace" momy lafiya suke saboda da babu lafiya 'ai dakinji , momy ce ta d'ake tana masifa tana cewa yanzu ka nuna ban isa dakaiba kenan ko?"to walhai tun wuri kaje ka dubomin su kokuwa ranka ya 6aci !!Dady dake saukowa daga bene yace"karka kuskura kaje gidan su , nagaya maka d'ago kai momy tayi tana kallon fuskar dady _dady dake magana cikin bada umarni yace "ka koma gurin aikin ka, to Jalal yace" batare da yakalli k'wayar idon momy ba." "Momy ce takalli dady can kuma tayi k'asa da murya tace"haba habiby maiyasa kayi hakan?" tana dad'a matsowa kusa dashi , dady ne ya kawar da kai alamun maganar da momy tayi d'azu nazuwan Jalal gidansu Humaid ya 6atamai rai, k'arasawa kusa dashi momy tayi kana tace"haba mana mijina banason fushinka ta kuma marai raice fuska kamar zatayi kuka tace" please afuwan habiby, hugging d'inta dady 'yai tare da janyota jikinshi a lokacin da yake k'ok'arin zama akan d'aya daga cikin kyawawan kujerun,dasuka haska parlorn ,dady ne yake rad'awa momy a kunne yana cemata walhai Aisha saboda salonki dakuma siye zuciyata da kyawawan kalamanki yasa nak'i k'aro aure amma badan hakaba da yanzu matana hud'u . Tunda ya gama had'a komai ya bud'e mata gefen hanunta jitayi abu na shigarta kamar'ruwa kasancewar ko a hospital ne kowa nason alurar shi saboda batada zafi,haka yayi mata 'alura tana bacci ,jin alamun kamar ana tsikarin ta yasata saurin motsawa, Humaid na ganin haka ya koma parlor saboda karta gane ,tun tanajin abin kad'an har tazo tanajin k'ai k'ayi sosai, inta Sosa k'afa saitaji a kunne inta sosa kunne saitaji a baya ,haka tadinga susa kamar mahaukaciya ganin lamarin yafi k'arfinta yasa tafara ihu tana tsalle tana cewa wayo Yadikko, da gudu ta fice a d'akin tayi d'akinta tana tsalle ,rasa 'abinda yake yimata d'ad'i tayi ganin batada mafita yasata d'auko farar hoda ta cire kayan jikinta duka ta shafe ko ina na jikinta ,ganin abun babu sa'a yasata cewa yaya Humaid!!, "Kazo ka temakeni walahi narasa inda na kwaso k'ai k'ayi ,shiko Humaid ganin tana magana tana soshe _soshe yasashi sakin killer small yace" to yanzu mekikeso inyi miki nikuma ?"kije wanda yafara ganin komai ,ya baki magani ,tana susa tace"bangane ba sokakeyi kacemin 'ni mazinaciya ce?!!! menayi ma dahar zaka k'ullamin wanan mummunan sharin oho yace"daganan yabarta tana soshe ssoshe. Tana kuka tana susa wani gurin har yayi rud'u rud'u tsabar susa tausayin da tabashi ne yasashi shigowa ya mik'o mata magani k'waya biyu yace"ta shanye duka ,babu musu ta k'ar6a tanasha ba'a d'au lokaci masu tsayi ba ,bacci ya kwasheta , said a ya koma d'akinshi yadinga dariya yana k'arawa saboda ya 'ajiye CCTV a bedroom d'inshi kuma bakowane zaisan akwai CCTV a d'akin ba ,kusan k'arfe hud'u na rana ta mik'e had'e da salati a bakin ta ,wata masifaffiyar yunwa takeji mik'ewa tayi ta nufi kitchen tana shiga taji k'amshin indomie jollof ,bud'e murfin tukunyar tayi ganin kayan k'wad'ayin da 'aka samata yasata zaro ido k'wai ne dafaffe sai karas ,abinka da gidan kwad'ayi ai dandanan taji ranta ya biya tuno mai girkin tayi wato Humaid tsaki tayi kana ta sunkuci tukunyar tayi d'aki ,bathroom ta shiga seda tayi wanka tayi brush sanan ta fito ta zauna 'a gaban dressing mirror tana shafa mai tana wak'a tunowa tayi ai bata kulle k'ofa ba ,dagudu ta mik'e taje tasa key tadawo taci gabada Kwaliya bayan ta d'au makeup mai kyau ta ciro shadda bugaggiya mai ruwan coffee tasa takuma ciro bra da pant da warwaro da sark'a wow ba k'aramin kyau tayi ba ,zama tayi gurin tukunyar indomie tafara baiwa cikinta rabonsa saida taci ta k'oshi tayi gyatsa sanan ta mik'e tayi gurin madai daicin fridge d'inta taciro hollondia mai sanyi ta kkora." Daganan ta 6oye tukunyar . Yana fita direct kitchen yanufa ganin baiga tukunyar daya d'ora ba yasashi zaro ido had'e da dogon tunani ,komawa parlor yayi ya murd'a handle d'in k'ofar jin a kulle yafara tunanin kodai Khadija ce ta d'aukemai hanyar d'akinta ya nufa jin k'ofar ansa key 'yasashi cewa "wallahi koki bud'emin kokuma duk lokacin da kika fito sainayi maganinki , tanaji yana sababi amma fur tak'i fitowa ,gajiya yayi da tsayuwa , komawa d'akinshi yayi ya watsa ruwa daganan ya fito yayi shirin tafiya gurin cin abinci . Tanajin k'arar motarshi ta fito rik'e da gyale a hannunta dakuma takalmi mai tsini yiwa drivern gidan "magana tayi da saurinshi ya taho ya durk'usa 'a gabanta yace " hajiya Mota zakishiga ?"eh tace"daganan ta shige mota suka nufi 6ukur park wato anguwarsu momy ,murna take sosai kamar mai shirin tafiya hajji ,suna isowa kusada gate d'in drivern ta yafara horn mai gadi ne yaje ya bud'e mai daganan suka kutsa ciki ,suna sauka ta ruga ciki da gudu,turuss tayi ganin Humaid zaune yanacin farfesu ,zaro ido tayi tana jujuyasu shikwa yiyayi kamar bai ganta ,fakar shi tayi ta shige bedroom d'in momy da gudu ....✍️✍️✍️. ~MOM ISLAM CE~✍️. *LADIDIN K'AUYE* Funny & love story. *Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa* *NA* *MOM ISLAM* *ZAINAB HABIB* *MARUBUCIYAR:* *ZAINABU ABU* *AND NOW* *LADIDIN K'AUYE* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *Episode:* 25_26 _____Samun momy tayi ta fito daga wanka ,dagudu taje ta rungume momy saikuma ta fara kuka Momy datake murna saikuma 'annurin fuskarta ya disashe kasancewar taga Khadija na kuka ,janyota momy tayi zuwa bakin gado bayan sun zauna ne "momy take tambayarta tare sukazo da Humaid ne ?" saboda taga Humaid 'din bai dad'e da zuwa ba ,Khadija ce ta share hawayen ta tace"momy babu komai kawai farincikin ganinki ne ,badan momy ta yarda ba tace"to nima nayi farinciki da ganinki my daughter ,saidai naga kin rame sosai kodai da wata matsalar ne? a'a tace" Momy ce tace"to gyramin gaban mirror d'innan ,to Khadija tace" tafara 'abinda momy ta sata momy tayi hakane domin tasami damar zuwa gurin Humaid saboda shid'in ma ya rame sosai,bayan momy ta fita ne Khadija tace" na shiga uku gara da ban fad'awa momy komai ba da walhi zata iya fushi da Humaid. "Momy nazuwa parlor tasamu Humaid na danne _danne a waya yana ganin momy 'ya d'ago kai yace" barka da fitowa momyna dafatan kin fito lafiya ? Lafiya lau momy tace"Allah yayi albarka cike da kulawa yace amen momy _momy ce takai dubanta ga Humaid tace"amma dai kuna zaune k'alau ko?"cikin rawar baki yace"eeh eeh lafiya Lou ,momy ce tayi murmushin su na manya tace"bakwa zaune lafiya Humaid a zabure Humaid ya kalli momy 'yace ita Khadijan ce tagaya miki haka ? ko d'aya momy tace"daganan kuma duban Humaid a karo na biyu saboda 'akwai abinda take karanta "cewa tayi karka manta yarinyar nan marainiya ce bamu baka ita dan ka cutar da ita ba kuma na fuskanci ko a lokacin auran kayi farinciki amma metayima dahar zaku dinga cutar da rayuwar ku?" sunkuyar dakai yayi kana yace nikam 'momy saidai kiyi hak'uri dani dan wallahi bazan ta6a son Khadija ba kuma wlhi ko meye ya wanketa zaro ido momy tayi had'e da d'an gutun hawaye tace"ni Humaid kake gayawa wanan kalmar ni ko kukane ya kufcewa momy cikin k'araji tace tunda kazo.duniya bamu ta6a musu dakai ba 'amma zuwa yanzu ne zakace zamudinga musayar yawu dakai ,hak'uri ya shiga bata ganin bata kulashi ba yasa ya durk'usa kan guwaiwar shi yana bata hak'uri,ko kallon shi momy batayi ba ta mik'e cike da matsanancin 6acin rai tace "wallahi wallahi inhar ka cuci Khadija 'Allah ya isa tsakanina dakai!!!." Cikin firgici ya d'ago kanshi da yayimai nauyi yace "ni momy kike yiwa mugun baki " nafad'a nace nafad'a kozaka mareni ne tunda yanzu ka isa yiwa kanka komai "momy tace" cike da takaicin halin da takeciki, komawa tayi cikin bedroom ta sami Khadija ta zuba uban tagumi girgiza kai momy tayi daganan tace"kitashi kibi mijinki ,Kadija ce ta dubi fuskar momy tace"momy maiya faru naga kamar kuka kikayi ?cikin sasanyar murya momy tace "ba kuka nayi ba kwai raina ne ya 6aci ,adu'a Khadija tayiwa momy daganan ta d'auko mayafinta ta fice, bata sami kowa 'a parlorn ba hakan yabata damar wucewa parking spice da sauri jin anata kiraye _kirayen sallah magrib yasa ta k'walawa drivern daya kawota kira jin shiru bai zoba yasa fara jin haushi tafara cewa kodai'in kar6o keyn mota ta ne?komawa tayi tace" momy bani mukullin motar da dady 'yasiyamin 'nabaki ajiya ,momy ce tace"ina mijinnaki yayi ?"cewa tayi ya tafi wlh kuma driver ba banganshi ba ,d'auko mata momy tayi daganan tayiwa momy sallama ta wuce mota . Ganin motar a lulu6e yasata yayewa ta shige da bismillah ta fita daga cikin gidan tahau titi ,tafiya takeyi cike da kulawa har Allah yakawota gida lpy, da saukarta ne taga Humaid bai dawo ba hamdala tayi daganan ta wuce kitchen ta d'ebo kayan shayi duka har indomie kwali biyu ta d'ibo kwai kuma ciko kwali tayi kasancewar yafi k'arfin abin d'ora k'wan a cewarta tadena fita mancewa tayi bata d'auko abin girki ba zuwa tayi tana tunanin da gas da electri wane zata d'auka ,kinkimo gas tayi tana cikin tafiya ne taji alamun dawowar Humaid ,cikin azama ta ruga dashi d'aki tana nishi ,ta rufe k'ofar da key. Yana shigowa da sallama 'a bakinshi ya doshi k'ofar d'akin Khadija jin ta rufe k'ofar ne yasashi k'wafa yace"wallahi tunda kikaje kika had'ani da momy na wallahi saina miki jina jina ,tana daga d'aki tana yimai gwalo haka yagama sababin shi ya fice ,yayi d'akinshi". Bayan Khadija tayi sallah taji wata fitinanniyar yunwa na mata sallama mik'ewa tayi ta kuna gas duba tukunyar dazata d'ora ruwan zafi tayi bata gani ba zaro ido tayi tana salati tace yanzu ni mezanci d'anyan k'wai kokuma d'anyar indomie kokuma lifton zanci? babu madara babu sugar ?wayo Allah na nashiga uku ni LADIDI!!.tasa indomie a gaba tayi ta farke leda d'aya tanaci tanashan ruwa kasancewar lemu ya k'are a d'akinta bayan tagama cine tayi ,isha 'I daganan ta haye gado bayan tayi addu'oin dasuka zamemata wajibi ta kwanta badan ta k'oshi ba , asbha ta gari. Washe gari bayan tayi sallahi ta mik'e tanason fita tanajin tsoro ,shiko gogan tunda yadawo daga masallaci ya zauna ' a parlor ya kunna TV kuma yaune komawar shi gurin aiki wato hospital d'inshi dan tun dare ake ta yimai waya'akan anason ganinshi ,shi burin shi bai wuce yaga ya illata Khadija ba ,ita kuma Khadija tak'i fitowa saboda tsoron Humaid ,gajiya yayi da zama duba 'agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunshi yayi ,k'arfe goma da rabi 10:30 bai fita ba duk akan wanan shegiyar yarinyar?"yake tambayar kanshi tsaki yaja ya fice zuwa bedroom d'inshi wanka yayi yana fitowa yaga har sha d'aya tayi 11:am zaro ido yayi ,kamar maijin kashi ,shiri yakeyi jikin gaggawa kamar mai tashi sama da sauri yayi waje gurin motar shi , ya tayar ya mik'i hanya". Tanajin fitarshi ta fito da gudu tayi d'akin shi ganin kayayyakin daya siyo tayi zaro ido tayi tace"shiyasa ko ya nemi abubuwan dana d'ebo tabb aikuwa saina kwashe wa in an ma ,fara jidowa tayi tana haki ta kwashe kayan abincin dukka harda su carton d'in maltina dana madara dakuma k'wai duka ta kwashe tana dawowa taga wani kayan ganin jikin kwalin anrubuta golden ai kawai ta loda takai d'aki a ranta ko tana cewa shikenan 'na huta da girki ko lemon kwalba ma ya isheni, kitchen taje ta d'auko tukunya da wuk'a dakuma mangyad'a da kayan miya tadawo d'aki tasa key . Misalin k'arfe biyar na yamma yadawo a gajiye ya shige toilet ya watsa ruwa yana fitowa kwai yaji yana sha'awar shan golden beer zuwa inda ya 'ajijiye kayan yayi ganin baiga komai ba yasashi zaro ido ,cikin kunar 'rai yace "wato wanan tsinanniyar bacin zina har giya takesha?" zama yayi a bakin gado yadinga girgiza k'afa yana bala'i arayuwa bayason a d'auki abinshi ba'a tambayeshi ba ,cikin masifa yafice daga d'akin 'nasa yana zage zage kuma ya kudurta 'a ranshi ko k'ofar zata 6alle yau saiya ci uban Ladidi ,yana zuwa yaji kamar kullum k'ofar a rufe take da key dukan k'ofar yakeyi kamar mahaukaci amma tak'i bud'ewa itako tana tsoron karfa ya 6allah k'ofar nan yazo yakusa kasheta dan yau kamar yasha ya bugu,shigewa cikin drower tayi tanata zaro ido kasancewar akwai gurin sa sak'ata ta ciki kuma tanada zurfi ba lallai mutum ya bud'eta da garaje ba....✍️✍️✍️. Mom Islam ce *LADIDIN K'AUYE* Funny & love story. *Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa* *NA* *MOM ISLAM* *ZAINAB HABIB* *MARUBUCIYAR:* *ZAINABU ABU* *AND NOW* *LADIDIN K'AUYE* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *Episode:* 27_28 _____Cikin k'arfi ya bigi k'ofar har saida ta bud'e tsayuwa yayi yana maida nunfashi kasancewar k'ofar bata ra'go bace ,kutsa kai yayi cikin d'akin yana haki yana cewa inakike dan ubanki yau saina karyaki ,dube dube yakeyi amma ina baiganta ba bud'e toilet yayi nanma bata nan rik'e k'ugu yayi kamar mace yanason yaga ta inda zata bullo amma inna ko alamun ta baigani ba, wata muguwar tsawa ya daka, Khadija dake cikin kaya saida ta firgita 'amma dayake tasan tayi lefi ko k'ok'arin guduwa batayi ba , ficewa yayi da gudu yaje ya d'auko wani key a d'akinshi yazo ya kulle k'ofar a tunaninshi ta fice yawo ne, yana fita ta fito.daga ma6oyar ta sai gumi take sharewa ,zuwa gurin kwalayen data d'ibo tayi ganin golden beer dama tasa biyu a fridge ta bud'e ko karantawa batayi ba ta hau sha jin zak'i zak'i yasata lumshe ido ,tanagama sha ta wurgar da gwangwanin ." Luuu tafara gani wata zabura tayi tafara maganganu tanacewa wai naga kamar duniyar tak'ara haskene tabb naga ta kaina yaukuma gashi goma na dare amma basai ankunna fitillah ba tafara layi tana surutai ,gyatsa tayi tace"sweet lemu kamar nasha zuma kai firig zonan kabud'e in k'ara ,ganin dai fridge bashida niyar zuwa yasata mik'ewa tana layi ta bud'e zata d'auka tafad'i k'asa tana cewa to wane mugunne kuma yake k'ok'arin ganin bayana?"can kuma tasa dariya tace"ni wallahi nagaji da wannan duniyar kuzo ku kaini duniyar ku. Jin alamun bud'e k'ofa yasata zubawa da gudu yana bud'e k'ofar yad'n matsa yana so ya kamota aikuwa ta fice da gudu tayi kitchen tasa sak'ata lokacin tafara dawowa hayyacin ta ,baibi takan d'akin 'nataba bare yaga 'abinda tasha hannu ya buga'a bango yanacewa kokuma 'ajanun k'auye sun shafeta ne shiyasa take 6acewa?"can kuma ya mik'e yayi d'akinshi jin ana kiran sallahr mgrib , bayan yayi alwala ne ya kulle gidan ta baya ya wuce masallaci ,Khadija najin fitarshi taja jiki tana tafiya tana layi tayi d'aki ,ganin gwangwanin madara yasata bud'ewa ta saida ta shanyeta tass tukun ta kuma kwanta 'a gurin bacci mai nauyi ya d'auketa ... Jin wani sanyi mai kamada ruwan k'an k'ara ya tashe daga baccin da takeyi duka taji ko ta ina tarasa waye mai dukan 'nata ihu takeyi 'iya k'arfinta 'amma innaa bbu halin tashi bud'e idanuwanta dasukayi mata nauyi tayi ganin Humaid a tsaye kamar wani soja yasata cewa to Allah ya isarmin mugu kawai buge bakin yayi ya cire bell d'in wandinshi yana dukanta ta ko ina ganin babu mai ceton ta yasata juye juye tananeman abinda zata buga mai ,ganin babu komai yasata dai daitar saitin wandonshi ta murd'e gabanshi ta zura da gudu wani wahallalen k'ara yasa mai wuyar fassara wa yarasa maiyakeji ,jiyayi kanshi na juyawa rike da mararshi ya fad'i k'asa sumamme, Khadija ko kitchen tanufa ta fere doya ta wanke ta dafata daganan ta soya da mai tanayi tanacewa kafin ya tashi naci nak'oshi mugu kawai ,tana gamawa ta soya miyar k'wai kasancewar akwai kayan miya batasha wuyaba seda taci ta k'oshi dak'yar take iya tafiya da ruwan gora 'a hannunta ta k'arasa d'akin ,ganinshi kwance yarik'e gurinda ta murd'e kumfar yawu na zuba 'a bakinshi yasata rugawa d'akinshi da gudu cikin tashin hankali wayarshi tagani a kan gado duba number tahauyi ,ganin doctor Umar yasata danna kira ring d'aya ya d'auka 'a zatonshi Humaid ne ,jin muryar mace yasashi cewa madam barka dai, cikin firgici Khadija tace "Umar dan Allah kazo ka duba Humaid dan Allah kayi sauri ko motsi bayayi ,a tsorace Umar yace " karki damu ganinan zuwa to tace"kawai domin hankalinta yafi na 6arawo tashi. Ba'a d'au wasu mintuna ba saiga horn d'in motar doctor Umar yana zuwa ya nocking d'aga murya tayi tace"shigo doctor ,da y'ar jakarshi a rataye ya k'araso yana haki'i tsabar kukan daya ku6ce mata bata iya magana ba nunamai d'akin da Humaid yake kwance tayi , shigewa yayi da sallama Doctor Umar ganin halinda Humaid yake ciki yasashi rik'e kai yana cewa innalilahi wa innailahirraji'un ya Allah help me,idonshi cike da hawaye ya kinkimi Humaid kamar gawa yasa 'a mota cewa Khadija ta kulle gidan ta biyoshi yayi to kawai ta iya cewa kasancewar gani takeyi kamar Humaid ya mutu ne." Rufawa doctor Umar baya tayi dole ta shige gidan gaba saboda 'an kwantar da Humaid a back side ,tun doctor Umar na hanya yake waya akan a tanadar musu d'akin saboda Humaid babu lafiya kuma yana buk'atar temakon gaggawa kasancewar hospital d'in akwai nisa saida sukayi tayi maid'an 'nisa sannan suka iso a keken tura marar lafiya 'aka turashi direct d'akin da 'aka tanadar musu suka tafi likitoci biyar ne akanshi amma kowa sai share gumi yakeyi ,itako Khadija sai safa da marwa takeyi a harabar asibitin ,likitoci sun shafe wajen awa 1 hour suna bincike akan suma samu nunfashin ya tsaya 'abin ya citura sai da suka kuma shafe mintuna talatin sanan sukayi sa'a ceto rayuwar shi ,ba'amayi batun gurinda 'akayiwa illa ba tukun ganin ya bud'e ido yasa likitocin cewa Alhamdulilh Allah mun gode maka ,jin ana hamdalah yasa Khadija saurin k'arasowa tana kuka tana ganin Humaid ya bud'e ido takama dariya tana yiwa Allah godiya. Likitocin'ne sukace to yanzu saimu koma kan inda yaketa nunawa tun d'azu a kunyace Khadija ta fice daga d'akin ganin ana k'ok'arin duba gurin bayan sunyi y'an bincike ne suka gano cewar yasami matsala 'agurin kuma indai ba fita dashi k'asar waje akayi ba to kafin yayi sex da matarshi zai iya kaiwa shekarar biyar kokuma k'asa da hakan kasancewar Nigeria basuda cikkakun kayan aiki,kwanansu hud'u a hospital d'in Doctor Umar shike jigila 'akan kayan abinci asibiti dai babu bataun biyan kud'in domin mai asibitinne a kwance babu lafiya. Yaune aka sallamesu Khadija na tsoron gayawa momy halin da 'ake ciki saboda hukuncin dazai biyo baya ,amma babu inda ta iya dole ta sanar dasu ,tanashirin d'aukar wayane Humaid yace "karki kira su momy dan wallah natashi saina kusa karyaki ,Khadija ce taja baya ta murgud'a mai baki tace a hakanne zaka karyani tabb wlh gara kayi a hankali karka famo gurin da 'akayima bandeji hhh, harararta yayi sanin bazai iya tashi ba yasata fad'ar hakan, rugawa tayi da gudu ta d'auki wayar ta danna number momy ring biyu ta d'auka momy ce tace" my daughter yakike lafiya tace"cankuma tace momy Humaid babu lafiya fa momy ce tace"maiya sameshi ? Shiru tayi can kuma tace" fad'uwa yayi a toilet momy ce tace"to yaji ciwo ne?eh Khadija tace"dan yanzuma 'a kawance yake kwananmu hud'u a asibiti shine yace"wai karna fad'a muku,momy ce tace"to gamunan zuwa 'Allah yakawoku lafiya Khadija tace"daganan ta shige bedroom d'inta ta kwaso kayan abincin datakai can tana cikin kwasowa ne hankalinta yakai kan kwalin golden beer d'inda tasha tana karantawa tahau salati ,can kuma tayi gumm da bakinta mayar da kwalin golden beer d'akin Humaid tayi ta tura 'a k'ark'ashin gado sauran kuma takai kitchen ,wanka tashiga tayi kwaliya kamar maishirin fita anguwa ,shidai Humaid na parlor magana ma ta isheshi ....✍️✍️✍️. Mom Islam ce *LADIDIN K'AUYE* Funny & love story. *Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa* *NA* *MOM ISLAM* *ZAINAB HABIB* *MARUBUCIYAR:* *ZAINABU ABU* *AND NOW* *LADIDIN K'AUYE* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *Episode:* 29_30 _____Momy ce ita da dady suketa sallama cikin sassanyar murya Humaid yace"wa'alaikumussalam shifowa sukayi ,ganin Humaid ya mugun ramewa yasa momy k'araswa kusada shi da sauri tace"my son maiya faru dakai naga ka koma haka ?"cewa yayi momy babu komai kwai banida lafiya ne dady daya saki baki yace"to ai Khadija tace "mana zamewa kayi ?" shiru yayi yana tunanin k'arya irinta Khadija cewa yayi eh hakane kasancewar inya fad'a musu halinda suke ciki zai 'iya fuskantar matsala dukda ciwon dayake damunshi , Allah yabada lafiya sukace daganan saiga Khadija ta fito sake baki momy tayi ganin wata uwar 'rama da Khadija tayi amma taja bakinta tayi shiru ,rungume momy Khadija tayi tana murmushi tace "momy na kinzo lafiya ?dady ne yace" to gani a gefe tunda 'an manta dani rufe fuska tayi tace"dady afuwan kunzo lafiya cikin farinciki dady 'yace"lafiya yamai jikin ? dasauk'i tace "cankuma ta shiga damuwa momy ce taga 'alamun fuskarta tace" lafiya Khadija??" fashewa da kuka tayi shidai Humaid na gefe ido ne nashi ,tsagaita kukan tayi kana tace "momy matsala Yaya Humaid yasamu momy ta bud'e baki tace" a ina?shiru tayi can kuma tace"kuma doctors sunce sai an fitar dashi waje!!! jin wanan kalmar ta k'arshe ya girgiza su momy sukace to matsala yasamu a brain d'inshi?a'a tace" tashi tayi taje ta d'auko file d'in asibitin mik'awa momy tayi ,momy na kar6a ta mik'awa dady Humaid ko dariyace taso kufcemasa wai takasa fad'ar abinda yasameshi hhh,dady na dubawa yace"innalilahi oh Allah momy ce tace"maiya faru ne ?dady daya had'a zufa ba kud'in fita k'asar wajenne damuwar shi ba larurar Humaid d'ince damuwar shi ,dady ne yagawa momy komai dagan suka fara jinjina lamarin. Dady ne yace ”Allah yakaimu gobe ,dady ne yakira waya airport saboda 'ayimusu tanadin jirgi , yayi sa'a zasu samu na k'arfe 4pm zasubi , dady ne yace ”maganar hospital d'in babu matsala wuyarshi Allah ya kaiku lafiya ,Khadija ce tace ”dady nidai bazanje ba momy ce tamaida dubanta ga Khadija tace ”to ko maiyasa bazaki ba Khadija? "shiru tayi ta sunkuyar dakai ,tana wasada fingers d'inta ,momy ce tace ”aikuwa tafiya dake dole kece matarsa mukuma daga baya zamu biyoku anjima zan sa driver yakawo miki waya saboda gaisawa ,to kawai tace” saboda musu ba halinta bane mik'ewa sukayi suna yiwa Humaid Allah yak'ara lafiya 'amen kawai yace”daganan suka fice ,mita tashiga yi tana cewa mutum bai damu dakaiba baidamu da damuwarka ba baisan darajar kaba 'amma kaje kayimai jinya daga baya 'yazo ya wulak'antaka,shidai Humaid na jinta bashida lokacin bata 'amsa kasancewar shi ta ciwon jikinshi yakeyi ,wurgamai harara tayi daganan takuma cewa wallahi mukaje ka walak'antani saina k'ara janyo wani jan aikin tunda mutum cin zali yayimai yawa ,zaro ido yayi kuma yana mamakin wai yatsaya wanan shegiyar yarinyar tana gayamai maganganu baid'au mataki ba ,tunawa yayi sai an temakamai zai 'iya tashi k'wafa yayi ya maida kai ya kwanta 'akan kujerar bud'e baki Khadija tayi tace ”da dukana zakayi ahayye ni Dije wallahi kama sameni ne da lokacin da nake garinmu ne tabb dakadinga yimin ladabi dan bana d'aukar 'raini, Humaid maganganun Khadija sun 6atamai rai sosai amma da yanada lafiya babu abinda zaihana ya hukuntata, amma 'akwai lokaci ." Komawa d'aki tayi tafara had'a kayanta dakuma 'abubuwan dazata buk'ata kitchen ta wuce ta d'ebo naman kaza 'a fridge ta sa kayan k'amshi dasu atta ruhu ta tafasa naman yana dahuwa ta d'auko turmi tafara dakawa da 'alamu dambun 'nama zatayi bayan tagama ne tahau suya rana gama suya ta d'ibo dakkaken yaji ta zuba 'a roba takai jakar tafiya , d'akin Humaid ta nufa tana duba kaya tana dariya gajerun wanduna ta d'ibar mai sunkai guda ishirin sai t sheet guda goma ,nikwa nace to ina manyan kayan ?" golden beer d'inshi ta d'iba har guda biyar tasa 'a jakarshi ,saikuma man shafawa dakuma takalmanshi tana gamawa ta fice ta nufi d'akinta . Washe gari misalin k'arfe 9am saiga driver da abincin karyawa dakuma kwalin waya ,tana rawar jiki suka gaisa mik'a mata sak'on yayi godiya tayimai tashige ciki da gudu ,ganin babu Humaid yasata rik'e baki tace ”toshi harya sami sauk'i ne?"batada mai amsa mata tambayarta yasata yin shiru ,tafara duba wayar spark 2 ce maikayau sosai bud'e abincin tayi ganin soyayyen dankali dakuma wainar k'wai a gefe yasata kwashe k'wan tabar dankalin a dining, komawa d'aki tayi tacigaba da shiri wnka tayi ta fifito da kayan data d'ibar musu komawa tayi hanyar d'akin Humaid tana shiga ta hangoshi rik'e da waya 'a hannu da 'alamu charting yakeyi ,girgixa kai tayi tafara cewa lallai to ai basai anje Indian ba tunda kaji sauk'i barin cewa su momy wai abarshi ,da mamaki yake kallonta dubanta yayi 'irin kallon kinrainani d'inan yace”wallah zan 6a66allaki wucemin anan dan ke bata yimiki amfani shine zakimin mugunta ko muguwa kawai dariya tasa tace”kai kadamu da iskanci nikam Allah ya sitiri buk'wai ,shiru yayi ganin raini zai shiga tsakani ,k'arawa gaba tayi tace ”daya d'auka ni yar iska ce ,hmm to ma wai da dayakecemin mazinaciya menene amsar hakan?tana yiwa kanta tambayoyi can kuma tace ”ok natuna lokacin da Ammar ya saceni shine yake zargin 'nice naje d'akinshi?rasa maibata 'amsa tayi hakan yasa takoma d'akinta tana saka sim card a wayar ta memo ta d'auko wanda tayi seven number k'awayenta dakuma ta momy saka numbobin tashiga yi tana murna." Da misalin k'arfe 3:dai dai dady 'yakira Khadija kasancewar sund'au number tata tana d'agawa dady yace”to inkun kammalah gamu nan a hanyar zuwa airport ku hanzarto angama komai tun jiya to tace”gamunan zuwa dady ,zuwa d'akin Humaid tayi tace ”kafito gasu dady can a hanyar airport mik'ewa yayi jiki babu k'wari yace ina kayana?cewa tayi gasunan a jaka bud'e gurin kayan 'nashi yayi yakuma lodar 'rigada wando kamar yasan bata d'ibarmai ba ,cemata yayi bar 'rawar jiki dan kona sami lafiya 'aure zan k'ara ,Khadija ce tace ”a hakan da babu k'arfin jikin kana tafiya kamar mace,zaro ido yayi yace"wlh zanci ubanki shigewa tayi tarabu dashi tasandai koba komai ta gasamai magana. Shigewa mota sukayi sun d'anyi tafiya sanan suka iso airport d'in samunsu momy sukayi a zaune suna jiransu k'arasawa gurinsu sukayi suka durk'usa suna gaisuwa Humaid dak'yar ya mik'e itako Khadija dariya takeyi k'asa k'asa jin lokacin tafiyarsu yayi yasa momy yimusu fatan 'nasara ta mik'awa Khadija wani babban jaka mai zurfi ,dady ne yace ”nayima transfer na kud'i bakada matsalar su godiya yayiwa dady daganan suka shige jirgi ,hawaye Khadija tafara shareware saboda tasan momy ma dauriya kwai takeyi ,jin tashin jirgin yasata rik'o Humaid ta matseshi tsaki yaja yace ”dalla ni karki sakamin k'azamin jikinki banza kawai ko kulashi batayi ba tacigaba da rik'eshi ,shikuwa bashida k'arfin kokawa yasa ya k'yaleta....✍️✍️✍️. Mom Islam ce *LADIDIN K'AUYE* Funny & love story. *Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa* *NA* *MOM ISLAM* *ZAINAB HABIB* *MARUBUCIYAR:* *ZAINABU ABU* *AND NOW* *LADIDIN K'AUYE* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *Episode:* 31_32 _____Suna sauka cikin ikon Allah saiga wani bature yazo yake cemusu ance yanuna musu masaukin su Humaid saboda rashin yarda yace "saiya kira dady aikuwa yana kira dady 'yace”nine na turoshi dafatan kun sauka lafiya ?lafiya Lou Humaid yace”daganan suka shige motar wanan bature ,itadai Khadija gajiyace ta buwaye ta dan burin ta bai wuce taganta tana hutawa ba ,wani katafaren hotel suka sauka Khadija ce tazaro ido tace"nifa tsoron jajayen fata nakeyi wallahi kar azo angama cinikinmu, Humaid ne ya gimtse dariyar sa shikuwa wanan Bature babu abinda baijiba wanada Khadija tafad'a kasancewar yana mu a mula musulmai sosai amma shi Christen ne saboda baya sallah ,door bell baturen ya danna k'ofar ta bud'e da kanta zaro ido Khadija tayi tace”to Allah gamu gareka tana tafiya tana sambatu shikuwa Humaid ko kallonta baiyi ba ,direct wani rantsatsen step naga sun hau d'aki mai number goma suka shiga ,Humaid ganin ba'ayi maganar komai ga shuwagabanin hotel d'inba yasashi cewa to sukuma masu hotel d'in anbiya sune?eh baturen yace”tun jiya dadynku yayi komai ,godiya Humaid yayimai mutumin 'ne yace”sunanan Joseph barin baka number ta musayar lamba sukayi daganan Joseph yace”suyi wanka su huta za'a kawo musu abinci . Tana shiga d'akin Humaid ma yashigo tunda tashigo take kallon d'akin kyau tsari gakuma nerorin da 'aka kashemai tabb tace ”lallai wasu basusan zafin kud'i ba ,Humaid da gajiya ta tarumai yace”to sannu 'uwarsu zaki 'iya fita ki sanar musu ,ko kallon inda yake batayi ba tashige bathroom wanka tafarayi kasancewar akwai sabon sabulun wanka da sabbin brush da man goge baki saida tayi wanka sanan ta d'auro alwalah tafito ganin har bacci yafara d'aukar Humaid yasata kurma uban ihu tace”wayoo nashiga uku ,a firgice Humaid ya farka yana salati ganin Khadija tayi shuru yasashi cewa komai aka had'a da jaki saiyyaci kara ,zaro ido tayi tace”waye jakin nikake kira da jaki, murmushin takaici tayi tace ”d'an adam mai mance hallacci babu komai kasan ba'acin bashina ,mamakinta yakeyi dahar take gayamai maganganu san ranta saboda taganshi a kwance bazai 'iya 'aikin k'arfi ba yasa takeyimai wulak'anci ,dariya yasa lokaci d'aya kuma yace”yaro baisan wutaba saiya taka." K'yaleshi tayi tafara sallah tana idarwa ta dubo al qur'anin data taho dashi tafara rera karatu , idon Humaid a lumshe kamar mai bacci ya bud'e ido yana saurarrar karatun Khadija jiyakeyi kamar karta dena ,bayan takammala karatunne ta mik'e tayi gurin kayansu bud'e jakarta tayi ta dubo atamfa rigada skirt mai adon flowers green zatasa kayan ta tuna 'aifa Humaid na d'akin juyawa tayi tace ”malam zaka iya juyawa saboda zansa kaya karkuma 'a kalleni ehe, juyowa Humaid yayi yace”wanan banzan jikin'naki mezan kallah jikinda kowa yagama ganinsa ,tanajin takaicin wanan kalmar amma 'akwai lokacin ramako, d'ibar kayan tayi takoma bathroom ta sanya sanan tazo tana shafa mai kasancewar garin da zafi kuma dukda sanyin AC mutum gumi yakeyi ,kwaliyarta tayi a nitse sanan wuce dining table d'inda 'aka kawomusu abinci ganin cimar kamar ba irin tata ba yasa ta had'e fuska tana rik'e ciki ,hango wayar tafida gidanka tayi ganin 'number su a calendar yasata d'auka cewa tayi nifa bazan iyacin wanan jagwal gwalon ba 'akawomin tuwo kokuma indomie mutumin da baigane maitake cewa ba yace ” give me one minute please am coming zaro ido tayi tace ”tabb 'banza shima turancin bai gama bakinsa bba." Humaid daketa dariya yana k'arawa yace”LADIDIN KAUYE y'an mata had'e rai tayi tace”wallahi kabari dan banhuce na d'azu ba, shiru yayi dan yasan komaiye ma zata rina 'aikatawa ,nocking aka farayi Humaid ne ya lala6a ya mik'e saikuma ya tsaya yace ”saikije kiyimai bayani,Khadija ce tace”bagane nawa turancin zaiyi ba dan 'naga shima koyo yakeyi yanzu hakama brain d'ina tafi tashi ,wucewa kawai Humaid yayi ya bud'e k'ofar mutumin 'ne d'auke da farantin abinci bud'ewa yayi yaga indomie ne aciki godiya yayiwa mutumin daganan yasauka k'asa da tiren abincin samun guri yayi yafara loda indomie saida ya cinye duka sanan ya tashi yabar plet d'in agurin yakoma sama. Samunta yayi ta rafka uban tagumi tana kuka ko kallon gunda take baiyi ba bare tasanma yaganta taji dad'in 'narkewa bathroom ya wuce yayi alwala yazo ya gabatar da sallah tunda yayi sallama yaketa jero adu'a 'akan Allah yabashi lafiya ,itadai Khadija tarasa meke yimata dad'i a duniya kasancewar bata ragawa ciki ko kad'an mik'ewa tayi taduba maid'an dama dama tafara tuturawa badan yayi mata ba tana gamaci ta d'auki waya takirawo momy cikin farinciki momy tace” daughter dafatan kuna lafiya dai ko?eh muna lafiya Lou "amma momy 'yaushe zakuzo?momy tana murmushi tace”gobe ne insha Allah muna zuwa zamu wuce hospital amma zaku rigamu wucewa,to kawai tace shikuwa Humaid dama can magana ba damunshi tayiba, daganan sukayi sallama da momy. Dare nayi basuci wani abinci mai nauyi ba ,Humaid na k'ok'arin hayewa gadon tarigashi ,hak'ura yayi ya koma k'asa ya shinfid'a bargo ya kwanta . Washe gari bayan sunyi sallahr ashba babu wanda ya koma shirin tafiya 'asibiti sukeyi bayan Humaid ya fito daga wanka yaduba jakarda Khadija, ta lodamai kaya 'acikin ganin gajerun wanduna yasashi salati yace”wato kinmaidani d'an iska kenan ko ?cigaba tayi da kwaliyarta daganan ta mik'e tana cewa to inka shirya nizan wuce ,Humaid ne yace”kin dad'e baki wuce ba banza kawai jibeta 'ahaka kamar saliha ,shiru tayi saboda batason wanan kalmomin da yake jifanta dashi amma burinta lokacin yazo . Yana gama shirin ya fice ko magana baiyi mataba jitayi yana kiran Joseph a waya dagudu ta fito tana tsaki ,ganin Humaid yashige mota yasata bud'ewa tashige da sauri wani katafaren hospital suka nufa suna sauka koshi Humaid ' d'in saida ya jinjina kyau irinna asibitin suna zuwa 'aka tarbesu office suka wuce domin ganin babban likitan suna shiga sukaci karo da wani mutumin farine dogo yanada jiki amma ba sosai ba yanada bak'in gashi dakuma gashin baki wanda yafito da tsananin kyawunshi ,kallon Humaid yakeyi kallon a ina nata6a ganinka Humaid ne yace ”aslamu alaikum mutuminne ya mik'awa Humaid hannu cankuma mutumin yace”naso nasanka koba kaine Humaid Abdullahi ba ?gingina kai Humaid yayi yace ”nine nima kamar nata6a ganinka 'a lokacin da zamu bud'e hospital d'inmu ,tunani mutumin yayi cankuma yace”ai dadynka abokina ne sosai kuma yayimin bayanin komai toya jikinnaka dasauk'i Humaid yace ”daganan yafara yimai tambayoyi." Doctor d'inne yakai dubanshi ga Khadija yace” wanan iyalinka ce? a'a Humaid yace”. K'anwata ce OK doctor yace ” please zaki iya bamu guri akwai wata magana danakeso muyi maganar ta doki Khadija to kwai tace tafice daga office d'in ,tasami guri ta zauna tana zuba uban tagumi ✍️✍️✍️. Mom Islam ce *LADIDIN K'AUYE* Funny & love story. *Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa* *NA* *MOM ISLAM* *ZAINAB HABIB* *MARUBUCIYAR:* *ZAINABU ABU* *AND NOW* *LADIDIN K'AUYE* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *Episode:* 33_34 _____Zuciyarta na k'una tarasa maike yimata dad'i amma babu komai ,doctor ne yakai dubanshi ga Humaid yace” yakamata kasani akwai aikin dazamuyi maka kuma yana buk'atar nutsuwarka gaskiya ko kanada mata saidai tayi hak'uri har na tsawo one month kasancewar aikin 'na buk'atar kulawa ,cikin farinciki Humaid yace” doctor ashe zan warke daganan suka fito doctor yanunamai d'akin dazai shiga ,batare da yayiwa Khadija magana ba yashige d'akin yana murmushi 'itako Khadija dataga batada muhimmanci yasata komawa masaukin su zama tayi tadinga rusa kuka kamar wace akayiwa mutuwa ,had'a kayanta tashiga yi tana surutai da alamu ranta ya 6aci sosai ATM d'inshi ta d'auka ta d'auki jakarta tayi waje ,rasa ina zatayi tayi zuciyarta ce take cemata ki koma Nigeria kawai ,hakan ko akayi ta d'auki shawarar zuciyar ta ,mutumin dake jigila dasu wato Joseph shi ta kirawo a waya tacemai dan Allah yazo ya kaita airport ,cemata yayi aisu alhaji suna hanya mezatai a Nigeria ,cikin zak'uwa tace ” fils na maganin Humaid aka manta kuma dole saidasu za'ayimai aikin , cemata yayi to bari yakirawo y'an airport d'in yaji ko jirgin 'Nigeria ya tashi, to tacemai dan burinta taganta 'a k'asarta yana kira yacemata nanda 30 minutes sasu tashi ,cikin hanzari taje ta tarkato kayaanta tafito ta kullo d'akin ,barin keys d'in tayi a hotel d'in suka wuce filin jirgi 'itada Joseph ,lokacin da suka isa 'ana kiran Nigeria dagudu tashige kasancewar yanzu harkar Bank akeyi tabiya kud'in komai . Duba lokaci tayi a ’agogon dake d'aure a hannunta k'arfe 10:23am jin jirgin zai tashi yasata yin adu'a can kuma taji hawaye tafara cewa kuyi hak'uri momy ba'asan raina nadawo ba 'amma babu inda na iya saboda bak'incikin da Humaid ke k'unsamin bayan wasu mintuna ta jirgi ya sauka murna dakuma danasani fall cikin Khadija saboda tana ganin kamar batayiwa su momy adalci ba ,tana sauka tacire sim card d'inta tasai wani wanan kuma tasa 'a jakarta direct gidansu ta wuce wato gidan Humaid ganin mai gadi nanan yasata farinciki nocking tayi had'e da sallama cikin gaggawa mai gadin ya bud'e mata yana cewa hajiya sannunku da dawowa ywwa tace”tashige ciki mai gadin mamaki yafara to ina Humaid d'in??tabb 'bashida mai bashi amsa yasa shi yin shiru, da k'atuwar jaka tafito saboda ta d'ibo kayan abinci su katan d'in indomie dakuma su Maggi star da mangyad'a duka ta loda 'a jakar ,mai gadi naganinta da d'irmemiyar jaka yasashi zaro ido amma babu batun magana ,ficewa tayi batare datace ga inada zataje ba , bank taje taciro kud'i masu ywwa daganan ta dawo gida ,maida jakar tayi tana haki . *ACAN INDIA*? Tunda momy suka sauka take gwada number Khadija shiru a kashe ,dady ne yakira Joseph yace”yakaisu hotel d'in da Khadija suka kama d'aki acan ,Joseph da jikinshi yafara sanyi yacewa su dady wanan madam d'in yau tatafi Nigeria, what!!! Dady 'yace”cikin kid'ima ya 'akayi hakan tafaru maikuma yafaru momy da batada wuyar kuka tace”wallahi Humaid ne sanadi dama ba sonta yakeyi ba shine ko rayuwarta ta salwanta bashida matsala ko tana kuka tana magana ,dady ne yace” Joseph muwuce hospital d'in kawai ,mota suka shige suka nufi asibitin da isarsu sunyi sa'a wanan doctorn yanan office d'inshi suka wuce bayan sun gaisa ne sukace ya mara lafiyar yake dasauk'i doctor yabasu amma tare da shada musu d'azu akayi aikin kuma 'akwai alamun nasara masha Allah sukace yanzu ina yake?doctor ne yace” yana room 3 , amma naga bank'ara ganin sister nashi dasukazo d'azu ba ,lokacinne momy tace”matarshi ce doctor ne yace”amma shine yacemin ba iyalinshi ba ,dadyne ya mik'e suka fito dasu momy dakuma doctor room d'in aka nuna musu suka shige." Ganinshi kwance yana bacci yasa dady dka mai tsawa yace ”ina kakai Khadija?? "arazane ya tashi yace”dady 'yaushe kuka iso ?babu wanda ya kulashi dan haka yayi shiru ,can kuma yace”ai takoma hotel ,dady dayaga Humaid nason raina masa hankali yace ”hotel d'in ubanka !!!... Momy ce tace ”nidai yanzu damuwata number Khadija kuma gashi a kashe kiran number Jalal sukayi yana gurin aiki yace”bai gantaba rasa yazasuyi sukayi saboda halin marainiyar Allah, ... Haka sukayi kwana uku a daddafe duk a tunaninsu Khadija tana gidanta ,a kwana na biyar ne aka sallame su kasancewar Humaid yaji sauk'i sosai gobe zasu dawo Nigeria tunda suka koma hotel d'in Humaid yashiga damuwa dan yasan indai ba'aga Khadija ba to shima ya 6ata dan wallahi saisu momy suncimai mutunci fiyeda tunani, washe sukayi shrin zuwa Nigeria ,jirgin safe sukabi . *NIGERIA* Sun sauka lafiya daga saukarsu gidan Humaid suka wuce maigadi ne yace”hajiya fa jiya tabar gidannan saboda naga ta loda kaya 'a wata k'atuwar jaka tashiga motar ta ko magana batayiba ta shige ,momy ce tazaro ido tace”yanzu fargabar da Khadija take jefamu yayi kenan ?" Dady cikin k'unar 'rai yace”kai kuzo muwuce duk inda zataje taje zamatadawo da k'afarta momy na kuka tana kiran sunan Khadija gashi wayarta bata shiga ,Humaid kam yakasa magana dan yasan kad'an suke jira sufara balbaleshi da masifa 'a motar Humaid suka wuce can anguwarsu momy suna sauka Jalal na shigowa yana ganinsu yace”ina Khadija fa momy ce tashige ciki da 'alamu kukanne zai ku6ce mata shikuwa dady cewa yayi ta 6ata ,Jalal daya tsaya kamar gunki yarasa takamai man amsa yace ”to nikam yaya Humaid ina Khadija? "wani mugun kallo Humaid yayiwa Jalal daganan yashige ciki. Damuwa iya damuwa sun shiga sosai amma shi Humaid bai damu sosai ba kasancewar ba damuwarshi bace ,dady dayaga abin babba ne dan yau da dawowarsu kwana uku yacewa su momy su shirya suje k'auye ko tana can ,momy batayi wata kwaliya sosai ba ta fito suka wuce itada dady ... Da isarsu malam Adamu yafara yimusu lale marhabun shigewa gidan sukayi suka sami 'inna tana zaune tayi k'wad'on rama ,zubo musu tayi aka kawo musu ruwa mai sanyi na randar k'asa ,malam Adamu ne yace”ina zuwa can anjima saigashi yadawo da k'waryar fura da nono dakuma ludaya ,zuzubawa su momy akayi bayan sunci sun k'oshi sukace dama 'abinda yakawomu shine mund'auka Khadija tazo nanne?"inna dake cin rama tace”walhi rabona da ita tunda 'akayi bikinsu nikam mukuma bamu k'ara wai wayarku ba malam Adamu ne yace”to yar marainiyar Allah ina tashiga momy ce tace”har wayarta sun gwada amma 'a kashe ,shirin komawa sukayi dady 'yabawa malam Adamu dubu hamsin sukayi gaba,godiya su inna suka dinga jerowa suka yimusu rakiya,har zuwa gurinda sukayi parking d'in motarsu. Dady 'yana tuk'i yana tunani anya ba wani abin Humaid yayiwa Khadija ba dan sunsan halinta batada son zuciya ,momy ma 'a tata zuciyar tunani takeyi kodai Humaid ya cusa mata wani mugun abunne yasata guduwa ,har suka bar garin babu maiyiwa wani magana,da isarsu jos suka wuce gidan TV da gidan redio domin bada sanarwa ko 6ata tayi ...✍️✍️✍️. Mom Islam ce *LADIDIN K'AUYE* Funny & love story. *Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa* *NA* *MOM ISLAM* *ZAINAB HABIB* *MARUBUCIYAR:* *ZAINABU ABU* *AND NOW* *LADIDIN K'AUYE* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *Episode:* 35_36 _____Daganan sukayi gida jiki babu k'wari kowa ya sauka 6atan Khadija yazame musu tamakar mutuwa tayi ,dady ne yakira Humaid a waya yake cemai maza _maza yazo yanason ganinshi ,gaban Humaid na fad'uwa ya shigo gidan bayan yayi parking d'in motarshi ne ya shiga parlor ganin babu kowa yasashi wucewa d'akin dady ,samun dady 'yayi a kishingid'e kamar mai bacci, da sallama ya shiga yanemi guri ya zauna zaice ina wuni dady, _dady 'yace”bana buk'atar gaisuwar ka saboda yanzu batada 'amfani kuma wallahi kaje ka nemomin Khadija duk inda tashiga kokuwa kayi danasani a rayuwarka ,gumi ne yafar a keto mai tako ina yace”dady nimafa wallahi...wani azabbaben mari dayaji saida ya mik'e yana shirin bigewa da bango ,ficewa yayi daga gidan yana gunguni ,shima Humaid d'in gidan TV da gidan redio ya nufa yabada cigiya daganan yakoma gida yana 'adu'oi akan Allah ya baiyyana ta yafita daga masifar da iyayenshi suka kirari ,yaukam hankalinshi ya tashi sosai ganin fushin dady ba k'aramin tsorata yayi ba . Washe gari ko gigin zuwa gidansu baiyi ba kasancewar bayason jin kalmomin da zasu hargitsamai k'wak'walwa , gashi yau saura sati d'aya ciwon jikinshi ta warke ,kuma yanada burin yin aure domin 6arje sabon shafi ,amma baisan wazai tunkara da maganar ba tunda wanan muguwar ta gudu ai ta jazamai fitina ,kwata_kwata bashida kwanciyar hankali kamar shine marar gata 'a duniya 'amma yasan mafita k'auye ya nufa gidansu malam Adamu yana shiga yasamesu suna ,zaune shida inna bayan ya gaishesu ne yake yimusu jajen 6atan Khadija ,malam Adamu ne yace”yau kimanin sati uku kenan Allah yasa tana raye ,amen yace ”can kuma yace”dan Allah baba inaneman wata 'alfarma ne ,babane ya maida hankalinsa ga Humaid yace” inajinka yaron kirki maiya faru ?"sunkuyar da kai Humaid yayi yace” baba sonakeyi nayi aure kafin Allah ya baiyyana Khadija muci gaba dayi mata 'adu'a." Jinjina kai malam Adamu yayi saboda lamarin babu dad'i wato shi ta 'aure ma yakeyi ,cankuma yace” karka damu yarona yaushe iyayen ita yarinyar sukace ka turo ?"cikin rawar jiki Humaid yace” ranar juma'a ne ,malam Adamu ne yayi lissafi yace” saura kwana hud'u kenan to insha Allah zanzo kuma kafin inzo zankira mahaifinnaka muyi magana ta waya ,inna ko sai jinjina kai takeyi tana tuno Khadija, godiya Humaid yayi tsabar farinciki bandir d'in y'an dubu ya 'ajiye masa yana komawa mota ,yakira budurwar tashi saida sukayi hira sosai sanan sukayi sallama , ya mik'i hanya tafiya yakeyi cikin farinciki da nishad'i saboda yakusa zama 'ango hhhh... Tunda yakoma gida ya kirawo masu decorection d'in gida gyra 'aka yiwa gidan kasancewar yarinyar y'ar manya ce shiyasa yakeson shima 'asan d'an manya ne ,part d'inta na can gefe gaban d'akin Khadija kayan Khadija kuma 'yadawo dasu k'asa 'amarya takoma sama ,kwana uku da magana ,dama Humaid ko k'ok'arin dosar gidan baiyi ba ,momy dajin zancen auran Humaid batace uffan ba haka shima dady 'yace” babu hannunshi ,malam adamu ne sukaje gidan surukan shida Humaid shikuma Humaid ya wuce gurin budurwar sa mai suna khairat ,hira sukeyi cikin so da k'auna dama irinta ya dad'e yana nema wato mai budadd'en ido ,ruk'omai hannu tayi tace”zomuje zagayeshi tadingayi da girma dakuma shuke shuken gidan suna rik'e da hannun juna.... Malam Adamu na fitowa ya koma can gidansu dady baisami dady a d'akinshiba yasa ya danna number Humaid, yana d'agawa malam Adamu yace” to kazo anyanke magana ,cikin azama Humaid yabaro gidan yayo gidan su ,samun malam Adamu dayayi shi kad'ai yaji dad'i sosai ,malam adamu ne yace” sun yake dukiyar aure nabada cikin kud'in da kabani d'azu to ansa biki sati uku masu zuwa ,godiya Humaid yaketa yimai daganan malam Adamu yace” zai koma, wasu mahaukatan kud'i Humaid ya d'ibo yabawa baba ragewa yayi kana yace” Allah yasa 'albarka saganan sukafice ,Humaid da sauri yafice daga gidan kamar marar gaskiya hmm.. Da kanshi yaje ya had'o kayan akwati daganan ya zarce gidan mahaifiyar momy yabata labarin abinda yafaru da Khadija amma yad'an had'a da k'arya ,su hajiya lefinsu dady suka dinga gani kuma sukace insha Allah zasu tsayamai kan maganar auran ,godiya yayi musu yabar kayan a gidan yadawo gidanshi ... Yau saura sati biyu biki shirye²akeyi ta kowane 6angare amarya kuwa gyara takesha kamar ba gobe ,batun soyayya kuma sai abinda yayi gaba dan babu baya, ana biki saura 1 week ne dangin momy suka kai kayan akwati ,da shigarsu dangin maman khairat suka hau gulma suna cewa ji wanan banzan akwatin kamar na y'ar talaka ko besan wa ya 'aura bane?,sudai dangin momy haka suka kai kaya suka dawo jiki a sanyaye, dady ne yakira Humaid a waya yake cemai duk wasu takkaddu dayasani na hospital d'inshi to ya tarkato ya kawomai dan haka shima tuna 'aure zaiyi yafara neman 'nakanshi tashin hankali gamida rikicewa Humaid yashiga ko 6atan Khadija baisashi shiga damuwa irinta yauba ,hak'uri yake bawa dady amma ina dady 'yace” aina rantse ,daganan dady 'ya katse wayar .... Yau saura kwana biyu d'aurin aure Humaid yayi d'inkuna sunkai kalla goma saboda murnar khairat ,a yaune dady 'yabada saukar alkur'ani mai girma masallatai akan 6atan Khadija , Humaid ne ya tattarawa dady kayanshi ya kaimai ,dady ko kallonshi baiyiba shikuwa Humaid mamakin abinda dady 'yayimai yakeyi ,kiran Jalal yayi a waya yake fad'amai halinda yake ciki ,Jalal cikin k'unar'rai yace ”to Allah ya kayauta nikam ina goyon bayan dady kasancewar baka damu da Khadija ba,Humaid ne yaja waya ya kashe saboda 6acinran yafara isarsa." Washe gari akayi dinner anzubar da kud'i a bikinnan ,Humaid ko tunaninshi in kud'inshi suka k'are ina zaisami wasu ?amma bashida 'amsa gashi yarinyar sai k'irk'iro hidimomi takeyi kuma bayason yin harkar k'aranta hmm ,momy kam tamik'wa 'Allah komai ganin Khadija batada niyar dawowa gashi yau watanta biyu bata gida 'Allah yasa dai tanacikin k'oshin lafiya . *WEEDING💖💫* Yaune dubban jama'a suka shaida d'aurin auran Humaid ADAM da 'amaryarsa KHAIRAT USMAN DOLLARS akan sadaki dubu d'ari biyar hmm tofa riders kunjifa 😉,kowa mamakin kud'in auranan yakeyi amma babu mai bakin mgna kasancewar gaba da baya securitys ne kewaye da gurin ,y'ar manya kenan,misalin k'arfe 9pm aka wuce da ita gidanta ,duk iskancin su saida suka yaba da gidan saboda ba k'aramin kyau yayi ba misalin k'arfe 10pm kowa ya watse daga 'amarya sai ango ,bayan sunyi sallah ne ya dafa anta yayi mata 'adu'a daganan aka faracin kaji ,bayan sun kammalah ne Humaid yashige wanka 'a can toilet d'in shi itama 'amaryar wanka tashiga ta sanya sleeping dress.....✍️✍️✍️. Mom Islam ce *LADIDIN K'AUYE* Funny & love story. *Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa* *NA* *MOM ISLAM* *ZAINAB HABIB* *MARUBUCIYAR:* *ZAINABU ABU* *AND NOW* *LADIDIN K'AUYE* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *Episode:* 37_38 _____Da sallama yashigo yana sanye da gajeren wando ,ganinta 'a kwance kan gadon yasashi rungumo ta ,itako amarya jin haka yasata fara kissing Humaid cikin zumud'i humaid dai rasa kuzarinshi yayi saboda Khairat na neman sauya salon izuwa cire kayanta ,humaid ko mamakin inda khairat bata tsoron wanan dare yakeyi saboda yaji ance duk mace na tsoronsa, mirginawa gefe yayi yana maida nunfashi khairat kuwa haushi yabata dan ita bataso hakan ba ,Humaid zai mik'e takuma taroshi tace ”wallahi baka isaba kamance da hakk'ina daya rataya a wuyanka?"shiru Humaid yayi can kuma yakoma gurinta ,kasancewar itace jigon abin yasa baisha wuyar samun hanya ba ,ko jigata sosai batayi ba ,lokacinne Humaid yafara sambatu yana shimata 'albarka kasancewar tana tareda budurcin ta ,bayan yasami nutsuwane ya sauka 'aikuwa yana sauka ta matsoshi ,cewa yayi wanka zanyi na kwanta lokaci yayi nisa, zaro ido Humaid yayi yace”to ai saimu kwanta amma yanzu tashi muje muyi wanka ,mak'e kafad'a tayi tace ”wallahi ni bai 'isheni ba 😒garama kadawo ,ficewa yayi ko kallinta baiyi ba itako Khairat kuka tafara tanacewa namiji kamar mace babu kuzari wallahi saina gyaraka. Tunda Humaid yakoma d'aki yafara tunanin ko.Khairat na daga cikin wa inda' ake cemusu harijai ne shifa bazai 'iya yin abu kullum ba kamar abincin gida ,ya shige wanka ,6angaren Khairat kuwa lokacinne takumajin wata sabuwar sha'awa na tasomata zabura tayi ta mik'e tafito part d'in Humaid ,ganin k'ofar a bud'e yasata shigewa batare datayi sallama ba ,cire kayan jikinta tayi ta kwnta d'ai d'ai tana jiran shigowar Humaid ,Humaid yaga lokacin datashigo yasashi k'in fitowa daga bayi ,yanemi guri ya zauna kamar zaiyi kuka, itako gajiya datayi da jiranshi yasata batasan lokacinda bacci mai nauyi yayi gaba da itaba ,yana ganin tayi bacci ya fice kamar munafiki cikin sand'a ,parlour yakoma ya kwanta. *WASHE GARI*🤙 Washe gari kowannen su yatashi yayi sallah shiko humaid masallaci ya wuce saida gari yayi haske sanan yadawo gida, yana shigowa ya tarar da khairat da fara'arta tazo dagudu ta rungume shi ,shima fara'a yayi mata daganan tajashi zuwa dining, k'arewa kwaliyarta kallo yakeyi dan ba k'aramin kyau tayiba ,sanye take cikin riga doguwa ta shadda mai ruwan pink 'suna isa dining ta bud'e wani food flaks mai shegen kyau ,humaid ne yace ”wanan kuma daga Ina "tana murmishi tace ”daga gidan momy na ,masha 'Allah yace Allah yabasu lada 'amen khairat 'tace ”daganan tafara saving d'inshi tana bashi a baki ,farinciki fall zuciyar humaid yana cewa yanzufa nayi aure ,aini 6atan khadija yayimin rana tabb da tanan babu maibarina inyi aure ,shima bata'a baki yashiga yi saida suka k'oshi tukun khairat ta taso daga chair d'in datake zaune ta haye jikin humaid ,wasu abubuwa takeyi mai masu wuyar fasarawa abinka da farin shiga dan danan yafara sauya sallo ,kinkimarta yayi sukayi bedroom d'inshi ,ya shafe minti hamsin suna 'abu d'aya." Dazai tashi saitace ita bata gaji ba ,fuska kamar ta mai kuka🤣 yace ” please Khairat live me tofa hmm cikin kasalaliyar murya tace ” yanzu wasan yafara dan wlh nikam ban gaji ba ,jiki a sanyaye ya zame yaje yai wanka ya dawo ,ganin zata kamoshi yasashi ficewa da gudu yana haki, misalin k'arfe goma sha biyu 12pm zaune suke shida Khairat suna kallo ganin abinda take gari yasashi had'e fuska yace ”kewai saikace ba mutum ba kullum abu d'aya ?"k'ara matsoshi tayi ,can kuma sukaji ana nocking ,humaid ne yace ”jeki sako hijab ,mik'ewa tayi ta shige ciki ,shi kuma humaid yaje domin bud'e k'ofa ,yana bud'ewa yaga doctor umar ne dakuma doctor sufiyan ,da fara'a ya tarbesu yana yimusu sannu da zuwa zama sukayi ,aka fara yiwa humaid tsiya, akan ango ya 6uya ko office yak'i zuwa murmishi yayi musu yace ”insha Allah yanan lek'owa ,Khairat ce tafito da hijab hark'asa ta zauna suna cemata 'amarya kinsha k'amshi dariya takeyi amma idanunta nakan humaid saboda tsananin buk'atarshi takeyi ,drinks ta mik'e takawo musu da cincin dakuma dubulan sunci babu laifi daganan suka ce zasu wuce , humaid ne ya fice rakasu ,daganan yadawo domin kwanciya yake buk'ata saboda gurin da 'akayimai aiki yanayimai zafi ." Khairat ce tashigo da wasu mahaukatan kaya rigace ko cinyarta bata k'arasa ba ta fad'a jikin humaid ,juyawa yayi yana rik'e da gabanshi yana wani ihu ,khairat na ganin abin kamar wasa kuma dai taga yafi k'arfin k'wa_k'wal warta, mik'o mata waya yayi yace ”ki kiramin doctor Umar please ,jiki na rawa ta dubo number ,ring d'aya doctor Umar ya d'auka gamida yin sallama ,Khairat ce tace ”Umar humaid babu lafiya wallahi ,a tsorace doctor Umar yace ”to kicewa drivern gidanku ya kawoku hospital d'inmu , to kawai tace ”daganan ta kamawa humaid ya mik'e ,parlor takaishi ,itakuma takoma bedroom d'inta ta sauya kaya ta d'au hijab da takalmi marar tudu suka wuce, driver takirawo dagudu yazo ya tsuguna yace ”hajiya gani "cemai tayi maza_maza fitoda mota asibiti zamuje ,angama hajiya yace ”yana fitoda mota ta rik'e humaid tasashi a mota ,mintuna kad'an saigashi sun iso ,cikin gaggawa doctor Umar ya taresu yashige da humaid room d'in da 'aka kwantar dashi kwanaki.... Dubashi yashigayi da na urori , ganin lamarin yakusa dawowa nada yasashi share ,wahalalen gumin daya tsa tsatsafo mai ya dubi humaid daketa maida nunfashi yace ”humaid kana wuce gona da iri fa ,humaid cikin wahalaliyar murya yace Umar babu inda na iya naje na 'auro wacce k'arfin halittarmu batazo d'ayaba ,Umar ne yace ”to wallahi 'inkacigaba da sex kullum kokuma sau hud'u a rana wallahi saidai wataran ka hak'ura da mace ,kana kallonta amma bazaka iya ta6uka komai ba ..... Humaid ne yace ”Umar please help me yanzu ya za'ayi ,iska Umar ya fitar ta bakinshi cankuma yace ”umm.... Yanzu shawarata bazatai amfani ba cox kuna cin amarcin Ku yanzu ,humaid ne yace ”yanzufa ba maganar wasa mukeyi ba dan Allah kaduba please, Umar ne yace ”karka damu amma ka kiyaye fa kar asami matsala ,insha Allah humaid yace ”daganan ya basu magani kasancewar Khairat na waje suka wuce gida, tunda suka koma khairat keta tattalin humaid, kwana uku a tsakani saiga humaid yaji sauk'i ,alkacinne tazomai da buk'atarta ,humaid bayason tasan halin dayake ciki shi yasa yakeson 6oyemata ... Yaukam zama tayi tafara kuka kamar wacce akayiwa duka humaid na bacci yajiyo kukanta 'a zabure ya mik'e yayi gurinda tazuba uban tagumi ,tambayarta yashigayi ,ko kallonshi batayi ba tafara magana ,tana cewa wallahi nayi nadamar auranka 'ashe dama kaida mace banbancin Ku kad'anne to wallahi ni bana auranka kaje ka nemi dai_dai kai walhi bazaka d'auki hakki naba kokuma kasani bin mazan banza "ka d'an d'anamin Zuma 'a baki yanzu kuma kace bazaka iya daniba ,humaid jiki a sanyaye yace ”dan Allah Khairat kiyi hak'uri bazan iya rabuwa dake ba karki gujeni ,tashi tayi kamar wacce aka zabura tayi cikin bedroom d'inta ,firfito da kaya tafarayi ta lodasu a 'akwati tana kuka....✍️✍️✍️. Mom Islam ce...🤙 *LADIDIN K'AUYE* Funny & love story. *Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa* *NA* *MOM ISLAM* *ZAINAB HABIB* *MARUBUCIYAR:* *ZAINABU ABU* *AND NOW* *LADIDIN K'AUYE* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *Episode:* 39_40 _____Tsugunawa yayi a gabanta yana bata hak'uri ,ko kallo ma bai 'isheta ba tacigaba da kwasar kayanta ,tana gamawa tace ”saura takadda ta ,humaid da yad'auki lamarin k'arami saiyaga 'abin ya zarce gona da iri ,yana rok'arta itako tana tafiya ,ficewa tayi daga gidan da k'atoton akwati tayi bakin titi ,napep ta tara ya kaita har k'ofar gidansu , tana sauka ta mik'a mai kud'inshi tayi nocking mai gadi ya bud'e mata da sauri ta shige cikin gidan ,samun momynta tayi a parlor tana kallo a tashar MBC 2 ,kwanciya tayi tafara rera kuka ,momyn ce tace ”kiyimin bayani mana maiyafaru daga biki yau kwananki biyar amma kice kin taho da k'aton akwati ?"ko wata matsalar ce kinfi k'arfin ki kiarani a waya? Momy tadinga jero mata tambayoyi a jere, Khairat ce ta dubi momy tana hawaye tace ”momy ki fahimceni please karkiyimin mumunanr fahimta ,momy ce tace” tashi mu shiga ciki kinsan gidan baya rabo da mutane, rufawa momy baya tayi tare da 'akwatinta ,suna shiga momy tace ”ina jinki daughter ya 'akayi wani sabon kukan tafara tace ”momy wallahi mutuminnan bashida lafiya , momy bazan iya zama dashiba wallahi ,momy da bata fuskanci 'inda y'ar tata _ta dosa ba yasata cewa rashin lpy kuma ?eh Khairat tace”daganan ta bata labarin hirar dasu humaid sukayi a hospital dakuma 'yanayin zamansu .... Momy cikin jinjina, lamarin tace ”gaskiya zama bazaiyyi ba za'a cuci d'aya dama yasan bashida lafiya ya auro ki tabb, amma bari yau dadynki yana hanya sai muyi maganar aji inda lamarin zai kaya, to tace” daganan ta kwanta momy kuma tayi waje.. Gidan su Humaid momy ce tacewa”dady anya baka zargin wanan yaron Ammar shine ya sace Khadija?",dady shiru yayi nad'an wani lokaci cankuma yace ”eh to gaskiya ban zargesa ba kasancewar baya gari ,kinsan iyayensa ba Nigeria suke ba ,amma zansa 'a bincika min ko da wata mak'ark'ashiyar ,momy ce tashare wasu zafafan hawayen dasuka kwaranyo mata ,dady cikin tausayawa yace ”dole sai hak'uri uhm 'momy tace ”Jalal ne yashigo cikin sallama , bayan su momy sun amsa ne Jalal yace ”dady kunji abinda yafaru ?" Momy ce ta dubi Jalal tace ”menene yafaru ”gyara zama Jalal yayi yace ”momy wlh matar yaya Humaid ce tace ”wai saidai ya saketa ,cikin ko inkula dady 'yace ”to saime ni banga dalilin da kowa zai tada hankali ba ,inace aurene ?to tinda yariga yayi shikenan yaje yaci aure ,momy uffan batace ba, ta mik'e tayi cikin bedroom d'inta.... *AFTER 1 MONTH* Kwance yake a parlour ,kallo ya kunna 'amma hankalinshi baya gurin ,tunani ne suka taru sukayimai yawa yarasa tudun dafawa ,jin nocking yasashi mik'ewa ,handle d'in k'ofar ya murd'a ganin Khairat yasashi mamaki ,cikin fushi tace ”karkayi zaton ko nazo ne ,dama nazo in gayamaka ciki ne dani kuma kuma three3 weeks kenan ,hamdala Humaid yayi yace ”kinga munada rabon samun baby's ko ,murmishin da baikai zuci tayi ,tace ”a cikin wa? cemaka 'akayi zanyi shayarwa tabb, to kasani aihuwar ma bazanyi ba dan yaron daba 'a gidan ubanshi nake ba mezan haifa? Humaid jiyayi damuwar tashi takuma nunkuwa over ,cewa yayi please khairat ki fahimceni mana ,nifa bani na koreki ba cox kekika tafi da kanki bansan lefin danayimiki ba, bud'e baki tayi tace ”au bakamasan lefin dakayimin ba to bari 'in tuna maka koka manta dakaida mace banbancin ku kad'anne?." Dafa kai Humaid yayi yace ”kibar ganin ina lalla6aki wallahi zanyi miki dukan tsiya kuma inga mai tsaya miki, kallon up and down tayimai kana tace” turr tayi gaba ,tana fita Humaid yamaida k'ofa ya rufe yafara kuka kamar k'aramin yaro ,yana tambayar kanshi wai shi meyayine a rayuwa bashida sa'a yanzu yayi aure dan yaji dad'i amma sai tozarci dayaketa biyo baya ,ga wanan shegiyar yarinyar tayi sanadiyar had'ashi da iyayenshi ,wayoo Allah na yafad'a cikin k'unar'rai dazanga Khadija saina kusa kasheta ,domin ita masiface..... Momy ce zane rik'e da carbi tana lazimi jin sallama yasata d'ago kai ,ganin Khadija ce take shirin shigowa parlor yasa wani matsanancin kuka ya ku6cewa momy ,tana cewa daughter ashe zanganki ? three months kenan bakya gida ,itama Khadijan wani kukane ya su6uce mata tana momy kiyi hak'uri nasan nayimuku lefi ,amma kafin in zauna kuyafemin ,ta had'a hannuwanta biyu ,tana rok'arsu momy ,rungumeta momy tayi tace ”bakiyi mana komai ba daughter amma kinsamu fargaba ,rik'o hannunta momy tayi tace ”zonan kije kiyi wanka sai kizo kici abinci ,babu musu tabi momy ,bayan momy ta rakata d'akinta nada kafin tayi aure ta fice , wanka tashiga tayi alwalah ta tada sallah tana idarwa ta zauna gaban dressing mirror tafara tsara kwaliya ,wata doguwar 'riga tagani bak'a mai adon stone ajiki dakuma flawoyi masu kyau ,farinciki ne ya lulu6eta tafara magana cikin zuciyar ta tanacewa 'anya nayiwa momy hallacci dahar natafi nabarta ? gashi duk da haka bata ganin lefina kuma bata fifita y'ay'anta 'a kaina ,share guntun hawayen daya kwaranyo mata tayi tasa rigar dakuma bra da pants tasanya rigar ,rolling d'in d'ankwalinta tayi tafito ,ganin bataga momy a parlor ba yasata wucewa bedroom d'inta ,canma batanan ,k'ara fitowa tayi ta zuwa kitchen.... Rungume momy tayi ta baya tace”momy da kanki kike girkin ?"ina ummi fa ?momy ce tace ”ah ai yau dole nayi miki girki daughter na guda tadawo ,daganan suka shiga hirar duniya ,amma momy batace ina taje ba , itama bata ce komai ba ,bayan sungama girkin 'ne suka wuce dining ,cikin so da k'auna suke cin abinci momy nata janta da hira,Jalal ne yayi sallama 'amsawa sukayi da Khadija da momy Jalal jin muryar Khadija yace ”tabb yaushe a gari ?kodai Makkah kikaje ne ?bud'e baki Khadija tayi tana dariya tace ”yaya Jalal nasiyoma kalo kalo ,bashiba har momy saida tayi dariya ,zama yayi shima yace ”to momy ina 'abinci na ?Khadija ce tace”kaga zomuci anan inbamu k'oshi ba ma k'aro ,zaro ido Jalal yayi yace ”tabb kinaso yaya Humaid yazo ya ganni 'inacin abinci da matarsa kenan ko ?"d'aure fuska tayi tace"barin zuboma naka to ,momy na kallon yanayinta 'amma bata nuna mataba ,tana fita Jalal yace ”ina tajene wai” cikin rad'a ,momy ce tace”wlhi bata gayamin ba nikuma ban tambayeta ba...... Tana dawowa rik'e da plet na 'abinci Jalal yace ”to sannu a yawo ,dariya tasa tace” yaya nifa ba yawo naje ba ,to ina kikaje inji Jalal ?to garinmu naje ,momy ce ta 'ajiye cokalinta ta tsaya kallon Khadija wacce magana takeyi ko a jikinta kuma babu alamun damuwa 'a fuskarta ,wallahi yaya Jalal ina gidanmu ganin babu wanda yake shiga gidan ,yasani yin saukar dare na bud'e gidan na zauna 'aciki kuma ko inna da malam Adamu basusan inanan ba dan babu Wanda na gayawa.....✍️✍️✍️. Mom Islam ce🤙 *LADIDIN K'AUYE* Funny & love story. *Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa* *NA* *MOM ISLAM* *ZAINAB HABIB* *MARUBUCIYAR:* *ZAINABU ABU* *AND NOW* *LADIDIN K'AUYE* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *Episode:* 41_42 _____Shiyasa ba'asan inanan ba ,kuma koda na koma banida matsalar abinci kasancewar komai na d'iba ,momy sai lokacin tayi magana tace ”to me ya had'aku da Humaid?? "nisawa tayi tace ”tunda mukaje India yake wulak'antani nikuma yasa na gudo kawai nakoma can gidan ,kuka momy tasa tana cewa dama,cin mutunci da tozarcin da Humaid zaiyi mana kenan hamm ya kyauta , Jalal ne yace ”to momy ai tunda tadawo farinciki zamuyi ,shikuma yaya Humaid d'in ku yafemai ,momy batace komai ba ta share hayenta tace ” daughter Allah yayimiki albarka mu mun had'aku ke baki bijire mana ba 'amma shi ya bijire mana ,hak'uri Khadija tashiga bawa momy .... Washe gari dady 'yadawo daga tafiyar dayayi ,ganin Khadija 'a parlour yasashi dad'a wara iadanu tace” Khadija saukar yaushe?cikin ladabi ta gaida dady tace ”jiya kanta 'a sunkuye masha Allah dady 'yace daganan ya wuce ciki ,Jalal ne yashigo da y'ar dariyarsa yace ”albishirinki ?goro Khadija tace fari ko ja Khadija ce tace ”fari k'al ma ,zama yayi kujera mai kallon tata yace” nakusa yin aure ,tsalle ta buga saida su momy suka fito suna cewa ,maiyafaru ne hayaniya tayi over ¿" Khadija ce tace ”yaya Jalal ne zaiyi aure zaro ido momy tayi tace ”to yaushene mukam bamu sani ba?Khadija ce tayi shiru cankuma tace ”yaya Jalal gayamin in sanar dasu ,dukkansu tabasu dariya har dady sanda ya dara ,shiyasa tafiyarta kokwa yai missing d'in dariya..... Dady ne tace ”ai bikin da saura tunda saura 3 weeks ,Khadija cikin murna tace ”tabb nikam wazaiyimin anko?tazuba tagumi momy ce tace ”da kinada saurayi da saiya yimiki ,dariya tasa tace ”tabb aikuwa momy ke zakiyimin atamfa da material dakuma gwagwaro tunda naji d'azu yaya Jalal suna waya da 'antyn tamu ,momy ce tazaro ido tace ”to wanan kayan da kika kirawo sunkai 50k Khadija ce tace ”hh momy karki damu inbasu isaba zan k'ara miki dady dayaketa dariya yace ”momy and daughter anfansu a rana,dariya Jalal yayi ,momy ce tace ”to naji karsujimu , juyawa Khadija tayi tace ”ywa dady kai kuma gyale da takalmi da jaka da sark'a da d'an kunne ,dady shima ganin abin yazo kanshi yasashi cewa kekuwa bakida samari ne ?dariya tasa tace ”dady nadena samari ,kowa yazo yagansu zaiyi sha'awarsu kasancewar dady da momy suna wasa da y'a y'ansu ... Dady ne yace ”to naji shikuma Jalal mai zai siya miki ,shima juyawa tayi tana kallonshi tace ”yaya ango turare da kayan makeup ,dariya yayi yace ”karki damu autar momy ,daganan suka mik'e kowa ya shige nasa dakin , dare nayi tazo yiwa momy sallama saiga wani yaro nan ya shigo wai ana sallama da Khadija ,zaro ido tayi tace ”to koma waye ya makaro ,momy da take jinta tace ”kaje kace yayi hak'uri gobe yadawo ,to yace ”yaron ... Washe gari momy da dady da Jalal da Khadija sun taru a palory ,dady ne ya dubo number Humaid ya danna kira ,Ring daya kamar mai jira ya d'auka yace ”aslamu alaikum dady ,dady cikin kakkausar murya yace ” ba doguwar sallama mukeso ba kazo yanzu kuma banason 6ata lokaci ,insha 'Allah ganin zuwa , gaban Khadija ne fara fad'uwa tana zaro ido ,had'a ido da Jalal sukayi yayi mata gwalo ... Cikin mintuna kad'an saiga Humaid nan ya rame sosai yayi bak' ,duk tsanar da momy tayimai saida ta tausaya mai sosai saboda ko shima dady bai nuna'a fuska ba ,sallama yai yashigo ,ganin Khadija takuma k'iba da kyau yasashi tsayawa kallonta ,wani mugun kallo ta watsamai ,saida yasami guri ya zauna ,yana zama dady 'yace ”dama ba komai yasa na kirawoka ba saidan inason kabawa Khadija takardar saki kuma ba saki biyu ba saki uku nakeso ,cikin bada umarni dady 'yayi maganar ,kid'emiwa gamida k'arewa Khadija kallo yakuma duban momy kozatace wani abu ,ko kallon inda 'akeyin magana batayi ba , wasu zafafan hawaye ne suke fitowa daga fuskarshi ,ya durk'usa gaban su momy 'yace ”mom da dady dan darajar fiyayyen halitta dan darajar al qur ani ku yafemin wlh na gane kuskurena ,dan Allah ,kuka Jalal yafara 'abinka da d'an uwa yace ”momy da dady maizai hana ku yafewa yaya Humaid tunda har yagane kurensa kutuna fa 'Allah munayimai laifi a kullum kuma mu rok'eshi ya yafe mana wasuma bazasu rok'eshi ba kuma baya fushi dasu to dan hasken annabi Muhammad kowa yace”sallalahu alaihi wa sallam ,mun yafe maka, momy tace ”idanunta na tsiyayar k'wallah dady ma cire farin gilass d'insa yayi yace ”mun yafe maka Humaid .... Wani farinciki da nishad'i suka ziyarci zuciyarshi d'a hannu yayi samma yana godewa 'Allah ,dady ne yace ”to saura maganar takardar saki ,Humaid ne yaji k'irjinsa na dukan uku uku yace”dady ai na d'auka shikenan ,momy ce tace”yanzu dai za6i yarage ga mai zaman gidan ,Khadija dai an d'aure mata kai dan tarasa yazatayi kawai tafara kuka tana cewa walhi bazan komaba , Ran momy yad'an 6aci kad'an to kunsan tsakanin d'a da uwa sai Allah haka 'aka tashi taro abin babu dad'i . Washe gari har k'arfe goma bata ko lek'o parlor ba ,momy da bata iya daure rashin ganinta yasata nufar d'akin Khadija , zaune tasameta tanata gurshek'en kuka ,momy ce ta dafata tace ”au akan maganar Humaid ne kike wanan kukan ?to sha kuruminki saikin yarda zaki koma, amma inason baki shawara inhar kina sinsa to walhi karki zurfafa jamasa rai 'inkuwa bakya sansa kiyi magana tun wuri ,shiru ne yabiyo baya ,momy jin Khadija tak'i magana yasata mik'ewa ta fice, kukane ya kuma ku6cewa Khadija jitakeyi dama mutuwa tayi ta huta da duniyar nan saboda k'uncin da take ciki... Gobe juma'a gobe ne d'aurin auran Humaid duk da bak'in cikin da Khadija take ciki bai hanata murna ba ,kar6o kayanta tayi a gurin momy tanata yimata godiya dady ko tun kafin bikin agama tashi siyayyar haka ma Jalal... *WEEDING*💍🥰. Kowa na gidan shirin zuwa d'aurin aure yakeyi Humaid kuwa shine kan gaba ,misalin k'arfe biyu dubban jama'a suka shaida d'aurin auran JALAL ADAM DA AMARYARSA SAUDAT KABIR akan sadaki dubu d'ari ,kowa kagani yana cikin farinciki ango kuwa inkaga bakinan kamar gonar auduga sai gaggaisawa yakeyi da mutane sunata yimasa Allah ya sanya 'albarka ,shirin komawa gida sukayi ,saboda zasuyi shirin zuwa reception gurin rawa ... Humaid na shigowa da fara'arsa kamar shine angon yacewa momy an d'aura fa ,cikin farinciki momy ta kwararo adu'oi tana murna cikin zuciyarta kuwa saitaji tausayin Humaid sosai ,amma 'a kullum tana adu'ar Allah yasa Khadija tasoshi, motoci ne zasu wuce itako Khadija batasan lokacin tafiya ba domin tatafi gurin kwaliya ,basu jima da wucewa ba saigatanan ta dawo ,momy na ganinta tace”kai kai kai ko amarya albarka dariya Khadija tasa tana cewa momy barinje in shirya kar masu moto suzo ,rik'e baki momy tayi tace ”tabb aikuwa sun wuce ,ida nunta sunyi rau rau alamun zatayi kuka tace ” nashiga uku nikam wazai kaini ,momy ce tace ”barin kira Humaid ina tunanin k'ila basu fara d'aukar y'an matan ba ,wani kishi ne yataso mata amma bata nuna inda momy zata gani ba ,ring d'aya biyu akayi sa'a ya d'auka Aslamu alaikum yace ”momy ce tace ” walaikumusalam kazo ka d'auki matarka tarasa mota ,cikin zumud'i yace ”ganinan zuwa momy ,Khadija ko harta shige gida sa kaya saboda kafin ta tafi tayi wanka , wow tana sanya kayan suka fito da ainihin kyawun ta inka ganta zaka rantse itace amaryar dukda nima banga amaryar ba ,da k'yar tasa skirt d'in domin ya matseta sosai gakuma takalmi mai tsini sosai ga nad'in gwagwaro da 'akayi mata ,d'ankunne da sark'a tasa ta d'ibi kud'ad'en datakai akayimata canji aka bata sababi ,mayafin kayan ta yafa a kafad'a ....✍️🤙. Mom Islam ce *LADIDIN K'AUYE* Funny & love story. *Labari mai ban dariya had'i da fad'a karwa* *NA* *MOM ISLAM* *ZAINAB HABIB* *MARUBUCIYAR:* *ZAINABU ABU* *AND NOW* *LADIDIN K'AUYE* *BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* *Episode:* 43_44 _____D'akin momy ta nufa ,momy na ganinta ta rangad'a gud'a mutane sai kallonta sukeyi wasu na gulma wasuna cewa tabasu sha'awa ,momy ce tajata gefe tace ”please daughter karkiyiwa mijinki rashin kunya kinga can jama'a suna kallonku dan Allah badan niba ,sunkuyar da kai Khadija tayi tace ”momy wallahi bazan yimai rashin kunyaba ,cikin jin dad'i momy ta mik'o mata dubu biyar sabbi tace ”tayi manni ,godiya tayiwa momy ,suna cikin magana saiga Humaid nan yashigo cikin shadda mai ruwan coffee shimafa ba k'aramin kyau yayi ba kai kace shine angon ,durk'usawa yayi har k'asa ya gaida momy ,bayan ta 'amasa ne yashiga ya gaida jama 'ar dasuka taru ,daganan yafito ,ya yiwa Khadija magana ,cikin yanga tace ”inzo mutafi ? wani kalo yake yimata mai kamada na so hhh masoya kenan 😘,momy ko ganin hakan yasata shigewa ciki ,Humaid cikin wani salo maijan hankali yace”muje lokaci na tafiya ,ohk tace ”daganan suka wuce ,gidan gaba ya bud'e mata ,shigewa tayi shima yashiga hmm riders duk wanan ladabin da khady take yiwa humaid duk a cikin umarnin momy ne hhh🤣 driving yafarayi cikin k'warewa rik'o hannunta yayi da d'ayan hannunshi d'ayan kuma yana driving dashi ,ko k'ala batace ba .... Da isarsu yayi parking gurinda kowa ya parka motarshi ,fitowa yayi yana jiran Khadija tafito ,hhh abinku da gimbiyar mata saida ta jima yana tsaye sanan tafito ,a yangace take tafiya ,Humaid ne ya hango wasu samari suna k'arewa shigar Khadija kallo, cikin zafin nama ya rik'o mata hannu suka wuce ,da shigarsu Hall din kalo yakoma gunsu ,sai tafi ake yimusu ,kusada ,amarya Khadija ta zauna shikuma Humaid friends d'insu nacemai ga guri yana cemusu shifa kusada gimbiyar zai zauna ,dole aka mik'o wata ha d'ad'iyar chair ya zauna ,kammo hannunta yayi yana mata rad'a 'a kunne ,nimafa banji meyace ba nadaiga suna dariya ,duk abinda sukeyi doctor Umar yana yimusu photo ... Kiran Amarya akayi dakuma k'awayenta ,mik'ewa amaryar tayi Jalal kuwa yana rik'e da 'amarya dan haka suka mik'e a tare yana cemata wananfa matar yayana ce ,cikin fara'a 'amaryar ta rik'o hannun Khadija tace" kitaso muyi rawa dayake Saudat tasan rigimar Humaid ko kallonshi batayi ba 'amma tana jan hannun Khadija ,saboda daga ganinta saudat taji tashiga ranta sosai da sosai ,humaid kuma damk'e hannun Khadija yayi wai adole bazatayi rawa ba ,fakar idonshi Khadija tayi ta mik'e aka fara cashe rawa ,ganin bai hangota ba yasashi tashi yana lek'e ,hangota yayi kusada mai d'aukar photo ,zuwa yayi ya janyota yana mata kallon soo💖 ammafa 'akwai kishi over, ahaka dai akayi abubuwa kamarsu yanka cake dakuma bada tarihin amarya da sauransu ,ana shirin tashi ne aka sake kid'a mata da maza suna rawa ,Humaid na waya Khadija ta mik'e taje tafara rawa ,cikin zafin nama ya figota yana cewa kinada hankali kuwa ?ko kulashi batayi ba ya rik'e mata hannu suka fice..... Direct wani katafaren hotel sukaje kayan dad'i yasa 'aka kawo musu ,sunci sun k'oshi daganan ya wuce gurin mai saida kaza tofa🤦‍♀️, Guda biyu yasiya saboda yasan mutuniyar akwai son cin dad'i ,daganan ya wuce da ita wani katafaren shago kayane na Makkah su dogayen riguna da etc.. cemata yayi kiza6i wanda ranki yakeso cikin zumid'i ta hango wata riga da tun tana budurwa take burin sata 'amma saboda tsananin tsadar 'rigar yasata hak'ura ,yaukam zata gwada d'auka ko zai siya mata ,nuna rigar tayi tace ”nidai wanan rigar nakeso ,Humaid ne yace ”to ita kad'ai ta isheki ?eh tace ” saboda tana tunanin inyaji kud'in rigar cewa zeyi ya fasa ,mik'a rigar yayi ,mai lissafin kud'in kayanne yace”50k take ,cikin ko d'ar yace ”ok yabada ATM aka cire suka wuce,mamaki ne yacikata ,amma babu bakin mgna tayi shiru ,hanyar gidanshi ya nufa da ita ,zaro ido tayi tana kallon ikon Allah ,momy ce take kiranshi a waya ,ganin kiran yasashi cewa osh momyyy ,d'auka yayi ,yace ”momy mundawo fa momy bata yardaba tace ”to yanzu kuna ina? Munje kasuwa yace”a tak'aice hmm momy tace ”to maza _maza kudawo gida ,farinciki ne ya lulu6e khadija ta fara murkishi tana cewa hhh kaza zanciki ina komawa gida ,shiko humaid haushine ya cikashi ganin yaufa momy ta takura masa ,yanzu yasiyo kajin a bati kenan ya tambayi kanshi ,juya kan motar yayi zuwa unguwar su momy .... Suna isa yayi Horn mai gadi ya bud'e mai ya shige da motar ,khadija ce ta juya ta hango ledar kazar a back side ,saida tafara bud'e k'ofa tukun ta janyo ledar ta ,arce da gudu tana dariya ,wata muguwar yaunwa humaid yakeji gashi Khadija ta d'auke kajin ,kaii yace yana mai d'ora kanshi a booth d'in motar , Cikin sanyin jiki ya shige parlor yana mai sallama wucewa part d'inshi yayi ya kwanta idanunshi a rufe amma ba baccin yakeyi ba,yanason su zauna da khadija yaji ko tana sonsa kokuma zata sauya ra'ayi ,amma yana tsoron yimata magana ta taso da 'abinda yariga ya wuce , bacci ne ya d'aukeshi yana cikin tunanin khadija ,wani mumunan mafarki yayi wai ga khadija nan wani mutumi ya rik'e mata hannu sunata gudu, a tsorace ya farka yana salati ,çikin azama yayi part d'in khadija ,samunta yayi tayi bacci akan sallahya gakuma plet d'inda taci kaza ga ragowar kazar a gefe,zama yayi shima ya cika cikinshi sosai sanan yashiga toilet d'inta yayi alwalah yazo ya tada sallah ,yana idarwa ya kwnta ta bayanta ,khadija jin mutum a kusada ita yasata kurma uban ihu tana salati ,lokacin dare yayi sosai dan 11pm na dare ,dady ne yafito shida momy cikin razana ,kai tsaye d'akin khadijan suka nufa ,humaid najin alamun zasu shigo ya shige toilet yana rawar jiki ,ganin harta koma bacci yasasu komawa bayan momy tayi mata 'adu'a ta fice ..... humaid ganin khadija zata iya tona masa 'asiri yasashi komawa d'akinshi babu shiri ... Dady ne yata humaid da khadija akan maganar komawarta hhh jiyafa humaid kwana yayi yana sallah akan Allah yasa khadija ta yarda ,dady ne yace ”to gareki khadija zaki koma gidan humaid 'd'inne kokuwa ,dogon 'nazari tayi akan hallacin da su momy sukayi mata ko d'an cikinsu albarka gaskiya koda batason humaid bazata iya duban idanunsu tace ”bazata komaba ,sunkuyar da kai k'asa tayi tace ”na 'amince wow kuzofa kuga rawar jiki ko kunyar dady baiyi ba ,ba humaid ba har dady 'yaji dad'i sosai ,albarka yadinga samusu dakuma fatan alkairi da zuri'a d'aiyyiba ,momy ce tafito itama tana tsaye tanajin duk abinda 'ake cewa ba k'aramin murna tayi ba..... Washe gari wani gyara momy tafara yiwa khadija su dilka ne su tsumi ne dasu garin sha magani dai kala_kala gasu humra da ta jiki data kaya gakuma kayayyakin d'aki da dady 'yasa 'akawo daga kamfani a fitar da na gidan......✍️. Kwanaki k'alilan khadija ta sauya tayi kyau sosai ,humaid kuwa jira yakeyi ace yatafi da ita 'amma shiru ,hhh yadai fara shawarar ya gudu da ita , saida 'kayi one month da magar sanan momy ta amince yake zuwa gurin khadija washe gari kuwa dady 'yace ”ya tattara matarshi su wuce ,aikuwa kamar yana jira yace ”tafito ,momy ce tace ”ya kara mata one week 'komawa d'aki yayi yana kuka hhh manya, washe gari kuwa ko sallama baiyi musu ba Yakoma can gidan ganin Sabin gyaran da dady 'yasa 'ayi yasashi farinciki.... Yana 'alfahari da iyayenshi sosai da sosai adu'oi yadiga kwararo musu ,yana cikin hakanne yaji ana nocking zuwa yayi bud'e k'ofar yana budewa yaga khairat ce ,tsaki yaja ,cikin k'ufula yace ”mekuma kikazoyi gidana ?"tsaki taja tace ”naje na zubar da cikin kuma yanzu takarda ta nake jira ,cikin sauri yayo kanta ,kome ya tuna ya fasa ,cikin azama tace ”wallahi daka doka hmm kabani takaddata in ficema daga gida ,domin wanan ai bak'inciki ne ace mutane na sonka insunji da igiyar aure a tsakani saisu gudu mtsw ,humaid ne yaje ya d'auko takadda ya rubuta mata 'abinda ta buk'ata ,godiya tayiwa 'Allah daganan ta fice ,shikam ko damuwa baiyi ba tunda Khadijanshi zata haifamai y'ay'a ... Sati ya cika yaune ake shirye shiryen komawar khadija ,humaid ne yakoma gun doctor Umar akan ak'ara dubashi ,congrat yayimai yana dariya yace ”aci amarci lafiya yanzu kazama normal fa ,dariya humaid yayi yace ”nikam tun yau na d'auki hutu sai wata biyar dariya sukasa ,daganan yawuce gida zuwa d'auko gimbiya khadija ,tana kukan rabuwa da momy ,yashigo momy ce tace ”ka kula min da yarinya dan Allah ,insha humaid yace ”daganan momy ta rakata zuwa mota ,tuk'i yakeyi a hankali ,har Allah ya kawosu gida lafiya tana sauka zata fito ya ,sunkuceta ya goyata ya direta 'a k'ayataccen d'akinta ,ammafa d'akin yayi kyau ,tafad'a cikin zuciyarta ,humaid ne yace ”lovely dan zaki biyoni shine harda kuka ?"murmishi tayi ta nemi gefen gado ta zauna ,soyayya 'kuwa humaid ba bayaba dan jin k hadija yakeyi inta k'ara guduwa bazata dawoba*LADIDIN KAUYE* Funny & love story 45 _46 Zai iya rasa rayuwar shi lalla6ata yakeyi akan taci kaza 'amma sai wani sharewa takeyi murmishi ne ya su6ucewa Humaid cikin zuciyar shi yace ”kamar ba ita bace kwad'a yayyar kaza ba ,haka yadinga bata 'a baki tana ci tana yanga suna gama ci yace ”taso muje muyi sallah dan nuna godiya ga Allah ,a gajiye take amma batada za6i dole ta mik'e sukaje yin alwalah ,suna idarwa ne yazo yaja musu sallah raka'a biyu sukayi yai sallama bayan sunyi adu'oi masu yawa , ya d'ora hannu a kanta yana yimata 'adu'a ,suna kammalawa ya mik'e ya nufi bedroom d'inshi sleeping dress yaje ya sako ita kuma lokacin tsabar gajiya kwanciya tayi da kayan jikinta ,Humaid bai kulata ba yaja filo ya kwanta 'acan gefe ." Washe gari bayan tayi sallah ta duba bataga Humaid ba ,jin alamun shigowarshi yasata durk'usawa har k'asa tace ”barka da safiya yaya ,yww barka dai amaryar yaya ,da 'alamu baki damu da yayan naki ba ko ¿sunkuyar da kai k'asa tayi tana wasa da fingers d'inta surarta yai yace ”zomuje mu kwanta bacci nakeji please ya marai raice kamar yaro ,dariya yaso bata tace ”gaskiya not ni yanzu bazan kwanta ba buh wlh wanka zanyi tana magana kamar zatayi kuka Humaid ne ya shige ya barta 'a gurin ,juyi yakeyi baccin ma yak'i d'aukarshi tunani ya fara ,ina murna farinciki na ta dawo ashe akwai problems a gaba oh god Allah kadawo min da Khady kan hanya ." Breakfast ta had'a musu mai rai da lafiya chips ne na dankalin turawa sau wainar k'wai dakuma tea mai kauri wanda yaji kayan kamshi ,dining room ta wuce dashi kasancewar ankuma gyara gidan ,tana fitowa ta koma kitchen kayan data 6ata ta wanke ta rufo kitchen d'in ,tsintsiya ta d'auko tafara share parlorn tanayi tana hutawa 'a haka ta gama mopping d'in tayi daganan ta kuna turaren wuta ,wani sihirtaccen k'amshi ke tashi a gidan ,bedroom d'inta ta shige ta cire kaya ta d'aura towel ta shiga wanka ,ta dad'e tana wanka da sabulun da momy ta bata mai kamshi tana fitowa ta ciro kayanta , gaban dressing mirror ta zauna simple makeup tayi ammafa ta had'u atamfar ta d'auko mai ratsin wait and black tayi d'auri mai kyau ,kin shiga bedroom d'in Humaid tayi can kuma ta shige da sallama tana cewa yaya Humaid katashi breakfast is ready ohk yace ”dagan ya mirgino yana yimata wani kallo cikin sigar wasa yace ”ke bakisan inda ake tashin miji daga bacci bane ¿" am sorry tace "daganan ta fice, brush yaje yayi daganan yai wanka ya shafa manshi man kamshi ya fito sanye da shadda pink sai d'aukar ido takeyi ,murmishi ya sakarwa Khadyja yace ”lovely mai yasa baki kirani nazo na tayaki ba ¿cikin sanyi murya tace ”nagama ai ,janyo gwangwanin madara da ragowar kayan tea yayi saida ya k'ara komai bacin wanda tasa dagan yace ”to bud'e baki naga 'alamun bakison cin abinci sosai ko ¿shiru tayi daganan tafara cin abincin ,kad'an taci tace ta k'oshi." Kallonta Humaid yakeyi yarasa mai yasa yarinyar nan yanz bata sakewa dashi ,duk rashin kunyarta da neman tsokana yanz duk sunyi sanyi ,tunani ya shigayi to aure babu hira ina labari ,duk inda naso naga ta fahimceni amma lamarin ya citura ,mik'ewa yai yace ”lovely biyoni ki kar6i wani abu ,cikin sanyin murya tace ”ya Humaid banajin dad'i ynz kaina nayimin ciwo ,subhanallah to zomuje hospital a'a kabarshi inada maganin a d'aki please zani in kwanta ohk yace ”yarasa mai yaiwa khady take wanan slow d'in ,kodai har yanzun bata sonshi ne kwai tabi umarnin Momy da dady ne ,iska ya fesar mai zafi ya bugi bango yana dogon nazari itako tun tuni ta shige part d'inta." Kwance take tana kallon sama tana tunanin rayuwarta tada 'a cikin gidan hmm da yace ”baya sona yanz kuma yace ”yana sona kai da 'ayar tambaya wlh but naji masoya na cewa in mutum ya k'ika daga frko to karshe koyace yana sonka yai karya , haka ta dinga juyi a bed d'inta tarasa maiyake damunta . Washe gari ai yuka ta gabatar inda tasaba ko ina ta gyareshi gidan sai zuba k'amshi yakeyi ,yau 7 days da auransu ,nocking taji batayi azamar tashi ba saboda Humaid na nan ,ganin gimbiyar bata tashiba yasashi mik'ewa ya bud'e k'ofar ,su inna Hauwa ya gani ita da wata yarinya zatakai 13yrs a duniya sanye take da rigar banba lasta rigada wando sai hijab da yaji jiki ,inna ce tace ”munsha hanya fa khadija najin muryar inna ta mik'e da gudu tana oyoyo ,Humaid ne ya kar6i kayansu ya shige dashi d'akin bak'i yadawo suka gaisa ya fice sbda ana kiran sallah ,khadija ce tace ”inna kunsha hanya ya su baba ,lafiya Lou inna tace ”tana kalle² khadija ce ta dubi wanan yarinya tace ”inna naso in ganeta amma ta 6acemin ,yarinyar ce tace ”uhm ai wanan daular haka dole bazaki ganeni ba to inkin manta nice sahura waro ido khadija tayi tana duban sahura tace ”wai kece kika girma haka ? Sahura ce ta dubi khadija tace ”to ke kinga inda kika koma ne walahi kamar matan turawannan da muke gani a shagon mai shayi na anguwarmu ,dariya sukasa dukansu ,khadija ce ta shige kitchen sbda yimusu girkin lokacin 11am shinkafa jollof mai kifi da carrot dakuma green bean's dataji alaiyahu lokaci k'alilan gidan ya kaure da kamshi sosai ,Sahura ce tayo kitchen d'in da sauri tana cewa kufa y'an gayu inzakuyi girki bakwa gayya dariya khadija tasa tace ”to a wanan girkin menene abin wahala ?Sahura ce tace ”walhi ku kula saboda ance yawan ciye _ciyen kayan dad'i nasa ka mance da lahira Khadija dai bata kulata ba sai aikinta takeyi ,Sahura ce taga bread a saman fridge tsalle tayi ta d'auko ta yaga tace ”oh sai natuna lokacin da kike cutar mutane ki gudu amma yanzu ana yimiki magana ma sai kinyi ra'ayi ,hmm kawai khadija tace ”sbda hankalinta na kan girkinta." Khadija ce ta dubi sahura tace ”to muje muyi sallah sai muci abinci ko ?Sahura ce ta yago bread tace ”tabb inma zaki zubo abinci ki zubo dan ni wata shegiyar yunwa nakeji yasin khadija ce tace ”zan zuba miki naki nikam zanyi sallah , tunda khadija ta zubo abinci Sahura ke had'iyar yawu tana lashe baki ,khadija ce ta mik'a mata tare da wani soyayyan nama a kai Sahura ce tace ”ke bakida wayo nikam kawo naman injishi a hannuna kar azo ba'a sawa inna ba tace saitaci ,khadija kam wucewa tayi tabarta a gurin tana tura nama cikin aljihun wando, bayan sun kammalah cin abincin khadija ta kwashe takai kitchen saida ta wanke sanan ta fito ,inna ce ta mik'o wa khadija wani k'ullin buhu tace ”lalle ne da barkono da kuma citta godiya khadija tayi sosai daganan inna tace ”zasu wuce Sahura da ido yai ja tace ”nifa inna kitafi walahi bazan koma k'auye ba kicewa babanmu sai yazo aurena ,dariya suka sa khadija ce tace ”to kizaune in kikayi sati biyu ko uku saiki koma ,tsalle sahura ta doka ta cakumi khadija tana murna ,inna ce tace ”to anta6a yanke hukunci babu mai gida khadija ce tace ai ya Humaid bashida matsala, haka inna ta tafi tabar Sahura ." Washe gari Sahura ce gaban TV tana kallo a MBC action wani film suke yi mai fad'a suna cikin fadanne wani ya kaiwa dan uwansa naushi Sahura ce ta doka tsalle ta kaiwa khadija naushi har tana neman k'ara mata ,a razane khadija ta dago tana kallon Sahura da hankalinta ya tafi ga TV nuno gurin kuka 'akayi aifa ta zauna tadinga kuka harda gumi ,khadija ce ta tashi ta kashe TV n sallamar humaid sukaji Sahura ce ta dubi humaid tace ”barka mijin ta jikin t b juyiwa yai yace ”to waye ta jikin t b ?kallon khadija data had'e rai tayi tace ”to ai naga yan gayu idan mijinsu ya dawo fara'a sukeyi kekuwa kin wani had'e rai kamar dillaliya anzo cin bahi lolz ,wani mugun kallo khadija ta jefeta dashi shikuma humaid na kallonta baice komai ba ya *LADIDIN KAUYE* funny & love story 47_48 Ganin abin zuba sharar gidan ya cika mai zuwa kwashewa bai zoba yasata d'auka ta nufi wani guri tafiya takeyi tana dube dube a uban kwandon zuba shara a kanta ,hango wani k'aton kare tayi yana shirin dosota jikinshi duk gashi cikin tsoro tafara gudu aikuwa kare yadinga binta duk inda ta shiga saiya bita gudu takeyi da kwandon shara a kanta ,tama manta layin dazata dosa gashi gidajen duk kusan kala d'aya wani mutumi ta hango yana gyra parking din motarshi k'arawa tayi da gudu tace ”dan Allah ka temakeni karya halakani ,mutumin ne ya kalli karen yace ”mai tayi ma kake binta ?itako Sahura ganin yana neman raina mata hankali tace ”shi mutumne dazaka tsaya tuhumarshi ko kaima mugune irin karen ,mutumin ne ya rike baki tana salati cewa karen yayi duk inda tashiga kabita karka raga mata." Aikuwa kare yafara bin Sahura gudu take ci babu mai temakon ta ,humaid ne tafe a cikin mota hango ta yai tana gudu ashe harta zo anguwar takuma juyawa yanzukuma ta dawo duk bata sani ba ,fitowa yai daga cikin motar yana cewa keee!!da k'arfi ziwa tayi ta cakumeshi tana ihu ,karen humaid yabawa hak'uri daganan yace ”to ga gidan nan amma ina zaki da kwandon shara cewa tayi naje zubar muku da shara shine kare ya biyoni wata shu'umar dariya humaid yasa yace to jeki gida maganin mai yawo kenan ,murgud'a mai baki tayi ta shige ciki , tana shiga tafara cewa Ladidi ki fito yau nakusa mutuwa ,da sauri Khadija ta fito tana cemata na k'arshe karki sake cemin ladidi ,to natuba dan kunga ku yan gayu ne shine kikeso kisa a maidani gida to ta Allah ba takiba ta shige d'akin da yake mazaunin nata." Washe gari salamar momy ce ta karad'e harabar gidan da gudu khadija ta fice tana oyoyo momy a tare suka shigo parlor rik'e da hannun juna ,Sahura na zaune tana kallo tace ”hajiya barka da zuwa momy ce tace ”yww daughter yar aiki kika samu ne ¿khadija ce tasa dariya tace ”tare sukazo da inna hauwa ,oh momy tace ”na tuna ai ta fad'a min amma bbu wani matsala kho eh momy komai normal , nan momy ta jata zuwa bedroom d'inta tanata bugar cikinta 'akan ko tana cikin wata damuwa ,juyin duniya khadija tak'i fad'awa momy komai,momy ce ta fiddo da wani turare tace ”yau d'inan 'nakeso kiyi using dashi ,to Khadija tace ba tare data musa ba ,nasihoyi momy tayi mata akan ladabi dakuma hak'urin zaman aure,momy ce ta d'au jakarta tana shirin tafiya narai _narai Khadija tayi da fuska zatayi kuka momy tace ”nazo kuma dan inganki inji dad'i shine zakiyi kuka kull kiyi hak'uri zaman aure ba wasa ba ,raka momy tayi har gurin motar da tazo sukayi sallama ,magrib nayi tayi wanka tasa riga da wando rigar dai _dai cinya wandon kuma dai _dai gwuaiwar k'afarta ,turaren da momy ta bata ta fito dashi shafawa tayi a fuska tana mai jin k'amshin yayi mata dad'i ,,jin sallamar Humaid yasata fitowa a kunyace tace ”barka da dawowa yaya uhm barka yace yana k'are mata kallo ,wani lamari yakeji mai wuyar fasarawa sabda inya kalli fuskarta ,cewa yai kaimin bag d'innan ciki ohk tace ”ta wuce taje kaiwa ,tana shirin fitowa taga an kashe light d'in d'akin anbar kadan zaro ido tayi lokaci guda kuma tsoro ya baiyana a fuskarta ,cikin zuciyar shi yana cewa da nace sai lokacin da kika amince to yau na soke wlhi ,nufota yakeyi tana ja da baya ,a haka har tasamu tayi d'akinta da gudu ,6acin rai ne ya dirarwa Humaid sabda yafara wani tunani daban akan Khadija yafara zarginta sosai sabda had'in kan datak'i bashi tana nufin Allah bazai kamata da laifi ba kenan?takoma kamar jahila wacce batayi karatun islama ba ,yau dai 6acin rai yasa Humaid maganganu marasa kan gado juyi yakeyi yana tunanin anya wani bai rigashi ba hmm ." Yaune Sahura zata koma gida sai kuka takeci kamar an aikota wai zatayi kewar burodi da shayi ga kayan dad'i harda bubuga k'afa ,a haka suka had'a mata goma ta arziki akwati sabo Humaid ya siya mata hardasu atamfofi driver akasa ya kaita. Khadija batada wal walah kwata ²komai cikin sanyin jiki takeyi gashi ta koma very silent abin haushi ma dariya tsada takeyi mata ,washe gari da safe kira ya shigo wa Humaid cewar wanan doctorn yanason suyi wani aiki tare urgent yaje ya sanar dasu momy fatan alkairi sukayimai sanan sukace to matarka fa ?"sosa kai Humaid yai yace ”tace batason yawo lolz tunkafin ka tambaya hh,a tunanin su momy cikine da ita dan yau bikinsu 1 month kenan ,ficewa yai sunata sanya mai albarka komawa gidansa yai yasami gimbiyar na goge TV k'arasawa yai ya rungumeta yana cewa lovely munsami cigaba fa kitayani murna ,murmishinta tayi mai tsada tace ”Allah ya tabbatar da alkairi ,wanan adu'ar tasa yaji dad'i sosai ,yace to kishirya muje tare a'a tace ”a tak'aice shiru yai bai sake magana ba ,yanason cewa ki shiryamin kayana a jaka yakasa ,hakadai ya shirya da sauri sauri ,Jalal ya kira akan yazo ya kaishi airport sai ya dawo da motar ,yayi yayi Khadija ta rakashi koda airport d'inne amma ttak'i." Haka tayimai Allah ya tsare ,yana tafiya ta fashe da wani matsanancin kuka ,ring d'in wayarta taji mik'ewa tayi ta d'auko wayar ganin number babu suna yasata kallon number, dauka tayi had'e da sallama dagacan 6angaren akace ya kike kwalli lpy Lou Khadija tace ”dan bata gane mai maganar ba Fati ce kokin manta da mukayi school tare oh na tuna yakk hope kina lpy eh ya amarci dariya Khadija tasa tace ”amarci nan sai wanda ya k'aru daganan sukayi sallama ,zaman shirunne ya isheta ta zari hijab ta shiga mak'otan su gidane tangameme kuma tsararre da yafi nasu komai ma nocking takeyi amma shiru , can mai gadi ya bud'e yana kallon Khadija yace ”daga ina ne ?cewa tayi ga gidnmu nan wanan na jikin nakun ,Allah sarki yace dagan an yabata hanya ta shige ,da isaera k'ofar parlorn wata k'ofa ce ta glass tana haske kala kala sallama tayi jitayi an amsa ,matar dai batasan Khadija ba amma dayake batada girman kai yasa tace toshigo mana sister." Shiga tayi matar da a shekaru zatayi 27 tace ”saidai ban ganeki ba wlhi tana murmishi ,Khadija ce tace ”ga gidanmu nan jikin naku ,oh ko kece amryar da aka kawo kwanaki 8 months da suka wuce ,jinjina maganar Khadija tayi tace ”wata takwas kina nufin Humaid yayi aure kenan ?matar ce ta dubi Khadija tace ”oh su6utar baki please karki tada hankalinki ita wacan ba zaman aure ya kawo ta ba ,kinga ni sunan na Rahma yarana biyu kin gansu nan a photo yarane kyawawa masu kamada uwarsu sunsha kyau sosai Khadija ce ta dubi Rahma tace ”ni kuma sunana Khadija danan hira ta 6arke kamar sun dad'e da sanin juna horn sukaji Rhma ce ta mik'e tana lek'awa ta window ,oh kinga sweety ya dawo please ina zuwa , Khadija ce ta mik'e window da Rahma ta lek'a nanta fara lek'awa wani kya kyawan magidanci ta gani fari sol kamar bature ,hango Rahma tayi ta bud'e masa mota ta kar6i jakar ta rataya ta kuma ruk'o masa hannu shikuma ya rungumota suna tafiya suna dariya ,Khadija ce tace ”danasan iskancin da zan gani kenan da banzo gidannan ba wlhi ni nazo domin d'ebe kewa amma naga abinda yafi k'arfina nifa bazan iya k'arewa a yiwa namiji bauta ba hmm ,ita kad'ai taketa maganarta ,can kuma taji gabanta na fad'uwa sosai ,yarinya tagani wacce zatayi shakara hud'u a duniya tace ”jeki cewa momynki bakuwar ta tafi ,da gudu ta shige tana cewa momy bakuwa zata wuce ,OK kice ganinan Rahma ce tace ”sweety zani yiwa bakuwata sai gobe ,janyota yai yace ”daga ina tazo a mak'otanmu take ,Rahma ta fice tana dariya ,samun Khadija tayi a bakin get a tsaye ,Khadija ce tace ”to aunty Rahma sai wani lokaci godiya Rahma tayi mata ,Khadija ta fice.shige ciki....✍️.*LADIDIN KAUYE* funny & love story 49_50 Jin fad'uwar gaban ya tsananta sosai yasata k'ara saurin tafiyar ta ,tana dosowa bakin get abinda taganine yasata kurma uban ihu ta fad'i sumammiya . Sahura ce zaune tana cin tuwo tana turo baki ,inna Hauwa ce tace ”nifa banasan kinibibi garama abincin gidanmu naku da ko kafi zabo babu ,kuka Sahura ta fashe dashi tace ”ni walahi sonakeyi in koma jos gurin Ladidi ,zaro ido inna tayi tace ”to ga hanya nan kitafi k'wad'ayayya sunmayi namijin k'ok'ari da har kikayi musu sati biyu batare da sun koroki ba ,wani kallo tayiwa inna harda murgud'a baki tace ”to dan kiji ma yasin ni bazanyi aure a nanba saboda talauci yayi muku kanta ,salati inna keta jerowa ita ko sahura surutunta take jerowa ,jin salamar yaro yana tallar alele hhh fans means allale ,tace ” kai d'an hanse kawo dan uwarka ,inna ce tace ”walhi ki kiyayi zagi saikace baki zuwa islamiya ,mugud'a inna baki tayi hakan yabawa inna damar yin shiru ,Sahura ce tace ”wa yaron biyar biyar ko¿" a'a yaron yace wake ya k'ara tsada goma goma ne , cewa tayi to sako na wazobiya inna mik'omin kwanon kusa dake ,mik'o mata inna tayi duban yaron tayi tace ”kasamin manja da yaji sosai ,bayan yasa ne tace ”inna bismillah kawo kwanonki ,inna da bata wuce tayi ta mik'a kwano aka samata guda d'aya ,Sahura ce taga yaronna kallonta cewa tayi d'an hanse zakaci alelen ne eh yace aikuwa tace to ci d'aya da rabi ninikuma inci biyu inna ga wanan rabin ki kara ,inna na rawar jiki ta kar6i alale tanaci tana lashe rroba." Saida suka gama ci yaron yace ”Sahura bani kud'in ?" cewa tayi kai na nawa kaci ?" yace ”to ai kece kika bani kyauta ,juyawa tayi gurin inna tace inna kinci na sha biyar ko ? eh inna tace tana zaro ido to talatin kenan ungo murtala sauran kuma sai kubiya ,yaronne yafara kuka yana ihu ,shigowar malam Adamu yasa Sahura zamewa ba tare da kowa ya ankare ba ." 6angaren su Jalal kuwa soyayya suke zubawa wacce babu algus kowa bayason yaji 6acin ran d'an uwansa shiri takeyi zatace hospital gaishe da Khadija da ake yimata k'arin ruwa Jalal ne yace ”Honey inkin gama kizo mutafi ,shagwa6e fuska tayi tace ”anya babyn ma zaibari na fita kuwa ,k'arasowa Jalal yai dai _dai saitin cikin nata da zaiyi wata hudu ya kasa kunenshi yana dariya ,girgiza kai yayi yace ”to baby's sunce ko America zaki saikin dawo ,dukan wasa ta kaimai tana cewa tabb barinzodai mu tafi dan naji ance jikinata yayi tsanani ." Emergency room aka kwantar da ita saboda lokacin da ta yanke jiki ta fad'i Allah yasa da mutane a gefe ,kwance take ansa mata oxygen wato abin nunfashi ,nunfashinta baya fita sosai kowa ya cire rai da khadija momy kuwa sarkin kuka kullum cikinsa take tanacewa kukuma jarabawarku kenan wayo rayuwa, Saudat ce tayi sallama ita da Jalal amsawa su momy sukayi itada k'anwarta durk'usawa har kasa sukayi suka gaidasu momy dagan an ya ajiye food folks a gefe yace "ya jikin Khadijan da sauki momy tace ”had'a baki sukayi gurin cewa Allah yabata lafiya amen momy tace ”bayan Jalal ya zauna ne yace ”momy number ya Humaid bata shiga yau 3 days kenan ina gwadawa amma a kashe ,momy ce ta share hawayen da suka zubo mata tace ”shima dajin wanan lamarin da yafaru a gidannasu ya kwanta rashin lpy dan naji ance jikin ya tsananta sosai ,Jalal ne ya tausayawa yayan nashi yace ” momy insha Allah jibi zantafi dubo shi to Allah ya kaimu tace ”daganan shiru ya biyo baya." Momy ce ta shiga room d'inda aka kwantar da Khadija samunta tayi ido a kakkafe tana kuka momy tsabar firgici tayi gurin doctor tana kuka ,da sauri doctor Umar ya shigo yafara gawaje gwaje ,cikin sa'a nunfashin ta ya dawo normal can tafara bud'e ido ruk'o hanunta momy tayi tace ”alhamdulilh daughter Allah yakara miki lafiya ,Khadija babu bakin magana sai kalle kalle takeyi.. Tabarmai nagani da mutane a k'ofar gidansu dady kowa kaganin fuskarsa bbu dad'i zaman makoki akeyi dakuma adu'oi , dady ne keta kar6ar gaisuwa gurin jama'a suna yimasa ya karin hakuri ,washe gari jikin Khadija yayi kyau sosai dan har tana cin abinci sosai ,sallama aka basu suka wuce gida ,Khadija na ganin yan zaman makoki tafara tambayar waye ya rasu ,momy ce ta tuno da sharud'an da doctor ya gaya mata akan ta kiyayen 6acin ranta kokuma shiga damuwa ko gani ko jin fargaba ,momy ce tace ”suna hutawa ne kinsan wanan watan dolle sai anyi meeting da ma'ai kata ta gamsu da baya nin momy shiyasa ma bata k'ara d'aga hankalinta ba.... Kai nimafa mom Islam abin ya d'auremin kai 😢meya faru a gidansu Khadija ??waye ya rasu ??? tabb todai kubiyoni danjin inda muka dosa👏. Kwance take tana wani matsanancin kuka rabonta da abincin kirki tun da wanan abin ya faru ,tarasa ina zatasa kanta gashi Allah ya jarabeta da abubuwa duka biyu ,alwalah ta d'auro tazo tafara nafilfili tana gayawa Allah damuwarta ,washe gari yaune akayi sadakar uku mutane sun ragu sosai ba kamar daba ." Kale ² takeyi a d'akin tarasa meyafaru bazata iya tunowa ba ihu tafarayi dan razana take koda wane lokaci ,momy da tatashi akan darduma tayo d'akin da gudu ta sami Khadija nata juya kai tana ihu ,wasu zafafan hawayene suka zubowa momy tayi waje da sauri ,driver ta k'walawa kira cikin azama yazo ya drk'usa a gaban momy _momy ce tace ”maza ka fito da mota mu koma hospital ,komawa tayi ta ruk'o Khadija tafito da ita hijab d'inta ta Sanya mata daganan sukayi mota ,dak'ayar momy ta sata a mota suka wuce hospital, sunyi sa'ar ganin doctor ,inda yake sanar musu cewar su dage da adu'a kuma akwai abinda take tunawa yake tsorata ta magunguna ya kuma basu yace ”ku kulla sosai da ganin tasha magani." Haka driver ya dawo dasu gida ,matane keta shigowa gidan momy suna yimata ya karin hakuri ,wanan su shigo wanan su fita dayake momyn ta mutane ce . *KAUYE* Sahura ce ta shigo gidan inna da gudu tana shewa ,had'e fuska inna tayi tace ”fitarmin a gida nace kifice ko ,dariya Sahura tasa tace ” inna ya alelen ranan waya biya kud'in ¿"ubanki ne ya biya kinji ,sahura ce ta zaro ido tace ” ubana fa sirikinki ne ,inna ce ta d'auko sanda tana shirin buga mata wani yaro yai sallama yace ” Aslamu alaikum zakusi kai da kafar kaza ?" tsalle Sahura ta doka tace ”kai yaro kawo nan shigowa yaron yayi ya nemi guri ya zauna ,Sahura ce ta dubi inna tace ” hmm sai na tuna lokacin da mukaje gidansu Ladidi kullum sai naci kaza ,amma yauma Allah yasa inada ragowar kud'in da Humaidu ya bani d'ari biyu na siya ,dajin haka inna ta washe hak'ora tana dariya tace ”yoo ai siyama zakiyi koda na d'ari ne Sahura ce ta tambayi yaron nawa nawa ashirin ashirin yaron yace ”kasiyar uku hamsin ¿"eh kawo . Kai ta d'iba guda biyu k'afa kuma d'aya duban inna tayi data zuba tagumi tace ”toke bazaki d'auka bane ?inna ce tace ”to masu abin basuce in d'auka ba ni na isa ,dariya Sahura tasa tace ”laaa ina ki d'auki na hamsin ,inna na sid'ar hannu ta d'auka harda zubo romo ,yaron yana zaune har suka gama ci Sahura tace ”ga hamsin d'inka kajira wanan tsohuwar ta baka kud'inta inna na sud'e hannu tace ”kan uban ke kin biya naki hakafa kikayimin ranar sai malam ne ya biya yana fad'a Sahura dake taunar k'ashi tace ” maganin mai kwad'ayi komai mutum saiyyaci ,inna ce ta kunto zaninta gudar d'ari biyar ce a jiki mik'a wa mai kai da k'afa tayi tace ”k'aromin na hamsin ,dan ubanta ni zata rainawa hankali*LADIDIN KAUYE* funny & love story 51_52 Yaro dai na ganin ikon Allah ya je ya samo canji ya kawowa Inna ,Sahura ce tace ”au kewai inna kina gadarar zaki bani haushi ne aikin 6urr saidai inbaki haushi ta ja gyalena ta d'aura a kwankwaso ta fizge kwanon da inna tasa a dad'o mata naman ta ruga da gudu ,kuka inna tasa tana tsinewa Sahura tana cewa ,shegiya ga kashe d'ari danayi tashi d'aya gashi iya romo na tsaya sud'a ta wafce kwanon ,shidai mai talla gaba yai yabar inna tanata surutunta." _JOS_ da sallama ya shigo yana cewa momy yau akayi sadakar bkwai to Allah ya gafarta masa kuka momy takeyi sbda inta tuno abinda yafaru amma aikin gama ya gama rayuwar batajin dad'in yinta sbda Khadija har yanzu sai sauk'in Allah yanzu ciwon 'nata ya koma kamar na mai aljanu in ciwon ya tashi to guduwa take burin yi dady abubuwa sunyi mai ywwa sosai duka dai familyn gidan basuda wal wala ,kwance take tana bacci sai kuka takeyi kuma da k'arfi ,momy ce ta shigo d'akin ta sameta tana bacci kuma tana kuka ,adu'oi tashiga yimata tana tofa mata ,yunk'urowa tayi tana gurnani zata hankad'e momy ,cin sallamar Jalal yasa momy k'wala masa kira ,da sauri ya shigo yana cewa momy lafiya kuwa ¿inafa lafiya Jalal ?narasa yaza’ayi da ciwon Khadija kullum abin baya lafawa kullum cikin fad'a muke gashi banda kunu batacin komai y'an aikin gidan suntafi garinsu ,sai kuma tasa wani kuka mai ban tausayi ,hak'ik'a momy mace ce wace batada zalunci batada mugunta kuma bata fifita wani akan wani ,Jalal shima abin yafara damunshi kukan da momy keyi ya kuma tayarmai da hankali ,sukan sunga jarabawa Allah yasa su cinyeta duka." Washe gari antashi da wani sanyi mai shiga mai shiga jiki tunda gari ya waye khadija keta ihu tana k'ok'arin fitowa wani girgiza d'akin yakeyi ga wasu k'ara dake baiyyana a cikin d'akin ihu takeyi iya k'arfinta ,dady daya shigo yanzu yai d'akin da sauri ,ganin inda jikin khadija keta 6ari yana makyar kyata yasashi cire hular kanshi adu'oi yaketa karanto mata amma sauki sai lokacin da Allah ya nufa ,gefenta wasu abubuwa take gani masu ban tsoro sai nuni take yiwa dady ina shikam bai gani ba ,ihu take kuma yi tana ruk'o hannunshi amma dady babu abinda yagani yarasa wane ciwo ne ke damun khadija , adu oin da yai mata yasamu jikin ya lafa dan har bacci ya d'auketa." D'akin momy ya nufa zaune ya sameta kan sallahya tana azkar shigowar sa ne yasata shafa adu'a tace ” barka da dawowa mijin kirki ,dady ne ya fitar da wata zazzafar iska daga bakinshi ya d'aga hannu sama yana cewa Allah mun gode da jarabawar da kayi mana Allah ka kawo mana mafita ba yawan arzik'inmu ba bakuma yawan ibadunmu ba Allah ka dubemu ,suka shafa tare da cewa amen. Wata girgiza sukaji mai firgitarwa momy zata tashi dan taga meke faruwa dady ya tsayar da ita yana cewa kibari in lek'a ,momy na shirin kuka tace ”gaskiya sai dai muje tare ,hannun dady ta rik'e tana kuka suka fita , duk wanan hayaniyar da girgizar duk a part d'in Khadija yake faruwa hatta k'ofar ma girgiza takeyi kuma a bud'e take ,dady na shirin lek'awa momy ta rik'oshi tace muje mu nemo malamai dan Allah ,hankalin dady a tashe damu warshi wane hali baiwar Allah take ciki marainiya ,kutsa kai yayi momy na tsaye ya wuce ,kwance ya sameta d'akinta duk ruwa mai had'e da jan abu mai kamada jini sai wasu surutai takeyi ,kafin dady yace ”bismillah kawai aka d'aukeshi aka gwara da jikin bango ,ihu momy takeyi iya k'arfinta gadai khadija a kwance shikuma dady ,kowaye yayi mai haka oho , mai gadi ne da driver sukayo cikin gidan a tsorace ,momy babu magana sabda kuka yaci k'arfinta saidai nuni da hannu ,hango dady sukayi a mak'ale a jikin bango shi bai sauka ba shikuma bai yi sama ba, wani hayaki ne ke fitowa amma Khadija na kwance tana bacci ,driver ne yace ”anya babu shed'anu a lamarin kafin ya rufe baki yaji an wankamai mari ,ganin basuga kowaba yasa mai gadin da driver da momy suka arce da gudu , d'akinta momy ta koma ta d'auko wayarta ta kirawo Jalal ring d'aya ya d'aga yana sallam momy ko amsawa batayi tace ”Jalal.ka kirawo mai ruqyya dan Allah dadynku tana kuka to yace kashe wayar momy tayi tana adu ar datazo daga bakinta , bayan 30minutes sai gashinan shida wani babban malami sun shigo ." Gai sawa sukayi da momy daganan tayimai bayanin ciwon Khadija dakuma halin da dady yake ciki ,ruwa ya buk'ata domin alwalah bayan ya idar da alwalar ne yace ”a nunamai d'akin ,momy ce ta shige gaba itada Jalal shikuma malamin na baya da Qur'ani a hannunshi ,da hannu momy tayimasa nuni da d'akin ,lek'awa yayi ya hango dady jingine a jikin bango shi baya k'asa auxubillahi yace ” a lokacin da yake karanta suratul bak'ara ,jikin dady ne ke jijiga yana wani gurnani tsananta adu'a malamin yayi , Allah cikin ikonsa saiga dady ya fad'o yana tangad'i ,malamin ne yace ”asamu yayi wanka kuma ya kwanta ,kan Khadija aka koma daketa bacci ko motsi batayi adu'oli iri _iri malamin yayi amma har yanzu shiru ,d'akin sai fitarda wani hayak'i takeyi mai ban tsoro." Fitowa malamin yayi yana yarfe gumi yace ”zanje in dawo ,to su momy sukace daganan suka rufo k'ofar khadija ,da fitar malamin gidan duka ya kaure da kururuwa mai firgitarwa daga momy har Jalal sun kasa koda motsi ne ,dama dady bai tashiba tunda yai wanka ,jin girgizar tayi yawa yasa momy shiga bathroom d'inta d'auko buta tana shirin zuba ruwan alwal wasu abubuwa tagani na ban tsoro hakan yasata ficewa tana salati Jalal ne yace ”momy to yanxu ya za'ayi ¿ jin momy tayi shiru yasashi kallon inda take kallo ,wata halitta ce mai abin tsoro da girman ta ya zarce tsawon d'akin a sunkuye take tafiya ,idanuwan momy suk k'afe bataji bata gani ,kafin wanan abin ya iso Jalal cikin tashin hankali ya cici6i momy yai da ita d'aki suna gudu halittar na binsu Allah yabashi ikon rufe k'ofar ba tareda wanan halittar ta shiga ba." Ruwa yadinga yayafawa momy amma shiru ,a karo na biyu ne ya bud'e ma dai _dai cin fridge d'inta ya ciro ruwan sanyi yana yayyafa mata cikin sa'a ta mik'e tana salati, sallamar malam sukaji babu wanda yai k'ok'arin tashi malamin yace ”yanaga babu kowa Jalal ne cikin d'aga murya yace ” kaje d'akin mara lafiyar ,gamunan momy na ce babu lafiya ,shigewa d'akin malamin yayi daganan yafara adu'oi yana tofa mata yanayi yana tofa mata wata atishawa tayi mai k'arfi wacce tayi dai dai da tashin dady daga bacci ,momy take kira iya k'arfinta ,momy najin muryar Khadija ta fice da sauri tana cewa yaushe rabon da daughter ta kirani, fara'a ce ta baiyyana a fuskarta tashiga d'akin zaune ta sameta ,da shigar momy Khadija tace ” momy maiya faru ne babu komai momy tace ”daganan malamin yace ”hajiya muje parlor inyi miki bayani OK tace suka wuce Khadija tashi tayi ta shiga wanka ,ganin duniyar takeyi kamar sabuwa.*LADIDIN KAUYE* Page 53 & 54 Malamin ne yace ”dole sai kun kiyaye da shan maganinta to momy tace ”yabasu adu'oi da zasu dingayi a gidan , momy ce tacewa "Khadija ta shirya suje airport itada Khalel , cikin sauri ta nufi d'akinta dan yanzu burinta bai wuce taga mijinta ba , Jalal ne yashigo yana k'walawa khadija kira , fitowa tayi cikin wata shiga mai d'aukar hankali , less ne pink a jikinta sai gyalenta fari takalmi fari jaka pink and wait, wow kuzo kuga Khady , suka shige mota zuwa airport , mutane ne keta saukowa , hango wani had'ad'en saurayi tayi mai kamada Humaid ,tunani tafara kodai humaid ne ?" sanye yake da bak'ar rigar sanyi my adon flawoyi gashi yayi haske sai dai ya rame sosai , da zuwanshi yayi hugging gimbiyarshi , shidai Jalal na gefe yana zaro ido , sunkuceta yayi ya rungumeta yana yimata rad'a a kunne wanda nima banji me suke cewa ba ,Jalal ne yace ”wato ni an manta dani ko ?"dariya Humaid yayi ya doki k'afad'arshi yace ”am sorry kuna raina dukkan ku , mota suka shige ,Humaid da Khadija a Back side ,Jalal yana gaba yana driving,da isarsu gida sukaci karo da anshirya walima gagaruma gurin ya kawatu da flawoyi masu wuta suka shige ciki ." funny & love story 55_56 Dady da momy suka zauna a kujerun da aka zagaye gurin suna adu'a Jalal ne yace ”bari a yanka cake sai 'intafi gida ,momy ko dariya takeyi farinciki fall zuciyarta ,durk'usawa Humaid yayi ya gaida dady yaje ya gaida momy ya dawo kusada Khadija ya zauna sunci sunsha dan abinci ma daga hotel aka kawo ,misalin k'arfe biyar dady yacewa Humaid ya d'auki matarshi ya wuce ,wanan karon dai Khadija batayi kuka ba, sai da sukayi sallahr isha'i sanan suka d'unguma zuwa gidansu ,hira sukeyi jefi jefi ,da isar su gidan sabon mai gadin da dady 'ya sa musu ya wangale gate d'in yana yimusu sannu da zuwa ,da shigarsu yai parking a ya fito yana mai yiwa Allah godiya ,itama fitowa tayi suka nufi cikin gidan ,kowannensu d'auke da sallama a bakinsu ,da shigarsu parlor suka yada zango Humaid ne ke dariya yana kallon Khadija yace ”baby kingaji ko farr tayi da idonta tace ”yaya mungaji dai cikin sigar tsokana yace ”to gafa tsaraba na kawo miki dan nasan bakya bata kunya tasowa tayi tazo kusa dashi ta zauna wata leda ce mai kyau ya ciro mata gasashiyar kaza ,murna takeyi tana godiya Humaid ne yace ”to yanz mekuma kikeso ,rufe fuska tayi tace ”nakasa tashi d'auko ruwa zansha yana dariya ya mik'e ya d'auko ruwan ,bayan ta cika cikinta ne humaid yace ”to muje muyi alwala yaukam 'zamuyi nafila a sa'a lol." Hhh wata nafilar aka kumayi akayi adu'oi sosai daganan 'naga Humaid ya sunkuci Khadija yana harara ta ,garin gudu har nakusa fad'uwa 'asbha tagari amarya da 'ango. Bayan komai ya lafa ne na hango Khadija nata kuka tana cuno baki ,Humaid da fitowarshi daga wanka kenan yace ”haba baby kiyi shiru mana ya marai raice murya kamar mai shirin kuka ,dariyace da kufce mata tace ”kazo ka d'agani 'inka gama tsokanata ,kaya yafara cire mata sanan ya sunkuceta ya kaita bathroom cikin ruwan wankan daya tara mata wani ihu tasa kamar wacce ake shirin cirewa rai can anjima ta lumshe ido sabda zafin ruwan ya ragu ,zubarda wancan yayi yakuma tara wani ,dubanta yayi yace ”to fito inyimiki wanka ,kuka tafara tana yaya dan Allah kaje ka fitomin da kayan dazansa please zanyi da kaina ,zai juya ya hangota ta kwanta kamar wacce ta sami katifa cikin bahon wanka ,dawowa yayi ya fara yimata wankan tana had'ashi da Allah yanayi bai fasa ba." Nad'ota yayi cikin towel kamar baby hhh ashefa babyn ce ,kwantar da ita yayi a kan gado yafara shafa mata mai , yana gamawa ya d'auko ta ya zaunar da ita gaban dressing mirror ,itadai ta koma kamar photo ko magana batayi powder yafara shafa mata dagan an ya d'auko k'wali ya sanya mata ya d'auko janbaki ya shafa mata hh gurin yin jagira ne yayimata kamar titi fakaceciya dariya sukasa ,gogewa yai yace ”to ainayi mai wuyar ko kinga inda kikayi kyau kuwa hmm kamar sarauniyar kyau , to zomuje kisa kaya ko baby ,kuka zata fara yace ”mai yafaru kuma¿uhm uhm ni yaya bazan iya tafiya ba please help me ,cewa yai uhm uhm nima Ladidi da k'yar nake tafiya ,dariya da kuka ne sukayi nasarar k'wace mata shikuwa yana ganin haka ya sunkuceta ya dirita a gado ,had'ashi ta dingayi da Allah dama ba komai zaiyi mata ba kwai yanason sata yin shiru ne ,cewa yai zonan muyi adu'a ,cikin shagwa6a tace ”yaya kayanfa ?,riga da wando ya ciro mata masu flawoyi a jiki wandon iya gwaiwa ne rigar kuma iya cibiya bayan tasa ne ya kamo hanunta yana sunbatar k'amshin tiraren data fesa yace ”dan Allah ki yafemin Khadija dan Allah ,raahin fahimtar abinda yake cewa yasata kallonshi tace ” yaya ban ganeba ,kukane yayi nasarar kufce masa yace ”nayi miki mumunan zato Khadija asheke cikakiyar budurwa ce nagode da kika kularmin da kanki ,domin duk soyayyar da kuka zuba da buduraka muddin bata tare da budurcin ta to wallahi bazatai daraja a idon mijinta ba ,Khadija ce ta fad'a jikin Humaid tana kuka mai cin rai ,rungumeta yayi yana kwararo mata 'adu'oi akan albarkar rayuwarta ." Kitchen suka shiga suka had'a breakfast mai rai da lafiya bayan sungama ne Khadija ta zubo musu shikuma Humaid ya shiga wnka ,yana fitowa Khadija ta d'auko wayarshi tafara yimusu photo ,hotuna sukayi kala kala wani ya d'auketa wani kuma tana bayanshi wani kuma ya rungumeta daganan suka zauna cin abinci ,suna gama Humaid yace ”zaije ya dawo insha Allah baze dad'e ba ,rau rau Khadija tayi da ido tana cewa yaya please kaje dane man dariya yasa yace ”to shirya man am sorry sweetheart yanz zandawo afuwan kinji to Allah ya dawo dakai lafiya hubby ,zaro ido yayi yace ”dama inada Suna na musamman shine ake rowar gayamin juyi tayi tace ”yaya kaje ka dawo cikin sauri ya fice sbda Doctor Umar ne yake kiranshi a hospital ." Misalin k'arfe 1pm Khadija takuma shiga wanka simple makeup tayi ammafa tayi kyau sosai shadda ta d'auko kalar wacce Humaid yasa mai ruwan coffee ba k'aramin kyau shaddar tayi mata ba kasancewar farace sark'a da d'an kunne tasa sai kuma agogon hannu wohuu kamar ka saceta dan kyau, alamar nocking akeyi mai gadi ne ya tambayeta daga ina kike hajiya ? Matar ce tace ”sunanan Rahma to kishiga hajiyanna ciki ,tana isowa part d'in Khadija tafara nocking a nutse Khadija ta fito ganin Anty Rahma ce yasata rungumeta suka shige ciki ,Anty Rahma ce ta kalli Khadija tace ”amarya yakuma k'arin hak'uri alhamdulilh Khadija tace "ta mik'e ta dibowa 'Anty Rahma kayan motsa baki hira sukeyi cikin farinciki tana tabyarta ina yaranta twins dariya anty Rahma tayi tace ”kema ina yimiki fatan hakan rufe fuska Khadija tayi tace ”rainon twins da wahala anty ,sallamar Humaid ce ta katse musu hirarsu wani tsalle Khadija ta doka tatafi da gudu ta dalle bayan Humako.." Anty Rahma ce tace ”to ni zantafi masoya Khadija na baya ta rufe ido dagan an tacewa anty Rahma bye bye Humaid ne yace ”ina yini ya yara lafiya Lou tace ”daganan tayi gida ,hmm wato khady ko kunya babu 🤭. Sauketa Humaid yayi yana yimata wani irin kallo afuwan fans gaskiya zaman gidansu Khadija yafi k'arfin mom Islam . *AFTER TWO MONTHS* Kwance take kan cinyar Humaid wani amai ne ya taso mata ,kafin yayi yunk'urin mik'ewa ta wankeshi da aman kuka takeyi sosai sbda bak'on yanayin daya ziyarce ta sam batajin dad'in komai a rayuwa ,d'aukarta Humaid yai ya wanke mata jiki ya dawo ya kwantar da ita 'a kan gadonshi ,komawa bathroom yai ya wanka yasakeyi ya shirya ,hijab ya sanya mata ya d'auketa yafice da ita ,bud'e mota yayi yasata 'a back side ya rufe k'ofar ,direct hospital suka nufa da isarsu aka taresu kasancewar halin su kenan kowa na cewa doctor kak'i dawowa aiki hak'uri yaketa basu kasancewar yanzu hankalinshi ba 'a kwance yake ba ,office d'in doctor Umar ya shiga ganin bai ganshi ba yasashi komawa mota ya rik'o hannun Khadija da ta galabaita ya kaita wani d'aki da babu marasa lafiya ,pitsari yasata yi bayan tayi ne yaje wani lamp ya d'auko abin d'iban jini yana d'iba ya fice test yaje yayi zuwa minti talatin result ya fito bud'e baki yayi yana kabbara wani doctor Hashim ne yace ” doctor da kanshi yana awo tsabar farinciki Humaid yace ”Hashim yanzu ma zamuje d'akin awon munsami k'aruwa, kowa sai tayashi murna yakeyi." Khadija dake kwance tanajin kwad'ayin shan tsamiya ta taso tana shirin fitowa sukayi ido biyu da Humaid cewa yai haba baby yazaki wahalarmin da kanki 'ina zaki ,cikin shgwa6a tace ”tsamiya nakeson sha ,zaro ido Humaid yayi yace ”kekuma naki jarabawar kenan¿zata yimai kuka yace ” come down zomuje ayi awo sai mu k'ar6i magani mu wuce kasuwa ,babu musu tabishi suka wuce ana gama mata ya kar6o magani suka shige mota basu sauka a ko ina ba sai kasuwar farar gada ,kayane gasunan na masu ciki irin su tsamiyar biri malmo ali mai ruwa dakuma tsada da agwa luma lol dama wanda na manta haka yadinga jidar mata kayan tsami hhh yaufa babu sha'awar cin kaza saboda wari takeyi mata lol. Da isarsu gida ya zuzuba mata wasu a fridge wasu kuma ya wanko mata suka zauna tanata sha ko tayi babu ,hh Humaid da keta k'are mata kallo yace ”Alhamdulilh Allah yabani kyautar mata tagari kuma zata haifamin y'ay'a nagari am very happy wow Khadija bansan da bakinda zankuma yimiki godiya ba please kikula mana da babyn mu ita dai ko kallonshi batayi ba abinda yafi komai dadi takeshi ammafa a gurinta. TV Humaid ya kunna NTA wani rahoto ne yaja ra'ayinsu gani nayi Khadija ta tashi ta zauna ,shima Humaid d'in gyara zama yai wani matashin yaro aka nuno hannuwanshi a d'aure yana koro jawabi kamar haka. _Nidai sunana Ammar d'a daya tilo ga Alhaji Atiku dollars nataso cikin gata da kulawa a London aka haifeni iyayena basa zama a Nigeria amma ni a Nigeria nake rayuwa ,wani soja dake tsaye ga wasu kuma dake ririke da last speaker suna yimasa tambayoyi to maiya kaika aikatawa y'ar minista fiyad'e ? tsautsayine yace ”a takaice ,wasu tambayoyin aka kuma jeromasa akan cewar kwanaki ankashe mai gadi agidan yaron Alhaji ABDULL... ko zaka iya bamu cikakkiyar amsa eh ninne na kashe shi ,kuma ba shi naso kashewa ba tsohuwar budurwata naso kashewa kokuma mijin da ta aura ,bayan nan ko akwai wani kisan daka ta6ayi babu nasani tawa ta k'are k'arfin arzik'in mahaifina bazai fitar dani daga hannun hukuma ba_. Daganan aka wuce gurin . Kukane ya kufcewa Khadija sbda tayi dana sani akan sanin Ammar datayi amma Alhamdulilh tunda gashi a hanun hukuma . Suna cikin alhinin Ammar sukaji sallama ,Humaid ne ya mik'e jiki a sanyaye bud'e k'ofar yayi yana k'are mata kallo yace Khairat!!!! momy dake baya ta shigo sanye da hijab tace ” daughter kinga yarinyar da tayi sanadin ciwonki nan ,mik'ewa Khadija tayi ta fad'a jikin momy ta saki kuka mai tsuma zuciya d'ago kanta tayi tace ”momy wanan wacece ?"tsohuwar matar Humaid ce ,momy ce tabata kaff labarin auran Humaid 'dakuma abubuwanda suka faru bayan barinta gida da halin da momy ta shiga ,kuka Khadija takuma sawa ta durk'usa ta rik'e k'afar momy tace ”momy dan Allah ki yafemin,dana zauna da baki dinga zubar da hawayenki ba natuba momy ,d'agota momy tayi tace ” daughter na yafe miki karki damu kowane bawa da tashi jarabawar ,Khairat ce ta durk'usa 'a gabansu momy tace ”dan Allah nima ku yafemin ,nasan na cutar daku gashi ta sanadiyar bin bokaye fuskata ta k'one kowa guduna yakeyi kuma iyayena ma sun tsune min ta had'a hanunwanta biyu tace ”dan Allah Ku yafemin kodan guduna da duniya takeyi ,Khadija ce ta d'agota tace ”na yafe miki Allah ya yafemana ,Humaid da ko kallonta bayason yi sabda fuskarta tayi abin k'yama yace ”indai zaki ficemin a gida to na yafe miki jekiii ya daka mata tsawa momy ma cewa tai ta yafe mata daganan ta fice ,tana fita suka rufo k'ofar d'akin ,jin wani k'ara da wata mota tayi yasasu bud'e get suka fito da gudu ,motace ta kad'e Khairat jini ta baki jini ta hanci ,drivern kuma ya gudu ,cikin azama Humaid yazo ya jijigata jin alamun babu rai a tare da ita yasashi salati momy ma salatin takeyi Khadija kuwa na kuka gidansu ya nufa da ita inda da shigarsu suka tarar da mahaifinta da mahaifiyarta a parlor." Bayan ya gaishesu ne yake fad'a musu tare da Khairat yazo ,a fusace mahaifin nata ya mik'e yana nuna Humaid yana cewa karta sake ta shigomin gida da k'azamin jikinta mai za'ayi da mazinaciya !!! Kuka Humaid yafara yana cewa dady ku yafe mata motace ta kad'eta kuma babu alamun nunfashi a tare da ita momy a razane tayi waje dady ko ciki ya shige irin ko a jikinshi ,momyn Khairat na ganin ta tafad'i ta suma dady ne ya fito da gudu shima ganin gawar Khairat yasashi nadamar tsa tsauran hukuncin da ya yanke akanta yafa cewa nayafe miki Khairat Allah kayafewa Khairat . Wayo Allah mutuwa fa ta kori komai a rayuwa kana yawo da gangar jiki baka saniba to y'an uwa mudinga nufar kowa da alkairi mubi umarnin iyayenmu muzamo masu neman za6in Allah. Gida Khadija suka koma ita da momy sai kuka Allah sarki rayuwa . ********************* Kamar inda kuka sani ne ikon Allah yafi gaban wasa rayuwa tana juyi kala kala wani abin a zahiri wani ko a bad'ini farinciki ko akasin hakan . AFTER 5 MONTHS momy na kwance tana bacci aka kirata a waya cewar matar Jalal ta aihu murna bakin momy baya rufuwa ranar suna yaro yaci sunan Baban Khadija wato Musa yaro yasami gata ta kowane 6angare Khadija kuwa tayi rawar gani sosai dan ba'a barta a baya ba ,lokacin cikin Khadija yana 8 months dak'yar take tafiya y'an uwan momy ma sunyi wa yaron shatara ta arzik'i. Farinciki arzik'i kwanciyar hankali duk familyn sun samu kwanci tashi asarar mai rai cikin Khadija yakai aihuwa zaune take bayanta ya rik'e gakuma mara datasata gaba salati takeyi Humaid dayake kwance yana bacci ya jiyo salatinta ya fito da sauri ganin halin da take cikine yasashi cewa zomutafi hospital ,girgiza kai Khadija tayi tace ”insha Allah a gida zan aihu ,nishi takeyi iya k'arfinta Humaid ne yace ”kid'an k'ara nishi please kidaure rik'eshi tayi kam kam tasaki wani nishi sai ga yaro ya fad'o tana shirin kwanciya taji wata sabuwar nak'udar Humaid yace ”baby gyara na dubaki ,kafin yakai ga dubata sai ga wani yaron yakuma fad'owa ,kuka tafara sosai dan walhi tunda tazo duniya bata ta6a shan zafi kamar haka ba ,Humaid ne ya mutsike yaran da kwa6a6en lalle sbda yana fitarda datti gakuma k'arawa yara lpy bayan mintuna kad'an ya nannad'e yaran ya kwantar dasu kitchen yaje ya juyowa Khadija ruwan zafi ya taimaka mata ya rakata toilet,wanka yayi mata tana cewa da zafi hakadai ya gasa mata jiki ,dawowa yai kan yaran ya tattauna dabino yabasu ya juyo da kunnesu yayi musu kabbara alhamdulih farinciki baiyyane a fuskar Humaid sai da yayiwa yaran wanka ya sanya musu kaya masu kyau sosai dasu safa ,yaga Khadija ta shirya kamar ba mai aihuwa ba sai dai rashin k'arfin jiki ruwan shayi ya had'a mata mai kauri tasha sanan ya kira momy a waya, yake sanar mata ai Khadija ta 'aihu momy ce tace ”wanne hospital kokuma kuna nakune ,Humaid ne yace ”momy a gida ta 'aihu ,da sauri momy ta d'auko hijab tasa driver ya kaita gidan Khadija ,da isarta gidan d'akin Khadija ta nufa ganin babu kowa yasata komawa parlor ta zauna." Tace ”idan kagama kar6ar aihuwar kafito cikin d'aga murya momy take maganar ,Humaid 'dake kwance ya rungume twins d'inshi ya zaro ido yace ”kiyi baccin k'arya please Khady ,rufe idanuwa tayi alamun tana bacci shikuma ya fice parlor gurin momy ,sunkuyar da kai yayi yana sosa keya alakun jin kunya ,momy ce tace ”ina daughter tana ciki yace ”a tak'aice da shigar momy tasamu Khadija tayi baccin gaske hhh mata anji jiki ☹️ rungume yaran momy tayi tana wani farinciki ,number dady momy ta lalubo ring d'aya ya d'auka ,bayan sun gaisa ne take bashi labarin aihuwar khadija murna fall zuciyar dady barinma dayaji momy tace ”yan biyu, Humaid ne ya shigo bayan ya gaida momy tana cemai ya kar6i aihuwar lafiya ? dariya yasa yace ”momy babu wani abu da 'ake buk'ata eh bbu zaka fitane ,cewar momy Humaid ne yace ”yanzu Doctor Umar yakirani a hospital zanje duba wata bbu lpy OK tom Allah yayi albarka ,amma gobe khadija zata koma gidan mu ba hakan yaso ba 'amma babu inda ya iya yace ”Allah ya kaimu. Washe gari momy tazo aka shirya kayan Khady dana boys suka nufi gidansu momy ,tana sauka farfesu yayi mata sallama tana zama momy tasa Ummi wato y'ar aikin gidan ta kawo mata citakeyi bakinta babu dad'i bayan tad'anci kad'anne tacewa Ummi tazo ta d'age ,*LADIDIN KAUYE* funny & love story 57_58 Washe gari Humaid ne yazo cikin wani lallausan yadi blue my kyau fuskar shi sai fitar da tsananin murmishi yakeyi ,kai tsaye d'akin matarshi ya nufa ,sanin yanzu za'a fara yimai katanga da ita ,a hankali ya shige babu wanda ya ganshi ,kwance ya sameta tayi wanka taci kwaliya ,juya idanunsa yai bai saukesu a ko inaba sai akan babys d'insu ,bacci suke sha masha Allah ,ganin baccin ya d'auki Khadija sosai yasashi kwanciya gefenta sunajin nunfashin junya ya rungumeta ,jin d'umin mutum kuma an rungumeta yasa khadija k'ok'arin kwala ihu , Humaid da jikinsa keta rawa ya had'e bakinsu guri d'aya ,wani irin salo yake yimata 'hakan yabata damar k'ara rungumeshi tana lumshe ido ,hmm Khady ayi a hankali dai tamm🤐 Humaid 'da yakejin tsananin buk'atar Khadynshi ya ma manta jego takeyi yau kwananta uku ,Khadija ce ta dawo cikin hayyacin ta tace ”honey kasan fa momy zata shigo kartazo ta samemu fa ,shii ya sa hannunshi kan lip d'inta don't worry zan 6uya ,zaro ido Khadija tayi tace ”to ka sakeni karta shigo ,matseta yakumayi sbda wani yanayi da yakeji suna cikin hakane momy tafara nocking dan taji k'ofar rufe zaro ido Khadija tayi tana kai dubanta ga Humaid da shima ya zaro nashi kyawawan idanun ,to ya za'ayi ya rad'a mata a kunne ,ka shige toilet kawai kasa key ,mik'ewa yayi ya shige tareda murza key ,momy data gaji da tsayuwa tace ”nikam wane irin bacci kikeyi haka ,Khadija cikin muryar bacci Khadija tace ”momy kiyi hak'uri bacci ne ya d'aukeni ganinan zuwa ,mik'ewa tayi ta gyra wuyan rigarta tare da fuskarta ta shafesu da hannayenta taje bud'ewa momy." Fad'a momy tafara yimata ya'ayi ta rufe k'ofa bayan tasan ba ita kad'ai bace yanzu in yaran suka tashi suka kuka fa ,shiru tayi tace ”momy kiyi haku'ri bazan sake ba ,shigewa d'akin na Khadija momy tayi ta fiddo wasu magunguna data tafasa a kettle ta silba cewa tayi tashi da d'uminsa kije ki kama ruwa dashi karfa ki sirka to tace ”hhh tunowa tayi ai honey na toilet yasata cewa momy zanyi ,momy cikin bada umarni tace ”tashi yanzu ki shiga ina kallonki ,lol babu inda ta iya sbda bata yiwa momy musu ta shige toilet d'in ,ta rufo k'ofa ,lokacin ne momy ta fita ,ganin Humaid tayi yana zaune a gefen bahon wanka dariya tafarayi k'asa k'asa ,Humaid ko haryanzu a tsorace yake amma duk tsoron da yakeji bai hanashi rungumo ta ba cewa tayi to momyn ta tafi please ka koma parlor zanyi tsarki kallon ta yakeyi yana dariya ,to maganin menene aka baki oho tace ”a tak'ai ce au bazaki fad'amin ba ?"uhm uhm kwai na masu jego ne ,Khadija tace ”lokacinda take shirin tsugunawa ,Humaid da hankalinshi da idanuwanshi duk suna kan Khadija ,lura da hakan yasata cewa mo, aikuwa Humaid ya rufe mata baki ficewa yayi dan yasan zata tona masa asiri kan yaran ya koma yafara yimusu adu'a sanan ya fice . Yau kwanan Khadija bakwai yaune suna ,d'inkuna kala_kala Humaid yaiwa Khadija sosai sukayi kyau itada yaranta da sukaci sunan Adam da Abdullahi ,kyawawa dasu gashinsu kamar na turawa kuma kyau da dogon hancin duk na Humaid ne sunsha photo inkaga mijin mai jego kamar wanda akayiwa bushara da aljanna ,momy kuwa hidima akeyi sosai babu zama . Washe gari kowa ya watse sai momy da Khadija a gidan dady yayi tafiya ." Kwance take tana tunanin halinda mijinta ke shiga lokacinda yaji kewarta d'an halak tafad'a lokacin da taji alamun shigowar mutum Humaid ne sanye da gajeren wando fari ya shigo sad'af² kamar muna fuki key yasawa k'ofar dagan an yakai dubanshi ga Khadija yace ”baby gurinki nazo fa tana dariya tace ”to bagani ba ,no wai haryanzu shi wanan mai sarautar bai tafiba ,hh ta gane mai yake nufi sarai tace 'to menene hakan measses period uhm yakusa nanda 3 months zaro ido Humaid yayi yace ”ko tausayi na bakyani ko yayi alamun kamar yai fushi ,kamoshi tayi ta kwanta saman fafad'an k'irjinshi tana cewa yaya nayi missing ya rufe mata baki da nashi ,am to riders yakamata mu fito daga d'akin mai jego kasancewar lover's sunfara 😀, Kwance take wani azababen zafi takeji wayo rayuwata ,tafad'a lokacin da Humaid ya mik'ar da ita zai kaita toilet wani rawar jiki yakeyi ,lol ya had'a mata ruwan zafi ta shiga ta jima acikin ruwan maganin butar da momy tabata ,ya zuba ruwan zafi a ciki yace ”to yi tsarki da wanan ,bayan ta fito ne ta kar6a tayi tsarki dashi d'aure da towl suka fito rik'e da hannun juna ,Humaid ne ya shafa mai ya zura wandonshi ita ko Khadija bata sauya kayaba sbda tasan momy batada wuyar gano abu ,tana gama tunanin taji sallamar momy ,tunawa tayi yaumafa ta kulle k'ofa ,Humaid dayai nasarar ficewa kafin momy ta shigo ,bud'ewa momy k'ofar tayi ,momy sai kallon fuskar Khadija takeyi kamar mai son gano wani abu ,sunkuyar da kai Khadija tayi tana wasa da fingers d'inta ,murmishi momy tayi tace ”humaid ya shigo d'akinan ¿bb a'a.... hhh anan momy ta harbo jirgin zama tayi bakin gadon Khadija tace ”wato kunnenki bayajin magana ko daughter ,walhi kika biyewa namiji zakiyi dana sani because shi bashida problem kasancewar su basusan babu ba ko kina nufin gurin da kike tak'ama dashi bazai samu Matsala ba ?to wallahi jego kikeyi kikayi wasa da magungunan danake baki ruwanki ,kuka Khadija tahauyi tana cewa momy kiyi hak'uri bazan...dakatar da ita momy tayi tace ”inafa bazaki sake ba 'anjima nan zaki sake kemai miji ko hmm gata nake yimiki zomuje ki kar6i farfeshi kici wanan mijin naki 🤐shiru momy tayi lokacin da tabar part d'in Khadija. Da shigarta bedroom d'in momy kula momy ta mik'o mata wace aka cikata da farfesun kaji yasha yaji da kayan k'amshi bugu da k'ari ga magani kanaci kanajin alamunshi ,zama momy tayi a gefe tana jiran Khadija ta cinye kuma ta shanye romo ,ci Khadija yakeyi dan dauriya ba dan dad'i ba 'ajiye kular tayi tace ”momy na koshi ,spoon momy ta mik'o mata tace ”ungo shanye romon sai anjima ki cinye sauran tafi dashi. Yauma kamar kullum gogan ya shigo sanye da farar jallabiya Khadija ce ta fad'o masa kawai ya bar hospital ya dawo ganinta samunta yayi tana karanta wani littafi ,salama yai bayan ta 'amsa ne ya d'orata kan cinyarsa ,jin dady wato abdullah na kuka yasa Humaid ciro nono ya d'aukoshi yasa masa a baki ,saida ya k'oshi sanan ya kwantar dashi ,hankalinshi na kan wanan littafin 6oyewa Khadija take k'ok'arin yi amma yafita k'arfi dan haka yayi nasarar k'wacewa ,duba bangon littafin yayi ganin anrubuta *TARAI RAYA* yasa Humaid duban Khadija data rufe fuska janyota yayi yace ”zomu karanta a'a tace ”bacci zanyi, Humaid ne yace ”to zomu kwanta chii daganan labarin ya sauya nafice da gudu 🕺. Yau kwanan Khadija arba'in dady 'yace gobe zata koma d'akinta momy ma tayarda dan duk wani taku na Humaid kwai kallonsu takeyi amma tasan yawan zuwanshi d'akin KhadijaLADIDIN KAUYE 59_60 Murna sukayi dukkan su biyun amma momy tana tausayawa Khadija ,kiran ta d'aki tayi da zuwanta tace ”Khadija zanja miki kunne akan biyewa Humaid 'da kikeyi kina sakar masa fuska over ,yakamata kigane jego kikeyi karfa 'azo asami matsala ,kinga shi namiji babu ruwansa kezai bari da d'awai niya ,sunkuyar da kai Khadija tayi tana nazarin maganar momy . Bayan gyara da magunguna datasha daga momy fatarta tayi kyau sosai ga wani shining datakeyi kanan yasha kitso da lalle ga halawa da momy tasa ayi mata kai abindai sai wanda yagani ,washe gari misalin 11:am Humaid ne yai sallama cikin shigar shi ta 'alfarma samun su momy yayi a parlor lokacin suka gama breakfast kasancewar ba da wuri sukeyi ba Khadija na d'akinta tana shirya kayanta tunda momy tace ”sai k'arfe 5:pm zasu tafi. Durk'usawa yai ya gaida momy ,amsawa tayi cike da kulawa ta mik'e tabar gurin sbda tasan abinda ya kawoshi ,😥ayya mom kin maida Humaid....🤐 kai tsaye d'akin khady ya shige yana yanga yana dariya yau dai gani ga baby na ,ta6e baki Khadija tayi tace ”to anfasa ai zaro ido Humaid yayi yace ”hhh dana sunkuceki mun wuce ai, dariya suka sa d'aukar yaran yayi yana yimusu adu'a bayan ya gama yace ”to tashi muje ,momy data ke shirin shigowa kiran Khadija takawo yaran ayi musu wanka ta tsinto maganar Humaid a sama , yana cewa tashi mutafi ,dubanshi tayi tace ” Humaid yaushe kazamo marar kunya ne ?eyye sunkuyar da kansa yayi dan yasan tabbas yayi laifi ,muryar Momy ce tadawo dashi daga hayyacin sa tace ”to yanzu ba da bane ka kular min da yarinya ,insha Allah Humaid yace daganan ya tashi yai gaba ,nasihoyi momy take yiwa Khadija sosai kuma yana shiga kunnen ta." misalin 5:pm Humaid ya dawo suka wuce shida Khadija ,momy ta sanya musu albarka haka ma dady , fatan alkhairi yayi musu . Da isar su suka tarar da komai an gyara gidan sai k'amshi yake zubawa ,yada zango Khadija tayi parlor kan d'aya daga cikin kujerun tayada zango ,Dady na hanunta shikuma Humaid Abba ya d'auko ,duka sunyi barci ,d'aukarsu yai d'aya bayan d'aya yaje ya kwantar dasu. Soyayya suke zubawa sosai Humaid yayi k'iba hakama Khadija sbda momy ta d'aukar mata mai aiki ,watan su Dady da Abba biyu ,Khadija ta tambayi Humaid zuwa k'auye ,baiyi yink'urin hanata ba sbda yasan ta dad'e bata je ba ,sunsa rana kasan cewar gobe weekend ne ,Khadija ce ta kira momy take gaya mata , momy tai farinciki tace ”mata subiyo tanan tanada sak'o ." Washe gari misalin k'arfe goma na safiya ,sun gama shiri kwana biyu Khadija zatayi Humaid kuma 'a ranar zai dawo ,kayanta wanda bata sawa ta loda a d'an ma dai_dai cin akwati suka shige mota ,kai tsaye gidan momy suka nufa ko zama basuyi ba suna gaisawa ta tambayi lpyr yaran ta gansu suka wuce ,tsara sosai Humaid yayiwa su Inna hauwa. Da isarsu garin Humaid ya kwashe da dariya harda tafawa yace ”boys ko inbaku labarin momynku ne yakuma sa dariya ,Khadija ta gano shi sarai ta sha murr taki kulashi sai da suka sukane ya kar6eta yaran ,da sallama suka shiga gidan su inna ,cikin fara'a inna tace ”wa'alaikumussalm oyoyo da masu jego ,Sahura dake d'akin inna tana kwaliya tace ”to wai suwaye sukazo ne naji kinta wani zumudi ,inna ce tace ”y'an binni ne sukazo su Humaidu ,da gudu Khadija ta fito tana washe hak'ora bakinnan yasha jan janbaki ga wani lafcecen Baki a girarta , Khadija ce ta bud'e baki tana cewa Sahura ina zakikai wanan tsayin ,dariya Sahura tayi tace ”akwai kayane in kwaso ¿a lokacinne Humaid yai mgna yace ”eh suna bayan mota da gudu ta fice tana tsalle Inna ce tace ”angirma ba 'asan angirma ba jibeta ,takusa kaiwa waje tajiyo inna tace ”ed'in ta murgud'a baki ,kwaso kayan takeyi kamar wata giwa sbda k'arfi da Allah ya zuba mata 'abin ba'a magana. Ibayan sun shiga d'aki 'inna ta kawo musu fura da nono ,kar6ar yaran tayi ta goya d'aya d'aya kuma yana hannunta ,tsarabar suka mik'awa inna dakuma sak'on momy ,da kayanda Khadija ta kawowa Sahura 'aiko sunyiurna ,mik'ewa Humaid yayi sbda lokacin sallah yayi na azhar Khadija ma sallar tayi daganan ta kwanta a katifar inna Humaid na dawowa yce zai koma kasancewar yanada ,aiyuka masu yawa . Washe gari Malam Adamu na yiwa su twins wasa yace ”ya Jalal lpy Lou ai matarsa ta aihu ma ,masha Allah mai aka samu cewar Adamu ,Khadija ce tace ”namiji ,sukad'an ta6a yira ,da wuri ta kwanta sbda da wuri zata koma Sahura ko tace ”zatabi Khadija babanta yaki yarda wai yayi mata miji karta biyewa samarin binni lol. Da komawarsu wani zazza6i ya lulu6e Khadija ,Humaid da yashigo yake tambayar yaushe ta dawo ya ganta kwance kamar wacce ta dad'e tana ciwo amai ne yake yunk'urin taso mata ,dagudu tayi toilet tana gamawa ta wanke fuskarta , Washe gari hospital suka nufa inda shi da kanshi ya aunata result ne ya fito ganin Khadija na d'auke da cikin wata d'aya yasashi zaro ido ,sbda 'a lokacin Dady da Abba watansu Uku ,magunguna ya had'o musu ita da yaran masu k'ara lafiya ita kuma tana yawan shan fruits farin ciki ya wanzu a wanan familyn sai dai muyi mata adu'ar Allah ya sauketa lpy . Takuce har kullum mom Islam nayi muku fatan alkairi,abinda nafad'a ba dai_dai ba Allah ka yafemana Allah ka shirya mana zuri'a alhamdulilh🥰🤝. 08141799224👍 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels