An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels *BILHAQQI* *Fikrah writer's association* *Fareedah Abdallah* *Na fara da sunan Allah mai ni, mai ku, mai kifaye😍🤲🏼* *Shimfid'a* A jihar Kaduna, a k'aramar hukumar Kajuru, a cikin k'auyen Rimau, a wani d'an k'aramin gida da yake bayan gari. K'arfe biyu da minti talatin da takwas na daren ranar juma'ar shekara dubu biyu da d'aya. Jikinsa na kyarma ya d'aga kafarsa ta dama da kyar ya tura k'ofar gidan ya bud'e. Hannayensa duk biyu suna dafe da 6angaren cikinsa na dama, duk da dafewar da yayi bai hana jini d'iddiga daga in da ya dafe ba. A hankali cike da karfin hali da jarumta ya ja k'afafunsa zuwa cikin gidan, idanunsa sai lumshewa suke yi suna bud'e wa dan tsananin galabaita da jigata. Daga yadda yake tafe yana harhad'a hanya zai baiyana matsanancin halin da yake ciki, idan yayi taku d'aya sai ya tsaya ya nisa tsawon wasu dak'iku kafin ya k'ara taku na biyu. Sai zurga-zurga take yi a d'an tsukukun tsakar gidan kamar mai yin safa da marwa, ta goya hannayenta duk biyu a baya. Idanunta suna ta tsiyayar da hawaye, fuskarta na baiyana matsanancin tashin hankalin da zuciyarta take ciki, daga yadda kirjinta yake bugawa akai-akai ta san akwai wani mummunan al'amari da yake shirin faruwa da ita. Wannan tsawon awoyin da ya d'auka bai shigo ba tana ji a jikinta ba lafiya bane. 'Tabbas ba lafiya bane. Ita ta san Mahaifinta Luka da d'an uwanta Zidane tun da dad'ewa sam basa nufinta da alkhairi. Balle kuma sun shigar da Pastor Nuhu cikin al'amarin, ta san sai abinda hali yayi. Shi yasa ko da sak'on kiran ya riske su tayi kokarin hana shi amma ya kafe kai da fata akan sai yaje. Fuskarsa cike da tattausan murmushi ya fice daga gidan yana d'aga mata hannu alamar sai ya dawo.' Ko kad'an bata ji tsoron tsalawar da dare yayi ba, idanunta na kan saitin kofar gidan tana jiran ta ga shigowarsa a cikin hasken farin watan da ya wadaci tsalar gidan tar a daren goma sha hudu. Lokacin da taga shigowarsa da saurin gaske kamar za ta kifa k'asa ta k'arasa gare shi, a hankali ta rik'o shi zuwa jikinta, da ita da shi sai kyarma suke yi kamar ana kad'a musu ganga. Da ta fahimci halin da yake ciki lokaci d'aya ta sake fashewa da kuka mai tsananin k'arfi tana kallon cikinsa in da ya dafe da hannayensa, tsananin tsoron abinda za ta gani yasa ta kasa cire hannayensa. Da tsananin k'arfin hali ya tattaro d'an sauran jarumtar da ya rage masa ya haske ta da tattausan murmushi, taga-taga suka yi dan nauyinshi ya fara rinjayarta kamar za su kifa da saurin gaske ya dafe bango da hannunsa na dama. Zame wa yayi ya zauna a k'asa bayansa jingine da bangon ita ma ya zaunar da ita a gefensa, har lokacin k'afafunsa sai rawa suke yi. A karo na biyu ya sake tattaro dauriyar da ta rage masa ya sakar mata murmushi. Sam ta kasa mayar masa da martani, kuka take yi bilhaqqi. Zuciyarta cike da tsanar irin wannan bak'in rayuwa da bak'ar al'ada ta garinsu da mutanen cikin garin. Ga wata bak'ar al'ada da suka d'orawa kansu tun zamanin iyaye da kakanni. Hannunsa ya sake d'agawa a kasalance ya shafi cikinta. Gabansa ne ya fad'i, ya dago kanta daga kirjinsa ya tsattsareta da kallon tuhuma da idanunsa da suke lumshewa suna bud'ewa. "In... In...ina ciki na?" Ya jefa mata tambayar yana harhad'a kalmomi cike da k'arfin hali. Da saurin gaske ta mik'e tsaye daga jikinshi ta nufi cikin d'an akurkin d'akin da sassarfa. Ba a jima ba ta fito hannunta dauke da wani abu da aka nannad'e cikin jallabiya ta maza. Ta ajiye a jikinsa sannan ta bud'e rufar gaba d'aya sai ga kyakkyawar jinjira fara sol ta baiyana. Kanta har zuwa gaban goshinta lullu6e da bakin gashi luf-luf irin na jarirai. Baccinta take yi hankalinta kwance. Kyarmar da jikinsa ke yi ne ya k'aru da sauri ya ruk'unkume jinjirar a k'irjinsa. A karo na farko tun faruwar cukurkudaddun al'amuran ya ji zubowar wasu zafafan hawaye daga idanunsa. Bai damu da ya share ba ya maida hankali kanta gaba daya ya k'ure ta da kallo mai baiyana neman k'arin bayani. "Dazuh... Bayan fitarka na haihu... Shi ne na yanke mata cibi na goge jinin jikinta ina jiran ka dawo..." Ta amsa cikin kuka mai tsanani. Murmushi yayi ya janyota jikinsa ya rungume ita da Babyn yana sauke ajiyar zuciya, zafafan hawaye ke fita daga idanunsa yana sauka a gadon bayanta. A karo na farko zuciyarsa ta karye, irin karyewar da bai ta6a tsammanin zuciyarsa zata yi ba a gurin fuskantar gaggarumin k'alubalen da yake gabansu tun bayan faruwar aurensa da Rebecca. 'An katse mishi hanzari... Tabbas an katse mishi hanzari... Shi Mustapha bai ta6a tsammanin k'arewar al'amarinsu a d'an k'ankanin lokaci haka ba' Ya aiyana hakan a zuciyarsa. A raunane ya fara magana kamar mai rad'a yana bubbuga kafad'unta alamun rarrashi. "Da gaskiya a cikin tsananin k'aunar da nake miki Rebecca... Da gaskiya a cikin alkawuran da na sha d'aukar miki Rebecca... Na tabbatar da gaskiya a cikin tsananin son da muke yi wa Junanmu. Na so kwarai in zame miki tsanin da zaki taka ki kai k'ololuwa ta jin dad'in rayuwa Rebecca... Amma da yake komai na al'amarin bawa yana faruwa ne bisa yarda da amincewar Ubanjina. Tun kafin a haife ni rubuce yake a cikin kundin Kaddarata. Tafiyar tamu ba mai tsawo bace ni da ke, cikin k'ank'anin lokaci har mun zo iyaka... Fata d'aya gare ni Rebecca. Alfarma d'aya nake nema a gurinki kafin in koma ga mahalicci na. Ki musulunta Rebecca, ko bayan ba raina ki musulunta. Tabbas da gaskiya a cikin Addinina..." Yana zuwa nan a maganarsa ya fara jan numfashi mai karfi sauri-sauri, can kuma sai ya sarke da wani irin tari mai k'arfi, tsawon lokaci yana yi ita kuma tana jera mishi sannu tana hawaye, yadda take ji a jikinta tabbas da tana da iko da ta amshi duk ciwukan da yake ji a jikinshi. Ita ta cancanci mutuwa ba shi ba, bai kamata ita ta aikata laifi a hukunta shi ba, wannan bak'in hukuncin nata ne ita kad'ai, Musty bai san komai ba janyo shi kawai tayi cikin al'amrin, salin-alin ya kamata ya su rabu ba tare da ya d'and'ani wani azaba ba. Kaki yayi ya tofar bayan tarin ya lafa mishi, ko da ta kalli abinda ya tofar ba komai bane sai wani dunkulallen jini hade da majina. Gabanta ya sake fadi, za ta yi magana ya riga ta, hannayensa duk biyu dafe da kirjinsa, a yadda yake ji yanzu kirjin har ya fi mishi azabar ciwo a bisa cikinsa, idanunsa suna kan jaririyar. "Ga amanar 'yata nan a hannunki. Duk runtsi duk wuya da juyin-juya hali irin na kaddara ina fata ki kasance tare da ita. Ki bata kyakkyawar tarbiyya, ki rene ta akan turbar addinina. Na rada mata suna BILHAQQI..." "Fad'a min ya zan zama musulma? Me zanyi dan in cika maka burinka?" Ta katse shi ba tare da ta jira ya aje numfashin maganarsa ba, da sanyin murya ta fadi hakan tana kallonshi. A zabure ya dago kai yana kallonta, zuciyarsa tumbatse da farinciki. Sai hamdala yake jerowa a fili cikin dauriya da cije baki. Har zai biya mata kalmar shahada sai kuma yayi shiru yana karantar yanayinta. "Kin tabbata bisa son ranki za ki musulunta ko kuwa dan ki faranta min rai ne?" "Duk biyun" Ta amsa kai tsaye tana kallonshi cikin hawaye. Har yayi shiru sai kuma ya karanta mata kalmar shahada ta maimaita. A take ya fara dariya tana taya shi da murmushi kamar anyi musu albishir din warwarewar duk matsalolin da suke gabansu, a daidai lokacin sai nepa suka kawo wuta, dukda kwan lantarki d'aya ne a tsakar gidan sai ya hadu da hasken farin wata ya sake haske cikin gidan. Yadda yake dariyar sai ta ga yayi masifar yi mata kyau, kamar a ranar ta fara ganinsa. Fuskarsa ta kamo da hannayenta duk biyu ta hade bakinsu wuri d'aya tana aika mishi da wasu zafafan sakonni masu wuyar fad'e a baki, lumshe idanu kawai yayi yana amsar sakon cike da nishadi, hannunsa d'aya dafe da kan diyarsa yana shafawa. Tsawon lokaci sannan ta sake shi ta shige cikin d'an akurkin d'akinsu da sauri. "Alhamdulillah, ko yanzu na koma ga Allah buri na ya cika." Ya fada a fili yana murmushi, a hankali ya warware jallabiyar da aka nad'e jinjirar a ciki, ashe akwai zani a ciki sai ya warware zanin. Sanyin da taji ya fara ratsata da yadda yake jujjuya ta yasa ta bud'e manyan idanunta ta fara callara kuka irinna jarirai, lokaci guda kuma ta fara karkata bakinta gefe daya tana cigaba da kuka, Da alamun abincinta take nema. "Reza zaki dauko min a ciki" Ya fada a hankali bayan ta fito daga dakin, hannayenta rike da zannuwanta guda biyu da dankwalinta. Cikin dakin ta koma ta dauko masa sabuwar reza ta kawo masa, bata tambaye shi me zaiyi da rezar ba sai ta tsugunna a gefensa tana kallonsa. Ya haske ta da murmushi, tsawon wasu dakiku yana kallonta har lokacin jinjira Bilhaqqi bata daina kuka ba. "Ki yi hakuri Ummu Bilhaqqi. Wannan abinda zanyi mata shi ne zai tabbatar da nasabarta, ko bayan raina duk tsawon zamani kiyi kokarin sada ta da masarautar Maru, ta jihar..." Kafin ya karasa maganar tari ya fara sarke shi, cikin sauri ya farke rezar ya tsaga gefen hagu na kirjin yarinyar, ta sake callara ihu kuwa cikin k'araji, runtse ido yayi ya sake tsagawa ya maida tsagun kamar tauraro, d'an gefen nononta kadan yayi tsagun, gurin sai tsattsafar jini yake yi. Ita kuwa Bilhaqqi kamar zata shid'e dan tsananin kukan azaba, ko da ya mikawa uwar ta saka mata nono a baki kin kar6a tayi ta cigaba da tsalla kuka. Sai kawai suka zuba mata ido, zukatansu fal da tausayin gudan jininsu, kamar za su fashe da kuka. Dan wani tunani tayi da sauri ta mika mishi ita bayan ta sake nad'e ta da zani ta nufi cikin kicin, yanar gizo-gixo ta yayo mai yawa ta zo ta manna ma yarinyar a gurin da yake zuban jinin, wani abin ban mamaki nan da nan jinin ya tsaya. Tana saka mata nono a baki ta kar6a da karfinta tana ja tana kuka-kuka, daga baya kuma sai ta ci gaba da sha tana sauke ajiyar zuciya har ta d'an samu nutsuwa kad'an. Sake nad'e ta tayi sosai ta maida ita cikin d'aki ta kwantar da ita. Ta dauko wani garin magani mai ruwan kwai a farin roba ta fito da shi ta hada da yanar gizo-gizo ta ajiye guri daya, a hankali ta daga rigar jikinsa sai ta ja da baya da sauri bayan ta kwallah k'ara a tsorace, yadda taga cakar wuka ya shiga sosai ta san ikon Allah ne kawai ya kawo Musty har yanzu yana raye. Kuka mai k'arfi ta sake fashewa da shi ta dawo kusa da shi da sauri tana rawar d'ari, ta bude robar maganin da ta had'a da yana ta zuba mishi sosai a gurin, ashe zaman da yayi jini duk ya 6ata mishi wando sosai, zuba maganin da ta yi a gurin kamar ta tado mishi da wani azababben ciwo ne, cikin kankanin lokaci har ya fara fita daga haiyacinsa. Idanunta sunyi jajur saboda tsananin tashin hankali, dankwalinta ta ninka sosai ta danne ciwon, fuskanta hawaye shabe-shabe da majina, ta dauki zaninta ta raba biyu ta daure mishi cikin tun daga gaba har baya, tsananin azaba yasa ya sume a gurin, bata lura da halin da yake ciki ba ta koma cikin daki ta goya yarinyar a hankali saboda ciwon da yake kirjinta, ga danyen cibin da ba a gasa ba sai d'aurewar da aka yi da zare, a hankali ta fara callara kuka ita kuma ta cigaba da jijjigata ta rufe ta da zani, idanunta ne suka sauka a kan agogon dakin, karfe uku da minti ashirin da d'aya, da sauri ta fice gurin Musty bayan wani tunani ya darsu a zuciyarta. "Musty... Musty... Lets go... Ya kamata mu bar kauyen nan yanzu, na san Bro Zidane bazai kyale mu ba..." Ta fada a hankali tana jijjiga shi alamar ya tashi, hankalinta ne ya k'ara tashi bayan ta lura da halin da yake ciki. "Musty..." Ta sake kiran sunanshi cikin kuka. Wata wawiyar bugawa kirjinta yayi lokacin da ta ji kamar hayaniyar matasa daga can nesa sun nufo gidansu. Ta mike tsaye da sauri, kofar gidan taje ta lek'a, tabbas hayaniya take jiyo wa, kunnenta ba k'arya yaji ba. Tayi diri-diri tayi gabas tayi yamma, ta rasa wak'ar farawa. Hannu biyu ta dora a kai ta fashe da kuka mai tsananin karfi, Bilhaqqi ma da bata san wace wainar ake toyawa ba ta sake callarewa da matsanancin kuka. Bata bi ta kan 'yar ba ta shige d'aki da sassarfa ta ciko kwano da ruwa ta zo ta antaya mishi tun daga kanshi har jikinshi, tai tsai da ranta cikin kuka tana fatan ya farfad'o, shiru kake ji bai farfad'o ba. Ta zazzaro ido a tsorace, ta daga hannunsa ta saki ya tafi yaraf, ta sake ja da baya a tsorace. Duk da bata san mutuwa ba ta fara tunanin Musty babu. Runtse idanu tayi da karfi, wani abu mai kama da dutse ya danne ta a kirjinta, idanunta suka soye, banda matsanancin zafi babu abinda suke mata, lokaci daya suka kada sukai jajur kamar jan gauta. Jin hayaniyar yana kara kusantowa daf da gidan yasa tayi saurin nufar 'yar karamar katangar da ta zagaye gidan, tana tafe tana waiwayen Mustafa ko zai motsa har ta kama katangar gidan ta tsallaka ta baya, duk ihun da Bilhaqqi take yi bata bi ta kanta ba ta fara gudu a cikin dajin kamar wacce zata kai takarda, burinta kawai ta isa gidan kafin lokaci ya kure mata, duk da wani sashe na zuciyarta yana tunatar da ita babban kuskuren da take niyyar tafkawa... ********* ********* Tun daga nesa tururin zafin da yake cin gidansu gagga-gagga yake buso mata. Tana tafe da sassarfa cikin fita haiyaci, idanunta a rufe suke saboda tsabar rud'ani, babu abinda take tunani sai Musty masoyinta da yake cikin gidan. Duk da tana jin hayaniyarsu a gurin alamun har lokacin basu tafi ba baisa ta fasa abinda tayi niyya ba, kofar gidan ta nufa gadan-gadan. In dai Mustynta yana ciki gara ta shiga su k'one tare, ta gaji da hayaniyar wannan duniyar mai cike da rud'ani, gara ta bi masoyinta su had'u a sabuwar rayuwa tare Zidane ya fara lura da ita kafin ta k'arasa cikin fushi da masifa ya karasa gare ta, ganin kamar bata lura da shi ba yasa shi sa kafafunshi ya kwashe ta ta zube a k'asa. Nan da nan sauran matasan suka zagaye ta hannayensu d'auke da muggan makamai, ta bugu kwarai a k'asan, kokarin tashi zaune take yi tana cije baki ya kamo yalwataccen gashin kanta da fadin da tayi yasa d'ankwalinta ya fice ya dankwafar da ita a kasa, bai bata damar cewa komai ba ya gaura mata wani gigitaccen mari da yasa ta sake zubewa a gurin, bakinta ya fashe dan tsananin azaba. Bata jira ya daga ta ba ta yunkura ta mike a zuciye tana kallonsa, fuskarta a daure murtuk. Tofar da miyau mai hade da jini tayi ta sake maida idanunta kansa cikin tsananin fushi. "Zidane ! Live me alone. Ina ruwanka da rayuwata? Me yasa ba za ka barni in sha iska mai sanyi ba? Me mijina yayi muku da za ku kashe shi? Idan bakwa son zamanmu a kauyen nan ku kore mu mana za mu tafi ba dawowa me yasa zaku kashe shi? Are we no brother and sister? Ko Daddy ba mahaifina bane? Idan..." Wani 6arin makauniya ya kai mata a ciki da yasa dole ta hadiye sauran maganganun, durkushewa tayi a gurin ta kwalla wani mahaukacin k'ara dan tsananin azaban da taji, nan da nan numfashinta ya fara fita sama-sama dole ta kwanta a kasa tana gurmususu. A wulakance cike da rashin tausayi ya ja ta kamar kayan wanki ya watsar da ita a gaban k'onannen gidan da har lokacin yana ci da wuta, kanta ya bugu da wani dutse, ta saki wani marayan k'ara a hankali kamar wacce aka shak'e wa mak'ogwaro. Tsugunawa yayi a kusa da ita yana kyalkyala dariya, ya damk'i gashin kanta da k'arfi ya daga ta zaune sukai ido da ido, ya watsa mata wani mummunar kallo kamar zai cinye ta danye. Saukar da kwayar idanunta kasa tayi a hankali tana ci gaba da maimaita kalmar shahadar da Musty ya biya mata kafin rasuwarsa, irin azabar da take ji a jikinta da zuciyarta ta tabbatar yau zata bi Mustafa, zata je inda ya je... Katse mata tunani yayi ya fara magana da turanci, (Duk al'ummar kauyen Christian ne, duk da hausawa suna shiga kauyen sosai dan yin cinikayya da sarin kayan abinci hausa bai zauna a bakinshi ba kamar yadda ya zauna a bakin Rebecca, dan ita ta fita daga kauyen, tayi rayuwa a mabanbantan garuruwa na hausawa) fuskarsa na baiyana tsananin tsanar da yake mata. "Rebecca my sister, let me tell u something, I hate u. Do you know why? Because of your mother. She is a witch, ita ta cinye grandfather, shi yasa aka k'ona ta da ranta a gaban duk mutanen kauyen nan, wannan tsanar da aka yi mata shi ne ya koma kanki.(Rebecca 'yaruwata, bari in fada miki wani abu, na tsane ki. Kin san dalili? Saboda mahaifiyarki. Ita mayya ce.)" A zafafe ta dago idanunta tana kallonshi, dukda bata san mahaifiyarta ba kuma bata rayu da ita ba ta tsani duk wani kalma na aibatawa a gare ta, duk mutanen kauyen in dai za su fadi magana a kan mahaifiyarta mummunan kalma suke fada amma ba'a ta6a fada mata mai muni da zafin wannan ba, wani karfi da ya ziyarci jikinta yasa ta daga hannu ta zabga mishi wani kakkarfar mari, ta k'ara da tofa mishi miyan bakinta mai hade da jini a mummunar fuskarsa. "How dare you da zaka fadi mummunar kalma a kan Mum dina?" Ta tambaye shi cikin tsawa kamar ba ita ne take shesshekar mutuwa ba. Wani mugun murmushi yayi da ta rasa gane ma'anarsa. Da yake kakkarfa ne marin da tayi mishi girgijewa yayi kawai ya kakka6e, abinda ya fi 6ata mishi rai miyan da ta tofa mishi, faskeken hannunshi yasa ya shafo miyan ya kalla yayi dariya, sai ya goge a jikin burgujejen gajeren wandon da yake sanye a jikinshi. "Zidane we are westing our time, kawai ka bamu guri mu daddatsa ta" Daya daga cikinsu ya fada cikin fushi. "Karka damu Markus, akwai abinda nake jira ne. Lokacin da na ganta dazu na ganta da katon cikin da ta kusa haihuwa, yanzu kuma ka ga babu cikin, thats mean ta haihu kenan. Ina kika kai Babyn? Bai kamata ki mutu ki barshi ba" Ya karasa maganar bayan ya damki gashin kanta ya fincika da k'arfi. "Ahhhh !" Ta fada cikin kuka ta rike hannunsa da ya rike gashin da hannayenta duk biyu. Ya sake kwashewa da dariya, ya kalle ta yana cije gefen bakinsa, cikin tsawa ya tambaye ta. "Ina kika kai Babyn?" "He is inside, yay... Yay... Yana ciki tare da babansa" Ta amsa cikin kuka, muryarta na rawa. "Karya kike yi Rebecca, Markus kuyi searching zagayen nan na tabbata duk inda ta kaishi bata yi nisa da shi ba. So nake in cire liver na shi inci a gaban Rebecca sannan in kashe ta tabi shegen mijinta" Yana gama fadin haka ya wancakalar da ita gefe d'aya ya bada umarnin sauran su d'aure ta, nan da nan kuwa suka yi mata wani mugun dauri mai kama da na huhun goro a jikin wani bishiyan mangwaro da yake nesa da gidan kad'an. Sama da mintuna goma sha biyar suna dube-dube amma basu samu jinjiran ba, dole suka koma suka sanar da Zidane basu samu yaron ba, kila da gaske take yi yaron yana ciki tare da Babansa. Haushi da takaici yasa ya ringa gaura mata mari kamar Allah ya aiko shi, nan da nan ya hada mata jini da majina, tana langa6e kawai a jikin bishiyan tana kallonshi tana jiran ajalinta ya sauka, numfashinta ma dakyar yake fita. Galan din da suka ciko da fetur ya dauko ya fara zazzaga mata tun daga tsakiyar kanta har zuwa sauran sassan jikinta, yana yi yana kyalkyala dariya kamar mahaukaci. "Zidane !!!" Aka kwalla mishi kira daga can nesa a lokacin da yake niyyar kyasta mata ashana, idanunta a lumshe tana kalmar shahada a zuciyarta. Da mamaki yake kallon wanda ya kwala mishi kiran har ya karasa kusa da su. "Jocob ?! Mene ya faru?" Wanda aka kira da Jocob yana ta sauke numfarfashi sauri-sauri saboda gudun da ya yi, ya nuna Rebecca da yatsarsa manuniya. "Pastor ya ce karku kashe ta, idan kun kashe ta akwai matsala, spirit na Alheri yana yawo a kauyen nan, in dai kun kashe Rebecca spirit din Alheri zai kashe kowa a kauyen nan." Wani dunkulallen bakin ciki ne ya kawo mishi naushi a kahon zuci, ya so kwarai a ce yau ya shafe babin Rebecca daga doron k'asa. Da ya kalle ta a zuciye sai yaga tana mishi wani murmushi mai kama da na rainin hankali. Ta motsa bakinta a hankali ta ce *"I'm a Muslim"* Tsabar rud'ani yasa ya sandare a tsaye a gurin, sauran abokan tafiyarsa kuwa suka fara kwance Rebecca dan cika umarnin Pastor Nuhu. [12/12, 11:58 PM] Bilhaqqi: *BILHAQQI* **** ***** **** Ya kalle ta da wani irin tattausan murmushi, da idanu mai cike da rahama irin wanda tun da aka haife ta bai ta6a kallonta da irinsa ba. "Rebecca yarinya na" Ya kira ta a tausashe, bai jira ta amsa ba ya cigaba da jero mata dad'ad'an tausasan kalamai kamar yadda Pastor ya umarce shi. "Rebecca ! i'm your father. Duk da kike gani kamar mun tsane ki muna son ki sosai, addinin cristianity shi ne asalin addininmu tun iyaye da kakanni. Kina ganin kin kyauta kenan ki bar addininki ki koma wani addini na k'arya? Addininmu shi ne addinin gaskiya, addinin da idan kin mutu Yeso zai daukake ki ki shiga paradise, ki hadu da mahaifiyarki Alheri. I'm sure ko Alheri yanzu haka da zaki ganta a kabarinta tana fushi da ke, saboda kin bar addininki na cristianity. Ki tuba, ki dawo cikin addininki, ki roki Almasihu ya yafe miki laifukan da kika yi mishi a baya, ki gina sabuwar rayuwa a gaba, Idan kika yi haka mu kuma zamu nuna miki soyayya, za mu baki mukami mai girma a church. Zidane ma yayi alkawari zai karbe ki as a luvly Sister, zai ji da ke, zai baki kulawa a duk inda kike a kauyen nan. Pls my dear, ki zàma yarinya mai biyayya, kar kibi zugan wancan shegen mijin naki da ya dad'e da mutuwa, daman bai dace da aurenki ba, he is a muslim, yana kan addinin 6ata ne, shiyasa ko gurin mutuwarsa yayi mummunan mutuwa. Ke kuwa da Yeso yake sonki da shiriya kinga ya tserar da ke, ki dawo kan addinin gaskiya ki bi maganganun littafi mai tsarki." Yana kaiwa nan a maganarsa yayi shiru yana nazarin yanayinta, zuciyarsa cike da fatan ta amince kuma ta yarda tayi duk abinda ya umarceta. Dukda ba kaunarta yake yi ba sam ba ya fata a ce ta sanadin 'yarshi aka samu gur6acewa a cikin tarihinsu na iyaye da kakanni, dan ko a garin suna daga cikin familyn da aka sansu da tsananin riko da addinin kirista. A hankali ta dago manyan idanunta da sukai luhu-luhu saboda kuka da tsananin wahala ta kalle shi, ya sake sakar mata wani tattausan murmushi da wafcecen bakinsa. Ta maida idanunta kan Zidane da yake tsaye a bayan mahaifinsa, idanunsa cike da matsanancin tsanan da yake mata amma yana kokarin boyewa. Fuskarsa dauke da murmushi mai hade da dariya. Gaftara-gaftaran hakoransa suka baiyana a waje kamar zai cinye ta d'anye, amma shi ala dole dariya yake mata. Ta saukar da idanunta sai suka sauka a kan farantin abincin da suka ajiye mata, farar shinkafa ce k'al da miyan stew, a gefe guda kuma aka zuba mata hadin ganyayyaki da tsokokin nama soyayye manya-manya "Idan kika bi abinda na ce miki irin wannan delicious din i promise har karshen rayuwarki shi zaki dinga ci..." "Daddy !" Ta katse shi cikin zafin rai, runtse ido tayi dan jin wani azababben zafi da ya ziyarci kumburarren bakinta saboda maganar da ta yi. Saida ta d'an numfasa bakin ya rage zafi ta daga kai ta kalle shi ido cikin ido, fuskarshi na baiyana matsanancin fargabar abinda zai fito daga bakinta, ita kuma idanunta ciccike da hawaye. "Idan zaku bani duk abinda kuke da shi bazan bar musulunci ba. Ni musulma ce, daga yau sunana ba Rebecca ba, sunana Khadeeja Mustapha..." Wani gigitaccen tsawa da ya daka mata dole ta hadiye sauran maganar a cikinta, ya daga hannu zai zabga mata mari ya ji an rike hannunsa. Cikin fushi da tsananin mamaki ya juya dan ganin mai karfin halin da ya hana shi tattaka Rebecca, sai yayi ido biyu da Pastor Nuhu. "Luka calm down. Ka manta abinda na fada maka?" Bai jira ya amsa ba ya ja daya daga cikin kujerar robobin da suka yi wa falon kawanya ya matsa kusa da Rebecca ya zauna. "Rebecca, dukda mahaifiyarki mayya ce har ta mutu bata bar addininta na Christianity ba. Kin amince zaki dawo cikin addininki?" Da kai ta amsa mishi alamun a'a, idanunta ciccike da hawaye. "Ok ! Thats good. Baza mu kashe ki ba. But zaki yi rayuwa ne tsakanin mutuwa da rayuwa har zuwa karshen rayuwarki. Dakin duhu da yake cikin church a nan zaki zauna har karshen rayuwarki. Kullum za mu baki abinci sau daya dan kar yunwa ta kashe ki. But duk lokacin da kika ji a ranki zaki iya dawowa addinjnki na Christianity za mu baki 'yanci." Daga haka bai sake ce mata komai ba garadan samari suka cicci6eta kamar kayan wanki suka kaita inda ya basu umarni. Zuciyar Daddy Luka da Zidane cike da matsanancin bakin ciki, sun so kwarai su samu damar karar da rayuwarta a wannan lokacin. ***** Sai da ta kalle ta da kyau ta tabbatar tana kallonta, ta yi wani murmushi mai kama da na mugunta, ta mike da tak'ama tinkis tinkis ta isa gaban kulolin abincin. Faranti ta dauka da luddayin diban abincin ta fara bude kulolin abincin, duk da tashin k'amshin da miyar taushen yake yi yamutsa fuska ta fara yi kamar ta shak'i wari. Wainar da yayi kyau shar kuma yayi tashi su6u su6u ta dauki guda biyu kacal ta zuba a farantin, maimakon ta dibi miyar kawai sai ta d'auki jug din tangaran da yake cike da had'in sassanyar jinja, kamar zata tsiyaya a kofi kawai sai ta saki Jug din da gangar ya fadi a k'asa. Nan take kuwa ya tarwatse. Ta saki wani k'ayataccen murmushi tana kallonta, ta yamutsa baki da fuska ta ce "Sai ki dau na annabawa, wannan ma ya bi ayarin 'yan uwansa. Ya riga mu gidan gaskiya..." "Kan uban can! Uban kuturu ma yayi kadan ballantana na makaho, idan kin isa Allah ya tsine min." Kamar kububuwa ta tura kujeran teburin cin abincin da take zaune ta mike a fusace ta zagaya ta gurinta. Cikin tsananin masifa ta cigaba da magana bakinta har yana tartsatsin miyau, ko tsoron ta taka fasasshen kwalbar Jug din bata yi. "Ke Suraiya bari in fada miki, shiru-shiru fa ba tsoro bane gudun magana ne. Na ga alamar sai mun goge raini tsakanina da ke a gidannan, ki bar gani na haka-haka idan zamu kwana mu yini muna ba hammata iska ko kwarzane baki isa ki yi min ba. Wallahi ko ki biya ni dubu biyar din jug dina ko inyi miki magagan dukan kawo wuk'a a gidan nan, in daki banza a banza in daki kud'i na..." "Ni... Wace ni in had'a jiki da kishiya? Baki da labarin hakan tsiya yake janyo wa? Ke dai da kike matsiyaciya kije can ki nemi dai-dai da ke amma ni na fi karfinki." Ta fada hankalinta a kwance, sai karkad'e-karkad'en kafad'u take yi kamar tana ji fitsari. Haushi, takaici, wani dunkulallen bakin ciki da suka hade guri daya suka kawo mata naushi a kahon zuci yasa tayi kukan kura ta mika hannu biyu da nufin ta cakumo Surayyan sai dai duk abinda zai faru ya faru. Da mugun sauri ta ja baya, hakan da tayi yasa ta taka wani fasasshen kwalba dukda akwai tattausan silifas a kafafunta saida ya huda takalmin ya ratsa kafafunta. "Ahhhhh !" Ta fada cikin jin zafi ta durkushe a gurin tana kokarin kamo kafar ta duba. Ba tare da ta lura ba ta sake dafa hannunta daya a kan wani kwalbar, kwalla kara ta yi ta dago a zuciye ta kalle ta. "Rabi baki da hankali ko? kina so ki hallakani ne?" kafin ta amsa mata ta ji shigowar motar mai gidan, kwafa tayi tana murmushin jin zafi, "Zaki gani, tabbas zaki biya wannan" Tana jin ya kashe motar ta bude baki da matsanancin sauri ta kwallah ihu mai tsananin karan da yake barazanar fasa dodon kunne. Ita kuwa Rabi sakin baki tayi tana kallon ikon Allah, dukda ta san Surayya gwana ce gurin makirci bata zaci abin nata ya kai haka ba, da ta kalli fuskarta sai taga har ta jika shi da ruwan hawaye. A daidai lokacin ya sanyo kai cikin falon da sassarfa bakinshi dauke da sallama, hankalinshi yana kan Surayya da take durkushe a kasa tana kuka, ko da Rabi ta nufe shi tana kwarkwasa da yi mishi sannu da zuwa sakar mata jaka da ledojin hannunshi kawai yayi bai kalle ta ba ya nufi Surayya. "Menene? me ya faru?" Yana ganin fasassun kwalaben yaja da baya da sauri "Subhanallahi, me ya faru haka?" Yayi tambayar yana kallon Rabi da manyan idanunsa masu cike da tuhuma. Ranta a ɓace, fuskarta a cunkushe, zuciyarta a ƙuntace da irin wannan cin mutuncin da yake gwada mata a gaban kishiyarta. Ta dai daure ta cije tayi ƙoƙarin ɓoye ɓacin ranta, ta buɗe baki zata yi magana Surayya ta riga ta fara magana cikin kuka "Sweetat wai fa kawai dan na ture mata jug ban sani ba ya fashe shi ne tace sai na biya ta. Na fara bata hakuri da gangar ta hankaɗa ni cikin fasassun kwalaben, ka ga har na huda ƙafa da tafin hannuna..." Ta ƙara fashewa da kuka tana nuna mishi hannun da yake ta tsattsafar jini. Mugun kallo ya watsa wa Rabi, a hankali cikin takatsantsan ya ƙarasa gurinta ya ɗaga ta tsaye, cikin hila ta langaɓe a jikinsa ta kwantar da kanta a ƙirjinsa. "Ki tabbatar kin gyara gurin nan kafin in kaita asibiti in dawo." Bai ƙara kallonta ba yaja ta a hankali suka nufi dakinta, minti biyu tsakani suka fito yana riƙe da ita a kafaɗunsa a hankali suka nufi hanyar fita daga falon. Ita kuwa poster tayi tana kallonsu fuskarta cike da hawaye, zuciyarta sai lugude take yi kamar zata faso ta fito fili. Sai da suka kusa fita daga falon ta waigo ta kashe mata ido ɗaya ta yi mata gwalo. Ta sake rukunkume shi tana faɗin "Wash ! Sweetat zafi" Nan ya sake tarairayota jikinsa yana jera mata sannu kaman zai ari baki. Tana jin tashin motarsa ta ɗora hannu biyu a kai ta fashe da ƙaƙƙarfan kuka, kamar mahaukaciya ta fara watsi da ƙananun kofunan da Surayya ta fasa jug dinsu. **** **** **** "Ke ! har kin isa ince ga abinda zanyi ki ce min ga abinda kike ga ya kamata inyi?" Tayi mata tambayar cikin mamaki tare da zazzare mata idanu. Bata ba ta damar kare kanta ba ta ci gaba da zazzaga mata ruwan masifa tana hakimce akan kujera mazaunin mutum biyu ta dora kafa daya kan daya. Sai jijjiga kafar take yi alamun jira take yi a taɓa ta tayi bindiga. "Ke wacece ? yaushe kika zo gidannan? to kashaidi na farko kuma na ƙarshe kar in sake yin magana a gidannan ki tsoma min zumɓutun bakinki, a gidannan da kika ganni zaman kaina nake yi. Ko Madam Mary bata isa ince ga abinda nake da ra'ayin yi ta hana ni ba balle ku ƙananun ƴan iska. Idan kunne ya ji rayuwarki ta tsira. Ina fatan kin fahimce ni?" Da sauri ta dinga ɗaga kai alamar ta ji, da rawar murya ta dinga jera mata kalaman ban hakuri kamar me fadanci. "Ki yi hakuri Bibi, Allah ya huci zuciyarki. Ki yafe ni, in Allah ya yarda bazan sake ba. Allah ya baki hakuri." "Dallah ɓace min da gani shashasha kawai, kina wani sussunkwi da kai siffar tsoffin munafukai." Ko kafin ta rufe baki ma har Nafsi ta kusa shigewa cikin ɗakinta. Ta bi ta da harara kamar idanunta zasu faɗo ƙasa, tsawon wasu daƙiƙu ta kauda kanta ta dawo da kallonta ga sauran mutanen cikin falon, ganin kowa yana harkar gabansa yasa ta ja wani dogon tsaki, ta yi ƙwafa, sannan ta maida hankalinta kan wayar da yake hannunta. Madam Mary da duk abinda yake faruwa tana zaune a gurin amma ta yi kamar bata a gurin, zuciyarta ne ya ƙara cika da tumbatsa da tsananin tsanar Bibi, amma da yake gogaggiyar ƴar duniya ce kuma mace mai tsananin wayau ko kaɗan bata bari hakan ya baiyana a fuskarta ba. Ta kalli wasu saffa-saffan ƴan mata da suke zaune su huɗu suna buga karta ta ce. "Rose ku je ku shirya mana lokacin fa yana tafiya." "To Madam !" Suka amsa cike da ladabi. Suka tattara katunan suka shige cikin wani ɗaki da Bello makeover yake cancaɗa musu kwalliya su dawo ƴan cararas kamar sabbin ƴan matan da aka ƙyanƙyaso daga leda. Madam ta maida hankalinta kan Bibi fuskarta yalwace fal da murmushi. "Umm na ce Bibi..." Ta ɗago a lalace tana kallon Madam ɗin, ganin ta kasa ci gaba da magana yasa ta ce "Ina jinki Madam" "Ina ga ya kamata ki daina faɗen irin wannan maganar a gaban yaran nan, kar girma na ya zube a gabansu." "Wace magana ke nan?" Tayi tambayar da alamun rashin ba maganar muhimmanci, sai ma ta cigaba da daddanna wayarta. "Cewar da kike yi ko ni ban isa in hana ki abinda kika yi niyya a gidannan b..." "ƙarya na faɗa ke nan?" Ta tambaye ta bayan ta ƙure ta da kallo. "A'a ! ba ƙarya kika faɗa ba" Ta amsa tana ɗage kafaɗu sama, alamun maganganun basu ɓata mata rai ba. Ko a jikinta wai an tsikari kakkausa. "Ayyo... na zaci ƙarya na yi yanzu in tabbatar miki da gaskiya" Tana gama faɗin haka ta yunƙura ta miƙe tsaye ta fara takawa kamar wahainiya, sassan jikinta suna motsawa a hankali kamar wahainiya. "Amma ni ma na shinshini ƙamshin gaskiya a maganar Nafsi, waƙar da kika zaɓa tsohon yayi ne da aka fara mantawa da shi, ga sabbin waƙoƙi nan zafafa da aka yi su a cikin kwanakin nan ina ga za su fi ɗaukar hankalin Mazaje..." "Na fasa casun, ki nemi wata a cikin ƴan matanki ta hau role ɗina" Tana gama faɗin haka ta fara cire sarƙoƙin gwalalan da aka maƙala mata a kyawawan ƙafafunta da kunnuwanta tana watsi da su a tsakar tangamemen falon, wani abin ban mamaki shi ne fuskarta cike yake fal da murmushi take aikata hakan. "Madam lokaci yayi fa, tunda babu african time ya kamata Bibi tana can yanzu. Yau an samu masu siyan tickets sosai jin Bibi ce zata yi rawa, mun daɗe bamu samu customers irin haka ba." Jamus ya faɗa wa Madam yana tsaye daga bakin ƙofa, ganin da yayi Madam bata amsa shi ba ta yi suman zaune yasa ya maida hankalinshi inda take kallo, sai a lokacin ya lura da abinda yake faruwa. "Bibi me yake faruwa ne haka? kar dai kice min yau ma yarfa mu zaki yi...?" "ƙwarai ! hakan nake nufi" Ta katse shi har lokacin bata daina murmushi ba. Da sauri ya shiga cikin falon ya tsaya kusa da Madam ya fara magana fuskarsa cike da damuwa. "Haba Bibi wannan ba girmanki bane fa. Ban sanki da magana biyu ba karki fara daga yau. Duk masu siyan tickets babu wanda ya siya ƙasa da dubu biyar saɓanin mu da mukai niyyar saidawa dubu biyu. Minista Yugi dubu hamsin ya ca ke mana kuɗin tickets dan kawai ya ji ke ce zaki yi rawa" Ya jero jimlolin cikin tashin hankali bakinshi yana karkarwa, shi kaɗai yasan lagwadar da yake sharɓa a gurin manyan Mazaje masu ƙumban susa duk ranar da Bibi tayi rawa, mutuwar sonta suke yi ita kuma tana yanƙwana su, da shi ne kawai idan aka yi kamun ƙafa ake samun damar ganawa da ita na ƴan wasu daƙiƙu ƙalilan. "Ba ka da damuwa Jamus, Rose zata hau matsayina. Ta iya duk wani girgiza da zanyi ƙila ma ta fini ƙwarewa. Ku shirya komai da Madam ni bari in shiga ciki." Tana gama maganar ta hurga mishi belt din da ta ɗaura a saman ɓingilin sket ɗin da yake jikinta shi kuma ya ca fe, santala-santalan cinyoyinta duk a waje ta fara hawa matattakalar benen tana ƴan waƙe-waƙenta zuciyarta cike da nishaɗi. Da sauri ya zunguri Madam Mary da take zaune kamar mutum-mutumi, ranta a ɓace, ya ƙale mata ido ɗaya yayi mata alamun ta yi wa Bibi magana in ba haka ba asara zasu yi. "Bibi...!" "Kar ki ce komai Madam. Kiyi shiru kawai." ta katse ta tana riƙe da ƙarfen benen. Ta juyo tana kallonsu amma bata sauko ba, a wannan lokacin fuskarta a ɗaure ne tamau, idanunta har sun fara canja launi. "Yau fa ina tabbatar miki Galar taki baza ta yi armashi ba, casun ma baza a yi ba. Rikici sosai za a yi, dan haka yi ta kanki tun kafin a yi kisa a gidanki" Bata ƙara kallonsu ba ta haye saman ta shige ɗakin Madam tayi kwance ɗai-ɗai a makeken gadon da ya mamayi fiye da rabin ɗakin. Wayarta ta janyo a zabure ta danna kiran wata lamba, sai huci take yi kamar kububuwa tana ta jan tsaki akai-akai. "Madam lokaci ya cik..." "Jamus dan Allah ka barni inji da abinda yake damuna. Baka ji abinda Bibi ta ce bane? kasan duk abinda tayi hasashen zai faru tabbas sai ya faru. Kaje ka sallami mutane kafin ta janyo mana wani bala'in." Ta ƙarasa maganar cikin tsawa da hargagi. "Yanzu Madam duk kuɗaɗen da muka karɓa..." "Ka wuce ka mayar musu da kuɗaɗensu ka sallami kowa na ce..." A daidai lokacin kuma kiran wayan da take yi ya shiga, aka ɗauka daga can ɓangaren, bata jira an fara magana ba ta fara magana cikin ɗimauta. "Oga ! Bibi tana so ta janyo min masifa. yanzunnan ka bani makarin duk wata masifa da yake shirin tunkaro Gala ta a yau..." "Ki bata haƙuri, ki saka ta dariya, ki bata farin ciki duk a lokaci ɗaya. Yanzunnan fa kafin lokaci ya ƙure miki." ƙit ya kashe wayar ba tare da ya sake saurarenta ba. 'Bibi ! Bibi !! Bibi !!!? Amma anyi ƴar iskar yarinya shaiɗaniya, wallahi in banda Oga ya tabbatar min haske na yana jingine da wannan yarinyar da tuni na daɗe da turɓuna hancinta a cikin ƙasa. amma ba komai, lokacinki ne yarinya, ki yi komai ba komai, akwai ranar ƙin dillanci." Ta ƙarasa zancen zucin da yin ƙwafa, ta ja wani ƙaramin tsaki, da sassarfa kuma sai ta fara hawa matattakalar benen dan zuwa gurin Bibi. "Oh ni Jamus ! ko me yasa Madam take tsoron Bibi?" Yayi maganar a fili yana ƙara leƙen Madam Mary da ta kusa ƙule wa ganinsa, ya mele baki guri ɗaya kamar mace, tunda ta haura a zafafen nan ya san rarrashinta zata je yi. Daman tunda ta kora shi da cewar yaje ya sallami mutanen da suka sai tickets ya maƙale a jikin tangamemen ƙofar falon yana tufka da warwara da tunanin waƙar farawa. 'Mutane sunfi ɗari da suka sai tickets da manyan kuɗaɗe ta ina zai fara mayar musu da kuɗaɗensu...' Hayaniyar da ya ji yana tashi sama-sama daga can cikin gurin rawar yasa ya zura da gudu dan ganin abinda yake faruwa, ƙirjinshi sai bugun tara-tara yake yi. Kiciɓis mugun gamo yayi da tantirin ɗan sara sukan nan Yusuf Guba da tawagarsa suna ta farfasa kwalaben giyan da aka jera a gurin karɓar kayan shaye-shaye suna jifa kan mai uwa da wabi. Mutane da ma'aikatan gurin sai guje-guje suke yi suna neman matsera, ga tangamemen ƙofar shiga gurin a buɗe amma ruɗu da ɗimauta yasa sai zagaye suke yi a guri ɗaya da ɓuya a ƙarƙashin kujeru sun kasa ficewa waje. Wata makekiyar fasasshiyar kwalba da aka kawo jifa tush kake ji a goshin Rose da ta buɗe ƴar ƙaramar ƙofar da suke shiga ta ciki ta yadda zasu ɓulla a gaban jama'a cikin tsinanniyar shigar kwata sutura rabi da kwata tsiraici, tana yaye ƙayataccen labulen da ya hana mutane ganin ƙofa ne ta samu nata rabon. "Ahhhh !" Ta ƙwalla wani gigitaccen ƙara ta zube a gurin a sume. ƴan matan da suke biye da ita a baya da mugun gudu suka koma ta ƙofar da suka zuwa cikin falon suna iface-iface. "Hey ! Ko a fito min da babban maƙiyi na Ɗan filulu da na samu labarin shigowarsa cikin galar nan minti talatin da suka wuce ko kuma in farke cikin kowa da yake nan gurin. Kowa ya tsaya a gurin da yake..!!" Ya ƙarasa maganar cikin wata gigitacciyat tsaww da ƙatuwar muryarsa mai kama da an tada babban injin markaɗe. Cike da mugun tsoro kowa ya ƙame a gurin da yake, masu raunanniyar zuciya kuwa nan take suka fara sakin fitsari a wando. Can na hangi Jamus da wasu mutane kwance cikin jini suna gurmususun azaba. Yadda Madam ta ga idanun Bibi a rufe amma tana far-far da su kamar mai shirin buɗe su yasa ta san aiki ya kwana, wani irin ƙaƙƙarfar numfashi take ja kamar mai sauke ajiyar zuciya yasa ta cije baki cikin takaici, wannan alama ce da yake nuna Bibi tayi mugun nisa a cikin barci kuma tashinta wani gaggarumin matsala ne. A zuciyarta tayi ƙwafa, ta kai wawura kamar zata shaƙo wuyan Bibi wani tunani mai walƙiya da ya gilma a zuciyarta yasa ta kaiwa filon da yake ajiye a gefen Bibi raruma. Ihun da Rose ta ƙwalla ta jiyo sama-sama dan haka ta fita a guje ko nauyin jikinta bata ji. "Nafsi, Liyat lafiya? me yake faruwa ne yau a gidan galar Madam?" Ta riƙe ƴan matan biyu tana tambayarsu a ruɗe. Ko kafin su amsa mata ta jiyo ƙwaƙƙarar muryar Yusuf Guba yana sauke musu zazzafar kashedi, daga bisani ta ji ƙarar watsewar kayayyaki ratsatsa a cikin gurin sannan aka karci bango da wani kakkaifar wuƙan da ko da bata gani ba ta tabbatar gayawa jini na wuce ne. Wani wawan sufa sukayi a tsorace sai ga su a bayan kushin sun dunƙule guri ɗaya suna makyarkyata. "Akwai waya a jikinku?" Madam ta tambayesu cikin raɗa tana kallon yadda tsabar gudu da rige-rige yasa ɗan kamfan jikin Nafsi ya baiyana. Kamar ƙadangaru suka ɗaga mata kai alamun babu. Aljihun ɗamammen wandon jikinta ta fara lalubawa cikin sa a kuwa ta ji wayarta a ciki, da sauri ta rarumo ta fara kiran lambar da duk hannunta ya sauka a kai, jimlar magana ɗaya kawai take nanatawa da an ɗauki wayar. "Taimako !!! daga gidan Galar Madam Mary ne. Ku kira mana ƴan sanda Yusuf Guba ya rutsa mu a ciki zai hallaka mu" *BILHAƘƘI* Cikin mintunan da basu wuce goma ba jiniyar motocin ƴan sanda har guda uku suka cika unguwar zame wando na garin Kachia local govt. Kai tsaye gidan Galar Madam Mary suka nufa da yake ba ɓoyayye bane a unguwar. A lokacin Yusuf Guba ya gama bincike duk mutanen cikin gurin amma bai samu Ɗan Filulu ko ɗaya daga cikin yaransa ba. "Duk ku kwanta a ƙar ɗaya bayan ɗaya zamu biku da yankan rago. Na san wani munafukin ne a cikinku ya faɗa masa ina cin hanyar zuwa shi yasa har ya samu nasarar samfewa ban kama shi ba, to a jikinku" Ya ƙarasa maganar cikin fushi da hargagi, nan ya ba yaransa umarni suka farfasa duk wasu sauran kayayyaki masu amfani a cikin gurin, suka kwashe kuɗaɗen da aka sai tickets, suna cikin yin wannan aika-aikar ne ƴan sanda suka yi musu dirar mikiya. Jin isowarsu yasa Madam ta fito da kwarin gwiwarta, ta haɗa zufa tayi sharkaf tana ta hawaye, Liyat kam har tana fitsari a wando dan tsananin tsorata, ita kuwa Nafsi cikinta ne ya juya kashi ya matse ta gam amma tsoro ya hana ta zuwa bayi. Sai sassanyar tusa take sakewa mai bala'in wari. Gaba ɗayansu sun gama fidda tsammani da rayuwar duniya ganin an ɗauki wani lokaci ba tare da ƴan sandan sun iso ba, kuma cajin wayar Madam ya ƙare. A ranta ta tsinewa Bibi yafi sau dubu dan ta san duk wannan bala'in da asaran ita ta janyo musu. "Officer ku tafi da su. Matsiyata ina zaune lafiya sun janyo min masifa. Ku ɗaure su har igiya tayi rara" Ta faɗa tana sauke numfarfashi haɗe da nuna yaran guba da aka samu nasarar cafkewa su biyar da yatsarta manuniya. "Hey ! Madam ki mana shiru. You are under arrest. Duk wannan fitinar ke kika janyo shi." Wani gardin ɗan sanda ya daka mata tsawa yana nuna mata bakin bindiga. Cikinta ne yayi wani mugun murɗawa nan da nan ta fara rawar ɗari, hannu biyu ta ɗaga sama alamar sallamawa ta ƙame ƙam guri ɗaya. Guba da yaransa huɗu sun samu nasarar tserewa ta bayan gidan dukda matsanancin tsawon da katangar gidan yake da shi. Ba sani ba sabo ƴan sandan suka tattara mutanen gurin tas har da su Madam Mary suka wuce da su ofishin ƴan sanda, wani abin mamaki har cikin gidan wasu daga cikin ƴan sandan suka duba amma basu ga Bibi ba. Daga police station aka tattara masu rauni a cikinsu aka wuce da su asibiti da rakiyar wasu daga cikin jami'an ƴan sanda, sauran masu lafiya kuwa gabaɗayansu aka watsa su a cell cikinsu har da Madam da ƴan matanta. ***** ***** ***** *MASARAUTAR BAUCI, ƘARƘASHIN MULKIN SARKI ABDULFATAH NA BIYU. ƁANGAREN UWARGIDANSA SARAUNIYA SAFARA'U, WACCE AKE YIWA INKIYAR FULANI TAKA.* "Allah ya ja da ranki Fulani. Uwarmu maganin kukanmu, baya goya marayu, kinyi taki kinyi ta yaro kinyi ta masu manyan kaya, mulki tako shi kika yi tun iyaye da kakanni ba haye kika yi ba. Jikar sarki, ƴar sarki, matar sarki, uwar sarkin gobe in sha Allahu..." A hankali kuma cike da ƙasaita da tsananin mulkin da ya ratsa jinin jikinta ta ɗan ɗaga hannunta kaɗan alamun kirarin ya isa haka. Nan da nan ta ɗauke wuta ɗif kamar anyi ruwa an ɗauke, kanta a ƙasa cike da tsabar ladabi da biyayya kamar zata kwanta mata. "An gaishe ki Jakadiya Babba. Fulani Taka ta amsa miki. Ke take saurare" Ɗaya daga cikin bayin da suke gurin ta faɗi hakan cikin ladabi da biyayya. Shirun da Jakadiya ta yi shi ya ganar da ita ganawar sirri Jakadiyar take so suyi. Kanta ta ɗaga a hankali ta kalli babbar baiwarta da take ɓare ayaba tana miƙa mata, inkiya ta yi mata da idanu mai nuna alamun su basu guri. "Umarninki abin cikawa ne a gare mu Fulani. An gama mai babbar kujera a zuciyar mai martaba. Fulani tana buƙatar a bata guri dan ta samu damar ganawa da Jakadiya." "A huta lafiya Fulani" Suka faɗa a tare sannan duk bayin suka miƙe tsaye suka fice daga falon. Ɗan miƙewa tayi daga kishingiɗar da tayi ta kalli Jakadiya da jajayen idanunta. "Ya ake ciki Jakadiya? an dace?" "Ƙwarai kuwa ranki ya daɗe. Ba dolenshi ya amsa kiran uwar kowa ba? Ai umarni ne. Ko da ranshi baya so dole ya amsa kira. Yanzu haka yana cikin ɗakina yana jiran umarninki." Jakadiya ta ƙarasa maganar cikin ƙasa-ƙasa da murya. "A shigo da shi cikin sirri" Ta faɗa a hankali cikin ƙasaita. Minti goma tsakani Jakadiya ta shigo da wata mace mai girman jiki da suffar samudawa. Ta sa wasu tsofaffin kaya riga da zani da suka koɗe sosai alamun sun gama cin duniya, fuskarta kaca-kaca da kwalliyar ƴan ƙauye. Ganin bata nan a falon yasa suka nufi cikin turakarta kai tsaye. Suna shiga cikin ɗakin Jakadiya ta maida babbar ƙofar ta datse da makulli, ko da ta waigo sai taga wannan matar har ta tuɓe kayan matan da yake jikinta sai ga sangamemen gardi ya baiyana. Ba tare da ɓata lokaci ba ya baje kayan aikinsa a tsakar ɗakin, ya kalli Fulani da idanunsa masu barazanar tsorata ƙaramin yaro. "Bani hannuwanki" Ya faɗa cikin tsawa yana gwalalo mata idanu. A tsorace ta kalli Jakadiya ita kuma ta ɗaga mata kai alamar ƙarfafa gwiwa. Jikinta na rawa ta miƙa mishi hannuwanta da suka sha zabban gwal da awarwarayen gwal shi kuma ya kama ya riƙe gam! Ya janyo ta da ƙarfi tayi taga-taga kamar zata faɗa masa jiki amma ta cije ta tsaya daf da shi. "Rufe idanunki" Ya sake faɗa cikin masifa. Tana runtsewa ya fara wasu irin surutai yana zagaye kayan tsafe-tsafensa da ita tana binshi a tsorace kamar raƙumi da akala idanunta a gimtse. "Naga tsananin haske a tare da ke. Burikanki zasu cika. Mulki na duniya zaki same ta ke da zuri'arki. Amma kina da babban ƙalubale, na ga wata zazzafar tauraruwa mai wutsiya da za ta baiyana a cikin haskenki. Muddin kika bari ta baiyana za ta tarwatsaki, za ki wulaƙanta, asirinki zai tonu, duk mugayen abubuwan da kika daɗe kina aikatawa zasu baiyana, za ki yi mummunar ƙarshe a masarautar nan" Yana gama faɗin haka ya angije ta baya kamar zata kifa da mugun sauri Jakadiya ta tallafe ta, ta haɗa zufa tayi sharkaf kamar wacce tayi gudun famfalaƙi. "Ta ya zan gane tauraruwar?" Ta tambaye shi a tsorace. "Duk sadda ta baiyana zaki ji alamun ita ce a jikinki, amma shawarar da zan baki ki fara nemanta tun kafin ita ta shigo yankin da kike, muddin kika bari ta shigo sai kinyi da gaske sannan zaki ci ta da yaƙi." Daga haka bai sake ce mata komai ba ya fara harhaɗa kayayyakin aikinsa a cikin jakar da ya ratayo a kafaɗa. Sulallan gwal masu yawan gaske ta sallame shi da su zuciyarta cike da matsanancin farinciki. Ya maida kayan matan jikinsa suka fice shi da Jakadiya Babba ba tare da ya bata ko tsinke tayi amfani da shi a matsayin magani ba. Da yake an san girman matsayinta na Babbar Jakadiyar sarki babu wanda yake tare ta ko tambayar da wa take tare? ko da zasu shigo tun daga can ƙofar fada duk ce ma masu gadi tayi ƴar'uwarta ce, kuma ta sanar da Fulani kafin ta bata damar zuwa da ita, shi yasa ko gurin fita duk inda ta wuce sai dai a miƙa musu gaisuwa cikin girmamawa. Sarauniya ta kalli Jakadiya bayan ta fitar da shi har can bayan gari ta koma cikin gidan sarki. "Ni fa na fara gajiya da gafara sa banga ƙaho ba, amma Jakadiya kina ga shi wannan ɗin zai iya...?" "A kul! kul Ranki ya daɗe. Hattara dai, ki iya bakinki. Ba a saka kokwanto ko shakka a cikin aikin Na shuri, idan kika yi haka ke da kanki zaki ɓata aikinki, ki zuba ido kawai ki yi kallon biyan buƙata." Wani dariya tayi na jin daɗi tana ƙara ƙarfafawa zuciyarta yarda da aikin sabon bokan da Jakadiya ta kawo mata. "Madallah da ke Jakadiya. Lallai kuwa idan buƙatarmu ta biya kamar yadda ya alƙarwarta mana baza mu taɓa mantawa da alkhairanki ba, zamu ɗaukaka darajarki a cikin gidannan, za ki kwankwaɗi romo da daɗin mulki irin wanda baki taɓa tsammani ba." "Godiya nake ranki ya daɗe, Allah ya ida nufi. Ubangiji ya ja kwananki da na Yarima Muzaffar sarkin gobe a Bauchi bi'izinillahi. Alkhairi a jininki yake, kyauta halinki ne. Maƙiyanki sune fadawanki kina tafe kina take su a baya." Kanta sai ƙara kumbura yake yi yana neman fashewa dan tsananin jin daɗin wannan kirarin na Jakadiya. Sai murmushi take yi tana huhhura hanci ita a dole ta fi su. "Jakadiya a duba min wane hali Haye take ciki, a tambayi Raliya da fatan aikin da muka ɗora ta a kai tana gudanar da shi yadda ya kamata?" "An gama Ranki ya daɗe" Ta miƙe da zafin nama ta nufi sashen Sarauniya Safiyya, Amaryar sarki Abdulfatah, abokiyar zaman Sarauniya Safara'u. ***** ***** ***** HAYIN RIGASA, LAYIN MAI DUBUN TSUMMA. 19/6/2012 Tun daga nesa Maman Ushe ta zubawa buhun da take hange daga can nesa idanu, idan ba gizo idanunta suke mata ba sai taga kamar motsi buhun yake yi. A hankali cike da takatsantsan da rashin tsoro ta sake gyara riƙon addar hannunta, ta ci gaba da tunkaran buhun gadan-gadan. Ko da ta ƙarasa sai taga tabbas motsi buhun yake yi, alamun wani abu mai rai ne a ciki. Da sauri ta tsuguna ta fara kici-kicin kwance bakin buhun dan ceto rayuwar abinda yake ciki, ta fi tunanin wata dabbar ce. Fara kyakkyawar yarinyar da tayi arba da ita an ɗaure bakinta tamau da tsumma an kulle idanunta yasa ta ja da baya a tsorace. "Innahu min sulaimanu wa innahu bismillahirrahmanirraheem" Ta faɗa da ƙarfi tana sake kallon yarinyar da har lokacin bata bar juye-juye ba. Nan ta ci gaba da jan duk addu'oin da suka zo bakinta tana tofawa da nufin idan aljana ce ma ta ɓace amma taga ko gezau bata yi ba. 'Ina ga mutum ce' Ta ayyana hakan a ranta sannan ta ƙarasa da sauri ta zaro ta daga cikin buhu ta fara ƙoƙarin kwance mugun ɗaurin da aka mata. Yarinyar ta riga ta galabaita dan haka ta sunkuceta da sauri ta saɓa ta a baya, a maimakon ta ƙarasa cikin daji dan ɗiban ganyayyakin magunguna kamar yadda ta saba sai ta koma cikin gari ta nufi gidansu. Wani matashi da bai wuce shekaru ashirin da biyu ba yana tsungunne yana wanki a tsakar gidan ya kalleta fuskarsa cike da fara'a bayan ya amsa sallamarta. "Maman Ushe barka da dawowa, yau dai kin dawo da wuri. Allah yasa kin samo min sassaƙen gamjin..." "Amma dai Musa baka ji daɗin halinka ba, kai kam anyi ɗan banzan yaro mai kunnen ƙashi. Ban hana ka shiga harkar ƴar mai ganyen nan ba?" Mahaifiyarshi Indo ta katse shi cikin masifa tana bankawa Maman Ushe harara kamar idanunta zasu faɗo ƙasa. Ita ma ba kanwar lasa bace, ba a taɓa ta ta ƙyale, ba a nuna mata yatsa bata karya ba. Amma da yake tana cikin wani sha'anin ko kallonsu bata yi ba, kai tsaye ɗakinta ta nufa ta kwantar da yarinyar a kan yaloluwar katifar da take shimfiɗe a tsakar ɗakin. Shi kuwa Musa tura baki yayi yana ƙunƙuni kamar ƙaramin yaro ya ci gaba da jiƙa-jiƙan wankin da yake yi, daman ba kayanshi bane, kayan Indo ne. Waje ta fito ta girgije tokan abin girkin gawayinta ta ɗora ruwan zafi dan ta yi ma yarinyar wanka. "Musa kallamu saƙonka bai samu ba, Allah cikin ikonsa ko cikin dajin sosai ban shiga ba nayi gam da katar da kyautar Allah. In taƙaice maka dai rabo na minallahi ƴa daga sama nutsattsiya..." "Ahayye nanaye. Ƴa dai Karimatu?" Indo ta katse ta da shewa dan tana ganin surutan banza kawai take yi, dan ta share wa kanta tantama kawai sai ta bankaɗe labulen ɗakin dan gane wa idanunta. "Na shiga uku ni ƴar gidan mutum biyu jikar mutum huɗu. Karimatu wani bala'in ne kika kwaso mana haka?" Tayi mata tambayar bayan ta ja da baya a tsorace ta ɗora hannunta bibbiyu a ƙirjinta tana zazzare idanu. Ita dai Maman Ushe bata ce komai ba ta cigaba da haɗa wuta tana ƴan waƙe-waƙenta zuciyarta cike da nishaɗi. Musa ma ɗauraye kumfar hannunsa yayi yaje zai shiga ɗakin dan ganewa idanunsa da sauri Indo ta janyo shi baya, ta fara zazzaga mishi bala'i ta inda take shiga ba ta nan take fita ba. "Dan ubanka baka da hankali ne? kana ganin yarinyar da kamannin aljanu kake ƙoƙarin shiga inda take? yi sauri ka kira Malam yazo ya kashe wannan gobarar dan wallahi bazan zauna da aljana a gida ɗaya ba" Ta ƙarasa maganar haɗe da fyalla mishi mari a ƙeya. "Wai ke Indo sai ki ringa dukan mutum kiyi ta mishi masifa bai yi miki komai ba." Ya faɗa cikin ƙunƙuni lokacin da ya kama hanyar ficewa daga gidan. Cikin minti talatin Maman Ushe tayi wa yarinyar wanka da ruwa mai tsananin zafi ta gargasa mata jiki. Duk inda ta bi a tsakar gidan Indo sake mata habaici da baƙaƙen maganganu take yi amma ita ko a jikinta wai an tsikari kakkausa, a ƙarshe ma Indon gajiya tayi ta shige ɗaki tana jiran isowar Malam. Ita kuwa ta ɗauki sabon kayan Ushe guda ɗaya da ta ajiye dan ta ringa tunawa da ita tasa mata, kayan suka zauna mata cas a jikinta kamar dan ita aka ɗinka su. Riga da sket na ƴan kantin da ta cire mata kuma ta tsoma a ruwan wankan ta wanke su tas ta shanya. Ragowar kamu ta ɗauko a ɗakinta ta dama kunu tasa suger kaɗan ta fara ba yarinyar da har lokacin bata gama farfaɗewa ta dawo cikin haiyacinta ba, tana rungume da ita a jikinta take bata kunun tana jifanta da murmushi lokaci bayan lokaci, ta karɓa ɗaya biyu kawai sai ta fara kwara amai. A dai-dai lokacin kuma mai gidansu Malam Tanimu ya sawo kai cikin gidan bakinsa ɗauke da sallama. Daga cikin ɗakinta ta amsa sallamar tana yi ma Malam sannu da zuwa, cike da ƙauna yake kallonta da yarinyar, bai matsanta da jin komai ba kawai sai ya ɗauki buta ya zagaya banɗaki. Ita kuwa ba tare da damuwa ba ta sako ragowar ruwan zafin ta ɗauraye mata jiki ta canza mata kaya, ta kwance kuɗi a haɓar zaninta taba Musa saƙon kayan shayi. Ta sha shayin kaɗan kafin wani wahalallen barci ya ɗauketa a jikin Maman Ushe, ganin haka ta kwantar da ita a kan katifar ta nufi gurin Malam da ya ce idan ta gama yana jiranta. Cikin nutsuwa da balagar iya furta tausasan kalamai ta gama kora musu bayanin duk yadda aka yi ta tsince ta, ta ƙara da cewa. "Waɗanda suka yasar da ita da alamun hallakata suka so suyi, domin irin mugun ɗaurin da suka yi mata ba na wasa bane. Amma da yake tana da sauran kwana da shan ruwa a gaba cikin hikima ta Ubangiji ya tserar da rayuwarta ta hanyar haɗani da ita. Da wannan nake roƙon alfarmarka Malam in dai babu damuwa dan girman Allah ka barni in riƙe ta, Allah ya sani a kallon farko da na yi mata naji nutsuwa, ƙauna, matsanancin tausayinta duk sun mamayi zuciyata. Idan kuma kana ganin akwai damuwa a riƙonta da zanyi sai in haƙura, umarninka abin bi ne a gurina." Tun ɗazu take yunƙurin yin magana Malam yake dakatar da ita, daga ƙarshe ma har sai da yayi mata ƙwaƙƙwaran jan kunne ta hanyar ce wa idan ta sake yunƙurin cewa uffan ba tare da karima ta gama magana ba zaiyi mugun saɓa mata, dole ta haɗiye maganganunta, domin kura ta san gidan mai babban sanda, Malam ɗin tsayayyen namiji ne a gidansa da sam baya ɗaukar wargi daga gurin ko waccensu. "Gaskiya bazai yiwu ba, taɓɗijan! ta ya daga tsinto yarinya a dawa baki san mutum ce ko aljana ce ta fito da siffar mutane ki ce zaki riƙe ta a gidannan? sam hakan bazai yuwu ba gaskiya. Ko dai ki san nayi da ita ko kuma ki maida ta inda kika ɗaukota..." "Saboda nan gidanki ne?" Ya katse ta yana bin ta da kallon mamaki. Ta zunmɓuro baki gaba kamar shantu, ranta a ɓace, zuciyarta a ƙuntace ta ce. "Amma Malam..." "Amma me? Aisha ki fita daga idona in rufe. Tun kafin in saɓa miki ki fita daga batun yarinyar nan" Ya faɗa yana nuna mata ƴar yatsarsa manuniya alamar gargaɗi. Sai kuma ya maida hankalinsa kan Karima ya cigaba da magana. "Allah yayi miki albarka Karima, haƙiƙa taimako ko da niyyar aikata shi kika yi Allah zai baki lada balle kuma ki aikata taimakon, Allah ya miki albarka." Cike da jin daɗi ta amsa da "Ameen Malam" Kyakkyawar fahimta ke a tsakaninta da mijinta, shi yasa ko da Indo take ta zage-zage da habaici bata maida kai ta kalle ta ba. Ta san in kowa a gidan zai ƙi fahimtarta Malam zai fahimceta, kuma zai goya mata baya ya ƙarfafa mata gwiwa idan har tana da gaskiya. "A halin yanzu dai bani da ikon yarje miki ki ci gaba da riƙon yarinyar nan har sai munje da ita gurin mai unguwa, duk abinda ya zartar a kanta dole zamu yi haƙuri. Domin ba abin mamaki bane yarinyar sato ta aka yi, iyayenta suna can cikin tashin hankali da damuwar rashin sanin inda take, kinga idan muka riƙe ta ba tare da cigiya ba munyi zalunci. Kin fahimce ni?" Ta ɗaga kai a sanyaye alamar eh ta fahimce shi. "Dan haka ki shirya bayan an idar da sallar magriba muje gidan mai unguwa, in Allah ya yarda ma zuwa lokacin ta dawo cikin haiyacinta, ƙila baza mu rasa bayanin inda iyayenta suke ba, dan naga a ƙiyasce zata iya kaiwa shekaru goma sha biyu." BILHAƘƘI "To Malam, duk yadda ka ce haka za a yi. Allah yasa mu dace." Ta faɗa a ladabce, kanta a ƙasa. "Ameen Karima" "Gaskiya Malam idan ka ce a gidannan za a riƙe tsintacciyar nan zaka haddasa mummunar bala'i da masifan da idan ta taso duk unguwar nan baza su iya kashe wa ba. Ehe ! haka kawai ina da ƙananun ƴaƴa mata baza a jajubo tsintacciya a haɗa su min da su ba, yo wa ya sani ma ko ƴar gaba da fatiha ce? Wallahi bazai yiwu ba, maganin kar a yi kar a kuskura a fara." "Kin gama?" Ya tambayeta yana kallonta da mamakin tsabar rashin kunyar da take mishi ganin yadda ta miƙe tana masifa tana girgiza kafaɗu a gabanshi. "Eh na gama, fatan za a bi abinda na ce dan a zauna lafiya." "Indo?" Ya kira ta yana sake gyara zamanshi. Bata amsa ba sai ta waiga ta kalle shi alamar tana jinshi. "Nan gidan waye?" "Gidanka ne gadon ƴaƴana nan gaba kaɗan" Ta amsa kai tsaye ba tare da damuwar abinda zaije ya zo ba. Ya miƙe tsaye ya tsaya daf da ita "Da kyau! To tunda sai can gaba ne gidan zai zama gadon ƴaƴan naki har yanzu yana matsayin gida na ne ko? to kashaidi na farko kuma na ƙarshe muddin kika ƙara kuskuren furta baki yarda a riƙe yarinyar nan a gidannan ba wallahi zaki koma gidan iyayenki. ƴaƴan da kike faƙaƙa da su kuma in tattarasu in ba Karima ta riƙe da tsintacciyar da kike magana, sai inga yadda zaki yi da ni" Yana gama faɗin haka ya zura takalmanshi ya ɗauki buta ya shige cikin bayi, ya barta a gurin tsaye baki buɗe kamar mutum-mutumi. Maman Ushe ma ɗakinta ta shige ta ƙyale ta a tsaye a gurin. Kamar yadda Malam ya faɗa suna idar da sallar magariba ya tasa ta a gaba ta goya yarinyar suka nufi gidan mai unguwa, da yake tafiyar babu nisa nan da nan suka isa gidan. "Mu ga yarinyar?" Mai unguwa Mukhtar ya faɗa bayan Malam Ali ya gama kora mishi bayanin duk yadda aka yi mai ɗakinsa ta tsintota, nan da nan Maman Ushe ta kwanceta daga baya ta riƙo ta a hannu, sai ta miƙawa Malam ita shi kuma yayi niyyar miƙa ta ga mai unguwa, shi kuma ya dallare ta da tocilan hannunshi. Kuka ta sanya mai ƙarfi ta maƙale a jikin Malam alamun ita baza ta je ba, sai ma fara ƙoƙarin zillewa a jikinsa za ta koma gurin Maman Ushe har lokacin bata daina kukan ba, da sauri ta karɓe ta tana rarrashinta. "Ma sha Allahu, ga yarinyar tubarkallah da ita. Ta faɗa muku sunanta ne?" "A'a! Tunda ta dawo cikin hayyacinta bata yi magana ba, sai dai kuka kamar yadda ka ga tana yi yanzu." Malam Ali ya bashi wannan bayanin. "Ubangiji Allah ya baiyana iyayenta" "Ameen ya Allah" Malam da Maman Ushe suka amsa addu'ar cikin haɗin baki. "Kuna sha'awar riƙe ta ne kafin Allah ya baiyana iyayenta ko zaku barta a nan gurin iyali na?" Ya sake tambayarsu yana kallon yadda tayi luf a jikin Maman Ushe kamar ƴar kyanwa. "Karimatu tayi niyyar riƙe ta tsakani da Allah har zuwa lokacin da iyayenta zasu bayyana." "To madallah! hakan yayi kyau, ba laifi." Ya amsa yana sauke ɓoyayyiyar ajiyar zuciya, domin tunda suka fara bayanin sun tsinto ƴa abinda ya fara tunani 'cikin matansa uku da bataliyar ƴaƴansu ashirin da ɗaya a wani ɗaki zai jefa ta? Zaman gidan nasa da ake yi ta kai ta kai ko wace uwa ƴaƴanta ta sani, 35% ya ɗauke a batun duk hidindimun da Allah ya ɗora mishi matan a dole suka ɗauki 65% na hidimarsu da ƴaƴansu, da wannan babban dalilin yasa sam bashi da ta cewa a gidanshi.' "Yanzu abinda za a yi ku koma da ita, gobe idan mai duka ya kaimu zan turo yaro mai ɗaukar hoto ya ɗauki hotonta, da hoton kayan da aka tsinceta da su. Ki kuma bashi taƙaitaccen bayani na dai-dai inda kika tsinto ta dan zamu bada cigiya ne a gidan radio da talabijin ko Allah zai sa a gano iyayenta. Dan Allah Malam Ali ku ji tsoron Allah gurin riƙonta, ku kwatanta adalci tsakaninta da ƴaƴan da kuka haifa, ita amana ce a gurinku." "In Allah ya yarda Yallaɓai, mun gode ƙwarai. Allah ya ƙara girma." Suka sake haɗe baki gurin yin godiya. Nan ta sake goyata a baya suka koma gida zukatansu fal da farin ciki, tsananin ƙaunar ƴar tsintuwar da Malam yake gani a idanun karima yasa shima ya ji yana ƙaunar ƴar, da gaske fa son mace yana sa namiji ya so duk abinda take so. Sun koma gida ana daf da kiran sallar isha'i, a lokacin Indo ta cika tayi tam, dan ranar girkinta ne. Sai tsaki take ja ƙasa ƙasa tana tsoron yin magana a kaɗa ta gidan tsoho. Maman Ushe ko kallonta bata yi ba ta shige cikin ɗakinta, zuciyarta cike da farin ciki. ****** ****** Sati uku tsakani duk cigiyar da ake yi ko wanda ya san iyayenta ba a samu ba balle iyayenta. A lokacin ta riga ta zama ƴar gida, ta sake sosai tana wasanninta a cikin yara, sai dai har lokacin bata magana, idan abu ya bata dariya sai ta yi, kuka ne bata yi ko da abu ya ɓata mata rai. "Amira zo muje ki yi alwala, kinji an kira sallar la'asar ko?" A hankali ta ɗago fararen idanunta ta kalle ta. sai kuma ta miƙe a hankali ta bi bayanta zuwa cikin gidan. Butoci biyu Maman Ushe ta ɗauko ƙarami da babba, ta bata ƙaramin ta fara alwala da babban. "Ki ringa yin kamar yadda nake yi kinji?" Ɗaga kai kawai ta yi alamar ta ji tana wasa da ruwan butan. Tunda ta lura daga alwala har sallah yarinyar bata iya ba a hankali take koya mata komai na dangane da addini, ƙananun abubuwa waɗanda ya kamata yara su sani, duk da bata iya magana amma hira take yi da ita kamar mai baki, kuma wani abin daɗi duk abinda tace mata tana fahimtar abinda take nufi, amsawa ne kawai bata iya yi. Wata-rana suna zaune ta haɗa mata tea tana firfita mata da ɗayan kofin "Amira ƴan matan Mama, ji da ke nake yi kamar tsoka ɗaya a miya, Allah ya buɗa min bakinki Malam ya kaiki makarantar islamiya da boko." Kamar daga sama ta ji ta ce "Ma...ma?" "Laaa... Alhadulillah ! Amira magana kika yi? Mama kika ce min? Allah na gode maka, sake faɗa inji me kika ce?" "Mama" Ta sake faɗa tana dariya. Dariyar farin ciki ta tuntsire da shi tana ta jera hamdala Amira tana taya ta da dariyar farin ciki. Tun daga ranar kuma kamar an buɗe mata bakin magana, a hankali cikin nutsuwa take ci gaba da iya maganar, duk abinda tayi niyyar faɗe sai dai a ji bakinta ya faɗa. Sati biyu tsakani Malam Ali ya kaita makarantar islamiyar da yaranshi suke zuwa, boko kuma Maman Ushe ta bashi kuɗi ta ce ya saka ta a makarantar private mai sauƙin kuɗi. ******* ******* Maman Ushe da Malam Ali mazauna unguwar mai dubun tsumma ne a cikin rigasa na garin kaduna. Dattijon magidanci managarci, mai wadatacciyar zuciya cike da rufin asiri, matanshi biyu da ƴaƴa takwas. Indo ita ce amarya kuma ita ce mai yara takwas ɗin, maza huɗu sune manya sai ƙananun mata su huɗu. Maman Ushe haihuwarta ɗaya ne da Malam Ali, shekarar yarinyar goma sha biyu Allah yayi mata rasuwa. Asalin sunan yarinyar Usaina ne amma Zainabu ƴar gidan Indo da suke sa'anni tun suna yara bata iya cewa Usaina ba sai take ce mata Ushe, a hankali Ushe ya zagaya unguwa sai mata suka fara ce ma Karima Maman Ushe. Duk da Malam Ali tsayayyen miji ne a gidansa hakan bai hana ƙananun rikice-rikice da kishi ke janyowa tsakanin matansa ba, amma mafiyawancin lokuta Indo ita ce fitinanniya mai yawan tsokanar faɗa da yawan kai ƙorafi, tun Malam bai gane ba har ya gane, shi yasa kullum yake yawan kwaɓe ta da cewa bata son zaman lafiya. Sana'ar Maman Ushe shi ne saida ganyayyaki da magungunan gargajiya, ita ma ta gaji wannan sana'ar ne a gurin mahaifinta. Mafiyawancin ganyayyaki ita mata suke biya kuɗi ta je daji ta ɗebo musu, kuma idan typhoid ya tasa yaro a gaba cikin hukunci na ubangiji idan ta haɗa magunguna sai ku ga an samu sauƙi, shi yasa har daga wasu unguwannin ana zuwa gurinta karɓar magani, da wannan dalilin yasa a sati tana shiga daji sau biyu, kamar namiji haka take sassaƙo magunguna da saiwoyi da ganyayyaki, kuma Allah yana tsare ta babu wani abin cutarwa da ya taɓa samunta. ****** ******* Shigowar cincirindon yara sanye da kayan makaranta da gudu cikin gidan suna haki da numfarfashi yasa Indo ta fara zaginsu tana zazzaga masifa. "Wani irin iskanci da rashin tarbiya ne haka za ku shigo mana gida babu ko sallama? iye? ku wuce ku fita tun kafin in ci mutuncinku" Basu saurareta ba kai tsaye suka nufi gurin Maman Ushe da take tsugunne a ƙofar ɗakinta tana warware himilin magungunan da ta ɗebo a daji. "Maman Ushe, Maman Ushe, Amira ta sumar da Raliyan mai daddawa a makaranta..." "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" Ta katse su a tsorace hannayenta duk biyu dafe da ƙirjinta, ta juyo tana kallonsu idanunta a bubbuɗe. "Me ya faru haka? garin yaya har ta sumar da ita?" Nan yaran duk suka fara ƙoƙarin bata labarin abinda ya faru, amma tsananin ruɗewa yasa ta kasa fahimtar me suke cewa, hijabinta kawai ta ja a jikin ƙofa ta bi bayan yaran zuwa makarantar bokon. "Hehehehe! Ba na faɗa ance ba haka ba? na farko kenan!" Indo ta faɗi hakan tana ƙyalƙyata dariya, dan gulma har tana sake leƙa su ta zauren gidan. kai tsaye ofishin shugaban makarantar ta nufa inda ta ga Amira an saka ta hawa mashin a tsakar rana, wani malami yana tsaye da zabgegiyar bulala a kusa da ita da ta ɗan tsuguna kaɗan sai ya zabga mata, idanunta sunyi jajur, babu ko ɗigon ƙwallah a idanunta. "Hajiya akwai damuwa fa, yarinyarki tana cikin babban matsala. A binciken da muka yi na dalilin rikicin mun gano yarinyarki ita take da gaskiya a rikicin da suka yi, amma matsalar da ake ciki shi ne har yanzu ita wancan yarinyar tana asibiti bata farfaɗo ba..." "Ina Malam Buharin? wallahi Allah bazai yiwu ba, ta ya kuna ji kuna gani za a sabauta min yarinya baku ɗauki mataki ba? ina ita wancan yarinyar? ku bani ita mu tafi asibitin ta yi duk mai yiwuwa ta farfaɗo min da yarinya idan ba haka ba wallahi a station zata kwana, idan ta kasheta ku tabbaci haƙiƙa ita sai na kashe ta." Mai Daddawa ne ta banka ƙofan ofis ɗin ta shiga tana sababi, ta inda take ba ta nan take fita ba. *BILHAƘƘI* "Haba Maman Raliya, ki yi haƙuri a bi komai a sannu mana..." "Naƙi inyi haƙurin, Karime na ce naƙi inyi haƙurin. Haka kawai za a kashe min ƴar marainiyar Allah a kan wata ƴar tsintuwa can tsintacciyar mage da bata mage? yo wa ya sani ma ko mayya kika tsinto aka jefa ta a cikin yaranmu zatai ta musu ɗauki ɗai-ɗai tana lamushewa?" Maman Ushe dai shiru tayi ba baka sai kunne, dan idan ta ce zata tanka to tabbas zasu yi ɓatacciya, ta ga abin ya fara zama da cin mutunci, ranta dai yayi mummunar ɓaci zuciyarta cike da mamakin Mai daddawan. Shugaban makaranta dai sai haƙuri yake bata amma ta ƙi saurarawa, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba tana ta zazzaga masifa kamar wata zararriya. Daga ƙarshe dai da yaga sulhu bazai yiwu a nan cikin makaranta kai tsaye asibitin aka ruguntsuma gaba ɗaya da iyayen yaran. Isarsu asibitin suka tarar da Raliya ta farfaɗo cikin wani mawuyacin hali, ƙwararrun likitoci biyu ne a kanta amma jini take ta fitarwa ta hanci ta baki, duk iya ƙoƙarinsu sun kasa tsayar da jinin sai zurkuɗa mata allurai ake yi. Hannu bibiyu mai daddawa ta ɗora a kai ta rushe da kuka mai tsananin ƙarfi, ita ma Maman Ushe kukan take yi zuciyarta cike da fata da addu'ar Allah ya aiko wa Raliya Manzon sauƙi da gaggawa, idan Raliya ta rasu bata san yadda zasu yi ba. Suna tsaye cirko-cirko har Malam ya je ya tarar da su a asibitin, a lokacin wani ƙanin Mai Daddawa ya ɗauko ɗan sanda, sai masifa suke yi suna faɗin lallai a tafi da Amira a kulle ta har sai Raliya ta farfaɗo, idan ta mutu kuwa itama a kashe ta. Amma ganin ƙanƙantan Amira yasa basu tafi da ita ko ina ba, ɗan sandan dai ya tsaya a gurin zuwa jimawa su ga abinda hali zaiyi. "Likita yaya?" Malam ya tambaya da sauri ganin likitan ya sake fitowa daga ɗakin da aka kwantar da Raliyan. "Alhamdulillahi, ku kwantar da hankalinku, mun samu jinin ya tsaya. Sai dai har yanzu bata gama dawowa cikin haiyacinta ba." Yana gama faɗin haka ya kama hanyar barin gurin. "Dr zamu iya shiga mu ganta?" Mai daddawa ta tambaya muryarta na rawa, idanunta sun tasa luhu-luhu saboda kuka. "Eh zaku iya shiga ku ganta, amma kar kuyi hayaniya sosai." Su Maman Ushe basu samu sauƙi da rangwamen hantaran da ake musu ba sai da Alhaji Kabiru mahaifin Mai daddawa ya isa gurin, kakan Raliya. Ya nuna matsanancin ɓacin rai akan abinda su Mai Daddawa suka yi. "Yau idan mutuwa Raliya tayi lokacinta ne yayi sanadi ne kawai wannan yarinyar ta zama, haba ! sai kace baku yarda da Allah ɗaya ba? ina imaninku ya tafi Habiba? To wannan yana daga cikin ƙaddara mara kyau, Ubangiji ya jarabce ki ne dan yaga cikar imaninki. Kinsan kuma yarda da ƙaddara mai kyau da mare kyau yana daga cikin rukunan imani. Kai kuma Ibrahim tsalo-tsalo da kai ka biye wa Yayarka har kana ɗauko jami'an tsaro, sai kaje ka sallame su. Habiba ca nake ke da Karime ƙawaye ne tun na yarinta? Tare kuka yi ƴanmatanci, dan da zumunci da kara Raliya ai ɗiyarta ce, bai kamata ku titsiye su har haka ba. Sam banji daɗin abinda kuka yi ba." Da ya gama faɗa ya ƙara ba su Malam haƙuri sosai kamar zai ari baki, sannan ya ce idan zasu gida suna iya tafiya, su kwantar da hankalinsu in Allah ya yarda komai zai zo da sauƙi. ****** ****** "Wallahi Abba ba laifi na bane, dan Allah kuyi haƙuri. Kullum Raliya sai sun tsokane ni ita da Jamila suna ce min tsintacciyar mage, to ban taɓa damuwa ba sam bana tanka musu, yau kawai zan wuce sai ta shaƙo min hijabi ta baya ta yar da ni a ƙasa yara sukai ta min dariya. Shi ne naji haushi da na tashi na tunkuɗeta ta faɗi a ƙasa, daga haka ban sake mata komai ba har na kusa fita daga makaranta aka kamo ni wai na sumar da ita." Ta ƙarasa bayanin cikin kuka, tana ta jan majina da sauke ajiyar zuciya. "Kai ! Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! ya Allah kai mana maganin masifa. Dan Allah dan Annabi Amirah ki kiyaye karki kuskura ki sake yin faɗa da ko wace yarinya kinji ko? ita kuma Jamila zan ɗauki mummunar mataki a kanta kinji ko?" "To Abba. Bazan sake ba" Saboda mugun dukan da ta sha sai da ta kwana biyu Maman Ushe tana gasa mata jiki da ruwan zafi sannan ta bi ta shafe mata jiki da Mantaleta, daga bisani kuma ta haɗa mata da maganin gaɓoɓi, cikin hukunci na Ubangiji sai ga shi ta warke tsab ta cigaba da zuwa makaranta, bayan matsanancin jan kunne da gargaɗin da aka yi mata. ****** ****** "Mal Murtana na zo karɓar canjin jiya ne" Nan da nan ya haɗe girar sama da ƙasa yayi murtuk, ya kalleta yana zazzare idanu alamun rashin gaskiya ƙuru-ƙuru. "Ke karki kawo min zancen banza da na wofi, wani canji zan baki bayan wanda kika amsa da magriba." "Ko dai ka manta ne Mal Murtala? baka bani canji na ba fa. Yanzu ma Mama ce ta turo ni in amsa in siyo mata shinkafa kwano ɗaya..." "Amirah idan baki bar nan ba wallahi zan mare ki, ni zaki kawo wa rainin wayau? sau nawa zan baki canjin ne? ku ji min yara da rashin gaskiya, cuta ta zaki yi? ko sata zaki min? ki bar nan tun kafin in saɓa miki." Yanda yake ta masifa da tada jijiyar wuya a ƙofar shagon yasa mutane suka fara taruwa, daman kuma an fito sallar la'asar kenan ba daɗewa. "Mal me yake faruwa ne? subhanallahi." Wani daga cikin mutanen ya fara tambayarsa ganin har Amirah ta fara kuka, kuma ta cije a ƙofar shagon tace baza ta tafi ba sai ya bata canjinta. "Tun jiya da yamma tazo da dubu ɗaya na bata suger rabin mudu, wallahi Mal Liman ba a yi minti ashirin ba ta dawo na bata canjin ɗari bakwai da hamsin..." "Wallahi ƙarya yake yi ban dawo na karɓi canji na ba." Ta katse shi da faɗin haka cikin ihun kuka. "Baki da tarbiya ko? da girma na ni nake miki ƙarya?" Ya tambaye ta cikin fushi da zuciya, ko kafin Liman da sauran jama'a su tanka ya ɗaga zabgegen hannunsa ya kai mata ƙaƙƙarfar mari da hannunsa na hagu. Cikin sa a kuwa ya same ta da kyau, ta daddage ta kwalla ihu a ɗimauce ta fara diri-diri a gurin tsananin ruɗewa sai da Liman ya riƙo ta. "Assha ! Assha !! haba Mal Murtala? duk da ta yi rashin kunya wannan marin da ka yi mata baka kyauta ba, ka shiga babin zalunci kuma..." "Allah ya isa, mugu, azzalumi. Wallahi sai Allah ya saka min, kuma sai ka bani canji na." Ya miƙa hannu zai sake cafko ta dan shi mutum ne mai tsananin zuciya da sauri Liman ya janye ta, sauran mutane suka fara ba Mal Murtala haƙuri shi kuma Liman ya ja ta zuwa gidansu, yana zuwa ƙofar gidan kuwa yayi kiciɓis da Malam Ali ya dawo kasuwa dan haka ya damƙa mishi ita bayan ya kora mishi bayanin duk abinda ya faru. Godiya sosai yayi wa Liman ya ja hannunta suka shige cikin gida ɓangaren dama na fuskarta sashin yatsu ruɗu-ruɗu, cike da tausayinta shi kuma Liman ya wuce gurin nashi harkokin. "Me ya faru Malam? Subhanallahi, Amirah? wa ya duke ki haka?" Maman Ushe ta saki butar hannunta tayi kan Amirah tana duba yadda fuskarta ya kumbura sosai lokaci ɗaya. A tsaitsaye a nan tsakar gidan ya kora mata bayanin abinda ya faru kamar yadda Liman ya faɗa mishi, ya kalli Amirah da take ta sauke ajiyar zuciyar kuka akai akai yace "Amirah ko dai kin karɓi canjin kin manta ne?" "Haba Malam ! idan da ta karɓo canjin ta ya zan sake tura ta ta karɓo min canjin? wallahi bata karɓa ba. Jiya tun da ta karɓo suger yace ba canji taje ta dawo tana nan tana aikin makarantar da aka bata, bata gama ba ma aka kira sallar magariba, kuma ka san ka hana aiken ƴaƴa mata bayan magriba. Yau kuma tun safe tana makaranta ko da ta dawo ta ci abinci bacci tayi sai yanzu da tayi sallah na ce ta amso min canjin. Kila dai shi ne ya manta ko kuma cuwa-cuwar da ya daɗe yana gwadawa ne yau zai gwada ta a kaina..." "Karime kenan ! Ba dai a shaidar ɗan yau. Kika sani ko ta karɓi canjin ta kashe a makaranta?" Indo ta faɗa haka tana dariyar ƙeta. "Ko cikin ƴaƴa dubu zanyi shaidar Amirah, banyi mata tarbiyar karɓar abu har ta kashe ba tare da ta tambaye ni ba." Tana ba ta wannan amsar ta ja hannunta suka shige ɗaki zuciyarta yana tuƙuƙi. Malam Ali buta ya ɗauka a ɗakin Indo ya shige bayi dan kuwa girkinta ne, ita kuwa Indo ta ja tsaki ta ci gaba da tankaɗen garin tuwo tana waƙa tana yaɓa habaici. ****** ****** Washe gari unguwar suka tashi da gaggarumin gobarar da ya lashe shagon Mal Murtala tas da duk wani kayan da yake ciki, tsinke ba a fita da shi ba. Kuma wani abin mamaki da tashin gobarar ko kaɗan bata shafi gidan da shagon yake ba balle har ta shafi sauran gidajen da suke makwaftaka da shagon. Da saurin gaske aka garzaya gidan Malam Murtala dan sanar da shi abinda yake faruwa sai aka tarar da iyalinshi cikin wani mugun tashin hankalin, yana kwance baisan halin da yake ciki ba aman jini kawai yake yi ta hanci ta baki. Nan kuma sai jimamin ya zama biyu, a gurguje aka idar da sallah sannan makwafta suka taimaka aka kwashe shi zuwa asibiti. BILHAƘƘI "Amirah ya jikin naki?" Maman Ushe ta tambaye ta tana ƙoƙarin zama kusa da ita, ta sa bayan hannunta ta taɓa goshinta taji har lokacin zafi rau. Ta ɗago idanunta da sukai mata nauyi a wahalce ta kalleta, ta buɗe baki da kyar ta ce "Mama kaina ciwo, nauyi yake min kamar zai faɗi." "Sannu Amirah, zai faɗa in Allah ya yarda, bari in sake shafa miki maganin." Da sauri ta ɗauko wani roba da ta mutsittsika ganyayyaki ta tsiyayi ruwan ta shafa mata a kai tun daga goshi har ƙeya, sai wash wash take yi ita kuma tana jera mata sannu kamar ta amshi ciwon kan ta maida shi jikinta, zuciyarta cike da matsanancin tausayinta. Tun jiya da daddare da zazzaɓi mai zafi ya rufe ta, ta haɗiye kwayar paracetamol tun cikin daren amma har lokacin bai faɗa ba, shi yasa ta juya yi mata magungunan da ta fi ƙwarewa na ganyayyaki. Tana gama shafe ta da magungunan ta kama kan ta karanta fatiha ƙafa bakwai ta tottofe ta da shi, cikin hukunci na Ubangiji kuwa nan da nan bacci mai nauyi ya kwashe ta, nishe-nishen da take yi yai sauƙi sosai, cikin ƙanƙanin lokaci ta fara haɗa zufa alamun zazzaɓin ya sauka, sai a lokacin hankalin Maman Ushe ya fara kwanciya. ***** ***** "Uhmmm! Wato Mal Hadi mutane suna raina girman Allah da buwayarsa. Ban san me yake damun mutanenmu ba da har suke iya danne gaskiya su take ta ƙiri-ƙiri kuma suyi ta zabgo rantsuwa a kan ƙarya. Jiya zaka sha mamaki idan kaga yadda Murtala ya fututtuke yana ta masifan cewa ya ba yarinyar nan canjinta. Da ta ce mishi ƙarya yake yi ya shammace mu ya zabga mata wani wawan mari da duk saida muka ji a jikinmu. Ita kuwa tai ta zabga mishi Allah ya isa da cewar sai Allah ya saka mata, tabbas da gaske ne Allah yana saurin amsa addu'ar wanda aka zalunta, sai dai wani lokacin sakaiyar tana daɗewa kafin baiyanarta. Idan kayi tunani dakyau ba komai ne yake ɗawainiya da Murtala ba face hakkin wannan yarinyar, yanzu fisabilillahi dubi yadda shagonshi ya ƙone ƙurmus an ce ko tsinke ba'a fitar da shi ba, shi kuma yana can ya yini a asibiti har yanzu da yammacinnan an tabbatar mana baisan wanene yake kanshi ba." "Wannan gaskiya ne, tabbas gaskiya ka faɗa Mal Liman. Kuma ka san shi Murtala an daɗe ana mishi raɗe-raɗin riƙe wa yara canji, tun jiyan na ji mata suna ta surutun shi ne baida gaskiya." "Assha ! ka ji irinta ba? Allah ya kyauta. Tsakanin arha da tsada kaɗan ne fa amma mutane sun gwammace su ringa ɗaɗɗakawa cikinsu haramun. Allah ya tsare mana imaninmu." "Ameen ya Allah" Da waɗannan surutan suka isa ƙofar gidajensu kasancewarsu maƙwaftan juna, nan suka rabu kowa ya shige gidansa. ***** ****** ***** Ta sake gyara zama sosai ta kalli Magajiya, hannunta na dama riƙe da haɓarta ta ji zancen da ya shige ta, fuskarta cike da matsanancin mamaki. "Magajiya anya da gaske kike yi? na sanki da shafawa fa idan kika ji sanyin waje." Nan take ta ɗaure fuska tayi murtuk, ta ƙara ƙanƙance mitsi-mitsin idanunta ta kalle ta cikin fushi. "Indo ke fa baki da mutunci, daɗi na da ke ƙwaƙwalwar kifi gare ki, shi yasa kullu yaumin a doɗe kike." Ita ma ɓata fuskar tayi, zagin ya shige ta, har ta buɗe baki zata yaɓa mata baƙaƙirin sai ta maze, da tayi wani tunani kuma sai ta saki fuskarta ta fara dariya. "Yi haƙuri aminiyas, wai dan girman Allah da gaske kike yi?" "Wallahi Allah da gaske nake miki, idan kuma kina tantama ki tashi muje gidan Harisatu ki tabbatar da gaskiyar zance na." "Ki bari dan Manzo?" Ta sake tambayarta cikin tantama zuciyarta cike taf da wasi-wasi da shakkar abinda Magajiyar ta faɗa mata. "Ah ! Zancen kike so Indo, ai kuma sai kiyi." Ta juya mata baya ta janyo matankaɗin da yake ajiye can gefe ɗaya ta fara rairaye tsakin masara. "Haba mana ƙawalli, ke da zaki rakani gidan mai zobian ya kuma za ki tatago aiki? yi haƙuri zo muje mu dawo tun da kince nan layin bayan ku ne, kamar na san zan tadda harkar arzikin nan yau duk ƴan kuɗaɗe na hansin hansin ne." "Yanzu na ji batu, haba! Da ana nuna miki ga Annabi kina kaucewa, dan ma kin samu za a taimaka miki? Na yi wa mutane hanya gurin mai zobia sunfi mata hamsin, duk cikinsu banji wacce ta kawo ƙorafin buƙata bata biya ba." Nan ta janyo wani tsumman gyale a cikin ɗaki ta yafa a kai suka kama hanyar ficewa daga gidan, sai kuma ta buɗe ƙaton muryarta tana magana da wacce suke zaman haya tare a gidan. "Kuluwa ga sanwar fate na nan a wuta ki dinga duba min kar ruwan ya ƙone, yanzu zan dawo. Idan Baban khalifa ya dawo a ce mishi na je amso daddawa maƙwafta." Bata jira amsawarta ba suka fice daga gidan, suna tafe tana ƙara ƙarfafawa Indo gwuiwar tabbas buƙatarta zata biya. "Ni fa daman ba komai yasa kika ga ina zizzillewa ba kinsan abinda baka yi farkon yinshi ba yana da wahalar farawa lokaci ɗaya, har ga Allah ban taɓa bin gidan malamai ba balle har in kai sunan Karime, a duk wani abu na zamantakewarmu baki na yake ƙwatata a gurinta da gurin Malam." "Kar ki damu Indo, ba saɓo fa zaki aikata ba. Na ji malamai da yawa suna faɗin babu laifi mace ta nemi taimako a kan miji ko kishiyarta matuƙar taga a zamantakewar nasu ana cutar da ita." "Uhmmm! Magajiya ke nan!" Ta sake faɗin haka zuciyarta cike da kokwanto da rashin yadda da abinda Magajiyan ta ce. Sun isa ƙofar gidan ta sake jan tunga ta tsaya hannayenta duk biyu riƙe da ƙugunta. "Amma Magajiya kina ganin idan na je zan samu maganin matsalolina?" Wani dogon tsaki ta ja ranta a ɓace, cikin faɗa ta fara magana "Kinga Indo in dai kina kokwanto zuciyarki bata bada gaskiya akan aikin mai zobia ba daga nan kawai ki wuce gidanki nima in wuce gida na, dan Billahillazi in akwai rashin yadda ko tayi miki aiki bazai ci ba." "Maganar bai kai haka ba, yi haƙuri mu je." Ta faɗa cikin sadaƙarwa da miƙa wuya. "Kin yadda?" "eh" "Kin miƙa wuya?" A wannan karon kai kawai ta gyaɗa kamar ƙadanguruwa, alamar da ke nuna ta miƙa wuya. "To ki sa a ranki wannan tsintacciyar magen ta gidanku kamar ta ƙara gaba cikin duniyar ne, ita kuma Karime ki ɗauketa a matsayin bandaro ko kuma ince koma bayan-baya a gurin Malam Ali. Babu wacce zai dinga gani da haske kamar fitila da tsananin ƙyalli kamar tauraruwa sai ke Indo. Bani hannunki nan" Ta damƙi hannunta da sauri suka faɗa gidan mai zobia da ƙarfin jiki da na zuciya. Da yake ita sananniya ce kuma tsohuwar customer ce da take kawo mata da yawa masu zuwa ayi musu aiki kai tsaye ɗakin mai zobian ta shiga dukda ta ga wasu mata kusan su takwas a zaune a benci suna zaman jiran layi ya zo kansu. Nan take kuwa aka ba Indo umarnin ta shiga ciki bayan an sallami matar da take cikin ɗakin. "Ki shiga, zan jira ki a nan. Kar kiji tsoron komai kiyi mata bayanin duk abinda kike buƙata." Magajiya ta faɗi hakan tana kallon Indo, sai da taga ta shiga cikin ɗakin sannan ta nemi guri can gefe guda ta zauna tana jiran fitowarta. Indo na shiga ta ga wani abin mamaki, bisa ga yadda Magajiya taita bata labarin Mai zobia a zatonta tsohuwar mace za ta gani, saɓanin tunaninta sai ta ga matashiyar mace ce, a ƙiyasce ma baza ta haura shekaru ashirin da biyar ba zuwa ashirin da bakwai. Kyakkyawa da ita, alamar hutu baiyane ƙarara a jikinta. Duk da baƙa ce amma baƙinta irin mai kyau ɗinnan ne da sheƙi, ɗakin kuma a gyare tsaf-tsaf babu tarkace, an malaye tsakar ɗakin da tattausan kafet ita kuma mai Zobia tana zaune a gefen wani ƙaramin gado na bono da wasu kwanduna a gabanta... "Ba a kalle-kalle a nan, idan baki da matsala kina iya fita ta gaba ta shigo" Mai Zobia ta faɗa bayan ta zabgawa Indo harara da juyayyun idanunta masu matuƙar ban tsoro. Ba shiri ta zube a gabanta tana kwasan gaisuwa, sai inda-inda take yi cikin ɗimauta. Hannu ta ɗaga mata alamar dakatarwa ba tare da ta amsa mata gaisuwar ba. "Ina Zobia?" Da saurin gaske ta warware ƙullin kuɗi a haɓar zaninta ta zaro gudan naira hamsin sabuwa fil ta miƙa mata. Da hannu biyu ta buɗe kuɗin ta ƙura ma hamsin ɗin idanu kamar tana karantar wani abu a ciki, minti biyu tsakani sai ta fara wani surutai shi ba hausa ba shi ba larabci ba. "Indo..? Ige ke tare da ke mi'am matsalarki?" Mai Zobia ta tambayi Indo da hausar zamfaranci. "Ƴar kishiya ta ita ce babban matsala ta a yanzu, ba ƴarta bace ta cikinta tsinto ta tayi a daji watanni huɗu da suka wuce, yarinyar nan ta zame min alaƙaƙai. Hankalin mijina gaba ɗaya ya koma kan wannan tsintacciyar magen ne da kishiyata. Idan zai yiwu ina so a kaɗa min wannan tsintacciyar can duniya, ta nisance mu, kar ta ƙara waiwayar rayuwarmu. Sannan ina so kishiyata ta zama koma baya a gurin mijinmu, ya zama a duniyar rayuwarshi babu wata mace da zai dinga gani da haske sai ni." Ko da ta gama saurarenta bata ce komai ba ta ci gaba da kallon kuɗin. Can kuma sai ta kalli Indo ta ƙara maida hankalinta kan kuɗin "Gaggarumin bala'i nih hango tahe gare ki da iyalinki Indo, ita wagga ɗiya da kika kahwa wa ƙahon zuƙa zata tahi ta barku kamar yadda kika biɗa, amma ba yanzu ba da sauran lokaci, sannan tabbas zata bar wawakeken giɓi ga rayuwarki. Abu ɗai zani ƙara miki ga wagga batu nawa shi ne ki kula sosai, wagga ɗiya da munka yi duba a kanta sosai bata nuhinki da komai sai masifa, kamar yadda a kullun kika nuhinta da sharri. Gobe ki sayi ƙwarya ta nono kindirmo ga bahillata da ɗaurin huhun goro ki aiko mana da shi. Tashi ki tai mun sallame ki." A hanyarsu ta komawa gida hankalinta in yayi dubu duk sun tashi, cikin ƙanƙanin lokaci idanunta suka kaɗa jajur! Karime ta sha tsinuwa da Allah ya isa ita da tun farko ta kasance sila ta ɓullowar shaiɗaniyar yarinyar cikin rayuwarsu. Magajiya dai sai dannarta take yi tana bata baki, da haka har suka ƙarasa bakin titi inda zata hau ƴar ƙumbula zuwa layinsu na mai dubun tsumma. "Indo kar dai ki manta da Kwaryar nonon da Huhun goron." Sai kuma tayi sasarai a tsaye "Magajiya? kin san kuwa da har na manta? to ni ina zan samu kuɗi? siyo kayan nan fa hidima ta wajen dubu biyu da ɗari biyar idan ma basu haura hakan ba..." "Wannan kuma ai matsalarki ce Indo, tunda kinci ladan kuturu ya zama dole kiyi masa aski. Idan ba haka in suka shanye miki hannu ko ƙafa wallahi babu ruwana, karki kuskura ki faɗi suna na. Ki bar ganin Mai zobia kamar yarinya manyan baƙaƙen aljanu tamanin da takwas ne a kanta, su suka buɗa mata idanu tana bada maganin duk wani ciwo na duniyar nan. Na ga kanki yana rawa dan haka ki kula, ni kinga tafiyata." Saboda haushi bata jira ta samu ƴar ƙumbular ba ta tsallaka titi ta koma gidanta, tana tafe a hanya tana ta mita kamar cin ƙwan makauniya. ****** ****** BAYAN KWANA HUƊU da faruwar al'amura a lokacin har Amirah ta ji sauƙi sosai ta fara zuwa makaranta. Ana tashinsu bata tsaya wasa ba ta nufo gida kai tsaye, turus tayi a tsaye tana kalle-kalle, yadda ta ga mata har huɗu a ɗakin Maman ga Malam tsaye a bakin ƙofar yana ta sharce gumi alamun hankalinsa a tashe yake shi ne abinda ya ɗaga mata hankali, ta sake kallonshi a tsorace jin da tayi ko sallamarta bai samu sararin amsawa ba. "Abba sannu da gida." Ta faɗi muryarta a sanyaye. "Yauwa Amirah, kin dawo? yi maza ki shiga ɗakin Indo ki canza kaya ki ci abinci kinji ko?" Yayi maganar da sanyin murya, akwai alamun ruɗu da ɗimauta a muryarsa. "To Abba" har ta kusa shiga ɗakin Indo sai kuma ta juyo ta kalle shi. "Mama bata dawo bane?" Kafin yayi magana Indo ta fito daga banɗaki hannunta riƙe da buta tana gantsare-gantsare da ciccije baki, hannunta na hagu riƙe da kwankwasonta. "Ke keh lafiya ko? kar ki kuskura ki shiga min ɗaki." Ta daka mata tsawa ta ƙarasa jikin ƙofar da sauri ta tare bakin ƙofar dan kar Amirah ta shiga cikin ɗakin. "Haba Indo, me yake damunki? baki ganin halin da Karime take ciki ne...?" "Dan Allah Malam dakata. Ba fa na ce taje daji kunama ta harbeta ba, kuma ma naga tun kafin tafiyarta jejen ai ta tanadi abincin da ita ƴar gwal ɗin zata ci idan ta dawo makaranta, dan haka ta wuce ɗakin wacce take zamanta ba ni ba" Wuf ta shige cikin ɗakinta tare da danno ƙofar ɗakin tana haki, hannu bibiyu ta sa ta dafe ƙirjinta zuciyarta cike fal da tunanin maganganun mai zobia. 'Wannan yarinyar tauraruwa ce mai wutsiya, ganinta sam ba alkhairi bane. A yadda take sam baza mu iya cutar da ita ba, amma idan muka bi ta jikin abokiyar zamanki muka raunata ta zaki iya samun cikar burinki na barin yarinyar cikin rayuwarki. Amma fa akwai matsala kafin faruwar hakan, wace irin matsala ce dai bamu sani ba.' Ba tare da wani zuzzurfar tunani ba ko hangen abinda zai je ya zo kawai ta ce ta amince, ko ma mai zai biyo baya a shirye take. 'Da kyau! ki sa ido ranar laraba, duk abinda ya faru ga abokiyar zamanki mune sila. Makarin aikinki shi ne ki nuna tausayinki ga Karime a ranar larabar, idan kika yi hakan duk aikinki zai lalace, idan hakan ya faru mu kuma babu hannunmu.' Duk waɗannan maganganun sun yi su ne ranar lahadi da ta je kai musu ƙwaryar nono da huhun goro kamar yadda aka umarce ta, tsabar masifa da son ganin burikanta sun cika ƙaramin gadon da yaranta suke kwana ta ɗaga ta saida a wulaƙance ga wata Dillaliya da take bayan layinsu. Tayi matuƙar ƙoƙari gurin kiyaye duk sharaɗin aka gindiya mata, ido kawai ta zuba tana jiran ganin biyan buƙata. Tun misalin ƙarfe goma da rabi da aka kwaso Maman Ushe ranga-ranga daga gona kunama ta harbe ta ko kallo na mutunci da tausayi bata yi mata ba duk kuwa da yadda take ta gurmususu tana salati da sallallami dan tsananin azaban da take ji, anyi allurai an bata magungunan gargajiya amma har lokacin dafin bai daina yawo a jikinta yana wahalar da ita ba. Yayyinta mata biyu ne a kanta sai manyan ƙawayenta guda biyu. Amirah ko da ta shiga ɗakin ta ga yadda jikin nata yake sai ta fasa kuka, ko abincin ta kasa ci, rakaɓewa tayi a tsakar gida tana kuka da addu'ar Allah ya ba Mama sauƙi. Suna cikin wannan halin aka aiko daga ƙofar gida wai ana sallama da Malam Ali, a firgice ya fita wajen da takalman ƙafarsa haɗin bauta. "Malam Ali saƙo ne daga gidan Hakimi, yace lallai a tafi da kai da wannan baƙuwar yarinyar ƴar wajenka wacce mai ɗakinka ta tsinto. Tuhumar *MAITA* har biyu ne a kanta, mun samu labarin duk wanda yayi faɗa da ita a cikin mawuyacin hali yake ƙarewa, a taƙaice ma dai yarinya Raliya da Mal Murtala suna can fadar Hakimi cikin mawuyacin hali sai kiran sunanta suke yi, shi yasa aka bamu umarni lallai mu tafi da kai, ita, da kuma ita mai ɗakin naka da ta tsinto ta. Domin sarkin Mayu na hayin Mal Bello ya tabbatar mana da cewa samun warakarsu Mal Murtala ya rataya ne a wuyan ita wannan tsintacciyar yarinya ta wajenka bayan ta tsallaka su." "Waw... wane irin magana kake min haka??? Amirar ce mayya? nawa take da har za a mata wannan ƙazafin?" Mal yayi maganar cikin rawar murya da ɗimaucewa, sai sharce gumi yake yi kamar ya haɗiyi gatari. Ko kafin ɗan aiken ya amsa mishi Inna Talatuwa ta fito a ruɗe tana hawaye "Malam ka zo ka ga halin da Yaya karime take ciki..." Da saurin gaske ta koma cikin gidan jin muryar Inna Asabe babbar yayarsu tana kwantsama salati mai tafe da ƙaƙƙarfar kuka. "Dan Allah ayi min afuwa, a halin da ake ciki yanzu bazan samu amsa kira ba. Mai ɗakina wacce ta tsinto wannan yarinyar da kake magana ita ce a cikin mawuyacin hali na rai kwakwai-kwakwai. Ita kuma yarinyar tana makarantar boko bata dawo ba" Bai jira amsawarshi ya faɗa cikin gidan da sauri dan ganin a wane hali ake ciki. 'Matsiyaciya, Annoba. Da zata mutu ma da an rage mugun iri...' Haɗa idanun da tayi da Amirah yasa gabanta ya buga dam! Duk da idanun yarinyar ciccike yake da ruwan hawaye hakan bai ɓoye canja launin da ƙwayoyin idanunta suka yi ba. Ta balla mata harara, da masifa ta ce "kallon me kike min haka?" Bata yi magana ba, tsawon wasu daƙiƙu suna musayar kallo sai kuma Amirah ta fara matsawa kusa da ita, daman suna tsaye ta can bayan banɗakin gidan ne inda aka shuka rama da zogale. Indo tana tsinkar rama ne ta jiyo salatin da Inna Asabe tayi shi ne take zancen zuci da fatan Maman Ushe ta mutu ba tare da sanin zancen zucinta ya fito fili ba. Idanunta sun rufe da tsananin son cikar burinta ba ta da masaniyar Amirah tana rakuɓe a can gefe guda inda in ba tsananin lura mutum yayi ba ba lallai ya ganta a gurin ba. Ta tsorata sosai da yadda ta ga yarinyar ta nufo ta amma sai ta maze ta tsaya ƙyam dan ta ga abinda zai faru, a duke dai ta san baza ta doku ba. "Fata kike yi Mama ta rasu ko? to ki zuba ruwa a ƙasa ki sha, burinki zai cika. Amma fa ke ma zaki mutu, idan kuma za ki zauna gadin duniyar ne to ga ki ga ta nan." Bata ƙara cewa komai a kan haka ba ta fice daga gurin, ta barta a tsaye ƙiƙam kamar wacce aka zare wa laka. Wani abin mamaki kuma sai jikinta yayi mugun sanyi, zuciyarta ya cika da wasu tunane-tunane marassa amfani. Tsananin tsoro da fargaba ya kama ta, ramar da bata ƙarasa tsinka ba kenan a saluɓe ta bar kwanon da ta fara zuba wanda ta tsinka a ciki ta kama hanyar komawa ɗakinta. Kamar ta leƙa ta ga halin da Karime ke ciki sai kuma ta fasa shiga ɗakin. Tana daf da shiga ɗakinta taci wani mugun tuntuɓe da dandamalin ƙofar ɗakinta ta kifa ciki, ƙwalla ihu tayi a gigice nan da nan jini ya ɓalle mata ta hanci ta baki. A wannan lokacin su Malam suna zagaye da Maman Ushe da jikinta ya saki gaba ɗaya, alamun mutuwa ya baiyana a jikinta ƙuru-ƙuru, da ganin haka ba ɓata lokaci Malam ya fara biya mata kalmar shahada tana maimaitawa a hankali cikin shaƙewar murya, matan kuma sai kuka suke yi zuciyarsu na ƙara cika da tsananin tsoron Allah, lallai mai rai ba a bakin komai yake ba. Tashin hankalin da suke ciki yasa ba wanda ya bi ta kan ihun da Indo tayi, daman duk suna cike da ita ganin yadda take nunawa a fili ciwon Maman Ushe bai dame ta ba. Ta biya kalmar shahada sau huɗu a na biyar mala'ikan mutuwa ya zare ranta. BILHAƘƘI Ta sake shan gabanshi cikin matsanancin kuka, zazzafar marin da ya kimtsa mata ma shanyewa tayi ta girgije kamar ba ita ya mara ba, ita kam ta gaji, ta kai maƙura gurin gajiya da mugayen halayensa da na ƴan'uwansa. Yau gara a yi ta ta ƙare a tsakaninsu. Ta cigaba da magana a hargitse cikin kuka. "Masa'udu ya kake so inyi maka ? so kake in dinga bauta maka? to bari ka ji, duk yadda kake ganina kamar wulaƙantacciya wacce bata da wani makomar da ta wuce ta inuwarka da nake a ƙarƙashinta bazan zauna da ƙuruciyata ka ƙarasa kashe min rayuwa ba. Kar ka manta na canza abubuwa da dama saboda kai, na rabu da ƴan uwana da iyaye na duk saboda makahon son da nake maka, na rabu da addinina na shigo naka saboda tsananin son da nake maka. Amma saboda kai butulu ne duk waɗannan sadaukarwar da nayi dan kai baka kalle su a matsayin abinda zaisa ka mutuntani ba? A shekarunmu na biyar da aure ban tsinci komai da zan iya ƙararwa na jin daɗin rayuwa ba a gurinka da azzaluman ƴanuwa da mahaifiyarka..." Kafin ta rufe baki ya kai mata wani ɓarin makauniya nan take tayi juyin masa a tsakar ɗakin. Ƙaƙƙarfar ihu ta ƙwalla a gigice dan tsananin azaba ta sake tashi gadan-gadan tayi kanshi da dambe tana yaƙushinshi haɗe da cizo duk ta inda ta samu dama, shi kuwa ya ware ƙwanji sai narkarta yake yi ta ko ina kamar Allah ne ya aiko shi, ita kuwa duk da tsananin azaban da jikinta ke karɓa sam bakinta yaƙi mutuwa kuma taƙi saduda, bama-baman zagi take ta ɗura mishi kamar tsohuwar bamagujiya tana jifanshi da duk muggan maganganun da suka zo bakinta. "Wallahi yau sai dai ka kashe ni ko in kashe ka, mugu, azzalumi, maciyin amana. Abinci ne bazan daina saidawa a bakin titi ba tunda dai baka ɗauke min nauyin da musulunci ya ɗora maka ba. Musuluncinka bai ƙare ka da komai ba sai zalunci da butulci, in Allah ya yarda ko ka mutu wuta ne makomarka..." Saukar ƙatuwar sanda ta ji a gadon bayanta ba zato ba tsammani, nan ta gantsare ta sake ƙwalla ihu ta juya a gigice dan ganin wanda ya aikata mata haka, ido biyu sukai da sarkuwarta Baba Lauratu, zubewa tayi a tsakar ɗakin zuciyarta a ƙuntace ta sake fashewa da wani matsiyacin kuka tana sauraren baƙaƙen maganganun da take yaɓa mata. "Muguwa mai baƙar aniya, tubabbiyar banza da wofi. Bakinki ya sari ɗanyen kashi azzaluma, in Allah ya yarda ke ce zaki ƙarke a jahannama a wutar ma kina can ƙasan ƙoli, kafira kawai." Ta maida kallonta kanshi cikin masifa tana nuna shi da tsinin sandar hannunta ta ci gaba da zazzaga ta inda take shiga ba ta nan take fita ba. "Masa'udu indai na isa da kai kuma ka haifu a cikina a yanzunnan ba sai anjima ba ka sau auren wannan tubabbiyar, kuma saki uku nake so kayi mata ta yadda baza ta sake maƙale maka ba, idan ba haka ba yanzunnan zan ɗaga maka nono Wallahi." Da ita da take kukan, da shi da yake tsaye kamar zaki dan tsananin fusata yana ta sauke numfashi ɗif suka yi kamar ruwa ya cinye su, a take kuma sai jikinshi yayi mugun sanyi, nadama mai tsananin gaske ya rufe shi. Sai kuma zuciyarsa ta cilla da shi tunanin shekaru biyar baya da ya maƙalƙalewa Mary Barnabas har ya samu nasarar cusa mata matsananciyar soyayyarsa a duk wani lungu da saƙo na zuciyarsa, tun a lokacin ita Mary so tayi su ringa watsewarsu ba tare da zancen aure ya shigo ba a matsayinsa na musulmi ita kuma mabiyiyar addinin kirista amma sam yaƙi yarda da hakan. Sau ɗaya ya taɓa gwada yunƙurin kusantarta amma tunda ya fahimci ita budurwa ce dal a leda ya fasa mugun nufinshi, ya sha tsananin wahala kafin ya iya yaƙin shaiɗan ɗin da yake ta ƙawata masa ya keta rigar mutuncinta. Daga lokacin iyakar rungume-rungume da tsotse ke shiga tsakaninsu ba ya taɓa bari su keta iyaka. Daga baya kuma sai ya fara kwaɗaita mata batun su yi aure, tun tana noƙewa tana turjewa har dai ta amince da gaske zata aure shi, amma da sharaɗin bazai tursasata shiga addininsa ba, ya ce ya yarda. Ko da ya jewa da iyayensa batun aurenta sai sukayi tsalle suka dire kan cewar sam bai isa ya kawo musu Ahlul kitabi cikin zuri'arsu ba. A nata ɓangaren ita ma mahaifiyarta tace sam bazata auri musulmi ba, akan maganar aurennan sau goma sha biyar ana tale ta a zaneta a coci amma duk ta jure ta shanye tace in ba Masa'udu ba sai rijiya mai kwalabe. Da taga ma bai dawo garin Kacia ba daga zuwa sanar da iyayensa zaunannun hayin rigasa kawai sai ta tattara ƴan kayanta ta bar ƙannenta biyu mata da mahaifiyarta dan mahaifinta Barnabas ya dade da mutuwa ta gudu gurinsa, daman tana da cikakken adireshinsu shi da abokinsa Umar da suke zuwa cirani a garin kacia. Ko da taji halin da yake ciki da iyayensa sai tace in dai musulunta zaisa iyayensa su amince ya aureta ta amince za ta musulunta, amma tana so ya ɗaukar mata alƙawarin duk runtsi, duk wuya, komai wahala da juyin juya hali na rayuwa kar ya taɓa wulaƙanta ta. Ba tare da tunanin komai ba ya ɗau mata wannan alƙawarin sannan ya ƙara da cewar duk wani daɗi na duniya zaiyi iya ƙoƙarinsa wajen jiyar da ita ko da shi zai ƙuntata kansa da tasa rayuwar. Ba tare da ɓata lokacin komai ba suka je gurin wani limami ya musuluntar da ita, ko da suka yi mishi bayanin halin da suke ciki ya tausaya musu ƙwarai, bayan kwana biyu ya ɗaura musu aure akan sadaki naira dubu goma bisa shaidar abokan mahaifinsa biyu ba tare da sani ko yardar mahaifiyarsa da ƴan uwansa ba. Jagora yayi wa Limamin har gida yayi wa mahaifiyarsa zazzafar nasiha, ya jawo mata ayoyi da hadithai masu nuni akan cikar imani ta hanyar yarda da ƙaddara mai kyau da mare kyau, ya nusar da ita ɗimbin lada da romon da bawa yake sharɓa a wajen ubangiji idan yayi sanadiyyar musuluntan mutum ɗaya a ƙarshe ya dire da faɗa mata ɗaura auren Mary wacce musuluntan da tayi ya maida ita Maryam da Masa'udu ƙwallin ƙwal ɗin yaronta namiji a cikin ƴanuwansa mata bakwai, yaron da ta gama tattalinsa da ɗora burin duniya a kansa tana ganin nan gaba kaɗan shi ne zai zama Ɗangwaten hayin rigasa gaba ɗaya. Nan Liman ya cigaba da ƴan nasihohinsa da fatan alkhairi wa auren amma abinda bai sani ba tun da ya faɗi tabbatuwar auren ta daina fahimtar abinda yake cewa har ya kwashi tsumman ƙafufunsa ya ƙara gaba. Kamar gaske ta basu ɗaki guda a cikin gidan da cewar su zauna amma zuciyarta cike da alwashi kala daban-daban na yiwa tubabbiyar gashin ƙuma a tafin hannu har sai azaba yasa ta bar gidan da ƙafafunta. Tabbas tayi nasarar hakan, a hankali da zuga da makirci da sharrin abinda bata yi ba tace ta yi saida ta sa Maryam ta fice daga zuciyar Masa'udu, duk abinda yayi niyyar yi dan ya kyautata mata sai Baba lauratu tayi fiti-fiti ta hana, ta ƙara da ce masa ita mace ba a gwada mata tsananin daɗi in ba haka ba sai ta lalace, balle ma ita tubabbiya ai sun saba da wahala, matan kirista su suke noma su ciyar da mazajensu. A hankali har ya sangarce ya ci gaba da neman matan banza a waje dukda kuwa tsananin ladabi da biyayyar da Maryam take masa, tana iya ƙoƙarinta gurin shanye duk wulaƙancin da suke mata bango da bango, ba ga uwar ba ba ga ƴan'uwansa mata da shi kansa ba. Sana'a iri-iri tayi dan ta rufawa kanta asiri, gorin haihuwa kuwa da yana fitowa a jiki da ya fito mata dan tsananin gorin da suke mata, amma a gefe guda Baba Lauratu murna take yi da rashin haihuwar dan ta ce Allah ya kyauta ta haɗa jini da tubabbiya. A gurinsa ta ƙara gogewa da hausa ƙwarai kamar jakar kano, daman kuma ko a kacia suna cikin hausawa ne, tana ji sosai, a yanzu kam idan ba faɗa aka yi ba babu wanda zaice ba asalin bahaushiya ba ce. A lokuta da dama idan ta zauna tana kuka tana yawan tunanin wai dama haka musulunci da musulmai suke? Ita dai bata tsinci komai a musuluncin ba sai baƙin ciki da takaici da ɗumbin da na sanin shiga cikinsa. (Wa'iyazu billah. Ta haɗu da baragurbin musulmai😢😢) Abinda ya zafafa rikicinsu a kwanakin shi ne saida shinkafa da miya da ta fara yi a bakin titi kusa da shagon wani mai saida miniras, Allah ya sa mata albarka sosai take ciniki a gurin, shiga ta mutunci take yi kuma bata yarda wani maganar banza ya shiga tsakaninta da maza, tana da almajirai biyu da suke mata wanke-wanke da miƙa abinci. Ganin rayuwarta ya fara canzawa tana cikin walwala sai ƴan uwansa da Baba suke ta zuga shi da lallai ya hana ta saida abincin in ba haka ba zata kwaso cikin da ba nashi ba ta kawo mishi, dan duk unguwa an san bin mazanta take yi tana fakewa da sunan sayar da abinci... "Dan ubanka tunanin me kake yi? Za ka sauta ko sai na tsine maka?" Ta katse mishi zuzzurfar tunanin da yake yi cikin masifa da ɗaga murya. Ya kalle ta a hankali, ita ma shi take kallo, idanunta cike maƙil da hawaye, amma a hakan ƙoƙarin murmushi take yi dan ta nuna mishi ko ya sake ta bata da asara, fuskarta dama da hagu sashin yatsunsa ne kwance, bakinta a fashe, ya aune ya kumbura suntum, kyakkyawar halittarta duk ya canza zuwa mummuna dan tsananin dukan da ta sha, wani matsanancin tausayi da ƙaunarta da ya daɗe baiji irinsa ba ya tsirga a filin zuciyarsa. Ya maida kallonsa kan Baba Lauratu, a sanyaye kuma cike da ladabi ya fara magana. "Baba kiyi haƙuri, idan na sake ta zata iya komawa ruwa cikin addininta na kirista..." "To ta koma mana dan Ubanta. Ai daman ko yanzu ba musulma bace tunda bata shekara arba'in a cikin musuluncin ba, manyan malamai sun tabbatar da hakan. Maza sakatta mu yarda ƙwallon mangwaro mu huta da ƙuda." Ya zube a gabanta ya riƙe ƙafafunta da niyyar fara mata magiya. "Baba..." Ta katse shi da sauri ta hanyar fincike ƙafafunta ta ɗaga murya ta fara addu'ar cikin sauri "Ya Allah ka tsi..." "Baba zan sake ta, dan Allah karki ƙarasa" Ya katse ta da faɗan haka cikin gunjin kuka kamar mace. Jikinsa na kyarma ya rarrafa kusa da ita ya haɗa hannayensa biyu alamar roƙo, sai kuma ya miƙa hannu kamar zai ruƙo nata hannun da sauri ta ja da baya kamar ta ga kumurcin maciji. Bai damu ba ya fara magana sauri-sauri murya da jikinsa babu inda ba ya rawa. "Maryam ! ki yi haƙuri. Ban taɓa tunanin a nan kusa zanyi da na sanin irin abubuwan da na daɗe ina miki ba, a yau da Allah ya fargar da ni sai kuma na rasa damar da zanbi gurin gyara kuskure na. Duk da nasan zaiyi wahala ki iya yafe min amma dai bazan gaji da roƙon ki yafe min ba. Maryam dan girman Allah ki yafe min, ina roƙonki ko da kin tafi dan Allah karki koma cikin addinin kirista... Na sake ki ! Saki uku!!" Yana ƙarasa sakin ya zube wanwar a gurin yana jan numfashi sama-sama kamar mai cutan asma. Suman wucin gadi ta yi, Allah ya sani ta so Masa'udu so mai tsanani, duk da irin azabtar da ita da yake yi bata taɓa tsannanin akwai saki a tsakaninsu ba, yanzu da sakin ya afku sai tayi tsam da ranta jijiyoyin shige da fice wajen kai saƙonni a ƙwaƙwalwarta suka tsaya da aiki na wucin gadi. Ƙaƙƙarfar guɗar da Baba Lauratu ta daddage ta rangaɗa shi yayi nasarar dawo da ita cikin haiyacinta, bakin ta kamar gonar auduga, burinta ya cika. Yau dai Allah yayi sun rabu da alaƙaƙai. "Zaman me kike yi? ai sai ki yunƙura ki fice mana daga gida tunda igiyoyin da suka sarƙafa mana sun tsittsinke..." "Dakata Baba Laurata !" Tayi ƙarfin halin dakatar da ita cikin tsawa tare da ɗaga mata hannu. ɗan ragowar jarumtar da ya rage mata ta tattaro ta yunƙura ta miƙe tsaye jikinta babu inda ba ya mata ciwo. "Ta fi nono fari, ɗanki ga shi nan ki jiƙa shi ki sha. Idan kinso ki aure shi ƙarewar hana shi auren tubabbiya..." "Keeee karki kawo min iskanci da zancen banza irin naku na kafurai" Ta katse ta cikin zafin rai ta ɗaga sandar hannunta da nufin sake kwaɗa mata. Caraf ta riƙe sandar tana gwalalo ido waje "Wallahi kika sake duka na saina zubar da ke a nan gurin, matsiyaciya wacce bata san Allah da ikonsa ba." Yarɓar da sandan tayi Baba ta tafi taga-taga kamar zata faɗi ta yi ƙoƙarin tsayawa. Bata sake kallonsu ba ta nufi ma'ajiyar kayanta ta ɗauki doguwar riga ta canza riga da zanin jikinta da suka yayyage. Ta ɗauki wani siririn gyale ta rufa a kanta ta ɗauki jakar hannu inda take tara ƴan kuɗaɗenta ta nufi hanyar ficewa daga ɗakin hannunta jaye da akwatin kayanta. "Masa'udu na barka har abada, kamar yadda na bar maka addininka har abada." Daga haka bata ƙara cewa komai ba ta fice daga ɗakin ta bar gidan gaba ɗaya, tana fita taga wani mai mashin ta ɗare a kai ta ce ya kaita bakin titi. ******* Duk yadda ta so ta ƙarfafi kanta kar ta sake kuka ta kasa, bata san lokacin da wani ƙaƙƙarfar kuka ya sake ƙwace mata ba. Da saurin gaske ta sa hannu biyu ta toshe bakinta ta rufe fuskarta dan kar hankalin mazauna cikin motar ya dawo gare ta. "Ki yi haƙuri" Ta ji saukar kalmar da ƙaramar murya kamar a tsakiyar kunnenta, a hankali ta ɗago kai dan ganin mai maganar sai tayi arba da kyakkyawar fuskar yarinyar da take zaune kusa da ita. Tsawon minti biyu suna musayar kallo sai yarinyar ta haske ta da tattausan murmushi, ta miƙa mata wani ɗan ƙaramin tsumma. Fahimtar abinda take nufi yasa ta karɓa ta fara share hawayen fuskarta, tana gogewa wasu sabbi na sake gangarowa har ta goge gaba ɗaya bayan ta samu nasarar tsaida kukan da ƙyar. Pure water ta miƙa mata mai sanyi, ba tare da musu ba ta karɓi ruwan ta huda ta fara sha wani sanyi yana kwarara a zuciyarta. "Na gode. Ya sunanki?" "Bibi" Ta amsa a hankali bayan shirun da tayi na second talatin kamar baza ta amsa ba. Dan ma kar ta sake tambayarta sai ta sanya tafukan hannayenta duk biyu ta rufe fuskarta tana tunani kamar mai bacci. 'Maman Ushe ta mutu, Indo ta mutu, Mal Muntari ya mutu, Raliya ta mutu. Ya zama dole ta gudu daga layin mai dubun tsumma in dai tana so ta cigaba da rayuwarta. Ta ji lokacin da aka zo gurin Mal daga gidan hakimi da cewar a tafi da ita ana tuhumar ita mayya ce, tun a lokacin ta yanke wa kanta shawarar abinda zai fisshe ta, da wannan dalilin yasa ta ɓuya can bayan gidan gurin shuke-shuke har sukai kiciɓis da Indo tana fata da mugun alkaba'i a kan Maman Ushe. Ko da Indo ta koma ɗakinta ta faɗi cikin mawuyacin hali bata fito daga maɓoyarta ba, da yake mutan gidan suna cikin tashin hankali shi yasa ma babu wanda ya tuna da ita balle har a neme ta. Indo tun kafin a kaita asibiti ta ce ga garinku nan. Mal Ali da duk wani wanda ya kusance su da al'ummar unguwa sun shiga cikin tashin hankali matsananci, rashin mata biyu a lokaci ɗaya ƙarfin imani da addu'a ne kawai ya hana Malam Ali zaucewa. Cikin dare ta yiwa gidan kallon ƙarshe ta bar kowa da komai na gidan ciki har da sunan Amirah da Maman Ushe ta raɗa mata ta fice daga ita sai kayan makarantan jikinta da naira saba'in a aljihun wandonta. Tafiya kawai take ba tare da sanin inda take jefa ƙafafunta ba ta wayi gari a bakin titi misalin ƙarfe takwas da rabi na safe, motocin Ganjal sai wucewa suke kwandastoci suna ta shelar "Kasuwa... kasuwan bacci." Ba tare da tunanin komai ba tasa hannu ta tsaida motar. "Yarinya ina za ki?" "Kasuwa" Ta amsa shi da sassanyar murya. "Naira hamsin" Ya faɗa mata bayan ya sauka daga kujerar farko ta shige ciki, har motar zata tashi ta hangi mai pure water sai ta sayi guda ɗaya. Sun fara tafiya ba daɗewa Maryam ta tsaida motar ta shiga bayan ta ce ita ma kasuwa za ta...' "Bibi kina bacci ne? mun iso fa." Maryam ta katse mata tunanin da take yi ta hanyar jijjiga ta da ɗan ƙarfi dan ta dawo cikin haiyacinta. ******* ******* "Mary kwana da yawa? gaskiya mun daɗe bamu haɗu ba, amma bana tunanin wannan ƴarki ce dan naga ba ƙaramar yarinya bace, ko sistan mai gidanki ce?" Taja tsaki fuskanta a ƙuntace, duk da tayi wanka kuma ciwukan jikinta duk anyi dressing ɗinsu ta ci abinci mai rai da lafiya ta sha magunguna har lokacin tsamin da jikinta yayi bai saki ya koma mata dai dai ba. "Mercy daina tuna min batun ɗan iskan nan. Mun rabu da shi gaba ɗaya." Ta maida kallonta kan Bibi da take barci hankalinta kwance, ita ma anyi mata wanka an canja mata kaya da sabbin ƙananun kaya ƴan kanti riga da wando. "Wannan yarinyar a mota muka haɗu, fahimtar da nayi bata san kowa ba kuma bata san inda zata je ba tsawon lokaci tana zaune a gefen titi shi yasa na taho da ita dan kar ta faɗa mugun hannu. Idan ta samu nutsuwa zan tambayi inda iyayenta suke sai in mayar da ita." "Ok ! kin kyauta. Ni zan fita, akwai komai da zaki iya buƙata, idan kuma kina son wani abu ki kira Grace ki yi mata magana. Maybe zan dawo kunyi bacci." Makullan motoci huɗu da suke zube a kan ɗan ƙaramin teburin gilas ta ɗauki guda ɗaya ta nufi hanyar ficewa daga falon, Maryam tana mata fatan dawowa lafiya. 'Tun a hanya da ta tuna yanayin yadda jikinta yake ciki ta yanke shawarar baza ta koma garinsu a wannan halin da take ciki ba. Dole ta nemi inda zata huta ta samu nutsuwa raunin jikinta su warke kafin ta koma gurin mahaifiyarta da ƴan uwanta ta basu haƙuri, tana cikin tunanin ne ƙawarta Mercy Abom ta faɗo mata a rai, tana zaune ne a Kamazou, ta san babu inda zata je ta samu tarba ta mutunci da girmamawa da ya wuce gurin Mercy, dan haka kai tsaye ta yanke shawarar nufan can ita da Bibi. Kamar yadda tayi tsammani kuwa Mercy ta tarbeta da tsananin murna, ta kaisu har cikin tanƙamemen ɗakin barcinta, ta haɗa musu ruwan wanka mai zafi suka gargasa jiki. Ba tare da ɓata lokaci ba ta kira likita ya duba ta ya bata magani, ta bada umarnin a haɗa musu lafiyayyen abinci har saida suka ture. Kafin ta fita tace su shiga duk inda suke so a tangamemen gidan nata su yi duk abinda suke so ta basu dama. A cikin kwanaki goma da suka biyo baya Mary wacce ta daina sallah, kuma ta daina amsa sunan Maryam sunyi shar da su daga ita har Bibi, alamun hutu da jin daɗi ƙarara ya baiyana a jikinsu. Ko a fuska Mercy bata taɓa nuna ta ƙosa da su ba harkokinta kawai take yi tana kashe musu manyan kuɗaɗe ta hanyar sai musu suturu masu tsada kamar bata san zafin kuɗin ba. Mary tun tana magana tana roƙon ta rage kashe musu kuɗi har dai ta gaji ta zuba mata ido. Satin su uku a gidan Mercy ta ɗebi kayanta kala biyu ta nufi kacia dan ganin halin da Mahaifiyarta da ƴan uwanta suke ciki, tayi kyau sosai cikin matsattsiyar rigar da ta saka a jikinta da ɗan ɓingilin sket ɗin jikinta, fuskarta ya sha kwalliya kamar wacce zata je gasar sarauniyar kyau, ta kawo wani faskeken glas ta ƙwama a idanunta. Idan ba sani mutum yayi ba baza a taɓa tunanin ta taɓa zama musulma ba balle har ayi tunanin ita ce Maryam ɗinnan da ta sha matsanancin gwale-gwale a hannun Masa'udu da Mahaifiya da ƴan'uwansa ba. Bata ji daɗin labarin da ta samu na mutuwar mahaifiyarta watanni huɗu da suka wuce ba, ta ci kuka sosai tayi mata addu'a a jikin kabarinta da yake cikin gidan, ƴan'uwanta kuma duk da basa cikin wahala rayuwa suke irinta cikakkun karuwai masu zaman kansu, da wannan dalilin yasa a daddafe ta kwana biyu ta tattara ta koma gidan Mercy bayan sunyi musayan lambobin waya da ƴan uwanta, sunyi murna sosai da ta sanar da su ta bar musulunci, har suka ƙara da ce mata barinta musulunci daɗaɗɗan buri ne da mahaifiyarsu ta daɗe tana addu'a a kai, sunsan ko yanzu tana can tana murna a kabari. "Mercy ina tunanin zamana ya isa haka nan. Ina so in kama sana'a ko wani abu da kuɗi zasu dinga shigo min." Ta kalle ta fuskarta na baiyana rashin jin daɗin maganarta, ta tashi zaune daga kishingiɗar da tayi. "Mary akwai wani abu da kike so ki siya ne ko ki siyawa Bibi baki faɗa min ba shi yasa kike so ki kama business?" "No wallahi ba haka bane, kin ɗauke nauyin duk wani abu da muke buƙata har ma da wanda bamu nema ba. Amma a zaman da nayi cikin hausawa na ƙaru da wani magana da suke cewa da a ba mutum kifi gara a koya mishi yadda ake kamun kifin, kin gane? just kawai zaman haka ya ishe ni, kuma ina so inga nima ina walwala da kuɗaɗe na ko dan in rage miki wasu ɗawainiyan, kinga ga nauyin Bibi ma da har yanzu bata tuna da inda iyayenta suke ba. Ni ko a cikin business ɗinki ki sama min wani abu da zan dinga taya ki da shi..." Dariyar da Mercy ta kwashe dashi shi ya katse Mary daga maganganun da take yi, tsawon lokaci tana ƙyaƙyatawa kamar taɓaɓɓiya kafin ta tsagaita ta ce "Za ki iya yin irin sana'a ta?" "Why not? in dai kin iya jurewa nima ai zan iya." Ta amsa da ƙwarin gwuiwa. "Ok ! yau da daddare zan kaiki gurin Oga. Amma fa indai muka je dole ki amshi duk abinda zai ce miki in ba haka ba zaki mutu. Kin yadda?" "Eh !" Ta amsa ba tare da zurfafa tunani ba. ****** Misalin ƙarfe uku na dare tana gurfane gwuiyawunta a ƙasa gaban ƙaton mutumin da yake zaune a kan wani danƙareren kujera da yake ta walwali yana ɗaukar ido, wasu mutane maza da mata sanye da shuɗayen dogayen riguna sun jeru a gabanshi kamar masu assembly, a kansu ɗaure da jajayen ƙyalle, Mercy tana cikinsu. Da ta hurga idanu lungu da saƙo na cikin gurin sai taga manyan tulu masu kama da tulun giya suna yawo a mabantan gurare su ba a ƙasa ba su ba a sama ba, kuma bata ga wanda yake riƙe da su ba. A matsayinta na sabuwar zuwa ce aka gurfanar da ita gaban Oga dan a karanta mata dokokin ƙungiya kuma a sa mata albarka. "Ba fita har mutuwa... hukuncin kisa mafi muni idan kika yi yunƙurin tona asirin ƙungiya..., za ki yi sadaukarwar jini... kuma duk inda kika shiga a faɗin duniya idanunmu na kanki... Za ki samu duk abinda kike so a duniya, za ki yi fice, za ki yi suna..., amma duk sadda ƙungiya ta nemi abu a gurinki komai wahala za ki bada..." Sautin ƙatuwar muryar da ta karaɗe gurin kenan ba tare da taga wanda yayi maganar ba, tsananin tsoro da fargaba ne ya kamata, mararta ya ƙulle dam da fitsari. Cikin ƙanƙanin lokaci ta fara rawar ɗari, haƙoranta sai haɗuwa suke gaf-gaf. Wani ƙwarya ta gani a gabanta yana yawo shi ba a ƙasa ba shi ba a sama ba. "Ɗauki ki sha dan zama cikakkiyar ƴar ƙungiya." Ƙatuwar muryar ta sake faɗa cikin tsawa. Da sauri ta damƙi ƙoƙon mai ɗauke da wani baƙin abu mai tsananin kauri da wari, da ɗoyi ta kafa a bakinta bayan ta runtse idanunta ta fara kwankwaɗa. "Hhhhhhhhh.... Barka da shigowa cikin ƙungiya Mary... Barka da zama cikakkiyar ƴar ƙungiya Mary..." Abinda ake ta maimaitawa kenan da mabanbantan muryoyi ana ƙyalƙyala dariya. Can kuma muryar ta ɗauke ɗif kamar anyi ruwa an ɗauke. Wannan ƙaton mutumin da take durƙushe a gabanshi ne ya miƙa mata hannunsa da yatsun suke a dunƙule irin na kutare da sauri ta miƙa hannunta ta riƙe nashi hannun. "Kuɗi, mulki, ko suna a duniya?" Ya tambaye ta da siririyar zazzaƙar muryarshi mai kama da ta ƙananun yara. "Kuɗi." Ta amsa da rawar murya. "A cikin seconds biyu ki faɗi sunan wanda za ki sadaukarwa ƙungiya..." "Baba Lauratu." Ta amsa da sauri tun kafin ya rufe baki. "Arzikinki yana tare da ke, wannan yarinyar Bibi ita ce hanyar arzikinki, ita ce zata samar miki suna da ɗaukaka da mulki. Amma sai kin jure, dan zata baki wahala. Duk tsananin wuya kar ki kuskura ki rabu da ita." Yana gama maganar ya sakar mata hannu ya juya bayansa yana wasu surutai masu kama da na tsafi, minti biyu tsakani ya fara ƙwala kiran sunan "Lauratu... Lauratu... Lauratu..." Sai ya haska tafin dungulmin hannunshi a bango. Nan take hoton Baba Lauratu ya baiyana a jikin bangon, tana kwance a kan yar karamar katifarta tana bacci, sai soshe soshe take yi da alamun sauro ne suke damunta. Ta jikin bango ya miƙa dogon hannunshi ya kama agarar ƙafarta ya cisgo da tsananin ƙarfi, nan take ya finciko jijiya da ƙashin gurin ya tara wani ƙaton ƙoƙo ta ƙarƙashin ƙafar jini yana ɓulɓula a ciki.. BILHAƘƘI Tana hakimce a kan wata ƴar ƙaramar kujera da take fuskantarsa, saɓanin duk wasu sabbin shigowa ƙungiyar da ake gurfanar da su gwuiwa bibiyu a gaban Oga ita a zaune take. kuma babu wasu dokoki da aka karanta mata, kai tsaye ya miƙa mata hannunshi duk biyun da nufin ta kama, ƙin kamawa ta yi, a maimakon haka ma sai ta sadda kanta ƙasa tana wasa da yatsun hannayenta. Bai daddara ba ya sake matsawa kusa da ita sosai ya tura mata hannayenshi jikin nata hannayen, ta ɗago kai a fusace ta kalle shi idanunta jajur, minti ɗaya suna musayar kallo sai kuma ta sake sadda kai ƙasa ta ja wani dogon tsaki kamar bakinta zai taɓa ƙasa. Hannu yasa ya ɗago fuskarta da yake ƙasa suna haɗa idanu wani kakkaifar walƙiya ya fito daga idanunta ya maka shi da jikin bango, da yake shi ma a shirye yake bai bari an watsar da shi ba ya tsaya da ƙafafunsa. Wani ƙaƙƙarfar huci yayi ya kamo ɗaya daga cikin tulunan da suke ta zagaye tsakar gurin ya wanke fuskarsa da baƙin ruwan ciki, yana sakin tulun ya ci gaba da zagaye kamar yadda yake yi da farko shi kuma ya nufe ta gadan-gadan. Hannayenshi duk biyu yasa ya damƙo gashin kanta ta ɗaga ido ido tana kallonshi da idanunta da suke tsattsafar jini a maimakon ruwan hawaye, hannunta ɗaya ya sa a cikin nashi hannun yana ci gaba da kallon ƙwayar idanunta dan neman abinda yake son gani. Tsafi gaskiyar mai shi, wannan magana tabbas haka take. Nan take a cikin ƙwayar idanunta ya ga hoton wata kyakkyawar matashiya a cikin tsakiyar dare, a tsakiyar dokar daji tana ta gudu, a bayanta goye da jaririyar da take ta tsala kuka cikin fita haiyaci. Saida tayi gudu mai tsanani sannan ta cimma wani bukka ƙwallin ƙwal a dokar daji, a bakin bukkar ta tsaya tana haki da sauke zazzafar numfashi, second goma tsakani sai kuma ta fara waige-waige kamar tana tunanin an biyota daga bisani kuma ta afka cikin bukkar da sauri tana ƙoƙarin sauke goyon bayanta. Bata tsaya a ko ina ba sai a gaban wata yanƙwananniyar tsohuwa da take zaune a kan wani gadon kara, tana zaune daga ita sai ɗaurin ƙirji da wani baƙin zanin saƙi, wuyanta kuwa ƙashi ne ƙwara-ƙwara kamar ta shekara biyar tana jinya, gashin kanta fari fat, idanunta ƙulu-ƙulu masu barazar firgita ƙaramin yaro, aje a gabanta wasu manya-manyan sarƙoƙi ne zube da matuƙar yawa masu kama da murjani, gefe da gefenta kuma duma ne a ajiye da wasu luddan duma a kansu an jingina su sun fuskanci gabas. "Re...bec...ca..." Tsohuwar ta kira sunanta a rarrabe fuskarta na baiyana matsanancin mamakin ganinta a daidai irin wannan lokacin. Bata jira komai ba ta aje jaririyar a jikin tsohuwar sannan ta zube a gabanta gwuiyawunta a ƙasa ta haɗa hannuwanta duk biyu alamar roƙo ta fara magana cikin kuka. "Mama Vero ita wannan ƴata ce... ita ce rabon da kika tabbatar min akwaita a tsakanina da Musty. kin daɗe kina bibiyata akan in faɗi abinda nake so ko menene kiyi min saboda Mummy na ta taimake ki, duk tsawon wannan lokacin duk da matsanancin halin ƙuncin da nake ciki a ƙauyen nan ban taɓa roƙonki komai ba. Yau ga ni ina neman abu a gurinki, Pls ki tsare min ita, ki kare ta, ki ɗaukakata a duk inda ta shiga, karki ba wani mutum ikon ya cutar da ita, ki kaita duk inda ɗaukakarta yake, za ki iya, na tabbatar za ki iya, shi yasa na kawo ta gare ki..." Bata ƙarasa aje numfashin maganar ba ta sake tashi ta fice ta runtuma a guje dan komawa inda ta fito... Tsohuwar da aka kira Mama Vero kuwa yarinyar ta rungume a ƙirjinta tana mata wasu irin maganganu da ba a gane me take cewa a cikin kunnenta, wani abin ban mamaki nan da nan kukanta ya fara yin ƙasa har daga ƙarshe tayi shiru sai sauke ajiyar zuwa take yi. Zanin da aka naɗe yarinyar ta warware tana ƙare mata kallo, can kuma sai ta shimfiɗar da yarinyar a kan gadon ta buɗe bakinta tasa yatsarta can ciki ta ɗago ɗan ƙanƙanin harshen yarinyar ta haske da tocila mai tsananin haske, wani tafkeken baƙi ne a jikin harshen yarinyar, minti ɗaya tsakani ta gwale idanun yarinyar tana kallon ƙwayoyin idanun ta cikin madaidaicin haske, wani saɓulallen murmushi ne ya suɓuce mata, ta ɗaga ƙafafun yarinyar sama kanta yana kallon ƙasa ta fara wujijjigata. "Alheri...? welcome back." Tsohuwar ta faɗa cikin ɗaga murya fuskarta cike da murmushi, sai kuma ta ɓarke da wata ƙaƙƙarfar dariya muryarta a buɗe zaƙi cau kamar ta matashiya ƴar ashirin da biyar. Ludayin duman nan ta ɗauki guda ɗaya tayi wani magana ta tofa miyau ta manna a ƙirjin yarinyar inda Mustapha ya tsattsaga da reza, haka taitayi tana maimaitawa har sau uku, da ta haska gurin sai na ga ya dausashe ya bada wani tabo mai kyau alamu na tsohon ciwo. Aje yarinyar ta sake yi a kan gadon karan ta fita waje cikin daren ta zagaya ta can bayan bukkarta ta tatso madarar shanu a jikin wata saniya da take ɗaure ƙwallin ƙwal a gurin ta dawo ciki ta ɗiga wa yarinyar sau uku a baki, zanin da aka naɗe ta da shi ta yayyaga ta ɗaurawa yarinyar a ƙirji kamar yadda ita ma zanin saƙi ne kaɗai ɗaure a ƙirjinta. ****** ****** Sake gyara zamanta tayi a kan ɗan kututturen icen tana kallon yarinyar ƴar kimanin shekara biyu da take ta wasa da wasu tarin dutsuna farare tas, a fili idan aka kalli tsohuwar za a ga kamar yarinyar take kallo amma haƙiƙanin gaskiya idanunta ne kawai a kanta zuciyarta ta cilla ne cikin zuzzufar tunani. 'A tsawon shekaru biyun da tayi tana renon Alheri kamar yadda take kiranta tayi su ne cikin tsuma ta da ɗura mata duk wasu sirrikan tsafi da ta sani, lamarin yarinyar ne yayi mata daidai har ma fiye da yadda take buƙata. A karan kanta ita yarinyar ƴar baiwa ce da aka haife ta da wasu sirrika na tsafi kamar yadda aka haifi kakarta Alheri mahaifiyar Rebecca. Da wannan dalilin yasa ƴan ƙauyen suke ce wa Alheri mayya har daga ƙarshe suka yi gangamin ƙona ta da ranta a lokacin Mama Vero bata nan. Ita Mama Vero ta zame wa mutanen ƙauyen tamkar ƙadangaren bakin tulu ne, a karta a kar tulu a barta ta ɓata ruwa. Matsafiya ce ta gasken gaske wacce da farkon yarintarta ta fara ne da bada magunguna, duk ciwon da ya gagara indai har aka je gare ta ta bada magani cikin hukuncin Allah sai ciwon ya warke, daga nan kuma sai mutane suka lura ai Mama Vero tamkar wata ƴar baiwa ce domin duk abinda tayi hasashen zai faru tabbas komai daren daɗewa zai faru, ta ba mutane magunguna da dama musamman masu neman haihuwa, har daga ƙauyukan da suke nesa da su ana zuwa gurinta karɓar magani kuma a cikin farashi ƙalilan. Wani abin mamaki daga cikin aikinta idan ta kalli mace in zata haihu tana faɗin ta ga haihuwa a tare da ita, idan kuma bazata haihu ba kai tsaye zata faɗa mata kuma ta ƙara da cewar idan zata zagaya duniya tana neman magani baza ta taɓa haihuwa ba. Da wannan dalilin sai mutanen ƙauyen suka maida ita kamar ta biyun abin bautarsu duk abinda zasuyi sai sun nemi amincewarta, idan suka bijirewa umarninta kuwa tana amfani da alƙaluman tsafinta ta tura musu masifu kala daban-daban, kamar fari na abinci, ko cutar amai da gudawa manya da yara suyi ta mutuwa, ko kuma ta lalata duk noman da suka yi a shekarar amfanin gonar sam yaƙi yin kyau ko da kuwa an samu ruwan sama yadda ake buƙata. Akwai aminci mai ƙarfi tsakaninta da Alheri mahaifiyar Rebecca tunma kafin a haifi Rebecca, wata rana Mama Vero tana cikin daji tana tsafe-tsafenta aka sami wani baƙon iskar maciji da ba zaunannen cikin dajin bane ya sare ta, ko kafin tayi wani yunƙuri macijin ya silale ya ɓace daga gurin, tayi duk dabarar da ta sani na magani dafin ya ƙi tsayuwa guri ɗaya, a bincikenta dole sai ta kashe wannan macijin sannan zata samu damar fitar da dafin daga jikinta ga shi tayi neman duniya bata ganshi ba. Har ta fara galabaita sai ga Alheri da macijin riƙe a hannunta ta shaƙe wuyanshi tana ƙoƙarin kashe shi, a gaban Mama Vero ta kashe shi, ba tare da jin tsoron komai ba ta durƙusa ta sa bakinta a inda ya sari Mama Vero ta zuƙo wani kakkauran jini ta zubar, ta yanki naman bindin macijin ta manna a gurin. "Sannu Maa ! ciwon zai warke, zafin zai tafi." Tayi maganar a hankali tana murmushi. Ita ta kama Mama Vero ta raka ta har cikin bukkarta hannunta riƙe da mushen macijin, da zata tafi ta aje mata macijin ta ce kullum ta yanki tsokar jikinshi ta manna a gurin ciwon zaiyi saurin warkewa. "Yarinyata mene sunanki?" Ta tambaye ta tana bin ta da kallon ƙauna da yabawa ƙoƙarin da ta yi mata. "Alheri" Ta amsa a lokacin da take daf da ficewa daga cikin bukkar. A wannan lokacin Alheri tana amarya lamarin ya faru ko cikin Rebecca bata da shi, tun daga wannan lokacin jefi-jefi tana zuwa gurin Mama Vero har ma tana taya ta da wasu aiyukan harhaɗa magani dan ita ma tana da nata baiwar, ko da Mama Vero ta nemi da ta taimakawa Alheri gurin ninka mata ƙarfin baiwar da take da shi ƙin yadda ta yi, ta ce bata so. Istifanus shi ne mahaifin Luka, mijin Alheri, mahaifiyar Rebecca. Ciwo ne mai tsanani ya kama shi tun ranar auren Alheri da Luka, tun a ranar wasu daga cikin mutanen ƙauyen suka fara surutun amaryar mayya ce tunda an auro ta ne daga wani ƙauye da yake nesa da Rimau, sunan ƙauyen gefe, tafiyar mashin ce miƙaƙƙiya daga Rimau har sai an haye ruwa sannan a isa gefe, kuma mutane suna ta hasashen akwai mayu a garin. An yi maganin amma sam ba a dace ba, Mama Vero kuma ta ƙi ba shi magani wanda hakan da ta yi babban alamu ne da yake nuna musu Istifanus mutuwa zai yi. Sai da ya shekara cur yana jinya a ranar da Alheri ta haifi Rebecca a ranar shi kuma ya mutu, abinda ya ƙara dasa wa mutane yarda da cewar Alheri maiya ce kafin ya mutu yana ta kiran sunanta yana mimmiƙewa a zabure har ya tunkuyi burji. Sai kuma suka cigaba da cewa ai Lidiya mahaifiyar su Zidane ma ita ta cinye ta tunda anyi aurensu ba daɗewa ta mutu. Nan fa gaba ɗaya ƙauyen ya ɗauki ƙananun maganganu ita kuwa tana gida rungume da jaririyarta bata da masaniyar abinda yake faruwa har sai da Luka ya koma gidan afujajan yana tuhumarta. "Alheri ki faɗa min gaskiya, ke mayya ce?" Luka ya tambaye ta da jajayen idanunsa cikin fushi da tashin hankali. Matsanancin firgita ne ya kamata, har saura ƙiris ta suɓutar da yarinyar a ƙasa saboda jin tambayar tayi tamkar saukar aradu, bakinta na rawa ta ce "Luka kana cikin hankalinka kuwa? me kake cewa haka?" Ta mayar mishi da tambayoyin tana kallonshi a tsorace, fuskarta ɗauke da matsanancin mamakin maganganunsa. "Daga yadda kika yi da na faɗi maganar nan ya tabbatar min da zargina gaskiya ne, amma baki min adalci ba Alheri. Menene bana yi miki a gidannan? ki rasa wanda za ki cinye sai Lidiya da mahaifina?" Kaɗa kai kawai yayi ya fice daga ɗakin fuskarsa a cunkushe, zuciyarsa ɗauke da zallar takaicinta, baƙin ciki, da da-na sanin aurenta. Tun daga ranar mutanen ƙauyen da shi kanshi mijin nata suka tsangwame ta, sun ɗauki wannan matakin na tsangwamarta ne a cewarsu idan ka nuna kana tsoron maye shi ne zai bashi damar samun galaba a kanka. Ba ta da halin ta shaƙi iska mai sanyi sai su fara zaginta suna jifanta da baƙaƙen maganganu, idan ta kuskura ta fita waje kuwa da kuka take komawa cikin gida saboda da jifa suke rako ta, ta rame tayi baƙi ta fice daga haiyacinta, Rebecca ma ta fige tayi firit kamar bakwaini saboda rashin samun kyakkyawar kulawa daga mahaifiyarta. Tun kafin ta haihu ta ɗauke ƙata ɗif daga gurin Mama Vero, ta daina zuwa gaba ɗaya, ita ma ba ta neme ta ba, ba ta da masaniyar abinda yake faruwa a cikin ƙauyen saboda wani muhimmin aiki da take yi, har daga ƙarshe tafiya ta kama ta. James wan Zidane ne ya kamu da mummunan ciwon da aka rasa gane kansa da gindinsa, da farko ya fara da haɓo ne sai kuma jinin ya ɓalle masa ta hanci ta baki, kwana biyu yana cikin mawuyacin hali kafin ya mutu a daren ranar asabar. Nan ƙauyen ya sake ɗauka kwam zancen Alheri mayya ko ina shi ake yi, wasu suna cewa a kore ta kafin ta gama musu ɗauki ɗai-ɗai wasu suna cewa a kashe ta. Washe gari lahadi a coci manyan pastocin ƙauyen su huɗu ƙarƙashin jagorancin babbansu pastor Nuhu suka yanke shawarar kashe ta, da yammacin ranar kuwa suka aiwatar da ƙudirinsu bayan an tsige Rebecca daga bakin nono, Alheri tana kuka tana magiyar su barta ta gama shayar da ƴarta suka ja ta bayan gari a wulaƙance suka ɗaure ta a jikin bishiya aka diddila mata fetur Luka ya ƙyasta ashana ya hurga mata. Ko da Mama Vero ta dawo ta samu labarin abinda ya faru tayi kuka kamar ranta zai fita, da ta saukar da annobar amai da gudawa matasa mata sa'annin Alheri masu aure da marasa aure su talatin ne suka mutu. Sai da suka shekara huɗu amfanin gonansu yana lalacewa, sun shiga matsanancin hali da yunwa mai tsanani, kuma duk wanda yayi nufin barin ƙauyen sai dai a tsinci gawarsa a hanya. Ko da ƙauyukan kusa da su sunyi niyyar kawo musu tallafi sai dai a ga kayan abincin ya lalace tsutsotsi manya manya masu kama da gwazarma suna safa da marwa a ciki. Da tashin hankali yayi tashin hankali bala'i yayi bala'i tsofaffin ƙauyen da pastoci ne suka haɗu aka je gurin Mama Vero neman tuba dan sun tabbatar wannan bala'in daga gurinta yake. Cikin fushi take sanar da su laifin da suka aikata mata ta ƙara da cewa sai sun shekara goma a cikin wannan hali. Rebecca da aka nuna mata a matsayin ƴar Alheri yasa ta sassauta musu daga fushin da ta yi da su har daga ƙarshe ta barsu suka ci gaba da harkokinsu cikin lumana da zaman lafiya. A kwan a tashi Rebecca tana girma amma wani abin mamaki ga Mama Vero sam Rebecca ta tsane ta, bata ƙaunarta bata ƙaunar ganinta, shi yasa sai ta shafe wata guda cur bata je gurin Mama Vero ba duk da matsanancin halin da take ciki a ƙauyen a gurin Mahaifinta da ɗan uwanta da wasu daga cikin mutanen gari, tsananin tsanan da aka gwada wa mahaifiyarta ne yake bibiyarta duk da an tabbatar ita ba mayya bace. Duk yadda Mama Vero take bibiyarta akan idan akwai abinda take so tayi mata ko a kan mutanen garin ta faɗa za ta yi mata amma bata taɓa neman alfarmarta ba sai akan riƙon BILHAƘƘI wacce take kira da sunan kakarta Alheri saboda ta fahimci tana ɗauke da irin baiwar da Alherin take da shi, yanzu ga shi ta ƙara mata da manyan sirrika na tsafin da ta sani kaf rayuwarta. Mama Vero ita ce ta aikawa Pastor Nuhu saƙon gaggawa akan matuƙar suka kashe Rebecca to tabbas zasu ɓallowa kansu masifu da bala'in da basu taɓa tsammani ba, za ta tado ruhin Alheri ta ɗauki fansar kisan da suka yi mata. Da wannan daliin ne yasa yayi gaggawar dakatar da kashe Rebecca.' Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke bayan ta dawo daga duniya mai tsananin nisa na tunanin da ta lula, ta sake kallon Alheri tana sakin tatausan murmushi, har lokacin yarinyar bata san me Mama take yi ba, amma yanzu ba wasa da fararen dutsuna take yi ba, wasu ma'auratan malam buɗe littafi take ta jujjuya su da ƙarfin tsafin idanunta tana ƙyalƙyala dariya cike da matsanancin nishaɗi. Nan da nan kuma Mama Vero ta ɓata fuska bayan wani tunani ya faɗo mata a rai. 'Ba a halicci Alheri dan ta rayu a ƙuntataccen ƙauyen nan ba, a binciken da tayi cikib sanin ta Alheri za ta zaga sassa daban-daban na jihohin ƙasar nigeria da ma ƙasashen ƙetare, za ta yi gwagwarmaya da mutane mabanbanta, za ta ɗaukaka, kuma ƙarfin baiwa da tsafinta zai kareta daga duk wani abin cutarwa a duk inda ta shiga. Kuma ta gano Alheri za ta zama fitacciya gagara duniya ne a lokacin da ta cika shekaru ashirin da haihuwa, domin a lokacin ne zata iya sarrafa duk wani baiwa na tsafi da yake jikinta... abinda yake bata takaici da saka ta a cikin tunani da ɓacin rai bai wuce ganowar da tayi dole su rabu da juna ko tana so ko bata so, ƙaddarar zamanta da Alheri na shekaru biyu ne kawai...' "Mama... come and see..." Alheri ta ƙwalla mata kira daga inda take zaune. Da sauri ta nufi gurinta kamar ba tsohuwa ba idanunta ciccike da hawaye... ****** ******* Daga nan kawai sai hotonta da Mama Vero ya ɓace a idanunta sai wata walƙiya ta baiyana bayan washewar hasken sai Oga ya ganta sanye da kayan fulani a hannun wani dattijon makiyayi. Irin fulanin nan masu zagayawa da dabbobinsu da iyalinsu daga wannan jeji zuwa wancan jeji zuwa wancan jeji. Da yake dattijon babban malami ne da ba ya sake da ambaton Ubangiji, mai yawaita ibada da addu'o'i hakan ne ya dakushe kaifin tsafin da yake jikinta. Da farko tana yawan firgita da tsorata a lokuta mabanbanta amma da ya tasa ta gaba da manyan addu'o'i sai ta fara komawa dai-dai, sam ba ta iya amfani da tsafin da yake jikinta sai asalin baiwar da Allah ya halicceta da su. Kamar misalin idan ta kalli abu da zafin rai cikin kankanin lokaci abin yake lalacewa, idan ta ji haushin mutum to tabbas wani mummunar abu sai ya faru da wannan mutumin ko da kuwa dabba ce. Da Baffa ya fahimci yanayin halittarta sai yake ta cusa mata duk maganar da zata yi ta ringa ƙarawa da ambaton Allah hakan ne yake dakushe kaifin baiwarta ba ta lalata abubuwa kuma bata cika cutar da mutane akai akai ba. A gurin dai wannan dattijo rayuwarta abar sha'awa cike da tarbiyyar musulunci har ta shekara biyar a gurinshi idan aka haɗa da biyun da tayi gurin Mama Vero shekarunta bakwai kenan, suna kiranta da suna Aisha. Nutsattsiyar yarinya mai cike da kamala da kyawawan halaye. Juyin juya hali irinna ƙaddarar ta kamar yadda Mama Vero ta gano za ta rayu a mabanbantan gurare da mabanbantan mutane. Wata rana ta raka matar Baffa Inna Danejo siyan ɓahe (kuka) a cikin kasuwa kawai ta sunɓule mata, haka taita garanba a cikin kasuwar daga ƙarshe da ta ji ta gaji ta lallaɓa ta buɗe wata kyakkyawar mota ta shige ciki ta kwanta luf a ƙasan kujerun bayan motar, nan da nan kuwa nannauyan barci ya kwashe ta. Ba tare da sanin akwai wata halitta a cikin motar ba Allex yaja motarsa ya bar cikin kasuwar zuwa gidansa da yake ɗirkaniya cikin garin kaduna. Da farko sun firgita da ganinta amma a kallon farko Allah ya jefa musu matsanancin ƙaunarta a zukatansu, daman a tsawon aurensu shekaru goma basu taɓa haihuwa. Dokas da mijinta Allex sunyi murna ƙwarai da wannan kyauta na ƴa sukutum da guda da Ubangiji yayi musu, dan sunyi tambayar duniya har coci sun kaita gurin pastor amma ta kasa faɗen takamaimai inda iyayenta suke. Abu ɗaya kawai suka fahimta, ita yarinyar musulma ce. Nan fa ƙabilancin addininsu ya motsa, Pastor ya basu shawarar idan suka riƙe yarinyar nan da amana kuma suka yi ƙoƙarin maida ita mabiyiyar addinin kirista suna da gwaggwaɓar lada a gurin Allah, wai kuma Yeso zaiyi alfahari da su. Da wannan dalilin suka ɗaura ɗamarar riƙe ta gam tare da mantar da ita duk wani harka na musulunci da addinin musulunci da ta sani a baya. Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa suka fara cimma nasarar hakan, dan a lokacin shekarunta bakwai ne bazaiyi wahalar mantar da ita abubuwan da ta sani a baya ba. Cikin shekara biyu da suka yi na riƙonta babu wata matsala sai ci gaba da suke samu ta ko wane ɓangare da alkhairai da dama, sun tabbatar tsintarta alkhairi ne a gare su. Sun bar ɗan madaidaicin gidan da suke da shi sun gina tamfatsetsen gida duk a nan ɗirkaniyar, sun mallaki danƙara danƙaran motoci na hawa da miyagun kuɗaɗe a asusun bankinsu. Idan aka ga Alherin Mama Vero, Aishan Baffa Yallero, Happy ɗin Dokas da Allex kamar yadda suke kiranta babu wanda zai gane ta, saboda ta canza gaba ɗaya. Sun maida ita wata hutacciya ƴar gatan yarinya wacce ake mƙatuƙar ji da ita da gwada mata gata ta ko wane ɓangare... A dai dai wannan lokacin ne kuma ta fara dama musu kunu da kwaɓa musu al'amura bayan ƙannin Dokas mata biyu sun koma hannunta da zama, gori suke mata a fili dan sun san ba yayarsu bace ta haifeta, abu kaɗan sai su sa hannu da nufin make ta. Wata rana dai da ta zuciya ta kaiwa ɗaya daga cikinsu wani mugun shaƙa bata sake ta ba saida ta shaƙa mata ƙamshin mutuwa sosai sannan ta yarɓar da ita, Dokas kuwa ta zuciya ta yi ma Happy duka da dorina dan ta ladabtar da ita. Tun daga nan lamuransu ya fara taɓarɓarewa, duk abinda suka taɓa sai ya lalace, duk yawan tattalin arzikinsu cikin ƙanƙanin lokaci ya taɓarɓare gaba ɗaya. A ƙarshe dai suka zauna su biyu suka yanke shawarar rabuwa da ita, shi ne suka ɗaɗɗaure ta suka ƙulle a buhu Allex ya fita da ita a mota ya biya wani yaronshi da cewar ya kaita can cikin musulmi ya hurgar da ita. Walƙiya ne ya sake baiyana a cikin idanunta da tsananin haske, bayan ɓacewar komai sai ga hoton yadda Maman Ushe ta tsince ta, da irin abubuwan da sukai ta faruwa har zuwa haɗuwarta da Mary har yau da ya buƙaci Mary ta kawo mishi ita. Yana gama ganin komai ya saki hannunta kakkaifar hasken idanunta ya sake maka shi da jikin bango ya watsar da shi a sume a tsakar gurin. Tana miƙewa tsaye da nufin barin gurin wani jiri mai ƙarfi ya kwashe ta ta zube a gurin kusa da ƙafafun Oga.... BILHAƘƘI Bibi ce shimfiɗe a ƙasa a gaban gunkin tsafin shi kuma yana tsungune yasa gwuiwoyinshi a ƙasa, idanunshi a rufe, dungulmin hannayenshi duk biyun ya haɗe su guri ɗaya alamar roƙo, wani irin maganganu yake yi na tsafi sam ba a gane me yake cewa. Can kuma sai yayi sujuda a gaban gunkin tsafin na tsawon daƙiƙu, ya ɗago ya sake gurfana gwuiwoyinsa a ƙasa ya ci gaba da surutan kamar yadda yayi da farko, tsawon wani lokaci yana a wannan hali sannan ya juyar da kansa gefe da gefe kamar wanda ya idar da sallah, cak ya ɗauki Bibi kamar wata ƴar tsana a kafaɗarsa ya fita da ita daga ɗakin tsafe-tsafen ya nufi gurin su Mary. "Ki tafi da ita, kamar yadda na faɗa miki duk wata ɗaukaka da arziki na duniya da zaki nema yana tattare da wannan yarinyar. Za ki ji daɗinta, za ki sami abinda kike so, amma a tattare da samun abinda kike so akwai tsananin wahalar da za ta baki. Wannan kuma ƙaddararki ce." Yana gama wannan maganar ya shafi cinyoyinsa ɓat ya ɓace a gurin kamar bai taɓa baiyana ba, su ma basu jira komai ba suka rungume Bibi idanunsu a rufe, nan take suka ɓace basu baiyana a ko ina ba sai a tsakiyar kan gadon Mercy. Tun daga wannan lokacin duk wani abu da Madam za ta taɓa da niyyar sana'a dan samun kuɗi matuƙar Bibi ta amince da shi sosai yake samun karɓuwa agurin mutane, cikin ƙanƙanin lokaci ita ma aka fara kiranta tana amsawa, ta mallaki manyan kuɗaɗe da manyan gidaje a cikin kaduna da can garinsu kacia, daga ƙarshe sai ta tattara komai nasu ta koma can garinsu bayan Oga ya bata shawarar hakan, ya ƙara da ce mata a can ne Bibi zata haɗu da ƙaddararta. Tamfatseten gidan rawa, haɗaɗɗen abinci, da kayayyakin shaye-shaye ta gina a fitacciyar unguwar Zame wando, inda ya zama nan ne matattarar duk wani shege da shegiya na cikin garin har ma da baƙi masu zuwa cin kasuwa, da ƴaƴan masu hannu da shuni. Unguwa ce da tayi fice sosai gurin samun duk wani nau'in kayan maye da ake buƙata, cikin ƙanƙanin lokaci GIDAN GALAR MADAM MARY ya samu mugun karɓuwa fiye da yadda tayi tsammani, ta ko wane fanni na sana'ar gidan, abinci, drinks, rawa tana da ma'aikata fiye da mutane goma. Aiki ake zuwa nema a gidan kamar yadda ake zuwa neman aikin gwamnati, dan ita ma sai mutum yana kwalin karatu mai kyau da hanyan na sama a gidan, kuma idan Bibi ta yaba da ƙwazon mutum sannan za ta duba in ka cancanta ta ɗauke ka da kyakkyawan albashi dubu talatin ko sama da haka, ya danganta da yanayin aikin da mutum zaiyi mata. A daddafe ta sa Bibi makaranta mai shegen tsada ta ci gaba da karatunta har ta kammala Secondry, ta fito da mafi kyawun sakamako. Tun daga nan ta sa almakashi ta datse karatun, ta kaita gurin koyon rawa na musamman aka koya mata zafafan rawa da iya murguɗa duk wani komaɗo da lungu da saƙo na jikinta, a ƙarshe bayan ta ƙware sosai ta maida ita shugabar ƴan matan da suke rawa a gidan, nan da nan kuwa ta ƙara janyo manyan kwastomomi ƴaƴan masu kuɗi da su kansu masu ƙumban susan, dan idan Bibi tana rawa duk wani mai kallonta shagaltuwa yake yi, basa ji basa gani sai ita da tsananin sha'awarta dan tsananin gwanancewarta. Shi yasa duk ranar da zata yi rawa cika da tumbatsar da gidan yake yi daban ne da na kullum. ****** ****** "Oyoyo Madam Mary" Ta faɗa tana sauke tattausar murmushi kamar ba ita ba. Wani sabon takaicin ne ya sake ƙume ta, ƙoƙarin murmushi tayi da kumburraren fuskarta ta ci gaba da ɗingishi tana takawa zuwa cikin falon, jikinta babu inda baya ciwo saboda tsamin da jikinta yayi. "Bibi ta" Ta faɗa har lokacin murmushin bai bar fuskarta ba. Gimtse dariyar da ya taho mata tayi, ta ajiye kofin tea da yake hannunta da sassarfa ta ƙarasa gurinsu ta rungume Madam. "Jiya nayi kewarku, duk gidan ba daɗi saboda rashinku." "Ayya... muma haka Bibi, bari in watsa ruwan zafi duk jikina ciwo yake min." Ta zame jikinta a hankali duk zuciyarta a ƙuntace ta nufi saman Benen, suma Liyat babu wacce ta tsaya a gurin, ɗakunansu suka nufa duk suna ɗingishi dan gasa jikkunansu, a zukatansu bama-baman tsinuwa kawai suke saukewa Bibin, dan sun tabbatar duk ita ce silar wannan uwar wahalar da suka sha daga daren jiya zuwa yau. "Ammm Madam..." Sai kuma tayi shiru ta ci gaba da takawa a hankali zuwa inda ta ajiye kofin tea ɗin, kamar ba ita ce ta fara maganar ba ta ci gaba da kurɓar tea ɗin a hankali tana ta hurga idanunta a lungu da saƙo na falon ta share Madam da tayi poster a saman benen tana jiran jin me zata ce. "Uhmm! ina jinki Bibi" Ta faɗa a ƙagauce bayan ta sauke wani nannauyan numfashi. "Ummm na ce kafin ki gargasa jikin ko zaki kira ma'aikata su gyara gurin can? na leƙa na ga ɓarnar da aka yi jiya ba kaɗan bane, a taƙaice dai gurin bashi ma da ko kyan gani. A gyara da wuri a tari galar yau ko? Nima na gama shiryawa" Murmushin yaƙe wanda bahaushe ya ce ya fi kuka ciwo ta yi, ta taka a hankali ta dawo da baya har ta ƙarasa kusa da ita ta tsaya, ta kalle ta fuskarta ɗauke da wani irin yanayi na ƙoƙarin danne ƙuncin da yake danƙare a zuciyarta, a hankali ta fara magana kamar ba ta cikin damuwa. "Ki huta abinki kawai Bibita. Saboda abinda ya faru jiya da har ya jawo rasa ran mutane biyu da mutane talatin marassa lafiya, DPO ya bada umarnin in dakatar da duk wasu harkoki da nake yi a gidannan har zuwa nan da wata ɗaya. Kuma duk waɗanda aka raunata ni zan ɗauki nauyin maganinsu da duk wani abu da zasu buƙata har zuwa lokacin da za a sallamesu daga asibiti. To duk wannan ba wani abin damuwa bane, Mu ci gaba da jin daɗinmu kawai, kafin wata ɗayan ya cika a hankali zamu ƙara ƙayata wajen fiye da yadda yake a baya, kin gane?" Ɗaga kai kawai tayi alamun ta fahimta, a sace take kallon Madam ɗin har fara tattaka matattakalar tana ɗingisawa zuwa ɗakinta da yake saman Benen. "Madam wai sun duke ku ne?" Ta sake dakatar da ita da tambayar tana dariya ƙasa ƙasa. Tagwayen tsaki take ta ja a zuciyarta, tayi banza da ita kamar bata ji tambayar ba ta cigaba da nufar inda tasa gaba. "Madam..." "Basu dake mu ba Bibi, amma mun kwana a takure a zaune cikin cell, ga azaba ta manyan saurayen da sukai ta bidiri bireɗe akan naman jikinmu, bayan duhu da tsananin sanyin da muka kwana a ciki. Da wannan dalilin yasa duk jikinmu ba inda ba ya ciwo har zuwa lokacin da DPO Peter ya iso ya bada umarnin a sallame mu bayan ya kafa min waɗannan sharuɗɗan. Dan Allah Bibi ki kyale ni, ko zan iya shiga inyi wankan?" Ta katse ta da maganganun cikin zafin ran da take ta yunƙurin dannewa. "Madallah, ba laifi, Hakan yana da kyau. Ki je kawai." Sai kuma ta ja wani dogon tsaki ta dangwarar da kofin hannunta ta fice daga falon zuwa harabar gidan. Itama bata jira komai ba ta shige ɗakinta, nannauyar ajiyar zuciya ta sauke lokacin da tayi arba da makeken gadonta, a zuciyarta take saƙe-saƙen me ma ya kamata ta fara yi a farko? Gargasa jiki da ruwan zafi, wanka, bacci ko cin abinci? Daga ƙarshe dai ta faɗa banɗaki bayan ta tsayar da shawarar yin barci a ƙarshe. ****** ******* "Me kake cewa ne Yusuf? Sam ban fahimce ka ba. Ta ya za a ce an rasa kaya a gurin mutanen nan? yanzu kana nufin har Alhaji Barazana baisa baki sun baka kayan ba?" Ya ƙarasa maganar cikin damuwa yana ƙoƙarin zama a kan kujerar. "Ƙwarai kuwa Yallaɓai, wallahi duk yadda kake tunanin al'amarin ya wuce nan. Wani irin zazzafar doka shugabannin suka kafa ma sauran ƙananun ƴan kasuwan na duk wanda aka kama ya fitar da kaya ko rabin buhu ne ba tare da farashin ya tashi sosai zuwa yadda suke buƙata ba tara ne mai tsanani a kan mutum. Kuma ka san bara duk manoman sun faɗi warwas irin muguwar faɗin da basu taɓa tsammani ba, shi yasa yanzu suka ja tsayin daka baza su saki kayan ba sai farashi ya haura aƙalla zuwa ashirin da biyar..." "Kai ! Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un. Wannan wani irin mugun ƙari ne har na dubu sha uku a lokaci ɗaya? mu nawa muke saida kayan?" Ya katse mai maganar ta can ɗaya ɓangaren cikin matsananciyar damuwa, bai jira ya ci gaba ba ya ce "To yanzu dai ya kake ganin za a yi? menene mafita da hanyar ɓullewa? kasan dai dole muna buƙatar kayannan ko da babu yawa tunda har muka yi saken da ya ja baya sosai a gurinmu. Amma kun shiga har maraban walijo duk babu kaya?" "Duk bakinsu ɗaya fa Yallaɓai, ƴan kasuwan gaba ɗaya suna bin umarnin dokar nan. Tunanin da muke yi ko zaka shigo da kanka ne kuyi magana da Alhaji Barazana tunda shi ne shugaban ƴan kasuwan? ina ga idan aka yi haka ko bamu samu kayan da yawa ba za mu samu kaɗan, kuma ko sunyi mana ƙarin kuɗi zasu sassauta farashin saboda ganin idanunka da kuma daɗewar da aka yi ana cinikayya a tsakani." "Ok! To ina ga hakan za a yi. Gobe juma'a ko? asabar da sassafe in Allah ya yarda zan taso da wuri." Da haka suka yi sallama ko wa ya katse wayar, tallabe kansa yayi da yake tsananin sara masa kamar zai faɗo, sai a lokacin ya lura da zamanta can gefe ɗaya, tana ta cika da batsewa da huci ita kaɗai kamar zata yi bindiga. "Sannu da zuwa." Tayi maganar a kumbure. Lumshe kyawawan idanunsa yayi yana hamdala a zuciyarsa. 'Ɗan Adam ba ya rabuwa da matsala daga wannan sai wancan' Tunanin da yake yi kenan a ransa. Bai amsa sannun ba sai kawai ya miƙa mata hannu alamar tazo gare shi. Jan fasali da hura hanci ta ci gaba da yi kamar baza ta amsa kiran ba, sai kuma ta miƙe tana yauƙi ta isa gurinshi ta tsaya ɗan nesa kaɗan da shi. "Ga ni" Ko kafin ta rufe baki yasa hannu ya janyo ta gaba ɗaya ta faɗo jikinsa, za ta fara zille-zille ya riƙe ta sosai ya gyara mata zama a kan cinyoyinsa, yadda take kumbura baki ita a dole har lokacin fushi take yi shi ne abinda ya ba shi dariya ya kasa dannewa har saida ya murmusa. Hakan ya ƙara ƙular da ita ta ci gaba da yunƙurin tashi daga jikinsa amma ko gezau bata yi ba dan riƙon da yayi mata ba na wasa bane, sake tunawa da abinda ya faru a jiyan yasa kawai ta fara hawaye. "Kuka kuma? Amma ba nayi maganin wannan damuwar ba?" Yayi maganar a tausashe yana ƙoƙarin ɗago fuskarta dan su haɗa ido. "Honey jiyan fa..." Ba zato ba tsammani kawai ta ji bakinsa cikin nata yana aika mata da wani sassanyar salon kiss mai mugun daɗi da kwantar da hankali, hakan shi ya kashe bakinta da jikinsa gaba ɗaya, ya hana ta ƙarasa abinda tayi niyyar faɗa, tun tana turjewa har ta bada kai bori ya hau ta fara mayar masa da martani. "Bana son kina damuwa a kan abinda bai kai ya kawo ba kinji Honey? ko kina so ciwo ya kama min ke?" Yayi tambayar yana riƙe fuskarta da hannunsa biyu, yana ta sakar mata tattausan murmushi mai kashe zuciya. Girgiza kanta kawai tayi alamar a'a. "To ki bar damuwa, komai ya wuce. Ba na son nacin magana, Allah yana tare da masu haƙuri." "Tam! ya wuce." Ta amsa da sanyin murya tana ƙara lafewa a kan ƙirjinsa. Ɗan kwalin kanta ne ya zame yiri-yirin kitsonta suka bayyana. Shafa kitson ya fara yi yana bata labarin tafiyar gaggawa da ta kama shi zuwa Kacia jibi da safe. "Ni dai Honey sam bana son kana yawan zuwa kudancin kadunan nan, su baza su iya shawo kan matsalar bane har sai ka je?" Yayi ƴar dariya kawai, shi kanshi ba son tafiyar yake yi ba, amma ta kama mishi kamar dole ne yaje, kaya sunyi ƙasa sosai a shagunansu, sakankancewar da suka yi a ko wane lokaci za a iya samun kayan yasa ya saida Buhu ɗari wa Alhaji Baballe, ga shi tun ba a je ko ina ba sun fara nema. "Ba daɗewa zanyi ba, idan na samu yadda nake so kwana ɗaya ma kacal zanyi..." Siririyar sallamar da Surayya tayi da cusa kanta cikin falon yasa ya tsaida maganar da yake yi, shi kaɗai ya amsa sallamar ita kuwa Rabi ƙara narkewa tayi a jikinsa tana sake ƙwaƙume shi. Ita kuma ganin yanayin yadda suke yasa ta juya da sauri da nufin komawa inda ta fito, ranta banda tafarfasa babu abinda yake yi saboda tsananin kishi, nan take ta fara saƙe-saƙen da ta san a halin da za ta tarar da su kenan da bata shigo ba. "Madam bismillah mana, ina za ki je kuma?" Ya tambayeta bayan ya fahimci abinda take ƙoƙarin yi. Murmushi ta ƙawata fuskarta da shi sannan ta juyo ta kalle su, ta kalli fuskarsa ta kalli hannunsa da yake shafa gashin kan Rabi, shi baima san me take kallo ba ya ci gaba da abinda yake yi, bisa ga dukkan alamu sosai yake jin daɗin haka, ita kuwa Rabi tayi luf kamar ƴar kyanwa, har wani lumshe ido take yi dan tsananin jin daɗi, zuciyarta cike fal da farin ciki. Har wani tunani take yi a ranta 'Anya akwai abinda yafi miji ya nuna yana tattalin mace a gaban kishiyarta daɗi?' Rai fes sunan wani zani, a ɓoye sai doka murmushi take yi. "Ƴallaɓai dama gani nayi ka dawo baka fito ka duba ni ba kamar yadda ka sabawa duk wacce ba ta da girki, shi yasa na shigo in duba Allah yasa dai lafiya." Ta ƙarasa maganar a hankali, a sace kuwa gallawa Rabi wata muguwar harara tayi kamar idanunta zasu faɗo, tayi ƙwafa a hankali yadda ba wanda zai jiyo ta. "Lafiya ƙalau ne fa, na shigo ina waya da Yusuf, bayan na gama kuma ƙanwarki ta tsare ni da shagwaɓarta. Afuwan Sweetheart, bari inyi wanka ga ni nan fitowa. Kin yini lafiya ko? ya jikinki?" "Lfy kalau, da sauƙi, a fito lafiya Yallaɓai. Bari in jira fitowarku a falo..." "Baby muje in taya ka wankan" Ta faɗa a shagwaɓe tare da miƙewa tsaye, ta ja hannunsa suka shige cikin ɗaki ɗan ɓingilin sket ɗin jikinta ta ɗagawa, santala-santalan cinyoyin Rabin duk a waje. Shi kuwa kamar raƙumi da akala yake bin ta a baya, yana tafe yake amsawa Suraiya ba tare da ya waiga ya sake kallonta ba. "To Madam, sai na fito" Da sauri ta fice taja ƙofar da ƙarfi ta buga gam dan haushi, a jikin ƙofar ta tsaya dan jiran ko ɗaya daga cikinsu zai biyo jin ba'asin buga ƙofar da tayi sai ta ji shiru, cikin falon ta koma tana ta masifa ita kaɗai kamar taɓaɓɓiya. "Shegiya, da kwasassun ƙafafu kamar na agwaga, za ki gani in dai ni ce, ramuwar gayya zan miki da ta fi ta gayya zafi. Jarababbiya daga yin faɗa jiya har sun shirya yau dan tsananin fitina." Taja tsaki, ta sauke wani zazzafar huci ta baki kamar kububuwa, ta riƙe ƙugunta da hannu bibiyu tana safa da marwa a tsakiyar babban falon, daga ƙarshe ta zube kan kujera a kan kujera a kasalance kamar wacce aka naɗawa mugun duka, kishi sai nuƙurƙusarta yake yi, ba abinda take haskowa a ƙoƙon zuciyarta sai hoton miji kuma abin sonta Maheer tare da kishiya kuma maƙiyiyarta Rabi suna tsotse-tsotse da shafe-shafe a cikin bahon wanka. Lokacin ne taga yayi mata wani mugun tsawo saboda munanan saƙe-saƙen da zuciyarta yake mata. Shiru-shiru basu fito ba ta wuce ɓangarenta zuciya na ƙuna, idanunta ciccike da hawaye ta maida kofar falonta ta datse, har tana danna key saboda ko sun fito kar ma ya neme ta. Hannayensu sarƙe da juna kafaɗunsu na gogayya suka fito daga cikin ɗakin suna ƙyalƙyala dariya, sanye suke da ƙananun kaya na shan iska duk su biyun saboda yanayin zafi da garin yake ciki. suna zama akan dining table ɗin ya ce "Je ki yi wa Auntynki magana ta fito muci abinci." Ɗif ta ɗauke wuta, duk wani fara'ar fuskarta ya ɓace. Ɗan jim tayi kamar baza ta je ba sai kuma ta miƙe dan cika umarnin da yayi mata bayan ta tuna da halinsa na rashin son wargi, yanzunnan idan tayi wasa sai ya saɓa mata ya canza yanayin walwalar da suke ciki. "Honey?" Ya kira ta lokacin da har ta kusa ƙarasawa ƙofar ɗakin Surayyan, waigowa kawai tayi tana kallonsa. "Dawo ki zauna, bari inje da kaina. Na tuna ɗazu ko da na dawo ban shiga na duba halin da take ciki ba." Tsawon minti uku yana ƙwanƙwasa ƙofar amma ta ƙi buɗewa, kuma tana jinshi tayi biris da shi, da ya gaji sai ya koma ya zauna. "Ina ga tana banɗaki, mu jira ta minti biyu." Hira suka ci gaba da yi sama-sama suna zaman jiran fitowarta, ita kuwa tayi bulum-bukwui a cikin ɗaki kaman baza ta fito ba. "Honey ko inje in sake ƙwanƙwasa mata ƙofar?" Rabi ta tambaye shi tana kallon agogo ganin lokacin ya ja sosai har an kusa kiran sallah. Cikin sauri ya dakatar da ita. "No ƙyale ta kawai, idan na dawo sallah sai mu ci abincin na san zuwa lokacin ta gama abinda take yi." Sai da ta gama ɓata musu lokaci har aka fara kiraye-kirayen sallar isha'i a masallatan kusa da su sannan ta fito tana ɗingishi, fuskarta cakuɗe da yanayin ban tausayi, idanunta har da guntun ƙwallah ta ƙarasa kusa da su, ta fara magana a raunane. "Sweetat..." Sai kuma tayi shiru hawaye suka ɓalle mata shar-shar kaman an buɗe famfo. Gabanta ne ya faɗi, bata san me kuma za ta zo da shi ba, ita dai Allah ya sani har tsoron makircin Surayyan take yi. Tagumi tayi kawai tana kallo da saurarenta dan jin da wacce kuma ta zo yau. Ya kalle ta sama da ƙasa sheƙeƙe, yana ta ƙoƙarin danne ɓacin ranshi dan kar Rabi ta fahimta. Da ya rasa ta cewa sai kawai ya jefa mata tambayar "Lafiya?" "Santsi ne ya kwashe ni nayi muguwar zamewa a bayi, ka ga har na gurɗe ƙafata..." "Allah ya kyauta, sai ki nemi man zafi ki shafa. Idan kinso ki fito muci abinci bayan na dawo masallaci." Ya faɗa cikin rashin kulawa da ba maganarta muhimmanci, haka kawai yake ji zuciyarsa bai gamsu da gaske ta faɗi ba. Dan ma kar kukanta ya karya mishi zuciya sai ya shige banɗakin falon ya ɗauro alwala. "Honey na wuce masallaci." Ya faɗa idanunsa a kan Rabi, da ɗan murmushi a fuskarsa. "Tam ! A dawo lafiya Honey" Ta amsa ranta ƙal bayan tayi fari da idanunta, har bakin babban ƙofar falon ta raka shi sannan ta juya ciki dan sauke nata faralin, tana tafe tana karkaɗa ƙugu da satar kallon Surayya da tayi poster a inda take tsaye baki da hanci hangame, fuska duk hawayen makirci kamar mai shirin ɗaukar hoto. ****** ****** Maheer Abdulganiyyu Mai Anini ingarma kuma kyakkyawan matashi mai ji da samartaka ɗan kimanin shekaru talatin da uku. BILHAƘƘI Haifaffen unguwar rimi ne a cikin garin kaduna. Mahaifinsa Malam Abdulganiyyu da uwargidansa Hajiya Balaraba haifaffun jihar zamfara ne a ƙauyen Maru. Tun duniya na kwance aiki ya dawo da shi garin kaduna a lokacin bai daɗe da yin auren fari ba, dukda iyayensa basu so ba a dole dai suka haƙura ya tattara ya dawo garin kaduna. Tsawon zama a kaduna da gogayya da zallar hausawa yasa ko cikin maganarsu shi da matarsa sai jefi-jefi ake gane su zamfarawa ne. Ta ko wani fanni na ilmin boko da islamic gangaran ne, mutum ne da ko wani lokaci hannunsa a buɗe yake. Kuma babban malami ne a nan unguwar rimi da kewayenta. Ga shi da balaga ta iya wa'azi da iya nasiha wa al'umma, cikin hikima yake isar da saƙon Allah da fiyayyen halitta SAW, da waɗannan dalilan yasa al'umma suke matuƙar ƙaunarsa da ganin girmansa. Shekaransu uku a kaduna Allah ya albarkace su da samun haihuwar Maheer, nan da nan kuma sai haihuwar ta buɗe musu dan shekara ɗaya da rabi tsakani Balaraba ta haifi ƙanwarsa Shafa'atu, Lukman ya biyo bayanta shekara ɗaya da wata takwas tsakani, daga nan kuma sai haihuwar ta tsaya cik! Ba sa jimawa sosai basu je mahaifarsu sun gaida iyayensu da sauran dangi ba, duk wani abu da zai faru na jaje ko na murna suna tafe shi da iyalansa. Amma sam baya daɗewa saboda aikinsa. Shekarun Lukman uku a duniya Malam Abdulganiyyu ya ƙara auren wata bazaura mai suna Salamatu, a zahirin gaskiya sadakarta mahaifinta ya ba shi amma ko da wasa bai taɓa furtawa Balaraba sadaka aka bashi ba, ba dan komai yayi hakan ba kuwa sai dan ya kare wa amaryar martabarta a idanun abokiyar zamanta da ƴaƴansa. Da yake tsayayyen namiji ne a tsakanin iyalansa kuma adalin miji da tsananin sa'ar da aka yi duk suna da hankali sai suka haɗe kansu sosai kamar ya da ƙanwa. Nan kuma haihuwa ta ƙara buɗe ƙofa a gidan suka fara yi a jejjere, Salamatu ta haifi huɗu, Mustapha, Saudat, Fahad, Faruk. Ita kuma Balaraba ta ƙara yara uku suka zama shida, Badiyya, Asma'u da ɗan auta Yunus. Tsananin haɗin kan da yake tsakanin iyalan gidan idan ba saninsu sosai aka yi ba babu yadda za a yi a gane ƴaƴan wannan ɗakin da ƴaƴan wancan ɗakin, yaran suna kiran Hajiya Balaraba da Ummee, ita kuma Hajiya Salamatu suna kiranta da Mummy. Maheer ya taso nutsassten yaro ne mai tsananin ƙwazo da son karatun boko da islamiyya. Mutane da dama a waje suna kiranshi da magajin Malam ne dan duk cikin ƴaƴan gidan shi ne ya ɗebo Malam sak kamar yayi kaki ya tofar. Kuma a fannin malanta ma shi ne dai ake ganin bisa ga dukkan alamu zai iya biyo Malam ɗin, dan yana shekaru goma sha biyu ya sauke Alƙur'ani mai girma, sauka ta gaske ba karatun zuƙu ba kuma ko a lokacin yana da haddar izufi goma sha biyar a kwanyarsa. Wani dabara da hikima da Malam ɗin yake yiwa duk yaransa shi ne sai sunyi nisa sosai a karatun addini sannan yake saka su a makarantar boko. (Wannan wata hikima da baiwa ce irinta Alƙur'ani mai girma. Insha Allah matuƙar yaro ya fara buɗe ƙwaƙwalwa da sanin alƙur'ani sosai kuma ya samu ƙwarewa a karatun Alƙur'anin duk wani karatu da zai biyo bayanta bi'iznillahi za ta zo da mugun sauƙi wa ƙwaƙwalwar yaro ko yarinyar. Wannan kaifiyyan ce an gwada an gani kuma an dace. Allah yasa mu dace) Yana da shekaru goma sha takwas cif ya amsa sunansa na Mahiru (Gangaran) a fagen karatun Alƙur'ani mai girma, ya haddace ta tsaf kuma yasan tafsirin duk ayoyinta, kuma karatunshi bai tsaya a nan ba sai da ya haɗa da haddar wasu ƙananun littattafan addini. A lokacin ne kuma alƙiblar karatun nasa ya nutsa cikin karatun boko gadan-gadan, a fagen karatun addinin ma ba tsayawa yayi ba, ci gaba yayi da neman ilimi lungu da sako na zaurukan malamai daban-daban, dukda haka dai babban malaminsa Mahaifinsa ne Malam Abdulganiyyu. A kance taura biyu ba sa taunuwa lokaci ɗaya amma ga Maheer ya haɗe biyun ya taune su tsaf ba tare da ya jigata ko ya galabaitar da haƙoransa ba. Haka suka ta so har girma shi da ƴan uwansa, kyawawa kuma nutsastsun yara masu cike da tarbiyya ababen koyi ga sauran yara, da rayuwa mai cike da nasara. Shafa'atu tana kammala secondry Malam ya aurar da ita ga ɗaya daga cikin ɗalibansa Nuhu, daman tun tana ƴar ƙanƙanuwa Nuhu yake son aurenta har ma yayi wa Malam ɗin magana. Aka yi sa'a kuma ita ma Shafan ko da ta girma bata watsa mishi ƙasa a ido ba, tana son shi. Har ta ƙare karatun aka yi auren cikin mutunta juna. Cike da nasara Maheer ya haɗa digirinsa na farko ya samu aiki a matatar ruwa da yake cikin garin kaduna. A lokacin kuma sai ƴan mata suka fara kawo mishi cafka ta ko wane ɓangare, a gefe guda kuma manyan aminan Malam guda biyu sun nuna sha'awar son haɗa shi aure da ƴaƴansu mata. Da yake baida wani zaɓi kuma ba shi da wacce yake so sai kawai ya barwa Malam ɗin zaɓin matar da ya ga ta dace da shi. Lokacin da Malam ya nemi shawaran matansa akan wacce suke ganin tafi dacewa da Maheer a cikin ƴan mata biyun Ummee Balaraba cewa tayi "Ga Mummynsu nan ita taya ka zaɓe, ni dai nawa addu'a da fatan tabbatuwar abinda ya fi alkhairi." "Ameen ya Allah. Kin gama magana." Malam ya amsa yana murmushi, fuskarsa baiyane da tsananin farin cikin furucin da tayi, daman ba ya hasashen samun matsala daga gare ta. "Ni dai in a son raina ne gaskiya na fi so ya auri Surayya ƴar gidan Malama Hauwa, yarinyar nan ta daɗe tana ƙaunarsa. Duk da kunya da aka san ɗiya mace da ita har ta kai ba ta zuwa gidannan sai ta tabbatar Maheer yana gari, soyayyar da take masa ba kaɗan bane. Kuma na ga tana da nagartattun halayen da ake buƙata ga duk matar aure. Amma dai duk shawarar da ka yanke mu masu biyayya ga umarninka ne Malam. Fatanmu zaɓin alkhairi kamar yadda Ummee ta ce." "Ma sha Allah ! Wannan ma hange ne mai kyau kika yi. Amma fa Alhaji Ghali shi ne wanda ya fara min maganar in dai Maheer bai tsaida wacce yake so ba yaje su daidaita da ƙanwarsa Rabi'a. Bayan kwana biyu kuma kamar haɗin baki shi ma Malam Hassan ya nemi in dai ba matsala ya ba Maheer sadakar Surayya..." "To tunda haka ne mai zai hana ya aure su duk su biyun? Namiji ai mijin mata huɗu ne." Mummy Salamatu ta katse Malam da murmushi fal a fuskarta. Daga wannan zancen kamar wasa auren zuƙa-zuƙan ƴan matan biyu ya tabbata ga Maheer cikin ƙanƙanin lokaci, amma fa duk su biyun babu wacce taso hakan, sosai kishi ke cin zukatansu. Dan Maheer zankaɗeɗen saurayi ne na nunawa tsara, irin mijin da duk wata mace zata so mallakarshi ita kaɗai. A dole dai duk suka danne kishinsu dan Maheer ya faɗa wa ko waccensu duk wacce baza ta iya zama da ƴar'uwarta sai dai ta haƙura da shi, duk su biyun sunyi mishi kuma su biyun zai aura. Aurenshi da Surayya aka fara ɗaurawa, bayan sati biyu aka ɗaura aurenshi da Rabi'a. Wani irin zama mai cike da drama suke bugawa a gidan domin an samu saɓanin halaye a tsakanin matan biyu, ita Surayya irin matan nan ne masu siffar munafurci da tsananin kissa da kisisina. A mafiyawancin lokuta da waɗannan halayen nata take gasawa Rabi gyaɗa a hannu, a gurin Maheer kuwa da yake ya fahimceta a baibai kallon mace mai tsananin ladabi da haƙuri yake yi mata, cikin hikima da waɗannan halayen take zurma Rabi a rami ita kuma ta ke ƙara siyo wa kanta martaba a gurinsa, ga tausayinta da yake yi dan mahaifinta malami ne mai ƙaramin ƙarfi saɓanin mahaifin Rabi da yake da arziki sosai. Ita kuwa Rabi zawayi ce, sam bata da haƙuri, in dai abu ya ɓata mata rai komai ƙanƙantarsa bata iya ɓoyewa sai ta baiyana. Ga zallar tsiya da masifa a cikinta kamar mai aljannu, sam bata iya munafurci da ɓoye-ɓoye ba. Waɗannan halayen nata yasa Maheer yake kallonta a mace fitinanniya mai tsananin mitar tsiya, wacce bata cika son zaman lafiya ba. Shi yasa a mafiyawancin lokuta idan suka yi rikici da Surayya kai tsaye ita yake ba laifi. Duk da waɗannan halayen nasu jajurtaccen namiji ne kuma tsayayye a gidansa, yana matuƙar ƙoƙarin sauke hakkin ko wacce daga cikinsu, ba ya taɓa fifita ɗaya akan ɗaya. Yana gwada musu soyayya sosai kamar auren soyayya ne a tsakaninsu ba auren haɗin iyaye ba. A bayan aikin gwamnati da yake yi Maheer babban ɗan kasuwa ne, bai dogara da aikinsa kaɗai ba, yana sha'awar kasuwanci sosai tun yana ƙaraminsa. Manyan shaguna biyu gare shi a kasuwar central da yake cikin garin kaduna, kayayyakin abinci irin na gida ake saidawa buhu-buhu, sosai kasuwancin ke gara mishi, yana samun alkhairi sosai fiye da yadda yake zato. Shi yasa duk yaran da suke mishi hidiman shagunan sosai yake fitar musu da hakkinsu, bai zama cinye du ba. Kamar wasa wata shekara da citta ya faɗi rugu-rugu babban yaronshi kuma abokinshi Yusuf ya bashi shawarar ko zasu siya su ajiye ne? bai ki shawararshi ba kuwa suka sai buhu ɗari biyu suka ajiye, ƴan watanni kaɗan aka nemi cittan aka rasa a kasuwa, suka saida akan farashi mai rahusa, dukda sauƙin da suka yi sun samu riba sosai da har ya kusa kamo uwar kuɗin. A wannan shekarar ya biya wa Malam da Ummee kujeran makka, da alƙawarin in dai yana raye bi'iznillahi shekara na zagayowa zai biya su tafi shi da Mummynsa. Tun daga wannan lokacin ya zama dilar saida citta, lungu da saƙo na garuruwan kudancin kaduna irinsu kachia, kubacca, walijo, maraban walijo da sauran kasuwannin ƙauyaku yake tura yaranshi su saro mishi buhunhunan citta. Tun manyan dillalan citta a kudancin kaduna basu san sunanshi ba har suka sanshi, ko bai tura yara ba za a aiko mishi da kaya gangariya yawan yadda yake buƙata har shagunanshi na kasuwa, shi kuma ya tura musu da kuɗaɗensu ta banki. Kamar wasa sai ya zamana daga lungu da saƙo na manyan jihohin arewacin nigeria ana zuwa siyan citta a gurinshi, dan ko ta yi wuya a kasuwa ba a rasa ta a gurinsu, kuma daidai gwargwado ba ya tsawwala riba, yana bada cittan akan farashin da wanda ya siya zai ji daɗi ya koma gobe. Da wannan dalilin yasa Allah yake saka mishi albarka a kasuwancinshi. A wancan shekaran da ta gabata citta ya faɗi warwas a kasuwa tun daga watan ɗaya har zuwa watan goma da sha ɗaya lokacin da ake haƙo sabuwar citta, ganin har lokacin darajar cittan bai ɗaga ba yasa manyan dillalan suka yi miting, dan wancan shekarar ba ƙaramar asara suka yi ba. Dokar ta ɓaci suka sanya a kan duk wanda aka kama ya fitar da citta ba tare da farashin ya ɗaga zuwa yadda suke so ba zai biya tara mai tsananin yawa, ɓoye ta suka yi daga tsohuwar har sabuwar aka neme ta ɓat aka rasa a kasuwa. Wannan dalilin ne yasa Maheer yin takakkiya da kanshi tun daga kaduna har garin kachia dan ya gana da manyan dillalan ko zasu rangwanta mishi farashin su bashi kaya yadda shi ma zai saida ya samu rabonshi. Ashe ƙaddara ce ta cillo shi kachia... ***** ****** ****** "Ƴallabai ciwon kan ne har yanzu?" Tsaki yayi ƙasa-ƙasa, ya sake lumshe idanunsa da suka ɗan canza launi kaɗan zuwa jajaye. "Wallahi kuwa Yusuf. Ka san tun ɗazu da na kwanta da niyyar baccin sam na kasa yi? daman tun shekaran jiya da yamma naji kan ya fara sara min amma baiyi tsananin haka ba, da na yi barci ma sai na daina jin ciwon kan. Ina ga yau dan ya haɗu da doguwar tafiyar da nayi ne" "To ko dai zamu je kaga likita? tunda Alhaji Barazanan ya ce sai zuwa dare zai shigo." "Ok ! ina ganin dole hakan za a yi, bari in ɗan watsa ruwa tukunna, sai mu sha iska ma daga can." Yana shirin shiga banɗakin kira ya shigo cikin wayarsa, a hankali ya duba fuskar wayar dan ganin mai kiran, Surayya ce. Bai ɗauka ba ya shige bayin ya bar wayar a kan gadon. Yusuf ma fita yayi zuwa gurin sauran abokan tafiyarsa dan ya bashi damar shiryawa a nutse. Kafin ya fito daga wankan a jejjere saƙonni har huɗu Surayya ta tura mishi duk na ban haƙuri, da addu'ar Allah ya huci zuciyarsa. Ta gane kuskurenta, in Allah ya yarda baza ta sake ba. Yadda ya karanta haka ya aje wayar ko reply ɗaya baiyi mata ba, ya canza shiga cikin wani yadi ruwan madara mai tsananin kyau, ɗinkin tinibu da aka yiwa yadin ya ƙara fito da kyan kayan a jikinshi, sosai kayan ya ƙara fito da kyawunshi kamar ɗan ashirin da biyar. Ya miƙawa Yusuf makullin motar suka fice daga ɗakin. Nan da nan suka isa asibitin da yake ba nisa sosai da ɗakin Otal ɗin da suka yi masauki, babban asibiti ne na gwamnati. Babu laifi ko wane lokaci ba a rasa likita a asibitin, da yake yamma ne mutane sunyi sauki bayan sun yanki kati mutane uku suka jira kafin layi ya zo kansu. A daidai wannan lokacin kuma Bibi da Madam Mary suna tsaye kan gadon da aka kwantar da Rose, tana ta jan numfarfashi sama-sama cikin mawuyacin hali, sai sannu suke jera mata kamar za su ari baki. "Bibi kinga har yanzu numfashinta bai daidaita ba kamar yadda nose ɗinnan ta ce, yi sauri ki kira likita kawai kar ki saurari nose ɗinnan." Ko kafin ta rufe baki ta fice daga ɗakin da sassarfa dan kiran likita kamar yadda Madam ta umarceta. "Ke ke ina zaki je?" Ɗaya daga cikin noses ɗin ta tare ta da sauri tana tambayarta ganin ta nufi ofishin likita gadan-gadan. Wani kallon ke a suwa ta watsa mata, ta buɗe baki daƙyar kamar anyi mata dole ta ce "Dr. zan kira..." "Ki ɗan jira shi minti biyu, yanzu yana wani mare lafiyan ne..." Ko kafin ta gama maganar cikin laƙaiƙaita da yanga Bibi har ta kai ƙofar ofis ɗin likitan, ta murɗa handle ɗin ƙofar tana niyyar cusa kai cikin ofis ɗin take magana cikin masifa "Ta mu mare lafiyar tana cikin wani yanayi kike min zancen wani? ciwo ai baifi ciwo ba..." Kamar wacce lantarki ya ja ko kuma wacce ta taka ɓawon ayaba ba zato ba tsammani ta tafi suu sai a kan ƙirjinshi a daidai lokacin da shi ma yake ƙoƙarin fitowa daga ofis ɗin, hannunshi riƙe da wayarshi ƙirar Samsung. Kirjinshi ne ya buga dam ! ya sake wayar a ƙasa da sauri ya tallafeta ganin tana ƙoƙarin zamewa ta faɗi ƙasa warwas! "Subhanallahi ! hankali dai, ba kya gani ne?" Tattausan muryarsa da yake fita a hankali ya daki dodon kunnenta. A zabure cike da tsoro ta ɗaga kanta daga jikinsa ta ja da baya a ɗimauce. Ta sake kallonsa a gigice, abu ne da bai taɓa faruwa da ita ba kwanciya a jikin wani namiji. Wasu ababe masu kama da kibau ne suka fito daga cikin kyawawan idanunsa suka cake ta a ƙahon zuci dai-dai saitin ɓangaren dama. "Sorry... I'm very sorry pls." Ta faɗa cikin rawar murya. Shi ma a ruɗen yake, idanunshi na kanta ya tsugunna ƙasa dan ɗaukar wayarsa, a daidai lokacin ita ma tayi ƙasa dan ɗaukar tata wayar da ƙaramar jakarta da suka zube a ƙasa. Hannayensu ne suka sake gogar na juna sai suka janye da saurin gaske kamar shokin ne ya jasu, idanunsu na cikin na juna. Yana samun nasarar ɗaukar wayarsa da sauri ya zagaye Nose ɗin da ta biyo bayan Bibi dan dakatar da ita ya fice daga ofis ɗin, bai sake yarda ya haɗa ido da ita ba. Itama gurin likitan ta ƙarasa da sassarfa da ya saki baki da hanci buɗe yana abinda yake faruwa kamar a fim ta fara magana cikin rawar murya, ƙirjinta sai bugun tara-tara yake yi. "Dr. Rose tana cikin wani hali, numfarfashi take yi sama-sama..." Bai ce komai ba, ko kafin ta aje numfashi kayan aikinshi kawai ya kwasa ya fice da sauri suka bi bayanshi ita da Nose ɗin. Tsawon wasu mintuna likita da Noses uku ne a kan Rose suna ta iya ƙoƙarinsu dan daidaita numfashinta. BILHAƘƘI Daƙyar suka samu nasarar daidaita al'amarin, numfashinta ya koma yana sauka kamar yadda ake buƙata. Suka sake gyara zaman ƙarin ruwan da yake ɗaure a hannunta, sannan suka fice daga ɗakin likitan ya haɗa zufa sharkaf. Madam Mary da take tsaye a ƙofar ɗakin hannayenta naɗe a ƙirji babu abinda take yi sai tsiyayar hawaye. Duk cikin yaranta tana bala'in son Rose, ƴar uwarta ce, mahaifiyar Rose ƙanwar mamanta ce. Sosai take yi mata biyayya da aikata duk abinda take so, shi yasa take matukar jin daɗin aiki da ita. Duk cikin ƴan matan gidan bayan Bibi Rose ce ta ba muƙami kamar shugabansu, duk abinda Bibi tace za ta yi idan ta canza shawarar yi Rose ce take hawa a makwafinta dukda ba a samun abinda ake so kamar Bibin amma tana iya ƙoƙarinta wajen ƙayata abin. Idan ta mutu bata san yadda zata yi ba. Ganin fitowar likita yasa ta sha gabansa da sauri fuskarta na baiyana matsanancin tashin hankali. "Likita yaya? Ya jikin nata?" Tayi maganar da rawar murya, hawaye wasu na korar wasu a fuskarta. Ya goge zufan goshinsa da wani farin hanki da yake riƙe a hannunsa, ya kalleta da ɗan murmushi a fuskarsa. "Is ok! komai ya daidaita. Za ku iya shiga ku ganta, amma banda hayaniya pls" Daga haka bai ƙara komai ba ya wuce ya barta da sassarfa, sauran Noses ɗin suka rufa masa baya a hanzarce. Tsananin damuwa da ruɗanin da take ciki yasa ta manta tare da Bibi suke tsaye, bata ko kalli inda take tsaye kamar mutum mutumi ba ta shige ɗakin da Rose take kwance da sauri dan ganin halin da take ciki, zuciyarta cike da addu'a da fatan samun sauƙi a gare ta. Tunani da saƙe-saƙe kala daban daban ne a ranta har bata san Madam ta shiga ciki ba, wani irin shauƙi take ji a zuciya da gangar jikinta, irin shauƙin da tunda uwarta ta haifeta bata taɓa jin irinsa ba. Tana tuna yadda ya tallabota jikinsa sai taji ƙirjinta yana luguden daka, yanayin ya kasa ɓacewa daga ranta. Babu abinda take ji a ranta tana so a yanzu da take tsaye irin ta sake jin tattausan muryarsa, ta sake tozali da kyakkyawar fuskarsa, ta sake haɗa jiki da tattausan jikinsa mai tsananin ƙamshin daɗi. Ita kawai komai na shi yayi mata, a kallon farko ta ji ya bala'in burgeta. Sai wani yuyu yake mata a duk wani lungu da saƙo na zuciyarta. Runtse ido tayi ta shaƙi daddaɗan ƙamshin jikinsa da ya gauraye da tattausan ƙamshin turaren jikinta. "Waye shi?" Tayi maganar a fili tana huhhurga idanunta lungu da saƙo na harabar gurin kamar za ta sake ganinshi, ko alamunshi bata gani ba, sai noses da masu jinya da suke wuceta lokaci bayan lokaci. Ta daɗe tsaye a gurin tana tunani, daƙyar taja sanyayyun ƙafafunta ta shiga cikin ɗakin dan ganin halin da Rose take ciki, ita bata san ma lokacin da likitan ya fita ba. Saboda yanayin da take ji a jikinta bata jira Madam ba ta karɓi makullin motar da suka taho da ita ta koma gida, sai rawar ɗari take yi kamar wacce zazzaɓi yake neman kamawa. Duk tunaninta ya tattara ne a inda zata sake gano wannan mutumi. ****** ****** Shi kam bai tantance wani yanayi yake ji game da ita ba har ya sai magungunan da aka rubuta masa suka bar cikin asibin. Cikin hikima ta Ubangiji tun kafin yasha magungunan ya nemi ciwon kan ya rasa, ko da ya faɗawa Yusuf kan ya daina ciwo godiya sukai ta yi ga Ubangiji mai yadda yaso a lokacin da ya so. "Amma dai dukda haka kar ka fasa shan maganin." "Eh daman dole zan sha. Ina ga mu koma Otal ɗinnan kawai na ga gaf ake da kiran sallar magrib, idan mun idar sai in kira Alhaji Barazana inji ko ya dawo." Ya ƙarasa maganar yana sake gyara kwanciyarsa a jikin kujeran mai zaman banza, shi kuma Yusuf yana tuƙa motar. Kafin ya amsa shi kiran waya ya shigo cikin wayarsa, da yake wayar tana aljihun gaban rigarsa ne sai ya rage gudun motar ya zaro wayar. "Kaga Alhajin ne ma yake kira na, kila ya nemi lambarka bata shiga ba." Ya ƙarasa maganar tare da danna madannin amsa kira ganin yana gaf da tsinkewa, buɗe sipikar wayar yayi dan duk su biyun suji abinda zai faɗa daga can ɓangaren. "Ka faɗawa Alhaji Maheer don Allah yayi haƙuri, duk yadda naso in shigo yau bazan samu shigowa ba. Amma in Allah ya yarda gobe zan shigo da yamma, wani muhimmin al'amari ne ya taso min a nan ɗin wallahi. Na kira wayarsa in bashi haƙuri kuma wata yarinya ce ta ɗauka." Ƙit kiran ya katse daga can ɓangaren ba tare da an jira amsawar shi ba. "Kash ! Amma na so ƙwarai gobe inyi sammakon komawa gida wallahi, amma ba damuwa, Allah ya kaimu goben. Ubangiji yasa hakan shi yafi alkhairi." Ya faɗa yana lumshe idanunsa. "Ameen Yallaɓai..." "Ji nayi kamar ya ce ya kira wayata wata yarinya ta ɗauka ko?" Ya tambayi Yusuf fuskarsa cike da mamaki sannan ya zaro wayarsa a aljihu. Kirjinshi ne ya buga dam! a kallon farko ya gane wannan sam ba wayarsa bace, irin tasa ce dai sak amma ita wannan an saka mata riga mai masifar kyau da ɗaukar hankali irin na mata. Jujjuya wayar ya ci gaba da yi yana tunanin aɗan fitar nan da suka yi zuwa asibiti a ina ne har yayi canjin waya da wata? "Wannan ai ba wayata ba ce." Ya faɗa hankalinsa akan Yusuf kamar mai neman ƙarin bayani. "Tooo... subhanallahi. Ta ya akayi hakan ta faru Yallaɓai? Ashe da gaske an kira lambar taka wata ta ɗauka. To ina ga wacce kuka yi musaya da ita ne." Yayi maganar tare da gangarawa da motar gefen titi, kashewa yayi kafin su yanke shawarar abinyi tsakanin juyawa inda suka fito dan cigiyar mai wayar ko kuma ci gaba da tafiya zuwa inda suka nufa? Shiru yayi zuciyarsa cike da tunanin inda aka haihu a ragaya. Da ya rasa tunawa sai kawai ya danna madannin kunna wayar, sai a lokacin ya fahimci wayar ma a kashe take. Bayan tsawon minti ɗaya da kunna wayar ɗanɗasheshen hotonta ne ya baiyana a fuskar wayar tana dariya. Tayi kyau sosai kamar wata zara a cikin taurari, ga tsananin ɗaukuwa da hoton yayi kamar a kirata ta amsa, zallar ƙuruciyarta baiyane a fuskarta ta cikin hoton. "Zillaziyya" Yusuf yayi maganar a zuci ba tare da sanin a fili yayi ba, da ya ƙara kallonta sai kuma ya sauke wani nannauyar ajiyar zuciya yana yabawa Ubangiji sarkin ƙawata halitta. "Sunanta kenan?" Ya tambaye shi yana wani basarwa, idanunshi na kan hoton shi ma yana sake ƙare mata kallo. "Wa ɗin?" "Ita na jikin hoton mana, na ji kace Zilliya-zilliya" "A'a ni bansan sunanta ba, zallar kyau dai na gani da ƙuruciya, shi yasa na kira ta da hakan." Yusuf ya amsa da murmushi a fuskarsa. Ya taɓe baki, har lokacin idonsa na kan hoton, da hasken wayar ya ɗauke sai ya danna ya ci gaba da ƙare mata kallo. "Muje kawai, ka ji can nesa ana kiran sallah. Na gane yarinyar, ɗazu a ofis ɗin likitan nan muka yi karo da ita. Na san ita ma za ta kira dan ta karɓi wayarta, gobe in Allah ya kaimu sai ka kai mata ka amso min tawa wayar." Da wannan maganar yaja motar suka ci gaba da tafiya zuwa masaukinsu. A can ɓangarenta lokacin da ta fahimci sunyi canjen waya ba tare da saninsu ba wani sakaran murmushi ne ya suɓuce mata. "Waww!" Ta faɗa a fili kamar taɓaɓɓiya kuma sai ta fara ƙyalƙyala dariya tana madungure a kan gadon dan tsabar murna. Da ta gaji wayar ta tasa a gaba ta zurawa ido, hannayenta duk biyun dafe da ƙuncinta, fuskarta cike da murmushi. 'Ashe dai zan sake ganinsa? Oh my God wannan gayen ya haɗu wallahi, ohh Allah ni ina son shi ma... wallahi ina son shi. Kai !? wai da gaske sonshi nake yi? tabbas wannan so ne duk da ban taɓa yin so ba ina gani a fina-finai.' Ita da zuciyarta take ta zancen zuci tana dariya. Daga ƙarshe ma falo ta koma ta ƙure sauti sosai cikin waƙar Me and you again ta fara taka rawa tana lanƙwasa kamar zata karye. Sauran ƴan mata da ma'aikatan gidan da sun leƙo falon dan yin masifan sautin da aka ƙure bayan jimamin da suke ciki na halin da marassa lafiyarsu suke ciki suna haɗa ido da ita sum-sum suke juyawa zuwa ɗakunansu. Gaba ma da gabanta ai, Madam ma kanta lallaɓa Bibi take yi balle su karan kaɗa miya, yanzunnan in ta sa ma mutum ido sai duniyar warwala da jin daɗinsa ta dagule. Sai da ta gama sharafi da nishaɗinta ta gaji sannan ta tattara ta koma ɗakin Madam a sama, tayi ɗaiɗai a kan gadon ta zubawa wayar idanu, zuciyarta cike da tunaninsa. Ƙarfe goma sha ɗaya dai-dai na dare kira ya shigo cikin wayar, da sauri ta kaiwa wayar raruma kamar shi ne a gabanta ba wayar ba. Bata tsaya duba lambar ba ta danna madannin amsa kiran ta kara a kunnenta, shiru tayi tana sauke numfashi a hankali bata yi magana ba, a can ɓangaren shi ma sai yayi shiru yana saurarenta. Ɗan gyaran murya yayi ita kuma a hankali ta buɗe baki ta ce "Na'am" "Me kika ce?" Ya tambayeta da mamaki. "Oh sai naji kamar ka kira sunana." Ta faɗa a hankali. Sake gyara kwanciyarsa yayi a kan gadon, ya lumshe idanunsa. Wani iri yake ta ji a jikinsa kamar ana mishi tafiyar tsutsa. "Na kira sunanki na ce me?" Yayi maganar yana sake ƙasa da muryarsa kamar wanda ya fara bacci. "Ji nayi kamar ka ce Bi....bi" Tayi maganar da wani irin salo mai kama da na shagwaɓaɓɓun yara. "Uhmmm!" Yaja ajiyar zuciya ya sauke. Bai jira cewarta ba ya ci gaba "Kawai ɗazu kuma sai kika ɗauken wayata ko?" "Laaaah... ni ce ma na ɗauke maka taka wayar? kaine fa ka fara ɗaukar tawa baka sani ba" Ta faɗa a sanyaye, sai yaji kamar ma zatayi kuka. Haka kawai yaji yana son janta da hira, ya kuma rasa dalilin da yasa hakan. "To yanzu dai ya za a yi? kinga dai ni baƙo ne a garin. Ya za ayi ki bani wayata?" "Kai kana ina ne? Sai in kawo maka ko yanzu in kana so" Agogon bangon da yake maƙale a sama ya kalla, sha ɗaya da minti goma. "Ke yanzu zaki iya fitowa a darennan?" "Eh mana. Ai dare bai wani yi ba" Ta amsa kai tsaye, a muryarta ya gane zallar gaskiya ce a maganarta. "Kuma har sai a barki ki fito a gida?" Yayi mata tambayar muryarsa na baiyana zallar mamaki. "Eh mana. Kana ina ne?" "Ina Garuje hotel, ɗaki na 102" Yana gama faɗa mata ƙit ya katse wayar yana dariyar shirmenta a ransa, bai taɓa ɗaukar da gaske take za ta iya fitowa a wannan daren ta kawo masa wayar ba, sai da yaji ana kiran wayar tarhon da yake cikin ɗakin. "Oga kana da baƙuwa fa, sunanta Bibi. Ka san da zuwanta?" "Eh." Ya amsa a mamakance. Ko kafin ya ƙara wata magana har an ajiye wayar daga can ɓangaren. Rigarsa ya saka yana ƙoƙarin sauka ƙasa ya tare ta kawai yaji ana ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin, yana buɗewa kyakkyawan murmushinta ne ya fara mishi maraba. "Hi" Ta faɗa da zazzaƙar muryarta haɗe da karkaɗa mishi yatsu biyu. Yana ta tattare hanya dan kar ta shiga ɗakin ganin irin shigar da yake jikinta na kayan barci, ita kuma sai cusa kanta take yi dole ya kauce ya bata guri ta shiga ciki. "Daman da gaske kike yi?" "ƙarewar gaskiya ga tabbaci ka gani" Jinjina kai kawai yayi alamun hakane. Kan gadon ya ƙarasa ya ɗauko wayarta ya miƙa mata. "Ga wayarki, bani tawa kiyi hanzarin tafiya gida. Ke ko tsoro ma bakya ji? ki fito a tsakar daren nan ba tare da rakiyar wani ba?" Sai kuma yaja tsaki, ya ɗaure fuska tamau alamun lamarin ya ɓata mishi rai. Ya galla mata harara ya ci gaba da masifa. "Ji wani banzan shiga da kika yi kamar wata shashasha. Bani ki ɓace min daga nan" Ya karasa maganar haɗe da daka mata tsawa. Jikinta na rawa ta miƙa masa wayarsa ta karɓi nata, idanunta ciccike da hawaye ta fice daga ɗakin. Ko kafin ta isa gida sha biyu da minti uku na dare, ko gama daidaita fakin ɗin motar bata yi ba ta shige cikin falon hankalinta a tashe, har lokacin tunaninsa da kyakkyawar surarsa na maƙale a zuciyarta. A wannan daren duk iya ƙwarewar sarkin ɓarayi bacci baiyi nasarar sace ta ba. Washe gari da sassafe bata san yadda aka yi ba kawai zuciyarta ta dinga tunzurata haka ta sake ɗaukar makullin ɗaya daga cikin motocin Madam ta koma gurinsa, a lokacin ko tashi baiyi ba. "Me ya kawo ki?" Ya tambaye ta a tsorace, yana tsaye ya babbake ƙofar ya hana ta shiga. "Just kawai... na zo ganinka ne" Ta amsa tana narai-narai da idanu ciccike da hawaye. "Jiya ka hana ni bacci..." Ko kafin ta ƙarasa magana Ruf ya maida ƙofar ya kulle ya saka key ta ciki, haka ta gaji da kwankwasa kofar taja sanyayyun ƙafafunta ta koma gida. Bata gaji ba da rana ta ɗanɗasa wanka tayi kwalliya cikin wani figigin sket da guntuwar riga ta sake komawa gurinsa. ɗakin a rufe yake, duk yadda take ta ƙwanƙwasawa bata ji alamun yana nan ba, dan haka ta koma reception zaman jiransa. ****** ******* A cikin kwanaki biyun da yayi a garin ta zame masa wata maƙale masa komai lilo, kusan duk inda yasa ƙafa tana biye da shi. Tun yana ganinta da marmari har ya fara mata kallon tsoro. Da daddare da ta je ɗakinsa bagatatan zuru yayi yana kallonta kawai cikin rashin abin cewa, a zuciyarsa sai jan ta'aweezi yake yi yana neman tsari da wannan hatsabibiyar yarinyar da ta addabi rayuwarsa cikin kwanaki biyu kacal. "Maheer...!" Ta sake furta sunanshi cikin wani irin salo mai kiɗimarwa. Ganin ya ƙi kallonta yasa ta sake cusa mishi jikinta kamar za ta faɗa masa duk da ta san baya so tana kusantarsa, kusan rabin ƙirjinta suka sake baiyana a fili. Hannu ta miƙa da nufin ta dago fuskarsa dan ya kalle ta da sauri ya sake ja da baya. Ya sake galla mata wata muguwar harara a karo na barkatai mai baiyana tsananin tsanar da yake mata. Ita kuwa ko a jikinta, tayi wata dariya mai ban sha'awa. Daman burinta ya kalleta, kuma ya kalle tan, dan haka burinta ya cika. Ta sauke ajiyar zuciya, ta karkaɗa idanunta tayi fari da ido, ta nuna shi da yatsarta manuniya tana taune gefen bakinta na dama, ta kashe idonta na hagu. "Gangaran ! Ina son ka! Ka daina ja min aji fa, bai dace da kai ba. Sam bai dace da kai ba. Ka huta, anjima da daddare zan dawo in taya ka hira. Ya kamata kaima ka ji kana so na fa, cikin kwanaki biyun nan duk ka hana zuciyata sukuni..." "Bana sonki, kuma kar ki kuskura ki dawo anjima" Ya katse ta cikin masifa. Bai jira ta amsa ba ya ci gaba. "Wai ke wace irin maiya ce? Anya kuwa akwai zuciya a kirjinki?" "Kirjina dai Gangaran? Barin zo ka duba. Amma dai ina da tabbacin tun daga ranar da idanuna sukai tozali da kai na daina jin bugawar zuciyata a kirjina." Tana gama faɗin haka ta fara kici-kicin cire 'yar yaloluwar rigar da ke sanye a jikinta. "Nooo..." Ya faɗa cikin tsawa tare da runtse idanunsa duk biyu. Da hannu ya nuna mata hanyar ficewa daga d'akin. A maimakon ta fita sai ta koma cikin ɗakin sosai ta zauna a kan kwallin kujeran da yake ajiye a ɗakin, ta zauna ɗai-ɗai ta ɗora ƙafa daya kan daya tana ƙare mishi kallo, zuciyarta na sake tumbatsa da tsananin so da kaunarshi. "Au! Baki tafi ba?" Ya tambaye ta da zallar mamaki a fuskarsa bayan ya buɗe idanu, shi kam ya haɗu da alaƙaƙai. "Me kike jira?" "Yau a nan zan kwana" Ta amsa hankalinta a kwance, tana jifansa da tattausan murmushi. Kiran da ya shigo cikin wayarsa ya hana shi bata kyawawan marukan da zai sa ta fice masa daga ɗaki. Surayya ce, tun kafin ya amsa kiran ya fara sakin tattausan murmushi kamar tana gabansa, tsawon kwanaki biyun bata taɓa gajiya da bibiyarshi ta waya tana bashi haƙuri ba, ya yafe mata. A taƙaice ma dai sun shirya, daman tsakanin mata da miji sai Allah. Ire-iren zaƙaƙan kalaman da taji yana furtawa wacce suke waya ne yasa ranta yayi mummunar ɓaci, abinda ya ƙara tunzura ta shi ne ganin yadda ya ma manta da ita a cikin ɗakin. Ta mik'e tsaye ta fuskanci jikin bango, a hankali kyawawan dara-daran idanunta suke canzawa daga farare tas zuwa jajaye, ƙwayar baƙin cikin idon kuma ya koma launin ruwan bula. Taja rigar jikinta sama-sama sosai cikinta ya baiyana a fili, kawai sai ta durk'ushe a ƙasa ta fara motsawa tana kanannaɗewa kamar mai aljannu. Da wani irin tafiya kamar tsohuwa mai k'usumbi ta nufi hanyar fita daga d'akin. Jini yana d'id'd'iga daga cikin idanunta a maimakon hawaye. Daga can 6angaren Suraiya ta yanka ihu ta zube k'asa sumammiya, wani irin ruwa bakikirin mai yauki yana fita daga bakinta. ****** ****** BILHAƘƘI Suna tsaye su biyu a bakin wata tsohuwar rijiya mai matuƙar zurfi da mugun faɗin baki, da ganin rijiyar irin tsoffin rijiyoyin nan ne masu daɗaɗɗen tarihi. Gugan da yake ajiye a gefe duk yayi ƙura alamun an matuƙar daɗewa ba'a ɗebi ruwa da gugan ba, harabar gurin ma a bushe yake ƙamas duk rairayi. Matsanancin ƙishin ruwa ke damun duk su biyun, amma suna ta muhawara akan su janyo ruwan ko kar su janyo? Shi Maheer ya dage akan kar su janyo dan kila ruwan bazai rasa datti da ƙwayoyin cuta ba tunda alamu sun nuna an daɗe ba'a ɗibi ruwan rijiyar ba. Shi kuma Malam ya dage akan su janyo ruwan, babu wani ciwo da zai kama su sai abinda Allah ya ƙaddara zai faru da su. Daga ƙarshe dai Malam ne ya haƙura yabi ra'ayin Maheer da yace su tafi kawai sa ɗibi ruwan a rijiyan da yake can gaba wacce bata kai wannan zurfi, haɗari da faɗin baki ba. "Maheeeeer...!" Suka ji an ƙwalla kiran sunan da murya mai matuƙar amo da hargagi daga can cikin rijiyar. A tsorace suka dawo da baya suka leƙa kawunansu cikin rijiyar, da farko basu ga komai ba sai tsananin duhu saboda tsananin nisan ruwan, minti ɗaya tsakani sai wani matsanancin haske ya baiyana, da sauri suka kare idanunsu dan kar hasken yayi musu illah. "...Ga hannuna... ku taimaka min... za su hallaka ni..." Aka sake faɗa da rawar murya daga can cikin rijiyan. A tare suka sake leƙawa a karo na biyu bayan sun buɗe fuskokinsu, yanzu kam babu hasken nan mai yunƙurin cutar da idanu. Wani abin mamaki da ban tsoro kuma sai ruwan rijiyar ya ɗago sama sosai suna ganin cikin ruwan garai-garai kamar a sa ƙoƙo a ɗiba a sha. Minti ɗaya tsakani ruwan ya rikiɗe ya zama jini ja jajur, zara-zaran yatsu suka fara bayyana a saman jinin, daga haka hannun ya ɗago sama sosai har zuwa kafaɗa "Ku taimaka min..." Ta sake faɗa a karo na biyu tana miƙa musu hannun, kanta da gangan jikinta suka taso sama gaba-ɗaya daga cikin jinin, wasu hannuwa ne zasu kai goma daga can cikin rijiyar suka riƙe ƙafafunta tana ƙoƙarin ƙwacewa suna yunƙurin janyeta su dulmiyar da ita can ƙasa cikin jinin. "Ku taimaka min, so suke su hallaka ni wai dan zan bar cikinsu." Ta faɗa cikin raurawar murya tana ci gaba da miƙa musu hannunta ɗaya, kallonsu take yi da idanunta fari ƙal babu ko ɗigon baƙi a ciki, hawayen jini na zuba daga cikinsu, gashin kanta duk yawanshi a tsattsaye yake kamar kibiyoyi, fuskanta yayi fari fat kamar ba daga cikin jini ta fito ba. Cike da jarumta da rashin tsoro Malam da Maheer suka miƙa hannuwansu da nufin su janyota waje, kafin su ankara wani guguwa mai matuƙar ƙarfi da tururin zafi ya fito daga can cikin rijiyar ya watsar da su gefe ɗaya. Duk da buguwar da suka yi shanyewa yayi da saurin gaske ya yunƙura da ƙyar ya riga Malam miƙewa tsaye, ya sake nufar rijiyan gadan-gadan da nufin ya janyo hannunta, dan har lokacin tana ihun su taimaka mata. "Maheer..? Ka dakata kar kaje" Ya ji an ƙwallah kiran sunanshi daga can baya ana dakatar da shi, muryar kamar ta wacce ya sani. "Ku taimake ni... ku taimake ni mana... za su komar da ni cikinsu." Ta sake faɗa a galabaice daga can cikin rijiyar cikin kuka. Daga bayansa ana ta ƙwallah mishi kira, ana dakatar da shi, daga cikin rijiyar kuma tana ta roƙon su taimake ta. Ruɗewa yayi ya rasa gaba zaiyi ko baya, daga ƙarshe kawai sai ya yanke shawarar waigawa baya dan ganin wacce take dakatar da shi. Ido biyu yayi da Surayya, wani farin haske mai kama da hazo zagaye da inda take zaune, an ɗaureta jikin wani ƙaton bishiya, hannayenta da ƙafafunta duk an ɗaure ta baya da wani dogon kaca mai matuƙar tsaho da ya kasa hango ƙarshensa. "Kar kaje gurinta, mayya ce. Muguwa ce azzaluma, ka ga ita ta ɗaure min kurwa tana so ta hallaka ni. Idan ka ciro ta daga ciki mutuwa zanyi" Tayi maganar cikin gunjin kuka mai baiyana fita haiyaci. ƙafafu da hannayenta inda aka ɗaure sai tsattsafar da jini suke yi dan tsananin azaba. Da mugun gudu ya nufi gurinta dan ya taimaka mata ya kwance ta daga mugun ɗaurin da aka yi mata, duk da ihun kiran sunanshi da ake yi cikin murya mai amo da amsa kuwwa daga can cikin rijiyar sam bai waiga ba har ya isa gurin Surayya. A daidai wannan lokacin Malam ya yunƙura da ƙyar ya miƙe ya ƙarasa bakin rijiyar ya leƙa, ko da ya miƙa hannunsa dan ya janyota sai yaga waɗancan hannuwan da suke jan ƙafafunta ta can ciki har sun kusa janyeta zuwa cikin jinin. "Kai mahaɗi ne, shi ne jigon da za ku iya haɗa hannu da yaddar Allah ku fitar da ni a halin da nake ciki... shi ne zai iya zama garkuwata a duk lokacin da suka tunkaroni da mugun nufinsu... ku taimaka min..." Ɗif muryar ta ɗauke, ruwan jinin ya ɓace ɓat kamar bai taɓa wanzuwa a cikin rijiyar ba, kusa da ruwan ya ɗago sai ya koma can nesa kamar yadda yake a da, hasken da ya baiyana ya ɓace matsanancin duhu ya baiyana. Firgigit Malam ya farka daga nannauyan barcin da ya ɗauke shi mai cike da hargitsattsun mafarkai, bakinshi ɗauke da salati da hasbunallahu wa ni'imal wakeel. Shiru yayi yana tunanin mafarkin da yayi tiryan-tiryan a zuciyarsa. Matsanancin tsoro ne da fargaba ya kama shi, bai cika yin mafarki ba a rayuwarsa, amma duk lokacin da yayi mafarkin wani abu in Allah ya yarda mafarkin ko akasin abinda ya gani zai tabbata. Ɗai-ɗai ne mafarkan da yayi basu tabbata ba. Fuskar yarinyar mai siffar ban tsoro sam ya ƙi ɓacewa daga idanuwansa, har lokacin bai daina jin amsa kuwwar muryarta tana ihun su taimaka mata ba. Ko da ya kalli agogo sai yaga ƙarfe biyu da minti goma sha biyu na dare, addu'o'i yayi ya sake maida haƙarƙarinsa kan katifa ya fuskanci gabas, da nufin gyangyaɗawa zuwa ƙarfe uku da rabi. Amma sam ya kasa barci, da ya rufe ido ita yake gani tana miƙo masa hannu kamar yadda ya faru a cikin mafarkin. Sai juye-juye yake yi, daga bisani sai ya miƙe ya shiga bayi ya ɗauro alwala ya fara jero nafilfili kamar yadda ya saba ko wane dare. Amma yau akalar addu'o'insa gaba ɗaya ya tattara ne ga roƙon Allah ya tsare yarinyar nan ta cikin mafarkinsa, Ubangiji ya kawo mata ɗauki aduk halin da take ciki kuma a duk inda take a faɗin duniya. ****** ****** "Bibi wai me yake damunki ne? kwana biyun nan gaba ɗaya na rasa gane kanki da inda kika dosa. Faɗa min me yake faruwa? ina kike yawan zuwa a ƴan kwanakin nan bayan kuma na san yawo ba halinki bane" Shiru tayi kamar ba da ita take magana ba, idanunta ciccike da hawaye, hannayenta duk biyu dafe da ƙuncinta. Bisa ga dukkan alamu ta yi nisa sosai cikin zuzzurfan tunani. A kallo ɗaya za a fahimci sunƙi-sunƙin damuwan dake danƙare a zuciyarta, tana zaune sanye da wata ɓingilar vest da ya wuce cibiyarta da kaɗan, sai kuma wani burgujejen wando gajere wanda shi ma da kaɗan ya wuce gwiwarta. Gashin kanta a cukurkuɗe a yamutse kamar yadda take, a tsakiyar gadon take zaune digirgir kamar wata tashin iskokai. "Bibi?" Ta kira sunanta da ɗan ƙarfi haɗe da sa hannu ta jijjiga kafaɗarta guda ɗaya. Yadda tayi firgigit tana kallonta kamar wacce ta farka daga barci shi ya ankarar da Madam duk tsayuwarta a gurin bata san da ita ba, maganganun data yi ma ba lallai idan ta ji ta ba. Kusa da ƙafafunta ta zauna suna fuskantar juna, ƙare mata kallo take yi ko zata ci nasarar gano abinda yake damunta amma bata gano komai sai ramewa kaɗan da Bibin tayi. Abin mamaki kuma abin tsoro ga Madam sai kawai ta ga tsiyayowar ruwan hawaye daga idanun Bibi. Zaro ido tayi a tsorace, a duk iya tsawon shekarun da suka ɗauka tare baza ta iya tuna wani lokaci da ɗigon hawaye ya sakko daga idon Bibi ba, amma yau Bibi ce da kuka kashirɓin? alamun rauni da ragwanta bayyane a idanunta ƙuru-ƙuru? wannan babban abin mamaki ne. "Me yake faruwa? faɗa min me yake damunki?" Ta sake jefa mata tambayoyin a karo na biyu, muryarta a tausashe. "Madam..." Taja sunan wasu sabbin hawaye suna sake gangaro mata shar-shar kamar an buɗe famfo. "I'm in love !!" Ta sake faɗa a sanyaye tun kafin Madam tayi yunƙurin magana. "I love him with all..." "Ina fatan dai wasa kike min?" Ta katse ta da sauri, idanunta a warwaje. "Na taɓa yi miki irin wannan wasan? da gaske nake yi. Kinga nan?" Ta kamo hannunta guda ɗaya ta ɗora a ƙirjinta dai-dai saitin zuciyarta. "Kwanaki uku kenan kamar daƙiƙa na agogo duk bugawa ɗaya yana bugawa ne da tsananin soyayyarsa, tun da nake a rayuwata ban taɓa kasancewa a irin wannan halin ba, da gaske ina sonsa, soyayya mai tsanani fiye da yadda kike tunani, ina sonsa fiye da duk wani soyayya da kika taɓa gani wata mace ta yi wa wani namiji a rayuwarki..." Fincike hannunta tayi taja da baya a tsorace, ta kalleta zuciyarta cike da fatan maganganunnan da take furtawa su kasance mafarki tayi. "Bibi? kina cikin hayyacinki kuwa? ina fatan dai ba shaye-shaye kika fara yi ba tare da kin sanar da ni ba?" Tayi mata tambayar cikin ɗan tsawa, fuskarta bayyane da matsanancin mamaki da zallar takaicin maganganun Bibin. "Madam pls ki taimake ni, jiya ya tafi ya barni ba tare da yayi min sallama ba... ya tafi da zuciyata ba tare da ya bani tasa zuciyar ba kamar yadda nake muradi. Ki taimake ni... ji nake kamar zan mutu. Ina son shi. Ki dawo min da Maheer ɗina pls idan ba haka ba zan fita nemansa da kaina..." "Bibi ki dawo hayyacinki pls! kin manta abinda Oga ya faɗa miki? kin manta kashaidin da ya miki? wane mai gangancin ne yayi kuskuren shiga cikin rayuwarki? wani mahaukacin ne mai wannan kasadar? ki faɗa min in sa a ɓatar da shi a duniyar nan tun kafin yasa kwaɓarmu tayi ruwa. Gara ya mutu, ya tunkuyi burji dan rayuwarsa sam bata da amfani..." "Maheer...? Maheer ɗin nawa za ki sa a ɓatar? Maheer ɗin nawa kike so ki hallaka? Maheer ɗin nawa ne kike cewa rayuwarsa bata da amfani?" Ta sauko daga kan gadon ƙirjinta na sama da ƙasa ta nuna ta da yatsarta manuniya ta ci gaba da cewa. "Wallahi kar ki kuskura, karki kuskura. Ba ke ba har Ogan wannan kashaidi ne mai harshen damo. Ina rayuwata yadda naga dama ne, babu wanda ya isa ya kafa min doka ko wani sharaɗi da banyi niyyar yi ba. A cikinku duk wanda yayi kuskuren taɓa min wanda nake so wallahi zai ga abinda baya so. Idan kuma kina ganin cika baki nake yi..." Tayi ƙwafa ta jujjuya ƙwayoyin idanunta cikin fushi "Dan Allah ki kwatanta taɓa shi" Tana kaiwa nan wayarta ya kwaɗa kiran sallar azahar rangaɗaɗau da muryar ladani mai tsananin daɗi da garɗi. Bata ƙara saurarar Madam ba ta shige ban ɗaki dan ɗauro alwala, jikinta babu inda baya rawa da karkarwa. Rabon da ta yi sallah akan lokaci ita kanta ta manta, sai ta kwana biyu ma bata yi sallar ba, idan ta tashi yi kuma buga-buga kawai take yi ba tare da kiyaye farillai, sunnoni, da mustahabban sallar ba. Alwalar ma sam ba cika ta take yi ba, tana sallar ne kawai dan kiyaye ɗaya daga cikin ababen da ta koya a gurin Maman Ushe, amma bayan haka babu wani abu da take aikatawa da zai nuna ita cikakkiyar musulma ce. Dan ta Madam Mary ma da tuni ta daina sallar tunda ita ma ba yi take yi ba, rayuwarta take yi mai ƴanci. Ba zuwa coci babu yin sallah, bata da wani takamaiman abin bauta da ya wuce tana bin duk abinda Oga ya gindaya mata. Doguwar riga mai ɗan dama-dama ta lalubo a cikin jibgin gogaggun kayanta tasa, rigar da kaɗan ya wuce gwiwarta bai kai idon sahu ba, kuma ya matse ta tsam! Haka nan dai ta lalubo baƙin siririn gyalen doguwar riga ta naɗe kanta da shi ta fuskanci gabas ta tada sallah ƴar faki kamar yadda ta saba. Kamar kububuwa fuuu ta fice daga cikin ɗakin tana harhaɗa hanya, lallai ya zama dole a wannan karon su dakatar da Bibi daga iskancin da take aikata musu. Dole su ɗauki mummunar mataki a kanta ta bi abinda Oga ya shimfiɗa mata, idan kuma taƙi dole su ɗauki matakin ƙarshe a kanta. Ko da ta sallame shiru tayi tana tunaninshi, lokaci ɗaya kuma sai ga hawaye shar! Bata saba idan ta bubbuga sallah tayi addu'a ba yanzu ma zaune tayi tana tunanin rabuwarsu ta ƙarshe a shekaran jiya da yamma. 'Cikin tsananin sa'a ta tarar da ƙofar ɗakin nasa a buɗe, a hankali kamar ɓarauniya ta buɗe ƙofar ta shige cikin ɗakin. Bata ganshi a falo ba sai motsin ruwa da take ji a banɗaki, hakan yasa ta gane wanka yake yi. Bayan tafkeken labulen da ya rufe windo taje ta maƙale yadda bazai ganta ba. Har ya fito ya gama shiryawa bata leƙo shi ba dan bata san me zata gani ba, sai da taji yana fesa turare alamun ya gama shiri, ko da ta leƙa kanta sai taga ya bata baya dan haka da saurin gaske ta ƙarasa gurinshi ta rungume shi da sanyin murya mai kama da raɗa tace "My love..." A gigice ya juyo dan ta bala'in shammatarsa, yana haɗa idanu da ita ya finciketa daga jikinsa cikin tsananin fushi ya bata mari mai kyau a kuncinta na dama. "I love you..." Wani mahaukacin marin ya sake sauke mata a kumatunta na hagu saida tayi taga-taga kamar zata kife a kasa amma ta cije ta tsaya. Murmushi kawai tayi, idanunta ciccike da hawaye. "Ina sonka ne fa..." A zuciye yasa hannu yayi mata wani mugun shaƙa kamar mai neman fitar mata da numfashin ƙarshe, nan da nan ta fara ganin bibbiyu, ta fara jan numfarfashi a wahalce tana lumshe ido tana buɗewa, ya kusanto da ita jikinsa sosai ido cikin ido yake watsa mata wani matsiyacin kallo. "Kin ɗauka na rasa yadda zanyi da ke ne na ƙyale ki har kika zame min maƙale mata? ba fa tsoronki nake ji ba. Kawai ina tausayinki ne ganinki ƙaramar yarinya. Wallahi daga yau idan kika sake zuwa nan nema na saina sassaɓa miki kamanni, shashasha kawai. Ko mata sun ƙare me zanyi da ƴar iska irinki ƙaramar karuwa?" Yaja tsaki ya watsar da ita a wajen, inda Allah ya taimaketa kusa da gadon ɗakin suke da ba ƙaramin buguwa zata yi ba, da ya watsar da ita sai ta faɗi a kan katifa tana maida numfashi a wahalce. Ɗan ƙaramin jakar da ya zubo kayanshi kala biyu ya ɗauka ya ɗauki wayarsa ya nufi ƙofar ɗakin da ya ji ana ƙwanƙwasawa. Yusuf ne yake tambayarsa "Ka gama ne?" "Eh ! muje kawai. Ni yanzu zan wuce sai ku taho idan motocin kayan sunyi gaba. Sam banso na kwana uku a garin nan ba, amma tunda buƙata ta biya Alhamdulillah." Yana gama faɗin haka yaja ƙofar ya rufe kamar ba kowa a ciki suka sauka ƙasa yaba su makullin ɗakinsu, shi kuma suka fita da Yusuf a motarsa. Basu yi nisa ba ya sauke shi a bakin titi ya ba motar wuta ya ɗauki hanyar barin kacia dan komawa kaduna. So hana ganin laifi, bata ji haushinshi ba. Sam bata ji haushin abinda yayi mata ba. A maimakon ta ji a ranta ta tsane shi wani matsanancin soyayyarsa ne yake sake tumbatsa a zuciyarta, kawai sai ta lumshe idanu tana murmushi, bubbuɗe hancinta tayi ta ci gaba da shaƙar daddaɗan turarensa da ya kama ɗakin. Sai da ta gaji da kwanciya ta yunƙura da ƙyar ta sauka ta hau mota ta koma gida' BILHAƘƘI Ya ci gaba da kallon yadda ta zabge ta lalace lokaci ɗaya, da ganin yanayinta duk ta jigata. Kamar ba Surayya mai garin jiki da tsananin gayu ba, yanzu duk ta koma wata iri ta canza kamanni saboda tsananin ciwon da ita kaɗai tasan yadda take ji a jikinta. A cikin kwanaki uku kacal, iya binciken likitoci har lokacin basu samu nasarar gano takamaimai abinda yake damunta kuma yake haddasa mata haɓo a kai akai ba. Ƙarin ruwa kawai suke ta mata sai kuma manyan magunguna Antibiotics da ake ta ɗura mata, har lokacin dai sauƙi sai na musulunci. Ciwon ma kamar gaba yake yi, hankalin Maheer da na iyayenta a matuƙar tashe yake. Hatta Rabi da ba wani zaman lafiya suke yi ba a tsakaninsu tana matuƙar tausaya mata. Tsawon kwanakin da ta yi a asibitin tana kwance ne sharɓan kamar gawa, bugawar numfashinta ne kawai ake gane tana da rai. A hakan da take ciki duk bayan awa ɗaya jini zai ɓalle mata ta hanci ta baki, sai an ɗauki tsawon lokaci daƙyar likitoci suke samun nasarar tsayar da jinin. Yini ɗakin da take kwance yake yi cike da mutane ƴan dubiya, wani lokacin ma har sai likitocin sunyi kora, da yake asibitin private ne ko wane lokaci ana iya zuwa duba mara lafiya. Ta ko wane ɓangare addu'ar fatan samun sauƙi ake yi mata daga bakunan mutane daban-daban. Tunda abin ya faru Malam Abdulganiyyu baya nan, sunje wani taron Semina na kwanaki huɗu da sauran manyan malamai a Abuja. Duk abinda ya faru ta waya ya samu labari, sai yau ya dawo dan haka kai tsaye ya umarci direbanshi ya wuce asibiti ya duba jikin Surayya bayan ya kira Maheer ya faɗa mishi asibitin da aka kwantar da ita. Ya girgiza da ganin yadda ta koma a cikin ƙanƙanin lokaci, zuciyarsa ta ƙara cika da tsoron Allah. 'Lallai ɗan Adam ba a bakin komai yake ba, idan Allah yaso cikin ƙanƙanin lokaci sai ya jirkita ma mutum halitta. Allah yasa muyi kyakkyawar ƙarshe. Ameen' Tunanin da ya gama yi kenan a zuciyarsa, fuskarsa bayyane da matsanancin tausayinta, dafa ƙarfen gadon da take kwance yayi ya fara jero mata addu'o'i yana tottofa mata, ya ɗauki tsawon lokaci yana addu'ar a zuci sannan yayi magana a fili "Ubangiji Allah ya bata lafiya." "Ameen Malam." Mutanen cikin ɗakin suka amsa gaba ɗaya, fuskokinsu duk a jagule saboda damuwa da halin da take ciki. Malam ya maida idanunshi kan Rabi da take rakuɓe can gefe guda kusa da Mummy Salamatu, sanye da zumbulelen hijabi har ƙasa. Ita ma duk ta faɗa kamar wacce lafiya bata wadace ta ba. "Rabi'atu ance kuna tare wannan abin ya faru da ita. Menene zallar gaskiyar abinda ya faru a lokacin?" Cikin nutsuwa ta fara kora mishi bayanin, idanunta a ƙasa cike da tsananin ladabi da kunyarsa da take matuƙar ji. Ga wani kwarjini na musamman da Malam ɗin yake da shi ga duk wanda ya tsaya a gabanshi. "Ina fitowa daga ɓangarena zuwa cikin babban falo na ganta a tsaye tana waya fuskanta cike da nishaɗi tana dariya, ko da na saurara dakyau sai na fahimci da Ya Maheer take waya saboda irin kalaman da na ji tana furtawa. Tsaki nayi na wuce kicin na ɗauko kofi ina dawowa cikin falon ban zauna ba na nufi ɓangare na, banyi nisa ba naji ta ƙwalla ihu mai ƙarfi ta faɗi ƙasa, ko da na isa gurinta da gudu sai naga wani baƙin abu yana fita daga baki da hancinta. Shi ne na kira mai gadi ya taimaka min ya kira wani maƙwafcinmu muka kawo ta asibiti" Shirun da ta yi shi ya fahimtar da shi ta gama magana, girgiza kai yayi alamar ya gamsu da duk abinda ta faɗa. "Allah ya bata lafiya. Magaji muje in ga likitan nata ko?" Ya faɗa yana kallon Maheer sannan ya nufi hanyar ficewa daga ɗakin, zuciyarsa cike da saƙe-saƙe. Tsawon kwanaki uku kullum sai yayi mafarkin yarinyar nan tana neman taimakonsu a cikin mabanbantan yanayi, a jiya da yayi mafarkin ya ga wasu matsafa suna zagaye da ita suna azabtar da ita, tana kuka take miƙo ma Maheer hannu shi kuma ya juya mata baya. A can gefe guda kuma yaga Surayya cikin wani yanayi. Abu guda da ya iya fahimta a yanzu da yaga halin da Surayya take ciki shi ne tabbas ciwonta yana da alaƙa da waɗancan matsafan, in dai kuwa haka ne zamanta a asibiti bashi da wani amfani tunda basu da maganin ciwonta. Fagen nasu ne na manyan malamai. Bayan musayar gaishe-gaishe cikin girma da mutunta juna ba tare da ɓoye-ɓoye ba kai tsaye ya faɗawa likitan abinda yake ransa. "Likita sallama muke buƙata fa." Hankali a tashe likitan ya fara tambayarsa. "Malam lafiya? Wallahi muna iyakar ƙoƙarinmu akan ciwon nata, kar kaga kaman mun gaza ne. Kasan ciwo shiganshi ne babu wuya amma sauƙi dole sai a hankali. ku ɗan ƙara mana lokaci kafin kuyi tunanin canza mata asibiti." "Dr. Ni bance kun gaza ba, kuma ba asibiti zamu canza mata ba. Ciwon nata ne dai idan ka lura da yadda kuka kasa gano ainahin abinda yake damunta za ku fahimci sam ba maganin asibiti take buƙata ba, za mu koma gida ne mu gwada magunguna daga Alƙur'ani da Sunnah. Insha Allahu muna fatan dacewa a wannan ɓangaren." Cike da gamsuwa Likitan yayi musu fatan dacewa sannan ya rubuta musu takardan sallama, har ɗakin ya bisu yana musu fatan alkhairi. Iyayenta sun miƙa wuƙa da nama ga Malam ɗin, suna da kawaici da kyakkyawar shaidan da gangar Malam bazai yi abu dan ya cutar da Surayya ba. Shima Maheer kanzil bai ce ba har suka tattara yana su yana su aka kwashe ta ranga-ranga zuwa gidan Malam. Da yake gidan yalwatacce ne a wadace babban ɗaki guda aka ware mata kusa da na Ummee aka kwantar da ita, daman akwai komai a ɗakin. Yayar mahaifiyarta Inna Lantana ita ce zata ci gaba da jinyarta dukda sun san iyalan Malam baza su taɓa gazawa gurin kulawa da ita ba. Cikin ƙanƙanin lokaci Malam ya fara mata zafafan addu'o'i a cikin ruwa ana bata tana sha, ya rubuta duk magungunan da yake buƙata ya aiki Maheer babban shagon islamic chemis ya sissiyo mishi, nan da nan ya harhaɗa duk abubuwan da yake buƙata ya ba da ana mata amfani da su, a kullum kusan kwana yake yi yana salloli da yi mata addu'ar Ubangiji ya kawo mata sauƙi da gaggawa. ***** ****** "Yusuf ko?" Ta tambaye shi tana nuna shi da yatsarta manuniya, zuciyarta cike da addu'ar Allah yasa shi ɗin ne. "Eh! ni ne" Ya amsa fuskarsa yalwace da murmushi. Cike da ɗoki da tsananin murna ta ƙara matsawa kusa da shi kaɗan, ta cigaba da magana tana ɗan dariya "Ka gane ni kuwa? ni ce kwanaki na tambaye ka sunan abokinka..." "Ba abu bane mai sauƙi mutum mai hankali ya manta fuskar kyakkyawar yarinya kamarki fa. Yau kuma me kike so?" Ya katse ta shima yana dariya. "Shi nake so" Ta faɗa a shagwaɓe, sai kuma kunya ta ɗan kama ta da sauri ta rufe rabin fuskarta da hannunta ɗaya tana dariya. Maida hankalinsa yayi gaba ɗaya a kanta yana jin maganganun da ta zo mishi da su. "Da gaske nake jin tsananin son abokinka, amma shi sam ya ce baya ƙaunata." Sai kuma tayi rau-rau da idanu ciccike da hawaye, iya dauriya tayi gurin hana hawayen zubuwo, ta daure ta cije ta ci gaba da kora mishi bayanin da ke cin zuciyarta. "Soyayya... soyayyar nan da nake ji na shi a zuciyata wani abu ne da ko a muggan mafarkin da nake yi wallahi ban taɓa hasashen zai iya faruwa da ni ba, sam! A halin da nake ciki yanzu da tsarin rayuwar da nake yi soyayya bata dace da ni ba. A takaice soyayya ɓatan hanya tayi ta faɗa min. Ya zanyi? Dan Allah ka faɗa min yadda zanyi? kwata-kwata kwanaki biyar ne da haɗuwata da shi amma yadda nake ji a raina kamar na shekara ɗari da shi a zuciyata. Ina azabtuwa da soyayyarsa fiye da yadda kake tsammani." Ta nuna saitin zuciyarta da hannu, zafafan hawaye na tsiyaya daga idanunta. "Ji nake kamar nan zai iya tarwatsewa matuƙar ban mallaka mata abinda take tsananin so a cikin ƙanƙanin lokaci ba. Allah ya jarabceni, da gaske Allah ya jarabceni. Dan Allah ka kwatanta min inda yake da zama. A kanshi na yarda da zancen bahaushe da yake cewa garin masoyi baya nisa, yadda nake ji a raina tabbas zan iya binshi duk nisan duniyan da yake. Zan ci gaba da naci ina bibiyarshi har zuwa lokacin da zai fuskanceni ya karɓi soyayya ta. Dan girman Allah ka taimaka min, wallahi da gaske nake yi. Kuma ko kaɗan bana nufinshi da sharri." Shiru yayi yana kallonta ita kuma tana ta hawaye, a zuciyarsa yake jujjuya maganganunta yana auna su a sikeli na hankali dan tantance su. Bai san me yasa ba da gaske yake ji yana tausayinta, lallai soyayya bata da adalci, ƙaramar yarinya kamarta bai kamata ta afka cikin zuzzurfar soyayya irin wannan ba. "Amma kinsan yana da mata har biyu?" Ɗif ta tsaida kukan da take yi kamar ɗaukewar ruwan sama. "Da gaske kake yi ko kuwa kora da hali kake min?" BILHAƘƘI "Da gaske nake yi. Babu zancen kora da hali a tsakaninmu, ki ɗauka a ranki ni kamar Yaya ne a gare ki da zai iya yin duk wani fafutuka dan samarwa tilon ƙanwarsa farin ciki. Ban san me yasa tun a haɗuwarmu ta farko naji a raina ina matuƙar tausaya miki. Kuma daga maganganunki na ɗazu na gamsu a raina soyayyar da kike yiwa mai gida mai tsananin yawa ne, soyayyarki bata da wata tawayar da zata sa a ƙi karɓarta." Shiru suka yi duk su biyun, kowa a cikinsu biyun da irin saƙe-saƙen da yake yi a zuciyarsa. "Na yarda, ko mata ɗari yake da su zan aure shi in zam ta ɗari da ɗaya. Kwatanta min inda zan same shi, zan bishi duk da hakan. Ina son shi" Ba tare da wani zurfin tunani ba Yusuf ya bata cikakken adireshin gidan iyayen Maheer da ke unguwar rimi, sosai yayi mata gwari-gwari yadda duk sadda ta tashi zuwa baza ta sha wahalar gane kwatancen ba. "Amma iyayenki da ƴan gidanku zasu yarda ki bi saurayi har kaduna? kuma ina fatan dai ba zubar da mutuncin kanki kike niyyar yi ta hanyar shiga duniya neman saurayi ba..." "Karka damu da wannan, ni marainiya ce, ba na da kowa. Tsawon shekaru masu yawa rayuwa nake ƙarƙashin wata mata mai sayar da abinci. Binshi da zanyi ba abu ne da zai taɓa min mutuncin da kake magana a kai ba." Nan da nan fuskarsa ya kwaɓe da yanayin tausayi "Ayya... Ubangiji yayi musu rahama. Sorry" Shiru tayi bata amsa addu'ar ba, tunani take yi 'Ita a ina ma ta san iyayen nata da har za a musu addu'ar neman rahamar Allah ta amsa?' Amma da ta tuna Maman Ushe da sauri ta amsa da "Ameen ya Allah, na gode." Shiru ya sake ratsa tsakaninsu na ƴan wasu daƙiƙu. "Nima dai yau zan wuce kaduna, tun jiya ma ya kamata in wuce amma saboda motocin kayanmu basu wuce da wuri ba shi yasa na bar tafiyar tawa sai yau. Ba lallai ne mu sake haɗuwa a nan ba, dan a mafiyawancin lokuta idan ba cittan yayi wahala bane gaskiya ban cika shigowa da kaina ba. Balle shi mai gida da zuwanshi garinnan kwata-kwata baifi sau huɗu ba." "Kana da kirki. Na gode ƙwarai da taimakon da ka yi min, bazan taɓa mantawa da kai ba. Ka bani lambar wayarka ko ta waya sai in neme ka idan buƙatar hakan ta taso." Musayar lambobin waya suka yi a tsakaninsu sannan suka rabu, duk su biyun zukatansu yalwace da matsanancin farin-ciki. Babu ma kamar ita da ta samu cikakken bayanin inda za ta samu abinda take so. ****** ****** ***** "Madam ni fa babu inda zanje." "Kina wasa ne Bibi, wallahi dole sai kin je." Ta faɗa cikin fushi da tsananin harzuƙa tana zabga mata harara da manyan idanunta masu barazanar faɗowa ƙasa. "Ni ban gane abinda kuke nufi da ni ba Madam. Ca nake ina da ikon yin duk abinda naga dama? kiran Oga ne nace bazan amsa ba to dole ne sai na je? nima ina da tafiyar da zanyi a gaba na don Allah ku ƙyale ni inji da abinda yake nuƙurƙusata..." "Bibi? kina nufin har kinyi ƙwarin kan da Oga zai kira ki kice baza ki amsa kira ba?" Banza tayi bata amsa ba, a madadin amsawar ma sai ta buɗe banɗaki ta faɗa ciki tana jan tsaki. Ita ma Madam dogon tsakin ta ja ta raka ta da harara, a maimakon tsayuwar jira ta fito kawai sai janyo akwatunan kayan Bibin ta fara ciccire mata duk wasu kayayyaki da take ganin za ta buƙata idan sun tafi, ba ta tunanin zasu wuce kwanaki uku, idan kuma sunyi tsananin daɗewa a can su kwana bakwai, dan haka komai dai-dai da tunaninta take ɗauka tana sakawa a cikin jakar matafiya. Har ta gama duk abinda take yi ta rufe jakar ta fice daga ɗakin Bibi bata fito ba. "Oga bansan me ƴar iskar yarinyar nan take nufi da mu ba, ta ce fa baza ta zo ba..." "Dole zata zo, ki ƙyale ta, karki sake yi mata maganar. Ki cigaba da shirin zuwanku kawai." Ya katse ta daga can ɓangaren yana ƙyalƙyala dariya. Ita ma dariyar tayi, ta gyara riƙon wayar a hannunta ta ci gaba da cewa "Oga dan Allah kar ka yi mata da wasa, yadda ta wahalar da ni tsawon shekarunnan ina so a wahalar da ita sosai, shi kuwa wannan yaron ka kashe shi kawai..." "Ke har kin isa ki faɗa mana abinda zamu yi?" Ya faɗi haka cikin tsawa, bai jira cewarta ba ya ci gaba da cewa. "Ki zuba mana ido ki ga abinda zamu yi." Ƙit ya katse wayar daga ɓangarensa. Mummunar fuskarsa ne yayi jajur, alamun ɓacin rai ƙarara ya baiyana a idanunsa, ya miƙa dungulmin hannunshi ɗaya ya daki wani ƙaton tulu da yake ta zagaye a gabansa, tush ya fashe wani dunƙulallen hayaƙi ya baiyana daga ciki yayi tsiri zuwa saman ɗakin. Runtse ido yayi yana wasu surutai yana kiran sunan Bibi da ƙarfi yana kai naushi cikin hayaƙin. Daga can cikin banɗakin Madam ta ji ta ƙwalla ƙara mai tsananin ƙarfi ta zube a ƙasa cikin fita haiyaci, ko kafin ta buɗe ƙofar banɗakin ta shiga dan ganin halin da take ciki ƙafafu da hannayenta ne suka fara nannaɗewa suna lallauyewa kamar wata mai aljannu, a karo na biyu ta sake yanka ihun da yayi daidai da shigan Madam cikin banɗakin. Kafin wasu daƙiƙu ta sume. Murmushi tayi, ta cije leɓen bakinta tana kallon Bibin a wulaƙance. "Da kyau Oga, aikinka yayi kyau. Maganin shegiyar yarinya mai kunnen ƙashi kenan" Ficewa tayi da sassarfa ta kwashi jakunkunan kayansu zuwa cikin mota. Ta kira su Liyat suka yi a tara a tara da Bibin suka kwantar da ita a bayan motar Madam, ta buɗe wani ɗan madaidaicin akwati ta kwashi kuɗaɗe da yawa ta zuba a ƴar ƙaramar jakarta ta hannu, ta ɗebi wasu da yawa ta rarrabawa duk yaran gidan sannan ta faɗa mota ɓangaren mai zaman banza, ɗaya daga cikin direbobinta ya ja a guje suka fice daga gidan suka nufi hanyar kaduna. ****** ****** "Kina ganin za ku iya isowa nan da minti ashirin? ƙarfe biyar muka yi da su zamu haɗu ga shi yanzu huɗu da minti arba'in, kinsan Lion ya tsani a ƙara mishi lokaci ko da minti ɗaya." "Eh ina ganin haka, yanzun mun shigo refinary junction, za mu ƙaraso yanzu. Pls ki jira ni." Tsaki ta ja daga can ɓsngaren sannan ta katse wayar. Bata damu da tsakin ba ta maida wayar ta aje akan cinyarta ta maida kallonta kan direban. "James ka taka motar nan sosai mu isa da wuri. Mercy tana jira na akwai inda zamu je yanzu." Bai ce komai ba ya ƙara gudun motar sosai har ɗari da arba'in, lokacin da suka ɗauki hanyar shiga kamazou saboda babu yawaitar cunkoson motoci a hanyar. Maida idanunta bayan motar tayi tana kallon yadda suka kwantar da Bibin a jirkice, wani ƙaramin murmushi ne ya suɓuce mata. Ta san ba ita kaɗai ke adawa da Bibin ba duk ƴan matan gidan Madam sun tsane ta, ko ɗan yaya suka samu dama a kanta za su gwada mata iyakarta ne, dubi wani kwantar da ita da suka yi a wulaƙance, irin kwanciyar da in banda tana cikin halin suma ne tabbas ba ƙaramin jin jiki zata yi ba. A minti takwas suka ƙarasa cikin gidan Aunty Mercy. Gudu-gudu sauri sauri Madam ta faɗa cikin falon da ta tarar da tafkeken falon a buɗe, da alamun ƙarasowarta kawai ake jira. "Yi haƙuri ƙawata, gani na ƙaraso." Wani matsiyacin takalmi mai masifan tsini ta ɗauka a kusa da ita ta zura siraran ƙafafunta a ciki, tayi far da gashin ido na kantin da ta ƙara a idanunta dan ƙayata kwalliyarta, tayi magana idanunta a kan Marry "Muje ko?" "A hakan?" Tayi maganar tana nuna jikinta da mamaki, duk da doguwar riga ƴar kantin da yake jikinta baiyi datti ba amma ya ɗan yamutse saboda zaman mota, kwalliyar fuskarta ma duk ya ragu ya ɓace. Ta maida idanunta kan Mercy da ta sha kwalliya cikin wani T.shet mai matuƙar kyau da tsada, da wani ɗan ɓingilin sket baƙi kamar wata ma'aikaciyar banki. Fuskarta da bakinta sunsha penti-penti, ta kawo wani gashin doki mai siraran kitso ta ƙwama a kanta duk dan sake ƙawata kwalliyarta. "Na yi tunanin za ki bari in shirya ko a cikin minti biyu?" "No babu lokacin hakan Mary, duk abinda za ki buƙata yana cikin nan." Ta ƙarasa maganar tare da nuna wani babban leda da yake ajiye kan kujerar kusa da wacce take zaune. "Muje sai ki shirya a cikin mota." "Ok ba laifi. Ya za muyi da Bibi? ga ta can kwance a cikin mota..." "Linda da Agness zasu kula da ita har mu dawo." Ɗaya daga cikin ƴan matan biyu da suke mata aiki a gidan ne ta ɗauki ledar kayan tana biye da su a baya, ɗayan kuma ta riƙe jakar ƙaramar jakar Aunty Mercy har zuwa gurin danƙareriyar motar da ta sa aka wanke mata tun kafin ƙarasowar Madam Mary, har ta shiga mazaunin direba tayi key ɗin motar sai kuma ta kashe motar ta fito bayan ta yi wani ɗan tunani. "James?" Ta ƙwalla kiran direban da ya kawo su Madam, da gudu ya ƙaraso kusa da ita yana kallonta cike da ladabi. Makullin motar ta hurga mishi ya cafe ta buɗe ɓangaren baya na motar ta zauna. "Shigo ka sauke mu, yanzu yamma ta yi, cikin gari bazai rasa go-slow ba, kuma ina buƙatar muyi saurin isa akan lokaci. Idan munje can sai kayi odar abinci kafin mu fito." "Ok Ma." Ta maida kallonta kan su Agness ta ci gaba da magana. "Bibi tana cikin motar Madam ku shiga da ita ciki, ku kula da ita sosai kafin mu dawo. Ina fatan kun gane?" "Yes Ma" Suka amsa bakinsu a haɗe. Tada motar yayi bayan madam ta shiga ciki mai gadi ya wangale musu get suka fice daga gidan. Ko da ya daidaita motar akan titi a tsiyace yaja motar dan su isa akan lokaci bayan ta faɗa mishi inda za su je. ******* ******* Tana gama gyara mata kwanciyar kanta q kan filon ta juya da nufin barin ɗakin sai ta ji an riƙe hannunta na dama da masifan ƙarfi, jin hakan yasa ta waiga a tsorace tana kallonta, har lokacin tana nan yadda suka kwantar da ita. Abinda ya banbanta ta da ɗazu kawai yanzu ana ganin saukan numfashinta a hankali saɓanin ɗazu da take a sume. Taja hannunta dan ta ƙwace sai taji riƙon da ta yi mata ba na wasa bane, ƙura mata ido tayi tana karantar yanayinta, sai ta matsa da kunnenta kusa da bakinta sosai lokacin da ta fahimci kamar magana take yi amma ba ta jin abinda take cewa. "Ku fitar da ni daga nan gidan. Unguwar rimi, Kinshasha road, gida mai lamba ashirin da huɗu, gidan Malam Abdulganiyyu. Can za ku sa a kaini." Tayi maganar a hankali, yadda take yamutsa fuska tana mommotse baki ya fahimtar da ita cike da matsanancin ƙarfin hali da jin jiki tayi maganar. Zazzare ido Linda tayi bayan ta gama sauraren abinda Bibi ta ce, ta ƙure ta kallo da kyau sai taga har lokacin idanunta a rufe suke. Kafin ta ce komai Agness ta buɗe ƙofar ɗakin ta leƙo da kanta ciki. "Me kike yi haka?" Tayi tambayar idanunta a zazzare bayan ta ga yadda take a durƙushe gaban Bibin. Hannu tasa ta yafito ta, sai da ta shigo ciki sosai dan jin kiran me take mata sannan ta ce "Bibi ta ce mu fitar da ita daga gidannan, ta faɗa min wani adress a unguwar rimi wai mu sa a kaita can..." Tsakin da taja haɗe da banka mata harara yasa tayi shiru bata ƙarasa abinda take cewa ba. "Ina tunanin kin fara hauka, sai ki fitar da ita daga nan ɗin ni dai ba ruwana a ciki ooo, Idan Aunty Mercy da Madam Mary suka fara Ball da ke kar ki kuskura ki kira sunana." Ta ƙarasa maganar da ɗage kafaɗunta haɗe da taɓe baki alamun ko a jikinta. Ƙofar fita daga ɗakin ta nufa dan ficewa wani guguwa ya buga ƙofar gam! ya datse. Gurnanin Bibi ya cika ɗakin kamar mai naƙuda, ta buɗe baki da ƙarfi ta sake cewa "Kusa a fitar da ni daga gidannan na ce." Cikin tsawa da murya mai tsananin hargagin da saida lungu da saƙo na gidan yayi amsa kuwwa na maganarta. Ta saki hannun Linda da ta riƙe, ta buɗe idanunta gaba ɗaya wani farin haske mai tsananin walƙiya ya gilma ta tsakankanin idanunsu, hasken yayi gabas da yamma kudu da arewa na cikin ɗakin a ƙarshe ya daki wani danƙareren madubi da yake maƙale kamar tv a jikin bangon yamma na ɗakin, ratsatsatsatsa ƙarar tarwatsewar madubin ya daki dodon kunnuwansu. A tsorace cike da sadaƙarwa suka tsuguna ƙasa idanunsu a rufe, hannayensu duk biyu toshe da kunnuwansu. Gaba ɗaya sun gama tsammanin aradu ce zata faɗo a kawunansu saboda mugun rugugin da ya biyo bayan fashewar madubin, sai kuma suka ji ɗif! kamar anyi ruwa an ɗauke komai ya tsaya cak! Can bayan kimanin minti biyu suka ji murya a shasshaƙe tana magana a hankali kamar tsohuwa taci gaba da magiyar susa fitar da ita daga nan gidan. Sau ɗaya suka yi gigin kallon idanunta bayan sun buɗe nasu idanun a tsorace basu sake marmarin kallonta ba, saboda idanun sunyi ƙuru-ƙuru fari-fari ruwan hazo-hazo babu ko ɗigon baƙi a ciki. Zubewa suka yi a ƙasa a gaban gadon da suka kwantar da ita a tsorace suka fara bata haƙuri, bata tanka musu ba har suka gaji da tsugunon bata bar magiyar da take yi ba. Da mugun gudu Agness ta fita daga gidan mai gadi yana tsaida ita bata tsaya ba har taje bakin titi ta samo shatan taxi. Inda Allah ya taimake ta mai motan bahaushe ne ɗan cikin tudun wada, tana faɗin adress ɗin ya ce yasan layin kinshasha amma baisan gidan Malamin ba, sai dai idan sunje yayi tambaya. Suka tsadance akan dubu biyu ta biya shi kuɗin ya ɗauketa suka koma gidan. Mai gadi sai kallonsu yake yi yana mamaki su kuwa basu san ma yana yi ba. Babban burinsu su aikata abinda take buƙata dan tserar da ransu da lafiyarsu, ranga-ranga suka sake ɗaukota daga cikin gidan suka kwantar da ita a bayan motar yaja daga shi sai ita suka bar unguwar suka miƙe titi dan zuwa unguwar rimi. Ajiyar zuciya mai nauyi suka sauke a tare duk su biyun. Kafin su ce komai muryar mai gadin ta daki dodon kunnuwansu "Linda me yake faruwa ne haka? wace wannan da aka tafi da ita?" A tsorace suka maida kallonsu kanshi cikin rasa abin cewa, tsananin ruɗewa da tashin hankali ma yasa sun manta da mai gadi a gidan. "Aunty... Aunty... Mercy ce tace a kaita wurin wani Dr." Tayi maganar a ruɗe tana nuna hanyar da motar ta ɓace da yatsarta manuniya. Kallon rashin yarda ya bisu da shi har suka shige cikin gidan da sauri basu ƙara sauraren abinda zai ce ba. "Amma bakya ganin munyi kuskuren ba shi ita ba tare da mun bi su mun ga gidan da zai kaita ba Linda?" "Wani kuskure kuma kike magana? Thank God mun rabu lafiya ba tare da ta yi mana wani mugun abu ba. Yanzu kawai muyi tunanin abinda zamu ce da su Madam ya faru da ita idan sun dawo." Ta faɗa a hankali tare da ɗosana mazaunanta a kan kujera, jikinta a sanyaye. "Me kuwa za mu faɗa musu da ya wuce gaskiyar abinda ya faru? kinsan matuƙar muka faɗa musu ƙarya a cikin ƙanƙanin lokaci za su binciko gaskiyar abinda ya faru." Tana gama maganar ta fita ta ɗauko tsintsiya da abin kwashe shara ta shige ɗakin da suka kwantar da Bibi dan tattara madubin da ya tarwatse, ta bar Agness zaune da tagumi hannu bibiyu. ***** ***** "Malam dan Allah nan ne gidan Malam Abdulganiyyu?" Ya tambayi wani dattijo da ya gani tsuguno a jikin famfon masallaci yana alwala, ya nuna gidan da ɗan yatsarsa manuniya, idonsa yana kan lambar gidan ashirin da huɗu da aka rubuta da manyan baƙi a wani ɗan ƙaramin allo aka manna a jikin bangon ƙofar gidan da yake kusa da masallacin. Sama da ƙasa dattijon ya kalle shi sannan ya maida idanunsa kan kwararraɓaɓɓiyar motar da ya zo da ita. "Eh nan ne, lafiya?" "Eh to lafiya ƙalau. Daman wata mare lafiya ce aka ce in kawo ta wajenshi." "To Madallah! Allah ya bata lafiya, Malam ga shi can yana jan sallah. Sai ka jira shi a nan har a idar ko kuma kayi alwala ka shiga sallar dan ka samu jam'i." Bai jira cewarsa ba ya shige cikin masallacin da sauri. BILHAƘƘI Jikin motarsa ya koma ya jingina yana jiran a idar da sallar, zuciyarsa cike da saƙe-saƙen gara ya bar sallar idan ya koma gida sai yayi. Lokaci bayan lokaci yana leƙa kansa ta glass ɗin motar dan ganin a wane hali take ciki? sai yaga har lokacin tana nan kwance cikin fita haiyaci kamar yadda ya ɗaukota. "Assalamu alaikum." Malam ya faɗa a tausashe sannan ya miƙa mishi hannu suka yi gaisuwa irinta addinin musulunci. "Malam lafiya dai ko? yanzu mun idar da sallah aka sanar da ni kana jira na a waje." Nan ya faɗa mishi duk yadda suka yi da su Agness sannan ya buɗe mishi bayan motar dan ya ga mara lafiyar. Gabanshi ne ya faɗi, nan da nan fuskar yarinyar cikin mafarkin da yake yawanyi a cikin kwanakin nan ya faɗo mishi a rai 'kamar ita?' Ya tambayi kansa a zuciyarsa. Sai kuma ya rufe ƙofar motar da sauri ya kalli direban, ganin hankalin mutane ya fara dawowa kansu ya ce. "Bari mai gadi ya buɗe get ka shiga da motar sai mata a cikin gida su sauketa. Babu wani ƙarin bayani da suka yi maka kawai cewa suka yi ka kawo ta nan gidan?" Ya tambaye shi fuskarsa cike fal da mamaki. "Eh Akaramakallahu." Ya amsa yana sussunkuyar da kai. "To madallah. Ba laifi. Allah ya bata lafiya. Juyo da motar bari inyi magana da mai gadi ya buɗe maka ƙofa." Ya nufi cikin gidan da sauri shi kuma direban ya shiga motar dan juyo da ita ya shiga gidan kamar yadda Malam ya umarceshi. ****** ******* Danƙareren agogon bangon falon ya kalla, fuskarsa baiyane da matsanancin mamaki bayan ya ajiye wayar da ya amsa kiran Hajiya Shafa, ƙarfe goma saura kwata na dare. 'Wasu baƙi mata ne za su zo ganina a wannan lokacin baza su jira gari ya waye ba?' Ya tambayi kansa da kansa a zuciyarsa, amma da yayi tunanin ƙila ƙaƙƙarfar uzuri ne da baza a iya jiran wayewar gari ba sai ya zura takalmansa ya nufi cikin gidan ɓangaren Hajiya Shafa inda baƙin suke. Sallama yayi a ƙofar ɗakin ya jira aka amsa daga ciki kafin ya cusa kanshi cikin falon idanunshi cikin na maiɗakinsa. "Malam barka da shigowa" Hajiyar ta faɗa a ladabce, saida ya amsa sannan ta nuna mishi baƙi matan da suke son ganinshi. Ya kalle su a karo na farko yana karantar yanayinsu a cikin hasken ƙwayayen lantarkin da suka haske ɗakin kamar rana, sun sako dogayen riguna baƙaƙe har ƙasa, sun naɗe kawunansu da gyalen rigunan kamar wasu zuri'ar larabawa. A karo na farko suka gaishe shi idanunsu a ƙasa, kujerar kusa da Hajiya Shafa ya zauna sannan ya amsa gaisuwarsu a mutunce. "Madallah. Bayin Allah daga ina kuke? Ban shaida fuskokin ba." Kafin su ce komai ɗaya daga cikinsu ta fara shessheƙar kuka tana jan hanci, sannan ta fara magana da rawar murya "Malam ni sunana Maryam, ita kuma wannan ƴar'uwata ce sunanta Aisha. Ɗazu mun fita siyayya kasuwa da muka dawo sai bamu tarar da ƙanwarmu da bata da lafiya a gida ba. Ko da muka tambayi masu aikin da suke tare da ita sai suka ce wai an kawo ta nan gidan. Shi ne muka zo mu tafi da ita." Shiru yayi yana karantar yanayinta, baisan me yasa ba haka kawai yake ji a ransa bai yarda da su ba. Tun ɗazu da aka kawo mare lafiyar yasa su Hajiya Shafa suka yi mata wanka da ruwan magani, suka saka mata kaya na mutunci, ko da ya ƙare mata kallo da kyau ya fahimci tabbas ita ce yarinyar da yake mafarki tana neman taimakonsu. Rayuwa take a tsakankanin matsafa ko daga ina take bai san wane dalili ne yasa Ubangiji ya turo ta gurinsa ba, dan haka zaiyi iya bincike sosai har sai ya gamsu da gaskiyarsu kafin ya basu ita, ko zai basu ita ma sai ta samu lafiya sosai ya ji daga bakinta tabbas waɗannan ɗin yayyinta ne kamar yadda suka faɗa sannan zai damƙa musu ita. "Amma abin da mamaki, kika ce ita ɗin ƙanwarku ce?" Ya tambayi wacce ta kira kanta Maryam yana tsattsare ta da idanunsa masu cike da kwarjini. Majinar kuka ta sake ja ta ɗago jajayen idanunta karaf suka haɗa ido, saukar da nata idanun tayi ƙasa jikinta babu inda baya rawa "E ! Eh wallahi da gaske nake yi. Aisha kiyi mishi bayani mana." Ta ƙarasa maganar tare da zungurin cinyar abokiyar tafiyarta. Cike da taraddadi da maganarta mai baiyana alamar ita yare ce dukda hausan ya zauna a bakinta ita ma tace "Malam ka taimaka ka bamu ita, idan muka koma gida ba da ita ba wallahi iyayenmu zasu yi fushi da mu..." "Ma sha Allahu! Tunda iyayenku suna raye gobe in Allah ya kaimu ku dawo tare da su. Akwai wasu ƴan tambayoyi da zanyi musu idan na gamsu da amsoshin salin-alin zan baku ita ku tafi." Yayi maganar da dakakkiyar muryarsa tare da miƙewa tsaye alamun ya gama saurarensu. Tsam suka yi da ransu, cikin su biyun an rasa wacce zata sake cewa komai. Kawunansu a ƙasa alamu ƙarara ba hakan suka so ji daga bakinsa ba. Maryam ta sake fashewa da ƙaƙƙarfar kuka ta zube daga kan kujeran gwuiwoyinta a ƙasa. "Dan Allah Malam kayi haƙuri karka jefa mu cikin bala'i, wallahi idan muka koma gida ba tare da Bibi ba zamu shiga cikin mummunan masifa..." "Wa'iyazubillahi! sai kace ba musulmai ba? wane irin masifa kuma ana zaune ƙalau? anya ma maganganun da kuka faɗa min gaskiya ne? Ban ga alamun gaskiya a tattare da ku ba. Shafa'atu kira min Lukman yazo da yaransa su bincika min waɗannan mutanen ban yarda da su ba." Da sauri suka miƙe tsaye jin ƙarshen maganarsa, sum-sum suka nufi hanyar ficewa daga falon ba tare da sun sake cewa komai ba. "Ku tsaya mana idan ku yayyinta ne da gaske..?" "Za muje mu taho da iyayenmu ne." Maryam ta faɗa cikin zafin rai tana zura takalminta da yake ajiye a ƙofar ɗakin, ita kuwa Aisha har ta kusa ficewa daga gidan zuciyarta cike da tsoron tsohon Malamin mai masifaffen wayau da saurin fahimta. Tana fita ta ƙaramin ƙofar gidan Maheer yana sanyo kanshi zai shiga gidan, kaucewa yayi har saida ta wuce sannan ya shiga yana waigenta. A zuciyarsa yake tunanin su kuma waɗannan me ya kawo su gurin Malam a daren nan? Dan ya ga Aisha jingine da motar da suka zo da ita tana jiran fitowar Maryam daga cikin gidan. Ko da ya shiga cikin gidan kai tsaye ɗakin Mahaifiyarsa ya nufa nan ya tarar da su suna kakabin maganar. "Gara da kayi musu haka Malam, kana ganin waɗannan matan ka ga tsofaffin kwanti-kwan. Fuskarsu ta sha bilicin da ganinsu ba mutanen arziki bane. Idan ka gama binciken in da gaske ƙanwar tasu ce a basu ita daga baya amma ba a wannan halin da take ciki ba." "Ni duk ba ma wannan ba Shafa'atu. Ɗazu direban nan yace min ƴanmatan da suka ce ya kawo ta nan gidan sun faɗa mishi ita tace su kawota nan ɗin kuma ita ta bada kwatancen nan gidan. Dole ina buƙatar yi mata wasu ƴan tambayoyi bayan ta warke kinga batun in basu ita ma bai taso ba." Ya maida hankalinsa kan Maheer yana amsa gaisuwarsa sannan ya ce "Yauwa Magaji, zo ka gani." Ya ja shi har zuwa ɗakin baccin Ummee inda aka kwantar da Bibi akan gadonta, dukda akwai hasken ƙwanlantarki a ɗakin sai da ya sake haska mishi fuskarta dan ya ganta sosai. "Ko kasan wannan yarinyar?" Gabanshi ne yayi mugun faɗuwa, cikin ƙanƙanin lokacin walwalarsa ta ɓace ransa yayi mummunar ɓaci. Tsaf ya gane ta, yo ai dole ne ma ya gane ta, duk da tsananin tsanar da yayi mata da kuma ko a mugun mafarki baison ya ga fuskarta ba'a ɗauki dogon lokacin da zai ganta ya ce ya kasa shaida ta ba. 'Yanzu wannan mayyar yarinyar har nan gidan iyayenshi ta biyo shi kenan?' Kamar zai ce wa Malam bai santa ba amma da yake ƙarya ba halinshi bane sai kawai ya ɗaga kai, alamun eh ya santa. Cike da ɗoki Malam ya dafa kafaɗarsa fuskarsa fal da murmushi ya sake maimaita tambayar "Da gaske ka santa Magaji?" "E na santa Malam, amma ba a garinnan na santa ba." Ya amsa muryarsa a cuccushe. Hannunsa kawai Malam yaja suka fice daga ɗakin zuwa ɓangarensa, Hajiya Shafa ma da tayi niyyar biyo su dan jin inda aka haihu a ragaya dakatar da ita Malam yayi yace ta koma ta kunna wa mare lafiyar karatun Alƙur'ani mai girma ta jira dawowarsu. Suna shiga ya maida ƙofar falon ya rufe, ya zaunar da Maheer akan kujera shi ma ya zauna a gefensa kamar wasu abokai. "Magaji faɗa min inda kasan yarinyar nan ka ji? kar ka kuskura ka ɓoye min komai nima akwai abinda zan faɗa maka game da ita." Nan da nan Maheer ya warwarewa mahaifinsa inda ya santa da duk abubuwan da suka faru tsakaninshi da ita, yana maganar shi kuwa Malam murmushi kawai yake yi yana jinjina girman hikima da iko irin na Ubangijin sammai da ƙassai mai kowa mai komai. 'Yana nan yana ta addu'ar Allah ya bata kariya a duk inda take ashe ta taɓa haɗuwa da ɗansa wanda a mafarki take kira garkuwarta harta faɗa cikin matsanancin soyayarsa. Ko da ya fahimci Maheer ya gama ba shi labarin sai shima ya fara warware mishi bayanin duk irin yadda yake ganinta a cikin mafarki da yadda take neman taimakonsu. Ya ƙarƙare maganarsa da cewa "Da wannan dalilin yasa ko da na dawo Semina naga halin da Surayya take ciki ba wani ci gaba a asibiti shi yasa nace a sallame ta, kuma kaga cikin hukuncin Allah yanzu an samu ci gaba sosai tana mommotsa jikinta kaɗan-kaɗan, babbar matsalar kawai a yanzu maganar da bata iya yi sai dai tayi ta bin mutane da kallo." Kanshi ne ya buga, ransa ya ƙara ɓaci, zuciyarsa ta sake cika da matsananciyar tsanarta, babu abinda ya fahimta a maganganun Malam sai ciwon da Surayya take yi da sa hannun Bibi a ciki. Shi kam ko da matan duniya sun ƙare me zaiyi da wannan ƴar iskar yarinyar? yarinya ƙarama amma tun bata tafasa ba tana neman ƙonewa... "Magaji tunanin me kake yi haka ina ta magana ka yi shiru?" Malam ya katse mishi tunani ta hanyar girgiza kafaɗarshi da sauri. "E... na'am?" Ya faɗa a ruɗe, ganin irin kallon da Malam yake mishi sai yayi ƙoƙarin daidaita kanshi cikin nutsuwa ya sake cewa "Ni abinda ban fahimta ba zaman me zata yi a gidannan Malam? yarinyar nan tun a garinsu na fahimci ba ƴar arziki bace ko daga irin kayan da take sawa masu baiyana tsiraicinta. Ni ina ga idan sun zo gobe kawai ka basu ita su tafi da ita can su ƙarata, idan akwai abinda zamu taimaka mata da shi bai wuce addu'a ba. Amma ni dai ban goyi bayan zamanta a gidannan nan ba..." "Gidanka ko gida na?" Malam ya katse shi cikin fushi fuskarsa a tamke, ashe tunda Maheer ya fara magana yanayin fuskarsa ya canza amma bai lura ba sai da ya dire. "Ka yi hakuri Malam, Allah ya huci zuciyarka. Duk yadda ka ce haka za a yi." Ya faɗa a ladabce hankalinsa a tashe. "Babu komai Magaji, je kaga iyalinka ka wuce gida, sai gobe idan Allah ya kaimu." Yana gama faɗin haka ya shige ɗakin barcinsa ya barshi nan a tsugune. Gwuiyawunshi a saɓe ya miƙe ya fice daga falon, gurin Mahaifiyarsa ya koma sai ya tarar da ita tana sallar shafa'i da wuturi, daga can cikin ɗakinta kuma inda Bibi ke kwance karatun Alƙur'ani mai girma ne yake tashi a hankali cikin zazzaƙar muryar Alaramma Abdullahi Abba, cikin suratul Baƙara aya ta ɗari da biyu. Ɗakin Mummy ya shiga ya tarar da ita da casbaha a hannunta, da alamun ita ma sallar ta idar. "Magajin Malam ne a daren nan?" "Ni ne Mummy, barka da dare" Sama-sama suka gaisa saboda dare yayi, yayi mata sai da safe ya fice daga ɗakin. Ko da ya leƙa ɗakin da Surayya take sai ya tarar duk sunyi bacci ita da Inna Lantana, dan haka ya fice daga ɗakin yaja musu ƙofar ya kulle. Gurin Ummee ya koma yayi mata sai da safe ya fice daga gidan ya hau motarsa a waje ya nufi gidansa. A wannan daren ko Rabi sai da ta fahimci yana cikin damuwa, yadda ya koma gidan ba haka yanayinsa yake sadda ya bar gidan ba, sam ya kasa walwala. Tayi tunanin ko jikin Surayya ne sai yace mata ba haka bane, juyin duniya kuma yaƙi faɗa mata abinda yake damunshi dole ta ƙyale shi ta zuba mishi ido. Ya daɗe baiyi bacci ba sai juye-juye yake yi yana saƙawa yana kwancewa, shi kaɗai yaita jan tsaki zuciyarsa a ƙuntace, har gaf da asubah sannan wani nannauyan ɓarawo bacci yayi nasarar sace shi cike da muggan mafarkai mabanbanta duk a kanshi da Bibi. ****** ****** "Mery..." Aka ƙwalla kiran sunanta cikin murya mai tsananin ƙarfi da hauhawa wanda yasa duk wani lungu da saƙo na cikin babban ɗakin tsafin amsa kuwwar sunanta. Cikin tsawa da baiyana tsananin fushi aka cigaba da magana da muryoyi mabanbanta daga ko wani bango na ɗakin "Garkuwa yana daf da yayi mummunar fushi da ke Merry... ki kawo Bibi a cikin ƙanƙanin lokaci matuƙar kina so Garkuwa ya share miki hawaye... Merry... Merry... Merry..." Aka ci gaba da ƙwalla kiran sunanta cikin sauti mai baiyana ƙwaƙƙwaran kashaidi da jan kunne, hakan yasa ta ƙara ruɗewa, tana gurfane gwuiwa bibbiyu a gaban Oga, yafe take da wani jan ƙyalle a jikinta saɓanin sauran ƴan ƙungiya da suke sanye da shuɗayen riguna da jan ƙyalle a kawunansu, wannan jan ƙyallen da ta yafa babban alama ne da yake nuna ita mai laifi ce a ƙungiyar. Ba abinda take yi sai kuka. "Karki bari fushin Garkuwa ya sauka a kanki dan rayuwarki za ta ɗaiɗaice... rabuwar Bibi da ƙungiya tamkar tarwatsewar rayuwarki da na duk wani makusancinki ne Merry..." Ɗif sautin muryoyin ya ɓace kamar anyi ruwa an ɗauke, can kuma sai aka ƙyalƙyale da wani matsiyacin dariya da murya mai kama da na gyare, tsawon lokaci kafin dariyar ma ta ɗauke ɗif! Hannu Oga ya miƙa mata ta kama da sauri, jikinta babu inda baya rawar ɗari. "Sadaukar da jinin wacce kike tsananin so a zuciyarki dan lallashin Garkuwa ya ƙara miki lokaci." "Rose" Ta kira sunan tana kuka, ƙannenta biyu duk ta sadaukar da su a ƙungiyar, a yanzu babu wacce take ji tana so a zuciyarta da ta wuce Rose ɗin, ita ma ga shi yau ta bada jininta. Runtse ido yayi ya daki bangon yamma na ɗakin sai ga hoton Bibi ya baiyana a kwance tana bacci cikin kwanciyar hankali, a gefenta Ummee ce take sallar nafila. Ga karatun Alƙur'ani da yake tashi a hankali cikin ɗakin. "Kinyi sake Merry, kin bari Bibi tayi masauki a muhallin da duk tsafin matsafi sai dai ya zuba mata ido. Matuƙar tana tare da waɗannan iyalan babu wani abu da muka isa mu aika mata daga nan. Aiki ne ja a gabanki, cikin sati biyu ki san duk yadda za kiyi ki rabata da waɗannan mutanen ki dawo da ita cikinmu, suna da matuƙar haɗari a gare mu, ko ma me za kiyi dole ke kiyi in ba haka ba duk abinda Garkuwa ya saukar miki ki kuka da kanki." Ya zagi bangon nan take hoton ya ɓace komai ya koma yadda yake kamar wani abu bai taɓa baiyana a gurin ba. Dungulmin hannunsa ya nuna a jikin bangon kudu yana ƙwalla kiran sunan Rose haɗe da wasu surutai na tsafi da shi kaɗai yasan ma'anar abinda yake faɗe, nan take hoton Rose ya baiyana a jikin bangon kamar a majigi, tana kwance a kan gadon asibiti tana bacci cike da kwanciyar hankali. Alamun sauƙi sosai ya baiyana a jikinta, dan har ta ɗan ƙara kumari saboda hutu da kyakkyawar kulawar da take samu a asibitin. Kunnenta ya daka nan take jini ya fara ɓulɓulowa daga cikin kunnen kamar an buɗe famfo, da sauri ya tara babban ƙwarya jinin yana zuba a ciki har saida ya cika taf sannan jinin ya daina zuba hoton Rose ya ɓace, ya ɗauko ƙwaryar da hannu biyu ya ɗaga sama ya runtse ido yayi wasu maganganu sai ya sake ƙwaryar, kamar zai faɗo sai kuma ƙwaryar yayi sama a hankali har ya isa saman rufin ɗakin ya tsaya cak. Nan take masu matsaloli a ƙungiya suka fara zuwa gaban Oga ɗaya bayan ɗaya suna yi mishi sujada sannan su faɗi matsalolinsu shi kuma ya miƙa musu koke a gurin Garkuwa, da haka har suka gama taron duk suka ɓace kowa a cikinsu ya baiyana a makwancinshi. BILHAƘƘI "Ki yi haƙuri mana Marry, kiyi shiru haka nan. Is ok! Ni ina ganin kuka da damuwa ba shi ne solution ba. Ki kwanta ki huta gobe sai muyi maganar yadda zamu ɓullowa Malamin nan tunda kina da isasshen time da za ki dawo da ita." Tayi maganar cikin rarrashi, ta juya mata baya tana ƙara jan bargo, hannu ta miƙa ta ja wani ɗan igiya a gefen gadon nan take ƙwan lantarki mai haske ya ɗauke mai duhu ya baiyana. Rufe idanu tayi alamun ko wane lokaci tana maraba da ɓarawo bacci yayi awon gaba da ita. Taja wani dogon nishin kuka mai tafe da kakkauran majina, tissue ta ɗauka a gefen gadon ta fyace majinan, sai kuma ta ci gaba da sauke ajiyar zuciya akai-akai, ita kam ta shiga uku sau uku. Babu abinda yake ƙara ɗaga mata hankali a duk cikin abinda yake faruwa da ita sai idan ta tuno jimlar 'Fushin Garkuwa yana daf da sauka a kanki Merry...' Da ta zo nan a tunaninta sai wasu sabbin hawayen su sake ɓalle mata shar-shar kamar an buɗe famfo. Tsawon shekarun da tayi a ƙungiyar mutane biyu kawai ta taɓa ganin fushin Garkuwa ya sauka a kansu. Yadda suka ɗaiɗaice cikin ƙanƙanin lokaci bayan an gama wahalar da su haɗe da gana musu azaba shi ne abinda yake ƙara ɗaga mata hankali. Na baya-bayan nan da fushin Garkuwa ya sauka a kanshi shi ne Alhaji Zangina. 'Shekaru talatin da biyu suka kwashe shi da matarshi suna yawon neman haihuwa daga wannan ƙasa zuwa wancan ƙasa, basu samu ba sai da suka cika shekaru talatin da biyu cif da aure. Ba zato ba tsammani kwatsam ciki ya ɓulla a jikin matarshi Lailah. Murna a gurinshi faɗe ma ɓata baki ne, har a gurin Garkuwa ya sha neman tabarraki ga ɗan tun kafin ma a haife shi, da fatan matarshi ta sauka lafiya har zuwa lokacin da ta haifo zankaɗeɗen ɗa namiji mai tsananin kama da jinsin larabawa, ga tsananin shiga rai ga duk wanda ya ɗauke shi. Tsabar murna, ɗoki, zakwaɗi, matuƙar farin-cikin haihuwar ɗan Gaske yasa Alhaji Zangina ya dinga ɗiban manyan kuɗaɗe da manyan kadarorinsa yana rarrabawa ga abokai da ƴan'uwansa. Idan ya bada kyauta kalma ɗaya tak yake son ji daga bakin mutum. Allah ya raya Ɗan Gaske. Kwanan jinjirin huɗu a duniya da tsakar daddare suna zaman meeting na ƙungiya kamar yadda suka saba Garkuwa yazo da buƙatar da ta jijjiga hanjin duk wani member na ƙungiyar, buƙatar shi ne dole Alhaji Zangina ya sadaukar da jinin wannan jaririn a gare shi, Oga ya ƙara da cewa barin jaririn ya girma babban masifa ne kuma barazana ne ga ƙungiyarsu da shi kanshi Alhaji Zangina. Kawar da shi tun yanzu kuwa arziki da ƙarin buɗi da samun babban shugabanci a ƙasar nan ne ga mahaifinsa. Nan Alhaji yayi tsalle ya dire hankalinshi a tashe, idanunshi a rufe da alamun ya mance a inda yake ya ce babu uban da ya isa ya sha jinin jaririnshi, ko da girman jaririn zai zama ajalinshi da ajalin kowa na cikin ƙungiyar. Ƙwaryar tsafin da yake a mazaunin kamar ruhin Alhaji Zangina cikin fushi Oga ya kunna wuta da dungulmin hannunshi, naman jikin Alhajin ne ya fara zaizayewa yana narkewa a hankali kamar kitse, sai ihu yake yi yana make-make da buge-buge, sai da ya wahala sosai daƙyar yake iya motsi sannan Oga ya kashe wutan. Nuni yayi a bango sai ga hoton jinjirin kwance a tsadadden gadonshi na jarirai yana bacci hankali kwance, Da ƙarfin tsafi Oga ya zuƙe jinin jinjirin ta babbar yatsar ƙafarsa a gaban idanun Alhaji Zangina, matarsa Laila da ta kasance cikon farin-cikinsa tunda duk ya gama sadaukar da iyayensa ga Garkuwa ita ma tana bacci a makeken gadonta aka zuƙe jinin jikinta ta agarar ƙafarta. Ganin wannan babban abin baƙin-ciki da ɗaga hankali yasa shi yanka wani mahaukacin ihu ya fara fiffisga yana mimmiƙewa kamar sabon shiga a hauka, ya zura a guje zai kaiwa zakaran wuyan Oga cafka ayi mutuwar kasko da sauri Oga ya nuna shi da yatsar ƙafarsa nan take ya zama ƙatoton alade. Tun da Oga ya shafi kan aladen ya ɓace ɓat har yau da aka doshi shekaru biyar da faruwan al'amarin basu sake jin ɗuriyar Alhaji Zangina ko wani abu da ya shafe shi ba.' Tana zuwa nan a tunaninta ta sake fashewa da wani matsiyacin kuka tana surutai haɗe da tsinewa Bibi da su Agness da suka yi sanadin barinta gidan. "Oh my God ! Merry gaskiya zan barki kiji da damuwarki ke kaɗai in dai baza ki barni inyi bacci ba. Na gaji sosai ina buƙatar hutu, mun fita tun yamma muna gurin Lion har dare, mun dawo bamu huta ba saboda gudun da Bibi tayi kin ce dole muyi shigar muslims muje mu dawo da ita a gidan Malamin nan, bamu daɗe da dawowa ba mun shiga meeting yanzu kuma mun dawo kin hana mu huta me yasa hakan?" Ta ƙarasa maganar cikin fushi idanunta a ƙanƙance, sosai bacci yake a idanunta amma sukur-sukur da shessheƙar kukan Merry ya hana ta samu baccin a cikin nutsuwa. "Yi haƙuri Mercy, pls gobe za ki sake rakani gidan Malamin nan...?" "A'a!" Ta faɗa kai tsaye tare da sake juya mata baya tana jan wani dogon tsaki. "Abbeg in baki shirya yin bacci ba ki koma ɗayan bedroom ɗin ina so in huta." Ta sake jan tsaki haɗe da jan bargo ta rufe har saman kanta. Tana jin sadda Merry ta fice a ɗakin, kanzil bata ce mata ba sai ma ta rakata da harara. Nan da nan kuwa bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita. ******* ****** Cikin hukunci da ƙudura irinta Ubangijin sammai da ƙassai mai kowa mai komai SWT da sassafe Bibi ta farka lafiyarta ƙalau, kamar ba ita ce jiya ta yini ta kwana a cikin halin mutu kwakwai rai kwakwai ba. Babu abinda yake tashi a bakunan Malam da iyalinsa sai ma sha Allah Alhamdulillah, fuskokinsu ɗauke da matsanancin farin-ciki. Sai da ta rama duk sallolin da suke kanta, tayi wanka da ruwa mai zafi-zafi ta gargasa jikinta. Ummee ta haɗa mata tea mai kauri ta sha hanjinta ya warware. Ko da aka ce a kawo mata abinci mai nauyi ta karya da shi a kunyace idanunta a ƙasa ta ce ta ƙoshi da tea ɗin, a bar abincin sai anjima. Malam ne ya kira ta falonshi da matansa biyu sannan ya umarce ta da ta faɗa mishi gaskiyar ita wacece? Daga ina take? Wa ya bata kwatancen gidanshi? ya ƙarasa maganar da yi mata gargaɗin kar ta kuskura tayi mishi ƙarya, domin matuƙar ya gano tayi mishi ƙarya a cikin labarinta zai ɗauki mummunan mataki a kanta. Kafin ta ce komai Maheer ya cusa kanshi cikin falon bayan yayi sallama an amsa mishi. Ganinta a zaune digirgir a gaban su Malam abin ya bashi mamaki ƙwarai, jinjina kai kawai yayi, zuciyarsa cike da mamakin ƙwarewarta a makirci. A tsaitsaye ya gaida su Malam ya juya da nufin ficewa daga falon sai Malam ya tsaida shi. "Nemi guri ka zauna" Runtse ido yayi duk ransa a ƙuntace ya nemi guri a kan kafet ya zauna kusa da ƙafafun Malam, ita ma tana zaune a ƙasa ne kusa da ƙafafun Ummee, tunda ya shiga cikin falon idanunta ƙyam a kanshi zuciyarta cike da farin-cikin ganinsa har fuskarta ya gagara ɓoye hakan, shi kuwa sam ya ƙi yarda ko da wasa ya haɗa ido da ita. "Yarinya ke muke saurare" Mummy ta faɗa tare da dafa kanta dan dawo da hankalinta kansu. Idanunta ta sauke ƙasa, ta haɗe hannayenta biyu tana matsawa a hankali. "A haƙiƙanin gaskiya ni kaina bansan ko ni wacece ba." Da sauri duk suka ɗaga kai suna kallonta fuskokinsu baiyane da matsanancin mamaki, Maheer kuwa tsaki yaja a zuciyarsa dan tuni ya daɗe fahimtar ita ƙwararriya ce a fagen rainin wayau. Bata damu da irin kallon da suke bin ta da shi ba a sanyaye ta ci gaba da cewa. "Abinda zan iya tunawa kawai tun ina ƴar ƙanƙanuwa na rayu a mabanbantan gurare a hannun mabanbantan mutane. Waɗanda ƙarancin shekaru na a wancan lokacin bazan iya tuna su ko inda suke a yanzu ba. Sama-sama wacce nake iya zaman da nayi a gurinta wata baiwar Allah ce Maman Ushe. Bayan rasuwarta ne na haɗu da Madam Merry wacce har zuwa na nan gidan ina tare da ita." Cikin nutsuwa da kwantar da kai ta ci gaba da basu labarin duk wani abu da ta iya tunawa dangane da zamanta da Madam Merry har zuwa haɗuwanta da Maheer, da yadda tayi ta binshi da soyayya yana gwasaleta, haɗuwarta da Yusuf har ya bata adress ɗin gidan Malam. Da irin yadda Madam ta shiga tashin hankali bayan ta faɗa mata ta faɗa soyayya har zuwa kiran da Oga yake yi mata ta fice daga haiyacinta, har zuwanta nan gidan. Ta baiyana musu komai iya yadda ta sani. Tunda ta fara faɗan sarƙaƙan abubuwa masu matuƙar rikitarwa da ɗaure kai game da tarihin rayuwanta jinjina kai kawai suke yi, cike da mamaki har zuwa sadda tayi shiru alamun ta gama. Ummee da Mummy kallonta kawai suke yi suna mamakin ƴar ƙanƙanuwan yarinya ɗauke da manyan al'amura a cikin rayuwanta. Shi kuwa Maheer kanshi a ƙasa yake jujjuya maganganun a zuciyarsa, idan wani sashe na zuciyarsa ya ƙaryata labarin da ta basu sai wani sashen ya gasgata ta, dan tun a haɗuwarsu ta farko ya haƙƙaƙe bata da wani tsayayyen mai faɗa aji a rayuwarta, duba da yadda tayi ta liƙe masa kuma tana ziyartarsa a duk sadda ta so, ba tare da duba tsawon dare, sassafe ko tsakar rana ba. Da waɗannan tunane-tunanen da saƙe-saƙen sai zuciyarsa ta tsaya cak a guri ɗaya, shi kanshi bazai ce ga ainahin abinda yake ji game da ita ba. Tausayinta yake ji ko kuwa haushinta ya kamata ya ji? Ga Malam kuwa ya samu gamsassun amsoshin cukurkuɗaɗɗun tambayoyin da yake son ji game da ita. Da yawa daga cikin abinda suke ɓoye a cikin mafarkin da yake yawan yi da ita yanzu idonshi ya buɗe ya fahimce kusan komai. A karo na barkatai ya sake sauke nannauyar ajiyar zuciya yana kallonta. Kamar ya rasa ta cewa sai kuma ya daure cike da taraddadi ya ce "Bibi za ki iya barin Madam Merry ki dawo da zama ƙarƙashin kulawata da ta iyalaina?" "E zan iya!" Ta amsa kai tsaye ba tare da tunanin abinda ka iya zuwa ya dawo ba. Haka kawai take jin wani saukakken nutsuwa a cikin rayuwarta tun bayan dawowarta cikin hayyacinta, ta na ji a ranta zata iya ƙarƙare rayuwarta tare da Malam da iyalinsa da suke da wani girman matsayi na musamman a zuciyarta. A gefe guda kuma ga ta ga Gangaran ɓarinta, cikon farinciki da walwalarta. Ko da wasa baza ta taɓa yarda tayi sake da damar da yazo mata ba, waɗannan dalilan su suka tattaru suka sa tayi saurin amincewa buƙatar Malam. "Madallah! To daga yau ki ɗauke ni a matsayin mahaifinki, su kuma a matsayin iyayenki mata. Ina fatan zaki dage kiyi watsi da duk wani mummunan turba da mugun hali da Madam ta ɗora ki a kai? ki buɗe ƙwaƙwalwarki kiyi mata sabon zubi na kyakkyawan tarbiya da cikakkiyar rayuwa irinta addinin islama da za muyi iya ƙoƙarinmu wurin ɗora ki a kai. Kin gane?" "Eh na fahimta." Ta amsa a sace tana kallon Maheer duk da sam bata fahimci abinda maganganun Malam ɗin suke nufi ba. "Sunan Bibi ba shi da wata cikakkiyar ma'ana a musulunce, dan haka idan akwai sunan da kike so na hausawa mai asali ki faɗa mu dinga kiranki da shi kin ji?" Shiru tayi tana tunani, da kamar za ta ce Malam ɗin ya zaɓa mata sunan da ya dace sai kuma wani tunani ya gilma a can ƙasan zuciyarta. "Idan ina barci wani farin mutumi dogo yana yawan zuwa min da hawaye a fuskarsa, yai ta ce min in bar irin wannan rayuwar bai da ce da ni ba, yana kira na da wani suna mai daɗi amma yanzu na manta sunan." "Allah sarki. In Allah ya yarda yanzu ne za kiyi irin rayuwar da mutumin yake fata kiyi. Amma tunda kin manta sunan za mu dinga kiranki da Fatima. Idan kin tuna da wancan suna mai daɗin idan yana da ma'ana sai mu dinga kiranki da shi. Kin ji ko?" "Eh! Na gode Malam." Ya maida idununshi kan su Ummee. "Balaraba baki ce komai ba?" Murmushi tayi ta shafa kan Bibi, tana ƙara jin wani nutsuwa da tausayin yarinyar yana kwaranya a zuciyarta. "Bani da ta cewa Malam, sai addu'a da fatan Allah ya taya mu riƙo. Ko ba haka ba Mummy?" "Kin gama magana Ummee. Allah ya ƙara mana ƙwarin gwuiwa da haɗin kai a tsakaninmu." "Ameen ya Allah." Suka amsa gaba ɗaya. "Magajin Malam kana da abin cewa ne? Na ga kamar bakinka yana ta motsi tun ɗazu." Sosa ƙeyarshi yayi da makullin motarsa, yayi ɗan murmushi. "Ba komai Malam. Allah ya taya ku riƙo. In Allah ya yarda duk abinda take buƙata kamar sauran ƙannina kar ta ji shakkar faɗa min, zanyi iyakar ƙoƙarina gurin biya mata buƙatar duk abinda take so." Da alamun duk sun ji daɗin maganganun da yayi, sai zabga murmushi suke yi suna sa mishi albarka. "To kuje kai da ƙanwar taka ta gaida iyalinka. Ga mu nan fitowa. Fatima bi Yayanki kuje ki gaida maiɗakinsa da bata da lafiya." Ya ƙare maganar da sauke idanunshi a kan Bibi, hakan ya fahimtar da ita yake yi. Dan haka ta miƙe ta bi bayan Maheer suka nufi hanyar ficewa daga ɗakin. "Yauwa Malam na tuna sunan. BILHAƘƘI yake ce min." Ta faɗa da sauri ta juyo tana kallon Malam lokacin da take gaf da ficewa daga falon. "BILHAƘƘI?" Ya maimaita yana mamaki. "Eh! haka yake yawan ce min cikin kuka. BILHAƘƘI wannan rayuwar sam bai dace da ke ba. Tuntuni na ji ina son sunan" Ta ƙarasa maganar tare da sauke ƙwayoyin idanunta a ƙasa, a zuciyarta tana ƙoƙarin tuno yanayin damuwar da take gani danƙare da fuskar mutumin a duk lokacin da yazo mata a cikin barci. "Kinsan menene fassarar sunan?" "A'a!" Ta amsa haɗe da girgiza kai. "Da gaskiya." kallonshi tayi fuskarta da alamun rashin gane abinda yake nufi. "Sunan ne na fassara miki. Da gaskiya shi ne fassarar Bilhaƙƙi. Kalma ce mai kyau, babu laifi a sunan." Farare talatin da biyu ta buɗe su gaba ɗaya tana sakin tattausan murmushi mai haɗe da dariya. "Daga yanzu sunana Bilhaƙƙi ko Malam?." Dariya suka yi gaba ɗaya har da Maheer da yake tsaye a bakin ƙofar falon. "Ƙwarai kuwa Bilhaƙƙi." Ummee ta amsa tana dariya. Tafiyar kurame suka yi a tsakaninsu har suka ƙarasa ƙofar ɗakin, duk yadda take ta ƙoƙarin ta haɗa ido da shi ya ƙi bata damar hakan har suka shiga ɗakin da Surayya take jinya bayan an amsa sallamarsu. Da sauri suka koma da baya suka fice daga ɗakin ganin Inna Lantana tana sa mata kaya, da alamun wanka aka yi mata. Kamar haɗin baki duk sai suka nufi ɗakin Ummee. "Wash Allah na..." Ta faɗa a marairaice tare da zubewa ƙasa da hanzari ta kama babbar yatsar ƙafarta da hannu ɗaya hannu ɗaya kuma tana shusshushun zafi, nan da nan idanunta suka cicciko da hawaye. Da sauri ya ƙarasa gurinta cike da kulawa yake ƙoƙarin kamo ƙafar da ta riƙe "Ke me ya faru? Sannu. Mu ga ƙafar?" Sai ta sakar mishi ƙafar gaba ɗaya tana hawaye da rurin wayyo zafi. Ya gama dube-dube da jujjuya tattausar ƙafar haɗe da ɗaɗɗaga yatsar bai ga alamun komai ba. "Wai bigewa kika yi ko menene?" Ya tambayeta a tausashe yake kallonta, da yake ta riga shi shiga cikin ɗakin. "Ni ji nayi kamar wani ƙwaro ya cije ni." Tayi maganar cikin shagwaɓa tana tura baki gaba, ta kalle shi suka haɗa idanu tana mutsuttsuke ido da hannu ɗaya. Sai kuma tayi murmushin da yasa ya ramfo ta. "Ƙarya ko?" Ya tambayeta a hankali idanunsu cikin na juna. "A'a! to ba kaine ba duk ka wani ƙi kallona." Ta faɗa da wani irin salon magana da yasa shi yin shiru na wasu seconds yana ƙara kallonta. Sai kuma ya miƙe tsaye ya kama hanyar ficewa daga ɗakin bai ƙara yarda sun haɗa ba. "Sannu Aunty, Allah ya baki lafiya." Ya ji muryarta daga bayansa tana yiwa Surayya addu'a, sai a sannan ma yasan ta biyo bayanshi. Ya ɗago ya saci kallonta a hankali, yana jin wani abu da ya rasa gane ko menene yana tsungulinshi a ranshi game da ita. Karaf a idanun Surayya da tun shigowarsu cikin ɗakin idonta ke kan Maheer, duk sai taji ranta ya sosu. Da ta kalli Bilhaƙƙi sai taji ƙirjinta yayi wani mugun bugawa, kauda ido tayi daga kanta zuwa gefe ɓacin ranta yana ƙara ninkuwa. Ba komai ya ɗaga mata hankali ba sai zallar kyaun da ta gani da ɗanyen ƙuruciya, ga wani kwarjini na musamman da ta gani a fuskar yarinyar. Haka kawai a kallon farko taji ta tsane ta. Ta ɗaure fuska kuwa tayi katamau, ko ɗan murmushin da take yawan yi idan Maheer ya zo ganinta yau ta kasa yi. "Ayya... Sannu Aunty. Me yake damunta haka Gangaran?" Tayi masa tambayar fuskarta narke da tsananin tausayinta. Kallonta yayi tana naniƙe kusa da shi, ƙiris ya rage jikinsu su dinga gogan juna. Cikin hikima ya zagaya can gefen gadon kusa da Surayya ya zauna. "Cuta ce kawai daga Allah, amma da sauki sosai ma Alhamdulillah." Ita ma ƙara matsawa kusa da Surayya tayi ta kamo tafin hannunta na dama ta riƙe ta ƙura ido kamar tana karantar wani abu daga ciki. Ran Surayya in yayi dubu duk sun ɓaci, da ɗan ƙarfin jikinta da ta fara samu take ƙoƙarin ƙwace hannunta daga na Bilhaƙƙi, ita kuwa taƙi sakewa, sai tayi ma kamar bata fahimci me take ƙoƙarin yi ba. "Za ki warke soon. Sannu Aunty." Ta faɗa har lokacin yanayin tausayin bai bar fuskarta ba, idonta yana kan hannun. "Allah yasa hakan. Sake mata hannu na ga kamar ta gaji." Ya faɗa tare da amsar hannun Surayya ya sauke a kan katifan da take kwance. Duk sai suka yi shiru daga haka, ita Bilhaƙƙi ta maƙale ta ƙi fita shi kuma Maheer ya ƙi cewa ta fita. Hakan ya ƙara ɗugunzuma ran Surayya, da takaici ya ishe ta ga shi babu bakin ƙorafi kawai sai ta runtse ido kamar mai bacci. BILHAƘƘI BAYAN WATA SHIDA "Ummee ban ganta ba fa." Ya faɗa muryarsa a buɗe yana sake buɗe labulen falon sosai yadda zai iya ganin komai na ciki, tare da leƙa kansa ciki yana kalle-kalle. "To kila tana cikin ɗaki, ni dai yanzu nan na barta a falo tana kwance kitso." Ko kafin ta ƙarasa maganar ma har ya cire takalmansa ya shiga cikin falon, a bakin ƙofar shiga cikin bedroom ɗin ya tsaya yana ta doka sallama ta ƙi amsawa. Sai da ya kasa kunne sosai sannan ya ji kamar shessheƙar kuka. Yaye labulen ƙofar yayi yana kallonta, yadda ta ƙudundune a kan gado tana kukan sai abin ma ya bashi dariya, kamar wata ƴar Bebi. A hankali ya shiga cikin ɗakin yana ƙare mata kallo har ya ƙarasa kusa da gadon "Keeee... kukan fa? Uhmm! Wa ya taɓa ki?" Kanta na tsakankanin cinyoyinta take tura baki, a zuciyarta ta ce 'Ko rarrashi ma bai iya ba.' Kasa haƙuri tayi ta ɗago da kanta fuska jage-jage da hawaye ta galla mishi harara, ta sake maida kanta ƙasa ta ci gaba da kukan. "Kukan na shagwaɓa ne kenan?" Ya taɓe baki ya ci gaba da cewa. "Madallah! Ci gaba da yi. Ni bari in wuce tunda ba ki da abin cewa." Jin zai tafi da sauri ta ɗaga kanta ta kalle shi, sai taga yana nan inda yake tsaye. "Toh ba kai bane..." Sai kuma tayi shiru ta juya mishi ƙeya tana kumbure-kumbure da baki. Ya kalli gashin kanta da yake yala-yala mai yalwa ba laifi, ba shi da cika sai tsawo, washar da shi a ido kamar tayi saloon, ya sauka har ƙasan kafaɗunta, rabin kan a tsefe rabi a kitse. "Amma ba na hana ki zama babu ɗankwali ba?" Yayi maganar a tausashe. Da sauri ta yayimi hijabinta da yake ajiye a gefe ta rufe kan, ta juyo gaba ɗaya tana kallonshi idanunta a nannarke. "Ayya mana Ya Maheer ayya... dan Allah ka bani in ƙarasa zuwa dare ka ji?" "Na ƙi" "Dan Allah fa na ce?" "Tom na ji." "Za ka bani?" Ta tambaye shi cike da ɗoki tana murmushin farin-ciki. "A'a! yanzun nan fa kika gama galla min harara..." "Ayya mana... to yi hakuri ka ji Yaya Maheer ɗina? Magajin Malam. Babangidan Ummee da Mummy. Gangaran ɗin Bilhaƙƙi da gaskiya ba da kanka a sare ka je gida ka ce ya faɗi." Ta ƙarasa haɗe da ƙyalƙyalewa da dariya da sauri ta koma can cikin gadon ta duƙunƙune kanta da bargo, har lokacin bata daina dariyar ba. Shima murmushi yayi kawai yana kallonta, ya rasa inda ta koyo harhaɗa wannan sunayen da kirarin da take mishi a wasu lokutan, duk da ta canza sosai amma har lokacin wannan masifaffen surutun nata musamman a gabanshi bata daina ba. "Zo kiji." Maƙale kafaɗa tayi alamun ta ƙi. "Shi kenan! ashe bakya son wayar." "Laaa ina so mana, dan Allah ka bani." Ta dirgo daga kan gadon ta bi bayanshi suka fice daga ɗakin. Da sauri ta cimmishi a falon suka jera kafaɗa da kafaɗa dukda ya kere ta tsawo sosai. "Allah zan cewa Malam ya sai min waya tunda jan rai kake min duk sadda na ce ka bani aro..." "Karki ce mishi, zan sai miki nan gaba kaɗan idan lokaci yayi" Ya faɗa muryarsa ƙasa-ƙasa ganin sun kusa isa inda su Ummee ke zaune a tsakar gidan suna shan iska. Gaishe su ya sake yi a karo na biyu yayi musu sallama da cewar zai wuce gida. Saƙon gaisuwa ga matansa suka bashi ya kama hanyar ficewa daga gidan tana biye da shi a baya. "Ba ni to." Ta faɗa tare da miƙa mishi hannu. Wayarsa ya zaro a aljihu ya miƙa mata, sai da ta kusa karɓa sai ya janye wayar ya hanata. "Awa ɗaya kacal na baki Yarinya zan dawo in karɓi wayata." "Eh na yarda." Ta amince da sauri tare da miƙa hannu a karo na biyu. "Ke na ma fasa..." "Ummee kin ga..." "Riƙe riƙe ba dan halinki ba." Ya miƙa mata da sauri ta fisge ƙiris ya rage wayar ta faɗi a hannunta tayi saurin cafewa. "Bilhaƙƙi ya aka yi?" Mummy ta tambaye ta daga can inda suke zaune, hankulansu ita da Ummee duk yana kansu. "Ba komai Mummy." Ta waigo kanshi tayi mishi gwalo ta juya cikin gidan da sauri. "Ka gaida Antoci na" Ya tsinkayi muryarta lokacin da take daf da shigewa ɗakin Ummee. Murmushi kawai yayi ya fice daga gidan, ya ɗauki motarsa a ƙofar yaja da sauri ya nufi gida ganin magrib ta kawo jiki, baya so a kira sallah yana hanya. Ita kuwa can cikin ɗaki ta ƙule tayi ɗai-ɗai a kan gado ta buɗe wayar, wani korian film mai kyau ta ɗauko a youtube yau kwanaki uku kenan, ta fara kallo sai ya amshi wayarsa. Shi yasa kullum idan ya shigo ta dinga binshi tana mishi na ci kenan shi kuma yana ja mata rai, sai yau Allah ya ɗora ta a kanshi ya sake bata wayar. A hankali zamanta a gidan yasa wani gwaggwaɓar shaƙuwa ya shiga tsakaninshi da ita. Tun yana ɗari-ɗari da ɗaɗɗaure mata fuska har ya watsar da komai yake kallonta da babbar matsayi irinta Yaya da ƙanwarsa. Idan ya shiga gidan bai ganta ba ya dinga damuwa kenan yana nemanta ɗaki-ɗaki tunda sam ba fita take yi ba. Idan bacci take yi haka zai ta jan ƙafa ko zata tashi, idan bata tashi ba sai ya fice yana jin wani irin babu daɗi a zuciyarsa. Ita da Saudat da suke sa'anni kansu a haɗe yake, danma ita Bilhaƙƙi bata saba irin harka da sa'anninta ba sai ya zama ta fi sakewa sosai da su Ummee. Ta fara kallon kenan kiran Surayya ya shigo wayar, ta gane hakan ne ta hanyar sunan da yayi saving ɗin lambarta. "First wife" Ta maimaita a fili tana kyaɓe baki, shere wa tayi har kiran ya katse ta sake maida hankali kan kallon da take yi. Ganin kiran ya sake shigowa a karo na biyu kawai sai ta danna madannin amsa kira ta ɗauka, lokacin da kiran yake gaf da tsinkewa. "Sweetat ina ka tsaya ne?" Duk yadda taso danne dariyar ta kasa, sai da ta ƙyalƙyale da dariya jin yadda Surayyan ta maƙe murya ita a dole shagwaɓa take yi wa miji. "Aunty ba shi bane, yana hanyar zuwa gida. Kila ma yanzu yana daf da isa..." "Ke dakata da Allah ! Faɗa min, me wayarshi take yi a hannunki?" Ta tambaye ta cikin fushi da ɗaga murya, sarai ta ji dariyar da ta yi mata kuma ta san da ita take yi. Wata dariyar ta sake yi, cikin rashin damuwa da tsawar da tayi mata ta ce "Tunda yana hanyar gidan idan ya isa sai ki tambaye shi. Bye... ki gaida ɗayan Auntyn." Ta katse wayar tana ci gaba da ƙyalƙyala dariya da gangar dan dai ta ƙara kunnata. Ta kuwa ci nasarar hakan, dan sansarai tayi da wayar a hannunta ranta a ɓace, ita dai har a zuciyarta Allah ya sani ta tsani wannan Bilhaƙƙin. Ba dan komai ba kuwa sai dan irin yadda take wani shisshige wa mijinta bayan kuma basu haɗa komai ba. Ta ja tsaki ranta yana ƙara ɓaci, bari ya koma gidan zai same ta 'cikin hikima zan bugi cikinshi inji wai me ke tsakaninsu ne ma? Kar muna nan sake da baki garin kallon ruwa kwaɗo yayi mana ƙafa.' Ta sake jan tsaki a karo na biyu zuciyarta na ƙara ƙuntata "Shegiya da wani ƙulu-ƙulun idanu irinna mage." Ta faɗa a fili tana yanƙwane fuska kamar za ta fashe da kuka. Tana nan zaune har ya isa gidan, da yake gwana ce gurin ƙwarewa da abar sai ta watsar da komai a fuskarta ta fara tarairayarsa, dan ranar girkinta ne. Bata tarbe shi da maganar komai ba har ta haɗa mishi ruwan wanka ta taya shi ya sheƙa wanka, ya ɗaura alwala ya fice zuwa masallaci. Ko kafin ya dawo ta kusa cika ɗan madaidaicin teburin cin abincin da kala-kalar cimar da ta shirya mishi. Yana dawowa a gurguje ta barshi ya leƙa Rabi dan ganin halin da ta yini ya dawo ta ja shi zuwa gurin cin abinci. "Ai na kira wayarka na ji wannan baƙuwar yarinyar ta gidan Malam ta ɗauka..." "Yanzu ai ta wuce baƙuwa, ta zama ƴar gida." Ya katse cikin yanayin rashin ba wa maganarta muhimmanci. Ba ta daddara ba ta sake cewa, "Hakane kuma. Amma fa nayi mamaki sosai, dan har saida na tambayeta me wayarka take yi a hannunta amma sai tace min idan ka dawo in tambaye ka." Ta ƙarasa maganar fuskarta na burtso da yanayin ɓacin ran da take ta dannewa a can ƙasan ranta. Ya kalle ta sosai, sai kuma yayi murmushi ya ci gaba da shan fruit salad ɗin da ta haɗa mishi. "To shi ne kike tambayar tawa kenan kamar yadda ta umarce ki...?" "A'a fa!" Ta katse shi da sauri, ta ɗanyi murmushin yaƙe tare da saurin gyara zancen tun kafin ya ƙara cewa komai. "Kawai dai ganin yadda kake kaffa-kaffa da wannan babbar wayartaka saboda muhimman abubuwan da kake adanawa a ciki yasa nayi tambayar. Bayan wannan babu komai Sweetat." Shiru yayi kawai bai tanka mata ba, dan ya kwantar mata da hankali sai ya haske ta da tattausan murmushi mai narka zuciya. A can ƙasan ransa ya ce 'Mata? mata? sai a barsu da halinsu na kishi' ******* A cikin waɗannan watannin da suka gabata abubuwan duk sun zo wa Malam da iyalan gidansa da sauƙi fiye da duk yadda suke tsammani. Bilhaƙƙi ta warware sosai ta zama ƴar gidan Malam, idan ka kalleta kamar ba ita ce cikakkiyar ƴar rawan galar nan da tayi fice sosai a garin kacia ba. A yanzu ta zama wata nutsattsiyar yarinya wacce ilimin addini da kyawawan halaye suka ratsata sosai da sosai. Ta ƙara girma da cika, hankali da nutsuwa ga wata kunya ta musamman duk sun mamaye ta. Idan ta zauna tana yawan tunanin 'ita kam da me zata saka wa waɗannan iyalan?' Sai wani sashe na zuciyarta ya amsa mata da 'Sai dai addu'a kawai da fatan su cika da kyakkyawan ƙarshe.' Duk wani nauyi na ibada da Allah ya wajabta a kan wani baligin musulmi Malam da iyalansa sun koyar da ita. Ta koyi yadda za ta bautawa mahaliccinta da cikakken sani akan bautar, ta san farillai, sunnoni, mustahabbai na duk wani bauta da zata yi wa mahaliccinta. Da yake tana da matuƙar ƙwazo da ƙoƙarin mayar da kai akan duk abinda tasa gaba nan da nan ta iya harhaɗa baƙaƙe na larabci sai ƴan ƙalilan abinda baza a rasa ba. Ta san ƙabli da ba'adi, ta samu ilmi sosai daga ƙananun littattatafan addini irinsu Ahlari, Arba'una hadith, Sirah, Risala da sauran littafai. Malam da kanshi yake ƙara mata karatu safe da yamma. Tana da haddar izufi goma cas a ƙwaƙwalwarta, daga Suratul Ahƙaf zuwa Suratu Nasi. Har lokacin kuma bata daina ɗaukar karatun Alƙur'ani mai girma da sauran littattafai a gurin Malam ba. Madam Mary kuwa basu sake jin motsinta ba tun bayan da ta hayo iyaye na ƙarya ta kawo su a matsayin iyayen Bilhaƙƙi, cikin ƙanƙanin lokaci Malam ya ramfo su. Yayi musu kaca-kaca sannan ya kore su daga gidan, haɗe da zazzafan kashaidin muddin ta ƙara taka ƙafarta a cikin gidan ta tabbaci haƙiƙa hukuma ce zata raba su. Tun daga ranar bata ƙara waiwayar gidan ba, ko a wane hali take ciki ma oho. Ta tafi, amma kafin tafiyarta ta ɗaukar mishi wani alwashi ɗaya. "Gidannan da Bibi take ciki shi ne ya zama babban garkuwa kuma kariya a gare ta. Amma ina tabbatar maka da cewa duk ranar da ta sa ƙafa ta fice daga gidannan ka tabbaci haƙiƙa babu inda za ta faɗa sai hannunmu." Wannan maganar da tayi ya tsayawa Malam a rai, dukda kuwa a gabanta ya nuna ko a jikinshi. Da wannan dalilin ne ma yasa tsawon watanni shidan da Bilhaƙƙi tayi a gidan ko ƙofar gida bai barta ta fita ba. Dangane da batun tsafe-tsafen da suke damfare a jikinta kuwa da baiwar da take da shi na lalata abu idan abun ya ɓata mata rai yanzu duk sunyi sanyi sosai, Malam yana iya ƙoƙarinshi gurin yi mata zafafan addu'oi ya tofa a ruwa ya bata ta shanye safe da yamma. Kuma basa bari ta zauna cikin rashin tsarki saboda shaiɗanu, ako wani lokaci suna iya ƙoƙarinsu gurin ƙirƙirar duk abinda zai sanya ta cikin farin-ciki. Ko da kuskure ta aikata a hikimance cike da tausasan kalamai suke nusar da ita ba tare da lamarin ya ɓata ranta ba. Kusan a ko wani lokaci duk inda take zaune za a sami karatun Alƙur'ani mai girma yana tashi a gurin ko nesa kaɗan da inda take zaune. BILHAƘƘI "Shirya muje ki raka ni gidan Malam ɗin." "Yeeee... thank you Sweetat. I love you" Tsananin murna yasa ta kama ƙuncinshi ta sumbace shi bayan zaƙaƙan kalaman soyayya da take ta furta mishi akai-akai. Nan da nan ta miƙe a zabure kamar yayi mata allurar ƙarfi saɓanin da da jikinta yake a sanyaye tun da yace zai fita zuwa gidan Malam ya amso wayarsa. Kallonta kawai yake yi yana murmushi, kamar ba yanzunnan ta gama yi mishi ƙorafin bai dawo gida da wuri ba amma yana shirin sake fita. Tun da ya ce zasu je tare bakinta ɓakwui. Da yake a shirye take da kwalliyarta cas tun wanda tayi daf da ya shiga gidan na tarbar maigida, ko da tayi sallah shafa hoda ta sake yi ta zizara kwalli da man baki a lallaɓɓanta shi yasa har bayan sallar isha'i tsaf take. Gogaggen hijabinta ta ɗauka ta saka ta fita zuwa gurin mota shi kuma ya shige ɓangaren Rabi dan yi mata sallama. "Ko kema zaki je ne?" "A'a kuje kawai! Allah ya tsare. A gaida su Ummee." "Ameen. Ok za su ji Insha Allah." Ya amsa tare da sa kai ya fice daga falon. Hankalinta yana kan Tv a tashar arewa24. Shirin Tarkon ƙauna suke nunawa, tana bala'in son shirin ko da wasa ba ta so wani guri ya wuce bata kalla ba. Ko a jikinta har ta ji ficewar motarsa daga gidan. A mota sai hira take ƙoƙarin jan shi da shi amma ya ƙi sakin jiki, amsar shi baya wuce eh ko a'a. Haka kawai yake jin jikinshi kamar babu daɗi, tun da suka fito daga gidan yake jin zuciyarsa cike da tunanin Bilhaƙƙi. Duk ya ƙosa ya isa gidan yayi tozali da kyakkyawar fuskarta. Surayya da taga bai son hirar sai ta ja bakinta ta tsuke, a maimakon zaman shirun sai ya ƙara volume ɗin labaran duniyar da ya kunna a radion motar. A haka har suka isa gidan Malam. Ko da suka shiga gidan hankalin iyalan gidan a tashe yake, gaba ɗaya iyalan gidan har da Malam suna tattare a ɗakin Ummee. Bilhaƙƙi ce ba ta da lafiya. Tun dawowarta gidan idan akwai wani babban matsala da take fuskanta bai wuce ciwon cikin da take yi duk wata idan al'adarta zai zo ba. Ciwo ne na kwana ɗaya, amma kafin ya zo ya tafi sai ya wujijjiga ta ya fitar da ita daga hayyacinta. A zamanin zamanta a gidan Madam tun da ta mallaki hankalinta ta fara al'ada da wani mugun ciwon ciki da mara Oga ya bada wani magani aka ba ta tasha, tun wancan lokacin bata ƙara fuskantar matsalar ciwon cikin ba sai dawowarta gidan Malam. Duk wata idan zai zo tana tsananin shan azaba, kullum kamar ma ciwon ƙara gaba yake yi. Duk wata tsananin ciwon yana wuce na watannin baya. Yau tun bayan sallar magrib take kwance tana kuka da gurmususu haɗe da juye-juye kamar mai naƙuda, har zuwa bayan sallar isha'i ciwon bai faɗa mata ba. Dr. Bilyaminu da ya kasance shi ne likitan iyalin Malam tun su Maheer suna yara ƙanana wannan karon ma dai shi yake tsaye a kanta, magungunan sauƙaƙa zugi ya bata kamar yadda ya saba sannan ya ja Malam zuwa falon shi. "Malam kamar yadda na sanar da kai fa irin wannan matsalar ba mu da wani tsayayyen maganin da zamu bata ya yaye mata ciwon gaba ɗaya. Sai dai mu bata magungunan da zasu sauƙaƙa mata ciwon har zuwa lokacin da zai tafi gaba ɗaya. Amma dai kamar yadda na sanar da kai a baya yau ma zan sake maimaita maka, irin wannan matsanancin ciwon marar na al'ada da wasu mata suke fama da shi mafiyawancinsu da sunyi aure suke dainawa. Ina ga in dai ba akwai wata matsala bane kayi ƙoƙarin aurar da ita, da yaddar Allah ciwon nata zai zama na ƙarshe ke nan. Idan kuma bayan auren ciwon bai tafi ba sai mu zurfafa bincike mu ga menene ya ci gaba da haifar da matsalar." Ajiyar zuciya mai nauyi Malam ya sauke, ya sharce wani zazzafan gumi a goshinshi. Fuskarshi baiyane da matsanancin damuwa ya ƙara kallon likitan a karo na barkatai "Na gode Likita. In Allah ya yarda zanyi ƙoƙarin aiwatar da shawarwarin da ka bani. Ciwon ya isa haka nan, yarinyar tana tsananin bani tausayi. Allah yasa dai auren ya zama sanadin kawo ƙarshen ciwon." "Ameen ya Allah." Da wannan maganar suka cimma matsaya guda, ya sallami likitan yayi mishi tattaki har zuwa ƙofar gida, ya juya cikin gidan falon Ummee. A daidai lokacin Surayya da Maheer suka sa kai cikin gidan bakunansu ɗauke da sallama. Kai tsaye ɗakin Ummee suka nufa inda suka hangi ƙafafun takalma masu yawa a ƙofar ɗakin. "Malam lafiya kuwa?" Yayi tambayar yana tsaye daga bakin ƙofa, kallon fuskokinsu yake yi yana karantar damuwar da suke ciki. Nan da nan hankalinsa ya fara tashi, fuskarsa cike da taraddadi da tsoron irin amsar da zai fito daga bakunansu. Kafin wani a cikinsu ya bashi amsa Surayya ta zube a ƙasa cike da ladabi da biyayya ta fara gaishe su, duk sai suka maida hankali kanta suna amsa mata gaisuwar cike da kulawa. "Yaya, Bilhaƙƙi ce babu lafiya. Ciwon cikinta ne ya tashi." Saudat da take zaune a kujera mafi kusa da shi ta amsa mishi da muryarta ƙasa-ƙasa. Kallonta yayi kawai, da fuskar rashin fahimtar abinda take nufi. Bai taɓa katarin zuwa gidan a lokacin da take cikin tsananin ciwon ba sai yau, sai dai wani lokacin idan yaje gidan ya ganta tayi fayau jikinta a sanyaye, idan ya tambaye ta mai yake damunta sai tace kwana tayi bata da lafiya. Ko kuma ta ce yini tayi ba ta da lafiya. Shi kuma bai taɓa bin diddigin ciwon me take yi ba sai dai yayi mata fatan samun sauƙi kawai. "Magaji ƙanwarka Bilhaƙƙi ce bata da lafiya. Idan kun gaisa da iyayenka ka same ni a falo na, akwai maganar da za muyi." Malam yana gama faɗin haka ya fice daga falon Ummee. "Surayya zauna da kyau mana, kin takure ai sai ƙafafunki suyi tsami." Hankalinshi a tashe ya gaida su Mummy yana tambayar me yake damunta haka? "Ciwon ciki ne" Ummee ta amsa a taƙaice, muryarta a sanyaye, fuskarta baiyane da damuwa. Hankalinshi ne ya ƙara ɗugunzuma, wani irin mugun ciwo ne haka da ya ɗaga hankalinsu Ummee? "Kuma ba a kira likita ba? bari in ga yanayin jikin nata." Da sassarfa ya nufi hanyar da zata sada shi da cikin ɗakin sai Mummy tayi saurin dakatar da shi. "Magaji?" Cak yaja ya tsaya haɗe da juyawa yana kallonta. "Je ka amsa kiran Malam ka dawo sai ka shiga gurinta." Bai musa ma umarninta ba ya fasa niyyarshi na shiga cikin ɗakin, ya juya ya fice ya nufi ɓangaren Malam. "Saudah ku je ke da Auntynki ku ɗaga ta a hankali ki mayar mata da hijabin jikinta. Kuyi a hankali fa kar ku tashe ta tunda ta samu bacci. Ko kuma kawai ki ja bargo ki rufe ta, hakanma yayi." Tunda suka shiga cikin ɗakin Surayya sai wani yatsuna fuska take yi tana hura hanci kamar ta shaƙi warin kashi. Ta kalli irin kwanciyar da Bilhaƙƙi tayi a kan gadon, filo biyu aka jera mata ta kifa cikinta akai. Gashin kanta a warwatse, har lokacin bata ƙarasa tsifar da ta fara tun da rana ba. Bacci take yi, amma da ganin yanayin kwanciyar sam ba daɗin baccin take ji ba. Na dole take yi da taimakon magungunan da ta sha da kuma alluran da likita yayi mata, sai daɗa curewa take yi tana ƙara tattakure cikinta da ƙafafunta guri ɗaya, da alamun ako wane lokaci za ta iya farkawa. Ta sake taɓe baki a karo na barkatai, tana tsaye naɗe da hannuwa a ƙirji tana kalle-kalle da harare-harare har Saudat ta ja tafkeken bargon da yake ajiye a gefen gadon ta rufa ma Bilhaƙƙi tun daga ƙafa har saman ƙirjinta. "Wani irin ciwon ciki ne haka?" Kamar baza ta amsa mata ba, dan tun shigarsu cikin ɗakin tana lura da take-takenta. Amma da ta tuna girman matsayinta sai ta amsa mata a taƙaice "Mensturation problem ne." Duk su biyun babu wacce ta sake tankawa har ta tattare gashin kan Bilhaƙƙi guri ɗaya ta ɗora mata ɗankwali a kan, suka fice daga ɗakin zuwa falo. Zaman ƙudan da ake yi a falon saboda jimamin da suke ciki yasa ta ji duk ta takura, ga sanyi-sanyi da ake yi. Da wannan dalilin yasa ta ƙosa Maheer ya dawo daga gurin Malam su koma gida, ita da ta sani ma da bata biyo shi ba. Dan abinda ta so ganin idanunta ya hana faruwarshi sam ba shi ya faru ba. Ta ja tsaki a cikin ranta ta turo baki gaba, da sauri ta sauke kanta ƙasa tana mutsu-mutsu ganin sun haɗa ido da Ummee. Maheer bai shiga ciki ba sai ƙarfe goma saura minti uku. "Mummy mu za mu wuce gida..." "Ka shiga ciki ka ga jikin nata mana?" Ta katse shi tare da nuna mishi hanyar cikin ɗakin da yatsarta manuniya. Sosa ƙeya yayi cikin kunya, ya ɗan saci kallon Surayya da ta naɗe ƙafafunta da hannayenta. "Da yake Malam ya ce min ta samu bacci ne, shi yasa zan bari sai gobe da safe idan Allah ya kaimu. Allah ya bata lafiya." "Ameen ya Allah." Suka amsa gaba ɗaya. "To ku gaida gida. Ke tashi ku tafi daman na ga kamar duk kin takura da zaman." Wani matsanancin kunya ne ya rufe ta, ta sake ƙasa da kai cikin kunya "A'a ba haka bane Ummee. Sanyi ne ya takura ni." Babu wacce ta ƙara tanka mata har Maheer ya sake musu sallama a karo na biyu suka fice daga gidan. "Sweetat ka manta baka amshi wayar ta ka ba..." "Wani waya zan amsa kuma bayan wacce wayar ke hannunta ba ta da lafiya?" Ya katse ta cikin zafin rai. Bakinta taja ta tsuke, daman tunda ya fito daga gurin Malam taga kamar ba ya cikin yanayi. Taɓe baki tayi ta kauda kanta gefe tana kallon titi, a zuciyarta ta ce 'Ba ni na kar zomon ba.' Shi kuwa sai nannauyar numfashi da ajiyar zuciya yake saukewa akai-akai. Bisa ga dukkan alamu akwai abinda yake dannewa a can ƙasan zuciyarsa. A haka har suka isa gida, da yake duk sunyi sallar isha'i da shafa'i da wutiri kafin su fita wanka suka sake yi, Surayya ta sako kayan bacci mai ɗaukar hankali ta nufi turakar maigida. Tun da duk mai girki a can take kwana, ko da ta isa shi ma har yayi shirin bacci ya kwanta. ****** ****** 'Magajin Malam ina neman alfarmarka, domin ba tilastaka zanyi ba. Wannan alfarmar kuwa ba ta komai ba ce sai idan ka amince gobe da asubah idan Allah ya kaimu zan ɗaura aurenka da wannan yarinyar Bilhaƙƙi.' Ƙirjinshi ne ya buga dam a karo na biyu bayan tuno roƙon alfarmar da Malam yayi mishi ɗazu da suka je gidan, abu ne da bai taɓa tsammani ba. Zuciyarsa ne ta tsaya cak, ya sauke kanshi ƙasa kawai cikin rashin abin cewa. Daƙyar ya lalubo kalmomin "Me yake faruwa Malam? auren da gaggawa haka?" Malam bai ɓata lokaci ba ya koro mishi bayanin duk abinda likita ya faɗa game da ciwonta da hanyar da za a bi dan a samu maslaha, ya ƙara da cewa "Ni kuma a iya tunanina banga wanda zuciyata ta aminta in bashi aurenta sama da kai ba. Ko ba wannan ba ma yarinyar ta daɗe tana ƙaunarka. Amma idan baka so bazan tilasta ka ba, domin ba burina bane in aurar da ita inda za ta wulaƙanta. Sai in yiwa ɗan'uwanka Mustapha magana dan ya daɗe yana nuna min sha'awar aurenta ni kuma ina kaucewa zancen tunda na san ita kai take so." Bai san me zaice ba, tsakani da Allah ko da bai sonta zai iya aurenta kuma ya zauna da ita lafiya ko dan darajar Malam. Balle kuma ba shi da takamaimai sani na abinda yake ji game da ita, abinda ya sani dai kawai kuma ya tantance sam yanzu babu ko ɗigo na ƙiyayyarta a zuciyarshi. Yana jin wani ƙauna na musamman a zuciyarsa game da ita, jinta yake kamar wata ƙanwarsa ta jini da suka yi tsananin shaƙuwa. Bai bar cikin falon Malam ba sai da ya amince zai karɓi aurenta da hannu bibiyu, ya fita cikin layin gurin wani mai shago ya siyo katan-katan na ledojin sweet da cakulet wanda za a rarraba ma jama'a gurin ɗaura aure. Ya yi alƙawarin gobe da asubah zai taho da sadakin naira dubu talatin kamar yadda Malam ya yanke mishi in Allah ya yarda kafin a ɗaura auren. Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke bayan ya gama tunanin duk abinda ya faru, ya waiga ya kalli Surayya da take barci a jikinsa hankalinta a kwance. Ya kalli agogon da yake ajiye a jikin gadon, ƙarfe uku da minti biyu na talatainin dare. A hankali ya zare jikinshi daga nata ya rufa mata bargo, ya shige cikin banɗakinsa ya ɗauro alwala, ya zura jallabiya ya tada sallah ya fara jero nafilfili dan neman tabbatuwar abinda yafi zama mafificin alkhairi tsakaninshi da Bilhaƙƙi. Bai tashi daga kan dadduma ba har zuwa ƙarfe huɗu da kwata, yana ta addu'o'i da neman zaɓin Allah. A daidai lokacin ne kuma wani barci mai nauyi yayi nasarar yin awon gaba da shi, bai farka ba sai ƙarfe biyar dai-dai inda kiran sallar farko da Ladan Malam Isiya ya kwaɗa ya dira bisa kunnuwanshi. Miƙa yayi gami da salati, ya yunƙura da bismillah ya miƙe tsaye, zuciyarsa wasai duk wani nauyi yanzu babu. Sai ma wani sihirtaccen farin-ciki da nishaɗi da yake ji yana ratsa gangar jiki da duk wani lungu da saƙo na sassan zuciyarsa. Da wannan dalilin yasa cike da karsashi ya faɗa banɗaki ya tsallo wanka bayan ya wadata ruwan da turarukan wanka kala-kala. A gurguje yake komai, duk da yana da tabbacin idan ya fita yanzu zai iya samun sallar asubah a masallacin Malam. Tunda lokaci ya canza shida saura minti goma ake yin sallar asubahi. Farar shadda ghalila sabuwa kar a ire-iren waɗanda ya ɗinka bai taɓa sakawa ba ya ɗauko ya sa, yana shiryawa shi kaɗai yake sakarwa kansa murmushi kamar anyi mishi bushara da aljannah. A wannan lokacin Surayya ta farka saboda yawan zurga-zurgar da yake yi a cikin ɗakin, idanunta da suke cike da bacci ta ware a hankali take kallonshi. Ta buɗe baki za ta yi magana wani ƙaƙƙarfar hamma ya suɓuce mata dole ta rufe bakin da hannun dama. "Sweetat...? Lafiya kuwa?" "Me kika gani? Wankan ne ya baki mamaki ko mene?" Ya tambaye ta yana fesa turare a lungu da saƙo na jikinsa. "A'a! Wanka ai kana yi duk asubah. Shigar galleliyar shadda saɓanin ɗaya daga cikin jallabiyoyinka ta zuwa sallar asubah shi ne abinda ya bani mamaki. Ina tunanin akwai dalilin canjin ko?" "Eh ƙwarai kuwa." Ya amsa yana dariya. Ya ajiye turaren a gaban madubi ya ɗauki hularsa ya fara karyawa. "A masallacin Malam zanyi sallar asubah. Idan na fita yanzu bazan dawo gida da wuri ba sai bayan sallar azahar shi yasa kawai na shirya gaba ɗaya." Ya kafa hular a kansa ta zauna cas, ya kalli madubi ya ƙara gyarata sosai. Fuskarsa sai sheƙi take yi kamar wata a daren goma sha huɗu, ya kalle ta ya haske ta da tattausan murmushi. "Ki tashi kiyi sallah. Ki kwantar da hankalinki. Idan na dawo akwai muhimmiyar maganar da zanyi da ku ke da Rabi." Makullin motarsa ya ɗauka ya nufi hanyar fita daga ɗakin, ita kuwa ta bi shi da kallo baki da hanci buɗe cike da rashin abin cewa. Sai da ya isa bakin ƙofar fita daga ɗakin zuwa falo ya waigo ya kalle ta yana murmushi. "Sweety yau babu ko addu'ar Allah ya tsare?" "A dawo lafiya." Ta faɗa da ƙyar kamar wacce aka tura wa dutse a baki. "Allah yasa haka." Ya amsa tare da rufe ƙofar ɗakin. Tana nan zaune tana saƙe-saƙe ta ji tashin motarsa yana ɗumamata, can kuma ta ji mai gadi ya buɗe mishi get ya ja motar a guje ya fice daga gidaan. Fitarsa yayi dai-dai da wani mugun faɗuwar gaba da tayi, ta runtse ido da sauri kamar aradu ne ya faɗo a ƙirjinta saboda nauyi. Tana ji aka ta da sallar asubahi a masallacin kusa da su, daƙyar ta yunƙura ta miƙe gaɓɓan jikinta sai ciwo suke yi mata kamar wacce aka naɗawa shegen duka. ****** ****** "Gaskiya Gangaran ka tabbata. Wai dan Allah dama da gaske kake yi? Ka san Allah? Wallahi da naga saƙonnan na zaci mafarkinka ne kayi sharing da ni." Ya ƙarasa maganar yana tuntsura dariya. Shi ma dariyar ya kwashe da shi yana sha fa kwantaccen gashin kanshi. "Zauna nan dai Alaji garin kallon ruwa kwaɗo yayi maka ƙafa. Ba dai kai ka maƙale a ɗaya ba? Da gaske ta uku nake faɗa maka Alaji. Ina fatan dai ka fito? ka san da an idar da sallah za a ɗaura auren, ni yanzu haka ma ina ƙofar gidan Malam, Yusuf ma ya ce min ya kusa ƙarasowa." "Abu namu maganin a kwaɓe mu, ai dole ma in himmatu. Ka san na fi Yusuf kusa da su Malam yanzu zan ƙaraso..." "Yauwa! Mukhtar kar ka faɗawa Maman Imam fa. Da yake batun auren ya taso jiya da daddare ne ko su Surayya ban sanarma ba. Kuma na fi so kafin su ji a bakin kowa su fara ji daga bakina." "Ok.. ba damuwa, hakan ma dabbara ce. Sai na iso." Da haka suka ajiye wayoyin a duk ɓangarori biyun, sauri sauri ya gangara kusa da gidan Malam ya gyara fakin ɗin motar ya fita, masallacin ya nufa kai tsaye da sassarfa dan jin har Ladan ya fara tada iƙama. Alƙawari ya cika. Da kyakkyawar niyya da zuciya mai nufin ƙulla alkhairi bayan idar da sallar asubahi Malam ya bada auren Bilhaƙƙi Aliyu(Rashin sanin takamaimai sunan mahaifinta yasa Malam yi mata inkiya da Aliyu, dan gudun ƙananun maganganu. A zuciyarsa yayi tunanin idan yayi mata amfani da sunanshi a matsayin uba zai ɗiga wa mutane ayar tambaya a zukatansu. Da kyakkyawan niyya yake faɗa ma mutane ƴar ƙaninsa ne, ba dan komai yayi hakan ba sai don ya siya mata mutunci kuma ya kore duk wani zargi ko ƙananun maganganun da zai iya zuwa ya dawo daga gurin mutane.) Ladan Malam Musa mahaifin Surayya shi ya zama waliyyin Maheer Abdulganiyyu wajen karɓa mishi auren akan sadaki naira dubu talatin cif! Lakadan ba ajalan ba. Mutane da ba a iya musu sai mamaki suke yi ganin auren bagatatan babu wani shiri, kuma ɗaura aure da asubah kamar na marassa gaskiya? Babu dai wanda ya kawo kushe sai fatan alkhairi da fatan Allah bada zaman lafiya da ake ta yi ga Maheer. Shi kuwa Ango yana cikin manyan abokansa biyu Yusuf da Mukhtar bakinshi har kunne, fararen haƙoranshi talatin da biyu a waje kamar gonar auduga dan tsabar farin cikin da yake ciki a fili da baɗinin zuciyarsa. Nan da nan aka fara rarraba ɗaurin goro, dabino, sweet da cakulet a manyan ledoji ga duk mutanen da suka shaida ɗaurin auren. Zuwa ƙarfe bakwai da kwata na safe anyi komai an gama mai afkuwa ta afku, Bilhaƙƙi ta zama ta Maheer halak malak. Su Mukhtar suka yi mishi sallama da cewar sai sun gayyato sauran abokansu anjima su zo ganin amarya, dan a lokacin sama da ƙasa sun buga amma ya hana su shiga cikin gidan Malam ɗin balle har su ganar mishi Amarya. Daga nan falon waje na Malam suka yi sallama ya shiga cikin gidan su kuma suka wuce a motocinsu suna tsokanarshi. BILHAƘƘI Daddaɗan ƙamshin turaren jikinsa ne ya fara alamta mata zuwansa, kafin daga bisani ta ji tattausar muryarsa yana doka sallama a ƙofar ɗakin. Dangwarar da kofin tea ɗin da take sha tayi a ƙasa, da sauri ta lulluɓa ta sake tattakurewa a cikin bargo ta ƙudundune guri ɗaya a kan gadon. Wani matsanancin kunyarsa ne yake ratsa ta tun daga babbar ɗan yatsar ƙafarta har zuwa maɗigar kanta. Ƙirjinta sai luguden daka yake yi, da gaske tsoron ganinshi take yi, domin bata san da wani ido ya karɓi aurenta ba. Tunanin yadda auren mai kama da a mafarki yazo mata ta fara yi. 'Da yake jiya ciwo yasa ta yi baccin wahala tare da taimakon allurai shi yasa ƙarfe huɗu da wasu ƴan daƙiƙu na asubah ta farka, a lokacin ciwon ya faɗa mata sosai ba kamar jiya ba. Ummee ta gani zaune akan dadduma tana lazumi, motsin da tai tayi akai-akai yasa Ummin ta maida hankalinta kanta. "Kin tashi? ya jikin naki?" Ta tambaye ta cike da kulawa. "Da sauƙi sosai Ummee." Ta amsa a kasalance. "Allah ya ƙara afuwa. Sa hijabinki bari in kira Malam ya ce akwai maganar da zaiyi da ke." Bata jira amsawarta ba ta fice daga ɗakin. Can bayan wasu daƙiƙu sai suka shigo ita da Malam, bayan tambayarta yanayin jikinta da yadda take ji ne ya faɗa mata shawarar da ya yanke na ɗaura musu aure ita da Maheer, ya bata damar idan bata amince ba kar ta ji kunya ko kuma ta tauye kanta ta faɗa zallar gaskiyar zuciyarta. Shi bazaiyi abinda ba ta so ba. Kunyar Malam ɗin da tsananin ƙaunar waɗannan iyalan ne ya ƙara lulluɓeta, sai ta ja hijabinta ta rufe fuska. Su da ɗansu yake ɗan asali basu ƙi ta ba sai ita da ba a san cikakken asalinta bane za ta ƙi ɗansu? kai tsaye ta ce ta amince...' "Ka shiga ciki mana Magaji. Kila bacci ne ya sake ɗaukarta." Muryar Mummy da taji tana faɗin haka yasa tayi saurin katse tunanin da take yi, da mugun sauri ta sake curewa guri ɗaya. Yana shiga sai yaga tana ta mutsu-mutsu a cikin bargo. Nan da nan kuwa ya harbo jirginta. Ya saki wannan tattausan murmushi ya tsaya ƙyam! a guri ɗaya, ya ci gaba da kallonta yana karantar yanayinta. Ita kuma jin shiru yasa ta buɗe rufar kaɗan, a hankali ta leƙo da kanta waje. Karaf suka haɗa ido, cike da matsananciyar kunya da sauri ta sake ɓoye kanta tana murmushi. "Yarinya na ganki fa." Ko kafin ta ce komai ya haye kan gadon gaba-ɗaya ya ɗagata ita da abin rufar ya haɗa ya rungume a ƙirjinsa. Tsawon wasu daƙiƙu yana sauke ajiyar zuciya, daga can ƙasan ransa farin cikinsa yana ƙara ninkuwa. Ita ma luf tayi idanunta a rufe take sauke sassanyar ajiyar zuciya, mai alamta kwanciyar hankali da farincikin zuciya ta samu abinda ta daɗe tana muradi. A hankali kuma cike da wani irin nutsuwa mai tafe da daddaɗan shauƙi yake warware bargon daga jikinta, har ya buɗe ta gaba ɗaya ya tattare bargon ya ajiye a gefe. A nutse ya fara ƙare mata kallo tun daga kan kyakkyawar fuskarta zuwa ƙasa, sanye take da kayan bacci masu ɗan kauri riga da wando. Har lokacin idanuwanta suna lumshe, ƙirjinta sai luguden daka yake yi. Tana jin kaifafan idanuwansa masu kama da maganaɗisu a gare ta suna kara-kaina da zagayawa a duk wani sassan jikinta. Can ƙasan mararta ne ya sake tsirga mata da wani matsanancin ciwo, da sauri ta ware idanunta gaba ɗaya ta buɗe su tare da yamutsa fuska. "Menene... uhmmm...?" Ko kafin ya rufe baki ta kai mishi wani mugun riƙo tana tattakure jikinta a cikin nashi, tana ƙara riƙe shi sosai. Cike da raki da jin raɗaɗi ta ce "Asssshhhhh... Gangaran, Marata..." Sai kuma hawaye shar-shar kamar an buɗe famfo. Sai juye-juye take yi tana ƙara ruƙunƙume shi cike da azaban ciwo. Hankalinshi ne ya ɗugunzuma, zuciyarsa cike da matsanancin tausayinta. Da alamun ya manta ma a inda suke, ɗago ta yayi daga jikinsa ya ɗage rigarta ta ƙasa yasa hannu a ƙasan cibiyarta, da tunanin ko nan ɗin ne yake mata ciwo "Sannu, Nan ne yake ciwon?" Yayi maganar kamar yana mata raɗa. "A'a ƙasa fa" Ta amsa cike da shagwaɓa, wasu sabbin hawayen suna sake ɓalle mata. A hankali ya ƙara ƙasa kaɗan da hannunsa yana shafa mata mara sai kuma ya cire hannunsa da sauri kamar wanda shocking ya ja. Duk da sanyin da ake yi a garin shi zufa yake yi, ya ja ta jikinsa ya rungume tsam-tsam a ƙirjinsa yana bubbuga mata baya alamun rarrashi. "Baya na... cinyoyina ciwo... dan Allah ka danna min..." Ta faɗa cikin matsanancin kuka da magagin ciwo. Abin dariya abin tausayi, Bilhaƙƙi ke ciwon Maheer ke zufa da jin raɗaɗin a jikinsa, gaba ɗaya ma kamar a ruɗe yake, ya ruɗe ya susuce kamar wanda bai taɓa aure ba, shi bai taɓa ganin irin wannan ciwon a gurin matansa ba. Shi kuwa ciwon mara kamar ana ƙara tunkuɗoshi sai gurmususu take mishi a jiki tana kuka, gaba ɗaya ta gama yamutsa gallalliyar shaddar da take jikinshi. Jin yadda take ta ƙara maimaita bayanta da cinyoyinta ciwo suke yi yasa shi miƙar da ƙafafunsa akan gadon ya kwantar da ita rub da ciki akan cinyoyinsa kamar wata ƴar bebi, ya yaye rigarta sama sosai ya fara danna mata bayan a hankali da hannayensa biyu haɗe da ɗan bubbugawa kamar yana lallaɓa jaririya tayi bacci. Cikin sa'a kuwa lokaci kaɗan sai ta fara sauke ajiyar zuciya, da alamun sosai take jin daɗin abinda yake mata. Ya leƙa fuskarta yaga har lokacin idanunta a rufe suke, sai dabbara-dabbarar hawaye a kumatunta. "Ciwon ya daina?" "Ya yi sauƙi dai." Ta faɗa a shagwaɓe kamar za ta sake fashewa da kuka. Ajiyar zuciya ya sauke, ya kalli bayanta da yake buɗe, sai a lokacin idanunshi suka kai kan maɓallin bra ɗinta mai ruwan madara. Yayi kamar zai kai hannu ya ɓalle sai ya kwaɓi kanshi, ya maida idanunshi kan gadon bayanta. Fatan jikinta irin mai kyau ɗinnan ne ga sheƙi, ita ba baƙa ba ita ba fara ba. Karaf idanunshi suka gangara har zuwa kan mazaunanta da tudunsu ya ɗago a wandon baccinta. Saurin watsar da wannan tunanin yayi a lokacin da yaji tana ƙoƙarin tashi daga jikinsa, a kunyace ta saukar da idanunta ƙasa ba ta yarda sun haɗa ido da shi ba, ta janye jikinta ta matsa daga kusa da shi. Hannunta ta ɗaga za ta saukar da rigarta ta baya da sauri yasa hannunshi ya saukar mata da rigar. "Na gode" Ta faɗa da muryarta ƙasa-ƙasa. "Keeee godiyar miye? aikina ne fa." Yayi maganar fuskarsa fal da murmushi, ƙoƙarin haɗa ido yake yi da ita ta ƙi ba shi damar hakan, sai ya matsa kusa da ita, ita ma ta matsa baya. A haka ya matso ta matsa har suka ƙure ƙarshen gadon. Sai kawai ta takure kanta a cikin cinyoyinta tana murmushi. Shi baisan duk kunya yake bata ba. Kanshi ya cusa kusa da nata cikin raɗa ya fara magana. "Da gaskiya amaryar Gangaran kinyi farin ciki kuwa? Wani tukwuici za ki bani yau da zai tabbatar min kina taya ni farin-cikin da zuciyata take ciki?" "Kai Maheer... wani tukwuici kuma...?" Tayi maganar cikin sakalci da wani irin wawuyar shagwaɓar da tayi mugun tafiya da ɗan sauran nutsuwarsa. Kamar zai sake janyota zuwa jikinshi dan samun sauƙi-sauƙi sai kuma ya maze. Ya fara hurga idanunshi lungu da saƙo na cikin ɗakin yana ƙare mishi kallo, sai kuma yayi murmushi. A zuciyarsa ya ce 'Gaskiya cikin iyayenshi mata biyu duk wacce tayi tunanin mayar da Bilhaƙƙi ɗakin ƴanmatan gidan a safiyar nan da ta tabbata halaliyarshi ba ƙaramin taimaka mishi tayi ba. Shi kam da ya zai iya fita da wannan yamutsattsen kayan na jikinshi? Amma yanzu zai fita salin-salin ba tare da an ganshi ba tunda ɗakin yana can ta ƙarshen gidan ne, kuma akwai siririyar hanya ta baya da zai iya bi wacce in ba rashin sa'a yayi ba zai wahala iyayen su ga fitarshi.' "Yanzu haka za ki ta fama da wannan ciwon har sai baƙon ya tafi? kwana nawa ne yake yi?" Ya tambayeta da fuskarsa mai baiyana zallar tausayinta, alamun ya tuno irin azabar da ta gama sha ɗazun. Wayyo Allah... ina ma ƙasa ta tsage ta shige don kunya, can gefe ta maida kanta da jikinta tana ƙara ɓoye kanta tsakanin cinyoyinta. 'Ita yana bata kunya wallahi, bata taɓa tsammanin akwai lokacin da zai zo da za ta dinga jin kunyarshi har haka ba. Ita yayi ya tafi ma kar Ummee ko Mummy wata a cikinsu ta shigo a gansu a yanayin da suke ciki.' Da ya fahimci manufarta sai yayi dariya kawai, ya kwanta a kan gadon. "Kinga yarinya gara ma ki faɗa min, idan ba haka nan yini nan kwana saboda idan ciwon ya motsa in dinga miki matsa miki baya da cinyoyi..." "Wayyo Maheer ciwon na jiya da yau ne fa kawai. Ka ga ni na ma ji sauƙi, ka tafi in samu inyi wanka inje gurin Ummee." Ta ƙarasa maganar idanunta a nannarke take kallonshi, kamar za ta saka kuka. Da zallar gaskiyarsa ya ce "Kinga muje kawai in taya ki wankan tunda baki gama jin ƙarfin jikinki ba..." "Ni dai a'a!" Ta katse shi da sauri tana wawware ido a tsorace. "Ka bari zan iya yi da kaina. ka ga ni na warke ma gaba ɗaya dan Allah ka tafi." Ya ɓata fuska kamar ya shaƙa "Kora ta kike yi ko?" Tayi narai-narai da ido ta matsa kusa da shi sosai "Yi haƙuri ba fa haka bane Allah..." "To yaya ne?" Ya tambaye ta murya a tsaitsaye yana sake tamke giran sama da ƙasa. Tsoro ne ya fara kamata, lokaci ɗaya yana neman koma mata wancan murɗaɗɗen Maheer ɗin da ta sani a farko wanda sam baya ƙaunarta. Idanunta a ƙasa take mummurɗa yatsun hannayenta "Kawai... kawai... ina jin tsoron kar su Mummy su shigo. Ka yi haƙuri dan Allah..." Wawan rungumar da ya kai mata ba tare da ta ankara ba yasa ta kasa aje numfashin maganarta dai-dai "I'm sorry Babe. Da wasa nake miki tsawa." Ya raɗa mata a kunnenta yana dariya ƙasa-ƙasa. Ajiyar zuciya ta sauke a hankali ta runtse ido, ƙara ƙanƙame shi tayi tana jin wani irin baƙon yanayi yana ratsa ƙashi da ɓargon jikinta. "Je kiyi wankan anjima zan dawo kinji?" Ɗaga kai kawai tayi alamar ta ji, bakinta nauyi yayi mata ta kasa amsawa. Raɗan da yake yi mata a kunne a jikinta ji take yi kamar yana mata tafiyar tsutsa. "Me zan taho miki da shi?" Ya sake raɗa mata da wani rikitacciyar murya, domin ba ita kaɗai take karɓar saƙon ba shi ma yana ji a jikinsa. Ƙanƙameshi ta sake yi kamar za ta tsaga ƙirjinsa ta shige, ko kuma tana tsoron kar a raba jikinta da nashi. Da ƙyar ta yi ƙumajin buɗe tsukakken bakinta da yayi mata nauyi ta ce "Bana buƙatar komai" "Ba komai fa kika ce Babe ki tuna dai." Yayi maganar yana dariya ƙasa-ƙasa. Nauyayan idanunta da suka ƙara ƙasa-ƙasa ta sauke su a kanshi, ta tura baki gaba "Ni dai ba komai..." "Har Pad bakya buƙata?" Ƙwace jikinta tayi da sauri ta dira daga kan gadon ta faɗa banɗaki ta danno ƙofar cike da matsananciyar kunyarsa. Dariya yayi mai isarsa kafin ya ɗan gyaggyara rigarsa ya ɗauki hula, makullin motarsa, ƙaramar wayarsa ya fice daga ɗakin. Ta baya ya bi, yana tafe saɗaf-saɗaf yana waige-waige kamar mare gaskiya har ya fice daga gidan ba tare da ya haɗu da ɗaya daga cikin iyayen na shi ba. ***** ****** "Da girman kujerarki Sarauniya. Amarya a gurin mai martaba Sarki Abdulfatah na biyu. Ranki ya daɗe Innata ta kaina. Allah ya ja zamaninki ki daɗe kina yi ki ƙare da kyakkyawan cikawa." "Ameen ya Allah." Ta amsa daƙyar, muryarta baiyane da ƙasaita da matsanancin mulki. Ta sake gyara kishingiɗar da tayi a kan tuntum ɗin sarautar, ta gyara riƙon wayar a kunnenta tana jan fasali kamar baza ta ƙara tankawa ba. Har sai da daga can ɓangarenshi ya ce "Ina jinki Fulani." "Abdulganiyyu ya iyalanka?" "Duk lafiya ƙalau suke Fulani. Da fatan ku ma haka? Ya jikinki?" "Jiki mun gode Allah Abdulganiyyu. Gamu nan har yanzu muna turawa." "Ubangiji Allah ya raba ku lafiya Innata." Yayi mata addu'ar muryarsa na baiyana tsananin tausayinta. Daga can ɓangarenta hannu ta ɗaga ta shafi turtsetse cikin da ya turo sosai a cikin alkyabbar da yake jikinta, sannan ta amsa addu'ar a kasalance. Kafin ya ce wani abu ta ci gaba da magana jikinta a sanyaye, bisa ga dukkan alamu tana cikin tsananin damuwa amma fuska da muryarta na ƙoƙarin ɓoyewa. "Abdulganiyyu ka san mun shiga wata na goma sha huɗu, har yanzu kuma ba wani motsi. Mai martaba ya fitar da ranar da likitocinsa zasu yi min aiki, nan da sati biyu za a fitar da cikin in dai har zuwa lokacin haihuwar bata zo ba. Ina jin tsoro Abdulganiyyu, da gaske ina matuƙar jin tsoro. Ban sani ba ko wannan cikin shi ne zai zama silar ajali na... Idan zai yiwu ina son ganinka kafin lokacin." "Karki damu Ranki ya daɗe, babu komai da zai faru in Allah ya yarda sai alkhairi. Muna addu'a, kuma za mu ci gaba da bada ƙaimi, Ubangiji maji roƙon bawa ne. Na tabbata bai manta da halin da kike ciki ba, in Allah ya yarda addu'a ta karɓu sai dai jinkirin biyan buƙata. Ki kwantar da hankalinki kinji?" "Insha Allah. Na gode Abdulganiyyu. Allah ya maka albarka." "Ameen Inna. Na gode." Ya amsa cikin jin daɗi, kafin ta ƙara cewa komai ya ci gaba da cewa "Kamar yaushe kike buƙatar in zo?" "Kar ya gaza nan da sati ɗaya. Idan ka yi jinkiri da yawa kuma nan da kwanaki goma." "Tom In Allah ya yarda bazan wuce lokacin ba. Allah ya ƙara miki lafiya Ranki ya daɗe." "Ameen ya Allah. Ka taho min da Magajin Malam, shi ma ya kwana biyu bai zo ba sai a waya yake gaishe mu." "To za mu taho tare da shi. Sai mun iso." Da haka suka ajiye wayoyin a duk ɓangarorin guda biyu. Sa ke motsawa tayi cike da ƙasaita ta yunƙura daƙyar ta miƙe zaune daga kishingiɗar da tayi, nan take bayin da suke zagaye da ita wasu suna firfita wasu suna mammatsa mata ƙafafu suka fara jera mata sannu, haɗe da addu'ar Allah ya raba ta da cikin jikinta lafiya, Allah ya ja zamaninta. Ta kalli Amintacciya kuma Shugabar bayinta mai suna Lantana ta yi ɗan murmushi ta ce "Na gode Lantana, ku bani guri. Ina buƙatar in huta." "Hutawarki lafiya Fulani, baya goya marayu. Allah yaja zamaninki ki daɗe kina yi a zuciyar mai martaba. Allah ya raba ki da cikin Yarima lafiya." Tattausan murmushin da bai cika ɓacewa daga fuskarta ba ta sake sakar musu. A zuciyarta ta amsa kyawawan addu'o'insu. Ta yunƙura da ƙyar ta miƙe suna ta jera mata sannu, cike da nutsuwa take tafiya a hankali har ta shige can cikin turakarta. Ta daɗe a tsugunne kanta a ƙasa kamar an manta da ita. Tun tana jero kirari Babbar baiwar da take gefenta tana amsawa har ta rasa abin cewa, tayi shiru tana jiran umarnin magana daga Sarauniya Safara'u, inkiya Fulani Taka. Sai da ta mila ta mile ta gama jan fasali da tsananin mulki mai haɗe da jin kai cike da ƙasaita ta kalli gefen da take tsugunne, a wulaƙance ta ce. "Wane hali Safiyya take ciki?" "Har yanzu dai ba wani canji Ranki ya daɗe, tana nan jiya iyau. Ciki sai ƙara tsini yake yi babu wani motsi na naƙuda. Likitoci sun shawarci Mai martaba nan da sati biyu za a mata aiki a cire cikin, ya amince da hakan kuma ita ma ta amince. Ɗazu ta kira wani ɗan ƴar'uwarta da yake kaduna wai yazo tana son ganinshi kafin ayi mata aikin. Bisa ga dukkan alamu ita ma ta fitar da rai da rayuwar duniya." Wani murmushi ta sake tana cije gefen bakinta na dama cike da mugunta, ta jinjina kai ta ce. "Da kyau! Madallah! Haka muke son ji. Raliya a koma bakin aiki." "Godiya nake Ranki ya daɗe. Allah ya ƙara miki lafiya da nisan kwana. Ƴar sarki jikar Sarki Uwargidan Mai martaba Sarki Abdulfah na biyu, uwar Sarkinmu na gobe Yarima Muzaffar in Allah ya yarda." Da waɗannan kirarin a bakinta har ta fice daga falon cikin sauri tana waige-waige da basasarwa, haɗe da bagararwa dan kar a gane daga inda ta fito har ta isa ɓangaren Sarauniya Safiyya ta koma bakin aikinta kamar babu inda ta je. "Lami a isar wa da Ciroma saƙo ina son ganinshi." "Angama Ranki ya daɗe." Ta amsa da sauri ta duƙa kamar za ta yi mata sujada, sannan ta miƙe da sauri fice daga falon dan isar da saƙo ga Ciroma. ******* ****** Tunda yayi sallama a bakin ƙofar falon, ya ji duk su biyun babu wacce ta samu zarafin amsawa ya tabbatar liƙin da yake tunanin ya yi ya ɓalle. Ɗan murmushi kawai yayi ya girgiza kai yana mamaki a ransa, ganin wani abin dariya a tsakanin matan nashi. Haɗin kan da tun da babu a tsakaninsu ne yau suke neman farawa tunda sun samu labarin yayi aure. Duk su biyun suna zaune ne akan kujera mazaunin mutum biyu, sun zabga tagumi da hannu bibiyu fuskokinsu na baiyana yanayi na matsanancin jimami kamar waɗanda aka aika musu da saƙon mahaifansu na kwance a asibiti. Yana shiga cikin falon duk suka miƙe tsaye a zabure suna binshi da mugun kallo, kamar wanda yayi musu wani gaggarumin laifi. Surayya da take gwana a gurin abin kawai sai ta fara hawaye tana nuna shi da yatsarta manuniya, ta ma kasa magana dan tsananin ƙuncin da zuciyarta take ciki. Ita kuwa Rabi da take gwana a gurin tsiwa da fitsara ƙugunta ta riƙe da hannu bibiyu ta cokaɗo baki gaba, ta kalle shi da ƙananun idanunta da suka canza launi dan tsananin tashin hankali da masifar da yake cikinta. "E lallai, ba shakka! Na yarda goro na sa zawo. Amma kafin in ce komai bari in fara tambayarka dan ka share min tantama. Wai da gaske ne jita-jitar da muke ji yau an ɗaura aurenka da wannan ƙwailar yarinyar mai sunan aljanu da take zaune a gidan Malam?" BILHAƘƘI "Shegiyar yarinya kullum muka je gidan Aunty sama Aunty ƙasa ashe ƴar kunama ce neman gurin harbi take yi. Faɗa min da gaske ka aure ta ko kuwa duk maganganun da muka ji rumous ne? Don mun kira wayarka fiye da sau talatin baka ɗauka ba." Shirun da yayi bai amsa ta ba yana kallonta yana sakin murmushin da ta alaƙanta shi da na rainin wayau shi ne abinda ya ƙara ƙona mata zuciya. Ta ci gaba da binshi da kallo baki buɗe har ya shiga cikin falon sosai ya nemi ɗaya daga cikin kujerun ya zauna. Irin yadda yayi gurin zaunawar duk su biyun sun fahimci a matuƙar gajiye yake. Ga wani mugun yamutsewa da shaddar jikinsa tayi kamar an ƙwato a bakin kura. Ta sake runtse idanu zuciyarta na ƙara zafi cike da takaici, tunani take da saƙe-saƙe tunda a gidansu an ce mata bayan sallar asubah aka ɗaura auren kuma bai shigo gida ba sai yanzu sha biyu saura, alamun gajiyar da ta gani a jikinsa, yamutsewar kayansa, yalwataccen farin-cikin fuskarsa su suka haɗu suka tabbatar mata da aikin gama ya daɗe da gamawa tsakaninshi da Bilhaƙƙi. 'Ya rasa ranar da duk zayyi hakan sai a ranar girkinta?' Sabbin zafafan hawaye masu mugun raɗaɗi ne suka sake ɓalle mata kamar an buɗe ruɓaɓɓen injin markaɗe ta ɓare baki ta fashe da ƙaƙƙarfar kuka, da mugun gudu ta tashi ta shige ɓangarenta tana kuka tana danne baki ta bugo ƙofar da ƙarfi. Da kallo ya bita kawai, abin dariya abin tausayi har ta ɓacewa ganinsa sannan ya maida idanunsa kan Rabi da take ta cika tana batsewa. Ya shafi kwantaccen suman kansa ya ƙara sakar mata murmushi "Ummm me ma kike cewa Honey?" Wani mugun zuciya ne ya taso mata kamar za ta ɗuɗɗura mishi ashar sai tayi ƙumajin dannewa, ta buɗe baki za ta yi magana wani maƙoƙo ya taso daga ciki ya tsaya mata a maƙoshi, shi bai fito waje ba shi bai koma ciki ba kawai sai ta fara hawaye dan haushi. "Yi haƙuri Honey, bari inyi wanka muyi magana." Ya miƙe tsaye ya nufi hanyar ɓangarenshi ita kuwa ta bishi da kallon baƙin-ciki tana ta hawaye, sai da ya kusa ɓacewa ganinta ya juyo yana kallonta. "Honey ko za ki taya ni wankan ne?" Gudun hawayenta ne ya ƙara ƙarfi, da ta buɗe baki har lokacin maganar kasa fita tayi kawai sai tayi na Surayya da sassarfa ita ma ta wuce ɓangarenta tana kuka. Murmushi kawai yayi ya shige ɓangarensa. Ya san al'amarin da ciwo, shi yasa sam baiji haushinsu ba. Kuma ya ɗauki ɗammarar lallaɓasu har ya kwantar musu da hankali in Allah ya yarda. Ƙarin aure a gurin ƴa mace abin baƙin ciki ne mai girman gaske musamman irin nashi auren da yazo bagatatan ba tare da sun sani ba, ya san dole su ji damuwa da baƙin-ciki. Ya daɗe a cikin kwamin wanka yana saƙe-saƙe, shi kaɗai yake sakarwa kansa murmushi, zuciyarsa cike da tunanin yanayin da suke ciki shi da ita ɗazu da safe. Ina ma a ce yanzu tare yake da ita a cikin kwamin wankan nan? Ya ma kasa kwatanta yanayin da za su shiga dan tsananin shauƙi. Sosai yake jin nishaɗi da farin-ciki, yayi mamaki ƙwarai. Abu ne da bai taɓa tsammani ba a ce wai aurenta ne zai tsunduma shi a cikin irin wannan kogin na tsananin shauƙi da tunanin ƙara'i da ƴar ƙanƙanuwar yarinya mai shekaru goma sha... matansa duk cikakkun mata ne da suka ba ishirin da biyar baya. A lalace a sanyaye ya dinga komai shi yasa har aka kira sallar azahar bai kammala shiryawa ba, kiran sallar ne ma yasa ya ƙarasa da hanzari bayan ya koma banɗakin ya ɗauro alwala. A kunnuwansu ya fice zuwa masallaci, har lokacin cikin su biyun babu wacce ta fito falon. Hallau dai a kunnuwansu ya dawo gidan bayan an idar da sallah ya ɗau makullin motarsa ya ja ya sake ficewa daga gidan. Wani sabon ƙunci ne ya ƙara mamaye su, saƙar zuciyarsu da tunaninsu iri ɗaya ne. 'Gurin wannan shegiyar ya tafi.' Wannan tunanin yasa duk suka fito daga ɗakunansu dan zuwa gurin juna su tattauna ko za su samarwa kansu hanya mai ɓullewa sai suka yi kiciɓus a falon. A tare suka kalli juna, duk su biyun mamakin yadda suka yi ƙozai-ƙozai suka zabge a lokaci guda suke yi a ransu amma babu wacce ta furta hakan ga ƴar'uwarta. Sharewa suka yi suka zauna waje ɗaya a kan kujerun falon. "Rabi yanzu ya zamu yi?" Ta kalle ta kawai, haka kawai ta ji tambayar ta ɓata mata rai. Ta mele baki gefe ɗaya ta kauda kai "Ya za muyi kuwa Surayya da ya wuce muyi haƙuri? Tunda duk yadda muka tsara ɗazu ke kika wargaza mana shirin. Kawai daga ganinshi kin kasa cewa komai sai kuka kike yi, da yake ni ce nayi sunan tsiya ni kaɗai kike so in titsiye shi inbi ba'asin rashin adalcin da aka yi mana?" Ta ja tsaki ƙasa-ƙasa ta sake kauda kai gefe ɗaya ranta na suya. "Kiyi haƙuri, wallahi ɗazu kasa magana nayi dan baƙin-ciki. Amma yanzu zanyi mishi wurjan-jan idan ya shig..." Dawowar motarsa yasa ta haɗiye sauran maganar a cikinta. Ƙofar shigowa duk suka zubawa idanu suna jiran su ga da wani ido zai shiga cikin falon ya kalle su? Shi ma kamar ya san suna falon tsare gida yayi ya koma asalin Maheer ɗinsa da baya ɗaukar wargi ko raini ya murɗa hannun ƙofar falon bakinshi ɗauke da sallama. Ganin yanayin da ya shiga yasa Surayya amsa sallamar ƙasa-ƙasa ta kauda kanta gefe ɗaya. Ita kuwa Rabi jijjiga ƙafafu kawai take yi tana cika da batsewa. Jira take ya ce kule ta ce cas! Ya kalli Surayya da ɗaurarrar fuska mare walwala, ya miƙa mata ledojin abincin da yake hannunsa. "Je kicin ki haɗo mana abinci ki kawo kan dining." Yayi magana da tsayayyiyar muryar da ba shiri ta miƙe da sauri ta karɓi ledojin, jikinta na ɗan rawa ta nufi hanyar kicin da saurin gaske kamar za ta kifa saboda tsoro. Masifaffen haushin ɓarin jikinta ne ya kama Rabi, ta ja tsaki a fili. Ta miƙe a fusace za ta wuce ɓangarenta ya daka mata wani gigitaccen tsawan da ba shiri tsoro yasa ta koma daɓas ta zauna a inda ta tashi. "Ina kike shirin tafiya bayan na ce a haɗo mana abinci gaba ɗaya?" Ya jefa mata tambayar cikin fushi yana ƙara tamke fuskarsa. "Na ƙoshi." Ta faɗa cikin fushi tana tura baki gaba kamar shantu. "Zauna ina buƙatar magana da ku." Fitowar Surayya da farantan abinci yasa shi tashi daga kan kujerun falon ya koma kan kujerun cin abinci. Yana zaune yana daddana wata sabuwar waya saɓanin ta shi da suka sanshi da ita har ta gama jera kayan abincin da duk wani abu da za su buƙata, ta zuba mishi a faranti ta tura gabanshi. Za ta zuba nata ya miƙa mata cokali ya umarce ta su ci tare. A ɗarare take zaune kujerar kusa da tashi, cin abincinshi yake yi hankalinshi kwance. Ita kuwa dukda matsanancin yunwar da take ji dan ko karyawa bata yi tsattsakurar abincin kawai take yi saboda damuwa, tana ci tana share hawaye jefi-jefi. Kaɗan ta ci ta ajiye cokalin alamun ta ƙoshi, za ta tashi ya ce ta zauna ta jira shi. Sai da yaci yayi ƙat sannan ya bata damar tashi suka koma kan kujerun falon. Kusa da Rabi ta zauna, kamar haɗin baki duk sai suka sadda kawunansu ƙasa suka zabga tagumi, ababen tausayi ziryan dai ga duk wanda ya kalle su. Ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi, ya ajiye wayar hannunshi a gefe ya maida hankalinshi kansu ya fara magana a tausashe, cike da nutsuwa da baiwar balaga ta iya magana. Ƙwayoyin idanuwanshi suna zaga tsakanin duk su biyun. "Ƙarin Aure umarni ne na Allah SWT ga duk wani namijin da ya san zai iya adalci a tsakanin matanshi. Na san duk ku biyun kunsan wannan ba sai na janyo muku wani ayar Alƙur'ani mai girma ko in kawo muku hadithin kuyi aure ku hayayyafa ba. Amma duk da haka a matsayina na mijinku ina mai baku haƙuri, Allah ya huci zukatanku. Ba wai dan nayi muku laifin ƙara aure nake baku haƙurin ba, kawai ina ji a raina ne kamar ban kyauta muku da ban sanar da ku da bakina ba saidai ku ji a bakin mutane. Amma ina so ku sani nayi hakan ba don cutar da ku bane, ko kuma don in nuna baku da muhimmanci a guri na. Ko kaɗan ba haka bane, duk wacce ta ɗauki wannan tunanin ma ina so ta watsar da wannan daga zuciyarta. Allah ya sani ina son ku, kuma har gobe ina tsananin ƙaunarku. Ina martabaku da ganin darajarku, da waɗannan dalilan bazan taɓa yin wani abu da zai cutar da ku ba. Batun ƙarin auren nan dukda na san da shi amma ɗaurin auren baga-tatan ya taso min jiya da daddare saboda wasu tarin dalilai da ni kaɗai na barwa kaina sani. Zanyi matuƙar farin ciki idan kuka haɗa kanku kuka rungumi ƙanwarku da hannu bibiyu, zanyi matuƙar farin ciki idan kuka tallafa min gurin sauke nauyinku da Allah ya rataya min a wuyana. Zanyi matuƙar farin-ciki idan kuka juya akalar kishinku gurin tsere da rige-rigen faranta min dan ku sami aljannarku. Ina fatan za ku yi haƙuri ku danni zuciyarku ku bani haɗin kai? ni kuma in Allah ya yarda baza ku taɓa kama ni da yunƙurin yin wani abu na rashin adalci a tsakaninku ba." Shiru suka yi duk su biyun, aka rasa wacce za ta fara cewa komai. Amma tabbas tausasan kalamanshi sunyi nasarar zabge ɓacin ransu da kashi hamsin bisa ɗari. "Kun yi shiru? Baku ce komai ba?" "Insha Allahu za ka same mu masu yi maka biyayya da baka haɗin kai." Surayya ta ari bakin Rabi ta ci musu wawwarar albasa. "Na gode Sweetat." Ya amsa yana sakar mata murmushi. Ya maida idanunshi kan Rabi "Honey baki ce komai ba." "Nima in Allah ya yarda baza ka samu damuwa daga gare ni ba. Ka yi haƙuri da rashin kunyar da na yi maka ɗazu." Ta faɗa a sanyaye, cike da kunya. Murmushi yayi kawai ita ma yayi mata godiya. Nan ya dararrashe a falon ya ci gaba da jansu da hira. Tun suna ɗari-ɗari har suka sake aka fara wasa da dariya a tsakaninsu irin wanda ba'a taɓa yi ba tun da suka yi aure. Yinin ranar gaba ɗaya bai sake fita ko ina ba sai masallaci, shi ma da an idar da sallah ya gama lazumi nan da nan yake komawa gida. Hakan ba ƙaramin farin-ciki ya tsunduma zukatansu a ciki ba, sun tabbatar ko da yana son amarya to su ma fa har lokacin ƴan gaban goshi ne. Sun kuma ɗaura ɗamarar ƙara zage damtse gurin tarairayarsa da nuna masa kulawa, a taƙaice dai ko waccensu tata ta fissheta. Har washe gari da ya ƙarasawa Surayya kwanan girkinta suna ya fita Ofis da nufin idan ya koma gida yamma Rabi ce za ta amshi girki suna cike da nishaɗi. Saboda jiya bai je ofis ba aiki cakuɗe mishi yayi duk yadda ya so ya samu damar leƙa Bilhaƙƙi bai samu ba, kuma ya kira wayarsa da take hannunta a kashe. Shi kuma yana jin kunyar kiran su Ummee ya ce a bata wayar ko da ya kira gaishe su kawai yayi ya katse, sai da yamma ya samu ya yakice aikin ƙarfe huɗu ya bar Ofis saɓanin biyar da yake tashi kai tsaye ya nufi gidan Malam. Zuciyarsa cike da ɗoki da mararin son ganinta. Ko da ya isa gidan su Ummee basa nan, sai ƴanmatan gidan ya tarar a kicin suna toya wainar fulawa. Har da ita a cikinsu, suna tsaye gaban Gas ana zuba ƙullun tana soyawa suna wasa da dariya haɗe da caccafkewa, har da Asma'u da ta zo daga Maru. "Asma'u saukar yaushe?" (Asma'u idan ba ku manta ƴar wajen Ummee Balaraba ce, sa'anni suke ita da Saudat amma tun tana ƴar ƙarama Malam ya bada ita ga ƙanwarsa Aunty Ramatu da take aure a Maru saboda bata taɓa haihuwa ba. Zamanta a can yasa hausar zamfara ya kama bakinta raɗam) Ya tambaye ta yana murmushi. "Daɗa Yaya jiya munka taho da yamma ni da Aunty. Ina yini?" Ta zube tana gaishe shi cike da ladabi. Da murmushi ya amsa ta sannan ya amsa gaisuwar Saudat da Bilhaƙƙi da suka haɗa baki gurin gaishe shi. Duk da a gaban ƙannenshi ne ya kasa ɓoye ƙwayoyin idanunshi wajen kallonta, ta yi mishi kyau sosai. Ta sha gayu cikin riga da sket na atamfa, kayan sun kamata tsam sun fito da hips ɗinta, ta yi ɗaurin ture ka ga tsiya, gashin kanta da ta ƙarasa tsefewa ta wanke tas ta kame shi da ribom jelarshi ya sauko ta ƙasan ɗaurin ɗan kwalinta. "Ina su Mummy?" Yayi tambayar hankalinshi a kanta. Hankalinta yana kan wainar fulawa bata san ma da ita yake yi ba sai da Saudat ta zungureta a gefen ciki. "Sun tafi unguwa." Ta amsa tana hararar Saudat. Ficewa yayi daga kicin ɗin ya shiga falon Ummee ya zauna yana jiranta. "Amaryar yaya ke fa yake jira..." "Inji wa?" Ta yi saurin katse saurin katse Saudat tana dariya. "Zaman jiran dawowar su Ummee yake yi ba ni ba yarinya." "Daɗa ke kam Matar Yaya na raina wayonki, wa ka whaɗa miki a wagga zamani ana sake da tarairayar mai gida? Billahillazi idan kika yi sake waɗannan manyan matan nashi za su saye hilin zuciyarsa ke kina nan sake da baki. Kinga tai ki tarairayi mai gidanki kawo suyat in amshe ki kafin ki dawo" Asma'u ta faɗa tana kame da haɓa cikin mamaki. Dariya tayi kawai ta aje cokalin juyawar ta fice daga kicin ɗin ta nufi gurinshi. Daga bakin ƙofar falon ta turje bayan ya amsa sallamarta, ta kalle shi fuskarta babu walwala sosai. "In kawo maka wainar fulawa?" Hannu yasa yafito ta alamar ta je gare shi. Tana yauƙi da yanga yana bin ta da ido har ta ƙarasa kusa da shi ta zauna a ƙasa kusa da ƙafafunshi. "Ga ni" "Ina wayata?" Tashi tsam tayi ta nufi cikin ɗaki da nufin ɗauko masa sai ya bi bayanta. Suna shiga ya janyota tsam ya rungume a ƙirjinsa yana sauke wasu wawayen ajiyoyin zuciya akai-akai. Luf tayi a kirjinsa suna shaƙar ƙamshin juna. "Babe baki yi kewa ta ba ko?" Ya raɗa mata a kunne. "Ummm kamar yadda kaima baka yi tawa ba..." Haɗe bakinsu da yayi guri ɗaya ya fara aika mata da wani sassanyar sumba a nutse yasa tayi luf tana ƙara ƙanƙameshi, jin da yayi kamar za ta zame yasa hannu biyu ya ƙara tallafo mazaunanta ya ci gaba daga inda ya tsaya, tsawon lokaci har tsayuwa na neman gagararsu sannan ya saki bakinta ya ja ta ya zauna a gefen gado ita kuma ya zaunar da ita saman cinyoyinsa. Kanta na kwance kan kirjinsa yana shafa gashin kanta. "Idan za mu kwana mu yini bazan iya kwatanta miki yadda na kwana na yini cikin kewarki ba. Ya jikinki?" Ta ƙara langaɓe kanta sosai kamar za ta shige cikin ƙirjinsa, ta tura baki a hankali ta ce. "Ni na ji sauƙi." "Ciwon bayan da kafar duk sun tafi?" "Eh" "To Allah ya ƙara miki lafiya Babe. Tashi ki ga abinda na kawo miki." Ta mike za ta sauka daga kan cinyarsa ya sake zaunar da ita, ya dauki ledar da ya shiga da ita ya buɗe sai ga kwalin waya sabuwa dal. Samsung ce sak irin ta hannunsa da yake bata aro, ya ɗauko sabon layin mtn ya saka a ciki sannan ya kunna wayar. "Wannan wayarki ce, daga yau bazan sake baki aron tawa wayar ba..." Tsananin murna yasa kafin ya rufe baki ta sake ruƙunƙumeshi tana dariyar farin-ciki. "Na gode Gangaran..." "Ke tsaya. Ki canza min suna, bana son Gangaran ɗinnan da kike ce min." Tana dariya ta kalle shi da sigar tsokana ta ce "Laaaa fassarar sunanka ne fa." "Na sani ai, amma bana so kina ce min." Ya faɗa yana canza fuska. "Tom, sorry Heart." Tayi maganar tana shafa saitin zuciyarsa. "Zan nemi sunan soyayya mai daɗi in dinga faɗa maka ka ji?" BILHAƘƘI Ya ɗaga kai kawai alamar ya ji. Ya sake kallonta sama da ƙasa, gaba ɗaya hankalinta yana kan wayar da ya kawo mata, ta shiga nan ta fita can. Ya raɗa mata a kunne. "Kinyi kyau Babe. Amma ire-iren waɗannan kayan da suke fito miki da shape ki daina saka su a nan gidan, ki adana su sai kin je can gidanki sai ki dinga min kwalliya da su. Zan shiga kasuwa gobe in nemo miki dogayen riguna masu kyau ki dinga sakawa a nan. Kin gane?" Murmushi tayi, ta ɗaga kai ta kalle shi tayi far da ƙwayoyin idanunta. "Na gane, na gode Gangar... Au! Ba Gangaran ba. Yi haƙuri." Ta ƙarasa maganar haɗe da ƙanƙame shi tana dariya. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke ta runtse idanuwanta da suke cike da shauƙi. "Bir tanem. Thank you Bir tanem." "Bir tanem?" Ya maimita sunan da ta raɗa mishi da sigar tambaya, fuskarsa cike da mamaki bayan ya ɗago kanta daga ƙirjinsa suna kallon-kallo. Ƙasa sosai ta yi da idanunta, suka yi wani lauuuu kamar tana jin bacci, ta ɗaga mishi kai alamar eh. "Waw!! Fassara min. Yadda kika furta sunan yayi daɗi sosai a kyakkyawan bakinki. Bir tanem! Da wanne yare ke nan? ba turanci bane ko?" "Eh ba turanci bane, a wani yaren fassararshi sunan soyayya ne. Ka nemo fassarar..." Sallamar su Ummee da ta ji sama-sama a can tsakar gidan yasa ta yi saurin miƙewa daga jikinsa tana zazzare idanu kamar wacce ta yi wa Sarki ƙarya. Bai ji abinda ta jiyo ba sai da ta ankarar da shi "Wayyoo... Su Ummee sun dawo." Ta yi kwaɓa-kwaɓa da fuska kamar za ta fashe da kuka. "To miye dan sun dawo?" Ya tambaye ta cikin rashin damuwa, fuskarsa fal da murmushi. Hannu ya miƙa zai sake janyo ta jikinsa da sauri ta zille ta nufi wardrope ta buɗe tana duba wayarsa a inda ta ajiye. Jin su Ummee sun shiga cikin falon dole ya miƙe yana ya fita falon, suna haɗa ido ya fara sosa ƙeya cike da kunya. "Aunty sannunku da dawowa." Duk su ukun sai suka bishi da idanu, sai Mummy da Aunty suka murmusa ita kuwa Ummee ta haɗe girar sama da ƙasa ta ce "Me kake nema min a cikin ɗaki?" Wuf sai ga ta ta fito kamar an jefo ta, ta zunduma hijabin sallarta gaba a baya. Daga kallo ɗaya za a gane duk a ɗimauce ta ke. Ta ɗaga hannuwa duk biyu sama tana nuna musu wayar "Allah ba komai Ummee, kinga ma wayarsa ya ce in ɗauko masa." Duk sai ta basu dariya, ɗakinta ta shige ta ƙyale su a nan. "Daɗa ango kake ɗiyana Maheer, ƙyale Aunty Balaraba da wasu tuhume-tuhume. Yo a ina za a raba Ango da amaryarsa. Tai ka sha sharahinka ka jiya? Ya gidan? ya sauran iyalan naka?" A saɓe ta samu ta fice daga falon bayan ta miƙa masa wayarsa. Shi kuma ya zauna suna gaisawa da Aunty da Mummy. Suna can ɗakin ƴan mata Saudat tana ta tsokanarta ita kuma Asma'u tana koya mata yadda za ta tarairayi mijinta ba tare da kunya ba har ya fice daga gidan bata sani ba. "Yo wallah ko Aunty bar ganinta kamar ta whara tsohewa in kinkaga yadda take tarairayar Alhajinta abin zai baki mamaki. Wallah a can duk tsuhwar mace sam bata sake da gyaran jiki da tarairayar mai gida. In kinka zauna nan sake da baki kina ji kina gani garin kallon ruwa kwaɗo zai ɗamra miki ƙwahwahu..." Duk su biyun dariya suka kwashe da shi saboda yadda ta furta ƙafafun da hausar gusau gwanin ban dariya. Haka suka ci gaba da hirarsu mai haɗe da tsokana ta wani fannin kuma suna haɗawa da bata shawarwarin yadda za ta zauna da abokan zamanta. (kunsan dai mafiyawancin ƴan matan yanzu duk wani theory sun sanshi akan aure pratical ne kawai basu yi ba.) ****** ******* Bayin nata suna gama ficewa da sauri ta tashi zaune daga kishingiɗar da tayi, sosai ta fuskance shi tana ƙara miƙar da ƙafafunta. "Hamisu ya ake ciki? Wannan karon me Malam ya faɗa maka? Yanayin fuskarka yana baiyana min kaman akwai wani mummunan abu da yake shirin tunkaro mu. Ina fatan ba akan mai wutsiya ba ce?" "Ƙwarai kuwa a kanta ne Ranki ya daɗe." Ya amsa a sanyaye yanayin fuskarsa yana ƙara canzawa zuwa cikin damuwa da taraddadi. "Ina jinka. Faɗa min me ya ce?" Ta tambaye shi cike da nutsuwa, wani bahagon murmushi da yake fuskarta yasa shi kasa tantance a wani yanayi zuciyarta take ciki. Har ya buɗe baki zaiyi magana aka buɗo ƙofar turakar aka shiga ciki ba tare da sallama ko neman izini ba. Duk su biyun ɗaga kai suka yi suna kallon ƙofar. Yarima Muzaffar ne, babban ɗan sarki Abdulfatah na biyu. Yarima mai jiran gado a babbar masarautan Bauchi da kewayenta. "Yaya Safara'u na rasa dalilin da yasa har yanzu Muzaffar baiyi hankali ba. Fisabilillahi ta ya zai shigo mana nan kai tsaye ba tare da neman izinin shigowa ba...?" "Dakata Hamisu! Dakata Ciroma!!" Ta daka mishi tsawa har sau biyu, nan da nan ta ɗaure fuska ta haɗe girar sama da ƙasa ta yi murtuk. In da abinda ta tsana a rayuwarta bai wuce a kawo wani cikas ɗin halin Muzaffar ba, shi yasa ko Mai martaba suke yawan haurawa sama da shi akan tilon ɗan nata da ta kafa ta tsare gaba da baya sama da ƙasa a kanshi. "Ta ya dan zai shigo turakar Mahaifiyarsa ka ce sai ya nemi izini kamar sauran gama-garin mutane? Yo ko Mai martaba ya isa ya faɗi haka balle kai karan kaɗa miya? Ina ƙara jan kunnenka ka kama bakinka da kushe shi Ciroma. Ka san dai shi ne Sarkin gobe a masarautar nan ko? Ina maka tunin ana wanke ƙwarya ko dan gobe ne idan ba haka ba wallahi lokacin da ya samu dama a hannunsa bazan hana shi aikata duk abinda yake so akan ko wane shege a masauratar nan ba. Ba ruwana da kusancin da ke tsakanina da ko Uban waye." Ta maida hankalinta kan Muzaffar da yayi ɗai-ɗai a kan makeken gadonta can nesa da su, kamar ma baisan akan me suke magana ba. "Yarima? Lafiya kake kuwa? ina fatan dai yau ka sha maganinka?" "Na sha." Ya amsa da ƙyar a gaulance tare da dalalar da wani yayyauƙar miyau a bakinsa. Ba tare da duba tsadar zanin gadon da yake kwance a kai ba yasa hannu ya tattaro zanin gadon ya goge bakinsa, ya juyo ya kalle su duk su biyun. "Umma... Ki sanar da mai martaba aure nake so. Ya nema min auren Aisha ƴar gidan Waziri Lawal, sau shida ina aikawa gurinta amma sam ta ƙi saurarena. Da na sake aikawa jiya ma sai ta ce a faɗa min ita tafi ƙarfin ta auri Gaula iri na..." "Kan Ubancan!" Ta lailayo wani makeken ashar ta maka kamar ba Sarauniya Safara'u ba. "Inji ta ne ta ce maka Gaula? waye ma ubanta a garinnan balle ita banzan banza dillalin kashi? Tsiyan matsiyatan ƴaƴan talakawa masu haye a sarauta kenan basu iya girman kai ba. Amma Yarima ba na ce ka bari in gama tunanin wace ƴar sarki ce ta da ce da kai a cikin ƴaƴan manyan sarakuna sa'annin mahaifinka ba? ka san fa nan gaba kaɗan kaine Sarki a masaurautannan ta ya za ka fara da neman auren ƴar gidan waziri? ƙasƙantacce da yake a ƙarƙashinka...?" "Ni dai gaskiya ita nake so Umma." Yayi maganar yana bubbuga ƙafafunshi cike da shagwaɓa a kan gadon kamar wani ƙaramin yaro. Chiroma dai baki sake yake kallon wannan ya kalli wancan ranshi a dagule. 'Tsananin tsana da haushin Muzaffar da yake ji a ransa kamar ya tashi ya shaƙo shi har sai ya daina numfashi. Ya rasa dalilin da yasa ya tsani yaron tsana mai tsananin gaske. Ko don saboda iyakarshi da Yayarshi take gwada mishi a kan yaron ne? oho!' Tunaninsa ya katse lokacin da ya ji ta fara rarrashinsa da kalaman kwantar da hankali. "To shi kenan. Kwantar da hankalinka. Ai dole mu so duk abinda kake so ko da ranmu baya so. Anjima zanje in samu Mai martaba da maganar . Ka kwantar da hankalinka ka ji ko?" "Yauwa Ummata. Haka nake son ji." Dira yayi daga kan gadon ya nufi hanyar fita daga ɗakin, duk suka bi shi da kallo har ya fice ya ɓacewa ganinsu. "Ke Murja." Ya ƙwalawa ɗaya daga cikin bayin da suke ta kara-kaina a falon kira. Gabanta ne ya yanke ya faɗi, nan ta ke ta fara rawar ɗari idanunta ciccike da hawaye ta zube a gabansa. "Allah yaja zamanin Yarima. Ga ni! kiranka abin amsawa ne a gare ni Yarima mai jiran gado. Allah ya ƙara maka lafiya da nisan kwana." Wani mugun kallo da ya auna mata yasa kayan cikinta suka haɗe a dunƙule guri guda. Ya buɗe baki zayyi magana wani yayyauƙar miyau ya taho mishi da sauri ya kama rigar alkhabbarsa ya goge miyan da ita. Sai zazzare idanu yake yi yana ciccin magani a gaban Bayi dan kar su kawo mishi wargi ko kuma su ga wallenshi. "Anjima da daddare ki samu Bala zai baki saƙo ki kawo ma Umma." "To Ranka ya daɗe. Angama in Allah ya yarda." Ta amsa a sanyaye idanunta ciccike da hawaye. Wucewa yayi ya barta tsugune a gurin tana sharar ƙwalla, zuciyarta a ƙuntace. Kiran Yarima ba komai bane a gurinta fa ce masifa, ga shi yayi mugun matsa mata a cikin kwana biyunnan. "Chiroma ina saurarenka." Sosai ya ƙara ƙasa da muryarsa, ya fara magana fuskarsa cike da damuwa. "Yaya Safara'u wai kina nufin har yau Yarima bai daina taɓe-taɓen Bayin nan ba? kinsan kuwa ko jiya sai da Malam ya ƙara ja min kunne akan haka? ya kuma ce in faɗa miki muddin bai daina ba idan tauraruwa mai wutsiya ta gitto ƙasarnan cikin ƙanƙanin lokaci alkadarinki zai karye..." "Ƙarya ne wallahi." Ta katse shi cikin tsawa fuskarta na bayyana tsananin ɓacin rai da tashin hankali. A zabure ta miƙe tsaye ta fara kai kawo a tsakar ɗakin tana buga tafukan hannayenta ɗaya cikin ɗaya. "Chiroma kalle ni nan!" Ta nuna ƙirjinta da yatsarta manuniya, ta ci gaba da magana cikin fushi da isa mai bayyana tsananin izzar da take taƙama da ita. "Ni Safara'u na ci dubu sai ceto. Ƙarya ne a ce wata ƴar ƙanƙanuwar tauraruwa za ta kawo ƙarshen tsananin haskawar da na daɗe ina yi kuma har gobe ina kan yi a masaurautar nan da duk inda nasa ƙafa a faɗin duniyarnan. Wannan ƙarya ne. Ko babu aikin Malam akwai aikin tsafi. Idan kuma tsafin Boka yaƙi ci akwai tsananin makircin da na yi tsawon shekaru biyu ina tsotsa a nonon gyatumarmu Mai babban ɗaki. Karka kuskura ka sake faɗa min banzar magana makamanciyar wannan? kana ji na?" "Tuba nake Ranki ya daɗe. Allah ya huci zuciyarki Yaya. Zan kiyaye gaba." Tsawon lokaci tana ƙasa tana sama haɗe da gwama numfashi kamar wata kububuwa, a ƙasaice ta koma ta zauna a inda take tun kafin shigowarsa. Kishingiɗa tayi akan tumtum ɗin sarauta da suke ajiye jefi-jefi a kan kafet ɗin da ya malaye uwar ɗakin. "Ka sanar da Malam ya bar aikin tauraruwa mai wutsiya a hannuna. Na ga alamun bazai iya ba, zan nemi wanda zai iya yi kamar yadda nake so. Amma a wannan karon ina so yayi min aiki mai tsananin zafi a kan Safiyya. A yi mata mai gaba ɗaya, tunda dai sun dage ita da Mai martaba suna son ganin abinda yake cikinta ya tako duniya. Ka sanar da shi wannan karon biyu babu nake so ya tabbata da zarar likitoci sun ɗaura wuƙar tiyata a jikinta. Ka fahimce ni?" "Ƙwarai na fahimci abinda kike nufi Yaya, yadda kika ce haka za a yi. Angama." Ya amsa a tsorace, yadda ya ga ta fusata shi yasa ya haɗiye sauran maganganun tauraruwa mai wutsiya a cikinshi ya ƙi sanar da ita. Ya san fushinta ba kyau, yanzu sai ta nemi gwada sauke fushinta a kanshi duk da ba shi ya kar zomon ba. "Ɓace min da gani. Na sallame ka." Yana fita ta maida kanta ƙasa tana sakin wani murmushi, zuciyarta cike da muggan saƙe-saƙe. Ɗaya daga cikin amintattun bayinta ta aika aka yi mata kiran Jakadiya suka ƙule a can ƙuryar turakarta. "Ya zama dole Jakadiya ki koma gurin Ci dubu a wannan karon. Tauraruwar nan shi kaɗai ne zai iya min maganinta yadda baza ma ta taɓa tunanin giftowa yankin jiharnan ba. Idan kuwa ta kuskura ta yi yunkurin shigowa yasa hadimansa su hallaka ta tun kafin ta iso. Zan ba shi duk abinda yake buƙata a faɗin duniyar nan matuƙar aikinshi yayi kyau kamar yadda ya saba." ******* ******* "Bir tanem gaskiya ni dai A'a...! kunya nake ji ni dai gaskiya... Haka kawai sai inje in ce wa Ummee zan raka ka unguwa...? Kawai su ga kamar bani da kunya ina so inbi mijina ne...? ni dai a'a..." Sake ƙanƙame wayar yayi a kunnensa yana jin saukar daddaɗan muryarta, shauƙin da muryar yake saukar masa a jikinsa kamar misalin saukar sassanyar ruwan sama ne a jikin bil'adama lokacin tsananin zafi. Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya yana jin wani yam-yam kamar tana mishi tafiyar tsutsa, har ta gama zuba mishi shagwaɓa da ƙorafin ita baza ta iya cewa su Ummee za ta raka shi ba. "Tatlim." Ya kira ta da sabon sunan soyayyar da shi ma ya raɗa mata, a muryarsa cike da wani irin zazzaƙar salon da ya sa ta kusa shiɗewa a kan gado. Ƙara ƙanƙame filo tayi a ƙirjinta tana lullumshe idanu kamar yana gabanta. Ta sake ƙasa da muryarta sosai ta amsa da. "Na'am Bir tanem." "Ki shirya zuwa ƙarfe uku. Ni da kaina zan tambaya mana Ummee izinin fita. Sosai nake kewar lallausar fatarki fa. Cikin kwana biyun nan kuma na lura gaba ɗaya Ummee ta kasa ta tsare kamar zan wani cinye ki." Sassanyar dariya ta sakar mishi a kunne, dole tasa shi ma ya murmusa yana sosa keya. "Dariyar ta mecece?" "Dan Allah ba ka jin kunya Bir tanem?" "Tatlim kunyar wa zanji? ke ɗin fa matata ce. Mallakina ce. Halaliyata ce. To bayan waɗannan ƙwararan dalilan da suka haɗu suka damƙa min ke kunyar wa zanji gurin fita da ke?." "Hakane Bir tanem. Yauwa na tuna, faɗa min" "Me zan faɗa miki?" Ya tambaye ta cikin shaukin son da ya gagara ɓoyuwa har a muryarsa. "Yadda aka yi ka gano fassarar sunan da na raɗa maka mana? na ji kai ma har ka raɗa min daddaɗan suna. Amma da gaske ni Sweetheart ɗinka ce?" "Kina shakka ne? Bari anjima idan mun fito zan tabbatar miki, zan share miki duk wani tantama da kike yi. A google na nemi fassarar Bir tanem, sai suka bani amsar My one and only in Turkish. Sai na nemi yadda ake kiran Sweetheart a Turkish suka bani amsa Tatlim. Kinji yadda na samu amsoshin. Amma a ina kika san yaren Tukish?" "A makaranta suka koya mana." "Ashe kinyi karatu..." "Kai...! kyakkyawan sakamakon da ba kowa ke iya samu ba na fito da shi a jarabawar waec da neco. Kawai dan dai komai na barshi a can gidan Madam ne." "Ma sha Allah. Kina sha'awar ci gaba da karatu?" "E in dai za ka barni ina so." Shigar Rabi cikin ɗakin yasa yayi ɗif a wayar bai amsa mata ba. Ya bi ta da kallo ganin yadda ta ɗanɗasa kwalliya cikin ƙananun kaya, ta yi kyau sosai kam. Duk wasu albarkatun jikinta ta matso su sun bayyana a fili. Ya ɗanyi murmushi. "Tatlim. Will call you letter." Bai jira amsawarta ba ya katse wayar. A can ɓangarenta kuma sake da baki ta bi wayar da kallo, ta danna dan ganin lokaci. Karfe tara da kwata na safe ne, tunanin ko matarsa ne ta shiga cikin ɗakin yasa ta ja tsaki ta ajiye wayar a gefe taja bargo ta lullaɓa har kanta. Ko da Saudat ta shiga ma ganin kamar tana bacci yasa ta fita a hankali dan kar ta tashe ta. ******** ****** Cike da zakwaɗi da masifar ɗoki take komai da sauri-sauri har ta gama shiryawa cikin riga da sket na lesi mare nauyi. Duk da haka sai da yayi zaman jiranta na minti ashirin. Mummy da Ummee sai tsokanarta suke yi ita kuma tana dariya da sunne kai. Bayan tsawon watanni shida da wasu kwanaki da tayi a gida tana zaune ba tare da ta leƙa ko ƙofar gida ba sai yau za ta fita. Lallai wannan babban abin farinciki ne a gurinta. Ga Malam kam da ƙyar ya barta tayi rakiyar bayan ya keɓe Maheer yayi mishi ƙwaƙƙwaran jan kunnen ya kula da ita. Ya ƙara da tunasar da shi har yanzu waɗanda ke bibiyar rayuwarta ba wai sun haƙura bane, akwai muhimmin abun da suke so a tare da ita. Ya ce yaji ya gani in Allah ya yarda zai kula da ita har su koma gidan. "Babe duk wannan farincikin na menene...?" Ya tambaye ta yana murmushi bayan ya riƙo hannunta ɗaya, ɗayan hannun nasa kuma yana murza sitiyari. "Sai yau fa na fito. Darling sai yau na fito waje tun da na zo gidan Malam fa. Wawwww! Dubi unguwarnan ashe tana da kyau sosai har haka? Can ne masallacin Malam ko?" Ta nuna masallacin da yatsa. "Eh nan ne." Ya amsa yana dariya. Daƙyar ya samu ta nutsu har suka ƙarasa kasuwan central inda shagunansu yake. Duk da ba zaman kasuwar yake yi sosai ba sai a weekend yake leƙawa yana da babban ofis ɗinshi, a gefen nashi Ofis ɗin ne na Yusuf yake. Haɗaɗɗen Ofis ne har da A.C a ciki saboda tsabar son hutu. A ciki ya zaunar da ita. Ko da Yusuf ya shiga dan su gaisa da Amarya duk su biyun sun shiga matsanancin mamakin da ya gaza ɓoyuwa a fuskokinsu. "Laaaaa Ya Yusuf? Ashe rai kan ga rai?" "Bibi ke zan tambaya ai, bani labarin ta inda aka haihu a ragaya." Ya tambayeta yana dariya. Sosai ya ji daɗin sake ganinta da kuma kasancewarta matar Yallaɓai. Shima yayi mamakin sanin juna da suka yi, ganin ta gyara zama za ta fara zuba mishi labari da sauri Maheer ya katse ta, fuskarsa a ɗaure. "Ke me kike shirin yi?" Galala ta bishi da kallo baki buɗe, mamaki take yi fushin kuma na miye? Bai sake kallonta ba ya maida hankalinshi kan Yusuf. "Hirarku mai tsawo ne Yusuf, kuma yanzu sauri muke yi akwai inda za mu je." Dariya kawai yayi, dan ya gane Maheer kishi yake yi. Bai ji haushin shi ba, sosai ya ji daɗin kasancewarsu ma'aurata. Daman tun a ganin farko da yayi mata ya hango dacewarsu ta ko wane ɓangare. Wani babban jaka troley da yake ajiye a Ofis ɗin ya umarci yaran shagon suka ɗauka mishi zuwa mota, tana shiga ya ja motar fuuu suka tafi bayan Yusuf ya cika ta kyautan kuɗi. "A ina kika san Yusuf?" Ya jefa mata tambayar a bazata, ko da ta kalle shi ba ita yake kallo ba, hankalinshi na kan tuƙin da yake yi. Kyaɓe baki ta yi alamun can ta matse mishi. "A kachia. Tun wancan lokacin da nake ta nacin sonka kai kuma baka so na..." "Wa ya ce miki tun a wancan lokacin ba na sonki?" "Kai ka faɗa min da bakinka. Ko ka manta in tuna maka a mabanbantan lokutan da ka ce baka so na? har ma ka ce baza ka taɓa ƙaunata ba." Wani mugun ɓacin rai da ya taso mata dole ta gimtse sauran maganganun, ta ɗaure tamau ta maida kanta can gefen titin tana kalle-kalle. Shima sai yayi shiru kawai ya ci gaba da tuƙi har suka isa hotel ɗin. Gurin zama ya nuna mata a gefe ya ajiye jakan a kusa da ita ya ƙarasa ciki ya gama duk abinda zayyi sannan ya dawo gurinta ya ce ta bishi, bisa ga mamakinta ciki suka shiga maimakon gida da tayi tsammanin za su koma. Wani ma'aikacin hotel ɗin na gaba riƙe da jakar su kuma suna binshi a baya har ya kaisu wani ɗaki yasa makulli ya buɗe ƙofar. Har ciki ya shiga da jakar yayi wa Maheer sallama ya fice daga ɗakin. "Ki shigo ciki mana." Yayi maganar fuskarsa da murmushi ganin yadda ta doge a bakin ƙofar ɗakin. Kaɗan ta shiga ciki shi kuma ya maida ƙofar ya rufe har da murza key. "Me zamu yi a nan ɗin?" Ta tambaye shi har lokacin fuskarta babu walwala. "Sallah kawai za muyi mu huta zuwa ɗan anjima sai in maida ke gida." Bai saurari amsarta ba ya shige banɗaki don ɗauro alwala. Dole ta yi wa kanta mazauni akan kujeran ɗakin tana jiran ya fito. ***** "Fushi-fushin me kike ta yi haka Tatlim? zo kiji wani labari." Ya ƙarasa maganar haɗe da janyo ta gaba ɗaya zuwa jikinsa. Hijabin jikinta ya zare a hankali ya ƙara gyara zama akan daddumar da suka idar da sallan. Sosai ya kwantar da ita a jikinshi, ya zame ɗankwalinta yana shafa kwantaccen gashin kanta da hannu ɗaya. "Kinsan Allah ɗaya ne ko Babe? Tun ranar da na fara haɗuwa da ke a asibiti har muka gabza karo wallahi na ji wani abu na musamman yana tsattsarge zuciyata game ke. Sosai na shiga wani irin yanayi da a wancan lokacin na gaza gane ko menene. Da na fahimci munyi canjen waya ba ƙaramin murna nayi ba dan nasan wannan dama ce da zaisa in ƙara tozali da kyakkyawar fuskarki. To abinda ya sagar min da gwuiwa a kanki kuma yasa ƙarfi da yaji na ke ta ƙoƙarin yakice ki a raina har na ringa miki wulakanci ina faɗa miki bana sonki bai wuce abubuwa biyu zuwa uku ba. Kinga na farko yadda na fahimci sam ba ki da wani babba mai tsawata miki a gidanku. Na biyu kuma yanayin irin shigar da kike yi mai baiyana tsiraici da yadda sam bakya shakkar ki taɓa jikina. Dalili na uku kuwa bai wuce yadda ke kika fara furta min kina so na ba. Bazan ɓoye miki ba da gaske a baya ina ganin bazan taɓa iya son duk yarinyar da ta ce tana so na ba. Abinda zai baki mamaki wallahi a wancan lokacin duk sadda na miki wulaƙanci na kore ki kika fita kina kuka mugun zafi nake ji a zuciyata. Kuma ko da baki zo gidan Malam ba ni da kaina na san akwai lokacin da zuciyata za ta gaza jure zazzafar tunaninki dole sai na koma Kachia na nemo ki a duk inda kike. Ki daina tunanin bana sonki kinji Tatlim? Ban ma san yadda aka yi soyayyarki tayi min kamun kazar kuku haka ba. Da gaske soyayyarki a zuciyata mai zafi ce sosai, ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba kan cewa ban taɓa faɗawa kwatankwacin soyayya irin ta ki ba." Wayyooo daɗi, ina aljannah ta faɗa dan murna. Duk wani ƙunci da damuwa da take ciki waɗannan daɗaɗa kuma zaƙaƙan kalaman na sa sun yaye mata. Tsananin farin-ciki yasa ta rungume shi tsam, da ta ga duk hakan ma bai gamshe ta ba fuskarsa ta kamo da hannunta biyu tana aika mishi da zafafan sumbata a duk inda bakinta ya kai. Nan da nan ta kiɗima shi da zazzafar salonta tun yana murmushi har saida ya tallafota sosai ya fara maida mata da martani. Nan kuma sai idanunta suka fara raina fata da ta ji yana ƙoƙarin zuge mata zip ɗin rigarta ta baya, ƙam ta riƙe hannunshi tayi narai-narai da ido alamun ya dakata haka. "Tatlim pls ki barni kinji." Ya faɗa da shaƙaƙƙen murya yana kallonta da idanunsa da suka canza launi zuwa ruwan ɗorawa-ɗorawa. "Bir.... ta... nem... hotel ne fa." Tayi maganar a rarrabe idanunta ciccike da hawaye, kamar za ta rushe da ihu. "Na sani. Ba wani abu zanyi ba. Just...." Sai kuma yayi shiru, ya fesar da wani zazzafan huci ta bakinshi, ya cije leɓensa na dama, ya runtse idanu. A sanyaye ya waske da cewa "Kawai ina so ki gwada waɗancan kayayyakin da na siyo miki ne in gani ko sunyi daidai" Ya ƙarasa maganar tare da nuna jakar da ya taho da ita da yatsarshi manuniya. A zabure cike da tsoro ta miƙe zaune daga jikinsa, yanayin da ya shige lokaci ɗaya ya kiɗimata ya kaɗa mata hanji. Jakar ta ja ta nufi hanyar banɗaki "Bari inje in gwada." Da idanu ya raka ta har ta ɓacewa ganinsa, a sanyaye ya miƙe ya cire rigar jikinsa da ta fara yamutsewa ya koma kan gado ya kwanta, idanunsa na fuskantar saitin banɗakin. A cikin bayin ta daɗe tana gwaggwama numfashin tsoro kafin tayi ƙoƙarin daidaita kanta, da ta kalli fuskarta a jikin madubin da yake manne a bangon gabas na bayin kuwa ba ta san lokacin da wani murmushi ya suɓuce mata. Jambaki da man bakin da ta rangaɗa a leɓenta sun rabe sun shanye tas a tsakaninsu gurin tsotse-tsotse. Runtse idanu tayi tana tuno yanayi mai daɗin da take shiga idan suna tare, lokaci ɗaya kuma sai kunya ta kamata, hannu biyu ta sa ta rufe fuska tana dariya. Da ƙyar ta iya watsar da tunanin komai ta fara ciro kayan ɗaya bayan ɗaya take sakawa a jikinta, idan ta shirya tsaɓ sai ta fita ta nuna mishi, ya ce yayi kyau sannan ta koma cikin bayin ta canza wani. Dogayen riguna ne ƴan dubai masu tsananin kyau har kala bakwai. Rigunan sunyi mata kyau sosai, kuma daidai jikinta kamar ya san size ɗinta. Sai da ta gama gwada dogayen rigunan ta fahimci ashe ba su kaɗai bane, akwai ƙananun kayan bature har kala huɗu a ciki sai kuma Inner wears danginsu P/B🙈🤣 Mutumiyarku an daɗe ba'a haɗu da ƙananun kaya ba. Jujjuya kayan taitayi a hannunta tana murmushi da hasashen irin haɗuwar da za ta yi a cikin kayannan. Wata ficiciyar riga mai masifar kyau kalar pink da duk tsawonta bai wuce iya gwuiwa ba ita ce ta fi ɗaukar hankalinta. Hannun rigar ɗaya siriri ne kaman na vest ɗayan kuma ɗan daidai. "Wawwww!" Ta faɗa a fili tana sakin murmushi haɗe da juyawa gaba da baya tana kallon kanta a madubi bayan ta saka rigar a jikinta. Sai da ta canza tafiya ta fara wani sassanyar salo ta buɗe ƙofar bayin ta nufi gurinshi tana yauƙi haɗe da rangaji kamar reshen bishiya a lokacin iskar damina. "Sevgilim look at me..." Ta faɗa cike da yanga tare da juyawa gaba da baya a gabanshi tana fari da idanu. Ya kasa cewa komai, runtse ido yayi kawai, a zuciyarsa yake tasbihi ga ubangijin da ya ƙawata halittarta kuma ya mallaka mishi ita a matsayin matarshi. Kasa haƙuri yayi sai da ya janyo ta jikinshi yana ta sassake ajiyar zuciya a jejjere kamar wanda yayi tseren gudu. Ita ma a wannan karon ka sa hanashi yin abinda yayi niyya ta yi, idanunta a runtse har ya zare mata rigar a jikinta. Ya kalli ababen da suke ta tsole mishi idanu har ya ɓalle abinda ya tare idanunshi daga ganinsu gaba ɗaya. Runtse ido yayi ya rungume ta tsam, tsawon wasu daƙiƙu sannan ya ɗago ta yana sake ƙare mata kallo sama da ƙasa. Har lokacin idanunta a rufe suke "Tatlim... miye wannan?" A shaƙe ya tambaye ta tare da kai hannu ya shafi zanen mai kama da kalangu da suka fito raɗam a saman na shanunta. Kunya yasa ta sake ƙanƙame shi. "Nima ban sani ba fa. Haka nan na girma na ga zanen shi ma yana ƙara fitowa raɗam a jikinsu." A kunyace ta raɗa mishi haka a kunne. Bai yi yunƙurin keta iyaka ba dan bai manta a inda suke ba, ƙara rirriƙe ta yayi a jikinsa kamar yana tsoron za a ƙwace mishi ita, ya gyara musu kwanciya sosai a kan gadon. Cikin ƙanƙanin lokaci wani daddaɗan bacci mai cike da zaƙaƙan mafarkai ya kwashe su duk su biyun. BILHAƘƘI Karfe shida da minti hamsin dai-dai Bilhaƙƙi ta farka. A lokacin har an idar da sallar magrib, motsin da tayi shi ya farkar da Maheer daga daddaɗan barcin da yake yi. "Babe ya aka yi?" Yayi maganar a hankali, har lokacin idanunsa suna lumshe. "Kalli lokaci ka ga, kamar ma an idar da sallah fa." A hankali ya buɗe ƙwayoyin idanunsa da har lokacin suke cike da barci ya zube su a kanta, suka yi kallon-kallo da murmushi a fuskokinsu. Sai kuma ya kauda fuskarsa ya maida kan agogon bango. "Subhanallahi." Ya faɗa cikin sauri. Za ta miƙe ya riƙe ta a jikinsa. Ya tashi daga kwancen suka miƙe zaune gaba-ɗaya. "Muje inyi miki wanka, sai muyi alwala muyi sallah." Dariya tayi kawai, ta sake sunne kanta a ƙirjinsa cike da kunya. "Je ka fara yi, idan ka fito nima sai inyi." Murmushi yayi, ya shafi gashin kanta, ya ɗago fuskarta ya sumbace ta a goshi. Ya ɗauko rigarta da ke ajiye a gefensa ya sa mata. Ya sauke ta a gefe sannan ya sauka ya nufi banɗakin. Sharp-sharp ya watsa ruwa, ya ɗauro alwala ya fito sai ta shiga. Ita ma nan da nan ta gama ta shirya cikin kayanta da ta fito da su daga gida ya ja musu jam'in sallar magrib. Ta so su tafi bayan sun idar da sallah ganin dare yana ƙara nisa ya ce shi yunwa yake ji, dole ta jira yayi musu odar abinci. Hankalinta gaba ɗaya yayi gida shi yasa tsattsakurar abincin kawai ta yi, shi ma ba wani sosai ya ci ba suka harhaɗa kayansu suka fito. "Me kike so in siya miki?" Suna hanyar komawa gida yake tambayarta haka. "Bayan duk waɗannan siyayyar?" "Eh mana. Za muyi tafiya gobe da Malam, bana so bayan na tafi kafin in dawo ki nemi wani abu." "Ni dai bani da buƙatar komai. Ina za ku je?" Tayi tambayar idanunta yana kanshi. "Bauchi." Ya amsa a taƙaice. A ƙofar Ostrich backery ya faka motar ya ce ta jira shi minti biyu. Bai daɗe da shiga ba ya fito hannunshi riƙe da ledoji masu tambarin backery ɗin. Ya shiga ciki ya aje ledojin a kujerun baya na motar, ya ja suka ci gaba da tafiya. "Amaryar sarkin Bauchi Abdulfah na biyu ƙanwar Hajiya mahaifiyar Malam ce. Ita ce zamu je gaisarwa, gobe zamu yi sammakon tafiya saboda mu isa da wuri kar dare yayi mana a hanya, ni da Malam da Mummy." "Allah ya kaiku lafiya." "Ameen ya Allah." Ya amsa fuskarsa na baiyana jin daɗin addu'ar da tayi musu. Haka kawai ta ji a ranta tana mararin zuwa bauchin, hannunta ta kai ta dafa hannunshi guda ɗaya kalle ta. "Bir tanem ko za ku je da ni...?" "No ki haƙura kawai Tatlim. Tafiyar akwai nisa bana so ki wahala, muma kwana biyu kawai za muyi. Kuma Malam ya ce idan mun dawo weekend na sama za ayi biki ki tare a ɗakinki." Ya kalle ta da murmushi ya ci gaba da cewa "Kinga ko a irin wannan lokacin da nake gab da gurzar angwanci duk wani abu da zai jigatar min da ke bazan yadda ya kusanto ki ba." Dariya suka yi duk su biyun. Haka suka ci gaba da hira cikin nishaɗi da ƙoƙarin fayyacewa juna duk yadda suke ji a zukatansu har suka isa gidan Malam. Bai wani jima ba bayan ya sauke ta ya shiga mata da duk siyayyar da yayi mata cikin gidan. Sama-sama suka yi magana da Malan ya bar gidan da cewa sai ya zo gobe da safe. ****** ****** Kallonta yake yi yana ta doka murmushi har ta ƙarasa kusa da shi ta zube a gabansa, kanta a ƙasa ta fara gaishe shi yana amsa mata a tausashe. A ko wane lokaci idan ya kalleta yana jin wani ƙauna ta musamman a zuciyarsa game da ita, har yau ya rasa gane dalilin da yasa haka. Yadda yake jinta kamar wata ƴarsa da ta fito daga tsatsonsa, balle yanzu da sanadin da zaisa ta ci gaba da dauwama a ƙarƙashin iyalansa ya auku ba ƙaramin murna yake ji ba. "Bilhaƙƙi an maimaita haddar jiya ko?" "Eh na maimaita Malam, na iya ma. In biya maka ka ji?" Ta ƙarasa maganar tana kallonshi da murmushi. "A'a ki biyawa Umminku. Yau ita za ta ƙara miki karatun. Yanzu wanka zan shiga, akwai tafiyar da za muyi da maigidanki da safennan." "Bauchi ko? na manta ya faɗa min jiya. Allah ya kaiku lafiya ya dawo mana da ku lafiya." "Ameen ya Allah. Allah ya miki albarka." "Ameen." Harta kai bakin ƙofar falon za ta fita sai kuma ta koma ciki ta zauna a inda ta tashi. "Malam ko za kuje da ni? Na ji ya ce har da Mummy za ku tafi." "Kina son zuwa ne Bilhaƙƙi?" "Eh ina so. Har ma nayi mishi maganar ya ce in haƙura garin akwai nisa." "Eh da nisa kam." Shiru yayi kamar shi ma zai ce ta haƙura da son zuwan, sai kuma ya ce. "Ki shirya tunda kina son zuwa, zan nemar miki izini a wajensa." Murna kamar me a zuciyarta har ya gaza ɓoyuwa a fuskarta. "Tam! na gode Malam. Allah ya ƙara maka lafiya da nisan kwana." "Ameen." Ya amsa addu'ar shi ma yana dariya. Da idanu ya raka ta har ta fice daga falon. Girgiza kai kawai yayi ya yunkura da Bismillah ya tashi ya nufi banɗaki don yin wanka. A can cikin gidan ita ma cike da ɗoki ta faɗawa Ummee da ita za a je, Malam ya ce ta shirya su tafi tare. Wanka ta faɗa cikin ƙanƙanin lokaci ta fito ta fara shiryawa, tana shirin tana harhaɗa kayan sawarta da duk wani abu da ta san za ta buƙata a cikin kwanaki biyun da za su yi. Ganin har da ita za aje Saudat da Asma'u suka ce suma za su Malam ya ce a'a. Sai dariya da gwalo take musu tana tsokanarsu. Ko da Maheer ya isa gidan ya ganta cikin shiri bai ce mata komai ba, don Malam ya kira shi a waya kafin ya isa yayi mishi maganar. Bai wani so tafiyar da ita ba amma tunda Malam yasa baki ba shi da ta cewa, ko da ta gaishe shi bai nuna mata komai ba ya amsa. A tsaitsaye suka karya sannan suka miƙi hanya bayan sun ja addu'oin da fiyayyen halitta SAW yayi umarnin yi ga duk wani matafiyi. Ita da Mummy suna zaune a kujerun baya na motar, Maheer shi ne direba. Shi kuma Malam yana zaune a kujeran mai zaman banza. Suna barin kaduna an fara miƙar hanya sosai Malam ya kunna radion suna sauraren labarun duniya, jefi-jefi kuma suna hira kan abinda suka ji an taɓo a labarun duniyar. A wani ƙauye suka tsaya yin sallar azahar da la'asar, suka ci abincin da Mummy ta yi musu guzuri sannan suka sake ɗaukar miƙaƙƙiyar hanyar tafiya, sun fara tafiya ba daɗewa wani nannauyan bacci yayi awon gaba da ita. Bai fi saura minti talatin su isa cikin garin Bauchi ba ta fara wani irin mummunan mafarki mai cike da ababen tsoro. "Karki kuskura ki ce za ki shigo cikin garinnan... babu dai-dai da ke a masarauta... Mai wutsiya ki koma inda kika fito ko kuma in hallaka ki..." Yanƙwanannen tsohon mai ɗauke da jajayen idanu da zaƙo-zaƙon haƙora ne yake mata wannan kashedin yana nuna ta da wani dogon sanda. Ya bugi ƙasa da sandar nan take wasu ƙananun halittu masu kama da kwaɗi suka fara fitowa ta ƙarƙashin ƙasa kusa da inda yake tsaye, ita ya nuna musu da sandar hannunshi yana wasu irin surutai nan take suka yi kanta da gudu kamar tarin ƙudaje saboda yawansu suna yi mata feshin wani abu mai kama da dafi. Tsananin tsoro da firgici ya sa ta yanka wani ƙaƙƙarfar ihu ta fara cure jikinta a guri ɗaya tana dunƙulewa haɗe da tattakure ƙafafunta a cikin motar, duk yadda ta so ta buɗe idanunta ta kasa buɗewa. Kamar daga sama ta ji muryar Oga yana mata magana a cikin ƙwaƙwalwar kanta. 'Bibi... Karki shiga wancan garin... ki dawo gare mu... har yanzu muna jiran ki dawo gare mu... matsayinki a cikin ƙungiya yana nan yana jiranki... Ki dawo kafin Garkuwa ya saukar miki da mummunan bala'i a kanki...' Suffar shi ne ya baiyana tsaye a gabanta cikin mummunan shigarsu ta ƙungiyar tsafi yana jifanta da mummunan murmushi. Hannunshi ɗauke da wani ƙaton ƙoƙo da bata san ko miye a ciki ba. ƙananun halittun suna ƙarasawa kusa da ita ya fara watsa musu wani baƙin abu da yake cikin ƙoƙon, duk wanda baƙin abun ya sauka a kan shi sai yayi bindiga ya tarwatse a gurin. "Ku ƙyale ni... na barku har abada... Yanzu ni matar wani ce...ku ƙyale ni na ce..." Ta faɗa cikin ƙaraji da murya mai matuƙar amo da sauti, lokacin ne kuma ta samu nasarar buɗe idanunta gaba ɗaya tana kallon Oga fuskarta na baiyana matsanancin fushi. Wannan tsohon yana ganin Oga ya ɓace daga inda yake tsaye. Wani abin mamaki kuma sai motar ta fara jijjiga tana layi da su a kan titin kamar za ta kifar da su. Gaba ɗayansu sun shiga cikin ɗimuwa da ruɗewa sai salati suke yi da sallallami tare da jan duk wata addu'a da tazo bakinsu. Duk yadda Maheer ya so ya dakatar da motar ya kasa sai da Malam ya fara janyo karatun alƙur'ani mai girma farkon suratul baƙara, duk su biyun sai suka ɗauki karatun da ƙarfi. A hankali motar ta fara rage gudu da hajijiyar da take yi har ya samu damar faka motar a can gefen titi. Ihu ta sake ƙwallawa a karo na biyu ta ƙara wage manyan idanunta da suke fari ƙal babu ko ɗigon baƙi a ciki. Oga take gani zaune a gefenta yana ƙoƙarin zuba mata wani farin abu a jikinta. Cikin fushi ta kai mishi wani mugun shaƙa a wuya da hunnunta duk biyu tana magana da murya mai tsananin amo "Na ce ku ƙyale ni inyi rayuwata ko...? Baza ku barni ba...? Me yasa dole sai da ni a ƙungiyar...?" Wani kakkaifar walƙiya ne ya fito daga idanunta ya daki jikin Oga nan take shi ma ya ɓace. Abinda bata sani ba Mummy ta shaƙe wa wuya domin ita Oga take gani, nan da nan Mummy ta fara jiyo ƙamshin barzahu, nan take ta fara kakari, duk yadda take ta ƙoƙarin ɓamɓare hannun Bilhaƙƙi daga wuyanta ta kasa, wani mugun ƙarfi ne ta ke da shi kamar ta shaƙe ta da rodi haka ta ji hannayenta. Tsakanin Malam da Maheer har rige-rigen zuwa bayan motar suka yi don kai wa Mummy ɗauki kafin ta hallaka ta. Malam ya fara jan Mummy ganin haka sai Maheer ya fara ƙoƙarin ɓamɓare hannayen Bilhaƙƙi a wuyanta. A fusace ta ɗago kai za ta yi magana ƙwayoyin idanunsu yana haɗuwa sai tayi laƙwas, jikinta ya saki, ƙarfin nan da take ji duk ya tafi. Lauuu ta yi za ta zube da sauri ya tare ta ta zube a jikinsa. Malam matarsa ya ja suka koma gaban motar yana ta jera mata sannu, gorar ruwan swan ya ɗauko ya buɗe ya kafa mata a baki. Kaɗan ta sha ta cire goran a bakinta, idanunta jajur, sai haki take yi tana sauke numfashi akai-akai. Inda Allah ya taimake su hanyar babu cunkoson motoci sosai, motoci biyu ne suka tsaya don basu taimakon gaggawa ganin kuma al'amarin yazo da sauƙi sun samu nasarar tsayar da motar ba tare da an samu hatsari ba sai suka yi musu fatan alkhairi da addu'ar kiyaye gaba suka wuce. "Magajin Malam ka kula da matarka a nan. Ni bari in lallaɓa in tuƙa motar mu isa cikin gari. Kafin mu isa gidan sai mu fara zuwa asibiti a duba su ita da Salamatu." Plate ɗin karatun Alƙur'ani ya kunna ya buɗe volume sosai sannan yayi addu'a ya zauna a mazaunin direba ya ja motar suka bar gurin. Tunda ta zube a jikin Maheer bayan wasu daƙiƙu ta fara dawowa cikin hayyacinta. Ƙam ta rirriƙe shi zuciyarta cike da tsoro tana tunanin ababen da ta gaggani su ba a mafarki ba kuma ba a ido biyu ba. A haka dai har Allah yasa suka isa cikin garin Bauchi lafiya. Za su nemi asibiti Mummy ta ce in dai don ita ne su wuce masauta kawai, ta ji sauƙi. Ita ma Bilhaƙƙi ta ce ba ta buƙatar wani likita, ta ji sauƙi gajiya kawai yake damunta. Don haka kai tsaye suka nufi masautar bauchi fadar mai martaba Sarki Abdulfatahi na biyu. ******* ******** Tana hakimce a kishingiɗe tana zuba mulki a tsakiyar bayi da kuyangin da suke mata hidima kawai ta ji ƙirjinta yayi wani mummunan bugawa. Rabon da tayi irin wannan faɗuwar gaban tun shekaru aru-aru da suka gabata, lokacin da Jakadiya ta zo mata da labarin Safiyya amaryar mai martaba tayi ɓatan wata. Masokiya ce mai tsini kamar mashi ta sake taso mata tun daga tsakiyar ƙwaƙwalwarta ta cake ta har zuwa kan babban ɗan yatsar ƙafarta. Da saurin gaske ta runtse idanu saboda zafin jiki da na zuciya, nan wani zazzafan gumi ya fara antayo mata daga duk wani kafan gashi na jikinta, duk da A.C har uku ne suke fidda daddaɗan iska daga ko wace kusurwa na tafkeken falon. Ƙarin hutu da mulki kuma wasu bayi har biyu ne tsaye ƙiƙam a kanta kamar dogarai suna yi mata firfita da mafici irin na Sarakai. Ko da ta yunƙura za ta miƙe zaune sai taji kamar an saka wani nannauyan dutse an danne ta. 'Tauraruwa mai wutsiya...' Kamar walƙiya wannan tunanin ya gilma a duk wani lungu da saƙo na zuciyarta sai kuma ya ɓace ɓat! A tsorace ta fara waige-waige kamar za ta ganta a gabanta, sai kuma ta sauke idanunta a kan ɗaya daga cikin bayin da suke gurfane a gabanta suna bata daɗaɗan labarai don saka ta cikin nishaɗi. "Laraba anyi wasu baƙi yanzu a masaurautar nan ne?" "Baƙi kuma Ranki ya daɗe? Gaskiya ba ni da labarin haka. Sai dai kuma a fita a tattambaya ko wane sassa na gidan nan." "A je ayi hakan. Daga nan a isarwa da Jakadiya Babba saƙon ina son ganinta da gaggawa." "An gama Ranki ya daɗe." Ta tashi da hanzari don cika umarni. Ko da Jakadiya ta isa ta sake tabbatar mata lallai fa babu wasu baƙi da aka yi da magaribar farin nan. "Lafiya kuwa Fulani Taka?" Wani zazzafan huci ta ja ta fesar, ta kalli Jakadiyan a ɗimauce "Me yasa kika tambaye ni haka Jakadiya?" "Allah ya huci zuciyar Fulani ni ganinki nayi duk a ɗimauce kamar wacce ta haɗiyi kunama. Yo ba ma ni ba ai duk wanda ya kalle ki a yanayin da kike ciki yanzu kallo ɗaya zai fahimci kina cikin gaggarumin tashin hankali." Gefe da gefe ta waiga ta tabbatar duk baƙin da ta sallama sun fice daga falon sannan ta sake gwada yunƙurawa ta tashi zaune karo na biyu. Wani abin mamaki gare ta yanzu duk nauyin nan babu lafiya kalau ta zauna. Ta yafito Jakadiyar ta matsa sosai kusa da ita, sai ta fara mata magana cikin raɗa muryarta baiyane da tashin hankali. "Ta iso Jakadiya. Tauraruwa mai wutsiya ta iso. Wallahi na ji isowarta a jikina kamar yadda Na shuri ya tabbatar min zan ji da zarar ta iso. Amma nayi mamaki, rannan da kika ziyarce shi ba kin ce min ya ce zai hallaka ta kafin ta iso nan ba...?" "A'a Ranki ya daɗe mantawa dai kika yi. Ce miki nayi ya ce zayyi duk mai yiwuwa ya dakatar ita kafin ta iso. Idan tayi taurin kai ma zai iya hallaka ta in ya samu dama a kanta. Yo tunda kika ji ta iso kila shi ma tafi ƙarfinsa ne. Yanzu dai sai ki san mai yiwuwa daman tun farko ya sanar da ke wannan yaƙin naki ne ke kaɗai." Shiru suka yi duk su biyun, kowa da irin saƙa da tunanin da yake yi a ransa. Jakadiya ce ta sake katse shirun da cewa "Ni kam Ranki ya daɗe wai tauraruwar nan mutum ce ko aljana?" "Nima bani da masaniyar daga wane jinsin halittu ta fito Jakadiya. In kika bibiya ma dabba ce, dan na kwana biyu ina mafarkin gani a tsakiyar dokar jeje ina tiƙar dambe da wata ƙatuwar zakanya." Ta ƙarasa maganar a sanyaye. Laraba ce ta ƙwanƙwasa ƙofar ta jira aka bata izinin shiga sannan ta shiga ta zube a gaban duk su biyun. "Ranki ya daɗe Raliya ce ta iso, ta ce a sanar miki akwai labari da ɗumi-ɗumi." Jin haka da sauri ta bada umarnin a shigo da ita, daga ita har Jakadiyar fatansu Allah yasa labarin ya shafi zancen da suke son ji na game da Tauraruwa. "Ranki ya daɗe barka da hutawa. Baƙin Fulani sun iso daga kaduna, maza biyu mata biyu. A halin da ake ciki ma har an kaisu masauki suna hutawa..." Wani dogon tsaki da ta ja shi ya gwaɓarwa da Raliyan gwuiyawu. Ta fara magana cikin fushi. "Saboda ke dabba ce wannan ne wani labari mai muhimmanci da har za ki raɗa mishi da ɗumi-ɗumi? maza ki koma bakin aikinki karki sake zuwar min da banzan labari irin wannan." "Tuba nake Ranki ya daɗe, godiya nake. Allah ya huci zuciyarki." A sace ta fice daga falon cikin sauri tana haɗa hanya. Jakadiya ta buɗe baki za tayi magana da sauri ta ɗaga mata hannu alamar ta dakata. "Jakadiya bana son jin komai daga gare ki. Je ki sai na neme ki." BILHAƘƘI A fakaice ta kyaɓe baki, alamun ko a jikinta. Ciki-ciki ta yi magana. "Shi ke nan! Allah ya huci zuciyarki mai babban ɗaki ta gobe a masaurautar Bauchi, ki huta lafiya." "Jakadiya?" Ta kira sunanta a lokacin har ta kai bakin ƙofa za ta fita. Waiwayowa kawai ta yi ba tare da ta dawo ba ta amsa kiran "Na'am Ranki ya daɗe." "A nema min ison ganawa da Mai martaba a gurin mai Soron baƙi. Yanzu!" "To Ranki ya daɗe. Angama!" Tana hanyar zuwa gurin mai soron baƙi take dariya a zuciyarta. 'Lallai al'amarin mai wutsiya ba ƙaramin girgiza Sarauniya yayi ba. Da da ne yadda ta amsa kiran nan daga ƙofa kuma ta tsaya ƙiƙam a gurin bata koma ta zube a gabanta ba ƙaramin masifa za ta sha akan hakan ba. A hakan ma don dai Jakadiyar ce da a ɗaya daga cikin bayi ne tayi hakan sai tasa an hukunta ta. A ƙalla ta karɓi hukuncin zafafan bulalai talatin. Amsa kira daga tsaye ba tare da zubewa a ƙasa ba babban alama ce ta raini da fitsara ga duk wanda/wacce aka yiwa a Masautar.' Tana wannan tunanin har ta ƙarasa ɓangaren Mai soron baƙi da yake kusa da ɓangaren Mai martaba. Ƙara shiga cikin nutsuwarta tayi bayan ta nemi iso a ɓangaren an yi mata umarnin shiga. Tana shiga ta zube a gabanta cike da ladabi ta fara zuba mata kirari. Ita kuwa Mai soron baƙi babbar mace hakima tana zaune ta mimmiƙe ƙafafunta aka lallausan kafet ɗin da ya malaye tsakar ɗakin tana ta sakin murmushi, kanta sai ƙara kumbura yake yi da jin irin kirari da yabon da Jakadiya take jera mata. "Ranki ya daɗe. Barka da dare, sannu da hutawa. Allah ya ja zamanin tsani kuma ja gaba wajen neman izinin ganin Takawa. Sai kin so ake ganinshi idan baki so ba duk masarautar nan babu wanda ya isa ya ga Takawa. Allah ya ƙara wa Takawa lafiya da nisan kwana." "Ameen ya Rahmanu. Jakadiya? Me ke tafe da ke a daren nan?" Ta jefa mata tambayar har lokacin murmushi bai bar kan fuskarta ba. "Ranki ya daɗe Fulani Taka ce ta turo ni in faɗa miki tana neman iso za ta gana da Mai martaba akan wani muhimmin al'amari yanzu..." "A sanar da ita bazai yiwu ba Jakadiya. Yau ba ita ce da Mai martaba ba, a bayan haka ma Takawa yana da manyan baƙin da zai gana da su a darennan daga Birnin kaduna." Ta katse ta tun kafin ta ƙarasa aje numfashin maganarta. A sace Jakadiya ta ɗaga kai ta kalle ta sai taga wannan murmushin ya ɓace daga fuskarta, fuskarta ɗaure tamau. Cike da mamaki tayi mata sallama ta fice daga gurinta ta nufi gurin Sarauniya don isar mata da saƙo, tunani take ta yi a zuciyarta. 'Ta rasa dalilin da yasa tsakanin Mai soron baƙi da Fulani Taka sam basa ga maciji. Abinda ta lura da shi kamar duk sun zamewa juna dole ne, ga ko wannensu sun zama ƙadangarun bakin tulu. Ita Sarauniya Safara'u uwargidan Sarki ce. Ita kuwa Mai Soron baƙi Inna Laminde ƙanwar gyatumar Mai martaba ce. Tana tsananin ƙaunar Takawa tana ƙaunar duk abinda yake so, ita da kanta ta nemi ya bata wannan muƙamin yadda duk wani abu da zai isa gurin Takawa sai ya fara isa gurinta ta tantance tsaftarsa da halaccinsa saboda gudun a kai mishi abinda zai cutar da shi. Hatta matansa biyu sai sun bi ta gurinta suke samun isa gare shi ko da kuwa ranar girkin mace ne. Ta matsa lamba sosai a masarautar, ta tare gaba ta tare baya. Jajurtacciya ce kuma tsayayyiyar mace da sam bata ɗaukar wargi ko raini ga kowa a masarautar. Wani abin mamaki a yanzu Mai Soron baƙi tana tsananin ƙaunar Safiyya da duk abinda ya shafe ta, saɓanin da da tafi ƙaunar Safara'u akan Safiyya.' "Ina ga akwai wani ƙwaƙƙwaran dalili da ya juyar da akalar wannan ƙauna da ƙiyayyar, ko ma menene dai ma ji ma gani." Tayi maganar a fili da murya ƙasa-ƙasa tana murmushi. A hanya ta ci karo da Sarauniya Safiyya tare da baƙinta biyu (Mummy da Bilhaƙƙi) bayi da kuyangi suna take musu baya. Da alamun kai tsaye ɓangaren gurin Mai martaba suka nufa. Har ƙasa ta zube cike da ladabi da girmamawa ta fara kwasar gaisuwa ga Sarauniya. A mutunce ta amsa mata suka wuce zuwa inda suka nufa, sai da suka ɓacewa ganinta sannan ta daina kallonsu ta nufi ɓangaren Fulani Taka cikin sauri kamar za ta kifa. "Inji ita Mai soron baƙin ne ta ce a faɗa min yau ba kwana na bane?" Ta sake maimaita tambayar cikin tsananin fushi. "Ƙwarai kuwa Ranki ya daɗe. Ta ce yana da manyan baƙi kuma ni da idanuna naga Fulani da baƙinta mata biyu sun nufi ɓangarensa. Kinga ke nan su ne manyan baƙin." Ƙwafa tayi, ta cije gefen bakinta na dama alamun mugunta, ta ci gaba da ƙanƙance idanu cike da masifa. "Safiyya da wasu banzayen baƙinta har sun isa su fini muƙamin ganawa da Takawa?" "E to ga zahiri kin gani? ai ke kuma kin saka ƙafa a jarka tunda kika yi saken da mai wutsiya ta shigo masautar nan." Jakadiya ta faɗa ƙasa-ƙasa yadda baza ta abinda ta ce ba. "Magana kike Jakadiya?" "A'a cewa nayi Allah ya huci zuciyarki. Amma fa ke kika yi saken da Mai soron baƙi take kawo miki wargi." "Gaskiya kika faɗa Jakadiya. Bari inje da kaina in gani idan ta isa ta hana ni shiga gurin Takawa in gani." Ta miƙe a fusace za ta fita da sauri Jakadiya ta dakatar da ita. Ta rage murya ƙasa-ƙasa ta ce "Ranki ya daɗe a halin da ake ciki faɗa ko tayar da jijiyar wuya ba naki bane. Ki kawo sulallan gwal a kaita gurin Na shuri ya cika mata aiki kawai." "Shi kenan Jakadiya. Ya kamata saisaita mata hankali tabbas. Ki faɗa mishi a ganar da ita kuskurenta ta yadda gobe baza ta iya ɗaga idanu ta kalle ni ba balle har ta nemi musawa umarni na. Raini yana neman ya fara shiga tsakanina da ita. Amma abinda bata sani ba ni Safara'u wallahi na sha gabanta, ni ce fa uwar sarkin gobe a masarautar nan. Jakadiya ko akwai wani ɗan da zai gaji Sarki ne bayan Yarima Muzaffar?" "Ina..! Sam babu!! Wane mutum?!!! Yo ko akwai ma ai saidai ya biyo baya a kira shi ƙanin Mai martaba sarki Muzaffar..." "Ba ma zan taɓa bari a samu wani ƙani a masarautar nan ba Jakadiya. Muzaffar ɗin dai shi ne. Duk wanda ya ce ba haka ba kuma mu zuba mu gani. Shege ka fasa tsakanina da ko waye" Jakadiya dai ficewa tayi zuciyarta cike da matsanancin farin ciki. Ta fara gajiya da ganin baƙin hadarin da har yau ya kasa ɓallewa da ruwa, a wannan karon babu wani Na shuri da za ta kaiwa sunan Mai soron baƙi. Ita za ta maye gurbin Na shurin ta hanyar adana sulallan gwala-gwalanta. Yo miye a ciki? ta fara gajiya ne da gafara san da har yau ƙahonshi ya ƙi ya baiyana. ****** ****** Hannu ya miƙa a hankali cikin kejin tattabarun bakinshi cike da addu'o'i ya damƙo fuka-fukanta. Wani tattausan murmushi ne ya suɓuce masa, bakinsa ɗauke da kyawawan kalamai na godiya ga Allah da ya bashi nasarar kama ta. A yau dai bayan shekaru masu yawa da yayi yana yunƙurin kama baƙuwar tattabaran tana guduwa yau dai ya samu nasarar damƙe ta. Can gefe guda ya samu guri ya zauna a kan benci yana ƙare mata kallo. Duk yawan kiwon tattabarunshi bai taɓa ganin kalar irinta ba, ita ta fita daban a komai ma nata da sauran tattabaru. Shi yasa tayi ta ɗaukar hankalinshi, duk lokacin da yayi yunƙurin kama ta kuma sai ya neme ta sama ko ƙasa ya rasa a cikin tattabarunshi. Zazzaro idanu yayi cike da mamaki lokacin da ya buɗe gashin kanta, wani baƙin mayani ɗan ƙanƙani mai ɗauke da wani irin jagwalgwalon rubutu da jan alƙalami aka shimfiɗa a kanta. Sannan aka kawo wasu ƙananun allurai aka caccaka guri guri a jikin mayanin. Alluran za su kai guda goma. "La shakka wannan tattabara da gani mummunan sihiri aka yi mata." Yayi maganar a fili tare da ci gaba da bubbuɗe gashin jikinta, a hammatanta na hagu da dama ya ga allurai bibbiyu, sai kuma a gadon bayanta ya sake ganin alurai huɗu. Abinda yasa ya ƙara tabbatarwa da duk wanda yayi wannan sihirin babban matsafi ne ganin yadda aka shisshigar da alluran cikin fatar jikinta da tsananin ƙarfin tsafi ba tare da an aske gashin jikinta ba. Azabar zamansu a jikinta kuma baisa ta hallaka ba. "Innah zo ki gani." Ya ƙwallawa wata dattijuwa da take zaune can nesa da shi a kan tabarma tana murza zaren kaɗi. "Gidalle lafiya?" Ta tambaye shi tana zaune a inda take. Tattabarar ya ɗaga sama yadda za ta iya ganinta. "Kinga yau dai Allah ya bani sa'ar kama ta. Bayan tsawon shekaru huɗu da tayi tana shawagi da ɓacewa a cikin tantabarun gidannan." Da sauri ta miƙe ta nufo gurinshi dan ganin tattabarar ya dakatar da ita "Ɗan taho min da Jakar Baffa na magunguna, da kuma garwashi a cikin kasko." Ƙasa da mintuna uku ta gama aje duk abinda yake buƙata a gabanshi. Wani garin magani ya umarci Inna ta ɗauko a cikin jakar ta kwance mishi ya damƙi kaɗan ya watsa da ƙarfi a cikin rushin wutar. Nan da nan wani baƙin hayaƙi ya turnuƙe gurin har basa iya ganin junansu. Kan tattabar ya duƙar yadda za ta shaƙi hayaƙin sosai tsawon minti biyu, lokacin hayaƙin ya fara rage wa da sauri ya fara zazzare alluran da duk wani abu mai baiyana alamun na sihiri ne bakinshi ɗauke da addu'o'i, duk abinda ya cire kai tsaye a wutan yake hurgawa har ya gama zare komai daga jikinta. Wani irin kuka mai ƙarfi tayi kamar ba tattabara ba ta yunƙura za ta tashi daga hannunsa ya ƙara damƙe ta da kyau. Garin maganin ya umarci Inna ta jiƙa mishi kaɗan ya buɗe bakinta da ƙarfi suka ɗura mata maganin sannan ya saketa ta tashi sama. Ya zaci tafiya za ta yi kamar yadda ta saba sai yaga ta tsaya akan katangar gidan tana ƙure shi da kallo. Maganin ya damƙa ya ƙara watsawa a wuta, saidai saɓanin ɗazu da baƙin hayaƙi ya tashi yanzu wani farin hayaƙi ne ya taso ya lulluɓe gurin, sai daga baya kuma a hankali ya washe komai ya koma daidai. "Alhamdulillah !" Ya faɗa yana kallon Inna da dariya. "Sannu da ƙoƙari Gidalle. Wato dalilin wannan aikin ne yasa tsawon shekaru tana bibiyarka sai yau Allah yasa lokacin warware duk wani ƙulli daga jikinta yayi." "Ƙwarai kuwa Inna. Da yawan mutane yanzu sam tsoron Allah yayi ƙaranci a zukatanmu. An maida tsafe-tsafe ba komai ba. Allah ya tsare mana zuciyoyinmu. Da zaki ji irin ƙaƙƙarfar sihirin da aka haɗa da Baiwar Allahn nan za kiyi mamaki." Ya ƙarasa maganar yana nuna tattabarar da yatsarsa manuniya. "Wannan rayuwa sai a hankali. Allah ka iya mana da iyawarka." "Ameen ba don halayenmu ba." Kaskon wutan ta ɗauke daga gabanshi ta mayar cikin kicin. Ta koma kan tabarma ta ci gaba da kaɗin da take yi. Shi kuma Gidalle kayayyakin jakar ya fara cirowa ɗaya-ɗaya bayan yana ajiyewa a gefensa, da alamun wani maganin yake nema. ******** ******* RUGAN BAFFA YALLERU A cikin wani ɗan madaidaicin bukka da yake cikin rugar. Wani matashin dattijo ne kwance a kan wata yaloluwar tabarma. Yasa hannuwansa biyu ya tallabe kansa, da farko ya ƙurawa silin idanu ne jikinsa a matuƙar sanyaye kamar yana karantar wani abu. Daga baya kuma sai ya fara juye-juye yana rirriƙe kansa, domin jin ko ina a jikinsa yake yi kamar ana caccaka mishi kibiya. Kanshi kuwa kamar ana sarawa da guduma. A daidai wannan lokacin wani yaron fulani ya shiga cikin bukkar hannunshi ɗauke da ƙoƙon da aka shaƙe da damammiyar fura da nono. Da sauri ya koma ya sanar da Baffansa ganin halin da na kwancen yake ciki. Ba tare da wani ɓata lokaci ba kuwa ya biyo shi da sauri suka koma bukkar. Suna shiga shi kuma cikin zafin nama ya miƙe tsaye, har lokacin bai sake kansa ba, idanunsa sun kaɗa sunyi jazur saboda azabar da yake ji a jikinsa. A zafafe ya nufi hanyar fita daga bukkar da sauri dattijon ya riƙe shi yana tambayarshi lafiya? Ya fara kici-kicin ƙwacewa sai kuma ya ƙwalla ihu jikinsa ya sake gaba ɗaya a jikin dattijon da yake riƙe da shi. "Baffah kamar ya mutu ko?" "Bai mutu ba Bello. Yi sauri gurin Yafendo ka ce ta baka ruwa mai sanyi da magungunan Tukurere ka kawo min yanzunnan." Hankalinshi a tashe ya kwantar da shi a kan tabarmar yana mishi firfita. Sai tattaɓa saitin zuciyarsa yake yi da duk inda ya kamata ya taɓa don jin yana raye ko ya mutu? Manyan samari biyu ne suka biyo bayan Bello suna riƙe da magungunan da ruwan sanyi a kwanon sha na roba mai murfi. Ba tare da duba yawa ko sanyin ruwan ba yana amsa a hannunsu gaba ɗaya ya sheƙawa wanda ya kira Tukurere a jiki. Nan take ya ja wani nannauyan ajiyar zuciya alamun ya farfaɗo. Ko kafin ya buɗe ido ya dawo hayyacinshi sun buɗe bakinshi sun ɗura mishi wani magani da yake jiƙe a cikin gora. Idanunshi a rufe wani ƙaƙƙarfan amai ya taho mishi da sauri Baffa ya tallabe kanshi ya karkata gefe ɗaya yayi ta kwara aman mai haɗe da wasu baƙaƙen gudaji mai kama da jini a ciki. Ko kafin ya gama aman ya galabaita da ƙyar suka samu aman ya tsaya. Ruwa mai rangwamen zafi aka kai bayan bukka Baffa ya umarci Matasan nan biyu suka taimaka mishi yayi wanka ya canza kaya. Daga haka kuma sai wani nannauyan barci ya kwashe shi. Bai farka ba sai bayan sallar azahar, har lokacin su Baffa suna zagaye da shi, ganin ya farka yasa duk suka matsa jikinsa suna jera mishi sannu da tambayar yanayin jikinshi. "Tukurere ka tashi? Sannu! ya jikin naka?" Wawwaigawa shi ma ya fara yi don ganin wanene suke kira Tukurere sai yaga shi ɗin dai suke kallo. Da mamaki a fuskarsa ya kalli tsohon "Ni ? Sunana Mustapha. Babana sunanshi Abdulfah! Babana ne sarkin garin Bauchi. Ina ne nan? ku kuma su waye?" BILHAƘƘI Da mamaki matasan suka bi shi da kallo. Duk tunaninsu ɗaya 'Ko dai ya samu taɓin hankali ne daga farkawarsa?" Shi kuwa Baffa sai dariya yake yi yana godewa Allah. "Ma sha Allahu! Yau dai Allah yayi Tukurere tunaninka ya dawo bayan tsawon shekaru goma sha tara da kayi tsakanin mare hankali da mai hankali. Kwantar da hankalinka, mu ba masu cutarwa bane a gare ka. Muna nufinka da alkhairi ne a ko wane lokaci. Yanzu dai kafin inyi maka bayanin komai bari a kawo maka abinci ka ci." Da idanu ya raka su yana ta jujjuya maganganun tsohon a ransa har suka fice daga ɗakin. 'Shi Mustapha ya ga ta kansa! shi ne yayi shekaru goma sha tara tsakanin hauka da hankali?' Babu jimawa dattijon ya koma cikin bukkar matasan suna biye da shi. Tuwon dawa ne mai zafi-zafi da alamun ba a daɗe da kwashewa ba da miyar busassar kuɓewa. A hannun Baffa kuma kofin ruwa ne. Ruwan ya karɓa ya fita bakin bukkar don kuskure baki da wanke hannu. Nan ya tsaya yana ƙarewa rugar kallo. Bukkoki tsilli tsilli ne daga inda yake tsaye, sai can nesa ya hangi wasu tarin bukko ki, a gefe guda kuma akwai tarin dabbobi. "Tukurere me kake yi? kazo ka ci tuwon mana kada ya huce." Ya ji muryar Baffa daga cikin ɗakin yana mishi magana, wani ƙunci ne ya tsunguli zuciyarsa. 'Tukurere' Ya maimaita sunan a ransa cike da ƙyamar sunan, jin sunan yake yi yana neman saka shi amai. Da sauri ya wanke bakin ya koma cikin bukkar. Tunda ya yanki lomar farko na tuwon ya dangwali miya ya kai baki bai sake marmarin ci ba. Tun basu fahimta ba har suka gane bazai iya ci ba. Ko kaɗan hakan bai ƙona zuciyarsu ba "Ko a kawo maka fura da nono?" Da sauri ya ɗaga kai alamar eh. Nan da nan aka amso mishi gurin Yafendo uwargidan Baffah. Ya sha sosai kaɗan ya rage ya ajiye ƙwaryar ya ce ya ƙoshi. Tsohon ya ƙara kallonsa da tattausan murmushi a fuskarsa. "Kana buƙatar ƙara hutawa ne kafin ka ba mu tarihinka ko za ka iya ba mu yanzu?" A nutse ya buɗe bakinsa ya fara warware musu labarin tarihin rayuwarsa, tun daga kan nasabarsa, zuwa yadda ya bar masarautarsu a ranar ake murna da bikin cikarsa shekaru goma sha biyar. Da yadda yaita gararambar rayuwa da buga-buga a sassan jihohi daban-daban har Allah ya aje shi a Jihar kaduna, ƙaramar hukumar kajuru, a ƙauyen kasuwar magani. Da yake gari ne mai arzikin noma da kasuwanci sai Allah ya haɗa shi da abokai na gari, iyayensu suka riƙe shi kamar su suka haife shi ba tare da tuhumar waye shi ko kuma daga ina yake ba. Babbar kasuwar ƙauyen da take ci duk ranar alhamis a can ya haɗu da Rebecca tana kai tallen dafaffiyar doya da kunun zaƙi. Shi kuma a lokacin baro yake turawa, saboda tsaftarta da nutsuwarta yasa suke siyan abinci a gurinta daga bisani kamar wasa Allah ya sarƙa soyayya mai tsanani a tsakanin zuciyoyinsu. Babban abinda ke damun ƙauyen kasuwar magani yawan rikici a tsakanin arna da musulman garin, duk wadataccen zaman lafiyar da yake tsakaninsu akwai mummunan ƙabilanci a zukatan cristian ɗin ƙauyen. A ko wane lokaci idan rikici ya tashi yunƙurinsu su kori duk wani bahaushe da yake ƙauyen da ƙananun ƙauyukan da ke kusa dasu, irinsu Kallah, Rimau, Gefe, Dutsen gayya, da sauran ƙauyaku. Wata rana afujajan wasu ƴan mata biyu mazauna kasuwar magani da suke soyayya da yaran hausawa abokan Mustapha suka je masallaci da cewa za su musulunta. Saboda samarinsu sun yi alkawarin za su aure su matuƙar suka musulunta. Wannan shi ne abinda ya tada mummunan rikici a garin bayan an musuluntar da su. Da yake ko wani lokaci musulunci sama yake da kafurci kuma Allah yayi alƙawarin zai ka re addininshi a faɗin duniya musulmai ne suka yi nasara, cristian sun yi asarar rayuka sosai kuma basu ci nasarar dawo da ƴaƴansu ba. Da wannan damar Mustapha yayi amfani ya gudu da Rebeccah Cikin kaduna aka shiga da su gidan Musuluntattu ita da sauran ƴanmatan. Wani Alhaji mai yawan taimakon addini ya ce idan aurensu ya tashi a faɗa mishi zai yi musu kayan ɗaki na kece raini. Wata uku bayan rikicin aka ɗaura musu aure a masallacin musabaƙa da ke Kinkinau. Sauran samari biyun suka ɗauki matansu da suka musulunta ɗaya ya zauna a garin kujama da ke ƙaramar hukumar Chikun, ɗayan ya koma kasuwar magani da zama, shi kuwa Mustapha da matarsa Rebeccah da har lokacin bata mususulunta ba nan cikin garin kaduna ya zauna. Hayan ɗaki mai sauƙi ya nema a tudun wada, sai ya shiga kasuwar bacci gurin abokansa ƴan gwanjo da ya saba da su tun a kasuwar magani ya basu ƴan kuɗaɗen hannunshi suka tallafa mishi ya fara buɗe dilar gwanjo na kayan yara. Da yake yana da nasibi a harkar nan da nan ya fara samun ƴan kuɗaɗe suka ci gaba da rayuwarsu cikin rufin asiri shi da matarsa Rebeccah. Duk bayan sati biyu yana leƙawa kasuwar magani ya gaisa da abokan arziki ya kaiwa waɗanda suka riƙe shi a matsayin ɗansu ihsani. Bai je garin da Rebeccah ba sai da suka shekara ɗaya da rabi da yin aure, lokacin tana ɗauke da tsohon cikin haihuwa yau ko gobe. A lokacin kuma gari yayi lafiya kamar ba a yi wani rikici ba, da wannan ƙwaƙƙwaran dalilin ya sa yaje da ita garin don ta gaida iyayenta. A tunaninshi komai ya wuce, kuma tunda bata musulunta ba zai sa su rungumeta su rungumeshi a matsayin suruki ba tare da ƙyama ko tsangwama ba. Da suka kwana biyu a Kasuwan magani ya ce su je ƙauyenta ta ce a'a tana jin tsoro. Yayi yayi ta ce ita dai baza ta ba, sai da yayi fushi sosai sannan ta amince suka tafi ƙauyen tana cike da taraddadi. Wani tsohon ɗan ƙaramin gida da yake can ta bayan gari ginin ƙasa da ta gada a gurin Mahaifiyarta kafin ta mutu a nan suka sauka. Sai da suka huta sosai sannan ta je da mijinta suka gaida Babanta da ɗanuwanta. Yadda suka karɓe ta a wulaƙance ne ya ƙara sanyayar mata da jiki, har suka koma gidan da suka sauka tana mita da ƙorafin ita ba dan shi ba wallahi baza ta je garin ba. Yana murmushi yake tausarta da rarrashinta, basu daɗe da zama ba gaf da magriba sai ga ɗan aike wai Mustapha ya je. Hankalinta ne ya ƙara ɗugunzuma, cikin rashin nutsuwa ta ce kar ya je, dan tana tunanin akwai wani abu na mugunta da ɗan'uwanta Zidane da mahaifinta suke ƙullawa. Bai saurareta ba ya fice ya bi bayan ɗan aiken har zuwa ɓoyayyen gurin da Zidane da abokansa suke maƙale. Tashin hankalin fitarshi da tunanin abinda ka iya zuwa ya dawo yasa naƙuda ya taso mata gadan-gadan bayan fitarsa. Cikin hikima ta Ubangiji sai ya dube ta ya kawo mata haihuwar da matuƙar sauƙi, da yake a gidan da suke haya a kaduna su uku ne, ita, wata tsohuwar ma'aikaciyar unguwar zoma, sai wata matashiyar mata mai ƴaƴa biyu. Tsohuwar ta sha kwatanta mata yadda za ta gyara kanta idan ta haihu babu kowa a kusa da ita, wannan ɗayar matar ma da ta ƙara haihuwa kusan komai a gabanta aka yi ta ga yadda ake yanke cibi da goge jikin jariri. Nan da nan ta yanke cibi ta goge jikin jaririyar ta naɗe da jallabiya, ta gyara jikinta ta tsaya jiran ganin da yanayin da Mustapha zai koma gidan. Tsawon awa biyu da rabi suka ɓoye shi a gurin, sai da dare ya fara shiga sosai babu wani musayar ra'ayi a tsakani Zidane ya soka mishi wata kakkaifar wuƙa a cikinshi, suka sake shi bayan sun ce mishi idan zai iya ya koma gida za su zo har gidan su haɗa shi da tsinanniyar matarshi su ƙona su da ransu. Idan kuma ya mutu a hanya za su kaiwa Rebeccah gawarshi su ƙona shi tare da ita. (Idan baku manta ba daga inda ya koma gida a wahalce muka fara labarin littafin) Mustapha ya gyara zama ya ci gaba da cewa "Babban abinda yake bani mamaki a rayuwata tun bayan barowata masautarmu sam na kasa faɗawa kowa daga inda na fito. Kuma da farko-farkon barowata duk sadda na fara tunanin ya kamata in koma gida sai inji wani masifaffen ciwon kai da tsananin son in sake lulawa can cikin duniya. Da wannan dalilin yasa na daina tunanin komawa masautarmu. Lokacin da na tarar Rebecca ta haihu ne naji a raina ko ni ban koma gida ba ya kamata gudan jinina ta san asalin Ubanta. Musuluntar matata Rebeccah a wannan daren shi ne abinda ya ƙara tabbatar min lallai zan mutu da farin-ciki. Da na yi yunƙurin faɗawa matata daga inda nake sai naji kamar an naɗe min harshe da wani mugun ƙulli, dole sai masarautar Maru ta jihar zamfara na iya faɗi saboda mahaifiyata tana da danganta da can masarautar. A wahalce na samu na yiwa ƴata alamar da idan an gani a masarautarmu za a yadda ita ɗin gudan jinin Mustapha ne. Daga sama-sama na ke jin abinda yake faruwa har zuwa lokacin da na fice a hayyacina gaba ɗaya ban ƙara sanin me yake faruwa ba." Ya tuɓe rigarsa ya nuna musu ta shi alamar a ƙirji sak irin wacce yayi wa Bilhaƙƙi. Daga nan yayi shiru alamun ya gama basu labarin. Ko da Baffa Yalleru ya fahimci ya gama basu labarinsa mai cike da al'ajabi sai ya gyara zama shi kuma ya ci gaba da cewa "To kaga a daidai wannan lokacin da tunaninka ya ɗauke ka suma? A daidai lokacin Allah ya nufi ɗan'uwa Ilyassa'u ya kai maka ɗauki da taimakon gaggawa. Mutum ne da tun kafin a haifeshi aljannu suka shafe shi a cikin mahaifiyarmu. A bayan haihuwarsa kuma bayan tsananin wahalar da Innarmu da suka yi gurin nema mishi magani sai kwatsam suka buɗe mishi idanu yana ganin abubuwa da yawa da mu mutane ba ma gani. Tun yana ɗan shekaru ashirin ya bar gida ya koma bin jeji daga wannan zuwa wancan, rayuwarsa a cikin daji yake gudanar da ita. Sam ba ya kaunar zaman cikin gari, tun mahaifiyarmu tana ƙorafi akan ya dawo gida har ta haƙura ta ƙyale shi. Wata rana a hanyarsa ta wucewa ne ya ganka kwance a cikin wani ƙaramin gida, a waje kuma ga wasu matasa nan suna ta watsawa gidan kalanzir da alamun ƙona gidan za suyi. Ko da ya tattaɓa ka ya fahimci mummunan halin da kake ciki ba tare da tunanin komai ba ya ɗauke ka ɓat kuka ɓace daga gurin. Shi ya fara maka maganin sukar wuƙan da yake cikinka, daga baya kuma ya kawo min kai, ya ja min kunne akan lallai duk runtsi in kasance tare da kai. Ya faɗa min mummunan sammu da jifa ne a jikinka amma in Allah ya yarda lokacin warware asirin ya kusa zuwa. Haka na ci gaba da yi maka magani ina kula da kai ni da iyalina har ka warke. Ko da ka warke kuma sai ka zama wani irin mutum ba mai hankali ba ba mahaukaci ba, ba ruwanka da kowa. A haka ka rayu har zuwa yau da ka dawo haiyacinka. Kusan shekaru goma sha tara ke nan kana tare da mu." Tunanin irin gararamba da yawon da yayi guri-guri tun yana da ƙananun shekaru har zuwa yau da ya fara manyanta, tunanin a wane hali yanzu iyayensa da ƴan'uwansa suke ciki? tunanin a wane hali matarsa da tilon ƴarsa suke ciki? Waɗannan tunane-tunanen su suka haɗu suka dagula duniyar nutsuwa da ɗan guntun walwalarsa. Da ya rasa me zaiyi kawai sai ya fashe da wani ƙaƙƙarfar kuka kamar ƙaramin yaro. Basu dakatar da shi ba, sun san ya cancanta yayi kukan ko dan ya rage damuwar da ke cin zuciyarsa. Matasan nan da suke masu shekaru ashirin da ƴaƴaye su kansu girma suka yi suka ganshi a rugar, basu taɓa tsammanin babban al'amari ne haka a tattare da shi ba. Sai sharar ƙwallah suke yi cike da tausayinsa. Baffah ne ya dafa kafaɗunsa ya ce "Tukurere kukan ya isa haka. A ganina godiya ya kamata ka yi wa Allah da ya sa ka dawo cikin hankalinka, kuma har yanzu kana raye. Ka ga waɗannan manyan damarmaki ne da zasu sa ka sake haɗuwa da duk ababen da ka rasa a rayuwarka. In Allah ya yarda. Ka huta zuwa gobe, ayi maka aski a yanke maka akaifa, ka samu nutsuwa jibi idan mai duka ya kaimu sai mu ɗauki hanyar tafiya can garin naku. Domin daga nan tafiya ce mai tsawo da tsananin nisa." ******** ******* Ba tare da tsoron tsalawar da dare yayi ba ta ci gaba da zagaye duk wani lungu da saƙo na cikin babban gidan sarautar. Sai mamaki take yi ganin gida gari guda amma saboda tsananin mulki a ce duk na Sarki guda ɗaya ne. Duk daɗewarta tana bin lungu da saƙo da duk wata hanya da ta gani ba tare da sanin inda za a ɓulle da ita ba har yanzu bata gama zagaye cikin gidan ba. Haske tar ko ina a cikin gidan, da yake daren ya tsala sosai har lokacin bata haɗu da kowa ba. Wani irin kunne ne da ita kamar na maciji, tana da tsananin ƙarfin jin sautin magana matuƙar dai ab buɗe baki an furta. Daga can nesa take jiyo muryar wata mace tana magana cikin kuka. "Yarima dan girman Allah dan darajar iyayenka ka yi haƙuri yau ka ɗaga min ƙafa. Wallahi da gaske nake yi ina al'ada ka gani ma." Can kuma sai ta ji muryar namiji cikin fushi yana cewa "Babu ruwana da al'adarki. Wallahi Murja idan kika bari raina ya gama ɓaci sai na yi biji-biji da ke a cikin ɗakin nan sannan inyi abinda naga dama da ke. Ke da kike wulaƙantacciyar baiwa har kin isa ince ga abinda zanyi ki musa min?" Hankalinta a tashe da gaggawa ta ƙarasa inda take jiyo tashin sautin muryoyin, ganin babbar ƙofar a datse yasa ta yi turus a tsaye. A sanyaye ta murɗa hannun ƙofar ba tare da tunanin a buɗe take ba kawai sai ta ga ƙofar ta buɗe. Ta sauke ajiyar zuciya tare da godewa Allah ta cusa kanta ciki da sauri dan ganin abinda yake faruwa, ba su a tafkeken falon don haka kai tsaye ta cusa kai ɗaya daga cikin ɗakunan da ta tabbatar daga ciki muryoyin suke fitowa. Banka ƙofar da tayi da ƙarfi yasa duk suka ɗaga ido suna kallonta, Shi yana tsaye daga shi sai gajeren wando. Murja kuma tana tsugunne a gabanshi hannunta riƙe da tsumman ƙunzugunta a hannu tana kuka, ganin wacce ta shiga yasa a tsorace ta maida tsummar bayanta ta ɓoye. Shi kuwa ɗaure fuska yayi tamau yana kallonta a wulaƙance. "Ke kuma wace banzar ce? kinsan ina ne nan? kinsan ko ni waye da za ki shigo ɓangare na gaba gaɗi ba tare da neman izini ba?" Bata saurare shi ba kai tsaye ta nufi gurin Murja da niyyar ta ɗaga ta tsaye. Ko da ya fahimci abinda take da niyyar yi hannu ya kai da nufin ya fincikota ya watsar da sauri ta kauce ya kama iska. Kafin ya dawo cikin nutsuwarshi ta ɗaga hannu ta zabga mishi wani ƙaƙƙarfar mari a kuncinshi na hagu, kafin ya shanye zafin ya girgije ta ƙara mishi wani marin a ɓangaren dama. Tsananin tsoro da ruɗanin ganin mara-maran da aka saukewa Yarima dukda girman matsayinsa yasa Murja ta ƙara fashewa da kuka, zuciyarta cike da tunanin ita kuma wannan yarinyar wa ce mai girman matsayin ne har ta iya marin Yarima? "Yi haƙuri. Sam ba ni da nufin cutar da ke. faɗa min me yake faruwa kin ji?" Ta tambaye ta a tausashe, bayan ta saka hannuwanta biyu ta miƙar da ita tsaye. "Dan Allah ki yi hakuri ki yi min rai. Wallahi babu ruwana, shi ne yake takura min in zo turakarsa. Yau kuma na faɗa mishi ba ni da lafiya amma ya ƙi yarda..." Zazzafan marin da Yarima Muzaffar ya sauke mata a kunci yasa ta hantsila baya saboda azaba, ta sake fashewa da kuka tana yi tana toshe bakinta dan kar a ji daga nesa. Yayi wani mummunar dariya yana kallonta sama da ƙasa, miyau ya dalalo mishi a baki yasa hannu ya goge. Ƙofar ɗakin ya maida ya datse har da yana saka key. "Ni kika yi kuskuren mari ko? Wallahi sai na yagalgala ki a darennan inga uban da ya tsaya miki a garinnan. Yau za ki san ko wanene Yarima Muzaffar mai jiran gado..." Cikin tsananin fushi da ƙyama ta nuna shi da yatsarta manuniya ta ce! "Au! Akuya kai ne Yarima mai jiran gado a masarautarnan? Madallah! Ni kuma ina yi maka albishir ɗin mummunan tonuwar asirin abinda kake aikatawa akan bayin gidannan. Kai daga yau ma matukar ina raye baza ka sake yunƙurin kusantar wata yarinya a rayuwarka ba. Za mu gani, sai ka cigaba da zaman jiran gadon." Ta buɗe idanunta sosai wasu abubuwa masu tsananin haske da walƙiya suka fito a guje suka daki ƙirjinshi. Ƙam ya tsaya a tsaye kamar mai shirin ɗaukar hoto. Bata ƙara kallonshi ba ta finciki hannun Murja suka fice daga ɗakin. BILHAƘƘI ******* ******* Ba tare da tunanin komai ba ta zauna a gefen faffaɗan gadon irinna masu sarauta, ta janyo kyawawa tausasan ƙafafun ta ɗora a jikinta ta fara mammatsa mata cikin nutsuwa. A haka har sai da ta buɗe idanu ta zuba a kanta. Haɗa idanu suka yi, kamar haɗin baki duk sai suka sakarwa da juna murmushi. Da sauri Bilhaƙƙi ta sauke na ta ƙwayoyin idanun kan ƙafafun tana kallon yadda suke a ɗan kumbure. Tausayinta ne ya ƙara kamata, ita tun jiya a ganin farko da ta yiwa Sarauniyar ta ji wani sassanyar madarar ƙauna da tausayinta yana kwarara a cikin zuciyarta. "Bilhaƙƙi? mun tashi lafiya...?" "Au! yi haƙuri Ranki ya daɗe. Barka da tashi, na katse miki barci ko?" Ta katse ta tana maganar a jejjere cike da kunya. Dariya kawai ta yi tana kallon zallar ƙuruciya a gurin yarinyar. Matar Maheer ɗin ta burge ta, tun jiya da suka isa masarautar idan ta kalle ta tana jin wani abu kaman maganaɗisu yana fisgar tunaninta zuwa tunanin yarinyar, kamar ta taɓa saninta a wani wuri. Amma duk zurfafa tunaninta ta rasa inda ta taɓa ganinta, kuma ta rasa dalilin da yasa tunanin ya ƙi barin zuciyarta. Sakin murmushi ta sake yi tana kallonta. "Ba komai. Lafiya ko? ko akwai abinda kike buƙata?. Haka kike tashi da wuri? Ita Salamatun ta tashi...?" Da sauri ta sake katse ta a karo na biyu "Ranki ya daɗe yanzu na gama yin mafarki naga kin haihu lafiya ba tare da anyi miki aiki ba, shi yasa na kasa daurewa na taho gare ki." Ta maida idanunta kan danƙareren agogon bangon ɗakin, ƙarfe huɗu da minti arba'in na asubah. Ƙasa ta sauke idanunta ta ci gaba da magana " A mafarkin nawa na ga Mummy ce ma ta ke tare da ke har kika haihu. Kin san me kika haifa?" Ta ƙarasa tambayar tana kallonta. Daɗin labarin yasa ta yunƙura a hankali daga kwance ta miƙe zaune tana saurarenta. Biye mata tayi ta girgiza kai alamun bata sani ba, fuskarta cike da murmushi take sauraren daddaɗan labarin mafarkin da take ba ta. A zuciyarta cike da fatan tabbatuwar mafarkin da gasken gaske. A hankali ta ƙara amsa mata ta ƙara da tambayarta. "Ban sani ba Bilhaƙƙi. Me kika ga na haifa?" Maimakon ta ci gaba da faɗa mata mafarkin sai ta yi murmushi, a hankali kuma cikin nutsuwa kamar tana tsoron ji mata ciwo ta sauke mata ƙafafun a kan gadon, ta miƙe tsaye ta nufi inda ta ajiye galan ɗin addu'ar da Malam ya taho wa da Sarauniyar daga kaduna. Kofi ta ɗauka ta tsiyayo ruwan addu'ar ɗan madaidaici ta koma in da ta tashi ta zauna. Ta kara kofin a kusa da bakinta sosai ta fara karanto wasu addu'o'in a hankali. Tsawon lokaci sannan ta tofa addu'a ta nufi bakinta da kofin "Daure ki shanye duka Ranki ya daɗe. Yau ki sha addu'ar nan kafin ki ci komai. In Allah ya yarda za ki ga iko da hukuncin Ubangijin sammai da ƙassai. Dan Allah kar kisha idan zuciyarki na taraddadi, so nake ki sha zuciyarki cike da yarda da sakankancewar lallai Allah mai kowa mai komai ne, kuma shi ne ɗaya mai iko akan komai, mai yin yadda ya so a lokacin da yaso. Da shi kika dogara shi kuma cikin hukuncinsa zai fuskance ki da Rahamarsa. Zai biya miki duk buƙatunki kuma ya share miki hawayen da kika daɗe kina zubarwa na tsawon shekara da shekaru." Tun tana kallon Bilhaƙƙi da murmushi har murmushin ya ɓace a fuskarta, zuciyarta ya cika da tsoro. Amma fa ba tsoron kowa ba sai tsoron Allah shi kaɗai, da tsananin sakankancewar lallai Allah fa shi ne mai amsar addu'ar bayinsa. Wasu hawaye masu rangwamen zafi suka silalo daga idanuwanta, ta lumshe idanu ta buɗe. Haka kawai sai ta ji wani sanyi da ni'ima da yalwataccen farinciki suna sauka a duka sassan jikinta. Hannunta ta ɗora a saman hannun Bilhaƙƙi da yake riƙe da kofin ta buɗe bakinta, hannayensu a tare ta kafa kofin a bakinta ta fara shan ruwan addu'ar a hankali har ta shanye gaba ɗaya. "Na gode Bilhaƙƙi. Allah yayi miki albarka. Kije kiyi sallah ni ma sallar zanyi, bayan kin idar kizo zanyi magana da ke." Murmushi ta yi, ta mayar da kofin ta aje a inda ta ɗauke shi. "Nima na gode Ranki ya daɗe. Zan dawo in Allah ya yarda." Da ido ta rakata fuskarta fal murmushi zuciya cike da ƙauna har ta fice daga turakar ta ja mata ƙofar. Ta sauke wani nannauyan ajiyar zuciya, a hankali ta ture bargon da ta lulluɓe rabin jikinta ta zura ƙafafu ƙasa ta sauka daga kan gadon, wani zillo da ɗan cikinta yayi da ƙarfi yasa ta runtse idanu ta dafe cikin da hannu ɗaya, hannu ɗaya kuma ta dafe gefen gadon. Bakinta ɗauke da addu'o'i, sai da ta ji motsin ya lafa mata ta nufi banɗaki tana tafiya a hankali dan ta ɗauro alwalar sallar asubahi da ake ta kwaɗa kiran sallar farko. ****** ****** A cikin mugun mafarkin da ta saba yi cikin kwanakin yau hango Shalelenta Yarima Muzaffar tayi cikin wani mugun yanayi na ƙyama da tsangwama daga bayi da kuyangin gidan. A tsorace ta farka ƙirjinta na bugun tara-tara, idanunta a waje take sake tunano abinda ta gani a mafarkin. Ta haɗa zufa tayi sharkaf kamar wacce ta yi tseren gudu a cikin barci. Da taga tunani bazayyi mata ba da sauri ta dira daga kan gadon ta ɗauki jallabiya ta zura akan kayan baccin jikinta. Ko da ta buɗe ƙofar turakar ta fita falo ba ta bi ta kan bayi ukun da taga suna kai kawo ba kai tsaye ta nufi hanyar da zai sada ta da ɓangaren shalelenta bayan ta zura tattausan silifas a ƙafafunta. "Ranki ya daɗe Fulani Taka barka da asubah. Kina buƙatar rakiya ta ne...?" "Ba buƙata." Ta katse ta a hargitse tare da ƙara sauri zuwa inda ta nufa. Ta kusa isa ɓangaren sai ta hangi tahowar Mai Martaba da wasu mutane su huɗu ko biyar a bayansa. Ƙirjinta ne ya buga dam! Bugawar numfashinta ya fara hauhawa daga dai-dai zuwa yanayin da ba a cika buƙata ba a jikin ɗan Adam. 'Me zai kawo Takawa da kansa ɓangaren Yarima da asussubahin nan???' Tunanin zuciyarta ke nan. Da taga tunani da saƙar zuci bazai kaita ba sai kawai ta ƙara ɗaga ƙafa tana sauri dan ta riga su isa ta ga a wane hali Yariman yake ciki. Tana gaf da shiga mai Martaba ya dakatar da ita. "Safra'u?" Ya kira ta da muryarsa mai cike da izza da wani irin kwarjini mai firgita duk wani mare gaskiya. Runtse ido tayi kawai alamun sam bata so haka, ba ta da yadda ta iya dole ta ja ta tsaya cak har ya ƙarasa kusa da ita. "Takawa barka da asubah." Ta gaishe shi da muryar da ke ƙoƙarin ɓoye tashin hankalin da zuciyarta ke ciki, har da ɗan rusunawarta don nuna ladabi da girmamawa a gare shi. "Yauwa..! Barkanmu dai Safra'u. Me ke tafe da ke ɓangaren Yarima da sassafennan?" Ya ƙarasa tambayar tare da ƙure ta da kallo. "Babu komai Ranka ya daɗe. Kawai a zuciyata ce naji ina buƙatar ganin halin da yake ciki. Shi yasa na yo tattaki da kaina. Ko ga Takawa ma hakan ce ta kasance?" Ta ƙarasa maganar haɗe da sauke idanunta a kan mutanen da suke biye da Mai martaba, sai ta ga Liman, Waziri Umar, Chiroma, sai wani da bata san ko waye ba (Mal Abdulganiyyu ne mahaifin Maheer), da Bala babban Bawan da yake kula da al'amuran ɓangaren Yarima. Saboda biyayya shi Bala yana rakuɓe ne can gefe guda a bayansu. "Safra'u mu kam a gare mu ba hakan bane ta kasance. A ko wane lokaci muna da kyakkyawan tsammanin lafiya ko wane rai da ke ƙarƙashin masarautar nan zai wayi gari. Sai dai yau! Bayan idar da sallar asubah a bakin Bala babban hadimi ga Yarima mun wayi gari da wani mummunan labari, cewar Yarima yana cikin wani jarabta na Ubangiji. Da wannan ƙwaƙƙwaran dalilin yasa muka taho da Malam Liman don ganin halin da yake ciki. Don haka ina ganin ke ki koma ciki duk abinda yake faruwa za ki samu labari daga baya." Idanu ta gwalalo a tsorace haɗe da dafe ƙirjinta da hannu biyu, ba ta saurari umarnin da yayi mata na komawa cikin gida ba ta buɗe ƙofar da sauri ta afka ciki, bata tsaya a falon ba kai tsaye ɗaya daga cikin ɗakunan baccinsa ta nufa inda take jiyo wani ƙaƙƙarfar gurnani kaman na doki da wani kuka-kuka yana tashi a cikin ɗakin. Tana shiga su Mai martaba suka rufa mata baya, basu ganshi a tsakar ɗakin ba. Yana rakuɓe can saƙon tsakankanin gado da lokokin gadon yana kuka mai haɗe da gurnani, idanunsa jajur, bakinsa sai dalalar da yawu yake yi. Yana zaune ya naɗe hannayensa a ƙirji, babu riga a jikinsa daga shi sai gajeren wando. Yana haɗa idanu da Mahaifiyarsa ya miƙe a zabure ya nufi gurinta da mugun sauri yana waige-waige da raɓe-raɓe, kamar dai yana tsoron wani abu da yake gani a idanunsa. Yana ƙarasa kusa da ita ya rirriƙe hannayenta a tsorace ya fara maganganu kaman wanda notocin kansa suka kwakkwance. "Umma... Umma... ki ɓoye ni... ta ko ina ita nake gani za ta kashe ni... ta faɗa min daga jiya bazan sake iya haiƙewa wata baiwa ba... kin ganta can ko...?" Ya fara nuna jikin bango da yatsarsa yana ƙara rirriƙe mahaifiyarsa a tsorace, yayi wani ƙaƙƙarfar gurnani a lokaci guda kuma ya fashe da kuka mai ƙarfi ya ci gaba da magana. "Wai fa kawai dan ta ce min tana haila na ce ban yarda ba shi ne take neman kashe ni... ki gudu da ni Umma... wayyo... wayyo... wayyyo.... ga ta nan ta biyo ni da wuƙa..." Ya ruƙunƙume ta da ƙarfi yana nuna ƙunzugu mai ɗauke da jinin da Murja ta yar a tsakar ɗakin lokacin da ya kimtsa mata zazzafar marin da ya sa ra hantsila. Tsananin tashin hankali, ruɗani, firgici, da tsoron yadda Shalelenta ya buɗe baki yana tona asirin irin tsiyar da ya daɗe yana tsulawa akan duk wata saffa-saffar baiwa mai jini a jika yasa ta rungume shi a jikinta haɗe da sakin wani ƙaƙƙarfar kuka. Mai martaba da ya rasa na yi hannu ya naɗe kawai yana kallon ikon Allah yana sauraren saɗara-saɗarar abinda Muzaffar yake cewa. Mal Liman da Mal Abdulganiyyu sai jan ta'aweezi da a'uziyya suke yi. Shi kuwa Chiroma can gefe guda ya rakuɓe cike da tsoron kar maganganun tonuwar asirin da Muzaffar yake yi yayi kuskuren ambato sunanshi. Bala kuwa baki da hanci buɗe ya sake yana sauraren duk abinda yake faruwa. Ko da Mal Abdulganiyyu ya ga lokaci na ƙara tafiya, maganganun bakin Yarima sunƙi tsayawa kamar an kunna radio mai jini, ga wani zabura da yake yi yana mimmiƙewa kamar ana tsikarinshi da allura kusa da Mai martaba ya matsa cikin ladabi da tausasan kalamai ya ankarar da shi abinda ya kamata a yi. Daƙyar Takawa ya samu nasarar ɓamɓare Yarima daga jikin Sarauniya Safra'u. Tana kuka da turjewa yasa aka fice da ita daga cikin ɗakin shi kuma Yarima aka kulle shi a cikin turakar kafin isowar likitoci. A can ɓangaren Sarauniya Safiyya kuwa cikin hukunci na Allah SWT tana idar da sallar asubahi naƙuda mai ƙarfi ya taso mata. Wannan ruwan addu'a da Bilhaƙƙi tayi mata tasha shi ya zama kamar ruwan naƙuda da allurar naƙuda aka zurkuɗa mata a jikinta. Ko da Bilhaƙƙi ta koma turakar kamar yadda ta umarce ta bayan ta idar da sallah tana ganin halin da take ciki ta fara sharar ƙwallah don tsananin tausayin ganin yadda take salati da gurmususu. Ɗakin da aka sauke su ta koma wanda ɗaya ne daga cikin ɗakunan da yake ɓangaren Sarauniya Safiyya, kiran Mummy Salamatu tayi suka koma can turakar Sarauniyar da sauri. Ruwan addu'ar ta sake tsiyayowa ta ba Mummy ta ce ta bata ta sha sannan ta fice ta ja musu ƙofar. A nan falon ta hakimce tana dakatar da duk baiwar da ta yi yunƙurin zuwa turakar Sarauniya Safiyyar. "Barci take yi. Kuma ta ce bata buƙatar a dame ta har sai ta fito da kanta." Amsar da take ta basu ke nan wanda yasa dole suka dakata tunda sun ji umarni ne daga ita kanta Fulanin. A can lungu da saƙo na sassan cikin gidan kuwa abinku da gidan sarauta da ba a raba su da tsegumi. Cikin ƙanƙanin lokaci wannan faɗawa wancan, wancan tseguntawa wannan nan da nan zancen halin da Yarima yake ciki da irin maganganun da yake yi ya karaɗe lungu da saƙo na gidan. Sai hum-hum-hum ake yi da zancen ana tsoron Fulani Taka ta tsinci ana tauna maganar. Bayan isowar likitoci cikin gidan duk yadda aka so a fitar da Yarima daga ɗakinsa ƙiyawa yayi, sai zambarma yake yi yana zabura da jifan likitoci da mutanen ɗakin da duk abinda yake kusa da shi. Har lokacin kuma bai fasa irin surutun da yake yi yana zabura haɗe da cewa ga tanan za ta kashe shi ba. Dole dai likitocin biyu suka koma asibiti suka kwaso wasu ƙananun kayayyakin aikin da za su buƙata suka koma gidan. Mai martaba ne ya rirriƙe shi da taimakon su Mal Abdulganiyyu da ƙyar aka samu nasarar zurkuɗa mishi alluran barci mai ƙarfi. Minti goma tsakani barci ya ɗauke shi sannan likitocin suka samu damar fara binciken abinda yake damunshi, daga ƙarshe dai dole sai kwasarsa aka yi zuwa babban asibitin cikin garin Bauchi don a binciki halin da ƙwaƙwalwarsa ta ke ciki. Ita kuwa Fulani Taka kulle kanta tayi a cikin turakarta ta hana kowa shiga gurinta. A cikin ɗakin sai safa da marwa take yi kamar wacce ta haɗiyi taɓarya. Tana kuka da majina tana tsinewa tauraruwa mai wutsiya, don ta tabbata wannan mummunan al'amarin da yake faruwa da Muzaffar aikinta ne. A can ɓangaren Sarauniya Safiyya kuwa bayan awa biyu da minti goma tana gurmususu da jan ayar Summas sabeela yassara Allah ya kawo mata haihuwa lafiya da taimakon Mummy Salamatu, farar jaririya mai kama da turawa ce ta fara kunno kai bayan fitowarta da daƙiƙu ashirin kyakkyawan jariri mai kama da larabawa ya biyo bayanta. Kukan da suke ta tsalawa mai bayyana alamun lafiya suke shi ya fara tona asirin abinda yake faruwa a cikin ɗakin. Nan da nan jikin bayi da kuyangin ɓangaren ya fara kyarma don tsananin murnar wannan daddaɗan haihuwa ta bazata a lokacin da ba a taɓa tsammani ba. Guɗa suka fara rangaɗawa suna taka rawa da godiya ga Allah. Bilhaƙƙi ma baki ya ƙi rufuwa don tsananin murna, duk yadda take ta bubbuga ƙofar da son Mummy ta buɗe mata don ta ga abinda aka haifa ƙin buɗewa Mummy ta yi har sai da uwa ta biya. Bayan ta yanke ma jariran cibi a jikin Sarauniya da take ta zubda hawaye ta kwantar da su. Banɗaki ta shige ta haɗa mata ruwa mai zafi-zafi ta kama ta zuwa bayin, ta ce kukan ya isa haka ta daure ta tsarkake jikinta. Sai a lokacin ta buɗewa Bilhaƙƙi ƙofa tana shiga suka maida ƙofar aka datse, cikin zafin nama Mummy ta tsaftace gurin ƙal ta goge da klin da dettol kamar ba'ayi haihuwa a ɗakin ba. Ita kuma Bilhaƙƙi tana zaune akan gado tana aikin gogewa jariran jikinsu da dettol, abinku da wacce bata saba ba har saida Mummy ta gama ta amshe ta, bayan ta gama ta naɗe su a cikin kayan sanyi kafin ayi musu wanka. A lokacin ne mai Soron baƙi ta isa ɗakin da kanta ba aike ba don ganewa idanunta tabbacin abinda yake faruwa ba jita-jita ba. Kyawawan jariran da aka damƙa mata a hannunta yasa ta fashe da kuka don tsananin farin-ciki, daga bisani kuma ta fashe da dariya ta tattakura ta kama hanci ta rangaɗa ƙaƙƙarfar guɗar da ya karaɗe ɓangaren Sarauniya Safiyya gaba ɗaya. Su Mummy da Fulani sai murmushi suke yi cike da tsananin farin-ciki. Kwantar da jariran ta yi akan gado ta fita dan ta riga kowa kaiwa Takawa wannan kyakkyawan albishir ɗin, tana da tabbacin za ta samu gwaggwaɓan tukwuicin da zai jijjiga nutsuwarta. Duk wanda ta ci karo da shi a hanya umarni take badawa kan a shiga lungu da saƙo na cikin gidan a sanar da Sarauniya Safiyya ta haifo kyakkyawar Gimbiya da sabon balarabe Yariman Bauchi. Nan fa labarin ya sake fantsama a lungu da saƙo na cikin gidan. Haka Allah yake ikonsa, idan ya so sai ya haɗa wa bawa farin-ciki da baƙin ciki duk a lokaci guda. Hakan ce ta kasance ga Takawa, ga farin-cikin haihuwar Safiyya ga baƙin cikin abinda yake faruwa da Muzaffar. Da kanshi yay tattaki har zuwa ɓangaren Safiyya don ganin sanyin idanunsa. A karo na tara cikin kyarma da rawan jiki Jakadiya ta sake ƙwanƙwasa ƙofar turakar Fulani Taka, amma har lokacin ko alamun za a buɗe mata ƙofar bata ji ba. Kanta ta kwantar a jikin kofar ta buɗe murya sosai yadda za ta iya jiyo ta ta ciki "Ranki ya daɗe Jakadiya babba ce. Jaje haɗe da gwaggwaɓar albishir na taho inyi miki. Jajen akan abinda ya faru da Yarimanmu ne, albishir ɗin kuwa yanzunnan na samu labarin Fulani ta sauka lafiya, ta haifi ƴaƴa tagwaye lafiyayyu ƙosassu, da ita da jariran duk suna lafiya..." Ihun da taji an yanka ta can cikin ɗakin tare da jin rijib! alamun faɗuwar wani abu yasa ta kasa ƙarasa maganar da take yi, daga nan kuma ɗif ake ji. BILHAƘƘI Duk da jikinta yana bata wannan ƙarar da ta ji daga cikin ɗakin da alamun faɗuwar wani abu ba na lafiya bane. Amma don ta ƙara tabbatarwa sai ta sake kara kanta a jikin ƙofar tana kiranta. "Ranki ya daɗe Fulani? kina ji na? Allah yaja zamaninki ki daɗe kina yi a masarautar bauchi. Dan girman Allah ki taimake ni ki buɗe ƙofar nan." Shiru ne nan ma ya sake ba ta amsa. Hankalinta ne ya ƙara ɗugunzuma. Tana nan tsaye ita da bayin ɓangaren sunyi cirko-cirko da tunanin waƙar farawa sai ga shigowar Chiroma buguzum-buguzum yana baza babbar riga. Nan da nan duk suka dare suka bashi guri, kowa ya zube a ƙasa yana kwasar gaisuwa. Ko amsa musu ya kasa yi saboda tsananin tashin hankalin da yake ciki. Haihuwar Fulani lafiya ba tare da samun labarin mutuwarta gurin haihuwar ba shi ne babban abinda ya sashi ya zuge ya ƙare a lokaci ɗaya. Daman ga damuwar ciwon sambatu da ya kama Muzaffar farat ɗaya. Daga samun labarin haihuwar zuwa yanzu ya zaga bayi sau shida. Duk gwuiyawunsa a sake suke saboda rashin ƙarfin jiki. Fulani Taka yayarsa ce, tonuwar asirinta a masarautar nan tabbas babban tonuwar asirinsa ne. Domin duk wani tuggu da makirci da asire-asire tare da shi take ƙullawa, a taƙaice ma shi ne jakadan amsowa da isar da duk wani saƙo ko magani a gurin malamai da bokayenta. Da wannan dalilin yasa yazo tun da wuri kafin wankin hula ya kaisu dare, gara su san na kwatanci su nemawa kansu mafita da hanya mai ɓullewa. Ya kalle su shakaka da baki sannan ya daka musu tsawa dan kawo ƙarshen gaishe-gaishen da suke ta mishi. "Kai dallah ku saurara min! Ina ita Fulanin ta ke?" Jakadiya ce ta gyara tsuguno ta kora mishi bayanin duk abinda ya faru. A diririce ya matsa kusa da ƙofar shi ma yayi kirari, yayi magiya, yayi roƙo amma shiru ya ke ji, babu ma alamun za ta amsa balle har ya saka ran za ta buɗe ƙofar. Hankali a tashe ya kwashi jiki zuwa gurin Mai Martaba don ya sanar da shi halin da ake ciki. Mai soron baƙi ne ta tare shi da cewar baya nan ya shiga cikin gida gurin Mai Babban ɗaki (Mahaifiyar Sarki). Haka ya sake kwasan jiki zuwa ɓangaren Mai babban ɗaki bayan ya nemi iso anyi mishi izinin shiga ciki, ya tarar da lafiyayyiyar tsohuwar mai kyawun jiki an zuba mata jariran a gabanta tana tottofe su da zafafan addu'o'i. Takawa yana zaune a gefe yana kallon yaran da mahaifiyarsa fuskarsa cike da farin ciki. "Chiroma lafiya kuwa? Me yake faruwa da har aka gaza jira mu fito har sai an biyo mu nan gurin Umma?" Ƙasa ya sake kwantar da kanshi yana neman afuwa "Tuba nake Ranka ya daɗe. Tuba nake, Allah ya huci zuciyarka. Haƙiƙa ba lafiya ba, tunda Fulani taga halin da Yarima yake ciki ta bar sashen cikin tashin hankali da damuwa har yanzu bamu san a wane hali take ciki ba. Ta kulle kanta a turakarta ko motsinta ba a ji, munyi magana munyi magiya shiru har yanzu bata buɗe ƙofar ba. Tsoro muke ko tana cikin wani mummunan hali shi yasa nayi gaggawar zuwa in sanar da Takawa. Tuba nake Ranka ya daɗe." "Subhanallahi! Abdulfahi ayi gaggawar ba da umarnin a buɗe ƙofar ko ta wane hali don a ga yanayin da take ciki." "To Umma. An gama!" Ya amsa ma umarninta cike da ladabi da biyayya a muryarsa. Sai kuma ya maida idanunsa kan Chiroma. "Ayi gaggawar sanar da Badaru halin da ake ciki, idan ta kama ma a ɓalla ƙofar. Gamu nan fitowa." "A fito lafiya Ranka ya daɗe. Allah ya huta gajiya. Ranki ya daɗe a huta lafiya, Allah ya raya mana Gimbiya da Yarima ƙarami, Allah yayi musu albarka." Haka yayi ta surutai yana satar kallon kyawawan yaran har ya fice daga sasan gaba ɗaya. Ko da aka ɓalle ƙofar turakar Fulani a sume aka tarar da ita. Shi yasa ba tare da wani ɓata lokaci ba itama aka kwashe ta zuwa babban asibitin cikin gari, inda a can ne aka kwantar da Shalelenta. ****** ******** An kira babbar likita har gida ta duba Sarauniya Safiyya da jariran ta tabbatar da lafiyarsu ta ba Safiyya magunguna, Mai martaba yayi mata sha tara na arziki sannan ya sallameta. A wannan ranar Takawa kyaututtuka yake ta yi na bajinta da nuna godiyarsa ga Allah. Mai soron baƙi da ta kai albishir ɗin haihuwar jariran kyautar Raƙumi da doki aka yi mata. Malam da iyalansa kuwa anyi musu kyaututtuka na ban girma, ciki har da wani tamfatsetsen gida na Mai martaba da yake cikin garin kaduna. An ƴanta bayi talatin da biyu a cikin gidan. A wannan ranar dai duk wanda yake cikin masarautar zai shaida wannan gaggarumin abin farin ciki da ake ciki. Masu girke sai dafe-dafe suke yi kala-kala ana sadakar da shi. A wannan ranar ko zaman fada cikin farin ciki da walwala Takawa yake yinsa. Jariran har fada an fitar da su naɗe a gadajensu na jarirai, Hakimai, Galadima, Wambai da duk sauran masu mukami a masarautan sai leƙa fuskokinsu suke yi ana saka musu albarka. Da yamma lis ana gaf da tashi daga zaman fada wani firgitaccen labari da ya firgita duk wani mai rai da ke cikin fadar ya isa kunnensu. Wai ga wani tsohon bafullatani nan da wani matashin dattijo da ya ce shi ne Mustapha ɗan Sarki Abdulfatah. Kafin a ce kwabo Sarki ya bada umarnin ayi gaggawar isa da su cikin fadar don ya ganewa idonsa shin da gaske ne ko ƙarya ne mahassadansa suka yi mishi ture? Don yana da tabbacin in dai Mustapha ɗansa ne duk tsawon shekaru ko da komai na jikinsa ya canza akwai abubuwa da dama da zai iya gane shi da su. "Hattara Matashin dattijo! Nutsu!! shiga cikin taitayinka!!! Gaban Sarkin duniya kake Abdulfatahi na biyu wanda sam baya ɗaukar wargi." Wani Bafade ne ya dakawa Mustapha tsawa ganin yadda ake janshi yana ta turje-turje. Jin an ce a gaban mahaifinshi yake ya sa shi ya ɗaga idanunshi da suke ciccike da hawaye ya zuba a kan fuskar Takawa. Nan take sai hawayen suka gangaro shar... bisa kuncinsa don tsananin ƙunci, kewa, damuwar rashin ahalinsa na tsawon shekarun da bashi da tabbacin iyakarsu. "Abbbuu... bar...ka... da... yamma..." Ya faɗa a rarrabe bakinshi na rawa. Tsam Takawa ya miƙe tsaye daga kan karagar mulkinsa yana nuna Mustapha da ɗan yatsarsa manuniya. 'Tabbas duk da cika da alamun girma da muryar ta ƙara bazai taɓa manta muryar Shalelen ɗansa Mustapha ba. Muryar da ko da basa tare tsawon shekaru kusan kullum sai yayi mafarkinsa yana ce mishi duk daren daɗewa zai koma gare su.? Ta ya zai kasa tantance muryar masoyinsa?' Yana wannan tunanin har ya ƙarasa kusa da Mustapha ya cire hannunsa daga cikin alkyabbar jikinsa ya kama fuskarsa ya ɗaga ya ƙura mishi ido. Har lokacin hawayen idanun Mustapha basu daina zuba ba. Ya saki fuskar ya kamo hannunsa na dama ya ja hannun rigarsa har saman damtsensa. Wani ƙaton tawadar Allah ce da girma yasa ita ma ta ƙara buɗewa a damtsen hannun, yasa yatsarsa ya murje da ƙarfi ta ƙi goguwa. Zuwa wannan lokacin jikin Takawa ya fara kyarma, a hankali ya kama rigar jikin Mustaphan da niyyar cire mishi ita, ganin yadda jikinsa ke rawa yasa Mustaphan ya ƙarasa zare rigar da kansa. Sai ga wannan tambarin na ƙirjinsa wanda alama ce da ake yiwa duk wani jinin sarautar gidan da zai iya hawa karagar mulki. Taga-taga Sarki ya tafi zai faɗi da saurin gaske su Liman da waziri suka tare shi kafin ya kai ƙasa. "Mustapha na ne. Tabbas shi ne wannan..." Kafin ya ƙarasa jijiyoyin sadar da saƙonnin jikinsa suka tsaya ƙyam, ya suma a jikinsu. ******** ******** Zuwa dare gaggarumin abin farin-cikin da ya ƙara samuwa yayi tambari a duk wani lungu da saƙo na cikin garin Bauchi. "Babban ɗan Mai martaba Sarki Abdulfatahi na biyu Yarima Mustapha ya koma gida yau bayan ɓatarsa da shekaru ashirin da takwas." Wannan babban labari ne kuma abin farin ciki ne da ya jijjiga duk wani mai rai da yake rayuwa a cikin garin Bauchi da kewayenta. Ƙawayen masarautar ma sai kiraye-kiraye suke yi suna taya masautar murna. Ga Takawa, Sarauniya Safiyya, Uwar soro, mai babban ɗaki, Mal Abdulganiyyu da iyalansa na barwa masu karatu ku kwatantawa kanku irin kogin farin-cikin da aka tsunduma su a ciki🤣🥰👌🏽. Ƙarfe goma da rabi na dare Mustapha da Yalleru sun gama samun nutsuwa, sunci lafiyayyen abinci mai rai da lafiya. Mustapha yayi wanka ya shirya cikin kaya na alfarma da sarauta. Kasa haƙuri iyayen suka yi suka kulle kansu a turakar Mai martaba aka tasa Mustapha da Baffa Yalleru a gaba yana basu labarin irin gararambar rayuwar da yayi a cikin duniya. Masu saurin kuka a cikin ɗakin sai sharar hawaye suke yi. Tun bayan bayyanar labarin dawowar ɓataccen ɗan Sarki take jinta a cikin wani irin yanayi na faɗuwar gaba da sanyin jiki. Duk da bata samu ganin baƙon ba amma yadda ta ga Sarauniya tana ta murna da kuka tana godiya ga Allah da ya dawo musu da shi yasa ta tabbatar ba ƙaramin ƙauna suke yiwa Mustaphan ba. Shiru tayi a kan gado tana saƙe-saƙe da tunani. Mummy yau da wuri tayi bacci saboda gajiya, don yini suka yi zurga-zurga da hidiman jarirai, tunda ba kowa ake yarda ya ɗauke su saboda gudun abinda ka je ya zo na sharrin mutane. Wani matsanancin kewar Sevgilim ɗinta ne yake ta taso mata tana dannewa. Tun jiya da suka iso gidan bata sake haɗuwa da shi ba sai dai suyi magana ta waya. Da wannan tunanin yasa ta lalubo wayarta a jaka da nufin kiranshi sai ta ga an tura mata saƙonni biyu a fuskar wayar. Ko da ta buɗe saƙonnin ɗaya daga gurinshi ne, ɗayan kuma daga wani baƙon lamba ne da bata san ko ta waye ba. Saƙonshi ta fara buɗewa, zaƙaƙan kalamai ne yana faɗa mata yadda yake tsanani sonta da yadda yake kewarta, har yana ƙorafin shi fa shi yasa a rayuwarsa sam baya son harkar al'amarin gidan sarauta. Ace kai da iyalinka ba halin ku sake kuga juna a lokacin da kuke so? Da yadda ya ƙosa su koma gida a yi bikinsu ta tare a kusa da shi. Yalwataccen murmushin jin daɗi ne kwance a fuskarta, har za ta danna kiranshi sai kuma ta yanke shawarar fara duba ɗayan saƙon da aka tura mata, dan haka ta buɗe. Sunan da ta gani ne da abinda saƙon ya ƙunsa yasa ƙirjinta yayi wani mugun bugawa, kayan cikinta suka cure guri guda. "Bibi. Madam Mary ce. Duba whatsapp ɗinki ki ga wani babban abin mamaki da na tura miki." Da sauri ta wuce saƙon ta shiga whatsapp ɗin da kwata-kwata kwananta huɗu ne da buɗewa. Duk hange da tunaninta ya tafi ne ga tuhumar a ina Madam ta samu sabon lambar wayarta? Saƙon vidio ne Madam ɗin ta tura mata. Kafin ya buɗe sai jan tsaki take yi ƙasa-ƙasa cike da ƙosawa da son ganin abinda vidion ya ƙunsa. Yana buɗewa ta fara cin karo da fuskar wata tsohuwar mace, tana zaune cikin mawuyacin hali. An ɗaure ta tamau a jikin kujera, kanta fari fat! furfura ce ko wahala ce oho. Wani hannu da bata san ko na waye ba ya damƙi gashin kan matar aka ɗaga fuskarta yadda mai kallon vidion zai iya ganinta sosai. Sautin muryar Madam da ta ji ya biyo bayan ɗaga fuskar yasa ta miƙe tsaye a zabure, hankalinta a tashe, tsananin tashin hankali yasa idanunta ya fara canza launi daga fari da baƙi zuwa ja da kore "Bibi kinga wannan matar? ita ce Mahaifiyarki Rebeccah. Tsawon shekaru goma sha tara tayi a kulle a Coci ana gana mata azaba. Yau mun je mun ƙwato ta a hannun waɗancan da suke tsare da ita, idan kin damu da ita kina son ganinta a raye ki miƙo kanki gare mu, ki dawo cikin ƙungiya ki karɓi muƙaminki. Idan kika yi haka mu kuma munyi miki alƙawarin za mu sake ta lafiya ba tare da wani abu ya faru da ita ba. Kuma kafin ki taho ki tabbatar kin kashe wannan ɗan iskan auren da kika yi, domin a muƙaminki na ƙungiya sam babu aure a rayuwarki." Sai ta sake fashewa da dariya mai tsananin ƙarfi tana ta ƙyaƙyatawa har zuwa ƙarshen vidion. Tsigar jikinta ne ya fara wani irin mimmiƙewa kamar ƙayoyi don tsananin tashin hankali, bata san lokacin da hannunta ya danna amsa kiran wayar da Mustapha yai mata ba sai muryarsa kawai ta ji yana ta "Hello... helloo... Tatlim kina ji na?" "Ka fito yanzun nan ina so mu haɗu." Tayi maganar da wani irin murya da a can ɓangarensa sai da ya cire wayar a kunnensa ya sake kallon sunan da tunanin ko dai ba ita ya kira ba? ganin tabbas sunanta ne kuma lambarta ce yasa ya miƙe zaune da sauri, da jin muryar nan ya tabbatar ba lafiya take ba. Kamar walƙiya tunanin abinda ya faru da ita jiya a hanyarsu ta zuwa ya faɗo masa a rai. "La haula wala ƙuwwata illa billahil aliyyul azeem. Tatlim kiyi ta maimaitawa gani nan zuwa, ki fito mu haɗu yanzu. La haula wala ƙuwwata illa billahil aliyyul azeem." Haka yayi ta maimaitawa a wayar tun yana jinta shiru bata amsa shi har ya ji ita ma tana maimaitawa, cikin sauri ya zura rigarsa wayar na maƙale a kunnensa ya fice daga ɓangaren baƙin da aka sauke su. Kai tsaye cikin gidan ya nufa hanyar da zai sada shi da ɓangaren Sarauniya Safiyya. Saboda dare da ya fara yi don lokacin sha ɗaya ta gota jefi-jefi yake haɗuwa da bayi har yayi kiciɓus da ita a hanya, da sanyin jiki take tafe kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki. Hannunta ya ja da mugun sauri suka koma inda ya fito. Suna shiga cikin ɗakin ya maida ƙofar ya rufe, sannan ya janyo ta tsam ya rungume a ƙirjinsa yana tottofeta da duk wata addu'a da ta zo bakinshi. Ita kuwa sai ƙara riƙe shi take yi a tsorace tana ta sassauke ajiyar zuciya mai nauyi sauri-sauri. Sai da yaga ta ɗan samu nutsuwa ya riƙe ta a jikinsa suka zauna a gefen gadon, sannan ya ɗago fuskarta a tausashe ya fara tambayarta abinda ya ɗaga mata hankali. "Tatlim! kinsan bana son damuwarki ko? Ummm?! Faɗa min! Wa ya taɓa min ke? Menene abinda ya ɗaga miki hankali?" Sai a lokacin ta ji wani ƙaƙƙarfan kuka ya taho mata, karo na biyu ta sake kwantar da kanta a ƙirjinsa ta fara rera kukan a nutse kamar karatu. Shi kuwa bai katse ta ba sai shafa bayanta yake yi yana ɗan bubbuga ta alamar rarrashi har saida ta samu nutsuwa don kanta ta ɗago tana kallonsa ta fara magana a muryarta baiyane ƙarara da tashin hankali. "Sevgilim! Sun kama Mahaifiyata... ashe duk wannan gararambar da nake yi a duniya mahaifiyar da ta haifeni tana raye a can tsare a hannun wasu azzaluman mutane. Yanzu su Oga sun kamo ta, sun ce in dai ban koma cikinsu ba za su kashe min ita. Sevgilim ita Ummata ce wacce ta tsugunna ta haife ni, ya zama dole in miƙa musu tawa rayuwar don in cece tata rayuwar. Duk da ban taɓa ganinta a ido biyu ba na ji a raina ina tsananin son ta, sun faɗa min shekarunta goma sha tara tana cikin uƙuba a hannun waɗancan mutanen. Don tabbatuwar cika ta ƴar halas ya zama dole in zame mata silar jin daɗi. Ko bayan ba raina kai da Malam dan Allah ku riƙe min ita Sevgilim, ka jiyar da ita daɗin duniyan da ta daɗe ba ta ji ba. Idan kayi min haka ka gama min komai Masoyi." A karo na uku ta sake kwantar da kanta a ƙirjinsa wasu zafafan hawaye suna tsiyaya daga idanunta. BILHAƘƘI Shiru yayi yana saƙe-saƙe da jujjuya maganganunta. Kamar ya fahimta amma kuma bai gama fahimtar inda maganganunta suka dosa ba. Har sai da ya tambaye ta "Babe nutsu pls, ta ina ne suka faɗa miki sun kamo Mahaifiyarki?" Wayarta ta nuna mishi da take yashe a can gefen gadon. Zai tashi ya ɗauko ta hana shi ta hanyar sake ƙanƙame shi. Dole ya koma ya zauna ya ci gaba da shafa bayanta. Tsawon lokaci suna a wannan yanayin har yaji yanayin saukar numfashinta ya canza, alamun ta samu barci. Bai yi ƙwaƙƙwaran motsi ba sai da ya tabbatar barcinta yayi nisa sosai, ya zame jikinsa a hankali ya kwantar da ita a kan gadon, ya zare hijabin jikinta ya gyara mata kwanciyar sannan ya ɗauki wayar ya matsa can gefe ya fara dudduba saƙonnin cikin wayar. Dukda yana namiji al'amarin ya jijjiga shi, tsawon lokaci yana ta saƙe-saƙe da tunanin hanyar da zai bi ya taimake ta amma ya rasa na yi. Sai jan Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un yake yi. Vidion ya sake kunnawa ya kure fuskar matar sosai da kallo, tabbas tana tsananin kama da Bilhaƙƙi. Babu tantama wannan matar ko ba mahaifiyarta ba ce to tabbas sun haɗa dangantaka ta jini a tsakaninsu. Kamannin yayi yawa. Aje wayar yayi ya yakice tunanin komai a ransa ya shige banɗaki ya ɗauro alwala, nafilfili yayi ya haɗa da addu'o'i sosai a kan Allah ya kawo musu mafita da gaggawa. Cikin hukunci na Ubangiji kuwa bai tashi a kan sallayar ba sai da yaji zuciyarsa ta tsayar mishi da ƙwaƙƙwaran shawara na hanyar da ya kamata su bi. Hamdala yayi ta yi yana godiya ga Allah har ya tashi ya ɗauko wayarsa. Ƙaninsa Luƙman mai bi masa a haihuwa ya kira ya warware masa duk abinda yake faruwa. Maganganu mai tsawo suka yi sannan suka yi sallama kowa ya katse wayar. Fita yayi ya ja ƙofar ya kulle ta waje, ya nufi ɗakin da Malam ya kwana jiya wanda yake kusa da nasa ɗakin dan ya ga ko Malam ɗin ya dawo daga turakar Takawa inda suke ganawa. Sai ya iske ya dawo sallah ma yake yi. Ganin haka sai ya nemi guri ya zauna yana jiran ya idar da sallar. "Magajin Malam? lafiya a darennan? Na yi tsammanin tuntuni ka yi barci?" Tambayoyin da Malam ɗin ya fara jera mishi kenan bayan ya idar da sallar. "Lafiya ƙalau Malam. Barka da dare." "Yauwa barkanmu dai Magaji. Me yake faruwa?" Ya sake tambayarshi cikin zaƙuwa, dan ya ga alamun maganganu ne a bakin Maheer ɗin. "Malam daman kira ne mai muhimmanci aka yi min daga gurin aikinmu. Sun buƙaci lallai idan zai yiwu in koma kaduna gobe. Shi yasa daman na zo inji yaushe ne ka shirya za mu koma gida?" "Eh to nima da a niyyata mu koma gida gobe ko don saboda aikin naka. Amma a darennan Mai martaba ya zo min da buƙatar da bazan iya musa mishi ba. Ya ce akwai muhimmin al'amari dangane da Yarima Mustapha da zai kaisu can wani ƙauye a jihar kaduna. Ya buƙaci ko zan koma gida in bari muyi wannan tafiyar mu dawo, in yaso ma ni sai in tsaya a kaduna idan sun gama su sai su dawo nan ɗin." Shiru suka yi duk suna saƙe-saƙe, sai Malam ɗin ya ci gaba da cewa "Ina ga abinda za a yi gobe idan Allah ya kaimu kai ka koma gurin aikinka. Ni sai na iso kawai. Daman tun kafin bayyanar Mustapha Innah ta buƙaci in bar Salamatu da Bilhaƙƙi a nan har sai bayan an gama shagalin suna sai su bi tawagar masu zuwa daga maru su sauka a kaduna. Idan duk hakanma bai yiwu ba za ta sa a mayar da su har gida." Da 'To' kawai ya amsawa Malam wacce bahaushe yake kira da ba ta karya wuya. Amma ya san tafiyarshi ya bar Bilhaƙƙi a nan ko da lafiya ƙalau ne ba abinda ke faruwa ba abu ne da zai iya jurewa ba. Balle kuma ga gaggarumin tashin hankalin da ya ɓullo musu. Ya san ko ya hana Bilhaƙƙi tafiya ga mahaifiyarta tabbas za ta tafi, shi yasa da ta bi motar haya ba tare da saninsa ba gara shi ya kaita da kanshi. Ya zaɓi ya ɓoyewa Malam gaskiyar halin da ake ciki ne saboda ya san yana iya shiga cikin matsanancin tashin hankali da damuwa. Sallama yayi mishi da fatan tashi lafiya bayan ya sanar da shi gobe ana idar da sallar asubah zai ɗauki hanya. Ya fice daga ɗakin ya koma ɗakinsa gurinta. Ya tarar da ita har lokacin tana barci, shirin bacci yayi ya hau gadon ya janyota jikinsa ya rungume, yayi musu addu'ar barci gaba ɗaya ya shafe musu jiki ya ja musu bargo. A wannan ranar nan gurinsa ta kwana, kiran sallar farko ya tashe ta tayi wanka. Tana fitowa shi ma ya shiga ko kafin ya fito har ta maida kayan jikinta, har lokacin fuskarta danƙare take da damuwa. Shi ma bai yi ƙoƙarin damunta ba saboda ya san lamarin babu sauƙi, addu'a ya umarci tayi sosai idan ta idar da sallah sannan ya fice zuwa masallaci. Ana idar da sallah kafin jama'a su fara fitowa ya fice daga masallacin, sauri-sauri ya kira ta ta shige motar ya ja a sukwane suka fice daga gidan. Suna hawa titi ya ƙure ƙarar karatun alƙur'ani mai girma ƙira'ar Sudais. Sosai yake ba motar wuta duk da nisan tafiyar so yake su isa kaduna a cikin taƙaitaccen lokaci. ****** ******* Duk zamanta a gidan baifi a ƙirga ba da ta taɓa haɗuwa da shi, tunda shi ba mazaunin jihar kaduna bane. Tsananin ƙwazo da himmar aiki haɗe da tsage gaskiya yasa a cikin ƙananun shekarunsa aka ba shi muƙamin D.P.O na ƴan sanda. Shi yasa yau a cilla shi wannan jihar gobe a cilla shi wancan jihar don share tsagerun da suka addabi garuruwa. Bai fi sati biyu ba baya da aka yi mishi transfer zuwa jiharshi ta kaduna, yana tsaka da aiki Maheer ya kira shi yana faɗa mishi wannan sarƙaƙƙen al'amarin na Bilhaƙƙi. Shi ya bada shawarar duk yadda ya kamata suyi kuma Maheer ya gamsu ɗari bisa ɗari. A karo na barkatai ya sake kallonta da manyan idanunsa, shi mamaki ma yake yi ƴar ƙanƙanuwar yarinya kamar ita da babban al'amari. Da gaske in banda Yayanshi ne ya tare shi da case ɗin kai tsaye zai ƙaryata duk wanda ya faɗa mishi labarinta. "Amma ƙanwata kina ga mu barki ki tafi gurinsu ke ɗaya shi ne abinda ya fi? Ko dai in haɗa ki da jami'an da zasu taimaka miki a tarwatsa ƙungiyar..." "A'a! A'a Ya Luƙman. Dan Allah kar kayi haka." Ta katse shi da sauri jikinta na rawa, sai kuma hawaye shar... ta ci gaba da magana cikin kuka "Wallahi ba imani ne da su ba idan aka bi bayana na tabbata za su iya kashe min mahaifiyata. Idan kuwa hakan ta faru bazan taɓa yafewa kaina ba." Ɗage kafaɗa yayi alamun shi kenan tunda hakan ta zaɓa, ya sake tura kwalin lemun exotic da kofi a gabanta. Kisha kafin Yayan ya dawo sai ku wuce..." Buɗe ƙofar da aka yi tare da shigowar Maheer yasa shi yayi shiru, kallon juna suka yi, Maheer yayi wa Lukman wani alama da ido da na rasa gane ko me yake nufi. Gyaɗa kai yayi tare da ce masa "Ka dawo?" "Eh na dawo." Ya ajiye wani leda a gabanta ya ɗago haɓarta da hannunsa yana kallonta cikin ido. Kujera ya janyo ya zauna a kusa da ita har gwuiwoyinsu na gogar na juna "Babe kukan ne har yanzu?" Kafin ta yi magana Luƙman ya ce "Ina ga idan ta sha lemun za ku iya wucewa. Ta ce bata buƙatar mu bi ta, za ta iya zuwa ita kaɗai." Yana gama maganar ya fice daga Ofis ɗin sannan ya ja musu ƙofar. Hannayenta ya rirriƙe duk biyun fuskarsa baibaye da damuwa "Kin tabbata barinki ki tafi ke kaɗai shi zai sa su sake ta lafiya ba tare da sun cutar da ita ba?" Ɗaga mishi kai kawai ta yi alamun eh! "Babe kiyi min alƙawarin kema za ki dawo gare ni, wallahi ina tsananin sonki. Bazan iya rayuwa idan baki a kusa da ni ba." "Gaskiya banyi maka alƙawari ba Sevglim. Amma zanyi ƙoƙarin dawowa idan na samu dama in Allah ya yarda." Ta amsa tana ƙoƙarin ƙara ƙarfafa ma kanta gwuiwa. Janyo ta jikinsa yayi ya riƙe ta tsam a ƙirjinsa, sai sassauke ajiyar zuciya suke yi a tare, tsawon lokaci sannan ya kai hannu ya buɗe kwalin lemun ya tsiyaya a kofi. Ya ɗauko kofin ya nufo bakinta da shi, kauda kai ta yi, murya ƙasa-ƙasa ta ce "Bana jin zan iya shan wani abu yanzu." Shiru yayi bai amsa ta ba, ko da ta kalli fuskarsa sai ta ga yanayinsa ya canza, kamar bai ji daɗin ƙin shan da tayi ba. Kawai sai ta karɓi kofin ta kafa a baki ta fara sha, saboda sanyinshi yasa ta shanye gaba ɗaya ta aje kofin a kan tebur. Ajiyar zuciyar da ya sauke yasa ta kalle shi, sai ya sakar mata murmushi kaɗan. Miƙewa tayi daga jikinshi "Ya kamata in tafi, lokaci yana ƙara tafiya." "Tam! Ɗan jira ni minti biyu bari inga Luƙman a waje." Ko kafin ta amsa har ya fice daga ofis ɗin. Minti biyu, huɗu bai dawo ba, nauyin da ta ji kanta yayi mata yasa ta ɗan kifa kai a kan tebur ɗin kafin ya dawo. Nan fa wani nannauyan barci yayi awon gaba da ita. Minti takwas yayi da fita sannan ya koma cikin Ofis ɗin, ganin ta yi barci yasa shi sakin murmushi ya koma ya sanar da Luƙman, sannan ya kira Dr. Bilyaminu da yake zaune a wani ɗan ƙaramin Ofis suka koma ofishin Luƙman duk su ukun. ******** ******** "Madam ! kamar yadda na sanar da ku a shirye nake in koma cikin ƙungiya dan in cece rayuwar Mahaifiyata. Lokacin yayi, ga ni yanzu na fito daga gidan Malam. A ina zamu haɗu...?" "Ki rufe min baki Bibi!" Ta daka mata tsawa daga can ɓangaren, cikin masifa ta ci gaba da cewa "Me kika maida ni? Wacce ba ta da wayau ko me? karki manta duk iskancinki da wayon da kike ganin kina da shi a ƙarƙashi na kike. Ko kin manta kina ƴar ƙanƙanuwar yarinya na tsince ki? Ki ajiye wayar hannunki da duk wani abu da kike riƙe da shi a ƙofar gidan ki hawo titi ki ci gaba da tafiya kawai." Wani dogon tsaki ta ja sannan ta katse wayar. Daman wayar ce kawai a hannunta, jikinta a sanyaye ta aje wayar a ƙofar gidan ta ci gaba da tafiya cikin sauri tana waige-waige. Ko da ta isa kan titin tsayawa tayi tana tunani don bata san ina ya kamata ta bi ba. Gabas ko yamma, kudu ko arewa? kawai sai tayi shahadar ƙuda ta miƙe titin yamma samɓal tana ta tafiya. Ta jigata ƙwarai, domin ta shafe minti arba'in tana tafe da sassarfa kafin wata baƙar mota ta ci burki mai ƙarfi a gefenta, ko kafin ta waiwaya ta gama gane kalar motan an buɗe ƙofar da sauri aka fincike ta zuwa cikin motar, aka ƙara figar motar a guje aka harba titi. Basu barta ta gama nutsuwa daga firgitan janye ta da suka yi ba aka shaƙa mata wani hoda a hancinta. Daga nan bata sake sanin inda kanta yake ba har suka isa wani babban gida a sabon tasha. Wani ƙato a cikinsu ne ya saɓa ta a kafaɗa kamar ya ɗauki sillan kara ya shige gidan da ita, wani ɗaki ya kaita ya shimfiɗar a kan gado. Minti biyu tsakani wasu ƴan mata biyu suka shiga ɗakin suka caje ta gaba ɗaya bayan sun cire kayan jikinta tas! ɗaya daga cikinsu ce ta kira Madam a waya ta yi mata bayani "Madam! babu komai a jikinta. Sosai mun duba ta ko ina a jikinta bamu samu komai ba." "Ok! ku saka mata kayan nan da na ba Moses ya kawo muku." "Ok ma!" Wani doguwar riga shuɗi suka saka mata a jikinta saɓanin riga da zane na atamfar da suka cire mata. Suka ɗaure gashin kanta da wani jan ƙyalle mai ɗan faɗi. Garjejen ƙaton nan ne ya sake ɗaukarta ya kai mota, saɓanin motar da suka zo da ita a ciki yanzu wata ƙaramar mota suka ɗauke ta a ciki, a hankali suke tafiya har suka isa gidan Aunty Mercy da yake Kamazou, inda a can suke tare da Madam Mary. Bata farfaɗo ta dawo cikin hayyacinta ba sai ƙarfe biyu da minti biyar na dare, tana farkawa ta ga su Madam a tsaye a kanta cikin shigarsu ta ƙungiya, ko kafin ta ce komai sun dafa kafaɗunta sun ɓace ɓat! basu baiyana a ko ina ba sai a gaban Oga da sauran ƴan ƙungiya. "Barka da dawowa gare mu Bibi... Bibi barka da zuwa... kinzo ke nan ba komawa Bibi..." Sautin maganganu mabanbanta da ɗakin taron ya fara amsa kuwwa kenan ana yi wa Bilhaƙƙi murna da barka da komawa cikinsu. Tana zaune a hakimce kan kujera, idanunta jajur, gashin kanta a mimmiƙe, a kallo ɗaya za a yi mata a fahimci wannan ba Bilhaƙƙin Maheer ba ce, wata ce can daban wacce aka tsuma ta kuma aka rene ta da manyan kayayyakin tsafi tun tana jaririya. Fuskantar juna suke yi ita da Oga kowa fuskarshi a ɗaure. Ita ta fara katse shirun tayi magana da wani irin murya mare daɗin sauraro "Na dawo gare ku kamar yadda kuke so, ina Rebeccah?" Daga can ɓangaren a gigice Maheer ya ɗaga kai ya kalli Luƙman, shi ma luƙman ɗin ya kalle sa. Amma sai ya ɗaga mishi hannu alamun yayi shiru kar yayi magana, ya ƙara ƙure ƙarar maganganun da suke saurare ta jikin na'urar da suka jona da abinda yake maƙale a kunnensa. A can cikin ƙungiya kuma wani ƙaƙƙarfan dariya Oga ya fashe da shi yana nuna ta da dungulmin hannunsa. "Da kina tsammanin za ki iya guje mana mu barki ki rayu a wata duniya ba tare da mu ba? Bari in faɗa miki abinda baki sani ba. Tun ranar da Mary ta kawo ki cikin ƙungiyar nan Garkuwa ya bani daman ganin manyan sirrukan tsafe-tsafen da Veronika ta jiƙa ki da su. Amma kuma ke kanki baza ki san ke shahararriyar matsafiya bace sai ranar da kika cika shekaru ashirin a duniya, duk wani abu da za kiga kinyi ya faru ƙarami ne a cikin tsafin da aka raine ki da shi tunda baki kai shekaru ashirin ba. Da wannan dalilin yasa muka umarci Mary ta kula da ke ta raineki cikin gata, ta baki duk abinda kike so. Saboda ranar da za ki cika shekaru ashirin a gaban Garkuwa za mu kwana ni da ke muna bauta mishi. Idan muka yi hakan wannan ƙungiyar tamu za ta ɗaukaka, za muyi gogayya da duk wata ƙungiya ta tsafi da take ji da kanta a duniya. Sai da lokacin ya kusa kuma za ki barmu? Da farko mun barki kin huta a gidan wancan malamin ne saboda babu halin mu ɗaukoki daga gurinshi, amma aurar da ke da yayi abu ne da zai rusa mana abinda muke jira shekara da shekaru. Idan muka yi kuskuren barin wani namiji ya kusanceki duk wani tsafi da aka rene ki da shi zai gudu ya barki ke kaɗai da baiwar da aka haife ki da shi, wannan kuma ba komai bane fa ce wani abu da Hausawa suke kira KAMBUN BAKA. Idan kika cika shekaru ashirin ɗinnan za ki samu mulki, za a miki biyayya a duniya, duk girman ƙungiyarnan ke za ki zama mataimakiyar Oga. Bibi..." "Alheri." Ta faɗa da wata siririyar murya cikin tsawa tare da miƙewa tsaye a fusace, wani walƙiya mai tsananin haske tare da rugugi kamar aradu yayi fitan burgu daga idanunta ya maka Oga da jikin bango. Daga can ɓangaren su Maheer kuma wani ma'aikaci da yake gaban wasu na'urori da kwamfuta a gabanshi yana aiki ya waiga yana kallon Lukman "Yallaɓai! A halin yanzu mun gano dai-dai inda suke meeting ɗin." "Good!" Da mugun gudu Luƙman da Maheer da sauran ma'aikatan da ya shirya zai tafi da su suka fice daga babban ofishin suka shiga motoci biyun da suka zuzzuba kayan aikin da za su tafi da su, ba tare da ɓata lokaci ba direban da su Maheer suke ciki ya ja motar da gudu ɗayan direban ya bi bayanshi, kunnen direban maƙale da abin sauraren magana wancan ma'aikacin da ya gano inda su Bilhaƙƙi suke yana mishi kwatancen gurin. BILHAƘƘI Duk da mugun buguwan da yayi bai hana ya miƙe yana tangaɗi ba, kafin ta ankara ya nuna mata dungulmin hannunshi ya runtse idanu yana wasu irin maganganu na tsafi, nan take aka ɗaga ta sama cak! aka fara hajijiya da ita tsakankanin tulunan da suka yiwa saman ɗakin ƙawanya, ita ba a sama ba a ƙasa ba. Kanta ne ya fara juyawa a saman, duk yadda ta so ta sauka ƙasa da nata ƙarfin tsafin ta kasa, tana zuwa kusa da wani ƙaton tulu da yafi ko wanne girma yana tsaye cak a saman ɗakin kawai sai ta dunƙule hannu ta dake shi da mugun ƙarfi ranta a ɓace. Tush! ƙarar fashewar tulun da sakin wata siririyar ƙara da ya karaɗe ɗakin duk a tare suka fito daga cikin tulun. Cikin sauri Oga ya buɗe idanunsa a tsorace, ganin abinda ta yi yasa shi ƙwalla wani gigitaccen ƙara ya zube a tsakar gurin yana kururuwa da birgima kamar wani makaho, zuciyarsa cike da tunanin amfanin tulun a gare su. 'Wannan tulun da ta fasa shi ne babban turaku ko kuma murhun da yake riƙe da ƙungiyarsu, Garkuwa ya taɓa faɗa mishi duk ranar da aka fasa wannan tulu to tabbas ƙarshen ƙungiyarsu ne ya zo, kuma daga lokacin da tulun ya fashe baza su sake jin motsinshi ko kuma ya biya musu wata buƙata tasu ba.' Ita kuma Bilhaƙƙi ganin hakan da yake yi yasa ta gane lallai tayi musu babban ɓarna. Don haka cikin masifaffen sauri kamar walƙiya ta ci gaba da bin tulukan tana farfasawa, duk tulun da ta fasa da kalar ƙaran da yake yi. Nan wani irin mugun wari da tsananin ɗoyi ya turnuƙe ɗakin, ga wani hayaƙi da yake tashi da ƙauri kamar na ƙonewar wani abu mai bala'in wari. Su Madam da sauran ƴan ƙungiya sai guje-guje suke yi hankalinsu a tashe suna neman wajen ɓuya, sunsan yau sai dai wani ikon Allah. Da alamun ƙarshensu ne ya zo, ga shi kuma sam tsafinsu na ɓacewa ya ƙi aiki a daidai wannan lokacin, kamar makafi kuma ganin ɗakin tsafin suke yi a dunƙule kamar ƙwallo, sun rasa hanyar da za subi su fice daga ciki. Oga kuwa da ya fahimci manufarta na son kawo ƙarshen komai da kowa na cikin ƙungiyar a zuciye ya miƙe tsaye ya tashi sama suuuu sai ga shi a gabanta, hannunshi ya miƙa da ya zama kamar wani igiya ya shaƙo wuyanta ya matse sosai yana ƙoƙarin hallakata. Nan fa ta fara kakari da fisge-fisge tana zazzare idanu, duk yadda ta so ita ma ta shaƙo shi suyi mutuwar kasko hannunta sam ya ƙi kaiwa wuyansa. A daidai wannan lokacin kuma da tsananin ƙarfin addu'a Allah ya ba su Maheer ikon shiga cikin gurin, don da farko ko da suka isa gurin suna kallon ƙofar shiga gidan amma da sunyi yunƙurin shiga sai wani ƙaƙƙarfan iska ya watsar da su baya. Sun jigata sun wahala sosai, wani tunani da ya ɗarsu a ran Maheer yasa ya fara karatun Alƙur'ani da buɗaɗɗiyar muryarsa mai daɗin sauraro, Luƙman ya rufa masa baya, sai kuma ƙalilan daga cikin musulman cikin ƴan sandan suma suka rufa musu baya da karatun. Da wannan karatun suka sake dosar ƙofar gidan bisa ga mamaki ga sauran jami'an da ba musulmai ba sai suka ga sun danna kofar gidan sun shiga ciki, aka bar sauran jami'an a waje, domin har lokacin su sun kasa shiga. Ko da suka shiga gidan sai suka ga ɗaki ne ƙwalli ɗaya a tsakar gidan, da suka shiga ciki ta tsakiyar ɗakin suka ga matattakala ya gangara can ƙasa, ta wannan hanyar suka bi sai ga su a tsakiyar gurin meeting ɗin. Ganin abinda yake faruwa a saman ɗakin tsakanin Oga da Bilhaƙƙi yasa cikin sauri Luƙman ya saita ƙafar Oga ya sakar mishi harbi bayan yayi basmala da ƙarfi. A gigice ya sake ta zata faɗo ƙasa da saurin gaske Maheer ya caɓe ta faɗa hannunsa, shi kuwa Oga yana riƙe ƙafarsa ya faɗo ƙasa tim yana rarraba idanu tsakaninsu. Kafin yayi wani yunƙuri na yin tsafi Luƙman ya sakar masa wani gigitaccen naushi a mahangurɓa. Ihu ya sake ya buɗe baki zai yi wani abu ɗaya daga cikin jami'a ya sake sakar mishi harbi a kafaɗa. Nan Luƙman ya ci gaba da sakar mishi naushi da zafafan maruka a kumatun dama da hagu, sai da ya farfasa mishi baki da kumatu a kumbure wasu jami'ai uku suka cukwuikwuiyeshi aka maƙala mai ankwa hannu da ƙafa. "Duk wanda ya sake motsawa zan harbe shi har lahira." Luƙman yayi furucin cikin tsawa tare da sakin wani ƙaƙƙarfan harbi a saman ɗakin. Nan su Madam kowa ya tsaya a tsorace yana rawan banjo saboda gigita. Ɗaya bayan ɗaya aka iza ƙeyarsu zasu fice daga ɗakin. Bilhaƙƙi na saɓe a kafaɗar Maheer cikin wani mawuyacin hali, sun kusa fita gaba ɗaya daga ɗakin tayi magana da ƙyar muryarta na ciccijewa "Gan...gaa...ran...! Umma...ta..." Nan fa suka sake komawa ciki a gigice amma duban duniya sunyi basu ga Rebecca ba. Babu komai a ciki sai wani ɗan ƙaramin ɗaki mai ɗauke da wani ƙaton Gunki da tarkacen kayan tsafi, sai kuma nan babban falon da suke meeting ɗin ƙungiya. Hankalin Maheer da Lukman idan yayi dubu ya tashi, ga Bilhaƙƙi a lokacin ta suma bata san inda kanta yake ba. Anyi tambayar duniya Madam Mary da Oga sun ce basu san inda Rebeccah take ba. Sai da Lukman ya tattarasu kaf Oga da sauran ƴan ƙungiya ya ce ya rantse da girman Allah idan basu faɗa mishi inda suka ɓoye Rebeccah ba zai harbe su ɗaya bayan ɗaya sannan ya kulle su a cikin gidan ya cinna musu wuta. Jin hakan da suka yi ne ya kaɗa hanjin cikinsu, Mercy ta ce sun ɓoye ta ne a gidanta da ke Sabon tasha. Jin hakan yasa aka kwashe su gaba ɗaya zuwa caji ofis, Lukman ya bada umarnin aka cinnawa gidan wuta, gurin ƙonewar gidan sai fashewar wasu abubuwa da iface-iface suke ta ji marassa daɗin sauraro. ******* ******** A can Masarautar Bauchi na Abdulfahi na biyu kuwa labarin yadda ɗansu Almustapha yayi rayuwa a cikin duniya ya jijjiga tunaninsu. Anyi wa Baffah Yalleru kyauta mai girma cike da sakayyar alkhairi da alkhairai. Lokacin da zai koma gida Takawa ya haɗa shi da dogarai don a ga mazauninsu, aka raka shi har rugarsu ɗauke da sha tara ta arziki. Basu ɗauki al'amarin iyalan Mustapha da wasa ba, ran Takawa yayi mummunan ɓaci da jin abinda ya faru da ɗansa na cikinsa ƙarƙashin masautar Zazzau. Yasa magatakarda ya rubuta doguwar wasiƙa ya tada jakada tun daga Bauchi har masarautar zazzau akan abinda ya faru da kuma abinda yake buƙata ayi mishi yanzu. Sarkin Zazzau ma sam baiji daɗin abinda ya faru ba, domin akwai ƙawance mai girma a tsakanin masarautun biyu. Ya maida saƙon wasiƙar ban haƙuri sannan ya ce za a shirya komai kafin isowarsu. Shi ma Sarkin Zazzau ba tare da ɓata lokaci ba ya tada jakada har zuwa masautar kajuru da abinda yake buƙata a tabbatar mishi kafin isowar Sarki Abdulfatahi na biyu. Nan fa hankalin Sarkin kajuru ya tashi, domin abinda ya faru ko kusa bai samu labari makamancinta ba. Jami'an Soji da suke bada tsaro a nan ƙaramar hukumar kajuru saboda yawan rikice-rikicen da ke faruwa na ƙabilanci ya ɗiba ya haɗa su da dogarai suka tafi har ƙauyen Gefe dan a binciko labarin halin da Rebeccah da ƴarta Bilhaƙƙi suke ciki. Amma wani abin ban takaici basu sami wani gamsasshen bayani game da yarinyar ba, Rebeccah ma wai wasu da ba a san ko su waye ba sunje garin da sojoji kwanaki can sun tafi da ita. Jin zaluncin da suka aikata yasa Sojoji da umarnin Sarkin kajuru suka kama Zidane da duk abokansa da suke da hannu a cikin aikata al'amarin, Pastor Nuhu, Luka mahaifin Rebeccah aka wuce da su Kaduna aka watsar a State CID bayan anyi musu mugun duka an sauya musu kamanni, shi Zidane ma har da karaya a kafarsa ta hagu, da hannunsa na dama amma ko ta kanshi basu bi ba. Samun cikakken labarin rasa Rebeccah da ƴarta Bilhaƙƙi ne ya dakatar da zuwan Sarki Abdulfatah da jama'arsa. Yarima Mustapha kam ƙara shiga cikin tashin hankali yayi da tunanin wane hali iyalinsa suke ciki? A dole dai yake ƙoƙarin danne damuwarsa ganin yadda Takawa yasa aka tara manyan malamai suka fara karatun Alƙur'ani don yin sauka, da yin addu'ar duk inda iyalanshi suke Allah ya baiyana su da gaggawa. Ga kuma yadda ta ko wane ɓangare Iyaye da kakanninshi da sauran masu muƙami a masarautar kowa ƙoƙarin faranta mishi yake yi. "Ƙarya ne wallahi. Mustapha bazai taɓa dawowa ba, Na shuri ya tabbatar min yadda Mustapha ya bar nonon uwarsa bazai taɓa komawa ba haka yadda ya bar masarauta bazai taɓa waiwayarta ba..." Da sauri Chiroma da ya shiga ɗakin a lokacin ya haɗa hannuwansa duk biyu ya toshe mata baki hankalinsa a tashe, ƙasa ƙasa ya fara zabga mata masifa kamar tana jinsa "Ki yiwa girman Allah Yaya Safara'u ki rufa mana asiri ki daina wannan sambatun tona mana asirin da kike yi. Mustapha dai tabbas ya riga ya dawo masarauta ni da idanuna na ganshi. Gara ma ki farfaɗo ki daina wannan sambatun da kike yi ko zamu san na kwatanci. Idan ba haka ba kina ji kina gani mulkin da kika yi shekara da shekaru kina ƙwaƙwa da tanadi a kai zai suɓuce miki..." Wal kamar kawo wutan nepa ya ga ta buɗe jajayen idanunta duk biyu ta zuba su a kansa. Da sauri ya cire hannunsa a bakinta ya ja da baya a tsorace. Yunƙurawa tayi daƙyar ta miƙe zaune tana ciccije fuska, a hankali ta buɗe bakinta da yake mata wani mugun ɗaci kamar wacce ta kurɓi maɗaci ta ce "Chiroma da gaske ne Mustapha ya dawo masarauta?" Sai da yaja da baya sannan ya amsa ta "Ƙwarai da gaske ne Yaya. Ni ganau ne ba jiyau ba..." "A wani hali Muzaffar yake ciki?" Ta sake tambayarshi a cije tana wani jijjiga ƙafafu irin na bosawa "Har yau ba wani canji, ciwonshi sai gaba yake yi. Yanzu fa ɗakin da yake ciki ma indai ba alurar bacci aka zurkuɗa masa ba babu mai iya shiga. Hauka tuburan yake yi! A wani ƙaulin ma naji ƙishin-ƙishin Mai martaba ya bada umarnin a kaishi asibitin mahaukata na garinnan..." "Je ka karɓa min takardar sallama gurin likita. Yanzunnan!" Ta ƙarasa maganar haɗe da daka masa wani gigitaccen tsawa. A sukwane ya fice daga ɗakin kamar zai kifa saboda sauri. Ƙasa ta ƙurawa idanu har lokacin ƙafafunta basu daina girgiza ba. Sunƙi-sunƙin tashin hankali da damuwa ne danƙare a zuciyarta amma tana ƙoƙarin dannewa. Lallai Tauraruwa mai wutsiya ta cika hatsabibiya, tun bayan bayyanarta manyan masifu da damuwoyin da take tunanin ta shafe babinsu a doron ƙasa take ta tono mata. Wani abin mamaki a tarihin rayuwarta sai ga hawaye ya zubo mata shar... 'Ita Safara'u ƴar sarkin wokari yau ita ce take zubar da hawaye a kan Safiyya? Shekarunsu takwas da sarki Abdulfatahi ya auro Safiyya ƴar mitsitsiyar yarinya mai shekaru goma sha biyu. Safiyya ƙanwar matar wazirin Maru ne abokinsa, daga kai ziyara ya ganta ya ji yana so nan take kuwa aka aura mishi ita. Da farko ta ɗauki yarinyar ne a matsayin wulaƙantacciya masu haye a sarauta, ta ci gaba da zuba mulki yadda take so. Hankalinta bai fara tashi ba sai da taga Safiyya da ciki bayan shekaru biyu da auro ta, ita mai shekaru goma da auren mai martaba ko ɓatan wata bata taɓa yi ba. Duk yadda ta so zubda cikin Allah bai nufa ba sai da aka haifo Almustapha, tun daga nan ta ɗau karan tsana na duniya ta ɗora masa. Ido rufe ta fara neman hanyar da za ta kauda shi amma bokan da Jakadiya ta kawo mata na shuri ya ce dole ta jira sai ya shekara sha biyar. A shekaran da Mustapha ya ɓata Allah ya bata ciki ta haifi Muzaffar bayan uban magungunan da ta karɓa hannun malamai mabanbanta. Dukda ta haife shi tun yana ƙarami da ɗan matsala kamar wawa wannan bai dame ta ba, hausawa sunce da hanau gara mannau. Duk yadda za a yi dai shi ne babban ɗan mai martaba da bayan mutuwan sarki zai gaji mulki. Haka ta ci gaba da murza mulki a cikin gidan yadda take so, kowa a ƙarƙashinta yake, a zuciyar mai martaba ita ce gaba. Ita ce uwar Magajin sarki. Ɓullowar ciki kwatsam a jikin Safiyya bayan shekaru ashirin da ƴan kai da ɓatan Mustapha abin yayi mugun ɗaga mata hankali. Ita tasa Malamai sukai ta kwantar da cikin har lokacin haihuwar ya wuce sosai, ko an ɗaura mata ruwan naƙuda sai dai ta ƙaraci shan azaba ta wartsake ba haihuwa babu alamarta. Rayuwarta ta ko ina yayi haske, ta gama ganin gaggarumin hadarin ruwan farincikin cikan burinta a ko wane lokaci zai iya ɓallewa. Sai yanzu kuma kwatsam a ce komai ya tarwatse? haskenta da sannu sannu yana ƙoƙarin dusashewa? Bazai yiwu ba, tabbas baza ta taɓa bari haskenta ya dusashe cikin lokaci ƙanƙani haka ba. Tunda ta samu labarin Safiyya ta haifi ƴan biyu ta sume sai da ta kwana ta yini bata farfaɗo ba, ta farfaɗo ke nan kuma Jakadiya ta tare ta da labarin dawowar Mustapha, tsananin gigita yasa ta ƙara sumewa...' "Yaya ga takardar sallamar na karɓo." Nannauyan ajiyar zuciya ta sauke tare da katse duk wani tunani da take yi, ta yunƙura da ƙyar ta miƙe ta bi bayansa. BILHAƘƘI Tun isarta gidan ta samu irin tarbar da take buƙata daga gurin bayi da barorinta. Sai kai kawo suke yi suna shige da fice da yi mata fatan ƙara samun sauƙi. Hatta Mai babbar ɗaki (Umma mahaifiyar Takawa) ta aike Jakada na musamman a ce mata tana mata sannu da jiki da barka da dawowa. Uwar soro ma ta aika ɗan aike dukda ta ji haushin rashin zuwanta da kanta. Abinda ya bata mamaki kuma ya ɗaure mata kai shi ne ganin babu Takawa kuma ba ɗan aikensa. Daman tana ƙule da shi akan faɗa mata da Chiroma yayi tun da ta kwanta tsawon kwanaki biyu a asibitin sau ɗaya ya je duba halin da take ciki. Tana hakimce a falonta tayi ta zuba idon ganin Mustapha ya je kai gaisuwa gare ta amma shiru take ji, har aka idar da sallar isha'i. Dan haka ta aika gurin Fulani Safiyya a faɗa mata ga ta nan zuwa ganin jarrirai da murnar dawowar ɗanta Mustapha. "Amma Ranki ya daɗe kina ganin za ki iya zuwa?" Jakadiya ta tambaye ta tana mamakin ƙarfin halin da take gwadawa gurin ɓoye ɓacin rai da tashin hankalin da take ciki. "Eh zan iya. Gara inje Jakadiya. Annamimiyar nan ta riga ta tarwatsa duk wani aikin da Na shuri yayi min. Yanzu idanun kowa zai kasance a kaina ne, rashin zuwan nawa zai ɗarsa wani zargi a zuciyar ma su burin ganin baya na, ni kuma sam bana son haka. Ke dai ki tabbatar kin shirya yadda zan gana da Na shuri a daren yau, da zafi-zafi gara in tari komai kafin al'amuran su ƙarasa lalacewa." "To shi kenan Ranki ya daɗe. An gama! Allah ya iya mana da iyawarsa." Bata amsa addu'ar ba har ta fice daga falon cikin rakiyar bayi da kuyanginta ta nufi ɓangaren Sarauniya Safiyya. Duk yadda lungu da saƙo da ko wane kusurwa na cikin falon yake tashin daddaɗan ƙamshi sai wani huhhura hanci take yi tana basarwa kamar ta shaƙi wawwaran tusa. A hakimce ta zauna a kan kujeran kamar falonta, wani abu da tayi da ya bugi ran Sarauniya Safiyya ko da su Mummy suka kai mata jariran ƙin karɓarsu ta yi, ta wani yanƙwane fuska tana lelleƙa fuskokinsu daga nesa. "Na gansu! ku mayar da su kawai." Tayi maganar tana alamar kore su da hannu a wulaƙance. Ta maida hankalinta kan Safiyya ta ci gaba da cewa "Safiyya waɗannan yara ƴan firirit da ganinsu an ga kalar hanji. Yadda tsufa ya fara kama ki ma anya za su sami ruwan nono a jikinki?" Murmushin yaƙe tayi wanda ya fi kuka ciwo, da fari rasa abin cewa tayi tana ta jan a'uziyya a zuciyarta. Don yadda zuciyarta ke lugude da ɓacin ran action ɗin Fulani Taka da kuma irin baƙaƙen kalaman da ta sassaƙa mata idan ta buɗe baki tabbas zazzafar baƙa za ta faɗa, tsawon daƙiƙu casa'in zuciyarta ta fara sauka saboda addu'oin da take yi. Ta sake gyara zamanta akan kujerar da take kai tana ta sakin murmushi kamar ba ta da wani ɓacin rai "In banda abin Fulani Safra'u, haihuwar da ba ni na isa inba kaina ba ai kinga bani da ikon haifosu yadda kike so. Kuma cikin hukuncin mai kyauta da ƙari maimakon ya bani ɗaya ƙato sai ya bani biyu lafiyayyu. Allah da yayi wannan ikon a kaina ai kinga shi zai tsatso da ruwan nonon da zasu sha su ƙoshi. Kinga yau kwanansu biyu har yau basu fara shan madara ba saboda suna da wadataccen ruwan nono a jikin wannan tsohuwar dai da take zaune a gabanki..." Sallamar Mustapha da sa kanshi a cikin falon yasa ta maida hankalinta kanshi tana murmushi. Ita kuwa Fulani Safra'u bata gama farfaɗewa daga suman baƙaƙen kalaman da ake caccaɓa mata ba ta tsinci muryar Mustaphan a cikin falon. A hankali ta ɗaga jajayen idanunta ta mayar a kanshi. Gabanta ya yanke ya faɗi daram da taga ingarman jarumi lafiyayyen matashin da yake tafe a nutse har ya zauna kusa da ƙafafun Fulani Safiyya. Babu inda ya bar mahaifinsa kamar Abdulfatahi yayi kaki ya tofar. Kanta ne ta ji ya fara juyawa da ita kamar ana kaɗa ta a jikin fanka, nan ta fara gani bibbiyu kamar mai ciwon hawan jini, a sama ta tsinci muryar Safiyya tana cewa "El-Mustapha baka ga Ummanka a zaune ba? ta shigo ganin ƙannenka ne da murnar dawowarka. Duk da itama ta cancanci a je mata barka da murnar bayyanar babban ɗanta" Fulani Safiyya ta faɗa tana nuna mishi ɓangaren da Fulani Taka take zaune, fuskanta cike wani lallausan murmushi. Zuwa wannan lokacinta ranta fes dan furzar da kyawawan martani masu cike da hikima da tayi ya goge duk wani ɓacin rai da shigowar Fulani Taka ta ƙunsa mata. Hankalinshi ya maida inda take nuna mishi fuskarsa da ɗan murmushi. Ya ɗan sunkuyar da kanshi alamun girmamawa "Ranki ya daɗe barka da dare. Mun so mu shigo har can ɓangaren muyi miki sannu da jiki, amma sai muka yi tunanin mu bari ki huta zuwa gobe. Allah ya ƙara miki lafiya." "Ameen" Ta amsa a daƙile kamar mai ciwon haƙori, ƙirjinta sai lugude yake yi. A muryarsa ma cike da kwarjini sak irinta Mahaifinsa Abdulfatahi. Jin da tayi baƙin ciki na neman karta da sauran kwana ga yadda idanunta suka ciccika da hawaye, baƙin ciki ƙarara baiyane a fuskarta yasa da sauri ta miƙe da nufin ficewa ba tare da ta yi musu sallama ba. Taga-taga tayi kamar za ta kifa ta yi saurin dafa kujera tana jin saukar muryar Mustapha a kunnenta kamar yana doka taɓarya a ƙirjinta. "Subhanallahi. Hattara dai Umma." A sukwane ta fice daga falon tun kafin damuwa da baƙin ciki su ci ƙarfin zuciyarta su burtso waje, asirinta ya tonu ta hanyar fashewa da kuka. "A huta gajiya Ranki ya daɗe." Tsananin ruɗewa da ɗimauta ya hana ta gane a cikin su biyun wa yayi mata wannan sallamar mai kama da ta rainin wayau? ****** ******* Tsawon awa biyu ke nan da Dr. Bilyaminu ya tabbatar mishi da cewa a ko wane lokaci za ta iya farfaɗowa. Amma har lokacin shiru kake ji, babu ma wani alamu na za ta farfaɗo. Hankalinsa idan yayi dubu ya tashi, ga noses sai shigowa suke suna tambayarshi bata farfaɗo ba? tun yana iya amsa musu da baki har ya koma sai dai ya ɗaga musu kai. Daga ƙarshe ma shiru yayi musu yayi tagumi ya zuba mata idanu. Yana zaune ne a kan wani kujera gaf da gaf da gadon da take kwance. Ta rame ta yi fiyau a yini biyu kawai da faruwar komai. Sashin hannun Oga ne ɓaro-ɓaro a wuyanta, ita kaɗai ta san mugun azaban da ta sha a hannunshi kafin Allah ya kai su gurin su ceceta. Hannunta da babu ƙarin ruwan ya kamo ya riƙe ya zubawa hannun ido, gefen gadon da take kwance ya raɓa ya zauna yana ƙara kallonta. Bisa ga mamakinshi sai ga hawaye shar daga idanunshi, kifa kanshi yayi a kan gadon gefen cikinta yana jan wani irin nishi sauri-sauri mai kama da shessheƙan kuka. Duk tunani da addu'arshi ya tattara ne ga roƙon kada Allah yasa ta mutu ta barshi ba tare da ya gwada mata lagwadar soyayyar da ya daɗe yana mata tanadi ba. "Sev gilim..." Ya ji ta kira sunanshi kamar a mafarki. Da sauri ya ɗaga kai yana kallonta idanunshi jajur, fuskarsa ƙarara bayyane da mugun tashin hankali. Lura da yayi bakinta yana ɗan motsawa amma bata buɗe idanunta ba yasa ya matsa da kunnensa sosai kusa da bakinta. Ya ɗan matsa hannunta da ɗan ƙarfi yadda za ta ji a jikinta "Tatlim ga ni kusa da ke! Me kike so uuumm?" "Ina... son... ka...!" Ta faɗa a hankali kamar mai raɗa, jimlar kalaman suka fito a rarrabe kamar mai koyon magana. "Nima ina son ki Tatlim. Dan Allah ki tashi kin ji? kar ki mutu ki barni kin ji? Ga Ummanmu can ita ma tun ɗazu take ta son ganinki..." Buɗe ƙofar ɗakin da shigan Dr. Bilyaminu cikin ɗakin hankalinsa a tashe yasa shi ɗaga kanshi daga gurin fuskarta ya kalle shi, shi kuwa likitan ganin alamun ta farfaɗo yasa shi sauke ajiyar zuciya. "Alhamdulillahi. Ai ni kira na suka yi wai har yanzu bata farfaɗo ba. Wallahi hankalina ya tashi Maheer..." "Ni naga tashin hankali ba kai ba Dr. Alhamdulillahi dai tunda ta farfaɗo." "Allah shi ne abin godiya." Gurin ruwan da ake ƙara mata ya je ya fasa wani ruwan allura ya zuƙa a sirinji ya tsira a cikin ruwan. "Lafiya in Allah ya yarda, za ta ƙara farfaɗewa yanzu. Sauƙi gaba ɗaya kuma ka san dai sai a hankali. Bari in koma gida, sai zuwa dare. Daman rashin farfaɗowar da suka ce min bata yi ba shi ya dawo da ni yanzu." Sallama suka yi likitan ya fice daga ɗakin, shi kuma ya koma bakin gadon ya zauna a kusa da ita. Cikin hukuncin Allah kuwa minti ashirin tsakani ta farko sosai, amma a hankali take iya magana. Sosai take mishi kuka saman gurin kafaɗanta na dama yana mata ciwo, da ta yi yunƙurin taɓawa ma sai taji kamar babban ciwo ne a gurin. "Ki yi haƙuri Babe, ciwo ne da nasa aka ji miki jiya yau kuma na sa aka ƙara farke ɗinkin. Baki yi mamakin yadda aka yi muka bibiye ki har gurin su Oga ba?" Kallonshi ta yi da mamaki, sai yanzu ma wannan tunanin ya faɗo mata a ranta, yunƙurawa tayi za ta tashi zaune da sauri ta koma ta kwanta tana runtse ido. "Sannu Tatlim!" Ya faɗa mata a tausashe, ita kuma ta gyaɗa kai tana yunƙurin yin murmushi. Tarairayarta yayi a jikinsa yasa fuloli biyu a bayanta sannan ya jinginata yadda baza ta ji zafin sosai ba. "Kinga shekaran jiya tun kafin mu dawo daga bauchi na yi ma Lukman bayanin duk irin abubuwan da suke faruwa, shi kuma ya sama mana mafitar da na amince da shi. Jiya da na baki lemon nan kika sha maganin bacci ne a ciki, da wannan daman muka yi amfani Lukman ya ba Dr. Bilyamin wani ɗan ƙaramin na'ura ya tsaga kafadarki yasa a ciki sannan ya maida gurin ya ɗinke. Allurai yayi miki guda biyu da ko da kin tashi sosai zai kashe miki zafin ciwon. Sai kuma muka yi sa'a ma ko da kika farka tashin hankalin da kike ciki na son ki miƙa kanki gurin su Madam Mary don ki cece Mahaifiyarki bai barki kin ankare da wani ciwo a jikinki ba. Amfanin wanna na'urar shi ne duk inda kika za a iya gano wa, sannan kuma duk maganganun da kike yi ke da wasu za a iya jin duk abinda kuke cewa. Sosai munji tsoro da muka ji wasu suna cewa za a caje ki don ganin ko kin taho da wani abu a jikinki. Cikin hukuncin Allah kuma masu cajewar har suka gama basu yiwa Madam maganar ciwo da ɗinkin da ke kafaɗarki ba. Da wannan damar muka yi amfani gurin bin diddiginki da kai miki ɗauki." Ƙuri tayi masa da idanunta, fuskanta ɗauke da murmushi, zuciyarta cike da jin daɗin wannan tsananin ƙaunar da mijinta yake mata. Ta sakar mishi murmushi kawai, wani godiyar ya fi ƙarfin baki ya baiyana sai dai a bar kaza cikin gashinta. "Ina ita mahaifiyar tawa? ko su... su kashe..." "Tana wancan ɗakin tare da Ummee, ita ma a galabaice aka ɗaukota a inda suka ɓoye ta. Amma dai yanzu sosai jikinta da sauƙi, tun ɗazu ma take ta tambayar ina kike..." "Da gaske? shi ne baka kai ni gurinta ba tun ɗazu?" Tayi rau-rau da idanu kamar za ta fashe da kuka, nan fa jikinta ya fara rawa tana ƙoƙarin sauka daga kan gadon don zuwa gurin mahaifiyarta. Abin dariya abin tausayi ƙarfen ƙarin ruwan ya sunguma da hannu ɗaya ya tallafe ta a kafaɗarsa na dama bayan ya saka mata hijabi suka fice daga ɗakin don zuwa ɗakin da aka kwantar da Rebeccah. A kofar ɗakin suka ci karo da Luƙman shi kuma yana ƙoƙarin buɗe ƙofar, baki buɗe yake kallonsu da mamaki a fuskarsa ya ce "Ina zuwa haka?" "Ta matsa ita sai na kaita ta ga Mum ɗinta." "To madallah! kawo ƙarfen ƙarin ruwan in riƙe maka" Ba musu kuwa ya mika mishi. Duk inda suka wuce haka ake binsu da kallon mamaki baki buɗe har suka isa ɗakin Rebeccah... ******* ******** A wannan ranar, a wannan lokacin, a wannan tsakankanin, duk wadda ya ga yadda UWA da ƳAR suka yi da haɗuwar juna bayan tsawon shekaru goma sha tara da rabuwarsu dole mai imani da tausayi ya zubda hawaye. Gaba-ɗaya jikkunansu rawa yake yi, bakunansu kyarma yake, hawayen idanunsu bulbulowa suke yi, da suka kasa cewa komai ga junansu sai shafa fuskokin juna suke yi don jin da gaske wai yau Allah ya ƙaddara haɗuwarsu ne??? kamar haɗin baki sai suka fara sharce wa juna hawaye, a gare su gaba ɗaya haɗuwarsu ta kasance abu ne da basu taɓa tsammani ba. Ummee da take gefe sai sharce hawayen tausayinsu take yi, Lukman da Maheer kam ficewa suka yi daga ɗakin saboda raunin da zukatansu ta fara yi, a ƙarshe Ummee ma bin bayansu ta yi. Kaman jira take yi a fice a basu guri ta buɗe bakinta a raunane tana kuka tana dariya haɗe da tattaɓa jikinta da yatsa, ta fara magana da turanci "Da gaske ke ce? Babyn da na haifa a cikina na kaiwa Mama Vero? ina kika shige duk tsawon wannan lokacin???" Bilhaƙƙi dai ba baka sai kunne, hawaye sunki tsayawa ga murmushi ya ƙi ɗaukewa daga fuskarta, ƙarshe ma kwanciya tayi a jikin mahaifiyar tana ta sassauke ajiyar zuciya masu sanyi, mintuna kaɗan wani daddaɗan barci da tun da take bata taɓa yin irinsa ba ya kwashe ta a jikin Inna uwa mai bada mama😂🥰🥰 A haka su Maheer suka koma ciki suka same su, duk sai suka yi murmushi. Shi kuwa Maheer har da wani ɗan sosa kai alamun ya ji kunya. "Kun ganta ko? Haka kawai ta yi barci." Rebeccah ta faɗa tana kallonsu da murmushi, hannunta na gefen fuskar Bilhaƙƙi sai shafa mata kumatu take yi kamar wata baby. ******* ******* Ta kasa zaune ta kasa tsaye, tun da duhun dare ya fara shiga sai safa da marwa take yi tana jiran ganin ta inda su Jakadiya za su ɓullo. Jefi-jefi ƙirjinta yake bugawa ɗas! ɗas!! kamar alamun wani mummunan abu yana shirin faruwa da ita. Hankalinta ne ya ƙara ɗugunzuma, hannu biyu ta ɗaga sama idanunta ciccike da hawaye take roƙon Allah ya tsare ta da sharrin Mai wutsiya, babban burinta da fatanta bai wuce Na shuri ya samu shiga lafiya ta karɓi magunguna ba tare da wani mummunan abu ya sake faruwa da ita ba. Ƙarar buɗe ƙofar yasa ta juya a sukwane da burin haɗa idanu da Jakadiya, saɓanin ita sai ta haɗa idanu da ɗaya daga cikin bayinta. Kafin baiwar ta ce komai ta daka mata wani gigitaccen tsawa "Lafiya? Ban ce kar wacce ta shigo min nan idan ba Jakadiya ba?" "Afuwan Ranki ya daɗe. Tuba nake. Daman Takawa ne ya aiko yana son ganinki da gaggawa a ƙaramin falon ganawa." Baiwar ta faɗi haka cikin rawan jiki da rawan murya. Ƙirjinta ne ya buga da ƙarfi! Ta zazzare ido a tsorace. "Takawa kuma? Me zai sa Takawa ya neme ni a darennan?" "E Ranki ya daɗe, nima ban sani ba." Tsananin ruɗewa yasa bata san a fili tayi maganar ba sai da ta ji baiwar ta amsa mata. Alkyabbarta ta janyo ta sanya a jikinta, da muryar dakewa tana ƙoƙarin daidaita nutsuwarta ta ce da Baiwar "Kar a bar kowa ya shigo min nan in dai ba Jakadiya da ƴar'uwarta ba. Ku faɗawa Jakadiyar na je gurin Mai martaba yanzu zan dawo." "To Ranki ya daɗe, an gama.!" "Tana tafe tana saƙe-saƙe har ta isa kusa da ɓangaren Uwar Soro dan a yi mata ison shiga ciki, irin kallon da ta ga tana bin ta da shi da irin amsar da ta bata ne ya ƙara kaɗa mata ƴaƴan hanji, ta tabbatar ba lafiya ba. "Hakima mundiya ai yau ke kam ba kya buƙatar wani iso, ki shiga kawai Takawa yana can yana jiran isarki." A ɗarare take har ta shiga cikin falon bayan anyi mata izinin shiga ciki. Gabanta ya yanke yayi wani mugun faɗuwa da ta ga Takawa da Liman a zaune, fuskokinsu duk babu walwala. Yadda suka amsa mata gaisuwa wani sasakai yasa jikinta ya gama yin sanyi gaba-ɗaya, kawai sai ta sadda kai ƙasa cike da shahadar ƙuda. "Safra'u! A gidannan muna sane da abinda kika daɗe kina aikatawa fa, da kuma abinda kike yunƙurin aikatawa a yanzu. Kina ga har yanzu bai kamata ki nutsu ki san Annabi ya faku ba duk bayan ababen da kika aikata marassa daɗi da kuma abubuwan da suka biyo baya?" Ɗif ta ɗauke wuta tayi suman wucin gadi. Shi ke nan! Ta faru ta ƙare wai anyi wa mai dami ɗaya sata. Daga jin irin maganganun da Takawa yake yi ta san Mai wutsiya ta ƙarasa lalata komai. Da Takawa ya ji shirun yayi yawa ranshi a ɓace ya ci gaba da magana "Kinyi shiru baki ce komai ba Safra'u? ko da yake ba musu muka kira ki muyi da ke ba. Muna da ƙwararan hujja a hannunmu kan abinda kika daɗe kina aikatawa. Safra'u bazan hana ki ba, sannan bazan ce ki yi hakuri ki rungumi komai a yadda Allah ya ƙaddara miki ba. Amma ina so ki tuna da wani abu guda ɗaya. A cikin masarautar nan mun ɗaukaka ki, mun gwada miki ƙauna mai yawa. Mun baki duk wani girma a matsayinki ta matar fari a gare mu. Mun mallaka miki mulki da yin duk abinda kike so dukda a wasu lokutan munsan kuskure kike aikatawa. Bamu taɓa dakatar da ke ko mu kunyata ki a cikin mutane ba. Duk wannan gatan da muke gwada miki ashe kin daɗe kina burin tozarta mu da son ganin bayanmu? Safara'u mulki hauka ne da za ki dinga gwada son zuciya da zalunci irin wannan? Ko kinsan mun san ke kike da alhakin ɓatan El-mustapha daga masarautannan? Ashe ke ce da alhakin sa wa a hana Safiyya haihuwa duk tsawon lokacinnan?Ashe duk munanan abubuwan da suke ta faruwa da mu ke ce a bayan aikata su?" Ya haɗiye wani zazzafan miyau idanunshi a ƙanƙance, ya ci gaba da magana ranshi na ƙuna. Daman kunsan mai haƙuri bai iya fushi ba "A bayan duk abubuwannan nan kuma Allah ya nuna miki iyakarki ta hanyar kawo ƙarshen duk wani mummunan abu da kika taɓa aikatawa a baya shi ne kike ƙoƙarin sake aikata wani mummunan abun? To bari in faɗa miki wata magana da baki sani ba, Jakadiya, bokan da kika tura ta taho da shi, ƙaninki Chiroma da ya kasance abokin cin mushenki duk suna nan a tsare a hannunmu. Kici gaba da yin abinda kika ga shi ne miki dai-dai kuma shi zai sama miki ci gaba Safra'u. Ki ci gaba da yi!Allah yana ji kuma yana gani, shi zai ci gaba da kare mu daga duk wani mummunan jifa da sharri da kike nufinmu da shi. A yanzu arzikin Mal Liman kika ci da yake da matsayin kamar mahaifi a gare ki, a karo na gaba muddin kika bari muka sake karon batta wallahi za ki sha mamakin irin mummunan matakin da za mu ɗauka a kanki." Yana gama faɗin maganganun da suke cikinshi ya gyara kishingiɗa idanunsa a runtse, sai jan inna lillahi yake yi saboda tsananin ɓacin ran da zuciyarsa take ciki. Daga nan Liman ya fara magana shi ma ransa a ɓace, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba saboda ɓacin rai. Ya rantse mata da Allah wallahi muddin ta sake aikata wani abu na son zuciya ko ɗan ƙiris ne a masarautar nan shi da kanshi zayyi tattaki har can masarautarsu ya faɗawa Mahaifinta duk abinda take aikatawa. Daga ƙarshe kuma ya ɓuge da yi mata nasiha tare da nusar da ita muhimmancin yarda da ƙaddara mai kyau da mare kyau. Ita dai Fulani Taka kuka da majina kawai ta ke sharɓa tana gogewa da gefen alkyabbar jikinta, ta ji kunya ƙwarai, kunya ba kaɗan ba. Da wasa bata taɓa tsammanin asirinta zai iya mummunan tonuwa a cikin ƙanƙanin lokaci kamar haka ba. Tsamo-tsamo tayi a gabansu kamar kazar da aka sheƙawa ruwan zafi. Daga ƙarshe cikin tsawa da murya mai cike da tozarci da muzantawa Takawa ya ce ta ɓace masa da gani. Kuma ya kafa mata sharaɗin kar ta kuskura ya sake ganin gilmawarta a idanunsa matuƙar ba shi ne ya neme ta ba. Duk abinda za ta yi ta tsaya a can iya sashenta. Bata san yadda aka yi ta kai kanta ɓangarenta ba, kawai tsintar kanta tayi a turakarta, da mugun sauri ta danne ƙofar ta kulle da bayanta, nan ta zube a gurin tana sharɓan kuka kamar wata sabuwar kamu. Tattausan kalamai na rarrashi da ban baki Mal Liman ya ƙara faɗawa Mai martaba, sannan yayi mishi sallama shi ma ya fice daga falon ya nufi gidansa. Shiru Takawa yayi yana tunani, sai mamaki yake yi na yadda yayi saken da Safra'u ta daɗe tana cin karenta babu babbaka ba tare da saninshi ba. Ko jiya Allah ne yasa zai san abinda ke faruwa ta hanya Baffa Ilyassa'u (Dan'uwan Baffa Yalleru). 'Shi ya je har fada ya nemi ganawa da shi bayan ya sanar da ko shi waye. A wannan ganawar ne fa ya faɗa mishi duk munanan abubuwan da suke faruwa Uwargidansa ke da alhakin aikata su, da taimakon Jakadiyarshi, da kuma ƙaninta Chiroma. Yace mishi yasa idanu sosai dan har lokacin bata haƙura ba. Sai kuma ya kawo wasu magunguna ya bashi ya faɗa mishi yadda zaiy amfani da su shi da iyalansa gaba daya. Ya ƙara da cewa in dai suka yi amfani da maganin dai-dai kamar yadda ya ce in Allah ya yarda ba dai mutum ba sai dai Allah. Da wannan bayanin yayi amfani yasa aka titsiye Jakadiya da Chiroma, ya rantse da Allah idan basu faɗa mishi gaskiya ba zai sa Hauni ya tsire su a gaban jama'a. Tsoron mutuwa yasa cikin kuka da matsanancin tashin hankali duk suka warware mishi tuggun da suka daɗe suna ƙullawa a tsakaninsu.' ******* ******* Ido waje yake kallonta bayan ta gama basu labarin tarihin ko ita wacece. Ya nuna ta da yatsarsa manuniya bakinshi na rawa "Da gaske kike yi? ke ce Rebeccah matar Mustapha? kuma wannan ita ce Bilhaƙƙin da ya barki da ita tun tana jaririya?" Gyaɗa kai ta yi tana mamaki, ita ma sai jikinta ya fara tsuma bayan ta yi tunanin ko dai ya san Mustapha ne. "Eh! wallahi da gaske nake yi. Babu ƙarya ko ɗaya a cikin labarin da na baku." Gemai-gemai da shi sai ga hawaye sun zubo masa shar! nan yasa gwuiwoyinshi a ƙasa yana sujudush-shukur. Iyalanshi dai sai binshi da kallon mamaki suke yi har ya ɗago daga sujudar. Hannun Bilhaƙƙi ya ja ta koma kusa da shi "Ashe shi yasa tun da na fara ganinki nake jin tsananin ƙaunarki kamar ƴar da na haifa a cikina? ke ƴata ce Bilhaƙƙi. Da gaske ke ƴata ce ta tashin alƙiyama. Mahaifiyata Hajja matar wazirin Sarkin Maru ita ce tasha nono ta sake wa mahaifiyar Mustapha Inna Safiyyah matar sarkin Bauchi da muka je gurinta da ke kwanakin baya." Cikin rawan jiki da tsuma ya shige turakarsa ya ɗauko wasu tsaffin hotuna guda uku, Bilhaƙƙi ya miƙawa ɗaya kafin ta amsa da sauri Rebeccah ta fisge "Wannan ɗan yaron da yake riƙe da hannuna shi ne Mustapha." Hoton take ta kallo, ta gane Malam ne saurayin da yake tsaye a cikin hoton, sai kuma wani ƙaramin yaro da bai wuce shekaru huɗu ba, babu riga a jikin yaron aka ɗauki hoton. Abinda ta gani a ƙirjin yaron yasa ta miƙe tsaye "Exactly akwai irin wannan zanen a ƙirjin Musty, kuma ita ma Baby Bilhaƙƙ akwai shi a ƙirjinta. Infact ma shi da hannunsa yayi mata zanen kafin ya mutu..." "Wa yace miki ya mutu? Ai yana nan a raye. Ɗanuwanki bai samu nasarar ƙona shi ba saboda wani bawan Allah da yaje ya cece shi kafin a cinnawa gidan wuta..." Tsananin ruɗewa da gigitar jin Mistyn ta yana raye bai mutu ba yasa ta tafi Suuuu a sume za ta zube a ƙasa, da sauri Ummi da ta ankare da abinda ke shirin faruwa ta tare ta suka zube ƙasa gaba ɗaya. BILHAƘƘI Tunda ta farfaɗo jikinta babu inda ba ya kyarma, sai tattakurewa take yi kamar mai jin sanyi. Hannunta na dama riƙe da na Ummee ta ke ta maimaita mata tambayar "Don Allah Hajiya da gaske Musty yana raye? idan yana da rai to zaman me nake yi a nan? ku kaini gurinsa dan Allah. Akwai maganganu da dama da ya kamata in tattauna tsakanina da shi." Ummee cike da tausayi ta ke tausarta da kyawawan kalamai na kwantar da hankali. Shi kuwa Malam ficewa yayi daga falon don tsananin tausayinta, bayan yayi mata alƙawarin gobe da sassafe idan sun wayi gari lafiya za suyi sammakon zuwa Bauchi dan ta ga Mustafanta. Yadda ta ke gyaɗa kai da sauri kamar ƙadangaruwa tana mishi godiya da addu'ar Allah ya shirya mishi zuri'arshi shi ne abinda ya ƙara karyar mai da zuciya. Dauriya da jarumtakar ɗa namiji ne kawai ya hana shi ya zubar da hawayen tausayinta. Bilhaƙƙi kuwa tunda ta ga Rebeccah ta farfaɗo lafiya gefe guda ta koma ta zauna sai wani murmushi ta ke yi ita kaɗai, tunaninnika ne kala daban-daban a zuciyarta. 'Ashe dai ita ma yarinya ce kamar ko wace ƴa mai cike da nagartaccen nasaba? Ita Billhaƙƙi ce jikar babban sarki kamar Abdulfatahi da Sarauniyya Safiyya? Ga mahaifiyarta Rebeccah a raye kusa da ita, ga mahaifinta can Mustapha ɗan Sarki gobe za ta je ta haɗu da shi. Iyalan Malam da ta ke tsanani ƙaunarsu a ranta ashe ƴan'uwanta ne na jini makusanta? Kai ita kam farin ciki yayi mata yawa...' Fakar idanun mutane Maheer yayi ya ja hannunta da mugun sauri suka fice daga falon, ba ɗakin Ummee ya nufa da ita ba. Can ɗakinsu na ƴanmata ya zagaya da ita. Suna shiga ciki ya ga Saudat ta barbaza littafai a gaba da alamun karatu take yi. Idanu ya buɗe mata sosai tare da balla mata harara "Dallah Malama fice mana daga nan." Sum-sum ta kwashi takardunta ta fice daga ɗakin, sai satar kallon Bilhaƙƙi take yi tana gimtse dariya har ta bar ɗakin. Yana ganin ta fita ya janyo ta tsam ya matse ta a ƙirjinsa da ƙarfi yana sauke ajiyar zuciya. "Sevgilim za ka murƙusani." Ta faɗa da muryar da ke baiyana tana jin zafin riƙon da yayi mata. Sassauta riƙon yayi sannan ya ja ta suka zauna a gefen gadon. Kifa kanshi yayi a cinyoyinta yana sauke ajiyar zuciya sannu-sannu kamar mai shirin bacci. Ƙura wa kanshi idanu tayi tana murmushi, kwantaccen gashin kansa mai kama da na fulani yaja hankalinta sosai. Sai ta miƙa hannu tana shafa gashin a hankali, hakan da ta yi sai ya ƙara kashe mishi jiki. Da shaƙaƙƙiyar murya ya ce "Tatlim! Ina buƙatarki. Yau ɗaya pls ki zo muje ki taya ni bacci, kinji?" Narai-narai ta yi da idanu kamar za ta saka kuka, ina yaushe za ta iya bin miji ta ƙyale Mommanta Rebeccah? Jin tayi shiru bata ce komai ba yasa shi ɗaga kanshi daga jikinta suka ƙurawa juna idanu. Idanunshi sun ɗanyi ja kaɗan, fuskarsa nannarke da ɓoyayyiyar damuwa. Ita kuwa yanayin tsoro da firgici shi ya fi bayyana a idanunta, sai wasu ɓoyayyun hawaye da suka kwanta a kwarmin idanunta na tsananin ƙaunar mijinta. Janyota ya sake yi ya rungume tsam, a hankali ta ji yana zage zip ɗin rigarta ta baya. Bata yi yunƙurin hana shi ba, sai ta runtse idanu tana jin wani irin waiwayi a bayan kamar yana mata tafiyar tsutsa. Tana ji tana gani har ya zare rigar gaba ɗaya a jikinta, ya ɓalle ɓallin bra ɗinta ya zaunar da ita a cinyarsa, hannu ya kai cike da shauƙi da sha'awa ya shafi zane-zanen. Shi masifar kyau suke masa a idanunsa, ga kuma ɗaukar hankalinsa da suke yi tun ranar da ya fara gani a jikinta. "Amma gobe idan munje can babu wanda zai ce ki buɗe nan ya ga zanennan ko?" "Haba dai!" Tayi maganar a shagwaɓe. Kafin ya ce wani abu cikin kunya ta kwantar da kanta a ƙirjinsa ta ci gaba da cewa "Kai kaɗai za kaita gani Sevgilim. Nan ba gurin ganin kowa bane, naka ne kai kaɗai." Tsam ya ƙara riƙe ta, da baya ya kwanta a kan gadon ita kuma ya kwantar da ita a ƙirjinsa. Hannu biyu yasa ya riƙeta kamar yana tsoron wani zai ƙwace mishi ita. Da yake yana tare da gajiya a jikinsa nan da nan wani daddaɗan bacci ya fara fisgarsa. "Kin amince muje ki taya ni kwanan?" "A'a ni dai! Zan kwana kusa da Mamana." Ta faɗa a hankali. Shiru yayi bai sake cewa komai ba, can sai ya miƙe zaune har lokacin tana jikinsa, rigarta ya mayar mata ya sauketa ta zauna a gefenshi. "Zan tafi gida. Akwai abinda kuke buƙata kafin in wuce?" A sanyaye ta gyaɗa mishi kai alamar a'a, tausayi ya bata sosai. Da ganin yanayinsa yana buƙatar jinta a kusa da shi, to amma ya zata yi mishi? ita ko babu Mamanta ma baza ta iya barin Ummee ta bishi zizi su kwana a hotel ba. Ya jira kawai har ayi bikinsu. Tana ji tana gani ya fice daga ɗakin fuskarsa cukwuikwuiye da damuwa. ****** ******* A lalace cike da sanyin jiki haka yake tuƙa motar har ya isa gidan. Ko da yayi sallama ya shiga ciki damuwar da yake ciki ne ya hana ya karanci yanayin da fuskokinsu suke ciki. A sakarce duk su biyun suka yi mishi sannu da zuwa, basu jira amsawarshi ba suka ƙara mayar da hankali kan kallon da suke yi. Shi ma yana amsawa ya nufi ɓangarensa, ko da ya shiga ɗakin cike da kasala ya zauna a gefen gado yana jiran shigowar Surayya ta haɗa mishi ruwan wanka, tunda ranar girkinta ne. Ganin shiru bata shigo ba kawai sai ya faɗa banɗaki ba tare da wani damuwa ba. Jikinsa a mace yake, ga wata muguwar kasala da gajiya da take nuƙurƙusarsa. So yake ya kwanta da wuri saboda tafiyar da take gabansu gobe. Yana fitowa ya ga Surayya tsaye ƙyam a tsakar ɗakin, ya kalle ta kawai, ita ma shi ɗin take kallo. Sai a lokacin ya lura da kwantaccen damuwar da ke kan fuskarta, amma saboda bai shirya fuskantar wata damuwar ba bayan wacce yake ciki mazewa yayi. Ya watsa mata taurarin murmushi ya wuce ta ya nufi gefen gado ya zauna, hannunsa riƙe da ƙaramin tawul yana goge ruwan kansa da kafaɗunsa. "Idan ka gama ga abinci can yana jiranka..." "A'a Alhamdulillah! na ƙoshi a gidan Malam." Ƙanƙance idanu tayi cike da masifa, ɓacin ranta sai ƙara hauhawa yake yi, kwanaki biyar kenan tun da ya tsiri tafiya bauchi har yaje ya dawo yana wani wofintar da su a wulaƙance. "Ki shirya min kayan tafiya gobe da su Malam za mu sake komawa Bauchi..." "Bauchi kuma? bayan tafiyar da kuka yi rannan?" Ta tambaye shi cike da gatsali da rashin kunya. "E" Ya amsa ba tare da damuwa da yanayin yadda tayi maganar ba. "Madallah! To muma mu shirya ka tafi da mu ke nan...?" "Ina ɗin? A kan me zan tafi da ku?" Ya tambaye ta yana kallonta da mamaki, zama sosai ya gyara a gefen gadon yana fuskantarta da jiran jin da wacce ta zo. Ya lura da take-takenta tsiya take ji, shi kuwa zai sauke mata duk wani abu da yake damunta. "Can Bauchin, ko kana tunanin bamu san wancan tafiyar da Amaryarka ka tafi ba? Maheer wai me kake nufi da mu ne? Idan ka fara gajiya da mu ne tun kafin Amaryarka ta shigo gidannan ka sanar damu kawai. Ni gaskiya bazan iya zaman wulakanci da bandaro ba. Atoh! Tafiya ce ko dai gobe ka tafi da ni ni mai girki ko kuma kaima ka fasa tafiyar ka zauna a gida ka bani hakkina." Tana zuwa nan a maganganunta kawai sai ta fashe da ƙaƙƙarfar kuka ta zube a tsakar ɗakin tana rerawa kamar karatu. Shi kuwa kallonta kawai yake yi da mamaki, ashe Surayya ma fitsararriya ce bai sani ba. Lallai ya yarda ko wane gauta ja ne sai dai in bai sha rana ba. Wani ɗan tunani da ya gilma a zuciyarshi yasa shi sakin murmushi, ya fara magana a tausashe "Kina tunanin ko da muka je can ɗin wani hutawa muka yi ni da Tatlim? Hmmm! Rashin sani ya fi dare duhu. Any way! Shi ke nan! Ki faɗawa Rabi ta shirya ke ma ki shirya goben mu tafi gaba ɗaya. Ku shirya da wuri don Malam ya ce tafiyar sassafe za mu yi." A hankali ta ke rage sautin kukan kamar ana control ɗinta da remot har ta ɗauke sautin kukan gaba ɗaya. Ta miƙe tsaye bakinta a gaba ta fice daga ɗakin tana gunguni "Oho dai! Idanma tsananin wahala kuke sha a can ɗin muma a je damu mu sha tare." Shi dai ya raka ta da idanu har ta fice daga ɗakin gaba ɗaya. Murmushi ne ya sake kuɓuce mishi. "Mata? Hmmm! Sai a barsu da halinsu." Shiryawa ya ci gaba da yi har ya gama shirin bacci gaba ɗaya ya bi lafiyar gado, yayi mamaki da har ya kwanta bata shigo ba. Da yake yana tare da gajiya bai bari yayi zurfi a tunanin ba nannauyan bacci yayi awon gaba da shi. A can babban falo kuwa Surayya da Rabi sun daɗe suna shirya yadda idan aka yi tafiyar za su haɗu su cusgunawa Billhaƙƙi. "Ki ƙyale shegiyar yarinyar nan, da ƙafafunta sirara kamar ragowar amai da gudawa. Har fa yana wani ce min ba daɗi suke ji a can ɗin ba. Kila ko yana tunanin bamu san ƙanwar kakansu ita ce matar sarkin bauchin ba. Don Allah ina wata wahala da za a sha a kaiwa matar sarki ziyara?" "Ke ma dai Surayya kamar baki san rainin wayau na ɗa namiji ba? Ai tsabar dabara ce yake neman shirya miki. Yayi tunanin ko za ki ce mun hakura da tafiyar. Ai yau kam kin gama burgeni, aikinki yayi kyau, daman ke ce kike mishi lakwa-lakwa yana taka mu yadda yake so. Tuntuni da mun haɗa kai ai wallahi da ba haka ba..." "Ai yanzu duk wani batun rikici a tsakaninmu ya ƙare Rabi. Tunda an kawo wata rikicin me za muyi? mu haɗa kai mu kore ta tukunna sai mu cigaba da bugawa a tsakaninmu." Dariya suka kwashe da shi gaba ɗaya, suna tuna yadda da suke yawan faɗa a tsakaninsu kamar masu ganin hanjin juna. "Ke muje fa mu shirya kayanmu mu kwanta, dan ya ce gobe tafiyar sassafe za a yi inji Malam." Daga nan suka yiwa juna sai da safe ko wacce ta nufi ɓangarenta, zukatansu cike fal da farin ciki. ******* ******* Sauri-sauri ta shirya saboda kusan duk an gama shiryawa ita ake jira, ba wani kwalliya mai yawa ta yi a fuskarta ba, ɗaya daga cikin dogayen rigunan da ya sai mata kwanakin baya ta zura ta naɗe mayafin. Sosai ƴar doguwar fuskarta tayi kyau, dukda dai ta ɗanyi fayau alamun ramewa saboda rashin lafiyar da ta yi, don har lokacin wuyanta da kafaɗanta basu gama warkewa ba. Tana fita falon tayi turus ta tsaya tana kallonsu, suma ɗin ita suke kallo tunda fuskokinsu na saitin ɗakin da ta fito ne. Wani ɗan murmushi tayi da sassarfa ta nufi gurin Aisha matar Luƙman. "Aunty Aisha ina kwananku? kun ƙaraso ashe? Sam banji shigowarku ba." Da fara'a Aishar ta ke amsa mata gaisuwar, su kuwa fuskewa suka yi ko wacce ta ɗauki wayarta tana daddannawa, sun sha kwalliya na ƙure adaka kamar masu shirin halartar gasar zaɓen sarauniyar kyau. Sai yatsune-yatsune suke yi alamu dai na tsananin wulaƙanci. Ita ma da yake ta fi su gigi suna gama gaisawa da Aisha bata ƙara kallonsu ba ta wuce ɗayan Bedroom ɗin Ummee inda Mamanta ta ke. Ganin yadda Rebeccah tayi kyau cikin doguwar rigar atamfa ba ƙaramin daɗi ya tsunduma zuciyar Bilhaƙƙi a ciki ba. Duk wannan tsufa da lalacewar da ta yi kashi talatin da biyar sun ragu cikin ɗari. Ta ƙarasa cikin ɗakin da sassarfa ta rungumeta tana dariya "Mamata kinyi kyau sosai wallahi, kamar ba ke ba. Anya ma idan Babana ya ganki zai gane ki kuwa?" Zare idanu ta yi tana dariyar ita ma, ta ɗago fuskar Bilhaƙƙi suna kallon juna da murmushi a fuskokinsu, sai kuma idanun Rebeccah ya cicciko da hawaye "Baby Billhaƙƙ a wancan lokacin da Babanki ya aure ni kamar ke nake, kyau da dirin jiki, gayu da kwalliyar sosai ni kika biyo. Idanunki da bakinki ne kawai irin na babanki. Amma exactly ke kamar ni ce da nake yarinya. Ko a yanzu ma Babanki zai sake so na a karo na biyu? kila ma yayi aurenshi ya auri hausawa yarinya ba kamar ni da na tsufa ba." Sai hawaye suka zubo mata shar! Gwanin ban tausayi. "Oh noo! Kar kiyi kuka Mamana. Malam ya faɗa min har yanzu Babana yana tsananin son ki. Har fa sun saka anje can ƙauye nemanki, da ba'a same ki ba har yanzu yana can yana ta damuwa da addu'ar Allah ya baiyana mu ni da ke. Wannan ai babban alamu na soyayya ce ko?" "Eh Baby ta." Ta amsa zuciyarta cike da jin daɗin maganganun. Ummee ce tayi sallama ta shiga cikin ɗakin hannunta riƙe da kofi ta haɗo kakkauran tea a ciki, ɗayan hannun kuma riƙe da plate an zuba soyyyen dankalin turawa da ƙwai a ciki "Ummu Bilhaƙƙi ga tea ki sha. Kinsan fa mikakkiyar tafiya ce a gabanmu. Malam ya ce kowa ya karya kafin a ɗauki hanya." "Na gode Hajiya, Allah ya saka da alkhairi." Bata saurari godiyar ba ta maida idanunta kan Billhaƙƙi da murmushi a fuskarta. "Kije ku haɗa tea ke da Saudat, kwai da irish yana nan na ajiye muku a kicin." "Tam! Sannu da aiki Ummee. Shi ne yau ma baki kira ni na taya ki ba?" Tayi maganar a shagwaɓe. "To yi hakuri, ai kullum indai lafiya kike tare muke yi. Har yanzu baki gama jin sauki ba shi yasa na barki ki huta. Je ki maza ku karya kar mu makara." "Tam!" Ta amsa a ladabce da murmushi a fuskarta, ta fice daga ɗakin da sassarfa. Tana fita falon ta hange Maheer da Luƙman zaune a kan dining suna karin kumallo. Su kuma matan suna kan kafet sun shimfiɗa ledan cin abinci suna karyawa. Kusa da su ta ƙarasa fuskanta na kan Luƙman ta fara gaishe su. "Ya Luƙman ina kwana? Ya Maheer barka da safe." Da fara'a suka amsa mata. Maheer sai laluben fuskarta yake yi dan su haɗa idanu amma ko kallon ɓangaren da yake zaune ta ƙi yi. Suna gama gaisawa ta wuce da nufin shiga kicin. "Keeee!" Daga can tsakiyar falon Surayya ta kira ta a wulaƙance kamar bata san sunanta ba. Dukda faɗuwar da gabanta yayi, da yadda ranta ya ƙara ɓaci bata tsaya ba, balle kuma har ta juya. Tafiyarta bai canza ba daga inda ta nufa, sai da taji daga can Surayya ta sake cewa cikin fushi. "Ke Bilhaƙƙi baki ji ina kiranki bane?" Kamar baza ta tsaya ba sai ta tsaya, ta runtse idanunta, addu'oi take ta ja a zuciyarta sannan ta juya ta nufi gurin Surayyan. "Aunty Keee fa naki ji kina cewa ni kuwa ko Ummee bata ce min keee. Ga ni." Sai da taja wani dogon tsaki ta bita da mugun kallo cike da muzanci, ta nuna mata kofin da ta gama shan tea da yatsarta manuniya. "Ɗauke wannan kofin ki kai kicin." Duk mutanen falon basu ji daɗin yadda Surayyan ta yi wa Bilhaƙƙi ba, ba ma kamar Maheer da ya tsaya cak da cin dankalin da yake yi yana kallon Bilhaƙƙi har tazo ta wuce ta kusa da su hannunta riƙe da kofin, shi kaɗai ya ga yadda idanunta suka tara ruwa. Ummee ma da ta fito tun sadda ta ji keee ɗin tana tsaye a bakin ƙofar ɗakinta tana ji tana ganin duk abinda yake faruwa ranta a ɓace. Wucewar Bilhaƙƙi yasa ita ma ta fito zuwa ɗayan ɗakinta inda Bilhaƙƙi take kwana. Sai a lokacin matan suka lura da tsayuwarta, tsuuuu suka yi musamman Surayya da ta yi rashin mutuncin. Shi kuwa Maheer bai ma lura da Ummee ba, da sauri ya ture kujeran da yake zaune a kai ya bi bayanta zuwa kicin ɗin. Tana shiga ciki ta dangwarar da kofin hannunta a saman cabinet, ta dafa cabinet ɗin ta ƙurawa kofin idanu zuciyarta na tuƙuƙi. Sai ga hawaye shar! Ita a rayuwarta ta tsani a wulakanta ta a cikin mutane. A dai-dai lokacin shi kuma ya shiga cikin kicin ɗin, tana jin motsi a bayanta tayi saurin share hawayen amma bata san ya riga ya gani ba. Ƙugunta ya riƙe ta baya ya juyo da ita yana tambayarta "Kukan na miye?" "Ba komai!" Ta amsa a cushe tare da fisge jikinta, tana kyarma ta matsa kusa da gwangwanin madara da bounvita ta fara ambulawa a kofi ba tare da lura da zubarwar da take yi ba. Kusa da ita ya sake matsawa ya riƙe hannunta, yana ƙoƙarin kallon cikin idanunta "Idan babu komai shi kuma ɓacin ran na menene?" "Ba komai!" Cikin fushi ta amsa tare da watsa mishi wani birkitaccen kallo. Ta fisge hannunta ta haɗa hannu biyu alamar roƙo. "Dan girman Allah Malam ka fita daga harkata." Hanyar fita daga kicin ɗin ta nufa, shi kuwa a sukwane ya janyo gefen rigarta. "Idan za mu tafi fa motata za ki hau..." "Baza ta hau motarka ba." Ya ji muryar Ummee kwatsam ba tare da ya ga sadda ta shiga kicin ɗin ba. Sansarai yayi a tsaye, jikinsa yayi mugun sanyi. Fuskanta a ɗaure ta ƙarasa shiga kicin ɗin, hannunshi ta nuna da yake riƙe da gefen rigar Bilhaƙƙi. "Sakar mata riga ka fice min a nan." Da sauri ya sake ta ya nufi hanyar fita, yana zuwa daf da ita cikin murya mai baiyana ƙwaƙƙwaran kashaidi da jan kunne ta ce "Ka jawa fitsararriyar matarka kunne. Idan kai wasa daga kai har matan naka babu inda za kuje Wallahi." "Ummee dan girman Allah kiyi haƙuri..." "Ka ɓace min da gani na ce ko?" Da sauri ya cikawa rigarsa iska zuciyarsa cike da takaicin Surayya. Daman ya san tunda ta tada ballin sai ya je da su tabbas sai ta jaza mishi wani tsiyar. A maimakon ya koma cikin falon kawai sai ya fita waje. Ta kalli Bilhaƙƙi ta yi murmushi, ta ja hannunta suka matsa gaban kayan tea ta fara haɗa mata "Wai kishiyar kike wa hawaye? Wannan fa alamun jin tsoronta ne tun kafin ki shiga gidan?" Ta tura baki tana murmushi "Ba fa tsoro bane Ummee, kawai ni bana son a disgani a cikin mutane ne." "Eh lallai ba daɗi kam! Amma ki manta da ita kawai, ko ba yau ba kar ki ƙara yadda suyi miki wani abu ki nuna musu ranki ya ɓaci kinji ko?" "To Ummee na, in Allah ya yarda." "Yauwa Baben Yayanta, ungo maza je ki zauna ki cinye tas kuma ki shanye tea ɗin. Ki cewa Saudat idan bata fito ba da alama za a tafi a barta. Ni ma bari inje mu ƙarasa shiryawa ni da Mamanki." "To Ummeena." Da murmushi a fuskarta ta bar kicin ɗin. Ta ma manta da babin wata Suraiya. Ummee tana shiga falon ta kalli surukan da ɗaurarriyar fuska, irin kallon da take watsawa Surayyan yasa duk ta ji ta muzanta. "Ku zo ku gaida Mahaifiyar Bilhaƙƙi." A sanyaye duk suka bi bayanta zuwa ɗakin. Zukatansu cike da mamakin ko yaushe mahaifiyarta taje gidan? Haka dai suka gaishe ta a ladabce suka fice daga ɗakin. A wannan ranar dai haka aka yi tafiyar zuciyar Maheer babu daɗi, yana ji yana gani Bilhaƙƙi ta hau ƙatuwar jeap ɗin Luƙman, Malam ne a gaba, ita, Ummee, Mamanta a bayan motar. Shi kuma matansa biyu ya ɗauka, Aisha matar Lukman, sai Saudat. A gidan Malam dai ƴan samarin ƴaƴansa kawai aka bari da jiran gida. ******* ******* A can Masarautar Bauchi kuwa gaggarumin taro uku ne ake shiryawa, bikin sunan Ƴan biyun Gimbiya Safiyya, bikin murnar baiyanar Mustapha da iyalansa (Don Malam ya sanar da su ganin Rebeccah da ƴarta) Sai bikin naɗin Mustapha a matsayin tabbataccen Yarima mai jiran gado. Shi Takawa ma tun lokacin ya so yayi murabus ya sauka a naɗa Mustaphan amma yaƙi yarda, shi Mustaphan ya nemi alfarmar a ɗaga mishi ƙafa ya ƙara hutawa ya koma cikin nutsuwarsa sosai, kuma ya samu damar karantar harkar mulki da yadda ake gudanar da shi. Ta ko ina manyan baƙi masu sarauta, ƴan uwa da abokan arziki na nesa da na kusa sai tuttuɗawa masarauta suke yi. Tun ana gobe sunan algaita da bushe-bushe suka fara tashi a masarautar. Gaggarumin biki ne da aka daɗe ba'ayi irinsa ba a masarautar, kowa so yake ya kashe ƙwarƙwatan idanunsa. BILHAƘƘI Da yake a wannan karon an kawar da matsalar su Oga, Na shuri ma babu maganarshi. Lafiyar Allah suka yi tafiyar cike da kwanciyar hankali da nutsuwa ba tare da wani mummunan abu ya faru da Bilhaƙƙi ba. Ta daɗe tana sharɓan bacci a jikin Mamanta, sallah da cin abinci kawai ke tada ita. Sai da suka kusa shiga cikin garin sannan Rebeccah ta tashe ta, ta ce ta zauna da kyau ta wartsake an ce sun kusa isa gurin Babanta. Da yake wannan karon gudu suke yi ba na wasa ba, kuma basuyi tsaye tsaye a hanya ba, ƙarfe biyar saura suka isa cikin masarauta. Nan fa aka sake kacamewa da gaggarumin murna na bayyanar iyalan Yarima Mustapha, Jakadiya ƙarama da aka mayar da ita matsayin Jakadiya Babba tattakura ta yi ta kama hanci ta rangaɗa zazzaƙar guɗa mai tsananin ƙara da fitar sauti, ko minti biyu bata yi ba Uwar Soro ta karɓe da nata zazzaƙar guɗan. Wannan watan gaba ɗaya sun raɗa mishi suna WATAN FARIN CIKI. Sarauniya Safiyya da ta ga Bilhaƙƙi tsaye a gabanta matsayin jikanyarta, halastacciyar ƴa ga gudan jininta na farko suman zaune ta yi, kafin daga baya ta fashe da ƙaƙƙarfar kuka mai baiyana tsananin farin cikin da zuciyarta take ciki. Rebeccah sai ina za'a saka da ita ake yi. Babu kunya ba kara Sarauniya ta rungume ta a cikin mutane, uwar Soro da Umma sai tsokanarta suke yi irin na jika da kaka, wai ta tafi da zuciyar mai gidansu Mustapha gaba ɗaya ta hana shi nutsuwa saboda rashinta (idan baku manta ba su kakannin Mustapha ne). Ita dai ba baka sai kunne, sai sussunne kai ƙasa take yi saboda kunya da rashin sabo. A wani babban falo na musamman da yake ɓangaren Sarauniya Safiyya aka tarbe su da kalolin abinci na gani na faɗa na alfarma, sunci sunsha sunyi hani'an sai godiya ga Allah suke yi. Nama kala-kala sunci sun ture ciki har da na ɗawisu. Kai wani kalan naman ma basu san ko na wace dabbar bace su dai kawai ci suke yi suna tanɗe hannu, kunnuwansu kamar zai tsinke saboda tsananin daɗi. Tun daga nan su Surayya suka fara zubar da makaman yaƙinsu bayan sun fahimci abinda yake faruwa. Tsananin takaici da bakin cikin wannan al'amari na ɗaukakar Bilhaƙƙi lokaci ɗaya Surayya sai da ta shige banɗaki ta shaƙi kuka kamar ranta zai fita. 'Yanzu duk matan Maheer ita ce koma baya kenan? Daga ƴar sarki sai ƴar Alhaji ita ce ƴar Ladani? Ita wallahi da ta ma san abinda za ta gani kenan da bata zo ba.' Tana zuwa nan a tunaninta wasu sabbin hawaye suka sake ɓalle mata shar! shar!! kamar an buɗe famfo. Haka ta shaƙi kukanta ta fita tana yaƙe a cikin mutane. Ga dangin Maheer daga Maru sunje sosai, saboda sha'ani ne da aka daɗe ana cin burin lokacin zuwanshi. Duk ƙwaƙwar Musty da yadda ya ci burin son ganin Rebeccah da yadda ita ma ta ci burin ganinsa a karon farko da isarsu basu samu damar haɗuwa da juna ba sai da aka idar da sallar magrib. A lokacin ne Takawa ya bada umarnin a kira duk wasu dangi makusanta na jiki-jiki don a gabatar da Bilhaƙƙi da Mahaifiyarta. A wannan lokacin ne haɗuwar masoyan biyu ta kasance, dukda an raba su da juna na tsawon shekaru goma sha tara zuciyoyinsu na tare da juna. Sun ba kowa na cikin falon tausayi, duk wani mai rai da yake cikin falon nan sai da ya zubar da ƙwallar tausayin waɗannan masoya biyu. Lallai da gaske ne soyayya ba ta tsufa sai dai masoyan su tsufa, haɗuwa ce da duk su biyun suka daɗe da fitarda tsammanin yin irinta, idanunsu rufewa yayi ruf! basa ji basa ganin kowa a falon sai su biyun nan. A tsakiyar falon suka haɗe idanunsu na cikin na juna suna zubar da hawaye, hannuwansu na riƙe da na juna. Jikkunansu sai kyarma suke yi, lallaɓansu sai mazari suke yi. Kamar haɗin baki a tare suka kai gwuiyawunsu ƙasa har lokacin basu daina kallon juna ba. Rebeccah ce ta fara katse shirun da suka yi da magana cikin muryar matsanancin kuka da ciwon zuciya "Musty nah... Tsawon shekarun nan suna gana min azaba... kullum sai Zidane ya zane ni saboda na ƙi sakin kalmar da ka laƙaba min a baki kafin ka tafi... sun alƙawarta min dukiya mai yawa amma na ƙi ƙarɓa... sunyi min alƙawarin muƙami mai girma a coci na ce bana so... har Jerusalam sun ce za su kaini na ce bana so... Ka san saboda menene suka yi min haka? wai in bar musuluncin da na shiga a gurinka. Wai in daina kiran la'ilaha illallahu muhammadur rasulillah... Amma har yau ban bar Musuluncin ba Musty, ban bari ba. Na rantse maka ban bari ba... kullum sai na ce La'ilaha illallah atleast sau talatin... Amma duk tsawon lokacin nan bana yin sallah Musty, basu bani damar da zan fita cikin musulmai ba balle in koya yadda zanyi... har yau ban canza sunana daga Rebeccah zuwa sunan musulmai ba Musty... kana ganin musuluncina har yanzu yana nan Musty???" Jikinsa ne ya ƙara sanyi da ɗaukar matsanancin rawa kaman bugun zazzaɓi, hannuwanta duk biyun ya damƙe a ƙirjinsa kamar mai ƙoƙarin janta ta shige cikin jikinsa, cikin kuka shi ma ya fara magana da ya fahimci amsoshinshi take jira "Musuluncinki yana nan Rebeccah... Tabbas har yanzu ke cikakkiyar musulma Ummu Bilhaƙƙi... Addininmu mai adalci ne. Ubangijinmu mai jin ƙan bayinsa ne. Bazai taɓa kama ki da laifin da aka tilastaki gurin aikata shi ba... idan kuma kina tantama zo kiji daga bakin babban limaminmu." Tsananin tashin hankali yasa da rarrafe ya ja ta har gaban Malam Liman da shi ma ya sadda kai ƙasa yana ta sharan ƙwallah "Liman dan Allah ka faɗa mata. Ina ce har yanzu ita musulma ce ko? ka faɗa mata ko hankalinta zai kwanta. Matata ce ita da har yanzu nake tsananin son ta, ta sadaukar da abubuwa masu girma saboda ni da farinciki na. Don Allah ka faɗa mata, sam bana son tashin hankalinta. Har yanzu ita musulma ce ko?" "Ƙwarai kuwa Mustapha. Har yanzu ita musulma ce." A tare suka sauke wani nannauyar ajiyar zuciya, suka haɗa idanu ga kuka ga murmushin farin-ciki. A wannan lokacin dai sam sun kasa nutsuwa, tsananin tausayinsu kuma da ya cika zukatan mazauna gurin duk sun kasa magana. Liman ne kawai yayi dogon nasiha mai ratsa zuciya, a ciki ya nusar da kowa wannan tafiya da Mustapha yayi dukda akwai sila rubutaccen ƙaddara ne da aka rubuta zayyi tun kafin a haifesa. Ya ƙara da cewa ta wani fannin tafiyar ta haifar da alkhairai da dama, ciki har da jihadi na musuluntar da wata Ahlul kitabi. Wannan babban abin farin ciki da godiya ga Allah ne. Sannan ya maida akalar nasihan kan Rebeccah yana faɗa mata irin gwaggwaɓar lagwadar da duk bawan da ya mutu a matsayin cikakken musulmi mai imani zai sharɓa a gurin Allah SWT. Ya kuma gode haɗe da shi mata albarka na yadda tsananin wahalan da tasha a hannun ƴan'uwanta bai sa ta fita a musulunci ba. Ya sake janyo hankalin duk dangi da iyayen Mustapha kan su tsananta kyautata kamar yadda addininmu ya koyar da mu, ta yadda ko a mummunan tunani baza ta taɓa yin dana sanin shigowa musulunci ba. Daga nan ya bata damar zaɓen sunan da take so na musulunci ita kuma ta ce ta ba Mustapha wannan daman, yana daga cikin abinda take jira idan sun haɗu a aljannah ya raɗa mata. A nan kam sai da taba kowa dariya da tausayi. "Nana Khadeeja. Malam Liman na raɗa mata sunan Nana Khadeeja." Mustapha ya faɗa da sanyin murya. Nan gaba ɗaya falon ya kaure da kabbara. A nan sai Malam Abdulganiyyu ya karɓi bayanin, inda ya bada taƙaitacce tarihin Nana khadeeja da irin gudummuwarta ga addinin musulunci. Nanma wata kabbarar aka sake ɓarkewa da ita. A nutse ya ci gaba da bada labarin duk yadda aka yi Bilhakki taje hannunshi, har zuwa ɗaura mata aure da yayi, da yadda su Maheer suka samu nasarar karɓo Rebeccah. Bai ɓoye komai ba ci ke da nutsuwa ya gama warware musu duk bakin zaren. A nan ma dai wani jimamin aka sake yi, tare da godiya ga Allah da ya kawo ƙarshen komai duk da tsawon lokacin da aka ɗauka ana shan wahalhalu da gwagwarmaya iri-iri. Yarima Mustapha sai kallon kyakkyawar budurwar da aka kira a matsayin ƴarshi yake yi. Babu abinda yake tunani sai yadda ya rabu da ita tana jaririya ranar da aka haife ta. Lallai komai yayi farko yana da ƙarshe amma banda ikon Allah. Har lokacin bai daina share hawaye ba. Takawa ya kira Bilhaƙƙi ta je ta durƙusa a gabanshi, hannunta bibiyu ya riƙe fuskarsa yalwace da farin ciki. Shi mata albarka yayi sannan ya ƙara da yi mata addu'ar Allah ya ci gaba da tsare ta daga sharrin duk wani abin halitta. Haka ta ci gaba da zagawa tana gaisar da iyaye da kakanninta su kuma suna saka mata albarka, daga mai rike hannu ya shafa kanta a cikin maza, sai masu rungume ta a cikin mata. A haka dai har ta gaisa da kowa ta zube a gaban Babanta, lokacin ne wasu hawayen suka sake ɓalle musu duk su biyun "Ba...ba...na..." Ta kira shi da rawar murya. "Na'am Bilhaƙƙi" Ya amsa kiran a raunane tare da janyota jikinsa ya haɗa ita da Nana Khadeeja(Rebeccah) ya rungume a kirjinsa. Nan suka ƙara karyarwa da kowa zuciya. Sai da aka natsa, hankali ya kwanta Takawa da iyaye da ƴan'uwansa suka miƙa godiya ta misamman ga Malam da iyalansa. Ya kuma yanke bayan wannan taron na gobe in Allah ya yarda za a yanke ranar da za a yi bikin Bilhaƙƙi a kaita gidan mijinta. Jin hakan ba ƙaramin farantawa Maheer rai yayi ba. Sai wani sussunne kai yake yi cike da kunya lokacin da yake miƙa gaisuwa gurin Takawa, Umma, Yarima Mustapha. Mai soron baƙi kuwa sai tsokanarshi take yi yana murmushi kawai. Nan falon Takawa Liman ya ja su sallar isha'i zukatansu cike da farin ciki. Su kuma matan suka yi nasu sallar a cikin gida. ******* ******* "Ammi" "Na'am! ya aka yi El-mustapha? Baka yi bacci ba?" Sosa kanshi yayi cikin kunya, duk da ya fara girma a gaban iyayen jinshi yake yi kamar wani karamin yaro. "Ammi na zaci za ki turo Nana Khadeeja ta tayani hira...?" Ido warwaje take kallonshi da mamaki. Sai kuma tayi murmushi. "El-Mustapha ka fita daga idona. Ko za a baka matarka sai nan da sati uku. Lokacin ta gama hutawa kuma an gyara mata ɓangaren da zata zauna. Kar in sake jin wannan maganar ka ji ko?" "To Ammi" Ya amsa da alamun ba haka ranshi yaso ba. "To Ammi ki turo min ita inyi mata sai da safe." "Ai ta daɗe da yin bacci, faɗa min gobe idan ta tashi sai Balaraba ta faɗa mata saƙonka." Duk ta inda ya ɓullo mata sai da ta ɓille haka nan dai dole ya haƙura ya tafi ɓangarensa, ta bishi da kallo kawai har ya ɓacewa ganinta tana dariya a zuciyarta. "Ranki ya daɗe ke da waye a nan?" Ta jiyo muryar Bilhaƙƙi daga can nesa. Hannu tasa ta yafitota alamun tazo. Da sauri ta ƙarasa ta zauna a ƙasa kan kafet kusa da ƙafafunta. "Karki sake ce min Ranki ya daɗe kinji ko?" "Tom! Kakus, Kakaty, Sweet Kakas, Kakalliya, wanne sunan kike so a cikin waɗannan?" A tare suka kwashe da dariya duk su biyun. Hannunta ta kamo ta riƙe a cikin nata tana kallon fuskarta cike da tsananin ƙauna. "Wallah tun ranar da na fara ganin wannan doguwar kyakkyawar fuskar taki na ji ina tsananin ƙaunarki. Allah ya ci gaba da tsare mana ke kinji Ƴar jikalle?" "Ameen Sweet Kakaty" Ta amsa tana murmushi. "Amma yau a turakata za ki kwana ko...?" "A'a gurin Mamana dai. Ina zan ga Babana inyi mishi sai da safe?" "Iyyeee... abin ƴar hakane? Yarinya ƴar gatan Mamanta da Babanta. Mamanki tana can ita da Hajiya Yagana ana gyara mata jiki, yau kusan kwana za suyi ana mata gyaran saiɓee. Shi kuma Babanki yanzun nan ya tafi ɓangarensa. Dolenki yau a gurina za ki kwana, akwai maganar da nake so muyi." "Tam! an gama Sweet kakaty" Dariya duk suka sake yi gaba ɗaya. BILHAƘƘI ƘARSHE 💃🏽💃🏽💃🏽 A cikin dare ɗaya kacal Hajiya Yagana ƙwararriyar mai gyaran jiki daga maiduguri, aminiyar Sarauniya Safiyya ta gyara Nana Khadeeja ta yi kyau sosai fiye da tunanin mai tunani. Duk wani loko-lokon tsufa, da wani tudu da kwari da tabban duka a jikin Nana Khadeeja ta fara dirje shi da haɗaɗɗun kayanta na gyaran Saiɓi. Gashin kanta an wanke, an cuɗe, hallau aka sake wanke shi da haɗaɗɗun maya-mayan wankin kai, daga bisani aka sake cuɗe shi da wani haɗaɗɗen sabon salo na wankin kalkashi. Tattausan Ƙamshi mai tsananin daɗi ake ji a jikinta ga duk wanda ya kusanceta, sosai ƙamshin har ya fara kama jikinta. Lallai da gaske sayen na gari maida kuɗi gida, kuma idan kina da kyau ki ƙara da wanka. Ita kanta sai kallon kanta take yi a madubi tana sake murmushi, tunani take yi 'Ashe dai har yanzu da sauranta? lallai da sauran kallo a rayuwar aurensu ita da rabin ranta Mustapha. Soyayya za ta gwada mishi sosai irinta bugawa a jarida.' Zuciyarta cike da farin-ciki ta ke cewa ga Yagana "Aunty na gode na gode sosai. Allah ya saka miki da alkhairi. Daman ina ta tunanin wasu irin mayuka zanyi amfani da su don gyaran jiki na sosai in dawo yarinya." Ta ƙarasa maganar haɗe da rufe fuskarta da tafukan hannunta biyu tana dariya. Murmushi kawai Hajiyar tayi, sosai Khadeejar ta burgeta, saboda duk abinda ta ce tayi tana yi babu musu ko tambayar amfanin abinda tasa ta yi. Sosai ta ke son zura idanu da biyayya a tsarin aikinta. "Karki damu Khadeeja. Alƙawarin da na ɗaukarwa Safiyya cikin sati ɗaya in Allah ya yarda duk wanda ya sanki a jiya da wuya idan ya ganki zai gane ki. Gyara yanzu muka fara, ke dai ki ci gaba da bada haɗin kai. Ga ruwan wanka can an gama haɗa miki. Ungo wannan sabulun" Ta ɗauko mata wani sabulu na daban ba waɗanda suka yi amfani da su cikin dare ba "Yanzu kiyi amfani da wannan, shi wannan amfaninshi a cikin kwanaki uku kacal za ki ga fatarki ta fara sheƙi tana ɗaukar idanun mai kallonki. Asalin hasken fatar jikinki zai fito cikin ƙanƙanin lokaci." "To Aunty. Na gode." Ko da ta fito wankan sai da aka sake turare ta da wasu kala-kalan turaruka masu tsananin ƙamshi, aka mulke jikinta da wani haɗaɗɗen humra, sannan aka bata kwalakca ta shafa. Wani haɗaɗɗen lesi da a kallon farko ta gane zayyi mugun tsada ɗinkin Buba da bata san lokacin da aka shiga da shi ɗakin ba Hajiyar ta bata ta ce ta saka. Da yake Hajiyar a cikin yaranta akwai ƙwararru a wajen makeover nan da nan su kuma suka fara aikinsu bayan ta saka kaya. Sai da aka gama shirya ta tsaf aka naɗa mata ɗaurin ɗankwali sannan aka ba Bilhaƙƙi daman shiga ɗakin. Lokacin da tayi arba da Mahaifiyarta ƙam tayi poster a tsaye saboda kaɗuwa da yadda aka cancare ta da gyara, sai da Khadeejan ta je ta kamo hannunta tana dariya sannan ta dawo hayyacinta. "Mamana...? Ke ce haka? Aradu idan Babana ya ganki da wuya zai gane ki. Wallahi kinyi kyau sosai kamar wata amarya." Duk sai taba mazauna ɗakin dariya, haka taita sambatu tana dariya tare da zuzuta kyawun da uwar ta yi. Ta juya ta dinga godiya ga Hajiyar na irin kyakkywar gyaran da tayi wa Mamanta. "Oya common Baby, godiyar ta isa haka. Yanzu saura ke. Kakarki ta ce in gyara ki sosai yadda za ki fito a TAURARUWARKI. Ta ce so take ki fi kowa tsananin haskawa a gurin taron nan." "Haba Hajjaju. Yau ai fagen na Mamana da Babana ne. Su suke lokaci. Ni irin wannan gyaran ki bari sai gaf da bikina." Dariya suka sake sakawa ganin yadda ta haƙiƙance tana maganar babu ko kunya, tunda suka isa jiya sai a lokacin ta ɗauko wayarta ta kunna, tana ganin saƙonnin Maheer kawai ta danna musu delete gaba ɗaya don bata buƙatar karanta su. Tayi ta ɗaukar uwar hotuna kala daban-daban. Sai da ƙyar ta samu nutsuwa ita ma aka fara mata gyaran jikin. Da gaske dojewa ta dinga yi dole aka yi mata gyaran jikin sama-sama kamar yadda ta buƙata. Ita ma bayan ta yi wanka wani doguwar rigan material less mare nauyi aka bata ta sanya, rigar cas tayi a jikinta kaman an gwada ta kafin a ɗinka. Aka yi mata taƙaitaccen kwalliya sannan aka naɗa mata ɗaurin ɗankwali. Sosai ta yi masifaffen kyau kamar a sure ta a gudu. Ta matsa kusa da Mamanta sukai ta ɗaukar hoto tana ƙyalƙyala dariya, a lokacin tana ganin kiran Maheer yana ta shigo mata ita kuma tana ta rejecting. Har saida Mamanta ta ce "Baby ki ɗauki wayar mana. Wa ke ta kiranki haka?" "Manta kawai Mamana, bana son a dame ni yanzu. Bari inje gurinsu Ummeena. Yanzu zan dawo." Da sauri ta fice daga ɗakin tana murmushi, har yanzu zuciyarta cike ta ke da haushin Maheer, bata shirya sauraren ban haƙurinsa ba. 'Har ita zai gwadawa yana da mata biyu bayan ita? Bai faɗa mata tare da su za ayi tafiyar ba kawai ya wani taso su a gaba da wani kwalliyarsu dan su haɗu su nuna mata iyakarta? a gabanshi matarsa ta wulaƙantata amma ya kasa tsawatarwa balle ya ɗauki mataki?' Ƙwafa kawai ta yi ta jinjina kai, duk inda ta gilma bayi zubewa suke yi suna kwasar gaisuwa har ta isa ɗakin da aka sauki Rabi, Surayya, Aisha. Da ƴar fara'a ta shiga ɗakin tana wani shan ƙamshi haɗe da basarwa kawai dan ta guma musu takaici, ta ci nasarar hakan kuwa. Kishiyoyin nata zugudi suka yi suna kallonta duk jikinsu a sanyaye, sai suka raina kwalliya da suturar da suka sa duk da ƙure adaka suka yi. "Sas-sannunku da hutawa Auntys ɗina. Akwai wani abu da kuke buƙata ne in ba da umarnin a kawo muku?" Bata jira cewarsu ba ta maida idanunta kan Surayya fuskarta da wani lalataccen murmushi ta ce "Aunty yau ma ko kina buƙatar in ɗauke kofin daga gabanki ne?" Su biyun tsu suka yi a tsure, ba ma kamar Surayya da take ta zazzare idanu kamar ƙwai a ledan burodi. Aisha ce tayi dariya, ta matsa tare da dafa kafaɗar Bilhaƙƙi tana kallonta cike da sha'awa da yabawa "Ƙanwata ba ma buƙatar komai. An bamu komai a wadace har ma da abinda bamu buƙata ba. Har yanzu maganar jiya bata wuce ba?" Da dariya ta amsa tana wani karkaɗa ƙwayoyin idanunta. "A'a ta wuce fa Aunty. Da gaske ta wuce har abada. Bari in je gurinsu Ummeena." "Kinyi kyau sosai ƙanwata." Ta faɗa mata a daidai lokacin da take gaf da ficewa daga ɗakin. "Na gode Aunty Aisha. Na gode" Ta amsa da dariya tare da ficewa daga ɗakin. Sai da ta tabbatar tayi nisa sannan ta juya ta kalle su, kamar baza ta tanka musu ba sai kuma ta ce "Kunsan Allah? Idan kunso tsaf za ku zauna lafiya da yarinyar nan. Kune manya idan kun kame girmanku ba ta yadda za a yi ta raina ku. Amma wallahi idan kuka ce za ku riƙe ta a sakalce kuna gwada mata wani izza ko makirci wallahi za ku sha mamakin abinda zai biyo baya. Kun dai ga yadda reshe ya juye da mujiya ko? Ba gori ba kuma ban cire kaina ba duk ta fimu zuzzurfar nasaba da kusanci da mazajen da muke tunƙaho da su. Idan kun daure zuciyarku kuma kun kauda kai gare ta da Maheer komai mai zuwa da wucewa ne. Daman kuma kun san Amarya ko ta buzuzu ce dole miji sai yayi ɗokinta. Gaskiyar da zaku gwada mata gurin zama da ita shi zai sa ta saki jikinta da ku ta rungume ku kamar yayyinta na gaske. Kuci arziki ku bar arziki a inda yake. Idan kunƙi kuma sai ta kame dangin mijinku tayi hurɗa da su daman kuma yayyinta ne. Miji kuwa bayan aure ɗanuwanta ne makusanci. Idan kunne ya ji gangar jiki ya tsira da mutunci." Daga haka bata sake cewa komai ba ta shige banɗaki. Su kuwa shiru suka yi kowacce tana jujjuya maganganun a ranta. Da alamun dai duk sun gamsu kuma sun amince da shawarwarinta. ******* ******** Anyi gaggarumin taron lafiya an tashi lafiya. An gudanar da komai cikin farinciki, walwala, nutsuwa haɗe da kwanciyar hankali. Anci, ansha, anyi hani'an! Yara sunci sunan Yarima Fareed Abdulfatah da Gimbiya Fareedah Abdulfatah😝🤣 Wasanni kala-kala aka yi na sarauta sannan naɗin Yarima Mustapha a matsayin tabbataccen Yarima mai jiran gado ya biyo baya. A gaban dubban jama'a manyan mutane daga masarautu daban-daban da masu ƙumban susa aka gabatar da Gimbiya Nana Khadeeja Mustapha da Gimbiya Bilhaƙƙi Mustapha a matsayin iyalan Yarima mai jiran gado. Ƴan jarida, ma'aikatan gidan radio, ma'aikatan gidan T.v daga sassa daban daban na jihohin ƙasarnan sai ɗauka ake ana nunawa kai tsaye a gidan T.v. Can na hangi gungun haɗaɗɗun matan Rumbilhaƙ comment section, sun sha haɗaɗɗiyar kwalliya cikin ankon kyakkyawar atamfofinsu, ko waccensu ta ɗora alkyabba a kan kayan jikinta.😍😍😍 Da na matsa kusa da su don ɗaukar labari yanyame ni suka yi ko wacce tana tofa albarkacin bakinta. Jimla ɗaya da duk suka fi haɗuwa a kai dai shi ne "Muma baza a barmu a baya gurin taya Bilhaƙƙi, Rebeccah, Mustapha murnar kawo ƙarshen matsalolinsu ba. Alhamdulillah. Allah ya zaunar da su lafiya da mazajensu." Sai a gurin taron Maheer ya samu ganin Bilhaƙƙi, sosai tayi mishi mugun kyau a cikin alkyabbar da ta ɗora a saman kayan jikinta. Ba tare da kunyar idanun jama'a ba ya matsa kusa da ita ya ɗaɗɗaukesu hotuna kala-kala da wayarsa. An raba manyan kyaututtuka da dama a wurin. Taro dai yayi taro Alhamdulillahi. Komai an yi shi lafiya kuma an watse taro lafiya. Sai fatan Allah ya maida kowa gidanshi lafiya. ******* ******** "Wa nake gani haka a gabana kamar Safara'u. Lafiya kike kuwa? ko har yanzu jikin naki ne bai gama warwarewa ba..." Zubewa ƙasa da tayi cikin kuka tare da kama ƙafafun Umman shi yasa tayi shiru tana jiran jin da wacce ta zo. Cikin kuka ta fara magana har lokacin bata sake ƙafafunta ba. Cike da da na sani ta warwarewa Umma duk wani mugun ƙulli da ta daɗe tana tufkawa a masarautar, har zuwa kan tonuwar asirinta da kuma irin matakin da Mai martaba ya ɗauka a kanta. Tare da rantsewa da girman Allah kan cewa ita yanzu ta tuba ta gane kuskurenta, dan girman Allah a roƙa mata Takawa da Safiyya su yafe mata. In Allah ya yarda baza ta sake aikata wani kuskure makamancin wannan ba. Shiru Umma tayi zuciyarta cike da mamaki, duk da Mai martaba ya faɗa mata komai da ya faru amma ƙara jin labarin daga bakin Safara'un da kanta ya ƙara girgizata. Shiru tayi bata ce komai ba, sai da taji kukan Safra'un ya ki ƙarewa sannan ta ɗaga kai ta kalle ta "To ni yanzu me kike so inyi miki Safara? bayan sadda kika ƙulla irin wannan mugun aikin baki taɓa tunanin rana mai kaman ta yau zai iya zuwa miki ba?" "Umma dan girman Allah ku yafe min. Na tuba, na bi Allah na bi ku. Ki saka baki dan ya rasulillahi Takawa ya yafe min. Wallahi tallahi na yi nadama, na gane kuskure na. Ku taimaka ku bani dama a karo na biyu, na yarda na ɗauki alƙawari idan aka sake kamani da laifi makamancin wannan a jefe ni." Yadda take ta neman gafara tare da cin alwashin baza ta sake aikatawa ba cikin mahaukacin kuka yasa tayi masifan ba Umma tausayi. "Ya isa haka Safara'u. Allah ya yafe mana gaba ɗaya. Je ki sasanki sai na neme ki. Allah ya tsare mu da son zuciya." "Aameen. Na gode kwarai Umma. Na gode. Allah ya kara girma. Allah ya kara miki lafiya da nisan kwana. Na gode." Bayan ta bar ɓangaren Umma haka ta dinga raɓe raɓe a cikin daren tana rurrufe fuska don gudun haɗuwa da waɗanda ta sani har ta ƙarasa ɓangarenta. Bayan faruwan al'amarin sosai ta muzanta ta wulaƙanta a cikin mutane, ko cikin barorinta gani take yi kamar asirinta ya gama tonuwa. Sosai take kunyar fita cikin mutane. Duk abinda yake faruwa a gidan tana da labarinsa amma tsananin kunyan abinda ta aikata da tsoron kashaidin Mai martaba na karta kuskura ya sake ganinta yasa take lafewa cikin turakarta. Yanzu duk wani izza, isa, mulki, tunƙaho, taƙama babu shi a tare da ita. Wani tsoron Allah ne yayi matukar kamata, istigfari take ta yi tana neman yafiyar Allah. Tare da wani matsanancin tsoron mutuwa ya risketa a wannan halin ba tare da ta nemi yafiyar waɗanda ta zalunta ba. Da wannan dalilin yasa tayi ƙundubalar zuwa ta tari Umma da zancen a daren da aka gama taron nan, ta san ita ne kaɗai za ta iya tanƙwara Takawa ya dube ta da idanun rahama ya yafe mata kura-kuranta ko da bazai maida ita kamar da ba. Bata sake jin labarin halin da Chiroma da Jakadiya suke ciki ba, kuma ita ma ba ta ko marmarin sanin wane hali suke ciki. Washe gari tun da wuri duk baƙi suka fara watsewa bayan an cika kowa da abin arziki. Su Malam ma da iyalansa ƙarfe goma sha biyu suka gama shirin tafiya, sunyi rana sosai amma in Allah ya yarda a ranar kaduna za su kwana. Sosai suma an cika su da abin arziki kala-kala. Maheer suka tsaya jira yana can yana sallama da Bilhaƙƙi a falon Babanta. Wani abin mamaki yanzu duk babu fushin nan, sosai take kukan zai tafi ya barta. Tana riƙe a ƙirjinsa tana ta sharar hawaye. Shima dai duk zuciyarsa a damalmale ta ke, tsakani har ga Allah in banda dole ta kai dole babu yadda za a yi ya tafi ya barta a nan. Babban tashin hankalinsa ma shi ne har yanzu da zasu tafi ba a tsaida ranar da za a yi biki a kai masa amaryarsa ba. "Tatlim kiyi hakuri, ki kwantar da hankalinki. Ba ga waya ba? za mu dinga magana ta waya ai. Tuƙi zanyi mai nisa a babbar hanya, da wannan kukan za ki sallame ni?" Girgiza kai tayi ta sa hannu ta fara goge hawayen, amma wani abin tausayi tana gogewa wasu sabbi suna sake gangaro mata. Haɗe bakinsu yayi ya fara aika mata da wani zazzaƙar sumba, yana tsotsan bakinta yana ɗauke hawayen da babbar yatsarsa har ya share mata hawayen gaba ɗaya. Kudi masu yawa ya ɗauko a aljihunsa ya miƙa mata "Ungo wannan ba yawa. Ki rike a hannunki ko za ki nemi wani abun." "Ni dai ban so. Babana zai siya min komai..." "Kin manta yanzu nauyinki a kaina yake?" Kuɗin ya sake damƙa mata a hannu sannan ya ja ta suka fice daga falon, a hankali suke tafe yana faɗa mata tausasan kalamai na yadda yake tsananin sonta har suka ƙarasa falon Sarauniya Safiyya inda su Ummee suke jiransu. Yau dai saboda damuwa a hanya duk inda bayi suka zube musu ana kai gaisuwan ban girma kasa tankawa ta yi, sai shi ne yake ɗaga musu hannu har suka isa cikin falon. Shigansu ciki yasa idanun kowa ya koma kansu, sosai suka dace a matsayin miji da mata. Kamar wata da tauraruwa mai tsananin haske. Rabi da Surayya muƙut suka haɗiye wani dunƙulallen abu suka bi su da dariyar yaƙe. Kai tsaye jikin Ummee ta shige ta rungumeta "Ummeena zanyi kewarki." "Nima haka Bilhaƙƙi. Karki damu kinji? nan da lokaci kaɗan za ki dawo mana." Ta ɗaga kai kawai cike da damuwa, jikin Mummy ta koma tayi mata kamar yadda ta yi wa Ummee. A mutunce suka yi sallama da kishiyoyinta da Aisha. Tana ji tana gani dai haka suka tafi suka barta, kuka ta sake fashewa da shi Babanta da Sarauniya Safiyya ne suka tasa ta gaba da rarrashi har ta haƙura tayi shiru. Yinin ranar a ɗarare cike da sanyin jiki da damuwa ta ƙarasa shi, kuci-kuci kaɗan ta ɗaga waya ta kira Ummee ta ji suna ina? bata samu nutsuwa ba sai da ta samu tabbacin sun isa gida lafiya. Jin muryar Maheer gar alamun sun isa lafiya yasa hankalinta ya ƙara kwanciya, cike da salon soyayya ta ƙara kashe murya ba tare da jin kunyar kakarta ba ta ce mishi "Sevgilim ka yi wanka da ruwa mai zafi ka kwanta da wuri ka huta ka ji? kar ka kira ni ka kwanta kayi bacci. Da asubah zan tashe ka inji yadda ka kwana. I love you." "I love you too Babe. Zanyi hakan in Allah ya yarda." Ya amsa cike da mazewa tunda har lokacin yana tare da matansa. Ko waccensu haɗiyewa kawai tayi suka yi dariyar yaƙe haɗe da ɗan basarwa kamar basu ji ba. BAYAN SATI BIYU Jin dirin motarsa yasa a nutse ko waccensu cike da karairaya da gwalli suka nufi tsakar gidan. Sunsha gayu cikin riga da sket da ya kama ko waccensu ɗam! Cike da fara'a da soyayya suka tarbe shi suna mishi barka da zuwa. Da yake girkin Rabi ne ita ta maƙale shi a kafaɗa ita kuma Surayya ta ɗauki jakar aikinsa da wayoyinsa ta bisu a baya har zuwa cikin falon. "Aunty Surayya minti biyar kacal za ki bamu Honey yayi wanka yanzu zamu fito..." "Ba komai ƙanwata, a fito lafiya. Ki kular min da Sweetat da kyau fa." Duk su ukun dariya suka yi, ta ja hannun mijin suka nufi ɓangarensa. Kamar yadda ta alƙarwarta basu daɗe a ciki ba, yana gama shiryawa suka fito falo don cin abinci. Har lokacin tana zaune a inda suka barta, da dariya ta tare su suka nufi dining gaba daya. "Yau dai Honey mu za mu ciyar da kai gaskiya, hannunka ya huta. Ɗan gata kawai ɗari bisa ɗari. Kasan fa sosai muke ji da kai." "Haba Honey duk yadda kuke ji da ni ai bai kai yadda nake ji da ku ba. Bari kuma ki gani." Abincin ya ɗiba a cokali ya nufi bakinta gadan-gadan. Sai da ta buɗe baki har tana wani lumshe ido kawai ya kautar da cokalin ya kai bakinsa ya cinye abincin. Dariyar da taji sun fashe da shi yasa ta buɗe idanunta, ko da ta ankare da abinda yake faruwa kawai sai ta sa kukan shagwaɓa tana cewa ita bata yarda ba. "Wannan wayau ne Honey. Allah wannan wayau ne. Ban yadda ba ni dai." "Ƙyale shi kinji ƙanwata. Buɗe baki ni in baki" Ko da ta zuba mata abincin sai ta fara dariya tana mishi gwalo, ita ma ta ɗiba a cokali ta ba Surayyan, shi ma ya ɗiba ya ba Rabi sannan ya ba Surayya. Haka suka ci abincin zukatansu cike da farin ciki har suka gama. Falo suka koma suna hira suna kallon T.v "Sweetat tun shekaran jiya baka kira mana ƙanwarmu ba, yau dai pls ka kira ta mu gaisa." Babu musu ya ɗaga wayar ya kira ta, daga can ringing biyu ta ɗauka da sauri, daman tana cikin kewarshi. "Sevgilim" "Tatlim ga Auntys ɗinki ku gaisa." Bai jira ta amsa shi ba ya miƙawa Surayya wayar, a mutunce suka gaisa sannan ta ba Rabi wayar ita ma suka gaisa, aka mika mishi wayar a karshe. Hannu ya ɗaga musu alamun yana zuwa ya nufi ɓangarenshi wayar na maƙale a kunnenshi, "Babe gaskiya na fara gajiya. Haba sati biyu yau fa. Har yau shirin me kuke yi ne?" "Yi hakuri Tatlim. I love you..." Katse wayar yayi ranshi a ɓace, sai ma ya kashe wayar gaba ɗaya don kar ta kira shi. Zuciyarshi cike da tunanin zai daure bazai sake tada mata da zancen yaushe ne za a yi bikin ba. Kafin ya koma falon ƙoƙarin daidaita fuskarsa yayi dan kar su gane damuwarsa, kamar ba wani abu da ya faru haka suka ci gaba da hira cike da raha da farin ciki. Har zuwa lokacin bacci. Suka raka Surayya har ɓangarenta tare da yi mata sai da safe. Shi kuma da Rabi mai girki suka nufi bangarensa. Kyakkyawar tsarin da suka ɗauka a tsakaninsu ke nan tun kafin shigowar Bilhaƙƙi gidan. Sun yarda duk irin tsarin da suka shimfida na zaman gaskiya da amana a tsakaninsu idan ta zo kan wannan turbar za ta bi. Yanzu zaman lafiya suke yi sosai ba kuma zama na yaudara ba. Suna yawan nuna ƙaunarta da suke yi a gabanshi duk don su ƙarawa kansu kima da martaba a idanunsa, yo miye a ciki? wayayyun mata ne ke taya mijinsu son abinda yake so. Burinsu ya cika kuwa, domin sosai yake jin daɗi tare da alfahari da hakan a fili da sansanin zuciyarsa. Girmansu ya ƙaru a idanunsa, ƙaunar da yake musu ta sake ninkuwa a zuciyarsa. ******* ******* A can ɓangaren zugudi tayi da waya a hannunta tana mamakin kashewar da yayi, ba zato ba tsammani sai hawaye ya ɓalle mata. A daidai lokacin Mamanta da ta dawo ɗaukar karatun addini daga gurin malamar da aka ɗaukar mata tana zuwa har gida ta koyar da ita tayi sallama a cikin ɗakin, tarar da ita tana kuka ya ɗaga mata hankali. Da sauri ta cire hijabin jikinta ta nufe ta da sauri tana tambayar "Beby Bilhaƙƙ lafiya? Me yake damunki?" Da yake buɗaɗɗiyar yarinya ce da bata iya ɓoye ɓoye ba wayar kawai ta miƙa mata "Mamana wai ya gaji da jira na. Nima gaskiya na gaji. Allah idan baku shirya bikin nan nan kusa ba ni zan tafi kaduna in kyale ku. Haba dan Allah! tuntuni an ɗaura aure amma har yau ba a yi biki ba? Ni dai wannan tsare-tsaren na mulki sun ishe ni haka nan. Kawai ko ba a samu babban gidan ba a kaini nashi gidan haka nan zan zauna a ƙuntacen." Tana zuwa nan a maganar kuka ya ci ƙarfinta, daman ita ma bala'in kewar mijinta take yi kawai tana daurewa ne don kar a ce bata da kunya. Mustapha da har ya sa kai zai shiga ɗakin nata da yaji irin maganganun da takewa uwar kawai sai ya tsaya a bakin ƙofar. Murmushi yayi da ya fahimci ta kai ƙarshen maganganun sai ya juya kawai ya nufi can cikin gidan ɓangaren Takawa. Ko da yaje suka gama maganganunsu suna dariyar shirmen Bilhaƙƙin ɓangaren Mahaifiyarsa ya nufa. Ita ma ta ci dariya ya gama yiwa twins wasa ya koma ɓangarensa. Wanka ya tarar Rebeccah tana yi, dole ya zauna a gefen gadon zaman jiran fitowarta. Ko da ta fito wankan tattausan murmushi suka fara aikawa junansu sannan tayi mishi sannu da zuwa, da hannu ya yaficeta ta tafi gurinshi. Bai damu da ruwan jikinta ba ya zaunar da ita kan cinyarsa yana sansanar ƙamshin jikinta. "Ina Beby?" "Hmmm! Baby rigima? Ɗazu ta gama kukan mijinta na fushi da ita, ko mu kaita ko ta tafi da kanta." Dariya yayi mai isarsa sannan ya ce "Ke kinga laifinta? Mu iyayenta muna nan muna zuba soyayya da ƙara'in sabon amarci amma ita mun kyale ta ko oho." Ɗan dukan ƙirjinsa tayi cike da soyayya ta shagwaɓe murya tare da cewa "Kai Musty...?" "Ai gaskiya ne Umm Bilhaƙƙ! ɗazun ai ina jin sadda take miki kuka da ƙorafin. Shi yasa ban shiga ba na koma muka ƙare magana da Takawa. Yanzu dai in Allah ya yarda nan da kwanaki uku za a mika ta gidan mijinta. Daman Takawa ne ya ce a bari a siyawa mijinta babban gidan da zai ishe su a wadace tunda babu isasshen lokacin yin gini. To kuma an samu, gobe in Allah ya kaimu za a yiwa Hajiya Ladidi Turkiyya magana ta haɗa mata komai na kayayyakin ɓangarenta. (Wata hamshaƙiyar Hajiya ce mai kawo nagartattu kuma haɗaɗɗun kayan ɗaki masu shegen kyau da masifar tsada daga ƙasar turkiyya. Iya kuɗinka iya shagalinka) Har ma fa yayi waya da Malam ya sanar da shi duk halin da ake ciki saboda su ma sauran matan su samu daman gyara ɓangarensu su tare kafin a kaita." "Hakan yayi kyau Ɓarina. Amma gidan a wadace zai ishe su ko?" "Za suyi maneji dai Zumata, 4 bedroom flats ne ɓangare huɗu. Sai BQ daga can baya. Ba laifi tsarin gidan yayi kyau sosai kuma akwai wadataccen fili, dan akwai tazara tsakanin ko wane ɓangare ta yadda ba wacce za ta takurawa wata. Takardun gidan da komai ma gobe za a kaiwa Malam shi kuma ya damƙawa mijin nata kyauta halak malak daga Takawa." "Madallah. Allah ya basu zaman lafiya..." Daga nan kuma wasan ya fara sauya salo dan haka na ja tsumman ƙafafuna na ƙara gaba. Washe gari da wuri Hajiya Yagana ta dira a gidan ta ƙalƙale Bilhaƙƙi da masifaffen fitinannen gyaran jiki irin na tsadaddun amare masu tsananin gata. Na kwanaki uku kacal aka yi gyaran amma kamar an shekara ana yi saboda yadda ta canza gaba ɗaya. A rana ta huɗu bayan sallan azahar aka ɗauki Amarya Bilhaƙƙi cikin jerin gwanon motoci kamar wata ƴar gwamna aka nufi kaduna gidan mijinta da ita. Don tsananin gata rakiyar Amarya har da uwa da uba, bayi biyar mata Takawa ya haɗo ta da su dukda ta ce ita ɗaya ko biyu sun ishe ta. Sai da aka zo tafiya da ita kuma dakyar aka ɓanɓare ta daga jikin kakanninta. Ta sha kuka su kuma sun jiƙa ta da zafafan nasiha da jan kunnen haƙuri da duk irin rayuwar da aka tarar a gidan aure. Gidan Malam suka fara sauka suka huta, aka ci abinci, Hajiya Yagana ta sake sallawa amarya wanka aka tsantsara mata makeup mai sauki aka zuba mata tsadaddiyar alkyabba sannan aka mika ta gidan mijinta. Ɓangaren Amarya fa yayi masifar haɗuwa, da ganin irin shirin da aka yiwa ɗakunan za a san amarya jinin sarauta ce. Sai fatan Allah ya bada zaman lafiya. Ameen KANWA TA KAR TSAMI ƘWARNAFI YA KWANTA😍😍🥰🥰🥰🙈🙈🙈 Saboda tsananin zumuɗi, ƙosawa da kishi Ango babu wani abokin da ya ɗauka don ya raka shi ɗakin Amarya. Kayan siyan bakin da ya siyawa amarya ledoji uku ya siyi komai don tsananin son gwada adalci tsakanin matansa. Ko da ya isa gidan bai nufi ɓangarenta kai tsaye ba, ɓangaren Surayya ya nufa. Ya fahimci yanayin damuwar da ke tattare da ita dukda tana ƙoƙarin ɓoyewa, don haka cikin hikima ya zauna ya dararrashe yana janta da hirar soyayya tare da ƙara yaba kyan tsarin kayan da aka zuba a ɓangarenta, sosai iyayenta suka yi ƙoƙari bayan dubu ɗari da hamsin hamsin ɗin da ya ba ko waccensu kyauta ita da Rabi. Tun tana shan ƙamshi har saida ta saki suna hira da dariya, ita da kanta ta tunatar da shi dare ya fara yi ya kamata ya je gurin amaryarsa. Ya ɓata fuska kaman wani yaro ƙarami "Ni fa yau bani da abokai ku ne manyan ƙawayena. Muje dan Allah ku raka ni ke da Rabi. Ni tsoron zuwa ma nake yi." Dariya taita ƙyalƙyalawa yana ta zuba maganganun raha har suka isa ɓangaren Rabi, ita kuwa idanunta jajur suka tarar da ita. A nan ma ya ƙara dararrashewa har da kwanciya wai shi kanshi ciwo yake yi. "Ni dai ku barni in kwana a nan gobe sai inje gurin amaryar" "A'a hakuri zaka yi Oga. Wannan rashin adalcin ba da mu za a yi ba." Haka nan yana turjewa kaman baya so har suka raka shi ɗakin Amaryarshi, basu wani zauna ba suka yi musu sai da safe suka fice ko waccensu idanunta ciccike da hawaye. Ganin haɗuwar falon kawai da ɗakin da take ciki sai da ya ƙara tayar musu da hankali. Dukda dare ne amma da yake ko ina tar yake da hasken wutan lantarki sun fahimci kayan ɓangarenta ba ƙananun kaya bane, ga wani abin burgewa yadda babu tarkacen kaya komai an saka shi ne a tsare cike da ɗaukar hankali. Yana raka su bayan ya rufe babban falon ya koma ɗakin da ta ke, kan gadon cak ya haye tare da shigar da fuskarshi cikin hulan alkyabbarta yana sunsunarta. "Fatabarakallahu ahsanul khaliƙeen" Ya faɗa da wani sassanyar murya tare da sauke mata hular alkyabbar gaba ɗaya daga fuskarta. Kallon ƙuda suka yi na minti biyar kowa a cikinsu fuska cike da murmushi. A hankali ya kai hannu ya janyota jikinsa ya rungume tare da yin baya baya har ya kwanta a kan gadon ita kuma tana kwance a ƙirjinsa "Tatlim wallahi tallahi ina matuƙar son ki." "Nima ina son ka Gangar..." Haɗe bakinsu da yayi yana tsotsan harshenta kaman ya samu sweet ya hana ta ƙarasawa. Sai da ya gamsu don kanshi sannan ya sake ta. Shi ya zare mata alkyabbar daga jikinta sannan ya koma falon ya ɗauko ledojin da ya shigo da su. Duk abinda ya siya ƙin ci tayi ta ce ta ƙoshi a gidan Malam, tatacciyar madara kawai yasha ya bata tasha kamar yadda fiyayyen halitta yayi umarni. Ya umarce ta taje tayi alwala suyi sallah. "Ni fa nayi isha'i a gidan Malam har da shafa'i da wuturi." "Babe wannan ai Nafila ce zamu yi." Nan da nan tayi alwalar shi kuwa sai da yayi wanka sannan ya ɗauro alwala. Bayan sunyi sallah yayi musu addu'oi sosai, ya tattambayeta abubuwa game da addini. Alhamdulillah ta amsa komai yadda ya kamata. Nan suka canza kaya zuwa na bacci cike da ɗoki. Mutumiyarku Hajiya Bilhaƙƙi da farko biye masa tayi tana ƙoƙarin maida martanin duk wani tsotse tsotse da rungume rungume, saida kida ya fara canzawa sannan rawar ma ya fara canjawa. Sai kuka da majina tare da rokon dan Annabi ya kyaleta, da wuya yayi wuya ne ta fara kiran Mamanta da Babanta, kai a ranar har Malam sai da ta kira. Shi kuwa goga bai kyale ta ba sai da kanwar nan ta kashe tsami ƙwarnafi ya kwanta. Da kanshi ya kaita banɗaki yayi ta canza ruwan zafi yana gasa mata jiki, a karshe ya biya mata da wankan tsarke ya douko Babensa a galabaice ya kwantar a kirjinsa suka yi bacci. Washe gari babanta da yaje gidan makullin motoci biyu ya damƙawa Surayya da Rabi kyauta halak malak! Tare da rokon alfarmar a zanansu da Bilhakki suji tsoron Allah su dinga nusar da ita duk wani kuskure da ta aikata. Ƙarshe Alhamdulillah Sai mun haɗu a JA GABA bayan sallah in Allah ya yarda. Na gode kwarai da jumirin bi na da hakuri da ni har muka kai karshen wannan littafin🥰🥰🥰🙏🏼🙏🏼🙏🏼 Wallah wannan page ɗin babu editting, idan kunga kuskure afuwan Sweethearts🥰🥰🥰 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels