An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels [20/08, 2:11 am] Shuraihu Usman: 🌸🌸🌸🌸🌸 *ƘADDARA TA* 🌸🌸🌸🌸🌸 Na *Jiddah S Mapi* *Chapter 1* ~Garin yomen babban gari ne me ɗauke da yaruka da ƙabilu dayawa, amma yawanci kabilar fulani sunfi yawa, yau an wayi gari da ruwan sama, tun safe ake ruwa har zuwa yanzu ruwa bai tsaya ba, hakan yasa mutane basu fito ba kowa yana gida sai ɗaiɗaikun mutane da suke fita sabida uzurin dole, gidan sarkin yomen babban gida ne wanda yake ɗauke da family's dayawa, an ƙawata gidan da kayan sarauta na zamani dana gargajiya, sarkin garin sunanshi ABDALLAH ya kasance mutum ne wayayye wanda yake gudanar da sarauta cikin wayewa da sanin ya kamata, matarshi sadiya kyakkyawar macece me tsananin kama da larabawa, mutane dayawa suna mata kallon balarabiya har sai ta buɗe baki tayi magana da hausa zaka gane ba balarabiya bace, bafulatana ce ta asali, shima sarki hausa fulani ne, kyakkyawa ne shima ajin karshe amma shi chocolate color ne ita kuma fara ce dal, bari mu leƙa gidan sarki muga meke faruwa a wannan gari da masarautar, kyakkyawan main parlour ɗinsu ɗauke yake da furnitures farare sal royal ne komai anyi adon sarauta a jikin komai na ɗakin, busy falon yake kasancewar yau ɗansu dake karatu a kasar italy zai dawo hakan yasa suke shirye shirye kamar yadda suka saba idan zai dawo, kyakkyawar matar sarkin ce ta fito sanye da riga da skirt na atamfa tayi bala'in kyau tsayawa tayi hanunta rike da bowl cike da flower ganin yadda mai martaba da kanshi ya zage yana shirye shirye yasa tazo ta tsaya a gabanshi ta zuba mishi kyawawan idanunta kallonta yayi sai kuma yaci gaba da aikin yace "ya dai? kin sani a gaba kina min kallon soyayya?" ɓata rai tayi tace "waya faɗa maka kallon soyayya nake maka? sau nawa zan faɗa maka ka daina aikin nan kaifa sarki ne ya kamata ka gane, idan bayinka suka shigo suka ganka a haka ya kake so su fara kallon mu?" murmushi yayi ganin yadda ta ɓata rai yace "to na daina" zama yayi akan sofa yana kallonta, fara aikin tayi wani kyakkyawan matashi me nutsuwa sosai ya fito daga ɗaki yana mika tareda yin salati, sanye yake da farin siririn glasses a idonshi jallabiya ne me taushi a jikinshi da alama yanzu ya tashi, gashin kanshi kamar na larabawa ga kuma sajenshi da yake a kwance luf, a hankali ya karaso, ganin shirye shiryen da akeyi cikin nutsuwanshi yace "ABI meyasa ake shirye shirye waye zai zo?" kallonshi yayi cikin kaunan da yake yiwa yaron sabida nutsuwanshi yace "SULTAN ne zai dawo" da sauri ya cire glasses ɗinshi ya kalleshi da idanunshi masu kyau yace "sultan zai dawo yau?" jijjiga kai yayi yace "yes sabida kuna bacci ne yasa ban faɗa muku ba amma ya kiramu ya kammala secondary yau zai shigo nigeria harma sun tashi" da mamaki yace "ya Allah ai ban sani ba da zanzo na tayaku" kallon matar yayi yace "AMMI sannu da aiki" murmushi tayi tace "yawwa KASEEM" cikin nutsuwa yazo ya karɓi plate na hanunta yace "kawo na aje miki" kaiwa yayi dinning sannan ya dawo yace "sai kuma me za'a tayaki?" girgiza kai tayi tace "karka damu mun gama duka da Abbinku" ya sunkuyar da kai yace "to ammi bari naje ɗaki na shirya sai muje ɗauko sultan ɗin" tace "karka damu kaseem ana ruwa fa har yanzu ruwa bai tsaya ba" yana tafiya yace "ba zan iya zama a gida kanina ya dawo ba dole naje ɗaukoshi" murmushi tayi, muryan mace ne daga stair ta buɗe murya tace "waye zai dawo yau ya kaseem?" kallonta yayi sanye take da riga da wando na bacci gashinta ma bata rufe ba, kyakkyawa ce sosai da sosai tana matukar kama dashi da kuma Ammi, farace sal da gashi me tsayi yace "sultan ne" tsalle tayi tace "wayyo yau sultan zai dawo?" murmushi kawai yayi ya wuce ba tareda ya kara mata magana ba, ammi wacce take gyara labule tace MEENAT zoki rikemin stool ɗinnan kada na faɗi" da sauri ta sauko daga stair ta rike mata, shiri yayi ya fito sanye da shadda yayi bala'in yin kyau sanye yake da siririn glasses ɗin da alama baya rabuwa da glasses, zai fita sukaji tafi, da sauri ya juyo domin yasan mutum ɗaya ne yake tafi a gidan idan zaiyi magana, subhanallah tsarki ya tabbata ga ubangijin da yake halitta, wani kyakkyawan matashi ne da alama shine kaninshi na dab yayi bala'in kyau cikin yadi black color tamkar balarabe ga wani kwantaccen gashi dake kanshi me yawa, murmushi ammi tayi ganin yana saukowa tace "ABDULHAMEED" a hankali ya lumshe ido ya gama saukowa, kallonshi yayi, kaseem ɗin yace "hameed zamu je ne?" gyaɗa kai yayi alaman eh, murmushi yayi yace "to taho mana muje" a hankali ya fara takowa, ɗauke kai ammi tayi tana share hawaye, Abi ne yayi mata alaman ta daina kuka, da sauri ta share hawayen, itama meenat jikinta yayi sanyi ta sunkuyar da kanta, hanunshi kaseem ya rike suka fita, ruwa ya tsaya gari yayi haske hakan yasa yanayin garin yayi daɗi sosai, jerin manya manyan motocin da aka shirya domin ɗauko kaninsu sultan suka nufi wajen, dogari da masu gadin gidan duk sun shirya domin ɗauko kaninsu hameed, cikin girmamawa suka fara russunawa kasa suna aika gaisuwa tareda kirarin cewa "takawarku lafiya YARIMA HAMEED da yayan yarima, yarima me jiran gado" ɓata rai yayi sabida ya tsani ace mishi yarima" murmushi kaseem yayi ganin yadda ya ɓata rai, buɗe motan akayi musu suka shiga zazzafan tsadadden motan da suke fita dashi, convoy suka haɗa suka fita a gidan, kallonshi kaseem yayi ganin yadda ya ɓata rai sabida ance mishi yarima me jiran gado ya rike hanunshi a hankali ya murza kyawawan fararen yatsunshi da suke da laushi kamar hanun mace, ya kalli kyakkyawan fuskanshi ji yayi sonshi yana karuwa a ranshi, a rayuwa babu abinda yake so kamar hameed kaninshi, idan yaga hameed cikin damuwa sai yaji komai na duniya ya fita ranshi, nutsuwan hameed yasa duk cikin yaran gidan babu wanda yake so kamar shi, a hankali yace "hameed kar kayi fushi dan ance maka yarima Allah ne ya baka wannan matsayin kaga duk da na girmeka Allah ya zaɓeka ya baka matsayin yarima sannan nasan bakaso ace yarima me jiran gado sabida kana ganin kamar Abi zai mutu ne ko?" a hankali ya gyaɗa kai yana zubawa yayanshi da yake jin tsananin sonshi a ranshi ido, yace "karka damu kowa da lokacinshi idan lokaci yayi babu abinda zai hana mutum mutuwa, sannan matsayin yarima da kake dashi bashi zaisa abi ya mutu ba domin ka zama sarki kuma bashi zaisa abi ya rayu ba domin kada ka zama sarki, sabida haka ka saki jikinka ka daina sa komai a ranka kaji?" a hankali ya gyaɗa kai, murmushi kaseem yayi yace "yawwa kanina smile for me" a hankali ya saki wani smiling da yasa kyawunshi kara bayyana, ga wani lotsawa da gefen kumatunshi yayi, ya lumshe kyawawan idanunshi yana kallon titi, har yanzu ya kaseem yana rike da hanunshi. babban airport na garinsu suka shiga, ana ganin motocin gidan sarki ne aka basu hanya, tun daga wajen mota aka shimfiɗa red carpet har zuwa bakin jirgin da yanzu yayi landing, basu fito daga motar ba dogali da security's ne suka fito suna jiran fitowanshi, shine first na fara fita, yayi masifan kyau cikin baƙin jinx da riga polo da facing cap, yana kama dasu shima sosai da sosai, saide shi yaro ne sabida akwai yaranta sosai a tare dashi, dube dube ya fara yana karewa kowane mota kallo, turo karamin bakinshi yayi ganin babu ƴan uwanshi ko ɗaya da suka zo sai tarin dogarai da masu tsaron gidansu, ɓata rai yayi, ya kaseem da sauri yasa hanu zai buɗe motan hameed ya rike hanunshi, kallonshi yayi da mamaki girgiza kai yayi alaman kada ya fita ya ɗan dakata tukunna, yace "bakaga ya matsu ya ganmu bane?" taɓe baki yayi, saida suka ɗan ɓata lokaci kafin kaseem ya janye hanunshi ya buɗe ya fita, shima hameed fita yayi ya harɗe hanu a kirji yana kallon sultan, waro ido yayi yace "ya kaseem? yaya yarima?" da wani irin gudu yazo ya rungumesu a tare, cikin kewansu yace "i miss you all" murmushi ya kaseem yayi sannan ya zameshi daga jikinsu yace "let's go home ammi da abi sun damu su ganka" murmushi yayi yace "to ai har nayi expecting babu wanda yazo a cikinku" kallon hameed yayi da suka shiga mota yace "amma nayi mamaki da yaya yarima yazo" ɓata rai yayi, jikinshi a sanyaye yace "sorry yaya hameed" duk sukayi shiru, tafiya sukayi zuwa gida, sai hura algaita ake, shi kuma sultan sai farin ciki yake ya dawo gida yanzu zai fara zuwa wajen abokanshi zai samu sakewa ba kamar acan da Abi yasa ake tsareshi babu inda ya isa yaje ba, suna shiga Ammi ta rungumeshi kanƙameta yayi sosai yace "oyoyo Ammi" Abi dake tsaye ganin ba zasu saki juna ba yace "to sakemin matata hugging ɗin ya isa haka" dariya yayi ya saki ammi, rungume Abi yayi yace "i miss you so much Abi" yace "i miss you too my son" meenat ta baya ta rungumeshi tace "welcome sultan bro" yace "dallah sakeni ko so kike mu faɗi?" tace "wallahi ba zan sake ka ba nayi kewarka" tsaki yaja, ammi tace "zaku fara ko?" sakinshi tayi ammi tace "to dama babu wanda yayi breakfast a gidannan sai kuzo muci abinci" kalle kalle sultan yake yi, ammi tace "me kake nema?" yace "ina....?" shiru yayi ganin kallon da abi ya mishi, a hankali ya sunkuyar da kanshi, itama ammi ta ɗauke kai daga kallonshi kamar yadda ya kaseem ya ɗauke kai, dinning suka nufa jikin sultan a mace ya zauna suka fara cin abinci babu wanda ya kara magana a cikinsu har suka gama, hameed ne ya fara tashi cikin kulawa kaseem yace "ka koshi?" gyaɗa kai yayi, yace "ka tabbata?" ya kara gyaɗa kai alaman eh, cikin sanyinshi da nutsuwa ya fara tafiya, stair case ya haura ya shiga ɗakin da yake mamakinshi, zama yayi akan royal sofar da yake ɗakin, masha Allah ɗakin yayi masifan yin kyau ga wani maƙeƙen royal bed nashi, kamar parlour haka bedroom yake duk fararen funitures ne, lumshe ido yayi ya ɗaga kanshi sama yana tunani, turo kofan akayi ya buɗe ido a hankali ya kalli wanda ya shigo, ya kaseem ne rike da plate na yellow juice a hanu, zama yayi a hanun sofan kusa da hameed ɗin yace "karɓi kasha" a hankali ya girgiza kai alaman A,a ba zai sha ba, haɗa fuska ya jabeer yayi yace "ka karɓa nace ina wasa da kaine?" a hankali ya karɓa yasa a baki yasha kaɗan, cikin rashin dariya yace "shanye duka" girgiza kai yayi sannan ya marairaice fuska alaman cikinshi ya koshi, yace "ka shanye nace" da sauri ya shanye domin yana tsoron ɓacin ran ya jabeer ɗin, karɓan glass cup ɗin yayi ya ɗaura akan plate ɗin, ya tashi ya buɗe side drower ya ɗau wani kwalin magani karami yazo ya buɗe fridge ya ɗauko allura da ruwan da yake sawa a fridge sabida kada ya lalace, zuwa yayi yaja ruwan cikin sirinji, idanun hameed ya cika da hawaye ganin abinda yafi komai tsana a duniya wato allura, marairaice fuska yayi kamar zaiyi kuka yake girgiza kai alaman baya son allura, murmushi kaseem yayi yace "kai ko hameed shagwaɓanka yayi yawa, allura kullum ana cikin yi maka amma har yanzu baka daina tsoro ba oya tashi" kin tashi yayi, ya ɓata rai yace "ka tashi nace" a hankali ya tashi yana rufe ido, cikin tausayinshi ya ɗaga riganshi, sauke wandon yayi kaɗan, ji yayi ya rungumeshi ya rufe ido, haka ya saba yi idan za'a mishi allura, alluran yayi mishi kanƙameshi yayi sosai har ya gama kafin ya sakeshi, yace "sorry" a hankali ya koma zai zauna rikeshi yayi yace "ka kwanta a gado dan nasan yanzu zakayi bacci" rikeshi yayi ya taimaka mishi ya kwanta a gadon, duvet ya rufeshi dashi sannan ya kashe ac sabida sanyi, juyawa yayi zai tafi ya rike hanunshi, jikinshi yayi sanyi sosai a hankali ya juyo yana kallonshi, so yake yayi bacci dan sai lumshe ido yake, gashi ya rike hanunshi baida alaman saki, dawowa yayi ya zauna a kusa dashi, pillow ya gyara mishi sannan yasa hanu akan lallausan gashinshi ya fara shafawa, rufe ido yayi jin ya kaseem yana shafa mishi kanshi haka ya saba bacci sai yaji hanun mutum a kanshi yake iya bacci cikin kwanciyan hankali, saida yaji numfashinshi ya canja alaman bacci me nauyi ya ɗaukeshi kafin ya zame hanunshi a hankali ya gyara mishi duvet ɗin ya tashi ya fita daga ɗakin. Ammi tayi tagumi ta zauna tunani kawai take batama san ana knocking ba, kaseem daya fito yanzu ya kalleta sannan ya kalli kofan da ake knocking da sauri yaje ya buɗe, baiwa ce daga cikin bayin gidan, durkusawa kasa tayi tace "Allah ya taimakeka yayan yarima dama sako aka kawo wa mai martaba" kallonta yayi yace "wani saƙo?" tace "wani mutum ne ya bani wannan yace na bashi" karɓan takaddan hanunta yayi yace "to mun gode" ganin tana jiran ya tafi kafin ta tashi yace "tashi karki damu" tashi tayi ya shiga ciki, kallon Ammi yayi wacce ta dawo daga duniyar tunanin yace "ga sako an kawowa Abi" karɓa tayi ta kalli takaddan buɗewa tayi ta karanta sai kuma ta ɗago kai ta kalli ya kaseem daya buɗe ɗakinshi zai shiga, saida ta jira ya shiga sannan ta yaga takaddan, sultan wanda ya fito yana waya kallonta yayi da mamaki, saida ya gama wayan yazo ya tsaya gabanta yace "Ammi meyasa kika yaga sakon da aka kawowa Abi?" wani kallon da tayi mishi yasa yayi shiru bai kara cewa komai ba, tashi tayi zata tafi tace "matukar baka san yadda zaka iya da bakinka ba zakasha wahala a rayuwa" shiru yayi ta wuce ta barshi a wajen, juya maganan yayi a ranshi sai kuma ya taɓe baki ya zauna akan sofan yana kara kiran wayan ana receiving yace "yawwa baby kina jina? yanzu na dawo nigeria ba koda yaushe zamu rinƙa waya ba" da sauri ya katse wayan ganin ya kaseem ya fito sanye da labcoat yasa telescope a wuya, yayi bala'in kyau da uniform na doctor, kallonshi yayi cikin nutsuwa da sanin ya kamata yace "dawa kake waya?" da sauri yace "da abokina nabil" baiyi magana ba kawai ya wuce yana amsa call da alama kiranshi ake na gaggawa, hamdala sultan yayi yasan ba dan yana sauri ba saiya karɓi wayan ya duba. motarsu me kyau wanda yake zuwa asibiti dashi ya shiga, da kanshi yake driving bai yadda driver yana kaishi asibiti ba, a kullum shi yake kai kanshi, special hospital ne me matukar kyau da kuma tsafta asibiti ne kamar a kasar waje kwararrun likitoci yake dasu a asibitin, mallakinshi ne domin da kanshi ya buɗe DR K yayi matukar suna a garin sabida kwazonshi yana taimakawa mutane dayawa bai ɗauki kanshi komai ba duk da matsayin da Allah ya bashi na babban ɗan sarki, a rayuwarshi babu abinda yake kauna kamar family ɗinshi zai iya yin komai akan family ɗinshi, musamman hameed wanda yakejin har kyautan ranshi zai iya yiwa hameed, idan kanaso kaga ɓacin ranshi to ka taɓa hameed ya haɗiyi yaron a ranshi, shekaru dayawa ne tsakaninsu domin ya girmewa hameed nesa ba kusa ba, akwai mutum ɗaya tsakaninsu wanda ya jima da rasuwa, yana biyan ma'aikatanshi fiyeda aikin da sukeyi, kasancewar babu abinda zai bukata na kuɗi wanda zai rasa a gidansu yasa rabin aikin da yakeyi a asibitin kyauta ne, idan yaga bakada kuɗi ma kyauta zai maka aikin. office nashi me kyau ya zauna yana duba laptop nashi da yayi kwana biyu bai duba ba, wayanshi aka kira ya kalli sunan FADEEL dake yawo, fadeel yaron kanin Abi ne amma iyayenshi sun rasu tun yana yaro, a hanun Abi yake amma yana school, ya saba sosai da sultan hakan yasa da sultan ya tafi school shima ya tattara ya koma hostel da zama, Abi yaki ya haɗasu school ɗaya dan yasan ba karatu zasuyi ba, fadeel ya girmi sultan amma tasu tazo ɗaya sun zama kamar sa'o'i idan kazo gidan ba zakasan basu Abi bane suka haifeshi, karawa yayi a kunne yace "ina jinka" yace "ya kaseem na gaji da zaman hostel ne shine zan dawo gida tunda saura watanni na gama school ɗin" yace "shine kuma saika kirani? kaida gidanku amma saika kirani?" yace "sorry ya j" tsaki yaja kafin ya kashe wayan, wato fadeel ya maidashi yaro so yake ya nuna mishi baisan sultan ya dawo ba. aiki yake bai dawo ba sai dare kamar yadda ya saba, da leda a hanunshi ya shigo, duk suna zaune suna cin abinci banda Abi dama yasan ba koda yaushe yake cin abincin dare tare dasu ba, tun kafin ya zauna yace "ina hameed?" kamar yasan ya dawo a hankali yake saukowa daga stair yana yamutsa fuska, sleepy face ɗinshi yayi kyau lips nashi na kasa ya cusa cikin bakinshi yana tsotsa a hankali yake kallonsu da grey eyes nashi, a gefen ya kaseem ya zauna yayi shiru yana kallon fadeel daya maida hankali akan wayan sultan suna kallo, ko me suke kallo oho, jabeer yace "sai yanzu ka tashi a bacci?" girgiza kai yayi alaman A,a ya jima da tashi, ledan ya mika mishi yace "gashi na kawo maka" karɓa yayi ya buɗe, ganin ice cream yayi murmushi ya ɗau karamin spoon ɗin ya ɗibo ya kai bakin ya jabeer girgiza kai yayi yace "wa kai na kawowa" a hankali ya kai bakinshi yana sha, da kallo Ammi take binshi, hawaye yana cika mata ido, a spoon ya ɗiba ya kai bakinta girgiza kai tayi hawayen yana wanke mata fuska, aje roban yayi yazo gabanta ya fara share mata hawayen yana girgiza kai alaman ta daina kuka, fadeel yace "yaya yarima ka kyale ammi kullum sai tayi wannan kukan ta saba" harara yayi mishi da sauri ya rufe baki bai kara cewa komai ba, tashi kaseem yayi ya wuce ɗakinshi. _Jiddah Ce....✍️_ 08144818849 [20/08, 2:11 am] Shuraihu Usman: 🌸🌸🌸🌸🌸 *ƘADDARA TA* 🌸🌸🌸🌸🌸 Na *Jiddah S Mapi* *Chapter 2* ~Cikin dare kowa na ɗakinshi yana bacci gidan ya zama shiru kamar ba gidan sarauta me ɗauke da mutane dayawa ba, hameed wanda idonshi biyu ya kunna wutan ɗakinshi ya kasa bacci, zaune yake akan gadon ya rufa iya kafanshi da blanket duk yadda yaso bacci ya ɗaukeshi ya kasa, daga karshe ma pillow ya ɗauka ya rungume sosai yana rufe ido, wani azaban ciwon ciki yakeji kuma yasan yanzu haka ya kaseem yana bacci, wayanshi dake saman gadon ya ɗauka yana ciza lips nashi na kasa ya danna numbern da yayi saving da ya kaseem ya kira, karawa yayi a kunne yana jin kiran yana shiga amma bai amsa ba, katse kiran yayi ya tura mishi text _(ya kaseem my stomach_) iya short rubutun da yayi ya aika da alama baya magana amma asali ba me yawan surutu bane domin ko messages ɗin da yayi ta turawa ya kaseem magana ne a yanke kaɗan kaɗan baya tura rubutu me tsayi. ya kaseem daya fito daga wanka yanzu sabida aikin da yayi ya gaji sosai, har ya kwanta sai kuma yaga wayarshi yayi haske da sauri ya ɗauka ya buɗe yana karanta sakon hameed, kunna wutan ɗakin yayi ya sauka a gadon da sauri ya fita, direct ɗakin hameed ɗin ya shiga bai tsaya yin knocking ba sabida dare ne, yana shiga ya kalleshi zaune babu alaman bacci s tare dashi, tausayinshi yaji sosai da sauri ya karaso yace "meya samu cikinka?" nuna mishi maranshi yayi da hanu alaman shine inda yake mishi ciwo, rufe ido yayi yace "oh my god hameed da wannan ciwon cikin ya zanyi gashi babu alluran a gida" zama yayi kusa dashi yace "yaushe ya fara maka? yanzu?" girgiza kai yayi kamar zaiyi kuka, yace "okay ɗazu?" gyaɗa kai yayi, yace "to maganin da kake sha idan yana maka ya kare ne?" jijjiga kai yayi zuwa yanzu idonshi ya kaɗa yayi jajur, zama yayi ya dafa kai ya rasa abinyi, birgima ya fara akan gadon yana hawaye, yace "stop crying ina zuwa" fita yayi yaje ɗakinshi ya ɗauko ice a fridge dawowa yayi ya zauna a bakin gadon, mika mishi yayi "oya collect and calm yourself down" ya gane me yake nufi hakan yasa ya girgiza kai, cikin jin haushin kukan da yake yi yace "karɓa mana hameed" karɓa yayi yaja blanket ɗin ya rufe jikinshi kasa yayi da trouser ɗin jikinshi ya ɗaura kankaran daga maranshi zuwa kasa, ɗauke kai ya kaseem yayi daga kallonshi ganin yadda yake lumshe ido yana cija bakinshi, sam baison ko kaɗan yaga hameed cikin ciwo, wurgar da ice ɗin yayi ya kwanta rub da ciki ya fara raira kuka mara sauti, narkewa zuciyan kaseem yayi yaji kamar shima ya fashe da kukan, ganin kukan yaki tsayawa ya daka mishi tsawa yace "kamin shiru, meyasa baka daure ciwo ne?" shiru yayi yana cigaba da birgiman, fita yayi yaje kitchen ya ɗauko lemon tsami ya yanka ya tsiyaya a cup sannan yasa ruwa kaɗan yasa lipton, fitowa yayi yana juyawa Ammi wacce ta fito ɗaukan ruwan sha ta ganshi da cup tace "me zakayi da tea yanzu?" yace "ba tea bane magani zansha kaina ke ciwo" tace "Ayya sorry may be stress ne yayi maka yawa sam baka hutawa" yayi shiru kawai, ruwan ta ɗauka tace "Allah ya baka lafiya ka samu ka kwanta ka huta kaji?" yace "to Ammi" saida ta shiga ɗaki kafin ya koma ɗakin hameed ɗin, har yanzu yana kwance yana kuka, yace "tashi kasha" tashi yayi da sauri sabida so yake yayi bacci kuma ciwon ya hanashi, karɓa yayi ya shanye duka, runtse ido yayi jin bala'in tsami, ji yayi babu sauki marairaicewa yayi ya fashe da wani irin kuka, kaseem ji yayi kamar ya kai mishi duka, cikin lallashi yace "ka daina kuka zaka samu sauki" rage kukan yayi a hankali ya gyara mishi blanket ɗin hanunshi yasa a cikinshi daidai inda yake ciwon ya fara shafa mishi, rufe ido yayi yana jin ciwon yana sauki, gyara kwanciyan yayi zai cire hanun yayi saurin rikewa yana kara rufe ido, murmushi yayi ganin yanaso yayi baccin ɗayan hanun yasa a kanshi yana shafa mishi kanshi a hankali lokaci ɗaya yana shafa mishi maranshi dake ciwo, babu jimawa bacci ya ɗaukeshi, a ranshi yace "ya zama dole hameed yayi aure, zan yiwa ammi magana a nema mishi mata tunda duk tarin ƴammatan da suke aika mishi sakon soyayya yaki kula kowa" a hankali ya zame ya kashe mishi wutan sannan ya fita daga ɗakin ya rufe mishi. ɗakinshi ya koma ya kwanta take bacci ya ɗaukeshi, washe gari ya tashi da wuri domin zai tafi asibiti da wuri, shiri yayi cikin farin yadi me kyau ya ɗaura labcoat a sama sannan ya rike briefcase ɗinshi, farin glasses nashi a idonshi, yayi bala'in kyau kuma da manyance yake yin komai nashi a nitse, ganin an shirya abinci amma babu kowa kawai ya wuce part na mai martaba, sallama yayi ya tarar da hameed a fada ya kwanta kamar me bacci, murmushi yayi yace "hameed dama ka tashi?" a hankali ya tashi ya zuba mishi kyawawan idanunshi alaman eh na tashi, mai martaba ya kalli kaseem yace "har ka fito? yau da wuri zaka tafi kenan?" cikin girmamawa yace "Allah ya taimakeka yau zan tafi da wuri, ina kwana" yace "lafiya ƙalau Allah ya maka albarka kaseem" a hankali yace "ameen" tashi yayi ya kalli hameed daya bishi da ido, yace "zamu je ne?" da sauri ya gyaɗa kai, yace "tashi muje" tashi yayi ya yiwa mai martaba bye kafin suka nufi dinning fadeel ne da sultan zaune sun zuba abinci amma suna hira suna ganinsu sukayi shiru, gaishe da kaseem sukayi ya amsa sannan suka gaisa hameed, hanu ya ɗaga musu alaman lafiya, abinci suka sa suma suka fara ci, Ammi da meenat tare suka fito meenat ta rike hanun ammi, tayi kyau cikin uniform black and white rataye da jakan school, cikin girmamawa ta gaishesu duk suka amsa shi kuma hameed ya mata alaman ya amsa kawai ya sunkuyar da kai yana cigaba da ci abinci, sam bai fiye shiga harkan kowa ba koda a gida yake saide shi da ya jabeer amma baya sakewa da kowa, kallonshi kaseem yayi ganin ya ajiye spoon yace "tunda ka koshi jeka shirya kazo mu tafi" tashi yayi ya wuce ɗaki, bathroom ya shiga ya haɗa ruwan wanka, ya jima yana wankan kafin ya fito yana ɗaure da towel a kwankwaso, a gaban mirror ya tsaya yana kallon gashin kanshi dake a jiƙe, faffaɗan kirjinshi ɗauke da gashi kwantacce, kiran jikinshi kamar me yin gym a kullum, yanada cikakken sura me kwarjini sosai, dryer dake gefe ya jona ya fara busar da gashinshi, saida ya bushe sannan ya aje a gefe, tsadadden man gashin da yake amfani dashi ya shafa sannan ya taje kanshi, fuskanshi babu walwala kamar kullum, da wuya kaga yana murmushi bale yayi dariya, lotion me tsada da kamshi ya shafawa fatar jikinshi da ake kira da gold skin, wardrobe ya buɗe jerarrun tsadaddun kayanshi ya ɗau ɗaya kananan kaya yau yake da ra'ayin sawa, wandon ya fara sawa black ya ɗau pink ɗin polo zaisa, ta cikin madubi idonshi ya hango mishi wutan da yakeci kusa da dryer ɗin daya manta kashewa, grey eyes nashi ya waro a mugun firgice ya fara motsa bakinshi, kasa sa rigan yayi, wurgi yayi dashi ya fara yin baya ganin wutan yana nema ya fara cin ɗakin, jikinshi ne ya fara rawa, take idanunshi suka kaɗa suka koma jajur, banda motsa lips ɗinshi babu abinda yake yi, faɗuwa kasa yayi ya fara jan jikinshi zuwa waje, tsoron daya shiga ya nuna akwai mummunan alaka tsakaninshi da wuta, da kyar ya isa bakin kofa rasa abinyi yayi, hanu yasa da karfi ya fara bugun kofan, Ammi wacce take rike da cup na shayi jin bugun kofan da hameed yake yasa cup ɗin silalewa daga hanunta tarwatsewa yayi a kasa, tare duk suka juyo suna kallonta cikin tsoro ta tashi tana kallon stair, kaseem yace "menene Ammi?" tace "hameed shikenan ciwonshi ya tashi, hameed ne yake bubbuga kofa ku saurara kuji" shiru sukayi kaseem ne ya fara jiyo mugun bugun da hameed yake yiwa kofan, har rige rige suke dasu fadeel wajen haura stair, kofan ɗakin da yake a rufe suka fara bubbugawa kaseem yace "hameed are you okay? hameed ka buɗe kofan" shesheƙanshi sukeji, hankalin kaseem ya kara tashi, bubbuga kofan yake kamar zai ɓalla, yana cewa "hameed relax and open the door" zuwa yanzu ya fara rufe ido alaman zai iya suma a kowane lokaci, kaseem da gudu ya sauka kasa kitchen ya shiga ya ɗauko katon karfe zuwa yayi yace "duk kuyi baya" baya sukayi ya fara ɓalla kofan, da kyar kofan ya ɓallu, gani sukayi yana kwance luf a kasa ya suma, da sauri kaseem ya kalli wutan da yakeci kaɗan kaɗan, yace "sultan kashe wutan" zuwa yayi ya cire socket ɗin dryer ɗin take wutan ya tsaya, kaseem ya ɗaukeshi cak ya wuce dashi ɗakinshi, akan gado ya kwantar dashi Ammi wacce take kuka tace "wuta ya gani shiyasa ya fita hayyacinshi" kaseem yace "kawo ruwa meenat" da sauri taje ta kawo ruwan, karɓa yayi ya shafa mishi, ajiyan zuciya ya sauke me nauyi, ya kara shafa mishi buɗe ido yayi a firgice ya kalli kaseem sannan ya kalli gefenshi, da sauri ya rungumeshi yana hawaye, ammi juya baya tayi tana kuka, cikin muryan kuka tace "shikenan hameed rayuwarka ta lalace ba kamar hameed ɗina dana sani ba wanda bashi da tsoro, ba kamar hameed ɗina da baya tsoron komai ba a rayuwarshi, ba zan taɓa..." kaseem yace "ammi ya isa" juyowa tayi ta zuba mishi idanunta da suka jiƙe da hawaye tace "ya isa? ya isa fa kace kaseem kenan kada nayi magana akan ɗan dana haifa?" sakin hameed yayi yace "maganan bashi da amfani da magana me amfani zakiyi saina kyaleki" murmushin gefen baki tayi wanda yafi kuka ciwo, tace "kana nufin maganana bashi da amfani? kafi kowa sanin zafin da nakeji a kullum idan na kalli hameed, zuciyata kamar zata buga sabida abinda ya faru dashi...." a gabanta ya tsaya yace "ya isa haka ammi maganan ya isheki haka" kallonshi tayi da mamaki tace "kaseem ni kake yiwa tsawa?" ya dunƙule hanu yace "idan kikace zaki tuno da abinda ya faru a baya ba tsawa ba har..." sai kuma yayi shiru, hanunshi ta kalla daya dunƙule ta riko hanun tace "har duka ba? har duka na zaka yi ba kaseem? to dakeni ka dakeni kaseem, idan har da gaske nice na haifeka kaseem ka dakeni" huci yake yi, sultan jikinshi yana rawa yace "ya kaseem ammi dan Allah" fadeel jingina yayi da jikin kofa yayi shiru, meenat juya baya tayi sam batason abinda ya faru ya kara faruwa, fizge hanunshi yayi yazo wajen hameed ya shafa kanshi yace "kar kaji tsoro babu abinda zai sameka ina tare da kai, bari na ɗauko maka riganka saimu tafi ko?" gyaɗa kai yayi, ta gefen ammi ya wuce ko kallonta bai kara yi ba, zama tayi a kasa ta ɗaura kanta a bakin gadon, wasu zafafan hawaye ne suke wanke mata fuska, bata damu data share ba, kallonta hameed yake ya kasa yin komai sai binta yake da kallo, a hankali yazo yana share mata hawayen, a time ɗin ya kaseem ya shigo rige da rigan hameed ɗin bashi yayi yasa sannan yace "muje" sauka yayi a gadon suka fita ammi tabi bayansu da kallo hawayen yana kin tsayawa. "ɗan sarki jikan sarki yarima hameed barka da fitowa" ko kallonsu baiyi ba suka shiga motan ya kaseem yaja suka tafi, har suka hau titi kafin ya kaseem yace "sai can dare zamu dawo" gyaɗa kai yayi. _jiddah ce...✍️_ 08144818849 [20/08, 2:11 am] Shuraihu Usman: 🌸🌸🌸🌸🌸 *ƘADDARA TA* 🌸🌸🌸🌸🌸 Na *Jiddah S Mapi* *Chapter 3* ~Asibitin sukaje, ya saba zuwa dama a office ɗin kaseem ɗin yake zama, akan royal sofan ya zauna ya kaseem kuma ya zauna a kujeran da yake zama kullum, yana duba laptop nashi, ɗago kai yayi ya kalli hameed ɗin yaga ya zuba mishi ido, gira ya ɗaga mishi alaman ya akayi? murmushi kawai yayi, wayanshi ya ciro daga aljihu ya fara typing ya kaseem ya ɗau wayanshi dan yasan sako zai tura mishi, gani yayi ya rubuta mishi "ya kaseem ka daina yiwa Ammi tsawa please" kallonshi yayi sai kuma yace "okay zan daina" wayanshi aka kira da sauri ya ɗaga ganin numbern asibiti ne, amsawa yace "dr na'eem ya akayi?" yace "emergency ne yanzu sir kazo dan Allah abin yafi karfinmu" da sauri ya tashi yace "ina zuwa" fita yayi hameed yabi bayanshi da kallo, ɗakin emergency ya nufa, gani yayi rabin ma'aikatan lafiyan asibitin suna tsaye a kanta sun rirriketa amma duk da haka tana kokarin watsar dasu, jujjuya kanta take idonta a rufe, masha Allah kyakkyawa ce ajin karshe fara ce sal gashinta me tarin yawa ya barbazu a bayanta amma yayi datti sosai kuma da alama birgiman da takeyi yasa bakin kayan jikinta da gashinta sukayi datti, suna ganinshi sukace "ga babban dr yazo" matsa mishi sukayi tana ganin sun saketa ta dira daga gadon zata fita ya rike hanunta cikin sanyin muryanshi yace "ina zakije?" tunda aka kawota asibitin sai yanzu taji anyi mata magana cikin nutsuwa jikinta ne yayi sanyi ta tsaya amma bata juyo ba, bai saki hanunta ba yace "fita zakiyi? me zakije yi a waje?" muryanta yana crack tace "zanje wajen mama na" ya kalli dr na'eem yace "tare dawa suka zo?" na'eem yace "mamanta ce kuma tun kafin a karaso dasu maman ta mutu itace tayi rai a motar da sukayi accident harda karamin yaro shima ya mutu" jikinshi a sanyaye yace "zakije kiga gawanta ne? meyasa kike fizge fizge sabida zakiyi faɗa da ƙaddara?" girgiza kai tayi, a hankali yazo gabanta ya tsaya sunkuyar da kanta dake fitar da jini tayi yace "koda kinyi kuka wanda ya mutu ba zai dawo ba" faɗawa tayi jikinshi ta kanƙameshi, sai yanzu ta samu wani kuka me cin rai ya kubce mata, shiru yayi yana kallon bayanta, cikin kuka tace "na kasa taimakon mama da Aliyu duk sun mutu ina kallo na kasa yin komai yanzu banada kowa banada kowa" cikin tausayinta da yaji ya ɗaura hanu a bayanta a hankali ya shafa bayanta yace "kiyi hakuri ki rinƙa addu'a insha Allah komai zai zamo miki da sauki" tace "to na gode" sakinshi tayi tace "zanje naga gawan mama" yace "muje" tafiya ta fara wani irin jiri da yunwa suka zo mata a lokaci ɗaya baya baya ta fara tana rike da kanta da har yanzu bai daina jini ba, zubewa kasa tayi, kaseem yayi saurin ɗagata, ta suma ya fita da ita, hameed daya gaji da zaman office ɗin ya fito domin yasha iska ganin ya kaseem rike da mace ga jikinta duk jini kuma a sume take yayi saurin bin bayanshi, akan gadon marasa lafiya ya kwantar da ita kallon hameed ɗin yayi wanda ya zuba musu ido da alaman tambaya akan fuskanshi, kaseem yace "accident tayi kuma da alama akwai damuwan da take ciki ka zauna kusa da ita bari naje na kawo abinda za'a bukata na kulawa da ita" a hankali yaje kusa da ita ya tsaya, ido ya zuba mata yana kallon kyakkyawan fuskanta, babu jimawa kaseem ya shigo ɗauke da abubuwan buƙata, fara dubata yayi ya tabbatar bataji ciwo ta ciki ba, sannan ya wanke mata jinin goshinta yayi dressing ciwon, ɗaura mata farin bandage ya fara, gashinta da yake da tsawo ya rufe mata fuskan, baya kaseem ya fara maida gashin amma idan wuyanta ya ɗan faɗa sai gashin ya kara zubowa ya rufe fuskan, hameed dake tsaye yana kallonsu kaseem ya kalla, yace "taimaka min na ɗaura mata bandage" zama yayi kusa da ita, zai rike hanunta yaga kaseem ɗin ya saketa ta faɗa jikinshi, ji yayi kirjinshi ya bada wani sautin da baisan na mene ne ba, ji yayi ya rasa duk wani tunaninshi na lokaci ɗaya, kaseem yace "gyara mata gashin" a hankali ya dawo hayyacinshi kame gashin yayi ya mayar baya, ɗaura bandage ɗin yayi saida ya gama yace "yawwa kwantar da ita" kwantar da ita yayi akan gadon kaseem yasa mata drip ɗin da zai kara mata karfin jiki, tashi hameed yayi zai tafi kaseem yace "ka zauna kusa da ita mamanta ta rasu tareda kaninta kuma inada tabbacin harda mahaifinta domin gawa huɗu ne a motan duk da driver, tana fizge fizge dole a samu me zama kusa da ita zanje ayi shirya gawan kafin ta tashi" shiru yayi ya zubawa kaseem ɗin ido har ya gama maganan, bai jira reaction nashi ba ya fita ya rufe kofan, shiru yayi yana kallonta ji yayi tana bashi tausayi tunda mamanta da babanta sun rasu bayaso yaga mutum maraya sai zuciyanshi ya karaya. Kaseem yasa aka shiryasu suna jiran tashinta kawai domin ta faɗi inda ƴan uwansu suke, yayi tagumi ya gaji gashi har yanzu ya kaseem bai shigo ba so yake yaje yayi bacci har kanshi yana ciwo sabida ɗan zaman da yayi, a hankali ya fara motsa hanunta kallonta yake tana buɗe ido har ta gama buɗewa ta kalleshi, kallon drip ɗin tayi sai kuma ta kara kallon ɗakin da take ciki, fizge drip ɗin tayi da ihu tace "mama, baba, Aliyu" toshe kunne yayi sabida baison ihu, grey eyes nashi ya zuba mata yana kallonta, dira tayi daga gadon zata fita a guje, riketa yayi sabida tuna maganan ya kaseem kada ya bari ta fita, tana kwace kanta tace "ka sakeni nikam ka sakeni mama!!! baba!!!" danneta yayi da karfi ta kasa ko motsi sai ihu take, akan gadon ya komar da ita ya kwantar da ita sannan ya zuba mata ido, tana kallonshi tace "waye kai? meyasa bakayi magana ba?" ɗauke kai yayi daga kallonta amma har yanzu bai saketa ba, ta fara tsorata dashi tace "kai ba doctor bane kuma ban sanka ba, meyasa ka rikeni? ka sakeni naje nayi wajen mama" bai saketa ba, shiru tayi ganin baida niyan cutar da ita, numfashi ta fara maidawa a hankali ta jingina kanta da bangon gadon tana kallonshi yadda ya kauda kai daga kallonta, a haka ya kaseem ya shigo, da sauri ya karaso yana cewa "am sorry na barka tun ɗazu wani aiki ne ya taso" sakinta yayi ganin ya kaseem ɗin ya shigo, karkaɗe hanunshi ya fara wai sabida datti, sai kuma ya juya zai fita ya kaseem yace "hameed" tsayawa yayi yace "dawo" dawowa yayi, ya kaseem yace "ki faɗi gidanku da ƴan uwanku sai hameed ya kaiki ki kirasu suzo su karɓi gawan" wani sabon kuka ne ya kwace mata, har tayi me isanta kafin ta share hawaye tace "banada kowa sai mama da baba da kanina Aliyu, baba yace baida dangi itama mama haka yauma barin garin zamuyi sabida baba baida lafiya kuma mai gidanmu yace idan bamu biya kuɗin haya yau ba zaisa a watsar mana da kayanmu waje hakan yasa baba yace mu koma kauye da zama shine a hanyan zuwa mukayi hatsari" shiru sukayi suna kallonta su duka, tausayinta ya cika musu zuciya, kaseem ne yayi karfin halin cewa "kenan babu wanda za'a kira?" jijjiga kai tayi, cikin tausayi yace "to bari mu tara mutane aje ayi jana'iza" kanta kasa tana kuka me cin rai, tun kukan yana fita har muryanta ya dishe, kallon hameed yayi wanda ya kasa ɗauke idonshi a kanta, yace "muje hameed" a hankali yabi bayanshi koda zasu fita juyowa yayi ya kara kallonta, fita sukayi aka kaseem yasa aka fito da gawan, kwantar dasu akayi a kasa kafin mutane su taru ya koma ya fito da ita domin tayi musu addu'a, babu takalmi a kafarta ga kanta dake ɗaure da bandage ga kuma idonta da suka koma kamar jan gauta, a hankali ta zauna a gabansu ta haɗa hanu biyu ta ɗaga sama, addu'a ta fara da larabci kamar ba zata tsaya ba, kowa saida ya tausaya mata, da haka har ta gama ta tashi ta juya baya, hameed ne yaji zuciyanshi yayi nauyi, ɗaukansu akayi aka fita dasu, a hankali yazo inda take ya rike hanunta, bata kalleshi ba amma tana ji yana murza yatsunta cikin nashi, kaseem ɗauke kai yayi daga kallonsu, har akaje aka birne suka dawo, cikin sanyin jiki ta janye hanunta daga nashi, ɗan durkusawa tayi cikin girmamawa ta cewa kaseem "na gode sosai da taimakon da kukamin Allah ya saka da Alkhairi Allah ya biyaka da aljanna, ni zan tafi" tashi tayi zata tafi hameed ya kalli kaseem girgiza mishi kai yayi alaman kada ya bari ta tafi, kaseem yace "tsaya" taki tsayawa tace "babu abinda zan tsaya yi taimakon da kukamin na gode" kaseem yace "kinada inda zakije ne? ko a titi zaki rinƙa yawo ba tareda sanin inda zakije ba?" kasa tafiya tayi, sai kuma tace "koda banida inda zanje asibiti ba wajen zamana bane" yace "idan kin yadda muje gidanmu na tabbata amminmu zata rikeki sabida tanason rike marainiya" shiru tayi tana tsoron binsu kuma aki karɓanta a gidansu, yace "idan kin amince to" a hankali ta juyo ta share hawaye idanunta sunyi mata nauyi so take ta huta koda na ɗan lokaci ne, tace "na amince kuma na gode" murmushi hameed yayi, kaseem ya kalleshi rabon da yayi irin murmushin ya jima, yace "ina zuwa" office ya nufa ya ɗau makulli da laptop nashi da sauran kayan bukata ya rufe sannan yazo yace "muje" cikin ladabi tace "to" tafiya sukayi, gani tayi sun buɗe mata wani lafiyayyen mota, a hankali ta ɗago ta kalleshi cikin nutsuwanshi yace "shiga mana" shiga tayi ta zauna a baya, shi da hameed suka zauna a gaba, jan motan yayi suka tafi, kallon titi take tana wasa da yatsunta, ta kasa sakin jiki domin bata saba da shiga mutane ba, bacci takeji a hankali ta fara rufe ido, baccin da bata shirya mishi ba ya ɗauketa, hameed ta cikin madubin ya saci kallonta, ganin tana bacci ya zuba mata ido yana kare mata kallo, murmushi ne akan face nashi, kaseem ya kalleshi sai kuma ya ɗauke kai yaci gaba da driving yana kula dashi har suka isa gida yana kallonta ta madubi, makeken gate ɗin aka buɗe musu ya shiga, a compound yayi parking sannan yace "ke? ke? tashi mun iso" a firgice ta buɗe ido tace "mama!!!" shiru yayi ganin yadda ta firgita, cikin tausayi yace "mun iso fito" bin gidan ta fara da kallo, ganin gidan sarki ne yasa jikinta yayi sanyi ko dai sun kawota gidan sarki ne sabida ba zasu iya kaita gidansu ba? hameed ne ya fita, kaseem ya buɗe mata marfin a hankali cikin tsoro ta fito tana kallon dogalin da yazo da bulala a hanu yana russunawa yana yiwa su hameed ɗin kirari, hameed yayi mata alaman muje, kin tafiya tayi, dogarin ya ɗaga bulala ya nunata dashi yace "hattara ƴar talakawa yarima hameed ke miki magana" a tsorace taje bayanshi ta ɓuya domin ta tsani ko ganin bulala ne bale ace za'a watsa mata, murmushi yayi suka nufi ciki, a ranta tace "ashe yaran sarki ne" sunyi knocking ammi ce ta buɗe kofan turus ta tsaya tana kallonsu, kaseem yace "zamu iya shiga?" matsa musu tayi suka shiga, da ido yarinyar yake bin ko ina da kallo, a ranta tace "koda ta amince ba zan iya zama ba a wannan gidan ban saba da irin wannan gidan ba nafi sabawa da gidanmu wanda ɗakina dana Aliyu kanina katifa kawai muke dashi da kujeranmu guda ɗaya, sannan na saba da lalataccen gidanmu wanda muke zaman rufin asiri a cikinta, na saba da talauci ba zan iya zama a wannan kuɗin ba" ji tayi kaseem yana bawa ammi amsan tambayan da tayi na wacece ita? shiru ammi tayi jin abinda suka faɗa, sai kuma tace "amma kaseem...." hanu ya ɗaga mata yace "na san me martaba ba zai taɓa yadda a kyaleta ta tafi ba domin koda yaushe shi yake faɗa mana kada mu kyamaci kowa musamman talaka" tayi shiru tana kallon yarinyar data sunkuyar da kai kamar ma a tsorace take, tace "ya sunanki?" shiru tayi ta kara cewa "ya sunanki?" ganin batama san ana mata magana ba ta taɓata, firgigit tayi tace "wayyo" hameed kallonta yake yadda take tsorata yafi komai tsaya mishi a rai, tace "ki nutsu babu me cutar dake a cikinmu ya sunanki?" a hankali tace "ANEETA" murmushi tayi tace "sannunki Allah yaji kan iyayenki" tace "ameen" meenat data shigo ta aje jakanta tana kallonta tace "Ammi wacece wannan?" tace "sunanta aneeta kaita ɗakinki tare zaku zauna tayi wanka taci abinci ta huta" tace "to" hanunta ta rike tace "muje" tashi tayi a yanayinta na tsoro take binta, stair da zasu hau tayi saurin yin baya taki tafiya, minat tace "muje mana" tana kallon stair idonta cike da tsoro tace "ba zan iya ba" dariya minat tayi sosai Ammi tace "ba dariyanta zakiyi ba riketa zakiyi sabida ba lafiyane da ita ba" riketa tayi tace "to muje" damke hanunta tayi suka fara hawa, ihu tayi kafanta yana rawa tace "zan faɗi" minat tace "ba zaki faɗi ba" da kyar ta haye da ita, kallon kasa tayi sai kuma taji jiri yana ɗibanta tace "ina jin jiri" minat tace "ki daina kallon kasa" tace "to" hanunta ta rike suka tafi ɗakinta, a bakin gado ta zauna tayi shiru, minat ce ta shiga ta haɗa mata ruwan wanka tazo tace "muje kiyi wanka" tace "to" tashi tayi cikin tsoro ta bita, nuna mata yadda zatayi wankan tayi sannan ta fita, cikin rashin iyawa ta fara wankan bata taɓa ganin wannan abin ba ko a tv bata kallo bale tasan yadda ake amfani dashi, saida ta gama kafin ta fito ɗaure da towel kanta yana yoyon ruwa, minat wacce ta cire mata kayan da zata sa tace "kin fito?" cikin sanyin muryanta tace "eh" dryer ta ɗauka tace "bari na busar miki da gashin" kallon abin take babu ko kyafta ido da alama fa yau ta fara gani, jonawa tayi zata kai kanta da sauri tayi baya, minat tace "busar miki da kai zaiyi" tace "amma ba zaiyi zafi ba?" tace "babu zafi" dawowa tayi tana kallonta ta fara busar mata da kan, tace "yawwa ya bushe saura kisa kaya" kayan ta karɓa tasa yayi mata kyau dogon riga ne na kanti ta bata hula tasa a kanta da tayi mata parking na gashin, tace "bari na kawo miki abinci" fita tayi jim kaɗan ta dawo da katon plate, aje mata tayi tace "sauko kici" girgiza kai tayi tana hawaye tace "ba zan iya cin komai ba" minat ta lallaɓata da kyar ta yadda taci abincin kaɗan sannan tace "zanyi bacci" tace "ki kwanta" kwanciya tayi a kasa, da sauri tace "tashi ki hau gado" tace "a,a anan ya isa" tace "dan Allah ki tashi" a hankali ta tashi ta hau gadon ta takura kanta ta kwanta ta rufe ido, wahallallen bacci ya ɗauketa. Ammi ta kalli kaseem da zai tafi tace "baka tunanin zaka iya kuskuren kawo wata gidannan?" yace "babu kuskuren da za'a kara yi a gidannan wanda ya kai naki" tace "kaseem kasan fa..." hanu ya ɗaga mata yace "dan Allah, dan Allah ammi ki kyaleni banaso ina faɗa miki magana mara daɗi" ta goya hannaye a bayanta tace "shikenan kaseem komai kayi daidai ne" tafiya yayi, hameed ya jima da komawa ɗaki, magani kaseem ya bawa minat yace idan ta tashi a bata tasha. _Jiddah Ce..._ 08144818849 [20/08, 2:11 am] Shuraihu Usman: 🌸🌸🌸🌸🌸 *ƘADDARA TA* 🌸🌸🌸🌸🌸 Na *Jiddah S Mapi* *Chapter 4* ~Har dare tana bacci babu wanda ya tasheta, sultan dake zaune a dinning suna cikin abinci tare yace "minat ya akayi bata tashi ba har yanzu? ko dai ta mutu ne itama?" hameed wanda yasa abinci a baki kwarewa yayi jin abinda sultan ya faɗa, ruwa kaseem ya mika mishi, karɓa yayi yasha sannan yace "sultan ka rinƙa faɗan alkhairi ko kuma kayi shiru" yace "to yaya" a hankali take takowa tana rike karfen gam gam da iya karfinta, rufe ido tayi sabida tana tsoron abin sosai, minat data kula da ita da sauri ta tashi, missing step tayi zata faɗi duk suka waro ido a tsorace harda me martaba, minat ce tayi gudu ta riketa, kankame minat ɗin tayi sosai taki buɗe ido, karasa sauka sukayi tare, a hankali ta buɗe idon ta sauke akan hameed dake rike da spoon cike da abinci har yanzu yana kallonta, murmushi tayi mishi me sanyi, sunkuyar da kai yayi yaci gaba da cin abincin, minat taja mata kujera ɗaya tace "ki zauna" kin zama tayi ta durkusa kasa ta gaida Abi, cikin kulawa ya amsa sannan yayi mata ya hakurin rashi, ta amsa da Alhmdllh, yace "tashi ki zauna ki saki jikinki ki ɗauka nan gidanku ne" shiru tayi tana durkushe, yace "tashi mana" cikin sanyin muryanta tace "zaifi kama na zama baiwa a gidannan banida matsayin zama ƴa" da mamaki abi yace "baiwa kuma?" tace "eh" yace "no kema kamar ƴa kike a gidannan bada sonki kikazo ba, kuma ke marainiya ce gaba da baya insha Allah zakiyi zama kamar kowa a gidannan ki zama me ƴanci ba baiwa ba" tace "to idan ba zaiyi na zama baiwar ba ko ƴar aiki zan zama" murmushi yayi yace "tashi ki zauna ko ɗaya ba zaki zama ba" a hankali ta fara kuka, yace "share hawayenki kema ƴa ce a gidannan tashi ki zauna" ganin dogari ya shigo kuma da bulala a hanunshi shine yayi mata tsawa ɗazu tayi saurin tashi a tsorace ta zauna tana kallonshi da manyan idanunta, abinci minat tasa mata tace "kici sai kisha magani" ta fara ci kamar bata son ci, sultan yace "ni sunana sultan shi kuma wannan sunanshi fadeel, wannan shine babban yayanmu ya kaseem, shi kuma wannan shine yarima hameed shine magajin sarki" kallonshi tayi ya ɓata rai yana cin abinci, saida gabanta ya faɗi ganin yadda ya ɓata rai, a hankali tace "ni sunana Aneeta" yace "nice name unty aneeta" abincin taci kaɗan sannan ta karɓi maganin tasha, Ammi tace "sannu Allah baki lafiya" tace "ameen" Abi yace "gobe za'a naɗawa hameed rawanin yarima" tsit wajen ya zama babu wanda ya kara magana ko motsin kirki, yace "kwarai gobe zai zama cikakken yarima" ammi jikinta ya fara rawa, tayi karfin halin dannewa tace "Allah ya kaimu" sultan kallon kaseem yayi saide kaseem hankalinshi akan abinci ya ɗago yace "Allah ya kaimu" kallon Ammi aneeta tayi tana ganin yadda take danne halin da take ciki, da mamaki take kallonta to ba itace ta haifeshi ba? sultan yace "na manta ban faɗa miki ba wannan itace ammi itace ta haifemu duka banda wannan iyayenshi sun rasu ɗan kanin abi ne" ya nuna fadeel, murmushi tayi mishi tace "sannu" yace "yawwa" da haka suka gama cin abincin kowa ya watse, ɗakin ta koma itada minat taga minat tana karatu murmushi tayi tace "zaki rinƙa koyamin karatu?" tace "eh me zai hana?" tace "na gode" kwanciya tayi amma bacci yaki ɗaukanta sai tunani kala kala take a cikin ranta da kyar baccin ya ɗauketa. hameed yana zaune a bakin gado yayi tagumi, turo kofan kaseem yayi a tsorace ya kalleshi sabida yasan allura zaiyi mishi, murmushi yayi yace "sannu hameed" ɓata rai yayi dan fa shi ya tsani wannan alluran, zama yayi kusa dashi ya mika mishi hanu suka gaisa yace "congratulations in advance" taɓe baki yayi alaman for what? yace "zaka zama cikakken yarima gobe duk ranan da babu Abi ina alfaharin zamanka sarki" ɓata rai yayi, yace "ka daina ɓata rai sabida Allah ne ya baka wannan matsayin" alluran ya ɗauka yace "time for injection" hawaye ne ya taru a idonshi ya fara girgiza kai, cikin tausaya mishi yace "sorry bro ba zaiyi zafi ba i promise" hanu ya mika mishi alaman yayi alƙawari, sarke hanun yayi cikin nashi yace "promise" a hankali ya tashi da kanshi yayi kasa da wandon aka mishi alluran baiyi zafi sosai ba, yace "kwanta to" kwanciya yayi akan gadon kamar kullum shafa lallausan gashinshi ya fara har yayi bacci kafin yayi mishi kiss a forehead ya fita, ɗakinshi yaje ya zauna akan sofa yayi shiru yana tunani idonshi a rufe kamar me bacci, ajiyan zuciya ya sauke ya fesar da iskan bakinshi. Fadeel ne kwance akan gado ya ɗaura kanshi a kafar sultan dake waya, yana jinshi yadda yake hira kamar wani babba, saida ya gama yace "sultan" yace "yes bro" yace "meyasa ya hameed baison zama yarima?" taɓe baki yayi yace "kuma dole zai zama ba?" yace "to idan baya so kada a bashi mana aba ya kaseem" sultan pillow ya janyo ya ɗaura kanshi yace "ka samu Abi ka faɗa masa" tsaki fadeel yaja yace "kai sai ana magana ka sakowa mutane shirme" yace "good night" bacci ya fara shi kuma fadeel tunani yake meyasa zasu bashi bayan ya nuna bayaso? kuma ga ya kaseem shine babba meyasa basu bashi ba? sai wanda bayaso za'a bawa?" da wannan tunanin yayi bacci. washe gari shirye shirye ake a gidan sarkin duk bayin gidan suna girki saura suna shirya babban wajen da ake taro a gidan, komai ya zama daidai akan tsari ga kujerun manyan bakin da za'ayi ciki harda governor, wajen zaman yarima kusa dana sarki, ciki kuma kaseem ne yake shirya hameed wanda yaki yin komai tunda yayi wanka yake zaune yaki yin komai, da faɗa kaseem ɗin ya fara shiryashi, tsadadden alkyabban da Abi ya bashi yasa mishi akan shaddan jikinshi me tsada, murmushi yayi ganin yadda golding na alkyabban yayi mishi kyau sosai, hulan sarautan yasa mishi sannan ya bashi mafici irin na sarkin, durkusawa yayi kasa yana sa mishi takalmin da yake irin alkyabban, ido ya zubawa ya kaseem ɗin yana jin sonshi har cikin ranshi, a hankali ya ɗago ya kalleshi, yace "kanina kayi kyau sosai" a hankali ya tashi ya rungume kaseem ɗin, shiru sukayi, kaseem yaji baida niyan sakinshi janye jikinshi ya fara sai kara kanƙameshi yake, da kyar ya janye yana kallon kyakkyawan fuskanshi da yake hawaye, share mishi hawayen yayi yace "yau ranarka ce bai kamata kayi kuka ba, idan Abi ya gani ranshi zai ɓaci" sunkuyar da kanshi yayi, sandan sarauta me tsada da kyau ya mika mishi ya karɓa, nan take wankan ya kara mishi bala'in kyau, turare me kanshi ya fesa mishi sannan yace "masha Allah kanina kayi kyau sosai" knocking akayi yace "yes" Ammi ce ta shigo sanye da alkyabban da bayan yake jan kasa, tasa hulan alkyabban akan gashinta da yasha gyara sannan tasa ɗankunne da abin goshi na gold, rike take da plate na flower a hanunta, saide fa fuskanta babu annuri ko kaɗan babu alaman murmushi, kaseem kallo ɗaya yayi mata ya kauda kai, hameed kuma ya zuba mata ido har ta karaso, tace "mai martaba yace mu fito tare an gama shirya komai kuma baƙi sun hallara" kaseem yayi saurin sa kayanshi shadda maroon me masifan kyau, ya fesa turare sannan yasa hula maroon ya riko hanun hameed ɗin yace "muje" tana bayansu suna gaba da plate ɗin flower a hanunta, suna fita su sultan da sukayi anko cikin maroon na shadda irin na ya kaseem ɗin suka zo suna mishi sannu, murmushin karfin hali kawai yake musu, minat da gudu ta sauko daga stair ɗin ɗakinsu tayi bala'in kyau cikin baƙin shadda irin wanda ammi tasa kafin tasa alkyabban, dogon riga ne fited gown sai red veil da tasa a gefen wuyanta, tace "wow yaya yarima kayi kyau" murmushi yayi mata sannan ya fara kallon sama inda yake kin karan takalmi da kamshin turare, aneeta ce take takowa cikin tsoro ta damƙe karfen stair masha Allah tayi bala'in kyau cikin baƙin shadda, itama irin ɗinkin minat ne amma ya kama jikinta sosai hakan yasa take rufewa da red veil ɗin sabida bata saba sa kaya masu kama jiki ba, bata mantawa kullum mama cewa take kada ta rinƙa sa kaya masu kama jiki domin yanayin jikinta mai ɗaukan hankali ne, ya kasa ɗauke idonshi a kanta, kaseem da yake mishi magana yaga yana kallon waje ɗaya shima ya kalli inda yake kallo, murmushi yayi ya zuba mishi ido, har saida ta sauko kafin ya kauda kai daga kallonta, sai a lokacin ya kalli kaseem, da sauri ya sunkuyar da kai sabida kunyan kashe mishi ido da kaseem ɗin yayi, durkusawa tayi ta gaida kaseem ɗin tareda hameed ɗin, bai amsa ba ya ɗauke kai, ya kaseem ne ya amsa, ta gaida ammi ta amsa ba yabo ba fallasa, hanunta minat ta rike, kaseem da hameed ne a gaba su kuma suna bayansu, suna fita a falon suka fara taka red carpet ɗin da aka shimfiɗa me matukar kyau, duk bayi da dogarai suna tsaye a gefe gefe sun sasu a tsakiya kan red carpet ɗin, ammi ta mikawa ɗaya daga cikin bayin plate ɗin sannan ta fara watsa mishi flower, algaita ake hurawa tareda busa sarewa, masu kiɗin garaya suka fara, ana mishi kirari, da haka har suka isa inda zasuyi taron, makil mutane suka cika wajen, manya manyan mutane ne harma da kanana, mutanen gari dana nesa dana kusa duk sun hallara, tun daga nesa mai martaba ya fara murmushi ganin kyaun da hameed yayi, hankalinshi kwance yake idan ya mutu ya bar hameed ne zaiyi gadon sarauta hakan yasa yake gaggawan bashi wannan matsayin na yarima, har ya karaso ya durkusa kasa ya yiwa abi alaman gaisuwa, ɗagashi yayi ya zaunar dashi akan kujeran, flower aka watsa sannan aka tafa mishi domin ya zauna a kujeran yarima, su kaseem dasu ammi suna kujeran gaba gaba, gomna aka bawa waje ya fara jawabi, daga nan Abi yayi magana cikin nutsuwa, karɓan sandan hanunshi yayi ya aje a gefe sannan ya kalli sabon sandan da aka bawa gomna wanda dashi zasuyi amfani wajen mikawa hameed wannan girman na yarima, ɓare tsadadden sandan gomna yayi a leda sannan yazo gaban hameed ya tsaya Abi ya tashi shima yasa hanu akan sandan zasu mika mishi, hameed ganin baiwa rike da plate da kuma wuta kaɗan akai, ya zuba mata ido, jikinshi ne ya fara rawa, Abi ganin haka yace "relax hameed babu abinda zai sameka" baya baya ya fara yana waro manyan idanunshi, girgiza kai ya fara kamar sabon mahaukaci, da sauri ya bige sandan zai gudu, ya kaseem dake zaune da gudu ya tashi yazo ya rikeshi, a kunnenshi yace "hameed ka nutsu cikin mutane muke" girgiza kai ya fara yana kwace jikinshi daga na kaseem ɗin, fizge fizge ya fara yana nuna wutan, mutanen wajen kowa ya fara tsorata ganin halin daya shiga, take zufa ya jiƙa goshinshi, ya kaseem ya kankameshi sosai yana hanashi fizgewan, Aneeta da mamaki take kallonsu sai kuma ta kalli minat tace "me yake faruwa dashi haka?" share hawaye minat tayi tace "baya son ganin wuta ko kaɗan ne, kuma...." kuka ne yaci karfinta ta kasa karasa maganan, a hankali ta janyota jiki tana shafa bayanta alaman tayi hakuri, idonta akan hameed daya kasa nutsuwa zuwa yanzu kaseem yanaso ya gagara control nashi, ga mutane da suka fara tashi zasu tafi sabida abin ya fara worst, a hankali ta saki minat ɗin ta tashi, wajen taje zuwa yanzu ya fara kaiwa kaseem duka a kirji, cikin sanyinta ta rike hanunshi dake dukan kaseem ɗin, ɗago jajayen idanunshi yayi yana kallonta, addu'a ta fara yi mishi a hanun, ji yayi jikinshi yayi nauyi, kaseem ganin ya ɗan nutsu ya fara sauke ajiyan zuciya, cikin sanyinta take addu'a tana tofa mishi, a hankali kaseem ya sakeshi tana rike da hanunshi, ji tayi ya faɗa jikinta ya kanƙameta kamar zai maidata cikinshi, bata damu ba taci gaba da karanta addu'o'i masu karfi tana tofa mishi a kunne da kuma kanshi, saida yayi shiru kamar wanda yayi bacci kafin ta tofa addu'a a hanu sannan ta zameshi daga jikinta ta shafa mishi a fuska, kallon baiwar dake rike da plate da wuta a kai wanda ta zuba turaren wuta tayi, da hanu tayi mata alaman ta tafi da wutan a wajen, tafiya tayi da wutan, a hankali ya dawo hayyacinshi ya kalli inda wutan yake yaga babu, kallonta yayi tayi mishi murmushi tace "babu wuta ka koma ka zauna" a hankali ya koma ya zauna yana kallonta, ya kaseem ya share zufa yace "ya Allah" gomna wanda ya ɓuya a bayan kujera ganin ya daina abinda yake ya fito yana neman sandan daya wurgar a gefe, ɗauka yayi yazo sarki ya tashi ya rike shima har idonshi yayi ja saboda halin da ɗanshi ya shiga, bashi sandan sukayi sannan sarki yace "YARIMA HAMEED" tafi akayi kowa yana murna, murmushi jabeer yayi yana tafa mishi, kowa ya shaida shine yarima, hulan kanshi aka cire sannan gomna ya ɗaura mishi rawanin sarauta nan take ya kara zama me kwarjini na musamman, tafa mishi ammi sukayi, da haka aka gama taron. kowa sai zuwa yake yana gaisawa da hameed tareda mishi congratulations, saide yayi murmushi ya gyaɗa kai da haka har taro ya watse, cikin gida suka koma su duka, kaseem wanda jininshi yake tafasa yana kallonsu da tsananin ɓacin rai akan fuskanshi yace "wallahi ban taɓa rantsuwan karya ba wannan abinda ya faru set up ne" Ammi wacce take huci tace "set up kamar yaya kaseem? baka ganin turaren wuta ta kawo?" idonshi sunyi jajur yace "turaren wuta? waya sata? dama ana kawo turaren wuta wajen naɗi ne?" tace "to kaseem wa kake zargi?" itama tayi maganan ranta yana tafasa kamat idanunta zasu zubo waje, kallonta yake babu ko kyaftawa yace "koma wa nake zargi babu ruwanki kuma na rantse idan har na tabbatar da wanda ya shirya wannan abin wallahi sai na hukunta meshi koma waye shi" da ihu yake maganan kamar zai fasa gidan, fita yayi daga ɗakin, hameed ya zube kan kujera yana rike kanshi ya tsani tashin hankali, ya tsani ihu jininshi hawa yake idan ana hakan, babu jimawa kaseem ya shigo hanunshi rike dana baiwar data kai wutan wajen yana janta kamar zai cire hanunta daga jikinta, wurgi yayi da ita a falon ya nunata da yatsa, jijiyoyin kanshi sun tashi yace "na rantse da Allah, na rantse da ubangijin daya halicci sammai da kassai idan har baki gayamin waye ya saki wannan aikin ba saina kasheki" Aneeta dafa kirji tayi jin abinda ya faɗa tayi baya a tsorace, bakin baiwar ya fara rawa, ya taka hanunta dake kasa yace "zaki gayamin ko ba zaki faɗa ba?" rufe ido ammi dasu minat sukayi ganin yadda ya taka hanun babu tausayi, ihu tayi ya sauke mata marin da yasa tayi shiru sabida azaba ya kara taka hanun wannan karon idanunsa kamar zasu zubo kasa yace "zaki faɗa ko saina kashe ki?" jikinta yana rawa ta kalli Ammi, da sauri Ammi ta juya baya, ya kalli inda take kallo ya kara taka hanunta wannan karon saida ya fara jini yace "zaki faɗa ko kuma?" ganin ba zata faɗa ba ya cire kafanshi daga hanunta a fusace ya haura stair da mugun gudu ɗakinshi ya shiga babu jimawa ya fito da bindiga karami a hanunshi, waro ido hameed yayi, sultan ya ɗaura hanu aka zaiyi ihu yasa hanu a baki ya toshe, Aneeta fitsari ne kawai bata yi ba, duk hantar cikinta ya kaɗa, batasan time ɗin data kankame hanun minat ba, tunda take bata taɓa ganin me zuciya idan ranshi ya ɓaci kamar kaseem ba, nunata yayi da bindigan yace "idan na irga uku baki faɗa ba wallahi saina harbeki" jikinta yana rawa tace "zan faɗa" duk suka kalleta a tsorace kenan da gaske sata akayi? yace "ɗaya...biyu...." tace "A..." kafin ta karasa ammi ganin yace "three" taje da gudu zata buge bindigan ba tareda ya cire hanu ba bindigan ya tashi take goshin baiwar ya fashe da bullet ɗin daya fasa mata har ƙwaƙwalwa, tsit ɗakin yayi babu wanda ya kara koda numfashi me kyau, bindigan rike a hanunshi ita kuma ammi tasa hanu a baki ta rufe idanunta a waje, Aneeta kuma fitsarin da take rikewa ji tayi kamar ma ya zubo, minat kuma tasa hanu aka ta kasa fasa ihun, hameed rufe ido yayi tareda kunnenshi ya toshe, Abi daya shigo yanzu ya kasa maida kofan ya rufe, jikin hameed ya fara rawa ganin ya jabeer baiyi dana sanin abinda yayi ba domin ko gezau baiyi ba bale yaje ya duba ko tana raye ko ta mutu, sunfi minti goma sha biyar a haka, da kyar ammi taja kafarta da yayi nauyi taje inda take kwance tana kiran sunanta "A'isha? Aisha?" da ihu kamar zata fasa gidan tace "A'ishaaaa?" kanta ta ɗaura akan ruwan cikinta tana kuka, ɗago jajayen idanunta tayi tana kallon kaseem da har yanzu yake rike da bindiga, cikin ihu tace "meyasa ka kashe ta?" murmushin gefen baki yayi yace "na kasheta? ko kuma kika kashe ta ba? ai da gangan kikazo kika bige bindigan sabida nayi harbi ban saniba" tana kallonshi da mugun mamaki har ta karaso wajenshi, hanu tasa ta shaƙe wuyanshi tace "akan me zan kasheta? me zaisa na kasheta?" tureta yayi yace "sabida bakyaso ta faɗi wanda ya sata" tace "kana nufin ni kake zargin na sata taje da wuta wajen naɗin hameed ɗana sabida ya fita hayyacinshi? ɗana dana san ganin wuta yana iyasa ya rasa rayuwarshi?" yace "kin damu da rayuwarshi ko mutuwanshi ne?" kara shake wuyanshi tayi tace "kaseem kana nufin nice nasa taje da wuta?" yace "idan bake bace me yasa kika kashe ta? sannan kalman A ba Ammi yake nufi ba?" tureshi tayi ta kwala ihu cikin tashin hankali tace "kaseem ni kaɗai ce me farin suna da A a wannnan gidan? ni kaɗaice?" Juya baya yayi yace "ke take nufi" cikin zafi da raɗaɗin rai tace "Abi shine sarki Abdallah ba A bane? Aminat itace minat ba A bace? Abdulhameed shima ba A bane? ko kuma wannan bakuwar da kuka kawo itama ba Aneeta bace A ce ko ba A ba?" da ihu tace "kaima ba A bane? ko ka manta asalin sunanka Alkaseem ne?" shima da ihun kamar zai fasa ɗakin yace "sunana ba Alkaseem bane sunana kaseem ne" tana kallon cikin idonshi tace "ba zaka taɓa canjawa tuwo suna ba kaseem sunanka na gaskiya shine Alkaseem" jikinshi yana rawa yace "karki kara kirana da Alkaseem" tana huci tace "idan kuma na kara fa me zakayi? me zakayi Alkaseem" ganin yana nufota Abi wanda ya gama sankarewa a wajen yace "kaseem!!!" tsayawa yayi yana huci, yace "ko taku ɗaya idan ka kara zan tsine maka" bai kara ko taku ɗaya ba kawai ya juya baya, ammi tana kuka tace "kowa ya manta da baya, nice kaɗai ake ganin laifina kowa ya manta da abinda ya aikata a baya, wallahi tallahi saina tona" sultan yace "please ammi dan Allah kiyi shiru" tace "nayi shiru sultan? nayi shiru ana zargina? bayan kowa abin zargi ne a gidannan, har an manta farin sunan kowa nice kaɗai aka tuna nawa? ko kun manta wanda yake kulle a bayan gidannan shima ba A....." kujeran da hameed yake zaune akai ya ɗaga da karfi ya buga da kasa jin abinda ya faɗa, duk suka kalleshi a firgice, huci yake yi jikinshi yana wani irin rawa yana kallon ammi da idanunshi da suka rikiɗe suka koma jajur, take ya canja daga hameed ya koma asalin Abdulhameed, ammi ɓuya tayi a bayan sultan ganin yadda kujaran ya karye ga kuma hanunshi daya dunƙule yana huci sosai kamar zaki. _Jiddah Ce...✍️_ 08144818849 [20/08, 2:11 am] Shuraihu Usman: 🌸🌸🌸🌸🌸 *ƘADDARA TA* 🌸🌸🌸🌸🌸 Na *Jiddah S Mapi* *Chapter 5* ~Babu abinda yake cin ranshi kamar maganan dake bakinshi wanda ba zai iya faɗanshi ba, Abi ganin haka yazo da sauri zai taɓashi yayi baya yana girgiza kai alaman baison kowa ya taɓashi, Abi yace "hameed dan Allah kayi hakuri" juyawa yayi a fusace yaje wajen kaseem, bindigan ya kwace ya saita kanshi, waro ido kaseem yayi ganin yana huci yana shirin harba bindigan, Aneeta cikin tashin hankalin da tunda mama da baba suka haifeta bata taɓa gani ba tace "dan Allah kada ka kashe kanka dan Allah" ya kaseem yace "hameed kada kayi wannan kuskuren wallahi idan ka kashe kanka shima saina kashe shi" hawaye ne suka fara wanke mishi fuska ga magana amma babu bakin faɗa, ganin da gaske yake kaseem ya buɗe drower dake bayanshi kusa da tv, ciro bindiga yayi ya nufi waje, a kiɗime ammi tace "kaseem ina zakaje?" juyowa yayi ya kalli hameed yace "kina ganin idan hameed ya mutu zan kyaleshi ne? kafin ya kashe kanshi saide su mutu a tare" hameed bindigan yasa hanu a kunaman ya harba, Aneeta da tazo da gudu ta rungumeshi ta wurgar da bindigan gefe kafanta bullet ɗin ya sama, kara tayi cikin azaba ta kanƙame hameed da suka zube kasa tare, akanshi ta faɗi hakan yasa ya rike waist nata sosai idonshi a rufe, jigidan dake waist ɗinta yaji hanunshi a kai, cikin kuka tace "kafata" kaseem ne ya wurgar da bindigan yazo da gudu ya ɗagata yana duba kafarta dake jini, ammi hawaye ta share tace "shikenan tunda nice yanzu abin zargi kowa ya manta da laifinshi wanda aka lulluɓe sabida muninshi kafin ku kashe junanku ni bari na kashe kaina" Abbi dake tsaye yana jin kanshi da nauyi ya lumshe ido a wahale ya buɗe yana kallonta ta ɗau bindigan, sultan ne yaje ya rungumeta ya kwace bindigan yayi wurgi dashi, tace "sultan mutuwana shine alkhairi, sultan komai baya tafiya daidai komai baya gyaruwa sai daɗa ɓaci yake, sultan watakila idan na mutu komai zai daidaita" kanƙameta yayi yana shafa bayanta yace "shiru ammi" kuka take yi, kaseem ne ya rike aneeta ta zauna akan sofa tana ciza baki cikin hawaye, ɗaki ya koma ya ɗauko kayan aiki yazo ya fara cire mata bullet ɗin, tashi hameed yayi ya zauna a gefe yayi shiru yana kallon yadda take ciza baki tana rufe ido, cire mata yayi, rikeshi tayi tana ihun zafi, minat tace "sorry" shima cikin sanyin murya yace "sorry" saida ya tabbatar jinin ya tsaya kafin yayi dressing wajen, a hankali ya tashi yana kallonta zubewa kasa yayi ya haɗa hanu biyu yace "thank you, na gode sosai da kika ceci rayuwar hameed na gode" raba hanunshi tayi tace "ka daina min godiya ba kunce mun zama ƴan uwa ba?" cikin kuka yace "na gode" tace "ka daina yafi karfin komai a wajena kune kuka taimakeni kuma zan iya taimakonku a koda yaushe matukar zan iya" a hankali ya tashi, Abi waya ya kira babu jimawa wasu maza suka shigo gawan ya nuna musu cikin bala'in ciwon kai da nauyin da kanshi yayi yace "kuje ku binneta ku ɓoyewa kowa kada kowa ya sani" amintattunshi ne suna iya ɓoye komai wanda ya shafeshi matukar yace musu su ɓoye koda baice su ɓoye bama ɓoyewa suke bale yace su ɓoye, fita da ita sukayi ta kofan baya, aneeta binsu tayi da kallo har suka fita suka rufe kofan, bata taɓa sanin akwai kofa a wajen ba sai yau da taga sun buɗe domin ɓoye sirri, tashi hameed yayi ya fara tafiya fadeel ne ya rikeshi yace "yaya bari na kaika ɗaki" ɗakin ya kaishi ya zauna kawai akan gado yayi shiru, fita yayi, minat ce ta taimakawa Aneeta suka tafi ɗaki, ammi ma sultan ya kaita ɗaki, abi yana rike da kanshi ya wuce fada, har zazzaɓi yake ji baisan meyasa ba kullum lamarin gidanshi ɓaci yake, babu abinda yake tafiya daidai. Aneeta tana kwance tana kallon minat tana kuka, shiru tayi dan ta kasa gane meke faruwa a gidan, cikin sanyin murya tace "kiyi hakuri ki daina kuka komai yayi zafi zaiyi sanyi Insha Allah" share hawaye tayi tace "babu abinda zaiyi sanyi a wannan gidan babu shi aneeta komai kara lalacewa zaiyi babu abinda zai dawo daidai" shiru tayi tana kallonta, sai kuma tace "amma kada nayi shishigi waye ya kaseem yace zai kashe?" shiru tayi kamar ba zata amsa ba sai kuma tace "wani ne" tace "wanene shi?" girgiza kai tayi tace "wannan sirrin gidan sarautarmu ce, wannan sirrin babu wanda ya sani sai mu kaɗai ƴan gidannan kuma alƙawari ne babu wanda zaiji" tace "to shikenan Allah ya daidaita komai kiyi ta addu'a" tace "insha Allah" duk yadda taso tayi bacci ta kasa abinda ya faru yau ya tsaya mata a wuya data rufe ido yarinyar take gani a kwance, kenan suna iya kisa kuma su kwana lafiya? tsoron gidan ma ta fara fitsari takeji amma ta kasa tashi taje tayi haka take kwance data motsa kaɗan sai taga kamar zasu harbeta itama, kuma tasan babu abinda zai faru idan ta mutu, tashi tayi tace "anya aneeta ba zaki nemawa kanki hanya ba? anya ba gudu zakiyi ki bar gidannan ba?" kallon minat dake bacci tayi sai kuma ta kalli kofa, cikin sanɗa ta sauka daga gadon ta manta ma da zancen hijabi kawai ta nufi hanya ta fita a ɗakin, cikin sanɗa take tafiya duk gidan duhu ne sabida an kashe wutan, wannan al'adansu ne idan zasuyi bacci su kashe wuta, cikin gudun tayi tuntuɓe ta zube a kasa kara zatayi tayi saurin rufe bakinta da hanu, tashi tayi zata tafi taji kamar ana bubbuga kofa da sauri ta kalli kofan da ake bubbugawa taga kofan ɗakin hameed ne kamar zata tafi sai kuma wani abu yace ta tsaya ta duba menene, a hankali ta buɗe kofan ta shiga, taka mutum tayi ta waro ido a firgice zata kwala ihu taga hameed kwance a kasa yana birgima, da sauri tace "hameed? meyasa sameka?" hanunshi ya mika mata da sauri ta rike hanun, taɓa jikinshi tayi taji da zafi sosai, cikin tsoro ta taimaka mishi ya tashi, da kyar yake ciza baki yana runtse ido, takalmin data rike a hanu ta zubar ta zauna a bakin gadon ta taimaka mishi ya kwanta, tace "me yake damunka?" hanunta ya rike a razane ta kalleshi ganin ya cusa hanunta a cikinshi, zata kwace hanun ya damƙe da nashi, shiru tayi jikinta yana rawa ta kasa ɗauke idonta akanshi, gani tayi yana lumshe ido tareda kara tura hanunta cikin jikinshi, fizge hanunta tayi cikin tsoro ta tashi zata gudu dan bata taɓa ganin abu haka ba a rayuwarta, fizgota yayi ta faɗo jikinshi baki ta buɗe zatayi ihu ya toshe bakin, waist beads nata da yaji ɗazu ya fara wasa dashi, ganin tana kanshi idanunta sun kara girma sosai ba kaɗan ba, kwace kanta take ya kara danneta a kanshi yana kara wasa da waist beads ɗin, da kyar ta samu ta zame hanunshi daga bakinta zatayi ihu ya haɗa bakinshi da nata, cikin tashin hankali take bugunshi da karfi tana hawaye, wuntsila kafafunta takeyi tana neman hanyan tsira, so yake yace mata ta nutsu babu abinda zaiyi mata amma babu bakin magana, tun tana iya fizgewa har jikinta yayi sanyi tayi shiru kawai tana jinshi, a hankali ya zame bakinshi daga nata, juyar da ita yayi ta kwanta a gefenshi numfashinshi ke sauka akan dogon wuyanta, hanunta ya rike wanda ta kasa ko ɗagawa yasa a maranshi yana shafawa, jikinta har yanzu bai daina rawa ba, kuka take yi sosai kuma ta kasa magana, saida taji yayi shiru kafin ta faki idonshi ta dira a gadon da gudu zata fita a ɗakin, baya tayi a razane ganin ya kaseem daya shigo yanzu, da waya a hanunshi, kallonta yayi sai yaga ta sunkuyar da kai jikinta yana rawa, kallon miss calls ɗin da hameed ɗin yayi ta mishi yayi yau bacci ne ya saceshi shiyasa baiji kiran ba, baiyi magana ba itama batace komai ba, yace "jeki" raɓawa tayi ta gefenshi ta wuce a guje, kallon hameed daya lumshe ido kamar me bacci yayi, karasawa yayi ciki ya zauna a bakin gadon yana kare mishi kallo, lips nashi da sukayi pink sosai ya kara kallo sai kuma ya kalli kofan yace "tashi kasha magani" make kafaɗa yayi alaman no, cikin tsawa yace "tashi mana" tashi yayi yana yamutsa fuska, ya bashi ruwa da maganin yace "sha" buɗe baki yayi yasha maganin yana rufe ido, kwanciya ya kuma yi yana kokarin rufe kanshi da blanket ganin yadda kaseem ɗin yake kallonshi, ya rike blanket ɗin yace "me kayi mata?" shiru yayi yana turo karamin bakinshi, yace "me kayi mata nace?" yasan bazai iya amsawa ba amma tsaban haushi yasa yake mishi tambayan, tsawa ya daka mishi yace "me kayi mata nace?" a hankali ya ɗaura hanu akan lips nashi ya shafa, kaseem yace "kiss?" gyaɗa kai yayi, yace "kenan ba zaka iya hakuri ba idan kana ji bakasha magani ba? shine har zakayi kokarin raping mace?" girgiza kai yayi da sauri alaman ba raping nata yayi niya ba, tsaki yaja yace "hameed na rasa wani irin jaraba ne da kai sam bakada hakuri ko kaɗan bakasan a matsayin kanwarka take bane?" kanshi kasa yaki yadda su haɗa ido, ya kara jan tsaki yace "to Allah ya shiryeka ko ni da nake yayanka na girmeka nesa ba kusa ba banada wannan masifan jaraban" tafiya zaiyi ya rike mishi hanu, ya juyo yace "me kuma?" lumshe ido yayi, tsaki yaja shifa ya fara gajiya da lamarin hameed sai shegen lumshe ido kamar mace, yace "me kake so?" wayanshi ya karba ya fara typing, mika mishi yayi ya karanta (Aneeta nakeso) da mamaki ya kalleshi yace "to ai ba matarka bace ba yadda za'ayi tazo ta kwana anan" lumshe ido ya kuma yi ya kara typing (ka auramin ita) murmushi yayi bayan ya karanta kawai ya fita daga ɗakin ya rufe, Aneeta nunfashi take saukewa da kyar bayan ta koma ɗakin ta laɓe a bayan minat, a mugun tsorace take da gidan da kaseem harma da hameed wanda ya mata abinda bata taɓa zaton zaiyi ba yau, kuka ta fara tace "aneeta kin shiga uku baki lalace ba" minat da tayi kamar tana bacci dariya takeyi sosai sabida itace ma taje ta kira ya kaseem tunda ta fita taji karan kofa tabi bayanta har zuwa lokacin daya kaseem ya shiga ɗakin kafin ta dawo ta kwanta. haka har tayi kwana biyu a gidan bata yadda ta fito idan yana falo shima bai damu ba yasan idan ta gaji zata fito da kanta, a rana na uku minat ce ta sata dole ta fito sanye take da bakin dogon riga tayi kyau sosai fuskanta ya kara yin haske da kyau, zama tayi a kujeran dinning ta gaida Abi sannan ta gaida Ammi dasu kaseem, harda sultan ta gaishe sannan ta saci kallon hameed dake cin abinci bai ko kalli inda take ba, a hankali tace "ina kwana" gyaɗa kai kawai yayi kamar ma baisan da ita ba, kaseem ya kalleshi sannan ya kalleta yaci gaba da shan tea, mai martaba daya gama yace "Alhmdllh, Aneeta" da sauri tace "na'am Abi" yace "zan haɗa aurenki da hameed" ba ita ba har ammi da minat saida suka kaɗu da jin maganan, da kallo ammi ta bishi, kaseem yasan da maganan shiyasa bai damu ba, aneeta cikin bashi girma tace "to Abi" yace "kina sonshi?" shiru tayi tana kallon hameed dake cin abinci bai kalleta ba, yace "kina sanshi?" wasa take da yatsun hanunta a hankali ta gyaɗa kai, murmushi sultan yayi yace "wow abu yayi kyau" tashi Abi yayi yace "juma'a me zuwa aurenku saura kwana biyar kenan" tafiya zaiyi ammi tace "mai martaba" tsayawa yayi yana kallonta, tace "kamata a tabbatar tana sanshi kada a cutar da ɗaya" yace "gashi ta amsa shima da kanshi yace yana sonta" tana kallonshi tace "amma ai batasan komai ba" mai martaba ya ɓata rai kamar bai taɓa dariya ba, tace "ni ba zan bari a cutar da mutum ba, ya kamata tasan cewar Abdulhameed ya taɓa aure...." wani irin tsawa kaseem ya daka mata, shiru tayi tana kallonshi yace "ko sau ɗaya ko sau ɗaya ki zama...." tace "karka kuskura ka gayamin magana kaseem sabida kafin kowa sanin abinda yake faruwa, sannan kai kanka kasan cutarwa ne ayi aure da ɓoye ɓoye" cikin haushi da ɓacin rai da yake ciki yace "me amfanin tuna baya?" tace "sabida kasan duk bamu aikata mai kyau ba?" yace "kece dai amma ni..." tace "amma kai me? kai mutumin kirki ne kaseem? bakayi komai ba? kafi kowa sanin auren hameed ba karamin tashin hankali zai tono ba kafi kowa sanin irin masifa da bala'in da za'a shiga matukar hameed ya samu sarautan yarima kuma yayi aure kafi kowa sanin abinda zai faru..." buga kujeran yayi kamar zai ɓalla, saida abincin dinning ɗin duk suka zube, yana kallon cikin idonta yace "me zai faru? me zai faru nace idan hakan ya faru?" dariyan bakin ciki tayi wanda kana gani kasan ba har cikin ranta tayi ba, tace "ina fatan baka manta cewar ABDULHAKEEM bai mutu ba yana raye......" kamar zai fasa kunnuwansu yace "ya mutu zuwa yanzu ya mutu a inda yake baya raye" itama kamar zata fasa kunnuwansu tace "Abdulhakeem...." ihun da aneeta tayi yasa suka kalleta babu shiri, tana rike da hameed daya yanka jijiyan hanunshi yana zubar da jini kamar jikin jikinshi zai kare, ammi ce ta kwala ihu taje da gudu zata taɓashi kaseem yace "stay away from my brother" yayi maganan cikin tsananin ɓacin rai, kasa taɓa hameed ɗin tayi sai rawa da jikinta yake, kaseem yana hawaye yace "idan ya mutu shikenan? duk zaku huta idan ya mutu?" zama yayi akan kujera ya harɗe hanu a kirji yace "to shikenan Aneeta barshi ya mutu, watakila komai ya dawo daidai idan Abdulhameed ya mutu" yana maganan yana hawaye me zafi, yace "amma ki sani" ya nuna ammi yace "wallahi idan Abdulhameed ya mutu ko Abdulhakeem bai mutu ba saina kasheshi nayi alkawari" zata taɓashi cikin tashin hankali ya kara daka tsawan da yasa jikin aneeta fara rawa yace "don't dare touch him Ammi" cak ta tsaya, mai martaba kirjinshi ya rike yana jin jiri, kasa tim ya faɗi kaseem yana kallonsu babu abinda yayi sai naɗe hanu da yayi a kirji, yana kallon sultan dasu fadeel suna ihu, masu tsaro ne suka shigo jin ihu da wani irin tsawa kaseem yace su fita, jikinsu yana rawa suka fita, aneeta tana ganin jini yaki tsayawa ta sauke kanshi daga cinyarta daya gama ɓaci taje gaban kaseem ɗin ta durkusa, kafanshi ta rike cikin tashin hankali tace "dan girman Allah ya kaseem dan girman Allah ka taimaki hameed idan ya mutu ban san yadda zanyi ba, dan Allah ka taimakeshi jininshi yana gab da karewa" ɗauke kai yayi ya juya yana kallon gefe yace "Aneeta ki barshi ya mutu" ganin ba zai kulata ba taje da gudu ta cire ɗankwalin kanta ta ɗaure hanunshi dake jinin gam, janshi tayi a kasan zuwa kan sofa, kankara ta ɗauko a fridge tazo da gudu kamar mahaukaciya manna mishi tayi a hanun sabida ya daskarar da jini, tayi sa'a jinin ya daina gudu sosai ya ɗan tsaya, ta sauke kanshi daga cinyarta ta ɗaura akan sofan ta haura sama da gudu, first-aid-box ta ɗauko da sauri ta dawo ta ciro audiga da bandage kamar yadda taga anayi ta fara dressing ciwon, cikin sa'a Allah ya taimaketa hanun ya daina jini, tashi tayi ta fita ta kira driver taje asibiti, yaki shigowa da kanta ta ɗagashi ta fita dashi, sai nishi take sabida wahala, a mota suka tafi asibitin ya kaseem ɗin, suna ganinshi suka fara taimakonshi da gaggawa, Allah yasa suka ɗinke ciwon, yana kwance akan gadon tana zaune a gefenshi ta haɗa kanta da jikin gadon tana kuka, a hankali ya buɗe ido yana jin sautin kukanta, ji tayi ya rungume waist nata ya manna kanshi da bayanta, shiru tayi ta share hawayen, a hankali ta juyo gaba ɗaya ta yadda zaiji daɗin hugging ɗinta, a hankali ya matso sosai ya manna kanshi da kirjinta yayi shiru, shafa kanshi tayi cikin jin daɗi tace "Alhmdllh baka mutu ba na gode Allah" murmushi taga yayi, hanunta ya rike yana kara cusawa a kanshi, cikin farin ciki taci gaba da wasa da gashinshi, lumshe idonshi kawai yayi. turo kofan akayi ya kaseem ne ya kasa zama duk yadda yaso ya bari hameed ya mutu ya kasa yin hakan, da sauri ta ture kanshi yaki sakinta sai daɗa kanƙameta da yake, cikin jin kunya tace "sannu ya kaseem" hawaye yake yi yana jin kunyan haɗa ido da kaninshi da ɓacin rai ya hanashi taimakonshi yace "ke zan yiwa sannu aneeta gaskiya sai yanzu hankalina ya kara kwanciya idan kika yadda kika aureshi zanfi samun nutsuwa" a hankali tace "karka damu babu abinda zai hanani auren yarima hameed saide idan kaine ka hana ko kuma shi yace bayaso" yace "na gode" kallon hameed daya lumshe ido a jikinta yayi sai kuma ya kalli hanun dake ɗaure da bandage, yace "sannu hameed" gyaɗa kai kawai yayi yana kara kanƙame waist na Aneeta, tureshi takeyi ta kasa sakin jikinta duk a takure take, ganin haka kaseem yace "ina zuwa" fita yayi, da sauri tace "baka ganin ya kaseem ne?" shiru yayi mata, sun wuni a hospital ɗin sai dare kafin kaseem yazo yace su tafi, tafiya sukayi suna shiga gida kaseem yace "sultan ya jikin Abi?" yace "da sauki ammi tana can wajenshi" yace "Allah kara mishi sauki" sukace "ameen" sukace "sorry ya hameed" lumshe ido kawai yayi ya wuce ɗakinshi. _jiddah ce....✍️_ 08144818849 [20/08, 2:11 am] Shuraihu Usman: 🌸🌸🌸🌸🌸 *ƘADDARA TA* 🌸🌸🌸🌸🌸 Na *Jiddah S Mapi* *Chapter 6* ~Har aka fara shirye shiryen bikin babu wanda ya kara ɗago maganan, aneeta kam batama fita su zauna bale magana yayi nisa, kwance take akan gado dare ne kowa na bacci banda ita da take da tarin tambayoyi dayawa a kanta amma ta rasa wa zata yiwa, minat bata bata amsa koda ta mata tanbayan, shiru tayi sanye take da kayan bacci me kyau dogon riga silk, kasancewar silk yasa yake mannewa a jikinta sosai duk shape nata suka bayyana, net ne a wuyan rigan hakan yasa saman kirjinta da yake fari tas ya fito sosai, gashinta dake cikin net ta cire net ɗin sabida zafi sosai takeji, ishi ma ta fara ji, a hankali ta kunna wutan ɗakin ta sauke fararen santala santalan kafafunta, fita tayi daga ɗakin tana hamma ga bacci a idonta amma ta kasa yinshi ga ishi har gani take kamar ba zata isa wajen fridge ɗin tasha ruwa ba, wutan a kashe yake, sauka tayi ta buɗe fridge ɗin bayan ta kunna wutan, kashe wutan tayi ta haura stair ta buɗe ruwan zata fara sha, ji tayi an fizge goran, ihu zatayi ya toshe bakinta ya mannata da jikin bangon, idanunta kamar zasu zubo tsaban firgita, bakinshi yasa a wuyanta yayi mata sassanyar kiss, ta hanyan numfashinshi ta gane shi, ajiyan zuciya ta sauke, hanunta ya rike yana murzawa a hankali kuma yake kissing wuyanta, tureshi tayi tace "ka tsorata ni yarima" murmushi me sauti yayi sannan ya kara mannata jikin bangon ta yadda ba zata iya kwacewa ba, jin kiss ɗin yayi yawa tace "sakeni bacci nakeji" kin sakinta yayi, hanu taji yana sawa ta kasan riganta da sauri tace "kai yarima ka kyaleni" bakinshi ya haɗa da nata ta yadda ba zatayi magana ba, yadda yaso yakeyi da jikinta sai numfashi yake saukewa a hankali yana samun wani kyakkyawan nutsuwan da rabonshi dashi ya jima, idan yana tare da ita ji yake kamar ya mallaki komai na duniya na jin daɗi, tafiya take da imaninshi musamman idan tasa kayan da yake kama jikinta, hanunshi taji a bayanta yana pressing duk yadda tayi ta kwace ya hanata saima kara mannata yake da bangon kamar zai shige jikinta, so much pleasure yake samu idan yana taɓa jikinta, kaseem da ya tashi cikin bacci sabida ishi ya buɗe fridge nashi baiga ruwa ba sai drinks tsaki yaja yasa slippers ɗinshi ya fita, kunna wutan yayi zai sauka ya gansu, da sauri hameed ya saketa, kamar zatayi kuka ganin ya kaseem a ranta tace "na shiga uku nikam asirina ya gama tonuwa a wajen ya kaseem" hararan hameed tayi sannan ta juya kamar munafuka ta wuce ɗaki da goran ruwan a hanunta, kallonshi yayi baiyi magana ba ya wuce ya ɗau ruwan ya buɗe yana sha, har yanzu yana tsaye a wajen yana wasa da yatsunshi kanshi a kasa kamar munafuki, aje sauran ruwan yayi ya kama hanya kawai zai tafi, rike hanunshi yayi ya juyo yana kallonshi, hanu biyu yasa ya rike kunnenshi kanshi kasa alaman sorry, tsaki kawai yaja yace "wuce kaje ka kwanta" a hankali ya tafi zuwa ɗaki, kaseem ɗinne ya rufe mishi kofa yace "bad boy" Aneeta saida tayi hawayen kunya share hawayen tayi tace "yanzu zai rinka min wani kallo ko?" da kanta take tambayan kanta, tace "ba zan kara fita ba wallahi bale na haɗa ido da ya kaseem" da kyar ta samu tayi bacci. washe gari kin fitowa tayi tana kwance a ɗaki, jin hayaniya a waje yasa tayi saurin tashi domin leka meke faruwa, gani tayi wasu ƴammata guda biyu sun shigo da trolley ɗinsu, sunyi masifan kyau suna kama da alama yaya da kanwa ne, murmushi tayi jin ammi tace "oyoyo yarana yaushe a kasa?" karamar tace "jiya muka dawo momy tace mana auren ya hameed jibi shiyasa mukazo sai an gama zamu koma school next week" cikin jin daɗi minat ta rungumesu tace "gaskiya aurennan zaimin daɗi tunda kuna nan, muje ciki" ammi sai farin ciki take, dakinsu suka shiga tana ganinsu ta fara murmushi kamar ta sansu, ɗayar tace "itace amaryar ya hameed?" minat tace "yes itace" murmushi tayi tace "wow she's beautiful" minat tace "unty Aneeta waɗannan yaran kanwar momy ne amma ta rasu tun da jimawa a hanun dadynsu suke suna karatu a kasar cyprus yanzu ma hutu suka samu ya haɗu da aurenku" murmushi tayi ta buɗe musu hanu suka rungumeta tace "ya sunanku?" karamar tace "ni sunana Amnah ita kuma Amrah" tace "masha Allah sannunku da zuwa" sakin jiki sukayi suka fara hira kamar dama sun san juna, zuwa sukayi suka gaida me martaba sannan suka dawo suka zauna a falon, ganin babu aneeta minat taje ta kirata fitowa tayi ba dan taso ba suka fara hiran tare, sultan ne ya shigo tareda fadeel da gudu sukaje suka rungumesu cikin jin daɗin ganinsu yace "amnah da Amrah yaushe kukazo?" sukace "ɗazu" zama sukayi a falon suka suka fara hira, aneeta ma tana ɗan hira itama tare da ita suke yi, kaseem ne ya shigo da uniform a jikinshi yace "suwa nakejin muryansu kamar ƴan kauyen nan" dariya sukayi shima sukayi hugging nashi, Aneeta sunkuyar da kanta tayi tana jin mugun kunyanshi, murmushi yayi yace "Amarya harda ke aketa surutun?" a hankali tace "eh" janta yayi da hira har ta saki jiki. hameed bacci yake a ɗaki sai can ya tashi yana sanye da jallabiya ya fito yana murza ido yana yatsine fuska tareda turo bakinshi cikin shagwaɓan ɗaya same mishi jiki, ganinsu Amrah yayi musu smiling sannan ya musu alaman welcome, shi tsoronshi suke shiyasa basa sakewa sosai idan yana waje, kallon Aneeta yayi tayi saurin ɗauke kai tana tuna abinda yayi mata ranan, smiling me kyau yayi sannan ya kalli ya kaseem dake danna waya, ji yayi hankalinshi ya kwanta ganin ya kaseem lafiya lau yana smiling da alama abinda yake a waya me muhimmanci ne. Minat tace "unty aneeta zamu gyara miki kanki ko?" gyaɗa kai tayi, tace "muje to sabida me lalle zatazo da dare tayi miki" tashi tayi jikinta dama ba a sake ba ta bita suka nufi ɗaki, gyara mata tulin gashin tayi sannan da dare akazo aka mata lalle me kyau. kaya ammi ta siyo mata masu tsada da yawa da kuma kyau sannan ya kaseem yasa aka sauya ɗakin hameed aka kara ƙawatawa da kayan adonsu na sarauta, rana bata karya kamar yadda Abi yasa yaune auren yarima hameed da kuma Aneeta, gidan ya zama busy sai gudanar da biki ake tun yanzu da safe kafin ma a ɗaura, Aneeta tana ɗaki banda kuka babu abinda take yi, saida minat tayi da gaske kafin ta yadda tayi wanka ta fito akayi mata kwalliya me kyau, leshi fari da golding me masifan kyau tasa, fited gown ne ya kama jikinta sosai hakan yasa tasa babban mayafi, mutane sai shigowa suke suna tayata murna, ɓuya tayi dan batason mutane sosai, Amrah wacce take yawan rike waya tace "unty amarya kafin musa kayanmu kizo nayi miki hoto" murmushi tayi tace "a,a ban iya hoto ba" tace "please unty" a hankali ta gyara mayafin ta tsaya me kyau tayi mata hoton, tace "wow kinyi bala'in kyau" sawa tayi a status sannan ta kashe data a ranta tace "sai anjima zanga comment na mutane akan kyakkyawar matar yayana" shiryawa suka fara saida sukayi kyau kafin suka fara hotuna duk a wayan Amrah. Amrah ta zauna a bakin gadon kafin ta canja wani kayan tace bari ta duba watsapp, saura awa ɗaya a ɗaura aure domin an tafi sallan juma'a, message ta gani ya shigo mata voice ne amma da tsayi jin hayaniya a ɗakin yasa ta tashi ta shiga toilet playing tayi tana ji, jikinta ne ya fara rawa ta kara sawa a kunne tana ji ta kara maimaitawa, wayan Amnah ta kira kusan sau biyar bata ɗauka ba sai kuma ta kira wayan minat itama bata ɗauka ba, tsaban rawan da jikinta yake yi ta kasa fita a toilet ɗin, ji tayi ɗakin yayi shiru, fitowa tayi da kyar ta buɗe kofan ta tsaya tana kallon Aneeta wacce take kallonta tana murmushi tayi kyau cikin shaddan data sauya, gani tayi babu kowa a ɗakin sai ita tace "inasu... minat?" taɓe baki tayi tace "sun fita ammi ta kirasu" hanyan fita ta kama da sauri ta tsaya a gabanta, gabanta yana faɗuwa tace "meyasa kika tsaya a gabana? ki matsa min na wuce" murmushin gefen baki tayi tace "naga kinamin wani kallo kin sanni ne?" tace "ban sanki ba ki matsamin na wuce" dariya tayi me sauti sannan ta kalli wayan dake hanunta, nuna kanta tayi tace "ANEETA LAWAN LAMBA nice nasan shine abinda aka faɗa miki kike ɓoyewa kinaso kije ki faɗawa su minat ko?" jikinta yana rawa tace "meyasa kike shirin auren ya hameed?" dariya tayi sosai sannan ta takaita dariyan fuskanta kamar wacce bata taɓa koda murmushi ba tace "zaki iya zuwa ki faɗawa kowa kamar yadda kikayi niyan tonamin asiri" juyawa tayi zata fita saida ta bari ta kai bakin kofa kafin tasa igiyan dake gefenta ta harɗe kafanta dashi, waro ido tayi ta zube a kasa, baki ta buɗe zata kwala ihun azaba da raɗaɗi tanada tabbacin ta samu karaya a jikinta, toshe bakinta tayi tace "kina tsammanin bana ankare da ke ne? to ai tunda naga kin ɗaukeni hoto kinsa a status nasan akwai abinda zai faru, kuka naga kin shiga toilet ai nasan da akwai wata a kasa, inaso ki sani aneeta ba sakara bace ta san me takeyi kuma tasan takunta, ki sani wannan auren na shafe shekaru masu yawa ina neman hayan da zan samu a yishi bayan burina ya kusa cika baki isa ki rusamin arana ɗaya ba, da ki tonamin asiri gara na kasheki" hanu ta haɗa tana rokonta alaman dan Allah ta kyaleta ba zata faɗawa kowa, bakinta ta ɗaure sannan ta sauko da sabon akwatin ta juye kayan a kasa, sata tayi cikin akwatin bayan ta rufe hancinta da bakinta ta ɗaureta ta kulle akwatin ta yadda ko motsi ba zata iya ba bale asan akwai mutum, kallon kofan bayan tayi sannan ta fara jan akwatin, zata fita dashi taji karan kafan mutum, da sauri ta saki akwatin ta kwanta a gado kamar me bacci, minat ce ta shigo tana cewa "laaa unty Aneeta bacci yanzu? ki tashi dan Allah an ɗaura aure yanzu ki fito ayi hotuna gasu Abi a falo" kamar me bacci taki tashi, bubbugata tayi da sauri ta buɗe ido aɗan firgice tace "na'am" dariya tayi tace "amarya amma tana bacci ran aurenta? kizo muje ayi hoto" murza ido tayi sannan tace "to" sauka zatayi a gadon tace "tsaya na gyara miki makeup ɗin" gyara mata tayi sannan ta kara mata sabon ɗauri suka fita tare, juyowa tayi ta kalli akwatin sannan ta tura kofan gau, Amrah ta kasa motsi tana jinsu amma babu halin magana, tun tana iya numfashi da kyar har numfashin yazo ya gagareta. hotuna suka fara Amnah wacce tayi kyau da ankon da sukayi da Amrah ta tsaya a gefen Aneeta akayi hoton tace "ina Amrah ne? tazo ayi hoto" meenat tace "wallahi ban ganta ba may be ta fita" Amnah tace "no babu inda taje kin san Amrah bata son yawo" meenat tace "eh kuma fa hakane bari na dubata a ɗakin Ammi ko tana can" dubata tayi bata ganta ba ta dawo tace "babu ita muyi hoton may be tana shiri" cigaba sukayi da hotonsu, har yamma ya fara babu Amrah, amnah zuciyanta ya fara tsinkewa domin wayan Amrah akwai caji kuma ta kira taji a kashe, meenat tace "ki kwantar da hankalinki kin san da ba zata ɓata a wannan fadan ba ko?" Aneeta fakan idonsu tayi ta koma ɗakin taja akwatin ta fita dashi, jim kaɗan ta dawo tana gyara mayafin tace "naje fesa turare" Amnah wacce ta damu sosai tace "gaskiya na tsorata amrah bata yawo kuma wayanta a kashe bayan tasa caji?" meenat ma ta fara damuwa, Ammi data zo yanzu daga fada fuskanta da yanayin damuwa tace "wallahi babu ita nasa an duba ko ina" Amnah ta ɗaura hanu aka tace "na shiga uku na lalace ina Amrah ta shiga?" Aneeta ta rike ta tace "karki damu za'a ganta" hameed wanda ya shigo cikin damuwa tareda su sultan fuskokinsu kaɗai ya isa ya nuna halin da suke ciki, ammi tace "an ganta?" duk sukace "A,a" itama ammi zuwa yanzu ta gama tsorata tace "na shiga uku Amrah ina kike?" kafin ta rufe baki sukaji faɗowan abu daga saman silin, a mugun tsorace sukayi baya ganin Amrah ce ta faɗo kasa kan tiles, jini ne ya fara bin tiles ɗin bakinta ɗaure da ɗankwalin kanta hanunta ma a ɗaure idonta a rufe alaman bata raye tun da jimawa. Ammi duhu take gani ta zama kamar makauniya sai tattaɓa hanya take, zubewa kasa tayi, da rarrafe ta isa wajen zata taɓata ya kaseem yace "dakata ammi kar kiyi saurin taɓata bari a kira police, a rufe gidan babu me fita sai an gwada hanun kowa" gaban aneeta yayi wani irin mummunan faɗuwa ji tayi kirjinta kamar zai fashe tsaban tsinkewan rai, ganin kowa ya tsaya babu wanda ya taɓa gawan an fara rufe kofofin gidan ta kalli Amrah dake kwance sannan ta rufe ido, faɗuwa tayi a kanta kamar ta suma, ganin haka kaseem ya dafa kai yace "wayyo Allah shikenan aneeta ta taɓa ta" Ammi ganin haka ta rungume Amrah kawai ta fara ihu, Amnah kam tana tsaye tana bin kowa da kallo, da masu ihu da masu kuka ita kam batasan ma me take yi ba, tasan dai kawai ta kasa ɗauke idonta daga kan ƴar uwarta abin alfaharinta wato Amrah. _Jiddah Ce....✍️_ 08144818849 [20/08, 2:11 am] Shuraihu Usman: 🌸🌸🌸🌸🌸 *ƘADDARA TA* 🌸🌸🌸🌸🌸 Na *Jiddah S Mapi* *Chapter 7* ~Jikin kaseem yana rawa yace "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un me yake faruwa?" hameed ma jikinshi rawa yake sai kallonsu yake ya kasa yin komai, minat kallon Amnah tayi yadda ta bushe a tsaye, da sauri taje ta riketa cikin tashin hankali tace "kija numfashi amnah" girgiza kai tayi alaman ba zata iya ba, tace "Amnah kija numfashi" girgiza kai kawai take ta kasa magana, meenat da karfi tace "ya kaseem Amnah fa bata numfashi" da sauri yazo ya riketa, wani irin rikeshi tayi ta kwala ihun daya amsa gidan gaba ɗaya, mai martaba wanda ya shigo yanzu ya zuba musu ido ya kasa cewa komai sai zufa da yake, Amnah da Ammi ihu kawai suke meenat tana tayasu, cikin kuka tace "Amrah meya kawomu? Amrah tarefa mukazo meyasa zaki tafi ki barni?" hameed ɗaga Aneeta dake kwance yayi ya ɗaurata akan sofa, ruwa ya ɗibo ya watsa mata, da sauri ta buɗe ido tana kallon shi, kallon Amrah dake kwance tayi sai kuma ta rungumeshi tana kuka tace "wa yayi haka? waye ya kashe ta ranan aurenmu ayi kisa hameed? hameed na fara tsorata da wannan gidan wallahi akwai wani abinda yake faruwa" mai martaba ne yayi karfin halin yin magana yace "ayi jana'iza kada a ɓata lokaci" kaseem yace "Abi a bari ayi bincike" Ammi dake kuka idonta ya jika da hawaye tace "kaseem a birneta babu wani bincike da za'ayi a bari sai an birneta komai ma za'ayi sai ayi daga baya" yace "sabida bakiso a gano wanda ya kasheta?" da mamaki ta kalleshi sai kuma ta share hawayen tace "banaso kuma? me kake nufi kaseem?" murmushin gefen baki yayi yace "ai kinfi kowa sanin me nake nufi..." a fusace ta mike tana kallonshi da tsananin ɓacin rai akan fuskanta tace "me kake nufi kaseem? kana zargin zan iya kashe ƴar kanwata? ko kana nufin zan bada goyon baya a kasheta?" shima yana huci yace "to meyasa zaki hana?" cikin raɗaɗin mutuwan Amrah da haushin maganan da yakeyi tace "sabida nice na saba kisa? ko ka manta kaine...." mai martaba a tsawace yace "ya isa haka!!! nace ya isa haka!!! wai meyasa kullum ba zaku faɗi alkhairi bane? meyasa kullum cikin zargin juna kuke? maimakon ku maida hankali akan mutuwan da akayi ayi bincike me kyau domin a hukunta wanda yayi amma kuna wannan banzan maganan mara am....." rike kirjinshi yayi yana salati jin wani zafi da kirjinshi yake, idonshi ya rufe kasa ya faɗi da mugun gudu hameed yazo ya rikeshi, kallon kaseem dake tsaye yayi ya kalli jakadiya sannan ya nuna mata kofa alaman ta buɗe mutane su fita, da sauri tace "to yarima" zuwa tayi ta buɗe kofan mutane suka fara fita, saida ya tabbatar mai martaba ya farfaɗo kafin hankalinshi ya ɗan kwanta. har aka fita da Amrah kanwarta Amnah bata cikin hayyacinta, gidan ya zama shiru babu me magana, amnah tana zaune a gefen meenat da ammi tayi tagumi har hawayenta sun tsaya yanzu sai kukan zuci take, Aneeta kuma tunda ta faɗa zazzaɓi ya kamata tana ɗaki kwance, kaseem ne ya shigo sanye da jallabiya yayi shirin kwanciya amma yace bari ya dubasu, da sallama ya shiga sannan ya zauna a kusa dasu yace "sannu Amnah" a hankali tace "yawwa yaya" yayi shiru har na ɗan lokaci, cikin nutsuwanshi yace "dama akwai wanda suke gaba ne?" girgiza kai tayi sannan cikin muryanta daya dishe tace "ko ɗaya Amrah batada abokin gaba, maganan bakinta ma baida yawa kaima ka sani, bata fiye shiga harkan kowa ba..." kuka ta kara fashewa dashi, yace "kiyi hakuri na san zafin da kikeji Amnah kiyi hakuri kuma na miki alkwari saina samo wanda ya aikata wannan mummunan abin" yayi magana yana kallon ammi, itama kallonshi tayi, tun daga kasa suke jiyo karan buga kofa, sunan Amnah ake kira babu kakkautawa, Amnah dake zaune tashi tayi farat tace "Dady ne" tare suka fita yana tsaye sanye da babban riga da alama daga tafiya ya dawo hulanshi ya cire ya wurgar jijiyoyin kanshi sun tashi, hameed dake ɗakin Abi yana bashi malt yaji hayaniya da sauri ya kalli Abi sannan ya kalli kofa, tashi yayi ya fita Abi yabi bayanshi, Aneeta dake zaune akan stool tana kallon kanta a madubi taji hayaniya murmushi tayi ta shafa fuskanta da yayi jajur sabida kukan karya da tayi, rigan bacci ne a jikinta milk color ya bala'in karɓan jikinta, murmushi tayi tace "haka nakeson ji, ko kaɗan banason ganin gidannan babu tashin hankali, ko kaɗan banaso naga ana zaman lafiya a wannan gidan, idan ana hayaniya da tashin hankali ji nake kamar na zuba ruwa a kasa nash" tashi tayi tana kallon jikinta da kayan baccin ya matukar karɓanta, hijabi tasa dogo har kasa sannan tace "bara naje naga me yake faruwa" fita tayi ta maida fuskanta kalan tausayi, tana ciza baki kamar mara lafiyan gaske, dadyn Amnah cikin tsananin fushi yaje yaja hanunta yace "ko kwana ɗaya ba zaki kara a wannan gidan ba, saida na faɗa muku keda Amrah wannan ba gidan zuwa bane, na faɗa muku har mahaifiyarku ta mutu bata magana da wannan matar duk da uwa ɗaya uba ɗaya suke amma kunki jina, saida kuka zo Amnah gashi yanzu sun kashe ƴar uwarki" Ammi tace "amma salisu daka bari ta kwana idan yaso zuwa gobe...." cikin masifa da zafin mutuwar ƴarshi yace "gobe? gobe fa kikace, to nasan me zai faru da ita da darennan idan ta kwana? wannan gidan naku da yake ɗauke da mummunan tarihi an gaya miki ban san komai bane? kuma wallahi ku sani ƴata ba zata mutu a banza ba, na rantse da Allah saina ɗau fansa, ke kuma....." ya nuna ammi jikinshi har yana rawa, Abi wanda ya gama cika yace "an gaya mata itace tayi kisan da zaka zo kana gaya mata bakaken maganganu?" ya kalli Abi da idanunsa da sukayi jajur yace "a cikin gidannan waye baya kisa?" kaseem wanda shima ranshi ya gama ɓaci yace "ka daina yi mana kuɗin goro ai laifin wani ba zai shafi wani ba" jan hanun Amnah dake kuka yayi yace "muje babu ke babu su daga yau ba zasu sake ganinki ba kema kin rabu dasu" meenat tana kuka tace "dady dan Allah kada kayi haka dan Allah ka barta mu zauna tare, ka barta mu ɗibe mata kewan ƴar uwarta data mutu, dady yanzu haka Allah ne kaɗai yasan zafin da Amnah take ji dady kada kayi haka" yace "meenat na gommace Amnah ta mutu yau a gidana sabida zafin mutuwan Amrah data kwana a wannan ƙazamin gidan naku" fita yayi da ita tana tirjewa tana cewa "dady ka bari na kwana anan" suna fita kaseem ya kalli ammi dake rusa kuka yana huci yace "mutum ɗaya ba zai ɓata mana suna ba nasan wanda yayi wannan kisan" Aneeta saida jinta da ganinta suka ɗauke na lokaci, yana kallon Ammi yace "kema kin sani hakeem ne zai iya wannan mummunan kisan..." tace "ya isheka kaseem ya isheka nace" jikinshi yana rawa yace "meyasa zaki danne gaskiya? meyasa zaki ɓoye abinda yake a bayyane? hakeem shine ya kashe Amrah" marin data ɗaukeshi dashi yasa yayi shiru yana kallonta hanunshi dafe da kuncinshi, ta nunashi da yatsa tace "inaso ka san nice na haifeka kaseem ba kai ka haifeni ba, kaseem zan iya yin komai idan ka kara sa sunan hakeem a cikin abinda yake faruwa a gidannan" murmushin da yafi kuka ciwo yayi sannan yace "okay kina nufin hakeem baida laifi?" tace "hakeem baida laifi kuma ko za'a kasheni ba zan taɓa yadda cewar yanada laifi ba" yace "to waye me laifi?" hameed dake tsaye ta nuna tace "hameed shine babban me laifi, yarima hameed shine da laifi ba yarima hakeem ba" hameed dake tsaye ya kalleta da manyan idanunshi a hankali ya fara yin baya jin abinda ta faɗa, Aneeta dake tsaye ta kasa karasowa ta zuba mishi ido tana gani jikinshi yana rawa, showglass dake cike da turare ya buɗe, kwalban turare ya ɗauka sannan ya fasa, aneeta tana tsaye tana kallonshi murmushi take a ranta tana kallo yadda kwalban yayi tsini, ganin hankalinsu baya kanshi sunata faɗa tsakaninsu yasa itama bata ankarar dasu ba domin so take taga gawanshi kwance baya motsi hakan zaisa taji ranta yayi sanyi hakan zaisa ta yafewa kanta, daɓa kwalban yayi a cikinshi, tana kallonshi har ya faɗi kasa jini ya fara bin tiles, sai a lokacin tayi wani irin ihu tareda kiran sunanshi ammi da kaseem waɗanda suka kai karshe wajen fushi suka juyo a tare suna kallon hameed dake kwance hanunshi akan cikinshi jini ya ɓata inda yake kwance idonshi a rufe da alama ya mutu. Meenat hanu ta ɗora a kanta tana ihu, kaseem da sultan da kuma fadeel tare sukaje suka ɗaukashi jikin kaseem yana rawa yama rasa wani taimako zai iya mishi kawai yace "mu tafi hospital" tare suka fita dashi a hanunsu Aneeta da meenat suka bisu a baya, ammi itama binsu tayi, a mota ɗaya babba suka tafi asibiti a cikin daren da yayi nisa basu sani ba, babu mutane dayawa akan titin sabida dare yayi sosai ba kaɗan ba, banda kuka babu abinda aneeta take yi, tana cewa "dan Allah kada ka mutu ka barni hameed dan Allah ka buɗe idonka kada ka mutu ka bar marainiyar matarka" a hankali meenat ta rungumeta tana bubbuga bayanta tareda kwantar mata da hankali, shiru tayi a ranta tace "inama ace ya mutu, inama ace da gawanshi muke tafiya" suna shiga asibiti kaseem ya fito babu takalmi a ƙafarshi ya ɗaukeshi, shiga ciki yayi dashi duk masu aikin night sukayo kanshi suna bashi taimakon gaggawa, jikin kaseem banda rawa babu abinda yake yi, gani yake hameed ya riga ya mutu tun kafin suzo asibitin, zama yayi akan dakali ya rike kanshi da hanunshi, kukan da bai shirya ba ya fashe dashi, sultan dake safa da marwa ya kasa zaune ya kasa tsaye yazo ya durkusa a gabanshi, rungumeshi yayi yana bashi hakuri yayi shiru. Aneeta a bakin kofan ta tsaya kamar zata shiga kofan da aka rufe tana kuka tana addu'a, Ammi kam tsaban tashin hankali bin kowa kawai take da kallo kamar kanta ya taɓu. Aneeta cikin ranta tana addu'a tace "Allah kasa ya mutu ya rabbi kasa baya raye" a fili kuma cewa tace "Allah kada kasa hameed ya mutu ya barni dana sani da banyi wannan auren ba matukar zai kawo tashin hankali" Ammi da jikinta ya gana sanyi tace "saida nace kada ayi wannan auren nasan babu mu babu kwanciyan hankali matukar hameed ya samu yarima kuma yayi aure amma sunki jina, kowa baya jin maganata" kuka take yi sosai, bayan lokaci dayawa suka buɗe kofan, har rige rige suke wajen tambaya ammi tace "ya mutu?" da mamaki dr ya kalleta yace "kinaso ya mutu ne?" shiru tayi, ya kallesu su duka sannan yace "yana raye bai mutu ba amma yaji mummunan rauni" hamdala kaseem yayi sannan ya ɗago kai ya share hawayen, farin ciki ya bayyana a fuskanshi yace "Alhmdllh hameed bai mutu ba" shiga dakin yayi hameed yana kwance akan gadon hanunshi ɗauke da jini sun san jininshi kuma ya zubar da jini sosai, fuskanshi yayi fayau sosai, a hankali ya zauna a gefenshi ya rike hanunshi dake free, murza yatsunshi yake hawaye suna wanke mishi fuska yace "hameed kayi hakuri ka yafemin ban zama yaya na gari ba na zama yaya mara amfani a wajenka, kullum cikin ciwo kake baka taɓa samun kwanciyar hankali koda na kwana ɗaya bane" shafa kanshi yayi yace "ka yafeni hameed" shigowa sukayi aneeta ta tsaya a bakin kofan tayi shiru, kallonta kaseem yayi sai yaji ta bashi tausayi, yace "aneeta zoki zauna kusa da mijinki" cikin jin kunya ta sunkuyar da kanta, tashi yayi yace "kizo" a hankali tazo ta zauna kusa dashi, shiru tayi, kaseem yace "zaku iya tafiya gida idan yaso gobe saiku dawo zamu kwana da aneeta anan tare dashi" duk sukayi shiru basason tafiya, yayi kamar bai taɓa dariya ba yace "kuje mana" tashi sukayi ba dan sun so ba harda Ammi suka fita, kallon Aneeta yayi yace "kiyi hakuri da duk abinda yake faruwa sannan ki kula da mijinki ko sau ɗaya banaso ki tambayeshi abinda yake faruwa a wannan gidan, ko su meenat dasu sultan banso ki tambayi kowa, kici gaba da zama mutuniyar kirki kamar yadda kike" a hankali tace "to ya kaseem insha Allah" shiru yayi yana kallon hameed dake bacci, ya tashi yace "zanje office ina zuwa" tace "to" fita yayi, ta kalli hameed a ranta tace "meyasa baka mutu ba? nace me yasa baka mutu ba hameed?" ta kalli jinin dake tafiya a jikinshi, fizge canulla ɗin hanunshi tayi ta bar jinin baya tafiya, murmushi tayi tace "ko kaɗan banso naga kana rayuwan farin ciki, so nake naga kullum kana kuka hameed, na tsaneka na tsani ƴan gudanku hameed na tsaneku" rashin jinin dake jikinshi yasa jikinshi ya fara zafi, fizgewa ya fara yana neman karya gadon, tana ganin yadda yake jin zafin ciwon a jikinshi da yadda yake fizge jikinshi sabida rashin jini, tace "ka mutu hameed ka mutu mana hameed" knocking akayi da sauri ta fara rike hanunshi tace "shigo" ya kaseem ne ya shigo da juice a hanu, ya kalleta ya kalli hameed wurgar da juice ɗin yayi yazo yana rikeshi, yace "ya akayi jinin ya fita?" tace "wallahi fizge fizge ya fara kuma na rasa yadda zan yi" ganin tana kuka yace "karki damu babu abinda zai sameshi" gyara mishi jinin yayi yana jin jini a jikinshi ya koma luf ya kwanta akan cinyarta. shiru tayi tana kallonshi, juice ɗin kaseem ya mika mata yace "gashi kisha nasan rabonki da abinci tun safe" girgiza kai tayi tace "bana jin yunwa, ba zan iya cin komai ba" yace "ki daure kisha dan Allah" shiru tayi tana girgiza kai hawaye yana wanke mata fuska, da kyar ya lallaɓata tasha kaɗan, a wajen tana zaune bacci ya ɗauketa. _jiddah ce...✍️_ 08144818849 [20/08, 2:11 am] Shuraihu Usman: 🌸🌸🌸🌸🌸 *ƘADDARA TA* 🌸🌸🌸🌸🌸 Na *Jiddah S Mapi* *Chapter 8* ~Sunyi kwana biyar a asibiti kafin aka sallamesu, da kyar yake takawa sabida ciwon da yake cikinshi, wajen jeep ɗin dake fake suka nufa tareda ya kaseem da yayi kyau cikin yadi maroon, Aneeta kuma sunye take da hijab peach color tayi kyau sosai tasa mayafin a kanta bayan tasa hula me kyau baƙi, tana rike dashi yana takawa a hankali har ya shiga motan, itama shiga tayi sannan ya kaseem ya shiga, driver ne yaja suka tafi, koda suka isa gida a hankali yake tafiyan har aka kaishi ɗaki, kwanciya yayi akan gadon yayi shiru yana kallon Aneeta dake kallonshi, gira ya ɗaga mata alaman ya akayi? murmushi tayi ta kauda kai, zata tafi yaja hanunta ta faɗo kanshi, rungumeta yayi sosai yana sauke ajiyan zuciya, shiru tayi a jikinshi har zuwa lokacin daya fara shafa duk jikinta, duk wani taɓata da yayi ji take kamar wuta ne yake taɓa mata jiki, bakinshi zai haɗa da nata tayi saurin tashi ta bar wajen, binta yayi da kallo, sultan ne ya shigo yace "yaya yarima a kawo maka abinci?" gyaɗa kai yayi, yace "to" fita yayi jim kaɗan yazo da abinci yace "tashi na baka" tashi yayi ya zauna, jallof rice ɗin ya fara bashi yana ci cikin nutsuwa, fitowa tayi daga toilet ta karɓi plate ɗin tace "karka damu zan bashi" kallonta yayi shifa gabanshi yana faɗuwa idan yana kallonta ya rasa dalili, tace "tashi mana sultan zan bashi da kaina" a hankali ya tashi ba dan yaso ba, bashi ta fara, sultan ya fita daga ɗakin, fadeel yaga yanayin sanyin jikinshi yace "ya akayi sultan?" yayi tsaki kaɗan yace "wallahi haka kawai hankalina yaki kwanciya da Anti Aneeta musamman idan tana tare da ya hameed sai naji gabana yana faɗuwa" caraf a kunnen Ammi wacce ta fito daga ɗaki, kallon sultan tayi, ashe ba ita kaɗai bace takejin haka akan aneetan shima yana ji, idan taga aneeta gabanta yana faɗuwa, idan tana tare da hameed sai taji bugun zuciyarta yana karuwa, tana kallonsu har fadeel ya dafa wuyanshi suka tafi yana cewa "ka kwantar da hankalinka babu wani abu mara kyau da zatayi mishi kasan tana masifan sonshi" fitowa Aneeta tayi da plate ɗin a hanunta ido huɗu sukayi da Ammi, murmushi tayi mata tace "sannu ammi" bata amsa mata ba kuma bata daina kallonta ba, taɓe baki tayi ta wuce taje ta aje plate ɗin ta dawo ta shiga ɗakin ta rufe. meenat wacce taga duk abinda ya faru tazo wajen ammi ta riketa, tace "ammi me yake faruwa ne?" girgiza kai tayi tace "ba komai meenat" tace "ammi amma kamar naga kina yiwa anty Aneeta wani irin kallo kuma naga ya sultan ma kamar jikinshi a mace da ita" ammi taja numfashi sannan tace "meenat wallahi na kasa nutsuwa da wannan yarinyar haka kawai banason ganinta kusa da hameed" tace "comon ammi babu komai fa kawai dai kinsa abu ne a ranki" tace "to amma meenat" tace "amma me ammi muje please ki huta kin gaji sosai" shiru tayi suka tafi, meenat kallon kofan ɗakin tayi itama haka kawai taji kamar akwai abu a kasa, itama ta kasa nutsuwa da aneeta tunda Amrah ta mutu, sannan tunda akayi aurensu da hameed sai taga kamar ta canja duk da tana ɓoyewa amma ta lura da hakan. sharewa kawai tayi. zaune suke a dinning daka anan ne suke haɗuwa su duka harda Abi, abinci sukeci da hameed wanda yake cin abincin a hankali yake kallon matarshi, murmushi yake idan sun haɗa ido, meenat tace "Abi zanso naje nima naga wani kasan saudiya kawai na taɓa zuwa gaskiya zanso naje wata kasar kuma" murmushi yayi yace "shikenan meenat zaɓi kasar da kikeson zuwa hutunki" tace "turkey" aneeta ta sauke cup na tea da take sha tace "me zakiyi a turkey? akwai sanyi sosai acan gara kije cairo yafi daɗi sabida babu sanyi sosai kuma babu za..." saurin yin shiru tayi ganin yadda duk suke kallonta bata sani ba ashe tayi ɓarin zanje, meenat da mamaki take kallonta sai kuma tace "ya akayi kika sani? keda kikace baki taɓa fita ko wani gari ba bale wata ƙasa?" gabanta ya fara faɗuwa da sauri ta kalli ammi wacce ta aje spoon tana kallonta tana jiran amsa, tace "a tv na gani ai, film na kalla ranan naga an faɗa" sultan yace "wani film?" ruɗewa tayi domin ta rasa amsan da zata bayar, tace "to ai ba zan iya rike sunan film ɗin ba sabida da turanci ne kuma bana jin turanci" meenat tace "kuma kikaji me suke cewa a film ɗin har kikaji sunce kasar turkey da sanyi?" tace "to ai naga suna saka rigan sanyi su kuma..." kaseem ne yace "ya isa haka" shiru tayi meenat kuma ta fara binta da kallo haka Ammi, hameed yana gamawa ya tashi ya tafi ɗaki. itama Aneeta bata jira yau ta gama duka ba ta tashi ta tafi, da kallo meenat ta bita. tun daga ranan bata kara yadda tayi suɓul da baka ba, yau weekend ne suna zaune a falo su duka banda hameed dake bacci a ɗaki, meenat ce kwance akan sofa tana chatting, tace "yanzu zasusa favorite film ɗina bara na kashe data nayi kallo" sunan jarumai aka fara nunata tana rike da wayan taji Aneeta tace "michael marrone, ashe kina kallon film ɗinshi wannan film ɗin After marriage ne ko?" kallon da meenat take mata yasa tayi saurin rufe baki, meenat zuwa yanzu ta gane karya take yi akan abubuwa da dama domin yadda take kiran sunan abu kamar tanada masaniya sosai a kai, shakku ta fara a kanta, batayi magana ba kawai ta kawar da kai tana kallon tv, a zahiri kallo take amma a zuciyarta tana kara kallon Aneeta ne, a hankali tace "ya zama dole nasa ido sosai a kanta" saida aka gama film ɗin ta musu saida safe ta tafi ɗaki, ta rufe kofan ta jingina da jikin kofan tayi shiru, a hankali ta lumshe ido ta buɗe tace "wacece wannan?" zata wuce ciki taga sim a gefen gado, da sauri tace "sim ɗin waye?" ɗauka tayi tana kallo, sai kuma tace "ba nawa bane, ko dai na Amnah ne?" shiru tayi tana tunani sai kuma tace "no Amnah batada sim biyu saide Amrah itace take canja sim" da sauri tace "wannan na Amrah ne" da sauri ta buɗe wayarta tasa sim ɗin a ciki, dubawa ta fara taga sunayen duk yawanci a bakin Amrah takejin sunan, numbern Amnah taga tayi saving da blood sis, tace "tabbas wannan sim ɗin Amrah ne" barin sim ɗin tayi a wayarta ta kwanta ta fara bacci. Aneeta kwance take itada hameed ya rungumeta sosai yana bacci cikin kwanciyan hankali, so take ta samu waje tayi waya amma tana tsoron kada a kamata, a hankali ta cire hanunshi daga jikinta kunna wuta tayi taga karfe biyu na dare cikin sanɗa ta buɗe drower ta ɗau waya karami data ɓoye fita tayi daga ɗakin cikin sanɗa take tafiya, tsayawa tayi a jikin bango ta fara kunna wayan saida ya kunnu zata kira taji karan tafiyan mutum, da sauri ta rufe baki tana waro ido, sanye yake da bakin kaya ya rufe fuska kofan jabeer taga ya buɗe, fasa kiran wayan tayi a hankali ta fara bin bayanshi, tsayawa tayi a baya taga ya ɗaga hulan, alluran da ake yiwa hameed kullum taga ya ɗauka ya juyo dashi, zaro manyan idanunta tayi ganin sultan ne ya canja alluran ya ɗau original ɗin ya kalli kaseem dake bacci cikin kwanciyan hankali sannan ya juya zai tafi, da sauri ta ɓuya a bayan kofa, fita yayi ya rufe kofan, yana fita itama ta fita cikin sanɗa tana mugun mamakin me zaisa sultan ya canja allura? kiran wayan da batayi ba kenan ta koma ɗaki taga hameed ya buɗe ido yana kallonta, tasan da tambaya sosai a ranshi amma ba zai iya furtawa ba, a hankali ta kwanta ta rungumeshi tace "na fita shan ruwa ne kasan na saba da shan ruwan dare" shafa kanta yayi sannan ya mata kiss a forehead ya kara rungumeta ya lumshe ido, a ranta har yanzu ta kasa gane me yasa sultan zaiyi haka? tana ganinshi ta cikin dim light yana bacci like innocent baby boy, yadda yake turo baki kamar karamin yaro da ake shayarwa, shafa kanshi tayi a hankali ta fara shafa sajenshi, da sauri ta ɗauke hanunta daga jikinshi ta rufe ido tana cewa "bai kamata ba, bai kamata ba sam Aneeta" matsawa tayi daga jikinshi tace "ba wannan ya kawoki ba aneeta abinda ya kawoki daban kada kiyi kuskuren da ba zaki yafewa kanki ba aneeta" pillow ta ɗauka ta rungume, zuciyanta yana tafasa tana jin zafi a ranta. washe gari breakfast sukeyi Aneeta tayi kyau cikin baƙin kaya, akan ferfesun da take sha idonta yake bata yadda ta kalli kowa ba domin bata bacci idonta kamar na ƴar kwaya ya zama tsaban baccin da takeji, kaseem yana sanye da uniform cikin sauri yake cin abincin saida ya ɗan koshi yace "thank god, tashi hameed nayi maka alluranka sauri nake" ya ɓata rai sabida baison kalman allura, yace "oya tashi" badan yaso ba yaga yaja ruwan alluran, idanunta masu cike da bacci ta kalli sultan, baiko kalli inda suke alluran ba, zai mishi tace "ka tabbata alluran bs fake bane?" jikin sultan ne ya fara rawa, tana kallon cikin idon sultan tace "ina nufin ka tabbata ba'a canja ba?" cokalin hanun sultan ne ya faɗi, abincin yabi kanshi take ya fara tari, Ammi da meenat sai kallonta suke yadda take jujjuya cokalin tana magana da kwarewa cikin rashin tsoro, kaseem murmushi yayi yace "nifa babban dr ne aneeta sabida mijinki ya samu lafiya kikeso a samu allura me kyau ko?" murmushin gefen baki tayi har yanzu idonta akan sultan tace "so nake ya samu lafiya ya kaseem amma ka kara duba alluran kada watarana a canja" gama mishi yayi yace "good boy yanzu ba gashi an gama ba?" kwanciya yayi a wajen kan sofa, shifa idan anyi mishi alluran maimakon yaji sauki sai yaji jikinshi yana zafi kuma bacci me nauyi mara daɗi saiya ɗaukeshi, bayan ya tashi sai yaji jikinshi yana ciwo kullum haka yake fama, amma ya kaseem ya nace da alluran kuma baison ɓacin ranshi shiyasa yake yadda. tashi tayi daga wajen ta wuce ɗaki ba tareda ta gama ci ba, ido ta rufe tace "no ba zan bari wani ya kashe hameed ba nice ya kamata na kashe shi da hannuna" tayi maganan tana kallon dogayen hannayenta. meenat school ta tafi, bayan ta dawo ta gama aikinta sannan ta zauna a falon tareda su Aneeta kamar kullum suna hira kiran wayan meenat akayi ta duba taga sim ɗin Amrah da tasa ake kira da sabon number, ajewa tayi bata amsa ba, aka kara kira ta amsa tace "hello" muryan mace taji tace "Amrah inata kiranki ba zaki ɗauka ba? yau na dawo nigeria naga tun ranan baki kara hawa online ba, ina fatan yanzu kin gane wacece ita, na faɗa miki Aneeta babu wanda bai santa ba a gidanmu" da sauri ta tashi ta wuce ɗakinta, tace "ki nutsu baiwar Allah wannan ba Amrah bace Amrah ta mutu amma wannan ƴar uwarta ce meenat" tana jin yarinyar ta kwala ihu tace "ta mutu? ko kuma ta kasheta ko?" meenat cikin ruɗewa tace "wacece?" tace "Aneeta lawan lamba" dafa kirji meenat tayi ta zaro idanu a razane tace "Aneeta lawan lamba?" tace "tabbas nasan itace ta kasheta" faɗa mata duk yadda sukayi tayi sannan tana kuka tace "ashe mutuwa tayi" meenat cikin tashin hankali tace "dan Allah ki faɗamin inda zamu haɗu yau da dare inason ki faɗamin komai" tace "kece ƴar sarki da take bani labari kullum?" tace "nice" tace "shikenan zanzo da dare amma kisan yadda zaki fita kada ki nuna mata kin gano komai kawai ki sameni a bakin titin kwaltan farko zan jiraki" tace "kamar karfe nawa?" tace "karfe goma sha biyu sabida banso kowa ya sani" tace "to na gode me sunanki?" tace "sunana fauza" "na gode fauza" kashe wayan tayi ta zauna a bakin gado tana maimaita kalman Innalillahi wa inna ilaihiraji'un, da kyar ta saisaita kanta ta fito, Aneeta ta kalla sai kuma ta mata murmushi tace "Anty Aneeta ki gyaramin gashina" tace "zauna" a tsorace ta zauna amma bata nuna mata ba, har dare tana bin komai a hankali sannan bata nunawa kowa komai ba, kallon agogo take bacci yaki ɗaukanta har karfe sha biyu kafin tasa dogon hijabi ta fita cikin sanɗa, cikin sanɗa ta fita a gidan tana sauri har taje bakin titin, gani tayi babu ita, kiran wayanta tayi taji a kashe, hankalinta ne ya kara tashi tace "fauza kizo mana ina kike?" jiranta tayi babu ita babu dalilinta, saida ta gaji ga dare ya gama yin nisa kafin ta koma gida jikinta a mugun mace, ɗakinta ta shiga ta zauna kawai tana addu'a a fili da haka har gari ya waye batayi bacci ba, tana zaune akan sallaya tana addu'a, saida ta gama ta fito waje cikin uniform na school, kallon kofansu hameed tayi tsaban tsinkewan zuciya har ta rame. knocking akayi a hankali tace "ana zuwa" zuwa tayi ta buɗe kofan, gani tayi ɗaya daga cikin masu aiki ne namiji rike da katon ghana most go yace "Allah ya taimaki ƴar sarki meenat wannan sakon ance na kawo miki naki ne" ta kalleshi ta kuma kalli sakon da yace, tace "waye?" yace "nima ban sanshi ba amma yace a kawo miki fuskanshi rufe yake" tace "to na gode" ɗauka zatayi taji da nauyi, gabanta yana faɗuwa taja zuwa ciki da kyar, buɗewa tayi dan ganin me aciki, idonta kamar zasu zubo bakinta yana rawa kamar yadda jikinta yake rawa ta kwala ihu tace "ya kaseem? ya hameed? ku fito, ku tainakeni" hameed ne ya fara fitowa, sannan sauran suka biyo bayanshi kallonta suke yadda take tsaye jikinta yana rawa ta kasa barin wajen, Ammi wacce itama ta gama ruɗewa da ganin ƴarta haka taje domin gani, ihu ta kwala tace "gawa" hameed da kaseem sunzo a tare, kaseem ne ya kalla yaga kyakkyawar budurwa ce kwance yaga takadda a gefe, ɗauka yayi yaga an rubuta FAUZA da manyan harufa, kallon meenat yayi yace "fauza wacece ita? meyasa aka kawota nan?" tana girgiza kai tace "ban sani ba yaya" aneeta tana kallo ta rike hameed jikinta yana rawa cike da mugun tsoro tace "gawa hameed ba zan iya kallo ba a ɗauke anan" ɓoye fuskanta take a jikinshi, mai martaba ganin abinda yake faruwa yace "kada kowa ya sani aje a binneta tunda bamu santa ba" har yanzu jikin meenat bai daina rawa ba, fita da ita akayi, ammi tace "wai me yake faruwa ne damu?" shiru suka zauna school ɗin da meenat bataje ba kenan, haka ta wuni da zazzaɓi da masifan ciwon kai, har dare tana kwance a ɗaki cikin bargo ta kasa fitowa, tunani ta fara, sai kuma ta tuna jiya data dawo kamar taji karan motsin buɗe kofa kuma tasan ba kofan ya kaseem bane, da sauri tace "Aneeta ya zama dole na bincike ta yanzu ma" sauka tayi daga gadon ta fita a ɗakin, tana fita taga ta fito cikin sanɗa ta nufi kitchen, bin bayanta tayi taga tana tsaye ta juya baya a kitchen ɗin tana kallon hoto, a hankali ba tareda ta bari taji zuwanta ba taje ta bayanta ta tsaya, fige hoton tayi tana kallo, a razane tace "me haɗinki da ZEENAT LAMBA?" juyowa tayi da jajayen idanunta tace "na san dama zaki biyoni kuma nasan kina bibiyata meenat" tace "baki bani amsan dana tambayeki ba, me haɗinki da zeenat?" murmushi tayi sai kuma tace "zeenat haka kawai babu respect? ba matar yayanki bace ita? da zaki kirata da sunanta gatsau" tace "Aneeta baki bani amsa ba me haɗinki da zeenat?" tace "sunana Aneeta lawan lamba ita kuma zeenat lawan lamba ina fatan kin gane me haɗina da ita?" jikin meenat yana rawa tace "ki..ki...kina nufin ke...ke...kanwar zeenat ce?" jijjiga kai tayi cikin rainin hankali tace "kwarai zeenat tsohuwar matar hameed ni kanwarta ce uwa ɗaya uba ɗaya ina fatan kin fahimta?" jikinta yana rawa hoton ya faɗi, su biyu ne a hoton tana rungume da ɗayan ta baya sunyi hoton cikin nishaɗi, murya meenat ta ɗaga tace "A..Am..ammiii" rufe mata baki tayi, kokarin kwacewa ta fara, ɗankwalinta ta ciro tana ɗaure bakinta suka fara kokawa, cikin muryanta dake cike da ban tsoro tace "kina nufin bansan abinda yake faruwa bane? fauza data kiraki jiya nice na kasheta sannan Amrah itama nice na kasheta, ki sani ba zan taɓa bari ki tonamin asiri ba har sai na gama duk abinda ya kawoni gidanku, zeenat wacce hameed ya kashe jininta ba zai tafi a banza ba, saina tarwatsa family ɗinku, saina kashe hameed kamar yadda ya kashe zeenat ya rabata da farin cikinta, dan rashin imani har yaron data haifa baku bari ba saida kuka haɗa da ita to ku sani ni kanwarta ce ta jini saina ɗau fansa, babu me yin rai a gidannan nayi niyan na barki ki kara wasu kwanaki a duniya amma ba zan taɓa barinki ba meenat" ɗaureta tayi tana girgiza kai, ɗagata tayi ta fita da ita, kasancewar dare ne yasa ta fita ta kofar baya, a motan dake fake wanda itace ta ɓoye ta sata a ciki, shiga tayi itama taja motan da gudu ya bar bayan gidan, gudu take akan titi cikin iyawa, kamar zata bar garin saida ta iso wani babban ruwa sannan ta tsaya, kallonta tayi taga idonta a buɗe itama tana kallonta, murmushi tayi tace "karki damu watakila kinada tsawon rai shiyasa ba zan kasheki a take ba, amma dole zan rabaki da kowa naki" fitowa tayi ta buɗe marfin motan ta ɗaukota, a cikin babban ruwan garin ta wurgata ba tareda ta kunceta ba, saida taga ta lume cikin ruwan sannan ta shiga mota ta koma gida, Allah ya taimaketa hameed bai tashi ba kuma babu wanda ya tashi a gidan kwanciya tayi a gefenshi ta rufe ido, cikin bacci taji ya riketa, rufe ido tayi tana jin wutan kinshi yana ruruwa a zuciyarta. _Jiddah Ce....✍️_ 08144818849 [20/08, 2:11 am] Shuraihu Usman: 🌸🌸🌸🌸🌸 *ƘADDARA TA* 🌸🌸🌸🌸🌸 Na *Jiddah S Mapi* *Chapter 9* ~Kauyen da yake nesa dasu babban ruwan ne ya raba tsakaninsu da kauye ne sosai sabida babu abin more rayuwa ko kaɗan a ciki, wani kyakkyawan matashi ne yake sassake bishiya, sanye yake da kayan maharba fari ne dal asalin bafulatani ne, ya rataya takobi a bayanshi hankalinshi duk akan saran itacen da yake, wata kyakkyawar yarinya ce durkushe tana tsintan wasu ƴaƴan itacuwa da suka zubo, ɗaya ta ɗauka ta kai bakinta sanye take da riga da zani amma zanin guntu ne sosai, kanta babu ɗankwali gashinta an kumbutsa sau huɗu an ɗaure da igiya, jin karan faɗuwan abu a bayanta ta juyo subhanallah tsarki ya tabbata ga ubangijin halittu, wani irin wutan kyau take dashi, fara ce dal tana kama da matashin sosai amma ta fishi hasken fata, murmushi tayi ganin katon mango ya faɗo da sauri taje ta ɗauka, kallon ruwan da yake gudu me yawa dake gabanta tayi, sai kuma ta kalli yayanta fuskanshi babu fara'a kuma da alama ya saba da hakan, cikin zazzaƙan muryanta tace "bari naje na wanke" tafiya tayi da duka kayan itatuwan a hanunta taje bakin ruwan ta zauna ta aje a kasa, fara ɗauka tayi tana wankewa da ɗaɗɗaya, sa ɗaya tayi a karamin bakinta ta fara tsotsa zaƙi zaƙi tsami tsami abin yake dashi, tashi tayi tace "bari na wanke jikina dama nayi datti" sa kafanta tayi cikin iya ruwan ta fara shiga ciki sosai, kafanta ta wanke sannan ta wanke hanunta, nishaɗi take yi sabida sai dariya take tana wasa da ruwan, cire kafanta tayi zata fita taji kamar ta taka abu kuma ba dutse ba, da sauri ta kara kallon ruwan sannan ta kara takawa, hanu tasa tana taɓa abin, jin kamar mutum ne jikinta ya fara rawa, a tsorace ta durkusa ta ɗaga, waro ido tayi ta buɗe murya hanunta rike mutum data tsinta a ruwan tace "HAMMA NAJEEB? kazo na tsinci mutum" aje addan da yake sara dashi yayi sannan ya kalleta yayi tsammanin haukan data sama ne zatayi mishi, baiyi magana ba yazo inda take, niyanshi idan karya tayi saiya sassauke mata mari, yana zuwa ya kalleta yaga da gaske tana rike da abu, waro ido yayi ganin mutum ne an ɗaure baki da hanci, goshinta ya farfashe ga kuma jikinta daya farfashe sabida duwatsun dake cikin ruwa wanda tayi ta karo dasu, da sauri ya shigo ya ɗagata ya cirota daga ruwan, a kasa ya kwantar da ita yana kallonta, tace "hamma najeeb baya raye ko? ya mutu?" taɓa hanunta yayi sannan ya girgiza kai yace "yana raye bai mutu ba" cikin gurɓataccen hausanshi da yafi nata muni yayi maganan, kwanceta yayi sannan yace "kawo ganyen kalgo" da gudu taje inda yake saran itacen ta ɗauko wani ganye a kwarya tazo dashi, yace "daddaka" dakawa tayi tasa a kwaryan yace "sa ruwa" hanunta tasa ta ɗibo ruwa kaɗan ta zuba sannan ta juya sosai da hanunta ta kawo mishi, yace "zauna" zama tayi, yace "shafa mishi a wuya da goshi da kai" shafa mata tayi sosai yace "kara ruwa ki bashi yasha" kara ruwa tayi sannan tazo ta ɗaga kanta ta ɗaura a cinyarta ta fara bata ruwan ganyen, tari ta fara amma bata buɗe ido ba, ta kalleshi yace "cigaba da bashi" tace "to" cigaba tayi da bata, shi kuma ya riko hanunta yana shafa hanunshi sosai a nata, ya saki hanun ya rike kafan yana shafawa sosai yana kallonta har yanzu idonta a rufe, sun ɗau lokaci a haka kafin yace "kwantar dashi ki kawomin itacen dana sara" kwantar da ita tayi ta ɗauko itacen da yake ɗanye ta bashi, ɓare bayan yayi ya murza a hanunshi sannan ya shafa mata a fuska yace "rike kafanshi sosai" rike kafanta tayi, shi kuma ya rike kanta yasa baki a kunnenta ya fara wani irin karatu yana murza tafin hanunta da karfi, buɗe ido tayi a firgice ta kalleshi, fuskanshi babu alaman wasa ya saketa, dariyan farin ciki yarinyar tayi tace "hamma najeeb ta tashi wallahi" ya tashi yace "rikeshi mu tafi gida" tace "to" kallon meenat dake binsu da kallo tayi tace "tashi muje gida idan ka huta saika koma garinku" a hankali ta tashi, rike hanunta tayi shi kuma ya kwashe itacen duk yawan itace da nauyinsu bai nuna gajiya ko kaɗan ba sai tafiya yake yana gaba suna biye dashi, tafiya me nisa sukayi kafin suka shiga kauyensu mutane ta gani suna kallonta ga mutanen garin kamar mayu, tsoro ne ya kamata yarinyar tace "kar kaji tsoro babu abinda zai sameka hamma najeeb ba zai bari ayi maka komai ba" binta kawai take da kallo, tanada tabbacin wannan mayu ne domin daga suturan jikinsu da kuma dattin dake jikinsu da fatarsu da idanuwansu da suka nuna tsantsan rashin imani dake tare dasu, hanunta gam ta rike na yarinyar dashi, da haka har suka isa wani gidan taɓo me ɗaki kanana biyu, shiga sukayi wata kyakkyawar karamar yarinya tazo da gudu ta rungume yarinyar tace "kun dawo Adda" ta gyaɗa kai alaman eh, ta kalli meenat tace "waye wannan adda?" tace "bako ne mukayi" tace "sannu bako" a hankali ta gyaɗa kai tana kallon yarinyar wacce tayi kyau cikin kayan fata brown, skin nata kamar bana mutanen kauye ba, shimfiɗa mata tabarma tayi tace "ka zauna anan" zama tayi tana bin ko ina da kallo harda shi hamma da yake dama wani abu a kwarya, suma suka zauna a gefenta tace "yaya sunanka?" nuna kanta tayi, tace "ni?" gyaɗa kai tayi tace "eh kai" ta girgiza kai tace "nima ban san sunana ba na manta sunana" kanta ta rike tana jin yana sarawa sosai, da sauri ta riketa tace "sannu" kwanciya tayi a wajen tace "kaina yana ciwo sosai" tsaye yayi a kansu ya bata maganin daya dama a kwaryan yace "ka bashi ya kara sha ka shafa mishi a jiki" ɗagata tayi tace "tashi kasha" tashi tayi tana rufe ido tasha, shafa mata sauran tayi a jiki, take bacci ya ɗauketa ta kwanta a wajen, tagumi yarinyar tayi tana kallonta tace "Allah sarki ya manta komai watakila faɗuwa yayi a ruwa" yana alwala yace "wurgar dashi akayi ba faɗuwa yayi ba" daga nan bai kara cewa komai ba ya fice daga gidan. tana zaune cikin tausayinta sannan ta tashi ta ɗau buta tayi alwala kusan sau biyar biyar take wanke duk inda ake wankewa sau uku idan za'ayi alwala, wani fata ta ɗauka ta shimfiɗa sannan ta ɗau karamin ɗankwali ta yafa ta fara salla, kasancewar mangariba ne yasa tayi raka'a shida idan Isha kuma raka'a goma sukeyi, sallama tayi ta tashi, taje bakin randa buɗewa tayi maimakon ruwa sai farin nono ne tas wanda babu datti ko kazanta, babban kwarya ta ɗauko ta zuba a ciki sannan ta ɗibi furan dake gefe tasa ta dama da cokalin duma sannan ta ɗau sugar ta zuba, ɗanawa tayi taji sanyi sosai, lumshe ido tayi tace "bari na kara madara sabida bako" madara ta kara sannan ta kara sugar yayi daɗi sosai ta rufe, saida tayi sallan Isha kafin taga hamma ya shigo hanunshi rike da leda, da sauri taje ta karɓa, zama yayi a inda ya saba zama zuba mishi nonon tayi a karamin kwarya tasa mishi cokali ta kawo mishi, ledan da yazo dashi ta buɗe taga nama gasashe me zafi cike da ledan taje ta ɗauko kwano ta zuba mishi dayawa ta kawo mishi, meenat ce ta fara motsa hanu, a hankali ta buɗe ido taji kanta ya daina ciwon sai ciwon jiki da takeji kaɗan kaɗan tashi zatayi yarinyar tazo da sauri ta ɗagata, zama tayi ta kalleshi baya kallonsu nonon kawai yake sha, ta kalli yarinyar tace "ina nake? nan inane?" kawo mata nonon tayi tace "kisha sai nayi miki bayani" sha tayi sosai sannan tace "nasha to ki faɗamin nan inane?" tace "sunan kauyennan tudum mu ba mugaye bane mu fulani ne masu kiwo da kuma bada magani a ruwa muka tsinceki nida hamma na" tace "to daga ina nake? me yasani a ruwa?" girgiza kai tayi tace "wannan tambayan ke zamu yiwa sabida bamu san daga ina kike ba" tace "bazan iya tuna komai ba" karamar yarinyar tace "abani naman da kawu ya kawo" bata naman tayi ta fara ci, tayi shiru tana kallonsu tace "ya sunanta?" nuna yarinyar tayi tace "wannan?" gyaɗa kai tayi, tace "sunanshi MIMI" da mamaki tace "ke kuma fa?" nuna kanta tayi tace "ni?" tace "eh" tace "sunana ASMEETA amma ana kirana Asmee" da mamaki a wannan kauyen amma suka san irin waɗannan sunayen tace "Asmee? tace "eh ke kuma me sunanki?" girgiza kai tayi tace "ban san sunana ba" murmushi tayi ganin tana damuwa ta riko hanunta tace "karka damu zamu rinƙa ce maka AMEENA" maimaita sunan tayi "Ameena?" gyaɗa kai tayi tace "yayi daɗi ai ko?" tace "me yasa zaku kirani da Ameena?" tace "sabida sunan mamana ne amina kuma ta mutu" shiru tayi tana kallonta yadda take share hawaye da alama tana jin zafin maganan. tace "wannan kanwarki ce?" tace "a,a ƴata ne" shiru tayi tana kallon ysrinyar, saida duhu yayi sosai kafin suka shiga ɗakin da yake da matsi sosai sai tarin magani da alama suna bada magani sosai. Aneeta bacci take cikin kwanciyar hankali, hameed ne ya fara tashi kallonta yayi sai kuma ya sauka ya shiga bathroom yayi wanka tareda alwala ya fito yasa jallabiya me kyau salla yayi sannan ya zauna akan sallayan yana addu'a a cikin ranshi, a hankali ta fara buɗe ido sauke idon tayi a kanshi sai kuma ta rufe ido, a hankali ta sauka daga gadon ta shiga toilet tayi wanka tareda alwala ta fito, cire towel ɗin tayi ta ɗauko simple dogon riga tasa, sallayan da yayi sallan tayi salla akai, juyowa tayi cikin respect ta gaisheshi, a hankali ya mika mata hanu suka gaisa, murmushi tayi tace "bari naje na gaida su ammi" tashi yayi suka fita tare, ɗakin ammi taje ta buɗe kofan ta tsaya a bakin kofa babu sallama, Ammi wacce yanzu kenan fitowanta daga bathroom baya tayi da dafa kirji tace "Innalillahi" tsirata tayi da ganin Aneeta, murmushi tayi tace "ammi tsoro na baki?" shiru tayi tana kallonta, tazo ta zauna a bakin gadon tace "kar kiji tsoro Ammi niba abin tsoro bace" ammi tace "meya shigo dake?" tace "gaisuwa" yadda take amsawa a tsaye yasa take jin wani iri a kanta, tace "to tashi ki fita na amsa" make kafaɗa tayi tace "um um babu inda zanje tare dake zamu fita" tace "tashi ki fita aneeta" tace "meyasa kike koran sirikarki? ko dai haka kike kore kowace sirikarki ne?" ammi ranta ya gama ɓaci tace "ni kike gayawa wannan maganan aneeta?" tashi tayi tana nufota, baya ammi ta fara a tsorace, saida ta isa jikin bango ta tsaya tana kallon Aneeta a mugun tsorace, ɓata rai tayi ta zama asalin aneeta tace "haka kike koran zeenat?" a razane ammi ta kalleta, ya akayi ta san zeenat? shine tambayan da takeyi a zuciyarta, murmushin gefen baki tayi tace "karki damu ni ba zaku kasheni kamar yadda kuka kashe zeenat ba" fita tayi daga ɗakin, da razanannen kallo Ammi tabi bayanta, banda rawa babu abinda jikinta yake, idanu a waje tace "waya bata labarin? hameed?" da sauri ta girgiza kai tace "no hameed ba zai taɓa bada wannan labarin ba, kaseem? no kaseem ba zai bata ba to waye? meenat?" da sauri tace "meenat" fita tayi daga ɗakin a tsorace ta shiga ɗakin meenat bayan tayi knocking sosai bata buɗe ba, tana shiga tace "meenat" gani tayi babu ita akan gado, tayi knocking toilet taga ya buɗe alaman babu kowa a ciki, fita tayi daga ɗakin tana kwala mata kira "meenat? meenat?" sultan daya shirya domin zuwa school ɗin da Abi ya sashi yace "ammi ina meenat ɗin ban ganta ba nima tun ɗazu nake nemanta" tace "to ina taje sultan?" yace "wallahi ban sani ba har fada na dubata ban sameta ba" ammi tace "ka sanarwa kowa a fara nemanta" yace "to" sanarwa sukayi take aka fars nemanta a gidan babu ita, ammi cikin tashin hankali tace "na shiga uku na lalace ina ta shiga?" kaseem wanda zufa ya wanke mishi fuska share zufan yayi yace "Innalillahi me yake faruwa a wannan gidan?" kamar da wasa sama da kasa aka nemi meenat aka rasa, har gidan rediyo da gidajen tv an dubata babu ita, ammi hanu ta ɗaura aka ta kwala wani uban ihu tace "meenat kar kimin haka" kaseem jiri yakeji zama yayi akan sofa, sultan kuka ya fara, hameed kuma yana tsaye cikin tashin hankali, ammi idonta ne ya sauka akan Aneeta wacce itama kallonta take, cikin hawaye da zafin rai tace "ina zargin Aneeta da ɓatan meenat" duk suka kalleta a razane jin abinda ta faɗa, tace "wallahi Aneeta tanada sa hanu a ɓatan meenat" kaseem cikin gajiya da lamarin gidan yace "kada ki kara maimaita wani kuskuren" tace "babu kuskuren da na aikata ban yadda da ita ba" aneeta kallonta take tana hawaye, hameed dafa kanshi yayi idonshi a rufe ya rasa me ma zai fara yi. Ammi tace "ina ƴata?" Aneeta tace "wa..wa..wallahi ban san komai ba..." da mari ta ɗauketa tace "ina ƴata nace?" tana girgiza kai a tsorace taje bayan hameed ta tsaya tace "wallahi ban san komai akan ɓatan meenat ba" zata kara marinta kaseem yace "ammi kada ki kara taɓata domin batada laifi, yadda kika yiwa zeenat kikeso kiyi mata?" toshe kunne haneed yayi, tace "kaseem ai zeenat kafi kowa sanin waya kasheta, kasan kaine babban abin zargi tunda kaine...." cikin wani irin rawa da jikinshi yake na ɓacin rai yace "kece abin zargi bani ba ke ai kin san kece kika kasheta sabida kisa rayuwan hameed a masifa" sultan ganin kamar zasu daki juna yace "dan Allah ku daina tuna abinda ya wuce ku daina" yace "ka barni na faɗi komai ka bari a tona komai, yau saina tona kowa ma ya sani, matar hameed zeenat kowa yasan ammi ce ta kasheta..." Ammi tayi dariya wanda yafi kuka ciwo tace "me zaisa na kashe zeenat tana matsayin matar ɗanal? kai de kaida kake da kyakkyawan alaka da ita kaine ka kasheta sabida kada ta tona asirinka idan kuma ba kai ka kasheta ba to ko kaffara ba zanyi ba hameed ne ya kasheta...." centre table ɗin dake gabanshi yayi watsi da kayan dake kai yace "dani da hameed kike zargi?" tace "ba zargi bane na tabbatar kaseem" ya nuna hanunshi zuwa kofa yace "saide ke da hakeem ai kinfi kowa sanin menene tsakaninta da hakeem sabida kada ta fada kika kasheta, na rantse da Allah dake da hakeem a cikin biyu ku kuka kasheta kuma hakeem shine wanda ya kasheta domin a hanunshi akaga...." wani tsawan da ammi ta daka a wajen saida duk suka tsorata tace "babu abinda zai haɗa hakeem da matar ɗan uwanshi..." yace "shiyasa kullum yake zuwa ɗakinta da dare? me yake zuwa yi?" tace "kai me ya kaika har kasan tana zuwa?" sultan idonshi akan Aneeta wacce take murmushi kasa kasa da alama wannan sirrin take son ji, hanunta ya rike kara tayi tace "ka sakeni sultan" kaseem yace "ka saketa sultan" bai kallesu ba kawai ya fara janta har stair, wurgar da ita yayi bayan ya shiga ɗakin ya rufe kofan yace "ina meenat?" tace "wallahi sultan ban san komai ba" yana nufota yace "ina meenat?" baya ta fara daga zaunne tana girgiza mishi kai tana hawaye tace "wallahi ban sani ba" mari zaiyi mata ta rike hanunshi gam, tashi tayi tana kallon cikin idonshi tace "me kake tsammani sultan kanin mijina? nice zaka mara? hmm tunda kanason jin komai bari na faɗa maka meenat na kasheta kuma na bawa kifaye gawanta su cinye, kasan meyasa?" dariya tayi kaɗan tace "sabida sunana Aneeta lawan lamba" a razane yake kallonta bakinshi yana rawa yace "m...m..me?" ta saki hanunshi ta juya baya tace "eh sunana kenan na gaskiya" yace "kenan ke kanwar zeenat ce?" juyowa tayi tana smiling face "unty zeenat ko kuma zeenat haka gatsau? Anyway ni kanwar zeenat ce wacce kuka kashe a ranan data haihu ba ita kaɗai ba har jaririn data haifa saida aka salwantar, kuka bata wahala kamar baiwa, kuka sa ta tsani rayuwa da abinda ke cikin duniya baki ɗaya, kuka azabtar da ita har saida ta haukace sabida azaba daga karshe kukayi ajalinta, na rantse banzo gidannan ba saida na shirya, dukanku saina ɗau fansan abinda kuka yiwa yayata, daga ni sai ita mahaifiyarmu ta haifa na taso cikin kaunar yayata zeenat, batada masoyiya saini" share hawaye tayi tace "dani da zeenat wannan auren shine ya fara raba duk wani shaƙuwan da mukayi, yayanku hameed shine mugun daya fara lalata mata rayuwa yasa mata ɗaci a ranta, yasa ta rasa hope, daga karshe ya kasheta" kallonshi tayi tace "jeka ka faɗawa kowa cewar ni kanwar zeenat ce, jeka" a hankali ya fara yin baya yana kallonta, hanu yasa akan kofa zai fita tace "sultan" tsayawa yayi, tace "idan kaje faɗa musu kada ka manta ka faɗa musu kana canja alluran da ake yiwa hameed" a razane ya cire hanunshi dake jikin handle yana kallonta idanunshi kamar zasu zubo, tayi murmushi me sauti tace "ka fasa zuwa ne? kaje mana sultan allura kawai kake canjawa idan ka faɗa musu ba zasu maka komai ba" ganin ya tsaya turus ta fara takawa a hankali tasa hanu akan handle ɗin tace "tunda ba zaka faɗa musu ba ni bari naje na faɗa musu" hanunta ya rike yana girgiza kai, murmushi ta kumayi tace "sakeni mana sultan" bakinshi yana rawa yace "ki rufamin asiri ya kaseem zai kasheni" tace "zan rufa maka amma akan sharaɗi" ganin ya kasa magana tace "ko da wasa kada bakinka yayi kuskuren faɗawa kowa abinda ya faru, sannan duk abinda zanyi ya zama dole ka tayani ko kanaso ko baka so har sai na cimma burina a gidanku" tace "ka amince?" a hankali ya gyaɗa kai, tace "deal" fita tayi daga ɗakin ta gansu tsaye hameed kuma yana zaune dafe da kanshi. _Jiddah ce...✍️_ 08144818849 [20/08, 2:11 am] Shuraihu Usman: 🌸🌸🌸🌸🌸 *ƘADDARA TA* 🌸🌸🌸🌸🌸 Na *Jiddah S Mapi* *Chapter 10* ~Share hawaye tayi tace "na bashi hakuri kuma ya fahimci banida sa hanu akan ɓatan meenat hasalima ban san komai ba" tayi maganan tana kallon sultan daya fito jikinshi kamar ba jini, tace "ko sultan?" gyaɗa kai yayi, tace "amma idan kuna zargina zan bar gidan" kaseem yace "babu inda zakije" ta tsaya kawai tana kuka, a hankali hameed ya daure ya tashi, share mata hawayen yayi ya rungumeta, ammi da kallo kawai take bin Aneeta, kashe mata ido tayi. har kwana uku babu meenat babu dalilinta har ammi ta fara cire abin a ranta, cikin baƙin dogon riga me masifan kyau Aneeta take saukowa daga stair, dogon takalmi ne a kafarta me tsini ta rungume alkyabba a kirji tana taku kamar hawainiya, saida ta sauko ta tsaya tasa alkyabban da yayi masifan yi mata kyau, har kasa bayan yake ja, kallon sultan dake cin popcorn tayi sai kuma ta kalli fadeel tazo ta kwace popcorn ɗin, murmushi tayi mishi ganin yana kallonta tace "baka iya bismilla bane?" shiru yayi, fadeel yace "unty aneeta kinyi kyau" tace "sosai ko kaɗan?" yace "sosai" dariya mara sauti tayi sannan tace "sultan ka rakani mana" a tsorace ya kalleta yace "zan zan" tace "common yanzu fa zamu dawo ba nisa zamuyi ba" a hankali ya tashi yace "to" hanunshi ta rike zasu fita muryan ammi sukaji tace "ina zaki kaimin ɗana?" tsayawa tayi bata juyo ba, ta karaso ta cire hanunshi daga nata tace "ina zaki kaishi nace? ko shima kashe shi zakije kiyi?" murmushi tayi tace "ni ba kamarki bace..." ammi cikin hasala zata mareta sultan ya tare, girgiza mata kai yayi alaman dan Allah kada ta mareta domin yanzu yana masifan tsoron aneeta zata iya kashe kowa kamar yadda ta faɗa. murmushi tayi tace "tare mata kake sultan?" yace "ammi please" tace "shikenan ka bita amma inaso ka sani wannan yarinyar batada imani zakazo kayi dana sani" yayi shiru, juyawa tayi zaiyi magana Aneeta taja hanunshi suka fita. motar dake wanke tas bakin jeep me tsadan gaske ta shiga, gani yayi ta zauna a mazaunin driver tace "shigo mana ka tsaya kana kallona" shiga yayi taja motan suka fita, ganin yadda take gudu da motan cikin kwarewa yasa yake kallonta, murmushi tayi bata kalleshi ba tace "karka damu bazan kasheka ba" shiru yayi yana kallonta har suka yi nisa da gidan, wani unguwa yaga ta shiga dasu, a wani gida ta tsaya tayi hon buɗe gate akayi ta shiga, parking tayi ta fito, ganin baida niyan fitowa tace "fito mana" a hankali ya fito, hanunshi ta rike suka shiga ciki, wutan gidan a kashe ta kunna sannan taja hanunshi zuwa wani ɗaki, buɗewa tayi suka shiga, ya kalli matar dake kwance akan gado ansa mata oxygen idonta a rufe duk gadon ansa wayoyi da remote nasu da alama kyakkyawan kulawa ake bata, tayi kissing na matar a forehead sannan tace "zauna mana sultan" a hankali ya zauna akan stool dake gefe, tace "kasan wacece wannan?" girgiza kai yayi tace "wannan itace momy itace ta haifeni kuma itace ta haifi zeenat wacce yayanka ya kasheta, kasan meya sameta take kwance haka?" girgiza kai yayi, tace "sabida mutuwan zeenat shi yasa tsinkewan zuciya ya sata a wannan halin har yau bata kara tashi ba, tana da likitoci biyu masu sirri da suke zuwa dubata a lokacin da abin ya sameta sai kuma daga baya na gane bs likitocin amana bane domin alluran da suke mata na kashe gaɓoɓin jiki ne, kasan da nayi bincike mena gano?" girgiza kai ya kuma yi, tayi murmushin da yafi kuka ciwo tace "na gano wannan likitan da yake mata wannan mugun alluran hameed ne" a razane ya kalleta sabida yasan hameed ba likita bane, tace "kana ganin karya nayi?" yayi shiru, buɗe side drower tayi ta ɗauko wani waya ta kunna, hoto ta nuna mishi hameed ne sanye da kayan dr yana tsaye a ka matar yana jan ruwan allura, tace "wannan bashi bane? shine yake mata alluran da yake kara ɓata jikinta har yasa bata iya taka kafarta ta zama mara amfani tun tana iya magana har tazo ta daina, bayan ya kashe ƴarta kuma yazo ya lalata rayuwarta?" share hawaye tayi cikin bushewan zuciya tace "bana kasarnan amma na dawo sabida ciwon da momy take ciki, na tsaida komai nawa na bar komai na bar karatuna da nakeyi a kasar cyprus, na rasa yayata wacce nafi sonta akan komai na wannan duniyan na rasa farin ciki na rasa komai sabida hameed kana ganin zan iya yafe masa?" shiru yayi yana karewa hoton kallo tace "idan na yafe mishi ai Allah ma ba zai barni ba" tace "wannan shine abinda yasa na fito da kai" baice komai ba sai kallonta da yake, ta share hawaye tace "muje lokacin alluranta yayi dr zaizo yanzu" binta kawai yake yi har ta rufe kofan suka koma motan, yana kallo ta share hawaye taja motan suka tafi, koda suka koma gida ɗaki ta wuce ta barshi a wajen. Asmeeta Asmeeta? sunanta yake kira yana haska toci, cikin bacci ta murza ido tace "uuumm waye yake tashina a baccina me daɗi?" cikin tsawa yace "tashi mana" tashi tayi da sauri tace "hamma najeeb meya faru?" yace "ina take?" da sauri ta kalli gefenta cikin yarantan da bata iya dainawa tace "ko ya shiga banɗaki" yace "babu fito inaga ya tafi a shikin daren nan" da sauri ta tashi ta fito, yana haska fitilan yace "muje" fita sukayi domin nemota, da mamaki ya ganta a kofar gida tayi tagumi tana kallon shanyen dake cikin garke, lumshe ido tayi ganin suna haskata da fitila, itama sanye take da kaya irin nasu, murmushi tayi ganin ya haskata tace "hamma najeeb kaine?" ya sauke ajiyan zuciya yace "me kakeyi anan? mutanen wannan garin basuda imani zasu iya kasheka tashi mu tafi gida" tashi tayi suka sata a gaba suna baya, har ɗaki ya rakasu da fitilan ya fita yaji Asmee tace "meyasa kake son fita waje?" murmushi tayi tace "idan mace ne ba kake zaki ce ba kike zaki ce, kice meyasa kikeson fita" murmushinta me bala'in kara mata kyau tayi sannan tace "to me yasa kike son fita?" tace "sabida banason ina zama a gida ina kallon hamma najeeb" da sauri tace "sabida me?" tace "ban sani ba amma idan na kalleshi sai naji zuciyata tana narkewa kuma nasan zan iya faɗawa soyayya dashi kuka na zan sameshi ba dan naga duk ƴammatan kauyen nan naku idonsu a kanshi kuma naga baya kula kowa ni kuma banaso nayi abinda zaizo ya dameni" shiru tayi tana kallonta batace komai ba, murmushi tayi mata tace "amma Inaso wannan maganan ya zama tsakanina dake karki fada mishi kinji? sabida nasan watarana dolene mu rabu" shiru tayi tana kallonta, tace "amma meyasa kike ganin ba zai soki ba?" tace "sabida naga abinda yake gabanshi kawai yake yi baya shiga harkan kowa gashi baya magana wani lokaci idan kika tafi kiwo baya magana sai shi da mimi kawai yake surutu idan ta fita kuma sai gidan ya zama shiru" murmushi tayi tace "ki mishi uzuri abinda ya faru a rayuwarmu shiyasa baya kula kowa ya saba da hakan idan kinga yana magana sai idan dani ko mimi, hakan ya samo asali ne saboda rashin kaunarmu da mutanen kauyen nan suke yi, hamma najeeb yasha wahala sosai kafin mama ta mutu" tace "zaki iya bani labarinku?" gyaɗa kai tayi tana kuka tace "babanmu ya mutu tun mama tanada cikina, mama batada lafiya mutanen kauye sunki kulata sunce wai itace ta kashe baba sabida ta gaji shanayenshi, hakan yasa suka tsanemu duk inda hamma yaje neman taimako sai su koreshi hakan yasa baya zuwa gidan kowa harda ƴan uwan babanmu dana mama, da haka har mama ta haifeni cikin wahala da azaba ta bawa hamma amanata, duk duniya babu abinda yakeso sai ni wacce na ɗaukeshi kamar babana shi yake kula dani tun ina jaririya har na girma, sana'ar baba ne bada magani hamma ya koya tun yana yaro yake bada magani hakan yasa nake binshi jeji kullum idan zai tafi har nima na iya bada maganin watarana idan baya nan nice nake bawa mutane, hamma yasha wahala kuma har yanzu yana sha shiyasa kikaga baya kula kowa, kada kiga laifinsa ko abokai baya dasu basa sonshi tun yana karami hakan yasa shima yake janye jkinshi daga su. tace "kenan duk iyayenku sun rasu?" tace "sun rasu hamma shine iyayena sabida yana sona fiyeda yadda yake son kanshi" tace "to mai zai hana ku bar kauyen ku koma wani wajen da zama" tace "ba zai yadda ba sabida na taɓa mishi maganan yashe zamanshi anan yafi mishi domin yana taimakon mutane da magani, macizai suna yawan taɓa mutane yana basu magani sannan duk wanda yake rashin lafiya da yaddan Allah idan hamma ya bashi magani yana jin sauki" murmushi tayi ta lumshe ido haka kawai taji yana kara kwanta mata a rai. wucewa yayi ɗakinshi bayan ya gama jinsu, akan tabarman da yake kwana ya zauna yayi shiru yana juya zancen ta a ranshi, bai taɓa jin zuciyarshi ya buga a lokacin da wata ta furta tana sanshi ba sai akan wannan aminan to amma yasan wannan batayi kalan kauye ba, daga ganin kayan jikinta da suka tsinceta dashi da kuma fatar jikinta duk da suma fatarsu me kyau ne amma nata ana gani zaka san wannan ba ƴar talakawa bane, kada ya yadda ya fara sonta shima suyi aure tazo ta tuna komai data manta, yasan ba zata yadda dashi ba idan ta tuna komai a kanta, har dare yayi nisa yana tunani da kyar ya samu bacci. washe gari tunda tayi salla take zaune akan tabarman tana kallon Asmee wacce har yanzu salla take, saida ta idar tace "Asmee" tace "na'am" "sallah raka'a nawa kikeyi?" tace "ni raka'a shida nake asuba shi kuma hamma da shike namiji ne yana yin takwas" dariya tayi sosai saboda abin dariya ya bata, ta turo karamin bakinta tace "to me kina mana dariya? ba haka bane?" tace "ba haka bane" fara mata bayanin yadda ake salla tayi, mimi ta tashi daga bacci tace "Adda zanyi salla" meenat wacce take jin yarinyar har cikin ranta tace "muje na miki alwala" tace "to" fita sukayi tayi mata alwala sannan ta dawo da ita ɗakin, salla me kyau ta sata tayi tace "haka zaki rinƙa salla kullum" hamma ne yayi sallama ya ɗaga labulen cikin rashin magananshi yace "kuna lafiya?" meenat data kasa ɗauke idonta daga kan kyakkyawan fuskanshi tace "muna lafiya" ya kalli Asmee yace "zan fita idan kika kuskura na dawo gida naji kinyi faɗa da mutane a wannan kauyen wallahi saina kakkaryaki" ta sunkuyar da kai tace "to" fita yayi ta leka tace "yawwa ya fita yau zan zagaya dake ko ina na cikin kauyennan ki gani" tace "to shikenan" nono sukasha sannan sukaci shinkafa da wake tace "muje" kallonta tayi babu mayafi babu komai amma wai zasu fita? tace "kisa ɗankwali" bata musa ba tasa ta duƙa mimi ta hau bayanta suka fita, yawo ta kaita ko ina na kauyen har wajen me tsire da yace yana sonta ai kuwa ya cika musu leda Asmee sai jin daɗi take ta karɓi ledan, murmushi meenat take tana kallonta wallahi yarinyar tana ranta sosai take jinta har cikin zuciyarta, ɗago manyan idanunta kamar kwai cikinsu fararen sal tayi ɗan karamin bakinta da nama tana tauna tace "kici mana ƴar uwa" murmushi me kyau tayi sannan ta fara ci, tace "kin san me?" girgiza kai tayi tana cin naman tace "kinga wannan me naman? kullum cewa yake yana sona, ni kuma sai naje kiwo na dawo saina ɗauko mimi muzo nan muci nama mu koshi da dare hamma najeeb ya kara kawo mana bakiga banida rama ba? baki ganni da kiɓa kaɗan ba?" tace "sosai kinada hips kuma ance me cin nama sosai shine zai zama da hips" tace "me kuma hips?" bayanta ta taɓa tace "nan" dariya tayi tace "amma da turanci ko?" tace "eh" tace "nima hamma yace idan yayi kuɗi zai kaini birni nayi karatu" wasu ƴammata ne sukazo wucewa meenat taga sunata hararan Asmee itako asmee abinda ke gabanta take yi, har suka wuce basu daina hararanta ba harda tsaki, meenat tace "me haɗinki da waɗannan naga suna hararanki?" haɗiye naman bakinta tayi sannan tace "ai Indai harara ne suyi zasu gaji idan har an haifi yarinya da jini tayi kuskuren kiran sunana ko taɓani, saide su kare a harara domin ko mimi suka taɓa saina kusan kashesu" tace "me kika yi musu?" tace "cewa suke wai nayi cikin shege na haifi mimi wasu ma wai cewa sukayi hamma ne yamin ciki" shiru tayi tana kallonta zafi takeji a ranta idan tana maganan duk da tana kawarka ta mayar kamar ba komai ba amma zakaga tsantsan zafin da takeji akan fuskanta. ta kula batada kawaye babu me zuwa mata amma da alama tanada faɗa sosai, ta rike hanunta tace "sharri kayan kwalba ne gashi kin fisu da komai kinfi duk ƴammatan garinnan kyau duk da kyawawane amma kin fisu kyau ga kuma yayanki da yake bala'in sonki bayason abinda zai taɓaki" ta turo baki tace "to na gode" saida suka cinye tas kafin tace "mimi hau baya mu tafi lambun malam garba" hawa bayan tayi duk inda zasuje sai ta goyeta duk da yarinyar batada rama amma bata jin nauyinta ko ina zasuje tana goye a bayanta, tafiya sukayi da nisa har meenat tace "na gaji gaskiya ba zan iya tafiya ba" Asmee tace "kiyi hakuri ki daure mun kusa zuwa" saida suka kara tafiya me nisa kafin suka isa lambun, sauke mimi tayi ta kalli meenat da take tsoron wajen domin ga duhu ga kukan tsuntsaye, tace "rike mimi ku tsaya anan ku shirya zamu iya gudu a kowane lokaci domin idan malam garba ya kamamu zai kaimu gaban me gari ayi mana shegen duka a gaban mutanen gari" dafa kirji tayi tace "na shiga uku Asmeeta mu gudu to karki shiga" tace "ke dalla matsoraciyar banza ni ai sai idan banyi niyan tsinkan komai ba wallahi babu wanda ya isa ya hanani" tattare zaninta tayi tace "ku jirani" tace "dan Allah Asmeeta kar..." cikin sanɗa taga ta shiga lambun, a hankali take tafiya har ta shiga ciki, tsinkan mangoro da ayaba da gwaiva ta fara, tsinka take tana sawa a ɗankwalin data cire, tun daga nesa taji muryanshi yana cewa "waye? waye yake min sata?" durkusawa kasa tayi ta rufe baki cikin sanɗa take gudu har ta samu ta fita daga lambun, gani tayi ya biyosu a guje, tace "Ameena mu gudu" meenat cikin tsoro ta fara gudu da mimi a bayanta, tun yana binsu har ya gaji ya tsaya yana ɗura ruwan Ashar da tsinuwa, saida sukayi nisa kafin meenat ta sauke mimi cikin wani irin gajiya ta kwanta a kasa tana nishi, itama Asmee zama tayi a kasa tana numfashin gajiya, mimi tace "kin tsinko mana Adda?" ta gyaɗa kai tace "gasu nan" saida meenat ta huta tace "gaskiya Asmeeta bakyajin magana" dariya tayi sosai tace "tashi muje gida kinga har dare ya kusa yi" tashi sukayi suka fara sabon tafiya suna isa gida ta fara shiga cikin sanɗa sabida kada hamma najeeb yaji shigowansu may be ya dawo, tana sa kafa taci karo dashi tsaye yana rike da bulala, mimi tace "wayyo kawu da bulala?" Asmeeta hawaye ta fara ganin kallon da yake mata, bulalan ta kalla take ta zubar da abinda ke hanunta, kallo yayi sannan ya kalli Ameena da itama take ɓuya a bayan Asmeeta, yace "ina farin shanun?" waro ido tayi ta dafa kirji tace "laaa na manta banje na ɗaukoshi ba yau" juyawa tayi zata fita a guje tace "yana bakin kogi" yace "dawo" dawowa tayi tace "hamma dan girman Allah kayi hakuri wallahi zanje na ɗauko" yace "bayan an sace shine zakije ki ɗauko? sau nawa nake faɗa miki ki rinƙa maida hankali akan kiwo kisan duk yawan shanayen?" cikin rawan murya tace "sau dayawa" yace "ina kika samo wannan abin?" tace "a..a...a wannan ne" mimi tace "a lambun malam garba" sallama akayi ya kalleta kafin ya amsa ya fita, malam garba ne ya kawo kara kamar yadda ya saba tareda cewa "wallahi dan inajin nauyinka ne sabida kaine kayi jinyan mahaifina kafin ya mutu ba dan haka ba wallahi dana jima da ɗaure kanwarka, yarinyar nan sata take min a lambu kuma ta gudu?" hakuri ya rinƙa bashi da kyar ya hakura ya tafi, yana shiga gidan tana zaune tana kuka dan tasan yau kam abinda zai hanata dakuwa a hanunshi sai ikon Allah, yace "meyasa kikaje lambun malam garba? ban hanaki ba?" ganin yana tsaye a kanta da bulala ta kasa buɗe baki sai girgiza kai take, watsa mata bulalan yayi rike bayanta tayi ta kwala wani uban ihu kamar zata fasa kunnen mutanen kauyen, shoɗa mata bulalan yake yana cewa "ban hanaki ba?" tace "ka hanani wallahi ka hanani yaya" saida ya zaneta me kyau, sai birgima take a kasa tana rokonshi yayi hakuri, meenat data ɓuya a ɗaki taki fitowa tana ji tana kiranta tazo ta taimaketa ta kasa fitowa, a hankali ta leka sukayi ido huɗu da najeeb da sauri ta koma ciki tana addu'a, yace "Ameenah" fitsari taji yana shirin zubo mata, ya kara cewa "Ameena" tana jin Asmeeta tana cewa "wallahi tare da ita mukaje" yace "Ameena" jikinta yana rawa ta fito ta durkusa kasa cikin tsoro tace "wallahi hamma najeeb na rantse maka da girman Allah itace tace muje nace mata kar muje kar muje tace sai munje" babu dariya akan fuskanshi yace "kinje ko baki je ba?" tace "na...." ihu tayi jin bulalan da masifan zafi, shoɗa mata yake yi tana birgima itama tana rokonshi yayi hakuri, da alama fa idan ranshi ya ɓaci baida sauki domin haɗasu yayi yana jibga yana kallon yadda gidan yake kaca kaca basu kimtsa ba suka tafi yawo saida ya musu duka me kyau suna kuka kafin yace "gobe zaku kara" barinsu yayi a wajen, Asmeeta tana kwance a kasa har yanzu bata daina birgiman ba, meenat kuma cikin rashin sabawa da duka tace "wayyo zafi" mimi ce tayi tagumi ta fara kuka ta ɗauko mangoro tana sha tana ce musu sannu, alwalan mangariba yayi sannan ya fita a gidan, da kyar suka tashi suka shiga ɗaki salla ma a zaune sukayi, daga nan Asmeeta taci gaba daga inda ta tsaya tana kuka. _Jiddah Ce....✍️_ 08144818849 [20/08, 2:11 am] Shuraihu Usman: 🌸🌸🌸🌸🌸 *ƘADDARA TA* 🌸🌸🌸🌸🌸 Na *Jiddah S Mapi* *Chapter 11* ~Tun daga ranan meenat take mugun tsoronshi ko magana yayi da sauri take amsa mishi, tareda Asmeeta suke zuwa kiwo bata taɓa yadda tayi abinda ba daidai ba sabida ɗan banzan duka yake musu daga ita har Asmeeta tsoron yin abu suke, duk da Asmeeta bata jin magana idan taji muryanshi nutsuwa take, yauma kamar kullum sun dawo kenan daga kiwon shanu suna zaune yayi sallama, da sauri meenat taje ta karɓi ledan hanunshi ta mishi sannu da dawowa, ɗakinshi ya wuce sallama akayi suka amsa yarone karami ya shigo yace "wai ana yiwa Ameena magana" dafa kirji tayi tace "waye?" yace "wani yaro ne wai wanda kuka haɗu yau a hanyan kiwo" alama take mishi yayi shiru amma saida ya gama maganan, hamma ne ya fito daga ɗaki yace "kace tana zuwa" fita yaron yayi yaje yace tana zuwa, da mamakinsu sukaga ya fita, meenat tace "na shiga uku na lalace shikenan yau kuma sai ɗan buzuna" babu jimawa ya dawo bai mata magana ba amma tana kallonshi a tsorace har dare yayi nisa mimi tayi bacci kafin yace "Ameenah" amsawa tayi gabanta yana faɗuwa ta fito daga ɗaki, yana zaune akan tabarma ya nuna mata gefenshi yace "zauna" zama tayi kanta a kasa yayi shiru kamar ba zaiyi magana ba sai kuma yace "Ameena?" a hankali tace "na'am" yace "ɗago ki kalleni" ɗago kanta tayi a hankali ta kalli idonshi masu kyau, sai taga ya kara yi mata kwarjini sosai, yace "Ameena inaso na aureki amma ina tsoron ranan da zaki tuna komai da kika manta watakila a lokacin na riga nayi sabo dake sabon da bazan iya rabuwa dake ba, ni maraya ne Ameena kuma banida kowa sai Asmeeta da mimi su kaɗaine rayuwata sai kuma ke da kika shigo rayuwarmu, wallahi Inaso na aureki amma ina tsoron ranan da zaki barmu" murmushi tayi ta ɗago kanta tace "hamma najeeb koda na tuna komai na rayuwata ba zan taɓa iya rabuwa daku ba, Asmeeta ta zama tamkar ƴar uwata da muka fito ciki ɗaya rabuwa daku zaimin wahala, idan har zaka aureni zanfi kowace mace farin ciki a wannan duniyan" shiru yayi yana kallonta, yace "to amma idan kika tuna kuma kikaga matsayina da naki ba ɗaya bane ya zakiyi?" tace "babu yadda zanyi saide na godewa Allah" yace "tom Ameena na gode tashi kije" tashi tayi cikin jin daɗi ta tafi ɗaki, Asmeeta data laɓe tana jira taji an fara jibgan Ameena sabida itama idan saurayi ya aika duka yake mata taji duk abinda ya faɗa, murmushi ne ya suɓce mata, da karfi ta rungume meenat kamar zasu faɗi tace "hamma zai aureki?" itama cikin jin daɗi tace "eh" murna sukeyi a ɗakin. Ammi ta rame sosai saboda halin da take ciki na ɓatan meenat amma zuwa yanzu ta daina damuwa kamar farko, hameed ne kwance akan gado yana juyi lips nashi na kasa cikin bakinshi yana tauna cikin azaban ciwon ciki, kallon gefenshi yayi yaga babu Aneeta a kullum baya ganinta tafiya take ta barshi, waya ya ɗauka ya kira numbern ya kaseem, ya kalli time karfe ɗaya na dare, ganin bai ɗaga ba ya tura mishi text, ya kaseem dake zaune da laptop akan ƙafarshi yana kallo yaji karan kiran waya kafin ya ɗauka kiran ya yanke, da sauri ya fara karanta text ɗin da hameed ya tura mishi (_ya kaseem kazo cikina_) yana sauka yace "ciwon ciki kuma? to ina Aneeta?" fita yayi ya nufi ɗakin da mamaki yaga a buɗe, knocking yayi sannan ya tura ya shiga, da sauri yaje ya rikeshi ganin zai faɗi garin birgiman da yake, yace "subhanallah hameed ciwon yayi worst haka?" jijjiga kai yayi yana rirrike hanun ya kaseem ɗin cikin azaban ciwo, yace "okay relax relax gani nan ai ko?" gyaɗa kai yayi, ya kalleshi sosai yaga ya rame sosai kamar yana cikin damuwa, ya kula da hakan cikin kwanakin hameed baya cikin kwanciyar hankali, ya kalli ɗakin yace "to ina Aneeta?" girgiza kai yayi alaman baisan inda take ba, ganin yanasa hanunshi a cikinshi yace "sorry amma ya akayi ciwon ciki yake kara maka Aneeta bata kulaka ne?" hawaye ya cika mishi ido ya taɓe baki zai fara kuka ya kaseem yace "karka sake kamin kuka anan" shiru yayi, yace "to me amfaninta? kayi s** da ita?" shiru yayi, shima ya kaseem yayi shiru da alama koda yayi to ba sosai bane sabida gashi har yanzu yana ciwon cikin da yafi ma na baya, ganin yana hawaye ya fara lallaɓashi yace "don't cry Allah zai baka sauki kaji?" a hankali ya jijjiga kai, jingina kai ya kaseem yayi da jikin gadon yayi shiru yana tunani, meyasa Aneeta zatayi haka? yadda ya yadda da ita yayi expecting idan hameed ya aureta zata kula dashi amma sai yaga kamar hameed ɗin ma yana lalacewa ne ya zama wani kala kamar akwai abinda yake damunshi, ɗaura kanshi yayi a cinyar ya kaseem ɗin yayi shiru yana kallon saman ɗakin hawaye yana wanke mishi fuska, ya kaseem yace "ya Allah ka ragewa kanina wannan wahalan, ya Allah yasha wahala sosai banaso ya kara shan wahalan da yasha a baya, hanunshi yasa a kanshi yana shafa gashinshi da suka hargitse, shiru yayi, sai kuma can ya kara fara jujjuya kai yana rike maranshi, ya kaseem yace "sorry bari nayi maka allura" fita yayi yazo da allura, mishi yayi yana rungume da ya kaseem har ya fara bacci sabida alluran me karfi yayi mishi, shiru yayi yana kallon innocent face nashi, bai taɓa ganin mutumin da yasha wahala a rayuwarshi kamar hameed ba, tun yana yaro yake shan wahala har yanzu bai samu nutsuwa ba, tun daga kan zeenat daya aura basu taɓa kwana ɗaya cikin kwanciyan hankali ba har zuwa yanzu da yake ganin rashin dacewa da auren Aneeta da yayi, cikin sanɗa ta turo kofan ta shigo, turus ta tsaya ganin ya kaseem ne zaune akan gadon ga hameed rungume dashi yana bacci da alama da kyar yayi baccin duba da zufan dake goshinshi, jikinta ne ya fara rawa tana sanye da bakin riga silk tasa hulan net, kanta ta sunkuyar kawai ya sauke kan hameed daga jikinshi ya kwantar dashi, kallonta yayi sama da kasa baice mata komai ba kawai ya fita daga ɗakin, taɓe baki tayi bayan ya fita sannan tazo ta hau gadon ta kwanta. ya kaseem safa da marwa ya fara a ɗakin a ranshi yace "anya bamuyi kuskure ba?" sai kuma ya zauna ya dafa kanshi, kullum baya bacci tunani baya bari yayi bacci idan yayi bacci to saide ɓarawon bacci ne ya saceshi, ga ɓatan meenat da yaga ya dami sultan duk ya zama wani iri kullum yana nemanta babu dare babu rana ga damuwan da yake gani da rashin kwanciyan hankali ƙarara a tare da hameed, wannan damuwan kaɗai sun isa su hanashi bacci. washe gari duk suna breakfast babu me yiwa juna magana, Aneeta ce ta fito tayi bala'in kyau cikin atamfa fited gown ya matukar kama jikinta ta ɗaura bakin After dress a sama, takalmi me tsini tasa sannan ta rike karamin jaka ta sauko ta kallesu duka bata gaida kowa ba ta zauna akan kujera itama ta fara cin abinci, kallo ɗaya ya kaseem yayi mata ya ɗauke kai, har suka gama breakfast ta tashi cikin yauki tana tafiya, ya kaseem yace "ai da tun farko kin nuna halinki da zamufi jin daɗin zama dake sabida babu wanda zaizo yayi tunanin akuya ce aka lulluɓe da fatar kura" murmushi tayi sannan ta ciro bakin glasses a jakanta tasa, juyowa tayi tana kallonshi tace "ya kaseem duk gidannan akuyoyi ne aka lulluɓe da fatar kura so banga laifi ba dan surukur gidan ta zama akuya da fatar kura" zaiyi magana hameed ya rike hanunshi ya girgiza mishi kai alaman please yayi shiru. bai kara magana ba ita kuma ta fita domin zuwa school, Ammi murmushin da yafi kuka ciwo tayi sultan kuma ya sunkuyar da kai ya rasa yadda zaiyi abin yana damunshi gaba ɗaya ya zama shiru shiru. ya kaseem labcoat nashi yasa ya fita a gidan ranshi a ɓace, sai dare ta dawo gidan, suna falo tace "sannunku" ya kaseem yace "daga ina kike?" tace "ya kaseem a ganina yarima hameed ne kaɗai yakeda iko akaina shine zai iya tambayata daga ina nake, to amma ba komai daga school nake" zaiyi magana sultan yace "dan Allah yaya kada mu kara wani tashin hankalin akan wanda muke ciki a gidannan" shiru yayi amma fa zuwa yanzu ranshi ya gama tafasa wallahi da yasan haka halin Aneeta da babu abinda zaisa ya taimaka mata harma tazo gidan bale ta samu fuskan auren hameed, banda ƙaddara ma ai tasan hameed ba sa'anta bane, hameed ya fita komai harma da kyau babu abinda bai fita dashi ba, amma tayi sa'a hameed yana sonta da wallahi saiya koreta, tashi yayi yabar wajen ranshi yana soyuwa. murmushi tayi lokacin data buɗe kofa taga hameed zaune akan kujera yayi shiru abin duniya duk ya isheshi haka takeson ganinshi cikin damuwa abin yana bata nishaɗi, kallonta yayi yaga tana mishi murmushi, shima murmushin yayi mata, a hankali tayi wurgi da jakan cikin gajiya ta cire after dress ɗin shima ta wurgar, zuwa tayi inda yake ta zauna akan cinyarshi, rungume kanshi tayi a hankali tasa hanunshi a waist nata, riketa yayi sosai yana jin sonta har cikin ranshi, a kunnenshi tayi magana cikin wani kasalallen murya tace "am sorry my prince" shiru yayi, a hankali ta haɗa bakinta da nashi, kissing nashi ta fara ta rufe ido, cikin damuwa da kewan da yake ciki ya fara mayar mata, Allah sarki jikinshi har rawa yake sabida Allah ya yishi da matukar needing, zuge zip ɗinta yayi yayi kasa da rigan, hanunshi yasa a chest nata ya fara wasa dashi, lumshe ido tayi cikin wani irin murya tace "Ahhh" ji yayi gaba ɗaya yana neman zaucewa, fuskanshi ya ɗaura a chest nata, shafa kanshi ta fara tana kara matsowa sosai ta yadda bom bom ɗinta zai haɗu da jkinshi, saida ta tabbatar ta gama fitar dashi hayyacinshi kafin ta fara zamewa a hankali, riketa yayi sosai yana ji yau idan ta matsa a wajenshi babu abinda zai hanashi suma, cikin sanyi tasa hanu akan nashi ta rabashi da jikinta, idanunshi da suka tsume yake kallonta dasu a hankali ta sauka daga jikinshi ta shiga bedroom, rufewa tayi harda makulli sannan ta jingina bayanta da kofan tana maida numfashi idonta a rufe. hameed sauka kasa yayi ya kwanta ya fara kuka, ya rasa yadda ma zai fara yi da kanshi. wayanshi dake gefe ya kalla ya janyo ya turawa ya kaseem text (_yaya zan mutu_) daga nan yayi jifa da wayan yana kuka sosai. ya kaseem sai safa da marwa yake ya kasa zama sai tunanin mafita yake, wannan aneetan wani hali takeso ta fara nunawa koma yace ta nuna, dunƙule hanu yayi ya fesar da iskan bakinshi karan shigowan text da yaji yayi saurin ɗauka yana dubawa, da sauri ya fita a ɗakin, ko sallama baiyi ba ya buɗe kofansu ya shiga, gani yayi yana birgima a kasa, da gudu ya karaso ya ɗagashi, kwanciya yayi akan sofa, idonshi yayi jajur kamar yadda bakinshi ya koma red, daga idonshi kaɗai zaka san me yake damunshi, dafa kai yayi yace "hasbunallah yarima ina Aneetan?" nuna mishi kofan ɗakin dake rufe yayi, a fusace ya tashi zaije ya rike hanunshi alama yayi mishi na yaya please, komawa yayi ya zauna, ganin yana kuka shima yaji kamar zaiyi kukan yace "yarima ya zanyi? da wanne zanji yarima? da wanne zanji?" sai kuma yayi shiru, ganin haka hameed ya ɗan rage kukan. tausayinshi yasa ya rike hanunshi yace "tashi muje ɗakina" tashi yayi a hankali yake tafiya yana mishi sannu har sukaje ɗakin, ya mishi allura sannan yace "kwanta" kwanciya yayi babu jimawa bacci ya ɗaukeshi, waya ya kira da sauri aka ɗaga yace "Alameen ya kake?" ya amsa da "ina lafiya ya kaseem ya abokina?" yace "gashi nan kamar yadda ka sanshi, kana gari?" yace "gobe zan dawo dai" yace "idan ka dawo ka rinƙa zuwa kuna fita da hameed" faɗa mishi duk abinda ke faruwa yayi dama basa ɓoyewa Alameen komai sabida good friend na hameed ne, yayi shiru sai kuma yace "wai ya kaseem har yanzu komai bai daidaita bane?" cikin gajiya shima yace "saima kara lalacewa da komai yake yi, please nasan yadda kuke aminta da hameed ya dawo kamar da ya rinƙa zuwa gidanku kaima ka rinƙa fita dashi may be ya ɗan samu sauƙin rayuwarshi may be ya rabu da depression, yanzu so nake ma ya rabu da wannan shegiyar Aneetan da naji na fara tsananta sabida abinda take mishi kuma naga kamar yana sonta sosai" yace "ba komai ya kaseem gobe ina dawowa zanzo" yace "yawwa Alameen Allah maka albarka" yace "Ameen" zama yayi a gefen hameed ɗin yace "ɗan albarka Allah ya baka ikon cinye jarabawa" shiru yayi yana tunanin meenat wacce har yau babu labarinta kullum sai mai martaba yayi zancenta sun kasa mantawa da ita. washe gari kamar yadda Alameen ya yiwa kaseem alkwari sai gashi ya shigo, duk sukayi murnan ganinshi cikin jin daɗin ganinsu shima yace "ina abokina?" sultan yace "dama ai mun san shi kazo wajenshi ba muba ya Alameen" dariya yayi, Alameen kyakkyawa ne sosai amma shi chocolate ne saide kalanshi me bala'in kyau ne, yace "wai ina yake?" Aneeta data fito yanzu daga ɗaki sanye da simple riga da wando tace "waye yake tambayan mijina?" murmushi yayi mata yace "nine amininshi sunana Alameen" kallo ɗaya ta mishi ta watsar, jikinshi yayi sanyi yace "yana ciki?" kaseem daya fito yanzu daga ɗaki yanasa uniform yace "meyasa zaka tambayi wanda basuda hakki a kanshi? ƴan gidansu zaka tambaya ba bare ba" yayi maganan yana kallon Aneeta, murmushi Alameen yayi yace "ya kaseem banga meenat tawa ba ina take?" yace "meenat ta ɓata" yace "innalillahi yaushe?" faɗa mishi komai yayi sannan yace "ka kwantar da hankalinka zamu samu meenat insha Allah kuma kamar yadda akayi maka alkwari kaine zaka aureta meenat ba zata auri kowa ba sai kai. yace "amma ya kaseem meyasa baku faɗamin ba?" yace "sabida nasan zaka iya barin komai da kakeyi a kasar waje ka dawo nigeria domin neman meenat sabida nasan yadda kake sonta da mukayi hakuri ba gashi ka dawo ba? kuma tare da kai zamu fara nemanta" yace "insha Allah sai inda karfina ya kare sannan duk wanda yake da sa hanu saina wulaƙanta rayuwarshi" ya kaseem yace "kaje ciki hameed yana ɗakina" da sauri ya shiga ciki domin ganin abokinshi. _Jiddah Ce...✍️_ 08144818849 [20/08, 2:11 am] Shuraihu Usman: 🌸🌸🌸🌸🌸 *ƘADDARA TA* 🌸🌸🌸🌸🌸 Na *Jiddah S Mapi* *Chapter 12* ~Yau ake ɗaura auren meenat da hamma najeeb, banda murna da farin ciki babu abinda Asmeeta take yi, itama meenat ɗin murna take yi sunyi wanka me kyau duk da babu mutane dayawa amma sun ɗan zo har aka ɗaura aure, tunda aka ɗaura aure ya dawo gida ya cire kayan jikinshi daya taƙura mishi, kayanshi na zuwa jeji yasa sannan ya ɗau takobi zai fita, meenat wacce ta ɓata rai tana kallonshi tace "to ina zakaje?" sajenshi me kyau ya shafa, sannan ya zuba mata kyawawan idanunshi da suke ɗaukan hankalinta kamat idanun turawa cikin idon brown ne, lips nashi na kasa ya tsotsa dama wannan ya zame mishi jiki yace "zanje bazan jima ba zan dawo" kamar zatayi kuka tace "yau fa akayi aurenmu amma shine zaka fita?" yace "kiyi hakuri ba zan jima ba zan dawo" tace "gaskiya babu inda zakaje" tsawan daya daka mata yasa tayi shiru tana kallonshi a tsorace yace "ni sa'anki ne? ko kin manta ni yayanki ne kike min wannan maganan nace miki ba zan jima ba" matsa mishi tayi ya wuce, ɗakinsu taje Asmeeta ta kalleta tayi shiru sabida tasan idan tayi magana hamma yana dawowa zata faɗa mishi daga karshe taci ɗan banzan duka shiyasa take kame bakinta yanzu ta daina ɓarin zance domin meenat tana mugun son hamma najeeb kamar ranta, ta harareta tace "wa kike kallo?" kama baki tayi tace "ni ban kalleki ba kuma bance komai ba, ki barni da dukan da nakesha ma ya isheni" tace "ni ɗin ya daina duka na ne?" tsit tayi, duk rashin kunyar Asmeeta idan taji hamma najeeb to shiru takeyi dan tasan dakuwa take a hanunshi, mimi tace "Adda na miki kitso?" tace "ban son kitso taho muje yawo na siya miki mangoro kinji ɗiyata?" cikin jin daɗi tayi tsalle tayi kyau da kwalliyan da Asmee tayi mata, durkusawa tayi ta ɗale bayanta zasu fita meenat tace "ku jirani zan biku" Asmeeta tace "ki tabbatar idan yaya ya dawo ba zakice tare muka fita ba" tace "naji" fita sukayi kamar ranan yauma dare suka dawo, cikin sanɗa meenat ce ta fara shigowa hamdala tayi ganin baya nan tace "ku shigo baya cikin gida" Asmee dake goye da mimi wacce tayi bacci tsaban gajiya ta shigo ta kwantar da ita a ɗaki kafin ta fito tace "da alama yau hamma ba zai dawo da wuri ba, kai amma fa na iya rawa kinga kuɗin da ake watsamin a filin wasa?" meenat tace "kin iya rawa sosai, ai nima yau nayi rawa ba kaɗan ba" fitowa yayi daga ɗakin ya kallesu, Asmeeta da gudu ta juya zata shiga ɗaki meenat ta bita yace "ku tsaya" tsayawa sukayi meenat tace "dan girman Allah kada ka dakemu mun tuba kuma Asmee ce tace muje" dafa kirji tayi manyan idanunta ta zuba mata tace "ni kuma ameena? a tashi mimi zata faɗi waye yace zai je" yace "kuzo magana zamuyi" sun kasa yadda dashi da kyar suka zauna, gani sukayi ya zauna yayi shiru, Asmee cikin mutuwan jiki tace "hamma kana lafiya?" ɗago kai yayi ya kalleta sannan ya girgiza kai, cikin sonshi da tausayinshi tace "hamma me yake damunka?" yace "Asmeeta" tace "na'am hamma" "tunda iyayenmu suka haifemu muke fama da talauci da rashin jin daɗin rayuwa, kin san duk duniya babu wacce nake so sai ke, bayan ke kuma sai mimi sai kuma Allah ya kawo mana Ameena cikin rayuwarmu wacce nake jinta har cikin raina, Asmeeta duk da mutanen kauyen nan suna ganin kin kai aure amma ni karamar yarinya nake ganinki hakan yasa ban damu kiyi aure ba, kullum addu'ata Allah ya baki rayuwa me kyau wanda zakiyi farin ciki saboda kin taso cikin maraici babu uwa babu uba nine uwa kuma nine uba a wajenki" tace "hamma soyayyan daka nunamin ko mama da baba sai haka" yace "Albishir nakeso nayi muku" da sauri tace "na me?" ya nuna musu wani dutse dake hanunshi yana yalƙi sosai, tace "me wannan hamma najeeb?" yace "wannan shine asalin gold, na samu a cikin ruwa yau da naje wanke takobina, nasan kuɗin gold wanda bai kai wannan bama zai iya ciremu a talauci bale wanda na samo dayawa" tashi yayi ya shiga ɗaki, fitowa yayi dasu dayawa a bakin leda yace "wannan sune arzikin da Allah ya bani a yau bayan aurena da Ameena" rufe baki asmeeta tayi tana kallonshi with surprise, bakinta yana rawa tace "hamma gold?" ya bata a hanunta yace "tabbas Allah ya karɓi addu'ar mu zakuyi rayuwa cikin farin ciki, zamu bar wannan kauyen zamu koma birni muyi rayuwa me ɗauke da gata, dama alƙawari nake miki tun kina karama cewar zan kula dake kamar sarauniya yanzu tare da matata Ameenah zan kula daku tamkar ƴaƴan sarki" tashi tayi ta rungumeshi tana murna, Ameena hawayen farin ciki ta share tace "Alhmdllh dama banada buri kamar naga yana cikin farin ciki gashi yau yana dariya" ido kawai ta zuba mishi yadda dariya yake bala'in yi mishi kyau. hanu ya buɗe mata tazo itama ta rungumesu, yace "gobe zan tafi birni da asuba zan tafi ba lalle ya zama kun tashi a bacci ba, zanje na siyar may be na kwana may be na dawo da wuri, zanja kunnenku musamman ke Asmeeta na sanki da taurin kai da rashin jin magana, ku kula da gidannan ku kula da mimi kunji?" duk suka amsa da "to hamma" sakinsu yayi yace "shine maganan dana kiraku muyi" murmushi akan face nasu suka koma ɗaki, yana kwance a ɗaki yayi shiru yanata juye juye tunanin yadda zai gyara rayuwarsu yake, sallama yayi, da mamaki ya amsa jin muryan meenat, shigowa tayi ya kalleta ta cikin haske kaɗan na fitila yace "Ameena kece?" tana tsaye ta gyaɗa kai a hankali, yace "me kikazo yi?" tana turo karamin bakinta tace "Asmeeta ce tace min idan anyi aure ɗaki ɗaya ake kwana da miji shine nazo" dariya yayi kaɗan sannan yace "to ki karaso" a hankali ta karaso ta zauna a gefenshi, ba zato taji ya janyota jikinshi, rungumeta yayi cikin sanyin murya yace "ina sanki sosai" wani sanyi taji a ranta jin kalman daya faɗa, ta jima tanason jin wannan kalman daga bakinshi, a hankali tace "nima ina sanka" yace "kar kice nima kice ina sanka" tace "ina sanka" a hankali ya juyo da face nata yana kallonta, lumshe ido yayi yace "kimin alkwari duk inda naje ba zaki taɓa mantawa dani ba" murmushi tayi tace "ba zan taɓa mantawa da kai ba har karshen rayuwata" a hankali ya kara mannata da jikinshi, ji tayi ya fara yawo da hanunshi a bayanta yadda take jin sonshi batajin zata iya hanashi yin komai da ita. a hankali ya matso da lips nashi ya ɗaura akan nata, kiss ya fara mata ta rufe ido, a hankali yake sauke numfashi me wuyan fasara, kashe fitilan yayi sannan a kunnenta yace "kiyi hakuri zakiji zafi kaɗan" rufe ido tayi tace "idan kaine ko mutuwa zanyi ban damu ba" wani irin sonta ya mamaye zuciyarshi, a hankali yake bi da ita, duk da taji zafi amma ta daure saida zafin yayi yawa kafin ta buɗe baki zata fara kuka cikin lallashi yana hana kanshi rasa control yace "yi hakuri" a daren saida ya tabbatar ya maidata nashi kafin ya fara bata hakuri, sai kuma yayi shiru yana jin saukan numfashinta a faffaɗan kirjinshi. ji yake kamar su dawwama a haka, karo na farko daya fara jin farin ciki da kaunar mace a ranshi ji yayi Ameena ta zame mishi komai a rayuwa idan ya rasata da Asmee zai iya rasa rayuwarshi. bacci ne ya ɗaukeshi. washe gari ya fara ɗaukanta da asuba ya kaita banɗaki ruwan zafi ya dafa sannan yazo yayi mata wanka, sai ciza baki take cikin azaba yace "sannu kinji?" alwala yayi mata sannan ya fito da ita, kwantar da ita yayi a ɗakinshi yace tayi salla, salla tayi shima yayi salla sannan ya shirya yace "kiyi hakuri nayi ɓarna kuma zan tafi na miki alkawari zan dawo duk inda naje kina raina kuma zan dawo bada jimawa ba zan baki rayuwa me kyau zakiyi rayuwa kamar ƴar sarki" a hankali ta shafa kanshi tace "Allah baka sa'a amma ka dawo da wuri" yace "insha Allah" yace "kimin murmushi to" a hankali tayi murmushi yace "yawwa matata abin alfaharita" tashi yayi ya ɗau jakan da gold ɗin yake ciki yace "na tafi" tace "Allah tsare hanya" a hankali yace "Ameen" fita yayi ya shiga ɗakinsu Asmeeta baccinta da takeyi kamar wacce ta mutu shi takeyi yasan ko za'a kwana ana tashinta ba zata buɗe ido ba, tsaki kaɗan yaja yace "Allah shiryamin ke asmeeta Allah yasa ki girma kisan fari da baki" kallon mimi yayi yace "Allah yasa kada kibi halinta" murmushi yayi yace "na barku lafiya" fita yayi daga gidan. saida gari yayi haske sosai kafin Asmeeta ta fara buɗe ido, tashi tayi da sauri ta kame tulin gashinta daya barbazu ta tashi da sauri tace "Allah sa hamma najeeb bai tafi ba" ɗakin ta buɗe taga meenat ce kaɗai kwance tana bacci, da sauri ta fara tashinta, cikin gajiya meenat ta buɗe ido, kallonta asmee tayi cikin wauta da rashin sanin komai tace "kinzo sai bacci kike ina hamma najeeb?" tana hamma tace "ya tafi" shiru tayi bataji daɗi ba taso suyi sallama kafin ya tafi, cikin kwantar da hankali meenat tace "kiyi hakuri zai dawo ko yau ko gobe ba zai wuce jibi ko gata ba" tace "to wanne zan ɗauka? yau? gobe? jibi? gata?" tace "zai dawo Asmee karki damu kinji?" tace "to Allah yasa ya dawo mana da kuɗi dayawa dako kullum sai mun siya abu me daɗi munci" dariya tayi kaɗan sai kuma ta rufe ido zata koma bacci tace "bakida lafiya ne?" gyaɗa kai tayi, tace "Ayya sannu kinji?" shiru tayi bacci har yayi gaba da ita, fita asmee tayi ta fara salla sannan tazo ta fara girki ta gama ta kawo musu sukaci meenat ta kara komawa baccin. Aneeta ce tsaye a cikin school ta kasa zaune ta kasa tsaye hanunta goye a baya kawarta billy wacce suka alaka sosai tazo ta dafata tace "haba Aneeta meyasa kike wannan damuwan?" ta kalleta sannan ta cire glasses black na idonta tace "meyasa nake damuwa kuma billy? kin san ni ƴar sarki ce ban taso cikin wahala ba, na taso cikin jin daɗi da kwanciyar hankali yau ace bayan tashin hankali da nake ciki wai ina ɗauke da ciki? ciki nefa dani billy cikin yarima hameed" billy tace "common Anee ai yarima yana son yara sosai kema kin faɗa me zaisa ki damu to?" tace "ya zanyi da karatuna? kuma ya zanyi na haihu na tsufa kenan?" tace "Aneeta..." rufe mata baki tayi tace "please billy idan zaki taimaka ki taimakamin na zubar da wannan cikin" tace "karki damu muje yanzu ma zan kaiki wajen dr na zai zubar yau ɗinnan" ajiyan zuciya ta sauke tace "ko kefa billy ta?" tace "muje class zuwa anjima" tace "da zafi ake dukan karfe mu tafi yanzu" zatayi magana ta turata suka tafi kawai, motar billyn suka shiga direct sai wajen Dr ɗinta, da suka mishi bayani magani ya bata a wajen ta haɗiye sannan ya bata sauran yace zuwa azahar tasha cikin zai zube yau, ta amsa da godiya sannan ta bashi kuɗaɗe masu yawa, school suka koma sai kusan azahar tasha sauran ta fito daga school ɗin tana jin cikinta har ya fara ciwo, motar yarima ta gani da sauri ta karaso tana mishi murmushi shima murmushin yayi mata yayi bala'in kyau cikin ƙananan kaya, shiga tayi ya tada motan suka tafi, suna isa gida taga yasa hanu a baya ya ciro leda, mika mata yayi ta karɓa tana buɗewa, teddy ta gani da sauran kayan jarirai, gabanta ne ya faɗi tayi saurin rufewa tace "sunyi kyau sosai my prince amma basu kaika kyau ba" ta lakaci karan hancinshi, murmushi yayi suka fito tare, tsayawa yayi yana duba flower ɗin da yaga sun karye kuma ba'a cire ba shiga ciki tayi tana amsa call ɗin daya shigo, da sauri tace "billy inaga fa cikinnan yama fara zubewa kuma banaso yarima yasan na zubar da ciki sabida inada task dayawa da ban gama ba a gidannan..." sauke wayan tayi tana kallon fadeel da yake kallonta cike da zargi da alama yaji duk abinda ta faɗa, zata wuce ya tare hanyan, tace "ka matsa na wuce meyasa zaka taremin hanya fadeel?" yace "Anty Aneeta meyasa kike cutar da innocent soul? meyasa kike cutar da yaya yarima bayan kin san baida niyan cutar da kowa a ranshi?" tace "me kake nufi fadeel?" zaiyi magana ta tureshi ta wuce binta yayi yace "naji duk abinda kike faɗa kuma wallahi saina faɗa mishi" tafiya take har ta kusa haura stair ta juyo tace "fadeel kada ka shiga abinda bai shafeka ba" yace "wallahi saina faɗa" ya kaseem daya fito yanzu ya tsaya yana kallonsu, zata wuce fadeel ya rike hanunta, tace "ka sakarmin hanu fadeel" yace "ba zan sakeki ba har sai yaya yareema yazo...." juyi tayi ta rike hanunshi gam ta fara gangara daga stair wani irin ihu ta kwala tace "cikina ya zubar da cikin" yarima daya shigo yanzu tsayawa yayi a razane idanunshi sunyi girma yana kallonta jini yana zuba daga kasanta, fadeel ya fara girgiza mishi kai yace "wallahi yaya yarima na rantse da Allah...." kuka ya fara ganin yadda take rike cikinta tana ihu, take abi dake salla ya idar da wuri baima san sanda ya shigo ba, ammi ma da hijabi a jikinta da calbi ta tsaya ta kasa sakin kofan tana kallon Aneeta dake kwance tana birgima jini yana zuba, ya kaseem ya kasa gane me yake faruwa, abinda be gane ba shine itace ta faɗi da kanta ko fadeel ne ya tureta? fadeel wand ya gama tsorata yazo da gudu zai ɗagata, marin da hameed ya ɗaukeshi dashi saida ya faɗi a gaban ya kaseem da yake zuwa wajen, ba bakin magana amma wani kallo yake mishi, nufanshi yayi zai rikeshi ya kanƙame ya kaseem yace "dan Allah ya kaseem na san fushinshi na san idan ranshi ya ɓaci ba abinda ba zai iya ba dan Allah ka tainakeni karya kasheni" jikin Ammi ya fara rawa, Aneeta sai juyi take a kasa cikin azaba tana kuka domin ciwon da gaske yake mata bada wasa ba, da tasan haka azaban yake da bata zubar ba. hameed da hanu ya nunawa fadeel kofa, yace "yaya yarima kayi hakuri wallahi" idanunshi sunyi jajur ya kara nuna mishi kofan, abi wanda ya kasa magana da kyar yace "hameed ka kyaleshi dan Allah abi komai a hankali" idanu jajur ya juyo yana kallon abi, sai kuma ya nuna mishi Aneeta dake kwance a kasa ya girgiza kai ya kara nuna mishi hanya, ammi tace "hameed kada kayi abinda zakazo kayi dana sani" wani bugun daya yiwa tv ɗin ɗakin saida tv ya tarwatse, ya juya ya bugi showglass da hanunshi take shima ya fashe, yana huci yake kallon fadeel, aneeta dake kwance tace "ya zubar da cikin hameed ya zubar da cikin zan mutu" a hankali fadeel ya raɓa ta gefen sultan zai wuce sultan ya rike hanunshi yace "dan Allah kada ka tafi fadeel na saba da kai ina zakaje?" ganin yadda hameed yake huci ya sakeshi, yana kuka ya fita, hameed ne yaje ɗakinsu ya buɗe wardrobe ya ciro duk kayan da yasan fadeel yana sawa yasa a akwati ya fito, buɗe kofan yayi ya kira dogari ya bashi ya mishi alama ya kai mishi, karɓa yayi shi kuma ya koma ya rufe kofan, kaseem wanda ya rasa abinyi kawai sai kallonsu yake zuwa yanzu ya gaji, yarima yayi mishi alama da roko akan ya dubata, ɗagata yayi ya kaita ɗaki ya canja mata kayan da ya ɓaci sannan yazo ya goge jinin, ya kaseem wanda jikinshi kamar an zare laka yazo yana dubata, kallon yarima yayi cikin jin tausayinshi yanaso yace mishi magani tasha ya zube amma yasan ba zai taɓa yadda ba sabida ya yadda da Aneetan, kawai yace mishi "cikin ya zube saide kayi hakuri" daga haka ya fita daga ɗakin, zama yayi a kasa ya fara kuka, ɗaki kaseem ya shiga yayi shiru yana, yace "me yake faruwa ne?" hameed fita yayi daga gidan yaje gidansu Alameen acan zai samu yayi kuka cikin kwanciyan hankali, da gudu yake jan motar har ya isa gidansu me kyau ne sosai, shiga yayi mamanshi dake zaune tace "A,a yarima yau kaine a gidan namu? wato abokinka ya dawo ko?" murmushi yayi mata sannan yayi mata alaman gaisuwa ta amsa sannan tace "yana ciki" tashi yayi ya shiga, yana shiga dakin yaga Alameen kwance akan gado yana kallo a laptop, jingina yayi da kofan kuka me zafi yana zuwa mishi, a hankali ya silale kasa Alameen ya kashe laptop ɗin ya sauko daga gadon yace "yarima meya faru kuma" wani irin kuka ya fashe dashi, Alameen cikin damuwa yace "wai yarima har yanzu baka daina wannan kukan naka ba idan abu ya sameka? zaka karyawa mutum zuciya" kukan yake yi sosai, shiru Alameen yayi yana kallonshi harda shesheƙa saida yayi me isanshi kafin ya tashi ya hau gadon yaja bargon ya rufe har kanshi yayi shiru, Alameen ma baiyi magana ba yayi shiru yayi tagumi, rayuwan yarima abin tausayi ne kullum yana cikin damuwa. _Jiddah Ce....✍️_ 08144818849 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels