Showing 1 words to 3000 words out of 42826 words
[3/27, 9:56 AM] +234 803 957 7698: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄
*02*
WRINTING BY *SAJIDA*
Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai,
Sako zuwa ga mabiya novel dina: *gaisuwa mai dumbin yawa, godiya da jinjina, ga wani ya zo fatan zaku karbe shi, taku ce, SAJIDARKU CE*
MARUBUCIYAR:
*YAR MAHAUKACIYA*
*DUK KARYAR KADA*
*DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA*
*NEMAN NA KAINA*
................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH....
A darare ta juyo tana kallon mahaifiyar tata
Inna na karasowa ta jawo hannunta daga cikin gidan kadan, cikin yannayin lalaba ta ce" WUJDANE , karki fita ki yi masa rashin mutunci , du layin nan bawan Allahn nan shi ya ji ya gani ya nace, karki ringa aiki da kyakyawar halitarki yanzu fa duniya tafi karfin tunaninki, Wujdane ki yi fatan gamawa da duniya lafiya, karki yi masa rashin mutunci ba.a yiwa dan adam hakan baki san irin baiwar da Allah yayi masa ba
Kanta a kasa tamkar gaske take amsawa mahaifiyar tata, dokar malan ce ba.ai masa zance da dare, sai dai da safe ko yama , hakan ya saka Sule mai tahuna lokacin zuwansa da safe ne ya zo ya sha darga da yar rigimar tasa
Fitowa tayi da hijabinta baki yauma har kasa, shi dai ne hijabin nan tun na salarsu ne da Malan ya saya masu dan kanti ne
Sai da ta gama harararsa daga nesa kafin ta karaso
Tana zuwa cikiciki ta ce" ina kwana
Cike da murnar ganninta yake amsa mata ya shiga wasata kamar yanda ya saba
Ga mamakinsa a yau bata yi masa tsawar ya isheta ba, saima wani gu da take kallo kadan kadan tana dan juyowa ta kale shi
A ranta ayanawa take" sam baiyi mata ba, shi dai ba qani tsayi ba ga wasu idannuwa micik micik, kuma banda wannan shegen mugun halin tsiya ne da shi, matarsa Aliya yar masifa ce duda tana shayin Wujdane din aman bata da aiki sai masifa
A hankali ta juyo ta ce" zan tafi gidan yawa
Yana murmushi ya ce" tototo ba damuwa ai ina fatan yau za.a karbi kudin nawa
Ya fada yana miko mata yan hansin hansin watar har ta cire dan wuyar da ta sha,
Kudin ta karewa kallo, Wujdane ko yayunta bata rokq kudi ko iyayenta ita dai barta da jarabarta aman ba dai na kwadayi ba
Dagoshi tayi da firgitatun idannuwanta da mutane da dama ke tsoron kallonsu ta watsar gefe , bata ce da shi komai ba ta juya ta nufi gidan yawa
*Wacece Wujdane?*
*Wujdane* jika take wajen Malan Hamza marigayi, mahaifin nana Fatima matar Malan Laminu
Malan Hamza irin bayin Allahn nan ne wanda ya gaji kujerar mahaifinsa a wani kauye dake arewacin Maiduguri,
Bafilatani ne na usul , wani irin fari gare shi da wata irin halitar idannuwa , kwayar idannuwansa tamkar na mage ko maciji kala daban sannan yana sheki,
Malan hamza ya tara iyalai matansa hudu wanda du cikinsu ba wada ta taba haihuwa sai matarsa ta farko wace ake kira da Ya, Allah ya bata ciki har ya cire tsamani
Malan Hamza mai almajirai yana zaune a gidansa dake cike da almajirai yakan fita daji yayi watanni ya kilace kansa sosai ya jima a can kafin ya dawo hakan ya saka ake kiransa aljan domin jejin kansa abin tsoro ne
Tafiyar da yayi *Ya* nada cikin wata uku harda doriya aman bata fada masa ba domin ko kadan bata kawo hakan a ranta ba sun cire tsamani
Wannan fitar sai da ya dauki wata bakwai wanda yana zuwa ya tarar sa yanda aka mayar da *Ya* tamkar banza dan ta haihu a cikin matansa
Sannu a hankali zama ya gagara da sauran matan inda suka sako su a gaba da shi da Ya da yar yarsa wace ya saka mata sunnan yar ma.iki Nana Fadima
Daya bayan daya sai da suka bar masa gidansa dan gani suke baya son haihuwar ne da su, ya kasance a gidan Malan Hamza daga Ya sai yarta Fadima sai almajirai yan matasa
Haka Fadima ta taso cikin gata da karatu, domin a cikin almajiransa akoy wanda suka fi shakuwa sosai da sosai har ake ce masa dan malan wato Laminu
Haka rayuwa take tafiyar masu, tunda Fadima ta taso sai ta taso da wani kyau sosai idannuwanta kuwa tak irin na mahaifinta ne,
Samari da dama suna son kyakyawar fuskarta aman kalar idannuwanta ya saka aka canfa su ko wani gida sai a hana yaro neman aurenta da nufin kamaninsu sun hada iri da maciji
Kauye da ake aurar da yarinya tun tana shekara goma watar sha daya idan kin jima sha uku sai ya kasance Fadima har ta kile sha biyar shiru, sai abin ya zama na zunde idan dai ta fito daga gida sai dai ta dawo tana kukan irin wulakancin da aka yi mata a waje
Sosai abinnan ke ciwa malan tuwo a kwarya, cilon yarsa a irin wannan rayuwar sai ya kasance abin na nukurkusarsa na damunsa har yakan jajantawa Laminu dan malan
Wani lokaci suna zaune Laminu dan malan ya zowa malan da labarin ya samu aiki a birni na tsaron kofar gidan wani Elhaj,
Sosai malan yayi murnar hakan yayi masa sha tara ta arziki
Tunda Laminu ya tafi sai ya samu gurbi mai kyau ya kasance a wajen aikin nasa masha Allah ya samu karbuwa,
Ya kan yiwa malan aike du wata sannan Ya kuwa ya turo mata da su magi da makaroni da shinkafa cimar yan birni dai yakanyi sayayarsa daidai gwargwado ya bayar a kawo
Hakan ya kara dadada ran Malan gannin irin yanda Laminu bai zubar da zumunci ba sannan bai manta alkhairi ba domin Laminu maraya ne na uwa da uba tun yana dan karaminsa ruwa ya cinye iyayensa da dabobinsu
Wani zuwa da Laminu yayi ya jewa malan da muradin Auren Fadima, ba dan yana tausaya mata ba sai dan soyaya ta tsakani da Allah
Malan yayi dogon bincike inda yayi ta istihara, banda alkhairi da kwaituwar hada auren ba abinda yake gani du kwanan duniya hakan ya saka ya daura masu aure Laminu ya dauko matarsa suka kama dan gidan haya suke rauwarsu
Sannua hankali Fadima ta haifi yaronta na fari Malan ya saka masa Hamza, shekara biyu tsakani ta samu wani aka saka masa Abdul Fatah, daidai nan malan yayi dan ginninsa a wata anguwar talakawa tukuf suka koma wanda ya dauki daki hudu yan madaidaita sai bayi da zaure da balbalin gida, da rijiyarsu
Bayan Abdul Fatah ta jima ta kai shekara bakwai shiru har ta fara tunanin haihuwar ta tsaya ne sai Allah ya bata wani cikin ,
Sanu a hankali cikinta ke girma ta kai wata tara da kwanaki kwatsam mumunan labari ya sameta rasuwar mahaifinta da sati mahaifiyarta itama tace ga garinku
Du irin yanda ta kai ga hakuri da juriya taci kuka sosai da sosai ba.a jima da hakan ba ta haihu, wannan karan ya mace
Malan ya saka mata Aisha
Basu kai ga yada wanka ba Aishar ta rasu ta koma, sannu a hankali ta kuma samun wani cikin wannan karon sai ya saka mata *Wujdane*
Wujdane na da shekara uku ta haifi wata macen malan ya maida mata Aisha sunnan Ya
Tun daga wannan lokacin sai haihuwar ta dauke bata kuma koda batan wata ba
Yayan Malan Laminu sun taso da karatu da tarbiya sosai da sosai domin a anguwar ba kowa ya san cewar a cikin gidan yan matan biyu bane sai dadaya wa.ina suke shiga
Cikin ikon Allah sai Allah ya basu Tsagaira, Wujdane ja rigima Wujdane shiga sabgar da ba tata ba, har siyan fada take du girmanka kuwa sai ta daku da kai cikin ikon Allah ta nausaka da kasa
Wujdane ta kwashe gaba daya kyan kakanta domin har idannuwansa bata bari ba, Wujdane ta kasance yar matsakaiciya bata da wani tsayi sosai sannan ba gajeriya bace, bata da rama ko kadan jikinta daidai da ita ne, haka yannayin kirar jikinta a tsare take sosai das da ita
Wujdane gashin kanta ba baki bane kalar ja ne sam bashi da baki hakan ya saka take saka masa lale baki dan yayi baki aman baya sati zaya fara dawo da kalarsa,
Gashinta har bayanta sannan sam baya kitsuwa hakan ya saka mahaifiyarta ke yi mata doka sai ta kindime kan bata bude shi
A kulun ta Allah sai an kawo karar wujdane, domin ko mai hucewa ne bata bari ba, sannan ga shiga gidan yawa gidan da ba mai tarbiya kowa gashin kansa yake ci, gidane a unguwa da suka yi kaurin suna ba mai shiga sai gagarare domin a ciki ne zaka ji kani na lailayawa yayansa zagi idan uwa ta shiga itama a bata rabonta da fitsara da komai
A nan cikin gidan Wujdane tayi kawa suke zaune a ciki tana kara darisan rashin mutunci da tsayaya
Yayanta Abdul Fatah idan da abinda ya tsana bayan halayarta to wutar jahannama ce, baya son halayarta yakan ya saka yake yi mata dukan jaka idan ya shiga yin kwalo da ita sai ka rantse idan ta tashi ba zata kuma ba aman abinda zata aikata sai ya ninka wanda tayin
A kulun yayanta Hamza yakan yi mata gargadi bayan mahaifinta yayi mata aman mahaifiyarta a kulun takan yi mamakin wai shin Wujdane wace irin mutun ce? Ita da ba dan *BATA DA ZABI* ba da ta jima da rabuwa da WUJDANE tun kafin ta kashe ta
Wannan kennan
[3/27, 9:57 AM] +234 803 957 7698: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄
*01*
WRINTING BY *SAJIDA*
Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai,
Sako zuwa ga mabiya novel dina: *gaisuwa mai dumbin yawa, godiya da jinjina, ga wani ya zo fatan zaku karbe shi, taku ce, SAJIDARKU CE*
MARUBUCIYAR:
*YAR MAHAUKACIYA*
*DUK KARYAR KADA*
*DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA*
*NEMAN NA KAINA*
................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH....
Zaune take bakin rijiya bayan ta janyo ruwa ta cika buta , hannayenta bibiyu ta dafe kuncinta tana duban daidai kofar gidan, yar datijiwa ce zata kai shekara arba.in da dori, gaba daya yannayinta yannayin cikin damuwa take domin lafiyar kirki ma bata da ita
A hankali take takowa har ta karaso kusan wannan mata ta tsuguna a kusa da ita, ta ce" INNA ki tashi ki yi alwallar kin saba yi da wuri kinga kina zaune har an fara kiraye kirayen sallar magaribar shi kuwa a makaranta malan ya ce a gagauta shan ruwa a jinkirta yin sahur
Dago da kanta tayi ta sauke kwayar idannuwanta masu wani irin kala tamkar na mage saman yar tata, ajiyar zuciya ta sauke ta ce" Aisha shin da kika je baki cewa Uwa ni nake nemanta ba?
Wace aka kiraya da Aishar ta furzar da iskar takaici ta ce" Inna na fada mata, aman bara na koma ko wani abin ne ya rike ta
Kai ta kada tana kokarin mikewa ta ce" kiyi sallah tukunnan, ba kyau tarban magariba,
Haka ta shige bayin nasu na laka wanda yayi kasakasa sosai aman an saka wani yadi an rufe shi bazaka hango na ciki ba
Uwata kika zaga? Ke Binta kin san na fiki rashin mutunci ko gaban babarku sai na bi ki na daki banza, na yi maki kashedi kula Hamza, ke har kin isa saurayin fa nace bana so ke ki so shi? Ai Hamza ya kade sai dai ya fita ya auro wata ba dai a nan layin ba, shi ne dan na fada zaki ce wai idannuwana girma tamkar na mujiya kwayar ciki sai kace kalar na mage??? Ni? Ni jarin...
Kau kake ji an dauketa da mari, tana dagowa ta ga yayansu ne Abdul fatah, ai kuwa ta nade hijabinta ta artaya a guje ,,
Dubansa ya kai kan Binta dake yashe a kasa tana share hawaye, ya kada kai ya ce" ki tashi ki yi hakuri kin ji???
Binta ta danyi murmushi ta ce" ba komai Abdul Fatah daman bata fahimci zancen bane kuma sai Anasiya tace da ita wai na zage ta
Kai ya girgiza ya juya ya bi bayanta
Tunda ya shigo ya kasa ya tsare yana jiran ta gama sallar da ta kabarta a dakinsu ita da kanwarta, aman kamar mai sauke alkur.ani a cikin sallar bata da alamar gamawar shi kuwa baya so yayansu Hamza da Babansu malan Laminu su shigo su hana shi yi mata dukan mutuwa
Juyowa yayi wajen mahaifiyarsu, ya karaso ya zauna a kusanta yanai mata barka da shan ruwa
Cike da kulawa take amsa masa ta tura masa kankanar da ya shigo mata da ita tsarabar yan azumi,
Kalon yannayinsa take ta ga sai shan mur yake tayi dan murmushi dan ta san kwannan zancen bazai fice Kanwarsa ta tabo shi ba
Asalamu alaikum warahamatulah
A tare suka dago suna amsa salamar Malan da ya shigo da carbinsa , ya gama jan salar isha.i kafin ya karaso gidan, bayansa kuwa yaya Hamza ne rike da dardumarsa
Yana zama dadaya suna gaishe shi Inna ta mike tana gabatar masa da kayan buda baki dankalin hausa ne ta dafa ta yanyanka danyen tumatur da yar albasa sune mahadinsa
Budewa yayi yana murmushi yana yi mata sannu, aman bai ga *WUJDANE* ba
Dubansa ya kai wajen Aisha, a hankali ya ce" MAMANA, shin ina yayarki ne? Ko bata shigo gidan ba??
Inna ta juyo ta juyar da kanta tana sauke ajiyar zuciya, bata ce komai ba, AISHA ta mike tana fadin " bara na duba Aba ko ta gama sallar? Tana nan
Cike da murmushin yau ta dawo gidan da wuri yake fadin "Masha Allah,
Sannan ya bi Abdul fatah da kalo ya mike yayi gaba cike da fushi can cikin ransa yake yiwa yayan nasa gaba daya adu.ar shiriya
A hankali ta fito cikin hijabin nata baki wanda ya tsufa iya tsofewa sosai, ta karaso ta duka kusa da mahaifin nata cike da ladabin karya kanta a kasa tace" barka da shigowa baba, an sha ruwa lafiya???
Yana murmushi yake amsa mata da" lafiya lau WUJDANE ya gida, na same ku lafiya?
Cikin nutsuwa take amsa masa
Ya dago yana hangen fuskar Innarsu, ya ce" Allah ya shirye ki Wujdane , Allah ya kara nutsar min da ke kin ji?
Inna ta juyo cikin yannayin sanyin nata ta ce" uhum, Malan nutsuwar munafurcin?
Kallonta yake yana salamar yaren dan baya son suna irin wannan maganar a gabansu
Bayan sun tafi ya nisa yana kallonta ya ce" ba sai na tambaya ba yauma tayi halin, aman da sauki tunda ban tardo ana jirana a kofa ba, sannan ina tsakar ganawa da iyalina ba.a katse ni ba, Fatima Allah yakan jarabtar bayinsa ta hanyoyi daban faban dan ya auna imaninsu, idan sun yi hakuri sun jure sun kawar da kansu sun mika lamarinsu wa shi , zai wanke masu zukatansu, Kaf cikin yayanmu ba wanda ya kai *WUJDANE* konya, aman karatun bokon ya gagara ke kin san na islamiya ba.a rabarta cikin ikon rabah tana da konya, wannan halaya na yau da kulun wanda na sani koda namiji ne sai hankalinmu ya tashi bare a mace, sai mu dauka tamu Salon jarabawar kennan, mu bi ta da adu.a Fatima sai Allah ya shiryar mana da ita
Inna ta sauke ajiyar zuciya, a hankali ta ce" malan, ai *BANI DA ZABI* , aman ina tsoron rayuwar WUJDANE, ke mace ? Macen ma mai rauni sosai? A shekarun Wujdane goma sha takwas da doriya yaci ace tana gidanta aman du ba wannan fitinar nan ita ta saka a gaba ya zamu yi???
Malan ya lumshe idannuwansa ya ce" ADU.A, ita zamu ci gaba da yi, jinkiri ba kin amsawa bane, Allah ya shiryar mana da ita ya bata miji na gari
Ka.ida ne, karfe hudu na bugawa Wujdane zata bude idannuwanta , ita zata bi dakunnan yan uwanta du ta tashe su daga baci dan su fito balbalin gidan nasu su yi karatu kafin lokacin sallar asuba su tafi masalaci su kuwa su yi sallah su yi zaman azkar
Yauma hakan ta faru, zaune suke suna karatu kowa a hankali Malan na gefe shima ya bude alkur.aninsa Inna na zaune itama rike da carbinta tana ja
Wujdane ta juyo tana kallon Innarsu, juyawa tayi ta maida kanta wajen mahaifinsu ta ce" Baba, ni mai yasa inna bata karatun ne,?
Dago da kansa ya yi yayi mata nuni da ta maida hankalinta kan karatun ba tare da yayi magana ba, hakan ya saka ta mayar da kanta bata ko lura da irin hararar da Abdul fatah ke watsa mata ba
Safiya na yi ta fito ta shiga aikin tsakar gidansu, Wujdane akoy kin ji aman kuma shegiyar tsafta tamkar wata mai aljannun tsafta,
Yaro ne yayi salama karfe goma na safe ya gota,
Yana gannin Wujdane ya dan rabe yana raraba idannuwa dan tsoro
Dago da kanta tayi bayan ta kwashe shara ta wurga masa harara ta ce" shege mai kai tamkar duniya, ubanme kuma kake nema a gidan da safiyar nan? Anzo a ga yau mun samu abin karin ne ko aa ko???
Jikinsa ne ya fara bari yana kallonta ya ce" Mama, ( sunnan da ta dorawa du yaran anguwar nan cewar koda wasa shegen da ya kirayeta da sunnanta sai ta karya masa wuya, tsabar balakinta ya saka yaren dake kiran sunnayen iyayensu ma idan suka hadu da ita sai kaji sun ce *mama* dan idan ka fadi sunnan nata har gaban mahaifiyarka zata bika ta daki banza), yaci gaba mama yaya sule ne ke magana a kofa
Ido ta zaro a fili ta ce" Kan Uba, da safiyar nan ubanme yake nema a kofar gidanmu? Ai kuwa yau zai san bashi da wayo
Saurin saka hijabinta take dan ta fita innarsu kuwa na kokarin fitowa da sauri dan ta tsayar da ita
Har ta saka kafa guda a zauren gidansu ta ji muryar inna na fadin" *WUJDANE WUJDANE!*
........
[3/27, 9:57 AM] +234 803 957 7698: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄
*04*
WRINTING BY *SAJIDA*
Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai,
*SAJIDARKU CE*
MARUBUCIYAR:
*YAR MAHAUKACIYA*
*DUK KARYAR KADA*
*DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA*
*NEMAN NA KAINA*
................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH....
Cike da takaici ta dago da kanta ta sauke idannuwanta a fuskar saurayin da ya duka gefenta kowa na gudunta banda shi, ya zuma mata ido yanai mata wani