Showing 9001 words to 12000 words out of 23028 words

Chapter 4 - HASNAU YAR NAJERIYA COMPLETE

Start ads

10 Aug 2025

105

Middle Ads

fili ta neman tsari daga sharrin karfe sannan yayi reverse ya fita daga harabar Unity Kachako suka hau kan burjin da zai kai su titi. Sai ya kunna mata a|c ya kuma kunna sautin Shaikh Abdurrahman AS-Sudaith cikin Suratul Nisa’i. Shiru ya ratsa a motar baka jin komai sai sautin Sudaith-Abdurrahman da kuma karar a|c wadda ta soma takurawa Hasna’u. Tunda take bata taba jin sanyi mai ratsa jiki irin wannan ba. Sai ya lura tana takure jikin ta cikin hijabinta kamar mai jin sanyi.
Ya rage gudun motar yana tambaya “ko in kasha ne Hasna’u?” “da dai ya fi min” ta bashi amsa da sauri. Murmushi yayi ya kasha a|c din suka cigaba da tafiya.
Barci mai alaqa da yunwa suka soma fizgar Hasna’u, tayi hamma ya kai sau uku Saheeb na hankalce da ita, yadda yake hankalce da duk wani motsin ta cikin motar baya kula da tukin motar haka. “Yaya dai Hasna, barci?” “Umh” kawai tace, tana cigaba da hamma.
Sai ya mika hannu zuwa kujerar baya ya dauko wani dan madaidaicin foodflask ya mika mata. “ungo nan ki ci wannan kan mu isa Kano, eat fast, I cooked it for Hasna’u.
Tun jiya na fere dankalin nasa a firij ina idar da sallah na soya shi”.
Hasna’u sai taji dariya na son kwace mata don bata taba jin namiji da girki ba.
“Uncle baka da mata ne?”
Ya lura dariya take tana kunshe baki ta kuma karbi flask din da hannu biyu. Ya dubeta da kyakkyawar siga sannan ya maida kai ga tukin sa yana murmushi.
“Ana dai nema min har an kai kudi, amma ni gani nake ban isa aure ba”.
Dariyar Hasna’u ta fito fili yanzu, “me yasa kake ganin hakan? Katoto da kai haka? A garin mu kamar ka zaka samu yana da ‘ya’ya hudu”.
Ya rage gudun motar yana kallon ta keenly. “kice kema an kusa yi miki aure, tunda kin kusa gama makaranta”.
Nan da nan fuskar Hasna’u ta canza, wani yanayi mara dadi ya bayyana, duk abinda zai jawo mata gori da tozarci akan halittar ta tana gudun shi, ta san kuma aure shine a haqqu na janyo mata babban tozarci, don haka ta dade da haramtawa kan ta shi, kamar yadda Innar ta ma bata sa a ka ba.
“Kin yi min shuiru Hasna ko baki ji me nace ba?” tayi dan murmushi mai ciwo wanda ya fito daga kasan ruhin ta, a hankali ta yi Magana, wadda ba don ya kasance cikin masu kyakkyawan ji ba, da bazai ji ta ba.
“Da dai a ce ba ZABIYA bace!!!"
Ta bashi amsa a gajarce.
Zuciyar Saheeb ta yi wani irin nauyi, wani ignition ya soki ran sa, sai da yayi nadamar sa ta yin maganar da ya ga hawaye sun tsatstsafo a idon ta. Sai ya tuna Hasna kwarin gwiwa take bukata daga kowa ba nuna raunin ta ba, ko nuna mata yes, ita din nakasahshiya ce.
Muryar sa da karsashi yace.
“Shi zabiyan ba mutum bane? Koko shi zabiya bashi da human feelings?”
Hasna’u ta yi shiru, don bata san ma’anar sentence din sa na biyu ba. Daga bisani ta ce “a wurin mafi yawan mutane hakane Uncle Saheeb, ba'a dauki zabiyan mutum komai ba, kamar wani aljani ake kallon sa. Just because of skin, eye and hair colour wanda ya barranta da nasu.
Duk da haka akwa mutane kalilan, very few, irin wannan da ke gefe na. (Ta dube shi da murmushi) kafin ta cigaba da cewa "Zuciyar ku daban take da ta sauran al’umma. Na gane hakan tun daga ranar da na hadu da kai, sai dai ka yarda irin ka din baku da yawa. You are extraordinary Uncle…..”.
Saura kadan ya karawa motar dake gaban sa, sabida yaddda kalaman Hasna’u suka girgiza shi, kallon wadda bata iya banbance komai yake mata ashe da hankalin ta da kyakkyawan tunanin ta.
“Hasna…!” Kawai ya iya ambato, sai ya rasa mai zai ce yayi shiru. Daidai lokacin da suka shigo Hotoro.
Hasna’u ta wara ido tana kallon birnin Kano, ta Dabo cigari ko da me ka zo an fi ka. Bata taba kiyastawa haka Kano take da girma da kyau ba. For the first time yau gata a Kano mai sunan Baban ta (Kanon-Dabo).

Kai tsaye Murtala Mohammed Specialist Hospital suka nufa. Dama tuni ya musu booking na ganin likita tun kafin su zo don ya san mutane a wurin, amma koda likitan ya duba Hasna’u cewa yayi is better yayi referring din su zuwa Aminu Kano Teaching Hospital su ga Dr. Turaki (duba littafin KULSUM). Koda suka je Aminu Kano sun dade akan layi kafin su samu ganin ophthalmologist din.
“Ocular Albinism shine albinism mai taba lafiyar ido, kuma shine na Hasna.'u. Ka san Albi ism din kala-kala ne. In this case, a person might need to wear special glasses or 'contact lenses' don ta huta da saka gilashi kullum. Saidai kulawa da shi da wahala. Yanzu in kun amince zan saka mata 'Eccentric Contact Lenses' mai kyau a cikin idon ta. Bayan mun auna 'nearsightedness (myopia) farsightedness (hyperopia) and astigmatism' din ta yanzu. Ku kwantar da hankalin ku ‘Ocular Albinism’ baya kasha ido gabadaya.
As she grow older idon ta zai ke gyaruwa. Kuma contact lenses ba’a sanin da shi a cikin idon mutum, sabida a kan kwayar ido ake saka shi”. Inji Dr. Turaki Gaya.
Saheeb yace “it will be difficult for Hasna’u ta iya kulawa da 'contact-lenses' sabida a kauye take kuma babu wanda zai taya ta kula dashi, disposable din kuma zai yi mata wahalar samu akai-akai, don haka ayi mata glasses kawai”.
Dr. turaki ya yarda da shawarar sa don haka ya tura Hasna dakin awon ido, bayan an rubuta prescription aka bata zabin gilashi karami mai kyau ta zabi wani shade dan siriri, Saheeb ya biya komai aka bashi sanda zai dawo ya karba.
A cikin AKTH ya kaita restaurant ta ci abinci mai rai da motsi, tana ci tana kallon sa ganin shi ko ruwa bai sha ba. Sai ta aje cokalin ta ta tura mishi plate din gaban sa.
“Na koshi Uncle”.
Ya dago daga kan wayar hannun sa cikin damuwa ya dube ta ya ce “babu dadi ne?”
Tayi rau-rau da ido tace “gani nayi kaima baka ci komai ba tun safe” sai yayi murmushi yace “kada ki damu da ni ni namiji ne, kuma sau biyu nake cin abinci a rana, amma yanzu to mu cinye tare”.
Ya debo abincin a spoon ya kai bakin ta, ta rufe ido cikin jin kunya amma sai ta kasa tankwabe wannan nagartacciyar kulawa ta Uncle Saheeb, ta bude bakin ya saka mata.
Sannan shima ya diba ya ci. With one spoon, one plate haka suka cinye abincin. Tun Hasna’u na jin nauyi har ta ware suka ci suka koshi, daidaikun mutanen dake cikin restaurant din sai kallon su suke.

Da suka gama tsaf ya bata tissue ta goge bakin ta yace. “Yanzu zamu je gidan mu kiyi sallah nima in yi, sai mu kama hanyar Kachako”.
Da sauri ta dago ta dubeshi da blue eyes din ta, sannan ta girgiza kai tace “a’ah Uncle, ka nema min masallacin mata inyi a nan”.
Seriously Dr. Saheeb ya ci magani “sabida me bazaki gidan mu ba Hasna'u?”
Ba komai Hasna’u ta tuna a wannan lokacin ba sai Maman sa, wadda ta ce “Allah ya raba ta da mummunar haihuwar zabiya", kuma ta kwashi kafa ta je har gidan ta? Ta gan su again tare da Saheeb? Kamar ya san tunanin da take yi sai y ace “ta shi mu je, in dai Mama ce bata nan ta tafi seminar Abuja. Nusaiba ce kadai a gidan”.
In ta juyawa maganar Uncle Saheeb baya ai ya zama rashin adalci da rashin kunya, ta gama gane Saheeb ko me zai yi zai yi ne for her own benefit bai da wata riba a ciki. Sannan ba zai taba cutar da ita ba.
A hankali yake zura hancin motar zuwa cikin get din gidan wanda ke a sahun farko na unguwar Giginyu. Hasna’u ta daga ido tana kallon gidan su Uncle Saheeb, ko cikin mafarki bata taba ganin kyakkyawan farin gida kamar sa ba, hawan bene ne mai tsayi wanda ya kunshi sassa uku. A lokacin da maigidan ke raye daya nasa ne, daya na Sahib wanda ya kasance da namiji kwaya daya da Allah ya basu sai sassan Haj. Muneera wadda ‘ya’yan ta ke kira Mama, daura da dakin ta dakin auta Nusaiba ne.
Alhaji Bello Wamakko tsohon ma’aikacin SHELL ne. Wanda ya rike manyan mukamai a SHELL Company a lokacin rayuwar sa. Ya auri Muneerah a Kano wadda sabida ita ya bar Wamakko ya dawo Kano don tace bazata iya zaman kauye ba haka bazata iya zama a Sokoto ba. Ko a lokacin da yake raye kowa ya san mama itace mijin shine matar. Mama akwai son nuna isa da son ‘ya’ya kamar agwagwa. Haj. Muneera ‘yar siyasa ce ta gani kashe ni domin har mukamin senator ta yi, a yanzu kuma tana cikin shuwagababnnin jam’iyyar su.
Bayan rasuwar Alhaji Wamakko Mama bata kara yin aure ba sai rainon ‘ya’yan ta biyu, dai dai gwargwado mahaifin su ya bar musu dukiyar data ishe su rayuwa har suka tsaya da kafafun su. Saheeb (Abubakar Wamakko) kamar yadda abokan sa ke kiran sa yayi karatun sa a jami’ar Ahmadu Bello inda ya karanci MBBS (Medicine), a yanzu yana hidimar kasa a matsayin karamin likita karkashin hukumar hidimtawa kasa (NYSC). Shekarunsa 27 cif. Yayinda kanwar sa Nusaiba da suke kira Nusy take da shekaru 18. Zata kammala Unity a bana. Set din su daya da Hasna’u sai dai aji kowa da nasa, kuma babu wata mu’amala data taba hada su bayan ta ranar da suka wulakantata. Amma ta san ta, don jefi-jefi tana ganin ta.
Yayi parking a inda suke adana motocin su cikin wata rumfa mai ban sha’awa sannan ya juya ya dubi Hasna’u wadda ta saki ido da hanci tana kallon komai kamar cikin mafarki. Yanzu wannan muhalli ne da ‘yan adam ke zaune? Shi kansa Saheeb ta jinjina masa yadda ya iya barin wannan gidan ya tafi kauye ya zauna don hidimtawa kasar sa.
“welcome home Hasna, yanzu muje wajen Nusaiba ki sallah, if possible kiyi wanka don kiji karfin jikin ki, sai mu kama hanya, amma lallai ne kan mu isa Kachako sai magriba”.
Hasna’u ba tace komai ba ta fito ya rufe motar, ta wani corridor suka bi sai gasu a wani yalwataccen falo komai dake cikin shi ruwan goro ne da ratsin lemon green. Nusaiba ce a zauna a daya daga cikin luntsuma-luntsuman kujerun falon tana sanye da doguwar riga ta atamfa kanta babu kallabi, gashin kanta mai yawa sosai, tana kallon tashar Bollywood tana shan cornflakes a cikin wani bowl. Sahib ne yayi sallama amma Hasna’u a cikin cikin ta tayi tata sallamar. Zuciyar ta na dar-dar don bata san irin tarbar da zata samu daga Nusaiba ba.
Da sauri ta juyo tana kalonsu suna shigowa. Dogo da doguwa, black and white, cikin uniform din makaranta. A hankali idanun Nusy suka hau kara girma. Wannan zabiyar again? Bata san cewa a fili ta fada ba.

Saheeb yayi kamar bai ji ta ba, ya ce “Nusy ga bakuwa ta ki kaita tayi sallah pls yanzu zamu kama hanyar Kachako, in tayi sallah sai tayi wanka”.
Nusaiba ta zaro ido tana kallon sa da idanu a zazzare. “Yaya Saheeb? A toilet din wa? Kuma da soso da sabulun wa? Zabiya ce fa!”.
Saheeb ya kifa kai a jikin kofa ya rufe idon sa yayin da Hasna’u ta sunkuyar da kan ta. Sai da tace bazata zo ba ya takurawa baiwar Allah. Ya manta Nusy ba hankali. Gata da kyankyami. Shi ba'a bun ya dake ta ba ya firgita Hasna’u ko ya zageta Hasna’u ta ji mummunar kalma ta fito daga bakin sa.
Kawai sai ya kama hannun Hasna’u ya jata zuwa ciki. Dakin Nusaiba ya kaita, ya bude mata toilet yace "shiga kiyi alwallah in kin fito ga darduma. In kika yi sallah sai kiyi wankan mu tafi” idon ta fal hawaye tace “kayi hakuri Uncle bazan yi wanka anan ba innaje gida zan yi” baya so ya tsaya ya ga gangarowar hawayen idon ta dson haka ya fita.
Rasa yadda zata yi tayi amfani da komai dake cikin toilet din tayi, she has never been in a place like this, gashi komai kal-kal tana tsoron kada ta bata wani abun. Da kyar ta yi alwala a tsaye cikin sink ta fito. Ta tada sallah kenan taji muryar Saheeb yana ta yiwa Nusaiba fada. Maganar da ya fada a karshe ita ta kusa sa ta sakin fitsarin da ta makale mata a mara bata yi ba don gudun kada ta batawa Nusaiba toilet.
“Gara ma tun wuri ki sayo majanyi da zanin goyo ki soma shirin goya ZABIYU, domin wannan zabiyar ce uwar ‘ya’ya na insha Allahu!!!
Fitsarin ya kwace ba shiri daga marar Hasna’u ya jika wandon makarantar ta tun daga sama har kasa……….
******











DAGA ZARAR BUNU…… (KARAMAR MAGANA TA ZAMA BABBA)
Saheeb, yana falon su a zaune yana jiran fitowar Hasna’u cikin tsananin bacin rai bayan shigewar Nusaiba dakin Mama. Ya ji shiru-shiru har wajen mintuna talatin ba Hasna’u, sai yayi tunanin ko ta canza shawara tana wankan ne don haka ya cigaba da jiran ta yana yi yana duba agogon hannun sa yana tsaki, don ba karamin bata masa rai Nusaibah ta yi ba har bai san sanda yayi furucin da ya yi ba, kuma an ce Magana Zarar Bunu ce… ta riga ta fita, bashi da ikon mayar da ita.
Tsoron shi Allah tsoron shi kada ta je ta hada shi da Mama, don haka yayi maza ya bi ta dakin Maman, ilai kuwa yana gab da shiga ya ji ta tana waya ya kuma tabbatar ba da kowa bane da Mama ne “…..wannan zabiyar ta Unity ya kawo mana gida har yana neman duka na don nace bazan bata soso na da sabulu na tayi wanka ba har da cewa……”. Saheeb ya yi maza ya doke wayar daga hannun ta ta fadi kasa, ya bi ta ya take da takalmin sa ta wargaje. Nusaiba ta kwalalo ido tace .
“Yaya Saheeb! My phone?”
“An fasa din, bakin ki ma ina gab da fasa shi in kika fada mata abinda kikai niyya. Wallahi Nusaiba ki fita harka ta na ga alama raini ya fara giftawa a tsakanin mu” ta zumburo baki ta sunkuya tana tattare fasashshiyar wayar ta, sai yasa takalmi ya take mata hannu sai da ta saki kara don azaba. Ya ce “wallahi Allah na kara jin zancen zabiya a bakin ki ko a kunnen Mama sai na fyato ki. Ni sa’an ki ne ko abokin wasan ki? Ina ruwan ki da duk wanda zan kawo gidan nan? Gidan ki ne ko na Uba na ne?”
Nusaiba ta soma hawaye. Tace “tun kan ka auri zabiyar kenan? Ranar da ka aure ta ashe raba ni zata yi da kai. You never talk to me in this manner Yaya Saheeb sai akan Zabiya, don haka kasa a ranka wallahi (I hate her with passion) kuma ta yi kadan ta aure ka.
Na ji bazan gayawa Mama abinda ka fada ba amma kasa a ran ka bazan taba son Zabiyar ka ba.
I want my darling brother back to me….this is not my Yaya Saheeb…”. Ta fashe da kuka sosai.
Saheeb sai ya ji jikin sa yayi sanyi, wai meke da Zabiya ne da al’umma ke kyama haka? Ya dauka digon maniyyi ne ya samar da kowanne dan adam kuma shi ya samar da Zabiya? In haka ne kenan ashe duk daya muke (irrespect of skin colour) sai wanda ya fi tsoron Allah? Kanwar sa Nusaiba needs a counseling on disability ba fada duka ba.
Ya zauna a kusa da ita yace “Nusaiba-Nusy, you are my only sister da bani da kamar ta ya kamata ko me na zo da shi ki fahimce ni, ni ban ce auren ta zan yi ba, tausayin ta nake ji. Na yi alkawarin kulawa da rayuwar ta a matsayin ta na marainiya ba uwa ba uba ga nakasa. Ina son ganin rayuwar ta yi kyau kamar ta kowa despite her abnormality.
Kin san yawan ladan dake cikin hakan? Ita din miskiniya ce dake bukatar tausayi da jin kai daga al’umma, amma irin abinda kike yi a kan ta jahilci ne, mai ilmin addini in ya san farkon sa bai san karshen sa ba, kada ki manta kema mace ce, kuma haihuwa zaki yi nan gaba kadan, kin san irin halittar da zaki haifo?
Zaki so al’ummar duniya su taru su juya mata baya don tafito ba irin sauran mutane ba?

Nusaiba yanzu haka Maman ta ta mutu, yau sati biyu ba tare da ta sani ba!”
Ya karasa fada yana kifa kansa a kafadar ta, Nusaiba could not believe it, da taga hawaye cikin idanun sa.
“This is serious!” ta fada a fili, “Yaya Saheeb da gaske son yarinyar nan ka ke yi?”
Kai ya shiga girgizawa har yanzu kan sa a kafadar ta. Yace.
“Nusaiba I don’t know, son ta nake ko ba son ta nake ba. All I know shine zan sadaukar da rayuwa ta don ganin tata ta yi kyau. Zan iya batawa da duk wanda ya tozarta ta” Nusy ta ture shi daga kusa daga ita tace “Har Mama, har ni?”
Ya dago a hankali ya dube ta idanun sa sun kada, a hankali yace “I tried my best to make you understand amma kina komawa wani direction din daban. Now, face your business and leave me”.
“I will not leave you Yaya Saheeb, I must get my brother back, yarinyar nan ba haka ta barka ba”.
“Me kike nufi da ba haka ta bar ni ba?” “It’s possible charming din ka tayi, in ba haka ba meye hadin zabiya da Yaya na Saheeb duk ‘yammatan da ke fadin duniya da irin matar da Allah ya baka mahaifiyar ka ta zaba maka? Sai ka kare a disease?”.
In bai kai zuciyar sa nesa ba zai kare ne da yiwa Nusaibah dan banzan duka, haka take da kafiya da taurin kai kamar Mama, shikuma as softhearted as their father late Alh. Wamakko. Kullum yayi gabas, Nusaiba da Mama sun yi arewa.
Fita yayi ya

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login