Showing 30001 words to 33000 words out of 44439 words
"Iy! Shi ne."
"Har sun dawo ne?"
"Eh, da yake fitar wuri suka yi, zuwa mai Ludayan shi yasa suka dawo da wuri."
Sai yanzu ya fahimci kan me ake zancen.
"Eh, Yaya na dawo, da yake mun fita da wuri."
"To sannu da dawowa."
Ya juya, yana tunanin nacin Yayar tasa.
_Ilu mai amalanke Allah ya tsare hanya_
_Ummyn Yusrah_
[11/23, 3:07 PM] B²: *ABULLE TA MAI UNGUWA*
*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*
_Ummyn Yusrah_
_39_
Ta daɗe sosai a titin, tana tunanin yadda za ta yi ta tsare abin hawa, daga bisani ta sanya hannu ta tsare mai mashin, ganin da ta yi mutane da yawa haka suke yi. Domin a tsayuwar da ta yi mutane da yawa sun tsare kuma sun tafi.
Da ƙyar ta iya tuna sunan tashar da mai mashin ɗin zai kai ta.
Ganin da ya yi mata, wata kala ya sa ya cajeta murtala biyar. Ba ta damu ba, babban burinta kawai ta ganta cikin motar da zai kaita gida.
Suna barin wajen, Hamusu yana yankowa, ya nufi gidan Alhaji Shitu domin aiwatar da aikinsa.
Ya yi sa a kuwa akwai aiki, don haka ajiye tirensa ya yi, ya sunkuya aiki ba tare da ɓata lokaci ba.
****
"Lahhhh! Alƙur'an na yi mantuwa cikin jakata."
Abulle ta faɗa lokacin da suka yi nisa da tafiya.
Bai kulata ba, sai ma wuta da ya ƙara ma mashin ɗin.
"Malam don Allah ka maidani, na yi mantuwa ne." Ta faɗa ganin da ta yi, bai da alamar tsayawa.
Masifa ya hauta da shi,
"Idan na kai ki sai kin ƙaramin kuɗi, haka kuke, tsabar son abin duniya irin na iyayenku, sai suyi ta turoku birni yin aiki, don ku tara musu abin duniya, ko duba irin rayuwar da za ku faɗa ciki basu yi, abin duniyar kawai shi ne burinsu. Ke da gani ma gudowa kika yi daga gidan aikin naki ba a sani ba."
Takaici ne ya kamata, meye nashi a ciki idan ma hasashen nasa haka ne?
"Nawa zan ƙara maka to?" Ta tambayesa don ba ta son jan wani zance.
"Mu je tukunna in ga inda zan ajiyeki, sai mu fara sabon ciniki."
"Wajen da ka ɗaukoni, wajen za ka ajiye ni."
"Yauwa, Ko ke fa! Gara dai ki koma, idan ya so, sai a mai dake gaban iyayeki a mutunce ai ya fi."
"Yau na ga ikon Allah! Ni fa ba aikatau na zo yi ba."
Ta ba shi amsa.
"Ƙarya kike!"
Ya faɗa har yana wani zabura akan mashin ɗin.
"Idan ba aikatau ba, to menene? Ko aure za a yi miki, kika gudu?"
'Sai ka yi kuma, ni ba danginka ba, ka wani daddage. Da zan iya gane unguwar ma sauƙa zan yi in hau wani, don dai kawai kai ka ɗaukoni shi ya sa.' Ta faɗa a zuciyarta.
Har suka isa inda ya ɗauketa, ba ta kuma ce masa komai ba. Haka ya yi ta zuba tamkar injin markaɗe har suka iso wajen da ya ɗauketa.
Yana sauƙeta ta ba shi murtala shida. Mita ya shiga yi, daga bisani ya ja mashin ɗin ya yi gaba.
****
Ɗayyabu ne ya turo ƙofar gidan ya shigo duk jikinsa ba ƙwari.
"Ya ya, ka sameta kuwa?"
Afreen ya tambayesa cikin zaƙuwa.
"Wallahi na duba, har bakin hanya ko mai kama da ita bangani ba."
Shiru ne ya gifta na wani lokaci, kowa saƙar zuci yake.
"Mommy ko za a faɗa ma Daddy?"
Lubna ta faɗa hankalinta a tashe.
Kallonta Mommyn ta yi,
"Kada mu yi gaggawar sanar da shi, yanzu Afreen da Ɗayyabu za su fita su sake dubata ko Allah zai sa a dace."
"Allah yasa a ganta, In Allah ya yadda ba za ta ɓace ba."
"Allah yasa Mommy!" Ta faɗa tana kwantar da kanta a kafaɗar Mommyn
"Ɗayyabu kuma ka ce baka ji fitarta ba?"
Hajiya ta sake tambayarsa.
"Gaskiya banga fitarta ba, ina zaune a nan tun safe, sai kuma banɗaki da na shiga, bayan nan ban je ko ina ba."
Ya bata amsa.
"Ku je da Afreen ku sake dubata to."
Afreen kam ya ma kasa magana, gaba ɗaya jin lamarin yake kamar almara.
Lokacin da take faɗamasa ko ba a sani ba sai ta gudu, ya ɗauka kawai faɗa take, ashe zancen gaskiya ne.
Lallai kowa ya raina mai labari, in kaga mai gudu shi ne.
****
Har ya ɗau hanyar fita daga gari, sai kuma zuciyarsa ta yi ta tunatar masa da rashin adalcin da yake shirin aikatawa.
Gara yakoma ya sake ƙiran Hajiyar, wataƙila ta ɗauka sai ya yi mata bayani.
****
"Kai Afreen! Ka ko ji abinda nake cewa kuwa?"
Mommy ta taɓa shi, kafin ya dawo daga dogon hanyar da zuciyarsa ta ɗauka, na tunani.
"Na'am!"
Kallonsa ta yi,
"Na ce ka ji me na ce kuwa? Ku je da Ɗayyabu ku sake dubo..."
Ƙiran da ya shigo wayarta ne ya yi silar katsewar maganar da take.
Ba yadda ta iya, dole yanzu ta ɗaga wayar tasa.
Sai da ta tattaro duk wata natsuwarta kafin ta ɗaga, gudun kada ya fahimci wani abun daga gareta. A daidai lokacin da suke jimamin ɓatan 'yarsa.
Bayan gaisuwa ba tare da ya jira komai ba, ya fara wassafomata bayani da yadda suka yi da Yayan nasa, da kuma yadda lamarin zai shafi Ahalinsu.
Sosai ta fahimce shi, ta kuma basa haƙuri, ta sanar da shi cewar, za ta dawo yau, yanzu haka ma shiryawa take.
Daɗi ne ya rufesa, nan ya shiga yi mata godiya, da fatan isowarta lafiya ya datse ƙiran, ya nufi cikin gari, yana mai farin ciki.
"Ku je ko? Allah yasa a d..."
Turo ƙofa da shigowar Abulle ne ya yi sanadin tsaida maganar tata, ba tare da ta kai aya ba.
Duk suka juya, ganin Abullen ce ya sa suka ɗunguma gareta, har suna rige-rigen isa gareta.
Wani irin razana da faɗuwar gaba ne ya ziyarceta a lokacin da ta buɗo ƙofar ta yi tozali da mutanen gidan, tsaye cirko-cirko a harabar gidan.
Ba don sun ganta ba, da juyawa za ta yi ta gudu, ta yafe ɗaukar hotunan da ya dawo da ita.
_Ummyn Yusrah_
[11/25, 8:20 AM] B²: *ABULLE TA MAI UNGUWA*
*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*
_Ummyn Yusrah_
_Ashe haka Abulle ta yi kasuwa? Ina tayata murna, ta ce a yi ma duk mai bibiyarta godiya, a kuma ƙara haƙuri da ita na rashin ganinta a kan lokaci._
_Maman Nour, Beauty Queen, Abu Hisham, Yayana. Taku gaisuwa da godiyar daban ce, har kullum Abulle ba za ta taɓa gajiyawa wajen miƙo saƙon godiyarta gareku ba, koda kuwa za ta cinye shafin nan ne, sai dai za ta taƙaita saboda masoyanta. Amma tabbas tana tare da ku a kodayaushe, tana kuma jin daɗin kwament ɗinku. Mun gode ni da ita. Saura in ji ance kalan dangi.😏 sins shis ma kozin sista ehe!_
_40_
Har wajen da take suka ƙaraso, suna tambayarta ina ta je. Ba ta basu amsa ba, sai da Mommy ta sake tambayarta,
"Zainab ina kika je? Duk kin tashi hankalinmu."
Hawayen da ke shirin gangarowa kan ƙuncinta ta goge, ta ce
"Gida zan tafi."
Duk suka kalleta, Afreen ya ce,
"Gida? Kin san hanya ne? Kina da kuɗin mota ne?"
Kai ta gyaɗa, Mommy ta riƙota,
"Zo mu je, yanzu Tukur zai zo ya kaiki dama. Alhaji ya mayar wajen aiki, ki yi sauri ki shirya maza kafin ya iso."
Da murna ta shiga ɗaki, jakar kayanta ta ɗauko, ta dawo falo wajen su Mommy da ke tattaunawa ita da Afreen. Lubna kam sai ido, don ko da Abulle ta dawo ma ba ta tanka mata ba.
Mommy ta kalleta ta ce,
"Yau sai gida ko?"
Dariya ta yi, ta gyaɗa kai.
"Muma goben muna hanya In Sha Allahu, idan an je a gaida mutanen gidan."
"To!" ta ce, don ɗokima ba zai iya barinta ta yi dogon magana ba.
"Afreen duba Tukur ɗin, idan ya iso yazo ya fita da kayan su tafi ka da su yi dare a hanya."
Jiki a sanyaye ya fita, ba jimawa ya dawo,
"Ta fito, ya iso, motar tana bakin get."
Da sauri ta suri jakarta.
Afreen ya ce,
"Ohh! Wannan saurin fa? Kamar kin gaji da mu?"
Dariya ta yi, Mommy ta ba ta saƙon kuɗin da Daddy ya bada, ta yi mata addu'a da fatan alkairi, itama ta yi godiya suka fita.
Suna tsaye a jikin mota ya kalleta ya ce,
"I miss You!"
"Almisyu?" Ta tambayesa,
"Yeah! I really miss you."
Kallon rashin fahimta ta yi masa, ganin hakan ya sa ya fahimci ba ta gane abinda yake nufi ba.
"Cewa na yi, idan kika tafi zanyi kewarki sosai."
Murmushi ta yi,
"To, ka zo mu tafi mana."
"Na so hakan, sai dai ina da uzuri. Amma zamu zo da su Mommy gobe ko jibi aure."
Jin an ambaci aure, ya sa yanayinta ya canza, ƙirjinta ya shiga bugawa. Haka kawai ta ji sam ba ta son auren nan, tana son komawa Mai Ludaya ne don ta ga Hamusu da mutanen cikinta ba don ayi aurenta da Mai Unguwa ba.
Kallonta ya yi cikin kulawa, ya ɗaga mata gira ya ce,
"Ya aka yi? Ko a fasa tafiyar ne?"
Kai ta girgiza ba tare da ta ba shi amsa ba, sai ma hawayen da take gogewa.
"Kukan fa? Barin je in faɗa ma Mommy a fasa tafiyar kawai."
Ya juya zai tafi, da sauri ta riƙo rigarsa ta ce,
"Don Allah Yaya Afreen ka yi haƙuri! Na daina."
Juyowa ya yi,
"To, me ya sa ki kuka?"
"Nima ban sani ba, kawai dai bana jin daɗi ne."
"To, ki daina kuka, ki yi ta karanta Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! Za ki ji daidai."
Kai ta gyaɗa ta ce,
"Na gode."
Hira suka ci gaba da yi, har Tukur ya fito da kaya ya sa a but, ya shiga gaban motar.
Suna sallama da Afreen ne Lubna ta fito, jikinta ya yi sanyi, duk ta ji ba daɗi, haka kawai ta ji ba ta son tafiyar Abulle.
Kusa da su ta iso tana faɗin,
"Da gaske tafiya za ki yi?"
Kallonta ta yi, ta keɓe baki, zuciyarta na faɗin
'Ji wani kinibibi! Ko meye damuwarta da tafiyata?'
A fili kuma ta ce,
"Eh, zan koma ƙauyenmu inda nafi wayo, inda aka san kimata da darajata."
Duk sai ta ji ba daɗi, da kalaman Abullen.
Hannayenta duka biyu ta riƙo, tana murmushi ta ce,
"Ki yi haƙuri."
"Allah ya kara mana duka."
"Me fa?"
"Haƙurin."
Duk suka sa dariya
Lubna ta ce,
"Zamu zo, jibi. Me za a ajiye ma..."
"Tsareta kuka yi ashe? Sai ta rasa mashin ko?"
Mommy ta katse Lubna, daga maganar da take yi lokacin da ta fito.
Juyowa suka yi su duka, za su yi magana, Mommy ta ce,
"Shiga ku tafi, so suke ki rasa mashin ɗin da zai ƙarasa dake ko?"
Jin zancen rasa mashin ya sa ta daka tsalle ta shige cikin motar.
Duk suka sa mata dariya, Afreen ya rufe ƙofar ya leƙo ta taga, ya ce,
"Allah ya kai ku lafiya, sai mun zo."
"Amin."
Ta amsa ya matsa ya rufo ƙofar. Motarsu ta ɗaga. Hannu suke ɗaga mata, itama haka har tana leƙowa ta taga. Sai da motar ta ɓace ma ganinsu kafin suka juya cikin gida zukatansu cike da kewa da rashin jin daɗin tafiyarta .
_Ummyn Yusrah_
[11/25, 2:25 PM] B²: *ABULLE TA MAI UNGUWA*
*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*
_Ummyn Yusrah_
_Tsangayawa kuma ga naku. Tsangayar Marubuta da ke Fuskanr littafi (Facebook). Ina godiya, ga kyautar shafi gareku musamman Umman Maryam. Na gode._
_41_
Koda Malam Ilu ya isa gida bai iya shiga ba, don a cike yake da mata, sai kai kawo ake, ga wasu manyan tukwanen girki da aka ɗaurasu kan murhu.
A zauren gidan ya tsaya, ya tura aka yi ƙiran Inno.
Da sauri ta nufo wajen har tana tuntuɓe, don tunda ya fita hankalinta ke tashe.
"Malam ya ya kuka yi?"
Ta faɗa lokacin da ta iso, idanunta akan fuskarsa.
Kallonta ya yi, lokaci ɗaya duk ta canza, hakan kuma ba zai rasa nasaba da zancen rashin dawowar Abulle da ya yi mata ɗazu ba. Da shima ya tafi da taraddadi.
"Malam an dace kuwa?" Ta sake tambayarsa.
Dogon numfashi ya ja.
"Eh, mun yi magana da Hajiyar tana hanya."
Itama numfashin ta ja, na jin daɗi,
"Alhamdulillah! Yanzu hankali ya kwanta."
"Suma goben za su iso, a gyara musu ɗakin da Muntari yake kwana ko?"
"To, Allah ya kai mu, ita kuma Allah ya dawo da ita lafiya."
"Amin, barin fita."
"To, a dawo lafiya."
Ya fita, itama ta koma bakin aiki.
****
Gudu kawai yake shararawa, domin yana sauƙeta zai juyo, rediyo ne ke ta aiki, Abulle kuma ta afka kogin tunanin yadda za ta je ta sami Hamusunta har barci ya ɗauketa.
"Hajiya Zainabu! Mun iso."
Tukur direba ya faɗa lokacin da suka iso tashar garin Guwal, anan ne ake hawa mashin ɗin da zai kai mutum Mai Ludaya, don mota ba ta shiga.
Miƙa ta yi, fuskarta na bayyanar da farin ciki. Gari ɗaya za ta wuce yanzu ta isa garinsu.
Tafiyar kwana uku, ji take tamkar ta shekara uku. Lallai bahaushe ya yi gaskiya da ya ce,
'Kowa ya bar gida, gida ya barshi.'
Tana tsaye ya gama fito mata da kayanta, Mai mashin ya tafi ya ƙira mata, ita kuma ta tafi kanti sayen oyoyo ma yara da kuɗin da Afreen ya ba ta, idan ta ga abu a hanya ta saya. Biredi manya ta saya guda biyu, sai bisko da minti mai kan ɓarawo (Lollipop). Ta samu, har mai mashin ya iso, sun tsadance da Tukur ya biyasa. Mutum biyu suke ɗauka a mashin ɗaya, sai dai yau ba zai yiwu ba domin kayanta ya tare wajen.
Jakar kayanta aka sa a gaba, sai babban buhun kayan kicin ɗin da Mommy ta ba ta aka ɗaureshi tamau a baya, ita kuma ta hau tsakiya, ledar oyoyonta na hannunta.
Godiya ta yi ma Tukur sosai, ta kuma ba shi sautu wajen Ɗayyabu ya taho mata da kayan jerenta da ta ɓoye, wanda ɗoki ya sa ta manta da su idan za su taho aure. Addu'ar Allah ya kare hanya suka yi ma juna.
Sai da ya tabbatar da tafiyarsu kafin shima ya shiga mota ya juya lokacin ƙarfe biyar saura.
****
Yau aiki sosai Hamusu ya yi, bai sami Alhajin ba sai Hajiya. Har wankin labulaye ya yi, bayan share harabar gidan da kuma zubar da shara. Ya ci ya sha ya yi hani'an. Nan ta ce ya riƙa zuwa kullum yana yin aiki, a wata ana biyansa ya fi tallar da ya ke yi.
Ya ji daɗi sosai, sai dai ya sanar mata gobe zai je gida ya duba mahaifiyarsa zai yi kwana biyu, idan ya dawo sai ya fara zuwa.
Da zai tafi, ta yi masa sha tara ta arziƙi ta kuma yi masa kyakkyawar sallama ya tafi yana farin ciki, yadda abin ya zo masa da sauƙi.
Duk gajiyar da ya ke ji take ta washe. Ga kuɗin moto harda kyautar kaya ya kai ma mutanen ƙauye.
Sosai ya jinjina karamcin mutanen gidan, ya kuma yi alƙawarin yana zuwa kwana biyu zai dawo don bayason a yi bikin abar ƙaunarsa yana garin.
A haka ya isa ɗakinsu ya hau shirin tafiya.
****
Tafiya kawai suke, ba ka jin komai sai ƙaran mashin, da kuma karo da suke yi da duwatsu.
"Kai! Hanyar nan tamu sam ba kyau. Kodayaushe cikin sayen sabuwar taya da gyaran babur muke."
Idirisu mai mashin ya faɗa lokacin da suka shige cikin yashi.
"Hakan ma ai kamar da sauƙi ko?"
Ta tambaya, ba tare da jiran amsa ba ta ɗora.
"Na ga lokacin damina wajen ya fi haka lalacewa."
"Iy! Da sauƙi kam za a ce, mun maƙale fa ina ga sai kin sauƙa mun tura."
Sauka ta yi, suka hau turi.
Da ƙyar ya fita, ga shi hanyar yau kamar an yi ruwa an ɗauke, ba mutane ko kaɗan, duk da wajen ba ya rabo da masu shiga ko fita daga ƙauyukansu. Amma yau shiru.
Hawa ta yi suka ci-gaba da tafiya, wani sanyi ta ji ya ziyarci zuciyarta lokacin da ta hango Tudun mun tsira.
Wajen wani ƙaton tudu ne, da gangara shi ya sa ake ƙira da Tudun mun tsira.
Ba ko wani mai abin hawa ke iya hayewa da mutum ba, masu tsoro idan sun zo wajen sauƙa suke, wasu kuma haka suke hayewa a dari. Kariyar Ubangiji kawai ke kai mutane ƙasa lafiya.
Yanzu haka an fara aikin rage tudun, saboda yawan hatsarin da ke afkuwa a wajen, aiki ne na ƙarfi da ƙarfe da mutanen ƙauyukan ke yi, don rage afkuwar hatsarurrukan.
Suna isowa Idirisu ya ƙure ma mashin ɗin gudu, a ɗari ya haura.
Haurawar ta sa ta yi daidai da cakar wani dutse, take duk suka yi sama, mashin da kayan da ke ɗaure suka hantsila can gefe, hakama Idirisu da jakar kayan Abulle.
Ledan oyoyon Abulle da ya yi sama, shima ya watse a hankali abinda ke ciki suke dawowa ƙasa.
Abulle kuma da ta yi sama, ta faɗo ƙasa yayin da kanta ya cakku da wani tsinin dutse ya nitse can.
_Ummyn Yusrah_
[11/26, 7:53 AM] B²: *ABULLE TA MAI UNGUWA*
*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*
_Ummyn Yusrah_
_42_
Ihu ta ƙwala mai karfi sakamakon azaba, raɗaɗi, da zafin da ya ziyarceta. A razane wasu tsuntsaye saman wata ƙatuwar bishaya suka tashi Furrrr! Dalilin tsorata da suka yi da ƙarar da ta yi.
Lokaci guda jikinta ya hau karkarwa, numfashinta ya shiga kaiwa da komowa, zuwa wani lokaci ya tsaya cak!
Idirisu kam,tunda ya wurgu ya faɗi bai san meke faruwa ba.
Tsawon mintuna kusan ishirin ba wanda ya ɓullo ta wajen.
Mudi mai Jaki ne ya taho a kan keke, yana tafe yana waƙe, ya taho daga cikin garin Mai Ludaya, zai je ƙauyen da ke gaba da su.
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un!"
Shine kalmar da yake ta maimaita lokacin da ya yi ido biyu da abinda ya faru.
Da sauri ya sauƙo daga kan keken nasa, ya ƙarasa garesu, duk cikinsu babu mai motsi. Da sauri ya juya ya hau kan keken nasa ya koma cikin gari, bakinsa na maimaita 'Innalillahi wa innalillahir raji'un!'
Gudu kawai yake ba ƙaƙƙautawa, yana isa cikin gari, kai tsaye gidan Mai Unguwarsu ya nufa.
Wurgi ya yi da keken ya rugo da gudu, ya gurfana a gaban Mai Unguwa, har lokacin bakinsa bai daina furta kalmar nan ba.
Jiki na rawa ya ce,
"Rankashidaɗe! Akwai matsala. Wallahi akwai matsala."
Duk mutanen dake wajen kallonsa suke.
Cikin muryar tsufa da sarauta Mai Unguwa ya ce,
"Subhanallahi! Wace irin matsala kuma Mudi?"
"Haɗari rankashidaɗe! Haɗari wallahi a daidai tudun mun tsira. Lamarin babu kyan gani, gaba ɗayansu babu mai numfashi."
Duk wajen ya dau salati, Mai Unguwa ne ya ba da umurnin a samo amalanke a kwashi mutanen a kaisu asibitin dake garin don duba halin da suke ciki.
Malam Ilu da suka taho da abokinsa yi ma Mai Unguwa godiyar kayan abinci da aka kawo musu, ya miƙe cikin sauri don ɗauko ta sa amalanken.
Haka kawai yake jin mummunar faɗuwar gaba, tunaninsa Allah ya sa Abulle su wuce lafiya.
****
Hamusu da tunda ya gama shirya kayansa ya miƙe akan tabarma.
Lokaci guda, gabansa ya tsananta bugawa, sosai ya ji jikinsa ya mutu, tunanin garinsu ya faɗo masa a rai.
Tabbas akwai abinda ke faruwa. Sai dai bai san