Showing 6001 words to 9000 words out of 44812 words
kanwar gaishina ta fad'ama sauran dangisu su zo a hadu a zauna ayi zaman makokin ana gidan su ummeen tunda Bature da Hassana nason temakonsu itama tana so.
Adamsy ya hana ta fad'ama Husaina dan ka hankalinta ya tashi baya kusa bare ya lallabata.
Haka kuwa akayi Ummee ta turo masa agali da gumar akayi komai aka gama aka basu gawar suka nufi gida, lokacin Ummee har tasa an kirawo yan tsarekun yan uwan su Ma'azzara wanda basu damu da rayuwarsu ba amma harda kukan munafurci kafin ma a iso da gawar, Hussaina kuwa tana can tana barcinta cikin nutsuwa dan ummee bata so ta tajima har sai na binne gaishina.
Ba'adau wani dogon lokaci ba adamcy suka k'araso da gawar gaishina aka shirya gawar aka tafi da ita gidanta na gaskiya.
Usaina ba ita ta tashi ba sai bayan da aka kai gashina yenuwan nasu ma sun soma tafiya , dama su mutuwar bawani damunsu tayi ba dan koh muazzara basu tambaya ba sunsha koke kokensu na karya da nuna tsantsar damuwar .
Daki Adamcy ya wuce dan dubo usaina ya tadda ba kowa a dakin karan ruwan dake fito a setin toilet ya tabbatar mai da usaina na ciki,Zama yayi bakin gado yana jiran fitowarta yashiga kololuwar tunanin Muazzara shi Yanzu ya zeyi da amarta da akabashi Yanzu matarnan tamishi adalci data hadashi da amarna mutum tayaya ze rike amarta bayan ko kadan bason yarinyar yake ba jininshi kwata kwata be hadu da yarinyar ba abunda yakuma samai tsanar yarinyar haukar datake mai tana kiranshi da uncle shi sam besan yazeyi ba ,
Yayi nisa cikin tunaninshi Hussaina ta fito daga wankan datake zaune saman gado ta ganshi yayi jugum kallo daya za'amai asan hankalinshi baya kusa dashi ita sam batasan ma da shigowarshi ba
Murmushi tayi ta k'arasa kusa dashi ta dafo kafadan tace" Mon trèsor meya faru yaushe ka shigo ne, k'okarin seta kanshi yayi da boye damuwarsa ya janyota jikinshi ta zauna kan cinyarshi yace "Ma babe shigowa kenan ,tashi muje na shirya ki Chak yadauke ya dire gaban mirrow yashiga shafa mata mai tare da shiryata cikin salon so da kaunar junaa...
Ta cikin mirror din ta kalleshi tace" Mon trèsor ya jikin Gashinan yaushe za'a mata aikin ne matar nan ba karamin tausayinta nakeji ba kaga irin halin datake ciki da jiya bamu taimaka ba bansan halin da zata shigaba zuwa yau kilama ta iya rasa ranta,
Hankalinshi ne yakuma tashi yasan Husaina batasan da mutuwar gashina ba taya ze Sanar mata da gashina ta mutu yasan halin Husaina da rikicewa akan abunda bekai yakawo ba bare kuma wannan da suka shiga ranta daga haduwar farko.
Maganar Husaina takoma da Adamcy daga duniyar Nazarin daya shiga ,
*💖BANI DA GATA💖*
*MALLAKAR*
👇🏻
```Real Ladingo Sweet Baby```
*Bismillahir Rahamanir Rahim*
*Chapter 4*
.... Suna shiga gun Ummee Hussaina ta zare hannunta ana Adamcy, ta nufi gun Ummee ta zauna kusanta cike da jin kunya tace "Ummeena ina kwana ya hakurin mu Nini ta tafi ta barmu Allah ya jiqanta da rahamarsa, Allah ya kai haske da ni'ima kabarinta.." janyota jikinta Ummee tayi tana shafa kanta tace "Amin ya Allah Husainata, ya kuma muka ji da ƙarin hakurin wannan baiwar Allah itama?" Da sauri ta dago kai tana kallon Ummee kafin ta juya a hankali ta kalli Adamcy dake tsaye, a bakin ƙofa hannayen sa zube a cikin aljihunsa ya zubo musu idanunsa zuciyarsa cike da fargaban damuwar da zata shiga idan aka fada mata mutuwar Gaishina.
Tana kallon Ummee fuskarta cike da alamar tambaya tace "Wace ce kuma ta rasu Ummee?" Juyawa Adamcy yayi ya dauke kansa gefe, domin baya son ya kalleta yaga irin damuwar da zata shiga saboda ba zai iya jurewa ba, kara kamota jikinta Ummee tayi a tausashe tace "Wannan baiwar Allahn mara lafiya itama Allah ya karbi abarsa..” a razane ta juya tana kallon Adamcy daya dauke kansa da sauri yayi kamar bai ji abinda Ummeen ta fada mata ba, tana girgiza kanta ta fada jikin Ummee ta kankameta hade da fashewa da wani irin kuka mai karfi da taba zuciyar duk wani mai sauraro, yayinda a gefe guda kuma ga tsantsar tausayin Ma'azzara da damuwar irin halin da zata iya shiga idan taji labarin mutuwar kakarta mafi soyuwa agareta ya risketa, saboda ta lura akwai tsantsar kauna da soyayya mai ƙarfin gaske a tsakaninsu ita da kakar tata.
Zuciyar Adamcy na tsananin suya da mugun radadin kukan da take yi, ya taka da sauri ya isa gabanta ya zauna a gefenta ya jawota jikinsa ya rungumeta tsam a kirjinsa yana lallashinta, Ummee na shafa kanta da bayanta itama tana lallabata da bata baki, sai da ƙyar da sudin goshi sannan suka samu tayi shiru bayan taci kukanta sosai ta gode Allah, a hankali ta share hawayenta tana sauke ajiyar zuciya tana jan numfashi ta kara lafewa a jikinsa, dan sosai taji mutuwar Gaishina ta taba zuciyarta ga wani tsantsar tausayin Ma'azzara dake manne a zuciyarta. Ganin tayi shiru yasa ya dan janyeta a jikinsa ta koma jikin Ummee ta kara lafewa ta rumtse idonta tana jin wani iri a jikinta, ya mike a hankali ya fice daga ɗakin ya nufi kofar gida wajen zaman makoki ya zauna gurinsu Harun da Gumar da Hashim suka kara yiwa juna ta'aziyya sannan suka ci gaba da karbar gaisuwa gurin jama'a da suke zuwan musu, daurewa kawai Adamcy yake yi, amma gaba ki daya hankalinsa da tunaninsa duk sun tafi, tunanin yanda zai iya rike amanar da akabar masa kawai yake yi, wanda yake ji a ransa da zuciyarsa kamar an daura masa nauyin duniya ne da abinda ke cikinta duka a kansa.
Haka yana nan zaune a daddafe har aka kira sallar Azuhur a masallaci, suka tashi sukayi, sannan ya shiga cikin gida yayi wanka ya canza kaya ya fesa turarukansa masu tsananin ƙamshi da daɗi, nan Husaina ta kafa masa rigimar ba zai fita ba ta hanasa sakat sai da ya kamota ya lallasheta yayi mata romance ya lallabata har tayi bacci sannan ya kwantar da ita ya sakar mata kiss a kumatu da goshinta ya juya ya fice daga ɗ'akin ya koma kofar gida rumfar zaman makoki.
Sai bayan La'asar sannan ya sake komawa cikin gidan ya yiwa Husaina wanka yasa ta daura alwala suka fito tayi sallah, ya shiryata tsab tayi kyau sosai shima ya sake kayan jikinsa suka nufi asibiti gurin Ma'azzara.
Suna isa direct ɗakin da aka kwantar da ita suka nufa, lokacin da suka shiga ta farka likita na tsaye a kanta tanata fizge-fizge tana zuba ihu tana kiran sunan Uncle da Gaishina, da gudu Husaina ta nufeta ta kamota jikinta tana ƙoƙarin lallashinta ta sake fizgewa taƙi tsayawa ta ci gaba da fizge-fizgen da takeyi tana kiran sunan Gaishina da Uncle tana kuka, cike da damuwa Husaina ta kara kamota jikinta tana lallashinta ta sake zamewa taƙi saurarawa, a marairaice Husaina ta ɗago tana kallon likita cikin tsantsar damuwa tace "Dr dan Allah kayi wani abu akai mana..?" Likita yana kallonta da damuwa a fuskarsa yace "Tun ɗazu faman da muke tayi da ita kenan tun da ta tashi amma taki tsayawa... sai kiran Uncle take." Ya faɗ'a yana juyawa ya kalli Adamcy yace "Kazo dan Allah kayi mata magana zata tsaya.."
Wani irin haushi da tsantsar takaici Adamcy yaji a zuciyarsa, shifa baya son sakakkun yara shagwaɓaɓɓu dan yaga alamar yarinyar kuma ta fiye sangarta da shagwaɓa da yawa ya buɗe baki zai mata tsawa kenan ya tuna da amanar da Gaishina ta kamo hannunsa ta damƙa masa, take sai jikinsa yay sanyi ya matsa a hankali kusa dasu ya zauna a bakin gadon, ya karb'eta a hannun Husaina ya riƙe hannunta a hankali ya ɗan dora kanta a kafad'arsa cikin lallashi da kwantar da murya yana bubbuga bayanta yace "To yi shiru ga Uncle d'in naki yazo... Mene ne.?" Jin muryar Adamcy da tayi yasa ta tsaida kukan nata cak tana sauke ajiyar zuciya ta kara nitsa kanta a ƙirjinsa tana shasshekar kuka haɗe da sauke numfashi, cike da ƙyanƙyani yasa hannu ya tattare mata gashin kanta mai tarin yawa da santsi ga tsayi ya daure mata, sannan ya gyara mata zaman hijabin jikinta, Husaina sai daɗi take ji tana sakin murmushi tace "Mon trèsor ko kai fa. Wallahi naji daɗin hakan da kayi, ka lallabata." Ta faɗa tana jin daɗi sosai a ranta.
Ma'azzara kuwa tunda dai taji muryar Adamcy a kusa da ita hankalinta ya kwanta tai luf ta kara lafewa sosai a jikinsa, shi kuma a hankali cikin ƙyanƙyami yake shafa kanta mai laushi a zuciyarsa yana jin tsananin ƙyamar taɓa jikinta da yake yi sosai yake jin ba daɗi a ransa, amma ya zama dole ne ya kula da ita dan babu yanda zaiyi saboda ta zama amanarsa.
Ganin ta natsu tayi shiru yasa Dr ya sake dubata yaga bata da wata matsala, Adamcy ya ɗago yana kallon Dr yace "Ko zaka iya sallamar mu idan babu wata matsala?" Jinjina kansa Dr yayi yace "Eh dama kaman abin ya firgita ta ne tayi doguwar suma, amma bata da wata matsala zan iya sallamarku." A hankali Adamcy ya janyeta a jikinsa ya matsa gefe Hussaina ta matso ta rungumeta, shiru tayi tana bin Adamcy da wani irin kallo kamar zata lashesa, dan ita babban burinta kawai ta kasance tare dashi, har wani farin ciki take ji yana ratsa zuciyarta wata natsuwa na saukar mata a gangar jikinta, sai a lokacin ta tuna da mutuwar Gaishina abin ya dawo mata, tana jin mugun ciwo da zafi mai haɗe da raɗaɗin baƙin ciki a zuciyarta ta sake rushewa da kuka ta fizge jikinta daga jikin Hussaina tana kuka haɗe da ihu tana fadin "Gaishinata...Wayyo Allah Gaishinata.... Wayyoooooo Gaishina ta.." ta sakko da mugun gudu ta rirrike Adamcy a kiɗime tana "Uncle ka gaya min da gaske ne ta rasu..?" Wani iri yaji a zuciyarsa a hankali ya kamota ya riketa yana kallon fuskarta cikin sanyin muryarsa da lallashi yace "Kiyi hakuri, dan rasuwa ta rasu, amma insha Allahu zan riƙe ki amana kamar yanda Gaishina ta bamu amanarki nida Hussaina..." Ya fad'a yana kamo Hussaina jikinsa suka haɗu su uku suka rungume juna, Ma'azzara tana kuka Husaina ma na kuka, da ƙyar Adamcy ya samu ya lallaɓasu, likita ya sallamesu, yana riƙe da hannun Husaina, Husaina na riƙe da hannun Ma'azzara suka fita, suka shiga mota suka nufi gida.
Ma'azzara na zaune a baya Adamcy da Hussaina na gaba yana riƙe da hannunta ɗaya yana tuƙi da hannu ɗaya, yayinda itama Husaina har lokacin take riƙe da hannun Ma'azzara dake ta rasgar kuka tana kiran sunan Gaishina, a haka har suka ƙaraso gida, Husaina ta kaita part d'insu ta had'a mata ruwan wanka ta kaita toilet tayi wanka ta wanke mata gashinta ta gyara mata jiki, ta dauko mata kaya a cikin nata ta bata ta saka, suka ki shigarta sai da ƙyar saboda sun mata kaɗan sosai, domin ita Husaina bata da jiki Ma'azzara ta fita ƙiba, duk surarta ta fito 'yan ƙananun matasan nonuwanta duk suka fito, ta gyarata sosai ta shiryata tsaf ta bata abinci taci sosai ta ƙoshi sannan ta kama hannunta suka nufi part d'in Ummee.
Suna zuwa Ummee ta riƙota ta rungumeta a jikinta tana jin tsananin tausayin Ma'azzara a zuciyarta, ta fara lallashinta cike da nuna tsantsar kulawa tana fada mata daɗaɗan kalamai, kan tayi haƙuri ta yiwa Gaishina addu'a itace kaɗai abinda take bukata daga gareta, tana gyaɗa kanta wasu hawaye na sake zirarowa kan fuskarta.
Da misalin karfe tara na dare su Hussaina na zaune a parlo da yan tsirarun mutane Adamcy ne ya shigo waya manne a kunnansa yana sakin murmushi, ya magana cikin siririyar murya sa tamkar baya son maganar ya zauna kusan Ummee, ya dora kansa a kafadarta cikin harshen fransanci ya ce "ma tant ga Ummee kuyi magana". Murmushi ummee tayi ta gano Rukaiyya ce mahaifiyar Hussaina.
Amsa tayi ta kara a kunnanta tana sakin murmushi. Ma'azzara kuwa tana jikin Hussaina tana bata labari mai dadi, amma Ma'azzara tayi nisa aduniya kallon Adamcy ko kiftawa bata yi Adamcy ya kai kallonsa gefen su Hussaini karaf suka hada idanu da Ma'azzara ta kafesa da idanu.
Kansa ya dauke gefe k'asan makoshi ya furta "Wannan inaga mayya ce tirr ina dalili". Ya fad'a yana kai kallonsa kan Hussaina wace ta dukufa tana ma Ma'azzara hira.
Haushi ya ciki Adamcy kenan bata ta tashi ma mik'ewa yayi tsaye, ya zura hannunsa aljihu ya ce"mon Bebe zo na ganki". Hussiana sai lokacin ta d'ago ta kalli Adamcy taga fuskarsa murtik ba walwala da sauri ta janye Ma'azzara ta mik'e tsaye ta nufi gunsa tana langwab'ar da kanta. Adamcy ya nufi kofar fita tabi bayansa da gudu Adamcy yana dab da fita Salamatu ta shigo da sallama, Adamcy ya amsa yana kallonta ganin suna yar kama da Ma'azzara tsaye tayi daga inda take, ta kalli Adamcy tace"Nazo na tafi da Ma'azzara ne ni kanwar Babanta ce uban mu daya dashi bazamu barta cikin daula ba taje ta manta da butar ubangaji, dan haka ke taso mu tafi ta nufi gurin Ma'azzara tana zaro mata idanu.
Ma'azzara a mugun tsorace ta mik'e jikinta na b'ari da gudu tayi kan Adamcy tana kiransa "Uncle ka ceceni karka bari su tafi dani" Adamcy ya warema Ma'azzara hannunsa ta kara so ta fada jikinsa tana kuka, jikinta sai kyarrrrma yake dan tana mugun tsoron Salamatu.
Adamcy ya maida hannunsa ya zagaye bayanta ya watsama Salamatu mugun kallo wanda yan hanjinta saida suka kada, amma saboda tsabar dauriya da mugunta da take cinta, dan yau ta tsara naunin azabar da zata mata ta ce" Haliru ku shigo a yita ta kare wlh sai sun bamu yarmu haka kawai salon a sata ta manta da Ubangijinta wlh sai kun bamu yarmu saboda.... tsawar da Adamcy ya mata ne, yasa sauran maganar ta mak'ale mata..................✍🏻
Real Ladingo ce😅
*Na kudi ne Kan fara shi Nera 200 kacal +22792589446/ +22796515805.*
Daga...✍🏻ummu Fareesa💋💋💋
*💖BANI DA GATA💖*
*MALLAKAR*
👇🏻
```Real Ladingo Sweet Baby```
*Bismillahir Rahamanir Rahim*
*Chapter 5*
.....Cike da tsoro ta matsa baya tana zare idanu. Haliru ya shigo yana Washe baki ya ce"Yauwa ke taho mu tafi gida, wannan ai rashin tarbiya ne ki shiga jikin samgameman kato haka subahanallahi, dole zan aura miki Mati mai wanki kya karasa girma a gidansa". Haliru ya fad'a yana nufo gun Adamcy. Ummee ta mik'e ta bisu da kallo cike da mamaki, haka sauran jama'ar ma kallon ikon Allah suke. Cikin kakausar murya Adamcy ya ce " Wlh kafin na kirga uku ku fice daga gidanan idan ba haka ba zakuyi nadamar zuwanku waye? zai baku ita, ba ta san daku ba tabani dan haka nine zan rike amanar Allah." Ya fad'a a tsawace. Wanda saida Ma'azzara ta tsorata tana k'ok'arin fizgewa, jikinta yana rawa. Adamcy ya janyeta jikinsa ya riko hannunta, ya damfaro su Salamatu yana cewa" d'aya biyu" yana kara damke hannun Ma'azzara. Ai yana cewa"uKu" Salamatu da Haliru a guje suka fice suna rigai-rigai, Salamatu tana cewa"Wlh da safe gidan megari zan Kai karan ku". Ta idar da maganar tana kara gudu, Haliru tuni ya fece.
Suna fita basu tsaya ba a guje suka bar layin Salamatu tana cewa Haliru" Wlh gobe sai mun kaisu gidan megari qara, bazamu barsu shegu masu zubin turawa gobe sai mun amso diyarm, shegiya ita kuwa har ta samu guri wai bazata zo gun mu ba". Haliru bai kulata gudu kawai suke dan duk wannan hira cikin gudu Salmatu take sai shasheka take, haka har sukayi nisa kafin su tsaya su fara tafiya.
Hussaina ta matso kusan Adamcy ta marerece dan ta tsani ta ganshi cikin damuwa da b'acin rai, tace"Yayana kayi hakuri pls banason abin ya dameka, baza'a rabamu da ita ba ina sonta" Ma'azzara ta kalli Adamcy yanda ransa yake b'ace sai kawai ta koma jikinsa ta kwantar da kanta kirjinsa ta fashe da kuka. Adamcy ya feso da isaka mai zafi ya Ja siririn tsaki, ya d'agota ya kura mata idanu yace"To meye? Kuma dallah malama ki mana shiru" Ya fadi yana buga bayanta. Ya kalli Hussaina, ya ce "Mon bebeta bazan damu ba wlh na tsani damuwa da takura....." Ummee ce ta matso ta ce" Bature ka rage zafin zuciya yarinyar amana take wajanka, kabar mata tsawa su kuma muna jiran karar da zasuyi goben, Ma'azzara zo taho muje ki kwanta". Ma'azzara tanajin haka da saurin ta janye jikinta daga na Adamcy ta nufi gun Ummee Ummee ta kamata tace" Kiyi shiru bari kukan babu wanda zai rabaki da uncle dinki kinji" Ma'azzara ta d'aga kanta. Adiya ce ta shigo tana waya sai banbami take tana kallon Ma'azzara ta ce"Wow ina kuka sami ba'akar yarinya kyakyawa..... Tsawar da Adamcy ya mata ne yasa da gudu tayi bayan Ummee ta lab'e, tana cewa "Ummeena ki rabani da wannan Nasaran ya fiye takura...." da sauri Ummee ta juyo ta rufe mata baki ta ce"Ke ban son fitina salon ya dokarmun ke ko". Adamcy ko kallo basu lasheshi ba ya d'ana mata tarko dan kafin su tafi sai yaci ubanta. Hussaina ta matsa kusan Adamcy tana marerece fuska ta ce" Yayana To kabar fushin yi hakuri" Adamcy ya lumshe idanunsa ya bude, ya fesar da iskar bakinsa waje ya kurama Hussaina lumsassun idanunsa masu mutikar hargitsa mata lisafi tun yarinta. Ya d'aga mata gira ya kama hannunta suka fice daga parlon. Adiya ta murguda baki ta ce"Allah Ummee ina ragama Bature ne saboda ke uwaramu, badan haka ba hummm" Hauwa'u da fitowarta Kenan ta dakawa Adiya tsawa ta ce"Ke Adiya wlh zaki ci k'aniyarki idan Adamu ya kamaki yar iska yarinya kawai". Ummee tabi bayansu Adamcy da kallo tana girgiza kanta ta saki murmushi kaunar yaran tana sakata nishadi. Adamcy ya burgeta da bai kula Adiyar ba, sai dai tasan tarko yake d'ana mata. ummee ta kalli Ma'azzara wacce ta bisu da idanu tana kallon Adamcy har zaro idanun take, saboda yadda yake takunsa cikin kuzari.
Adiya batayi magana ba ta zumburo baki gaba ta nufi bedroom.
Ummee ta ja hannun Ma'azzara suka shiga bedroom ta kaita toilet ta hada