Showing 3001 words to 6000 words out of 17004 words

Chapter 2 - SAKAR ZARE

Start ads

11 Aug 2025

106

Middle Ads

ai abin da wuya ma de yi copy copy.." "dama ai an saba"
nakai mata duka "An saba me? Allah ke ko? Ki kiyayeni".
Har kusan la'asar sannan mukai wanka domin fita yawon zaga gari gun buWe ido, a gurguje muka shirya muka fito driver ne zai kaimu..munje gurare da yawa na yawon buWe ido.
Sati muka jera kusan kullum sai mun fita muje nan muje can, na ko sha kallo munje gurare da yawa. Yauma kamar kullum mun dawo daga gidan Zoo, a gajiye muka ?arasa gida, umma muka tarar a parlour ta mana sannu da zuwa muka amsa da zama,
ta ce "amma dai daga Yau Kun gama fita ko?" Na ce "eh umma Dan ko ba'a gama ba ni nama gama wlh saboda bakiji yadda jikina ya gajiba yakemin ciwo" tace "ai dole wannan sintiri haka"? Walida ta dube ni "au mun fasa zuwa meseum Win?" Na ce "umm "Amma kinsan ba mi haka dake ba ko? Na ce "Allah walida baki San yadda nake ji baneshiyasa" ta ce "ai shi kenan",umma ta ce "ya fi muku dai ahto."
Da dare muna zaune da ita kafin mu kwanta take cewa "nikam Baby ban tambyeki ba Ina sir Ahmad?" Na ce
"hmm Allah sarki sir yana nan... wlh nasan yana nan ma ?ila fishi ya ke da ni don ban faWa masa zanyi tafiya ba" ta ce "aikam baki kyauta ba to saboda me?" Nace "wlh bkm kawai dan kar ya damu" "ai hakan ma sai ya pi damuwa in ya shafa ya ji bakya nan..
Allah baby Sir Winki yana birgeni wani salihi da shi ba ruwansa wai ko yana magana?" na Salla mata hararan wasa "aa bayayi kece me yi," tai dariya "aa maida wu?ar," "umm irin wa'innan ustazan masu shuru? sunfi kowwa ganewa..."
"wlh Baby mutuminnan yanada kirki ga shurushuru" nace "aikam Haka yake indai Sir ne bashi da damuwa," haka mukai ta hira har dare yai muka kwanta.

Kwanci ta shi ba wuya yau satina 2 cif da zuwa Kaduna yaune kuma nake Shirin komawa inda na fi kauri wato garinmu tun jiya na gama parking kayana na haWa don tafiyar wuri nake so na yi tunda ba nan bane tsakanin kaduna da kano akwai Nisa Kam Allah ma ya soni Abba yahaWi na da drivernsa ya kaini.

Tunda muka tashi na ganta wani sukuku duk ta damu wai bata so na tafi, na gama shirina tsaf! muka fito dasu zasumin rakiya bakin gate har yy Mubarak shi ma ze fita yace "Baby Allah ya kiyaye hanya ki gaida su Baa" na ce "to" umma ma "kigaeda Amma sai munyi waya munji ya kikaxo gida" su fadeel ma "yy baby a gaida su yy Al'ameen" nace "xasuji."
Abba harda bani kuWi nace to angode, Na kalleta "kowwa yana min sallama Banda ke my Waleeda" tace "Allah banaso ki tafi" nace "to ya zasu in anyi hutu ai zan dawo" tace "Allah ya kaiku lpy" na amsa da "Ameen" baba habu ma mukai sallama driver yaja muka wuce suna Wagamin hannu nima haka harda Wan hawayena.......

Na Isa gida lafiya baba idi driver ya shigarmin da kayana suka gaisa da Amma lokacin Baa baya nan, yai mana sallama ya juya. Na shiga da murna ta Amma na min sannu da zuwa na amsa da zama kan tabarma kusa da Ita ina tuSe hijabi,
"Ammata sannu da gida" "kece da sannu ummiena kunsha hanya" na ce "wlh kam ina yini mun sameku lpy?" "tace lpy ya kika baro iyayen naki da ?an uwa nace duk lpy.. tace "to madalla ynx ki je ki watsa ruwa ki sallah kizo ga abinci" na ce "to," da mi?ewa na shiga Waki.
[9/9, 17:30] E*O*W: SA?AR ZARE

BY
NA'EEMARH SADAU=؟?

(3E 'DDG 'D1-EF 'D1-JE
FREE BOOK=???

ELEGANT ONLINE WRITERs
'?


Page 3? __4?

&&& &&& &yu Al'mustapa aka fiddo tsaraba kowwa aka bashi nasa Baa yace "mamana ya kika baro su? in ce dai kowwa lafiya?" na ce "duk suna gaisheku da kyau," Amma ta ce "?an uwanki Kam sunzo da bakya nan nace "yy Aisha? tace "eh" na ce "ayya kinga Amma ban je ba sukam har sunzo gashi ba na nan wlh naso mun haWu rabona da zuwa fa kusan shekara," ta ce "to ya za ai Kinga hutun ku ma ya ?are ga shi zaku fara jarrabawa sai dai gaba" na ce "Allah ya kaimu don nayi missing Yy Indo,(haka nake tsokanarta don kusan sa'a ta ce tsiranmu shekara Biyu tsakani in na gaya mata kam mi ta faWa don bata so)." Al'mustapha ya ce "Yy Baby Yy Ahmad yana ta tambayata ke na ce masa bakya nan kinyi tafiya..."
"Eh kam wlh ya aiko ba kya nan ince ko baki faWa masa zaki tafiya ba?" Amma ta faWa na ce "wlh kam ba mi zancen da shi ba ta ce "ahto baki kyauta ba kam ba haka ake ba ai nace "amma mantawa nai fa.... muna haka ko aka aiko ana sallama da Baby Baa ya ce "Wan halak ga shi nan ma ka ce tana zuwa.. maza ta shi kije." na mi?e da zura hijab na fita da dadduma a hannuna ina fita na ganshi kan Wan dandamalin gidanmu zaune na ?arasa da sallama na zauna ya amsa ya juyo yana kallona "ai na yi fishi kam." zan fara bashi ha?uri ya tareni... "yanzu kin kyauta?? ..nace "wlh banaso ka damu fa shiyyasa ban faWa maka ba ka yi ha?uri dan Allah" na faWa ina kwaSe fuska uwa zanyi kuka... "Oh ni da Aka ma laifi bance zanyi kuka ba saike ko?" Ya faWa da watsomin idanu.. nace to kayi ha?uri karkai fishi ka ji...?" "ya za ai nai fishi da Gimbiya?" nai dariya da rufe fuskata, "ya kika baro mutan gidan? Kin dawo lfy ina tsarabata?" nace "duk suna lpy ana gaishe ka ma" (Sir Ahmad saurayina ne kuma Malamina na boko da islamiyya mun daWe da shi tun ina SS1 shekara biyu kenan kan ta uku muke tare da shi yana sona sosai haka nima ga ha?uri da kawaici zan iya cewa ni tunda nake ban taSa ganin mutum me ha?uri irinna Sir Ahmad Wina ba duk da nima ana faWa ina da shi dan nima ha da ganan ba da gada wajan Amma, to duk nawa a ganina ban kama ?afarsa ba ko kaWan ga shi mutum ne me alheri da son jamaa kowwa nasa ne yanada faran-faran da mutane kam an yabeshi duk abun mutum bazece ga aibun Sir Ahmad ba.
Dogo ne sosai ba shida jiki fari ne sosai saSanin ni da nake ba?a baza a sakashi sahun munana ha dan ko baya daga cikinsu yana da kyansa dai-dai gwargwado.
Ba me kuWi bane Amma yana da rufin asiri daidai malamin mu ne a secondary yana Waukarmu English sannan again yana koyarwa a islamiyya shiyasa kowwa ya ganshi mlm Ahmad shi kaWai ne wajan iyayensa haka ma mamansa na sona tunda taga tilon Wanta na qaunata dan har iyaye maza ma sun shiga maganar ana jirana na ?arasa makaranta amma ni a raayina ina son ci gaba da karatu gsky Kuma ya ce Zai barni in naje gidansa).
Ya ce "ya yi ranar Monday zaa fara exam ko?" na ce "eh,"
"Kinyi karatu ince ko?" na ce "eh" "to Allah ya sa a fara a saa" na ce "Ameen dan Allah nasan an kawo question paper ka bani wadda zaa fara" ya ce "aa Ai ba haka ake ba hajiyata" nai dariya "ummm nima da wasa nake..."
Haka muka sha hirarmu ta gari da ta soyayya kafin ya tafi na shiga gida har sun kwanta ma na shige Waki na canza kaya da yin Alwala kwanta.
&&& &&& &&&
&&& &&& &&&
Ranar Monday da wuri na gama ayyukana na shirya saboda karfe 8:00 zamu shiga jarrabawa. na kammala komai na shirya na fito Baa na gani shima yau da wuri ze fita na gaishe shi nace "Baa ka rage min hanya" ya ce "to bara na fiddo mashin Win," Wakin Amma na shiga gaisheta ta amsa da min ADDU'A samun nasara na amsa da Ameen don inajin daWin aduar da takemin a raina.
Har bakin gate ya kaini ya aje kafin ya juya. na ?arasa shiga da hanzari don naga takwas Winma saura mintina kaWan, direct ajin mu na nufa na tarar anata bada sit number aka bani tawa ni ce 36 can kusa da Window naje na zauna aka fara Announcement duk Wanda yasan da jaka ajikinsa ko waya ya fito da ita.
na de fita da ledan da Nazo da ita da nazuba pen da biro da cul, don ni ko wayan ma banada ita, kowwa ya pita da nasa kafin mu zauna zaman jira. Examiners da Supervisors da Invigilators ne suka shigo don haka kowwa ya nutsu aka raba answer sheet, kafin a raba question paper. NATIONAL BOARD FOR ARABIC AND ISLAMIC STUDIES. wato (NBAIS) na fara karantawa a hankali tun daga farko har qarshe kafin kafin na sauke numfashi a hankali. ADAB da ita muka fara na janyo answer sheet na fara rubuta sunana da Admition number da sauran abubuwan da aka bu?ata... Ina cikin rubutu na ji Invigilator yana bayani da Larabci wanda be gane ba yai tambaya.
Kowwa ya du?a ana fama da biro da takarda ajin yayi tsit! ba abinda ka ke ji kowwa ya du?ufa sai goma muka fito dama 2hrs ce. nanfa aka zauna ana maida yadda akai. Muna zaune nida hamida qawata aka aiko wata yarinya Sir Ahmad na kirana a staff room na ce "to," Hamida zata fara min tsiya nace "kina cewa tak! se na faWa" tai shuru dan ta san zan iya na wuce ina mata dariya.
Wasu Qpaper ma ya bani na English zan tafi da su gida.
12:00 dai-dai muka shiga next paper ita kuma se 2:00 lokacin tashi gaba Waya.
A matu?ar gajiye na koma gida Amma na min sannu da zuwa na amsa da cire uniform ina shiga banWaki. Wanka nai da Wauro Alwala nai sallah azahar kafin na ci Abinci ina bama Amma labarin jarabawa tace lallaikam Allah ya bada saa na amsa da Ameen.

Washe gari se sha Waya na fita don ta Rana ce da mu kuma paper Waya ina zuwa anata shirye shiryen shiga nima na shiga na zauna a sit number na muka fara. biyu muka pito. Gidansu Hamida zani zan amsa sa?o tare muka tafi da ita.
Haka mukai ta fama da exam Winnan ga satin farko kwata kwata ba interval wani lokacin ma uku zami a Rana tun takwas se shida na yamma aikam Har na fige dama ni ba jikin kirki ba. Satin yana fita muka samu intervel kusan kwana goma aikam mun huta. Washe gari ranar Alhamis yakama muna da guda2 ta farko Home management practical ce, amma ba'a Sami damar yi ba wai saboda lokaci sai theory mu kai a rubuce da yamma muna da English karfe 4:00 ina bitan Qpapers en da Sir ya bani. ana Kiran la'asar muka shiga masjeed don yin laasar.
Itama shida muka fito kowwa ya nufi gida. haka muka ci gaba da zana jarrabawar cike da nasarori. tunda muka fara exam sir Ahmad be zo ba wai kar ya Wauke min hankali ya hana ni karatu, aikam na dage sosai dan ganin na ba mara Wa kunya, domin ba laifi ina da ?o?ari gsky bani da da?i?anta ko don gida ana zafafamin akan karatun,? Gefe Waya kuma ga Sir Ahmad yana dagewa a kaina,, yo ko be dage ba ai nayi don da kunya a gabanshi ace banda ?o?ari abin Kam baze daWi ba. 22/July Yau kenan ya kama zami last paper Qur'an and Tafseer ta rana ce bayan mun kammala aka haWu Malamai da ?alibai da Copper's da ?an TP ana hotuna na tarihi muna ta ban kwana ranar candy kowwa yazo da abinshi da yayi wasu sticker wasu calendar wasu memo abubuwa dai kala kala aka rarraba ni memo ne da key holder wanda Sir Ahmad ya min be min sticker ba wai baza a dinga masa yawo da hoton mata ba nace "lallaikam." Mungama abubuwan mu kafin a rabu da exchange number nikam a paper nai copy dan banada waya Baa ya ce "in mun yi candy za'a semin.
Na dawo gida kusan la'asar na zubewa Amma abubuwan da na samo tana ta gani da sa Albarka. Baa ya dawo da daddare nake nunnuna masa Abubuwan da nasamu, ya ce "to mamana ina tayaki murna Allah yai wa rayuwa Albarka" na ce "Ameen ga islamiyya kuma anata Shirin sauka ko?" na ce "eh," amma ba'a tsayar ba a August Win nan dai za'a tsayar "oh watan jibi ma kenan?" na ce "eh" ya ce "Allah ya kaimu."
Washe gari Sir Ya zo gidan mu da safe se ga shi nace "to lpy da safen nan?" Amma ta ce "le?a ki ji" na zura hijab na fice, tsaye na taddashi jikin mashin Winsa ya harWe hannunsa a ?irji yana kallon ?ofar gidan namu.. ?arasawa nai da sallama na Wan rissina ina gaisheshi ya amsa da murmushi ?an matan candy nai dariya "uhmm wlh kam Sir dan yanzu mun girma."wai Baby bazaki dena cemin Sir ba ko?" Na balalo ido.. "me zance to wanda yafi wannan?" "My love.." rufe baki da fuska nai da tafin hannuna.. (dan kam zancen ya Wan min nauyi) ya zubo min cike da shaawa yake kallona ya son wannan kunyar tawa tana birgeshi.. ya ce "kinsan Allah kina shiga gidana wannan kunyar sai na sauke miki ita tas..." Kallonsa nai da cuno Wan bakina "sannan na tsotse wannan bakin da ake cunomin tas..." ji nai tamkar na nitse don kunya, "Oh bazaki min magana ba kenan?" na shagwaSe fuska da dira ?afafu, "dan Allah Sir ka bari.." hmmm yau kina so ki rikitani bara na tafi kafin kisa yanzu na c..... ?ar ?ara nai da rufa ba ki na "dan Allah kar ka faWa..." dariya yai yana hawa kan mashin Win da mi?omin kwali na sa hannu 2 na amsa "na meye?" ya ce "wayarki ce tunda Baa ya ce sai anyi candy cikin tsananin murna na kalleshi... "Sir dgsk?" ya ce "iyyi cewa nai bazan faWa miki ba suprize zan miki, da akwai sim card a ciki sai ki kunna anjima zan Kira" kissing wayar nai cike da jin daWi "uhmmm ban ma san kalan godiyan da zan maka ba Sir.." ya ce "adana ba yanzu ba" na ce "yaushe?" ya ce "se ranar da kika zo gidana zan faWamiki kalar godiyar da nake so." "Uhm uhm.. dan Allah ka Bari." "dariya yai yana tayarda mashin Win "na bari Oya maza je gida se munyi waya" na ce "to" na juya cike da Woki.. jan mashin Win yai yana Wan murmushi da ?issima abu a ranshi.
Amma na ke nunawa wayar ina kiciniyar buWe ta a kwali TECNO ce Android me kyau da cover Win ta me zanen love a jiki Amma ta ri?e baki.. "yanzu shi haka ya dan?aro wannan uwar waya haka?" na ce "umm.." ta ce "to ajiyeta se Baa ya dawo a nuna masa aji me zai ce,ko ya?" na ce "eh hakane daidai ai."
Da dare bayan ya gama cin Abinci Amma ke masa zancen, ya ce "to shi Ahmadu anyi haka? ina shirin siya ya rigani kenan mugani? na mi?a masa ya ce "Masha Allah ta ko yi kyau screen touch ce Allah saka masa da alkhyr." muka amsa da "Ameen." ya ce "a dinga kula mamana kinga wayar nan inkinso zaki abin arziki da ita yafi komai sau?i, haka ma in abin tsiya zaka shuka yafi komai sau?i a kula a ji tsoron Allah... Yai ta min wa'azi da nasiha a kula duk da nasan baki da rawar kai zan shaidar hakan, ki cigaba a yadda na sanki." Amma ma ta Wora. akai tamin nasiha kafin kowwa ya nufi makwancinsa. ina kwance na gama komai nai Shirin kwanciya sai ga kiransa na Waga da sallama ya amsa cikin sanyinsa.. "my love"? "ina yini," na fara gaida shi, ya amsa "ina fatan gimbiyata tana lpy.." "lpy ta lau Sir na ji muryan ka sanyi lpy?"
"Wlh bana jin daWi ne Baby.." zaune na ta shi, cikin Wan fidda ido na ce "me ke damunka?" ya ce "ciwon ciki ne amma na sha magani fa" cike da damuwa nace "pls , sir ka je Asibiti," "Oh! shi sa bana son faWa miki irin haka na ce miki na sha magani zanje gobe insha Allah ki kwantar da hankalinki kinji Babyna.." ya ci gaba da lallashi na (oh ni yake ba ha?uri

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login