Showing 3001 words to 6000 words out of 10318 words

Chapter 2 - BAGIDAJIYA CE cmplt

Start ads

26 Aug 2025

20

Middle Ads

Aisha diyace ga mal.abdullahi da mal.binta
Mal.Abdullahi asalin su fulanin usulne 'yan asalin garin zuntu a wani 'kauye da ake kiransa fallanki,babansa ,shi yakafa kauyen sunan shi mal.yahya ,amma shidan kauyen gabane ana kiran kauyen *fallankin sab'a dutse* to lokacin da ya bar kauyensu da matanshi ,sai yayi 'yar madaidaicin gidansu suka zauna anan.
sai ya zamana infulani sukazo wucewa zasu sauka awajen sudanyi bukkansu na wucin gadi sutashi wasu su tsaya,ahaka waje yayi tayawa har yazama gari ana cemasa fallankin mal.yahya.

Mal.yahya yana da matan aure hudu dayara Ashirin da uku ,Ashirin da daya matane biyu maza Abdullahi da Abdussalamu

Lokacin da yaran shi maza suka fara tasa wane yadaukesu yakaisu almajiranci abdullahi aka kaisa Zaria ,shi kuma abdulsalamu yafi kusa akabarsa a soba .

Abdullahi Dane mai hazaka saida yayi sauka sau uku da tishi ,abdulsalam baiyi dayaba. adon haka sai yafara sana'arn dinkin hula anan cikin Zaria ung. Albarkawa tunda ba halin komawa yabar dan uwansa bai dawoba,yina sana'ar sa yana karatun littafai don sun zama gardawa.Ahaka wata rana wani alhj Ilu dake sayan hula a wajen sa yayi masa tayin makarantan boko ,bai wani musaba don yana da sha'awar karatun dama can,yaroki mutumin da yazo ya rokar mashi malamin su in ya amince.

Bai sha wani wuyaba sakamakon toshe masa baki da kudi dayayi.
Damakarantan yaki da jahilci yasoma, daganan yawuce secondary yafara daga form 1 har 5 .lokacin har yafara sana'ar yadiddika da dinka Manyan riguna yana saidawa attajirai da masu sarauta duk da taimakon wannan alhajin

Koda yagama sakandire makarantan gaba yanema yasamu yayi diploma daganan karatun ya tsaya ,saboda hura masa wuta a kauyensu da akayi da yayi aure a lokacin tuni abdussalami yayi aure matansa biyu da 'yaya rututu.

Alhaji Ilu mai gidansa yasama da maganar, yagayama duk matsalar da yake ciki,kwantar masa da hankali yayi sosai yakarba takardunsa yasamar masa aiki a wani babban kotu dake a sabon gari.yakuma wanke 'yarsa bintu yabasa da kyautar gida.

Hankali kwance yake gudanar da rayuwarsa arziki na kara bunkasa har suka hayayyafa a lokacin da binta tahaifi yara biyune Fatima da ameena danginshi nacan suka matsa sai ya auri 'Yar uwansa yahadasu inbahakaba,'yan Zaria zasu kwashe arzikinsa inya rasu,binta tanada sanyin hali batada hayaniya samsam .

Bata matsa masaba ya auro matarsa kuluwa amma ana kiranta yaya yabarta acan fallankin bayan ya Gina gidansa me kyau acan.

Tunda binta tahaifi 'yarta Rahma haihuwar ta tsaya mata.bare kuma yaya da ko b'atan wata bata tab'a yiba.

Tuni fatima da amina sun girma har anyi bikinsu ameena a tudun wada tayi aure da yaranta uku dayake gwarne takeyi itakuma fatima tabiyo mamansune danta kenan daya alokacin sunansa Aliyu a hanwa suka fara zama da mijinta cikin danginsa.
Itakuma rahma ansamata rana da wani dan Abuja yazo bautar kasa makarantarsu,suka hadu

Sai a wannan lokacin ne ciki bul ya bayyana ajikin mama binta daabokiyar zamanta yaya .

Akuma wannan lokacin ne mal.yahya Allah yayi masa rasuwa.

Suka d'ibi jiki aka tafi gaisuwa bayan an share zaman makoki an raba gado mal.abdullahi yayi shirin komawa Zaria ,nan enuwanshi suke shaida masa wasiccin babansa dayayi akan yadawo fallanki da iyalansa da zama.

Yayi kukan bakin ciki bintama tayi ai wannan shi ake kira karkon kifi daga cikin gari sai dosun kauye?

Adole yakara fadin gininsa yayi masu wadataccen gini na sumunti ,yaje wajen aikin su aka bashi transfer yadawo kotun zuntu.

Basudawo fallanki da zamaba saida sukajira akayi bikin rahma acan zarian amarya tatare agidan mijinta a abuja

Anan fallankin tahaifi 'yarta aishatu danginta nacan nakiranta indo,itama yaya tahaifi danta namiji ana kiransa sanusi,sa'annine indo da sanusi wata biyu sanusi yabata.itakuma lokacin Fatima tana goyon 'yan biyunta sunba indo wata hudu.

A lokacin da indo da sanusine suka isa shiga makaranta babansu yasakasu a primary din cikin garin zuntu,kullum in zaije aiki zai tafi dasu.in lokacin tashi yayi yaje yadaukesu su wuce gida,a kullum cikin kawo masa kararta ake yau taci abincin wane,gobe ta Zane wane, tankwalace original duk jarabawa ita ke daukan na baya.ancancanja makarantu ba adadi amma Sam ba abunda ya sauyata nadaga kokari ko kawo kararta kan yaran mutane

Dama kuma tunda indo ta taso , tun bata wuce shekaru ukuba tayi tanbari a unguwansu to, cizon yaran jama'ah iyaye na ganin ta ,suke dauke yaransu su Goya, ga rigima.

Watarana ne anty Fatima tazo garin da 'yan biyunta,shikenan tunda yara sukazo garin suka daina shan ruwan garin ko anbasu sai sun amayar,A lokacin basufi shekaru biyar ba,take suka fara rama.da tana kawaici ne saboda alkunyar dake tsakanin ta da maman matsayin ta na 'Yar fari ,bata ko kula 'yayanta bare ita kanta.gashi basuyi sa'ar kishiyar uwaba don Sam harsuzo sutafi daga gaisuwa ba maganar da zai sake hada su.

Ganin 'yayan mutane na Neman halaka abanza ,ai ba arziki tazari keyn motarta taje nemo masu ruwan roba a cikin gari,don tasan ruwan rijiyar garinne badadi kuma ita bazata iya basu narafiba.
Cartons 5 tasiyo dasu caprison datarkacen chocolate takawo masu. Aikoba ajimaba ,yara suka murmure suka saki jikinsu.
Saidaime?tunda indo ta kyalla ido taga ruwa ,tashi ga jida ,tana bama yaran makota da almajirai kwaf daya, saida takrar da duka ,itace kwabin wasan kasa dashi ,tajika jiki ta bannatar.
tun Fatima na kawaici harta kare dai ta tsawa tar mata.
Haba dan fadarda taima ta keda wuya ,tasami karkashin inuwa tamike kafa ta runtse ido taringa kwarara ihu iya karfinta,kaf saida ta tada hankalin gidan,kowa yazo lallashinta sai aga ido a soye ba d'igon hawaye.

Tun safe har karfe biyu tayi zufa sharkaf ,kowa dayagaji dole suka shige daki suka barta ,harsaida tayi su amai sannan bacci ya sureta a wajen.

Fatima da yaran ta kam tundaga lokacin suka fara ganin babi babi na izaya,shiga dubu fita dari saita jibgesu,don dole ta tattara kawunan 'yayanta suka koma inda suka fito.

Haka rayuwa tacigaba da gungurawa ,har indo suka shiga shekaru takwas,nan akeyinta
Don ita gabadaya tatasone tsundum cikin 'yan kauye bata San komaiba daga zuwa dandali sai taya kawayenta Fulanin dasuke zama a kauyen kiwaon shanayensu.
Tsabagen karfi dajin naci tuwon dawa na kangare har siyanfada takeyi.

Za'ai girkin engayu adakinsu zata fitar suyi musaye da 'yayan makota wai bata iya cimarba ,itadai tasha fate da sugar ba manja,dan gauda,tukurkusu dadai sauransu don haka tataso kakkaura gidirgir kakkarfa da karfi kamar shara'a uwa wani namijin

Tunda yaya tahaifi da namiji bayan dogon zangon da ta kwashe ba haihuwa ,shikenan gori ya ishi mama binta ,wai sune da gida ,waye waye......

Wataranar sallah ce kaf yaran mama sunzo da yaransu duk mazajensu suka kawosu,basuyo abincin sallah ba saboda nisa amma sun kawo buhunhuna da gallons na mangyada da manja da komai namahadin girki.

Mama wayayyiyace don haka dasauri tadaura babban tukunya taraya masu girki dayaji tsokokin kaji,tahada masu lafiyayyen kunun aya dayaji madara ta aika akaje zuntu aka nemo mata kankara tasaka aciki
Ta wanke lafiyayyun plates ,warmers da spoons tagoge ,tazuba komai tashimfeda dardumanta na alfarma datayo a saudiyya tashirya masu komai a falonta
Suka baje kwansu da kwarkwatansu,sukaja gara cikeda barkwanci da wasa da dariya kamar zuri'a daya

Takaici kam habaici dayada magana mama sun shata, ko kusa taki ko zuwa su gaisa saboda bakin ciki

mazan da zasu tafi,kowa da kudinshi na albarka,Rafa Rafa sule yaya ba tasamu ba,yooo basuma San da itaba.

Fitonsu keda wuya tajawo murhu tahada wutankara tafara mulla tuwo,tana wake wake: "duniya rawar 'yan matane na gaba yakoma baya"
Sarai sumama sun gane mai take nufi amma bawanda yatankata
Cikin sa'a saiga daidai daita tashigo a keken almajiran gidansu data ara

"6ii6itttttttt!!!
abani waje kar nayi 6anna,akaudakaya harnayi kutubal dashi alkur'an....."
Hango yaya tatakarkare tana tuka tuwo,kawai sai ranta ya kissima mata ta roreta da fada

Kewaye ta da murhunta tashiga yi da keken "agafara ba birki Yaseen"wani gigir,gigir tashiga yi da kan keken kamar zata duro ta jikinta,raba mata hankali yasoma yi jiri nadibanta,ga hucin tuwo,ga wuta gakeke da ke wuliwuli akanta.

" ke dan iyayen ki bar nan" tafada tana zare idanuwa

"Hajiya nakwalla shugaban aiki maza tukesa Tass,din vamusan guda...don dole ki tuke katon tukuny mu danna .....wooooo 'Yar aiki ke daya daya dagake saidanki sanusi mai kan jaki.....kinaji zaki kwashe ki kawo mana"

Yo kanta tayi dagudu zata daketa ,tako zille ta watsar da keken ckan tukunyar ,yako 6are cikin wutan,ji kake cuuuuiuuu!!!


"Wayyo jama'a gudunmawa ta shekarmun da tuwo" tasa hannu aka tana kwarara ihu ,cikinta ba kululu na azababben yunwa.

Lankwashe murya indo tayi sannan tayi maganar da karfi ,yanda kowa zaiji a aza indon keda gaskiya

"Wayyo yayan mu saida nace maki ba burki ....kiyi hankuri bari naroko maki abincin en birni dakin mamanmu" tadaddalo mata ido tana mata gwalo da dariyan sak'e

"Saidai ki roko wa uwarki dinmu bamuyi gadon rokoba" tanayi tana matsowa kusada inda take

Tsalle tayi taje kofar fita waje"haba Yar tsohuwa ,tarrr nake kallon ki.....kije jira zamanku da yunwa dan aradu babana yau famfo zammai ga abinci gida baxai asaran kudi yabakiba......hahhhhh yau wata zataga malaikan mutuwa azzallaruruwa me wukaken azaba kala dubu"tafalla aguje tabar gidan



Vote
Share
Comment
[8/19, 10:13 AM] Haisahhtttttt💅🏻: 👠👠💅BAGIDAJIYACE I👠👠💅🏻


*©️HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*(Home of peace, joint entertainment to educate and enlighten our readers)*


Dis page ix dedicated to you my fanz 😍😍😍 indodo tace namiqa mata jinjinar ta gareku👍🏻 Allah ya bar kauna da zumunci🤝🏻

I reserve your comments my fam ,zanbisu daya bayan daya,ahankali zaku fara jin reply dina serially inshaallah,daga next update
amma sorry wasufa acikinkune , masu sharhi kadai zansa saboda groups din da yawa.
masu mun fatan alkhairi kuma da addu'oi kuma bazan mance dakuba zanware maku page na musamman in jero sunayenku, bayan next update.inayinku irin totally dinnan❣️💯



Written by
Hassenart



Litattafan marubuciyan
RAYUWAR AFREDARH

QASAITATTUN MATA

RAMUWAR GAYYA

_And now_

BAGIDAJIYACE


*littafina na kudine dashi da ramuwar gayya, anabiyar kowani daya #200,ake turowa ta katin MTN zaki turama wannan number 09065990265*
*Saiki screen shot a matsayin evidence ki turo,ko kuma zaki iya rubuto numbern katin ,ki turama numbern saman dai*


*Free page7️⃣~8️⃣*

Gidansu kawarta rahane tatafi,da sallama tashiga gidan kamar 'Yar arziki,ta gaida innansu rahane dake tuqe tuwon dare.
"Hannu innah ,shin rahane ko tana hiki?"
"Eh tana ciki ,tana shirin tafiya tallen gyada"
Cikin dakin takutsa kai batareda takuma cewa komaiba

"Kawalliya romon danga, kece haka se tsatso kyau kike abinki ?"

"To aminiya abun ai duk sirrine daka tsami nayi din wallahi innayi wanka ciwo nakeyi.... (Hikiciffff,atishawa tayi sannan tace)wasa da ruwan sanyi" tafada tana maida 'Yar kwallan da yazubo mata sakamakon tarin da takumayi
"H'ummm lallai zanzo inhana mamanmu yimun wanka dakanta,kinga nima sai ,inayin irin naki....mene kikace sunansa?"
"Daka tsami,eh daka tsami sunansa kenan... Bake ba tsamin rana...bare kije talle aki saya"
"Hakane fa kawalli li, muje kar dare yemana a waje mama tayi fada"
Saida tagama shirga hau kanta a fuska nan tafito rangandau fuska yasha dige digen ba'ki baki dal da janbankinda 24hours ,angoggoga janvakin asaman idon maikon hambakin ya hade Dana kwalli. Sallama sukayi ma inna suka tafi,zuciyar inna fal murna domin duk ranarda rahane tafita da indodo tas kayan su,ke karewa.
Jerawa sukayi suna tafiya duk yaran da yagansu saidai ya canza hanya don ko da kuskure yaro ya biyo ta wajen su ,saidai kaje fahhh!,ta kafta ma da mari .
Suna isa dandali ,rahane ta aje gyadarta a wajen masu sayarwa,itakam indodo Ku tsawa cikin gantsara,gantsaran 'yan mata tayi dasuke fili da samarinsu suna rawa,tana shiga kowace maison kanta da mutunci tayi waje, itakam ko ajikinta don tasaba haka ake mata ,ita aganinta hakanma isuwace.

"Masu hid'i canja Mani,wannan baiyi mun ba"
Rawa takeyi duk Wanda akasa ta iya rawarsa tana rawar tana bin wa'kar
"Kin gani kin gani kwalelarki,shegiya 'Yar banza" tamaimaita wa'kar data canja masa ma'ana kadan daga k'arshe tareda shako wuyar wata da ke daga kusa da ita tahankada ta wajen filin.aiko saurayin ta yazaburo kan indo,tsalle daya, tayi tafita filin tafara gurza kafarta a turbayen wajen k'ura yaringa tashi fuuuuuu! Take wajen ya hautsine.'yan kida suka hau tattare kayan su ,suna Allah ya isah don sunsan ,sin rasa kasuwar ranar.

Cike da barazana da cika baki tahau yiwa kanta kirari,koya tsorata yakyaleta .kirjinta na dukan taratara ,yau kam karyana takare inani ?,ina wannan rusheshen basamuden " da wannan zancen zucin takarasa gabanshi, kanta tsaye" Waye yace dani baniba,shima ince dashi bashiba,saini tururuwa mai idon zalinci,taboni kaga tarandangi saini dakalin majina ahauni a zame, saini....."
"Ke yimana shiru kinjiko?" Yadaka mata tsawa,"ke kin zama mana annoba a gari ,mai kike taqama dashine?....yauto zanci ubanki inga abunda zai faru!"

Wani kururuwa ta dauka da kaf saida 'yan filin suka arta da gudu har budurwan da akeson taremawan ,can nesa suka tsaya yau su sha kallo ,kodai amauji bakin muguwa suji dad'i,ko kuma ayi mai lilis susha kallo .
"Kucasu arna kucasu,Ku casu bamai rabaku" aka dauka yimasu waka don a kara gingering dinsu

"Tab yaro bakasan halin indodoba yoo, kaidin ka yimun kadan a danbena,ai ina hada jiki da kai kwashe mun k'arfina zakayi tassss!, kagako baka isa ba" takarasa maganar tana ja da baya,zuciyar ta na rayamata ta arce.

"Aini abun kunyane indanbe dake saidai in lallasaki" yajuya yazugo tafasan bayan su

daka tsalle tayi tatimu a kasa"Nasama Ku d'auka za'a taba maku god'iya"tafadi cikeda sadakarwa.

Abun tsoro ,kawai zai akaji karan bulalai ya kacame wajen ,aka shiga zubama saurayin,ihu yake kwarara wa,yana burgima akasa yana soshe soshe,amma saukan dukan akeji bamai dukan.....

Haba a matukar rude indo taci hanya ta dibi kasa ta watsama kafar tata,"kafa mainaci banbakiba?kimun gudun da baki taba yiba" fil ta b'ace kamar barewa.

Tana barin wajen aka dakanta da dukansa jikinsa rudu rudu duk ya farfashe ,kowa watsewa yayi sai masu balain abota daahine suka rakube daga nesa daya yasoma magana
"Iluwa tashi don Allah, Yaseen kaima danaka, Dana gani babu tambaya kasan yarinyar nan tasuce,don ni tun ranar Dana soma ganin ta raina taraya mun. 'Yar ruwace to 'ya kyau haka....du Allah wata rana Ku kare mata kallo zakuga yanda kalolin jikinta kesauyawa....abunda yafi muzueawa sarauta Allah ido ,don Allah baya dauka ka banza"

Daya kuma ya maida kallon sa sama "Ku kuke ganin mu bamu muke ganinku ba,agafarcemu muntuba,minbi Allah munbiku....kuskure irin haka bazata kuma faruwa ba"

Duhun darene suka farga yasoma riskarsu ,su kadai awajen

"Iluwa ko ,ka tashi wallahi ko mu barka afadansu,mutafi" suka juya zasu tafi ,ai a sittin ya mike ,d'afff yaji kamar an zare radadin dayake ji a jikinsa,tsabagen tsorata.




Koda indo tadawo gida sad'af sad'af tashige dakin su tawuce 'Yar gadon ta .ta kwanta

Anty amina ne ta hango kafarta bututu da kura kamar wacce tayi kwab'in k'asa
"Mun shigesu Aisha kece haka?... Ji yanda sababbin kayan ki suka koma? Ji kafarki?...tashi don kaniyarki ,kije kiyi sallah"

Sum sum tamike ta. Fita kamar mutuniyar kirki,yo ita kanta tsoron kanta takeji,gani take uwa a mafarki

"Ciftsi Ameenah kinganta kuwa ai ta cika botiki tai wanka tukum,don wannan najasace ,bazata yi sallah a hakaba"Cewar anty fatima

" mtseww laifin mamane,abani ita tayi sati biyu a wajena ,wallahi saita kintsu...to ina bazasu bakaba"

Sai anan mama takada baki tace"wallahi nabaku go ahead, kutafi da ita ,ita kenan ba tabar tsoho ba bare yaro?, Sam baki biyo halinaba,yanzu kujira zakuji yanda gidan zai hargitse itada yaya....nidani ne bazan ringa biyewa jikan cikina ba.da in sun fara ana zuwa ,yanzu bamai zuwa bada hakuri"

"To algungumai,gulmata kikayi ko,ai yau zata gane shayi ma ruwane,ina me idon mayun take?"
Dasauri anty Fatima taboyeta a bayan kyaure
Tagama waige waigenta,bata hango taba ta shige d'akinta ,tana 'yan zage zage,bawanda yace mata cikanki

Anty faty dakanta taje tayi mata wanka ta tsaya akanta tana alwala tana gyara mata. Har tagama suka shigo daki.


********************

Zau maganar fadan iluwa da indo yacika gari kowa yaji bai musawa yasan zata aikata,don abunda takeyi,inba shafar jinnuba bameyinshi bai ciwon jikiba. Amma ita kullum kamar kara Mata lafiya akeyi

Ganin sauyin data gani a fuskokin kowa lamarin yakuma burgeta ,tataka kowaye,bamai tankata.duk abunda ke faruwa ,bawanda yasani a gidansu har yayyenta suka gama kwanakinsu suka koma don tace bazata bi ameenaba,ranar dazasu tafi tunda tasha ruwan kunu ta arce,ba Wanda yakuma ganin keyarta sai dare lokacin tuni driven kowaccensu yazo ya kwashe su.

Wata makociyarsuce takira yaya gefe,watarana sunje gidan rasuwa, tagayamata rad'e rad'in da akeyi akan indo wai ba mutum bace,saida takoro mata labari kaf ,sannan yaya ta d'age hanci ta rangad'a gud'a
"Wohoho Allah matubi,Ku shashashun inane?, indonce aljan ?, tabdijam yanzu naji nasamu lasisin jibgarta da hujjah"

"Adaibi a hankali innan sanusi donko lamarinta ba karya cikinsa, don yanzu haka iluwa nanan yana jinya....."

"Bayin Allah, kuyiwa Allah kufita daga waje ,komaji da rad'ad'in rashin damu kayi....."
"Dubu daga kinganmu a gidanki shine har zaki koremu?" Yaya tafada cikeda jin haushi

"An koreku d'in inbanda rashin kamun kai yazakizo gidan mutuwa,kina mana gud'a ?...Yaseen 'Yar uwan zamanki na kokari dake,don ma tanada mai maganin ki akusa ,bacin haka dakin cutarda hakurarran baiwar Allah"

Ainan bakin yaya yafara tururi,bakin cikinta daya,anyabi kishiyarta anzageta,cikin kumfar baki tahau bala'i .da kyar mata suka rabasu ,don suna daf da dakuwa.
don itama abokiyar fadan babayabace.
nan dakyar aka jata suka fitar daita daga gidan.


Wayyo ina wuta tawatsawa mama binta da indo, nan komai yakuma jagulewa,kullum cikin bala'i gidan yake ,don yaya tana cewa tak!
Inbai gamsarda indo ba ,saita ramamasu.

Ana haka indo da sanusi suka gama primary, ba laifi tafara kokari don takan dauki na Ashirin haka cikin su sittin.
Kuma alhamdulillah tasama admission a makarantan day maza da mata na zuntu.

Akuma hutun datasamune ta shirya kayanta anty faty taturo ,aka dauketa taje tayi masu Hutu kafin sigama registration.




Vote
Share
Comment
[8/19, 10:13 AM] Haisahhtttttt💅🏻: *👠👠💅🏻BAGIDAJIYACE👠👠💅🏻*



*©️HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*(Home of peace, joint entertainment to educate and enlighten our readers)*


Story and written by✍🏻
Hassenart
☎️090- 659 -902 -65


*Basai na maimaita kaina ba ,littafin nan na kudine #200 ne kacal zaki turo mun ta

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login