Showing 6001 words to 9000 words out of 10318 words

Chapter 3 - BAGIDAJIYA CE cmplt

Start ads

26 Aug 2025

19

Middle Ads

wannan number 09065990265, VIP kuma #300 na katin MTN, kibiya kudinki don more karatun littafin ki a tsananki*
👏🏻



*Free page9️⃣~1️⃣0️⃣*



Saida tashake Ghana must go biyu taf ,dakaya .tunda tashigo dasu cikin motar gaba daya annurin fuskar idi driver ya dauke,sakamakon tsamin kayan datti da warin ajiya da yagauraye kamshin turaren motar saida tazo har tashiga motar metatuna oho!, tafara jijjiga hannun budewa,tana shirin karyeta,azabure idi ya zagayo ya bude mata,ranshi fal takaici,don inba cin akan aikinta yazo wannan garin da ba abunda zai hana ya jibgeta kamar Allah ya aiko sa,k'wafa yasoma yi sannan ya d'an
Sassauta murya yad'an rankwafo cikin motar ta windon waje"hajiya yadai,ko akwai abunda kika mantoshi ciki ne"da lalatattan hausanta tasoma bashi amsa"uhm'u uhmum rahane,k'awar arziki na manta bamuyi sallama ba hine ,yanzu ta hwad'o mun a rai ,kaga yazamammun tilashin wuya nadubo ta"wani malolon abune yazomar makogoro ya toshe,dakyar ya iya maida yawun bakinsa,bayan yad'an kauda kansa, jin wani irin mak'ak'in warin kore fet din bakinta dake barazanar d'aukemasa numfashi don inbaicikaba k'ila ta shekara batayi brush ba. Yinaji yana gani takuma fita a motar ta arta cikin unguwa ,ba'ajimaba saiga su tareda wata matashiyar yarinya da zasuzo sa'anni duk'u duk'u da ita ,k'afa bako takalmi.har gaban motar ta rakota"indona wazai ringa taremun fad'a inkin tafi" wani wawan tsawa tadaka mata"keeee!, to saiki gayyato uwarki tatare maki,tukunama waike dak'ik'iyar inace,na'aza nan nagama baki shawaran yanda zaki daki banzaye,yanzu kinamun maimaici ,salan inje zaria intarar 'yar farfesun nawa yagaji da jirana yahuce ya sandare....malama dan janye tsumman jikinki saura karki kwaso takalmi kisa kibari indawo insameki hakan"
"Wohoho! Indo waike wannan kawarkice ko 'yarki,kitsahirta mata hakamana ,ke kuma da azaban kwadayi 'yan uwanta dakike gani yasakike like mata tana maki gori da wulakanci..." Yayace tafito daga cikin gidansu ,jin karad'in indo dayacika layi,tafito taga dawacce takeyi.
"Ahayyye ,cas lallai,inbaka mutuba ,ba zaka daina ganin abun haushiba ,kekuma asuwa?, karuwa a masallaci?" Idi driver ne da kuluwa suka dauki salati atare "indo nice karuwan?" Mere baki tayi,bako d'ar aranta "ohoo tanan kika biyo to kilan hakanne...malam zakaja mato mutafi ko in kwashe tsummokarai nane inkoma ciki? " jinjina kai yayi cikeda gajiyawa ikon Allah "hajiya kiyi hak'uri d'an yau se allAllah shirya" baibi takan surutanda kuluwa tacigaba dayiba,ba kwama bare fullstop ,tasai fad'an tsaf ,don tuni rahane tasulale ,don tasan indo na jin zuciya zata fincikota tajibga.
Wuta yabawa motarshi yaci hanya ,yanbin kwazazzabon hanyoyin,duk in yashiga inzai fito saidai kaji k'ummm! Indo tak'ume , nan zata haujaraba bazata yi shiru ba zatajita takuma wani k'umuwar,zagi kam drivern nan yasha ta har sukafito titin zuntu.
Goshinta duk sunyi k'ulayen azaba,shikam duk tsiyar datake cikanki baice mataba. Basuyi nisa da tafiyaba ,barci ya sureta bata tashi farkawaba saida suka shigo Zaria.
Mik'a tayi tahau mitsike fuskarta da kwalliyar kwalli da janbaki datayi ya hade da zufa yayi dameji tadawo kamar aljana bakaganin komai sai farin kwarar idonta.
Tunda ya hango idonta tamadubin dake kusa dashi yake guntse dariya duk wannan kwalliyar haukan yadame guri guda,bata wani damu da murmushi dayake yiba .tsaki tamayi"mtseewwww,Allah yara bamu da motsatse"
Kanzil veceba saima shan kunu da yayi, shan kwana roundabout din p.z din da taga yayi a maimakon adauki hanyar hanwa shi ya tsoratar daita,shalll taga driver yadauki hanyar shiga GRA din gadan gadan,awani zabure ta k'walla mai wani gigitataccen k'ara a kunne , dagudu yataka wani wawan burki ,sakamakon kambin motar da ta nemi kub'ce masa a hannu. Aguje yayi parking a gefen hanya.
"Hajiya lafiya dai?" Tsaki tayi tafara babballa masa harara kamar aljana
"Ina fa lafiya zaka kaini inda za'ayi gandar kaina,kahe kai, in d'an yankan kaine,inbahakaba meyakawo mu nan,muda zamu unguwarsu.... Yo kodai kadauka bansan wuri bane,kana wani wuri wuri da ido kamar ifiritu,ja'iri tsokan kaina yafi karhinku ank'ur'an..." Takaicintane yacika mai zuciya don dai idi driver badai fushi ba
"To dan gidanku ,yanxu ya kikeso ayine?ko kibari inban kaiki gidan su hajiyanba daganan saiki nema hanyar matsera,dan inkika sake mun ihu aka saina karairayaki nawatsa ma karnukan layin nan Yaseen"
"Iyeee!, wata kan anty tasan kuna cin naman mutane,tokodai harda wannan mijin nata,dama ni tini nad'ibiya masa ayar tambaya, wannan talliyar kan nasa kamar na yahudu da nasara,to mujed'in inga dame kuke tak'ama,koka d'auka zan firgitane?, to aradu k'wank'waman kaina sunfi k'arfinka..."figar motarshi yayi a mugun zuciye,zuwa cikin GRA din ,don duk ak'agare yake ,yak'osa yakaita yahuta da jarababben surutunta maras kan Gado
Adaidai wani mahaukacin gida,taga drivern yana karkata akalan motar ciki,horn yayi tareda kokarin shiga harabar gidan bayan ankwaye get d'in. Wani hamshakin gida mai cikeda furanni da bishiyoyin kwakwa tagani yacusa kan motar ciki,sojoji birjik acikin gidan.tsurewa tayi take tahau sunbatu" lahaula walakuwata,ya bagabaga ya kilu ,wabillahi labinnasi ...idirisu ina zaka kaini ne? Daga wasa...aradun Allah wasa nake maka,mama na sona araye...nabi allAllah nabika ka maidani gida nafasa zuwa gidan su fatsiman..."
"Kinfasa,gayyato mitsa mitsankan naki? Bagidaji kawai to har gaban dodon tsafinmu zankaiki ,sai naga ya zuk'e jinin jikinki zanfita" nan yashiga da motar wajen adanasu,yayi fakin yafito "fito haka nan nace" zare gwalagulan idonta tashiga yi,hawaye na diga
"Yaseen banfita,saidai kakirasunan..." D'age kafad'arta sama yayi"to ki tazama ni kinga tafiya ta"
Daidai nan ta hango anty faty cikin shigar dandatsatsiyar leshi,sai walainiya takeyi ta hasken rana.
K'uri tayi da idanuwanta cikeda tantaman in antyn tace.da dariyarta takaraso ta bude mata kofan"autanmu sannu da hanya"ja dabaya tayi saurin yi su Hassana da Hussaina ma suka juya a zabure cikeda taraddadi,kwalla ma idi kira tayi
"Idi mai yafaru ne,ko iskantane suka bugeta a hanya?" Sauke wahalallan ajiyar zuciya yayi
"Kamar kinsani hajiya,naci wuya a hanya ,kar ala naimaita"
"Allahu sarki ,gaskiya naga fuskarta kamar daddawa sai dango takeyi ga jirwayen hawaye faceface.... Topah ya zamuyi kenan" zaraf Hassana tasoma magana "mommy akira kakkarfan kurtun can Joseph mana,sai yadauketa ashigo daita daga ciki"
Indo datun d'azu take jab'e kamar kayan wanki ba uhm bare um'um rungume da tarin kayanta ,jin an anbaci soja yasa tazabura tafito a sittin .hanyarda mom suka fito tanufa a tsiyace,karo tayida kakkarfan kirjin wani dake tunkaro cikin compound din,tipp tafadi 'kasa cikeda jin jiki................
Wani kakkausan muryane yasoma amsa kuwa a kunnenta
" Waye wannan? Hassenorh wata bagidajiyace wannan? "




Like
Vote
Share
Comment
[8/19, 10:14 AM] Haisahhtttttt💅🏻: *👠👠💅🏻 BAGIDAJIYACE👠👠💅🏻*



*©️HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*(Home of peace, joint entertainment to educate and enlighten our readers)*



Story and written by✍🏻
Hassenart
☎️090 -659 -902 -65


*Dedication*

*Wannan page din sadaukarwane gareku masoyana,🌹🌹 kuyi duk yanda kukaso dashi mallakinkune,saikunso wani ya karanta. 'yan groups d'ina masu nuna mun tsananin 'kauna ta hanyar turo mun zunzurutan comments 'dinku ,masu karamun k'warin gwuiwa,nima ina sonku kamar raina*
*•••HASSENART FANZ GROUP •••*

*•••RAMUWAR GAYYA/BAGIDAJIYACE COMMENT BOX•••*

*•••RAMUWAR GAYYA FANZ GROUPS1️⃣&2️⃣•••*

*My warm regard tareda jinjinar bangirmata baxai tab'a yankewaba agareku HASSENART NOVELS PAID GROUPs 1 & 2. Koban fad'aba kundaisan ance babbar masoyinka shine Wanda zai baka kudin shi don ya nishad'antu da labarin ka,don haka nima inayinku totally alqur'an🤪💯*


~*Littafin kudine books d'ina wato RAMUWAR GAYYA da BAGIDAJIYACE, only #200 na katin mtn .sai kuma idan VIP kikeso #300 ne shi,zaku turo katin ta wannan number 09065990265.*~
~*Hajiya karki biyoni inba biya zakiyi ba ,don aradun Allah zan blocking d'inkine nan take👌*~



*Free page 1️⃣1️⃣~1️⃣2️⃣*



Kecewa da dariyar 'keta su Hassana sukayi har suna duk'ewa a wajen don sunsan dai batazo gidan a sa'a ba tunda Allah yayi mata gamoda farouq.


girgiza kai mom tayi,sannan tawaigo tak'are ma umar da indo kallo.

"Umar wannan yarinyar dakake gani
Kanwarmuce,itace autarmu..."

Dafe k'irji yayi kamar Wanda yaga abun tsoro "mum,wannan abar ?...jitafa kamar bugun aljannu,nifa dafari na'aza gamo nayi...tabdi lallai wannan inhar kanwarkice,amma zama daku baisa ta gogeba tabbas ba k'aramar cikakkan BAGIDAJIYACE ba..."

Murmushi mum tayi don ita batafaye son hayaniyaba.jinjina masa kai kurum tayi
"In boy yazo katambayeshi relationship d'in dake tsakanin shi da ita"

Mikewa indo tayi cikeda masifa jin ankirata da bagidajiya tayi mai k'ur da dakwadakwan idan uwanta uwa na mayu,ai dasauri ya kauda fuska,donshifa rod'i rod'i yaga tana masa a ido ,tuni ya soma ganin jirijiri.
"Malam bar ganina haka ,kazata kanwar lasace,to kwarankwatsa nasaba danbe da shirga shirgan mazan k'auyenmu dagani sai guntun fatari ,bare kai me kamada tsinken sakace wani korekore dakai zibun cutar shawara, don haka kashiga cikin hankalinka inkuma saimun gwabzaneto"

Tsuru yayi mata da idanuwansa kamar yana hango wani najasa ajikinta. Kanzil yakasa cemata

"Hahahhh cabd'i yau yaya ba magana ne ?...gakafa ga indo,Ku d'ab kafta musha kallo don Allah" Cewar Hussaina kenan.

Juyowa yayi a mak'uran zuciye don gidanku yaushe nafara wasa dake ne?...bar wajen nan kar na b'arar dake" simsim tarab'e tawuce ciki. Hassana ma bin bayanta tayi dasauri don tasan yana iya zanesu yanzunnan .dama ita tuni mom tashige cike tabar su anan
Dawowa takan indo yayi datayi tsaye akansa tana jijjiga jiki
"Ke kin d'aga mun takalmina kinban waje nawuce kokuwa?k'afa kamar na tsinnaka"
Jan zogala zogalan kafarta data take masa takalmi tayi ta hankad'a masa takalmin gabanshi,tana faman ballare ballare tareda murguda masa baki.

"Mtsewwww,Toni me zanda takalmi nan har ake mun tsawa kansa ,takalmi sai kahe na hilanin garin mu"
tajuya tashige ciki,sai ya ??tana saka k'afarta a cikin falon da sauri tayi saurin dawo da kafarta wajen ,nan tasandare tsaye daga bakin k'ofa
"Ya rasulullahi manzan tsarki,jama'a inane hanyar dakukabi Nene?kut macizzai🤔"
Dakatawa da tafiyar farouk yayi da azamansa yadawo wajenta ,d'an nesa da ita ya tsaya,cikeda zullumi, yana toshe hancinsa yana k'arewa rafkeken falon kallo
" ke ina macizan?" Bata bashi amsaba saida ya zauna ,dab'as tayi a kasan varendarn tukuna.sannan ta bude baki hagaga tasaki 'katon hamma ,barufe baki bakomai tana gama hamman ta hau tofi da yamu tagefe,jikake tuftuf!

Jiyoda kansa tad'aya barin yayi,sannan yasake mata magana cikin tsawa tsawa
"Ke wai bakiji mai nace bane?"
Zare d'ankwalin kanta tayi zuwa gaban goshi tahau Sosa gashin kanta da akaima kitso 'Yar Hausa(two hands) tsabar dadewa har ya daskare baka iya ganin tsagon kitson,sai uwar k'ura kamar an barbad'a,wani hamma takuma yi harsaida tayi hawaye cikinta yabada kukan"k'uuuuuu" saida tashafa cikinta sannan tace "mai rogo....uhnm ,wai mekahe,macizzai ko?To eh maccizzai mana ni ,narasa ta inda sukaine, suka wuce ta wagga waje,sufa sukayi ne...yayane oho..."
"Ke wai macizan ?" Yafad'i a matuk'ar rud'e .Tab'e baki tayi
"malam bari inmaka gwari gwari,don naga kai din kamar bagidaje kake jinka... Tambaya nake ,shin ta ina ake shiga gidan saman Canne?...don dai kaga kasarnan kwalba ne,tekune menene allahu a 'alamu"tawatsa hannuwanta a siket din jikinta ,yaraffff.

"Mtseww ,nikike kira ma da bagidaje? Kodayake ba laifinkibane,tunda ga tayil kina kiransa teku?kaini wata jarrabtane yasameni ma,natsaya nake daka tataki?"

Juyawa yayi zai tafi,ai asittin tadank'o rigarsa."bawan Allah temaka muni kasadani da d'akin fatsime,kahin sanyin wajen nan yamaisheni k'ank'ara,bakajiyo ihun cikina daganan?....to Yaseen ko Karin safe banyi ba zumudin zanzo inci farfesu.....ko ka kwatantamun yanda kuke haye wannan wajen"

Daura hannu a goshinsa yayi kafin yafincike rigarsa dakyar
"Kedakata,wai wajena ne kikazo?, to bara inkira boy yazo yashigar dake"
yana magana yana maida numfashin wuya don tsamin jikinta ne yaji yana yin k'urin sashi amai,wayarsa yaciro yayi dialing wani number,ringing biyu aka d'auka

"kai haidar kana inane? ....ka Yiwa girman Allah kazo karabani da wata halittar....eh gamunan anan main door...tom"

k'arar k'ofar wani glass shi yadawo daita duniyarmu.bayan talula dunuyar tunani......

Takowa aliyu yayi da sauri fuskarsa fal fara'a
"A'aaah indororos ne yau a gidannamu?"

Kyar tayi mai idonta nakan sawayensa, saida ya karaso kusada su ta sauke numfashi,
"Gadanga ,karka gaya mun gurin nan ba tekubane?naga ka keto lakadan"

"Haba indo ,tayil dinne yau tazama sabo a wajen ki? "

"Ohooooo,kace mun sumuntin turawa,to ai naga wannan harda ratsin ciyawoyi,gashi kuma ina kallon idanuwa ta ciki.....shi yasa nakid'ima,gidan nakune kamar na masu cinkai..... "Umarne ya tsinketa ta hanyar cema aliyu yawuce shi.

" hmmm d'an daudu Allah yakiyaye hanya kayi mun taimakon....Allah yabaka macen kirki Irina"
Kwashewa da dariya,haidar yayi"aboki kace kazama d'an daudu"fusata yayi yajuyo a hargitse kamar zai kaimasa hanb'ari

"Kai karka gaya mun badadi kajiko?"
"Toohh,lallai katunzura dayawa,to ke indo me kika gani a jikinsa kikecemasa d'an daudu? (Yafada yana kamo hannunta sama)....sai anjima inanan shigowa.... Yanzu dai bari inji da bak'uwata"fita yayi cikeda takaicin wannan bagidajiyar indon .

Itakam indo sakin jiki tayi tafara kwararo mai surutu,ransa fal dariya badamar yi don gaba d'aya tazama kamar wata dodanniya.dakyar ya taitayota suka shiga cikin falon ,da sukazo hawa steps kuwa ,saida sukayi nisa tawaigo ,ai sai ta nemi rikitowa." Subhanallah rike nan mana"yanunama inda ake rikewa ,amma ina santsin silvern da zufan hannunta ,yasa hannunta tahau zillewa.karshe dai da rarrafe ta karasa shigewa ciki.

Alokacinne kuma mom tafito jin shiru ,bataga
K'yallin indo ba.gurus tayi tareda Rike baki "aifa namanta auta batasan gidaba...ji yanda ake taitayoki,sai kace tsohuwa"
Hussaina ce takaraso wajen
"Hmmm yaya haidar dama ka kyaleta ne,mugani juyawa zatayi ne?...ai nida Hassana na muna hangota ta window"
"Hussaina autan kikema haka....ko ,aidaidai daku take .bata bukatar atare mata"

"A'ah fatsima kefa kikejanmun raini,Sam basa ganin girmana, gadanga kadai kece mun ,anty shi yasa,nakeshimasa albarka akoda yaushe"

"Vassu kinji antyna ta kaina ni daya nama isheki,baki bukatar tadan yuyuyu" yadai lallabata suka shige ciki.don yalura ana dab da tsiyacewa itada Hussaina.




Vote
Share
Comment
[8/19, 10:14 AM] Haisahhtttttt💅🏻: *👠👠💅🏻BAGIDAJIYACE👠👠💅🏻*


*©️HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*(Home of peace, joint entertainment to educate and enlighten our readers)*



Story and written by✍🏻
Hassenart
☎️090 -659 -902 -65


*Dedication*
*pejinnan nakune 'yan k'asar nijer musamman 'yan damagaran da Agadaz.kuyi duk yanda kuka so dashi,tukwuicin soyayya🤸‍♀️🤸‍♀️🧚‍♂️*

*Ina 'yan nijar masu buk'atar biyan kudin Littafaina ,sun rasa yanda zasuyi,Ku garzayo Da shirin biyan kud'inku,donko 'Yar uwanku tabaku solution don ita tuni ma tabiya nata,karki bari abarki a baya inkin shirya Bini ta p.c*


Aradun Allah ink d'ina yafara gigir-gigir🙄,don haka ina dab da gama free pages, wainda kuka biya kunhuta,keda baki biya ba #200 ne ake biya na katin MTN sai a turama wannan number 09065990265 ,inkuma VIP ne #300.



*Free page1️⃣3️⃣~1️⃣4️⃣*

"Waikai haidar yanzu kai har zaka iya rayuwa da wannan bagidajiyar yarinyar a gida d'aya,kui using spoons da cups daya ?....h'ummm,katab'a k'arema hak'oran bakinta kallo kuwa?abu very greenish dagani baisan yanda ake gurza mai brush ba....haba gaskiya in nine wallahi daina mu'amala da komai na gidan zanyi har sai tatafi,innemi sabo kawai"

Sukuti haidar yayi batareda yatankashi ba,don shi harga Allah yana son Aisha, kuma baya iya ganin laifin ta don shi komai natama dariya yake bashi,kawai ya dauka yanda mutane ke mu'amalantarta shi yakesa take muzantasu in return...

"Abokina bakace komaiba ?"
"To mezance ,kadaisan bazan tab'a nunawa k'anwar mom ,k'yamaba....so aje magana tagaba kawai"

"OK nafahimceka,aliyu kanuna mun akwai banvanci tsakanina dakai ko ?,ai shikenan"
Azuciye yabar masa d'akin yayi ficewarsa,shi adole ya gaya masa magana
"Mtseww kahad'iyi garwashin wuta k'arewar zuciya...."
Jin shiru bai dawo d'akinba yasa yatashi ya nufi gidansu,shima.

************************
"Wohoho ya shafi ya kafi,yau wallahi zasu kashe mu da yunwa,aradun Allah banna iyawa..." Jan k'afarta tayi har kitchen d'in gidan ,iya ladi tagani tazage tana soyan plantain,wani takaici ne ya zo mata wuya ya k'ume ta

"Hod'ijam,menike gani hakane wai?, kina sane bayin Allah naji ranki da abinci kinzo kina soya ayaba,uwar me zakiyi dashi?iyeeh tambayarki nakeyi,koko silar mugunta da k'eta?...
kina cinnaro mun wa'innan 'yan micimicin idonuwan naki kamar k'wark'wata....hmmm yo gida babu dole azo nan anasoya ayaba gobema lemo zaki soya kenan ko...dake nakeyi"

Damuwane ,ya bayyana k'arara a fuskar iya ladi,batasan sanda tasoma yi mata magana tsawa tsawa fad'afad'aba

"Ke waike,wacce irin ja'ibace...kinzo kintasani gaba da sassafe kina cimun fuska?kamata nakusa jika dake zakina tsinata....to hirrrr d'inki donko inada marasa kunya irinki agida ringis,waenda zasuyi mun maganinki....
Maganar abinci kuma ki had'iyi hanjin cikinki,inbazaki iya jira k'arfe goma tayiba..."

"Caskalin kanbura'ube,nikeke zagi haka,yau zankoyama uban bakin nan naki hankali inyaso kya iya kiran me rama maki...."

Juyawa iya tayi tacigaba da suyan plantain d'inta ,irin tabarma banza ajiyarta d'innan

Cikin rashin zato tafyallota ta kafafunta ,jikake timmm!,kanta ya k'umu da kitchen cabinet, kafin k'ugunta yadaki k'asan tiles d'in wajen.

Wani k'ara ne na azaba ta k'walla,wacce batasan yafito ba.hakan Wanda saida yaja hankalin ilahiran mutanen gidan buuu,sukayo hanyar kitchen d'in,inda suka juyo k'arar

Waige waige tashigayi kamar zararriya ,can Allah yabata sa'an hango ladle agefe,dasauri tasura tasaka acikin mai d'in ta tsamo plantain d'in da tafashen mangyad'a yaroyaro,tayo bakin iya zata d'ura mata shi haba,kankaceme tuni tanemi zugin datake ji a k'eyarta tarasa, tafita a atamanin ,tana kururuwan Neman dauki

binbayanta tayi da spoon d'in, daidai sunfito sukuma da zuwan su farouk da aliyu,ai da gudu suka take masu baya.

ganin zasu kamota bata fansheba,yasa tayi watsi da ladle d'in plantain d'in mai cike da mangyad'a, tafinciko rigar iyan tabaya,daga daga tayi zata fad'i...

Daidainan farouk yazo bai saurari komaiba yashek'eta da mari.

Wani kururuwar ihu tasaki kamar zata cire masu dodan kunne
Tuni muryanta ya d'ashe,Nan tahau danna mai ashar kamar jikan maguzawa

Iya ladine datasha da k'er ta tsaya tana falaifalai da baki,tana karkad'a jibga jibgan albarkatun k'irjinta wanda suke har cikinta.tana lankwashe murya tana bashi hakuri,adole antare mata d'innan,tasamu fada.

Batai auneba saidai taji tayi kukan kura tayi caraf ta cafki nonuwarta.da duka hannayen ta biyu lilo takeyi kamar tasama jaka,dama ga abu zudun zudun kamar jarka,

kururuwa iya tashiga yi ji take kamar za'a yage mata k'irjin .

Salati da sallallami su baba me gadi suka d'auka lantai maishara kam dariyarta takeyi son ranta,don ita bata tab'a karo da irin salon fad'an indoba ,dama gashi sunada jik'ak'k'a da iya ladi.

Anyi juyin duniya tasaketa tak'i saki ,saima k'ara damk'arsu datayi uwa tasamu igiya.sukuma gasu maza ba abun su rababa,ita me rabawar kenan lantai ,tayi gefe abinta tana dariya.

Ganin ba sarki sai Allah, yasa farouk ya finciki indo tagaba,aliyu ya finciki iya tabaya

Nan iya tawatse yaraf a wajen kamar tsumma.
"Jama'a kukallanmun kirjina nonuwa na sunanan,ko sun fita?"

Indo nadak'wak'wo gula gulan idonta ta je gabanta ta tsaya tana numfarfashi,"don uwar mace tasake yi mun magana...alkur'an sainacire ma mutum hanci ...kinyi sa'a ba wuk'a kusane... Dakin sha yanka,nid'in nan dakike gani cikakkiyar 'Yar dabace,ina jiran yaran naki darabon lakhira tayi bak'i"

"Lamarin ashe babbane,tabbas kwalwar yarinyar nan ba lafiya" cewar farouk kenan cikeda al'ajabi

Ganin shikaran kansa ya jinjina ma al'amarin yasa ma'aikatan gidan dayazo kowa yafara ja baya yina sulalewa,kar tama hango fuskar shi ,bugun jujunta,nagaba tayo kansa.











I needs more and more comments so,
Vote
Share
Comment
[8/19, 10:15 AM] Haisahhtttttt💅🏻: *👠👠💅🏻BAGIDAJIYACE👠👠💅🏻*


*©️HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*(Home of peace ,joint entertainment to educate and enlighten our readers)*


Story and written by
Hassenart
☎️090 -659 -902 -65



Happy marriage life💞
Nafeesah,Allah ubangiji yasanya albarka acikin auranku,yakauda duk wata fitina,yabada dawwamamiyar zaman lafiya,da 'Karin k'aunar juna,yakawo zuri'ar da al'ummar annabi (s.a.w) zasuyi alfahari dasu.
Congratulations dear🤝🏻



*Last

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login