Showing 1 words to 3000 words out of 18004 words

Chapter 1 - BOKANYA

Start ads

05 Sep 2025

74

Middle Ads


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[26/10 à 08:37] MRS SADAUKI 💫: *BOKANYA👽🌪️🌪️🌪️*
```gajeren labari```



*MRS SADAUKI 💫✍🏻*

SADAƘARWA ga *ASSOCIATION DES ÉCRIVAINS MADUBI🇳🇪*

FCWA☀️

```Alherin Allah ya kai ma duk inda Marubutan Nijar🇳🇪 su ke tare da masoyansu😍 ina alfahari da Ƙasata banda tamkar ta```

*🚷Duk mai buƙata ya fara daga farko don kar sai na yi nisa ya yi mini magana ya na so ba kuma zan tura ba, sannan kar ku yi mamaki billahil azim duk groupe ɗin ba a comment ba zan ci gaba da posting ba.Zan yi amfani da sunayen jaruman na book ɗin CIKIN ALJAN saboda sun yi mini daɗi*😙


Page 1


Ina mutanen da su ke cewa ba su yarda da tsafi,asiri ko siddabaru ba? To ku matso na baku labarina.A da can farko in ana maganar da ta shafi sihiri sam ba na yarda,a cewa ta ma shirme ne da sa ma kai abu shi yasa lamarin ke samun wanda ya yarda.



Sunana Bahijja,mu biyu kacal iyayenmu su ka haifa.Anty Murja ita ce babba sannan Ni ,mun taso cikin maraici uban wanda jama'ar gari su ke ce-ce-kuce akan Umma ce ta kashesa saboda ana zarginta da maitar cin maza.Kamar yadda Umma ta bamu labari ta ce tun kafin ta auri mahaifinmu ta auri maza har biyu sun rasu,sannan shi ne kawai su ka haihu da shi.



Yadda a unguwa ake tsangwamar mu ya saka mu ka bar garin Maraɗi wanda shi ne garinmu na haihu mu ka koma Tillabery.Lokacin shekaruna goma sha uku,kuma daga nan ne wasar ta soma.Shinkafa da wake Umma ke yi na sayarwa,wannan ya sa mutane iri-iri kan shigowa gidanmu.
A nan ne na ci karo da Aliyu matashin yaro mai shiga rai,ba zan manta ba ranar da Aliyu ya nuna ra'ayinsa a kaina ina zaune kusan Umma ina cin abinci.


Wata kalma da ta furta ya saka ni fara ƙwanƙonto a kan shin ko dai dagaske Umma *BOKANYA* ce kamar yadda jama'a ke faɗa?
"Akwai haske sosai cikin aurenku da Bahijja,tun ranar farko da ka fara zuwa na ga hakan sai da na bar ka ne ka furta da kan ka.In dai a shirye ka ke to ka aiko magabatan ka na ba ka Bahijja" wannan shi ne furucin Umma,wanda ya saka ni cikin tantama da cakwakwalin tunanin ta yaya aka yi ta san Aliyu da Ni za mu yi aure kamar yadda ta furta? Mahaifiyata ce ba zan iya yi mata wannan tambayar ba saboda ina ganin girmanta sosai kamar yadda ƙaunarta ke cikin ɓargon zuciyata.



Na manta ban faɗa maku ba, Umma na gama furta haka Aliyu ya shiga jero godiya haɗi da tabbatar zai aiko magabatan.Furucinsa ya dawo da ni daga duniyar tunani,tamkar zarar bunu haka na furta kalmar "ba ni son ka!" Sai kuma na tashi na shige ɗaki.


Ƴan magana su kan ce ƙarfe da zafi-zafi ake bugunsa,bayan sallar magrib sai ga Aliyu ya dawo shi da wata dattizuwa wai sun zo neman aurena.
Ranar na ga ikon Allah yadda Umma ta tarbeta su ka zauna su na tattauna lamarin.
Bayan ƙyaure na laɓe ina sauraren su.
"Aliyu Maraya ne mahaifinsa ya rasu ƴan uwan uban shi kuma sun tsana mu wannan ya saka na zo da kaina,amman in shaa Allah cikin satin nan Babban yayansu zai zo sai ku yi magana " Dattizuwar ta faɗa,Umma ta ce "to babu matsala ai ita ma Bahijjar mahaifinta ya rasu ba ta da kowa sai ni"
"To tun da haka ne bari na fitar da kuɗin sadaki na bada tun yanzu,Allaso ranar da Yayan shi ya zo sai a ɗaura auren" Umma ta ce "da sauri haka? "
"Eh bai komi ai kin san Aliyu Autana ne wannan ya saka ya na gaya mini na shigo mota na zo"
"Wane gari ku ke?" Umma ta tambaya,ta bata amsa da "Kwalo" daga can inda na ke na waro ido,cike da mamaki ina leƙon matar ta ƴar hudar ƙofa.
Kun san wani abun mamaki? Hum! Duk da matar nan ta na zaune cikin ƙarancin haske amman hakan bai hana idonmu haɗuwa cikin na juna ba.
Ido huɗu mu ka yi da ita,haka kawai gabana ya faɗi na ji sam matar ba ta yi mini ba kamar dai Ɗanta.


Bayan tafiyar su na fito,Umma da Anty Murja sai ƙirga kuɗi su ke cikin murna.Gefe na koma ina jan ajiyar zuciya gami da kuka, Umma ta yi biris ta ƙi takan ni sai Anty Murja ce ta ce "amaya kukan mine ne ki ke?"
"Anty Murja wlh ban son shi,kuma garinsu fa Kwalo inda ke da Mayu wlh...." Ban kai ƙarshe ba Umma ta ce mini "rufe mini baki,auren ki da Aliyu tuni an tsara shi tun can farko.Kar ki ɗaga mini hankali don babu fashi,tashi ki koma ciki" Umma ta kore ni a doli na bi umarnin ta.




Abu kamar wasa sai gashi an ɗaura mini aure da Aliyu, duka-duka ko sati biyu ba yi ba da fara maganar kamar wata ɗiyar laka.

Tun safiyar yau gabana ke faɗuwa, wannan kuma bai hana Umma da Anty Murja shirya ni ba tsaf don tafiya ƙauyen su Aliyu gaishe da mahaifansa kafin mu tare.
Ban san Aliyu mai kuɗi ba ne sai da ya zo da mota ɗaukata,gidan gaba na shiga mu ka kama hanya.Shi kaɗai ke hirarsa ban kula shi har mu ka isa wani Ƙauye,bai da wani duhu sosai don akwai wutar lantarki sai dai ba ta yi yawa ba.
Yawancin gidajensu duk na laka ne,ƙwarara ne ke na siminti kamar dai na su Aliyu.


Hannuna Aliyu ya riƙe gam,kafin mu shiga cikin gidan.Taɓi matan da yaran su ka fara su na waƙa da wani yare wanda ban gane mi su ke nufi ba.
Tsakiyar tabarma su ka zaunar da ni su na mai yin Yaren,ɗaya daga cikin su ce ta ce "ba ka jin Zabarmanci?" Kai na gyaɗa mata.
Aliyu ya ce "ina Hajiya?" "Ya na cikin ɗaki"wannan matar ta basa amsa.
"Bahijja tashi ki shiga ga ɗakin Hajiyar can ina zuwa" Aliyu ya umarce ni haka na tashi na nufi ɗakin na yi sallama har uku ba a amsa ba kawai na kutsa kai.



Faɗuwar gaba,tashin hankali,tsaka mai wuya duk su ka sauko mini lokaci guda saboda abin da idona su ka yi tozali da shi......




Please share
[26/10 à 08:39] MRS SADAUKI 💫: *BOKANYA👽🌪️🌪️🌪️*
```gajeren labari```



*MRS SADAUKI 💫✍🏻*

SADAƘARWA ga *ASSOCIATION DES ÉCRIVAINS MADUBI*🇳🇪

FCWA☀️



Page 2


Jikina ya ɗauki rawa ganin Hajiya sanye cikin fararen kaya tamkar wata fatalwa,a gabanta ɓeraye ne kitikir-kitikir magana su ke yi ma juna tamkar yadda mutane ke hira.Abin da na fahimta Hajiya ba ta san na shigo ba,duba da yadda ta maida hankali su na hirar su cikin kwanciyar hankali.Na yi baya zan fita tsabar rawar jiki na buge wata langa ji kake kwarammmm! Nan fa na ga magie a idona ɓerayen kamar ƙyaftawar ido su ka ɓace yayin da kayan Hajiya su ka sauya daga luwahi zuwa kayan atamfa.
A wannan lokacin in an ce na fara yin fitsari a wando kar ku yi gardama,dakyar na saita kaina na ce "Hajiya ina wuni Aliyu ya ce na zo" Hajiya ta washe baki ta na cewa "ah! Ah! Bahijja ce? Zo nan Ƴata" ta buɗe mini hannuwanta.Ya zan yi? Doli na shiga ta rungume ni,tsawon minti biyar ta ƙi sakina sai wasu abubuwa ta ke furtawa wanda ba su da kan gado.
Kaina tuni ya fara juyawa,can kuma na ji ya sara mini yayin da idona su ka fara yin nauyi su na lumshewa amma ba bacci na ke yi ba.
Kwantar da ni ta yi kan capet,ta fara yin surkule abin da na fahimta ita ta ɗauka ina bacci ne sai dai kash tsafinta bai yi galaba sosai a kaina ba.
Duk da ban san manufarta ba amma na fi zargin burinta in so Ɗanta ne duba da yadda ta ke ta kiran sunan Aliyu.
An ɗauki lokaci kafin ta ƙyale ni,ba a fi minti biyu ba Aliyu ya shigo.
"Hajiya baƙuwar ta ki bacci ta yi kuma?" Ya tambaya ya na kallona, "eh wlh mun fara yin hira kamar yadda na yi ma alƙawari sai kuma ta ce kanta ke ciwo ƙila ko gajiya ce" ta ba shi amsa.
"Hajiya kin ce za ta so ni da zarar kun yi magana, Allah sa to ta yarda" Aliyu ya faɗa kamar zai yi kuka.
"Hum! Kai dai ba ka aure ta"cewar Hajiya .
"Ina so ya kasance mu na son juna ta yadda za mu kula da junanmu sosai,in tarairaye ta.Ina son Bahijja fiye da raina Hajiya ,in zama da ni ba tare da soyayyata ba a zuciyarta ba zan samu yadda na ke so ba"


Kar ku manta na gaya maku idona biyu ban yi bacci ba kamar yadda su suke tunani,hakan yasa na ga fuskar Hajiya ta sauya ta yi baƙi ƙirin ta cika da hassada da kuma kishi ƙarara.
"Sai ka ce wata ɗiyar gwal Auta duk ka bi ka rikice a kanta,ni wlh na fara ma jin ta fita raina"da sauri Aliyu ya rungume mahaifiyarsa ya na cewa "haba Hajiyar Aliyu kar ki ce haka in ba ki so Bahijja ba wa zai so ta? Don Allah ki bar faɗar haka" ina ganin lokacin da Hajiya ta ɗora hannunta kan zuciyar Aliyu sai yamutsa fuska ta ke,can ta taɓe baki ta ce "duk soyayyar ce haka?"
Aliyu ya sauya zancen da "ina abincin da aka girka mana? Ya kamata a tashe ta mu ci sai na mayar da ita" amsar da Hajiya ta ba shi ce ta saka ni yin tari ban shirya ba,duk suka maido hankalinsu gare ni.


Kwanciya na gyara don ban so Hajiya ta fahimci idona biyu.
"Hajiya ki ka ce mi?"
"Eh Bahijja ta zo kenan sai dai a kawo kayanta ba za ta koma can ba"ta sake jaddada maganarta.




Zuciyata sai bugawa ta ke da ƙarfi,ga mamakina sai na ji Aliyu na cewa "Yauwa Hajiyata kamar kin san haka ne a cikin raina" "bari na zuba ma abinci ka ci tun dai ita bacci ta ke" Hajiya ta zuba masa abinci sai ƙamshi ke tashi.



Ya na ci su na hira kai kace wasu masoya yadda su ke masayar kalamai.
"Tun da yanzu ka yi aure ai na san shikenan ba za a sake kula da Hajiya ba,ƙila ma in ku ka tafi can Niamey ba kullum za ka rinƙa kira na ba"
"Haba Hajiya ki bar cewa haka,aiki bai hana ni kula da ke ba sai aure? Bahijjar ma da ba ta so na" Aliyu ya faɗa.
"Ai kai ka na son ta"
"Sosai ma kamar na mutu"...... Tun daga nan ban sake sanin abin da su ka zanta ba saboda baccin gaske da ya ɗauke ni.




A cikin baccina na yi mafarkin Hajiya na zuba mini magani a abinci,yayin da ɓerayen nan ke taka rawa su na cewa "yau za mu ci daɗi! Naman amarya zai yi daɗi,ruhi! Ruhi! Ruhin amarya" yadda su ke rawa kawai ya tabbatar da su na cikin farin ciki.A cikin mafarkin sai na ga kaina kwance kan tabarma,Hajiya ta zo zare ruhina ta ɗaga yatsunta kenan za ta luma mini na farka a tsorace.
Da fuskar Hajiya na fara cin karo idonta ƙur kaina ta na kallona,dakyar na ari jarumta na tashi zaune ina miƙa tare da ambaton Allah.
Da sauri Hajiya ta matsa gefe,abinci ta miƙo mini ta na kallona.



Na girgiza kai na ce "ban jin yunwa" ba ta ƙara cewa komi ba ta ajiyesa tare da fita.Sai ga ta sun dawo da Aliyu,cikin bayar da umarni ya ce na ci abinci.Tamkar wacce ya sihirce haka na ɗauki abincin na fara ci zuciyata na bugawa,sai bayan na gama ne na fito.
Da sauri na waro ido ganin Anty Murja,da murna ta na ruga na rungumeta.
Ta na dariya ta ce "to sake ni kar ki kayar da ni" "yaushe ki ka zo?" Na tambaye ta,ta bani amsa da "zuwa na kenan,kayan ki ne na kawo miki zuwa jibi zan koma mu je na gaida Hajiya "


Na yi mata jagora ta je ta gaida Hajiya ,da za mu fita ne Hajiya ta ce "Bahijja ki kaiwa Akuwa sauran abincin nan da ki ka ci" ban ce komi ba na ɗauki plate ɗin wanda na ga tun shigar mu Anty Murja ta ƙura ma ido.



Akuwa guda ce tal a gidan,wacce tun da aka haife ni ban taɓa ganin irin ta ba.Akuwar baƙa ce ƙirin gashin jikinta har wani zazzalowa ya yi tsabar yawa,ga kuma wani uban gemu kamar bunsuru.
Gabana ya faɗi ganin Akuwa na kallona tamkar mutum,abinci na ajiye mata a gabanta.Ta sunsuna sannan ta ɗago ta kalle ni,kuka ta yi wanda ya karaɗe duka gidan.Da sauri Hajiya ta fito ta na riƙe zane,akuwar ta kalla ta dube ni sai ta yi ƙyaci kafin ta ce "Bahijja biyo ni" ban yin jinkiri ba na take mata baya har ɗakinta.



"Ungo sha" ta miƙo mini wasu ruwa koraye cikin budo,cikin tantama na kalleta wanda ita kanta ta ga alamun kamar ban yarda da ita ba."Ko sai na kira Aliyu ?" Ta faɗa ta na haɗe fuska,na karɓa na sha tamkar jira ake na fara kelaya amai.


Kamar raina zai fita haka na ke ji,duk abin da ke cikin cikina sai da na amayar da shi.Abin da ya fi ɗaga mini hankali yadda na ga tamkar wasu hallitu ne na ke amai don har motsi su ke,kamar almara haka aman ya ɓace ɓat ba tare da an kwashe ba.
Hajiya ta ja ni zuwa wani ɗaki,nan na tarar da Anty Murja na ta gyaran shi.Kwanciya na yi saboda na gaji sosai har jiri na ke gani.


"Mutane ba su da tausayi daga zuwanta yau har an samu masu yi mata barbarɗe,shi yasa wasu su ke cewa gwara kishiya da kishin sarmi(😂matar Magaji da matar ƙane kishin sarmi ko yaya ake cewa?)" Cewar Hajiya ta na kallon Anty Murja.
"Ai haka ne dama wani sa'in gwara wacce ku ka haɗa miji da ita"
"Ki bari yarinya balle ita Bahijja an ga matar Autana ce,kin san kaf cikin Ƴaƴana na fi son shi" ina jin Anty Murja ta kama ma Hajiya ana ta zagin matan Yayun Aliyu.



Bayan fitar Hajiya ne Anty Murja ta shafi fuskata ta ce "baiwar Allah har kin rame,mugaye mun bar su ga Allah.Ai tun shigowa ta na ga baƙin hayaƙi na tashi a abincin har addu'a na ke Allah sa dai ba ki ci ba,ashe-ashe..." Na katse ta da tambayar da ta sa ta yi saƙo.


"Anty Murja don Allah ta yaya ku ke ganin abin da idon mutane ba sa gani ke da Umma? Siddabaru ne ko tsafi?"
Ba ta tanka ni ba sai ma ta ci gaba da goge ledar ɗakin,na lumshe ido ina tunanin lamarin da ya faru tun da ga zuwa na har izuwa yanzu.


Na ja ajiyar zuci ina mai jin tsanar surukata na ratsa ɓargo da jijiyar jikina,a zuci na ce "wato raina mini hankali za ta yi ko mi? Ta na nufin ban gane duk makircinta ba ne da har za ta laƙa ma matan Ƴaƴanta? Tabbas Hajiya ko tantama babu *BOKANYA* ce! Waccan akuyar ma ban yarda da ita ba doli na zurfafa bincike"....



Don Allah share🫶🏻
[27/10 à 14:42] MRS SADAUKI 💫: *BOKANYA👽🌪️🌪️🌪️*
```gajeren labari```



*MRS SADAUKI 💫✍🏻*

SADAUKARWA ga *ASSOCIATION DES ÉCRIVAINS MADUBI*🇳🇪


FCWA☀️


Page 3



Kwana biyu Anty Murja ta yi a nan Kwalo kafin ta tafi.Kullum tare mu ke kwana da ita hakan yasa hankalina ya ke a kwance,sai dai yau goɗe-goɗe Aliyu ya shigo wai a tare za mu kwana.


Bisa tapis na yi kwanciyata,juyin duniya ya yi na je na kwanta kusa da shi na ƙi.A doli ya shafa mini lafiya,ina ganinsa sai faman juyi ya ke kan gado ya na riƙe ciki ni kuwa ko a kwalar rigata.


Washegari bayan sallar asubahi,Aliyu ya ɗana

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login