Showing 6001 words to 9000 words out of 18004 words
Na waro ido na ce "Umma shaf na manta wlh ,kin ga fah yanzu na gama haɗa abincin kumallo"
"In dai ba ki ci komi ba tun tashin ki to ki miƙe da azumi sannan ki yi Azkhar ɗin da na ce"
"To Umma in shaa Allah ! Ina Anty Murja?" Na tambaya , Umma ta bani amsa da "ta yi baƙi ne" "yanzu da safiyar nan?" "Hum! Bahijja ba za ki gane ba,masu neman magani" ban fahimci maganarta ba haka mu ka yi sallama.
Almajiri na baiwa abincin kafin na zo na zauna na fara zikirori da addu'a,haka na wuni aikin nan har marice ya yi.Ina tunanin inda zan samu ƙanƙara wacce zan sha in an kira sallar magrib Aliyu ya shigo,na miƙe da murna zan tarbesa idona ya sauka cikin na Hajiya wacce ke biye da shi a baya.......
Please share
[29/10 à 10:08] MRS SADAUKI 💫: *BOKANYA👽🌪️🌪️🌪️*
```gajeren labari```
*MRS SADAUKI 💫✍🏻*
SADAUKARWA ga *ASSOCIATION DES ÉCRIVAINS MADUBI*🇳🇪
FCWA☀️
Page 5
Wata juriya da dakiya na aro ma kaina,yi na yi tamkar ban gan ta ba na yi tsalle na laƙanƙame Aliyu "Masha Allah barka da zuwa mijina ya jikin Hajiya da sauƙi?" Na tambayesa ina mai ƙara riƙesa.
Dakyar ya sauke ni a ƙasa ya ɗan sosa ƙeya ya ce "tare fah mu ke da Hajiya!Ba ki gan ta ba ne ko mi?" Ya kauce ta yadda zan ganinta da kyau.Na waro ido na ce "laaa! Ai na zata gizo ta ke min kamar yadda ta saba! Hajiya ya jiki? "Na yi tambayar ina sakar mata wani murmushi.
A cikin idon Hajiya na hango zallar takaici da baƙin ciki,sai da Aliyu ya ce "Hajiya ba ki ji ta na miki ya jiki ba?" Sannan ne Hajiya ta ce "au! Daga nan tsaye zan amsa ba za a bani gun zama ba?"
"Wace ni Hajiya!? Ke da gidanki wa isa ya yi hakan? Bari na ɗauko miki kujera" na faɗa ina shirin wucewa in ɗauko mata kujera kawai sai ji na yi Hajiya ta bangaje ni.Ki gizau ban yi ba sai dai na ji wani mugun shock ya ratsa ni tamkar wuta ta raɓo ni sai dai dai ko 30s ba a yi ba ya fita daga jikina.Yadda mu ke kallon juna cikin ido na ke hango tsantsar mamaki a tattare da ita,ƙila ganin babu abin da ya same ni.
Aliyu ya ja hannunta su ka shiga ɗaki,ni kuwa tsaye na yi ina tunanin miye nufin Hajiya? Na maida lamarin gefe na leƙa waje.Wani shago na hango nan kusa da gidanmu,na ga har da frigo/frigine da sauri na fita na sawo ƙanƙara.Tuni an fara kiraye-kirayen sallah,a tsakar gida na tarar da Aliyu na alwala a yadda ya haɗe rai ya tabbatar min fushi yake da ni.Ban kula shi ba na shiga ɗaki,a zaune na tarar da Hajiya ta yi ɗaiɗaya kan kujera.Waje na samu mai kyau na kwankwatsa ƙanƙarar sannan na zauna bayan na matso da kayan buɗe baki.
"Ya Rabbil alamen ka tsarkake min zuciyata da dukan wani saɓon Allah,ka kare ni daga sharrin masu sharri, Ya Allah ina neman tsari daga sharrin aljanu da mabiyansu,da duk masu mugun nufi akanmu.Ya Allah yadda na shigo wannan gidan da aure Allah ka sa mutuwa ce silar fitata daga gare shi! Ya Allah ka azurta mu da zuri'a ɗayiba maza da mata masu farar zuciya.A ƙarshe ya Rabbi ka sa mu zame ma maƙiyanmu ciwon ido amen!" Ina gama jero addu'o'ina na yi addu'ar shan ruwa.
Bayan na gama na je na yi sallah,daga inda na ke a can bedroom ina jin shashekar kukan Hajiya yayin da Aliyu ke faman tambayar ta lafiya.
Na shafa addu'a na fito ina cewa "subahanallah Hajiya lafiya ko jikin ne?" Ba ta bani amsa ba sai harara da ta banko min.
"Auta ka tashi ka mayar da ni garinmu tun da matar ka ta ce ba ta son zamana" Hajiya ta na gama faɗar haka Aliyu ya yo cikina da faɗa ta inda ya shiga ba ta nan yake fita ba.
Nasihar Umma ta sake faɗo min hakan yasa na duƙa har ƙasa na ce "don Allah Hajiya ki yi haƙuri in na ɓata miki rai,Aliyu wlh na fi kowa murnar Hajiya ta zauna nan ƙila dai ba ta fahimta ba ne.Yanzu gaya min duk abin da ki ke so" Aliyu ya sauke ajiyar zuciya ya ce "tashi Bahijja sai dai don Allah kar ki sake,kin ga Hajiya ta tsufa ta na buƙatar kulawarmu sannan ba wata isassar lafiya gare ta ba" na gyaɗa kai na ce "to in shaa Allah mijina duk abin da ka ce haka za a yi,bari na je na gyara mata gun da za ta kwanta" ina gama faɗa na je na gyara ma Hajiya ɗaya ɗakin har da saka mata turare.
Abinci na zuba mata da ruwa da komi tamkar basarakiya,ta na ci ta na ɓata fuska kamar an yi mata doli.Na kira Umma tun kafin na kai ga gaya mata Hajiya ta zo ta ce mini "ki kula da kyau ki yi taka tsantsan da matar nan saboda ta yi mugun shiri ita da ƙawayenta,ki ƙara addu'a gobe ma ki tashi da azumi" na ja ajiyar zuciya na ce "to Umma zan yi,amma ni gaskiya ban so ta ci gaba da zama nan"
"Kar ki ce haka saboda da zarar kin nuna ba ki so to ta ci galaba kan ki.Kar ki nuna mata komi ki zama doluwa tamkar ba ki san komi ba,in shaa Allah zan tura miki maganin wanka da wanda za ki rinƙa shafawa" na yi ma Umma godiya na kashe waya.
Da dare mu na kwance da Aliyu na ke shaida masa gobe zan tashi da azumi,yi ya yi kamar bai ji ni ba har sai da na sake maimaitawa."Yanzu saboda Allah Bahijja azumin mine ne ki ka tsiri yi? To ko ma dai mi za ki yi kar ki manta sai kin yi girkin safe da na rana da kuma dare.Babu wanda zai sani fita ina sayo abinci kamar wani gwabro"
Na rungumesa ina mai cewa "zan yi mana ko saboda Hajiya! Gaya min abubuwan da ta fi so sai na rinƙa girkawa ina son yi mata surprise ka ga za ta ji daɗi sosai" Aliyu ya dube ni cikin ido ya sakar min murmushi kafin ya fara sumbatata.
Addu'ar da ya saba yi kullum in za mu kasance ya fara karantowa ba tare da ya kashe hasken ɗaki ba,ido huɗu mu ka yi ni da wasu idanu uwanda ba su da fuska da sauri na janye daga garesa na kashe hasken ɗakin.
Washegari na so tashi da azumi sai dai yadda idona suka matsa min da ciwo ya sa na ajiyesa dan doli.
Duk yadda za ku iya ƙiyasta yadda nake ji to ya zarce haka,sam ko idona ban iya buɗe wa.Wani irin raɗaɗi haɗi da tsikara suke min,Aliyu shi kansa ya yi mamaki.
Ina zaune kan kujera ta fito hannunta na ji ga haɓata yayin da Aliyu ke ƙoƙarin buɗe min ido,da sauri na jimƙe su gam."Ki buɗe Hajiya ta saka miki magani " cewar Aliyu ,na girgiza kai hawaye na min zuba na ce "a'a ban so ka kira min Umma" "mi yasa ki ke da taurin kai Bahijja? Wannan maganin ya na yi sosai tun ina yaro Hajiya ta taɓa saka min irin sa"
Na fashe da kuka ina kiran sunan Umma,a can cikin madubin idona abubuwan ban tsoro ne iri-iri ake wano min sai dai na gwammaci haka kan Hajiya ta zuba min maganin da ba san na mine ne ba.
Ta yaya? Ya aka yi? Ban sani ba,muryar Anty Murja ce ta ratsa falon.Ina jin haka na tashi zumbur,ina jin ta na gaishe su Aliyu kawai ya amsa yayin da na ji takun sawun ƙafafun Hajiya haɗi da ƙyaci.
Anty Murja ta jawo ni a jikinta ta rungume,ban sani ba ta hanyar tsafi ne ko siddabaru kawai dai na ji idona sun daina ciwo kamar ɗaukewar ruwa.
Na ware su kan fuskar ƴar uwata ɗaya tilo,cikin idonta na ke kallo inda a nan take wani haske ya fito daga garesu ya shiga cikin nawa.Har wani Flou na gani kafin na dawo ras,kun san wani abin mamaki? Hum! Hajiya ce ta fito da jakar kayanta wai Kwalo za ta koma.
Aliyu na faman ba ta haƙuri amman ta ƙi a doli suka fita tare,Anty Murja ta saki murmushi kafin ta shafi kumatuna ta ce "zan koma kar ta ga na jima" kafin na kai ga tambayarta ta juya baya ta fice.
Da sauri na fito amman wayam,har ƙofar gida na leƙa amma ban ga anty Murja ba.Wayata na ɗauka domin kira sai dai babu kuɗi,ina nan zaune jingum dabarar cin bashi ya faɗo min.Wayar Umma na kira sai dai har ta gama ringing ba ta ɗauka ba,haka ma ta anty Murja.
Tun da Hajiya ta tafi ita da Aliyu ba su sake dawowa ba,shi ma ɗin ya na can garin wai ciwon Hajiya ya ƙara rikicewa.Ban wani damu ba saboda sam matar ba ta yi min ba, ɓangaren su Umma kuwa da na gaya masu abin da ya faru sai suka yi saurin kawar da zancen.
Ina kwance ina game a waya na fara jin tashin zuciya,haka na fara daurewa can kuma sai amai.Maricen ranar sai ga Aliyu,da ya kai ni asibiti gwajin farko aka tabbatar ina da ciki.
Tsabar murna Aliyu sai da ya rungume ni,haka mu ka dawo gida nan ya fara nuna min tsantsar kulawa.A kullum sai ya kira Hajiya da ya tambayeta jiki sai ta ce babu sauƙi a ƙarshe ta fara yi masa kuka da magiyar ya dawo kusa gare ta.
"Aliyu ba fa zan koma Kwalo da zama ba,in ka gaji da ni to kai ni gidanmu.Ba zan je garin da ake firgita ni ba,to wai ma in mu ka je mu za mu bata lafiya?"
"Bahijja in ke ba za ki je ba ni zan je! Saboda Hajiya uwata ce ni ta haifa ba ke ba ko ma *BOKANYA* ce ina son aba ta"
"Au ! Yanzu ka yarda da maganar Bokancin? To madallah tun da har ka gane.Lokacin da ina Kwalo babu irin abin..." Ban kai ƙarshe ba ya sharara min mari ya na huci tare da nuna ni da yatsa "Bahijja duk yadda na ke guje miki sai kin san yadda ki ka yi kin ɓata min rai.To daga yau ki rubuta ki ajiye ni Aliyu ban sonki ban ƙaunar ki kuma wlh yau sai kin tafi gidan ku sakin ki zan yi" ya yi maganar ya na mai ɗauko takarda da abin rubutu.
Wata muguwar dariya na ɗauka tamkar mahaukaciya kafin na kama wuyan Aliyu na shaƙe na ce "ku kun yi kaɗan akan ku sa Aliyu ya sake ni,wacce ta aiko ku ma ta kasa ne to ku je ku ce mata ta sake sabon shiri wannan bai yi ba" wani baƙin hayaƙi ya fita daga bakin Aliyu nan ya fara yin tari.
Kallona ya yi ya ce " mi aka yi Bahijja wannan kallon na mine ne?" Shiru na yi ,sai kuma na basar na ɗauki madubi da zumar shafa hoda don na rantse da Allah yau sai na tafi Tillabery gun Umma.
Da sauri na saki madubin jikina na rawa,kun san mi na gani? Fuskar Anty Murja kan fuskata.......
Ga masu ra'ayi book ɗin nan 200 ne kacal duk wacce ta shirya biyan kuɗin karatu ta yi min magana ta WhatsApp +22795045822
[29/10 à 17:41] MRS SADAUKI 💫: *BOKANYA👽🌪️🌪️🌪️*
```gajeren labari```
*MRS SADAUKI 💫✍🏻*
SADAUKARWA ga *ASSOCIATION DES ÉCRIVAINS MADUBI*🇳🇪
FCWA☀️
Page 6
Aliyu ya matso ya ce "Bahijja ke ma kin ga abin da na gani cikin idonki ko? Wlh har sai da na ji tsoro" guntun madubin na ɗauko na sake dubawa a karo na biyu.
Wannan karon fuskata na gani sai dai can cikin ƙwayar idona wani birbuɗin launin kore ke ɓacewa a sannu tamkar hayaƙi.Na lumshe ido zuciyata na ɗan bugawa Das!Das tamkar wacce ta yi arba da mutuwarta.
"Bahijjana ???" Aliyu ya faɗa ya na rungumo ni,cikin ƙirjinsa na shige ina sauke wanin gwaron numfashi kafin na ce " Please ka kai ni gida gun Umma ina son yin magana da ita mai muhimmancin sannan don Allah mu tashi daga wannan gidan tsoro ake bani" bayana ya shiga bubugawa tamkar wata Baby.
Cikin so ya yi min magana wacce na ji ta har tsakar kwanyata "in shaa Allah Babyta duk abin da ki ke so shi za a yi,bari na kai ki gun Umma kafin ki dawo zan kama wani gida dama na sa ayi mana sabbin kayan ɗaki.Gaya min sai mi kuma ki ke so?" Na ɗan janye daga jikinsa ina zagaye cikinsa,ido cikin ido mu ke kallon juna.Ban sani ba ko na fara son Aliyu ne ko mi,kawai dai na ji wani shauƙi ya fizge ni.Ɗigirgire na yi ta yadda zan ƙara tsayi na sumbaci laɓansa,a yadda ya ke dubana ya tabbatar min abin ya zo masa a ba zata.
Tattausan murmushi ya sakar min haɗi da jawo ni ya haɗe bakinmu.Sumba mai tsayawa a zuciya ya yi min kafin ya ja ni zuwa mota,sai da ya saya mini snack sannan mu ka kama hanya.
Yau ji na nake wata sabuwar halitta,tsakanin Niamey da Tillabery babu wani nisa sosai hakan yasa mu ka isa cikin ɗan lokaci.Da mamakin matan da na tarar tsakar gida birjit na shiga ɗaki ina sallama, Umma ta fito ta na bayyana murnar ganina a fili.
Bayan na gaisheta na je na yi ma Aliyu iso,cikin falo mu ka zauna Umma ta kawo mana ruwan sanyi.
"Umma su uwancan matan mi su ke yi? Ko biki ake?" Na tambaya.
"Masu neman magani ne kin Murja ta fara bada taimako,to wasu ma can ƙila ba za su samun damar ganinta ba"
Dariya na yi irin ta in abu ya baka mamaki "Anty Murjar ce ke bayar da magani? Hhh! Don Allah Umma bari bani dariya.To wane karatu ta yi da har za ta zama likita?"
Maimakon Umma ta bani amsa sai ta mayar da hankalinta kan Aliyu su ka fara hira,tashi na yi na fita.
Wata ƴar buka na gani ta zana,sai da na yi dariya kafin na nufi ɗakin na shiga.Anty Murja ce a zaune ta kama kan wani yaro sai buga masa wutsiyar doki take,tsaye na yi ina kallon ikon Allah.
Kuka yaron ya fara kafin aljanin jikinsa ya yi magana,a ƙarshe dai Murja ta baiwa uwarsa magani su ka fita.
Ta dube ni ta ce "sai yanzu ki ka ga damar zuwa? Ina shi Aliyun?"
"Anty Murja yaushe ki ka zama *BOKANYA* ban da labari? Ita wannan wutsiyar ta mice ce?" Na tambayeta ina mai kai hannu zan ɗauka wata irin wuta ta fito fatseee.
Na zabura na yi baya ina waro ido,"kar ki take mata Ɗa" cewar Anty Murja ta na mai nuna bayana.Ihu na yi don kuwa ni ban ga kowa ba,dariya ta shiga yi min kafin ta nuna min waje na zauna.
Bayan na yi zaune ne ta ce mini "Bahijja ita rayuwa da ki ke gani wani sa'in doli ce ke sa mutane yin abin da ba daidai ba.Ni magani na ke bayarwa ba na duba sai in ya zama doli,kuma aikina na yi kyau shiyasa ma ki ka ga mutane na rububina"
Kai kawai na jinjina amma fah ban yarda ba, Anty Murja ta saki murmushi ta ce "leƙo ki gani" ta yi min nuni da ƙwarya gabanta wacce ke ɗauke da fararen ruwa.
Na duƙa na kai fuskata ina kallo,na ɗan waro ido ganin Hajiya ta bayyana,kamar ranar farko yau ma da fararen kaya sai dai wannan karon a bakin wani kogi ta ke a tsaye.
Idonta a rufe,ta riƙe baƙin Zakara kafin ta guntule masa kai jini ya fara zuba ya na tsarta cikin kogi .Abu kamar almara haka na ke kallonta kafin Anty Murja ta shafi ruwan duk komi ya ɓace.Murya na ɗan rawa na ce "Antyna don Allah mine ne Hajiya ke yi a nan? Allah sa dai ba raba ni da mijina za ta yi ba" wani kallon ƙasa-ƙasa Anty Murja ta ke yi min ba ta ce komi ba sai miƙewa ma da ta yi.
Baya ta juya min sannan ta ce "Bahijja soyayyar da Aliyu ke yi miki ce ta fi ƙarfin tunani,ba dan a gabana aka yi komi ba da na ce asiri ki ka yi masa.Kaf ɗiyan Hajiya ita ta ke juyasu su da matansu,ke ce ki ka gagareta.Ta bayar da ruhinta ga aljannu,sun gindiya mata sharaɗin har abada ba za a haifi namiji ba cikin zuri'arta domin a cewarsu duk ranar da aka haifesa to ita a ranar za ta mutu.Kar ki yi tunani mutuwa irin waga ta duniyar a'a mutuwar duniyar matsafa wato duniyar da babu wanda ya san da ita sai matsafi,Mayu da dai sauransu.Bayan soyayyar da Aliyu yake yi miki mai ƙarfi to alƙalamin ƙaddara ya nuna tabbas ke ce ɗaya macen da za ta iya haihuwar namiji muddin ba ki rabu da Aliyu ba.Tun a ranar farko ta zuba magani a abincin da ki ka ci,manufar maganin shine ƙone duk wani ƙwan haihuwarki sai dai kash! Akuyar tsafinta ba ta karɓa ba wanda hakan ya nuna da matsala gwara ta baki makari" Anty Murja na zowa nan a zancenta ta juyo ta kalle ni da kyau kafin ta ce "ko ba ta baki magani wanda ya saka ki amai ba?" Kai na gyaɗa mata alamun eh ta bani.
"Da kuma ki ka sha shine ki ka yi aman bala'in da ta zuba miki na san kin ga abubuwa dayawa tun dai ke ma ki na da aljannun gado " cewar Anty Murja.Jikina ya ɗauki rawa,tsoro nake ji a yanzun ita kuwa murmushi ta sakar min ta ce "na san doli ta shafa miki lafiya duk da hakan zai yi wuya amma faɗan da ya fi ƙarfinka ai sai ka mayar da shi wasa"
"Anty Murja yau kuma wani lamari ya faru tsakanina da Aliyu,kuma....kuma da na duba madubi sai na ga fuskar ki a ciki mi hakan ke nufi ?"
"Koma ciki Bahijja ina da patients a waje zan yi miki bayani daga baya" cewar Anty Murja ta na buga wata ƴar ƙarar rawa,nan wata mata ta shigo ni kuma na fita.
Aliyu ya dube ni ya ce "Ni fa wucewa zan yi tun ɗazu ake jirana" na ja baki na ce "to ka kula da kanka