Showing 3001 words to 6000 words out of 18004 words
mini tarko wanda ya na kasa fita.Idona banda lumshewa babu abin da suke,jikina duk ya saki sai kasala na ke ji.Ban yi wani dogon tunani ba na tabbatar maganin bacci ne Aliyu ya saka cikin furar da ya bani.
Da murmushi ya hauro gadon bayan ya ƙulle ƙofa,dakyar na ke ɗaga fatun idona wanda suka zame mini tamkar na mai dundumi.Riga da zanen jikina ya cire ya fara shafata,ba zan iya gaya ma ku abin da na ji ba a wannan lokacin saboda hankalina ya fara gushewa.
Wuraren ƙarfe goma sha ɗayan rana na farka daga bacci,tamkar wacce aka yi ma duka haka na ke jin jikina.Ido na sake warewa sai na ga Aliyu zaune bisa kujerar roba ya na bacci, kyakkyawar fuskarsa na ƙura ma ido wacce ke ɗauke da dogon hanci da manyan idanuwa,ga ɗan ƙaramin bakinsa wanda gyararen saje ya yi masa ado.
Karon farko da na ji ya burge ni,sai kuma na taɓe baki na yunƙura zan tashi "wayyo Ummaaaa!" Na furta da ƙarfi.
"Bahijjana ?" Aliyu ya faɗa ya na tasowa ya miƙar da ni dakyar,nan ne fa na ji ainahin ciwo da azaba da na gwada yin tafiya.
Duk da shekaruna sun yi ƙaranci a lokacin amman ba wai ya na nufin ban san komi da ya shafi rayuwar aure ba.Kuka na fara yi wiwi wanda ya yi masifar tayar da hankalin Aliyu ,rarrashi na ya fara amman na ƙi na yi shirun.
"Ni gida zan je gun Umma"na furta jin ya na tambayata abin da na ke so.
"Ki yi shiru to in shaa Allah zan kai ki,bari na amso miki abinci" Aliyu ya faɗa ya na mai fita waje.Bai jima ba ya kawo mini shinkafa da miyar kaji,yunwa na ke ji wannan ya saka na zauna na ci na ƙoshi sai kuma bacci.
Tsawon sati biyu Aliyu na wanke min allona tamkar ƴar makaranta,ko kuma malami da ɗaliba.Duk dare na Allah haka ya ke zo mini babu jinkiri ko tausayi,in na samu dama da sarari sai na yi ta cizonsa,hagi da kuma zagi.Amma duk wannan bai taɓa sa shi jin haushina ba sai ma soyayyata da ke rufe sa.
A sannu a hankali har na saba na bar jin zafi, wannan ya sa ban bijire masa ina tsayawa ya yi komi duk da ban biye masa amman hakan na yi ma Aliyu daɗi.
Wani abun mamaki shi ne tun zuwana gidan nan sau ɗaya tal na shiga ɗakin Hajiya,shi ne ranar farko.Tun daga nan ban sake shiga ba ita ma ta fi son haka, ɓangaren matan yayunsa ba mu wani saba da su ba kasancewar ba su iya Hausa ba sai guda tal wacce ake kira da Rahila ita ta na ji kaɗan-kaɗan.
Wannan ya saka mu ke ɗan ƙawance da ita duk da ta girme mini.
Ina zaune ɗakin Rahila ta na yi mini kitso,ajiyar zuciya haɗi da ƙyacci kawai ta ke faman yi.
"Ni kuwa Rahila lafiya ki ke tun ɗazu sai ajiyar zuciya ki ke?" Na tambayeta ta tsaya da yin ƙitson cikin ruɓaɓar Hausarta ta ce "saboda Bahijja abin da ake yi nan gidan daidai ne? Ka na ji ka na gani a cutar da kai amma ba ka da ikon yin magana? Hum! Ni dai ban yafe ba"
"Lafiya mi ke faruwa?" Na sake tambayarta ina mai juyowa mu na fuskantar juna.
"Cikina fah ya zube!" Ta faɗa cikin rawa murya,na waro ido ina cewa "ya zube kuma? Tun yaushe? Jiya fa ki na ɗauke da kayan ki ko?" na jero mata tambayoyin a jere ras ,sai da ta tashi ta leƙa waje kafin ta yi ƙasa da murya ta ce "jiya na yi mafarkin wasu baƙaƙen karnuka na bi na,to sai su ka ci galaba kaina shikenan ina tashi sai na ga babu cikin.Kin san waye sila?" Kai na girgiza mata zuciyata na bugawa "Hajiya ce ! " Na waro ido na ce "ya aka yi ki ka sani to?"
Sai da ta ja baki kafin ta bani amsa da "hum! Ki na nufin har yanzu ba ki fahimci Hajiya *BOKANYA* ba ce? To bari ki ji na faɗa miki kaf ƙauyen nan babu muguwa irin ta.Yara da manya uwanda ta lashe kurwarsu Allah kawai ya san su,kuma hatta jininta ba ta bari ba ta yi rantsuwa babu macen da ta isa ta haifa mata jika namiji" shiru na yi ina nazari tabbas kaf jikokinta mata babu namiji ko ɗaya.
In ban manta ba ga jiya Rahila ta dawo daga asibiti cikin murna ta ke shaida ma ƴan gida a ƙarshe za a haifi Mati a cikin gidan,yanzu kuma ga shi cikin ya zube.
Rahila ta katse mini tunanina ta hanyar cewa "Bahijja bari na gaya miki wani sirri,kin ga akuyar can ta Hajiya? To ba akuya ba ce kamar ko wace ita ɗin ta fi shekara arba'in a duniya .Yadda dai Hajiyar ta faɗa wai tun ta na amarya mahaifiyarta ta bata ita kiyo"
Kamar suɓutar baki na ce "ko ita ma mayya ce?" Sam ba mu ga shigowarta ba sai ji mu ka yi ta ce "wace ce mayyar?" Lokacin da muryar Hajiya ta bugi kunnena har sai da hantar cikina ta kaɗa,ban sani ba ita Rahila ta firgita kamar ni.
"Wata ce mu ke hira,ina wuni Hajiya?" Rahila ta bata amsa haɗi da gaisheta.Ba ta amsa ba sai ma dogon gashin kaina da ta ƙura ma ido,a cikin idonta na kalla na hango tsantsar baƙin ciki na yi mata yawo.
Kawar da kai na yi gefe,ina jin lokacin da Hajiya ta yi tsuki.Rahila ta ce "ki yi hankali da wannan matar don ta na iya ɓatar da ke lokaci guda" matsawa na yi ta ci gaba da yi mini kitso kawai.
Bayan an gama na fito zan je ɗakina na ji muryarta a bayana har sai da na zabura.
"Bahijja na ce ban kai matsayin da za ki gaishe ni ba?" Hajiya ta tambaye ni.
Kai na girgiza na ce "a'a Hajiya kin isa har kin yi yawa,ina wuni" "je ki gyara mini ɗakina" ta bani umarni.
Haka kawai na ji gabana ya faɗi sai dai ban da zaɓi ita ɗin uwar mijina ce.
Da na shiga ɗakin Hajiya wani irin hayaƙi ne ya turniƙe kai kace madafa,tari na fara yi babu tsayawa ina shirin fita na ganta tsaye ƙiƙam a gabana ta cika wajen kai kace Basamudiya.
Wuyana ta kamo ta matse gam da manyan aikaifunta sai kuma ta yi saurin sake ni.
Na yi baya na faɗi ina jin jiri,ɗakin na juya mini.
Ban san abin da ya faru ba sai tashi na yi na gan ni a gadon asibiti,hannuna an rataya mini salkar jini.Aliyu ya shafi kaina ya ce "Ban san mi yasa ki ka sha maganin zubar da ciki ba,ga shi ya yi miki illa sosai duk da cikin ya zube kin zubda jini sosai"
Na waro ido jin furucinsa,yaushe na samu cikin har na sha magani ya zube? Ban kai ga samo amsa ba na ji muryar Hajiya daga can waje ta na cewa "ai doli Aliyu ya rabu da ita wannan mai farar ƙafar,tun da ta shigo gidanmu ahalina ke fuskantar matsala"
"Kar ki damu da zancen Hajiya don ba zan iya sakin ki ba,ke rayuwata ce" Aliyu ke faɗa ya na mai ci gaba da shafar gashina.
Ido na lumshe ina tunanin abin da ya faru da ni kafin hankalina ya gushe,tabbas Hajiya ce silar komi na kasa gane dalilinta na yin haka.
Sati guda na yi cur a asibiti kafin na dawo gida,tun kwanciyata Hajiya kullum sai ta je asibiti a siffar mage ta na bani tsoro.Kar ku tambaye ni ta yaya na san haka saboda ni kaina ban sani ba abin da na sani shine ina tattare da wani sirri na daban wanda ya ke ci ma Hajiya tuwo a ƙwarya.
A sannu a hankali lokaci ke tafiya,kullum in na yi waya da Umma sai ta bani shawarar na ci gaba da yin addu'a.
Na zame ma Hajiya ƙadangaren bakin tulu,ƙarara ta ke gwada mini ƙiyayya a gaban idon Aliyu kuma kamar za ta goya ni.
Kun san tafiyar saƙa? To haka mu ke ni da Hajiya.A yau na zauna na yi tunani sosai,abin da na yanke shine barin gidan nan.
Aliyu na zaune ya na kallo na zo na haye masa ƙafafu,duk hankalinsa ya tattaro ya maido kaina.Baki na turo a shagwaɓe na ce "My Haidar na gaji da zama ni ɗaya a nan duba fa ka gani kullum sai ka shiga gari saboda aikin ka sannan ka dawo a gajiye,mi zai hana mu koma can da zama kawai" sai da ya haɗiye wasu yawu sannan ya ce "haka kike so?" Na gyaɗa masa kai ya ce "dama tun farko haka na tsara to Hajiya ce ta tsara lalle a nan za ki zauna" kukan sangarta na sakar masa,ban bar sa ba har sai da na tabbatar na ci galaba a kansa .
Washegari tun da safe zage-zagen Hajiya ya tashe mu daga bacci.Shegiyar akuyarta sai kuka ta ke,duk fitowa mu ka yi.Yayun Aliyu sai haƙuri su ke bata yayin da shi kuma ya sunne kai.
"Tun da ya zama mijin ta ce ai shikenan sai ku yi ta tafiya"Hajiya na gama faɗar haka ta shige ɗakinta.
Ban zo da komi ba sai kayan jiki wannan ya saka su kawai na ɗauka,bayan na yi ma ƴan gida ban kwana zan juya na nufi ƙofar fita nan fah wani al'amari ya faru akuyar Hajiya ta kubce tare da nufo ni a tsiyace......
Please share
[28/10 à 11:52] MRS SADAUKI 💫: *BOKANYA👽🌪️🌪️🌪️*
```gajeren labari```
*MRS SADAUKI 💫✍🏻*
SADAUKARWA ga *ASSOCIATION DES ÉCRIVAINS MADUBI*🇳🇪
FCWA☀️
Page 4
Na waro ido tare da yin tsaye ƙiƙam har sai da akuyar ta zo gat da ni ta saka ƙawonninta za ta tinne ni,ai kuwa na yi mata wata bangaza tsiya har sai da ta faɗi.
Shegiyar Akuwayar nan ta miƙe ta ƙara ƙoƙarin kai mini karo nan ma na ci galaba kanta,kunnuwanta na riƙe da dukan ƙarfina.Ban san inda na samo ƙarfin ɗaga ta ba kawai sai gani na yi na fara garata tamkar majaujawa na yi cilli da shegiya ta bugi ƙaton icce da ke tsakar gidan.
Tamkar wacce ta yi tsere haka na fara sauke ajiyar zuciya,yayin da matan gidan da yaransu su ke tsaye su na kallon ikon Rabbi.
Rahila sam ta kasa ɓoye farin cikin da ta ke,da murnarta ta ƙaraso guna ta na cewa "Bahijja fatan ba ki ji ciwo ba? Masha Allah ai gwara da ki ka yi magan..." Maganarta ce ta yanke lokacin da wasu dattija mata biyu su ka shigo.
Wani abun da ya bani mamaki gun akuyar suka nufa su na shafarta "Bahijja ke fa na ke jira tun ɗazu" Aliyu ya faɗa daga bayana.Hakan yasa Rahila ta saki hannuna ta na yi min fatan sauka lafiya.
Hanyar Niamey mu ka ɗauka ni da Aliyu ,ba mu yi awanni uku ba mu ka shigo garin.Gidan da ya ɗauka haya wanda ya ke rayuwa tun tuni mu ka sauka.Gidan ciki biyu ne da babban falo sai toilet, kitchen kuma na can daga waje.Tsarin gidan ya burge ni sosai,wanka na shiga yayin da Aliyu ya ce mini zai tafi nemo mana abin da za mu ci.
Har sai da na shirya na canza kaya sannan ya dawo.Dambun shinkafa da soyayen kifi ne ,sai da mu ka ci mu ka ƙoshi kafin mu zauna ya na yi mini hira dangane da garin Niamey .
Sauraren shi kawai na ke,amma hankalina na can Kwalo.Sam tunanin abin da ya faru ya kasa fita kwanyata,sannan matan nan biyu da ban san su waye ba na hangi wani lamari a tattare da su.
"Ya dai?" Aliyu ya faɗa tare da bubuga kumatuna,na ja ajiyar zuciya kafin na ce "Ni kuwa Aliyu miyasa Hajiya ke Bokanci?" Tamkar saukar aradu haka tambayar tawa ta ratsa Aliyu ,na fahimci haka ne duba da yadda ya zabura da kuma yadda ya ke jifana da wani mugun kallo.
"Ban gane Bokanci ba,wace Hajiyar dai tukunna?" Ya yi tambayar ya na tamke fuska.
"Hajiyar ku mana,ko kai ba ka da labarin abin da ta ke?"
"Mine ta ke? Bahijja ki na cikin hankalin ki kuwa? Bari ganin ina yi miki mugun so yasa duk maganar da ta fito bakinki ki rinƙa yaɓa min ita ,sam ba zan lamunci haka ba" ya na gama faɗa ya fice ya bar min gidan.
Na taɓe baki na ɗauki wayarsa na kira Anty Murja,bayan mun gaisa ta bani Umma.Tambayar farko da Umma ta yi mini ita ce "Bahijja a ina ki ka jawo magana? Mi ya kai ki shiga hurumin da ba na ki ba? Kin san illar Akuyar da ki ka yi faɗa da ita?" Shiru na yi ina nazari ta ya aka yi Umma ta san haka? Koko dai uwar tawa ce *BOKANYA* banda labari? Umma ta katse min tunani "ki na ji na ko Bahijja? Ki ƙara dagewa da addu'a kar ki yi sake! Sannan gobe ki tashi da azumi ki wuni cikin zikirori kin ji?" Da "to Umma" na amsa ita kuma ta ci gaba da cewa "kar ki saki ki yarda da mutane saboda ana haɗa kai da uwanda ka aminta da su wajen cutar da kai,abu na gaba da zan faɗa miki shine ki so mijinki ki yi masa biyayya kar ki sake yi masa maganar da za ta ɓata ransa wacce za ta kai shi da yin fushi da ke!" Zanrukan Umma sun ƙara saka ni cikin duhu sai ya zan yi? Doli na yi biyayya akan abin da ta ce.
Aliyu ya shigo ya na kallona,na turo baki ina kashe waya na miƙa masa abarsa.Hannnuna da wayar duk ya haɗa ya riƙe gam kafin ya fizgo ni,a doli na miƙe tsaye.Ƙara jawo ni ya yi ya haɗe da ƙirjinsa,da sauri na rufe ido saboda a duk lokacin da yake mini irin wannan kallon na kan tsinci kaina cikin shauƙi.
Ban yi zato ba na ji bakinsa kan laɓana,tun ina kakauce masa har na haƙura na bada kai bori ya hau.Dariya ya shiga yi mini,cikin jin haushi na fara dukan ƙirjinsa haɗi da ture sa."Allah zan cije ka,kuma sai ka san wa ka yi ma dariya " na faɗa kamar zan yi kuka.Aliyu ƙarshen ɗan duniya ne,maimaikon ya rabu da ni sai ya kama haɓata ya fara cizawa a hankali ta yadda ba zan ji zafi ba.
Tamkar fitar iska haka idona ya yi tozali da wani baƙin hayaƙi,ya na fita ta window.Na zabura na ci karo da ƙirjin Aliyu ,da sauri ya janye daga jikina ya tashi zaune haɗi da jawo ni "mine ne uhum?" Kai na girgiza masa.
Ya ja dogon hancina ya sake cewa "shine kuma ki ka firgita?" Na marairaice fuska na ce "wanka zan yi" ya ɗaga min gira ɗaya ya ce "ko na yi miki?" Kafaɗa na maƙe kafin na je na yi wankan gabanin shi.
Da dare ma abinci waje mu ka ci tun da har yanzu ban gama tsara komi ba.Aliyu na zaune a falo ya na kallon tv na fito cikin riga da wando na bacci,aza ƙafata cikin falon ke da wuya wata baƙar mage ta shigo ɗakin ta na kuka.
Aliyu ya ce "ina sauran abincin nan ?" "Mi za ka yi da shi?" Na tambaye shi."Mage zan ba ni shaf na manta da ita,kullum nan ta ke cin abinci" har zan yi magana sai kuma na tuna da nasihar Umma.
Sauran abinci na ɗauko,ga mamakina sai na ga ya fita waje ya ɗauko wani tsohon plate ya zuba mata abinci.Ci ta fara yi ni kuma ina kallonta,kusa da Aliyu na zauna ina kallon Film ɗin da ya ke kallo.
"Yanzu duk wannan bom ɗin da ke tashi ba gaskiya ba ne?" Na tambayesa ina kallon yadda wuta ke tashi cikin tv.Ya jawo ni ya ɗora kan cinyarsa ya ce "duk cikin ɗabi'un ki ƙurciyarki da wautarki sun fi komi burge ni!" Na turo baki ina gunguni saboda babu abin da na tsana irin a raina min shekaru.
"Haba ƴar ƙwaila ta wannan fushin fa?" Aliyu ya tambaya,cikin son ƙara nuna masa ina fushi na juya masa baya nan idona ya yi baƙin gani.
Idanuwa shidda na gani jere ras ta jikin window sai dai babu fuska,da ɗan yatsa na yi wa Aliyu nuni ko kafin na furta wata kalma sun ɓace ɓat.Na miƙe tsaye ina sake kallon windown amma babu komi,shiru na yi ina nazari duk tambayar duniyar da Aliyu ke yi mini ban basa amsa ba.
"Kira mini Umma dan Allah" na faɗa kamar zan yi kuka,zai yi magana na fara dire-diren ƙafafu doli ya kira min ita.
Bedroom na shiga na labarta ma Umma komi "Yauwa yanzu abin da za ki yi ki samu ruwa masu kyau ki tofa addu'a sai zuba su a duk wani bango na ɗakin" Umma na gama faɗa mini haka na kashe wayar na yi kamar yadda ta ce.
Aliyu dai sai kallona ya ke.Sai da na gama na ce "ban san mi na yi ma wannan matar ba ta ke biya ta da sharri ! " "Wace matar?" Aliyu ya tambaye ni,yi na yi kamar ban ji sa ba na shige ɗaki na yi kwanciyata.
Washegari ina kitchen ina soya wainar ƙwai Aliyu ya fito rataye da jaka,fuskarsa ba walwala.Ko kafin na kai ga tambayarsa ya ce "yanzu Ya Yusuf ya kira ni wai Hajiya ba lafiya jikinta ya matsa"
"Allah bata lafiya!" Shi kawai na furta.
"Amen! Ki kula da kan ki zan je ban sani ba ko can zan kwana"
Na waro ido na ce "ina za ka tafi? Wai ba dai Kwalo ba?" Ya tamke fuska ya ce "Bahijja wace irin tambaya ce haka kuma?Ba ki ji na ce Hajiya ba ta lafiya ba?"
"Allah tsare hanya" na faɗa ina mai ci gaba da aikina,"na aje ƙaramar wayata bisa table ki ɗauka ki fara amfani da ita kafin na sayo miki wata"Aliyu ya faɗa kafin ya fice.
Cikin ɗaki na koma na ɗauki wayar Umma na kira ko gaisheta ban yi ba na ce "Umma gida zan dawo na gaji da wannan lamari,makircin matar nan ya yi yawa wai kin ji ba ta lafiya kawai daga zuwan mu jiya shine har ya kwasa ya koma.Amma lokacin da mu ke can..." Umma ta katse ni da "Bahijja irin tarbiyyar da na baki kenan? Uwar mijin na ki ce makira? Kul! Kar na sake ji kin faɗi haka,ko ba komi Ɗanta ki ke aure.Ya ya kin ɗauki azumin?"