Showing 3001 words to 6000 words out of 17191 words

Chapter 2 - WAKE DAYA

Start ads

11 Aug 2025

207

Middle Ads

yaron talle kafin ta miƙa masa ɗari tace sun gode, suna isa gurin motocin dake pake dama saura mutum ɗaya ake jira, Hajiya Indo na shiga mota ta cika sai tafiya,

Inna Meramu

Fitowa tayi tana miƙa tana hamma lokacin gari yayi haske wai zatayi alwalar asbha, taja ruwa a rijiya ta shiga banɗaki ta fito tayi alwalah ta koma ɗaki tayi sallah, shiko malam Junaidu yanata tararradin kalmomin da zai gaya mata saboda tsoronta yakeji kamar ta shanyeshi,

Kamar an jefota ta faɗo ɗakinsa tana bambamin masifa, "wato barinta kayi tana bacci har yanzu ko?, to wlhi sai dai kaci tuwon da sanyi dan bazan taɓa ɗumamawa dakai ba, niba asararriya bace"

Tayi kiɗanta tayi rawarta ta fice baice mata ƙala ba.

Kamar inda ta faɗa bazata ɗumama tuwon dashi ba haka tayi, iya nata, tana gamawa ta shige ɗaki tanaci tana fifitawa.

Malam Junaidu yayi murmishi a zuciyarsa yace "duk abinda zai faru yanzu bazai sosamin raina ba, abinda zai tayarmin da hankali shine, inji ance Hanan ta dawo garinnan wlhi sai nakusa sheƙawa"

Yana faɗar haka ya fice ƙofar gida.

Kai tsaye ya wuce gurin Halliru mai shago, yasiyi biskit da ruwa,



GIDAN DUHU••

Gidane babba bazaka tabbatar da girmansa ba har sai ka shiga ciki, wani irin gini akayi mai matuƙar tsayin gaske, babu wanda ka isa ka hango to katangar ma takai tsayin gidan ina batun ganin wani abu, daga cikin gidan akwai ɗakuna goma, ɗaya na Usaini shine a farko, ƙofar shigowa gidan tana cikin ɗakinsa, dan haka idan zai fita koda yaushe gidan da ƙwaɗo yake wuni har kwana ma,

Daga can cikin gidan kuwa ɗakuna tara ne, uku a gabas uku a kudu uku a yamma nashi kuma a arewa, ɗakin dake gabas shine na Ladidi, tana riƙe da ɗakuna biyu ɗaya na yara, ita kuma wacce ɗakinta ke kudu tana riƙe da ɗaki ɗaya sunanta Iyami, saboda bata aihuwa yasa aka bata ɗaki ɗaya mai ciki da parlo, ragowar ana saka kayan abinci, mai ɗakin dake arewa shikuma Hauwa ce a ciki ragowar ɗakunan yaranta maza suna kwana a ciki ɗaya kuma yara mata,

Usaini yanada yara goma sha biyar, goma mata biyar maza ya tura su almajiranci, saboda shige da fice, inda ya tura shi ba'a dawowa Sai anyi sauka ko shekara hamsin zakayi inhar baka sauke ba bazaka dawo ba, a cikinsu babu wanda ya dawo shekararsu goma kenan, kuma shi Usanin bai damu da yagansu ba, idan yaji iyayen sun matsa sai yayi musu asiri sudena maganar yaran kwata-kwata,

Ladidi itace uwar gida, tanada yara bakwai, mata biyar maza biyu, matan nata akwai mai shekara goma sha biyar, akwai mai shekara goma, akwai mai shekara takwas akwai mai shekara biyar Sannan akwai mai shekara uku Sannan akwai mai shekara ɗaya wato yarinyar ta da take goyo,

Mai shekara sha biyar ɗin sunanta Sahura, mai shekara goma ita kuma Habiba, mai shekara biyar Lawisa, mai shekara ɗaya kuma Sa'ade, mazan da Muhammadu zangina shekarar sa Ashirin Fatihu kuma goma sha biyu duk basa gida.

Ita kuma Hauwa tanada yara takwas maza biyar mata uku, ta farkon mai shekara goma sunanta Hinde ta biyun kuma Barira, mazan da Saminu shekararsa goma sai Tanimu shekarasa bakwai sai Zubairu shekarar biyar sai Ashiru shekararsa uku sai Ashahabu mai wata shida a duniya,

Kaf yaran gidan maza basa gidan matan kuma haka suke rayuwa a cikin gidan da kansa yake biya musu karatun allo boko ko oho, tunda suke Babu wacce ta taɓa fita ko nan da ƙofar gida, haka suma iyayen tunda ya aurosu basa fita sai cikin dare,

Al'adar gidance kullum da safe da safe sai an surfa gero anyi dakan kunu, idan markaɗe ne da kansu suke yi a turmi ko a dutsen miƙa,

Duk yawansu magin talatin suke sawa a abincinsu farin magi guda ɗaya, ɗakunan biyu dake gidan duk kayan abinci da kayan miya ne, kama daga kabewa yakuwa tayin fate daddawa da sauransu.

Duk ranar juma'a sunayin tuwon shinkafa miyar kabewa babu alaiyyahu,

Da Sallah kuwa yana yiwa duka yaran ɗinki da iyayen amma babu mai gigin fita ko nanda ɗakinsa bare yakai ga ƙofa, babu kuma mai kawo musu abinci, matan basa zuwa gidan iyayensu sai ƙarfe takwas fuskarsu sanye da niqab, idan lokacin sallah ne kenan, idan kuma gaisuwar mara lafiya ne, sai ƙarfe shaɗaya na dare suke fita, shizai kaisu a mashin ɗinsa kana ya dawo dasu.

Wani abin mamaki idan matan suka aihu shi da kansa yake unguwar zoma, kuma ba'a suna, idan iyaye suka aiko da gudunmawa shi ake bawa ya basu,

Haka rayuwarsu take tafiya cikin matsatsi da tashin hankali, suke rayuwa, bayajin maganar iyayensa sam.

Hamud Lirwan••

Tunda suka koma gida Hamud ya kasa samun sukuni saboda har mafarkin Hanan takeyi, yau kwanansu uku da dawowa amman sai yakejin kamar yayi sati ne, tunanin Hanan ya hanashi sukuni idan yazowa Lirwan da zancen sai ya fara yi masa faɗa yana cewa, yayi asara duk yawan ƴan matan dake binsa amma zai ƙare a ƴar ƙauye wacce iyayenta ba sonta sukeyi ba, wata ƙila ma a waje aka samo cikinta,

Morning "Hamud an kammala breakfast tun ƙarfe bakwai 7:am kace yau zaka fita aiki da wuri amma naga baka shirya ba?"

Mom ta faɗa tana kallon Hamud dake dafe da kansa yana zaune akan kujerar parlon,

"Nafasa fita mom"

"Akan me?"

Yayi shiru bai ce komai ba, Lirwan dake fitowa yana sanye da lallausan yadin boyel me ruwan toka, yace "mom kibar Hamud kawai, ya kamu da ciwon so"

Mom ta zaro ido kafin tace "ai da nafi kowa farinciki inhar hakan ta kasance"

Hamud yace "wlhi momy ƙarya yake yimin kawai banajin ɗaɗin jikina ne"

Badan Mom ɗin ta yarda ba tace "to shikenan tasan Lirwan bazai yi mata ƙarya ba...

Banyi editing ba, littafin Falak sai ƙarfe takwas insha Allako tara ma'ana 9:pm ko 8:pm



Gaskiya bakwa comments

Mom Islam ce



08141799224















*WAKE ƊAYA💍*

MomIslam



_True life story_





*Arewabook@momislam11*





🆓page3





A hankali Lirwan ya isa dinning room ya buɗe warmers ɗin dake jere da abinci ya ɗauki plet yasa abincin, girgiza kai yayi yana murmishi sakamakon kai lomat abincin da yayi bakinsa, taliya ce jollof ta mangyaɗa , cikin d'aga Murya yace "momy wannan abincin zai tsinkemin kunne"

Momy na daga parlo tayi dariya ta kalli Hamud kana tace "ga mutuminka can yana aikin daya saba"

Hamud yayi dariya kafin yace "momy wannan gurin ɗiban girki baya wasa"

Bayan ya kammala cin abincin ya fito hannunsa riƙe da tissue paper yana goge bakinsa,

"Acici mala'ikun tauna baki baya zama sai ya ci"

Hamud ya faɗa yana shafa sumar kansa ya miƙe yabar gurin.

"Daka tsaya mana da kaji amsa"

Lirwan yace yana kallon momy dake yi musu dariya.



Ƙarfe sha ɗaya suka shigo Kaduna, aka saukesu a television garej, suna tsaye masu napep da mashina sunata cewa "Hajiya tafiya ne?"

Hajiya Indo tace "mezai kaini hawa mota a wannan tashar, gara in fita bakin titi inhau mota nera ɗari,

Hanan tace "nidai yunwa nakeji ki siyamin koko da ƙosai"

Hajiya Indo ta zarewa Hanan ido kafin tace "ke wato har kinga fuskar cemin in siya miki wani abu? nima banci ba, kuɗin da kikaga na bayar kuɗin masu dashi ne na tattaro shine nayi kuɗin mota, ko Allah zesa mu yagi rabonmu"

Hanan tayi shiru bata sake magana ba,

Suna tsaye a bakin titi Bus tazo wucewa, Hajiya Indo tace "Kinkinau"

Matemakin mai motar yace "muje mota ta cika"

Suna shiga motarsu ta ɗaga sai zuwa Kinkinau, a bakin titi aka saukesu tsakaninsu da gidan babu nisa, Hajiya Indo ta miƙa masa nera ɗari, suka wuce.

"Abinda nake so dake shine, ki nutsu fa su gidan ƴan gayu ba'a yi musu hauka yanzu sai su miƙa mutum ga hukuma"

Hanan tace "ni wlhi duk inda zasu kaini su kaini indai zasu bani shayi da burodi"

Hajiya Indo ta maka mata duka tana cewa "ai bama zakiji abinda nake faɗa miki ba kenan?"

"Naji"

Hanan ta faɗa a fili, a zuciyarsa tace "yabi ruwa ai ba ibada bane".

A bakin wani haɗaɗɗen get suka tsaya, Hajiya Indo tayi nocking, mai gadi ya leƙo ta ƙaramar ƙofa yace "waye?"

Yana ganin Hajiya Indo ya washe baki kafin yace "Barka da zuwa banma ganeki ba, dan kin kwana biyu rabonki da gidannan"

Hajiya Indo ta washe haƙorai tama tare da haƙorin Kano wato na Makkah tace "Hajiya Rashidan tana ciki?"

"Eh tana ciki amma inajin fita zatayi dan tasani wanke mota ɗazu"

Hajiya Indo tace "to bari muyi azamar shiga"

Suka wuce ciki.

Da shigarsu gidan Hanan ta riƙe baki, sakamakon ganin tsarin ginin gidan da flowers ɗin da sukayi luf gunin sha'awa, daga can ƙofar da zata sadaka da parlon Hajiya Rashida akwai wasu flowers a gefe da gefen ƙofar a cikin wata roba mai kyau, kasancewar tsaftace gidan da akeyi yasa duk wanda ya shigo sai yace ,sabone alhalin matar gidan zatayi shekaru ashirin da aure,

Hajiya Indo ta rangaɗa sallama cikin ɗaga murya,

Daga can ciki aka amsa kafin wata yarinya ƙarama ta fito wacce batafi 8yrs ba, kanta yasha kitson kalaba yarinyar fara, tana sanye da riga da skirt ɗan kanti, sosai tayi kyau itama ɗin kamar Hanan mai surutu tace "su waye ku?, momy tana wanka tare da dadyna"

Hajiya Indo ta zato ido, a zuciyarta tace "banda tacewar iskanci wankan ya gagareta ita kaɗai har sai ta haɗa da gardin mijinta"

A fili tace "zamu jirata ashe kin daɗa girma?"

Yarinyar ta washe haƙoranta wanda rabi giɓi ne tace "sunana Munipa"

"Ai ban mance da sunan naki ba jeki ce momynki tayi baƙi"

Munipa tace "toh"

Munipa ta ruga da gudu taje bedroom ɗin momyn tace "momy wata mata tazo wajenki"

Hajiya Rashida tace "to kikace mata inayin me?"

"Nace kina yiwa dady wanka"

Hajiya Rashida ta buge mata baki tace "surutunki yayi yawa fa"

Abu Uzaifa yace "haba momyn Munipa har tayi abin duka?"

Tayashi shafa mai takeyi ta bari ta fice tunda yana goyon bayan abinda tayi,

Tana isowa parlo ta washe baki sakamakon ganin mutuniyar Tata Hajiya Indo, Hajiya Rashida tace "Barka ashe kina hanya? wlhi ko jiya sai da nayi maganarki"

Hajiya Indo tace "aiko dai, mun shigo garin naku"

Hajiya Rashida ta tafi kitchen ta ɗibo musu soyayyen dankalin turawa da ƙawai ta ajiye musu ta buɗe fridge ta ɗibo drinks ta ajiye kafin ta kawo musu plet tace "wlhi ko girki banyi ba"

Hajiya Indo tace "abubuwanne sai a hankali, dama ƴar aiki na kawo miki"

Hajiya Rashida tayi murmishi kafin tace "ikon Allah ni yanzu bana ɗaukar yara wlhi, tunda na ɗauki wata yarinya ƴar ƙauyen Kano tun tana kamar wannan" ta nuna Hanan, taci gaba da cewa, naketa yi mata hidima, wlhi data girma cemin tayi wai Abu Uzaifa yana birgeta shine jikina yayi sanyi"

Hajiya Indo tace "inna likahi kice yaran sun koma tabbatattu banda baƙin hali ba ina kai ina mijin uwar ɗakinka mai temaka maka"

Hanan taga dai ba'ace taci abinci ba, tayi jiran harta gaji, kasancewar bata jurewa yunwa cikin marairace murya tace "in..inajin..."

Bata ƙarasa maganar ba, sakamakon Hajiya Indo data galla mata harara,

Hajiya Rashida ta fahimci abinda Hanan ɗin takeso,

"Kici mana"

Hajiya Rashida ta faɗa tana kallon Hanan,

Jikin Hanan na rawa ta dinga loma da dankalin, saboda tsabar laushinsa har wani bata tsunawa, tunda taji ba irin na garinsu bane, dankalin Hausa.

Sunanta hira ashe har ta cinye ta kora da fanta ta gora, saukar gorar da Hajiya Indo taji ne yasata kalli Hanan ɗin, a tunaninta dataga kular a rufe ko ta rage mata ne, sukaci gaba da hira, har Abu Uzaifa ya kira Hajiya Rashida ta tafi gurinsa,

Hajiya Indo ta buɗe kula taga wayam babu komai, ga wata uwar yunwa dake addabarta tashi ɗaya, tama rasa abinda zata cewa Hanan ɗin tsabar haushi, sai tace "Allah zai sakamin, dan yanzu ina dukanki zaki taramin mutane, wlhi idan aka samu gidan aikin dazan kaiki sai na ciri ɗari biyar a ciki"

Hanan tayi gyatsa tana shafa ciki, wani abun haushi ma batace wa Hajiya Indo komai ba sai rarraba idanu da takeyi.

Rashida ta dawo hannunta riƙe da kuɗi ta miƙawa Hajiya indo,

"To abin arziƙi muka samu?"

Rashida tace "Dadyn Munipa ne yace abaku 3k"

Hajiya Indo tace "aiko mun gode Allah ya saka masa da aljannatul firdausi"

Hajiya Rashida tace "amin, na tambayeshu zan rakaku gidan ƙanwar Ummana idan kun gama sai mu tafi, ina tunanin ƙila ta ɗauketa tunda naga ma'aikatan gidan ana ɗibarsu da yawa"

Hajiya Rashida tace "to Allah yasa a dace mun gama"

Ta faɗi maganar tana hararar Hanan.

Munipa ta taho da gudu tana cewa "momy anata kiranki a waya"

Hajiya Rashida tace "shine sai kinyi gudu?"

Ta ƙarɓi wayar, tana shirin kamawa kiran ya katse, cikin sauri tabi kiran tana cewa "aikuwa ƙanwar Ummana ce"

Hajiya Indo ta fara adu'a ranta, Allah yasa a dace idan ba haka ba ta shiga uku dan kuɗin da ake bata ajiya ne ta tattara ta taho dasu, da taga su Hanan sunzo da babanta shine tace musu tana shirin zuwa Kaduna, shikuma mai mashin dama sunyi dashi zai kaita tasha domin taje anguwar bawa sarin ɗanyar masara, dayazo tace tasha ze kaita.

Hajiya Rashida ta ajiye waya kafin tace "gaskiya tace "a halin yanzu yaran da sukeyi mata aiki sunkai biyar"

Gaban Hajiya Indo ya bada rass ta fara tunano kuɗin mutane, tazo dubu huɗu zata koma Allah masani ko nawa ne, gashi dai sun sami dubu uku, aciki ma sai ta cire kuɗin abinci, dan idan taci gaba da dauriyar wannan yunwar zata faɗi,

Ƙauye••

Jiki a sanyaye malam Junaidu ya shiga gidan tare da tsoron masifar Inna meramu, bai ganta a tsakar gida ba, yasashi shigewa ɗakinsa a hankali, ashe tana ganinsa ta labule kasancewar ba me duhu bane,

Cikin masifa ta miƙe tare da fitowa ta faɗa ɗakinsa tace "wai kana nufin nice baiwarku da zan dinga shiga nemo wannan makirar yarinyar? kwanaki nace maka bin maza takeyi kace ƙarya ne, yanzu ai kaga tabbacin abinda nake gaya maka ko?"

Malam Junaidu yace "dan Allah ki ƙyaleni ƙafata tana zugi idan kinada man zafi ki bani in shafa"

"Inna Meramu ta riƙe baki, kafin tace "yau naga makirci irinna munafurci wato saboda bakasan a faɗi lefinta shine zaka dinga yimin wani irin magiya ko?"

To ɗazu Usaini ya aiko ƙanin mahaifinsa da kayan lefe tunda nayiwa baba Isiyaku magana har an karɓi kaya an kawo sadakin aure, nace musu da bakinka kace a aiwatar da komai, tunda naga ka tafi yawo, nasan zakayi farinciki da hakan yau nayi abin farinciki ban mu tafa?"

Malam Junaidu ya juya zai fice tace "ah ko abinda nayi beyi maka bane?"

"Eh"

Kawai ya faɗa tare da ficewa yana juya kai alamar rashin jin daɗin abinda ta aikata, shikuma yaɗau alwashin ko dubu nawa ya kawo Hanan bazata dawo ƙauyennan ba bare ta shiga gidan masifa insha Allah.

Acan gidan Usaini kuwa, da kansa yake shafen farar ƙasa a wani ɗaki daya gina daga can nesa dasu, hatta ginin ma da kansa yayi,

Matan suna zaune sunanta gulmarshi, Hauwa tace "nidai da akwai inda zanyi inbar gidannan wlhi dana bari, ban taɓa nadamar shigowa ba sai da ya zagemin iyayena jiya akan nayi miya da yawa, dan nasa kuɓewa ƙulli biyu, Ladidi tace "nifa kamar masifarshi a kaina ta ƙare kullum yazo kwanciyar aure dani sai kiji yana cewa wai bayajin daɗi"

Walhi gwara Iyami yana ji da ita sosai kodan bata taɓa aihuwa bane?"

Hauwa tace "nidai da nice Iyami wlhi guduwa zanyi banga amfanin zamana a gidannan ba, banda ƙaddara da kwaɗayi mezai kawoka?"

Iyami ta taɓe baki kafin tace "koni nagaji da zaman gidannan kawai dai ina zaune ne, yaushe naga ƙofar fita ma bare in leƙs in fice?, kudai muyi adu'a Allah yasa ya gyara halinsa ya tabbatar da abinda yake yi ba mekyau bane"

Usaini yana daga can gurin ginin amma yace "sannunku munafukai, baku da aiki sai yi da mutum wlhi idan na sake jin Muryar wata ita zata surfa gero mudu ashirin"

Ko wacce tayi gum, saboda sunsan inhar ya fad'i magana sai ya aikata,

Yaran ma idan sun haɗu a ɗaƙi basu da zancen daya wuce hakan duk da basu taɓa leƙa wajen ba amma suna san ganin ko meye a wajen.

Bayan ya gama shafen yace "Iyami kawomin ruwan wanka"

Iyami ta miƙe jiki na rawa taje rijiya taja ruwa takai masa banɗakin daya kasance zagaye da karare ta ajiye, ta mance batace masa ga ruwan nan ba yana fitowa ya watsa mata mari da kafcecen hannunsa ya wuce.

A gigice ta durƙusa a gurin, sakamakon azabar dake addabarta a kumatunta, tama godewa Allah dayasa babu kowa a cikin gidan bare afara magana akai, tayi ɗaki idonta na zubar da hawaye...!



Hello fans labarin yayi muku kuwa???

08141799224 Mom Islam

*WAKE ƊAYA💍*

MomIslam

_True life story_

*Arewabook@momislam11*

🆓 Page 4

Harya fito daga wanka taji alamun ajiye bokitinsa tana kuka, bawai kukan marin da yayi mata takeyi ba, kukan rayuwar ƙunci da rashin ƴancin kai shi takeyi,

Daga can bakin ƙofa yace "an ƙona manajan da nace adinga shafawa kuwa?"

Iyami tayi tsit kamar ruwa ya cinyeta, bai shigo ɗakin ba ya wuce nasa ɗakin yana sababi harda cewa "nakusa yin amarya sabuwa fil duk wannan iskancin da kuke yimin zaku dena"

"Usaini ka siyo mana man shafawa rabonmu da shafa mai wlhi bamace ga ranar ba"

Hauwa ta faɗa tana daga bakin ƙofar Usaini,

"Ke mekikaji nace jiya lokacin dana taraku dukkanku?"

Hauwa tace "oho ina naji tunda ba abinda ze yuwu ka faɗa ba"

"Da sauri ya fito yana gyara mazugin wandonsa yace "wato kuna nufin kunaso kufi ƙarfi nane?, wallahi nasha gabanku sai amarya tazo duk wani iskanci nasan zaku dainashi, ga Iyami nan ma da kwata-kwata shekarata biyu ne a gidannan kun koya mata tsuguddidi da rashin kunya"

"Nifa kaga ba shine ya kawoni ba ka bani man shafawa dan nasan a ɗakinka baza'a rasa ba"

Cikin zafin rai ya wanka mata mari kafin yace "yau babu abinci a gidannan ku rubuta ku ajiye, me ragowar kokon safe tasha da ƴa'ƴanta wacce batadashi tayi ta hamma"

Yana gama faɗar haka ya koma ciki,

Sosai ran mutan gidan ya 6aci sakamakon Hauwa data janyo musu masifar zama da yunwa, gashi yanzu har ƙarfe tara da rabi na rana,

Iyami ta fito jiki a sanyaye ta ɗauki manja ƙulli ɗaya, kasancewar komai ƙullashi akeyi a leda, manjan ma befi na nera ashirin ba, sbda a ƙiyasi befi cikin cokali biyu ba shine nayi abinci,

Iyami ta ɗibo karare ta haɗa wuta tasa kwanon da take soya mai ta soya manjan har sai da yayi fari kafin ta sauke, daya huce ta juye a roba ƙarama ta koma ɗaki.

Duka yaran sun taru kashi-kashi, Sahura da kasancewar Hinde ce budurwa

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login