Showing 15001 words to 17191 words out of 17191 words
dariya tare da cewa "mutane basayin kyau wlhi rayuwar gidanmu tafi komai birgewa illar rashin yawo ne kawai"
Da sauri Alhji Munir ya kalleta kamar meson gano wani abun, sai Kuma yayi musu godiya ya shiga motar ba tare daya tanka mata ba suka wuce cikin garin Jos, suna tafe yana tunanin inda ze kaita,
"Gidan Affan"
Alhj Munir ya fad'a a fili"
Hinde da tsoro ya cikata ta rasa inda zatasa kanta saboda tsoro shiyasa tayi kamar ruwa ya cinyeta,
A Bauchi road yayi parking motarsa, gaban wani had'ad'd'en gida, mai d'auke da get biyu, daga yamma akwai d'aya sai hanyar shigowa ta kudu shima akwai d'aya, Alhji Munir yace "muje"
Hinde tak'i fitowa, har sai daya daka mata tsawa sannan ta fito jikinta na rawa, duk rawar da jikinta yakeyi bai hanata shafa jikin get d'inba tana shinshinawa, nanma sai dayayi mata magana sannan ta taho da gudu,
Hinde bata ta6a rudewa ba sai dataga tsarin gidan kasancewar tunda take Babu wani abin k'yle-k'yale da ta ta6a gani sai da ta fito waje, Alhji Munir ya rik'e hannunta suka k'arasa ciki, suna shiga parlon ta wani zabga uban ihu Wanda yasa Affan dake can d'akinsa na saman bene sai da yaji ihunta,
Alhji Munir yace "lafiya kuwa?"
Hinde ta nuna mutanen dake wulk'awa a TV tace "wlhi Kuna zaune da mutuwa baku sani ba"
Alhji Munir ya tsorata kafin yace "ban gane ba Hinde?"
Hinde ta mik'e da sauri ta tsaya cak akan kujera mai zaman mutum biyu kafin tace "laushi kamar kar in bar gidannan"
Wani saurayi yazo wucewa jikinsa sanye da blue d'in Kaya, da alamu uniform ne na ma'aikatan gidan"
Ya durk'usa har k'asa ya gaishe da Alhji Munir kafin yace "y'an mata sannu"
Hinde ta kwaikwayi maganarsa itama tace "y'an yata shannu"
Abin yaso bawa Alhji Munir dariya, sai ya gimtse yace "please kacewa Affan Abban Dogon agogo yazo"
Saurayin da keta bin Hinde da kallo ya wuce samma tare da isar da sak'onsa,
Wata budurwa ta shigo tana sanye da madai-dacin hijabi ta durk'usa ta gaishe da Alhji Munir kafin ta ajiye tran fruits d'in dake hannunta ta juya,
Hinde ta duro daga kan kujera tare da mik'a hannu ta d'auki mangoro tace "munada bishiyar mangoro a gidanmu Amma wannan yayi girma da yawa"
Ta kalli lemu da abarba da kankana da gwanda tace "wad'annan bansan ko meye ba, kai idan ka sani d'an gayamin"
Alhji Munir ya waiga baiga Wanda akace masa kai d'inba sai yace "au wai dani kike?"
Hinde ta ta6e baki kafin tace "to da dawa nake?"
A hankali yake sakkowa daga matattakalar benen, saurayi ne kyakkyawa fari yana d'auke da dogon hanci bakinsa madai-daici amma bashi da wani tsayi can yanada shi babu laifi, yana sanye da milk d'in riga, wandon jikinsa kuwa black ne mai kyau sai zubunan da suka wadata yatsun hannunsa zobunan sunkai guda uku, hannunsa na d'aure da tsadadden agogo mai jikin silba shima yayi kyau, kafarsa na sanye da takalmi silifas wanda ake Kira da d'an madina,
A hankali ya iso gurin Alhji Munir kafin ya nemi guri ya zauna sannan ya ce" Alhji Ina wuni ya jama'a"
Alhji Munir yace "lafiya Lau tun tuni nake jiran fitowarka amma shiru?"
Affan ya sosa kansa kafin yace "am sorry Alhji bacci nakeyi shiyasa"
"Ina Hajiya Amina?"
Alhji Munir ya tambaya kai tsaye,
"Tana part d'inta"
Alhji Munir ya mik'e kafin yace "au na d'auka ai a guri d'aya kuke?"
Affan yace "a'a dama tun tuni tana can sai dai tana shigowa nan kullum"
Alhji Munir yace "to Bari muje can d'in"
Yana rik'e da hannun Hinde data zubawa Affan ido tak'i kawarwa, janta da taji anyi ne yasata cewa "ammafa Alhji ka iya bak'inciki, Baabata tacemin a Aljannah akwai samari to wlhi naga d'aya, inba sa'a bama gidan Aljannah muka shigo"
Alhji Munir yayi murmishi,
A k'ofar parlon Hajiya Amina ya tsaya tare dayin sallama, Hajiya Amina ta amsa tana daga ciki a zaune kan kujera y'ar aikinta na mammatsa mata k'afa, Alhji Munir ya k'arasa cikin fara'a yace "Hajiya badai ciwon k'afar bane ya tashi?"
Hajiya Amina ta d'ago kanta tare da sakin murmishi tace "laahh Kaine a gidan namu?"
Alhji Munir yace "wlhi nine Ina wuni"
Hajiya Amina tace "lafiya Lau ya k'ok'ari?"
Alhji Munir yace "lafiya Lau na kawo miki bakuwa ne"
Hajiya Amina da son mutane tace "aikuwa inhar hakan ta kasance zanyi murna dama shekaran jiya y'an aikin namu suka tafi gida anyiwa mutum Uku aure kaga daga ni sai Ladidi can kuma gurin Affan Aisha ce"
Alhji Munir yayi hamdala saboda yasan idan yakai Hinde gidansa sai matarsa tayi Mata dukan tsiya, duk da dai yaje gurin malami dazu yace masa mutum ce ba aljana ba"
Alhji Munir yace to ai gatanan Hajiya na baki wuk'a na baki nama yarinyar yayar matata ne shine nace barin kawota"
Dama Hinde gurin zama take nema shiyasa da Alhj Munir yayi wannan k'aryar ko magana batayi ba.
Anan gurin Hajiya Amina yaci abinci shinkafa da Miya da aka kawo masa yasha ruwa yayi Mata sallama ya wuce.
Zuwa dare an kammala abinci an kunna engine haske ya gauraye d'akunan, Hinde ta mik'e tana tsalle"
Hajiya Amina tace "y'ata ki nutsu mana"
Hinde ta zaune tare da kallon mutanen da suka fara motsi a TV tace "Hajiya dan girman Allah ki fitomin da ko mutum daya ne mu gaisa"
A inda Hinde tayi maganar sai ta bawa hajiyar dariya,
Ladidi dake cin taliya tace "ke basa fitowa kallonsu kawai akeyi"
Hinde ta ta6e baki kafin tace "Hajiya Wai hakane?"
"Eh hakane jeki d'auki abinci kici naga kamar ba'ayi Kiran sallah ba"
Jikin Hinde na rawa ta d'auko abincin dake cikin Samira Mai kyau a rufe ta kawo inda take zaune ta ajiye shi, tana bud'ewa ta ruga da gudu tare da kallon hannun Ladidi data d'ago taliya zata kai bakinta tace "wayooo tsutsa wlhi ku mayu ne"
Ladidi ta zaro ido tace "ke ba tsutsa bace kici akwai dad'i"
Hinde tace "nidai a tsincemin naman kai a bani a hannuna wlhi bazan zo kusa da inda tsutsar nan take ba"
Da hajiyar ta lura da gaske Hinde takeyi tsoron taliya take, tace "to Ni wlh bani da wani abinci sai dai kunu da nayi na tsamiya"
Hinde Sarkin kunu ta buga tsalle tana murna tana cewa "wlhi zansha aini kin kaini maka, Allah yasa akwai y'ar zak'i a ciki"
Hajiya Amina tace "zau ma kuwa zak'in har zai yanke kunnen mutane"
Ladidi ta kawo mata kunun cikin dogon jug, kan kace me harta shanye tana yin wata irin gyatsa wacce ko hamdala Babu,
Kiraye-kirayen sallahr da aka fara yi ne yasa dukkansu mik'ewa suka wuce yin alwalah, Hinde tace "Hajiya in biyoki ne?"
"Lah zomuje mana"
Hajiya Amina ta fad'a fuskarta d'auke da murmishi,
Hinde ta taho tana tafe tana tsalle har suka iso bedroom d'in hajiyar, Hajiya Amina ta shiga toilet tabar Hinde a tsaye a tsakar d'akin tana ta kalle kalle, hajiyar na fitowa ta zaro ido sakamakon ganin Hinde da cinyar kaza da tayi, Hajiya Amina tace "y'ata mezan gani kin d'auki abu ba tare da kin tambayeni ba?"
Sai da Hinde tayiwa cinyar kazar kyakkyawan yaga kafin tace "dan Allah kiyi hakuri naga kinada kirki ne kuma bazaki hanani ba, "rabona dacin nama bansan ranar ba, inaga ma tunda aka haifeni sau daya na ta6 cin bama"
Hajiya Amina ta waro ido ta kamo hannun Hinde ta zaunar da ita akan kujerar roba kafin tace "idan kin gama ci ki shiga toilet kiyi alwalah"
"To kawai tace, sai dai tanada k'wakwalwar rik'e Abu, tunda taji d'azu hajiyar tace toilet, har k'ashin sai da ta tauneshi ta had'iye tare da sud'e hannunta ta bud'e k'ofar toilet d'in ta shiga,
Tofa
Abin yaso bata tsoro, a fili tace "anyi tsafi anan, wannan wane irin guri ne kamar na tsafi?"
Ta rufe bakinta da hannu kar hajiyan taji, ta d'auki buta taji babu ruwa, tsayawa tayi tana nazarin me zata danna a toilet d'in.
Gurin kunna pampo ta gani a jikin bango, tana kunnawa ruwa ya jik'ata sharkaf, ta tsala ihu tana cewa "sai da nace akwai tsafi-akwai tsafi Amma na kunna"
Hajiya Amina ta lek'o cikin tsoro tace "y'ata lafiya?'
Hinde dake tsaye ruwa yayi Mata jagab tana kuka tace "ruwane ya jikani"
"Kin ganki ko? "Ga buta can Dana ajiye miki ruwa kusa da abin wanka wannan ai ta fashe bana zuba ruwa a cikinta"
Hinde tayi shiru tana kallon Hajiya Amina,
Alwalar da batayi ba kenan ta fito tsamo-tsamo da ita kamar an tsamo a rijiya.
Har wani karkarwa takeyi tsabar sanyi da takeji, Hajiya Amina tai saurin d'auko mata bargo tare da tambayarta Ina kayanta?
"Mun mance a Tasha"
Hinde ta fad'a bakinta na 6ari, bayan ta lullu6a mata ta d'auki cup ta tsiyaya ruwan zafi ta jefa lifton tare da sanya Madara da Milo tace "tashi Kisha, Babu zafi sosai"
To Hinde tace "tana daga tsugune lullu6e da bargo, badan abin yayi Mata dad'i ba ta kafa kai ta shanye harda runtse idanu tanajin kamar zatayi amai.
A hankali ta ajiye cup d'in tare da kallon Hajiya Amina da take shafa mai kasancewar tana idar da sallah ta shiga wanka,
Feshe jikinta da turare take tayi kamar ba da kud'i aka siyesu ba, ta kamo hannun Hinde ta d'agata sama ta zaunar akan gado kafin tace "barin aro miki kayan Ladidi kisa kafin gobe muje kasuwa"
"To" kawai hinden tace, yanzu rawar sanyin da takeyi ya d'an ragu, ta gyara zamanta tana kallon agogo da yaketa tafiya ita kwallitarsa nema yayi mata kyau.
Da sallama hajiyar ta shigo hannunta rik'e da zumbuleliyar doguwar riga mai dogon hannu, da kanta ta sawa Hinde kafin tace "ya maganar sallah?"
Hinde ta fashe da kuka tabbacin dai babu magana,
Washe gari.
Anyi sallahr asbha dukkansu sunyi wanka, dole Hinde ta mayar da doguwar rigar Ladidi ta nemi guri ta zauna,
Hajiya Amina tace "Ladidi rakata part d'in Affan yakamata ko goge goge ta dinga yi masa tunda babu wasu masu aiki acan"
Ladidi ta rik'e hannun Hinde suka shiga part d'in sbda sun sami k'ofar a bud'e, saboda ragon azanci Ladidi tace "jeki ciki inaga yana sama"
Ladidin ta fice.
Hinde ta haura kamar inda taga Affan d'in ya sauko jiya da doguwar rigarta wacce tasa hannu take rik'eta har wuyan ma yayi Mata yawa, ga gashi har gadon baya duk yayi datti.
Duk da tana haurawa tana hutawa a haka ta isa, tana zuwa d'akin farko ta murd'a handle d'in k'ofar ta shiga, babu kowa a parlo dan haka ta murd'a handle d'in toilet, Aiko ta hangoshi zaune akan tukunyar Kashi, a zabure Affan ya....!
Wayoo masoyana lefin dad'i k'arewa idan kika ga littafin Wake d'aya a waje, to tabbas na sata ne saboda ayau na kammala Free pages sai mun had'e a paid group much love my fans
Zaki samu littafin akan farashin dari uku kacal 300 ga tsarin biya
Account number 3175689751 Zainab Habibu first Bank
Shedar biya ta wannan number 08141799224
Katin mtn da Vtu ta wannan number 08163626370
Shedar biya ta wannan number 08141799224
Y'an Niger zaku tura da katin Airtel ta wannan number 08141799224
Mom Islam
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels