Showing 6001 words to 9000 words out of 17191 words

Chapter 3 - WAKE DAYA

Start ads

11 Aug 2025

205

Middle Ads

a cikinsu, yasa ta tara yaran masu wayo tace "wai kuna ganin bazamu gwada fita waje ba watara?"

Sahura tace "wlhi baba bashi da Imani kalli fa inda yake dukan su Hauwa, Hinde ta taɓe baki kafin tace "ina sha'awar fita waje domin inga ko meye a wajenan"

Sahura tayi tsaki, kafin tace "ina gaya miki lefin baba kekuma kina cewa zaki fita waje, idan kin fita ina zaki kuma da wane idon zaki kalli baba"

Hinde ta lumshe kyawawan idanuwanta kafin tace "idan har Allah ya bani iko na fita a gidannan wallahi bazan dawo ba, ga gurin zuwa da yawa, gidan mahaifiyar baabata nan zani"

Sahura ta riƙe baki, tasan tunda Hinde ta fara aikata hakan to babu mamaki zata iya fitar, saboda Hinde wata irin yarinya ce mai saka abu arai, inhar kuma tasa abun a ranta sai ta aikata ko zai zamo matsala a gareta, ga kafiya ga taurin kai bugu da ƙari tanada kyau mai ɗaukar hankali, amma chocolate color ce, tanada matsakaicin baki, idanuwanta ƙanana masu kyau,

Sahura tace "nidai ina roƙonki idan zaki fita a gidannan ki sanarwa baba"

Hinde ta buge bakin Sahura kafin tace "idan na sake jin maka manciyar maganar nan wlhi sai na illataki kin Sanni kin san halina"

Sahura tace "naji babu wanda zan gayawa"

Barira wacce ta kasance mai shekara 15 tazo kusa dasu tace "me ake cewa ne?" Hinde da Barira suka harareta, bata da yawan magana shiyasa aka bawa Hinde girman saboda tsaurin ido irin nata,

Washe gari Juma'a, mutanen gidan sunata hada hadar girkin abinci tun bayan da suka gama dakan kunu aka sha suka shiga yanka kabewa wanan na gyaran shinkafar tuwo wannan na markaɗa tumatur wannan na kula da fannin girki haka sukeyi ranar juma'a, lokacin da aka sakko sun kammala girkin kowa an samasa a kwano ko wacce ta koma ɗaki, Hinde ta shigo ɗaki tabar gurinsu Sahura, Barira na ganinta tace "mekuma ya faru?"

Hinde ta taɓe fuska kafin tace "Baabata zan bar gidannan saboda kema ki fita a wannan rayuwar, da sauri Hauwa ta kalli Hinde saboda mamakin maganar da tayi, musamman da takeda ƙarancin shekaru,

Hauwa ta riƙe baki tare da kallon bakin ƙofa tace "Hinde karki bari mutanen gidannan suji wannan maganar saboda zasu iya gayawa mahaifinki"

Hinde tace "nifa yanzu bana tsoronsa kune masu tsoronsa"

Hauwa tace "ina tausaya miki inhar kika bar gidannan mahaifinki zai cutar dani bayan haka kuma tausayinki nakeyi idan yaganki a waje zai iya kasheki"

Hinde ta kamo hannun Hauwa kafin tace "idan na fita zan nemi gidan iyayenki ki gayamin ina ne?"

Hauwa ta fashe da kuka kafin tace "rabona da ganin wani nawa yau shekara goma kenan tun dana haifeki ko na aihu babu mai zuwa gurina"

"Baabata ki rubutamin duk wani abu na gidanku tunda kince kinyi karatun Arabia"

Jikin Hauwa na rawa ta ɗauko alƙalami tayi rubutu a wata takarda kafin tace "kina fita a ƙofar gidannan ki miƙe gabas sosai hanya ce anan ne zaki hangi titi, ga wannan ƙuɗin nayi ajiyarsa tun zuwana gidannan kinga ma sanyi ya fara kamashi"

Hinde tace "baabata idan ba'a karɓi wannan kuɗin ba zanyi aikin kuɗi insha Allah"

Hauwa tace "dan girman Allah karki zubar da mutuncinki a matsayinki na ƴa mace"

Hinde tace "nayi miki alƙawarin hakan bazai faru ba"

Hauwa ta ƙulle mata takardar a cikin jakar kuɗin tace "akwai wani malami yana zama a cikin masallacin juma'a kiyi masa magana kice ke ƴar Hauwa ce yarinyar Usaini mai gidan duhu"

Hinde tace "to"

Daganan sukaci gaba da shawarwari tana sake kwantarwa da mahaifiyarta hankali tace "naji baba yana cewa yau zeje Jos yana tafiya nima zan fita"

Hauwa ta share hawaye kafin tace "babu ƙofa a gidannan ko kinzo fita ƙofar zata rufe kuma ta cikin ɗakinsa take"

Hinde tace "nifa duk wannan ba damuwata bane"

Hauwa tace "Hinde kina bani mamaki baki taki komai ba kike cewa zaki fita"

Daga tsakar gida sukaji Muryar Usaini yana cewa "toni zan fita zanje Jas banda shashanci"

Babu wanda ya amsa masa, Allah ya temaka ma ba takalmin suke sawa ba bare ya gane su nawa ne a ɗakin, ya fice ba tare da ya shiga ɗakin kowa ba.

KD

Hajiya Indo da Hanan suna tafe a motar Hajiya Rashida zuwa gidan ƙanwar Ummanta, sannu a hankali suke tafiyar har suka isa anguwar Sarki, a bakin get ɗin suka tsaya tare da danna horn mai gadin ya leƙo ya koma kana ya wangale musu get ɗin, suka shiga, nan fa kallo ya koma sama, hausawa sukace shaho yaɗau Giwa, duk yawon Hajiya Indo bata taɓa ganin gida mai kyau irin wannan ba, ya haɗu matuƙa, Hanan kuwa sai rarraba ido takeyi, har Hajiya Rashida tayi parking suka shiga ciki, da shigarsu da sallama suka sami hajiyar tana zaune da wasu maƙudan kuɗaɗe a gabanta kan table, Hajiya Indo ta lashe baki a zuciyarta tana aiyana wannan kuɗi kamar baza'a mutu ba?"

Sai da hajiyar ta gama lissafi kafin tace "ƴata kune a gidan?"

Munipa taje da gudu ta faɗa kan hajiyar, Hajiya tace "ƙawata anata girma ga haƙora na cirewa"

Munipa tayi dariya tana rufe baki, bayan sun gaisa Hanan dake zaune akan kafet itama ta gaisheta, Hajiya Rashida tace "Hajiya dama wai yarinyar nance ake don sama mata aiki koda a gidanki ne idan zamu samu"

Hajiyar ta jinjina kai kafin tace "leƙa kitchen kigani wlhi ƴan aiki sunkai biyar a haka ma inasan in sallama wasu, bari a kawo muku ruwa"

Rashida ta sauke nannauyar ajiyar zuciya kafin tace "to ko hanya ta gurinki bazamu samu ba?"

Hajiyar tace "zaku iya samu tunda inada ƙawaye, zaki tafi da ita gidanki ne kokuma zaki barta anan duk abinda ya wakana sai a sanar dake?"

Hajiya Indo tace "to nidai duk abinda akayi amma yau nakeson komawa gida"

Hajiya Indo ta faɗi hakanne domin taji ta bakinsu shin me zasu ce?

Hajiya Rashida tace "a'a mu koma gida idan har aka dai-daita da masu ɗaukar Hanan ɗin sai ki tafi, abar Hanan ɗin anan"

Cikin jin dadi tace "to" sai kuma ta ɗaure fuska tace "to yanzu sai gobe kenen? duk da dai dayau da goben duk ɗaya ne a gurin Allah babu damuwa,

Sukabar Hanan anan gidan sukuma suka kama hanyar komawa gida,

Suna cikin tafiya Abu Uzaifa yakira Rashida a waya, tana ɗagawa yace mata ya dawo gida bayajin daɗi,

Rashida ta ƙara bugun mota jikinta a sanyaye suka ƙarasa gidan,

Koda ta wuce bedroom ɗinta bata ganshi ba, ta dawo palo ta nunawa Hajiya Indo ɗakin kwana kafin ta koma bedroom ɗinsa ta sameshi a kwance jikin ma yayi sauƙin dama ciwon kai ne,

A hankali ta isa gareshi ta rungume shi tana cewa, "babyna jikinne ko yayi sauƙi"

"Yayi sauƙi karki damu Alhmdulilah"

Hajiya Rashida tace "to yanzu me kakeson ci?"

"Tea kawai zaki haɗamin is ok"

Ta fice kai tsaye ta nufi kitchen ta zubo ruwa a flaks ta haɗa masa tea ɗin mai kauri kafin ta kawo masa yashs.

Acan ɓangaren Hajiya Indo kuwa, ta gaji tayi lilis sai kuma tunanin farauto zuciyar Abu Uzaifa ya fara kamata, a fili tace "gaskiya mijin Rashida yayi min kyau wlhi ina sonsa da zeyi ta biyu dani wlhi dana more da nafi ko wacce mace sa'a"

Ta runtse ido tana tuno ta ina zata sami phone number ɗinsa?

Ta rasa ta inda zata samu bare tabi hanyar, da wannan tunanin bacci ya kwashe ta har akayi kiran sallahar magriba bataji ba tana bacci,

Hajiya Rashida ta shigo tana sanye da riga da skirt na atamfa ya mugun matseta komai ya fito sosai ajikinta saboda yanayin zaman ɗinkin, tace "Indo ki tashi an shiga Sallah"

Indo ta miƙe ido yayi ja saboda bacci gashi bai isheta ba,

Ta kalli Rashida tace "to Nagode"

Rashidar na fita Hajiya Indo tayi tsaki mtsww tare da cewa "wlhi tallahi sai na mallaki zuciyar mijinki da izinin Ubangiji"

Tana gama faɗar haka ta buɗe toilet ɗin dake gefe a cikin ɗakin ta shige tayi alwalah ta fito ta shimfida sallahya ta kabbara Sallah.

Abin mamaki gari yayi duhu, duk da ba'a mamaki da ikon Allah, bata ta6a tunanin kwana anan gidan ba, ko lokacin da take zuwa, iyakacin ta bada ƴan aiki ta wuce.

Acan gidan Hajiya kuwa, Hanan ta sata magana kamar zata ari baki,

Lokacin da Hajiyar ta shiga Sallah tana dawowa ta samu Hanan a zaune akan fridge hannunta riƙe da DuDu drink, sha takeyi tana lumshe ido, hajiyar tace "dan Allah a gidanku ba'ayi miki faɗa ne?"

Hanan tace "wlhi ƴan gayu kuna morewa shiyasa bakwa tuna Allah...

Hajiya ta riƙe baki a fusace ta....!

Ya kunshi cakwakiyar cikin labarin, masoya ayimin afuwa inhar kuna comments zango gaba da posting

*ALBISHIRINKU MASOYA MAKARANTA LITTAFIN MOM ISLAM, IDAN BAKU MANCE BA A CIKIN LITTAFINTA MAI SUNA _Falak🍒_AN ZUBA RUWAN BASIRA DA HIKIMA GURIN SARRAFA LABARIN, MARUBUCIYAR BATA YI ƘASA A GUIWA BA TA SAKE KAWO MUKU LITTAFINTA WATO _Guntun Goro_SHIN KUNADA LABARIN JARUMAR DA JARUMIN CIKIN LABARIN KUWA?? KARDAI IN CIKAKU DA SURUTU LITTAFIN _Wake ɗaya💍_ YAZO DA ZAZZAFAN SALO WANDA ZAI RIKITA TUNANIN MAI KARATU, LABARIN _Hanan marainiya da gidan Usaini mai gidan duhu_SHIN KUNSAN GWAGWARMAYAR DA TAKE FAƊAWA A GIDAN AIKI, TANAYIN NASARA, MEYASA IDAN TA HAƊU DA PRINCE JABEER FATAR JIKINTA KE SAUYAWA KUWA? AMSARKU TANA CIKIN LITTAFIN _Wake ɗaya💍_KUNADA LABARIN LITTAFIN YA TAƁO YARUKA HAR GUDA UKU MUSAMMAN MA GIDAN YARBAWA DA AKE KWASAR GWARAMA?, LITTAFIN BA ANAN YA TSAYA BA HARDA SIRRUKAN ZAMA DA MAI GIDA INSHA ALLAH, MAZA KU GARZAYO DOMIN KARATUN FITACCEN LITTAFIN DAYA BAZA MEDIA, KARKU BARI A BAKU LABARI, MUNA YIWA MASOYANMU GODIYA A DUK INDA SUKE*

Gamsu neman ƙarin bayani ku tuntuɓi wannan lambar, 08141799224 Mom Islam takuce..



*WAKE ƊAYA💍*

MomIslam



_True life story_





*Arewabook@momislam11





🆓 Page 5



Hajiya tace "waye ya gaya miki bama tuna Allah?"

Hanan tayi shiru, sai Kuma tace "dan Allah zan roƙeki wani abu ki taimaka min Hajiya"

Hajiya tace "ina jinki"

"Rabona dacin nama wallahi tun sallar laiyya da aka yanka mana bunsuru"

Hajiya ta zaro ido kafin tace "kina nufin kinkusa shekara kenan?"

"Eh wlhi ki taimaka inajin kamar zan ciji mutane"

Ai da gudu Hajiya taje kitchen, ta ɗibowa Hanan nama cikin kwano mai murfi harda ruwan sha, Hanan ta sakko tana rawa tana tafi tana cewa "a haiyye zamuci daɗi, a haiyye munzo binni da ƙafar dama"

Ko uffan hajiyar batace mata ba ta shige ɗaki ta barta a gurin.

Rashida••

Ta kawowa Hajiya Indo abinci mai rai da lafiya, soyaiyyar taliya mai haɗe da kayan lambu a fili ma ta bada kala inaga a ankai baki?"

Cikin farinciki Hajiya Indo tace "Nagode Allah ya biya ki"

Rashida tace "Amin to sai da safe"

Hajiya Indo tace "to Allah ya tashemu lafiya"

"Ke ƴar gayu harda saka wasu tsinannun kaya sai kace wata roba a ƙauyen mu wai ita Binta tsirara, mtsw"

Sai kuma takai lomar abincin bakinta, lumshe ido tayi ta buɗe kafin tace "wai-wai ai sai ya tsinke kunne, barin samu leda insa naci a mota gobe"

Cikin sa'a ta buɗe loka dake gefe ta samu leda, ta raba abincin gida biyu kafin tasa Kashi ɗaya a leda taci ragowar.

Tana gama ci aka kira sallahar isha'i ta kuskure bakinta kafin tazo ta kabbara sallah, tana idarwa tayi adu'oi harda na mallakar Abu Uzaifa, daga nan ta ninke sallahayar ta bi lafiyar gado, a fili tace "ban taɓa jin jimamin rashin miji ba sai yau"

Ta runtse ido, nan da nan bacci yayi awon gaba da ita.

Acan ɓangaren su Hajiya Rashida tace "Please baby idan ka gama cin abinci inason muyi magana"

Abu Uzaifa yace "to momyn Munipa ina jinki"

Hajiya Rashida ta kwanto a kafaɗarsa kafin tace "uhm dama inason zuwa gobe idan Allah ya kaimu kakai wannan baƙuwar tamu tasha idan sun gama abinda sukeyi Please tanada kirki wlhi"

Abu Uzaifa yace "hamm Rashida kenan, nifa ban cika son ɗaukar mutane a mota ba gaskiya kice tahau haya"

Hajiya Rashida ta haɗe fuska cikin fushi tace "to ai naga na isa dakai tunda kai mijina ne shiyasa nace haka"

"To tunda kin matsa shikenan Allah ya kaimu goben"

"Please akwai wata tambayar ma"

Ya zuba mata ido yace "ina jinki"

"Meyasa bazaka dinga hutawa Weekend ba"

Abu Uzaifa yayi murmishi yace "zan huta wataran".



Ya kalli Munipa da tuntuni tayi bacci yace "Munipa iyayen surutu anyi bacci"

Washe gari.

Ranar ta kama asabar, an tashi da sanyi mai shiga jiki, tun bayan sallahar asbha da sukayi basu fito ba, suna rungume da juna cikin blanket, Hajiya Indo na taja bargo tanason azo a tasheta, taji shiru, dole ta sakko tana sababin cewa "dan asara baccin sukeyi har yanzu basu san gari ya waye bane?"

Bayan ta fito daga toilet ta kalli agogon dake manne a bangon ɗakin tace "ƙarfe takwas a fa? na shiga uku, amma mutanen gidannan sun zama shegu suka barini na dingayin baccin asara?"

Tana idarda sallah taje gaban dress mirror taja wata madai-daiciyar kujera ta buɗe lotion ta shafa tana lumshe ido, tace "har naga irin murmurewar da zanyi inhar na shigo wannan gidan, ku kalla fa ɗakin saukar baƙi ne akayi masa wannan aikin asarar Kamar basu san darajar kuɗi ba"

ta ɗauki hoda ta shafa ta sanya janbaki pink, sai gashi ta fito rass da ita kamar mutuniyar birni,

Ƙarfe 9:11am Hajiya Rashida ta shigo ɗakin da Hajiya Indo ta kwana, lokacin ta gama kwalliya harta kwanta,

Tana jin shigowar Hajiya Rashidan taƙi koda motsi ne, saboda tana daga kwance wani azababben kishi ne ya kamata, a zuciyarta tace "yanzu haka sunyi abin dan wlhi bazasu kasa yiba sun barni a gantale"

Hajiya Rashida tace "Indo ki tashi an kammala karin kumallo idan muka je gidan Ƙanwar Ummana sai kidawo mu tafi, kokuma Abu Uzaifa ya wuce damu idan an dace sai ki wuce tasha, a zuciyar Hajiya Indo farinciki kamar ta rungume Rashida haka takeji, a hankali ta sakko tare da ƙanƙance ido irin na mai baccin safe tace "to shikenan babu damuwa mungode da ɗawainiya, samun irinku a duniyar nan wallahi sai an tona"

Hajiya Rashida tace "harda zan kawo miki ruwan zafi ashe har kinyi wanka?"

"Eh nayi kinsan ni da ruwan sanyi nake wanka shiyasa"

A zahiri kuma kwas-kwarima tayi.

Lokacin da Hajiya Indo ta fito Abu Uzaifa ya koma ɗaki, domin yasa Uniform ɗin gurin aikinsu,

Hajiya Indo anzo dinning an ruɗe saboda abinci data gani kamar banza, kuloli uku ne a jere a gurin masu masifar kyau, ɗaya cike da soyayyan nama ɗaya kuma farfesun kifi ɗayar tuwon shinkafa ne fari ƙal miyar da miyar shuwaka taji busashen kifi da naman kaza, Hajiya Indo ta wato ido kafin tace "waɗan can kayan basur ne ga inda zanci in ƙoshi kuma in yaga kaza"

Indo ta fara ci kamar an aiko ta, sai data cinye malmala huɗu tasha ruwa, ta ɗibi soyayyan naman ta tura a breziya taci farfesun kifin tunda shidai baze ɓoyu ba, ta karƙaɗe zaninta, ta dawo ɗaki, tunani ta fara yi tace "kamar naga gwangwanin madara akan teburin nan fa, anya bazan koma ba ina kuma ci dan idan natafi bansan larabar dawowata ba"

Tana tsaka da tunani Hajiya Rashida ta shigo tace "to na shirya kizo mu tafi"

Hajiya Rashida na fita Hajiya Indo ta tura ledar data haɗa soyayyan nama da soyayyar taliya guri ɗaya ta jefa cikin haka kana ta zuge zip ɗin ta kuma zuwa gaban mudubi ta kalli fuskarta tayi waje, a parlo ta tarar da Hajiya Rashida a tsaye tana jiranta, Hjya Indo na zuwa suka wuce parking space, Hajiya Rashida ta shiga gaba, Indo ta buɗe baya, ta rufe ƙofar tana cewa "Alhaji ina kwana"

Abu Uzaifa yace "lafiya lau" daga haka sukaci gaba da tafiya.

Suna isowa gidan hajiyar yayi yayi, parking a ƙofar gida suka fito suka buɗe get ɗin gidan tare da ƙarawa ciki,

Sallama sukayi, hajiyar ta amsa da wlkslm tare da basu umarnin ƙarasowa, suna shiga suka zube kan kujera, bayan sun gaisa Hanan na zaune gaban T.V tace "Baaba Indo nidai bazan koma ba a gidannan zan zauna"

Ba maganar Hanan ɗin takeso jiba shiyasa bata ce da ita komai ba.

Hajiya tace "Rashida an sami gidan aiki ammafa matar tanada tsanani kuma yara basa shekara a gurinta wata huɗu zasuyi ta tura su wani gurin aikin"

Rashida ta kalli Hajiya Indo da hankalinta ya kwanta yanzu saboda damuwarta kuɗi ne bawai wahalar da Hanan ɗin zatasha ba,

Hajiya Indo tace "Alhmdulilah ai komai yayi dai-dai inhar kin yarda da ita Hajiya babu damuwa"

Hajiyar tace "ƙawata ce tun muna yara amma tanada faɗa, ga wannan dubu ɗari ne tace a baku"

Jikin Hajiya Indo na rawa ta durƙusa ta ƙarɓa, Hajiya tace "aciki dubu hamsin shine na aiki shikuma ragowar hamsin ɗin na kaya ne da zava siyawa yarinyar saboda batasan ƙazanta"

Hajiya Indo tace "ai shikenan komai yayi zan barwa Hajiya Rashida kuɗin wannan sai in kaiwa iyayenta"

Daganan tayi musu sallama tare da yiwa Hanan faɗa akan kintsuwa ta kuma karɓi lambar hajiyar Rashida ta rakata bakin mota sukayi sallama, Abu Uzaifa dake jiranta tun ɗazi harya ƙosa.

"Kayi haƙuri Alhaji na kanata jirana"

Abu Uzaifa yace "babu komai"

Tana shiga yatada mota, suna cikin tafiya ta fara karanto izaja'a nasrullahi sai da tayi ƙafa bakwai kafin tace "Allah ina roƙonka kasa duk abinda nacewa wannan bawan naka ya amince"

Duk a zuciyarta take wannan maganar har suka kusa zuwa tasha, tace "Alhaji dan Allah ko zaka bani lambarka in dinga jin labarin Hanan? na mance ban ɗauki lambar hajiyar ba"

Abu Uzaifa yace "ok babu damuwa kawo wayar insa miki"

Ta miƙa masa wayar tata wace ta gaji da gararin duniya me botir tace "ga ta"

Sai da ya shiga cikin tashar kawo sannan yayi parking ɗin motar yasa number tasa kafin yace "to Allah ya tsare ga dubu biyu babu yawa"

Hajiya Indo tayi masa godiya kafin tace "Alhaji badan kar kace nayi munafurci ba wlhi dana gaya maka wata magana"

Abu Uzaifa yace "babu komai ina jinki"

Hajiya Indo ta sosa gefen fuskarta tace "dama naji labarin ance Hajiya Rashida tasi gidaje har uku tana kan gina na huɗu shine nace in gaya maka tare da yi muku Allah ya sanya alkairi naji ance wai Munipa ma ba ƴarka bace wai ta wani mutumi ne mai kuɗi, wlhi ban riƙe su ansa ba"

A gigice Abu Uzaifa ya kalli Indo kana yace "wace hujja kikeda ita da zata bani damar amincewa da maganarki"

Hajiya Indo tace "ɗazu ka kaimu gidan wata Hajiya wace Hanan take gurinta, sun barmu a parlo suka shige ciki, nikuma dason jin gulma nabisu na laɓe a bakin ƙofa inajin lissafin da sukeyi har Rashida na cewa wai baban Munipa yafika iya kwanciyar aure, wai kai sai kace ba

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login