Showing 3001 words to 6000 words out of 22673 words

Chapter 2 - BAKIN SHAFI

Start ads

05 Sep 2025

85

Middle Ads

kirar jikinsa cikin dar dar tace


'' malam fuce min daga daki...,


shiru yayi mata ba amsa ratsawa tayi zata fita ta bar mai dakin ya riƙo mata hannu fisgewa tayi tana cewa bana bukatar ganin ka nace maka ka fitar min daga daki wannan wacce irin kaddara ce ba za a bar zuciyar mutum ta huta ba daga wannan sai wannan


ba ruwan Ubangiji ke kika saka kan ki a ciki


zama tayi a ƙafa tayi shiru zuciyar ta na tsananin bugawa daguwa tayi taga ya fita jan tsaki tayi ta rufe kofar ta dakyar ta samu tayi bacci


washegari wanka tayi ta shirya cikin riga da wando amma wandon falazo ne Golding colour da riga milk colour stocking dinta gashi wuyan rigar
up-shoulder ne ko yaya tayi motsi ana iya hango kirjinta ɗaukan jakarta tayi ta riƙe a hannu ta yafa mayafi a kafaɗa takalmin kafar ta hil ne shafa kanta tayi shaf ta manta da wula kawai sai ta saka mayafin ta a ka tafiya take tana taku dai-dai har ta fito Parlour kallon rashin fahimta dada take mata tace


'' Khadijah sai ina kuma...?,


kallon a gogon hannun ta tayi tace


'' zooroad...,


ban gane zaki tafi zooroad ba


dafe kanta tayi tace


'' ya Allah dada zanje na bude shagona fa..,


gutsurar tufa tayi tana ci tace


'' Allah ya shirye ki haka kurum kin zamar da kanki na miji in banda zamani ina mace ina buɗe shago ta zauna...,
ɗago wa za tayi suka haɗa ido da altab yana cin wainar shinkafa da miyar a gushi kau da kanta tayi daga shi har rufa'i wallahi ba wanda zata gaisar tace


'' Dada ba laifi bane mace ta nemi halak ɗin ta kinga Allah ya sakamin albarka na har shagon saloon na bude...tun ina yin online na buɗe shago..,


wallahi kuwa da ace miki zaune gari banza gwara ki nemi abin yi cewar rufa'i


ya tsuna fuska tayi ɗagowa tayi jin sallamar blood line hugging din sa tayi tana cewa good morning blood line


morning beautiful lady


cika shi tayi yace


'' beauty me ya samu wayar ki ina ta kira a kashe..,


ta sami matsala yanzu ma wata zani na siyo kafin na buɗe shagona


a'a nasreen ina zuwa haka zuwa fa anjima za a kawo amarya cewar adda asma


murmushi tayi me cike da ma'anoni ta samu damar kuntatawa altab tace


'' yanzu aunty me ya hadani da kawo amarya na tafi neman arziki ko da yake duk neman da kake baya cire ka daga zargin mutane ba..,


hannunta khalil ya kama yace


'' muje na siya miki wata special gift happy birthday to you..,


zaro ido tayi shaf ta manta da yau birthday din ta tace


'' wallahi na manta abubuwan sun min yawa nagode sosai..,


idanuwanta duk ya ciko da kwalla karki damu aini ina sani ummi ma tace '' na taya ki murnar zagayowar ranar haihuwar ki...,


da sauri ta kallesa cikin mamaki tace '' anya kuwa...,


Wallahi da gaske nake kinga sakon da ta turomin


ture wayar tayi tace '' basai na gani ba da motar ka za mu tafi ko da tawa...?,


farin cikin ki shine nawa


murmushi tayi tace '' nima haka..,


fita sukai a tare suna hira adda asma ce tace




'' Allah sarki khalil komai yana yi domin ya kawar mata da damuwar ta..,


taɓe baki dada tayi tana cewa kinga alamun ta damu ne kike faɗar haka


dada abin fa zai mata ciwo wallahi kawai dai tana kawar wane dan ma duk tarin kawayenta ba wanda ta gayyata wasu ma basu san za ayi bikin ba...


Wannan shine rufin ashirin da Ubangiji yayi mata da fita ma sai ta gagareta dada ta faɗa cikin takaicin abin


addu'a nasreen take buƙata Allah ya kawo karshen abin nan


cewar adda asma


tabe baki altab yayi yana tashi binsa rufa'i yayi yace




'' dada sai anjima..,


kun gama cinye mata waina ai dole kuce zaku tafi


dariya rufa'i yayi yana cewa adda asma kenan kuɗi muka bata tayi mana tambaye ta idan karya muka yi


a'a abin harda sharri ni ko ficika ba su bani ba


Dada wane be san halin su ba sai addu'a


barin kar wannan mutumin yaji labari wallahi ni tausayawa yarinyar nan nake auran soja ba dad'i wallahi daman gashi ga halinsa


wallahi kuwa kawai dai Allah ya saɓa hali
cewar adda asma


Wannan kenan


wani shu'umin murmushi take saki tun ɗazu ko banza ta nuna mata ƙarfin ikon ta wace mata barno gabas ce kaɗan ta fara gani wallahi


mamy da sauri ta jiyo tace


'' basma lafiya kika shigo min ba ko sallama...,


wallahi nayi kece dai baki ji ba kina tunani


ajiyar zuciya ta sauke tace


'' to me kika zo yi...nan ..?,


wani ne yazo a baƙar mota yace '' na ƙira ki...,


cikin sauri tace '' okay na gane ce ne mai muyi magana ta waya..


har ta juya zata tafi da sauri tace '' mata tsaya kawai tafi na ki guri za mu yi magana ta waya


amma mamy wane shi...?,


basma bana hana ki irin wa'yannan tambayar ba maza maza zo ki wuce ki bani guri


fita basma tayi batare da tace komai ba wayar tace tayi ringing da sauri ta dauka tace


'' aminiya ta wallahi ban taɓa zaton wannan shirik namu zai yi ta siri ba sai gashi lokaci ɗaya mun burkita zuri'ar me tangaran...,


wata shu'umar dariya kawar tata tayi tace


''ai idan har zaki ci gaba da ɗaukar shawarata to wallahi kowa sai kin gyara masa zama...,


limshe ido tayi tace '' ai kuwa dana fi kowa murna wallahi...,


sallama sukai sannan ta kashe wayar shaf ta manta da batun me jiranta a waje


Wannan kenan


Cikin nishaɗi suka fito daga wajen saida waya tsayawa yayi yace


'' ni zan koma akwa wanda zamu haɗu dashi anan ga shi can yana jirana...,


langwaɓar da kai tayi tana cewa gaskiya naji dadi sosai wallahi Nagode Allah ya bar zuminci


amin ya Allah ya faɗa yanayin gaba buɗe motar ta tayi ta shiga a hankali ta fara tafiya har ta isa zooroad fito da mukulli tayi ta buɗe shagonta tana shiga jazz da shi da pretty suka shigo kallon su tayi tace




'' Allah ya rufa muku asiri baku daki gurbi ba ban dade da zama ba..,


zama sukai jazz tace


'' lallai kam jiya nai ta kiran wayar ki switch up me ya faru bayan mu gama tsara guri har 2:49 ina club...,


BAƘIN SHAFI


oum yasmeen


EPISODE 3

Previous to the last page


'' lallai kam jiya nai ta kiran wayar ki switch up me ya faru bayan mu gama tsara guri har 2:49 ina club...,


Continue


ajiyar zuciya ta sauke tace '' wayata ce ta lallace..,


fito da syrup pretty tayi ta buɗe tace '' Allah ya kiyaye gaba..,


amin ya Allah amma dan Allah kar ki sha ba zai yiwu ba customer's su zo min ba ana kallon ki ki ta tun ɓele..
haba nasreen ya kike mana yawa ne yanzu ni nake tunɓelen yawa wata akuya ko tinkiya


Pretty ta faɗa tana kai Syrup bakin ta tunda ta saka shi tas sai da ta shaye shi ta wurlar da kwalbar fashewa tayi da sauri nasreen tace


'' wallahi sai kin share min anya kuwa ina cikin nutsuwar ki..?,


ina fa take cikin nutsuwar ta sunyi faɗa da bash


Jazz ya fada yana dariya


tashi nasreeen tayi ta cire mayafinta tace '' ya kake mata dariya..yau dara fa ba dad'i wallahi tama yi kokari da ba faɗi ba an kwashe ta..,


Nasreen kenan ya ali yaga ali fa akai ya fito daga dakin hotel ta fito ina abatun damuwa shine fa har da marin budurwar indai takaice miki labari kaca kaca akai har sai da yan sanda suka shiga cikin lamarin yanzu bashi ba ita shine fa ta shiga cikin wani hali


to mene abin damuwa tunda ke kin aikata shima ya aikata ga ani na gaskiya ba abin daga hankali ko ki damu


baza ki gane ba wai mutumin nan fa yan sanda ya faɗa suyi mana tsakani da shi kin ji fa wani rainin hankali


tashi tayi ta zauna kusa da jazz ta kwashe da dariya shima dariyar yake yace


'' wallahi ban taɓa ganin original yan iska ba irin bash da pretty yau ya saba kai ta gurin yan sanda nifa gani nake kamar fa ya raina su wallahi..,


buɗe fridge tayi ta ɗauko lemoka ta miƙa musu itama ta buɗe tana cewa gaskiya nima ban taɓa ganin haka ba kar kai mamaki dan da wani watan su koma su jone


wallahi kin kai da nisa ki basu nan da zuwa sati ki gani duk yadda kike tunanin su to wallahi sun wuce gurin cewar jazz yana shan lemo


ita dai pretty tayi shiru domin ba a cikin hayyacinta take ba dan ma dai Allah ya rufa asiri bata surutai beb yau fa naga tsohon dan iskan nan sabeer ke kinga kallon da ya jefe ni da shi...kin fa cool esay ce take faɗamin ya fasa auren ki yanzu maganar ake tayi a media


da sauri ta ɗago lemon da ta kurɓa kasa haɗewa tayi ta furzar dauko wayar sa yayi yace '' kalli..,


da sauri ta karɓa idan wata futsararriyar yar tiktok sanye da towel ta riƙe brush take cewa


Update update jama'a har zan shiga wanka naji wannan labari nace ba zan bari ta wuce ba tare da na faɗa muku ba asirin dai NASREEN MAI TANGARAN ya tonu ana ƙoƙarin daura auren ta miji yace ya fasa saboda yar iska ce akwai video ta duk me so ya je internet yayi searching wannan account din saboda gudun yi min blocking account Dina Zan dora muku anan


idanuwanta ne suka ƙada sukai ja sabeer ya gama cutar ta tsakanin ta dashi saidai Allah ya saka mata wayar ta ce tayi ringing da sauri ta dauki jaka ta buɗe ta dauko ganin sunan baffa rado rado gaban ta ne ya waɗi hannun ta na rawa ta dauka muryar ta na rawa tayi sallama a wannan karon ba be amsa ba daga jin muryar sa yana cikin tsananin baƙin ciki yace


''Duk inda kike ki zo parlour ina son ganin ki..,


jin sauti kamar ya kashe ta kalle wayar kallon jazz tayi tace


'' su mary za su zo yau naga ba su zo da wuri ba zan je gida ana son gani na..,


Okay ba damuwa sai kin dawo ɗaukan jakarta tayi da key ta fita cikin sauri ta buɗe motar ta ta shiga gudu ta dinga sharadawa har ta isa gida fitowa tayi ta fara knocking gate din


tana maida hannunta za ta ƙara bugawa me gadi ya buɗe shiga tayi yana mata magana ma da yake hankalinta ba akan sa yake ba har ta isa part din baffa tana tunani bata san me ya saka sa kiranta ba shiga tayi bakinta dauke da sallama


gabanta ne ya waɗi ganin daddy abbey abban yaya uncle Yusuf jikinta ne ya ƙara sanyi ta ƙarasa zama tayi wani kallo baffa ya watsa mata tare da miƙa mata waya bata san me yake nufi da haka ba hannunta na rawa ta amsa ɗagowa tayi suka hada ido da Altab sai a lokacin ta fahimci wa ya wura wutar kallar wayar tayi gaban tane ya waɗi ganin akan a ke maganar amma duk wanda ya tsaya yayiwa...


Video kyakkyawar fahimta ba ita bace ba ɗagowa tayi tace


'' yarfen yan media ne wallahi bani bace ko daban ba kunyar mutane ko dan kunyar Ubangiji na bazan so na aikata abin da zan zo nayi dana sani ba wallahi masu editing ne suka haɗa wannan baƙin shafi suka so su yi min amma kai wa vedio kallo na tsanaki bazan so na zubar da mutuncin gidan nan...,


Rufe min baki daman ke baƙin ki baya mutuwa to daga yau kune yayana ku sheda shima zan kirawo mahaifinta na sheda mai na cire hannuna akan ta ke Khadijah kema ban yarda ko kwayar shinkafa ki bata ba tun da bin da take kenan ta ci da kanta...


tana so ta ƙara maimaita mana abin da ya faru shekarun baya idan shekarun baya na iya ɗaukan tension din abin da ya faru to a wannan karon ba zan iya dauka ba kamar yadda na zare hannu akan ta kuma ku zare rayuwar duniya darasi ce wata ran zata koya mata darasi wanda zai zauna a kanta har abada tunda yanzu darasin da Ubangiji ya nuna mata be mata ba har taje ta ƙara wani abun


Baffa kai hakuri idan hankali ya gushe tunani ke dawo da shi be kamata mu zuba mata ido mudai ci gaba da yi da baki da kuma addu'a har Allah ya dawo da ita kan tafarki


Cewar dada


Wani kallo yayi mata ya ɗauke kai ya Khalil ne yace


"Baffa wallahi nasreen baza ta taɓa aikata haka ba kawai dai abin da nasani tana tare da mutane nan banza..ni zan aure ta..,


wallahi ban yarda ba ai daman idan ka ga kare na shinshina takalmi ɗauka zai yi to wallahi ban yarda ba wata kila ma yanzu haka ma wata kila tana ɗauke da cutar kanjamau..


Cewar mamy tana wura hanci shaf idanuwanta sun rufe ashe harda man tan gidan aka haɗa taron


ƙasa tayi da kai tace


'' ko baki faɗi haka ba zan taɓa auran sa ba ya khalil na gode da irin karamcin ka a gare ni...,


Cikin baƙin abba yace '' futsararriya ana magana kina mai da wa karya tayi ba ta hanyar ake samun cutar ba wallahi kin zame mana baƙar kadara...,


ko ganin gaban ta bata yi fita tayi bata tsaya ko ina ba sai a wajejen motar ta bude wa tayi ta shiga ashe ya khalil ya biyo ta ganin yana ƙoƙarin tsai da ita ta fisgeta yau zata aikata abin da kowa yake fatan aikatawa yau zata sama duk abin da suke cewa tana yi


basu da fahimta ne taya zasu ga wannan video suce ita ce a gaban wani joint ta faka ta fito shiga tayi wajensa ta zauna a gaban me sai da wine tana zuwa ya jera mata kwalba biyar ya buɗe wata ya zuba mata a glass cup ɗauka tayi har ta kai baƙin ta sai kuma tunanin ta da ya gushe ya dawo a hankali ta furta


Ya ayyuhalladhina amanu innal khamra wal maysira wal ansaba wal azlamu rijsun min 'amali shaytani..,


sauke wa tayi ta miƙa mai ATM ya cire kuɗin wacce ya fasa mata ta fito daga gurin jikin'ta na rawa cin karo tayi da ya khalil cikin rawar baki yace


'' nasreen daman kina shan giya...? Ina ilimin ki da tunanin ki yake me zata amfanar da ke abin da Ubangiji ya hana shi kike yi wallahi a yanzu kin fara saka min shakku akan ki..,


kai ta girgiza tace


'' I went because I drank, but one time God brought back my thoughts that I didn't drink..,


wani kallon rainin hankali yayi mata sannan ya juya batare da yace komai ba ya shiga motar sa cikin sauri ta ƙarasa amma tuni ya ja ya tafi shiga tayi cikin motar ta ko gabanta bata iya gani


a da tayi niyar daukan mataki akan wa'yanda sukai mata wannan abu a yanzu kowa da kowa ya zare hannunsa a kanta komai ta fice mata a rai tana fatan Allah ya ɗauki ranta ta huta daman maganar uwa da uba ba a maganar su suna can wata duniya ma banbanta suna can suna rayuwa successful ba wata damuwa ita dai sun ruga sun cutar da ita sun haifeta ta hanyar da bata kamata ba gashi nan rayuwa sai watan gaririya take da ita..


a hankali ta fara tafiya cikin gushewar hankali ji tayi ta ci karo da wani abu ɗaga nan bata ƙara sanin inda take ba


gashi titin nasrawa JRA ne ba mutane sosai mota ma zuwa take fit ta wuce tamkar walkiya raka raka gaban motar yayi kanta ya bugu da glass din taka ya fashe


BOMFAI JAR....


Sosai suka shiga harkar idimar abinci saboda masu kawo amarya suna kan hanya adda asma ce ta ajiye flask din hannunta tace


''maman iffa dan Allah kinga dawowar nasreen wallahi tun dazu zuciya ta ƙasa nutsuwa da fitar da tayi bata cikin hayyacin ta be kamata a barta ta fita a wannan lokacin ba duk kuwa irin laifin da ta aikata a wannan karon baffa ya nuna tsani da yawa wallahi ban taɓa zaton zai yi haka ba...,


to ke mece damuwar ki ina cewa iyayenta ma sun watsar da ita kina ga dan tashin nuna mahimmancin auren yar su ba wanda ya zo a cikin su gwara shi abban sufwan ma ya turo da kuɗi mahaifiyarta fa wa yasan inda take tunda iyayenta suka kawo ta suka wuce Cameroon sun ƙara waiwayar ta dan haka ba ruwanki da duk wata sabgarta ai daman buri yayi kama da mutum ke kinga uban shagon da ta bude a zooroad ta fake da bashin baki taci ubanta ne ya bata kudin da ta bude idan ba karuwanci take ba


innalillahi wa'inna'ilaihir raji'un kinga zato zunubi ne wallahi ta nuna min komai yanzu ma ta kusan biyan su


dariya dukkan su sukai maman iffa tace


'' lallai ta mai da ke wata bita can yanzu mene ba ayi fake domin ta rufe mutane abokin dan iska Dan iska ne wallahi ga mutanen da take yawo da su baki ga uban birthday din da tayi ba ko ina shi kaɗai wallahi ya ci a zarge ta nifa mamy tayi min dai-dai da tace danta bazai aur ta ba ko nice abin da zanyi kenan yar iska kawai sai aikin girman kai..,


Maman arfa tace


'' ai wallahi gwara da suka budewa shegiya aiki yau ma naji ance za aje a kwaso kayan da aka jera a gidan da za akaita sun dauki kayan lefen su ma...,


kai adda asma ta girgiza ta fita yan kawi amarya ne suka zo da uwar gararsu bayan an Kaita gurin

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login