Showing 15001 words to 18000 words out of 22673 words
kanwa kamar haka amma be fada mai ba yasan irin matar da yake burin aura amma be taɓa faɗa mai ba khalil ne ya shigo kallon ta yayi yace
'' ina zaki bace min kikai ba kin gaji kina so ki wuta..,
dan ya tsuna fuska tayi ta langwabar da kai tace
'' blood line ina so na je saloon kaina yayi min nauyi sannan zan biya restaurant nayi take away zan je na siya mota tun da waccen ba a san ranar dawowarta ba..,
da sauri ya kalleta jin wannan uban lissafi da take yi ko da yake kayan dubu nawa ne a shagonta yace
'' amma kya bari ki sami lafiya sannan dan girman Allah ban da zuwa..,
da sauri ta saka mai yan yatsunta a bakin sa kasa kasa tace
'' ban da zuwa club..,
Sannan ta cire hannun ta daga bakin sa dafe kanta tayi tace
'' da ace karatu ne wannan maganar da na ruga da na gama cin jarbawa idan aka zo yi min saboda na hadda ce kullum maganar ka ɗaya...,
komai da ke nake yi domin kyautatuwar taki rayuwar nake yi nasreen
juyawa tayi ta haɗa ido da altab murmushi ta sakar mai wanda ya kusan zumar da Nasir tace
'' are any way barana na tafi kar nayi wasting time..,
muje na sauke ki
girgiza mai kai tayi dan mayafin da ta yafa ya zame daga kanta raba gashin ta gida biyu tayi tayi kitson nan two step tace
'' okay muje..,
kallon abokanan altab yayi yace
'' soja marmari daga nesa sannun ku kun iso lafiya..,
dukkan su suka masa da alhamdulilah Nasir yace
'' soyayya ta rufe maka ido sai yanzu ka gan mu..,
dariya Khalil yayi yace
'' wacce soyayya kuma muna tauna babban issue ne ya aiki..?,
Alhamdulilah nasreen gaba tayi tana fito da chingum ta saka a bakin ta ganin suna neman cinye ta..,
binta Khalil yayi tabe baki sharifa tace
'' da wannan kyawun nata take rudar maza kinsan shekaran jiya basma da tazo wucewa ta islamiyyar mu lokaci kina aji ta ga wata ta fito malam sunusi wanke hannu ya dinga yi ranar ba ƙaramar dariya nayi ba ..,
dariya basma tayi tace
'' ai ta can canta wallahi komai nata me kyau ne..,
duk da kasa kasa suke hirar su amman altab yana jin su da sauri basma ta tashi tana cewa kai wallahi na manta kinga ban tambaye ta ba nawa take Saida wannan lace din da best tace a shagonta ta siya da sauri sharifa ta riko ta tace
'' ga wani zubar da kai ki tambayi besty mana kinga ina rabaki da shiga sabgar nasreen wallahi a kirkine da ita ba...,
dariya mubaraka tayi tace
'' wallahi ba kusan wace ce ita ba , bata da girman kai tana da saukin kai a haka ne zaku zata kamar zata wulakanta dan adam..,
dada ce ta jiyo tace
'' kudak tsai gumin ku yayi yawa wallahi.. anya ba kai ku zan yi ai muku irin training din sojojin ba ko kwayo hankali...,
dariya dukkan su suka saka ban da altab da ya nuna kamar ba me san be ake ba sai danna waya yake nasreen ce ta shigo da sauri dada ta kalleta tace
'' kin fasa fitar ne..,
a'a ban fasa ba abu na manta wallahi gaji bana son sake hawa saman nan amma ba yarda zanyi dole na hau
Dada tace
'' kinyi dai kidan ki kinyi rawar ki ai gwara ki dinga motsa jikin ki in ba haka ba kiba za tayi miki yawa..,
adda asma da ta shigo yan zun nan tace
'' ai ita nasreeba ƙiba ce da ita ba kawai tana da hibs ne da girji shi yasaka wasu ke mata kallon kiba ce da ita..,
Dada ce tace '' eh kuma fa haka ne .,
gaishe da ita sojojin nan sukai nasreen ta hau sama bata dade ba sai kata ta sauko da wata leda a hannun ta cikin sauri ta fita tana zuwa wajen da khalil yayi parking ta tarar yana zaune zaman jiranta tace
'' ya khalil Dan dai da mutane na kasa yi maka musu dazu baka ji abin da mamy tace ba mahaifiyar ka ce yi mata biyayya ya zama dole nagode sosai da nuna kulawar ka amma ka barshi zan tafi a napep..,
haɗe rai yayi yace
'' yaushe muka fara ja in ja dake ki shiga mu tafi..,
ba yarda ta iya haka ta shiga amma zuciyar ta ba dan ta so ba tafiya suka fara yi ba wanda ya cewa dan uwansa komai wayar ya khalil CE tayi ringing a kusan lokaci ɗaya suka kalli wayar ɗauke kai nasreen tayi tana limshe idanuwanta kallon ta yayi ya ƙara mai da kai ya kalli wayar nasreen kishin sa take ko me abin da ya kasa tantance wa matar da yace zai aure ta , tace bata so ko kuma akwai wani abu a sau uku ana kira ba picking sai me gyaran ya katsai
ci gaba yayi da tukin ya sakae musu waka kaɗan ya rage volume din yana bi ɗa gowa tayi tace
'' ya khalil waka daman ka iya...?
dariya yayi yace
'' ai duk wakokin yayin nan na iya nasreen ina zaune a office ba ni da aiki na gaji da bincike sai kawai na shiga na internet naji..amma bana dauko ta ,
dariya tayi tace
'' ya khalil kenan me ne marabar dambe da faɗa daman barta kayi a cikin wayar ka ta rage maka saukin batar da data..,
Jan kumatun ta yayi yana yar waka kau cewa tayi tana dariya sosai yanayin na yau ya sata cikin nishadi da walwala tace
'' blood line duk ran da kai aure baka da lokacina ko sai na matar ka..?,
sakar staring wheel yayi ya juyo ya kalleta yace
'' ke ba zaki auren ba ne...?,
ba tayi tunanin fitowar wannan magana ba daga bakin sa wasa ta fara da faratan hannunta tace
'' I don't feel like getting married ya khalil abubuwa da yawa sun faru I think not getting married is the solution muryar ta ce ta sarke tissue ta yago ta goge hawaye da ya taru a idon ta taci gaba da cewa whoever his parents will tell him ya ji ya ɗauki shawarar su ba zai iya aurena ba saboda The black paint that people gave me ban yi tunanin zan ci gaba da rayuwata normal ba tunani nake gwara na mutu na huta wannan rayuwar cike take da fake love, fake people dakyar ka samu mutum ɗaya like you wanda zai so mutum dan Allah gaskiya sabeer ya cuce ni temakon da Allah yayi min ba a daura ba yace ya fasa...,
idanuwanta ne suka kada sukai ja ta kasa ƙarasa maganar sai ta rushe da kuka kyalete yayi, tayi me isarta sannan yace
'' nasreen ko wanne bawa akwai irin jarabawar da Ubangiji yake mai idan ya saka hakuri sai kiga ya cinye jarabawar da Ubangiji yayi mai ko bayan aurena zaki ce na faɗa miki insha Allahu komai zai zama tarihi..,
da sauri ta ɗago tace
'' insha Allah zan bi shawarar ka amma saboda me ya saka kace ko bayan ranka...,
dariya yayi yana shan kwana yace
'' kullu nafsin za'ikatul maut duk kan me rai mamaci ne wannan ran da aka bamu arone wannan duniyar ba ta gaskiya bace akwai gidan gaskiya...,
Please kayi shiru bana son wannan maganar mutuwar gurin me gyaran mota kenan zamu fara zuwa cewar nasreen ta fada tana kallon titi
eh nan zamu fara zuwa akwai wani abun ne ...?,
kai ta girgiza mai tafiya kadab suka ƙara suka isa yana ganin su ya taso tare da dauko wayar nasreen dewa sukai suka fito Khalil ya miƙa mai hannu suka gaisa yace
'' ya gyaran komai yana tafiya dai-dai..,
eh komai yana tafiya dai-dai mu ka kusan gamawa ya fada yana miƙowa nasreen wayar ta amsa tayi tana juyawa ba abin da tayi ƙasa kasa tace '' thank..,
mai da hankalin sa kan khalil yayi domin wannan yar rainin hankalin besan lokacin da zai duddura mata ta maguzawa ba yar rainin hankali ce yace
'' kuɗin gyaran ta dubu dari uku...,
kai khalil kawai ya gyaɗa ya dauko wayar sa transfer yayi mai sannan yace
'' ka duba nayi maka..,
da sauri nasreen ta kallesa za tayi magana saka hannunsa yayi abaki yace '' shiiii..,
ƙasa ƙasa me gyaran mota yace '' daman aurenta kayi ka huta kayi yidima da ita me hujja..,
da sauri nasreen ta kallesa sai kuma ta fasa maganar ta dauke kanta ba komawa tayi cikin motar bayan su gama ya shigo ya tada motar tana danna waya bata dago ba tace
'' kaga yan amana kaf cikin su ba wanda be kirani ba saboda ajiya bar musu shagon nayi na fito...kulawa na dad'i wallahi... yayin da ni kuma narasa kulawar ban gare biyu,
parking yayi ya ɗauki wayar sa batare da yace mata komai ba cikin contact dinsa ya shiga ya danna layin uncle rasheed bugu ɗaya ya ɗauka a hands free ya saka ta yace
'' Assalamu alaika uncle barka da rana..,
amasawa yayi tare da cewa ya mutan gidan
kallon nasreen yayi yace
'' kowa lafiya...,
to masha Allah ka gaishe da kowa ga nasreen zaku gaisa
Uncle yace '' ina kan aiki ne idan na dawo ka turo min da number ta za muyi waya daddy kalli wannan kayan zabar min wanne zai fi kyau dani suka jiyo Muryar yarinya ƙarama tana fadar haka kai nasreen ta girgiza kai ta rufe idanuwanta khalil da jikin sa yayi sanyi zuciyar sa tayi ba dad'i me makon gyara ya ƙara jagula komai yace
'' tom shikkenan zan turo maka...,
atake anan ya tura mai number yace
'' zai kiraki na tura mai number ki..,
dariya tayi tace
'' me kake tsammani zuciyar ka ita kanta bata yarda da zancen da labban ka suka faɗa ba , ni yanzu tunanin da nake ya za a yi rayuwata ta dawo kamar da ...,
tada motar yayi yana cewa insha Allahu zata dawo kamar da sun gugare da dama har take away sukai sannan ta bada rabin kuɗin mota gobe zata cika sauran a gajiye suka dawo lokacin ƙarfe 3:40 dafe kansa yayi yace
'' namana ta zan je office sannan banyi sallah ba har 3:40..
shagwabe fuska tayi tace
'' ayya sorry ni na ja maka wallahi nima ban san lokaci zai tafi haka ba kai hakuri...,
Domin yin payment sauran three pages free ya ƙare ₦500
8141785374
Amina alhasan Muhammad opay sai ku turo da shedar biya ta wannan number 09061890481
ƁAƘIN SHAFI
EPISODE 8 BOOK 1
Murmushi yayi yace
'' ba komai haka Allah ya tsara...,
amsar take away din hannun sa tayi ta shiga parlour bakin ta ɗauke da sallama duk suna zaune yawa an kafa ƙusa a inda ta barsu anan tazo ta same su kallon ta adda Asma tayi sultan na cinyar ta tace
'' sannu da zuwa ya jikin naki..,
dan murmushi tayi sannan tace
'' da sauki ...,
Allah ya ƙara sauki
amin ya Allah tace ta hau sama ajiye kayan hannun ta tayi ta fito da abincin da ta siyo shiga toilet tayi ta wanke hanyenta a hankali ta fara tsakurar abincin bawai dan be mata dadi ba aa kawai turawa take baza ta ita cewa ga daɗin abincin ba
wayarta ce tayi ringing da sauri ta ɗauka ganin me kiran tace '' hello humy kwana dubu...,
kai nasreen wanne kwana dubu ina kika shiga two days ba ma ganin ki ko an samiki ta kunkumin fita ne
dariya tayi tana matsar da take away din da ke gaban ta tace
'' wane mutum inji mutuwa aini an bani lasisi yanzu zaman kaina nake so nake abubuwa su lafa na yanki visa nayi gaba karatu zan tafi na ƙaro idan kasuwanci ya juya min baya sai na karkade takarduna na tafi aiki duk da bana fatan haka..,
dariya humy tayi tana ɗaukan lemon da ke gaban ta a cikin kofi tace
'' kina wuta kawata wallahi kin min daidai su basu san wace ke ba sai nan gaba za su sani..,
dan jim tayi sannan tace
'' ya maganar kayan nan kin magana da me kayan ko kuma kawai bani number wayarsa..,
Oka zan turo miki ta WhatsApp kin san kuwa sabeer yayi aure bara na turo miki picture's din bikin
da sauri tace
'' bana buƙata barshi yanzu na soke shi a rayuwata kwata kwata babu shi ki ɗauka kamar ma ba mu taɓa sanin juna ba hakika sabeer ya cutar dani tsakani na dashi Allah ya isa ban yafe ba..,
kai ka kai amma gaskiya be kamata ki ɗauki wannan mataki ba iyayen sa ne suka ce ba zai aure ki ba , ba shi ba wallahi yau da na saka miki voice dinsa da sai kin tausaya mai wallahi
tausayi, tausayi fa kika ce lallai humy kin ga mu bar maganar sai an jima
kar ki kashe wayar ki yi min alkalanci mana shi da bakin sa ya faɗa miki haka su basu san wane dan nasu ba basu san irin temakon da kikai musu ba kece sanadiyar sa shi ya dena shaye shaye wallahi nasreen da ace za su wannan irin temako kikai mai
Please dan girman Allah mu bar maganar nan sai an jima
okay amma yau zaki fito ko
a'a ba zan fito ba..,
Dariya humy tayi tace
'' okay sai mun haɗu..,
kashe wayar tayi ta ajiye ta janyo take away dinta ta ci gaba da cin abincin
*CAMEROON YAOUNDÉ CITY CENTRE*
A gajiye ta dawo daga gun aiki ajiye jakar hannun ta tayi parlour yayi tsit ba kowa ɗaga murya tayi tace
'' juhud holi to ngarɗaa suudu, gujjo ari wujji geɗe am, a anndaa ..,
da sauri juhud ta fito tace
'' a wartii e jam...?,
zama tayi tana cewa Alhamdulilah ba tare da papa din ku nake ba yau ni kaɗai na dawo mana idan na tafi aiki haka kuke komawa daki yanzu da ace ɓarawo ne da shikkenan sai ya zari abin da yake so yayi gaba..,
zama tayu tana cewa
'' wallahi mama yasmeen ce bata son zaman parlour nan ga masu gadi ba me shigowa kawai dai sai dai mu kiyaye gaba...,
ajiyar zuciya ta sauke tace
'' ina Yasmeen din take..?,
tana bacci bara na haɗa miki ruwan wanka ga nyaamdu maa dow dining
okay Allah yayi albarka
Amin mama ya maganar tafiya tawa America papa ya yarda
dan jim mama tayi ta cije lips dinta nan da nan yanayin ta ya sauya tace
'' ba inda zaki ko shi ya yarda ni ban amince ba me kike nema da anan ƙasar tamu ba zaki samu ba har sai kin tafi can wata uwa duniya karatu..,
kwallace ta taru a idon juhud tace
'' mama..,
da sauri ta tari numfashinta tace
'' na gama magana zaki iya tafiya..,
hawa sama tayi tana kuka zama mama tayi ta zuba tagumi itama da ta hana juhud karatu zuwa wata ƙasar ranta be so ba ita lokacin ta am barta result din da ta dawo da shi ne shine babbar matsalar da ta gamu dashi a rayuwar'ta sannan ko wanne bawa da irin tashi kaddarar wata kila juhud ta samu kaddara me kyau amma tunda tana tsoro ko bacci baza ta iya ba dama abubuwan sun caɓe mata ballanata yanzu da wayewar da da ta yanzu ba ɗaya ba sannan mutane kiris suke jira shikkenna mutum ya shiga uku zare ta gumi tayi ta hau sama lokacin har juhud ta gama haɗa mata ruwan wanka a bathtub cire kayanta tayi ta saka towel tace
'' ki ɗauka ki zuba min a Landry basket ko kuma kawai samin a washing machine..,
Kai ta gyada mata da sauri ta juyo tace
'' are you okay..?,
karo na biyu ta ƙara gyaɗa mata kai mama tace
'' dawo zo muyi magana...,
dawowa tayi ta zauna a bakin gado itama ta zauna tace
'' kina fushi dani dan na hanaki zuwa wata ƙasa karatu..,
kai ta girgiza da sauri mama tace
'' yi magana mana kurma kika zama..?,
kai ta girgiza ta buda baki kenan za tayi magana sai kuka ya kubbuce mata kwantar da kanta tayi a kafadar ta tana kuka bubbuga bayanta mama ta ci gaba dayi tana cewa juhud bawai na hanaki zuwa wata kasar karatu ba haka kurum ina da nawa dalilin a dama tarbiyya tana lalacewa ballantana yanzu akwai hatsarurruka da mutum ke haɗu a idan ya tafi karatu abroad ana din ma ana haduwa dashi amma nacan din yafi risk saboda ba uwa ba uba ba wani dangi abin da mutum yaga dama shi zai yi wani zai tafi lafiya dan ƙaramin abu ya canza mai ƙaddararsa,
dan jim tayi muryar ta tayi rauni kamar ta tuno wani abu da ya shude shekara da shekaru ta ci gaba da cewa ke yarinya ce ba zaki gane me nake nufi ba sai nan gaba wasu zugar ƙawaye su yi aiki akansa har ya wada wata hanya ta daban duk tarbiyyar ka wallahi a lokaci ƙalilan aboki yana iya canza maka ita a kullum kina min tambayar nan me ya saka naƙi barin ku , ku dinga kula abokai yau zan amsa miki juhud,
aboki yana da mutukar tasiri, iyaye sai su shekara ashirin suna tarbiyya amma rana daya zai rushe wannan tarbiyyar yayin da shedan ke tun zura shi ya akata abin da sai lokacin da mala'ikan mutuwa ya tsaya akan sa sannan zai manta da abin bayan mutuwarsa iyayen da ya bari idan za ayi kwatance ba za a yi da kyawawan halin mutumin ba sai ayi da abin da ya taɓa aikatawa ba ya mace da kike ganin ta yar taka tsantsan ce duk abin da namiji yayi adone ,
bawai shima ba kyau ba amma na macen yafi illa saboda shi ba me fahimta sai dai dole ayar Ubangi tayi aiki akansa saboda Ubangiji ne ya hanemu da yin zina sannan yace idan kayi da yar wani dole ayi da yarka ko da yar uwarka wanda dai dole sai kafi jin zafi sannan ita bin jini take idan kika duba wannan zamani juhud ba'a mai da zina da kallon fina finan banza ba wani abu ita rayuwar nan me sauki ce idan har mutum ya ɗauke ta da sauki sannan akwai wanda baya aikatawa amma ,
saboda yana tare da mutanen banza sai halin su ya nashe shi a dinga yi mai kallon yana aikatawa kuma wallahi Allah ba me fitar dashi sai Ubangiji shi yasaka duk wani waje da ake aikata badala juhud kar kuje hali na so yake yau da gobe tun abin baya burge