Showing 3001 words to 6000 words out of 24637 words

Chapter 2 - YAR CASKELE cmlt

Start ads

24 Aug 2025

179

Middle Ads

ashirin,Allah ya dawo dake gidan kafin babanku ya dawo zanci ubanki,Dan nasan idan Yana Nan nace Zan dakeki hanawa zaiyi,dai dai ta jawo ruwan ta Kara antayawa cikin robar,Maryam ta Kuma sakin ajiyar zuciya saboda sanyi,kun San ruwan rijiya lokacin zafi.
Daurewa kawai umma tayi ta kara zura gugan,dan wannan Kar kam da gaske taji anyi ajiyar zuciya,hakan yasa zuciyarta Fara rawa amma wai ita jaruma saita dake,taci gaba da antya ruwan cikin robar,jin da maryam tayi ruwan na neman kawo mata wuya,yasata mikewa ta buga tsalle ta fito jagab da ita,ta zura a guje ta shige dakinsu.


Wata kara umma ta saki tare da karanta ayatul kursiyyu iya karfinta,tana nan tsaye Kuma ta kasa sakin gugan yana hannunta,irin d'an dutsen nan na rijiya ya rike gugan Nan umma tawage Baki tana kuka da neman agaji.

Mallam Shu'aibu da shigowar shi kenan ya hango matarsa na makyarkyata da sauri ya karasa Yana fad'in"subahanallahi! Huwaila waye ya fada rijiyar,bawai garin jarabar Taki Kika jefamin Yara rijiya ba,ya fada Yana fuzge gugan hannunta,Yana lekawa rijiyar,ganin da duhu ba komai zai gani ba yasa ya juyo a fusace Yana fad'in,kin mun shuru ki fadamin meyake faruwa!

Cikin rawar murya da tsoro tace 'matashiyar 'yar ruwa ce ta fito daga rijiyar ta shige dakina".

Tsaki yaja,kafin ya saki gugan ya nufi dakin yaran,a zuciyarsa Yana fad'in yaga ranar da Huwaila zatayi hankali.

A kudundune yasamu Maryam da kayanta jikakku,tunda yaga Haka ya tabbatar da itace tayiwa uwarta haka.karasawa yayi inda ta kwanta kusa da Isma'il ya tashesu duka,Nan Maryam ta shiga rarraba ido,Bai nuna Mata wani bacin Rai ba,yace ta tashi ta cire kayan jikinta,aikuwa ta mike ta canza ,Nan yake tambayar ta ko taci abinci,Nan ma tace mishi ah'ah ,yasan za'a rina,Dan haka ya fita dakanshi ya fita kicin ya zubo mata,yace taci Yana zuwa.

Yana fita ya tarar da Huwaila tsaye bakin kofar dakinta Taki shiga,Yana zuwa yaja hannunta ta shiga tittirjewa,ganin tana cijewa ya juyo yace "Wai miye haka ne Huwaila?ba fa na son sakarcin banza wuce muje,Dan Yara na baro wurin Ina son magana ne dake a gaggauce".

Ganin ya shige ciki Bai Kuma dawo ba yasa tayi shahada ta biyo shi,ta samu guri ta zauna tana waige-waige.

Bai kulata ba yace,"dama ba komai ya dawo Dani ba sai akan Maganar Maryam, Huwaila bazan boye Miki ba,komai ya faru da yaran nan kece sila, wallahi na tabbatar bakinki ne,gashi yanzu kin samu a damuwa,kullum maryama da kalar tsokanar da zatayo,a tsokaneta Kuma ta jawo magana Nan ma,ba babba ba yaro duk Kan me uwa da wabi takeyi,gashi Bata Jin tsoron ko mu iyayenta Dan kin Gama horar da jikinsu da duka,tasan bazai wuce muma dukanta zamuyi ba intayi ba dai-dai ba,Kinga yanzu abinda ya faru dazu,yanzu Haka maganar da nake Miki mijin Rakiya ne yaje da yaranshi maza manya har gurin san'ata sunce wallahi idon su idon Maryam sai dai wata ba ita ba,na rasa abinyi da kyar aka Basu hakuri suka bar gurin.To shine nake fadawa malam Garba abinda ke faruwa shine ya bani wata shawara yace in Kai Maryam almajiranta kawai".

Da sauri Huwaila ta d'ago ta kalleshi tace,"wace irin almajiranta Kuma malam ? Wai ma Isma'il kake nufi ko wa? Dan Naga dai shine namiji Kuma maza ake kaiwa almajirci ba Mata ba".

Murmushi yayi kafin yace ," Maryam dai nake nufi kamar yadda Kika ji,malam Garba yace babanshi Yana da almajirai Mata,idan yarinya ta gagara to shi ake kaima,sannan Kuma cikin yardar Allah sai kiga yarinya ta kimtsu ta samu ilimi,sannan bawai bara sukeyi ba,zamu had a Mata kayane kamar zata boading school,shima Kuma acan gidansa ana Basu abinci Dan suna mu'amulla ne kamar yaran gidansa,Ina gudun abinda Maryam zata jawo Mana ne Nan gaba in mun barta Haka.
Nanfa ya shiga gayawa Huwaila muhimmancin Kai Maryam makaranta.

"Naji malam na Kuma gamsu,amma kasan fa halin Maryam,kana ganin bazata iya dawowa ba?"

"Kada ki damu na shirya yadda za'ai tafiyar,Kuma yace min garin lungu ne can jihar jigawa ne".

"Shikenan malam, Allah yasa karshen wahalar kenan"

"Amin ya amsa,kafin ya mike Yana fadin ta hadawa maryam kayanta kala biyar,Dan da asubar nan zasu tafi a motar malam Garba.

Haka ko akayi Daya tashi dawowa ya tahowa da Maryam harda robar almajirai,dasu gari da dakaken kuli magi dadai 'yan wasu abubuwan bukata na 'yan makaranta๐Ÿคฃ.

*********

Asubar fari suka fito aka tashi Maryam Huwaila ta sallara mata wanka,itadai Bata cewa komai,ana shiryata ana Mata nasiha.

Gani sukayi malam ya fito da zundumemen buhu yace"maryama ta taho ki shiga Nan kinji"

Make kafada tayi alamar ah'ah,Nan ya shiga.lallabata harta yarda ta zura kafafunta tace"baba kasheni zakuyi?"

Zaro ido yayi yace "injiwa yace Miki kashe ki zamuyi?"

"Gashi Nan zaku je ku jefani a ruwa".

"Ah ah,madinan Nigeria zamu kaiki ki sauke farali,shiyasa muke son mu boyeki anan,kar Yara su ganki suce Suma sai anje dasu,bayan ke kadai ce 'yar gata...."

Bai gama ma maganar ba,yaga ta shige buhun tana fadin"to ummana Allah ya kaddara saduwar mu,nidai yau Zan hau jirgi" sai Kuma ta fitoda kanta tace,"to amma baba a maleji zani ko Kuma a booth,da Naga za'a Sani a buhu?"

"Ai a kujerar boye Zaki shiyasa,Dan Haka ma Zan yanka Miki inda Zaki dinga Shan iska bakida matsala kinji".

Komawa tayi tana fadin,baba k'ulle bakin buhun muyi sauri Kar jirgin ya tafi,amma Allah ya taimaki ummita,da nace wallahi saina mata dukan tsiya,amma yanzun ma idan na dawo indai ban manta ba saina dake tan".

Haka malam Shu'aibu ya daure bakin buhun,bayan ya yanka mata wani gurin,yace tasa hancinta dai-dai gurin,Dan ta dinga Shan Iska,Nan ya kinkime ta zuwa bakin motar.

Malam Garba ya bude musu gidan baya yasata, shima malam Shu'aibu bayan ya shiga,yayin da Huwaila ke tsaye tana musu sallama da addu'a Allah ya tsare,tana Jin ba Dadi rabuwa da 'yar tata,badan rashin lafiyar Isma'il ba da da ita za'a ,Amma tana musu fatan sauka lfy da Kuma fatan samun shiriyar 'yar tata,ance kowanne yaro da kalar kuruciyar sa,to ita Kam ta Maryam ta dabance.

Jin an tada motar Maryam ta saito bakinta saitin bular buhun tace"mama ke bazaki filin jirgin ba?"


"Eh Zan biyo ku daga baya kinji mairo ta,ta fada tana goge kwallar data zubo mata.

Haka aka ja motar suka tafi suna fatan sauka lfy.

****

Da yake tsakanin Kano da jigawa ba wani nisa,Koda Tara tayi sun shiga garin,a irin hakan ne,malama Garba ya kalli malam Shu'aibu yace,"Amma fa munyi sauri,duk da ba wani nisa tsakanin Kano da jigawa,amma gashi har mun iso".

Yana shirin bashi amsa,Maryam ta saito bakinta tace,"wace jigawa Kuma? Badai wadda nakeji a state and capital ba? Kenan a filing jirgin jigawa zamu tashi?"duk ta jero wannan tambayar tana jiran amsa.......


_to readers Ku fada Mata gaskiya mana๐Ÿคฃ_


*Gaskiya Naga ruwan comments jiya,na Kuma gode muku masoya Allah yakara kauna,Ku tayani addu'a Banda lfy wlh*



*Alkalamin khady* โœ
๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€

*_YAR CASKALE_*
( _Sanadin bakin uwa_)

*ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู….*
____________________________________


*๐ŸŒˆKAINUWA WRITERSโœ๐Ÿผ ASSOCIATION*๐Ÿค๐Ÿป
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________


1โƒฃ1โƒฃ-1โƒฃ5โƒฃ


Sai yanzu suka San sun tabka katobara na ambatar sunan garin da sukayi,Dan Haka dukansu suka kalli juna da ido kafin malam Garba yace,"wato malam Shu'aibu,Inka fahimci wani abu, shi zuwa madina a biyo ta jigawa sai Mai babban rabo,yanzu dai kaga sunan fa garinmu na asali shine bakada suna,amma yaran zamani suke kiranshi da Kano,bayan Kuma in zaka shekara cewa a kaika Kano bamai ganewa,inhar ka fita daga garin,sai dai kace a kaika kanoma,Kuma fa Inka sake mutum Bai gane ba kace ya kaika Kano to lamari ya b'aci,Dan gidan wannan mashahurin d'an yankan Kai za'a kaika wato d'an kano,dan Haka gara kawai kayi zamanka inda Allah ya ajiyeka".

Murmushi malam Shu'aibu yayi,danya fahimci inda zancen ya dosa,Yana shirin yin magana suka k'araso karamin kauyen,kofar gidan malam Jafaru mahaifin malam Garba.

Jama'ar garin sunyi murnar ganin malam Garba,Dan haka duk alamajiran malam suka shiga murnar ganin d'an malam d'in,dan ko ba komai Yana kawo musu tsarabar lemo da biredi,kun San dai k'auye,duk k'in ka da biredi ko baka ci,to idan kaje k'auye ka kwana biyu,wallahi saika yi marmarin biredi๐Ÿ˜œ

Tunda motar ta tsaya malam Shu'aibu ya zagaya ya kwance Maryam a buhu,wadda ya zuwa yanzu ta jik'e da zufa,aikuwa Yana bud'ewa ta Fara rarraba ido,Nan idonta ya sauka akan tarin yaran da suka kewaye su.Zaro ido tayi kafin tace,"baba yana ganni cikin ba'kak'en fata,ba dai ta filin jirgin k'auye zamu tafi ba?"

Dariyar data bayyana hak'oransa ya yi ,sannan yace,"ai gurin bita muka kawoki,Kinga Yara can dayawa" yayi Mata nuni da tarin yaran dake zaune duk rike da alluna,sannan yaci gaba,"muna hanya aka fad'a Mana sai mun Fara kaiki gurin bita tukun,Dan haka muka kawoki anan in kin Gama haddace komai saiku wuce kawai,lokacin ma yarinyar ta k'ara girma ko?" Ya karasa maganar Yana shafa kanta,kafin ya kamo hannunta suka fito,yayin da suka doshi rumfar da malam Jafaru yake.

****

Duk abinda yakamata ayi Kuma su Sani dangane da zaman Maryam anyi,Kuma Alhamdillah duk malam Shu'aibu ya gamsu,bayan sun gama ganawa akace a dauki jakar Maryam a shiga da ita ciki.Duk k'iriniya da rawar Kai da Kuma son ke ta hazo na Maryam Saida ta zubda kwalla da babanta zai tafi,bayan yayi Mata nasihan ta daina rashin ji da sauran k'iriniya,ta tsaya tayi haddarta Dan ta kasance a 'yan tashin farko.Haka suka rabu bayan ya bawa malam kud'i yace a dinga bata intana bukatar wani abun.Kuma itama ya zaro nera goma sabuwa fil ya Bata,hakan ya d'an sanyaya ranta.

****

Bayan an shiga da kayan Maryam itama ta shiga gidan malam.Babban gida ne irin na k'auye Daya kunshi bangarori da dama,matan malam biyu,yayin da duk yaransa maza ne baida 'ya mace ko d'aya.D'akin da aka Kai kayan Maryam,d'akine da akayiwa kanta irin wadda akeyiwa almajirai maza,sai dai su abin birgewa harda katifunsu.kuma dakin duk da na kasa ne amma a lailaye yake da sumunti,Kuma an shimfida musu katon buhu,inda kusan duk Mai gata a cikinsu ita keda katifa,wasu Kuma bargo,wasu Kuma tabarmi,daki biyu ne irin hakan,yaran matasa ne 'yammata,sai Kuma irin su Maryam d'in,dan gaskiya kusan sune ma kanana.


*****

Matan malam akwai iya salame itace uwar gida kasancewar mahaifiyar su malam Garba itace matarsa ta farko ta ladan noma Allah yayi Mata rasuwa da dadewa,a yanzu dai salame uwar gida itace yaranta duk manya maza,Dan malam Garba shi kadai ne mahaifiyar sa ta haifa.Sai matarsa ta biyu Zuwaira,ita ma yaranta duk mazan ne,amma kuma sune kanana,duk da ta daina haihuwa,autanta bazai wuce shekara 8 ba.


Zaman gidan malam Garba shima zamane na kishi,irin kishin kauyen nan.sam matan Nan basuda mutunci yaran da aka kawo irin su Maryam,su keyi musu shara da wanke-wanke harda girki.Idan kaga suna haba-haba da yarinya,to sunsan 'yar masu dashi ce,iyayenta in sunzo suna musu abin hasafi,Kuma in an kawowa yarinya kayan dad'i suna sammasu.

Tun daga kawo kayan Maryam da suka bude sukaga kayane na dangin irin namu ya ku bayi,Nan suka hau gatsine-gatsine,basuyi Mata wata tarbar mutunci ba.

*****"************"******

A d'an wannan lokacin zamu iya cewa marayam ta sake,dan ba ruwanta da bakunta,sa kanta da tayi a zata keta hazo,yasa bata fara Nuna Hali ba,Kuma Bata Fara halartar karatun ba,tunda litinin aka kawota,malam yace ta huta zuwa asabar saita Fara daukar karatun.

A iya wannan kwankin Maryam ta Fara fahimtar halin matan gidan,tazama mage Mai kwanciyar daukar Rai,saika rantse Bata San wani abu Wai shi rashin mutumci ba.


Yau aka tashi a dakin su Maryam anyi sata,aikuwa Nan fa gida ya kacame aka shiga tone tonen kaya,dayake yarinyar da akawa sata,wata 'yar kaduna ce,Kuma 'yar masu dashi,sosai su Zuwaira suke karuwa da ita,hakan yasa sukafi kowa zakewa akan abin,nan ko suka shiga bincike kayan kowa,ganin Basu samu ba yasa salame tsayawa ta rike k'ugu tace" Ni fa gaskiya abin Nan akwai abin mamaki,tunda muke cikin almajiran malam babu Wanda yataba Mana sata,nidai inaga wannan yarinyar" ta nuna Maryam" inaga sata ta addabi jama'a da ita shiyasa suka dungumo ta suka kawota gun malam,Wanda shi kowacce tantariya a cewarsa zai iya da ita,to ai Sai ya zo yayi Mata kafi,tun kafin ta Gama damu".

Dafe kirji Maryam tayi tare da zaro ido tace,"Ni d'in ce barauniyar ko wata?"

Zuwaira ce tayi caraf tace,"uwar wace bakuwar zuwa da bamusan halinta ba inba ke ba".

Hawaye Maryam tafara yi sannan tace" Ni d'in Nan 'yar Karamar yarinya Dani Ina Zan iya wani sata,Kuma ma idan nayi satar abinda kukace Ni da Banda aljihu Ina Zan boye,wallahi tunda kukaimin sharri da banyi ba ma nayi d'in".

"Dan ubanki mu kike murgudawa Baki,sharri zami Miki ko me?"

Maryam dai batace komai ba illah kuka data Fara yi, a zuciyarta tana jin ita Tama fasa zuwa makkan tunda akayi haka,gara azo a koma da ita gida tama yiwa ummita dukan datace zatayi Mata.

Haka dai aka karaci tujarar aka gama,shi malam ma baisan abinda ke faruwa ba.

*****

Ranar asabar kuwa kamar yadda Maryam taga kowa nayi itama Haka tayi,duk da ta tashi da kewar yayanta Isma'il da Kuma mamanta,tace ba yanzu zata tuna babanta ba,su din dai ta damu dasu da son gani,Dan tasan yanzu da umma ta lakada Mata duka yafi a kirga.Ina sonki ummana ta furta a hankali.Dayake duk kusan 'yammata ne shiyasa bamai bi takanta bare har ya tabota.


Yau su Maryam an hallara a makarantar,rumfar malam ta cika,Yara da manya,dayake ya hada da yaran gari suna zuwa daukan karatun.


Kamar a boko Haka malam ya dinga wa Maryam interview,bai samu komai ba,illah fatiha,Dan itama da kyar takaita,yayi mamaki kwarai,inda yasata ajin Yara aka Bata allo da aka rubuta basin mi'a ra,aka ce ta Fara da nan.

Aji-aji abin nasu yake cikin tsari,Dan Haka ajin Yara aka kaita,duk da itama yarinyar ce,amma tafi son akaita cikin manya,aikuwa nan Saida ta bayyana a fuskarta Bata so ba.

Tana zaune amma ba karatun take ba,wata yarinya dake bayanta,ta bude murya tace "malam ga wata Bata karatu".

Aikuwa malam ya zaburo Yana fadin "wacece?"

Nuna Maryam tayi,aikuwa ya tsulawa Maryam bulala,har Saida yayi Mata bulala biyar,Yana jaddada Mata Nan ba gurin Wasa bane.Kema dagas Maryam babu ko hawaye, aikuwa ta rasa me zatayi wa yarinyar ta huce,Nan ko ta dage ta gallara Mata mintsini,yarinya ko ta callara ihu,ko kafin malam ya juyo wata ta bude Baki da niyar Kai Kara ita data kusa da ita,aikuwa ta Maryam ta ankara,ta Kama kawunansu ta gwara,Suma ko kukan suka saka,Nan da Nan tahau rankwashin yaran da Kuma gwarawa wasu kawuna,kukansu ya karade ko'ina Wanda ya jawo hanakalin malam d'in,dama sauran wadanda ke karatu.

Ganin malam yayo gurin da Dan ganin duk yaran sun rude yasa ta kwasa da gudu tayi cikin gida,Wanda tana shiga dai-dai salame ta gama miyar dumamen tuwo,Dan jiya miyar karewa tayi,shine malam yanzu ya Aiko yace a bashi dumame Dan hantsi yayi yunwa yakeji,shine salame gimbiya tace yadan dakata Babu Miya za'ai sabuwa,yace to a kada Masa miyar kubewa,aikuwa tana saukewa Maryam na shekowa,akuyar dake tsaye bakin danga ta zabura tayi ciki da miyar Maryam na bayanta,aikuwa har wani salo miyar ta bayar gurin zubewa ji kake lemmmmmmmm........




_nagode da addu'arku Alhamdillah,Ina sonku sosai fans,Naga comment dinku ya girgiza zuciyata,da yasa nayi Mana addu'ar Allah yakara kauna.



*Alkalamin khady* โœ
๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€ ๐ŸŒ€๐ŸŒ€๐ŸŒ€

*_'YAR CASKALE_*
( _Sanadin bakin uwa_)

*Nร€*

*KHADIJA USMAN*
( _Real Tame Gari_ )



*ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…*
____________________________________


*๐ŸŒˆKAINUWA WRITERSโœ๐Ÿผ ASSOCIATION*๐Ÿค๐Ÿป
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________


1โƒฃ6โƒฃ-2โƒฃ0โƒฃ


"Kam balastin!" salame ta furta a fusace,hakan ko ya jawo hankalin Zuwaira dake d'aki tana magana da yaranta.Dukansu tsaye sukayi suna kallon maryam,wadda ta tsaya wuk'iiii tana kallon kowa.Ganin hakan yasa salame yo kanta tana fad'in"yau Banga shegen Daya Isa ya hanani cin uban yarinyar Nan ba,Ni dama tunda aka kawota Bata kwanta min ba Dan Haka yau sai kinsan kin taba salame".

Shan gabanta Zuwaira tayi tana fadi'in"ah ah salame,gara ki Kira malam ki fad'a Masa,dan kin San Bai bamu izinin dukan dalibansa ba,Dan Haka Ni ba ruwana".

"Dayalla gafara can tsohuwar munafuka,wato Dan ba miyarki aka zubar ba shine Zaki ce kada in daketa,ke uwar tausayi,harda wani yen yen yen! Mayam jeyi fata" tayi maganar tana kwaikwayon Wai maganar zuwaira.Dan haka saina daketa wallahi".

Tsalle Zuwaira tayi taci d'amara tana fad'in" Ni Kuma zanga uban dazai tab'ata,miyace an zubar,Kuma ma ai akuyar lado ce ta zubar kibi akuyar Mana ki daka in gaskiya kike bi".

Aikuwa Nan hayaniya ta kaure,yaransu ma suka shiga cikin rigimar,itako Maryam tana tsaye gefe tana kallonsu,ganin sai cacar Baki sukeyi sunki suba hammata iska yasata fad'in"mu in zakuyi kuyi dan Allah kubar sa Mana rai,nagaji da kallon tsohon yayi".

D'aya daga cikin yaran malam me suna Idris ya kalli Maryam yace"A daina sa muku rai da me?"

"Da fad'an Mana,in zasuyi suyi kawai musha kallo".Suna Shirin yin magana sukaji sallamar malam da gyaran murya,Nan da nan kuwa kowacce ta nutsu,dan duk bala'insu,to yanayi musu kwarjini kuma basayi a gabansa,Dan haka suka nutsu kowacce taja baya.

Tsayawa yayi Yana Kare musu kallo kafin yace "Ku kuma lfy naganku tsaye kamar tab'are?"

Zuwaira ce ta gyara tsaiwarta sannan ta ce,"wallahi malam gara da Allah ya kawoka,wai fa wannan 'yar kwiciciyar yarinyar ce,sabuwar dalibarka,ta shek'o da gudu inaga ko Kashi takeji,shine tsautsayi yasa tabi takan miyar da Yaya salame tayi,to shine fa tace yau saita Mata mugun bugu,shine na hanata nace tabari idan kazo ta fad'a maka,shine ta taso zata dakeni".

"Ke uwar 'yan sharri!cewar salame,ni d'in ce nace Zan dakeki,to in dakeki ince na daki wa?"

"Kin daki uwarki,shegiya Ni Zaki tambaya ma in kin dakeni kice kin daki wa? 'yarki ce ni ko k'anwar ki,in kina ganin damata ko zamu gwada ne.Jin hakan yasa salame fusata suka kacame da dambe.Su malam da ke gefe sai sukaja da baya,Dan wata mulmula da akayi da Zuwaira ji kake makkkkk an maka ta da k'asa.Ganin hakan yasa Maryam rugawa da gudu, ta dauko wata k'arama da wani sillen Kara tazo ta tsugguna saitin inda aka tร ushe Zuwaira,ta shiga kid'a tana fad'in"jaruma! Jaruma! Baba Zuwaira jaruma! Wannan kid'an ya fargar da Zuwaira taji wani sabon k'arfi,aikuwa saita juye da salame ta shiga kintsimar ta,ganin haka yasa yaran sukayo caaa! malam ya

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login