Showing 18001 words to 21000 words out of 24637 words

Chapter 7 - YAR CASKELE cmlt

Start ads

24 Aug 2025

184

Middle Ads

koma kan gado" laushin hannunta yasa shi lumshe ido dan haka ya miƙe da kyar.

Ita ta kama shi dan a halin dayake ciki ko abinci baya sha'awar ci,dan haka suka ƙarasa ɗakin nan fa labari yafara canza salo,domin duk yadda yaso kawar da kai abu yaci tura,haka dai fa malam ya runtse ido ya kawar da batun ramuwa ya fara lulawa duniyar masoya da Laraba.

🔅🔅🔅🔅🔅🔅🔅🔅🔅


Gari ya waye duhu ya yaye,malam kam ya dangwali arziƙin Laraba,ya manta duk wata damuwa,jinsa yake yi kamar ba wanda yakaishi kasancewa cikin farin ciki,dan jinsa yake kamar bai taɓa kusantar irin wannan ba,dan haka tuni yayi watsi da batun ɗaukar fansa.......


_Kuyi manage,wallahi yanzu ma daurewa nayi nayi muku zama ɗaya_


*Alƙalamin khady*✍
🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀

*YAR CASKALE*
( _Sanadin bakin uwa_ )

*NA*

*KHADIJA USMAN*
( _Real Tame gari_ )

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*


5⃣5⃣-5⃣6⃣



" Kiyi maza ki shirya mana Huwaila,dan malam Garba yacemin yakamata muje da wuri,dan inaga malam ɗin baida lafiya ne,yake son aje a ɗauko ta tazo ta kwana biyu saita koma,saboda haka dan Allah kiyi sauri,shi Isma'il ɗin ya shirya ko?"

"Gani nan malam hijabi kawai zansa, Isma'il yana ɗakin sa ai inaga ya shirya,dan tun ɗazu yayi wanka".

"Yauwa to yi sauri dan Allah kin san jira ba daɗi".

A hannu ta fito da hijabin tana faɗin"malam Allah dai yasa bawani abun matsayaciyar yarinyar tayi ba aka mana kiran gaggawa,amma ai kai kanka kasani babu yadda za'ai kwatsam ace azo a ɗauki yarinya sama ta ka,bayan kai da kanka ka faɗa cewa,malam ɗin yace sai anga nutsuwar yarinya tukun,sannan ake bada damar tazo gida ta kwana biyu,amma ban sani ba ko ciwon ajali ne yakama tsohon tunda kace ya tsufa".

Ransa a ɓace yace"wai ke Huwaila yaushe zakiyi hankali ne?haka jiya ma inajinki kina cewa Isma'il maƙetaci la'ananne,shin ke wai har abada alkhairi baya fita a bakinki akan yaranki sai sharri,in sun lalace waye zai kaiki baƙin cikin hakan,shashasha, wadda bata san ciwon kanta ba" yaƙarasa maganar yana me ficewa a ɗakin.

Taɓa baki tayi ta faɗa a hankali" kaji malam da wata magana,da kuma bana tsawatarwa ace na cika sakaci,to yaran yanzu kana tsawatar wa ma ya aka ƙare,bare ka zuba musu ido,to wallahi bada ni ba,inna kyalesu sakaka kuma a zagen" Tana kaiwa nan tasa kai ta fice a ɗakin,tana saka makulli a ƙofar ta shiga kwalawa Isma'il kira,jin yayi shuru ya tabbatar mata da ya fita wajen baban shi, kenan ita ake jira,dan haka ta ƙara sa kulle ko ina ta fice ta damesu a waje suna jiranta.Dayake tasan ran mai gidan a ɓace yake,saita buɗe baya ta shige abinta ita da Isma'il suka ɗauki hanya.....


🔅🔅🔅🔅🔅🔅🔅🔅🔅🔅

Tunda asuba malam inka lura dashi zaka tabbatar yana cikin farin ciki,haka yabi duk ya tashi jama'ar gidan nashi dan suyi sallah.Ko yau a masallaci malam ne yayi limanci, yayinda tsabar farin cikin dayake ciki yasa yau har karatu da wa'azi ya gabatarwa da mazan ƙauyen akan riƙon aure.

Wajen ƙarfe takwas malam ya shigo gidansa,bayan yasa an sayo masa Lipton da Suger ,tare da ɗuma-ɗuman biredi ya shiga dasu gidan.Batare da damuwar komai ba ya ware iya na matansa kowacce,dan tunda akayi auren nan ya lura basa bawa Laraba abinci insun dafa(kunji fa malam sai yau yasan da hakan) Allah sarki 'yar marainiya bata ko damu ba,yanzu idan ya koma zaisa ta lissafa masa abinda ta kashe tsawon wannan kwanakin🤣

Duk wadda yabawa a cikinsu babu wadda tako kalleshi,shima bai damu ba,dan yasamu biskit ɗin zuciyarsa,dan haka ya shige ɗakin Laraba hankali kwance,baiwar Allah kun san dai yadda budurwa take duk girman ta in har Bata siyar da mutuncinta a waje ba,dayake zazzaɓi take ɗan ji,amma haka ta daure ta yi masa sannu da zuwa,ya miƙa mata Lipton da Suger ɗin,tare da lalubo sachet ɗin madara da bombita(oh su malam an iya almundahana ashe🤣)gashi maza tashi ki dafa mana shayi,sannan ki haɗa da waccan yarinyar mairamu,dan itama tare damu zata karya da ita,dan yarinyar na yaba da hankalin ta ba tun yanzu ba,bari ma in kirata mu ɗan taɓa hira kafin shayin ya dahu tunda naga a madafin zamani kike girki" ya ƙarasa zancen yana me fitowa ƙofar ɗakin,daga nan ya shiga kwalawa Maryam kira"Maryama! Kina ina mairamu?" Ya shiga tambaya yana daga bakin ƙofar Laraba.

Daga cikin ɗakinsu ta amsa masa,ta fito sanye cikin kayanta masu kyau da hijabin ta.Sai da ta ƙara so gabansa ta ɗan tsugunna tace"Gani Baba malam"

Washe baki yayi kafin yace"yauwa 'yar albarka taso dama neman ki nake yi shigo ciki kinji" ya faɗa yana me juyawa ya shige ita kuma Maryam ta miƙe tabi bayanshi.

Zuwaira da salame dake can gefen ɗakunan su da yau ɗin nan suka tashi da sabon haɗin kai, kowacce saita ja dogon tsaki suka saki dariya a tare suka tafa.

************

Gefen tabarmar malam ya nuna mata ta zauna,aikuwa tasami guri ta zauna,tare da aro ladabin kunama tayi shiru.A haka har larabar malam ta kammala haɗa shayin aka kawowa kowa nasa,nan ko Maryam ta zage tasha abinta,dan saiya zame mata abin marmari,dan tunda tazo bata sha ba,danma ita ɗin hamburin hayam ce,ba ruwanta da zaɓar abinci, komai in zaiyi Mata maganin yunwa to tana maraba dashi.

Bayan sunsha sun ƙoshi nan fa malam hira ta ɓarke,ya shiga bawa su Laraba labarin samartaka da irin gararin da yayi lokacin dayaje almajiranta,ita kam Laraba wani farin ciki take ji ,wai yau itace da miji suke hira.Yayin da ita kuma Maryam sam hankalinta na ga gida,danta matsu a zo a tafi da ita taje taci uwar ummita😡.Tana shirin tambayar malam shin yaushe su babanta zasu zo? Kawai sai taji ihun yara suna faɗin, ga yaya Garba! Ga yaya Garba na kano.Aikuwa a zabure ta miƙe tayi waje,yayin da sukayi ido huɗu da babanta suna gaisawa da wasu mutanen ƙofar gidan.A dai-dai nan ta ga Isma'il na ƙoƙarin fitowa daga motar.Da gudunta cike da murnar ta ta nufeshi,shima da sauri ya fito,a nan kuma taga ummanta itama ta fito aikuwa da gudu ta canza akala ta nufeta, tare da fashewa da matsanancin kuka,itama umman saida zuciyar ta tayi rauni,hawaye suka fara zubo mata na ganin 'yar Tata da tayi.Haka suka rungume juna,kafin malam Garba yayi musu jagora zuwa cikin gidan.

Koda malam ya gansu ya nuna farin cikinsa,dan yanzu duk abinda ya shafi Maryam to yana daraja shi,dan shi Sam Yama manta shiyace Suzo su ɗauki 'yar su.


'Ɓangaren su salame ya musu jagora,yayin da suka shiga ɗakin salame,amma sam babu wadda tayi musu koda kallon arziƙi,hakan yasa jikin umma yin sanyi,ganin hakan da malam yayi ne yasa yakama yin yaƙe tare da cewa"Maryama idan sun gama gaisawar maza ki raka su ɗakin amarya kinji" yafaɗa yana me juyawa ya fice,dan su gana da mahaifin Maryam ɗin.

Batare da ɓata lokaci ba kuwa Maryam tace"Umma tashi in kaiki ɗakin Anty Amarya dan ita tanada kirki,amma yanzu tsofaffin matan Baba malam sun koyo rashin mutunci".

Jin furucin na Maryam yasa umma jin kunya,ta kalli salame dake duƙe tana leƙa ƙarƙashin gado,kome zata ɗauki oho,bata bi takansu ba har Maryam taja hannun Isma'il suka Umma ta bisu a baya,har zuwa ɗakin Laraba.

A kwance take kan tabarma, dan zazzaɓi takeji,hakan yasa koda suka shiga da kyar ta iya ɗagowa ta amsa musu,dan ciwon da kanta keyi.Jinjina kai Umma tayi datayi arba da Laraba ,a zuciyarta tana jinjina girma da ƙudura irin ta Ubangiji,"Allah me halitta kenan" ta furta a zuciyarta,a fili ta shiga amsa gaisuwar da laraban keyi mata,bayan tayi musu nuni da gurin zama, Isma'il ma ya shiga gaisheta ta amsa mishi cikin sakin fuska kafin ta yunƙura da niyyar miƙewa."Wash Allah "ta furta a hankali,Da sauri Maryam tace," Menene Anty?"

Cije baki tayi kafin ta furta" Bakomai" ta ƙarasa miƙewa da kyar ta je ta ɗebo musu ruwa.Nan ma da kyar ta zauna,duk umma na lura da motsin ta, amma saita kyale Ita kuwa Maryam sai hira take yiwa Isma'il tana tambayar shi ina 'yan layinsu,sannan ina su Rakiya? Nan take faɗa mishi ai ita tama fasa zuwa madinan nan,dan ta tambayi su Hafsa (waɗan da suke ɗaki daya)suka ce mata ai ba'a zuwa Madina ta ƙauye,nan suke faɗa mata duk wanda taga an kawo shi nan,to kangararre ne,dan haka wayo aka mata dan a kawota nan ɗin.Tunda taji haka tace itama saita nuna musu tanada wayo,badai ita za'a kai ba,to saita ce tafasa zuwa Madina a maida ta gida,kuma wallahi koya za'ai da ita bazata zauna ba.
************************
Tunda umma ta kalli Laraba ta fahimci inda matsalar take,dan koda take da ƙiba gamai hankali inya lura zaiga yadda tafiyar ta ta sauya.Ganin da umma tayi maryam taja hannun Isma'il sun fice wai zasuyi sirri,nan tasamu damar kallon Laraba tace"Ni kam amarya in tambayeki Mana?"

"To Innar Maryam" cewar Laraba dake rawar sanyin zazzaɓi kaɗan-ƙadan.

"Mene ne ya jawo miki zazzaɓi haka? Ko bakya kwana cikin gidan sauro ne?"

"Ah ah,ai bama Musa sauro,kawai dai inaga dan....."sai kuma tayi shuru.

Sosai Umma ta shiga nazarin ta,zuwa wani lokaci,sannan tace"kin gasa jikinki da ruwan zafi ne?"dan ta fahimci kamar abinda ya faru wannan ne na farko.

Girgiza kai tayi a hankali tace"ah ah,dan ban san ma ana gasawa ba ai".

Cike da tausayin ta,da kuma yaba tarbiyya irin ta yaran ƙauye tayi,domin dai duk da ana kiransu da kidahumai to Gara hakan,dan yanzu wata wayewar da buɗewar idon basuyi ba.

Kallon ta tayi sama da ƙasa,taga yadda mazaunan nan suke,ta jinjina kai,to yanzu ya za'ayi a gasa wannan,dan ko bataga robar da zata ɗauke Laraba ba,amma dai bari tasa a samo ta wankan jego ko zata yi,dan haka tace " a ina za'a samu baho irin babban nan na wankan jego?"

Kanta a ƙasa Laraba tace"ai inada shi,dan Innar mu ta siyomin tace wai mu fara tanadi ,robar tafi ɗa wuya".

"Tohhhh ! Umma ta faɗa tana riƙe haɓa ,tare da mamakin abun,amma saita cewa Laraba ta ɗauko robar.Haka ta miƙe ta ɗauko robar ta kawota gaban umma,umma ta shiga gyaɗa kai a zuciyarta tana faɗin"lallai wannan uwa tasan 'yarta dan robar ma kamar ƙirar kamfani,dan kamar an auna larabar ne akayota fankaceciya.Miƙewa tayi tace" to ina madafin ku yake ?"a ɗora ruwan zafi".

"Ai ni bana girki da ice Maryam ta hanani,sai da riho"

Kallonta umma tayi tace au kema sunan mamanki Maryam kenan,lallai mama bata son 'yar nan tata tayi ƙaurin hayaƙi ko?"

Murmushi Laraba ta sannan tace"Ah ah maryam fa 'yarki itace ta hanani girki da ice"

"Wai kina nufin Maryam dai dana sani?"

Gyada kai alamun ita.

Dariyar takaici umman tayi,tabbas mai hali baya fasawa amma inba haka ba,yanzu Maryam yazatayi da wannan rushe shiyar idan ta tsokano ta,to a yadda take gani ko ita da Baban su Maryam ɗin ai sai sunci ƙaniyar su gurin ta,dayake ma da sauƙi dan taga akwai jituwa a tsakanin su,sai dai ta lura Laraba girman ne kawai ba wayo.Haka dai tasa Laraba ta kunna risho aka ɗora ruwan zafin.

A banɗakin Laraba umma ta haɗa ruwan bayan takai robar,sannan ta ce Laraba ta tashi taje ta faɗa mata yadda zatayi cikin hikima.

Umma na zaune kusan minti goma taga laraban ta shigo ɗakin kanta a duƙe.Umman ce ta kalleta tace "har kin gama gasa jikin naki?amma dai ba baki shiga ruwan nan da kyau ba,inba haka ba du-du-du mintinki nawa,dan haka maza ki ɗauko bokitin a ƙara zuba wani,in kin tsaya son jiki kece da wahala,dan kar kiga mijinki tsoho,su maza kullum jinsu suke kamar sabbin ƙyanƙyasa,dan haka maza miƙo a ƙara wani ruwan".

"Dama ba ƙin shiga nayi ba ina zama ne sai robar ta fashe"

"Ta fashe fa kikace?"umma ta faɗa tana zaro ido waje😳



*Alƙalamin khady* ✍
🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀


*YAR CASKALE*
( _sanadin bakin uwa_ )


*NA*
*KHADIJA USMAN*

_Real Tame gari_



*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*


5⃣7⃣-5⃣8⃣



"Oh ni Huwaila,tunda roba ta fashe ya zamuyi? Gashi dai ba abin a samo daro ba ya ɗau zafi duk kibi ki ƙone,garin neman gira kuma a zo a rasa ido,ya muka iya,kawai ɗauko butar ki babba a zuba ruwan ki kama ruwa,gashin dama ai shine dai-dai tunda muna son ruwan ya shiga ciki ya gasa miki ciwon,to kodai ɗan ƙaramin tiyo zamu samu a zira a bakin botar sai kema kisa ko ruwan zai shiga? Kai nan ma ba dabara bace,kinga kawai kawo butar a zuba kar ruwan ya ƙone".
Ita dai Laraba kanta a sunkuye Batace komai ba,har Sai da akace ta miƙo buta ta shiga ta ɗauko.Sai da umma ta haɗa mata ruwan ta sanar da ita yadda za tai sannan ta bata ta nufi ban dakin.Ita kam umma al'ajabi take tayi,a haka har larabar ta kuma dawowa ta haɗa mata wani ruwan ta ƙara watsawa😂.
**********************
Suna nan zaune ba wata hira suke ba a tsakaninsu,sai ga malam ya aiko da Isma'il da kayan miya da ledar taliya, kasancewar yasan su salame sun koyo azzalumin rashin mutunci,yasan bazasu bawa uwar albarka koda ruwa ba.Duk yadda Laraba take ji,haka ta daure ta tashi ta ɗora musu taliyar,maman Maryam ta so ta bari amma tace zata iya.Koda ta kammala a kwano mai kyau nan ma aka zubawa malam,suma Baban Maryam nasu daban aka zuba musu shida malam Garba.Maryam kam ɓatan dabo tayi,sai da kowa yaci ya ƙoshi sannan ta dawo gidan.Isma'il ya gama cin abinci kenan,ya ɗago ya kalleta ganin ta faɗo ɗakin a guje ko sallama babu tana haki"Ke Maryam shi ne kika gudu kika barni kin san ban san gari ba ko?, Badan gidan nan bai da wuyar ganewa ba ai da na ɓata".
Humm yaya Isma'il ai dan baka san ina naje bane shi yasa,da ko cewa nayi kazo muje bazaka ba,Anty Laraba ai kin san gidan su maraba da wari ko?"
"Eh mana gidansu Iro mahaukaci".
"Yauwa can,to dama rannan ne fa da na je ta wajen layin,kin san wai ɗaureshi ake yi,ni ban sani ba sai naga an ɗaureshi jikin bishiya, ina zuwa nace mishi sannu yaya,sai naji yace min yauwa,nace laifin me kayiwa me gari yasa aka ɗaureka?sai yace min babu komai,tsabar zalunci ne,shine nace masa idan na kwance ka nawa zaka bani? Shine yacemin biyar,Nikuwa na kwance shi,ina kwance shi kuwa ya riƙe Ni,yaita zabgamin igiyar nan,da kyar aka kwaceni,shine ban faɗa wa kowa ba nace saina rama,dana san yau zan tafi shine nace nasami bulalar malam ƙatuwar nan dayace yana dukan masu kunnen ƙashi da ita na ɓoye,yauma ina zuwa na tarar dashi a ɗaure, na kuma cewa in kwance ka? Yace "eh" na ce,idan na kwance ka nawa zaka bani? Yace ɗari,shi ne nace masa Ni kuma zan baka ɗari biyu kana so? Ya cemin "eh" shin Ni kuwa na fito da bulalata na shiga zabga masa,Allah yau ba kalar kukan da Iro baiyi ba,da farko ba wanda ya fito sai daga baya baban su kandala ya fito shi ne ya ganni ya biyo ni,wallahi da kyar na sha" ta ƙara sa maganar tana mayar da numfashin gudun datayi.


"Na shiga uku na lalace! Dama har yanzu Maryam baki daina halin ba? Malam fa cewa yayi kin kintsu kin zama kamila mumina,ashe ƙarya ne,ai ni dama nasan da kamar wuya wannan matsayaciyar ace cikin ƙanƙanin lokaci wai ta nutsu,to wallahi yau sai dai abin ya ƙare akanki,mahaukacin da kika tsokano abin sai dai ya tsaya akan ke da kika jawo,ni kinga ma tafiyata, in an gama lallasa ki a kawomin ke nayi jinya,'yar iska kawai".

Laraba dake tsaye jin abinda umma ke faɗi,dan haka ta tattaro jarabar ta ta da ta can tace"Ai wallahi indai ina nan ba wanda ya isa ya taɓa maryam,ba dai Iro bane kawai,to yazo ni zan lallasa shi,Ni na ma warke,Maryam jeki ki ƙara tsokano shi,yazo wallahi saina ci hancin babarsa".

"Oh Ni Huwaila ! Nikam naga abinda yafi ƙarfina, ah kice malam mazahabar caskale ya kawo ki bawai ki shiryu ba,kidai ƙara tambaɗewa da lalacewa,dan haka tashi maza gara ma mu koma gidan nasan yadda zanyi ki daina wannan hatsabibancin,tunda gashi har da masu ƙirar katafila ke tare miki faɗa,ba dole abu yaci gaba ba tunda kunsa zalunci a harkar, kije ki tsokano ƙananan ɗiba,ita kuma ta markaɗe miki su,to kinga tashi maza musan nayi".
Haka tá kama hannun Maryam tana faɗin taso 'yar jaraba ai banga ta zama ba tunda kika tsokano motsatstse".

"To ai ban ɗauki jakata ba umma"

"Ba buƙata ki barwa wasu almajiran ita,tunda baza'a rasa masu buƙata ba".
"Dan Allah Innar Maryam ki barta karki tafi da ita kinga itace ƙawata,kuma ita ke bani shawara a komai,na rantse ki kyaleta duk wanda ta tsokano Ni zan tare mata".

Numfashin takaici umma taja sannan tace,"kice Maryam ba koyon tarbiyya aka kawo ki ba kawai an kawoki koyon CASKALE,to wallahi bada ni ba,gara ki koma gabana duk abinda zakiyi kiyi shi da a gaban idona".


Da matsiyacin gudu sukaga malam ya shigo,yayin da ya buga wani uban tsalle ya ketare kan Maryam ya afka ɗakin Laraba ji kake bamm ya banko ƙofar.Salame da Zuwaira na zaune kofar daku nan su su na aikowa su Laraba harara a fakaice dan suna jin duk abinda suke faɗa.laraba ta buɗe baki da niyyar tambayar malam sai ji tayi anyi ciki da ita amma bata faɗi ba sai dai ta motsa daga inda ta ke.Malam Garba ne da baban Maryam suma a guje yayin da duk suka ruɗe suka shiga laluben inda zasu ɓoye,daga can malam Garba ya shiga faɗin"yo ta nan Shu'aibu,biyo nan ɓangaren Inna salame".Suma su salame ganin mazan na gudu yasa suka shiga wurga ido dan ganin meke faruwa,aikuwa a guje malam Garba ya bangaje salame ,itama Zuwaira dake tsaye tana son ganin meke faruwa nan baban Maryam yayi gaba da haɓarta,wadda saida tayi wani juyi kafin ta kifa saman randar ruwanta nan kuma kowanne ya shige ɗaki ya banko batare da la'akarin ko wanne ɗakin suka shiga ba.

Da nufin yin bala'i Zuwaira ta ɗago,amma sai me.Ido biyu tayi da Iro daya shigo a guje yana muzurai hannunsa riƙe da wata sharɓeɓiyar adda tsirararta,na ya shiga raba ido.Ganin hakan da sukayi duka hankalinsu ya tashi, kafin kace me salame duk

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login