Showing 6001 words to 9000 words out of 24637 words
dakatar dasu,Babu wanda ya raba su,malam ya Hana,saida suka gaji sannan suka Bari,bayan an daddaki bakin juna.Kuma har wannan lokacin maryam bata daina kid'an ba.Sai da kowacce ta koma gefe tana mayar da numfashi, itako Maryam ta janye fanteka gefe ta zuba musu ido bayan ta tallafe fuskarta da duka hannuwanta biyu.
Shi kam malam baice dasu komai ba,illa zuwa da yayi ya kama hannun maryam yaja ta itako batare da Nuna tsoro ba ta bishi,Dan tasan dai bazai wuce ya daketa ba.
D'akinsa ya nufa da ita,batare da yace da ita komai ba ya zaunar da ita Kan wani buzu dake gefe.Wata jaka ya jawo ya dauko wani daurin magani ya jawo wani kwano ya dauko d'aurin rubutu ya tsiyaya a Kofi ya hada da wannan maganin.Yakai wajen minti biyar Yana Kara tofa addu'a a ciki,sannan ya mikowa maryam yace ta karba tasha.
Zaro ido waje tayi sannan tace"miyau d'in zansha malam?"
"Wane irin miyau Kuma maryama,bakya ganin addu'a nayi miki,Dan haka yi hakuri karbi Kisha kinji mairoro" ya fad'a Yana Mata alamar rarrashi.
Karba tayi takai bakinta da niyyar sha sai Kuma ta dawo dashi tace"tsakaninka da Allah malam ka wanke bakinka kafin kayimin addu'ar Nan?"
Yak'e malam yayi yace "nawanke Mana baki gani ba tun safe nake asuwaki".
"Tab da da asuwakin safe zaka tofeni wallahi bazan Sha ba" ta fad'a tana dungurar da kofin.Duk yadda malam yakai ga lallaba ta kin Sha tayi,hakan ko ya fusata shi,Saida ya dauko wata narkekikiyar bulala wadda yake maganin irin su Maryam da ita ya zuba mata,.Duk yadda ta Saba da duka Amma taji wannan bulalar ta dabance,aikuwa ta shiga canyara kuka,shi kuwa Saida ya tabbatar tayi laushi sannan ya kyaleta Kuma bayan ya tabbatar ta shanye rubutun,ya fada Mata da niyyar da zata Sha a zuciyarta amma sai cewa tayi a zuciyar tata"ka da Allah ya shiryeni".
**************
Wannan dukan da malam yayiwa maryam Saida ya sata zazzabi,dayake kusan d'aliban suna da had'in Kai a wannan fannin Kuma ganinta k'arama yasa suka kula da ita.Babanta yayo Mata aike amma baizo ba hakan yasa ta samu k'arin wasu kayayyakin,wanda suke masu dadi,duk da take yarinya Amma ta lura da halin matan malam,Dan Haka saita Zama zakara me neman suna bada kwaya kaci tsakuwa,hakan yasa suka d'an Fara janta a jiki,duk da su a tsakaninsu babu wata jituwar kirki.
Tun dukan da malam yayiwa maryam yasa ta nutsu,Nan shida kanshi malam ya Kira babanta Yana Masa albishir da ci gaban da aka samu,nan kuwa ya Nuna farin cikinsa har yake fadawa huwaila,wadda tace in an kwana biyu zasu zo suga Maryam din.
************************
Yau ta tashi da niyyar aiwatar da kudurin dake ranta,Maryam yarinya ce Mai ra'ayin rik'au,batada hak'uri Sam,duk da batada yawan shekaru,amma tanada akidar rama abinda aka Mata,sannan ga bak'ar mugunta a gun Yara sa'anninta,Sam batada tsoro ta Saba da duka da zagi,hakan yasa duk wani duka ko hargagin mutum baya tsoratata.
****
Duk da irin kyautar datayiwa su salame,hakan baisa sun barta haka ba,Saida suka bi suka k'ara da wasu abubuwan a gabanta,Dan Haka tace Suma sunci bashi.
Laraba me d'an bagalaje,irin narka-narkan matan Nan ne,saboda ma girmanta yasa tak'i auruwa,Dan gaskiya ita d'ince komai nata na musamman ne,hakan yasa dataga tak'i auruwa,saita Fara sana'o'i kala-kala,da sana'ar cikin gida takeyi,to kun San matan aure da cin bashi,yazamana idan mace taci bashinta,har gidanki har dakinki zataje ta jawo ki,in kin Bata kudinta kin tsira,in Kince Babu kuwa,Nan zata kamaki kamar 'yarta taita jibga,har sai anzo an kwaceki,hakan da takeyi ne yasa duk aka daina siyen kayan ta.Saita yanke shawarar komawa sana'ar yara,Kuma da biyar goma tana samu abinta.Tunda Maryam tasan da ita duk wani tattalin arzikinta ya Fara k'arewa a can.
Yauma can ta nufa,tana zuwa kuwa laraba tahau washe Baki,Dan jininsu ya had'u Dana maryam,aikuwa ta tsugguna tana me kokarin bude murfin da aka rufe farantin d'an malele,Saida ta k'ara zambada yaji a iya Wanda zata iya siya,dayake yau batajin cin d'an ba galajen ,d'an malelen take sha'awa,kuma gashi yau yajin laraba yasha kafi zabo yayi chauuu dashi.
Jin cikinta kamar ta shafa mota ga wani mugun kwadayi datakeji,ji take idan aka Bata farantin d'an malelen tana iya cinye shi.dan haka ta gyara zamanta saman wani d'ab karamin dutse tace,"Anti laraba kin San me?"
Dai-dai tana make wata yarinyar data siyi d'an malele ta tsaya lasar faranti tace" sai kin fad'a mairo?"
Gyara zaman ta kumayi sannan tace "Wai malam naji yace Yana sonki".Tsabar farin cikin Jin wannan kalmar me tsada yasa laraba ta saki Baki da hanci ta kasa motsi,illa jawo hannun yarinyar data make yanzu da tayi ta dan gwarar da ita,da kyar ta iya bud'e baki tace "cinye duka"Aikuwa yarinya ta gyara Zama tana washe baki,ganin haka yasa itama Maryam matsowa tana saka hannu suka hau cin d'an malelen,yayinda laraba take fad'in" taho farar yarinya me farin labari ki k'ara fad'a mun inji a wane kalar yanayi ya furta Miki Yana so na"
"Um um Anty laraba, Bari in gama tukun"sam laraba tak'i barin Maryam ta sake da cin d'an waken,fad'i take ta taso inta Gama Bata labarin zata yi Mata Wanda yafi wannan dad'i,amma Sam Maryam tak'i bari.Ganin haka yasa laraba tasowa cak tayiwa Maryam daukar jarirai ta zauna ta d'ora ta bisa cinyarta tana fadin,bani labarin malam ja'afar d'ina ta fad'a tana karkada ido".
"Nidai gaskiya Anty laraba ki daina marmar da idon Nan kina tsorata ni kamar fa zabi yar aljana haka Kika koma".
Duk da taji haushi amma Dan Jin ance ana sonta ta maze tace to na daina fad'amin kinji,Dan in munyi aure da malam bazaki k'ara kwana d'akin Nan ba,sai d'akina kece 'yar tayin kwana na".
π³"amma ba gado d'aya zamu rink'a kwana ba dai ko?"
"A gado d'aya mana,ai Ni yanzu banida wadda ta fiki".
"Har babarku da babanku?"
"Eh Mana,yanzu dai tashi muje nayiwa malam girki me dadi,ki tafar mishi da shi".
Aikuwa suka rankaya gidansu laraba,ranar ma danba galajen harshi kyautar shi ta bayar.
Danwaken fulawa tayiwa malam,aka daka Masa had'ad'd'en yaji Wanda yaji onga,itama Maryam an sammata nata nana ta k'ara ci ta sud'e kwano sai kace me cikin zani.
Cikin kwanukan da aka d'ebi shekaru ana tarawa Dan jiran ranar aure.Ciki aka dakko falleliyar langa aka zubawa malam a ciki ,har Maryam ta d'auka zata tafi saita ajiye.Da sauri laraba ta kalleta tace "tawajena ya akayi ne?"
"Ba komai,kawai jinai bazan iya Kai Masa bane,abin yayimin nauyi"
Da sauri laraba ta matso tana fad'in"haba 'yar d'akina ,taimaka kikai Masa,kice Masa Nima Ina sonsa ungo wannan ma,ta ciro naira ashirin ta Bata, aikuwa Nan da Nan Maryam ta d'auka ta fice.Laraba dake tsaye mamanta na tayata murna kawai saita buga tsalle,Amma abin mamakin ko rabuwa da k'asa batayi ba,illa mazaunan ta da sukayi sama da k'asa da Kuma teb'arta datayi rawa.
***********************
Tana shiga gidan cikin sa'a ta Sami duk ahlin gidan a hallare,aikuwa gaban Zuwaira taje ta mik'a Mata d'anwake,Koda Zuwaira ta bude ta gani nasha-nasha da Mai,babu tambayar daga Ina,kawai tahau juyawa tahau kasaf ta shi,bayan ta jefa biyu a bakinta tana fad'in "um um um,gaskiya kowace tayi d'anwaken Nan ta kwararriya ce",Nan ta mikawa kowa ya d'auka.
Saida kowa ya cinye ana sid'e hannu sannan salame ta juyo ta kalli Maryam,wadda Dan tsabar dadin da d'anwake yayi,an Manta da ita data kawo a rabo ko Bata ba ai ba,tana gefe tadau wani siririn Kara tana Wasa dashi a k'asa taji salame nacewa"'yar albarka Ina Kika samu uwar d'aki harta Baki wannan danwaken,Dan nasan wannan na musamman ne".
Batare data d'ago daga abinda takeyi ba tace"budurwar malam ce"
Wata irin kwarewa Zuwaira tayi,wadda tasata Fara kelaya Aman danwaken dataci,itako salame cewa tayi "wane malam din Kuma?"
Saida Maryam ta d'ago wannan karon,harda cewa zuwaira,"sannu baba" sannan tace "malam Mana,Daya dakeni rannan a dakinsa,malam dai na Nan gidan,baban su Idiris".
Cikin hargowa da bala'i dukansu suka shiga fad'in,malam yaci amanarsu wace shegiyar ce wannan,harda Masa girki,wato shiyassa yau yak'i cin abinci yace a koshe yake,ashe dama abincinta yake jira,aikuwa yau zaizo ya samesu,Nan suka kalli maryam sukace ta fada musu wacece ta aikota.
Cikin ko in kula tace" laraba tirela"
A tare suka dafa kirji suka maimaita "Laraba tirela fa kikace!"
Hakan yayi dai-dai da shigowar malam Wanda Bai San wainar da ake toyawa ba yace "me laraban tayi naji ana Kiran sunan ta..........."
_kuyi hakuri wallahi Banda lafiya ne,Amma nasami sauki Amma ban warke ba,insha Allah idan na warware zaku jini sosai_
*Alkalamin khady* β
ππππππππ πππ
*_'YAR CASKALE_*
( _Sanadin bakin uwa_)
*NΓ*
*KHADIJA USMAN*
( _Real Tame Gari_ )
*Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
*
____________________________________
*πKAINUWA WRITERSβπΌ ASSOCIATION*π€π»
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
2β£1β£-2β£5β£
_Hakika masoya basa taba k'arewa a rayuwa,Allah yak'ara k'auna da zumunci amin_
_Gasikya ba abinda zance muku sai godiya_
*TAME GARI FANS NOVEL,1,2,3*
*KAINUWA FANS*
*HAUSA NOVELS GROUP 1,2*
*HAZAK'A GROUP*
*KOMAI DA RUWANKA GROUP*
*MUTUNTA JUNA GROUP*
*MASOYA NOVELS GROUP*
*MUK'ARU DA JUNA GROUP*
*KOWA NAMU NE GROUP*
*Kai alk'ur,an Kuna da yawa bazanma iya lissafa ku ba,dukka wadannan groups din,sune Kan gaba wajen yimin comment,nagani Kuma nayaba na Kuma gode,Allah yabarmu tare yabamu aron rai da lafiya*
_________________________________
Dukansu shiru sukayi suna huci.Shikuma cikin rashin lura da yanayin su yak'ara cewa"nace me laraban tayi ake Kiran sunanta?fatan dai ba wani yaron bane ya tsokano ta,Dan ni bana son rigimar yarinyar nan wallahi".
Tsaki salame taja sannan tace"dama Ina zaka so Yara su tsokano amaryar ka,tunda kasan abinda ka k'ulla,ashe shiyasa kwana biyu in an kawo maka abinci sai kace ka k'oshi,dama kasan inda kake zuwa kake cika cikinka,to asirinka ya tonu yau d'in nan,Kai inba ma rashin Sanin kala ba,me zakayi da laraba tirela, yarinyar da naji Yara na fad'in da daddare tifa take Zama,shi ne Kai zaka je ka kwaso Mana ita ko,duk tabi dare ta markad'e mu ace munyi hatsari da safe,to nidai wallahi zan furta haram,kawai ka sakeni nace astagafirullah daga baya" ta k'arasa zancen tana girgiza.Itama zuwaira ta amshe da fad'in" kema kenan Yaya da kukayi aure tun zamanin k'uruciya har aka girma tare,bare ni sabuwar zuwa wadda ko yau ya shek'e zan iya aure in haihu,da dai a auromin laraba tirela a matsayin kishiya,wallahi na gwammace a kaini gidan mahaukata in dinga musu burushi".
"Wai ni duk ku tsaya"ku wane munafikin ne yace muku zan k'ara aure,auren ma Kuma Wai yarinyar Nan laraba, yarinyar da aka Haifa a gabana".
"Oho dai,ko ma dai Kai ka karbi haihuwar mudai bazamu yadda ba"cewar zuwaira,"Dan tun yanzu anayo maka wannan zazzak'an girkin Ina zaka iya hakura"
"Wane girki Kuma? au shi munafikin har ce muku yayi tanayo min girki kenan?
Samiran da aka kawo d'anwake salame ta dauko ta dungurar a gabansa tace"ga shaida Nan ai Kuma ga Maryam Nan ka tambayeta Dan ita ta aiko"
"Hummm! Kawai malam yasami zarafin cewa,Dan ya lura yau sharri matan nasa sukeji,Dan Haka ya juya ya kalli Maryam dake zaune saman wani d'an dutse tana gwagwiyar taura yace"ke maryama waya Baki abinci ki kawo,Kuma wa akace ki kaiwa kikayi batan Kai Kika kawo Nan?"
Saida ta tsotse kwallon ta yar sannan tace"Anty amarya ce tabayar a kawo maka,Kuma tace Wai kazo da wuri yau tunda ba makaranta,sannan Wai in fad'a maka,malum- malum dinka dakaje da ita rannan ita zakasa Wai kafi kyau,saika koma kamar halifa d'anka,sannan Wai ka tafi Mata da lemon Nan na jarka irin na jiya Wai taji dadinsa,Kuma Wai maganar kazar baba Zuwaira dakace......" Uban babanki!π Malam ya furta a fusace bayan yayo kan maryam,wallahi kedai wannan ba k'aramar jaraba bace,ashe shiyasa aka had'oki aka kawomin ke,dayake uwarki 'yar k'aramar hukumar Gama ce,shine Kika zo ki gama ni da iyalina tun kin 'yar kankanuwar ki Ina ga kin girma Kuma,gashi marabina da ashariya tun banfi shekara shida zuwa bakwai ba,harna manta harrufan da ake hadawa ayi zagi,amma yau gashi kin sa na tunosu a guje,Dan haka yau sai jikinki ya fad'a miki,sai kin furta da bakinki cewar karya kike".
Dukansu suka Sha gabansa suna fadin yafara bugunsu kafin ya daki Maryam,danta Fadi abinda yake boyewa shine zai musu borin kunya.Hakan ya Kara fusata malam, musamman Daya ga dukkan dalibansa sun taru suna kallon su,hakan yasa yafara ball da duk wani abu dake tsakar gidan yashiga sababi.Nan fa gida ya kacame,inda Yana Fadi matansa na Fadi,abinda Bai taba faruwa ba a tarihin aurensu,hakan yasa wasu daga cikin yaran suka ruga suka kirawo wasu daga cikin abokan malam dake zaune kofar gida.
Sam ba Wanda ya lura da sulalewar maryam,tsawon lokaci ana fama da malam da matansa suyi shuru amma Abu ya faskara,shi yanaso su fahimci gaskiyarsa su yadda baida wata alaka da laraba,su Kuma sunki amincewa.Zuwaira ce ta mike tana fad'in,ai wallahi tunda kaki sakinmu to daga Kai har amaryar taka inta shigo zaku gane kurenk......" Maganar ta makale ganinta ta shigo famkam-famkam,aikuwa da matsiyacin gudu Zuwaira ta shige dakinta ta banko kofa,yayin da salame tace"ke kuma lafiya Kika wani shige d'aki ko ya tsorata ki ne da idanu,to Ni yanzu Sam kallonsa baya firgita ni,Dan Haka Bari na karasa abinda Baki fada ba,idona idon laraba wallahi sai dai buzun t........" Itama ta kasa k'arasawa ganin an budawa laraba hanya ta nufo ta.
Wata irin k'ara ta saki tana fadin"na shiga uku malam,badai aikawa kayi aka kirawota ba,muna Nan muna tsara yadda za'ai muyiwa dakin da zata zauna saukar kur'ani ,shine ka aika a kirawota salon ka wahalar da amarya,sannunki da zuwa amaryar mu,yanzu nake cewa idonki idona saina gode Miki bisa dawainiya da malam" ta karasa maganar tana me karkade tabarma Dan laraba ta zauna.Aikuwa hankam-hankam ta shiga washe baki,ta juya ta nufi gurin Zama,Dan dama Maryam ce taje tace Mata Wai tazo malam nason ganinta zai musu nasiha,shine fa ta debo jiki ta taho,Dan Koda ta fadawa uwar cewa tayi taje kawai,inma ba matsala tayi zamanta sai su biyota da kayanta a daura aure da la'asar,ita duk Bata fahimci ma abinda matan malam din ke fada ba,shiyasa take fara'a, musamman data gansu duk Ahlin gidan a had'e hakan ya k'ara tabbatar Mata da gabatar musu da ita zaiyi,"kaiiii gaskiya malam d'an soyayya ne" ta furta a zuciyarta........
_Idan naga comment dayawa zaku Kara birgeni,sannan ga Wanda ke cikin group Dina,bazan gaji da shara ba,domin duk wadda Naga ta karanta babu comment ko tana zaman labe to zata jita a waje,sannan duk group din da kukaga na daina musu posting,to basa comment ne,Dan haka kada aga laifina Kuna Raina masoya._
*Alakamin khady* β
ππππππππ πππ
*_'YAR CASKALE_*
( _Sanadin bakin uwa_)
*NΓ*
*KHADIJA USMAN*
( _Real Tame Gari_ )
*Ψ¨Ψ³Ω
Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ
Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
*
____________________________________
*πKAINUWA WRITERSβπΌ ASSOCIATION*π€π»
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
2β£6β£-3β£0β£
π€£π€£π€£π€£π€£π€£π€£π€£π€£
Gaskiya na Dade Banga comment din Daya dinga bani dariya ba,kamar jiya da yau,Ashe Haka laraban malam keda masoya,to muje zuwa danjin yadda zata Kaya.
πππππππ
________________________________
Ji malam yakeyi kamar yayi hauka yau,Dan inya juya suka hada ido da laraba saita sakar mishi wani makahon fari,Wanda ke Kara sashi yaji wani yarrr,idan Kuma yakai duba ga inda take zaune yaga yadda ta mamaye fiye da Rabin tabarmar Saiya ji gabansa ya fad'i,Dan Haka ya kasa cewa komai,illah laraba daketa zuba mishi murmushin soyayyaπ.
Suna a Haka Zuwaira ta Dan bude K'ofa ta leko,Dan taji batajiyo ihun kowa ba,hakan yasa tace Bari ta fito taga meke faruwa.Ganin Maryam dare dare bisa cinyar laraba daga fitowarta ta kasa hakuri tace" na shiga uku,ke laraba nono kike Shirin Bata kome? Wannan shi ake Kira tayani kallon lalle a duwawu,inba Haka ba,ai gara kice a kaiki gidan marayu in nonon ne yayi Miki nauyi kike son ragewa,saikije ki rabar wa marasa iyaye sadaka,amma ba kizo ki dauki tsohuwar yaye ba kice Zaki shayar da ita".
Tunda ta Fara maganar laraba ta tsareta da ido,sannan ta Fara yinkurin sauke Maryam ta shiga kiciniyar mik'ewa.D'an autan malam ne yace" wallahi baba Zuwaira ki gudu,in laraba ta kamaki alkur'an dukan tsiya zatai miki,Kuma babu me iya kwatarki daga baba har babarmu gara ki gudu kafin ta mike".
"Ba inda zani,ita harta Isa tazo har gidan mijina tace zata dakeni wallahi da saina b'ara Mata Kai gida biyu "ta fad'a tana rarumo k'atuwar tabaryar da suke surfe da ita.
Itako Laraba,Sam hargagin Zuwaira Bai tsoratata ba,Dan Haka ta mike ta nufeta yayin da Zuwaira ta tattale ta d'aga tabaryar tana fad'in" kina k'arasowa Ina sauke Miki ita".Ganin da gasken zuwan zatayi yasa malam daka musu tsawa duka,tare da umartar kowacce ta dawo ta zauna.Cike da salo laraba ta juyo ta Fara bada wani taku Wanda take ganin zai jawo hankalin malam ji kake taffff,taffff,taffff.Malam baisan lokacin da yayi baya ba ya dafe bango Yana Kiran astagafirullah,saboda ganin manyan Kaya,yayinda ya dinga kallon matansa kamar wasu 'yan daudu,Dan gani yayi kamar halittun matan k'auyen aka hadowa laraba duka gaba da baya.
Malam labaran ne ya shiga fad'in" subahanallahi,malam yi a hankali kada ka Fadi,yakarasa maganar Yana me kallon bayan laraba,a zuciyarsa Yana ayyana sai an Dora bokin ruwa ko kwarya ta zauna das a bayan laraba saboda tudun mazaune,"Masha Allah" ya furta a fili.
Shikuwa malam nuhu Yama kasa motsi,illa ido Daya zubawa kowa a gurin,sai daga baya ya k'arasa ga malam din shima Yana tambayar lfy?,Yara kuwa duk suna Nan sun Sami t.v suna kallo.Ganin da salame tayi Zuwaira nata sababi shiyassa itama ta shiga nata sababin suka hadu gaba Daya.
Da dai akaga za'a Bata lokaci Nan malam yace kowacce tasami guri ta zauna zaiyi magana.Dan tsabar biyayya irinna laraba dukawa tayi,ai abinka da ba'a sababa take Taji kamar ta tsugunna Kan k'aya,Dan yadda kafafunta sukayi mata,batasan lokacin data sulale ba tana haki.
Bayan kowa ya nutsu dan har abokan malam suna Nan sannan yayi gyaran murya kafin yakai duba sa ga Maryam yace ta zo,.Kowa yayi tunanin bazata iya zuwa ba,amma kawai sai gani akayi taje gabansa ta tsugunna.
Kallo yaci gaba da binta dashi kafin yace"Maryam"
"Iyi" ta amsa
"Hmmmm" yace ya girgiza Kai yace "kina