Showing 15001 words to 18000 words out of 24637 words

Chapter 6 - YAR CASKELE cmlt

Start ads

24 Aug 2025

180

Middle Ads

da kyar ta lalubo minsileta da tasa aka siyo Mata Dan tana shafawa a jikinta inda ke d'an Mata ciwo take shafawa saboda har yanzu gajiyar biki Bata Gama sakinta ba.Aikuwa jambaki tayiwa malam dashi,bayan tafi tudun leben ta shafeshi dashi,Wanda malam ya saduda yanzu badan Allah ba,Koda ya kalli laraba a kaikaice ya banka Mata harara kafin yace cikin zuciyarsa"Hummm ki gama wahalar ki yarinya,kwanton bauna zanyi Miki inta Miki kisan mimmike har saikin rame,duk wannan jikin naki wallahi saina maidashi kamar sillen kara" ya saki murmushi a zahiri,Wanda ya Kara kwab'e fuskar,laraba da karaf a idonta tace" sannu malam,kadaina Kuka haka,bari gobe da safe sai in dafa ruwa in gasa maka wurin sannu kaji mijina"
Dammm! Kirjinsa ya buga,take yaji zuciyarsa tayi Masa d'aci,banda damuwa dayake ciki,daba abinda zai hana shi yiwa laraba d'an banzan Duka ya tattara ta a baro gobe yakaiwa iyayenta,amma yanzun ma Bari ya warke zai Rama ne.

Laraba da kanta ta tallabi malam ta Dora Kan gado,sannan tajawo Masa bargo ta lullube abinta Dan taga Yana rawar sanyi.Shikuwa malam,sosai yaji dadin gadon, musamman da laushin katifa kirar zamani ta ratsashi,ga lallausan bargo da aka luntsume shi dashi,kawai sai yake Jin wani k'aramin nishadi,duk da kudirin dake ranshi na tarin daukar fansa.Laraba Bata Bari malam ya kwanta ba,Saida ta lalubo ciwo takwas ta bashi yasha, Bata San waya yadda shi ba ranar da aka kawota,da har zata jefa shi shara,sai Kuma ta bari dan gudun Kar a aiko cigiya,to gashi ma yayi Mata rana.

Allah sarki baiwar Allah laraba,Sam kasa runtsawa tayi,tana kwance a katifar kasa,Amma ta zubawa malam Ido tana sharar kwallar tausayinsa.Duk abinda takeyi Yana kallonta sai Kuma yaji tabashi tausayi,Dan Haka ya rage yawan hukuncin da zaiyi mata,a Haka har bacci ya kwashe su.
🔅🔅🔅🔅🔅🔅🔅🔅🔅🔅


Tun asuba laraba tafarka danta d'ora ruwan zafi ta gasawa malam fuska kafin ya tafi masallaci.koda ta fito d'ibar ruwa,saita tarar gaba d'aya matan malam ba wadda randarta ke tsakar gidan,komai sun kwashe yau,hatta duwatsun girkin da sukeyi,bare Kuma azo maganar ice.Ashe dai Maryam tayi Mata dabara,da tace Mata jiya ta kawo a siyo Mata kananzir karta yadda ta dinga girki da ice,zatayi warin hayak'i,tunda ita 'yar gata ce,Kuma anyi Mata auren gata,to gara kawai ta nuna itama wata ce,kawai ta dinga girki a risho ta nunawa su baba salame ita wayayyiya ce.Shine ta bayar aka siyo Mata din ta zuba a rishon Dan dama da lagwani a jiki,Ashe zaiyi Mata amfanin kusa Dan a da ta dauka ba amfanin dazaiyi mata,duba da yadda taga tuwon gidan malam nada yawa,shiyasa,amma yanzu ta fuskanta ko a Dora ruwan zafi zai Mata àmfani.

Randarta ta ruwa ta bude ta debi ruwan ta shige d'aki.Cikin kankanin lokaci ta Gama dafa ruwan,ta tashi malam da kanta ta zuba ruwan a wata roba me Fadi,aikuwa cikin hikima da tattali ta shiga gasa malam,Wanda yake jinsa kamar jariri,saboda Jin sabuwar tarairaiyar dayake Samu,aikuwa sai a zuciyarsa tuni ya yanke shawarar karawa laraba tsawon Zama a gidan bayan yagama morewa.Haka ta gama gasa Masa,Kuma Alhamdillah yaji Dadi sosai,aikuwa a gida ma yayi sallar asuba,Dan Bai samu fita ba, Dan har yanzu kansa na Masa ciwo.Dan Haka Yana idar da sallar ya koma ya dada luntsume wa cikin katifar sa mahadi ka lotsa😜 Tuni kuwa bacci yayi awon gaba dashi.Ita Kam laraba bata samu zarafin komawa ba,illa dauko kayan malam datayi Wanda jini ya bata,da kayanta da suka Baci lokacin data rungumeshi,ta zuba a bokiti,tana jiran gari ya ida wayewa a siyo Mata klin saita wanke su.

🔅🔅🔅🔅🔅🔅🔅🔅🔅

Su kuwa su salame,kusan sa iya cewa cikinsu babu wadda tayi baccin kirki,kowacce ta so ta leko ta ga meke faruwa a dakin laraba,amma Sanin gidan gida ne mutane,yasa ba wadda ta fito Dan Kar taje a ganta,amma Kuma kowacce window da kofarta a hangame suka kwana.Lokacin da sukaji rakwacam din Nan k'arar zubowar kwanuka,kowacce matsuwa tayi taga meke faruwa amma sai suka dinga jiyo nishin malam,hakan ya Kara daga hankalinsu,a takaice dai ba wadda ta runtsa Dan suna son suga Taya za'a kashe arna(d'orawa Kai wahala).

Da farko sun dauka kwashe ruwan da sukayi da Kuma itace da murhu sunyi nasara.Itako laraba wani dan gidan Zuwaira da taga zai fita da bokiti karami zai siyo Koko,shi ta bawa ya siyo Mata klin din.

Kusan a tare matan malam suka fito tsakar gidan,yayin da kowacce ta shiga sabgar gabanta, amma kuma hankalinsu naga ɓangaren ɗakin Laraba,dan ganin me zai wakana.Itako Laraba bata ko bi takansu ba,tana son zuwa ɗakin dasu Maryam ke kwana,amma Bata s dokar gidan ba,dan duk abin Laraba bata da ɗabi'ar shiga shirgin daba nata ba,amma kuma kai inka shiga nata,tofa nanne ake kuturun bala'i,dan danƙarar ka zatayi kamar uwar data haifeka.

A gaban idonsu yaron yabata klin ɗin ta shiga wanke kayan da shaddar ta da ta malam.Sai da ta gama ta shanya duk suna kallonta kowacce idonta ya sauka aka dabbaren jinin daya kama zanin Laraba yaƙi fita,aikuwa nan da nan zuciyar kowacce tayi baƙiƙirin,tare da cin alwashin cima malam mutunci idan ya fito.

Shikuwa malam bai sami zarafin farkawa ba saida rana ta take,ya miƙe da addu'a a bakinsa,yayin da yaga Laraba kwance tana bacci, ƙara miƙa yayi da hamma,dan wata kafirar yunwa yake ji,ga kuma fuskarsa da gefen bakinsa daya hau,dan ma Laraba ta gasa masa jiya,ya kuma ji daɗin gashin,dan tanayi ne cike da salo,ga kuma wani ƙamshi datake yi wallahi.Hararar ta ya shiga yi,a ƙasan zuciyar sa yace ba ƙamshi ba,saina gama zuƙe ƙamshin zan karairaya ki in ƙara dake gaba,ko ba komai ai na ɗan more.Haka yasa kai ya fito waje,ya nufi ɗakunan matan nasa.a zaune ya samesu,duk da suna zamani irin na kishi,amma hakan bai hana yau wani zumunci ƙulluwa a tsakaninsu ba.

Koda yayi musu sallama ba wadda ta amsa masa dan sun hango shi amma basu kalli fuskarsa ba.Jin sunyi shuru yasa shi magana cikin faɗa"wai bakwa ji ne ina muku sallama kunyi banza dani?"

Batare da sun ɗago ɗinba salame tace"kabari ka haɗiye naman daka ƙunso a bakin naka tukun ,inka kammala cinyewa sai mu sami zarafin tanka maka.

Ran malam ya ɓaci dan duk abin matan nasa,bai taɓa fuskantar irin haka dasu ba,ko rikicin su sukeyi in yayi musu tsawa suna shiga taitayin su,amma ya fuskanci yanzu raini ya shiga tsakaninsu,dan haka cikin kakkausar murya ya shiga yi musu faɗa.Babu wadda ta tamka masa a cikin su,dan sunga ɓacin ran da basu taɓa gani ba.jin yana faɗan amma a cunkushe ,yasa Zuwaira ɗagowa da nufin bashi haƙuri,aikuwa tayi katari da fuskar malam.

😳zaro ido tayi,sannan ta kalleshi cikin sauri tace" Ala gafatta me ya sameka a fuska haka?"

Salame da maganar Zuwaira tasa ta kallon malam ɗin itama,aikuwa saita sheƙe da dariya ta shiga tafa hannuwa tare da rangaɗa ƙaramar guɗa "lallai wani kaya sai amale,wannan shi ake kira tafashi kaɗa miyar farin shigar girki,Ni da mandali,lallai yau malam kasan kayo aure, ashe mu duk sauƙi muka biɗar ma yau kayi babban kamu,ah lallai na yadda namiji baya tsufa da son duniya da yin ƙara'i,amma inba haka ba ina sauro ina Giwa,Ni wallahi na ɗauka ma yadda wajen yake haka cikin ma,ashe hangen dala bashi ne shiga birni,su ƙuda an tafi kwaɗayi gashi nan ana shirin gamuwa da ajali" ta ƙarasa zancen tana dariyar shakiyanci.

Cikin rashin fahimta Zuwaira ta kalli salame tace"wai ni yaya me kike nufi da Waɗan nan maganganun naki ne?"

Dariya salame ta kuma sawa kafin tace"haba zuwai sai kace ƙaramar yarinya,ki kalli Ala gafatta da kyau zakiga hannun mata ya shiga aka sashi a kwana,ki dubi can,tayi mata nuni da kan igiyar da Laraba ta shanya kayan ta,ai da gani kin san kwanan zancen,dan haka malam Barka da arziki dan an samu abinda ake nema,sannan kuma Barka da tsira da rayuwa...." Bata ƙarasa ba malam yakai mata wani harbi da ƙafa ta kauce da gudu ta faɗa ɗakinta,itama Zuwaira hakan tayi,yayin da malam ya shiga masifa yana ball da komai na gabansa.Nan ma salame ta leƙo tana faɗin "ina ni ina tsayawa sabon ango mai ji da ƙarfi ya bugeni,ah ah bada ni ba,kai dai ka tsaya ayi maka inda bazaka iya ramawa ba,amma mu bazamu bari can a ɗime ka ba ,mu kuma kazo ka rama a kanmu" nan tajawo windon ta rufe ruff ganin malam ya nufota.

Shikuwa malam yarasa meke damunsa kwanakin nan,"anya kuwa ba yarinyar nan ce Maryam ke da aljanna ba tabar kanta ta dawo kaina ba".tabbas da sake,dan haka dole yaje yayiwa kanshi ruƙiya yanzu.

A hanyarsa ta shiga ɗakinsa na zauren ya haɗu da Maryam zata shigo"cikin daka tsawa yace"ke Dan ubanki daga ina kike?"

Gyara tsaiwarta tayi sannan tace"Anty Laraba ce ta aikeni wai inyo cefane a dafa maka kaza?"

"Au to to Haka ne, i maza kikai mata dan nasan tana can tana jiranki hanzarta" harta juya da ledar dake hannun ta sai.kuma tace"to baba malam ta yaya zaka ci naman? Naga kaji ciwo a bakin?"

"Ke ban son shegantakar banza,idan an dafa kya ga yadda zanyi inci tunda ai ba bakin aka ciremun ba"

"To idan tayi yaji fa?" Ta jefo masa tambaya."Ko uban yaji tayi ba abinda zai hanamin cin naman nan".

"To idan.......,ke jakar ubanki nace,zaki wuce kikai kayan miyan ko kuwa saina zo,wallahi kadai wannan wannan yarinyar da magana a gurin nan,kima je ki haɗa kayan ki,dan nasa faɗawa ubanki yazo ya ɗaukeki,dan haka ki zama cikin shiri".

Batare data ƙarasa saurarar abinda yake ƙarasa faɗi ba tayi cikin gidan da gudu.inda bata zame ko ina ba sai ɗakin Laraba,ta tarar tana shara nan ta samu guri ta zauna ta miƙawa laraba ledar dake hannunta tace inji malam yace a kawo mata.Cike da farin ciki Laraba ta kaɓar,ko da ta buɗe sai taga rogo,aikuwa tayi murna dan ta kwana biyu bata ci ba,nan ta baje tace Maryam tazo suci tace ta ƙoshi,itako ta cinye abin ta dan dama yunwa takeji.Sai da ta gama nan Maryam ta kalleta tace"Ina na baba malam ɗin?"

"Me kenan?"cewar Laraba.

"Rogon mana,ce Miki fa nayi ki raba biyu ki ajiye masa nasa".

Cikin marairaice murya Laraba tace"wallahi banji ba,amma kije gida kicewa babarmu ta dafowa malam rogo"

"Kam bala'i, cewar Maryam,ai wallahi ba ruwana dan kafin ma inje gidan ai yazo ya tambaye ki,kije kice masa nice ban faɗa Miki ba,ya dakeni Ni kuma inda ya sakeki,kawai ki tashi ki kamo wannan kazar taki budurwa a dafa masa,dan dama dazan shigo naji yana cewa wani abokin sa shi kaza yake son ci,mai romo da ɗan yaji-yaji.Yauwa wai ni Anty meye yasameshi a baki naga ya daddauje ya kuma kumbura?"

"Wallahi faɗuwa yayi ina faɗa Miki, kwanukan Nan Kuma na jere suka faɗo masa,danma na shafe mishi da minsileta na gasa masa da ruwan ɗumi"

Dariya Maryam ta shiga yi tuni muguntar Tata ta motsa,jin wai babanta zaizo ya tafi da ita,ai yaseen saita yi na karshe.Dan haka ta kalli Laraba tace"Ai Anty ba minsileta zaki shafa masa ba, Wannan baya warkar da ciwo da wuri,loko zaki kawo a siyo masa,sai ki shafa masa yanzu kafin kazar ta dahu Kinga ya ɗan ji dama saiya cinye kayar sa,amma yace irin ta rannan yake so wadda tayi masifar yajin nan"

"Ke Maryam yaushe yace Miki haka,bayan kince abokin shi yake faɗawa".

"To ai nima bance Ni ya faɗawa ba,ji nayi nima,dan haka tashi mu kamo kazar in tafi da ita bakin kasuwa a gyarota, sai in taho Miki da lokon daga can harda ma kayan miya.".

Haka ko akayi suka kwamuso kaza,sannan ta bawa Maryam kuɗin gyaran dana loko dana kayan miya🤣




*Alƙalamin khady* ✍
🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀

*'YAR CASKALE*
( _Sanadin bakin uwa_ )



*NA*

*KHADIJA USMAN*
( _Real Tame gari_ )



*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*



5⃣3⃣-5⃣4⃣


_________________________________

*ALHAMDILLAH! Wannan shafin dukansa sadaukarwa ne ga Admin of admin wato yaya Hayat,ina farin cikin tayaka murnar ƙara shekara, Allah yaƙaro shekaru masu albarka,arziƙi da dukkan nasaran rayuwa,kasancewa cikin amincin Allah da tabbatar dukkan alkhairinsa* _HAPPY BIRTHDAY TO YOU YAYA HAYAT,ADMIN OF ADMINS_ 🎂


_____***************_____


A taƙaice dai,saida Maryam ta taya Laraba duk abinda Yakamata,idan tayi wani abun sai Maryam tace baiyi ba ta gyara,haka dai ta biye mata har suka gama dafawa malam kaza mai yaji da romo.
Wanka kuti Laraba ta ɗauka,Maryam ta callara mata ɗaurin ɗan kwali,tace irinshi mamanta takeyi in tayi kwalliya,ta taɓa tambayar mamanta ya sunan ɗaurin,tace mata ɗaurin fati Muhammad.Haka dai tasa Laraba a kwana.

Babu yadda Maryam batayi ba akan Laraba ta bata naman nan takai wa malam,amma Laraba tace ah ah,ita zata kai masa da kanta.Hakan yasa Maryam nuna jin haushinta amma sai taga wannan karon Laraba ko'a jikinta,hakan yasa ta tashi ta koma gefe tana ta tunanin yadda zata ɓullowa Laraba taci naman nan,dan Laraba wannan karon kai tabawa Maryam ita kuma taci ƙafafun ta ajiyewa malam kaza sukutum.Da farko Maryam bata damu ba da Laraba ta bata kai,dan tasan ita zata cinye kusan rabin kazar ko duka ma,sai kuma gashi Laraba ta gwanya mata.
Haka taita saƙa wa lokacin Laraba ta shige ɗaki,dan haka ta ta tsaya jiran ta fito.Koda Laraba ta fito da hijabinta tana niyyar sawa nan Maryam ta tareta tana faɗin"ai karma ki wahalar da kanki Anty,yanzu malam ya aiko yace a faɗa miki gashi nan shigowa.Jin hakan yasa Laraba saurin ɗaukar langar ta ƙara gogewa ta faɗa ɗaki,tare da ɗauko turaren ta samfur ɗin wanda na faɗa muku a baya ta ƙara fesawa.Itako Maryam tashi tayi ta nufi ɗakin zauren na malam.sallama taitayi amma shuru ba'a amsa ba,kawai saita yanke shawarar leƙewa taga ko baya ciki ne.Tana yaye labulen ta hango malam lulluɓe da bargo yana hayaƙi,sallamar ta kumayi, nan ya yaye duk ya haɗa zufa da kyar ya amsa mata,"Baba malam meya same ka? Ko bakin naka kake gasawa ne da hayaƙi?"

A kaikaice yake kallonta a zuciyarsa yana faɗin"kaji min shegiyar yarinya,ko ma meye ai ke nake yiwa,dan idanma aljanar kanki ce ta dawo kaina to na mayar miki abarki, kuje can ku ƙarata da iyayenki,dan gobe goben nan kina gidanku i War haka,ko ubanki bai zo ba Ni zan kaiki"amma saiya saki murmushi yace,"Eh bakina nake gasawa ko na ɗan ji dama".

"To da zafi ne naga ka kwaɓe fuska zakayi kuka?"ta jefo masa tambaya.

"Yaushe zanyi kuka kuma Maryam?" Ya faɗa yana ƙara faɗaɗa murmushin sa".

"Gashi nan yanzu ma ka ƙara alamar kuka zakayi da yawa".Sai yanzu ya lura da abinda take nufi,wato murmushin dayakeyi shine kukan,nan da nan ya mayar da fuskar ya haɗe sannan yace" ke tashi ki bani guri dan gidanku,ba nace ma ki haɗa kayan ki ba,me kika tsaya yi kuma har yanzu.

Gyara tsagunnon tayi tace"dama Anty Laraba ce ta aikeni nayo mata cefane,nakuma kai kaza aka yanko tayi maka farfesu,shine yanzu ma tace inzo in kiraka,ince maka komai ya kammala"

Murmushin yakuma niyyar yi,tunawa da abinda Maryam zata kuma faɗi saiya haɗe kayansa yace"ina nan zuwa kinji jeki faɗa mata".

Aikuwa da sauri Maryam ta koma ta faɗawa Laraba cewar ga malam ɗin nan shigowa fa,bayan ta sanar da ita wai ta ɗora ruwan ɗumi taƙara gasa masa bakin.
Haka Laraba ta tashi da ɓarin jikin ta ɗora ruwan ɗumi,shikuwa malam bai samu shigowa ba dan yaga magariba tayi saida ya tsaya yayi sallar magariba da ishsha.

Itako Maryam koda tabar ɗakin laraba ɓangaren matan malam ta tafi,babu wadda ta kula ta,dan sun san 'yar ɗakin Laraba ce yanzu.Ganin nan ɗin babu wani farin jini,yasa ta koma ɗakinsu gurin 'yan uwanta,nan suka shiga hira har magariba suma kowa ya tashi yayi sallah.

Ko da malam ya shigo ya tarar da wannan Gara,ga ƙamshi nata tashi,saida ya lumshe ido,tare da haɗiyar miyagu,duk da bakinsa da ciwo,amma zaisa yanzu a ɗan ƙara gasa masa dan yaji daɗin cin abinda aka dafa masa,sai ma ya gama cin daɗinshi zaije yayiwa su salame rashin mutunci,danya lura yanzu sun raina shi wallahi.Cike da ladabi Laraba tayi masa sannu da zuwa,bayan ta idar da sallar ta,aikuwa ya amsa cike da jin daɗin siririyar Muryarta.Nan yasamu guri ya zauna a kan tabarmar da aka shimfida,babu ko jiran a gabatar masa da abinda ke kwanon yace" Ɗan taimakamin ki sake gasamin bakin nan kafin inci abin nan ko naji dama-dama".

Cike da ladabi ta amsa da "Toh yallaɓai"(cikin salon da mamanta ta koya mata,da sunan da yayarta tace ta dinga faɗa masa dan jan hankali🤣)miƙewa tayi ta fice,yayinda malam ya bita da kallo yana kallon yanda kayan masarufi ke motsi😜.

Haka dai harta dawo da ruwan ta ajiye ta ɗauko tsumma ta zauna gefensa,yayinda ta shiga ga sa masa a hankali tana masa sannu.Sai da ta gama ga sa masa sannan ta fito da lokon dake kan cinyar ta ta buɗe.Kallonta yayi yace"Amarya ba'a barin man nan kuwa sai nazo kwanciya a shafa,dan kinga abinci ai baya ciyuwa da maiƙo a baki ko".

Mayarwa tayi ta rufe tana murmushi,yayinda ta buɗe masa murfin kwanon da ƙamshin daddawa ya bugi hancinsa,nan ko ya jawo kwano tare da jawo dankwaleliyar tsoka yasa a baki.Tsananin azabar da yaji yasa shi haɗiye naman tun bai gama tunawa ba.nan ma naman ya tsaya masa a wuya yasashi wata kwarewar data sa Laraba miƙewa da sauri ta bashi ruwa.Har naman ya wuce bai daina jin raɗaɗin a bakinsa ba,dan haka ya fuzge kofin ruwan ya kafa kai yana sha.Duk hankalin Laraba ya tashi,dan tsawon lokaci yana zaune ya jingina da bango Ya saki baki miyau nata dalala,nuni ya shiga yiwa Laraba da hannu akan ta kawar da kwanon kazar,aikuwa taja ta rufe.nan tayi tagumi dan bata da meke damun malam ɗin ba.

Sun jima a haka, kafin malam yasamu raɗaɗin ya lafa,nan ya juya ya kalli Laraba cikin haɗe rai yace"Ke wannan wace irin dahuwa kikayimin,dake ƙoƙarin kasheni da raina kinji ɗan karen yajin dake ciki kuwa?".

"Dama Maryam ce....." Zuruf suka ganta ta faɗo ɗakin tace"salamu alaikum gani Anty,an ragemun ne?"

Baki buɗe Laraba ta kasa magana,shima malam haka,har Maryam ta fita da kwanon basu sani ba,saida malam yace"ke kika kira wannan tauraruwa me wutsiyar?"

"Ni ban kirata ba wallahi ,inaga dama tana kusa ne,jin na ambaci sunan ta shine ta ɗauka ko kiranta nayi".

Bai ce mata komai ba,sai zamewa da yayi ya kwanta,itama Laraba Batace komai ba,sai da suka ɗauki lokaci a haka kafin tace" yallaɓai katashi ka

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login