Showing 27001 words to 30000 words out of 39731 words
wani irin karfi Hurriya ta ture ta ta fadi kasa fuskarta na nuna zallar bacin rai tace wa ya baki damar taba ni tana binta da idanun masu nuna zallar bacin rai saidai tana kokarin saita kanta saboda batasan yanayi fuskarta ya canza saboda da wuya Hurriya ta canza yanayin fuskarta zuwa damuwa ko farin ciki ko firgice ko kuma gazawa ko gajiyawa da rayuwa fuskarta akoda yaushe a yanayi daya take wato ta daurewa wadda za’a iya kiranta bata da mutunci
Imad ne ya tashi yazo Daidai saitin Hurriya wadda take idonta har wani jaa yake kawowa
Shima imad din rannshi a matukar bace shida neela zuwa yayi zai dauke ta da mari Ammar yayi saurin rikeshi Imad please don’t touch her ba tarbiyya bane dukan mace.
Hurriya Dukansu kallonsu tayi ba tare da tace masu komai ba ta fita daga dakin Hamdan ne ya ruga zaibita Liya ta rikeshi
Amrah kam kuka takeyi sosai wanda yasanya duka hankalin su ya dawo kanta
Neela ta rungumota tana lallashinta Ammar shima lallashin yakeyi Imad tashi yayi ya shige daki zuciyarshi na tafarfasa sannan ya barsu a parlon
Hurriya har bata ganin gabanta da kyar take tafiya ga dare da yayi ga sanyi ga fargaba abubuwa duk sun hade mata
Da kyar ta kawo kanta dakinsu tsitt kakejin ko ina adakin wani irin shiru wurin ya dauka don da yawansu sunyi bacci .
Ahankali ta kwanta tare da lumshe idonta tana fadawa duniyar tunani tambayoyi take ma kanta ina wannan yaron ya iya yaren Amarich sannan yace suna kama da Princess Layla Al-Khasheem shin har yanzu kamarsu a bayyane take itada Layla
Zuciyar tace ta buga don tana tsoron kalubalen da zata iya fuskanta nan gaba idan har identity dinta ya fito fargaba tsoro kadaici duk sune suka suka cikata
Bacci ne ya fara fizgarta Mai cike da gajiya ahankali baccin ya fara nauyi saidai saukar Ruwa mai matukar sanyi ajikinta ne ya sanya ta farkawa da sauri kuma a firgice bata Ida warwarewa ba taji an kara zuba mata ruwan mai matukar sanyi ga yanayin sanyi irin na farkon January
Rungume jikinta tayi idanun ta da hakoranta na gab gab wani ruwan taji ankara zuba mata mai matukar sanyi numfashinta ne ya fara ja yana dawowa kirjinta yana wani irin duka gab gab kankame jikinta ta karayi numfashinta na rage sauri dariya suke a kunnenta suna ihu suna kashewa
Tafiya su barira sukayi suka barta tana kokarin saisaita numfashin ta saidai mi ba abinda take gani irin past dinta rayuwarta ta tabaya yadda kawunta yake zuba mata ruwan kankara yana dukanta ne ya dawo mata kanta ne ya farayi mata wani irin nauyi sai wani irin duhu da ta fara gani sannan numfashinta ya dauke.
Hello readers ya kuke tunanin salon labarin namu
Ya akayi Hamdan yayi wani yare wanda Hurriya kadai takejin yaren
Miye tsakanin Layla Al -Khasheem da Hurriya Faisait Hamood
Ga Amrah da Hamdan da suke tsanin son Hurriya mi yasa suke sonta?
Ga Barira da suke barazanar tsoma kansu a rayuwar Hurriya anya basu debo ruwan dafa kansu ba
Ga wasba yar yarinya Karama da Hurriya ke burgeta
Miye yake faruwa ne da kyauwawan masarautar Qamar wanda ya sanya ake kiran masarautar da mysterious palace
Wacece Hurriya?
Ku biyoni cikin labarin masarautar Qamar a hankali komai zai warware.
Waye star dinmu a maza?
Shaho,Kumurci,imad ko Ammar kuma Hamdan
Muje zuwa kawai don salon labarin namu ya bambamta da kowani irin labari.
[12/02, 4:53 PM] Khadyn Sp: 🌚Masarautar Qamar
A story about a mysterious palace
By Khadija (KMU)
23&24
Kwance take male male cikin ruwa mai matukar sanyi wanda kwata kwata bata ko numfashi ba wanda ya lura bare ya ankara
Da kyar suka lallashi amrah aka sanya kuyangu suka tafi da ita chamber dinta Mai matukar kyau da daukar ido
ruwan wanka Neela tazo ta hada mata ta fito mata da kayan bacci sannan tayi mata addu'a tare da kashe mata wuta
Liya kam tare suka tafi itada Hamdan don ba wanda yace ma dan uwanshi komai har suka isa chamber dinshi
Ammar shima chamber dinshi ya nufa ya haye saman gado tare da lumshe ido yana tunanin duka abinda ya faru yau so yake ya hada komai wuri daya don samun ma'anar abun saidai ya kasa hada komai
Amman yarinyar tayi matukar bata mashi rai donmi zata ture Amrah shiru yayi yana tunanin kilan tana da uziri don kowa da uzirinshi.
Karfe 5:44 Allah ya kawo Bintu domin tada Hurriya sallah asuba saidai ganinta kwance ya sanya ta fasa ihu agigice tazo tarinka tadata tana Hurriya Hurriya ki tashi don Allah ki tashi ki daina bani tsoro inna lillah wa'inna ilaihi raji'un Bintu ta shiga furtawa tana bude ma Hurriya ido Amman shiru
Ruwa ta debo da sauri ta yayyafa mata tare da shafa mata a fuskarta bude idonta Hurriya tayi wanda sukayi matukar jaa wani seizure numfashin ta ya fara tana tari mai sarkewa don kamar zata mutu haka numfashin yakeyi ga kuma tarin yaki sassauta mata Bintu banda hawaye babu abinda yake kwarara daga idonta don ta rasa mi zatayi wanda zai taimaka ma Hurriya saidai kukan
Kirjin Hurriya taga yana sama yana kasa numfashinta yazama abnormal don abinda take yafi nada bintu sakinta tayi ta ruga ta fita aguje ta rasa ma inda zataje watar yar matashiyar budurwa tagani tace mata don Allah akwai likita anan yar budurwa tace Akwai inna hanne mai bada taimakon gargajiya idan ansamu mararsa lafiya godiya kawai tayi mata batasan ya akayi ba sai ganin ta tayi a kitchen. ganin kanta a kitchen datayi ya sanya ta fashe da wani irin kuka inna hanne ce ta kalleta tace ke kuma lafiya kike mana sintiri kina kuka
Bintu zuwa tayi ta rike mata kafafunta tace ki taimaka mani ki ceci rayuwar Hurriya ta kusa mutuwa ki taimkeni yatsine fuska hanne tayi sannan tace wacece kuma haka Hurriya yar doguwa mai kyau tureta hanne tayi tace ni likita ce da zaki zo ki tsareni da magiya
Ki taimake ni don Allah ko nawane nayi maki alkawarin idan ta warke zan baki shiru hanne tayi tana tunani kafin ahankali tace muje.
Barira dasu wasila ne sukaje wurin da Hurriya take yashe kwance Hansa'u ce ta ture mata dogayen kafafunta ahankali Hurriya ta bude idonta wanda suke rufe hakoranta suna gab gab kirjinta na sama na kasa binsu take kawai da kallo dariya suwaiba tazo tayi tana take mata yatsun hannunta ita kuma barira ta take dayan hannun da nuna itadin watace tayi dariya tace yau zan kwanta da wannan kaskantaciyar baiwar sannan na sanya a farfasa mata jikinta sai inbi tada gishiri a ko ina kuma kullum kowa da kowa acikinku zai kwanta da ita sannan zansa bawa mafi muni da kaskanci ya kwanta da ita ta fasa wata dariya su Hansa'u suma sukayi dariya Hansa'u ce ta kalli barira sannan tace ina fatar a aske mani gashi kanta murmushi barira tayi sannan tace angama
Wasila ce ta fashe da dariya tazo ta haye Hurriya tare da kama hannun rigarta zata farka mata riga
Hurriya kam ta kanta takeyi don numfashinta kiris ya rage ya kara daukewa Amman tana cikin tsananin tsoro don tabbas idan har ta bude mata baya dolene taga zanen tatoo din dake da tambarin daga inda ta fito nobody is allowed to see the tatoo idan ba haka ba rayuwarta will be at more risk don tatoo din shine yake rike da sirrin ko ita wacece miye zai faru da ita idan wani yaga sirrin dake Zane abayanta
Shiru tayi zuciyarta da kirjinta na wani irin bugawa hannun rigar aka farke wanda hakan ya kasance daidai da daukewar numfashinta.
Bintu da inna hanne da suka shigo yanzu wanda yayi Daidai da daukewar numfashin Hurriya da kuma ida farkewar hannun rigarta
Wani irin kyakyawan mari inna hanne ta dauke wasila dashi tana binsu da wani irin matsiyacin kallo rike kuncinta wasila tayi ta fita daga wurin a hankali Hansa'u ta bita a baya sauran ma Dukansu suka bita a baya duk a masarautar nan ba wanda Suke tsoro irin inna hanne da reza dan daya hatsabibiyace daya kuma fitinaniya ga uban karfi
Bintu kam rungume Hurriya tayi tana kuka inna hanne ta kalleta tace ta fita ta debo masu ruwan zafi Bintu ta tafi don samo ruwan zafin
Taba Hurriya inna hanne tayi saidai abinda tagani saida ya girgiza ta daman har yanzu tanada aljanun da suka so bude mata ido kenan to mi ya kawosu miyasa suka karantar da ita bayanin Hurriya abinda rabon da tasan wani abu game da rayuwar wani andade
Inna hanne kallon Hurriya take tana tunanin abinda tagani tattare da rayuwar yarinyar lallai Hurriya tana cikin hadari acikin masarautar nan don irin duhun da tagani da kalubalen dake lullube da ita sunan Allah kawai inna hanne take fada don ta dade bata ga Abu irin haka ba
Don kwata kwata aljanun da suke son bude mata ido sun tafi tare da karfin ikon Addu'a da azkar don bata ganin komai tafi shekara goma rabonta da budewar idon jinnu sai wannan karon mi hakan yake nufi Akwai matsala babbar matsala tattare da rayuwar yarinyar nan
A hankali ta daga rigar Hurriya a firgice tace masarautar Heral Inna lillah wa'ina ilahi raji'un ta ambata tana kallon zanen tatoo din Hurriya dake kwance agadon kafadarta ta baya kenan itace yarinyar da kusan shekara biyar dasu ka wuce akazo ana nema don kusan ko wace babbar masarautar dake duniya anje don harda masarautar Qamar akazo tare da alkawarin duk wanda ya samota akwai gagarumar kyautar da za'ayi mashi don dashi da zuri'ar shi hatta tattaba kunnenshi sun gama talauci saboda irin zunzurutun abinda aka alkawarta sannan kuma idan nameji ne zai aureta tare da nadashi sarautar kasar baki daya
Shiru tayi tana hasko Labarin irin masarautar Heral da ake basu irin mulkin da akeyi da irin tarin arziki da daular dake shimfide a cikin kasar don masarautar na daya daga cikin jerin masarautar duniya da ake ji dasu
Shiru tayi tana tunanin duhun da tagani tattare da Hurriya wanda ba'a masarautar Qamar kadai ya kare ba hatta masarautar Heral din idan ta koma zata fuskanci kalubalen da kilan zai iya sanadin rayuwarta don ko masarautar Qamar din Qalubalene da zai iya sanadin rayuwarta ko kuma ya tarwatsa mata duk wani farin ciki na rayuwarta wanda yarinyar ga dukkan alama ta dade ba farin ciki rayuwarta
Inna hanne ta sauke ajiyar zuciya tana kallon kyakyawar fuskarta tana nazarin dalilin da aljanunta sukayi nuna mata bayanin Hurriya yarinyar abar tausayi ce saboda zagaye take da makiya Amman In Sha Allah zata taimaketa da addu'oi Sosai da azkar masu matukar muhimmanci saboda tasan tsafin da akeyi a masarautar Qamar
Bintu ce ta shigo aguje da ruwan zafi sannan ta ruga aiken da inna hanne tayi mata don amso mata magungunan hausa Bintu bata wani dauki lokaci ba sai gata da magungunan
Kallon Bintu baba hanne tayi tace ta dan fita Bintu batayi musu ba ta basu wuri
Maganin ta hada mata na lamoniya hade da sanyi sannan ta bude bakinta ahankali ta shiga bata don ko motsi batayi rabin maganin na shiga rabi na fita baba hanne kallonta take cike da tausayinta don itadai tunda ta taso rayuwarta A daji kuma babansu magani yake badawa itama har ta gaje shi to bata taba cin karo da makamanciyar lamoniya irin wannan ba
Bayan tagama bata magani ta samu farin tsumma mai kyau sannan ta shiga gasa Hurriya da ruwan zafin
Tana dora hannnunta ajikin Hurriya ta zabura
Haka ta rinkayi da ta taba mata jiki sai ta zabura saida ta taimaka mata sosai wurin ganin gasa jikinta da magungunan gargajiya
Wasba ce zaune à inda Hurriya tazauna jiya tayi wanki tana wasa da karamin icce wanda ke nuni da kamar Hurriya take jira
Kallon hanyar da ta biyo jiya tayi saidai bata ga ko mai kama da ita ba
Bata rai tayi tana turo baki ta tashi ta koma cikin gidansu
Hurriya shiru shiru bata tashi ba saaidai Bintu na zagaye da ita kamar wacce zata gudu don har tayo aikinta ta dawo
Inna hanne ta dade a wurin tana kula da ita kafin ta koma kitchen domin ayyukanta saida Inna hanne tagama ayyukanta sannan ta dawo inda Hurriya take kwance hannunta rike da kofin shayi cikin hikima ta shiga zuba ma Hurriya ruwan shayin duk da rabi ya shiga rabi ya fito haka abun yake
Bayan tagama bata shayin tayi tagumi tana tunanin ikon Allah tunda take bata taba tunanin ko a rayuwarta zata iya zuwa masarautar Heral ba saboda sai an ketare kasashe shin bama wannan ba itadin wacece ba kowa bace face ma'aikaciya a masarautar Qamar sai kuma Qaddara da ta hadata da long lost princess din Qasar
Saidai Tana Addu'a Allah yabata ikon taimokon yar marainiyar yarinyar nan Allah kada ya sanya san zuciya ya debeta ta tona mata asiri
Su kuma su barira zatayi maganinsu Lallai da ace sun san wacece ita da ko hanya daya basu isa su hada ba
Don duk yan masarautar Qamar tafi karfinsu hatta sarkin idan tagadama tace a sauke shi daga kan mulki to tabbas babu tantama za'a sauke shi don masarautar su tana mulkin masarautoci da yawa a afirca so masarautar Qamar na ciki
Ta dade tana tunanin sannan ta tashi ta fita tana fita saiga Bintu na shigowa dan sauke ajiyar zuciya tayi sannan tace ki kula da ita don Allah.
Abun kamar wasa Amman har yanzu Hurriya bata bude idonta ba har anyi wata daya da sati daya
Su barira suna sane da halin da Hurriya take ciki don har anfara yada jita jita su barira sunyi kisan kai saidai da yake su din suna da power sosai ba wanda ya tarbesu da maganar
Saukin Hurriya daya data samu Inna hanne tayi bake bake ganin taji sauki don lallabata take kamar kwai kowa yana mamakin dalilin don baba hanne bata da irin wannan kirkin da take nuna ma Hurriya don itama ba Ruwanta da kowa
Bintu kam ta zuge ta rame tass kallo daya zakayi mata kasan cewar tana cikin matsinaciyar damuwa .
Imad kam shima ya shiga damuwar rashin ganin mai aikin nan don Hamdan da amrah duk sun gigita su don yanzu a chamber shi suke kwana Neela kam batasan mi zatace ba a al-amarin don tun tana kushe su yanzu ita kanta burinta da fatanta a samo Hurriya
Imad yafi kowa damuwa don kowa kallo yake yasan inda take don yanzu haka suna tare da Ammar ne a balcony Ammar ya kalleshi yace twin Imad kallonshi yayi yana daga mashi kai dafashi Ammar yayi yace nifa na rasa gane mike faruwa wacece wannan yarinyar miye hadinta da Hamdan da Amrah mi yasa suke sonta har haka yaran da basu damu da kowa ba rayuwarsu Amman sun damu da ita fiye da yadda suka damu damu
Shiru Imad yayi yana nazarin maganar saidai baisan yadda zai hada komai ya bashi ma'ana ba don haka ba tare da karayin wani tunanin ba yace Allah yasa lafiya dai
Shiru Ammar yayi sannan yace ka tambayi ma'aikatan ko lafiya? Girgiza kai yayi yace mashi Aa
Shigowar Liya ne ya sanya Dukansu suka juya suna kallonta cikin jumpsuit din Rimowa wanda sukayi mata kyau sosai zuwa tayi gefen imad ta rike mashi hannu tace na samo labarin maid dinka ka kwantar da hankalin ka
Ammar ne ya zagayo ya rike ma Liya hannu yace lafiya miye ya faru shima rike mashi hannu tayi , murmushi tayi sannan ta gyara zama tace kwantar da hankalin ka tana cikin masarautar Qamar
A hankali ta zayyane masu duk abinda aka gaya mata ance bata lafiya har yanzu batasan inda kanta yake ba tundaga ranar da ta ture Amrah
Shiru sukayi suna kallon yadda takeyi masu bayani har takai karshe ba wanda yace kala Ammar ne yace wani irin ciwo take Liya tace bansaniba Imad baice komai ba ya tashi ya bar masu wurin ba wanda ya damu da tashin da yayi saboda susan halinshi na miskilanci
Hamdan kam ko da yagama jin bayanin da Neela da Liya suka gama mashi sai ya fara sauke ajiyar zuciya kallonshi suka rinkayi da mamaki don abinda basu taba gani bane
Amrah ce ta shigo jikinta sanye da wani crazy jeans sai yar top kunnenta sakale da AirPod Dukansu kallon yar autarsu da damuwa ta bayyana a fuskarta sukayi Hamdan ne ya tashi yaje saitin da take sannan ya zare AirPod din kallon shi tayi ta dage mashi gira guda daya alamun lafiya
Cikin muryar shi mai dadi yace I found her Amrah kallonshi take da alamar bata gane nufinshi ba murmushi yayi mata sannan yace the beautiful young lady bude hakoranta tayi tana kallon hakimi tace like seriously daga mata kai kawai yayi Amrah zuwa tayi ta rungume Hamdan tana mai tsananin murna
Inna Hanne zaune tayi tana kallon Hurriya wadda fuskarta tayi fayau gashin kanta da girarta kwance sai bakinta da yayi pink ta riga ta gama sawa a ranta idan har Hurriya ta cike wata biyu bata samu sauki ba to zataje kauyensu ta taho da yayanta domin ya dubata
Tausayin yarinyar takeji sosai don yarinya mai gata kamarta yaushe ne Zata jira wani maganin gargajiya saidai da yanzu tana asibiti kasar waje Maganar Bintu da taji ya sanya ta dawo daga dogon tunanin da ta shiga ta kalleta sannan tace kindai ci abinci ko? Daga mata kai tayi
Wasba kije innani na kira wani karamin yaro ya gaya mata dauke kanta tayi daga kallonshi hawaye na zuba a idonta yau tasan dukan tsiya zataci bare tun dazu innani take kiranta Amman taki zuwa ta tsaya tana duba hanya ko zataga inda Hurriya zata bullo
Tashi tayi tana kuka tana share majina har tazo dan karamin gidansu dake cikin masarautar Qamar
Aiko tana shigowa innani ta rufeta da duka tana zaginta shegiya daga gidan ubanwa kike yar iska matsiyaciya tsintarciyar mage kin raina mutane ko ta cigaba da dukanta ba tausayi bare tausayawa har saida taga tana Neman daina numfashi ta daina dukanta.
Hurriya a hankali ta fara motsa yatsunta kafin ta bude idanunta Bintu