Showing 18001 words to 21000 words out of 39731 words
mata suturar ta
Barira wadda take shugaba acikin su ta taso tazo wurin tana kallon yan matan uwale tayi ma alama da tazo uwale banda kyarma ba abinda takeyi nan ta fara ja da baya wata irin muguwar faduwa kasa tayi wadda suwaiba ta sanya kafa ta shureta ta fadi kasa tana dafe goshi kuka uwale takeyi mai taba zuciya tana dafe goshin ta Barira tsoki tayi dallah sakara taso kema ai dadi zakiji bamu kadai zamuj dadin ba kuma da kun saba zakuzo kuna nema dakanku kinzo kina ma mutane kuka
Wasila tayi wata shegiyar dariya sannan tazo ta take ma uwale hannu tace shegiya daga gani ma zaki yi jaraba ta kara halba ta tana tsirta mata miyau Barira tace ku shigo man da ita
Suwaiba da wasila suka kamata suka kaita har makwanci Barira don ita har wani labule gareta wanda baka iya kallon komai dake cikin wurin
Uwale sam taki bamaBarira hadin kai don cizo da tsunkuli ba wanda batayi mata da kyar Barira ta barka mata riga wani irin cizo uwale ta kaimata a cinya mai dan banza zafi aiko barira ta hankadeta uwale kam ta rugo a guje tana hawaye Barira sanya kayanta tayi ta fito itama tana bata fuska alamar taci wuya
Kallonta su Mardiya da suwaiba da wasila sukayi sukace lafiya kallon uwale da take sharbar kuka tayi tace gatanan ta kusa illata ni don haka kuyi maganinta
Dariya sukayi a tare ita kuma ta samu wuri ta zauna
Dukan uwale suka farayi wanda kamar daman abinda ya kawosu duniyar kenan don basu ji basu gani hada halbinta sukeyi cike da mugunta suna wata yar iskar dariya ita kuma uwale kuka takeyi mai ban tausayi da taba zuciya
Mutane na kallo Amman waye ya isa yace zaiyi magana don daurin gindi suka samu wurin manya ma’aikatan masarautar don sai suyi maka dukan tsiya kuma su kira mararsa imanin samarinsu suma su dasa
Su Karime kam kyarma kawai sukeyi suna kallon ikon Allah wasu kam acikin su ma kuka sukeyi
Hurriya baccin gajiya takeyi saida bata da nauyin bacci tun dazu takejin kuka da hayaniya saidai bata maida hankali ba ta koma baccin ta amman hayaniyar da kukan damunta sukeyi don duk sai juye juye takeyi cikin baccin tsoki tayi ta janye hijab din dake jikinta ta tashi takalminta kawai ta sanya ta fito ba inda ta tsaya sai wurin su wasila da su suwaiba wanda banda bugun uwale ba abinda sukeyi
Hannunta duka biyun a bayanta sai gashinta da yayi loosing tie saboda bata daureshi da kyau ba
Kamar hadin baki dukansu suka dago suna kallonta itama kallonsu takeyi wanda da alama idanunta basu gaji da bacci ba
Kallon uwale Hurriya tayi wadda take durkushe tana kuka wasila ce ta kara kai mata mari sannan ta dago tana kallon Hurriya tace ke kuma fa babu wanda tace ma kala
Hurriya Dukansu kallon yadda suke binta da kallo takeyi kamar wasu hungry lions
Barira ce ta taho tana karairaya sannan ta kalli Hurriya a izgilance tace wa kike nema tanabin long slender legs dinta wanda rigar ta ko cinya bata gama rufe mata ba ,her legs shine like a sparkling water don wani salki sukeyi na tsantsar kyau hutu da jin dadi da duk suka bayyyana
Cikin isa da kuma rainin wayau Hurriya tace Are you lesbians sai kuma tayi licking gefen bakinta taciji lebenta tace kuna neman mata ne ?kowa acikin zuciyar shi ba wanda baya muradin ta saboda basu taba ganin lafiyaryar mace mai kyau dinta ba don ko gimbiya subira albarka
Barira ce ta taho cike da iyayi da kaudi tace kina son ki tabbatar ne ?sannan ta daga kai tace ma Hurriya Eh muna neman mata sannan ta lashe bakinta tace bari kingani matsowa tayi inda Hurriya take tsaye wadda kyakyawar fuskarta take blank she looks fierce and scary don da Barira tayi gigin kallon idonta da ta shiga taitayinta
Hurriya kallon Barira takeyi wadda har tazo kusa da ita da alama kuma tabata take so tayi don har ta dora hannunta saman gashinta tana lumshe ido bude idonta tayi tar akan na Hurriya sai a lokacin taga yanayin fuskarta mai firgitawa sharewa tayi tana kokarin kai hannunta a cinyar Hurriya saidai saukar zazzafan tuwo da miyar da taji a fuskar tane ya sanya ta sakin ihun azaba don ta tabbata fuskarta ta kone wani irin kuka takeyi mai ban tausayi da taba zuciya
Kowa kallon Hurriya da ta konata da tuwo a fuskarta yakeyi babu alamun ko tsoro ko nadama a fuskar Hurriya don da alama inda akwai saura to kilan Sai ta watsa mata a ko ina na jikin Barira
Wasila ce ta taso da wani irin zafin nama da alama zata kaima Hurriya mari da sauri Hurriya ta kauce sannan ta kalleta ido cikin ido tace i dare you to slap me with your filthy hand licking lips dinta tayi sannan tace da ni Hurriya faisait Hamood na sanya an yaken yatsunki guda biyar
And duk randa kika kwatanta yin haka I promise this ta nuna mata alamun sai an yanke hannun sannan ta kallesu wanda banda kallonta ba abinda sukeyi don ko daga idonka zai tabbatar maka da duk abinda tace zatayi zata iya
Bintu hannunta rike da bakinta don mamakin yadda Hurriya ta kona Barira da tuwon da ta kawo mata yanzu saboda tasan duk yau bataci komai ba kuma ko a jikinta don yadda take acting kamar ba abinda tayi don ta san Hurriya zata iya yin fin haka indai maganar wani zai taba mata jikine
daman Bintu tunanin Hurriyar bataci abinci ba don haka tace bari ta kawo mata tuwon tare da fatan Allah ya sanya taci sai ga abinda ya faru da tuwon da Kuma Barira
Hurriya zuwa tayi ta kwanta ta mike kafafunta ta lumshe idanunta Bintu tarugo tazo tace Hurriya shiru Hurriya tayi Bintu ta kiranta yafi a kirga Amman shiru karshe ma saidai ganin bacci ya dauke tayi don alamar numfashin ta ya canza ya koma na mai bacci
🌚Masarautar Qamar
By Khadija (KMU)
Page 17&18
Karfe 6:10 goma Hurriya ta tashi
saboda ayyukan da take dasu yau murza idanunta tayi sannan tayi mika ba addu'a abakinta ba komai bata dauki komai ba don haka taje babban toilet dinsu ta kama ruwa sannan tazo tayi Alwala Tayi sallah wanka takeso tayi saboda tsamin jikin da takeji duk batajin dadi saboda Rashin cikakken wanka data sabayi don ta saba kafin tazo masarautar nan sai tayi wanka sau uku a rana kuma da ruwan zafi don batasan ruwan sanyi indai wurin wanka ne saboda ciwonta tsoki taja ba tare da ta cire hijab din sallahrba ta nufi babban kitchen
Aiki akeyi a kitchen din sosai shigowa tayi wata yar babbar mace ta gani a gaban tukunya ruwan sai tafasa yake Daidai saitin matar Hurriya ta tsaya saida tagama kallonta don kamar bazatayi magana ba cikin miskilanci tace ruwa zafi zaki bani
Dagowa inna hanne tayi don ganin isassar don batayi mata sallama ba sannan bata gaisheta ba sai ruwa zaki bani cikin tsiwa ta dago domin tsiyaya rashin mutunci saidai ganin kudin da Hurriya take mika mata datayi ya sanya tayi shiru ta fara washe baki tana toh toh miye zakiyi da ruwa yar albarka kamar don dole tace wanka amshe dari biyun inna hanne tayi tace samo bukiti in zuba maki kinji Hurriya juyawa tayi ba bata lokaci sai gata da bucket nan inna hanne ta fara zuba mata ruwan zafi masu yawan gaske har saida Hurriya tace ya isa sannan ta daina zuba ruwan
Toilet ta shiga tayi lafiyayyen wankan ta wanda tasan zataji dadin jikinta Sosai a hankali ta shafa bayanta inda zanen tatoo ke kwance a bayanta wurin saitin wuyanta lumshe idonta tayi ta cizi lebenta masu kyaun gaske sannan ta fito tana tafiya ne a hankali kuma duk da safiya ce sosai tanajin yadda ake nunata
Tana zuwa ta iske Bintu a zaune kamar bacci ma takeyi Don haka Hurriya ta shirya tsaff cikin uniform dinta wanda ta samu ta wanke jiya da kyar wadanda sukayi mata wani irin kyau na musamman fuskarta sai fidda annuri takeyi sanyi da takeji na safiya wanda yake shiga kanta ya sanya ta bude kayanta domin neman Hula Aiko ba tare data sha wahala ba sai gashi ta samu hula mai kyau ash colour hular irin ta sanyi ce duk a wurin asabe ta siye su
Bata fuska tayi don tana dadewa bata daura ma gashinta wani Abu ba don sai idan abun ya kadota sosai .shine take rufe gashinta don a shekara baifi ta rufe gashinta ba sau hudu akwai lokacin da har shekarar ta kare bata damu da rufe gashinta ba idan ba wurin sallah ba
Cikin kyankyami take rike da hular da sam bata wanke ta ba don duk kayan gwanjon duk hasken su sai ta sanya hannunta ta wanke su tas kafin ta sanya.
Warware gashinta tayi wanda ya zubo mata har bayanta sosai don ma akai akai take rage gashin kanta da batasan yadda zai rinka takura mata ba kuma data rage nan da nan yake fitowa har yafi wanda ta rage din tsawo da cika da yawa
Taba gashin tayi sannan ta dan shinshina ko yana wari kamshin coconut oil din da taji ya sanya ta dan saki ajiyar zuciya
Daure gashinta tayi Sosai yadda duk bala'inka baka iya hango tukar don ta linketa ta sanya ta cikin gashin yadda ba mai iya gane yawan gashin ko tsawonshi ko yawanshi
Bintu da ta bude idonta masu kyau ta kalli Hurriya tace kindawo daga mata kai Hurriya tayi tanabin ko ina na jikinta da kallo alamar rama kuma da yar damuwa tattare da ita
Ganin Hurriya nabin ta da kallon minene matsalar ki ya sanya ta washe baki yan hakoranta suka fito tace Hurriya jiya nazo in ganki na kawo maki abinci Amman Saita kasa ida maganar alamar kamar tana kuka ta hade kafafunta da gwiwarta Hurriya ta duko tace Bintu miye ya faru waye ya taba ki fadamin shi. Daga muryar ta zakaji alamar kulawa duk da yadda take kokarin boye emotions a cikin maganarta ,duk wani mai tsantsar fahimta zai iya fahimtar damuwa a maganar ta Amman a yadda take maganar kadai sai mutum yace bata damu ba
Hurriya kara matsowa tayi kusa da Bintu kamar tanajin tsoronta tana tambayar wai lafiyar ki kuwa ki fadamani manah itama maganar ta kubce mata da alamun shagwaba Wata irin kyakyawar runguma Bintu tayi mata sannan ta fashe da matsinacin kuka Hurriya dan ture ta tayi ta zame jikinta Bintu dagowa tayi ta kalleta da idanun ta da sukayi jajir ta kalli Hurriya da take bata fuska kamar kashi ya tabata kuka ta kara fashewa dashi Hurriya dafe kanta tayi tace ki daina kuka ki fadamin abinda ya faru shiru Bintu tayi kamar daman abinda ta jira ta fada mata kenan don haka tayi shiru kafin a hankali tace cikin muryarta mai rauni tace nayi kewar ummanah Hurriya inajin tsoro tana maganar hawaye na zubo mata shiru tayi sannan ta goge hawayenta tana kallon Hurriya data tsura mata ido tashi tayi zata mike Hurriya tace Bintu yadda ta fadi sunanta saida ya sanya tsigar jikin Bintu ta tashi don da wata irin kulawa ta fadi sunan Bintu kallonta takeyi da mamaki tace Hurriya tana zare ido dan murmushi Hurriya tayi kadan wanda duka dimples dinta saida suka lotsa sakin baki Bintu tayi tana kallonta don tunda take a duniya bata taba ganin wanda murmushi yayi ma kyau ba irin Hurriya itakanta har goosebumps saida taji itada take ma mace kenan inaga ta fito tana murmushi bama dariya ba murmushi kawai tabb akwai matsala don ta tabatta duk inda ta matsa mazane zasu rinka binta kamar sleeves Dogs inaga tayi dariya ita kanta Bintu tunda take bata taba ganin mace mai kyaun Hurriya babu ta inda Allah ya rageta a fuskarta ko jikinta
Gyaran murya Tayi ta kalli Hurriya da kamar tana cikin good mood a hankali Hurriya cikin muryar ta mai dadi da sanyi tace Mai kike tunani Bintu ke nake tunani yar dariya tayi wadda har saida hakoranta saida suka fito shiru Bintu tayi tana kallon ratsin gold din dake tsakankanin hakoranta wanda bata taba lura dasu ba sai yau tunda take da Hurriya idonta har wani sparkling sukeyi dimples dinta kam duk sun lotsa Bintu cewa tayi Hurriya daman kina dariya dan gyara fuskarta Hurriya tayi ta koma yadda take da sannan ta juya ba tare da tace komai ba Bintu kiran sunanta tayi Hurriya tsayawa tayi bata juya ba kuma batayi gaba ba Bintu matsowa tayi cikin rauni da sanyi tace Hurriya ki zama yar uwata wadda zan rinka fuskantar ta da matsala ako dayaushe don Allah kada ki Rabu dani ko ki juya min baya ni ko baza kiyi fira dani ba nizan yi maki fira .
Inajin kadaici sosai wanda kwata kwata banda kwanciyar hankali ke kadai nike gani inji dama dama a raina don ni kallon yar uwa nike maki cikin muryar ta mai dadi Hurriya tace Bintu kin zama kanwata daga yau Bintu bata fuska tayi ta bayan Hurriya tace na girme ki Hurriya shiru tayi batace komai ba ta fita don tasan kilan ta makara dage kafadarta tayi sannan tace who cares
Tana tafiya taji ana nunata saidai ta saba sosai safiya ce ga kuma sanyin da akeyi mai shiga kasusuwa Hurriya idan ka kalleta zakayi tunanin batajin sanyin don ba dankwali A kanta amman akwai hula a hannunta tafiya tayi Mai nisa kafin tazo bangaren daza tayi aiki Ma'aikata ne ta gani tun abakin kofar chamber sunata aikinsu a hankali ta shiga bangaren kallon parlon takeyi wanda komai na ciki ya burgeta tun daga ceiling din dakin har zuwa painting komai fari ne kallon chandeliers din dasuke jere a saman popn tayi wanda yake bada wani irin mahaukacin haske wanda yake neman tarwatse mata idanu kujerun parlon royals ne masu matukar tsada kuma very light saboda at first glance ba Lallai ka kirasu royal ba fa sai ka san furnitures Sosai zaka iya ganewa kallon dogayen labulen da aka jerasu tayi komai na parlon is rich and elegant carpet din wanda ya cinye katon parlon da kusan set of chairs guda hudu kuma dukan su luxury royal chairs ne
Sai dining table dake cin kujeru guda shidda saida ta gama kallon komai magana taji daga bayanta don haka tajuya yar budurwa wadda bazata wuce sa'arta ce tagani sai kallonta takeyi kamar zata cinye ta baiwar Allah Amman ke ba yar najeriya bace shiru Hurriya tayi fuskar ta a hade bata ko amsa mata ba gyara tsayuwarta tayi sannan tayi murmushi tace hala kece sabuwar ma'aikaciya to muje In kaiki wurin mama rabi nan ma Hurriya batace mata komai ba don ganin irin kaudinta ta katon kitchen suka bi wanda Hurriya ke biye da ita har suka zo inda mama RaBI take
Matar yar dattijuwa ce tsaye tana kallon sabbin ma'aikatan da aka kawo
Zubaida tace mama rabi ga sabuwar Mai aikin da aka kawo saitin kunnen mama rabi tazo tayi mata rada tace kinga kyaunta sai tayi dariya tace akwai kallo a masarautar nan Amman fa shegiyat akwai miskilanci kamar jikar Qamar wata dariyar tayi tace itada tazo masarautar Qamar ai komai ta ajiyeshi tana dariya mai cike da zallar munafunci da makirci kuma da mugunta
Duk abinda suke cewa Hurriya tana jinsu saidai basuyi tunanin don babu ko alamar hakan a fuskarta mama rabi tazo Daidai saitin Hurriya saida ta kare mata kallo sannan ta washe baki tace sannu yan mata Hurriya daga mata kai kawai tayi
Mama RaBI abun ya bata haushi Amman da yake yar duniya ce sai ta share ba bata lokaci ta fara lissafo mata dokikin Imad shiru tayi tana saurare har tagama Hurriya batace kala ba Amman ga dukkan alamu ta dauka
Mama RaBI ta kalleta tace ki gwada mata hanyar dakin zubaida tace muje ko tare suka koma itada zubaida har zuwa inda zai sada ka da dayan parlonshi kallon Hurriya zubaida tayi tace ki shiga idan kika wuce parlo na biyu zakiga dakinda yayi hanyar da tayi kasa Tohm sai ki shiga kasa din da kin wuce parlon to dakin dake kallon ki sai daki na hagu da na dama daga mata kai kawai Hurriya tayi sannan ta bude kofa ta shiga parlon wanda yake dauke da set of turkey chairs parlon ya hadu don har batasan wanda yafi kyau tsakanin na farko dana biyu ba
Bata tsaya kallon parlon ba don ganin lokacinta ya tafi don ayyuka ne gareta da yawa don haka ta hau steps din da zasu kaita dakin kasa wanda kamar underground
Parlon da tagani akasa saida kam ta tsaya ta gama kallo da yabonshi saboda komai da aka sanya a parlon zata iya cewa abinda ta fiso kenan kamar ita aka tambaya mi takeso ta fadi aka bi zabinta
Cikin tafiyar ta mai kama da catwalk ta shiga dakin kallon dakin tayi wanda yake da matukar burgewa ba bata lokaci ta shiga gyarawa da sauri take komai bayan tagama ne ta shiga toilet din ta wanke komai tass
Sannan ta fito ta kara shiga dayan dakin shima ta gyara komai da sauri takeyinshi kuma cikin rashin ha’inci don ko ina tayi mashi kalkal
Sannan ta shiga dakin karshe tana bude kofar ta lumshe idonta ta dan tsotsi bakinta bude idonta tayi tana kallon ko ina banda kamshin turaren wuta ba abinda mini falon yakeyi
Shiga tayi ta fara kakabe komai ba wani bata lokaci tagama sannan tayi mopping ta goge ko ina tass
A hankali ta nufi kofar dakin da take kallonta ta bude kallon Komi take na dakin wanda yake fari subahanallah dakin ya hadu kowaye yake da dakin ta jinjina ma fashion sense dinshi Komi is extremely expensive and superb a dakin tun daga wall decors din dake a bango dakin hadaddun paintings ne da canvas masu matukar kyau da tsada wanda ko wani zane is worthing millions ba wani tarkace Sosai a dakin wanda alama ta nuna mata mai dakin bai