Showing 30001 words to 33000 words out of 89323 words

Chapter 11 - MACIJINE SHI COMPLETE

Start ads

10 Aug 2025

487

Middle Ads

tayi cikin kuka tace " dan Allah HAMMA karka zauna cikin wannan yanayin,bazan iya rayuwa Ni kadai cikin wannan gidan mai aljanu ba, dazuma saida Hulwarka tazo ta tsoratani, gaba daya ta sanja duniyar wannan dakin ,ya koma wata kala,kalli kagani yanzu yadda ya koma,Hamma inajin tsoro"fattu ta faɗa tare da ɗora hannunta akan macijin tana shafawa.
Dagowa macijin yayi tare da zuba mata idanu,itama kallonsa take hawaye na zubowa daga idanunta. Jikinta ya fara zagayewa yana yana nannaɗeta,kafin kuma yayi baya da ita akan gadon,kwanciya fattu tayi tare da runtse idanunta .
Ita kam tariga ta gama sallama wa rayuwa, tasan idan har macijinta bai dawo mutum ba to mutuwa zatayi, ahalin da ake ciki yanzu tana jinsa ne har cikin ranta,kome takeyi shi take gani,ba abinda take bukata akullum kamar tajita kusa dashi,ta san duk ransa wani ya ganshi matsayin maciji ,to za'ayi ƙoƙarin kashe mata shine,wanda tayi imanin duk randa aka kashe Hamma, to tabbas da gawarsa za'a binnesu.

Shikuwa maciji bayan ya kwantar da fattu saiya zare jikinsa daga nannaɗetan da yayi,sannan ya kamo bargon dake kan gadon ya lullaba ajikin fattu,duk abinda yake kallonsa fattu keyi cike da tausayawa,ace mutum yana komawa wata da bar daban?kuma mai haɗari wacce kowa ke gudunta.saukowa yayi daga kan gadon tare da tsayawa daga can gefenta yana kallonta, itama kallonsa take ,kusan minti uku suna kallon juna,yayin da fattu ke zubda hawaye,juyawa yayi tare da nufar ƙofar dakin.
"Dan Allah Hamma ka dawo mutum,kada ka tafi ka barni,ina don kasancewa tare da kai,bani da kowa awannan sabuwar duniyar saikai"abinda fattu ta faɗa kenan lokacin da taga yana ƙoƙarin ficewa daga ɗakin.

Aikuwa tsayawa yayi kamar wanda yake sauraron me take faɗi .saida ta kai aya azancenta,kafin ya kalleta da idanunsa masu naunuka daban daban,sannan ya fice daga ɗakin.

Kuka sosai fattu ta fashe dashi,tana daga kwancen nan,shikenan komai yazo mata ƙarshe,idan Hamma ya tafi ya barta,ita ahalin yanzu ma, ta fara tunanin kodai duniyar aljanu ya kawo ta?
Haka tayi ta kukanta tana daga kwance har barcine wahala yayi gaba da ita.

Shikuwa Adeeb yana fita kai tsaye dakin daya baro ya nufa ,ahankali yake jan jikinsa , harya kai kan gadon ,hawa yayi tare da kwantawa lamo kamar baya nunfashi,rufe idanunsa yayi yana nishi da gyar, kafin kuma jikinsa ya kama girgiza sosai yana hayaƙi, sosai dakin ya turnuƙe da hayaƙi kafin ya washe.

Ikon Allah Adeeb na hanga kwance akan gadon nan,ya duƙunƙune jikinsa,sai rawa yake kamar mai jin sanyi,ahankali ya ɗaya hannunsa dake ta faman rawa ya dage kansa,yana mai yamutse fuska ,da alama kan ke masa ciwo,kusan minti goma ya ɗauka cikin wanan halin kafin naga ya miƙe jiki ba kwari,ya nufi toilet ,wanka yayi tare da sake kaya,ya fito cikin fara tass ɗin jallabiyya.
Zama yayi akan wata kujera dake gaban gadon,kujerar tsabar kyanta ,kai kace da zallar kwal akayita.sai ƙamshi yake bugawa, kallon ɗakin yake yana mai mamakin shidai yasan ya fita zuwa kitchen kuma har yayi girki,bayan nan kuma ya nufi dakin Hulwa, kuma...

Da sauri ya mike yana mai zafi ido,tabbas asume ya ganta aɗakin ,amma kuma me yasa shi yaganshi ana ?me ya dawo dashi ɗakinsa.
Da sauri ya nufi ƙofa yana ficewa daga dakin,saidai yana fita kafin ya kai dakin nata,yaji sanarwar zuwan tareeƙ,kallon kofar Tata yayi sannan ya nufi bakin ƙofar shigowa falon, yana ɓudewa ya ga tareeƙ da kaya riƙi-riƙi ahannunsa.
Kallonsa tareeƙ yayi yace "yallaɓai lafiya kuwa?
Ahankali Adeeb ya lumshe idanunsa kafin ya jinjinawa tareek din kai,alamu lafiya ba komai.

Shigowa tareeƙ yayi da kayan ya ajiye yana mai cewa"yallaɓai idan an duba sai afadamin abinda babu aciki." Nan ma dai kai kawai Adeeb ya daga sannan ya kalli kayan ,ledojine kusan guda goma manya-manya.
Kallon Tareeƙ yayi na dan wani lokaci kafin yace "an shirya komai na zuwan gurin mai Abie"?
" Eh yallaɓai komai ya kammala ,lokaci kawai muke jira" cewar tareeƙ kenan cikin girmamawa .
Jinjina kai Adeeb yayi kafin yace " U can go"

"Ok yallabai"
Tareeƙ ya faɗa yana mai barin falon .
Kayan da tareeƙ ya ajiye Adeeb yayi da kallo kafin ya ɗauki leda ɗaya yana ɗan leƙawa, idanunsa ne suka sauka kan inner wear masu bala'in kyau da tsada,da sauri ya rufe ledar yana ɗan kallon ƙofa, dan sosa kansa yayi kafin ya dauko bra guda ɗaya da hannunsa yana mai kallonta,shiru yayi yana tunanin lallai zatayiwa fattu daidai,dan ahalin yanzu yana kallon abubuwan ta daya taɓa gani a toilet,murmushin yay tare da dan sosa kansa kafin ya ɗauki ledojin duka ahannunsa yayi dakin fattun.

Yana tura ƙofar kuwa ya jiyo ƙinkishin kukanta,tana zaune a tsakiyar gadon ta haɗa kai da gwuiwa tana kuka.dan bata wani jima tana barcin ba ta farka kuma ita tsoro takeji taje ta taɓa kofar wannan hulwar ta kuma tsoratata.

Da sauri ya ƙarasa cikin dakin yana kallonta,tsayawa yayi akanta bayan ya ajiye ledojin dake hannunsa,sosai yake jin tausayin fattu cikin zuciyarsa,sam baya kyaunar ganinta cikin damuwa,yanzu zaiji zuciyarsa tayi masa zafi sosai.

"Hulwa " Adeeb ya furta cikin muryarsa mai sanyi da nutsuwa.
Da sauri fattu ta ɗago kanta ,sakamakon jin Muryar Adeeb da tayi,
Ai bata san lokacin data diro daga kan gadon nan ba ta wani ƙanƙame Adeeb da iya ƙarfinta tana kuka,
"Hammana dama nasan bazaka gudu ka barni ba, Hamma na shiga damuwa sosai lokacin danaga ka koma macijin nan,nayi tunanin guduwa zakayi ka barni Hammana dan Allah karka rabu dani"fattu ta faɗa cikin matsanancin kuka,wanda zamu iya cewa na farin cikine.

ahankali Adeeb ya lumshe idanunsa,tare da sakin ajiyar zuciya"har abada bazan taba rabuwa dake ba,ina tare dake komai rintsi komai wuya hulwatee" abinda Adeeb ya faɗa kenan , cikin zuciyarsa,amma azahiri kawai rungume fattu yayi shima ,yana mai shafa bayanta ahankali.
Kuka sosai fattu keyi tana kara rungume Adeeb,bazata iya faɗin irin farin cikin da take cikiba,
" Ya isa haka kukan " Adeeb ya faɗa yana mai ɗago kanta.komar da kan nata tayi tare da kara kwanciya akan faffaɗan ƙirjinsa.

Murmushi kawai Adeeb ya tsinci kansa dayi,yana mai shafa bayan fattu,sosai yake jin wani nishadi idan fattu ta ruƙunkume shi nan ,ji yake kamar su tabbata ahaka.
Bangaren Fattuna dai hakan ne ,ji tayi bata don rabuwa da jikin Adeeb ɗin,dan ba ƙaramin nutsuwa take samu akan wannan ƙirjin nashiba.
Kusan minti goma suna rungume da juna ,kafin Adeeb yayi karfin halin cire ta daga jikinsa yana mai cewa" waike bazai sakeni ba saikin karyani?kin fiye son jiki fa" ya faɗa yana ɗan harararta .

Kai ta duniyar ƙasa kafin tace "Hamma yunwa nakeji" kallon inda ya ajiye abincin dazu yayi kafin ya janyo table ɗin zuwa gaban gadon,
" Zauna "yace mata.
Zama tayi abakin gadon tana kallonsa,farin ciki fal cikin ranta.

Tea ya haɗa mata sannan ya mika mata flate ɗin kwan da bread zuwa gabanta.wani bowl ya mika mata ta wanke hannunta,kafin ta fara cin abincin,lallai fattu na jin yunwa ,dan kuwa tass ta kawar da abincin nan,shidai kallonta kawai yake,azuciyarsa yace "wannan badai ciba" tana gamawa tayi hamdala tana mai lashe lips ɗinta,ɗago kai tayi suka haɗa ido da Adeeb ,saikuma kunya ta kamata,ganin yadda ta kawar da uban abincin nan.
Shikuwa Adeeb cewa yayi " kin koshi ko zaki ƙara dan naga kedin akwai ci kamar Gara"
Dan shagwabe fuska tayi kafin tace "Allah Hamma abincinne ke wuce silik -silik,ba dan ma na cinyeba.ta faɗa tana kallon farantin.

Ƙureta kawai yayi da ido yana kallonta baice komaiba,dagowa tayi suka haɗa ido ,harararta yayi yace "zaki fara kallonsa ko" girgiza kai tayi tare da maida kanta ƙasa."zanyi sallah Hamma"ta faɗa kanta a ƙasa.

Nuna mata toilet yayi da hannunsa ,ba tare da yace komai ba.

Mikewa tayi yake bakin ƙofar ta tsaya tare da juyowa.
Yana kallonta baice komai ba,dan yasan me take nufi,ita komai bata iyaba
Saida yayi jimmm!kafin ya mike ya ƙarasa jinkin ƙofar, ya murda handle ɗin yace "kin gani haka ake yi"jinjina kai tayi tare da mamakin wai ƙifama sai anwani murɗata kamar kan fanfo"
Maida ƙurar yayi ya kulle sanan yace "buɗe"kallonsa tayi kafin ta kalli ƙofar, hannunta ta sanya tayi kamar yadda yayi aikuwa saiga ƙofa ta bude.wata dariya ce ta kwacewa fattu ganin tayi nasarar buɗe kofar tace " hahhahhh laaaah Hamma dan Allah kaga abin sauƙi wllh kuma budewa daɗi"ta faɗa tana kara sanya dariya cikin farin ciki.
Shikansa Adeeb dariyar tayi har saida fararen haƙoransa suka bayyana.jijjiga kai yayi kafin ya wuce ciki yana faɗin"Allah ya shiryeki"

Komai saida ya nuna mata ,sanan yasa ta kunna da kanta,aikuwa fattu gaba ɗaya yau ta zama kamar wata shasha ,data kunna abu yayi zata kama dariya,wataran harda ɗan tsallenta takeyi.
Shidai fitowa yayi ya barta dan tayi wanka da alwala.

Bude kayan da tareeƙ ya kawo yayi ,wata doguwar pink ɗin riga ya dauko da mahaifinta ya ajiye mata,sannan ya dauko wani fant da bra ya ajiye akan gadon,sannan fice.

Bayan fattu tayi sallah ne taga kaya akan gado,ɗauka tayi tana kallon kayan,sunyi mata kyau a ido sosai ,amma saita ajiye da sauri tace "ƙilama na hulwar tasane ,Ni wllh na tsani wannan hulwar" ta faɗa tana hararar kayan.
Adeeb me ya shigo cikin dakin da sallama can ƙasan maƙoshinsa.
Tsayawa yayi yana kallon fattu ganin bata sake kayan daya ajiye mata ba.

" Baki Ga kaya bane kika maida wannan. Dan ƙazanta" Adeeb ya faɗa tana hararar fattu.

"Kayi hakuri Hamma nayi tunanin a hulwar taka ne ai" fattu ta faɗa tana daga kayan,
"Hamma wannan fa " ta faɗa tana daga bra ɗin nan.

" Baki san me ake yi da itaba maza ki shirya ina jiranki" ya faɗa harararta tare da ficewa daga ɗakin.

Fattu kuwa data rasa ya zatayi da bra ɗin na sai kawai ta sanya kayanta haka tayi waje .
Tana fitowa Adeeb ya biya da kallo ganin bata sanya bra dinba ,yace ........


Mu hade next page banda cajine.


Mrs babi ce💘💘💘
[8/23, 9:06 PM] +234 813 465 3007: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄



MACIJI NE🪱🪱🪱


Na mammy kabeer
(Anty mammy)




Elegant online writers📚📚



Free book

Page 33/34






________________Fattu kuwa data rasa inda zata maƙala wannan abun ,sai kawai ta sanya kayanta haka ta yi waje gurin Adeeb, kafin ta fita daga ƙofar saida ta buɗe ta rufe kusan sau biyar,idan buɗe saitayi dariya ta ƙara rifewa, sannan ta buɗe,murna take sosai itama yanzu ta iya buɗe kofar yan wata duniyat.

Tana fitowa kuwa Adeeb ya bita da kallo, so yake yaga ko tasaka wannan abun,saidai kamar yadda ya tsammata ,bata saka ɗin ba kuwa,dan haka kallonta yayi tare da dalla mata harara yace " kingama shiryawa kenan?" Kai fattu ta daga masa tana gyara lullubin da tayiwa matakin kamar wata amarya,ta rufe kusan rabin fuskarta ,sannan ta kama wuyan ta rike ƙam da hannunta.

Shiru yayi yana ɗan wani tunani,shi baisan ta yaya zai faɗa mata cewar tasaka bra ɗin ba,dan haka sai yace" ina wannan abun da kika tambayeni na menene?"ya faɗa yana kallonta.
Itama kallonsa tayi kafin tace " na barshi agurin ne ,dan bansan a ina ake sakawa ba" ta faɗa tana ƙara riƙe wuyanta, dan kar mayafin ya faɗi.

Kallonta yayi har zaiyo magana sai kuma ya fasa ,wayoyin da tareeƙ ya taho masa da su ya ɗauki daya daga ciki , ya daga tare da kiran tareeƙ .
Yana dagawa yace "ka tahomin da make up artist yanzu ta shirya yarinyar nan"

"Ok sir " tareeƙ ya faɗa yana mai kiran wata number.
"Koma daki" Adeeb ya faɗa yana mai mikewa shima ya bar gurin.juyawa tayi ta koma tana mai tunanin kodai tayi masa wani abunne ? Taji yace ta koma ɗauki?zama tayi bakin gado tana mai cire mayafin nan ,dama duk ya isheta.gashin kanta ta shafa,tun wannan daurin dake kanta ,shine har yanzu,kuma kan nata ƙaiƙayi yake mata amma Indai ta zata ƙaramin wanka saita nemi omo ta wanke kan dashi .

Ba komawa saiga tarin ya shigo gidan,waya ya kira Adeeb yake sanar dashi sun karaso.
Cewa Adeeb yayi ya nuna mata ɗakin farko shikuma yashigo ɗakin hutu.
Kasancewar ba inda tareeƙ bai sani ba acikin gidan,dan haka ya nunawa matar wacce take balarabiya ce dakin yace tayiwa yarinyar ciki duk abinda ya dace .
Shikuma ya shiga dakin da Adeeb ke ciki.
Da sallama ya shiga dakin,Adeeb na kwance akan gado, ba barci yake ba ,amma idanunsa alumshe suke .zama tareeƙ yayi yana mai cewa" yallaɓai fatan dai kana cikin ƙoshin lafiya"

Ahankali Adeeb ya yunƙura ya tashi zaune,kallon tareeƙ yayi kafin ya sauke ajiyar zuciya yace " tareeƙ ina tunanin abinda nayi ne ,kada yarinyar nan taga kamar na cutar da itane"Adeeb ya faɗa yana kallon tareeƙ da yanayin damuwa akan fuskarsa.

"Ko kaɗan yallaɓai,idan har tayi tunani zata gane baka cutar da itaba, kuma Allah yaga niyyarka, kayi hakan ne dan kare martabarta da kiyaye hakkin Allah, amma yallaɓai mai zai hana kasanar da ita abinda ke faruwa ,dan gudun samun matsala nan gaba"tareeƙ ya faɗa yana mai kallon ogan nashi .

Shiru Adeeb yayi na kusan minti biyu kafin yace" no tareeƙ ,she's too young ace munyi wannan maganar da ita,is better mubar maganar atsaninmu har zuwa lokacin da Allah zai bayyana iyayenta,inyaso saina basu ita ahannunsa,sannan kaga tayi free .

"Shikenan yallaɓai amma yanzu kana ganin ,zaka kaita can gidane,ko kuma zata zauna anan?"tareeƙ ya faɗa yana kallon Adeeb da jiran jin me zaice.

Kusan minti biyu Adeeb ya ɗauka kafin yace" ko zamanta anan tare dani akwai matsala tareeƙ bana so wataran zuciya ta Kani ga aikata wani abun da zai zamo na cutar da ita,zan kaita can gida gurin ammi ne tunda nima mafi zama can din" ya faɗa yana mai lumshe idanunsa.

" Hakan yayi yallaɓai, Allah ya baka nasara akan kudirinka na alkairi" tareeƙ ya faɗa cike da ƙaunar ogannasa.

"Ameen "Adeeb ya amsa ahankali tare da kwanciya.

Ita kuwa wannan matar mai make up,kasancewar tareeƙ yayi mata bayanin komai tun kafin su zo gidan,dan haka da sallama tashi ga cikin dakin,juyowa fattu tayi da sauri tana kallon matar.

Murmushi matar tayi tare da kama hannun fattu ta miƙar da ita tsaye tana murmushi,
Kallonta kawai fattu keyi cikin tsoro da rashin sanin ko itaɗin wacece?
Cikin harshen larabci matar ke cewa" kai masha Allah yarinya mai kyau da daukar hankali,gaskiya kina da sihirtaccen kyau,ƴata, zanyi Mali kwalliya mai kyau kamar ke" ta kai karshen magannarta tana murmushi. ita dai fattu kallon matar take tana tunanin wannan ɗin kuma daga ina ?wacece?kodai itace hulwar?

Ahankali matar ta kama fattu ta zaunar da ita bakin gadon,gashin fattu ta fara warwarewa, " kai masha Allah,kina da gashi mai tsananin kyau,samun irin gashinki ba kowacce mace ba,larabawan ma" matar ta faɗa cikin harshen labarci,

Ita dai fattu tayi gurum cike da tsoron matar,gashi kuma ta kasa koda yunƙurin gudawa ne bare ta tsere.haka matar ta kama fattu sukaje toilet ta wanke mata kanta tass,sanann suka fito.

Gaban madubi ta kai fattu tare da ɗauki handryer ta busar da kan na fattu,mayuka kala-kala ta shafawa fattu akanta,kan kame tuni kan fattu ya ɗauki wani sheki da ƙamshi, ita kanta fattu wani sawai takejin kan nata.
Gyara mata kan tayi sosai sannan ta ɗaure mata shi da wani ƙaton ribom mai kyau.
Kwalliya tayiwa fattu cikin nutsuwa ba mai yawa ba,daga powder sai lips da kwalli ta sawa fattu a idonta,irin sakun nan da larabawa keyi,kusan rabin ido.
Kai fattu fa tayi mugun kyau fuskar nan Tata kamar farin wata dan haske,kwalliyar ta karbi fuskarta sosai,kodan ba tabayin kwalliyar tayi ba oho?
Ledojin nan mata ta buɗe tare da ɗauko wata bakar doguwar riga,dama kuma kayan duk dogayen riguna ne masu kyau da sutura jiki.
Har zata dauko su bra,sai taga wata akan gadon ,dan haka sai bata daukoba.

Wani ƙaton towel ta ɗauko ,dake gefen kofar bandakin asaƙale ,mikawa fattu tayi tare da cewa ta cire kayan jikinta ,saita sanya bra ɗin sannan tasa kayan nan.cikin harshen larabci matar ke magana.dan bata san cewa fattu bata jin larabci ba,dan kuwa ita tayi tunanin fattun ƴar Misran ce itama.

Kallon fattu tayi gurum! Kamar kurma,dan bata san me matar ke faɗi ba.ganin fattu bata karɓi towel ɗin ba tana zaune kawai yasa matar tunanin kodai kurmace?
Kwatance ta farayiwa fattu da hannu,cikin ikon Allah kuwa fattu ta gane wai rigar zata cire ta ɗaura towel din .karɓa fattu tayi tare da daura towel din asaman ƙirjinta.murmushi matar tayi tare da ɗaukar bra ɗin ta mikawa fattu.kallon brar fattu tayi tare da kallon matar" tab Ni nasan me zanyi da wannan abun da kina wani mikomin" fattu ta faɗa cikin ranta tana mai turo baki tare da kauda kanta.

Murmushin matar tayi tana mai rayawa aranta ,kodai fattun kunyar saka bra ɗin take?dan ga dukkan alamu wannan ne karonta na farko asaka bra ɗin.

Cikin hikima da dabara matar ta sakawa fattu bra bayan sun sha artabu,dan fattu sam ƙin yarda tayi da farko, aganinta wannan hulwar so take ta gane mata abubuwa,amma cikin hikima matar tayiwa fattu munin ba ganin jikinta zatayi ba tana son rufe mata jikinta ne,sannan ta dagawa fattu rigar jikinta tare da nuna mata itama ta saka irinta.sai lokacin fattu ta fahimci inda ake saka bra ɗin.ikon Allah wato suma waɗannan abubuwan harda jakar da ake boyewa?lallai zakaga abu da yawa idan baka mutuba.

Aikuwa tsif bra din tayiwa fattu ajikinta,Dan dama koda tareeƙ yaje karbowa cewa yayi budurwa yar kimanin 16 za'a haɗawa kayan,
Saidai fanties ɗin duk sun mata kaɗan sosai,da gyar matar ta samo mata wani mai kama da gajeren wando sannan tasaka.

Da kanta ta sanya rigar ajikinta,masha Allah masu karatu duk wanda yaga fattu awannan lokacin zaiyi tunani wata fattun aka sake,dan tayi kyau har ta gaji da yin kyan.
Tauraruwa matar ta fadawa fattu ajikinta masu daɗin ƙamshi,sannan tayi mata rolling ta ɓame da wani kyakykyawan abinda ake riƙe mayafi dashi dan gudun zamewa.

Sosai matar ke yaba kyan da Fattun tayi , ga sarƙarta sai walwala take,matar sai kallon sakar take cike da jinjina irin kuɗin da aka batar wajen siyanta,kafin ta kama hannun fattun ta juya da ita gaban madubi.saida gaban fattu ya faɗilokacin datayi arba da kyakyakywar fuskarta jikin madubi,hannu tasa tare da shafa fuskartata,dan tabbatarwa itaɗince kuwa.
Ƙuri!! Fattu ta kure kanta da kallo ta jikin madubi,wai dama haka take ko kuma dai ba ita bace wannan ɗin?anya matar nan ba sake mata fuska tayi ba ?dan dan ita bataga tsohuwar fuskarta ta da ajikin madubin ba.
Murmushin tayi lokacin data ɗan mintsini hannunta kadan,kuma taji zafi.
Wllh nice ,nice fattun baffa, gaba

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login