Showing 6001 words to 9000 words out of 89323 words

Chapter 3 - MACIJINE SHI COMPLETE

Start ads

10 Aug 2025

485

Middle Ads

saida numfashinsa ya ɗauke .

Haroji kuwa ya mugun tsorata ganin halin da jauro ke ciki,ga wannan ƙaton macijin daya kanannadeshi yana ƙoƙarin karya masa ƙasusuwa.

Cikin kiɗima ya rarumo wani ƙaton dutse yayi kan jauro da wannan macijin,yana zuwa baiyi wata wata ba ya ɗaga dutsen ya kwaɗawa macijin nan abayansa.
Aikuwa nan da nan bayan macijin ya fashe jini yayi tsartuwa har kan fuskar haroji,wani ihu haroji ya kwala ,sakamakon sauƙar jinin macijin nan akan fuskarsa ji yayi kamar an watsa masa ruwan batir,nan da nan gurin ya sale kamar wanda ya ƙone sai turiri gurin yake.
Jifa haroji yayi da dutsen hannunsa yana ihu yana faɗin"wayyo Allah idona bana gani wayyo kwayar idona ta zazzage na shiga ukuna "abinda yake daɗi kenan yana ihu da tsalle.
Shikuwa macijin nan silalewa yayi daga jikin jauro ya koma gefe guda tare da kwantar da kansa akasa ,dan kuwa sosai haroji ya kwada masa dutsen nan,kuma da alama ya shige shi .

Gaba ɗayan abinda ke faruwa akan idanun fattu ,tana kwance tana kallon ikon Allah,tabbas zuwa yanzu ta gama yarda cewa macijin nan bashi da biyar cutar da ita ,saima taimakon ta da yake,shin wanene wanan macijin?meye alaƙarta da shi?me yake nema agurinta?anya ma MACIJINE wannan ?kodai aljanine yake zuwa mata asiffar macijin? Wadanna sune tarin tambayoyin da fattu ke yiwa kanta tana daga kwancen wanda bata da amsarsu.

Saidai kuma gaba ɗaya hankalinta ya tashi ganin yadda macijin nan ya kwanta lamo kamar ya mutu.nan da nan tsoro ya mamaye zuciyarta ,cikin dauriya da jarumta ta yunƙura ta miƙe tsaye tana yamutse fuska,hannunta mai ciwon yana riƙe aɗaya mai lafiyar.

Gurin macijin ta nufa gabanta na ci gaba da faɗuwa,dan tsoro take kar ita kuma yayi mata wani abu.tana ƙara sawa ta durƙusa ahankali dai dai inda haroji ya buga masa wannan dutsen ,hannu ta sanya ahankali ,cikin karkarwa jiki ta ɗan shafa gurin ciwon.ai tana ɗora hannunta agurin macijin nan yayi wata irin juyowa tare da fasa kai kamar zai sareta, cikin tsoro da fargaba ta cire hannunta tare da matsawa baya da sauri tana zare ido tana kallon macijin.
Shima yana juyowa yaga fattu ce ,sai ya tsaya yana kallon ta,tare da komawa yadda yake ,wato ya sassauta fusatar da yayi ,kawai ya tsaya yana kallon ta.
Itama kallonsa take cikin tsoro da bugawar zuciya,ahankali macijin ya fara tahowa ,har ya zo gareta ,runtse idanu tayi tana karanta addu'ar Allah ya tsareta.
Ga mamakinta kawai saitaji macijin ya hau kan cinyarta ya kanannaɗe jikinsa ya dora kansa a saman gammon da yayi da jikinsa.

Ahankali ta buɗe idanunta tana kallonsa,shima ita yake kallo saidai idanunsa na zubar da hawaye kuma na jini .

Jikinta kawai rawa yake cike take da tsantsar tsoron abinda zai faru .juyawa tayi tana kallon haroji dake ta faman ihu yana yaɗuwa kasa.sannan ta kalli jauro wanda yake kwance ba alamun numfashi atare dashi,ga jauronsa nan tayi wani irin kumbura na ban mamaki sai jini ke zuba .

Tsorone ya ƙara kamata cikin azama ta yunƙura tare da mikewa tsaye, ture macijin tayi daga jikinta ta kwasa da gudu tayi gida tana kuka .
Koda taje gidan, da sanɗa tayi saurin shiga ɗakinta tana kuka,zama tayi akan tabarmarta tare da kife kanta a tsakanin cinyoyinta tana kuka.damuwace fal cikin ranta,wai meke shirin faruwa ne da rayuwarta?wacece mahaifiyarta?waye wannan macijin da yake ɗaukan hukunci akan duk wanda yayi nufin cutar da ita?tanasan sanin wannan macijin waye shi,kokuma waye ya aikoshi gareta.tana cikin kukanta ne kawai taji abu yana hawa jikinta silililili!!! Afirgice ta ɗago kanta tana kallon macijin daya gama hawa jikin nata. kansa ya ɗora akan wuyanta yana fidda wani irin huci ,shiru tayi tana sauraron yadda macijin ke huci,sanan jikinsa yayi wani irin zafi sosai.duk yadda akayi bashi da lafiya ,kuma dukan da haroji yayi masane solar hakan.
Tausayinsane taji yayi mugun kamata,ahankali cikin tsoro ta miƙa hannunta tare da riƙo saitin wuyansa ahankali ta janyoshi, ko motsi baiyi ba bare ya hanata abinda yake yi ɗin.

Akan tabarmar ta ɗorashi tare da ci gaba da kallonsa,cikin muryar kuka tace "bawan Allah kai waye?meke tafe dakai?waya aikoka zuwa gareni?meyasa kake ƙoƙarin daukar mataki akan duk wanda ya zalumceni?dan Allah karka cutar dani, bani da kowa sai baffana,dan Allah kayi tafiyarki ,idan mutanen garin na suka farga da kai zasu kasheka ,bazan so hakan ba dan Allah na roƙeka ka tafi"ta ƙarasa maganar tana haɗa hannunta cikin kuka.

Shidai macijin nan ko motsi baiyi ba sai huci da yake yi sosai,
Ahankali ta kalli gurin da yaji ciwo dazu sai taga gurin yana turiri kuma yayi wani fari fat.shiru tayi tana kallonshi ,yanzu ya zata yi masa ne?dan da alama fa yana jin jikine, data rasa abinyi kawai saita lulluba zanin sallarta ta fara karatun Alqur'ani mai girma.cikin abinda bai wuce sakwan biyar da fara karatunta ba kawai macijin nan ya fara wata irin murmurɗewa yana sauya kala, da farko yayi jajur dashi,sai kuma yazo yayi baƙiƙirin sosai ,wani irin hayaƙi na fita daga jikinsa .
Duk abinda yake sam fattu bata kulaba ,dan ta ɗaga kanta sama ne tana karatun ,kuma idanunta na zubda kwalla.

Shikuwa macijin nan burburwa ya ci gaba dayi yana murɗewa jikinsa na turiri tare da sauya kala.can kuma ya fara wani irin ƙara mai kama da gurnanin zaki.cikin tsoro fattu ta dawo da kanta ƙasa tana kallon macijin , sakamakon wannan sautin ƙara da taji yanayi.sai lokacin hankalinta ya kai kanshi taga abinda ke faruwa.
Tsorone ya kamata ƙarara "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un"shikenan ta tabbata wannan ba maciji bane tabbas aljanine ,ko kuma aljanine ya shiga jiki sa,na shiga uku ni fattu ya zanyi da rayuwata?meke shirin faruwa dani" ta faɗa cikin muryar tsoro da shiga ruɗu.
Shikuwa macijin nan tana daina karatun saiya daina burburwar da wanann gurnanin,ahankali kuma jikinsa ya dawo yadda yake . Ya jima kwance lamo kafin ya fara motsi,kansa ya ɗago tare da fasa kan yana kallon fattu,gaba ɗaya idanunsa sun koma baƙiƙirin dasu sannan wasu irin ƙananan layoyi suka bayyana kusan guda uku aƙasan kanshi, sai wani irin motsi suke kamar ya'yan tsutsa.

Karkarwa jikin fattu keyi kamar an saka mata shokin, lamarin ya matukar bata tsoro ,meye wannan ɗin haka suka bayyana jikin macijin nan? Me yasa daga fara karatun Alqur'ani gaba daya ya sauya kama?tabbas akwai wani boyayyen al'amari game da wannan halittar dake gabanta,kuma zata ci gaba da bibiyar macijin nan sannu kan hankali har saita gano menene tattare dashi.

Tana nan maƙale jikin katangar karanta kamar ƙadangaruwa dan tsabar tsoro da shiga shock ,idanunta ƙuri akan macijin ,wanda shima ita yake kallo ,kusan minti biyar suna haka ,taga macijin ya sulale ya bar ɗakin ta wannan hanyar tashi.

Rarraba idanu ta farayi tana dafe da ƙirjinta ,yau kam tana ganin ikon Allah kala kala ,anya kuwa bata janyowa kanta masifa ba?waima meye alaƙarta da wannan halittar ne?ko dai baffanta zata sanarwa halin da ake ciki ne?kai a'a ba yanzu ba tukunna ,ya kamata ta zama jaruma tayi wanann aikin koba komai zata taimaki rayuwar macijin,dan ta fahimci akwai boyayyen al'amari atareda shi.

Su haroji kuwa gaba ɗaya ya fice daga hayyacinsa sai ihu yake yana faɗuwa ƙasa ,ahaka ya nufi gidan lamiɗon garin ,wanda shine mahaifin jauro ,yana ihu yana tumami, har yaje gaban lamiɗo ya faɗi yana "wayyo idanuna ,wayyo fuskata lamiɗo ka taimaka min.

Ruɗewa lamiɗo yayi wanda yake tsaye jikin wata sanuwa yana bata ciyawa, lamiɗo bashi da imani ,azalumine sosai ,kuma mutanen garin suna matuƙar tsoronsa, dan haka yake mulki na zalumci agarina,ganin halinda haroji yake ciki"kai haroji menene hakan ?ina jauro?me yasameka?sune tambayoyin da lamiɗo ya jerowa haroji

Cikin azabar ciwo da fitar hankali haroji yace "jauro ya mutu maciji ya cinye masa jauronsa yana bakin rafi"
Ai dajin wannan batu hankalin lamiɗo ya tashi ,nan da nan yayi kan haroji yana faɗin wane macijin ?me kake cewa ?jauro ya mutu?ƙaryane badai agarina ba ,ba wanda ya isa ya zo garina ya kashe min ɗana."lamiɗo na gama faɗin haka ya kira mazan garin ,ya sanar dasu maza aje bakin rafi ataho da jauro.
Aikuwa cikin ƙanƙanin lokaci aka ɗauko shi kamar gawa .

Nan da nan lamiɗo ya nemi haroji ya sanar dasu abinda ya faru .
Nan ya sanar dasu iya abinda idanunsa suka gani,dan shima yana cikin mugun halin mutuwa ko rayuwa dan tuni gurin da jinin nan na macijin ya taɓa ajikinsa yayi wani irin kore shar yana zubar da wani yallow ɗin ruwa .

"Lamiɗo fattu ce ta Turo mana macijin nan ,shine ya kashe jauro"abinda haroji ya faɗa kenan ya sume.

Nan da nan mutanen gurin suka fara maganganu Suna faɗin da "da hansai ta faɗa tace mayyace yarinyar ,tunda har ta fara kashe mutane ba zasu yarda ba sai an hukunta itama.
Ran lamiɗo ya ɓaci sosai ,dan dama yana jin haushi yarinyar da ubanta,ya shirya neman aurenta amma sam taƙi yarda wai karatu take,yanzu kuwa dama tasameshi da zai hukunta su ita da tsohon nata.dan haka cikin bada umarni yace lallai lallai aje ataho da fattu da ubanta .

Nan da nan fusatattun maza suka nufi gidan malam bukar dan aiwatar da ƙudurin lamiɗo........

Masu karatu meke shirin faruwa ne ?

Wane hukuncin lamiɗo zai zartar akansu fattu?

Mai zai far nan gaba?
Muje zuwa yaki ce dai anty mammy

Mrs babi💘💘💘

Share and comments fisabilillah.

More comments
More typing.
[7/19, 10:10 AM] Abue Saleh AlQuyraemey: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄

MACIJINE 🪱🪱🪱

Na mammy kabeer
(Anty mammy)

Elegant online writers📚📚

Free book

Page 11/12

Domin samun update fiye da ɗaya a rana kayi join

https://www.facebook.com/groups/2803452939899949/?ref=share

Ta ƙabbalallahu Minna waninkum.
Slm, ƴan uwa masoyan littafin MACIJINE, ina miƙo gaisuwa tare da Barka da Sallah ,Allah ya maimaita mana,yasa munyi karɓaɓɓiyar
Ibada.

________________Kai tsaye su baffa suka nufi gurin lamiɗo,hannunsa riƙe da na fattu ,wacce ke tafiya ahankali cikin azabar raɗaɗin da hannunta keyi,dakuma ciwon jiki.yayinda su arɗo ke mara musu baya burinsu kawai suga wane irin hukunci lamiɗo zai ɗauka akansu fattu ,cikin zuciyarsa arɗo yake fatan inama lamiɗo ya kori su fattu daga rugar ,inyaso su bisu hanya suyiwa fattun fyaɗe,dan su kashe ƙishirwarta dake cin ransu.

Shikuwa mai gari tun daga nesa ya hango su fattu,gaba ɗaya nutsuwarsa ta bar jikinsa,ƙureta yayi da ido guri!!yana haɗiyar yawu da lasar leɓe kamar tsohon maye.
Kallonta yake yana ji kamar yaje ya kamota yayi ɗaka da ita.

haba malam ,yarinya bul-bul da ita kamar nunannen tumatur,lallai yau zai sha shagali.lamiɗo ya faɗa cikin ransa yana mai kallon fattun.

Baffa kuwa suna ƙarasowa gaban mai gari ya nemi guri ya zauna tare da zaunar da fattu kusa dashi,wacce gaba ɗaya arikice take ,tsorone ƙarara shinfiɗe akan fuskarta.tayi luƙus ajikin baffanta jikinta sai rawa yake, ta kasa ɗaga kanta ta kalli kowa ,sai hawaye take sharewa.

Kowa yanemi guri ya zauna ,masu tsayuwa suka tsaya , da ƙyar lamiɗo ya iya saita kansa ya aro nutsuwa ya yaɓa akansa, tare da ɓata ransa ya kalli baffa yace "malam bukar kana sane da irin abinda ƴarka take aikatawa awannan garin ?lamiɗo ya faɗa cikin kakkausar murya .
Ahankali baffa ya gyara zama kafin yace ,naji anata wai wai agari cewar ƴata tayiwa su jauro turen maciji ,amma sam ban yarda da wannan magana ba,dan kuwa ƴata ba mai kashe mutane bace ,sannan ba mayya bace kamar yadda ake faɗa"baffa ya faɗa cikin ɗaure fuska .
Cike da ɓaci rai lamiɗo ya fara magana.
"To wllh malam bukar bazan ɗauki wannan abun agarina ba,yanzu ace abun nata ya wuce kan kowa sai kan ɗana ?sannan kuma kace wai baka
yarda da zancen ba ?kana nufin nayi maka ƙarya ne?to bari kaji dole ne saina ɗauki mataki mai ƙarfi akanka da ƴar taka ,dan ka nuna rashin ɗa'a a gaban fada.bayan kuma kowa yaga abinda ƴarka tayiwa yaranmu,
Dan haka bazan yanke hukunci yanzuba sai zuwa gobe ,idan yaranmu sun sami lafiya,dan haka yanzu za'a shiga da ita cikin gida anan zata zauna cikin wancan bukkar da ake ajiye masu laifi .
Dan haka kowa ya watse sai zuwa gobe da la'asar adawo nan dan jin hukuncin da zan yanke"mai gari yana gama faɗin haka ya jingina da jikin kujerar da yake zaune akai.
gaba ɗayan mutanen dake gurin sunyi na'am da wannan hukuncin nacewar fattu ta zauna a gidan mai gari ,dan karta gudu.

Kuka sosai fattu ta sanya tana riƙe hannun baffa "wayyo Allah na baffa ka taimakeni,dan Allah karka bari akulleni adakin hukunci ,wllh bani nayi musu haka ba ,kuma sunzone da nufin keta min haddi baffa ka kalli Yadda ya famamin targaɗe na wllh ba laifi na bane" fattu ta faɗa cikin matsanancin kuka kamar zata shiɗe.

Cikin tashin hankali baffa ya riƙe hannun Fattu ,ji yake kamar ya fasa ihu,aduniya ba abinda ya tsana irin yaga Fattu cikin damuwa,"kiyi haƙuri fattu ba abinda zai sameki,in Sha Allahu Allah zai saka mana dan wannan mugunta ce ake son yi mana ,kuma Allah yana bayan mai gaskiya"yana gama faɗin haka ya juya gurin mai gari yace "lamiɗo ina neman alfarmar abarmin fattu mu tafi gida ,zamu dawo da ita zuwa goben,dan bata da lafiya kuma barinta ita kaɗai akwai matsala" ya faɗa cikin damuwa da alhinin wannan rashin adalci da ake ƙoƙarin aiwatar musu.

Cike da mugunta lamiɗo yace "kai bukar ina ganin girmanka karkasa in daina gani ka iya bakinka a faɗa kake,kasan idan na riga yanke hukunci ba mai ja dani ,dan haka ka tashi ka bani guri tun kafin raina ya gama ɓaci kuma yanzu zansa aje anemomin macijin duk inda ya shiga daga nan zuwa safiya ,"lamiɗo ya faɗa yana mai kiran wasu matasa yace su shigar da fattu cikin bukkar.

Kuka fattu keyi tana faɗin"wayyo baffana wayyo Allah ka taimakamin zasu tafi dani wayyo Baffa na karka bari su nemo shi zasu kasheshi. "amma haka suka tura ƙeyarta suka tafi da ita ɗakin hukunci.baffa yana ji yana gani ,hawayene masu zafi suka silalo daga idon bawan Allah ,zuciyarsa kamar ta faso ƙirjinsa yakeji, ashe ma ƙoƙarin keta masa haddin ƴa akayi?amma saboda rashin imani da adalci aka ɗora mata sharri,ba komai Allah zai saka musu.

Juyawa yayi ya nufi gida ransa amatukar jagule,yanzu idan wani abun ya sami yarinyar fa?idan wasu suka ƙara yunƙurin cutar da rayuwarta fa?"ya Allah ka karemin yarinyar nan Allah ka duba matsalolin dake kanta da wanda suke shirin samunta.ya Allah ka sauƙaƙa mata ƙalubalen dake gabanta.haka yayi ta mata addu'a harya ƙarasa gida kwata kwata hankalinsa baya jikinsa.
Yana shiga gidan gwogwgo hansai ta sanya dariya cike da mugunta harda riƙe ciki tana nuna baffa da hannu."wllh malam Gara ka cire wannan yarinyar daga zuciyarka, inba haka ba kana tsaye zaka yanke jiki ka faɗi ka mutu.ba ruwa na bani da asara, ai wllh banso lamiɗo ya kyaleta wai har sai gobe ba,daya sani yasa anyanke mata kai yau -yau ɗin nan ,da mun huta da nauyinta akanmu" ta faɗa tana turo wani baƙin ɗan kwalinta mai shegen datti zuwa gaban goshinta.

Kallon ta kawai baffa keyi ,cikin zuciyarsa yake kissima iri saɓawa gwogwgo da zaiyi dan yau zai nuna mata matsayin fattu azuciyarsa ,sai dai yana yunƙurowa da nufin maida mata martani,kawai yaji bakinsa yayi nauyi,wani irin shayinta da tsoro ya mamaye zuciyarsa.kai kawai ya girgiza ya wuce ɗakinsa ,wato itama gidan mai garin taje kenan?ba komai akwai Allah.

Fattu kuwa tunda aka turata cikin ɗakin nan banda kuka ba abinda takeyi, ita damuwarta ma yanzu bai wuce na rashin ganin macijinta ba,duk wannan abunda ke faruwa baizo ba.anya kuwa lafiya?kodai wani abu ya sameshi ne?
"Ya Allah ka kare wannan bawan naka ,ka bashi kariya daga sharrin mugayen mutane .

Shikuwa maciji adaidai wannan lokacin yana gidansu fattu yaje nemanta bai ganta ba yayi ta zagaye aɗakinta amma bata nan,tun lokacin datayi masa karatun nan daya fita yaje can jeji ya kwanta ,sam bayajin daɗin jikinsa sosai yake jin ciwo ta ko'ina ajikinsa,sai da lokaci yaja sannan ya nufi gidansu fattu ,ahankali yake tafiya cikin ciyawa da jikin katanga, harya ƙarasa gidansu fattu.
Koda yaje yaga bata nan saiya yi ta zagaye ɗakin yana nemanta ,amma bata nan. Kwanciya yayi akan ɗaurin kayanta yayi lamo kamar ya mutu.saidai hawayene ke zuba cikin idanunsa .

Can kuwa gidan mai gari ,da misalin ƙarfe bakwai na dare sosai hadari ya haɗu agarin, dan haka kowa ya shige cikin gida dan gudun zubowar ruwan,da akowane lokaci yana iya sauƙa.

Daidai wannan lokacin kuma fattu na duƙunƙune cikin ɗakin hukunci sai kuka take zuciyarta tayi mata ƙunci ga yunwa dake addabar ta rabo ta da abinci tun madarar da baffa ya bata da safe.hannunta sai zagi yake mata.
Ahankali taji ana turo kofar ɗakin hukuncin,da alama shigowa za'ayi,ga duhu aɗakin.
Zabura tayi cikin sauri ta miƙe tsaye jikinta na karkarwa,kar dai ace su jaurone suka dawo ?wayyo Allah na " ta faɗa tana dafe ƙirjinta ,zuciyarta kamar zata fito dan tsoro da firgici.
Cikin rawar murya tace "wa...w....ayee."
Ahankali cikin murya mai kama da raɗa,yace "ke kwantar da hankalinki,nine nan lamiɗo"
Ya faɗa yana mai haska tocilan ɗinsa .

Cikin zubar da hawaye tace "dan Allah lamiɗo ka fitar dani daga gurin nan ,wllh ban aikata komai ba,bani na kashe jauro ba"ta faɗa cikin kuka.

"Kinga ki nutsu jauro bai mutu ba yana raye ,kuma idan kika bani haɗin kai muka yi komai cikin sirri ,to zan kyale ki ki tafi gida abinki"lamiɗo ya faɗa yana matsowa gareta.

Ja tayi da baya cikin sauri tace "me kake so nayi maka ?dan Allah ka gyaleni na tafi gida ,an fara ruwa"ta faɗa cikin kuka,dan ta gano manufarsa ,irin tasu jauro ce ,wato fyaɗe yake son yi mata.

Matsowa lamiɗo yayi tare da ruƙo hannunta yana mai cewa"Ayya fattu yarinya mai kyau da kyan jiki ki yarda dani mana duka -duka minti nawa ne ba dayawa zanyi ba kinji ki taimaka min"ya faɗa yana mai janyota jikinsa sosai .

"Wayyo Allah na baffa kazo ka taimakeni,dan Allah lamiɗo kayi haƙuri wllh ba kyau kaji tsoron Allah ka tausaya min na roƙeka"fattu ta faɗa cikin rawar jiki da matsanancin kuka,tana mai tureshi daga jikinta,banda warin tsufa ba abinda yake yi.

"Ke dan ubanki ki tsaya ko saina miki ta ƙarfine?Shegiyar yarinya haka zamu zuba miki ido muna kallonki kin cika kinyi tunjum dake amma ba mai morarki,ki tsaya dan ubanki"lamiɗo ya faɗa yana mai ɗauke

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login