Showing 42001 words to 45000 words out of 89323 words
duk masu don kawo masa hari arayuwarsa.
Amma ce zaune cikin ɗakinta,yayin da Rashad ke zaune shima kusa da ita ,fuskarsa sam ba walwala, da alama dai suna tattauna wata magana ne mai muhimmanci,
"Rashad bana son irin rayuwar da kakeyi ko kaɗan,sam baka jin maganata,ka maida ammi itace uwarka itace ta isa dakai,kasani ba'a yarda da kishiyar uwa dan wasu ba alkairine azuciyarsu ba,Ni dai nina haifeka ,kuma kasan bazan taɓa cutar da kaiba,amma ka haɗa kai da maƙiyiyata sai abinda tace kakeyi ,to wllh ka kiyayeni,idan na juyo kanka bazakaji daɗi ba,yau kusan kwana uku baka ko leƙo dakin nan ba da sunan ka ganni ,sai yau da kazo min da wani zancen banza,to ina mai gargaɗinka akan yarinyar nan ba ruwanka da ita,kasan halin Adeeb sarai ,kome yayi maka kaika sani" amma ta kai ƙarshen batunta tana mai huci da jin ciwo cikin zuciyarta,sam Rashad bai ɗauke ta matsayin uwa ba,ya mika al'amarinsa kaf ga ammi ,hakan na matukar yiwa amma ciwo,yazo su hada kai susan me suke ciki amma yaƙi.
Rashad kuwa banda hura hanci ba abinda yake,yana zatace wani wai baruwansa da babyn na?wannan ma ai shirmene,wllh saidai kome zai faru ya faru ,amma ya gani ya gyasa kuma saiya ɗana.ya faɗa cikin zuciyarsa,kafin ya mike cikin rashin biyayya ga mahaifiyar tasa yake magana" nufa ba wanda ya isa ya hanani yin abinda naga dama,ke dayake hanaki naki uzurin, ko kina tunanin duk irin mugun abinda kike ƙullawa Adeeb ɗin ban sani ba?wllh idan aka takuramin zan fasa kwai ba ruwana,kinji kinsawa mata ido,baiwar Allah ita kuma tana ta nunawa danki so da kulawa" Rashad ya faɗa cikin rashin kunya yana ficewa daga ɗakin.
Kallonsa kawai amma keyi,idan da sabo yaci ace ta saba da rashin kunyar rashad,sam baya ganin girmanta, amma zatayi maganinsa.
Ta faɗa cikin ranta tana mai tunanin yadda zata wulaƙanta ammi cikin ruwan sanyi.
Fattu kuwa barcine yayi nasarar ɗauke ta ,har cikin barcinta mafarkin Hammana tayi tayi,yana mata wasanninsa masu nutsar da jiki da zuciya .sai kusan la'asar kafin ta farka daga barci,ba laifi marar ta daina ciwo,dan likatar nan ta dawo dan ta dubata lokacin tana barci .
Wanka nanny ta sata tayi tare da bata wata always ɗin ta saka bayan ta lika mata jikin pant.abinci taci tasha magani sannan ta zauna akan gado tana kallon Film ɗin da nanny ta kunna mata jikin kayan kallo.
Ta maida hankalinta sosai tana kallon Film ɗin ,indian yayinda take ganin kamar itace da Hammana suke lobayya.lol
Nanny ce ta shigo ɗakin ta zauna kusa da fattu tana mai faɗin" sannu ƴar nan ya jikin naki? Nanny ta faɗa tana ajiye wani bolw duke da kayan marmari a cikinsa.
Kallonta fattu tayi tare da sakin murmushi,dan tana ƙaunar matar har cikin zuciyarta,tana da kirki ga kulawa da mutum,dan zaman da sukayi sosai fattu ke cintar wasu kalmomin na larabci,saidai baya iya maidawa ba.
Jinjina kai tayi alamun da sauƙi, kafin ta fara cin apple.sosai take jin dadin wannan abun mai kama da dankali aradu idan tanacinsa har wani lumshe ido take.
Ammi ce ta shigo ɗakin cikin shigar ta ta koda yaushe wato doguwar riga mai shegen kyau da ɗaukar ido,gaba daya jikinsa sarkokin gwal ne ,sai ƙamshi take bugawa,cikin murmushi take shafa fuskar fattu tare da mata ya jiki,sunkuyar da kai fattu tayi cikin kunya,bata e komai ba.
Kallon wuyan fattu ammi tayi, tare da kafe sarƙar wuyan nata da ido,tabbas tasan wannan sarƙar da masu alaƙa da ita,amma ta yaya sarƙar zata kasance a wuyan wannan yarinyar,lallai dole ta raba ta da sarƙar nan dan kawar da zargi.zama tayi abakin gadon,cikin murmushi tana shafa lalausan bakin gashin fattu,kafin ta kalli nanny cikin murmushi tace " nanny ƴar taki fa akwai kunya sosai,ban sani ba kodai sirikata ce ita?da alama ko suna soyayya da dana ne " ta faɗa tana mai shafa sarƙar da hannunta.
Murmushi nanny tayi wacce ke tsaye can gefe tun shigowar ammi dakin,kafin tace " ranki ya dade gimbiyar uwar magajin faɗa,ba wannan alamun atare dasu,yana mata kallon ƙanwa itama tana masa kallon yaya ne,wannan shine abinda na fuskanta atsakaninsu" nanny ta faɗa cikin murmushi tana kallon fattu.
Murmushi itama ammin tayi,tana mai jin wani sanyi cikin ranta,yanzu ta sami nutsuwa ,akan ba wata alaƙa atsakaninsu,saura biye duk wata alama da zata sa agane iyayen fattu.
" Nanny kawo mata lemo mana ,naga ba wani drinks agabanta " ammi ta faɗa dan son fitar da nanny ɗaga ɗakin.
Da sauri nanny ta fice tana faɗin " angama ranki ya dade" tana fita ammi ta kalli fattu tare da sakar mata wata uwar harara,ta gefe ,kafin ahankali cikin dabara ,ta yadda fattu bazata taɓa tsammanin ancire sarƙar wuyanta ba ,ammi ta zare sarƙar tare da damkewa cikin hannunta.
Lokacin da take zare sarƙar ,da sauri fattu ta kai hannunta dan jin abu yana ɗan yawo awuyanta. Cikin sauri ammi tace " ayya ƴata bari incire miki wani ɗan zarene awuyan naki" ta faɗa tana mai karasa cire sarƙar.
Nanny na shigowa ita kuma ammi ta mike tare da ficewa daga ɗakin cikin tsantsar farin ciki.da alama komai zaizo mata cikin sauƙi.
Adeeb kuwa bayan yayi wanka ya huta,sannan yaci abinci kaɗan ,kafin ya janyo computer yana ɗan wasu ayyukan da ita,har lokacin yana jin ciwon marar kaɗan,saidai ba zazzaɓin.yana aikin ne kawai amma zuciya da tunaninsa suna kan fattu,dan so yake yaga Wane hali take ciki.kasa ɗaurewa tayi ya dauko wayarsa ya kira nanny, Tana dagawa ta ce " magajin fada ɗana ɗan albarka,me kake buƙata.
Murmushi yayi yana mai ɗan kumshe idanunsa,bayan amminsa nanny itace uwar riƙonsa da bazai taba daina ƙaunarta ba.cikin sanyin murya irin ta masu jinya yace "nanny ya jikin nata" ?
"Jiki kam da sauƙi ka gantama tana kallo bari na bata wayar."
Cewar nanny Tana mai karawa fattu wayar akunne.
"Hmmmmm Indai wanna ce Allah yasa tasan me ake yi da wayar ma"Adeeb ya faɗa cikin zuciyarsa.
Fattu kuwa kallon nanny tayi jin ta ƙara mata waya akunne,meye kuma wannan haka ?nanny ta doramin akunne na?
Fahimtar kamar fattu bata gane me zatayi da wayar bane yasa nanny tace " yayanki ne Adeeb ya ke magana,riƙe bari naje kitchen" nanny ta faɗa tana damkewa fattu wayar ahannunta.
Kallon haɗaɗdiyar wayar fattu tayi tana mai cewa acikin" Hamma kuma anan,to ta yaya yashiga cikin wannan ɗan karamin abun har yake magana?wayyo Allah na ta yaya Hamma zai fito ?na shiga ukuna Hamma kana ina ?kana jina ?dan Allah ka fito" fattu ta faɗa cikin muryar kuka,nan da nan hawaye ya fara wanke mata fuska.
Lumshe idanu Adeeb yayi ta can bangaren dan yana jin duk abinda yake fadi,kuma yasan za'ayi hakan .ya rasa wane irin shirme ke samun fattu,yanzu inda zuwa yayi ta ganshiba shikenan zatayi ta kukane gashi bata da lafiya.
Mikewa yayi da sauri ya nufi ƙofa.
Rashad ne tare da ammi suna tsaye jikin wata ƴar ƙaramar runfa mai kama da bukka ,magana suke mai muhimmanci,dan kuwa sai murmushi Rashad keyi yana kallon ammi.
" Aikuwa ammi yanzu zanje na ɗan ganta dan wllh ko barci bana iyayi,gaba daya babyn ta rikitani " rashad ya faɗa yana mai dage gira daya.
Dariya ammi tayi kafin tace " maza ɗan jeka abinka ,ba mai hanaka abinda ranka ke so,amma karka sake kayi mata komai,kajira lokaci,kawai kaje ka ganta kasami nutsuwa ranka" ta faɗa tana mai shafa kan Rashad din.
Murmushin jin dadi yayi tare da sumbatar hannun ammi,yace " shiyasa nake sonki fiye da mahaifiyata ammina"ya faɗa yana barin gurin.
Wani shegen murmushi ammi tayi tana mai binsa da kallo kafin tace " dani kike magana hafsat, nayi alƙawarin saina kawo karshenki afadar nan, keda ɗanki.koba dani zakiyi gasa ba?muje zuwa" ammi ta faɗa cike da gadara tana kaɗan kai.
rashad na shiga dakin da fattu take ya ganta zaune tana kuka,ga apple ɗin ta ahannu wani abaki,cike da shaukin babyn ya ƙarasa inda take ya zauna kusa da ita sosai ,da sauri fattu ta matsa can gefen gadon tana kukanta.
"Ohhh baby menene kike kuka?masu kyau ga basa kuka kiyi shiru,fadamin abinda ke saki kuka ?ko zakuɗa chocolate?ko ice cream kike so,Rashad ya faɗa yana mai ƙara matsawa kusa da fattu sosai .
Yunƙurin mikewa fattu tayi daga gurin da take ,dan ya kunaceta sosai,rashad yayi saurin janyota jikinsa ya rungume ta, ta gefe" haba babu kiyi shiru mana bana son ganin ki cikin damuwa,zo in baki chocolate kinji" ya faɗa yana ƙoƙarin hade bakinsu guri daya bayan ya riƙe fuskarta.
Cikin kuka fattu ta hankaɗe shi tare da fitowa daga kan gadon tayi kofa da gudu tana kuka.biyota yayi shima,saidai kafin ya ƙaraso ta buɗe kofar ,tana buɗewa kuwa taji ta faɗa jikin mutum,da sauri cikin tsoron ko rashad ne fattu ta dago kanta tana kallonsa. Ai tana ganin Adeeb ne tayi sauri ƙanƙameshi tana kuka.
Riketa yayi da sauri shima yana mai shafa bayanta ahankali,idanunsa alumshe" ya isa haka ba gani ba ?ki daina kukan " Adeeb ya faɗa yana mai dago kanta.
Cikin kuka fattu take nuna masa rashad" Hamma kace ya fita bana son ganinsa tsoro yake bani"ta faɗa tana mai ƙara kwantar da kanta aƙirjin Adeeb.
Da sauri Adeeb ya dawo kansa ,aikuwa carab idanunsa ya sauka akan na rashad,wanda yayi tsilli -tsilli dashi yana kallonsa.
Cikin wata irin zuciya da ɓaci rai Adeeb yace "what? rashad ?ubanme kakeyi anan?me yakawoka dakin Hulwa?me kayi mata" Adeeb ya faɗa cikin karaji yana ture fattu gefe guda tare da tunkarar rashad gadan-gadan kamar wani zaki.
Rashad kuwa cikin rashin kunyarsa ,duk da yana jin tsoron Adeeb ɗin,yace" kamar ya me ya kawoni ɗalibta?nazone in dubata kamar yadda ammi tace ,kuma kaima ai...bai karasaba sakamakon wani bahagon mari da Adeeb ya ɗauke shi dashi,kafin ya dawo hayyacinsa ya ƙara ma wani marin,nan da nan hancin rashad ya fara zubar da jini,kuma Adeeb ya shaƙe masa wuya tare da haɗa shi da bango.
Jikinsa banda karkarwa ba abinda yake" idan ka sake ka ƙara kallon koda inda Hulwa take ,wllh,billahi,saina illataka .wawa jaki dan iska "Adeeb ya faɗa cikin zafin rai da jin kamar ya karkarya rashad ɗin.
Rashad kuwa tsoro ya gama kamashi, gashi Adeeb ya shaƙe masa wuya yana neman kashe shi.sai dukan hannun Adeeb yake akan ya sake mai wuya,yana kakari
Kuka kawai fattu keyi tana daga tsaye jikinta na rawa ganin abinda ke faruwa,nan da nan jini ya ƙara balle mata sai zuba yake bul-bul yana bin ƙafarta.
Da gudu nanny ta shigo ɗakin tana salati" magajin fada zaka kashe shi ,maza sake mai wuya " ta faɗa tana mai kama hannun Adeeb ɗin.
Gaba daya hankalin Adeeb baya jikinsa.tsantsar kishi da tsanar rashad ke dukan zuciyarsa.sam yaki sake mai wuya.
Rashad sai kakarin mutuwa yake.
Ammi ce ta shigo ɗakin arude tana zuwa ta kama fuskar Adeeb tana faɗin"my prince meye hakan?zaka kashe shine sakeshi mana ,nice fa na aikoshi"ammi ta faɗa cike da tsoron kar Adeeb ya kashe rashad.
Amma ko gezau Adeeb baiyi ba ,ba kuma alamun zai sake rashad ɗin.
Rashad kuwa gaba daya jikinsa yayi kaishi dan ko hannunsa ma ya kasa dagawa bare ya kwaci kansa.
Da jan kafa fattu ta ƙaraso garesu,tare da rungume Adeeb ta baya cikin kuka take faɗin"Hamma ka sakeshi,zai mutu dan Allah Hamma ka bari,jinina yana zuba zan mutu Hammana " ta faɗa tana mai ƙanƙame Adeeb sosai ta baya tana kuka.
Sakin rashad Adeeb yayi yana mai runtse idanunsa da mugun ƙarfi,kafin ya dunƙule hannunsa ya daki bango da karfin gaske.
Juyo da fattu yayi zuwa gabansa tare da ƙanƙame ta ajikinsa yana sauke wata zazzafar ajiyar zuciya.
Ba tare da yayi magana ba ya kama hannunta suka fice daga ɗakin.
Da gudu su ammi sukayi kan rashad daya fadi ƙasa yana ta tari,ruwa nanny ta kawo masa mai sanyi,ɗan kwalla Uba daya kafa kai saida ya shanye ruwan tass.yana sauke ajiyar zuciya da shafa wuyansa cikin azaba.
Sannu suke ta masa ,kafin ammi ta kamashi suka bar ɗakin tare da nufar nata ɗakin.
"Wllh ammi tunda yayi min wannan ƙamshin mutuwar akan wannan yarinyar,nayi alƙawarin gobe saina yi mata fyade mafi muni agidan nan,saina yi mata abinda ko likitoci bazasu iya ɗin keta ba Adeeb ya yawo bala'in da bazai kare ba agareshi da ma yarinyar" rashad
Ya faɗa cikin azaba yana lumshe idanun.
Kai ammi ta jijjiga cikin bashi kwarin gwuiwa tace "ina bayanta ɗana kayi mata hukunci wanda ya dace da ita"
Ammi ta faɗa tana mai goge masa hancinsa.
Azuciyarta kusa ,dariya take cike da jin daɗi tana mai cewa"haka nake son ku kasance kullum cikin masifa da tashin hankali,kaida uwaraka yanzu ma kuka fara gani,Allah ya kamu goben...
To masu karatu nima dai haka nace ,Allah ya kamu goben ɗan ganin ya zata kaya.
Hausawa gareku, masoya,jiya ƙunƙuni shiru ,wllh ina uzurine amma kuna raina.One luv💓💓
Anty mammy ce
Mrs babi💘💘💘
Share and comment fisabilillah.
More comment
More typing.
[8/23, 9:06 PM] +234 813 465 3007: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄
MACIJI NE💘💘
Na mammy kabeer
(Anty mammy)
Elegant online writers📚📚
Free book
Page 45/46
________________kai tsaye Adeeb part ɗin sa ya wuce da fattu ,wacce ke kuka kamar ba gobe ,gaba ɗaya atsorace take da ganin yanayin na adeeb.ita tsoronta ma kada wani abu yasameshi, ko ya sanja halitta .
Suna shiga Adeeb ya zaunar da fattu akan kujera ,sam baidamu da yadda jikinta ya ɓaci ba,wani irin tuƙuƙin baƙin ciki yake ji cikin zuciyarsa ,lallai Rashad ya taɓowa kansa ,inhar ya ce zai nuna halin ɗan akuyancinsa akan fattu,to zai iya aikata masa komai ma,dan bazai taɓa iya daukar kowane irin abu akan fattu ba,duk ƙanƙantarsa kuwa.
Kaiwa yake da kawowa atsakiyar ƙarin falon kashi,banda dukan hannunsa ba abinda yake ,idanunsa sunyi bala'in sauyawa ,wannan karon gaba ɗaya idon nashi sun koma blue sosai ,sai wani irin huci yake kamar zaki.
Fattu kuwa ta takure guri ɗaya ,atsorace take sosai,ta kasa koda kallon Adeeb ne ,dan gaba ɗaya kamanninsa sun sauya,har wani bari jikinsa keyi.
Kuka take ƙasa ƙasa ,yayi da take jin yadda jini ke zuba ajikinta,dan har zuwa lokacin akiɗime take.
Juyowa Adeeb yayi yana kallon fattu ,tausayi ta yake ji sosai cikin ransa,yana tuna cewa itaɗin amanace agurinsa,dole ya kula da rayuwarta,bayan haka yana jin tamkar ita ɗin rayuwarsa ce ,bazai bari wani abu ya cutar da ita ba.
Gurin ta ya nufa cikin takunsa mai cike da izza,tsugunnawa yayi agabanta tare da tsura mata ido,dagowa tayi da sauri itama tana kallonsa.da sauri ta sunkuyar da kanta tana kuka ." Dan Allah Hamma kayi haƙuri,kada wani abu ya sameka " ta faɗa tana mai dagowa tare da kallon cikin idanunsa.
Shima kallonta yake cike da tausayawa,hannunsa ya ɗora akan fuskar fattu yana mai share mata hawaye,idanunsa akan fuskarta,
Ɗayan hannun nashi yasa tare da riƙe duka kumatunta,yana kallonta,tsawon mintuna yayi yana kallonta ,kafin ya sauƙe ajiyar zuciya da ƙarfi kafin ya fara magana ,cikin ƙunar zuciya .
" Hulwa " ya faɗa ahankali yana mai kallon fuskarta.
Kallonsa take tana mai tunanin sunan daya kiranta dashi.
Jinjina kai yayi tare da ci gaba " daga yau idan kikaji na kira sunan Hulwa ,to dake nake wannan shine sunan dana zaɓa dan kira ki dashi,saboda ke ɗin ta musamman ce agareni,kina da matsayi mai girma acikin nan ɗina.ya faɗa yana mai nuna saidin zuciyarsa.kafin yaci gaba" ki faɗa min me Rashad yayi miki?yaushe ya fara kulaki? " Adeeb ya faɗa trying to colmn his mine,Dan kar fattu ta ƙara tsorata .
Girgiza kai fattu tayi tare da share hawayen idanunta ,kafin cikin sanyin murya tace " Hamma Ni bansanshi ba, amma na taɓa ganinsa lokacin da mukazo gidan nan,yayimin magana amma ban kulashi ba,sai dazu ina kwance shine yazo zai taɓani" fattu ta ƙarasa cikin muryar kuka.
Runtse idanu Adeeb yayi da ƙarfi,yana mai jin zuciyarsa kamar zata ƙone,cikin wata irin murya Adeeb yace " ya taɓaki ne ?kuma ina ya taɓa miki?Adeeb ya faɗa jikinsa na wani irin bari.
Girgiza kai fattu tayi tana mai cewa " bai taɓani ba shine na gudu zan fita kai kuma kazo"
Ƙara riƙe fuskarta yayi cike da haɗe fuska sosai yace " ki faɗa min gaskiya Hulwa ya taɓa ki ne ko a'a" Adeeb ya faɗa cikin dan tsawa,har saida fattu ta ɗan zabura.
Kuka fattu ta ƙara sanyawa tana mai faɗawa jikin Adeeb " Hamma ka daina kana bani tsoro " ta faɗa cikin kuka tana kanƙameshi.
Shima ƙanƙameta yayi ajikinsa kamar zai maidata cikinsa.ahankali yake shafa bayanta alamun rarrashi,ita kuwa sai kuka take ahankali tana mai ƙanƙame dashi.
"Ya isa haka Hulwa ,ki daina kuka ,bana so zuciyata tana zafi idan na ganki cikin damuwa,Please stop crying" Adeeb ya faɗa yana mai shafa baƙin gashin fattu ,wanda ba ko ɗan kwali akanta.
Ahankali fattu ta rage sautin kukan ta,har tayi shiru gaba ɗaya,sai ajiyar zuciya take sauƙewa.
Kusan minti biyar suna rungume da juna,kafin fattu ta ɗan motsa tare da kiran sunansa"Hamma"
Ahankali ya buɗe idanunsa dake lumshe yana sauraran bugun zuciyar fattu ,tare nashi bugun zuciyar,ji yayi suba bugawa akusan tare.
Dagota yayi daga jikinsa yana kallonta da sauraron abinda zata faɗa masa.
Kallonsa tayi itama tana mai dan gwaɓe fuska kafin ta kalli ƙafafunta ,sannan ta ƙara dagowa tana kallonsa" jini Hamma"ta faɗa tana ɗan yarfe hannu.
Da sauri ya kalli ƙafafun nata,aikuwa jini har kan lallausan kafet ɗin dake tsakar ɗakin.miƙewa yayi da sauri tare da miƙa mata hannu,alamun ta mike tsaye.
Kama hannun nashi tayi tare da mikewa tsaye,gaba ɗaya gurin da take zaune ya ɓaci da jini .dan dafe kai Adeeb yayi tare da kallonta yana mai faɗin" sannu ba inkijin ciwo ?kai ta daga masa alamun ehh.hannunta ya kama ya nufi toilet da ita.ruwa ya haɗa mata mai zafi da kansa,sannan yace tayi wanka .
Kallonsa tayi bayan ta gama ƙarewa toilet ɗin kallo,kafin tace " Hamma nifa ban iya shiga kogi ba" ta faɗa cikin muryar ta mai daɗin sauraro .
Kallonta yayi tare da dan hararar ta sannan ya ce " aikuwa yau sai kin shiga kogin nan ,ko kuma nayi miki wankan da kaina" ya faɗa yana harararta ,wai kogi ji shiririta ko ina taga kogin?
Juyawa yayi da nufin fita daga toilet ɗin dan tayi wankan ,da sauri fattu ta riƙo hannunsa ,juyowa yayi ya na mai kallonta da alamun tambayar menene.
Marairaicewa tayi kafin tace " Hamma dan Allah ka zubamin ruwan acikin bokiti, Ni banason wannan abun , kalli fa kagani idan na shiga nutsuwa zanyi" fattu ta faɗa tana mai nuna masa wai ya kalli girman kwamin wankan.
Dafe kai kawai Adeeb yayi yana mai kallon fattu,shikam baisan yaushe