Showing 1 words to 3000 words out of 20356 words
jihadi
JIHADI
ABDUL’AZIZ SANI MADAKIN GINI
1
jihadi
Hakin mallaka:- M.kwalisa
Shekarar bugu na farko: 2014
Shekarar bugu na biyu:-2022
Shekarar bugu na uku:-2023
2
jihadi
A
JIHADI
wani zamani can baya mai tsawo da ya
shuxe bayan shuxewar mulkin fir’auna na
birnin misra an yi wata azzalumar sarauniya
mai suna Zuhaira bin masrud.
Sarauniya zuhaira tana mulkin wata babbar
qasa dake bakin gavar tekun bahar sufiya kuma ta
gaji sarautar ne a wajen mahaifinta sarki masrud bin
zaurid. Sarauniya zuhaira ta kasance tana da wata
baiwa guda xaya tun tana qarama duk lokacin data
kwanta barci ta yi mafarki da abu to babu makawa
sai wannan lamarin ya faru da ita a gaske.
A cikin wasu ranaku ne lokacin bata wuce
kimanin shekara bakwai ba a duniya ta yi mafarki ta
ganta a gaban wani akwati na baqin qarfe, tana ta
faman qoqarin ganin ta buxe shi domin xauko wata
bulalar tsafi amman ta kasa buxeta, ganin ta kasa
yasa ta koma gefe ta zauna tan ataman haki.
3
jihadi
Tana nan a zaune sai wani boka ma’abocin
yalwar gashi a jikinsa ya bayyana a gareta ya dubeta
yace mata.
“Idan za ki ninka qarfinki sama da haka ba
ki isa ki buxe wannan akwatin ba, tabbas ya tabbata
ke za ki mallaki bulalar tsafi da matsafi marganu ya
samar da ita, kuma idan kika mallaketa za ki zama
gagara badau a duniya, don haka yanzu ki koma
gida ki jira lokacin da za a haifi yarinyar da zata iya
buxe miki wannan akwatin ki xauko bulala tsafi.
Koda Gimbiya zuhaira ta zo nan a barcinta
sai ta farka a cikin tsananin firgici, ga mamakinta sai
taga duk ta haxa gumi, zufa tana faman zuba daga
jikinta kamar an stomata a cikin ruwan qorama.
Cikin sauri ta xauko madubin tsafinta ta
shafe shi, tun kafin ta sauke hannunta Boka kanzul
ya bayyana a gabanta ya zube ya yi gaisuwa kafin ta
tambaye shi yace mata.
“Tabbas abinda kika gani a mafarki gaskiya
ne ya shugabata, za ki zama sarauniya maxaukakiya
idan kika mallaki bulala tsafi, amma kuma dole ki
jira lokacin da za a haifi yarinya da zata iya buxe
baqin kwatin da bulala take ciki” Cikin tsananin
fusata tace masa.
4
jihadi
“Me yasa jini na ba zai buxe ba?” Ya kuma
sunkuyawa gareta.
“Saboda ba da irin jinin zuri’arku aka kulle
baqin akwatin ba” Tana jin haka ta kwarara wani
ihu cikin tsananin fushi tace masa.
“Vace min daga xaki”.
Mahaifi Gimbiya zuhaira Sarki masrud ya
kasance gawurtaccen mayaqi wanda ya yi shura a
zamaninsa kuma shi a rayuwarsa babu abinda ya
tsana sama da ma’abota addinin musulunci ba komai
ne ya haddasa wannan mummunar gabar ba a
tsakaninsa da ma’abota addinin musulunci ba face
akwai wata rana da waxansu fatake ma’abota
addinin musulunci da suka zo giftawa ta birninsa,
sai suka yada zango a gefen garin domin su huta su
kuma samu ruwan da za su yi guzuri da shi.
A wannan lokacin akwai wani taqadirin
aljani a cikin birin na surfas wanda mutane ke
bautawa a matsayin ubangijinsu. A kullum sai an
yankawa wannan aljani raguna uku, shanu uku da
raquma uku, kuma sarki masrud ne da kansa yake
jagorantar yin wannan hadayar da ake yiwa aljanin
mai suna Burata.
5
jihadi
A ranar da waxannan fataken suka yada
zango a bakin birnin sufaras ne wata annoba ta zo
birnin ya zamana cewa gaba xaya dabbobin garin da
tsuntsayen su sun kamu da wata irin cuta ta gudawa
don haka sai suka rinqa mutuwa wasu kuma suka
lafke ya zamana cewa ko ta shi basa iya yi.
Bisa qa’idar hadaya da ake yiwa aljani
Burata ana yanka masa lafiyayyun dababbobi idan
kuwa aka kuskura aka yanka masa mara lafiya koda
guda xaya ce kacal a ranar babu wanda ya isa ya yi
barci a garin kuma duk qanannan yara dake garin sai
sun kamu da cutar da za su yi ta mutuwa haka kuma
idan aka sava lokaci na yin wannan hadaya to fa sai
wannan bala’i ya afku.
Sarki masrud yana samun dukkan biyan
buqatarsa a wajen aljani Burata bisa wannan dalili
ne baya yarda a samu matsala ko kaxan akan yi
masa hadaya.
Lokacin da ake yin wannan hadayar ga
aljani Burata da yammaci ne sakaliya daf da
magaruba tun da rana wnnan annoba ta afku a cikin
birnin na safras al’amarin da ya dugunzuma
hankalin sarki masrud ken an ya baza dakarunsa ko
ina a cikin birane da qauyuka na kusa dana nesa
6
jihadi
akan a nemo lafiyayun dabbobi da za a yankawa
aljani Burata kafin rana ta faxi.
Ai kuwa har gefen la’asar ba a samo
dabbobin ba sai ga dakarun da aka turo sun dawo
cikin gigita da ximauta, shugabansu ya zube a qasa
a gaban sarki masrud yace.
“Ya shugabana mun duba ko ina a cikin
birane da qauyuka dake kusa da wannan qasar tamu
babu inda wannan annoba bata je ba, mun rasa
lafiyayyun dabbobi amma akan hanyar mu ta
dawowa mun ga waxansu baqin fatake kuma suna
da dabbobi lafiyayyu fiye da adadin da muke da
buqata”.
Koda sarki Masrud ya ji wannan maganar
sai farin ciki ya lulluve shi yace.
“Maza ku koma wajen waxannan fataken
ku siyo dabbobin da muke buqata a wajensu komai
tsadar su kuma, idan suka qi siyar muku ko qwato
su da qarfin tsiya ku zo mana da su, domin mu
hanzarta zuwa xakin bauta”.
Koda jin wannan batu sai shugaban dakaru
ya miqe tsaye da sauri yana mai cewa.
“An gama ya shugabana”.
7
jihadi
Nan take ya jagoranci dakarunsa kimanin
su xari biyu suka hau dawakansu suka zaburesu da
gudu izuwa gefen gari.
Su dai waxannan fataken da suka yada
zango a gefen birnin surfas gaba xayansu basu fi su
ashirin ba ba kuma duka su zuri’a xaya ne na wani
attajiri da ake kira Abu salhaif.
A cikin wannan zuri’a akwai matarsa guda
xaya da kuma xansa shima guda xaya jal wani
matashin saurayi wanda bai fi shekara goma sha
huxu ba, shi ake kira da suna salhif saura mutane
goma sha bakwai daga qannensa sai matansu da ‘ya
‘yansu.
Abu salhif na tsaye tare da xansa salhif
yana koya mas yadda ake yaqi wato suna kaiwa
junansu sara da suka cikin gwaninta a gefe xaya
kuma matarsa da sauran abokan tafiyar na tsaye
suna kallonsu sai kawai suka hango qura daga can
nesa ta turnuqe sama, sannu a hankali suka hango
dakaru bisa dawakai a sukwane sun durfafosu.
A zaton su Abu salhif ‘yan fashi ne suka
kawo musu hari, har mazajen cikinsu sun yunqura
za su zare makamansu su tari mahayan sai abu salhif
ya daka musu tsawa, ya hana su don haka sai kowa
8
jihadi
ya tsaya a inda yake har mahayan suka qara so daf
da su suka yi tirjiya suna sanye cikin kayan yaqi
dakarun birnin surfras ne.
Koda abu salhif da jama’arsa suka ga cewar
ashe dakarun sarki masrud ne sai hankalinsu ya
kwanta suka mayar da takubbansu cikin kubenta.
Cikin biyayya abu salhif ya risina ga
shugaban dakarun ya yi gaisuwa sannan yace.
“Yaku dakarun sarki masrud me kuke
buqata daga gare mu har da za ku kawo mana
ziyarar bazata a irin wannan lokacin alhalin ko
shigowa cikin birnin ku ba mu yi ba?”
Koda jin wannan tambayar sai shugaban
dakarun ya sauko daga kan dokinsa ya matso daf da
abu salhif yace.
“Ya kai wannan attajiri tsohon abokin
cinikin mu ka yi sani cewa sarki ne ya turo mu
gareka domin mu siya masa raquma uku, shanu uku,
raguna uku daga cikin dabbobinka domin mu bayar
da jinin su ga abin bautarmu gunki Burata”.
Koda jin wannan batu sai hankalin abu
salhif ya dugunzuma yace.
“Subhanallahi ya kai wannan badakare ka
yi sani cewa mu musulmai ne waxanda suka yi
imani da bautar Allah sarki guda xaya wanda shi ne
9
jihadi
ya hallaci komai da kowa har da shi gunki Burata da
kuke bautawa, to ta yaya za mu bayar da
dabbobinmu kuje ku aikata wannan mummunan
savo da su?
Ai idan muka baku tamkar mun yi imani da
abin da kuke bautawa ne, ku koma ku gayawa sarki
Masrud cewa ni attajiri abu salhif nace ya yi haquri
ba za mu iya siyar masa da dabbobinmu ba” Koda
jin wannan batu sai shugaban dakarun ya tari
numfashin abu salhif yana mai daka masa tsawa
yace.
“Sarki ya bamu umarnin idan har ba za ka
bamu ba waxannan dabbobin ba lallai mu karve su
da qarfin tsiya”.
Koda jin haka sai mazajen ayarin na abu
salhif suka zare takubansu da nufin a gwabza yaqi
da dakarun sarki masrud, amma sai Abu salhif ya
sake daka musu tsawa a karo na biyu yace.
‘Baku da hankali ne ta yaya za ku iya yaqar
dakaru kimanin xari biyu alhalin gaba xayanmu
bamu wuce mu goma sha ba”.
Nan take mazajen suka sake mayar da
takubbansu cikin kubenta suka koma bayan Abu
salhif suka tsaya a wannan lokacin ne baqin ciki ya
lulluve salhif har zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar
10
jihadi
zata qone jikinsa ya kama tsuma koda shugaban
dakarun ya lura da halin da salhif ke ciki sai ya
bushe da dariya mugunta sannan ya dafa kafaxar
salhif yace.
“Yaro bai san wuta ba sai ya taka, ka
yayyafawa zuciyarka ruwan sanyi idan ba so kake
yanzu nan jinin zuri’arku gaba xaya ya gudana a
turvaya ba”.
Koda jin wannan batu sai salhif ya sake
fusata ya yunqura zai kaiwa badakaren sara da
takobin hannunsa amma sai mahaifinsa ya yi wuf!
Ya riqe hannunsa kuma ya zabga masa mari har sai
daya faxi qasa, cikin tsananin mamaki salhif ya
shafi kuncinsa a lokaci guda kuma hawaye ya zubo
masa ya qurawa mahaifinsa idanu saboda wanne ne
karo na farko daya tava xaga hannu ya mare shi.
Amman a tsakaninsu ko baqar magana bai tava faxa
masa ba, nan take abu salhif ya dubi shugaban
dakarun sarki masrud yace.
“Ka yi haquri quruciya ke xibansa” Ya xan
yi shiru sannan ya ci gaba da magana.
“Za mu baku dabbobin da kuke buqata
amma ka gayawa sarki masrud cewar buqatarku ba
zata biya ba ta hanyar amfani da dabbobin ma’abota
addinin musulunci” Koda gama faxin haka sai Abu
11
jihadi
salhif yasa aka kwanto raguna uku, shanu uku,
raquma uku aka baiwa dakarun suka juya suka kama
hanyar komawa cikin birni da gaggawa.
Bayan tafiyarsu sai Abu salhif ya miqawa
salhif hannu ya kama ya tashe shi tsaye sannan ya
dube shi yace.
“Ka yi haquri ya kai xana inda ban mareka
ba bisa kuskuren da ka aikata da tuni sun kashe ka a
gaban idanuna, ka sani cewar kai ne kaxai a gare ni
da mahaifiyarka, don haka bama son rabuwa da kai.
Kuma ina son ka sani har yanzu kana da
sauran lokaci kafin ka zama jarumi mai qarfin
damtsen da zai iya jayayya da dakaru, idan ka yi
haquri sannu bata hana zuwa wata rana kai zaka
zama mujadadi.
Ku mu kimtsa mu bar wajen nan domin
abinda zai biyo baya bamai kyau bane”.
Koda jin haka sai kowa ya ta shi aka hau
kimtsawa nan da nan kuwa aka gama aka kama
hanya domin ci gaba da tafiya izuwa birni na gaba
inda za a gudanar da harkokin fatauci.
**
Al’amarin sarki masrud ana kai masa
waxannan dabobin sai ya yi shiri ya tafi izuwa xakin
12
jihadi
bauta aka yanka dabbobin aka bayar da jininsu ga
aljani Burata kamar yadda aka saba.
Faruwar hakan ke da wuya sai suka ji aljani
Burata ya kwarara uban ihu al’amarin daya janyo
xakin bautar ya kama rugujewa, mutane dake ciki
suka ximauce suka rinqa zubewa qasa sumammu.
Cikin firgita sarki masrud ya zube gaban
gunki Burata yana tuba.
Nan take Gunki Burata ya buxe baki yace.
“Maza ka tura dakaru su je su kashe
waxannan baqin fataken domin jinin dabbobinsu bai
magance mini qishin ruwa ba face qaruwa, kuma ka
sani cewa lallai si an yi asarar duban rayuka a ciki
qasarka saboda fushina don haka ka hanzarta
samomin jinin da na saba sha, kuma kowa sai ya
xanxana kuxarsa”.
Koda jin wannan batu sai sarki masrud ya
sake ximaucewa ya miqe tsaye zumbur yana mai
qwalawa sarkin yaqinsa kira ya fice da gudu.
Ai kuwa ba a xauki wani lokaci ba sai
barde markus ya gabato gaban sarki masrud da
gagawa yana zuwa ya zube a gabansa yana mai yin
gaisuwa.
“Maza a bi sawun waxannan fataken a
dawo da su”.
13
jihadi
Tun kafin sarki ya gama rufe bakins barde
markus ya miqe cikin gaggawa tare da jama’arsa
suka hau dawakai suka zabure su cikin gagawa da
zumar isa wajen da Abu salhif suke, amman suna
zuwa suka tarar tuni sun bar wajen.
Nan suka nausa suka bi bayansu, amman
sam basu ga alamar su ba. Haka suka yi ta nema a
cikin daji har suka gaji suka koma gida suka sanar
da sarki abinda yake faruwa.
A washe garin ranar duk wasu yara da basu
wuce shakara biyar ba suka riqa kamuwa da wata
cuta ta quraje suna fito musu a jiki, nan da nan sai
zazzavi ya rufe yaro kafin wani lokaci sai yaro ya
mutu.
Kafin wasu awani yara masu tarin yawa sun
halaka, nan fa jama’a suka bazamo zuwa wajen
sarki masrud suka zube suna faxa masa wannan
anobar data same su, suna cikin faxa masa wannan
bala’in da yake faruwa sai ga matarsa ta shigo faxa
cikin tsananin ruxani xauke da ‘yarta Gimbiya
zuhaira itama wannan anobar ta quraje ta feso mata
a jiki.
Tana zuwa gaban sarki ta ajiye tana kuka,
koda sarki masrud ya qyala ido yaga yadda ‘yarsa
14
jihadi
qwaya xaya tilo ta kamu da wannan cutar duk ta
sandare, sai idanunta ne kawai suke juyawa tana
numfashi sama-sama, ai kuwa bai san lokacin daya
zabura ya sauko daga kan karagarsa ba ya saka
hannu cikin tsananin tashin hankali ya xauki
Gimbiya zuhaira ya nufi wajen abin bautar su Gunki
Burata.
Yana zuwa ya ajiye ta a gabansa ya faxi
yana neman yafiya da neman xauki.
“Ai na faxa muku ya zama dole ku nemo
waxannan mutanen a kashe su, idan ba haka ba zan
yi ta saukar muku da annoba kala-kala”.
‘Kayi mana rai ya abin bauta” Sarki masrud
yace masa kafin ya ci gaba da magana “Shekara da
shekaru muna bauta maka, muna biya maka
buqatarta da bin duk wani sharaxi naka don haka
muna neman yafiyarka”.
Gunki Burata ya qyalqyale da dariya.
“Zan yafe muku amman bisa sharaxin lallai
duk tsayin zamani za ka ci gaba da neman
waxannan maqiyan nawa ka kamo su kuma ka
halaka su”.
“Na yarda na kuma yi maka alqawarin zan
aiwatar da duk abinda ka ubarce ni”.
15
jihadi
Gunki Burata ya qyalqyale da wata dariya
wacce tafi ta farko sannan yace musu.
“Ku koma gida wannan cutar zata yaye”.
Koda jin haka sai sarki masrud ya xauki
‘yarsa Gimbiya zuhaira ya nufi gida da ita, sannan
ya yiwa sauran jama’a suma umarni da su koma
gida za su samu yayewar cutar.
Tun daga wannan lokacin sarki masrud ya
tsani duk wani ma’abocin addinin musulunci, kuma
ya baza ‘yan leqen asiri da nufin su nemo masa
bayani game da wajen da zai samu Abul salhif,
amma shiru kake ji kamar an shuka dusa.
**
A lokacin da sulalusi na dare ya shiga
Gimbiya Zuhaira tana kwance akan makeken
gadonta na alfarma tana tsakiya da barci kawai sai ta
yi mafarki da wata yarinya qarama kyakkyawar
gaske sarki masrud ya kawota tana zaune a gaban
dokinsa.
Bayan ya kawota sai yace a kula da duk
wasu buqatu na yarinya, kama daga cinta da kuma
suturarta haka kuma mahaifinya ya mayar da
yarinya kamar ‘yarsa duk wani iko da Gimbiya
16
jihadi
Zuhaira take da shi a gidan itama haka take da
wannan ikon.
A haka shekaru suka ci gaba da tafiya
bayan wasu lokuta, sai aka wayi gari sarki masrud
ya faxi ya mutu. Kawai abin mamaki sai ganin
yarinya aka yi ta fito daga cikin gidan sarauta sanye
da abayar sarauta da kuma sandar mulki hakan nan
kuma ta xora hular sarauta, tana zuwa sai ta xane
karagar mulki.
Faruwar hakan ba qaramin xaga hankalin
Gimbiya zuhaira ya yi ba, tana ji tana gani ta kasa
wani katavus bare yunqurin qwato mulkinta daga
hannun yarinya.
Tana zuwa daidai nan sai ta farka daga
barci cikin tsananin firgita da ximauta. Tana mai
faxin cikin qaraji da tsawa.
“Wallahi qarya kike, babu wacce ta isa
zama sarauniya bayan ni...” Nan take kuyanginta
suka shigo cikin xakin da gudu suna tambayarta
lafiya.
Kafin ta basu amsa har dakaru sun cika
xakinta zare da makamai a hannunsu suna faman
muzurai da rarraba idanu domin ganin wanda ya
17
jihadi
kawo mata xauki, a lokacin shima sarki masrud ya
shigo cikin xakin cikin sauri yana tambayarta lafiya.
Ganin yadda xakinta ya cika da jama’a yasa
Gimbiya zuhaira ta soma saukar da numfashi cikin
nutsuwa tana qoqarin gayato nutsuwa zuwa cikin
zuciyarta bayan wani lokaci ta kori duk fargabar da
take ciki, ba zaka fahimci komai ba sai idan ita ta
faxa maka.
Ganin haka sarki masrud ya ce kowa ya fita
daga cikin xakin ya basu waje, nan take kowa ya
fice ya zamo daga shi sai ‘yarsa Gimbiya zuhaira.
Cikin nutsuwa ya qarasa wajen da take ya
samu waje ya zauna a kusa da ita akan gado, a
hankali ya kai hannunsa ya kamo nata yana mai
nuna alamun rarrashinta sannan yace mata.
“Ya ‘yata shin mene ya firgita ki haka cikin
wannan daren?”
Gimbiya zuhaira ya numfasa tace masa “Ya
kai abbana ka yi sani cewar duk lokacin dana yi
mafarki da abu sai abun nan ya faru da ni a gaske,
don haka a cikin barina na yi mafarki da wata
yarinya daka kawota gidan nan da hannunka kuma
ka raineta da abinci da ruwan sha da sutura ta gidan
nan har ta girma, bayan ta girma har zuwa lokacin
da kai kuma ajali ya riskeka, to a lokacin ta fito daga
18
jihadi
cikin gidan sarauta xauke da kayan mulki kuma ta
haye kan karagar mulkinka”.
Koda jin haka sai hankalin sarki masrud ya
matuqar dugunzuma, ya yi shiru kawai yana duban
‘yarsa domin yana da masaniyar duk abinda ta faxa
gaskiya ne domin duk lokacin data yi mafarki da
wani abu a cikin barcinta to lallai sai abun nan ya
faru da ita a gaske. Idan haka ne kuwa wannan
lamarin dole ya xagawa ‘yarsa Gimbiya zuhaira
hankali.
Amman kuma sai ya daure yace mata cikin
kwantar da murya.
“Duk abinda kika faxa gaskiya ne,amman
ina son ki kwantar da hankalin ki zuwa gobe zan
aika boka kanzul ya zo domin ya yi min bincike
akan wannan lamarin, kuma da kaina zan yi hawa
zuwa wajen babban gunki da muke bautawa duk
qarshen shekara zan je neman xaukinsa akan
wannan lamarin, tabbas koda zan rasa raina sai na
tabbatar da ke akan karagar mulki tun kafin mutuwa
ta, a wannan karon sai na tabbatar miki da cewar
mafarkin ki ba zai zama gaskiya ba”.
Duk da waxannan maganganun da sarki
masrud ya faxa wa ‘yarsa amman hankalinta bai
19
jihadi
kwanta ba, maimakon haka ma sai damuwa data
qara mamaye duka fuskarta.
Haka dai mahaifinta ya xauki tsawon lokaci
yana mai kwantar mata da hankali kafin daga bisani
ya yi mata sallama ya fita, ai kuwa bai jima da fita
ba sai Gimbiya zuhaira ta yi zumbur ta sauko daga
kan gado, sannan ta taka cikin takun qasaita zuwa
wajen da wata durowa take, tana zuwa ta jawota ta
xauko wani madubi dake ajiye a ciki koda ta xauko
shi sai ta koma cikin nutsuwa ta zauna akan gadonta.
Bayan kamar wasu mintina sai ta soma
karanto wasu xalasimai na tsafi tana tofawa a fuskar
madubin, faruwar hakan ke da wuya sai hayaqi ya
turnuqe xakin sannan boka kanzul ya bayyana, ya
zube gaban Gimbiy zuhaira yana faxin.
“Ina gaisuwa ga sarauniyar gobe” Ta dube
shi cike da mamaki tace masa.
“Shin baka da labarin mafarkin da na yi da
kuma abinda na ya faru a cikin mafarkin?” Ya qara
duqawa yana mai faxin.
“Yanzu komai ya bayyana a gare ni, tabbas
babu makawa mahaifinki sarki masrud da hannunsa
zai kawo wannan yarinya har zuwa cikin gidan nan,
to amman ki yi sa ni cewar qaddara ta riga fata
domin babu makawa sai yarinya ta zo, amman kuma
20
jihadi
akwai amfanin da zata yi miki da kuma qasar nan
baki xaya”.
“Amfani kuma?” Da mamaki Gimbiya
zuhaira ta tambaya.
“Qwarai ma kuwa, tabbas ita zata taimaka
miki wajen xauko bulalar matsafi marganu”.
“Me yasa sai ita, kana gani na gani a cikin
barcina ta rabani da farin cikina, shin ta yaya zan
dawo kuma na mallaki karagata?” Boka kanzul ya yi
murmushi.
“Duk wasu taurari na nasara suna tare dake,
kuma tabbas ke