Showing 12001 words to 15000 words out of 20356 words

Chapter 5 - JIHADI

Start ads

13 Aug 2025

164

Middle Ads

ya malleket idan har
hakan ne kenan zai yi biyu babu koma yayi uku
babu ko xaya.
Ya rasa dukiya mai yawan gaske wacce zai
amsa a hannun mahaifinta ya kuma rasa Ramlatul
auliya kuma gashi ya rasa abokan tafiya wanda
burinsu shi ne su zagaya duniya suga abinda yake
cikinta na daga al’ajabi da kuma irin al’adun su
koda ya zo nan a cikin tunaninsa sai idanunsa suka
ciko da qwala.
A karo na farko ya ji nadama ta zo masa
cikin ranshi akan duk abubuwan daya aikata a cikin
rayuwarsa, nan take ya ji ya tsani komai na duniya
amma daya tuna bakin alqalami ya gama bushewa
sai yaga nadamar tashi bata da wani amfani hakan
yasa ya durfafi cikin daji yana mai nufar hanyar da
zata fitar da shi daga cikin qasar gaba xaya wannan
dalilin shi ne ya saka su Ashman suka kasa ganin
Muhisin.
72

jihadi
Haka dai jarumi Nusurul Ashman da zaiyan
suka yi ta yawo a cikin daji suna kai kawo cikin
loko da saqo suna neman Muhisin amma alamunsa
basu gani ba bisa dole suka juya suka koma cikin
birin sin.
Al’amarin sarki Baharu zaman kuma
lokacin da yaga Gimbiya Ramlatul auliya ta dawo
hannunsa salin alin babu abinda ya sameta sai ya
kamu da tsananin farin ciki, amman daya tuna da
maganar Nusurul da kuma batun musuluntar da ita
da ya yi sai ranshi ya vaci zuciyar shi ta kama
tafarfasa kamar zata qone nan take ya yafito wani
babban hadiminsa ya yi masa raxa a cikin kunnensa.
Ko da ganin haka sai zuciyar Gimbiya
Ramlatul auliya ta buga da qarfi amman sai ta basar
tasan dai akwai wani abu da sarki yake shiryawa
yanzu kam tasan babu abinda zata iya aikatawa
tunda tana tsakiyar dakaru. Haka suka ci gaba da
tafiya har suka qarasa cikin birnin sin.
Ko da suka shiga cikin birnin jama’a gari
suk gansu sun shiga da tuta a hannun alamar an
samu nasara sai suka ruxe da murna suna ihu da
kixe-kixe na murna akan nasarar da suka samu aka
73

jihadi
shiga yiwa sarki da dakarunsa jinjina. Gaba xaya ya
ruxe ana faman kixa da busa da don nuna farin ciki.
Ko da aka qarasa gidan sarauta sai Gimbiya
Ramlatu auliya taga an bata sababin kuyangi da
kuma dakaru masu tsaron lafiyarta aka xauke
waxanda suka saba yi mata hidima. Wannan
al’amarin ya bata mamaki ya kuma xaure mata kai
hakan yasa ta kalli mahaifinta sarki Baharu zaman
tace masa.
“Ya kai abbana yaya za ka yi min haka
naga ka sauya min dakaru da kuma hadimai na” Ko
dajin wannan maganar sai sarki Baharu zaman ya yi
mata murmushi yace mata.
“Ya ke ‘yarta ki sa ni ba komai yasa kika
ga na yi miki haka ba face don ganin na kuma baki
tsaro na lafiyarki, saboda mun fahimci cewar
maqiya suna son rabamu da ke ta ko wacce hanya.
Idan ma ba ki sani bas hi kansa wannan yaqin shi
kanshi Barhuza ya qirqire shi ne saboda ya samu ya
mallake ki.
Don haka za ki samu turakar ta ki ma mun
sauya miki ita, da wasu sababin don haka kiyi
haquri da duk irin abinda kika gani sabo saboda
bana jin za mu samu kwanciyar hankali har sai
lokacin da muka ga bayan maqiyin mu Barhuza”
74

jihadi
Koda kammala faxa mata haka sai sarki Baharu
zaman ya sauko daga kan dokinsa ya juya ya kama
hanyar da zata kai shi turakar shi.
A daidai wannan lokacin wata sabuwar
kuyanga ta zo gaban Ramlatul auliya tace mata.
“Ya shugabata yanzu zan shiga gaba don
yi miki rakiya zuwa sabuwar turakar ki” Koda jin
haka sai ta murtuke fuska tace mata.
“Ba zan je ko ina ba sai na soma zuwa
turakar mahaifiyata ta gani n ganta tukuna tunda
muna cikin qishir ruwar ganin juna” Kuyanga ta
kuma rusunawa tace mata.
“Bamu da ikon barinki kije face da izinin
sarki” Koda jin haka sai ran Gimbiya Ramlatul
auliya ya kuma vaci, cikin fusata ta kalli dakarun
tace musu.
“Duk wanda ya hanani zuwa ganawa da
mahaifiyata zai fuskanci vacin raina” Koda
kammala wannan maganar sai ta juya ta nufi wajen
da turakar mahaifiyarta take.
Amma sai dakaru nan suka yi wuf! Suka
kamota suka nufi wani vangare na daban da ita tana
ihu tana cije-cije da fizge-fizge kamar bata kasance
‘yar sarki ba har sai da aka kaita cikin xakin aka
warva da ita akan gado aka jawo qofar aka kulle
75

jihadi
xakin da duk wasu tagogi ta yadda babu ta wajen da
zata iya fita.
Can tana zaune sai taji an qwanqwasa qofar
xakin, kamar ba zata buxe ba sai kuma ta miqe ta
buxe. Tana buxewa sai taga jarumi Nusurul Ashman.
Tana ganinsa ta taso da gudu ta zo gaban shi cike da
farin ciki.
Ya mata murmushi ganin haka sai jikinta ya
yi sanyi.
“Na kamo maqiyin mu” Ta buxe baki zata
yi magana sai taga mahaifinta tsaye a bayan su. Nan
tsoro ya kamata ganin haka sai ya fashe da dariya ya
matso fareta fuska a sake.
“Ni ma na aminta da Addinin Nusurul
Ashman, na yi imani da Allah na amshi addinin
musulunci, don haka da ni da jama’ata duka gobe za
mu yi imani. Kuma a gobe za a kashe maqiyin mu”.
Koda sarki masrud ya zo daidai nan a
labarinsa sai ya ji zakara ya yi cara alamar gari ya
waye. Kawai sai ya miqe zumbur ya fita daga
turakar Gimbiya Zuhaira ba tare da ya yi mata
sallama ba ita kuma hankalinta ya dugunzuma
saboda tasan daman mahaifinta yasanta da son
labarin hikayoyi.
76

jihadi
Yanzu haka daya ta shi yabarta sai ta
kasance cikin tsananin damuwa.
**
kwatsam an wayi gari sarki masrud ya
ta shi da wata irin cuta wadda shi kansa Bokan nasa
ya kasa gano maqasudinta da yanayinta, haka ma
likitocinsa yanayin cutar shi ne haka kawai sai ransa
ya vaci, ya zare takobi ya yi ta saran hadimansa da
dakarunsa, tamkar wanda ya zautu.
Dole sai an riqe shi da qarfin tsiya, an
kwance takobi an bashi wani magani yasha sannan
hankalinsa ke dawowa cikin jikinsa amma rabin sa’a
na yi sai ciwon haukan ya dawo.
Bisa dole aka hana matan sarki da
iyalinsa kusantarsa, amma kuma a kullum a cikin
rusa kuka yake saboda an hana shi yin tarayya da
matan nasa, bisa wannan dalilin ne Bokan ya matsa
da bincike ya gano cewa dole sai an samo wa sarki
masrud sabuwar amarya kuma kyakkyawar budurwa
masaniyar labarai na ban al’ajabi, tana kusantarsa a
kowane dare sannan sarki masrud zai daina wannan
cuta ta hauka.
Akan wannan dalilin ne aka baza shela
ana neman budurwa da zata iya wannan aikin mai
77

jihadi
haxari wanda ta san cewa idan ta kasa gamsar da
sarki masrud da dadaxan labaranta kashe ta zai yi.
Nan fa aka yi ta cigiyar har tsawon wata
uku da qyar bokan sarki ya gano cewar duk faxin
duniya babu macen da zata iya wannan aikin face
Muzainat gano wannan lamarin ba qaramin xaga wa
boka hankali ya yi ba. Domin yasan akwai
gagarumin ta shin hankali.
Lokaci da Sarki Yaki Nasmira ya ji cewa
‘yarsa zata auri sarki bisa wannan sharaxi sai ya
fashe da kuka ya ce “Idan kika je mutuwa za ki yi,
idan na rasaki wa zai ci gaba da kula da ni?”
Koda jin haka sai hawaye ya zubowa
Muzainat ta dafa kafaxarsa “Ka kwantar da
hankalinka ya kai sarkin yaqi ka yi sani cewa ina da
waxansu labarai na hikayoyi masu ban al’ajabi
waxanda lallai za su iya magance wannan cuta ta
sarki, ka tuna cewa idan na auri sarki zan siya maka
gida mai daraja da tsada, , har abada abinda nake so
da kai kawai shi ne ka taya ni da addu’a, daman ni
nasan babu makawa sai na auri sarki, abinda
Gimbiya zuhairat bata sani ba ni ce mabuxin alherin
qasar su”.
Koda jin haka sai sarkin yaqi ya rungume
Muzainat yace “Ya ke ‘yarta ki yi sani cewa
78

jihadi
rayuwarki da farin cikinki ya fiye mini komai a
cikin wannan duniyar, da dai na samu gida da
dukiya koda ta kai cikin garin nan gwara na ci gaba
da kwana a kasuwa ina bara a titi muddin za ki rasa
rayuwarki, ko farin cikinki ki tuna cewa fa ni girma
ya kamani, ina nufin tsufa ya riske ni, abu ne
mawuya ci na daxe nan gaba, ke kuwa yanzu ne za
ki fara shirya rayuwarki ta gaba,idan kika sami
matsala tun a farko to fa abu ne mawuyacin komai
na ki ya tafi daidai.
Sa’adda sarkin yaqi ya zo nan a zancensa
sai Muzainat ta janye jikinta daga cikin nasa sannan
ta ruqe kafaxunsa da hannayenta biyu ta dube shi
cikin murmushi tace.
“Na yi maka alqawarin babu abin da zai
same ni kuma sai suna na ya shahara sosai a wannan
nahiya gaba xaya, bama wai a garin nan ba”.
Koda jin haka sai sarkin yaqi ya gyaxa
kai cikin alamun karayar zuciya yace “Haba yake
‘ya ta yaushe wannan mafarkin na ki zai zama
gaskiya? Ni dai kawai bazan hanaki jarraba sa’arki
ba amma dai hankalina ba zai tava kwanciya ba,
face na ga kin auri wannan sarki na mu da tsawon
watanni kin rayu”.Ta yi murmushi.
79

jihadi
“Kar ka damu duk wanda yace ayi wasan
jifa dutse ya taka”.
Gama haka ke da wuya sai itama ta je ta
kwanta a kan shimfixarta ta janyo mayafi da nufin ta
lulluva sai ta hango dakarun gidan sarki kimanin su
goma gami da wata kuyanga sun shigo cikin
kasuwar kuma sun durfafo inda suke.
A firgice Muzainat ta miqe tsaye, shi ma
marhat ya miqe tsaye lokacin daya ji motsin takon
sawayen dakarun sai ya miqe zaune zumbur a
tsorace, ya fara kiran Muzainat yana cewa.
“Motsin me nake ji kuma?”
Kafin Muzainat ta qara cewa wani abu
tuni dakarun da wanan kuyangar sun iso daf da su,
kawai sai kuyangar ta dubi Muzainat cikin
murmushi tace.
‘To yarinya mai sa’a ki yi sani cewa
gobe ne za a xaura aurenki da sarki bisa wannan
dalilin ne sarki ya bayar da umarnin a xauke ku daga
nan akai ku can sabon gidan daya baiwa mahaifinki
kyauta”.
A cikin gidan akwai komai babu abin da
zaku buqata a can ne za a yi miki kwaliyar amarya
kuma da magariba za a kai ki wajen angonki”.
80

jihadi
Koda jin wannan batun sai Muzainat ta
kamu da tsananin farin ciki shi kuma Marhat sai
hankalinsa ya dugunzuma ainun fiye da koyaushe.
Nan da aka ga waxansu hadimai na gidan
sarki sun qaraso da keken doki batare da vata wani
lokaci ba aka sanya Muzainat da mahaifinta a cikin
keken dokin aka tafi da su izuwa wannan sabon
gidan da sarki ya basu dakaru na take musu baya
tamkar sun kasance jinin sarauta.
Gaba xaya sauran almajirai dake kwana a
cikin rumfuna kasuwa kusa da gidan sarkin yaqi sai
suka tashi daga barci suka bisu da kallo kawai suna
matuqar mamakin yadda aka yi wannan xaukaka ta
zowa Muzainat da mahaifinta a dare xaya.
Mutane da basu da kuxi siyan doki su
hau yau ga su a cikin keken dokin ma sun kame ana
jansu.
To dama masu iya magana sun ce dare
xaya Allah kan yi bature wannan fa shi ne Allah ya
yi aure da mara kwabo.
**
A she lokacin da wannan kuyangar ke
faxawa Muzainat cewa gobe ne za a xaura mata
aure da sarki wasu daga cikin ‘yan uwanta almajirai
sun ji nan da nan kuwa labari ya cika birnin Hindu
81

jihadi
ya zamana cewa duk inda ka gifta sai di ka ji ana
tsagegumi ana faxin cewa gobe sarki zai auri ‘yar
almajiri marhat.
Aikuwa sai kowa ya rinqa faxin
albarkacin bakinsa, wasu su kushe wasu su yaba
wasu ma sai suka rinqa cewa ai talauci ne yasa
Muzainat ta siyar da rayuwarta domin ubanta ya
amfana tunda dai ta tabbatar da cewa ita mutuwa za
ta yi.
Lokacin da keken dokin su Muzainat ya
iso qofar gidan da aka basu suka yi arba da gidan sai
Muzainat ta kamu da tsananin mamaki domin gaba
xaya birnin in banda gidan sarauta babu wani gida
mai kyansa.
Koda ganin haka sai hawaye ya zubowa
Nasirat saboda tsananin farin ciki ta kama hannun
sarkin yaqi suka sauko daga cikin keken dokin a ka
yi musu jagora izuwa cikin gidan da shigarsu cikin
gidan sai Muzainat taga yadda aka qawata shi ainun
aka shirya aljannar duniya, a cikinsa sai ta sake
kamuwa da matuqar farin ciki mara misaltuwa bata
san sa’adda ta fashe da kuka ba.
Al’amarin da ya razana sarkin yaqi
kenan ya damqe hannunta da kyau kuma ya janyo ta
izuwa kan qirjinsa yace.
82

jihadi
“Ki kwantar da hankalinki yake ‘yata na
sani cewa tsananin farin ciki ne ya saki wannan
kuka gami da takaicin cewa ba ni da idanu bare naga
wannan daula da muka samu kanmu, to ki sani cewa
ni farin cikina guda xaya ne kawai cewa ko a yau na
mutu naga yadda qarshen ‘yarta ya yi kyau.
Ko a mafarki ban tava zaton cewa zamu
tsinci kanmu a cikin irin wannan daula ba, tabbas
mai rai baya fidda rabo.
Haka dai aka yi ta kewayawa da su
Nasirat a cikin gidan har sai da suka gama ganin ko
ina duk inda suka shiga sai sun ga bayi, kuyangi da
hadimai suna ta gabatar da aikace-aikace su, tamkar
a haka za su shuxe, har izuwa qarshen rayuwarsu.
Bayan hadiman da suka kawo su sun tafi
sai hadiman gidan suka kawo wa Muzainat da
mahaifinta abinci mai rai da lafiya suka kimtsa
cikinsu suka yi hani’an da yake dare ne sosai sai
Muzainat ta yi gyaran murya. Take wata kuyanga
dake tsaye a bakin qofar falon da suke ta rugo da
gudu ta zube a qasa gabanta bisa gwiyoyinta tace.
“Ya shugabata me kike da buqata?”
Koda jin wannan tambaya sai Muzainat
ta ji kamar kanta zai fashe wai yau ita ake kira da
83

jihadi
shugaba alhalin ta kasance ‘yar almajiri mai bara a
titi kuma mai kwana a kasuwar rumfa.
Cikin murna da annushuwa Muzainat ta
dubi kuyangarta tace.
“Ina son ki raka sarkin yaqi izuwa xakin
barcinsa, bayan nan kuma ina so ki faxa wa gaba
xaya hadiman gidan nan su je su kwanta su yi barci
tunda yanzu mun gama samun nutsuwa, ni da
mahaifina sai gobe da safe ku zo gaba xayan ku ina
son yin magana da ku”.
Koda jin haka sai kuyangar tace “An
gama ya shugabata”.
Nan take kuyanga ta miqe tsaye sannan
ta kama hannun tsoho marhat ya tashi tsaye sannan
suka fice daga falon.
Fitarsu ke da wuya sai Muzainat ta miqe
tsaye ta shige cikin qurya turakar inda tayi arba da
wanni fankacecen gado tun data ke a rayuwa bata
tava ganin shimfixa kamar wannan ba tun tana
qarama har kawo yanzu data girma ta zama
cikakkiyar budurwa.
Samari da dama gami da dattijan banza
sun sha nuna mata kuxi domin su yi lalata da ita
amma bata yarda, sau goma sha xaya ana yinqurin
yi mata fyaxe Allah na kareta, wannan rayuwa da
84

jihadi
take ciki ta jefa ta cikin matsanancin tsoro da
damuwa, don haka a yanzu da sarki yasa aka kilace
su aka kawo su, cikin wannan gidan sai ta tsinci
kanta a cikin nutsuwa da farin ciki mara misaltuwa.
Matsalarta kawai shi ne yadda zata kare
kanta a wajen sarki masrud ta rinqa ba shi daddaxan
labarai da za su gusar masu da ciwonsa na hauka
batare da ya kashe taba.
Dogaron Muzainat xaya ne, akwai wata
rana tun tana qasar su da ta shiga cikin daji domin ta
kawar da buqatarta a lokacin dama sun zo giftawa ta
bayan gari ita da mahaifin nata marhat.
Koda ta ji bawali ya matseta sai ta sanar
da shi, cikin kaxuwa yace.
“Yake ‘yarta kin gaya mini cewa yanzu
muna bayan gari ne,vangaren dajin husur kin sani
cewa yaune ranar farko da muka tava zuwa wannan
vangaren a yawon bararmu don haka ba mu san
haxarin da ke wajen ba kuma gashi nan inda muke
tsaye kan hanya ne mutane na xan giftawa lokaci
bayan lokaci,kinga ashe ba za ki iya kawar da
laruraki ba anan xin, ki shiga cikin wannan dajin ki
nemi inda ya dace amma dai ki yi taka tsantsan
kuma ki kula da kanki sosai ko yaya kika ga wani
85

jihadi
abu wanda baki yarda da shi ba ki juyo da baya da
gudu izuwa nan, inda nake mu gudu tare.
Koda tsoho marhat ya zo nan a zancensa
sai Muzainat tace “Babu komai ya kai Abbana ka
jira ni anan kada ka damu koda ka ga na xan vata
lokaci saboda dole sai na ga inda ya dace na kawar
da buqatar tawa”.
Marhat yace “Babu komai kije ‘ya ta mai
girma saljil zai kare ki”.
Saljin gunki ne na wata giwa wanda shi
ne abin bautar zuri’ar su tsohon marhat wannan
addini nasu yana daga cikin addinai na farko a
birnin Hindu.
Ba tare da vata wani lokaci ba kuwa
Muzainat ta bar tsoho marhat a bakin hanya ya sami
wuri ya zauna, ita kuma sai ta kunna kai izuwa cikin
daji.
Abin ka da wadda dama ta saba shiga
cikin daji ko alamar tsoro babu a tare da ita har ta yi
‘yar doguwar tafiya kaxan, kawai sai ta hango wani
qaton kogon dutse wanda qofar shigarsa duk ta
lulluve da yana tamkar fiye shekaru arba’in ba wata
halitta bata shige shi ba.
Al’amarin da ya yi matuqar baiwa
Muzainat mamaki ke nan tace a cikin ranta “Mene
86

jihadi
ne dalilin da yasa fatake ko dabobi ko waxansu
mugayen mutane basa shiga cikin wannan kogon
dutse don fakewa ko vuya? Amsar ta kasa baiwa
kanta ke nan kawai sai ta aiyana a cikin ranta cewa
za ta zagaya bayan wannan kogon dutse domin ta yi
bawalinta.
Koda ta zo giftawa tab akin qofar kogon
sai ta ji an kirawo sunanta daga ciki. Take hantar
cikin Muzainat ta kaxa, ta kamu da tsananin tsoro ta
yunqura da nufin ta falfala da gudu da baya kawai
sai ta ga an toshe hanyar da qaton dutse.
A firgice ta sake juyowa da baya don ta
koma inda ta fito nan ma sai taga an toshe hanyar da
wani dutse.
Kafin ta yi wani yunquri sai taga gaba
xaya yanar da ta lulluve qofar gogon ta vace vat
tamkar bata tava wanzuwa ba a wajen sai ga wata
mace tsohuwa tukuf gashin kanta ya zama fari sol
saboda tsufa, kuma tana sanyi da farare tufafi tana
dogara farar sanda ta fito daga cikin kogon dutsen.
Koda Muzainat ta yi arba da wannan
tsohuwar sai ta kamu da tsananin mamaki, ba komai
ne ya sata wannan mamaki ba face ta san wannan
tsuhuwar sosai, ana kiran wannan tsohuwar da suna
jarisa, kuma itama almajira ce wajen kjwanansu
87

jihadi
xaya a kasuwa kuma duk inda Muzainat da
mahaifinta suka je bara sai sun ganta a wajen koda
kuwa sun baro ta a can baya.
Hakan tasa suka fara tsorata da ita suna
zargin ko aljana ce, amma da yake tun kafin a haifi
Muzainat tsohuwa jarisa ke rayuwa a cikin almajiran
kasuwa kuma ba a tava ganinta cutar da wani ba sai
ba a damu ba duk da cewa kuwa babu wanda yasan
asalinta ko daga inda ta fito.
Lokacin da Muzainat ta yi arba da
tsohuwa jarisa sai jikinta ya kama tsuma saboda
tsananin tsoro ta qura mata idanu,kuma ta kasa
motsawa ko da taku guda, walau gaba ko baya.
Koda ganin haka sai tsohuwa jarisa ta
dub eta cikin murmushi tace “Haba yake Muzainat
tun fa kina cikin mahaifiyarki nake tare dake, in da
so nake na cutar da ke ai da tun a asannan zan cuce
ki, a gaban idanuna aka haife ki har kika girma a
matsayin marainiya mara uwa har kawo iyanzu yau
ne ranar da za ki san ko ni wacece, da kuma dalilin
da yasa nake ta bibiyarku, tun kina cikin
mahaifiyarki.
Ki kwantar da hankalinki na rantse da
darajar uwata da ubana ba zan tava cutar da ke ba, ki
sani cewa sau goma sha huxu ina kare mutuncinki
88

jihadi
daga sharrin mugayen mazajen dake kawo miki
harin fyaxe.
Tun kina jaririya nake kare lafiyarki da
rayuwarki, idan baki manta ba kimanin watanni
shida baya kin yi arba da wata qatuwar baqar
macijiya a bayan gonakin nan na cikin gari inda
macijiyar ta taso miki da nufin ta kashe ki a bakin
qoramar salbil amma sai wani kada ya taso

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login