Showing 9001 words to 12000 words out of 20356 words

Chapter 4 - JIHADI

Start ads

13 Aug 2025

169

Middle Ads

kuma
biyayyar haka kuma babu irin bautar da ban maka
ba amma ko kaxan baka tava saka min da alheri ba.
Sai dana kusa rasa raina saboda tsanani da
kuma begen ‘yarka wanda nake fama da shi a cikin
zuciyata amma kuma sai ka qeqashe idanu ka qyale
ni ka kuma yi min wulaqanci saboda na falasa maka
sirrin zuciyata.
To ka sa ni a yau kuma yanzu zan kashe ka
na kuma haye karagarka ta mulki na kuma aure
‘yarka Gimbiya da qarfin tsiya’ Kafin sarki yaqi
55

jihadi
Barhuzu ya kammala rufe bakinsa tuni sarki ya tari
numfashinsa cikin daka masa tsawa yace masa.
“Kai maqaryaci shugaban mayaudara na
duniya ka sa ni cewar koda giwa ta faxi tafi qarfin a
daka mata wawa, kuma ramin kura sai ‘ya ‘yanta,
kuma babban goro sai magogin qarfe ina baka
tabbacin cewar kai dai ba wani ba baka isa ka
kamani da qarfin damtse ba sai dai kuyi min taron
dangi.
Dan haka ina mai yi maka wani alqawari
idan ban kashe ka ba to zan maka wani lahani mai
muni a jikinka wanda da baqin cikinsa za ka shiga
cikin kabarinka idan kuma kana yin musu akan haka
to ka yaqe ni ka gani” A wannan lokacin daman tuni
tsurarun dakarun da suka rage na sarki Baharu
zaman sun saduda sun miqa wuya sun yarda
makamansu an kama su a matsayin fursunan yaqi an
zuba musu sarqoqi qafa da hannayensu.
Sa’ar da Barhuza ya kammala jin wannan
jawabin da sarki Baharu zaman ya yi sai ya bushe da
dariya yace masa.
“Ai wajen da babu qasa nan ake gardamar
kokawa kuma sai kuma an gwada akan san na
qwarai” Yana kammala faxin haka ya kalli dakarun
nasa gaba xayansu yace musu.
56

jihadi
“Tunda dai munci wannan yaqin yanzu
bana buqatar xayanku ya vata makaminsa ko sau
xaya da jinin wani dan haka duk wanda ya taimaka
min akan sarki Baharu zaman to da kaina zan kashe
shi da makami na don haka bana son ganin wani ya
kawo min agaji komai koda kuwa sarki Baharu
zaman zai halakar da ni” Yana kammala faxin
wannan maganar ya xaga takobinsa sama yana mai
riqeta da hannuwansa biyu sannan ya ruga kan sarki
Baharu zaman da gudu yana kwala wani uban ihu.
Ko da ganin haka sai shima sarki Baharu
zmaan shima ya yi xauki zuwa kanshi suna haxuwa
da juna a tsakiya suka kacame da wani azababben
yaqi cikin tsananin fusata.
Nan suka shiga kaiwa juna sara da suka
cikin tsananin zafin nama kamar jikin su babu jini
ko qashi a jikisu ai kuwa suna soma wannan yaqin
sarki Baharu zaman ya cika da mamaki kuma ya
firgita saboda ada sanin da ya yiwa kanshi
jarumtakarsa da kuma iya yaqinsa ya nunka na
Barhuza sau uku amma yanzu sai gashi jarumtakar
shi da kuma bajintar tasa ta kusa zuwa xaya harma
zafin naman Barhuzu yafi na shi kuma qarfin saran
shi da zafin naman shi ya nunka na sarki yakai sau
goma.
57

jihadi
Tun sarki Baharu zaman yana iya kare
saran da Barhuzu yake kai masa har takai ya gajiyar
da shi baya iya karewa har ya maida martani suna
cikin wannan azababen yaqin barhuzu ya xauki
numfashin sarki Baharu zaman ya dake shi da qafar
shi ta hagu.
Saboda qarfin duka da ya yi masa sai daya
yi sama ya faxo qsa da baya yana mai furza da aman
jini na wahala daga bakins a lokacin kuma takobinsa
da take riqe a hannunsa ta suvuce ta faxi qasa. Ya
yunqura zai tashi kafin ya tashi tuni Barhuza ya
daka tsale daga wajen d yake ya dirge a gabanshi ya
kai masa suka da takobinsa a ciki.
Cikin baqin zafin nama sarki Baharu zaman
ya yunqura zai kaucewa daya kai masa da tsini
takobin nasa amman duk da haka sai da takobin
nashi ta soki gefen cikinsa Baharu zaman ya kurma
uban ihu sakamakon mugun zafi da zogi daya ji.
A lokacin xaya jini ya yi tsartuwa daga
gefen cikin nashi amma saboda qarfin hali irin na
tsofafin jarumai sai ya yi wuf ya kama takobinsa
daga jikinsa ya yi wata alkafira daga qasa yana mai
dungurawa zuwa wajen Barhuza.
Kafin Barhuza ya yi wani yunquri tuni
sarki Baharu zaman ya yi wuf ya zaro wata
58

jihadi
sharveviyar wuqa daga cikin kubenta dake gefen
cinyar shi ta hagu yakai wa Barhuza sara a qirji
cikin tsananin zafin nama yaja da baya da zumar
kaucewa saran daya kai masa amma cikin rashin
nasara sai takobin ta sare masa babban xan yatsan
shi na hannu nan take yatsan ya guntule ya faxi qasa.
Hakan data faru ya kuma fusata Barhuza
ainun nan take ya zaro wata takobinsa daga bayan
shi ya haxa makamai guda biyu a hannunsa ya kuma
farma sarki Baharu zaman a karo na biyu yana mai
kai masa sara da suka da qarfinsa yana mai yi masa
mugun nufi.
In banda sarki Baharu zaman yana riqe da
wannan sharveviyar wuqar da tuni Barhuza ya
gididdibashi duk da haka sai da Barhuza ya yi
nasarar yankan jikin sarki Baharu zaman sau uku
wajen ya daddare ya yi rami mai zurfi jini yana
shatata daga ciki, nan take jiri ya soma xaukar sarki
Baharu zaman ya soma tangaxi.
Shi kuma Barhuza duk da babban xan
yatsan nashi ya guntule jini yana zuba amma hakan
bai saka ya nuna alamar cewar ya galabaita ba sai
ma ji daya yi kamar an qara masa qaimi akan na
baya da sarki Baharu zaman yaga jiri yana xibansa
sai ya soma tunanin mafita.
59

jihadi
Kafin ya kammala tunaninsa tuni Barhuza
ya shammace shi a karo na biyu ya kuma saka qafa
ya dake shi a qirji take sarki Baharu zaman ya yi
baya kamar an saka majajjawa an janye shi nan ya yi
sama ya faxo qasa ruf da ciki kuma cikin tsananin
galabaita domin sama-sama numfashin nasa yake
fita.
Barhuza ya rugo da gudu ya zo kanshi ya tsaya
yana kallonsa cikin tsananin wulaqanci ya tofa masa
yawu a fuska cikin wulaqanci sannan ya saka qafa ya
shure wuqar da take hannun sarki Baharu zaman cikin
wulaqanci yake kallonsa lokaci guda kuma ya qyalqyale
da wata dariya mugunta sannan ya soma cewa da shi
cikin nuna taqama da nuna isa.
‘Bana jin zan barka ka kuma ko da sa’o’i goma
numfashi yana matsawa a jikika yanzu nan zan shayar
da qasa jininka na kuma saka kanka a jikin makamina na
shiga da shi har zuwa cikin qasarka na kuma tsire shi a
jikin qofar shiga cikin fadarka har sai kowa na cikin
qasarka ya zo ya ganshi” ya ci gaba da cewa da shi.
“Yanzu ajalinka ya kusa qarewa tunda yana
hannu na kuma ‘yarka gimbiya Ramlatul auliya tana can
a hannun dakaruna a tsare a cikin tanti kaga kenan ina
kashe ka zan wuce da ita cikin gari na kawar da duk
wasu ‘yan majalisarka wanda basa goyon bayana na
kuma xane akan karagar ka na kuma aure Gimbiya
Ramlatul auliya.

60

jihadi
Koda jin haka sai sarki Baharu zaman ya miqe
cikin qarfin hali ya kalli Barhuza ya yi masa murmushin
mugunta sannan yace masa.
“Har abada wannan burin naka da kake son
cikawa ba zai tava cika ba koda bayan raina” Wannan
magana da ya faxa ta qonawa Barhuza rain an take ya
xaga takobinsa sama cikin tsananin zafin nama da zumar
zai sarewa sarki Baharu zaman kai.

Babu zato babu tsamani sai Barhuza ji ya yi
an daki qirjinsa da wani irin gaggarumin qarfi
saboda qarfin dukan sai daya yi baya kamar an
harba kibiya daga cikin baka sannan yaje ya gwara
kanshi da wata bishiya ya faxo qasa tim yana mai
yin aman jini.
Da sauri ya xago idanunsa don ganin
wanda ya yi masa wannan dukan ba kowa ya gani ba
face jarumi Nusurul Ashman wanda ya durgo daga
sama kamar tsuntsu mai fuka-fukai.
Sarki Baharu zaman koda ya xaga kai yaga
jarumi Nusurul Ashman ne ya kawo masa xauki bai
san lokacin daya soma qyalqyala dariya farin ciki ba.
Su kuma dakarun sarkin yaqi Barhuza ko
da suka ga shugabansu yana qasa ya kasa tashi
kuma yana aman jini sai suka tasowa jarumi Nusurul
ashamn gaba xayan su da zumar su yi masa rubdugu
61

jihadi
su gididiba shi yanda wani daga cikin su ba zai samu
tsokar namansa xaya ba.
Ko da jarumi Nusurul ashamn yaga wanna
runduna ta tunkaro shi kawai sai ya qwala kabara ya
tunkare su da gudu tun kafin su qaraso gare shi, ai
kuwa ana haxuwa sai ya kutsa ta cikin su da qarfin
tsiya ya hau su da sara da suka cikin wani irin zafin
nama na ban al’ajabi domin kamar guguwa ko
walqiya haka ya dunga katantanwa yana gididibasu
sai dai kaga jini yana tsiri yana fallatsi da vulvula
daga jikin sassan jikin xan adam yana malala a qasa.
Kawunan dakaru kuwa ya dunga shawagi a
sama kai kace takardu ne akai gutsu-gutsun da su
lokaci qanqani jarumi Nusubul Ashman ya yi wa
wannan dakarun mummuna varna ya kashe kimanin
mutum dubu daga cikinsu.
Don haka idan ka ji ana qi gudu to sa gudu
ne bai zo ba. Ganin irin wannan mummuna varna da
aka yi musu hakan yasa hankalin dakarun Barhuz ya
ta shi matuqa don sun san mummuna varna da ya yi
musu babu makawa idan aka ci gaba da tafiya akan
haka babu shakka zi qarar da su nan da wani xan
lokaci.

62

jihadi
Kuma sun yi imani da cewar aka ci gaba da
tafiya a haka babu shakka zai halakar da su gaba
xayansu duk da mugun yawan da suke da shi.
Shi kuma sarki Baharu zaman wanda yake
kwance ya kasa yin komai tsananin mamaki ne ya
hana shi yin komai. Yana mamakin yanda jarumi
Nusurul Ashman ya samu wannan irin qarfin tunda
yasan baya yin tsafi kuma babu makawa ubangijinsa
shi ne ya bashi wannan qarfin alhalin kuma duk
duniya babu wani addini daya tsana sama da wannan
addinin musulunci amman amman yanzu kuma ba
don ma’abocin musulunci ba da yanzu ya zama
gawa.
Wannan amsar ita sarki Baharu zaman ya
kasa baiwa kanshi hakan yasa ya saka idanu don ci
gaba da kallon yanda zata kasance tsakaninsu.
Koda dakarun Barhuza suka ga za su yi
biyu babu ba za su samu nasara akan Nusurul asham
idan suka tsaya yaqi da shi zai yi nasara akan su sai
suka ja baya suka daina yaqar shi suka koma wajen
shugaban a wajen da yake kwance suka sure shi
suka xora shi akan doki suka juya suka nausa zuwa
cikin daji suna masu yiwa dawakan nasu qaimi kai
kace duniyar za su bari gaba xaya.
63

jihadi
Har Nusurul ashamn ya yunqura zai bi su
don ya qure musu gudu ya kawo qarshen su sai sarki
Baharu zaman ya qwala masa kira yace masa.
“Maza ka je can wajen da suka yada zango
ka xauko min ‘yarta Gimbiya Ramlatul auliya tana
wurin su” Kafin sarki Baharu zaman ya kammala
rufe bakinsa tuni ya daka tsalle ya haye wani doki ya
yi masa qaimi ya nufi wajen da suka kafa sansanin
su.
Yana tunkarar wajen ya hango tsirarun
dakaru suna gadinta tun kafin ya qarasa suka soma
harbor masa kibiya amma duk kibiyar da suka
harbor masa kafin ta qarasa wajen shi sai yasa
takobi ya kaxeta.
Faruwar hakan ba qaramin mamaki ya
baiwa dakarun tsaron ba, hakan yasa cikin gagawa
suka yarda makaman su suka bazama cikin daji suka
bar wajen babu kowa kuma wajen ya yi tsit babu
komai sai tantuna da suka kakkafa sai kuma guzurin
yaqi na makamai da kuma dawakai a xaxxaure.
Cikin hanzari Nusurul asham ya qarasa
tsakiyar sansanin ya yi tirjiya ya sauka daga kan
dokin ya shiga leqawa cikin tantuna sai daya leqa
cikin tantuna bakwai amman bai ganta ba.
64

jihadi
Hakan yasa gwiwarsa ta yi sanyi ya soma
tunanin wata qila maqiya sun xauke Gimbiya
Ramlatul auliya hakan yasa ya juya da baya don
komawa kan dokinsa kawai sai ya ji motsi a wani
tanti dake can gefe xaya hakan yasa ya juya ya ruga
da gudu zuwa tantin daya ji motsin yana shiga ya
samu Ramlatul auliya su uku suna xaure da igiyoyi
a hannunsu da qafaffunsu kuma dukan su an rufe
musu bakunansu.
Cikin sauri da kuma farin ciki Nusurul
Ashman yana zuwa ya soma kwance sauran suka
rungume juna cikin murna ya qarasa wajen Gimbiya
Ramlatul auliya ya kwance mata hannu ta xaga
hannu sama tana yiwa Allah godiya sannan tace
masa.
“Ina labarin maci amana Barhuza” Nusurul
asham yace mata.
“Bani da labarin sa amman na sadu da
mahaifinki a lokacin da sarki yaqi Barhuza ke daf da
samun nasara halaka shi a halin yanzu sarki yaqi
Barhuza da duk dakarun sa sun sha kasha a hannu na
kuma sun tsere zuwa cikin daji bisa taimakon
ubangijin musulunci na baro mahaifinki a can baya
inda aka fafata qazamin yaqi tsakaninsa dana
65

jihadi
dakarun Barhuza tabas mahaifinki zai yi matuqar
farin ciki idn ya sadu dake a yanzu”.
“Wai shin ina labarin hashwan? Shin yabi
muhusin ne izuwa cikin birni don amsar dukiya a
wajen mahaifinki?” Ko dajin wannan tambayar sai
jikin su zaiyan ya yi sanyi, don haka ba tare da vata
lokaci zaiyan ya kwashe duk abinda ya faru ya
faxawa Nusubul ashaman.
Ko dajin haka sai baqin ciki ya turnuqe
Nusurul Ashman ya kalli Gimbiya Ramlatul auliya
da su zaiyan yace.
“Ai sai ki zo mu hanzarta mu koma can
wajen da muka baro sarki Baharu zaman” koda jin
haka sai zuciyar Gimbiya Ramtaul auliya ta buga da
qarfi ta kalli Nurutul ashamn cikin alamun tsoro tace
masa.
“Yazan yarda na koma wajen mahaifina
bayan nasan ya tsani addinin musulunci sama da
komai a wannan duniyar, ni kuma zai iya halakar
dani duk da tsananin qaunata da yake yi” Lokacin
da Nusurul Ashman ya ji haka sai ya yi murmushi
yace mata.
“Ki kwantar da hankalinki yake Gimbiya
Ramlatul auliya nasan mahaifinki ba zai yi yunqurin
cutar da mu ba saboda yaga yanda ubangijin
66

jihadi
musulunci ya bani qarfin kuvutar da shi da jama’ar
qasar daga halaka. Don haka yanzu ya zamar masa
dole a cikin abu biyu ya yi guda xaya kodai ya barni
na tafi dake don nasan idan na barki a hannunsa zai
iya hanaki yin addinin Allah ko kuma idan ya so ya
zauna dake shima ya amshi addinin musulunci”
lokacin da jarumi Nusurul Ashman ya zo nan a
maganar shi sai hankalin Gimbiya Ramlatul auliya
ya xan kwanta kaxan harma ta xan yi masa guntun
murmushi sannan tace masa.
“Shi kenan na yarda zan bika mu koma ga
mahaifina amma sai ka yi min alqawari cewar ba
zaka bari ya cutar da ni ba” Nusurul ashamn ya
maida wa Ramlatul auliya martanin murmushin da
ta yi masa yace mata.
“Na yi miki alqawari ba zan bari
mahaifinki ya cutar da ke ba” Nan suka xunguma
zuwa wajen da Nusurul ashamn ya baro sarki
Baharu zaman suna zuwa kuwa suka tarar da sarki
Baharu zaman a wajen daya baro shi dakaru sun
kewaye shi likitan shi kuma yana kusa da shi yana
sa masa magani a jikin raunikan da aka ji masa.
Koda sarki Baharu zaman ya hango ‘yar shi
Ramlatul auliya tare da jarumi Nusurul asham sai
fuskarsa ta faxaxa zuwa ga murmushi harma ya
67

jihadi
miqe tsaye da zumar ya tare su saboda farin cikin
sake ganinta, cikin sauri Gimbiya Ramlatul auliya ta
rakave a bayan jarumi Nusurul Ashman saboda
rshin yarda da mahaifinta ko da ganin haka sai sarki
Baharu zaman ya kalleta yace mata.
“Yake ‘yarta ki sa ni ba zan tava cutar da
Nusurul ashamn ko kuma ke ba saboda yau naga irin
qarfi da taimakon da ubangijin musulunci yake da
shi saboda ba don shi ba da yanzu sai dai gawata
kuma nasan tabbas Barhuza ba haqura ya yi ba zai
dawo kuma nasan b qaramin shiri zai kuma yo wa
ba.
Kuma zai ci gaba da tunanin hanyar da zai
kuma volo mana dani da kuma ke don ganin ya
samu cikar burinsa. Yanzu dai abinda za’a yi ku zo
mu koma cikin birni mu zaun mu huce gajiya idan
ya so sai mu kuma tattaunawa akan wannan
lamarin” Koda Nusurul Ashman ya ji wannan
maganar sai ya saukar da ajiyar zuciya yace.
“Wannan maganar daka kawo ta yi daidai
amma yanzu ya maganar abokan tafiyata su
Hashwan? Shin ka bashi wannan dukiyar da kace
idan muka kawo maka maganin ciwon hannunka za
ka ba shi?” Sarki Baharu zaman yace masaa.
68

jihadi
“Ai ban ba shi ba cewa na yi ya bari sai
zuwa gobe sakamakon tasowar wannan yaqin daga
wannan lokacin ban san halin da yake ciki ba” Ko
dajin haka sai murna ta kama Nusurul Ashman yace
masa.
“Na yi farin ciki da baka ba shi ba kaga
kenan yanzu ya yi biyu babu ya rasa dukiya ya kuma
rasa abokan tafiya, amman duk da haka akwai
matsala guda xaya, abu mai wuya ne Muhisin ya ci
gaba da zama a cikin qasarka dole ya fito yaga
yadda abu ya wakana kuma dole ya koma can wajen
daya baro su Hashwan.
Yanzu abinda nake so dakai da su Gimbiya
Ramlatul auliya ku koma cikin birni yanzu ni kuma
da Zaiyan ku qyale mu kafawa Muhisin tarko mu
kama shi a hannu domin musan irin hukunci da
zamu yi masa akan cin amanar da ya yi mana na
yunqurin halaka mu” Koda jin haka sai hankalin
Gimbiya Ramlatul auliya ya yi matuqar tashi ta rasa
wajen da zata saka kanta cikin tsananin damu tace
masa.
“Shin yanzu har ka manta alqwarin da
muka yi da kai kafin mu taho?” Koda jin haka sai
Nusurul Ashman ya ja Gimbiya gefe xaya yanda za
69

jihadi
su tattauna ta yarda babu wanda zai ji abinda za su
yi magana akai.
Suka yi ‘yar magana akan abinda suke son
tattaunawa, bayan sun kammala si suka ga Gimbiya
Ramlatul auliya ta saki jikinta da ranta kamar babu
wani abu da yake damunta.
Nan take ta bi sarki Baharu zaman tare da
kuyanga Hibaila suka hau dawakai suka nufi cikin
birnin sin, shi kuma jarumi Nusurul Ashman tare da
zaiyan sai suka hau dawakai suka soma yawo a cikin
yanki wannan dajin suna shiga cikin loko da saqo
wani wajen idan suka je sai sun sauka daga kan
dawakan sun yi sanda sun leqa musamman wajen da
suka samu yana da duhuwa ko kuma sarqaqiya
saboda tunanin cewar Muhusin zi iya vuya a wajen.
Haka suka ci gba da karaxe ko ina suna
dubawa har cikin kogon dutse wajen da macijiya ta
cinye Hashwan sai da suka sake komawa suka sake
caje amma suka ga wayam babu Muhusin babu
xuriyarsa hakan yasa hankalin Jarumi Nusurul
Ashman ya tashi hakan kuma shi ya bashi damar
sani cewar duk yanda aka yi Muhusin yana nan a
cikin birnin sin yana jiran sarki Baharu zaman ya
dawo daga yaqi ya bashi wannan duniyar.
70

jihadi
Haka dai Nusurul Ashman da zaiya suka yi
ta saqe-saqe a zuciya gami da tunanin iri-iri a qarshe
suka haqura suka koma zuwa cikin birnin sin.
Duk wannan abu da yake faruwa she kifi na
ganinka mai jar koma bayan sarki Baharu zaman ya
kammala magana da Muhusin akan cewar ja bari sai
gobe da safe ya sallame shi.
Wannan maganar daya kawo sai hankalinsa
ya kasa samun kwanciya musamman daya ji
varkowa yaqi zuwa garin hakan yasa ya raya a cikin
ransa cewar matuqar sarki Baharu zaman bai samu
nasara ba shi kenan shirin nasa duka ya lallace babu
yanda za a yi ya samu wannan dukiyar daga hannun
sarki Baharu zaman.
Shin wane yaqini yake da shi akan sarki
Baharu zaman zai ba shi wannan dukiyar ba tare
daya yaudare shi ba? Ko da ya aiyana hakan a cikin
ransa sai Muhisin ya yanke shawarar ya fita daga
cikin birnin ya koma can cikin daji ya lave don
ganin abinda zai faru a filin yaqi.
Don haka duk irin gumurzun da aka yi da
dakarun sarki Baharu zaman dana Barhuza akan
idanunsa aka yi daya ga yanda Barhuza ya ragargaji
dakarun sarki baharu zaman harma ya kai sarkin
qasa sai ya yi saurin sulalewa yabar wajen ya nufi
71

jihadi
cikin kogon dutsen daya kai su Ramlatul auliya har
ya kusa zuwa sai kuma wata zuciyar tace masa.
Meye kuma amfanin zuwan naka bayan
gashi mahaifin nata an cinye shi da yaqi komai
nashi zai koma hannun Barhuza kuma yasan irin
tsananin son da Barhuza yake yiwa Ramlatul auliya
babu yanda za ai ya barshi

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login