Showing 6001 words to 9000 words out of 20356 words
na farko data soma shigowa
cikin gidan.
Nazari hanyar da zata bi domin shiga sashen
da muzainat take yi, tabbas tasan mahaifinta ya san
halinta sarai, ba zata haqura tabar wannan abun haka
kawai ya wuce ba, don haka ya qara yawan dakaru a
wajen, qalubalenta na biyu kuma tasan tunda sarki
38
jihadi
dakaru ya ganta a tsaye a wajen dole shima ya daxa
tsananta tsaro, kuma yana kula da duk wani motsinta.
Ta yi imani idan ya baiwa babanta labarin
ganinta tana nazarin wajen sai ya qara yawan dakaru
masu tsaron lafiyarta, saboda yasan duk
jarumtakarta ba zata qarar da dakarun ba har ta
samu nasara shiga wajen muzainat. A yanzu ta
sauya dabara ba zata son yaqi domin shiga wajen a
wannan karon abinda ta yanke, zata bi komai dakidaki cikin siyasa da qissa ta ga bayan muzainat.
Tabbas tasan abin kunya ne a ji labarin
cewar ta yaqi dakarun mahaifinta akan tana son
kashe yarinya qarama da shekarunta basu kai a yi
yaqi akanta ba.
Dan haka bata jin zata iya fita ta yi yaqi da
dakarun cikin gidan akan yarinya muzainat zata
nemi wata hanyar da zata bi don ganin ta kawar da
ita ba tare da an san cewa ita ta aikata wannan aikin
ba.
Matsala xaya zata samu da mahaifinta ya
riga yasan abinda take shirin yi idan haka ne kuma
zai saka idanunsa akan ta duk wani motsi nata shima
yana kallo. Ta ci gaba da kaiwa da komowa tana
nazarin yanda yanayin gidan na su yake sam ta kasa
39
jihadi
samun kanta a cikin nutsuwa. A haka sulasainin dare
ya kuma shiga qafa ta xauke.
Ta koma ciki xakinta tana nazarin abinda ya
kamata ta yi a gaba, domin ita ba zata jira zuwa
wayewar gari ba, domin ba zata laminci maqiyarta
shaqar iskar cikin gidansu ba.
Ta yi saurin juyawa ta shiga cikin xakinnta
kai tsaye wajen da take ajiye makamanta ta nufa, ta
xauki makaminta tare das aka kwalkwali fari ta rufe
fuskarta yanda ba za a gane ta ba. Bata tsaya vata
wani lokaci ba ta yo waje cikin sauri, har ta kusa
kaiwa bakin qofa ta ja ta tsaya domin wata magana
da bokanta ya faxa mata akan yarinya muzainat.
‘ba za ki tava samun nasara akan ta har sai
kin mallaki wannan bulalar ta tsafi, wacce matsafi
marganu ya samar...’ nan take ta ji gwiwarta ta yi
sanyi.
Amman kuma wani sashe na zuciyarta ya
bata qarfi gwawa akan kawai ta aiwatar da
qudurinta, domin ai sai an gwada akan san na
qwarai. Don haka ta sa kai ta nufi tsakar gidan tana
fita ta tsaya tana nazarin yadda dakaru masu yawa
suke faman kaiwa da komowa a cikin tsakar gidan,
amma da yake tun tuni ta kammala nazari akan
40
jihadi
hanyar da zata bi domin shiga sashen na muzainat
kai tsaye ta wuce.
Tana zuwa dakarun da suke tsaron qofa suka
miqe suna kallonta cikin, cikin daka mata tsawa
wani badakare yace mata.
“Wane kai da zaka zo cikin shigar yaqi?
Maza ka sauya hanya kafin kaifin takobin mu ya
sauka akan ka” Bata masa magana ba sai kallonsu
da ta yi ta qare nazarin ta hanyar da zata halakar da
su.
Kafin su kuma magana tuni ta zare
makaminta ta yi xauki zuwa kansu kafin su farga
tuni jini ya fantsama a jikin ganuwar ginin gidan.
Kawunan sadaukai suka soma yawo a sama kamar
tsuntsaye.
Kaifin takobi dana makamin Gimbiya
Zuhaira suka dunga haxuwa suna bada tartsatsin
wuta a cikin duhun daren daya mamaye ilahirin
gidan sarauta, kafin wani lokaci adadin dakarun sun
qare daga gaban gimbiya zuhaira saboda yanda ta
farauce rayuwar su a lokaci qanqani.
Bata jira wani abu ba ta daka tsale ta kama
katangar gidan ta dirga cikin farfajiyar wajen, tana
dirga ta samu kanta a tsakiyar wasu dakarun da
yawansu ya nunka na waje wanda ta fafata da su, ai
41
jihadi
kuwa suna ganinta suka ta so kanta a yunwace,
kamar mayuwancin zaki daya yi kwana ki bai ci
abinci ba. Ai ganin haka itama ta yi xauki kansu
suka yi wata muguwar haxuwa nan ma kasuwar
yaqi ta soma ci.
Mutuwar ta soma shawagi tana farauce
rayukan abokan dakarun ta soma kai sara da suka
tana kaucewa saran da suke kawo mata duk wajen
da takai sara sai kaga kawuna suna tashi jini yana
kwaranya qasa kamar an buxe bakin magudana.
Idan kaga yanda Gimbiya Zuhaira ta ke wasa da
makami kai kace ba filin daga ta fito ba.
Kafin wani lokaci ta wahalar da su da azabar
yaqi sun ximauce sun kasa sarafa kansu hakan yasa
wasu daga cikin tsirarrun da suka rage suka yarda
makamai suka juya da gudu suna masu neman
hanyar tsira.
Sauran da suka rage a qasa wasu a karye
wasu a mace wasu kuma kawunansu suna reto a
jikin wuyansu abin babu kyan gani duk wajen daka
duba sai kaga wani yana nishi na azabar yaqi da
gimbiya zuhaira ta azabtar da su.
Ganin suna neman hanyar gudu yasa ta kaxa
kaxai ta shiga cikin xakin da take da yaqinin
yarinya muzainat tana ciki, tana shiga cikin xakin ta
42
jihadi
tarar babu kowa a cikinsa, babu yarinya muzainat
babu alamarta, ta duba sama da qasa babu ita ta vace,
ta zubawa cikin xakin idanu cike da mamaki, cikin
nutsuwa ta riqa nazarin xakin.
Tabbas sai dai wani ne ya xauketa, domin
babu yadda za a yi ace bata cikin xakin. Ta yi aikin
banza kenan wani ya shammaceta, don haka duk da
haka ba zata daina farautar yarinya muzainat ba,
kuma a ko wane waje take sai ta nemota ta halaka.
Ta juya a hankali ta fita daga cikin xakin kai
tsaye ta nufi hanyar da zata maida ita turakarta tana
zuwa ta shiga cikin xakinta ta yi saurin cire kayan
jikinta ta saka na barci ta wanke duk jinin da yake
zuba a jikinta ta kwanta akan gado. A lokacin ta ji
wani qwaqwaran motsi dake nuna alamar wani ya
shigo,tabbas tasan babu mai shigowa xakinta kai
tsaye face mahaifiyarta.
Tana xago kai suka haxa ido da shi, ganinsa
ba qaramin xaga mata hankali ya yi ba, cikin sauri
ta miqe suka zubawa juna ido suna kallon-kallo.
“Me yasa bakya jin magana?” ta kauda kai.
“Me na yi kuma?”
“Yanzu za ki ce baki da masaniyar kashe
dakarun nan masu yawa waxanda suke tsaron lafiyar
yarinya muzainat?” Ta gyaxa kai.
43
jihadi
“Ba ni na aikata musu haka ba, kana ganin
tun dana shigo cikin xakina ban kuma fita ba, kuma
yanzu daka shigo banda na ji motsinka babu abinda
zai sani na farka daga barcin dana ke yi” Sarki
masrud ya zuba mata ido yana kallonta.
“Amma kuma duk irin kisan da aka yi musu,
irin saranki ne kuma nayi imani babu wani jarumi
mai zafin nama da zai iya qarar da dakarun dana
saka a lokaci qanqani idan bake ba” Ta miqe a
hankali.
“Baba na faxa maka ba nib ace, ni barci
nake ya kamata ka yarda da maganar dana faxa
maka, yanzu an kashe yarinya muzainat ne?”
Ya girgiza mata kai alamar a’a.
“Kash! Na yi baqin ciki ina ma wanda ya
kai harin ya samu nasarar kashe ta”.
Sarki masrud ya yi shiru ya zuba mata ido
yana dubanta kamar zai kuma magana amma ya fasa
ya kaxa kanshi ya fita abinsa yabar Gimbiya zuhaira
a tsaye a tsakar xakin.
**
Washe gari ma bayan duhun dare ya shigo
har dare ya raba Gimbiya zuhaira ba ta samu ikon
rintsawa ba. Saboda tsananin baqin ciki daya
mamaye mata zuciya,bata samu wani sukuni da zata
44
jihadi
iya yin barci hakan ya saka cikin sauri ta fita daga
cikin gidan sarauta gaba xaya ta nufi xakin bauta.
Gaba xaya dakarun da suke tsaron gidan sai
suka cika da mamaki ganin Gimbiya Zuhaira ta fito
a cikin wannan daren. Bayan kuma sarki ya kafa
doka mai tsnani aka cewar kada aga wani ya fito
yana kai komo a cikin gidan sarauta saboda abinda
ya faru a daren jiya, don haka sarki ya hana a
buxewa kowa qofa komai matsayinsa da kuma
qimarsa.
Fuskar Gimbiya zuhaira a murtuke take
kamar an aiko mata da saqon mutuwa don haka duk
qofar data zo da zara masu tsaron qofar sunyi arba
da fuskarta yanda take a murtuke sai su yi gaggawar
buxe mata qofa jikinsu yana rawa yana kyarma
saboda tsananin tsoronta da suke ji.
Sai data iso qofar qarshe ta samu matsala da
barde markus, ta same shi yana tsaye a bakin qofa
tare da yaransa. Ba tare data shirya ba taja linzamin
dokinta ta tsaya cak! Barde markus ya kalleta cikin
girmamawa yace mata.
“Ya shugabata lafiya, ina za ki haka a cikin
wannan tsohon daren? Ki sa ni cewar fita cikin
wannan daren ke xaya ba qaramin hatsari bane
kuma ki sani cewa sarki ya kafa dokar hana fita daga
45
jihadi
cikin gidan don haka ki sa ni ba za mu iya barinki ki
fita ba” sa’ar da Gimbiya Zuhaira ta ji wannan batun
sai ta yi murmushi na nuna isa tace masa.
“Bafa wani waje zanje ba face wajen abin
bauta saboda neman wata buqata da nake nema akan
wata matsala data hanani barci, kuma ina mai baka
tabbacin idan kaga ban fita daga cikin gidan nan a
yanzu ba to babu ruhi a jikina. Saboda haka duk
wanda yake ganin zai hanani to ya jaraba ya gani”.
Tana kammala faxin haka sai ta zare takobinta tana
kallon Barde markus tace masa.
“Ka saka a buxe min qofa ko kuma na sare
qofar da qarfin tsiya” Ko dajin haka sai hankalin
Barde Markus ya ta shi ainun ya rasa me yake masa
daxi bisa dole ya saka aka buxe wa Gimbiya
Zuhaira qofa ta fice daga cikin gidan da gudu tana
mai yiwa dokinta qaimi kamar zata tashi sama.
Ba komai yasa Barde markus yasa aka buxe
mata qofa face yasan halinta yasan idan har suka qi
buxe mata qofa za ta iya yaqar su kuma za ta kashe
su a banza.
Cikin qanqanin lokaci Gimbiya zuhaira ta
qarasa wajen xakin bauta tana zuwa koda masu
gadin abin bauta suka ga ita ce sai suka riqa zubewa
46
jihadi
qasa suna gaisheta sannan suka buxe mata qofa da
sauri ta shiga ciki lokaci xaya kuma xaya daga cikin
masu gadin qofar ya matso ya kama mata linzamin
dokin ta sauka.
Kai tsaye ta dirge ta shiga cikin xakin bauta
tana zuwa ta faxi a gaban gunki burata ta yi masa
sujada bata xago ba sai zuwa wasu ‘yan daqiqu har
ta buxe baki za ta yi magana sai gunki burata ya tari
numfashinta yace mata.
“Yake Gimbiya zuhaira ki koma gida cikin
kwanciyar hankali ki sa ni cewar har abada babu
wani wanda ya isa ya yi mulkin qasar nan idan ba ke
ba. Kuma babu wanda ya isa ya cutar dake matuqar
kina cikin gidan sarauta. Tabbas mafarkin da kika yi
akan yarinya muzainat gaskiya ne amman za mu yi
amfani da qarfin iko mu sauya qaddara.
Ki yi sa ni cewar bamu bar yarinyar ta zauna
da ku ba sai don yarinyar tana xauke da wata babbar
baiwa ta musamman, wanda qasar nan da jama’arta
za su amfana, kuma ita zata taimaka miki wajen
xauko bulalar tsafi wacce da ita za ki iya mulka
duniya.
Don haka bana son jin wani uzuri daga
bakin ki ko kuma wani abu kawai abinda nake so
dake ki tashi ki koma cikin gidan sarauta, ki kuma
47
jihadi
kwantar da hankalinki, don haka maza ki koma tun
kafin sarki ya kai ziyarar bazata cikin turakarki idan
ya samu bakya nan hakan zai kawo muku savani,
saboda nan da kamar rabin awa zai farka daga barci
kuma yana farkawa ke za ki faxo masa a cikin rai,
domin da fargabarki ya kwana”.
Koda ta ji abinda gunki burata yace, sai
zuciyar Gimbiya zuhaira ta xan yi sanyi ta samu
nutsuwa da kwanciyar hankali don haka ta kuma yin
sujada a gaban gunki burata tana mai yi masa godiya
akan wannan taimakon daya kawo mata, har zata
miqe sai ta ji gunki burata yace mata.
“Yana da kyau ki san dalilin daya saka
babanki sarki masrud ya kawo yarinya muzainat. Ba
komai bane sai don ci gabanki domin kwana nan zai
haxaki da ita ku yi tafiya mai muhimmanci domin
zuwa xauko bulalar tsafi wacce da ita za ki iya juya
duniya a tafin hannunki.
Ki yi sani Gimbiya zuhaira ke kaxai ba ki
isa ki xauko bulalar tsafi ba dole sai da taimakon
yarinya muzainat, hasali ma jininta za a zuba a
ramin akwatin baqin qarfe da aka rufeta idan jinin
ya shiga shi ne akwatin zai buxe. Kuma ita kaxai ce
za ta iya xauko bulalar daga cikin akwatin” Gimbiya
zuhaira ta yi jim zuwa wani lokaci sannan tace.
48
jihadi
“Wai mene ne amfanin wannan bulalar
tsafin a gare ni?”
Gunki burara ya qyalqyale da dariya.
“Yaro bai san wuta ba sai ya taka, ai
matuqar ba ki mallaki bulalar tsafi ba to tabbas ba za
ki mulki qasarki ba, ita bulalar tsafi duk wanda kika
doka da ita walau mutum ko aljani to take zai kama
da wuta ya qone, shin boka kanzul bai ba ki labarin
shu’umin matsafi marganu ba? Bokan daya samar
da wannan bulalar tsafi” Ta gyaxa kai.
“Ya ba ni labarinsa”.
“To ita bulalar akwai wani sirri da duk
duniya babu wanda ya sa ni sai ni, idan kika mallaki
bulala duk wani kangararen aljani za ki sarafa shi,
haka nan duk sanda kika jijjiga bulalar kika kai duka
da ita, to sai wani bala’in ya faru a wata qasa. Haka
nan duk sanda kika xauko bulalar tsafi to sai wani
mashahurin attajiri ko sarki ya mutu” idanun
Gimbiya zuhaira ya fito cikin kaxuwa.
“Kenan idan na mallaketa zan halaka
yarinya muzainat?”.
“Shan ruwa ya fi shi wahala”.
Wannan amsar ba qaramin daxi ta yiwa
Gimbiya zuhaira ba, nan ta koma ta qara zubewa
tana yiwa gunki burata godiya daga nan ta fito daga
49
jihadi
cikin wajen bautar tana zuwa ta kama dokinta ta
xare ta zaburi dokin ta nufi hanyar da zata kaita
cikin gidan sarauta, tana mai gaggawa tun kafin
sarki ya farka daga barcin daya xauke shi.
Cikin sa’a kuwa ta shiga cikin gidan sarauta
kai tsaye ta shiga turakarta ta haye kan gado ta
kwanta. Tana janyo mayafi da zumar rufe jikinta
saboda tsananin sanyi da yake busawa sai kawai ta ji
an turo qofar xakin nata hakan yasa ta yi saurin
runtse idanunta ta yi kamar barci take yi.
Sarki masrud ya shiga cikin xakin yana
shiga ya murxa fitila xakin ta kama xakin ya cika da
haske ya qurawa Gimbiya zuhaira idanu yana
kallonta tana kwance tana faman sharar barci, ba
komai ya saka ya qura mata idanu ba face yana son
ya gano ko yauma ta fita daga cikin turakarta domin
zuwa biyan buqatarta na kashe yarinya muzainat.
Sai daya qarewa xakin kallo tsaf sannan ya
zo ya zauna a kusa da ita a gefen gadon, ya qara
qura mata idanu yana son ganin idanunta sun motsa
ko yayane ya gane cewa ba barci take yi ba amman
sai yaga idanunta sun qi motsawa hakan ya saka
sarki masrud ya yi murmushi ya tashi da zumar ya
fita daga cikin xakin.
50
jihadi
Bisa tsautsayi sai hannunsa ya tava wani
kofin gilas dake kan wani tebur dake daf da ita take
kofin ya faxi qasa ya fashe. Qarar fashewar kofin
yasa cikin sauri ta tashi cikin tsananin zafin nama ta
zare takobinta, ko da suka haxa idanu da sarki sai
tayi qoqarin yin murmushi.
Ganin haka yasa ya koma da baya ya zauna
a kusa da ita ganin haka itama ta maida tatta takobin
cikin kubenta ta gyara zama tana mai yin hamma
alamar ya tasheta daga barci mai nauyi sarki masrud
ya kalli kayan jikinta cike da mamaki yace mata.
“Ya ke ‘yarta meye dalilinki daya saka baki
cire kayan da suke jikinki kin saka kayan barci ba?”
Koda jin haka sai Gimbiya zuhaira ta yi murmushi
saboda ta gane cewa sarki ya yi mata wannan
tambayar saboda yana zarginta akan ta fita cikin
wannan daren hakan yasa ya yi mata wannan
tambayar.
Ta kali sarki tana mai bashi amsa da cewar.
“Ya kai Abbana ka sa ni cewar saboda raina
a vace yake na kwanta a haka ba tare dana sani ba”
Jin maganar data faxa yasa ya yi murmushi kafin
yace mata.
“Nasan haka zata faru, hakan yasa nake
kuma tausasa zuciyarki kuma yake ‘yarta ina kuma
51
jihadi
neman alfarma a wajenki da ki min alfarma dana
nema a wajenki...” Kafin sarki ya rufe bakinsa sai ta
saka hannu ta rufe masa bakinsa,tana kallonsa cikin
murmushi tace.
“Na yi maka alqawari zan yi duk abinda ka
umarce ni dana yi maka, amma kuma nima ina son
ka cima min dokokin dana nema a wajenka, suna
nan ko kuma ba za su samu ba?” Koda jin haka sai
sarki ya yi murmushi tare kuma da saukar da wata
ajiyar zuciya yace mata.
“Tabbas dokokin sun yi tsauri sosai amman
saboda ki samu nutsuwa akan yarinya muzainat na
yarda zan kafa mata wannan dokokin da kika faxa”
Koda jin haka sai Gimbiya zuhaira ta rungume sarki
masrud cikin tsananin farin ciki tana mai yi masa
godiya akan haka, zuwa wani lokaci sai ta janye
jikinta daga cikin nashi tana mai cewa da shi.
“Tabbas yanzu hankalina ya kwanta saboda
haka ba ni da wata buqata yanzu a wajenka face
guda xaya jal” Cikin matuqar mamaki sarki masrud
ya dubi Gimbiya zuhaira.
“Wacce buqata ta rage miki a cikin wannan
duniyar wacce ban san da ita ba?”
“Ina son ka haxani da dakarun da za su je
nemo Abu salhif sannan kuma ka yi min izinin zuwa
52
jihadi
xauko bulalar tsafi wacce matsafi marganu ya samar
nasan kana da tarihinta” Ai kuwa sarki masrud yana
jin haka sai ya soma gyaxa kai cikin tsananin takaici
da kuma kaxuwa da damuwa data mamaye masa
fuska.
“Ba zan yi wannan ganganci ba irin wanda
barde Barhazu ya yi ba wanda yayi asara guda biyu
ya zamana bashi ga tsuntsu kuma bashi ga tarko.
Saboda tabbas idan na barki kika tafi farautar wanan
maqiyin nawa da kuma xauko bulalar tsafi, tabbas
nasan sai na yi nadama irin wacce na yi akan
sadauki Barhuza” Koda jin haka sai Gimbiya
zuhaira tace masa.
“Wane kuma sadauki Barhuza?” Sarki
masrud ya yi murmushi lokaci xaya kuma ya saukar
da murmushi.
“Wannan labari ne mai tsayi, amman kuma
zan datse shi na baki shi a gajarce, don haka ki yi sa
ni cewar koda za ki tafi nemo Abu salhif da kuma
xauko bulalar tsafi ba yanzu ba sai nan da shekaru
ashirin masu zuwa” Gimbiya zuhaira ta dubi
mahaifinta cikin tsananin kaxuwa.
53
jihadi
H
JIHADI 3
ar zuwa wani xan lokaci Gimbiya
zuhaira bata yi magana ba, sai zuwa
can ta xago kai tace wa sarki
masrud.
“Amma kuma me yasa ba zaka barni na tafi
neman su ba sai nan da shekara ashirin?” Sarki
masrud ya yi murmushi.
“Kar ki damu nan gaba zan faxa miki
daliliin faruwa hakan amma yanzu bara na baki
kaxan daga cikin labarin dana ce zan ba ki”.
‘Sadauki Barhuzu ya kasance sarkin yaqin
birnin sin wanda ya ci amanar sarki sa saboda ya
mallaki ‘yar shi ya kuma raba shi da karagar
mulkinsa bisa wannan dalilin ya sa yaje suke haxa
kai da wasu qungiyoyi ‘yan fashi suka haxa runduna
ta mayaqa ya yo gangami na dakaru suka taho qasar
sin da zumar su yaqi sarki baharu zaman.
Koda runduna guda biyu suka haxu a filin
fama sai sarki baharu zaman ya dunga daka masa
harara gami da yi masa wani mugun kallo wanda
yake nuna tsantsar qiyayya wanda nan take fuskar
sarki baharu zaman ta kama yin yatsine.
Yayin da barhuza ya kuma matsowa kusa
da sarki baharu zaman ya kuma matsowa kusa da shi
54
jihadi
hat takai tazarar da take tsakaninsu bata wuce taku
ashirin ba sai barhuza ya tsaya cak a wajen da yake
yana gyara tsayuwar sa irin tsayuwar sarkin daji
wato zaki a dabobin dawa sannan ya kalli sarki
baharu zaman ya taqarqare ya bushe da dariyar
mugunta.
Lokaci xaya kuma ya turvune fuska kamar
an aiko masa da saqo mutuwa ya daka masa tsawa
mai kaxa hantar ciki yace masa.
“Kai tsohon azzalumi ka sani na juma ina
jiran wannan rana da zan huce bautar dana yi a
qarqashin ka na tsawon shekara da shekaru domin
na cika burin zuciyata, babu irin ladabi da