Showing 3001 words to 6000 words out of 20356 words
kaxai ce za ki iya riqe bulalar tsafi,
ko ita yarinyar iyakacinta kawai ta yi amfani da
xigon jininta a jikin qofar mabuxin domin buxe
baqin akwatin, amman bata isa ta xauki bulalar tsafi
ba. Domin xaukar ita bulalar tsafi sai waxanda suka
fito daga cikin jinsi jinin sarauta, kuma ya kasance a
cikin manya dauloli huxu na duniya, Daular farisa
ko Daular misira ko kuma Daular birnin sin ko
kuma Daular Rum, ke kuma jini ce ta Daular birnin
sin.
Ki yi sani cewar ita wannan bulalar an
samar da ita ne ta hanyar amfani da jinin waxannan
sarakai na manya daulolin don haka idan ba jininsu
babu mai iya amfani da ita, ya kuma tabba a cikin
21
jihadi
binciken tsafi ke xaya ce za ki mallaketa. Ita kuma
har kika mallaki wannan bulalar ta matsafi marganu
to za ki mulki duniya ki kuma juya duk wani wanda
yake cikinta. Dole sarakunan duniya su biki su kuma
yi miki biyayya.
Ya ke Gimbiya zuhaira ke da za ki mulki
duniya mene na ki, na fargaba akan wata yarinya da
bata da wani tasiri akan ki...” Ta yi saurin xaga wa
Boka kanzul hannu cikin tsawa tace masa.
“Xan hakkin daka raina shi ne zai tsone
maka ido, tabbas gabana yana faxuwa tun daga
lokacin dana yi mafarki da wannan yarinya, kuma
na ji duk duniya babu wacce na tsana sama da ita,
tabbas ni zan zamo ajalinta”.
Boka kanzul ya sunkuya a gabanta yana
faxin.
“Amman kafin ki kasheta ki bari sai bayan
ta buxe miki baqar akwatin da bulalar tsafi take
ciki”.
Gimbiya zuhaira ta yi shiru zuwa wani
lokaci tana tunani akan maganarsa can ta saukar da
numfashi tace masa.
“Bani da tabbaci akan zan barta ta rayu har
ta girma, domin ni na matsu da ganinta domin na
gaggauta sare mata kai”.
22
jihadi
Boka kanzul ya yi shiru na wani lokaci, ba
tare da ya kuma mata magana ba ganin haka yasa
tace masa.
“Kana iya tafiya idan baka da wata mafita
akan lamarin”.
Koda jin haka sai ya yi mata sallama ya
vace daga cikin xakin. Ya bar Gimbiya zuhaira
zaune tana ci gaba da saqa da warwara a cikin
zuciyarta.
Washe gari tun da safe sarki ya saka aka
kirawo masa sarkin yaqi markus ya sanar masa da
cewar maza ya haxa runduna domin zai yi hawa da
kanshi zuwa wajen babban abin bautar su domin
yana da wata buqata da yake nema ta gaggawa.
Cikin gagawa barde markus ya fita, nan
take ya bada sanarwa kafin kace kwabo dakaru sun
fito cikin shirin yaqi, ko wanne yana haye akan
dokinsa.
Ba a xauki wani lokaci ba sarki masrud ya
fito cikin shiga ta alfarma yana haye akan wani
ingaraman doki, a vangaren gefen hannunsa na
dama kuma Gimbiya zuhaira ce itama cikin wata
kwalliya ta xaukar hankali duk wanda ya dubeta duk
23
jihadi
da qaranci shekarunta sai ya qara kallonta domin
Allah ya yi mata baiwa ta kyawu.
A haka suka jera har zuwa bayan gari daga
nan suka yi sallama da Gimbiya zuhaira ta koma
cikin birni shi kuma suka nausa da dakarun sa da
zumar zuwa wajen babban abin bautar su wanda
daga cikin birni zuwa can tafiyar kwana uku ce a
cikin qungurmin daji da yake tattare da mugayen
halitu, haka nan da hatsabiban ifiritan da aljanu
banda miyagun ‘yan fashi.
Wargi ma waje yake samu, domin wannan
haxaxiyar rundunar ta sarki masrud babu wani
wanda ya isa ya tunkareta bare ya dakatar da ita.
Don haka tunda suka nausa babu wani cin zango har
suka qarasa babbar majami’ar da aka ginawa abin
bauta, shi dai wannan babban abin bautar ya kasance
mafi girma a cikin abin bautar su kuma idan suka zo
wajen shi to lallai sauran qananun abin bautar sun
kasa fitar da su daga bala’in daya same su.
A lokacin da sarki masrud ya qarasa aka
buxe masa qofar shiga ya shiga, yana zuwa ya zube
a gabansa yana mai sujada har tsayin wani lokaci
kafin kuma ya soma ambaton wasu kalmomi na
bauta da suke yi ga wannan abin bautar.
24
jihadi
Tsawon lokaci yana haka, sannan ya saka
aka kawo duk wasu abubuwa da yake yi masa
hadaya na jini aka yanka masa. Bayan an kammala
sai kuma ya soma yin bayyani na abinda yake tafe
da shi.
Bayan ya kammala sai ya ji ance masa
“Tabbas duk abinda ‘yarka Gimbiya zuhaira ta gani
a cikin barci,zai tabbata amman kuma ita zata zama
sarauniyar duniya sai dai ka yi sani cewar ba zata
tava zama ta mulki duniya ba har sai ta mallaki
wannan bulalar tsafi.
Haka nan kuma kaima mulkin ka yana gab
da rushewa, domin maqiyinka Abul salhif a yanzu
xansa Salhif ya kawo qarfi ya zama sadauki, kuma
bashi da wani buri kamar ya kawar da daularka ya
kafa daular musulunci, ya mayar da jama’ar qasarka
ta ma’abota bin tafarkin addinin musulunci”. Koda
jin haka sai hankalin sarki masrud ya dugunzuma ya
zube gaban abin bautar yana neman xaukinsa da
neman ya kawo masa taimako domin yarje masa
wannan bala’in da yake qoqarin tunkaro shi.
“Taimako xaya za mu maka, idan ka
zagaya baya nan za ka samu wata yarinya mai suna
muzainat, ita wannan yarinya ita kaxaice zata iya
kuvutar da kai daga sharin Salhaf, kuma ta kuvutar
25
jihadi
da mulkinka daga komawa hannun maqiyan mu”
Koda jin haka sai sarki masrud ya faxi yana mai
godiya, daga nan ya miqe cikin gagawa zuwa wajen
da gunki ya faxa masa yana zuwa ya samu wata
kyakkyawar yarinya qarama a zaune tana ta faman
wasanta abinta sam babu abinda ya dameta.
Ya kamo hannunta cikin sanyi jiki, bata ce
masa komai ba ta miqe ta biyo bayansa, suka fito
daga cikin wajen bautar yana zuwa wajen da
dakarunsa suke sai ya kama dokinsa ya hau, sannan
ya xora yarinya muzainat a gabansa.
Koda ya qara duban yarinya muzainat sai
ya ji tsoro ya kamashi saboda tunano mafarkin da
‘yarsa Gimbiya zuhaira ta yi.
S
JIHADI 2
arki masrud ya saba duk lokacin da
ya yi ‘yar tafiya ya dawo a guje
Gimbiya Zuhaira ke tarya shi ra
rungume shi tana masa sannu da
zuwa, amman yau sai yaga savanin haka. Domin
yana hangota ya soma xaga mata hannu saboda a
zaton shi bata ganshi ba. Amma sai yaga ta kauda
kai ta turvune fuska.
26
jihadi
Nan da nan ya fahimci dalilin yin fushinta
don haka ya dane abinda yake ji a zuciyarsa ya nufi
wajen da take yana yi mata murmushi, yana
qarasawa ya sauka daga kan dokin sannan ya sauke
Muzainat cikin sauri ya juya ya miqawa wani
babban hadiminsa na gidan sarauta.
Ganin hakan da ya yi shi ne ya hana
Gimbiya Zuhaira aiwatar da qudurinta na zare
takobi ta file kan Muzainat.
Sarki yace wa hadimin sa mai suna sankar.
“A kaita can turakar manya baqi a kula da
ita, itama ta zama kamar ‘ya ta” Samkar ya rusuna
gami da faxin.
“An gama ya shugabana” Nan take samkar
ya kama hannun Muzainat suka soma tafiya.
Ita kuwa bata san lokacin data bi gine-gine
da kallo ta buxe baki tana kallon tsari da kyau na
birnin haka ta riqa kalle-kalle da waige-waige, kana
ganinta kasan ‘yar qauye ce bata saba ganin ginegine irin wannan da idanunta suke kallo a yanzu ba.
Bayan an tafi da Muzinat ne hakan ys
Gimbiya Zuhaira tax an saki fuska ta soma yin
murmushi ta rungume mahaifinta cikin daxin ganin
ya dawo. Ta yi masa barka da dawowa kuma ta yi
27
jihadi
masa murna akan nasara daya samu na kuvutar da
jama’a daga azabar gunki Burata.
Nan sarki masrud ya janye jikinsa daga na
Gimbiya Zuhaira y kamo hannun mahaifiyarta itama
ya rungume cikin farin ciki ta yi masa barka da
dawowa cikin nasara, nan dai suka xunguma su uku
suka nufi cikin fada suna shiga suka tarar an shirya
musu kayan abinci dana sha iri-iri sama da kala
ashiri akan wani dogon teburi nan suka zauna suka
soma cin abinci kuyangi suna zub musu abinda suke
so.
Tsawon lokci suka xauka suna cin abinci
xaya daga cikin su bai ce qala ba sai daga baya
Shadira ta soma magana tana kallon sarki masrud.
“Ran sarki ya jima wai shin ta yaya ka samu
abinda ka fita nema cikin lokaci qanqani, kuma naga
ka dawo tare da wata qaramar yarinya, na kuma ji
ka bada umarnin a karammata kamar ‘yar saki”.
Koda jin wannan maganar sai sarki masrud
ya qyalqyale da wata irin dariya bayan ya yi shiru
ya kwashe duk abinda ya faru a cikin tafiyarsa ya
faxa musu, tun kafin ya qarasa magana Gimbiya
Zuhaira ta murtuke fuska kuma zuciyarta ta soma
tafarfasa kamar zata qone.
28
jihadi
Ta miqe cikin fushi tana kallon sarki tace
masa, cikin vacin raid a qunar zuciya.
“Wannan yarinyar daka kawo mana ita cikin
gidan nan ba komai bace face mugun maciji mai
mugun dafi da zai sareni ya barmin dafinsa a jikina a
nan gaba.
Don haka ina da tabbacin duk duniya bani
da wata maqiya sama da ita, don haka tun daga
lokacin da muka yi ido huxu da ita na samu tabbacin
duk faxin duniya babu macen dana tsana sama da ita.
A nan gaba ita ce zata zamo abokiyar
takarata wajen nema kujerar mulkina, ta kuma riqa
yunqurin raba ni da jama’ata da mutanen da suke
bina suna bani girma suna darajarta ni, domin haka
ina baka tabbacin ni zan kashe ta da hannuna daga
wannan lokacin zuwa ko yaushe”.
Ko da sarki masrud ya ji haka cikin azama
ya miqe tsaye yana dukan teburin dake gabansa da
hannunsa nan take duk abinci da suke ci a kai suka
tarwatse suka zube a qasa.
Cikin tsananin fushi na fusatar zuciya, tunda
Gimbiya Zuhaira suke tare da mahaifinta bata tava
ganinsa a cikin irin wannan yanayin ba na yau, ya
zagaya wajen da take tsaye cikin fushi ya xaga
29
jihadi
hannu zai sharara mata mari amma sai ya fasa yace
mata.
“Mene hujjarki na cewa yarinyar nan za ta
yi duk waxannan abubuwan da kika faxa a nan
gaba”. Gimbiya Zuhaira ta xaga idanunta da suka
kaxa suka yi ja tace da sarki masrud.
“Wata na uku ina mugun mafarki da wannan
yarinya kuma ganin da na yi mata xa zu na gane ita
ce sak take zuwar min a cikin mafarki babu wani
bambanci. Kuma akan wannan mafarkin nawa ne na
tara duk wasu bokaye na qasar nan na yi musu
bayanin akan wannan lamarin bayan kwana uku
suka zo min da amsa iri xaya.
Suka bani tabbacin cewar tabbas wannan
yarinya marainiyace bata da kowa iyayenta sun
mutu kuwa zata dawo gidan ubana da zama kuma
zata samu xaukaka sama da ni harma ya zama ta
kwace komai daga hannuna ta zama it ace
sarauniyar wannan qasar tamu” Koda Gimbiya
ZUhaira ta zo nan a zancen ta sai hawaye ya kwace
mata.
Wannan shi ne karo na farko data tava zubar
da hawayen baqin ciki akan wani abun takaici daya
sameta amman babu shakka Gimbiya ZUhaira tana
30
jihadi
da dakakkiyar zuciya da ba ko wane xa namiji ne
yke da irinta ba.
Cikin tsananin baqin ciki da tashin hankali
tace wa sarki masrud.
“Ashe kai ne da kanka za ka kawo wacce
zata rabani da farin ciki na, ta raba ni da jin daxina
da mulkina ta kuma rabani da matsayina? Ashe duk
irin soyayyar da kaka nuna min tun ina yarinya
qarama bata kai zuciyarka ba? Kuma soyayya da
kake nuna min ba soyayya ce ta gaskiya ba” Sarki
Masrud yana jin wannan kalamin na gimbiya
Zuhaira sai hankalinsa ya tashi ainun yama rasa
abinda yake masa daxi.
Cikin sauyin jiki ya miqa hannu ya kama
hannu Gimbiya Zuhaira yana jin hannunta a cikin
nasa ya qara damqe shi da kyau, yana tsoron kar ta
kwace ta ruga da gudu ta je ta kashe muzainat.
Cikin kwantar da murya, da nuna kulawa ya
soma yi mata magana. Wannan karon maganar ta
shi tafi kama da rarrashi sama da faxa.
“Ki sa ni yake ‘yarta ni kaina ina shiga cikin
xakin abin bauta na yi niyar zare takobi domin na
cire kanta, saboda irin domin bayanin dana samu
akanta to amma kuma sai na kasa samun ikon yin
haka. Haka kuma hannuna ya kasa yin haka, don
31
jihadi
ban samu damar aiwatar da qudurina ba. Na so na
haxa su tare da tsofafin na kashe, tabbas na yi
nadamar xaukota da na yi.
A wannan lokacin da nake faxa miki
magana na riga na makara, domin babu wata amfani
da hakan zai min saboda ban samu ikon kauda ita
daga duniya, amman wata magana da mahaifina ya
faxa min ta ja hankalina yace min dole ne mutum ya
haqura da wani abu kafin ya samu wani abu.
Ki sa ni na jima da wani buri a cikin raina
kuma ina fatan ko ban samu ikon cika shi ba, ke za
ki cika min wannan burin nawa, saboda ya gagari
iyayena da kakanina amman yanzu dana samo
wannan yarinya bokana ya bani tabbacin da
taimakonta ne zan samu ikon cika wannan burin
nawa.
Ki kwantar da hankalin ki kuma na miki
alqawari zan yarje miki duk wani sharinta akan ki,
kuma ke za ki zama sarauniyar birnin nan, amman
kuma ni zan riqeta domin amfani da ita har na kai ga
cimma burina. A yanzu kin yi qanqanta ki san
manufata amman idan kika zama sarauniyar birnin
nan za ki gano ko mene ne wannan burin nawa.
Kuma ki sa ni mun xauki wani hukunci akan
afkuwar hakan, domin a yanzu wannan yarinyar zata
32
jihadi
taso ne bisa horo da kuma irin tarbiya da muka yi
mata kuma duk abinda na koya mata da shi zata taso.
Ni kaina na barta a raye ne domin amfani da
baiwarta wacce duk duniya babu mai irinta.
Ba za samu wannan biyan buqatar ba kuma
sai lokacin da Muzainat ta cika shekara goma sha
takwas ni kuma na yi miki alqawarin da zarar mun
samu cikar burinmu ni da hannuna zan saka kaifin
takobi na kashe ta” Koda jin haka sai Gimbiya
Zuhaira ta soma girgiza kai cikin alamun rashin
gamsuwa.
“Shin ka manta ya Abbana nan da shekara
goma sha takwas a lokacin ka kai shekara saba’in da
xaya a duniya a lokacin kai kuma qarfinka ya qare,
ita kuma Muzainat a lokacin take kan ganiyarta...”
Kafin Gimbiya Zuhaira ta kammala rufe bakinta sai
sarki ya tari numfashinta yace mata.
“Ke kuma fa? Ai kema a lokacin kina kan
ganiyarki fiye da yanzu domin a lokacin kina kan
shekara talatin da biyu, kuma kin samu horo da
qwarewa haka nan kin tsumu da tsumi na sirrin tsafi.
Ina son ki yi sa ni ‘yarta na shirya miki duk wani
abu na zama gagara badau a duniya, domin nan da
wasu ‘yan lokuta za a soma tsumaki a cikin
33
jihadi
kwatarniya na tsafi wanda sai an yi shekara guda
ana miki wannan tsumin.
Sannan sanin kan ki ne cewar a duk faxin
wannan nahiyar babu wata jaruma ko jarumi sama
da ke, ke koma rabin qarfin damtsenki da kuma iya
yaqin ki domin a yanzu kinsa salo-salo na yaqi har
kala tamanin.
Idan haka ne kuma akan wane dalili mafarki
da kuma bayanin bokaye zai tsorata jarumtakarki
shin kin manta cewar; ita qaddara ana sauyata don
haka idan har imaninki da abun bauta Burata bai
raunana ba to babu abinda zai same ki bare har
kumaa wani abu ya gaggare ki” Ta ja numfashi
domin kalamin mahaifinta sarki masrud ya soma yin
tasiri a cikin zuciyarta, amman duk da haka hankalin
Gimbiya Zuhaira bai kwanta ba.
“Ni dai ina so duk da haka ka qara komawa
wajen Gunki Burata akan wannan lamarin, kuma ka
qara ganawa da Bokan ka domin na samu yaqini
akan maganar nan”. Ya zuba mata idanu shima.
“Amman kafin nan zan so ki xaukar min
alqawari akan cewar hannunki ba zai aikata wani
laifi akan wannan yarinya Muzainat”.
34
jihadi
Koda jin hakaa sai hawayen baqin ciki suka
zubowa Gimbiya Zuhaira ta xauki lokaci mai tsayi
kamar ba zata ce uffa ba.
Can zuwa wani lokaci tax ago kai ta kalli
sarki masrud hawayen baqin ciki yana ci gaba da
surta akan kumatunta tace masa.
“Na yarda zan yi maka alqawari ba zan tava
Muzairat ba, amman kuma da sharaxi akan haka kai
ma zaka xaukar min alqawari guda uku, alqawari na
farko ba zaka tava barin Muzainat ta samu horon
yaqi ba koda a cikin garin nan ko kuma wajen gari,
alqawari na biyu ba zaka tava bata wani muqami a
cikin fadarka ba, kuma ba za ka barta tana zuwa
fadarka ba, haka ba zata shiga cikin duk wata harka
data shafi fada ba. Alqawari na uku babu wajen da
zata walau cikin gidan sarauta ko wajensa ba tare da
izinina ba, waxannan su ne dokokin da nake son a
cika min su akan yarinya Muzainat” A lokacin da
sarki Masrud ya ji wannan buqatar ta gimbiya
Zuhaira sai hankalinsa ya dugunzuma ainun saboda
dokokin sun yi tsauri ainun.
Wannan dalilin yasa ya yi shiru na tsawon
wani lokaci ba tare da ya yi magana ba zuwa wani
lokaci sannan ya xago kansa ya kalli Gimbiya
Zuhaira yace mata.
35
jihadi
“Ki ba ni nan da kwana uku zan yi nazari
akan wannan buqatar ta ki kuma ina gargaxin ki
akan kada ki tava yarinya Muzainat a cikin
waxannan kwanakin ki bari har sai mun gama
magana” Koda jin haka sai Gimbiya Zuhaira ta zare
hannunta daga cikin na sarki masrud, ta share
hawayen da suke zuba daga cikin idanunta ta juya
cikin tsananin fushi ta fita daga cikin falon.
Ko data fita sai sarki markus ya kira
shugaban Dakarun da suke cikin gidan sarauta mai
suna barde mauras yace masa ya yi sauri ya je ya
qara yawan dakaru masu tsaron turakar da aka kai
Muzainat, kuma a hana kowa shiga da fita sai waxan
da shi da kansa ya amince musu barde markus ya
sunkuya yace.
“An gama ya shugabana” Ya juya ya fita
cikin gudu-gudu sauri-sauri ya nufi can turakar
baquwar muzainat domin cika umarnin sarki. Ai
kuwa yana zuwa ya hangi Gimbiya Zuhaira ta
qurawa ginin katangar gidan idanu tana kallonta
kana kallon ta kasan kallon nazari take yi da kuma
tunanin yanda zata shiga cikin gidan a asirce ba tare
da kowa ya sani ba.
Tana hango barde markus ya nufo wajen sai
ta yi saurin basarwa ta juya ta nufi turakarta, tana
36
jihadi
shiga cikin turakarta ta soma kaiwa da komowa a
cikin xakin nata zuciyarta cike da tsananin baqin
ciki akan wannan abin da ya faru.
Ba zata tava haqura ta bar muzainat,
maqiyarta a raye ba bazai taba yuwuwa ba saboda
bokayenta ba za su tava faxa mata maganar da zata
zama qarya ba. Koda qarya suka faxa mata ya zama
dole ta kashe yarinya muzainat saboda hankalinta ba
zai tava kwanciya ba matuqar tana cikin gida.
Gimbiya Zuhaira ta kasa tsaye ta kasa zaune,
haka ma kwanciya ta gagareta. Sai kaiwa da
komowa take yi cikin tsananin baqin ciki, tun
lokacin da Allah ya halice ta bata tava samun kanta
a cikin tsananin baqin ciki ba kamar wannan lokacin.
Idan haka ne babu abinda zai hanata fita
cikin shiri domin yaqar waxannan dakarun da aka
saka domin kare yarinya muzainat, ba zata
saurarawa kowa ba a cikinsu har sai ta kashe
muzainat, tabbas idonta idon yarinya muzainat to
kisa ne. bata ga dalilin da zai saka a kawo mata
abokiyar gabarta har cikin gidan da take a matsayin
mai jiran gadon sarauta.
Wani ko wata jaruma bata tava sawa
hawaye sun zuba daga cikin idanunta ba amma ita
zuwanta tasa hawayen baqin ciki sun malala daga
37
jihadi
cikin idanunta. Me zai saka jaruma kamar ta mai
jarumtaka da juriya wace kaf nahiyar shi babu
jaruma kamarta amma wata zata sata cikin baqin
ciki da takaici ya zamar mata dole ta xauki mataki
akan yarinya Muzainat.
Haka ta yi ta kaiwa da komowa tana tunanin
abinda ya kamata ta yi akan wannan matakin da zata
xauka. Ba zata jira gari yaw aye ba bare har ayi
mata sakiyar da babu ruwa.
A hankali hawayen takaici da damuwa ya
kuma malalowa daga cikin idanunta, hawayen da
bata fatan za su daina zuba har sai lokacin da ta
samu damar biyan buqatarta.
Ta fito daga cikin xakinta a hankali ta soma
dube-dube tana nazarin yanda gidan yake, da irin kai
komo da dakarun da aka zuba suna tsaron yarinya
muzainat, a yanzu da take kallon su sai take ganin
kamar wannan ne karo