Showing 3001 words to 6000 words out of 18439 words

Chapter 2 - DUK GIRMAN GONA COMLT

Start ads

14 Aug 2025

179

Middle Ads

mahaifiyarsa ta tashin yin wani auren ne sai ancle dinsa wato kanin mahaifiyarsa ya dauke shi, yayin daya ci gaba da kula dashi tundaga primary 2 har zuwa girmansa. Daga nan kuma ya Allah yasa ya samu gurbin karatu a jami'ar BUK inda suka bashi biochemistry, yaso yaki zuwa amman ancle dinnasa yace yaje yayi, kawai dai yayi addu'a Allah yasa hakan shine mafi alheri.

Haka kuwa akayi inda cikin nasara ya fara katunsa, yayin da aka lika result din first semester mutane sun sha mamaki dan ganin sa da 5.00 points regis, wanda rabon da a samu mutumin da yakawo wannan point din a wannan makarantar an dade, duk kuwa da tarin daliban da take dashi. Wannan kokari da Abbas yayi ne yasa maza, mata, da kuma lecturers nuna mashi kauna wanda hakan yasa cikin kankanin lokaci yayi suna a duk makarantar duk wanda ka tambaya ? Ko kasan Abbas Mas'ud zai cema eh, duk da shi ba wani mai shiga jama'a bane sosai amman haka lamarin Allah yake idan yace kaci ko duka ne wlh sai kaci wannan kenn.

Nan fa yan mata suka fara yi masa ca dan daman su yan matan high institution haka suke da zaran sun ganka kana kawo wuta to shikenn fa ka bani wlh saidai Allah ya tsare ka, dukda dazaran kayi mu'amula da Abbas zakaji ya shiga ranka sbd kyawawan halayensa na gaskiya da rikon amana ga sanin yakamata, wannan yasa Abbas yake da farin jini a gurin mutane. Haka suka yita binsa amman shi bai damu da suba hasalima shi ta karatunsa yake, a hakadai har Allah yasa ya kammala karatun sa, inda wani kamfani suka ce a basu sunn dalibai 10 masu kokari zasu basu aiki, haka kuwa akayi inda sunan Abbas Mas'ud shine farko. Wannan labari ba karamin faranta wa Abbas rai yayi ba, kasancewar yana so shima ya taimaka wa ancle din nasa domin hausawa suna cewa yaba kyauta tukuyci. Angama magana cewa dazaran sungama bautar kasarsu zasu fara aiki a kanfanin Dan liti Brothers campany daya shahara a birnin kano. Anyi posting dinsa ne a Edo State a wani gari mai suna Akoko. Tunda ya tafi garin nan baizo hutu ba amman sunayi waya da ancle da momy sannan yana tambayar lpa yan gidansu, ahaka har ya kammala bautar kasarshi lpa inda ya samu Lambobin yabo a makarantar.

Bayan ya gama bautar 'kasar sane ya fara aiki a kamfanin Alhaji Liti brother's, wanda sannan nen mutum ne a garin kano duba da tarin dukiyarsa da kuma yawan kamfanonin sa, sannan ya kasance mutum ne mai yawan kyauta wanda duk watan duniya sai ya bada tallafi ga talakawa da kuma iyayen marayu, wannan taimako dayake badawa ne yasa sunn sa ya kara daukaka. Duk su goman da aka dauka suka fara aiki a kamfanin Alhaji liti brothers Abbas ya fisu jajir cewa da kuma kwazo gami da girmama na ganshi, wannan dabi'ar sa ce domin koda kwana daya akace ka girmeshi to duk inda ya ganka sai ya gaida kai, ga zuwa aiki akan lokaci wato shi baisan wani abu wai shi african time ba.

Wadannan halaye da Abbas yake dasu yasa Secretary na wannan kamfanin ya kaiwa Alhaji liti shawara cewa "tunda babu manager yanxu a kamfanin mai zai hana a ba wannan yaron manager" Alhaji yace "okh kar ka damu nima ina bincike akanshi sbd ba kai bane mutum na farko daya bani labarin haza'kar wannan yaro ba," ai kuwa haka akayi inda bayan 'yan kwanaki aka ba Abbas manager a wannan kamfanin, farin ciki kamar me haka akayita taya shi murna 'yan uwa da abokan arziki duk da ba wasu dangi garesu dayawa ba, duk a cikin masu tayashi murna babu wanda ya kai 'yar ancle dinsa mai suna Safiya saboda har hada masa liyafa tayi. Anyi taro kuwa yaci ya sha sannan uwar gayya ta dauki micro phone inda ta fara bayani kamar haka: "ina mika godiya ta ga Allah subhanahu wata'ala daya nuna mana ranar da yayana Allah ya bashi babbar kujera a kamfanin su Allah yayi jagora yakuma kara daukaka ameen summa ameen, nan mutane suka kaure da tafi ji kake raf, raf, raf. Taci gaba da cewa ina yiwa dukkan manya baki barka da zuwa da fatan Allah ya maida kowa gida lpa ameen", ba karamin burge mutane tayi ba sbd da kalam datayi kuma banda haka ma ita kanta Safiya kyakykyawa ce first class, duk inda mace takai safiya takai kasancewar hakan ne yasa samari suke rububin ta, amman sam taki kulasu sam, domin ita akwai wanda take so a zuciyarta kuma taki fada ma kowa a gidan mahaifiyar ta tayi-tayi ta sanar da ita menene ? Matsalar amman taki sanar da ita, haka ta hakura ta rabu da ita. Amman duk da haka bata barta hakaba saida tasaka mata ido domin gano wanene wann wanda yarta takeso haka kuma ta'ki fad'a mata sunn shi haka. Aikuwa momy tayi nasarar ganowa wanda yarta take masifar so, bawani bane face Abbas, dagano hakanne wata rana tazo wucewa xata je kitchen toh dayake kofar dakin zainab ta na awajen sai tajita tana magana kasa-kasa, sai ta dan kara kunnenta don tayi mai take cewa sai taji tana cewa wlh Farida indai har ban auri Yaya Abbas ba Mutuwa zanyi sbd wani bala'in sonsa danakeji yana taso mani daga karkashin zuciyata, momy bataji abunda faridar tace ba, takara gaba tana mai cewa a cikin zuciyarta daman Abbas kikeso shine bazaki sanar daniba toh duk yanda zanyi ki aureshi sai nayi kodan ki dauwama a farinciki, ta bar wajen tana mai cike da farin ciki, wuni tayi cike da farin ciki kai kace ma tafi yar tata farin ciki, ta kagara mijinta ya dawo domin ta sanar dashi abinda yake faru, dan acewarta baza iya fada mashi ta waya ba sai yadawo daga tafiyar dayayi.

Al'amarin Abbas kuwa sai kara samun daukaka yake yi kasancewar sa akwai mutunta customer, da darajta su wannan yasa manya mutane turuwa daga garuruwa da yawa, ai kuwa Alhaji Liti ya 'kara masa albashin sa ijuwa naira dubu dari bakwai {700,000}, duk wata sannan aka bashi mota da kuma gida kasan cewar haka ka'idar take.

Zaune yake a gaban ancle din nasa yana fada masa tagomashin daya samu a wajen aiki da kuma daukakar dayake samu, ancle din nasa ya fara magana kamar haka: "to yanzu abunda ya rage maka shine kayi aure Abbas kaima naga zuri'ar ka, kaga ka girma yanzu kusan 35yrs kaga ko ai kai ba yaro bane yaka mata kaima ace ka samu wadanda zasu rinka yi maka hidima" yace toh ancle in sha Allahu zanyi kwanan nan ma, yace toh ai shikenn Allah ya nuna mana ace Ameen cike da kunya kasancewar sa daman akwai kunya. Ana cikin haka saiga momy ta fito daga daki tanemi kujera 3sitter ta xauna, tace "wai alhaji mai ke gudanane kaida dannaka" alhaji yace "maganar aure ce mana nake masa ace ya girma amman yaki aure anya rayuwa tayuwu a haka kuwa", momy tayi murmushin jindadi domin kayanta ya kwance a gindin kaba ga damanan tasamu, tace "Alhaji ai komai lokacine kila zainab yake jira ne ta kammala exam dinta, dan inba hakaba ni bantaba ganinshi da budurwa ba," Alhaji yace "aiko danafi kowa jin dadi wlh kinga ni zanyi lefe kuma ni zanyi kayan daki," ya karkato da kallonsa ga Abbas wanda duk maganganun dasuke kansa na kasa sbd tsabar kunyarsu dayake ji, ya dago da kansa yayi dan mirmushinsa wand ya saba yace "Ancle ai ba wai zainab ba koma wacece kace na aura wlh bazan tsallake umarninka ba, sbd kagama min komai a rayuwata." Alhaji yace "a'a idan kana da wadda kakeso kayi mani magana ni kuma ko 'yar gidan wanene insha Allahu zan tsaya maka," Abbas yace "ni banida kowa," tun dazu sai yanzu momy tasa baki tace "a'a Abbas wlh bawai tirsasaka zamuyi ba idan kana da wadda kakeso kawai kasanar damu ba matsala duk da harga Allah momy bataso fadin maganar ba amman bata dayanda zatayi, yace "a'a momy zabinku ai nima shine nawa," aikuwa yana fadar haka momy ta sauke wata nauyayyar aziyar zuciya. Har ga Allah tanayi wa yar tata sha'aawar samun miji kamar Abbas sbd nutsuwarsa, hankalinsa, kyawunsa, da tsabtarsa ga fara'a kamr gonar auduga amman fa ga wanda ya sani, wannan halayenne yasa momy takeyi wa diyarta fatan samun miji kamar Abbas.



2 days later da yin magana tskanin Ancle da Abbas, ancle yayi wa Abbas waya yace zasu je katsina ziyara zuwa wajen wani abokin sa inda yake sanar dashi cewa kwana biyu zasuyi su dawo, amman bazasu je da Zainab ba sbd sun fara waec shiyasa bazasu je da ita ba amman za'a tafi da kanin ta, Ancle yaci gaba da cewa "da zarar mundawo kuma za'a sanya ranar bikinku ba wani lokaci mai tsawo xamusaka ba," nan dai Abbas yayi masa godiya ya katse kiran. Sun fito zasu tafi ne Zainab ta fito tana kallon su, tace "wlh Momy ji nake tamkar idan kuka tafi kun tafi kenn bazaku dawo ba," mahaifiyarta ta kalleta tayi murmushi duk da itama jikinta yayi matukar sanyi da jin wagga batu tace "kiyi hakuri in sha Allahu zamu dawo lapia kedai kiyi mana addu'a kawai kuma ki kula da kanki kiyi karatu banda shashanci", tace "to umma Allah ya dawo daku lpa." Yayin da Momynta ta bita da wani kallo irin na bankwana. Tana kallon su dai suka ja mota suka fice daga cikin harabar gidan, ita kuma ta fashe da kuka yayin data durkushe a kasa tana kuka mai tsuma zuciya, gwanin ban tausayi.......


*Abubakar saleh Al~Quyraemey*

_{Young Writer}_
[6:19AM, 6/7/2019] Abue Saleh Al~Quyraemey: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

*DUK GIRMAN GONA*

_{Akwai kunyar 'karshe}_


©2019


👨🏻‍💻👩🏻‍💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.
_____________________________________


*👉Page 7-8*


*Author.......🖋*

*Abubakar Saleh Quyraemey*

```@Facebook Abubakar Saleh AlQuyraemey```



*DEDICATED TO*

*Zamani Writers Association Group*

*Bismillahir rahamanir rahim*

Tana cikin kukan nanne taji gabanta yana mata dukan uku-uku tamkar zuciyarta zata fito, tarasa meke shirin faruwa da ita kawai sai ta fara fadar:

"Innalilahi Wa inna ilaihirraji'un acikin zuciyar ta"

Aiko bata jimaba bacci barawo ya dauketa. Can cikin baccin ta tajiyo ringing din wayar ta, ta bude idanunta da kyar ta mika hannunta kan table din dake gefen bed dinta, tayi duba izuwa kan screen din wayar taga Sunnan Abban tane ke yawo tayi saurin dagawa da Sallama, an amsa sallamar amman abunda ya bata mamaki shine a madadin taji muryar Abban nata sai taji muryar wani daban, jitayi ance maza-maza kizo Asibitin Aminu kano Teaching Hospital yanzu-yanzu, jitayi kamar mafarki takeyi ta murza idanunta dan farkawa amman ina sai taga da gaskene bawai mafarki take ba sbd haka tace "Mai yafarune da Abban nawa ne? Kuma ina Momy na?"

"Yace kedai kiyi maza kizo muna nemanki Emergency site"

"Tace toh gani nan zuwa"

Kiran number Momy tashiga yi amman kashh! an sanar mata da cewa wayar data kira a halin yanzu a kashe take saboda haka ta hakura. Tashi tayi daga kan gadonta tunanunnuka nata mata yawo acikin nazarinta komai ya faru da Abbana? Da Umma, tayi shiru ganin bata da wanda zai bata wannan Amsar yasata shiga bandaki ta watsa ruwa a gurguje ta fito, tasaka wata atamfa England wax dinkin yayi mata kyau masha Allah, snn ta dakko zunbuleliyar Abayar ta tasaka ta saka flat shoe, sannan ta dauki hand bag dinta har takai bakin kofar fita daga gidan sai kuma tajuyo ta dawo, ta dauki phone dinta ta fito ta saka dan mukulli ta rufe gidan, tafara tafiya da d'an sauri domin ta karasa babban titi, tana karasawa kuwa tayi sa'a ta samu mai Adaidaita Sahu

"Tace mashi Aminu Kano Teaching Hospital zaka kaini"

"Yace toh shiga muje"


••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••

Abbas na zaune haka kawai yau yatashi jikinsa ba kwari dukda yasan lapiar sa kalau amman jiyake jikinsa ba kwari, haka dai yaci gaba da yan rubuce-rubucen sa cikin karfin hali da jarumta, yana cikin wannan rubuce-rubucen ne yaji wayarsa ta soma ruru, ya daukota dan duba wake kiransa dubawar dazaiyi yaga number Ancle ce,

"Ya daga kiran cikin girmamawa da sallamar sa"

"Daga can bangaren yaji ance duk abinda kake ka bari kazo Aminu kano Teaching Hospital muna nemanka emergency room"

"koda yaji haka nan take jikinsa ya bashi ba lpa ba, yace ina Ancle din kuma, mai ya faru da shi?"

Daga can bangaren mai maganar yace "Kawai kazo koma menene kaji daga baya"

"Yace ohk toh ganinan zuwa"

Tashi yayi jiki ba kwari ji yake kamar bazai iya taka kasa ba sbd kasalar dayakeji a jikinsa, futowa yayi daga offishin sa wani offishin ya shiga wanda yake gaf danasa, ya tura kofa da sallama a bakinsa,

Aka amsa sallamar tasa hadi da cewa "come in"

Shiga yayi ya tsaya a tsaye yace "Barka da aiki Ranka ya dade"

Mutumin yace "Have a sit mana Abbas"

Abbas yace "Ba zama nazo ba wlh kiran gaggawa akayi mani daga Asibin Malam Aminu Kano wai duk abinda nake nabarshi nazo yanzu-yanzu nan shine nazo na sanar dakai"

Mutumin yace "Ohk ba matsala Allah ya tsare"

Abbas yace "Ameen thumma Ameen"

Ya juya ya fice daga offishin cike da tunanunnuka, karasawa yayi park space na kamfanin ya sa key ya bude motarshi ya fice daga harabar asibitin ya doshi Asibitin Malam Aminu Kano.


*AMINU KANO TEACHING HOSPITAL {AKTH}*

Tana can tana tunani taji mai Adaidaita yana cewa "Malam munzo fa"

Firgigit tayi tadawo daga duniyar tunanin datakeyi, ta bude jakarta ta bashi kudinsa ta fice ta shiga harabar Asibitin ta doshi Emergency site kasancewar kana shiga Asibitin zakaga indicated board ma'ana Allon dake dauke da taswirar asibitin, wani Dr ta hango ya fito daga emergency room din tayi, aiko da d'an gudu ta hada kada ya bace mata ta karasa tana dan haki

"Tace yauwa Dr nice wadda aka kira dazu akace nazo nan asibitin"

"Yace kece zainab Abdullahi?"

"Tace eh nicee"

"Yace mata toh zomuje"

Inda ya fito nan ya nufa, itama tabishi a baya suna shiga ciki ta kame saka makon abunda ta gani, ba wani abu tagani ba face Abba a kwance koh motsi bayayi ansa masa oxygen a hancinsa

Juyowa tayi a fusace ta shagi Dr tace "mai kukayi wa Abbana! Mai kukayimasa........." Ta fashe da kuka

Ana cikin haka ne shima Abbas ya shigo dakin ganin abinda yake faruwa ne yasashi saurin karasawa gurin da zainab take ita da Dr yana fadin lpa meyake faruwa zainab?

Ganin dayayi tana kuka yasa ya rikice ya juya akalar tambayrsa ga Dr yace "Mai ya farune likita?"

Likitan bai iya ce masa komai ba sbd muguwar sha'ka dayaji, duk da yake namijine amman ya gagara kwacewa daga hannun Zainab, idanunnan sunyi jajir kamr gauta, ganin da Abbas yayi likitan ya fara tarine yasa yaje ya fincikeshi daga hannun Zainab din aikuwa yayi maza ya jingina da bango yana haki sbd tsabar sha'ka dayaji, ita kuma Zainab ta karasa gurin Abba da gudu tana fadin "Mai sukayi maka Abba tana jijjigashi?"

Sai a sannan hankalin Abbas yakai ga inda Abba yake a kwance shima ya karasa cikin mutuwar jiki, koda yaga irin halin da Abba yake ciki, shima sai zuciyarshi ta karaya ya fara zubar da hawaye, suna cikin wannan halinne wani likitan ya shigo ya karaso wurn dasuke yace masu kuzo muje office nayi maku bayani.

Haka suka bi bayan wannan likitan badan ransu yasoba amman babu yanda suka iya, suna shiga office din ya nuna masu wasu kujeru guda biyu masu facing din juna "Yace have a sit" suka zauna suna mai zura masa idanu danji abinda zai fada masu dukda har a snn basu daina zubar da hawaye ba.

Dr ya nisa yace "Dazu aka bugo mana waya cewa mukawo agajin gaggawa, wata mota mai kirar fijo 406 tayi taho mugama da wta tirelar daukar kaya kafin akai Bichi, inda bamu bata lokaciba muka tada ma'aikatan mu sukaje wurin saidai koda sukaje masu tirelar sun gudu sun bar motarsu ita kuma 406 din mutum biyune suka mutu wani karamin yaro da kuma babba mace...." Ai kafin Dr ya karasa maganrshi saiji sukayi Zainab tayi wata kara ta kife a kasa ko motsi bata yi.

Nan fa hankalin Abbas yayi kololuwar tashi ya mike tsaye shima yaji kafafunsa sun kasa daukar gangar jikinsa sai ya fara fadar:

"Ina lillahi Wa innah Ilaihirraji'un"

Bashiri ya zauna kan kujerar yayin da likitan ya tashi daga kan kujersa ya kira wasu nurses su biyu suka dauki zainab suka fice da ita izuwa emergency room, domin cetoh rayuwar ta.

Ya dan samu nutsuwa saboda hailalar daya dinga yi sbd haka yace da Dr "Shifa Ancle"

Likitan yace "Shi ya bugune a kansa inda kansa ya tabuwa amman banda nan babu wani rauni a kansa, gobe xamu yimasa aiki insha Allahu"

Abbas yace "toh Allah ya kaimu" likitan yace "Ameen dai"


Zanci gaba Insha Allahu.


A mystery story just keep on following me.




*Abubakar Saleh Al~Quyraemey*

_(young writer)_
[6:19AM, 6/7/2019] Abue Saleh Al~Quyraemey: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

*DUK GIRMAN GONA!!!*

_{Akwai kunyar 'karshe}_

©2019


👨🏻‍💻👩🏻‍💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.
_____________________________________


*Page 9-10*


*Author.......🖋*

*Abubakar Saleh Quyraemey*


```@Facebook Abubakar Saleh AlQuyraemey```



*DEDICATED TO*

*Zamani Writers Association Group*



*Bismillahir Rahamanir Rahim*



: بِسْــــــــــــــــــــــمِ اَللّهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِِ"
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا نُودِيَ لِلصَّلَاةِ مِن يَوْمِ الْجُمُعَةِ فَاسْعَوْا إِلَىٰ ذِكْرِ اللَّهِ وَذَرُوا الْبَيْعَ ۚ ذَٰلِكُمْ خَيْرٌ لَّكُمْ إِن كُنتُمْ تَعْلَمُون
Alhamdulilah today is another beautiful day. Haza yaumul akbar; yaumul shukur, yaumul salama! Alhamdulillahi ala ni'matil Islam. May Allah shower His endless blessings upon U my fan's & Ur family.
Jumu'at Mubarak


.........Fita sukayi daga office din, koda suka fice basu zame koh ina ba sai emergency room inda Zainab take kwance bata koh motsi tamkar gawa, kusan a k'alla likitoci biyar ne a kanta, amman ankasa shawo kanta, sundau lokaci mai tsawo Allah cikin ikonsa, taja wani gauron numfashi aiko ba karamin dadi Abbas yajiba, kasancewar duk abunda yake gudana yana kallonsu ta mirror din dake dakin, ya samu wuri ya zauna yayi "Hamdala Ga Allah Subhanahu Wata'ala" ya samu wuri ya xauna.
Koda ya dan jima a zaune sai kuma ya wani xabura yayi dakin da Ancle yake jinya, shigarsa keda wuya kuwa yayi dai-dai da farkawar da Ancle yayi daman allurar bacci sukayi masa, kuma yanxu ta sakesa, saboda haka Abbas ya karasa gurin Ancle da sauri yana mai cewa "Ancle ya jikin naka?" da k'yar ya bude

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login