Showing 6001 words to 9000 words out of 18439 words
bakinsa yace "Abbas ina kanwarka?" Abbas yace "Ancle tana can itama ba lpa sakamakon ganinka da tayi a wannan hali" Ancle yace "Toh ka saurareni kaji abinda zan fada maka ga kanwarka nan ka riketa amana ina ji a jikina cewa bazan tashi daga wannan kwanciyar ba shiyasa nakeso tun kafin lokacina ya kure nakeso na baka wasiyyata, ko bayan babu raina karkuyi jinkiri wajen aurenku, kaje can Funtua wajen Kanin mahaifinku Alh Lawal ya zama maka waliyyi, ita kuma Zainab k'anina Shehu ya zama mata waliyi dan Allah ka bata hakuri ka lallasheta, ka tarairayeta kaga har yanxu ba wata babba bace...... yana zuwa nn a zance sa tari ya sarkafeshi ya fara aman jini da sauri Abbas ya tashi yana kiran Doctor! Doctor!.......... Amman ina kafin su dawo ai tuni rai yayi halinsa.
Abbas ne ya shiga office din likitan bako sallama yace "Dr yafa farka kuma yanata aman jini"
Dr yace "Subhanallahi" ya dauko stethoscope yace "Muje na gani"
Karasawa dakin sukayi inda Dr yayi 'yan gwaje-gwajensa, ya juyo dubansa izuwa Abbas yace Malam Abbas saidai hakuri amman abbanku shima ALLAH yayi mashi cikawa.
Ai Abbas jin maganr yayi kamar a mafarki, ya juyo a fusace ya shaki kwalar Dr yace cikin k'araji "Ya akayi kuka barshi ya mutu, meyasa! Meyasa!!"......... Sai kuma ya fashe da kuka ya durkushe a kasa bisa gwiywoyinsa ya fashe wani marayan kuka mai tsuma zuciyar mai saurarenshi.
Tasowa Dr yayi ya karaso inda Abbas yake yace "Hakuri zakayi sbd Wanda ya fimu sansa shine ya karbeshi mu yanzu abunda yafi dacewa mu shine muyi masa Addu'a amman ba kuka ba"
Wannan magana da Dr yayi wa Abbas ce tasahi ya tsagaita da kukan dayake amman har yanzu hawaye suna shatata bisa kan kyakykyawan kuncinsa, ya mike tsaye yama rasa ina zai sa kansa yaji dadi, sbd da haka ya bar dakin ya fito ya samu wata bishiya ya zauna a karkashi ta, yana mai tunano rayuwar dasukayi shida Ancle dinsa da iyalansa, rayuwa ce mai cike da so da k'auna gwanin bansha'awa, dan idan ba fada maka akayiba zaba kace ba dan gidan bane sbd yanda Ancle din nasa yake matukar ji dashi, amman duk da haka bai bashi damar ya sangarce ba, haka abun yake a 'bangaren Momy itama tana iya kokarinta na ganin ta ba Abbas tarbiyya tamkar 'ya'yan data haifa a cikinta, Abbas yana cikin wnn tunani ne yaji an dafa kafadarshi ya dago a razane!
Dr yagani tsaye kyam a gabanshi, Dr "Yace da Abbas angama saka gawarwakin acikin mota kawai kai ake jira"
Abbas bai tanka mashiba, shima Dr bai damuba yana gama fada mashi ya kara gaba izuwa inda ake ajiye motoci ya shiga cikin wata Ambulance yana jiran karasowar Abbas.
Abbas dai yaga ba wani sarki sai Allah haka ya tashi jiki ba karfi ya karasa inda wnn ambulance din take ya jagaya gaban motar yace wa da Dr "ina zainab koh a nan zamu barta"
Dr yace "Eh zatafi samun kulawa a nan kawai shiyasa bamu sallameta ba amman jikin nata" "Alhamdll".
Abbas yace "Toh shikenn" ya bude gaban motarshi ya zauna mazaunin driver, koda Dr Hashim yaga abunda Abbas yake shirinyi, sai yayi sauri ya fito daga ambulance dinn yace da driver "Ka biyo mu a baya" kawai abinda ya fada masa kenn ya fice ya karasa inda Abbas ke kokarin tada motarshi.
"Yace Mal. Abbas dan bude mani motar mana"
Abbas ya bude masa ba tare yace uffan ba, Dr Hashim ya zauna, Abbas kuma ya tada mota yana tuki snnu a hankali har Allah ya kawosu kurna masallaci wnda annan gidan Ancle yake.
Lokacin da suka kaso layin Abbas yasha mamaki sbd cikar da layin yayi ba masaka tsinke da kyar suka iya karasawa kofar gidan mutane suka taimaka aka fito da gawarwakin aka shiga dasu cikin gidan domin yi masu wanka.
Abbas bai kara cika da mamaki ba saida ya shiga gidan yaga mahaifiyarsa da 'yan uwanta, da kuma 'yann uwan momy anata koke-koke wasu kuma wadanda suka san abinda suke suna ta yi masu addu'a wanda dama haka Annabinmu, Annabi Muhammad S.A.W ya koyar damu.
Abbas dai shigowa yayi cikin gidan sbd kidimewa da rudewa da yayi baya ganin ko gabansa, Ummanshi tana tayi mashi magana amman ina baimasan tanayi ba, ya wuce izuwa dakinsa ya fada kan gadonsa ya limshe idanu jiyayi wasu hawaye masu zafi suna zubo masa akan kumatunsa bai damu daya sharesu ba, yana cikin wannan haline yaji Ummansa tana cewa "Abbas ance kafito kayi masu sallama za'a wuce dasu"
Tashi yayi da kyar yaje inda akayi wasu Momy da Ancle sutura yayi masu Addu'a sannan aka fita d gawarwakin nasu waje domin a sallacesu.
Babban limamin masallacin juma'a ne ya sallaci Mamatan, inda bayan angama sallar ne, dangin mamatan suka rushe da kuka harda masu na shiga uku na Lalace.
Wani dattijone datun d'azu suke shigi da fici daga wani d'aki zuwa tsakar gidan yace, "ya salam! Habadai Dan ALLAH, wannan kuka bashine zaidawo mana dasu duniyaba, amatsayinku Na musulmai wannan kururuwar da ihun bai kamacekuba, addu'ar ku suke buk'ata agareku amatsayinku Na 'yan uwansu, kukanmu bazai dawo mana dasuba, amma hak'urinmu da nutsuwarmu zaisa murok'a masu gafarar UBANGIJIN Al'arshi.
Dan ALLAH muyi hak'uri hakanan, ALLAH ya gafarta masu, yabamu hak'urin rashinsu.
Tunda dattijon yafara magana gidan yayi tsit, wannan nasiha tashi tayi tasirin saka kowa yin shiru, saidai shashshekar kukan wasu da ajiyar zuciya.
Ankai mamatan gidansu na gaskiya, inda kowa ya dawo yana alhinin mutuwar su, kasancewar Ancle mutum ne mai hakuri da kyauta, haka zalika matar shi Momy anata yabonta sbd ko leke ma baruwanta dashi balle Aliyu Haidar wanda kwata-kwata bazai wuce 5yrs ba, wnn dalilai yasa mutane suke kyautata masu zaton rahama. Bayan an dawone Abbas ya zauna kofar gidan yana kar'bar gaisuwa.
To saimuce ALLAH ya gafarta masu, da dukkan 'yan uwa musulmai dasuka rigamu gidan gsky.
*7days ago*
Ayau akayi addu'ar bakwai d'in Su Momy, Ancle Da kuma Aliyu Haidar, bayan lafawar komai kuma shak'ik'ansu Abbas suka had'a taro Na family.
Wanda a lokaci zainab ta dan warware sosai dan har an sallamota daga asibiti, Mal. Shehu ne Kanin Ancle shiya fara gabatar da sallama agaresu, yayi doguwar addu'a ga mamatqn, harmada sauran al'ummar musulmi dasuka rigamu gidan gaskiya.
Daga nan yaja dogon bayani akan gado da kuma biyama mamatan bashi da kar6o abinda sukebi, yaymusu nasiha da nusar dasu muhimmancin rik'e zuminci, da kuma addu'oi ga mahaifansu, yanda zasu rik'e maraicinsu harya amfanesu.
Daga nan kuma sai yayi magana akan wasiyyar daya bari na Auren Abbas da Zainab, duk mutanen dasuke wajen sunji dadin haka, amman duk cikinsu basu kai Umma farin ciki ba sbd bakinta kin rufuwa yayi don murna, haka dai taro ya wace cewa ranar 40 din su Ancle za'a daura auren Abbas da zainab. Sunso umma ta zauna, amman umma fur taki a cewarta "Mijinta yana can yana kewarta sbdn haka bazata xauna ba".
Rana bata k'arya yaune ranar 40 su Ancle kuma shine Ranar daurin auren Abbas da Zainab. Abbas yayi kokari dan har dubai sukaje shida Zainab din yayo mata lefe sannan ya shiyo mata furnitures, Mal. Shehu yaso shiyayi furnitures din amman Abbas ya hanashi yace "Shi zai yi mata komai" aiko nan Mal. Shehu ya fara samasa Albarka........
Bayan an kammala Addu'ar 40 dinne, dubban jama'a suka shaida daurin auren Abbas Mas'ud da Amaryarsa Zainab Abdullahi wanda ya samu halartar manyan yan kasuwa ciki kuwa harda Alh Liti Kulkul Mamallakin campanonuwa da gidajen mai masu inkiya da Liti Brothers.
An biya sadaki akan naira dubu dari 500 lakadan ba ajalan ba, inda abokan ango da yan uwansa suka rika tayashi murna, har dare yayi inda Umma ta tarasu tayi masu nasiha, bayan ta gama ne Mal. Shehu da Alh Lawl suka dora tasu nasihar.
*5 year ago*
Tafiya tayi tafi, lokaci yaja, shekaru sun fara lulawa, amman haryanzu Zainab ko bari batayiba hankalinta yayi matukar tashi, dan gani take kamr matsalar daga gareta ne, tq fara damun Abbas kan cewa suje asibiti, da yayi mata taurin kai amman daga baya ta shawo kansa ya yarda.
*Emirate hospital* Dake a Nasarawa G.R.A sukaje domin check up, likitan yayi dube-duben da zaiyi ya sanar dasu cewa "Babu mai matsala a cikinsu" duk da haka hankalin Zainab bai kwanta ba gani take kamar Abbas zai karo mata kishiya ita kuma har ga ALLAH ta tsani kishiya acikin gidan ta, Abbas ya fuskanci yanayin damuwar ta.
Sbd haka wata ranar week end suna zaune yana kallon TV, itama tayi kuri tana kallon TV amman a zahiri ba kallon take ba tana can ta luluk'a duniyar tunani, Abbas yace "Wai ni Zainab yaushe zamuje Funtua ne domin muyi ziyara?" Ji yayi tayi shiru batace komai ba, ya sake maimaitawa a karo na biyu kai har saida yayi maganar sau uku amman batasanma yanayi ba.
Takowa yayi har wajen datake zaune ya rungumeta tsam a jikinsa yace "Wai ni meke damunki ne sweetyn fada mani damuwarki naga two days dinnan kin rikice feye da da, bata boye masa komai ba tace wlh akan haihuwarnan ce, banason ka kawo mani kishiya wlh, yayi murmushi yace da gaske yace toh ai shikenn nikuma nayi maki wannan alkarin cewa "Da yardr ALLAH da Izininsa Bazan sake aure ba keda kishiya sai dai amakwafta fa sweety" Ba karamin dadi taji ba sbd wnn kalamai dadi mata sbd hak tace "Ina Alfahari dakai Habiby"
Tun daga wannan lokaci ta saki jikinta, yayin data ci gaba da harkokinta kamr da amman lokaci zuwa lokaci idan ta tuna cewa bata da d'a ballentana jika tana shiga damuwa kwarai da gaske.
Ana cikin hakane Abbas ya dawo da Albishirin cewa ya biya masu Aikin hajji shida ita dakuma umman sa, haka kuwa akayi inda ALLAH cikin ikonsa ranar tafiyarsu tayi Zainab tafi kowa murnar zuwan wannan rana, sbd haka sukaje Aminu kano Airport suka shiga jirgi ya garzaya dasu sai birnin jidda.
Bayan sunje ne Zainab ta jage damtse dare da rana Addu'ar Allah ya basu haihuwa suke, har lokacin dawowa gida yayi badan sunso ba suka dawo gida Nigeria ba.
*10 years ago*
Tun Hajiya Zainab tanasa ran cewa zata haihu hartafara fidda rai, toh shine fa ta bijiro da maganar cewa aje gidan marayu. Wannan shine asalin tarihin su.....
A mystery story just keep on following me.
*Abubakar Saleh Al~Quyraemey*
_(young writer)_
[6:19AM, 6/7/2019] Abue Saleh Al~Quyraemey: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?
๏ปฟ
*DUK GIRMAN GONA!!!*
_{Akwai kunyar 'karshe}_
ยฉ2019
*A mystery story just keep on following me.*
๐จ๐ปโ๐ป๐ฉ๐ปโ๐ป
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
โโWษ ษสษ ษฆษสษ tัณ ษษucษtษ, Mัณtiัตษtษ ษษณษ ษษณtษสtษiษณ ัณuส สษษษษสเธฃโ.
_____________________________________
*๐๐ผPage 11-12*
*Author.......๐*
*Abubakar Saleh Quyraemey*
```@Facebook Abubakar Saleh AlQuyraemey```
*DEDICATED TO*
*Zamani Writers Association Group*
: ุจูุณูููููููููููููููููููููููู
ู ุงูููููู ุงูุฑููุญูู
ูู ุงูุฑููุญููู
ูู"
ุฃูุนููุฐู ุจูุงูููููู ู
ููู ุงูุดููููุทูุงูู ุงูุฑููุฌููู
ู
I seek refuge in Allah from Satan the outcast.
*WACE CE HAJIYA LAMI*
Lami dai shine sunanta na Gaskiya, ita kadai Allah yabawa Mahaifanta Alh Sani da Hajiya Hafsat, sbd haka ne suka d'auki son duniya suka dora mata, komai tayi daidai ne acewarsu basu da kamrta a wannan duniyar, wanda a sanadiyyar hakane ta taso da mummunar ak'ida.
Shidai Alh Sani k'ani ne ga Mahaifin Alh Mubarak, wanda akafi sani Liti kulkul ko kuma Liti Brothers.
*WAYE ALH MUBARรK*
Sunanshi na gaskiya Mubarak Muhammad Amman anfi kiransa da Dan Liti, ya taso cikin gata, gaba da baya, kasancewar sa shi kadai ne gurin iyayensa Hajiya A'isha dakuma Alh Muhammad Dan Maliki, amman duk da haka idan yayi badai-dai yana gane kurensa, wannan ne yasa yazama abin alfahari sbd nutsuwar sa dakuma hankalinsa yana da farin jini kwarai da gaske sbd kowa nashine ba ruwanshi da kyamar talaka da wasu masu kudin keyi. Wannan halayya tashice kesawa mutane suji suna son shi. Wann kenn......
Alh dan Maliki ne ya gida katon gida wanda za'a iya kiransa da Aljannar duniya duba da yanda ya kawatu matuk'a gaya, part biyu ne a gidan cikin gidan, nashi da na kaninshi Alh Sani, bayan ankammala gidanne Alh Dan Maliki ya bukaci kanin nashi daya baro wnn gidan ya dawo nasu haka kuwa akayi inda yayi biyayya kamr yanda iyayensu kamin su rasu suka bammasu wasiyya.
Basu dade da dawowa ba ALLAH yabawa Hajiya A'isha haihuwa, inda ta haifi kyakywan danta namiji, Alh Dan Maliki yayi murna matuk'a da gaske, inda sbd dadin wnn haihuwa ya bawa mutane 15 kyautar kujerar hajji.
*7days ago*
Yaro yaci suna Mubarak, an bannatar da dukiya tamkar ba'aso, mutane koh wadanda aka gayyata da wadand ba'a gayyata bama zuwa suke kawai domin su kashe kwar-kwatar idanunsu, anci ansha anyi hani'an dan wasu muatanen ma harda spoon suka zo kai wani abun dariya harda masu zuwa da leda yadda idan sunyi ragowa saii su juye su tafi dashi gida lols.
Wani abu daya tsaya wa Hjy A'isha arai shine duk da suna gida daya tare da Facalar ta wato {Hjy Hasfat} amman hakan baisa tazo mata barka ba, ta ayyana a ranta anya kuwa lpa?, a ranta tace "bari in ALLAH ya kaimu gobe naje na dubota"
Bayan Mijinta Dan Maliki ya fita ne itama ta fice, ta tunkari part din Hjy Hafsat, tura kofar tayi da sallama a bakinta.
Hjy Hafsat ta amsa sallamar fuskar nan a murtuke, ganin ba walwala a tare da itane yasa Hjy Aisha tace "Wai niko Hafsat ko baki da lpa ne naga kamar kina cikin damuwa?"
"Eh kawai tace mata ta kauda kai" tamkar wadda taga kashi, haka Aisha tagama tsayuwar ta, tashi tayi tabar part din, ta nufi nata part din cike da tunanin cewa kishi take da ita sbd ALLAH ya bata haihuwa ita kuma babu.
*5years Ago*
Tun daga wannan ranar Aisha bata sake zuwa part din Hafsat ba itama Hafsat din bata kara zuwa na Aishar ba.
Ana cikin wannan zaman ne irin na 'yan marina, itama Hafsat din ALLAH ya bata haihuwa inda ta haifi santaleliyar yarta mace Masha ALLAH, zokaga rawar kai wajen Hafsat domin daman akwaishi ballanta yanzu anga ansamu magajiya. Ran suna aka rada wa yarinya suna Rahila amman ana kiranta da suna "Lami" kasancewar sunn mahaifiyar Hafsat kenn.
Tun ranr da aka haifi Rahila, Alh Sani yaje ya shaidawa yayan nasa, sanan ya sanar da yaya nasa cewa "Nifa yayi wa Lami miji"
Alh Dan Maliki ya kalli kanin nasa yace "Ban gane inda kadosa ba?"
Alh Sani yace "ina nufin na bawa d'ana Mubarak yar ka Rahila" Dan Maliki yayi murmushi yace amman gaskiya naji dadi wannan magana taka, fatanmu ALLAH ya hade kanmu danasu baki daya ya nuna mana lokacin.
Alh sani yace "Ameen summ Ameen"
Toh duk cikin su biyun babu wanda ya sanar wa da matarshi abunda suka yanke, kawai dai sun bar abun a zuciyarsu ne.
*10 years Ago*
Nifa wlh Ammi na gaji kullum waccan yar iskar yarinyar saita b'ata mani lokaci, kuma wlh Ancle's dinmu basu da mutunci duka suke mani amman banda ita inaga ma shiyasa take jawa muna latti sbd ita ba'a dukanta ya karasa maganar ta k'wata.
Ammi tace Son hakuri zakayi wata rana sai labari kaida saurama shekara d'aya ma ka kammala, kumama ai naga kanwar kace, bai kamata kana zagin ta ba daga yau karna karajin ka zagi wani, babu kyau kaji koh?"
Yace "Eh ammi" daman ya saka uniform dinsa ya dauko school bag dinshi ya rataya yace "Ammi na tafi" tace "ALLAH ya dawo daku lpa son" yace "Ameen Ammi" ya fice daga part din nasu zuwa parkin space.
Yana karasawa yace wa Musa driver "Baba wai haryanzu bata fitoba?" Cike da kulawa Mal musa yace "Wlh kuwa d'ana haryanzu"
Duba agogon dake hannunsa yayi *8:05am* ya nuna masa wani dogon tsaki yaja mtswwww.....
Yace "Wlh yau nasan zan daku wajen Ancle Ema aiko wlh sai na rama akanta" duk wadannan maganganun acikin zuciyarsa yake sakasu, suna nan tsaye sai gata ta fito daga part din nasu itama cikin school uniform iri daya dana jikin Mubarak din, tana tafiya a hankali kai kace tana tausayin kasa tana wani karairaya duk da kwata-kwata bata wuce sheka 12 ba, amman idan kaga yanda ta iya kissa da kisisina kace yar shekara 20 da doriya ce.
Wnn abunne ya kara bak'anta wa Mubarak rai yaji ya kara tsanar ta fiye da koyaushe, tana karasowa ya bude gaban mota yashiga, itama ta kama murfin kofar tana kokarin budewa, wata uwar tsawa daya daka matane yasa tayi saurin sakin kofar, ta bude ta baya tashiga tana share yar kwallar dake bin kumatunta, sbd ta saba idan za'a kaisu school a baya suke zama shida ita amman yau ya gujeta.
Shidai Musa driver baice k'ala ba ya shiga mota ya tada ya fice da matsiyacin gudu, sbd har ga ALLAH bayason yaga abinda zai b'ata ran Mubarak.