Showing 15001 words to 18000 words out of 18439 words
*
Horn take jerawa ba k'akkautawa kai kace biyota akeyi, jin horn din yayi yawa yasa mlam Hamisu tasowa duk da bai kammala biyan bukatarshi ba amman baya da zab'i kodan ya tsira da mutuncinsa.
Fitowa yayi daga bandakin rike da zariyar wandon sa a hannu yana kokarin daure tazugensa, zare sakatar karamar kofar yayi ya lek'a yace "Ahh.. Barka da zuwa Hajiya"
Maida kofar yayi ya rufe ya sake bude babbar kofar gate din a fusace ta sako kan motar banda yayi saurin janye k'afarsa da sai ta takesa.
Parking space ta nufa taje ta ajiye motar tata tafito sanye cikin bakin tabarau (glass) "kai zonan" abinda ta fad'a kenn.
Jiki na rawa ya karaso wajenta harda durkusawa k'asa ya sake cewa "Barka da zuwa hajiya" a karo na biyu sbd yasan jarabar ta, aiko bala'i ta fara masa.
Wai kai wane irin mutum ne? ehhh! Kullum in kayi wa mutum laifi saika dinga apolozising kai kurma nene da ba'a yima maka horn daya kaji sai anyita yimaka ehh...! Sai kace dakin naka na wata uwa duniya ne?
Malam Hamisu yace "dan ALLAH kiyi hakuri Hajiya wlh ina bandaki ko kammalawa ma banyi ba sbd kada na bata maki lokaci na taso kiyi hakuri dan ALLAH".
Tace "To Gaskiya ya kaqmata ka canza halinka dan wata rana kanaji kana gani wlh zaka rasa hanyar cin abincinka"
Tsaki taja Mtsww.....
Tafara tafiya sai kuma ta juyo tace "Abba ya dawo ne?"
Juyowa Malam Hamisu yayi yace "A'a bai dawoba"
Amman yanzu naga yayanki ya dauki mota ya fita inaga shiya tafi ya daukowa.
Batace komaiba tasa kai ta nufi harabar gidan, shiga tayi ba ko sallama a tunaninta babu kowa a falon.
Jin tafiya ne a cikin falon yasa Hajiya Zainab kai dubanta izuwa kofar shigowa cikin falon, ido biyu sukayi da Salma.
Ke salma dan K'anin ubanki baki iya sallama bane? Salma ta b'ata fuska tamkar zatayi kuka tace "wlh umma na zata babu kowa a falon ne shiyasa"
Tace toh dan babu kowa a cikin falo kuma sai k'iyi sallama karki manta da hadisin Annabi S.A.W dayake cewa koda kangone kazo shiga toh kayi sallama bare ma cikin gida so ki gyara halinki as from today kada na sake ji koh gani ohk..
Tace "toh momy insha ALLAH zan kiyaye", Momy wai wane shiri kk kallo ne naga kin tasa T.V Haka keda daga kin fara kallo sai bacci ta karashe maganar tana mai kyalkyala mata dariya.
Momy kallonta tayi tace a lallai Daughter yau abunma harda xolaya, toh kwana Casa'in nake kallo kinsan ranar Sunday din data wuce ban kallaba shiyasa yanzu nake kallon maimaicin sa.
Salma tace aiko nima bari na samu guri na zauna coz wlh bana gajiya da kallon shirin, samun guri tayi ta hakimce kan wata 2~siter itama ta maida hankalinta ga T.V.
Malam Hamisu yana zaune yana jin Radio ne yaji horn ajiye Radio yayi a gefe guda sannan ya bude babban gate din sbd daman yayi tunanin Alh ne shida Naseer.
Ai kuwa hasashensa yayi dai-dai inda yana bude kufar yayi arba da motar Naseer din, brka da zuwa ya soma yi masu kamar yanda ya saba inda daga bisani ya karasa bude gate din shigowa sukayi sannu a hankali suke tafiya har ya karasa inda aka tanada domin parking din motocin.
Naseer ne ya fara ficowa harda dan gudunsa ya zagaya wajen mai zaman banza ya bude wa Abba kofa, shi Abba abunma dariya ya bashi yace "Kai Naseer mai yasa bazaka barni na dinga bud'e kofar nima da kaina bane?"
Murmushi yayi wanda ya sa kyansa ya k'ara ficowa yace "Ai Abba naga kai ka tsufa ne shiyasa ya karasa maganar yana kokarin rufe kofar motar"
Alh Abbas yayi murmushi yace "Kai kana tunani akwai wani abu dazaka iyayi wanda ni baxan iya ba?
Abba kaifa ka tsufa shiyasa na fara rage maka aiki, suka yi dariya suka fara tafiya domin karasawa cikin gidan.
Au.... Na manta Abba yo ai bqn dauko maka jakarka ba, juyawa yayi da baya domin dauko jakar, shi kuma Abban baice komaiba ya cigaba da tafiyarsa.
Shiga falon yayi da sallama yayin da Naseer yake biye a bayansa, da sallama a bakinsa ya shiga falon amsawa sukayi gaba dayansu,suna mai fuskanto ganinsu izuwa inda sukaji sallamar duk da sun gane muryar mai sallamar amman sunason su tabbatar da hakan, Salma tashi tayi daga zaunen datake, shi Abba a tunaninsa shi zata tara amman saidai me? Wucewa tayi ta gabansa batace masa k'ala ba, jakar dake hannun naseer ta karb'a tace "sannu da zuwa Ya Naseer".
Abun ya bawa kowa na falon mamaki tunba Abba ba ta yanda Salma ta wuce shi, yakasa hakuri saida yayi magana yace "Eh lallai kin nuna mani yan uwan taka da har zakizo ki wuceni kije wajen 'Dan uwanki ko kin manta shima d'ana ne?"
Salma tace "Af! Dan ALLAH Abba kayi hkr banganka ba sai yanzu.
Hajiya zainab dake zaune tayi kuri tana kallonsu ta dako baki tace kai! Karya kike ba baban naki bane ya fara wuce ba, da zakice baki ganshiba.
Alh Abbas yace "Atoh Hajiya gane mini hanya wai makaho yaso gurma" ba karamin dariya ta basuba wannan karin maganar da Alh nasu yayi ba.
Naseer ne shima ya sako baki yanaso kare lilyn kanwar tasa yace "Ai Abba sai kayi mana hakuri kasan abun naka na 'yan uwa"
Alh Abbas yace "yan uwa"
Hajiya Zainab tabashi amsa da 'yan uwa kashin awaki kenn.
Alh Abbas yace "toh shikenn yan uwa sai ku bamu waje ku barni nida mahaifiyar ku........."
*Abubakar Saleh Al~Quyraemey*
_(young writer)_
[4:11PM, 6/22/2019] Abue Saleh Al~Quyraemey: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?
*DUK GIRMAN GONA!!!*
_{Akwai kunyar 'karshe}_
©2019
*A mystery story just keep on following me.*
👨🏻💻👩🏻💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
_____________________________________
*👉🏼Page 21-22*
*Author.......🖋*
*Abubakar Saleh Quyraemey*
```@Facebook Abubakar Saleh AlQuyraemey```
*DEDICATED TO*
*Zamani Writers Associati ALLAH ya k'ara hada kànmu Ameeñ ya ALLAH*
_*Life doesn't get easier you just get stronger*_
: بِسْــــــــــــــــــــــمِ اَللّهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِِ"
......Salma ce ta fara wucewa direct dakin Naseer ta nufa tana k'arasawa kuwa ta baje akan lalausan gadon ta, shima baya da zabin daya wuce ya biyo bayanta shiga dakin cire hularsa yayi ya jawo stool ya zauna, ya kura mata idanu kamar maison gano wani abu a tattare da ita.
Ganin kallon dayake mata ne yayi yawa tace yaya Naseer wai kallon meyene hakan?
Ya nisa sannan yace "Amarsu ta Ango, kinsan wani abu? ranar bikin ki akwai bidiri, ranar bikinki akwai lik'i, kinsan cewa ban tab'a yin rawa ba koh, toh wlh ranar bikin ki saina cashe zan gyagije, sannan na girgiza, saidai kawai in aka kaiki gidan mijinki zanta kuka ne kawai, ya k'are maganar yana kyalkyala mata dariya cike da zolaya.
Shagwabe fuska tayi tamkar zatayi kuka tafara magana "Yanzu yaya Naseer meye na kawo wann maganar dan ALLAH, kai kanka kafi kowa sanin bana sonta, kai kasan banason wnn maganar kasan banason rabuwa da kai, ni bazanyi aure ba yanzu.
Cike da zolaya yace "Toh naji Al-masifatu yi hakuri" Tashi tayi tana kokarin fita daga dakin hawaye ciki da idanunta yace nace kiyi hakuri mana gani bata da alamar tsayawa yasa yayi saurin rik'o hannunta sauri sakin hannun yayi sakamakon wani Yarrr.... Dayaji tun daga gangar jikinsa har zuwa kwakwalwarsa ji yayi tamkar wayar wutar lantarki ya tab'a.
A bangaren Salma itama taji irin wannan abun da Naseer yaji, wnn yana faruwane a duk lokacin da hannayensu suka hadu tun suna yara kuwa wannan dalilin ne yasa sam Naseer baya yarda ya taba hannun salma.
Su umma suna zaune Alh Abbas yana bata labarin tafiyar dayayi, sai kawai sukaga wucewarta fuuu......
Umma tace "wannan yarinyar kuwa lpa....?" Bata gama rufe bakinta ba suka tsinkayo muryar Naseer yana cewa "umma yarinyar nan dai magana dayace kullum dai itace maganar aure, daga na fad'a mata maganar aure sai ta fara kuka wai ita batason ta bar gidann."
Umma ta kalleshi cikin natsuwa tace "Batason barin gidann ko dai batason rabuwa dakai.
Toh umma rabuwa dani ai yazama dole tunda duk matsayin mace a cikin gidansu dole wataran ta tafi gidan wani, kinga kenn idan ta tafi gidan wani babu wani abu daya rage tsakanin nida ita face ziyara.
Alh Abbas da tun dazu baice komaiba kawai kallon ikon ALLAH yake yace toh amman kai meyasa tunda kasan batason irin wnn wasan meyasa kk matashi?
Naseer yace "Abba kanwata ce fa, kuma bata da wani wanda ya fini a duniyar nan, nine abokin shawarta, nine abokin hirar ta, kuma ni gani nayi babu wata magana da zamuyi mai mahimmanci a yanzu kamar maganar auren ta, toh amman daga na fara maganar sai ta fara kuka," yayi ajiyar zuciya yace "Bari naje na bata Hakuri".
Har ya fara tafi Hajiya zainab tace "Naseer ya juyo ba tare daya amsaba tace "kasan dai su Aiman an kusa tashinsu daga magaranta kuma kai sukeso kaje ka daukosu basason direba yaje ya daukosu".
Yace "Ai insha ALLAHU Umma bazan dade ba kawai dai dan lallabata zanyi".
Shiga dakin yayi da sallam yace "Assalama Alaiki ya yar uwata" Kwance ya tarad da ita tayi rufda ciki sai sharbar kukanta take, jin anshigo dakin ne yasata rage sautin kukan datakeyi ta d'ago kai don gani wanene ya shigo dakin ganinsa tayi a tsaye ya kame hannayensa guda biyu ya d'orasu a kirjinsa, filo ta dauko ta jefosa dashi tana cewa "Ni ka fita ka bani waje Malam".
Hmmm toh ai idan kin isa katifar zaki dauka ki jefeni da ita bawani abu waishi filo ba.
Salma tace "Ai wlh dan bazan iya bane shiyasa da zan iya wlh da saina dauko na jefo maka ita.
Kujera ya samu ya zauna ya fara magana cike da kulawa da sanyaya zuciya yace "Bana tunanin akwai wasu yan uwa dasuka Shak'u kamr yanda nida Salma muka shak'u, lallai mun shak'u matukar shak'uwa, saidai inaso kisani cewa an dade ana zaman tare tsakanin yan uwa sanan an dade ana rabuwa tsakanin yan uwa, haka abun yake a rubuce sbd da haka nida ke dole sai munyi hakuri.
Salma tace "Yaya Naseer na fada maka cewa nifa baxanyi auren nan ba period!"
Wani kasaitaccen murmushi yayi yace "Sbd tuwon Mama?" Tace "Wlh kaga bana son haka ka daina mun wnn zance inba haka ba ni zan fece na barmaka dakin"
Yace haka zalika duk inda kikaje nima sai nabiki, tashi tayi a fusace ta bar dakin, shi abun natama dariya yake bashi, murmushi ya sake yi a karo na biyu ya mike yace "Problem Girl kenan" ya fice daga dakin.
__________________________________________________________________
Ta kasance yau safiyar Monday ce wadda Hausawa ke mata kirari da tushin aiki ko nasara na tsoronki, Naseer ne sanyi cikin wani lallausan yadi sky in colour ba karamin kyau dinki yayi masa ba, fitowa yayi daga dakinsa yana kokarin daura agogonsa mai dan karen tsada, a falo suka had'u da momy ta kallesa tace "Ah masha ALLAH" takare maganar tana murmushi.
Juyowa yayi ya dubi umman yace "Good morning mum"
Tace "Morning son how are u?"
Yace "fine mom"
Daga haka ya karasa izuwa dining table dan daman kowa ya hallara shi kadai ake jira, yana zama kuwa umman ma ta dawo ta zauna suka fara cin abinci kamar yanda suka saba.
Tom anan cikin cin abincin ne Abba ya dago ya dubi Naseer da kyau cikin zolaya yace Naseer wai sai yaushe xakayi aure ne a shekarunka fa ya kamata ace kayi aure for almost 37 years fa ai ya kamata inji ana ce mani grandy koh? ya k'are maganar yana kallon Hajiya Zainab wadda tunda Alh ya fara maganr ta daina cin abincinta ta tsaya tanajin su.
Umma tace "wlh kam Gaskiyarka Alh indai baso yake ya xama baba na shago ba" suka kyalkyale da dariya harda Khadija da Aiman wanda khadija bazata wuce shekara 13 ba sannan Aiman shima yana da shekara 10. Duk da basu fahimci inda umman ta dosaba amman datace Baba na shago shine abun ya basu dariya.
Naseer dagowa yayi a hankali yace Abba zanyi in harna samu wadda ta kwanta mini a raina zan sanar maka insha Allahu.
Abba yace "Ameen Summa Ameen"
Tashi yayi tsam yana mai duba agogon dake hannunsa yace "toh dady nidai na tafi mom sai na dawo yan biyu mom byyy". Yana kokarin fita ne daga falon ya tsinkayo muryar Salma tana cewa ni anmanta dani koh toh mun b'ata"
Juyowa yayi yace "No ba haka bane kinga na makara so we will talk letter" ya k'arashe maganar yana ficewa ba tareda ya jira mai zata ce ba.
Alh Abbas kwance kan bed dinshi amman sam bacci ya gagareshi sai juyi yake, dan bubbaga bayan Hajiya zainab yayi yace "Hajiya tashi muyi wata magana"
Tashi tayi ta zauna tana mai murza idanunta alamun baccin nata ya soma dadi, tace "Ina jinka Alh"
Yace "Hajiya inaga ALLAH ya nufa haduwar wannan yara wata kila shiyasa ubangiji ya nufesu da had'uwa a gida guda.
Alh Ga dukkan alamu abun ya nuna haka. Toh Alh mai zai hana a samu a kirasu a fad'a masu, tunda akwai aure a tsakaninsu ni inaga zasuyi farin ciki indan sukaji wannan maganar kuma gashi misali sun ruga sun shak'u da juna kai hasalima koh mu da muka haifeta bamu shak'u kamar yanda suka shaku da junansu ba.
Ya nisa yace "haka ne amman Hajiya ke kinsan da cewa halayyarsu ba daya bace tamkar wuta da ruwa haka suke duk da sun shak'u da juna, zasu iya samun matsala a zaman takewarsu ta aure sbd banbancin hali, ke kanki kinsani cewa bakya bukatar na sanar dake irin halayyar su tunda kinfini sanin halinsu.
Girgiza kai kawai tayi tace "Gaskiya toh inaga abunda za'ayi kawai a hakura a kyalesu kar ayi wannan maganar, kowa ya samu nashi, ita tasamu mijinta ta aura shima ya samu matarsa ya Aura, inaga hakan zai fi?"
Um...Um..had'asun shine mafi A'ala ki barni ina ganin zan fito da wata dabara mugani ko zata bulle.
Dubanshi tayi cike da dokin jin wannan wace iri yar dabarace tace "Alh wnn wace iriyar dabara ce?"
Yace "kedai kawai xaki gani kisa ido kiyi kurum"
___________________________________________________________________
Kwance yake akan lallausan gadonsa yana sharara baccinsa mai matukar dad'i khadija ce ta shigo dakin ta fara kiran sa.
Yaya Naseer! Yaya Naseer tana dan dukansa ganin baya da alamar tashi yasata ta kwala k'ara a daidai saitin kunnensa aiko ba shiri ya mike biyota yayi da gudu cike da matuk'ar baccin rai aiko itama tace kafa mai naci ban bakiba ta fece ta baro dakin nasa tayo falon su cikin matukar sa'a kuwa tayi kacibus da Umma ta shigo falon aiko bayanta tabi ta lafe tana cewa "Umma dan ALLAH 'boyeni wlh yau ya kamani na bani"
Umma da ta shigo rike da ruwan zafi a hannunta tace "yi hankali karki kona kanki wlh tana maganr ne takai dubanta ga kofar shigowa falon ido biyu sukayi da shi sai muzurai yake yana cika yana batsewa sbd da tsabar takaici tace "mai ya hadaka da ita ne?"
Furzar da iska yayi yace "Umma wlh yarinyar nan ta raina ni, wai ina kwance taxo tanata mani ihu a kunne kamar kaina zai fashe haka ake tashin mutum in yana bacci?"
Umma tace "To ai Alh ne yace yanason ganinka yanzu ma haka Salma tana can tana jiranka koh"
Tsuka yaza ya fice daga dakin, yana shiga dakin nasa birthroom ya shiga yayi brush ya sanya jallabiya da 3quatr ya fito domin amsa kiran dady.
Direct dakin dadyn ya nufa, da sallamarsa a bakinsa ya shiga suka amsa sallamar tasa da mamakinsa kowa ya hallara shi kadai ake jira.
Har kasa ya duka yace "Ina kwana Abba"
'lapiya lau my boy da fatan ka tashi lpa?'
Yace "Alhmdll ala kulli halin"
Dady yace "To masha ALLAH have a set ya nuna masa wata kujera dake kusa da Salma, jawota yayi ya zauna, yana mai sauraron abunda ya tarasu a gurin.
Sake kallonsa Abba yayi yace "Kun gaisa da momynka ne yace eh tun dazu muka gaida"
Yace "ohk"
Naseer, Salma Abba ya kira sunanensu wanda sukaji wata faduwar gaba ta ziyarce su a lokaci guda Abba yaci gaba da cewa mun kirakune dan mu karanta maku wani labari da zai matukar baku mamaki kuma jin wannan labari na tabbata sai kunyi matukar kad'uwa, naso mu ci gaba da rufe wnn sirri bamu bud'e shiba har abada toh amman sai mukaga yanda kuke gudanar da al'amuranku sai mukaga ya kamata mu bude wnn sirrin ba don komaiba sai domin samun farin cikin ku dakuma namu gaba daya.
Naseer bayan ALLAH ya azurtamu da samunka da shekara biyu, mahaifiyarka taso ALLAH ya bata wata haihuwar amman ALLAH bai bata ba, haka muka zauna munata tunanin yadda za'ayi har tsawon shekara hudu kai fiye ma. Sai mahaifiyarka ta kawo shawarar ko zamu tafi gidan marayu? Don mu samo jaririn da zata raina bayan kai, sai na amince da wannan shawarar data kawo nace amman mu fara zuwa asibiti kafin muje gidan marayun, sbd asibitima ana samun jariran da suka rasa iyayensu da ixinin gwamnati sai aba wadnda zasu raineshi, ALLAH da ikonsa muna zuwa kuwa muka tararda an kawo wasu accident din mata da miji duk Allah yayi masu cikawa harda jaririya a tsakanin su amman wani abun mamaki wannan jaririyar kwata-kwata bata samu koda kwarzane ba, a wannan lokaci akayita k'ok'arin neman yan uwan wannan bayin ALLAH amman aka rasa........
*Abubakar Saleh Al~Quyraemey*
_(young writer)_
An