Showing 12001 words to 15000 words out of 18439 words
sani ya koma cikin gidan
Ai Dr muhsin bai tsaya ko rufe motasa ba ya dauko first aid bod dinsa ya biyo bayansa Alh sani da Gudu shima.
Tura kofar dakin yayi dayake Ammi itace a bakin kofa ita ya fara dubawa yanata yan gwaje-gwaje irin nasu na likitoci har dai saida ya tabbatar da bata numfashi sannan ya koma kan Alh Dan maliki shima haka baya da rai.
Innalillahi wa innan illaihir raji'un kalmar daya fada kennan a bakinsa wadda tasa Mubarak da Alh sani saurin ruguwa dan sanin abunda ke faruwa, shidai Alh sani wajen dan Maliki ya dosa shikuma Mubarak wajen ammi ya tunkara,
Jijjigata ya farayi yana cewa ammi dan ALLAH ki tashi karki tafi ki barni wlh idan babu ke duniyar nan to nima bani da amfani, Dr Muhsin ya lura baya cikin hankalinsa sbd haka ya duba cikin first aid box dinsa ya nemo allurar bacci ya lallabo ya caka masa aiko ko minti daya baiyiba ya baje a kasa tamkar matattace ya fara sharar baccinsa.
Shikuwa Alh Sani koda ya karasa wajen dan Maliki addu'o'i ya fara jero masa, ya dau a kalla minti talatin yana musu addu'o'i daga bisani ya fara kiran yan uwa da abokan arziki ana sanar dasu.
Da misalin karfe bakwai na safe (7:00am) aka kai Alh dan Maliki da matarsa hajiya Aisha gidansu na Gaskiya kowa ka gani a cikin masu kaisu yna cike da alhinin mutuwarsu kasancewar kowa yana masu shedar kirkinsu sbd tunda Hajiya Aisha take ba'a taba rabasu fada da wata ba kasancewar ta mai hakuri mautuka da gaske domin duk abinda kayi mata tana iya shanyewa saidai abun ya dinga cinta a jiki tana ramewa amman bazata tab'a fada maka cewa kayimata ba daidai ba da wannan halayyar tata tasa mutane ke yabonta. Uwa uba kuma dan Maliki wanda yai shura wajen tallafawa marasa karfi da gajiyayyu gami da marayu.
Duk wannan zirga-zirgar da ake tare da Dr Muhsin ake yinsa sbd kamar uba haka ya dauki dan Maliki, shikuwa Mubarak yana can yana sheka baccinsa tamkar ba abunda ke damunsa sbd allurar baccin da Dr Muhsin yayi masa.
_Wannan kenn,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,_
*7 Days*
Bayan anyi addu'ar bakwai ne aka mallaka ma Mubarak duk wani abuda Alh Dan Maliki ya mallaka sakancewar shine d'a d'aya tilo da Mahaifinsa ya haifa, Alh yaso tashi ya bar gidan amman sam Mubarak yaki yarda yace ai shine zai tashi haka kuwa akayi inda washe garin ranar mota tazo ta kwashe masu kayansu kaf,
Sun tare a sabon gidanshi dake a sallari Qtrs, gidane kato yasha farin fanti kaf kayan cikinsa ma fararene kai tarta motocin dake cikima farare ne, hakan ys gidan ya kara haskakawa duk kiyayyar mai kiyayya duba d'aya zaiyi wa gidann ya tafi da imaninsa,
Ba laifi a dan lokaci sun samu kwanciyar hankali Saidai har yanzu fa batayin girki saidai yaje hotel ya shiyo masu wnn abu ba karamin kona masa rai yake ba idan ya tuna cewa yana da mata fa amman wai shine yake yawon hotel ahaka har suka shari shekaru, ita bata iya girkin ba kuma bata damu ta iya ba siadai yar aiki ta ta dauko tana yi masu girki ba yanda ya iya bisa dole yake cin girkin amman ba dan ransa yaso ba,
Ana cikin wnn zama ne ALLAH ya hada sa da wata yar fulani wadda take kawo masa fura yana siya, yarinyar akwai hankali ga nutsuwa inda snnu a hankali shakuwa gami da k'auna ta fara kulluwa tsakanin Mubarak da saude, ai ranar daya je mata da batun kara aure a daren babu wanda ya rintsa sbd da bala'in ta,
Shi dariyama take bashi wai daman tana kishinsa ne taki taje ta koyo girki, ta bari yar aiki take masa, sannu a hankali maganar auren Mubarak da Saudat tayi nisa dan har ansa ranar daurin auren su.
Ba yanda Hajiya Lami batayi ba ita da babbar k'awarta Hajiya Binta na wajen yan bori da kuma bokaye Amman abunda ALLAH ya rubuta baya goguwa duk inda sukaje magana daya ce auren nan ba fashi sai anyishi, da kyar suka samu wni boka yace masu zai masu aiki amman sai bayan tashigo gidan sbd yarinyar akwai addini, ba dan taso ba haka ta hakura ciki lokaci k'alilan duk tabi tawani zuge kamar ba Hajiya Lami ba ta zama wata kazama duk sbd yawo wajen bokaye domin a lalata auren Saude da Alh Mubarak.
Duk halin datake ciki Alh Mubarak na fahimce da ita kawai dai ya kyaleta yaga iya gudun ruwan tane, shi dayaga ta daina bala'in nanma a tunaninsa ta hakura ashe ba haka bane tunaninta daban danashi.
*Rana bata karya saidai uwar diya taji kunya* A yaune aka daura auren Alh Abbas da saude inda daruruwan mutane suka shaida, an daura auren ne a garin dawakin tofa awata ruga mai suna rugar janare, akan sadaki naira dubu hamsin (50,000).
A ranar Alh Mubarak ya kira wani yaronsa ya sanar masa cewa ya je kantin el~Samt dake a kantin kwari ya had'o wa Hajiya Lami kayan lefe itama, inda ya turo masa one million a account dinsa yace yaje dasu idan basu isaba ya sanr dashi.
An dauko amarya da misalin karfe hudu na yamma idan aka kawota gidan Alh Mubarak itama part dinta da ban komai iri dayane da na Hajiya Lami, bai ban-banta komai ba.
Mani driver ya kawo wa Hajiya Lami laife har akwatina shidda, inda anan inda ya ajeye ko kallosu batayiba bare ta bude taga abunda ke ciki.
Motocin dasuke shigowane wta bayan watane da hayaniyar ke tadowane ya dawo da ita daga duniyar tunanin data tafi, maimakon ta tashi ai saima ta gyara zama tawani hakimce kai kace wata giwa ce, koda yan uwan saude suka shigo main falo din da sallama a bakinsu amman ko kallo basu isheta ba, shuma ganin haka yasa basu damuba suka wuce izuwa part din da Alh Mubarak ya sananr dasu shine na sauden, dayake komai a tsare yake daman yace baya bukatar tazo da wani abu face kayan jikinta, sbd haka suka yi mata nasiha irin wadda ake wa amare idan ankaisu dakin mijinsu,
Bayan sun kammala ne sai baki ya rabu biyu wasu na cewa aje wajen uwar gidan domin a damk'a mata amana haka akai ta tafka wannan muhawarar daga bisani ne aka yanke shawarar aje a gabatar da ita ga uwar gida.
Wasu dattijan Mata ne su uku suka kama hannun saude suka nufi main falo, da sallamarsu suka karasa wajen hajiya babba wadda sai wani shan kanshi take tana hura hanci, magana suka fara mata amman ko juyowa ta kallesu batayiba dama taji sun dameta sai ta nemo remote ta kunna TV ta kure volume anan cikin haka saiga Alh Mubarak ya shigo falon gani abinda yake faruwa ne yashi saurin karasowa Inda suke yace "kuzo mu wuce daki" abunda ya fada kenn ya kara gaba suma suka take masa baya.........
*Abubakar Saleh Al~Quyraemey*
_(young writer)_
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?
*DUK GIRMAN GONA!!!*
_{Akwai kunyar 'karshe}_
©2019
*A mystery story just keep on following me.*
👨🏻💻👩🏻💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
_____________________________________
*👉🏼Page 17-18*
*Author.......🖋*
*Abubakar Saleh Quyraemey*
```@Facebook Abubakar Saleh AlQuyraemey```
*DEDICATED TO*
*MUTAN KATSINA STATE HADI DA XAMFARA*
*INA JAJANTA WA 'YAN UWANMU MUTAN SAKOTO GAME DA IFTILA'IN DAYA SAMESU ALLAH YA JIKAN MUSULMI YA KARA KAREMU DA KAREWARSA SU KUMA MASU TA'ADANCINNAN ALLAH YA SHIRYAR DASU HANYA MADAIDAICIYA IDAN KUMA BAZASU SHIRYUBA YA ALLAH KAYI GAGGAWAR KAWAR MANA DASU DAGA DORON DUNIYA AMEEN YA ALLAH.*
........Hakuri ya shiga basu sosai, suka ce masa 'babu komai ai' har kofar gida ya rakosu saida yaga motarsu ta tafi sannan ya koma cikin gidan yana shiga kuwa mai zai gani!.. Saude ya gani tanata rusa uban kuka nan ya shiga lallashinta kamar wata yar goye, da kyar da shidin goshi ya samu tayi shiru.
Kama mata hannu yayi suka shiga bathroom suka dauro alwala, shinfida masu carpet yayi sukayi sallah kamar yanda Annabi S.A.W Ya koyar damu bayan sun idar da sallar ne ya dora hannunsa na dama a tsakiyar kanta, yayi addua ga addu'ar kamar haka ga wadanda basu iyata ba:
اللهم اني تساالك خير ها و خير ما جباتها عايه واعوز بك من شر ها وشر ما خباتها عايه.*
_Allahuma inniy as'aluka khairaha wa khairi ma jabaltaha alaihi, wa'auzu bika min sharri ma jabaltaha alaihi._
*Ya ubangiji ina rokon ka alhairinta da alkhairin abinda ka dabi'antar da ita agareshi ina neman tsari agareka daga sharrinta da sharrin abun daka dabiantar da ita agareshi.*
Wannan itace adduar ALLAH yasa mu dace Ameen Summa Ameen.
Bayan sun kammata ne ya yawo wata leda kaza ce a ciki da youghurt mai hade da kwakwa, tashi tayi ta dauko plate da cups guda biyu tayi saving dinsu, bayan sunci sunsha sunyi hani'an sai kuma suka kwanta kan gado suka bi lpa katifa nidai nace a angwance lpa na bar masu dakin.
Acan bangarn Hajiya Lami kuwa ta kasa koda rintsawa sbd bala'in kishi ta kasa zaune ta kasa tsaye sai safa da marwa take ta saka wannan ta warware, tama rasa mai ya kamata tayi har asuba tayi inda tadan kwanta kan gado sbd wani zafi da idonta yake mata kasancewar ko rintsawa takasayi a daren ranar, kwanciyarta keda wuya bacci barawo yayi awon gaba da ita, ba ita ta farka ba sai misalin karfe 10:12am. Tana tashi ta fad'a bathroom tayi wanka ba batun sallah tayi kwalliya cikin wani paper les green in colour, ba laifi yaudai andan kintsu.
Acan bangare amarya saudat kuwa angon nata dawani irin farin ciki ya tashi sbd shi sai a yanzu yasan yayi aure, shida kansa ya hada mata ruwan dumi ya kamata ya shiga bathroom din da ita, kukan shagwaba ta fara masa ita a dole sai ya fita ya barta, murmushi yayi ya fice yanacewa a ransa 'no Wonder ai daman fulani da kunya ba daga baya ba', kafin ta fito harya sa mai girkinsu ta hado masu kayan break fast ta jere masu a dinning, futowa tayi tana dan dingisawa ganin tana tahowa da kyar ne yasa yayi saurin rikota ya dagota kai kace jaririya ya rungumo, bai xame ko ina da itaba sai gaban mirror shida kansa ya taimaka mata tayi kwalliya sannan ya sake daukota ya direta a kan dinning din, shida kanshi ya dinga bata a baki tun tana kin karb'a hardai ta hakura, saida ya tqbbar da takoshi sannna shima ya soma karin kummalonsa.
Bayan ya kammala ne daki ya shiga fitowa yayi rike da briefcase dinsa a hannu sanye yake cikin gizna sky in colour a kwana dayannan ya yayi wani haske dashi kai kace bai wuce shekara 25 ba, kalloshi takeyi tana karajin sonshi na kara ratsata ta kofofin jikinta, shima kallonta yake harya karaso inda take yace "kallon ya isa haka" batamaji abunda yake cewa ba d'an hura mata iskar bakinshi yayi ai firgigit tayi ta dawo daga duniyar tunanin data tafi murmushi yayi mata yace toh ni zan tafi sai na dawo taso ta rakashi amman ya hanata. Futowarshi tayi dai-dai da fitowar Madam fuskarnan tata bakikkirin tamkar bata tab'a dariya ba a duniya daman gata baka sai abun ya kara cakude mata ta sake zama wata mummuna, kallon-kallon suka shiga yi shida ita kai kace wasu makiyan junane suka gamu, ba abinda take binsa dashi sai mugun kallo da harara, ahaka suka wuce juna shi baice mata kalaba itama haka kowa ya shiga motarshi ya kama gabansa.
Hajiya Lami bata tsaya ko ina ba sai gidan kawarta wato Hajiya Binta inda suka rankaya suka je wajen bokansu wanda yayi musu alkawrin cewa da zarar an daura auren to su dawo za'ayi masu aiki, haka akayi kuwa inda ya bata wani kulli a laida yace ta tabbatar ta saka mata a cikin abinci sbd wnn shine zaisa ta raunana wajen ibadah datakeyi kullum, ALLAH sarki saudat baiwar ALLAH. Sannu a hankali wnn magani ya fara tasiri a jikinta inda ta fara dana Azkar din safe da daren data sabayi, daman boka ya fada mata da zarar ta lura da cewa maganinsa ya fara aiki to ta garzayo tazo gidansa, anan cikin wnn haline ba zato ba tsammani ciki ya baiyana ga Hajiya Lami wnda wannan cikin ya taka rawa wayen hanata zuwa ko ina sbd laulayin dayazo mata dashi, babban bakin cikinta shine ko yar tafiya tayi nan da can to sai kafafunta su kumbura suyi suntum tamkar biredi, hakan ne ya hanata zuwa wajen boka kuma kota kira aminiyarta wato hajiya Binta bata shiga ta rasa maike damunta.
Ba laifi dai Alh Mubarak ya nuna farin cikinsa sbd bayason ya haddasa fitina tsakanin matan nasa, ba'afi sati biyu ba itama Saudat ta tashi da zazzab'i gami da amai koda Alh Mubarak ya kaita asibiti an tabbatar mai da cewa matarsa tanada juna biyu na tsawo wata biyu (2months), zo kuga murna wajen Alh mubarak bakinshi yaki rufuwa.
Kwanci tashi ba wuya gurin ALLAH a halin yanzu juna biyun Hajiya Lami ya kai wata tara ana expecting haihuwa yau ko gobe, a bangaren Saudat ma haka abun yake cikinta ya shiga wata na tara. Wani iko na ALLAH shine saudat ta riga Hajiya lami haihuwa inda saudat din ta haihu da safe ita kuwa saida yamma sannan ALLAH ya sauketa lpa.
Alh Mubarak yayi murna matuka da gaske inda yayita dawainiya ta bangaren abubuwan da masu jego da jariran zasu bukata, a bangaren Hajiya Lami tana cike da bakin ciki gami da jin haushi sbd ita Saudat da namiji ta haifa ita kuma mace ce ta haifa sbd haka kenn tazo daga bayanta amman zata fita samun gado kenn, wnn dalilin ne yasaka ta bakin ciki ta dauri aniyar cewa dazarar ta yi kwana bakwai to zata nemi gidan bokanta da wannan gudiri take kwana dashi take tashi.
Ranar suna yara suka ci suna shidai na mijin wato dan saude ansa masa suna zaharadden ana kiransa da Deen, sai mace diyar Hajiya Lami ita kuma Aisha ana kiranta da Humaira, ko wace daga cikinsu yan uwanta sunzo dayake gidan babban gidane babu ruwan kowa da kowa.
Yamma nayi taro ya watse ko wacce aka barta daga ita sai jaririnta, ai hajiya Lami tana ganin haka ta shirya cikin wani England wax, ta dauko makullin motarta ta fice da mugun gudu, wani karamin kauye ta nufa a farkon kauyen taci burki wni gidane ta nufa gidan gaba dayansa da dannin kara akayisa, fitowa tayi da jaririyarta a hannunta ta kunna kai cikin gidan, a zaune tasameshi yanata zane a kan wani faranti ta bude baki zatayi masa magana kenn ya dakatar da ita yace "munsan abunda ke tafe dake dan haka yanzu munzo matakin karshe ungo wnn kullin kina zuwa ki barba a kofar dakinta tana tsallakawa shikenn angama zata haukace tabi uwa duniya ita da gidann har abada ke har gaban abada", ya rushe da wata dariya mai ban tsoro ita ma murmushin takeyi sbd da farin cikin yau bukatarta zata biya. wnn shine asalin labarin....
*CIGABAN LABARIN*
*Abubakar Saleh Al~Quyraemey*
_(young writer)_
[11:38PM, 6/18/2019] Abue Saleh Al~Quyraemey: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?
*DUK GIRMAN GONA!!!*
_{Akwai kunyar 'karshe}_
©2019
*A mystery story just keep on following me.*
👨🏻💻👩🏻💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
_____________________________________
*👉🏼Page 19-20*
*Author.......🖋*
*Abubakar Saleh Quyraemey*
```@Facebook Abubakar Saleh AlQuyraemey```
*DEDICATED TO*
*Zamani Writers Association Group*
_Keep your hope alive and never lose your faith life doesn't get easier, you just get stronger._
: بِسْــــــــــــــــــــــمِ اَللّهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِِ"
Washe gari tunda safe Alh Mubarak ya tashi cikin wani farin ciki ya fara kiran sunn Hajiya Lami tana jinsa taki amsawa, taki zuwa ma inda yake, zuwa can ba'a dauki tsawon lokavi ba sai gashi ya shigo dakin ta.
Ya tarar da ita a zaune yace "Haba madam dita ina kika shine inata kiranki amman kink'i amsawa?" Cikin gadara tace "ina jinka ai banga damar amsawa bane kawai da wani abune?".
Jikinsa yayi matukar sanyi, harda wata yar kyarma yace "A'a babu komai ALLAH i ya huci zuciyarki kawai nake fata" bata ce komai ba face wani sanyin dad'i datakeji yana ziyartar zuciyar ta ganin yadda aikin nan ya kamashi sosai haka kuma cikin k'ankanin lokaci.
Kinga bari na gyara maki gadonki ma naga duk ya tattare ya lalace, batace masa komai ba ya fara gyara gadon babu kama hannun yaro, tana jin batace komai ba ta sake jin wani dadi gami da farin ciki mara misaltuwa ya gaurauraye mata ilahirin gangar jikinta.
Tsaf! Alh Mubarak ya gama gyara gadon nan cikin kankanin lokaci, ya juyo da dubansa yace "sai kuma mekike so ayi maki?" Ta danyi murmushin mugunta tace "Yanzu inason ka kori duk mutumin dayazo maka da maganar b'atan Saudatu gidannan, dan ninasan Saudatu guduwa kawai tayi ta tafi karuwancinta, daman ni tunda ka auro ta na kula da halayenta cikin gidannan idan bakanan maza take kawowa gidann, to a lokacin nasan konayi maka bayani bazaka yarda dani ba so shiyasa na ja bakina nayi shiru.
Cikin kunar rai yace meyasa tunda take haka baki fad'amani ba, da sauri Hajiya Lami ta zaro ido waje cikin kissar munafunci tace "ina! Wace ni da daura zanin suruka ai shiruna yafi mani alheri yanzu ba gashi ka ganiba da gaskiya tayi halinta ba.
Nan take Alh Mubarak yaji tsananin tsanar Saudat ya cika zuciyarshi fal! Bayamason jin ko labarinta aiko cikin yan kwanaki Alh Mubarak ya manta da wata mai suna Saudat ma.
*20 years