Showing 27001 words to 30000 words out of 32991 words

Chapter 10 - ABAR SO COMPLET

Start ads

24 Aug 2025

195

Middle Ads

kuwa kunya taji yakamata…

Dady ne yace"Nagane abinda kakeso, kaje zan neme ka"

Cikin sosa keya yace" Nagode Dady Allah yakara girma"

"Ameen" suka amsa sannan yafita daga palourn

Dady neh yamayarda duban shi zuwaga Abba sannan yayi gyaran murya yace

"Ina fatan kasan inda zancen yaron nan ya dosa??"

"Eh ranka shi dade" Abba yafada cos yana mugun ganin girman dady…

Murmushi dady yayi sannan yace "nalura baka son in cigaba da zama anan gidan fah"

"Na isa??"

"Bagashi kana kirana da ranka shi dade bah bayan ni yakamata nakira ka da ranka shi dade" dady yafada

"Toh nadaina"

"Yanxu yah kke ganin zamuyi??"dady yatambaya

"Ai duk yanda kace haka za'ayi"

"Toh InshaAllah ranar da za'ayi nasu Abdulkadir Sai ahada danasu, Sai afara shirye shirye" Dady yafada…

Wani irin farinciki yakeji acikin ranshi cos tindazu a labe yake ajikin kofa yanajin abinda suke fadi…

***********
*3 days later…*

Yen kwanaki ukun datayi acikin gidan ta kara Lura da abubuwa dayawa acikin gidan,daita ake kowani abinci agidan yanz u inda kuma yanzu Maimuna ce target dinta dan haka yau tayi niyyar fara aiwatar da kudurinta akan Maimuna din.

Maimuna mah bata fasa bibiyarta bah cos itama kowani motsin Nadhira akan idonta yake amma har yanzu bata samo komai gameda ita bah,

Data fadawa Big Dady Sai yace kawai su shareta , yanxu dai zance Maimuna ta share batun sawa Nadhira ido…

Tindazu take kitchen tana taya Maimuna aiyuka inda Maimuna ta Lura Maimuna ta fiye shan coke,abu kadan Sai adan kurbi coke dinnan,

Fakan idon Maimuna tayi tazuba mata codeine acikin coke dinta ,inda tsantsan mugunta irin na Nadhira babban kwalba tazuba mata aciki, su Maimuna kam banda waka babu abinda takeyi, kuma dayake tabawa coke din baya amma tsantsan rashin Kula irin na Maimuna ko jijigawan datake yi bata ji bah,

"Nikam Maimuna wannan coke din daya rage dinnan zaki iya shan duka alokaci daya"Nadhira tafada tana nuna coke dinda ko rabi bai kawo bah,

Sanda Maimuna tayi wani irin dariya kafin tace" ke bakisan nayi course a iya shan coke bah??"

"Toh taya za'ayi nasani inba gwada min kikayi bah??"

"Tsaya kisha mamaki" Maimuna tafada tana kafa goran abakin ta , tsantsan hadama ko irin kwarewan nan batayi bah,gyatsan da Maimuna tayi bayan ta ajiye gora neh ya katse mata mamakin ta.

"Ya Kika gani??"tafada tana dage mata gira

Dariyan jin dadi Nadhira tayi sannan tace " wlhy nadauka bazaki iya bah, barina dauko miki nawa kisake sha mugani"

Dadi kaman ya kashe Maimuna cos daman kullum guda biyu take sha arana amma gashi yau garabasa tasamu zatasha guda 3,

Fita Nadhira tayi straight dakinta ta nufa sanda taboye kwalban codeine dinda ta juye mata dafarko abayan gado sannan tasake fitowa dawani again sanda tadan zubar da kadan kafin tasake zubawa aciki(nace kaii Nadhira ke muguwar karshe ceh…) sanda Tajijiga dakyau sannan tayi takoma wajen uwar kwadayi

"Gashi harna bude miki"tafada tareda mika mata,karba tayi sannan tace

"Kin kyauta wlhy" aranta kuwa fadi take ashe Nadhira akwai mutunci(nace Maimuna kenan hhh),

Kafa goran tayi abaki amma ko rabi batayi bah tafara ganin Zion,wani irin zumm zumm take jin kanta na mata,

Ajiye goran tayi tafara ganin Nadhira shida shida, dagudu Nadhira tashige dakinta takwaso kwalaben codeine taje tazube su acikin sif din Maimuna,

Lokacin datakoma kitchen din ta tarar da Maimuna cikin maye,cikin muryan Masha ya tace

"Miye Kika samin a coke??dayake bata gama loosing sense dinta bah

Dariya mara sauti Nadhira tayi sannan tace" duk abinda naga zai zamemin matsala a harkan dana sa agaba toh lah shakka kawar dashi daga hanya nakeyi"

Wani irin sarawan da kanta yayi yasata sakin wani irin dariya amadadin kuka,

Jin dariyar da akeyi yayi yawa yasa mumy dakuma su Fatima saukowa daga sama cikin sauri,hanyan kitchen din da suke jin dariya suka nufa,

Turus sukaja suka tsaya SAKAMAKOn ganin Maimuna akasa,itakuwa Nadhira takurewa tayi jikin garu,tana ganin mumy tayi wajen ta gudu sannan tace

"Mumy bansan miye ke damunta Sai fadin maganganu maras a dadi takeyi akan itada big dady"

"Wlhy son Alhaji nakeyi irin sosai dinnan…"suka tsinkayo muryan ta tana fada,tana tashi tayi tana layi …

Mumy kam notin kanta taji yana neman kwancewa cikin dauriya mumy tace

"Wani Alhajin kikeso??"

Wani irin dariya tayi sannan tace "wani Alhajin kuwa baya…

*Comment,*
*Vote&*
*Share*

*💋💋 wurarh💋💋*


💝💝💝💝💝
*ABAR SO*
💝💝💝💝💝

*WRITTEN BY: NAFISAT MA'ARUF SHEHU*

WATTPAD: MHIZZPHYDO
🌟GEORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F🌟

HOME OF GORGEOUS INTELLIGENTAND EXPERT WRITERS, WE ARE THE BEST AMONG THE REST

*Page 96*

Wani irin dariya tayi sannan tace "wani Alhajin kuwa bayan mijinki?,wlhy Ina mugun son sh...."

Marin da mummy takife ta dashi neh ya katse ta, cikin bacin rai mumy tace

"Abinda zaki saka min dashi kenan Maimuna??"

Wani dariya tayi dukda marin mumy bakaramin shigan ta yayi bah sai tace"toh an fada miki don ke kadai akayi shi neh?, Kindai San yana da damar yakara auren ire irenki guda 3, toh miye abin daga hankali anan? Kuma bari Kiji har kwana dani yakeyi"

Haba kan kace kabo su mumy harsun sun mata taron dangi, mumy sai cewa take wlhy yarinya karya kikeyi, mijina babu abinda zaiyi dake(Niko nace daga baya kenan).

Dukan ta sukeyi kaman ba gobe har sanda sukaga tadaina motsi sannan suka kyaleta,sheka mata ruwa akayi amma ko gizau Maimuna batayi bah

"Kun kasheta!!!,kunyi kisa" shine abinda Nadhira ke fadi afirgice cos tinda suka fara dukanta taja gefe ta tsaya.

"Suma tayi" Fatima tafada in assuring tune,

"Bagashi ankwara mata ruwa bata tashi bah" Nadhira takara fada tana mai tsugunawa akasa.

Kanta tasa atsakiyar cinyarta tasaki kuka mara sauti,she can't imagine yanzu ace ita tayi sanadin barin Maimuna duniya.

"Yah Salam"shine abinda mumy tafada sannan tace

"Ku kamata mukaita asibiti" mumy tafada cikin sanyin murya cos gabadaya tsoro neh yadarsu acikin ranta.

Cicibarta sukayi suka sata amota Sai asibiti,suna isa asibiti aka karbe ta aka wuce daita direct emergency.

Ansamu numfashinta yadawo amma gabadaya bata cikin hanyacinta, doctor ne yasa aka Kira mai wa'inda suka kawo ta…

"Miye kuke kallon yarku tayi shaye shayen dayasa ta bugu dayawa?" Doctor ya gefawa mumy tambaya

"Yar aiki nace" mumy tabada amsa atakaice

"Yar aiki kuma??"yatambaya cikin mamaki

"Erh"

"Toh aina tasamu cocaine??"

"Cocaine" dukkansu suka fada cikin tsoro amma banda Nadhira

"Erh acikin aman datayi munsamu ashe tahada mixture biyu alokaci daya Wato da cocaine dakuma codeine which is not proper,gashi kuma dayawa tasha shiyasa condition dinta yazamo critical, ahalin yanxu kam Allah yasoku da akwai wani visiting doctor available dole shi zamu gayyato"

Kallon kallo akeyi acikin office din wajen cikeda jimami kafin suka tashi suka fita.

Wayar big dady mumy takira inda ta shaida mai halin da ake ciki.

Banda salati babu abinda big dady keyi, inda ya ce mata su hadu agida.

Komawa gida sukayi suna jiran big dady yadawo, chan saigashi da uwarsu babban riga, hula ma ahannu yariko Sai huci yakeyi kaman wani namijin zaki.

Shigowar shi yasa dukkansu suka tashi tsaye

Cikin bacin rai yake fadin" ina yar iskan yarinyar nan take??"

"Bata farfado bah" mumy tabashi amsa

"Yarinyar nan taci mutunci na dayawa harni zata mawa sharri don batasan hallaci bah??"Alhaji yafada cikin dacin rai kaman da gaske, Nadhira kam babu abinda take yi Sai binsu da ido

"Nima abin yabani mamaki,ai tanuna mana halinta kuma daga yau aikinta yakare agidanan" mumy tafada

"Abinda yasha minkai shine ina tasamo cocaine??"dady yafada

"Allah masani"

"Gaskiya ban yarda bah??"big dady yafada

"Toh aje a bincika dakinta mana I'm sure zamu samu wasu clue" Fatima tafada

"Kin kawo point sisto"daga nan suka dunguma zuwa dakinta, birkita koina sukeyi daga karshe suka samu kwalaben codeine manya manya guda biyu.

Salati suka hau yi sam basu taba kawowa aransu Maimuna zata iya shaye shaye bah cos ta fiye shuru shuru, ayyerh daman ance duk masu shuru shurun nan basuda dadi.

"Taya akayi tasamu cocaine??" Shine abinda Amin Yafada bayan yagama duba ta

Iska Amin ya furzar sannan yace"Toh gaskiya nikam banyin wannan aikin in har ba'ayi involving din police bah"

"Erh gaskiya nima haka nakeson cewa, bari nakira police din Sai suzo"doctor yafada

Isowar police yayi daidai da isowar su big dady da duka yen gida amma banda yen matan gidan

Statement yen sanda suka karba sannan sukace dole Sai anje an bincike gidan su big dady.

Batareda bata lokaci bah suka dunguma zuwa gidan gabaki dayansu harda Amin.

Ganin gidan da motansu yayi horn yasa Amin sauke boyeyyar ajiyar zuciya.

Zaune suke akan sofa suna kallo while ita Nadhira na kitchen tana girki, muryan su big dadyn dataji yasata fitowa dasauri tana goge hannunta da hand towel.

Runguman shi tayi irin na sannu da dawowa sannan tace"ya naga harkun dawo?"

Sam bata Lura da yen sanda dakuma Amin dinda takafe ta da ido bah,ji yake dama shi ta runguma bah wannan mugun mutumin daya nakasar da sirkinsa bah.

Kuma gaskiya yasha mamakin ta amma daya tina dadynsu yace ya yafe mishi saiya basar da zancen azatonshi itama Nadhira ta yafe mishi neh, dadi sosai yaji wai ABAR SOnshi tana da kyakyawar zuciya(nace Allah yasa)

"Muna tareda police neh sunzo duba gidan"wani irin rass taji gabanta yabada kafin tamiyar da dubanta kansu daya bayan daya take binsu da ido har ta tsaya cakk da idonta akanshi.

Wata uwar harara ta jefe shi dashi tareda hade fuska kaman bata taba dariya bah ganin yana mata murmushi, jikinshi neh yaji yayi sanyi sosai.

Banda kallon shi babu abinda takeyi dukda yanzu tafara mantawa dashi cos dakanshi ya hadata da abokin shi amma kuma abu mai wuya neh ta manta dashi gabadaya a babin rayuwarta.(First love)

Maganar yen sandan neh yakatse su ,inda aka musu gajora zuwa dakin Maimuna din, duk bincike anyi amma ba'a samu komai bah banda kwalaben codeine.

Daki daki suka shiga amma ba'a samu komai bah, saukowa kasa yace aje aduba kitchen.

Duk iya binciken su ba'a ga komai bah, fita suka yi daniyar tafiya, har sun kai bakin kofa wanda yamusu jagora ya tsaya cak tareda facing dakin Nadhira yayi sannan yace

"Bamu duba wancan dakin bah" wani irin dum dum taji gabanta ya bada, Adduan datake karanta wa azuciyar ta yasa halin da tashiga boyuwa kadan.

"Amana jagora" taji anfada cikin in in na tace toh,gawani zufan dayafara karyowa takowani gaba najikinta.

Amin neh ya Lura da halin da tashiga,

"Akwai matsala neh??" Yatambaye ta

Wani hararan takuma banka mai ahasale tace"ina ruwanka dani"

"Muje" tafada hade da yin gaba, big dady mah alokacin ya daura ayan shakku akanta.

Bincikan dakinta akeyi abinda suka ganine yasa dukkansu miyar da dubansu gareta cikeda mama....

*Nace toww miye suka gani?🙆🙆*

*Vote,comment&share*

*Mhizzphydo*
💝💝💝💝💝
*ABAR SO*
💝💝💝💝💝

*WRITTEN BY: NAFISAT MA'ARUF SHEHU*

WATTPAD: MHIZZPHYDO
🌟GEORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F🌟

HOME OF GORGEOUS INTELLIGENTAND EXPERT WRITERS, WE ARE THE BEST AMONG THE REST

*Page 97*

Bincikan dakinta akeyi abinda suka ganine yasa dukkansu miyar da dubansu gareta cikeda mamaki.

Amin neh yakarasa wajen tareda tsungunawa zuciyar shi na zafi sosai har ga Allah baiyi tsammanin haka daga gareta bah kuma zarginsu ya tabbata akanta .

Runtsa idonshi yayi sannan yabude su so yake ya karyata abinda yake gani.

Daya daga cikin police din neh yake karewa Nadhira kallo nan kuwa yayi harba da kafanta cos as usual short gown neh ajikinta.

Dawowa sama da idanunshi nan kuma yakara harbawa da kirjin ta wanda ko bra bata sanya musu bah, wani irin yawu ya hadiye tareda lashe kasar labban shi.

Ganin kallon da suke mata neh yasata tattara duk nutsuwar ta waje daya takuma aza murmushi asamar fuskarta tareda karasawa wajen Amin cos ita kam mah tadauka wani abin daban zasu gani shiyasa tsoro shiganta .

Karban kwallin Condom din tayi hannunshi, tareda lura da yanayin bakincikin dayake ciki kafin tace

"Akan wannan abin kuke kallo na kaman wata sabuwar hallita,nikam mah har kunsa naji kunya"

Ganin yanda take magana naneh yasashi tsura mata ido for some seconds gani yayi duk wannan tsoron dakuma rashin gaskiyan daya bayyana a fuskarta dazu babu su.

Cikin sanyin murya yace"miye kikeyi dashi??"

"Toh miye zatayi dashi ai kowa yasan amfanin wannan abun guda daya neh tal" wannan police din yafada cos bakaramin bata mai rai Amin yayi da wannan tambayan bah.

"Lah😨😨 waye cemuku amfanin shi daya neh??" Ta tambaye su cikeda mamaki.

Shuru dakin yadauka suka sake Baki da hanci suna mai neman dayan amfanin Condom cause gabadaya ta jefa su aduhu.

"Ke karki raina mana hankali fah" wannan police din yasake fada a kaushashe cos gabadaya tafara bashi haushi ,shidayake son neman hanyan daza su hadu soboda gaskiya ran shi yabiya(Niko nace kwalelenka)

"Yadai kana min magana saikace yar ka??" Tafada tareda maka mai harara.

Zaro ido yayi ganin abinda tayi mishi amma ba damuwa zaijira insun hadu yafada mata shi baya daukan raini( lallai kam)

"Just say what kikeyi da wannan" yafada cikeda zakuwa

"Packing din gashi na nakeyi dashi" tafada sounding relieved

"What a bullshit" Amin yafada afusace cos gani yake raina musu hankali kawai takeson yi

Itadin mah bai tsira bah sanda ta banka mai nashi hararan, rolling eyes dinta tayi sannan tacire dankawalin kanta.

Nan kuwa doguwar gashin ta ya bayyana wanda aka tufke atsakiya.

Zaro abinda ta tufke gashin tayi tareda mika mishi abin wanda shi bah roba Lin bah。

Karba yayi yana juyawa ahannu shi amma har lokacin bai dago miye bah, shima police din karba(inaga shi yayi leading dinsu) yayi yana dubawa.

Duka dakin sanda suka rike abin suna kallo daga karshe suka miyarda duban su gareta.

"Baku gane miye bah koh??" Batareda ta bari sun yi magana bah ta ciro Condom daya daga cikin kwali.

Fatima kam harda rufe ido wai batason gani, dariya kawai tayi sannan tayi wajen drawer.

Razor blade tadauko sannan ta ijiye Condom din akan dressing mirror.

Yanka daidai wajen band din rike ...🙈🙈 tayi Sannan ta dago shi.

Toilet tashiga ta wanke yanda maikon zai bar jikin abin bayan nan tafito.

Na mujiya suka zuba mata suna kallon ikon Allah.

Mika musu tayi suna kallo Sai sukaga iri daya neh da wanda tacire akanta.

Murmushi tasakar musu tareda fadin" akan nayi amfani da roba Lin ya tsinka min gashi toh gwanda nasa wannan, in takaice muku nafi jin dadin amfani da '''CONDOM BAND''' akan kowani band"

Mamaki neh yacika su jin abinda takeyi da Condom cos basu taba zargin haka abin yakeba sun dai San ana amfani da Condom neh wajen kariya

while Amin ya dinga blaming kanshi akan zarginta dayake yi, sosai zuciyan shi yasamu relief jin ba abinda yake tunani bane

Dariya da ita kadai tasan ma'anar shi tafashe dashi sannan tace" I knew you will all be shocked, shiyasa ma dafari tsoro tashigeni dana tina da na fito da kwallin kuma dafari I thought bazaku tsaya ku fahimce ni bah"

Ta karashe maganar da murmushi, dukkansu mah murmushi sukayi amma banda wannan police din cos gabadaya shirin shi ya wargaje.

Fita sukayi daga dakin, cewa sukayi zasu duba compound din ba bata lokaci aka musu izinin dubawa.

Har suka gama dube duben basu ga komai bah, haka suka koma akan in Maimuna tafarfado zasuji komai...

Zaune take agaban mirror acikin daki banda murmushi babu abinda yake fitowa daga Samar labbanta.

Daman tin randa taje tasiyi Condom ta lura wasu na binta amma dayake shu'umace saitayi kaman bata gansu bah.

Abin mamaki kuma saitaga abokin Amin neh yashiga nan tasan tareda Amin sukazo kuma sawunta suka biyo.

Washe gari takoma chemist din tareda tambayansu wanda yazo immediately lokacin da tafita ,basu tsaya bata lokaci bah suka zayyana mata abinda ya tambaya dayake bakin su baida rufi.

Nan tamusu godiya tareda ficewa, tana komawa gida tadinga sakawa da warware akan yanda zatayi da Amin cos tasan yanzu yadaura Ayar shakku akanta kuma mai yiyuwa mah yafara zarginta.

Daman tinda taga doctors sunyi confirming substance din Cocaine acikin abin da tasha tasan dole Sai anzo yin bincike shiyasa tinda wuri tasan inda dare yamata.

Amma agarin kwashewa Sai akayi rashin sa'a Condom yafadi,amma batasan takamen men abinda yafadi bah irin bari tagama saita dauka Sai Allah yasa tamanta shi awajen.

Sai alokacin da akace za'a duba dakinta ta tina ashe bata dauki abinda ya fadi bah shiyasa tsoro ya shigata.

Tana ganin Condom neh ranta yayi fari fatt tsantsan murna cos tasan in akan Condom neh zata iya kare kanta...

Numfawa tayi tareda sakin wani murmushi tinawa datayi yanda tayi da cocaine.

Jan drawern jikin dressing mirror din tayi tareda daukan hands glove sannan ta tashi, dayake dare neh kuma anriga da an rufe kofa kuma tana kyautata zaton kowa yayi bacci.

Ahankali tayi jikin window tayaye labule, sliding glass din tahau cirewa ahankali gudun karyayi kara.

Tana gama cirewa tasauke ajiyar zuciya mai karfi, zura kafafun ta tayi sannan ta dira ahankali.

Wajen bolan gidan tanufa sannan ta sanya gloves din ahannunta, sanda ta daddaga wasu abubuwa kafin tazura hannunta chan kasa.

Torch din wayan ta tukunna daidai tafito da wani bakin leda. Tsince leathern farko tayi wanda yariga da yayi datti sannan ta yasar kafin tabar wajen cikin tsantsan murna...(nace master planner bah...)


*Vote,comment&share*

*Mhizzphydo*
💝💝💝💝💝
*ABAR SO*
💝💝💝💝💝

*WRITTEN BY: NAFISAT MA'ARUF SHEHU*

WATTPAD: MHIZZPHYDO
🌟GEORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F🌟

HOME OF GORGEOUS INTELLIGENTAND EXPERT WRITERS, WE ARE THE BEST AMONG THE REST

*Page 98*

Tsince leathern farko tayi wanda yariga da yayi datti sannan ta yasar kafin tabar wajen cikin tsantsan murna...(nace master planner bah...).

Straight kitchen tanufa sannan ta dauko container din gishiri tazazzage gishiri acikin buhun gishirin cikin store kafin ta zuba cocaine din acikin container din.

Ajiyar zuciya tasauke sannan tasake wannan murmushin muguntan ta kafin ta koma dakinta...

Washe gari ita tafara tashi tashiga kitchen ta dafa musu lafiya yiyar breakfast.

Kafin su fito ma har tagama komai ta feso wankan ta as usual cikin short gown yau kam ko dankwali batasa bah.

Ta zauna da 10mins yen gidan suka fara fitowa, sosai suka sha mamakin ganin abinci asamar dining table.

"Babynmu kece kika bawa kanki wahala haka??"mumy tafada cikin farinciki cos Nadhira bakaramin burge ta tayi bah

"Ai bawani wahala bane" tafada cikin sune kai kaman da gasket

"Madalla Allah ya biya"

"Ameen mumy"

Tashi tayi tareda karasawa wajen dining table din cos su kam har sun zauna sun fara serving Kansu.

Lura datayi Nadhira batacin abinci yasa mumy cewan" ya naga baki cin abinci"

"Inajiran Big dady tinda naga baku jira shi bah" Tafada cikin murmushin daya zame mata jiki

"Kin kyauta Babynmu "suka ji muryan Big dady daga bayansu.

Tashi tayi taje ta taroshi tareda mai Ina kwana amsawa yayi cikin Jin dadi tareda kawar da duka zargin dayake mata acikin zuciyarshi.

Zaunar dashi tayi tareda serving dinshi nashi abincin, lokacin har su Fatima sun gama cin abinci.

Gaishe shi sukayi sannan ya amsa cos in suna cin abinci ya hana su magana tashi sukayi suka bar wajen...

"In hado maka coffee neh??"tayi requesting

"Gyada mata kai yayi tareda sakar mata murmushi

Itama murmushin tamiyar mishi tareda

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login