Showing 30001 words to 32991 words out of 32991 words
wucewa kitchen.
Tea cup tadauko tareda fara zuba cocaine din akasa sannan tasa garin coffee din.
Ruwan zafi tadauko ta sheka akai sannan ta dauka spoon ta gauraya su hasaida aka daina ganin garin cocaine din sannan ta fice.
Ta kaiwa ta dauki cube din sugar sannan tasa aciki..
"Allah yamiki Albarka" dady yafada cikin mouthful
"Ameen" tafada tareda Zama akan kujera tukun tayi serving din kanta mah.
Ganin yakai cup din bakinshi neh yasata cikin boyayyen murmushi...
Dayake baiyi changing taste bah shiyasa Big dady bai fahimce komai bah.
Tass ya shanye coffee din harda gyatsa.
Ya na mikewa itama ta Mike dayake tagama cos bata cin abinci dayawa.
Car key dinshi ya dauka sannan ya mawa mumy magana wacce taje shirin zuwa asibiti.
Chan saigata ta sauko daga sama cikin takunta na matan attajirai...
Da murmushi ta tareta itama tareda taka musu zuwa waje
"Ke bazaki zoh dubiyan bane??"mumy ta tambaye ta cikin kulawa.
Murmushi tasake sannan tace" ni bana zuwa dubiya hannu zalla ma'ana so nake na hada koda kunu neh in case inta tashi tasamu abin sawa abaki"
Sosai suka sha mamaki cos ko kadan wannan tunanin baizo musu bah.
"Madalla Babynmu Allah ya biya ki in kin tashi tahowa driver yakawo ki" dady yafada.
Toh tafada still akwai wannan murmushin afuskarta, bye bye tayi musu sannan ta shige cikin gida.
Straight kitchen takara nufa agagauce ta daura ruwan akan gas tareda kara sa cocaine acikin ruwan..
Sharp sharp tagama hada kunun sannan ta juye acikin flask..
Dakinta tawuce ta Kira wani number,dagawa akayi daga dayan bangaren akace
"Ranki shi dade baki da sauki fah" yafada cikin muryanshi irin na mashaya
Wata karamar tsaki taja sannan tace"ya ake ciki??"
"Gaskiya aikan ki yanzu ya kara kudi soboda da kyar ake samu amma dai Alhmdllh ansama miki "
"Nawa neh ??"ta tambaya atakaice
"Dubu goma zaki ciko"
"Toh inason mu hadu nan da minti 10 zan taho maka da cikon kudin"
"Toh Hajiya muhadu a inda kika ce zamu hadu??"
Sanda tayi Jim sannan tace "tsari ya chanza"
"Toh yanzu miye tsarin" yatambayeta
"Akwai wani mai shago a anguwan danake ta bakin titi, inkaje saika bashi kace za'a zo akarba nikuma kafin ka karaso zan bashi aika ya ajiye maka, yanajin kace aika kazo karba zai baka kudin amma kayi wrapping dinshi yanda babu wanda zai gane wani Abu neh aciki" tana gama magana ta katse kiran tareda deleting din numbern"
Dariya yayi yana jinjina irin kwakwalwar Hajiyan( bai taba ganinta bah daman) afili yace"komin kwakwalwar ki yau kam saina san wace ce ke"
Tana ajiye wayar tasauke wata ajiyar zuciya kafin tabar cikin dakin da leather a hannunta.
Waje tafita dashi sannan ta gaisar da baba mai gadi.
Yana ganinta yafara wangale baki musamman mah daya hangota da leather.
"Wa'inan yaran fah??"ta tambaye shi
"Ai basu nan amma sun kusa dawowa daga makaranta"
"Ohk in sun dawo amin magana" tafada tareda juyawa"
Yace"toh" yana mai yin adduan Allah yabashi y'a kaman ta.
'''5mins later...'''
Fitowa tayi amma yanzu leathers biyu neh a hannunta.
Yaran suna ganinta suka fara murna cos sosai suke sonta.
Wanda tasan tana da nutsuwa kuma wanda bata fiye magana bah takira acikin su sannan ta jata gefe daya.
Bata leather daya tayi sannan tace "ki kaiwa mai shagon bakin hanyan nan,kina bashi kice za'a zo akarba sannan kijuyo"
Gyada kai yarinyar tayi sannan ta wuce wajen mai shago din.
Kaman yanda tace haka yarinyar tayi, tana dawowa tabawa yarinyar nata alawan cos daman kullum saita raba musu shi sadaka
'''5mins later...'''
Hango wani huge guy nayi wanda kallo daya xaka mai kagane bashida mutunci shagon ya shiga tareda bashi aikan sannan aka bashi kudin.
"Waye neh yakawo kudin??"ya tambaye mai shago
Mai shago kuwa ganin babu rahama afuskarshi yasa shi fada mishi wata ce ta kawo,
"Ya take??"
Nan kuwa ya zayyana mai kallan kayan yarinyar dayake akwai niqab afuskarta(daga islamiya suka taso amma babu uniform ajikinta)
Gyada kai yayi tareda ficewa daga shagon, yaje ya zauna a inuwa yana jiran dawowarta.
Hango shi tayi tacikin mota awajen inuwa,wata murmushi tasake ganin zaton ta yazama gaskiya.
Sanda suka danyi nisa tace mai ya tsaya sannan tace"in bazaka damu bah aika zaka karbo min??"
"Haba miye kuma abin damuwa anan,kifadi komiye ni mai iya miki neh"yafada cikin sanyin murya
Murmushi tasake akaro na biyu sannan tace "shagon bakin titi dinnan zakaje kasiyo min flour mudu 5, sai kaga yafara auna flour din ma'ana in yajuya baya saika dan duba min karamin leathern da aka mai kyakyawan package. Wannan leathern zaka dauko amma fah karka bari yagani. Ga wannan saika ijiye shi awajen da kadauki leathern"
Yace toh tareda karban kudi da wata farar envelope daga hannun ta.
Fita yayi daga cikin motan tareda wucewa shagon ,kaman yanda tace haka yayi ,yana karba ya faki idon mai shago sannan ya tusa leathern acikin flour din kafin yafito.
Yana komawa ya Mika mata leathern flour din karba tayi tareda ajiye wa cos batason ya bata mata hannunta.
"Wajen matan ka zaka fara kaini kafin muwuce asibiti din"tafada mai
"Toh"amsa tareda nufar daita anguwan Mahaukata(karku ce fah Mahaukata neh a anguwan a'a sunan anguwa neh kawai)
Anguwan talakawa neh sosai wanda kowa harkan gabanshi yakeyi ga yen talla sai fitowa sukeyi yasu wajen cin kasuwan su.
Adaidai wani gida mai labulen buhu yayi parking itama fitowa tayi tana jinjina ma masu Zama a anguwan.
Iso yamata zuwa cikin gidan inda ya tayata rike leathers din flour din samun matarshi sukayi inda take cilla dan wake acikin ruwa.
Gaisheta takeyi amma abin mamaki Maimakon matar ta miyarda hankalin ta kan bakuwa sai takara miyarwa kan danwaken ta.
Duban agogon hannunta takeyi inda yanzu taci minti uku azaune cos tintini driver yafita.
Gyaran muryan da tayi neh yasa matar Dan juyowa"gashi ni natafi"tafada tana tashi tsaye
Cikin dan Jin kunyan abinda tayi matan tashi tsaye tareda gaishar da Nadhira.
"Gashi akwai wani leather acikin wannan kidan cire min sai ki karkada min flourn jiki"tafada cikin nutsuwa
Cikin rawan jiki matan tasa hannu ta cire sannan ta karkada harda gogewa da zanin jikinta.
Karba tayi sannan tace"ni natafi sai watarana in Allah yayi zamu sake haduwa tinda na Lura kinfi bawa kasuwan cin ki muhimanci fiye da mutane" tana gama fadin hakan tayi gaba tareda boye leathern acikin side bag dinta.
Sosai matar driver taji kunyan abinda ta aikata cikin sanyin jiki takarasa gurin tukunyan sana'arta...
Suna Isa asibiti tabar side bag nata acikin jaka sannan tafito da flask din kunu.
Shiganta dakin yayi daidai da farfadowan Maimuna kuma alokacin akwai doctors aciki, ciki kuwa harda Amin.
Gaishe su tayi cikin sanyin murya sannan ta karasa wajen gadon Maimuna din.
"Ya jikin ki??" Tafada a hankali,itakuwa Maimuna banda binta da ido babu abinda takeyi.
In akwai liquid abinci abata soboda taji karfin jikin ta"Amin yafada
Mumy neh ta dauki flask din tareda zuba kunun ciki acikin cup.
Nadhira neh dakanta ta sawa Maimuna cup din abaki, ita kuma banda kallon Nadhira din babu abinda takeyi.
So take tayi magana amma saitaji kaman an rike mata makogaron ta.
No tausayi haka Nadhira tabata kunun nan Tass...
'''3hours later...'''
Fita tayi don komawa gida soboda babu kowa, drivern neh dakanshi ya bude mata kofan motan.
Da murmushi tace "ai da baka wahalar da kanka bah"
"Girman ki neh" yafada shima...
Daidai gurin mai shagon takara ganin shi wata murmushi tasake sakewa dayake motan tinted ni shiyasa ba wanda yaganta.
Suna Isa gida tawuce daki, numbern shi tasaka awayan tareda danna mai Kira...
Ganin mai kiranshi yasa shi saurin dauka(private number)...
Dariyan dayaji anyi neh yasashi kallon fuskar wayan cos ko murmushi bayajin tayi in har takira.
Cikin nutsuwa tace...
*Vote,comment&share*
*Mhizzphydo*
ππππ
*ABAR SO*
πππππ
*WRITTEN BY: NAFISAT MA'ARUF SHEHU*
WATTPAD: MHIZZPHYDO
πGEORGEOUS WRITERS FORUMπ
πG.W.Fπ
HOME OF GORGEOUS INTELLIGENTAND EXPERT WRITERS, WE ARE THE BEST AMONG THE REST
*Page 99*
Cikin nutsuwa tace " I thought you're a smart guy but unfortunately you're not,
You thought zaka iya min wayo koh??"Wani dariya takarayi tace" I trust no one in fact I don't even trust myself cos tunani nah na iya chanza wa akowani lokaci so....
Katse ta yayi fadin"miye faru neh ranki shi dade??"
Dariya takuma yi tace" all pretence aside, daman shawara zan baka"
Sanda yayi Jim yana dan juyawa ko taganshi neh amma baiga alaman ana kallon shi bah.
"Miye sa kakeson sanin waye ni??" Tambaye shi batareda tajira cewar shi taci gaba" nagane sokake in polisawa suke kama ka kafito dani koh??
Dariyan rainin hankalin yayi yace"kina tunanin in suka kamani bazan binciko ki bane??"
"Toh ka sani ni nan inuwa ce baza'a iya kamani bah ko ka taba jin inda aka kama inuwa neh??"
"Kaman dagaske yafada in amusement, bayan zaki fito daukan aikan ki??"
"Aika?? Nawa yaushe kenan fah??"
"Nadazu mana"
"Kama daina bata lokacin fah soboda nariga dana dauki kayana!!"
A saba'in yamike daga inda yake yace"wannan mah karya neh"
Dariya tayi tace" go and check nabar maka aika awajen mah"
Baijira cewar ta bah ya katse wayar tareda nufar shagon, ko sallama babu yace"ina abinda nakawo dazu??"
Duba inda ya ajiye yayi yakalli farar takarda instead of bakin leather.
Hannu na rawa ya dauki takardan tareda warwarewa wata kyakyawan rubutu neh ya bayyana(irin na 3sweet besties dinaππ)
"FOOL!!!" Harya cakumo wuyar rigan mai shago kawai sai wayan sa ya dau kara dasauri yasake shi hade da picking din wayan.
"Karka mawa mai shagon komai cos shima baisan lokacin da aka dauka bah"
"Ke waye ceh??"
"Someone who is seeking for revenge on the death of her mom and sister!!!" Tana gama fadin hakan ta Kaste wayan.
"Hello! Hello!! Hello!!!" Ganin batayi magana bane yasashi duba screen din wayan
"Holy shit" yafada tareda nausar gini sannan yasa kai ya fice...
Zama tayi agefen gado ta bude ledar ganin abinda yake ciki yasata fashewa da kuka mai tsuma zuciya, sanda tayi mai isarta sannan ta share hawayen ta tareda shigawa toilet domin yin wanka.
Tana gama wanka tashige kitchen domin dafa musu abincin rana soboda 1 tayi..
Tana cikin hadan abinci mumy tadawo..
"Sannu da dawowa mumy"
"Sannu da aciki Babynmu"
"Ina big dady yake"
"Wai zai shiga ganin likitanshi cos baidan jin dadin jikinshi"
Wani irin faduwa gaban ta yayi amma ta waske tace"shine bakuje ganin likitan tareda shi bah??"
"Ai banma san kin fara abinci bah cos shi nazo dafawa".
"Ohk, ya jikin Maimuna din??"
"Hmm, jikinta sai sake rikicewa yakeyi gabadaya tafice hanyacin ta" mumy tafada cikeda jimami
"Ayyerh Allah yabata lafiya"
"Ameen" mumy tafada tareda ficewa
Ajiyar zuciya tasauke sannan tayi wannan dariyan muguntan data saba yi tacigaba da aikin ta.
'''Hospital'''
Big dady neh zaune agaban doctorn shi ya nutsu yanajiran yaji sakamakon test dinda aka mishi.
Gyaran murya doctor yayi ya gyara zaman medicated glass dinshi yace
"Sakamakon test dinda aka maka yanuna am sorry to say sir that it's obvious that ana sa maka some substance I mean like cocaine acikin maybe drink or something else
Afirgice big dady yace "what!!!"
"Yes sir and gaskiya it's like kaman ana sawa acikin stimulant drug substance kaman coffee"
"Nadhira" yafurta asarari tareda runtsa idonshi gam, bude idon yayi yana kallon doctorn daya kafe shi da ido.
"Any prescription??"
"Yeah" yafada tareda yin rubutu acikin paper sannan yamika mishi.
Musabaha sukayi sannan big dady yafita yana tunanin irin matakin da zai dauka akan Nadhira din...
Tana gama dafa abinci tashirya shi acikin basket sannan ta mawa mumy sallama tareda ficewa zuwa asibiti.
Clashing sukayi da big dady inda tasakar mai murmushi sanda idonsu ya sarke dana juna.
Kwafa yayi acikin zuciyar shi yace "kin kusa bin su kema!!!"
'''9:00pm'''
Big dady neh da mumy zaune akan sofa sai jijiga kafa yakeyi yana cizon labba mumy neh ta tabashi tace
"Lafiya kake kuwa?"
"Lafiya lau"yabata amsa zata sake magana kenan Nadhira tafito daga dakinta daga sanye da Silk Patterned Pyjama, wando Pyjama din dan guntu iya cinya.
Wani yawu big dady ya hadiya yana ayyana abubuwa da dama akanta
"Big dady barina hado mana coffee koh??"ta katse mai tunani tareda shigewa kitchen batareda tajira miye zai ce bah...
Cups biyu a hannunta as usual,mika mai nashi tayi sannan ta zauna gefen shi tana kokarin kai nata baki
Murmushi yayi azuciyarshi yace"shegiya saikema kinsha cocaine dinna"
"Babynmu muyi changing din coffee ma....
*Vote,comment&share*
*Mhizzphydo*
ππππ
*ABAR SO*
πππππ
*WRITTEN BY: NAFISAT MA'ARUF SHEHU*
WATTPAD: MHIZZPHYDO
πGEORGEOUS WRITERS FORUMπ
πG.W.Fπ
HOME OF GORGEOUS INTELLIGENTAND EXPERT WRITERS, WE ARE THE BEST AMONG THE REST
*Page 100*
"Babynmu muyi changing din coffee mana" yafada yana sakin murmushin mugunta.
Daukewa annurin fuskan ta yayi tace" big dady baka shan sugar sosai fah"
"No yau zan sha "yafada tareda karbe coffee din hannunta yabata nashi.
"Drink"yafada tareda kafe ta da Ido.
Ahankali ta dauki cup din ta nufi bakinta dashi.
Sipping takeyi ahankali sannan shima yakai nashi cup din baki azuciyarshi yace" in kinsan wani baki san wani bah"
Atare suka gama shan coffee din inda ta musu Saida safe ta shige cikin dakin ta.
Tana shiga ta sa key tareda yin wani irin super tafada kan gado.
Juyi tashiga yi asaman gadon cikin Jin dadi abinda yafaru dazu jira kawai takeyi su ta bacci ta aiwatar da next plan dinta...
Palour kuwa suna zaune kan big dady yafara sarawa cikin sauri mumy ta dauko maganin shi ta balla mai ya sha nan ta taimaka mai ya haura stairs suka shige daki...
```Washe gari```
Sosai big dady yadan ji saukin ciwon kanshi kuma daman zaiyi tafiya neh zuwa wani meeting nasu na masu kudi kuma shi kadai zaije...
As usual har Nadhira ta tashi tayi daily chores nata harda girki tayi ta jera su akan dining table...
Big dady sai satan kallon Nadhira yakeyi yana son gano reactions dinta.
Dago kai tayi ta kalle shi sannan tasakar mai da murmushi , ya dauki coffee zai kai baki tace" big dady ko yau ma zamuyi exchanging din cup neh??"
Kura mata ido yayi yace" no kowa yasha nashi"
"Gaskiya bazan yarda bah nikam sai mun yi exchange" tafada tareda komawa ta gefen shi
Ganin yanda ta dage neh yasashi fadin"nikam bazan sha sugar bah ko sokike diabetes dina ya tashi neh"
Bata fuska tayi tace"Oops am sorry"
Azuciyarshi fadi yake"Shegiya an gaya miki zan barki ki Kashe ni da raina neh?? Ai ina dawowa zanyi maganin ki shashasha kawai"
Cikin kwanciya hankali ta fara kurban coffee dinta acikin zuciyar ta kuwa ita kanta bazata iya fadin irin farincikin datake ciki bah...
Ita dakanta ta dauka mai office bag nashi zuwa mota,
Allah yakiyaye hanya suka mishi sannan suka koma cikin gida...
```30 minutes later...```
Zaune suke dukkansu acikin palour suna kallon wani Indian film mai suna Sanam Teri kasam sosai suka nutsu cos film din sosai yake kayatar dasu kuma suna jin dadin shi dukda su emmatan wajen sai share kwalla sukeyi(π€§nima ko yaushe na kalli film sai nayi kukaπ)
Daidai sun gama kallon wayan mumy yayi kara sanda tayi Jim tukunna kafin ta dauka soboda bakon number datagani
Sallama tayi sannan aka amsa daga dayan bangaren
"danAllah waye neh"tafada asanyaye cos haka kawai taji jikin ta yayi sanyi
"Kina magana da inspector Nasir neh"
Wani irin miyau mai daci ta hadiye tace" lafiya dai koh??"
"Erh akwai wani patients naki a teaching hospital"
Ajiyar zuciya tasauke tace to gani nan zuwa bata jira cewan shi bah ta katse Kiran...
Sosai inspector Nasir yasha mamakin ta amma sai ya basar...
"Miye faru mumy??"
"Ashe yau bamu leka Maimuna bah har an fara neman mu a asibiti so you guys should go and pick up ur khimars"
"OK " suka fada in chorus sannan fice...
```Teaching hospital Bauchi```
Suna isa wayan mumy yadau kara
"Ku taho emergency in kun iso"
"Ohk" tafada sukayi hanyan emergency din
"Yana ga munyi tanan??" Nadhira ta tambaya
"Erh inaga condition dinta yayi worse neh" mumy ta bada amsa
Basu kara magana bah har suka isa
"Kune aka Kira??" Wani yafada
Mumy tace"Erh"
"Ohk ni neh wanda kuka yi magana dashi wato inspector Nasir"
"Ohk nagane " Tafada tareda gaishe shi shima ya amsa
"Ku biyo ni" binshi sukayi kaman jela har suka iso casualty room...
Gurun gado ya nufa dasu inda suka cika da mamaki ganin Maimuna ba ciwo taji bah amma da sunyi la'akarin kwakwalwar ta yadan samu matsala sai hankalin su yadan kwanta ...
Cakk suka ja suka tsaya dalilin hango wanda basu yi tsammanin gani bah akan gado...
Nadhira batayi la'akari da cewan hospital sukeyi bah ta kurma wata iriyan wawaiyan ihu ai basu hankara bah suka jita ak...
*Vote,comment&share*
*Mhizzphydo*
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels