Showing 3001 words to 6000 words out of 32991 words

Chapter 2 - ABAR SO COMPLET

Start ads

24 Aug 2025

191

Middle Ads

dai wannan matar kallonsu takeyi cikeda sha'awarsu  dakuma sonsu, Amma zata iya cewan tafison yayar tashi.

"Adawo lafiya "shine abinda matar tafada

"Allah yasa antynmu"  yaron yabata amsa yana Kuma Jan yayar tashi , har bakin kofan gidan tarakasu hade dah jin tausayin babyn.

Suna fita Ido yadawo kansu as usual cos anguwan is an open area  , sanda ta kalli  da gefe Kaman xata tsallaka titi  anan kuwa ta Hango wasu  yanmata uku Wanda suka ci kwalliya Kaman zasuje gasar miss world  girgiza head nata tayi  hade dah juyawa tana karewa anguwan kallo  like ranar tafara zuwa. Salim neh ya girgizata sai alokacin tasauke ajiyar zuciya  murmushi yamata sannan yace

" babynmu mutafi kar nayi latti " sai a sannan tatina ashe rakiya tafito yih

Daidai Sun iso wajen masu zaman kashe wando ,Wani acikin samarin yake fadin

"Tinda nafara ganin yarinyan nan naji tamin Amma ina ganin Kaman tanada tabin kwakwalwa neh " 

" gaskiya yusuf nima Ina hankare da hakan  cos bantaba jin tayi magana bah" Wani yafada

" Inaga fah rainin hankali neh kawai dakuma rigima baku ga yadda take tafiya baneh,  tana tafiya tana yanga  Allah ni ban son irin su gashi kullum acikin manyan khimar saikace matar malam "

" kaidai khaleel kabari waye sani koh fuska biyu ce daita ,ai munsan irin su  ga kyau kaman wata yar  india "....

Shine magangannun da taji Suna fada among themselves. .....

Takaishi  kenan tanadawowa taga wannan emmata ukun dazu xasu tare adaidaita  taxo daidaisu kenan wata acikinsu tasamata kafa,saura kiris tafadi  dasauri tayi regaining din tsayuwar ta ,zatacigaba da tafiya taji anrike Mata khimar

"kewata irin dakikiya ceh,ko ke makauniya ce daharxaki takani Amma ko kiban hakuri "

inji wata ameera dafada, rolling din anime eyes nata tayi Wanda suka sha kohl, da eyes tabisu daya bayan daya ,Sanye suke cikin atamfa roba roba wanda akamai dinki cin mutunci ,ganin yadda take binsu da kallo yakara tunzira su

"mukike kallo Kaman kinga kashi lallai yau xamu koyamiki hankali " inji nana

"shegiya yar matsiyata harmu xakina mawa irin wannan kallon to bari kiji  muba tsararki bane  cos mu koh tuwo bamuci ,breadi mah idan mukaci tokara kirjinmu yake" inji zainab dafada

ita dai kuramasu ido tayi Kaman maison gano abu  ,can da ta yamutsa fuska hade dah fizge khimar dinta , cigaba tayi da tafiyanta  sukuwa abin yabata musu rai,ai wannan mah cin face neh  ace big girls dasu, wata tasharesu agaban samarika irin bari sukoya mata sense dinnan . Da sauri Ameera takarasa wajenta tareda kifa mata mari ai stars kawai tafara hangowa cos tunda take ba'ataba marinta bah ,ai kafin tagama tunani ankara kwashe ta dawani , tsantsan zafineh yasata sakin wata yar Kara kawai saiga hawaye sunfara running down her cheeks

"ai bakiga komai bah wlhy, saina ciremiki hakori shegiya yar Dangin mayu "wata daga cikinsu tafada .

Aunty kuwa jin haryanxu babynsu bata dawo bah yasa hankalin tab yafara tashi ,fitowa tayi kofar gida taga anyi circle dan nesa da gidan amma bata masaniyar abinda akeyi ,can kawai taji wani kara Kuma Kaman muryan babynsu ai dagudu takoma cikin gida hade dah sanyo khimar ......

Wannan karar da taji bana kowabane sai na baby sakamakon naushin da aka kai Mata akan hanci ,atake kuwa jini yafara fitowa ,ai tana ganin jinin tarude .... tana gogewa yanakara fita  ...batasan lokacin da tayi fling da khimar dinta bah "blood!blood!!blood!!!, wayyo Mommanmu, nafhi nah wayyo jini arikice take fadin wannan kalmomin Kuma Jini baifasa fitowa bah.

Dagudu antyn takarasa wajenta

" innalillahi wa innaillahi rajiun" shine abinda da antyn take Maimaitawa  daidai lokacin da takarasa wajenta

"Antynmu, there's blood everywhere  , kar NAFHI  na tamutu ,anty wayyo mommanmu  karki barni  nima mutuwa xanyi , wlhy saina  ga bayanka da hannuna zan kashe kah,  baxan taba barinka bah, saina dau fansa mugu azzalumi , macuci ,natsaneka wlhy "

shine Sumbatun da takeyi  duk Wanda yake wajen saida ya tausaya mata  Sun Ameera mah Sun tsorata da yanayinta , Antyne ta rungume tah itakuma agarin fizge fizge hulan kanta yafita

" masha Allah "

shine abinda nafurta , gashinnan har gadon baya Kaman na yan India cos har tsantsin Shi  daga ido xaka gani. Shiru naji wajen yadauka  ashe suma tayi  , antyn ne ta lalubo phone dinta tabugawa doctor kira ,acikin mintunan dabai wuce 10 bah  doctor din ya iso.

"Hajiya miye sameta ?"Shine abinda yatambaya haryanxu akwai mutane awajen saikace ana karban sadaka. ...lol.....

" wai jini tagani tafirgice "

antyn tafada cikin Sanyi murya . Ruwa yadauka yazuba mata a face  ai kuwa nan tabare baki  alaman kukan xatayi Suna hada Ido da antyn jikinta yayi Sanyi cos she was wearing a pity face  A hankali talafe ajikinta kamar wata yar baby.... ashe babyn ce hhhhhh.....

"Babynmu"

doctor yakira sunan ta ahankali ta dago takalle shi sosai sannan takawar da face dinta sbd tunowa abubuwan dasuka faru dazu , juyawa tayi ta kalli su Ameera Wanda suka yi zuruzuru dasu Kaman sunci kudin aika aikuwa a saba'in yatashi tanufe su

" nikuka mara,  kun kuwa San wace nih kuwa ?niceh yar matsiyata shegiya eh?" Saikawai tajuya ga antynsu

" wai gaskiya neh ? Girgiza kai antyn tayi alaman a'a

" toh Amman shine wa'innan villagers din suke zagina son ransu"

bata gama rufe baki bah wata hadeddiyar car takaraso wajen ai nan kuwa kallo yakoma wajen car din , Wani magidajin mutum neh yafito daga car din

" antynsu miye Sami babynmu  aikuwa muryan Wanda taji neh yakara bakanta mata rai  Amma dayake shu' umace  kawai saitafada jikinshi , fashe mishi tayi da kuka Mai tsuma rai

" big daddyna kaga wa'inan neh sukecin zalina harda zagina

" tafada cike da  shawagba tana Kuma numashi su ameeran da yatsa,  aikuwa nan ya balbale su Amma aranshi cewa yakeyi "da kasheta
Kukayi wlhy babu abinda zai hana ni baku money "sum sum suka bar wajen ...

Big daddy saina tarwatsa rayuwar ka , saina tabbata ka walakanta  , Ni NADHIRA nadau alkawarin hakan "  Sune maganganun da take fadi a ranta

LABARINSU.........

💋💋 wurarh💋💋

💝💝💝💝💝💝
                          *ABAR SO*
                                     💝💝💝💝💝💝

*WRITTEN BY* : *NAFISAT MA'ARUF SHEHU*
                                       💋💋 *WURARH* 💋💋

🌟 GORGEOUS  WRITERS  FORUM 🌟

                 🌟 G.W.F 🌟

HOME OF GORGEOUS INTELLIGENT AND EXPERT WRITERS,WE ARE THE BEST AMONG THE REST

*Page 30-35*

Nadhira Sheriff Ahmad  Salim Shine ainihin sunanta ,su biyu mommansu ta Haifa Wanda suka kasance yanbiyu ,wato NAFHIRA da NADHIRA.

Nafhira takasance mutum Mai hakuri,kyakyawa ce sosai fara tas,zamu iyacewa mah su identical twins neh cos haske kawai NAFHIRA zata nunawa NADHIRA  kasancewan ita tadauko hasken mommansu Wanda ta kasansance ba india , ita Kuma NADHIRA ta dauko hasken daddynsu  (bafulatani).

Daddynsu sha'araren international business man neh Wanda xa'a lissafa shi acikin top 3 din masu kudin Nigeria , a kudin dayake dashi har 7th generation nashi bazasu yi talauci bah , yakasance mutum mai yawan ibada, yanada kyauta .Alhaji shariff yanada yaya daya Wanda suka kasance uwa daya  uba daya  cos matan babanshi biyu neh amma Allah baibawa ita uwar gidan haihuwa bah shiyasa mamansu tabawa uwargidan kyautar Isah (yayanshi) .

ISAH  bashida mutunci ko kadan ,baitaba son cigaban kanin nashi bah ,yatsane shi amma agaban iyayen yafi kowa sonshi  tin shariff bai  ganewa har yazo yagane . Lokacin da suka tafi kasar waje karo ilimi alokacin neh gobara tacinye gidansu bb Wanda ya tsiradaga Wanda suke ciki aka suka kone kurmus. Lokacinda mutuwan iyayen ya riske su bakaramin tashin hankali  suka shiga bah , Sun girgiza da mutuwan Amma bb yadda suka iya tunda Allah yafisu sonsu a haka suka yi yakana.

Akwana atashi sai gashi Allah yayi Sun gama school  inda suka karanci course daya wato Business Admin  Suna dawowa aka raba gado inda Isah yadinga almubaxaranci Danashi kason Kuma yayi aure . Shi kuwa shariff yahada hannun jari   dawani company a China

*Two  years later*.........

Kullum arzikin shariff bunkasa yakeyi  Shi Isah yana neman aiki cos yaga yanashirin talaucewa matarshi Hauwa  mutumiyar kirki  kullum cikin yimai wa'azi take mai cos talura da irin kiyayyar da mijin ta kemawa Dan uwanshi.  Alokacin kuwa sunada yarsu Fatima dakuma sabon ciki . Lokacin da  HAUWA taga talaucin yakusan musu kamun kazar kuku ,saitabada shawarar yaje wajen Shariff tunda yanada shi ,aikuwa anan yake gwada mata babu abinda zaisa shi neman taimako awajen kaninshi ,babu yadda ta iya ,haka tabarshi.

Lokacin na tafiya arzikin shariff  kara bunkasa yaketayi ,yanxu Kuma Shirin aure yakeyi , sai wata mumunar labari yariske shi wai Fatima da kannuwata (kasancewan mamansu takara haifan wata maiSuna Maryam )Suna wasa da candle bisa ganganci  wutaya  diga a curtain, ahankali yake kamawada wuta ,dakyar aka samu aka fitardasu daga cikin gida ,ko kwandala ba'a fitar daga cikin gidan bah  kasansewan night neh . Daman ISAH Kuma da certificate yake takama  gashi yanxu ya kone,dolenshi ya amsa tayin matarshi nazuwa wajen Shariff,  batareda bata lokaci bah Shariff yabashi kyautar Wani katon gida daga cikin gidajenshi na  anguwar GIDA DUBU ,dakuma babbar shago wanda shida kanshi yake supplying dinkayan shop din  kasancewan ISAH baxaiya aikin office bah . Aganin Shariff kiyayyar da Isah yakemai zai rabu .

Shariff yayi aurenshi inda lokacinda yatafi India ya hadu dah CHANDRAMUKHI soyayya mai tsabta yashiga tsakanin su . Chandra ita kadai iyayenta suka Haifa Kuma talakawa neh sosai amma dukda hakan suna samun na daily bread . Iyayen sunyi iya kokarinsu naganin Chandra bata auri Shariff bah amman hakan ya gagara cos Chandra cemusu tayi in basu barta ta auri Wanda takeso bah she will elope with him ,babu yadda suka iya aka suka barta.

Anyi aure da wata daya ,Chandra ta musulunta inda tazabi Suna NARGIS cos a India ta musulunta Kuma wai sunan kakanta nawajen amminta neh .NANU (kaka) taji Dadi sosai inda Kuma iyayenta suka yi fushi da ita, dakyar  dai suka sauko kasancewan bakin alkalami ya riga ya bushe.

Aurensu da wata biyu  suka koma Nigeria sunyi kukan rabuwa barinma Nargis da amminta ,dakyar dai suka hakura inda shikuma yamusu alkawarin zasu nah zuwa lokaci zuwa lokaci.

Gidan yayanshi yafara sauka  donya gabatarda matarshi ga yayanshi , gigicewa neh kawai Isah baiyi bah sanda yakalle irin kyan Nargis  atake kuwa yakara tsananta tsanan dayamawa  kaninshi Kuma ya kudurta Wani aniya akansu. Sun tare awani big mansion  nagani nafada a G.R.A  cikin garin Bauchi.

Kwanci tashi babu wiya inda na Hango Nargis da bukekiyar ciki  wanda haihuwa yau ko gobe.  Cikin dare Nargis tafara naquda inda Shariff ya garzaya da ita NI'IMA Consultant  Hospital . Bata Dade dafara naquda bah Allah ya sauke ta lafiya inda ta haife yarinya dagabaya kuma aka gane ba ita kadai bace ,after one hour takara haifo wata ,kuma a haihuwan nabiyun neh tasha wahala. Yanbiyun ta  kyawawan gaske kasancewan Nargis mah ba'a baya bah wajen kyau.

Ranar Suna  yanbiyu sukaci suna HASANA ( NAFHIRA) dakuma HUSAINA(NADHIRA), alokacin Kuma ya'ya Isah  wato  Fatima da maryam Sun girme su .Daganan Kuma haihuwa yatsayawa Nargis  sbd mahaifan ta bashida kwari.

*12years later*.......

Abubuwa dayawa sunfaru ciki kuwa shine alfarmanda  Nargis  (momma)taroki mijinta daya Kara aure ,soboda yanda ta lura mijinta (dady)Mai son ya'ya ,dakyar da sudin goshi  ya yarda, inda Kuma yace tanema Mai Mata cos Shi babu wanda yake SO batayi kasa a guiwa bah  tazaba mai  yar ajikinta maiSuna Amatullah .

SU Amatullah talakawane sosai ,lokacin da aka mata maganar auren mijin uwar gidanta taso taki ,saida aka hada da roko kafin ta amince dayake Kuma tana mugun ganin  mutuncin Momma. Aisha irin mutanen nan neh masu saukin kai ,nutsuwa dakuma rike addini ,ita ta raini NAFHI da ABAR SO  tana mugun son yaran Kuma suma Suna son ta ,acikin halayen Momma  da antynsu babu wanda basu dauko bah . Anyi aure lafiya inda bayan yan watanni ciki yabayyana ajikinta ,murna awajen familyn ba'a  magana  alokacin neh suka jeh kasa mai tsarki sauke farilla dukda bawannan bane zuwansu nafarko bah Kuma alokacin suka hadu dah Amin.

Sun dawo da wata daya  aka nemi dadynsu   aka rasa , sunyi kuka harsun godewa Allah ,bayan yan watanni antynsu  ta haife baby boy inda yaci sunan Salim wanda daman kafin bacewar dadynsu yace sunan yake SO.

Nafhi (haka akecemata) da Nadhira ( ABAR SO KOKUMA BABY,haka sukecemata ) sunje gari ruka da dama Wanda ba'acikin Nigeria bah. NAFHI  tafi ABAR SO  hakuri nesa ba kusa  bah while ita ABAR SO tanada saurin fushi ga shegen zuciya Kuma duk sunada ilimi sosai ,babu abinda basu iya bah .

*2 years later*. .......

Cikin shekaru biyun da sukawuce anyi zaman Dadi dakuma bah Dadi a familyn. Saikuma labari tariskesu wai ansamu gawan dadynsu,basu yarda da abinda aka fada bah sanda aka kawo gawar dadynsu nan kuwa tashin hankali yadawo Sabuwa a familyn .

Sun fito takaba kenan wata Sabuwa alamari ya bullo wai dadynsu yayi signing din duk will nashi wa yayanshi Isah  wannan batu ya girgiza su ainun ace wai duk propertyn su basuda kaso aciki sai gidan da suke zaune ,ai atake jini.........

💋💋 wurarh 💋💋

💝💝💝💝💝💝
                            *ABAR SO*
                                      💝💝💝💝💝💝
WRITTEN BY:NAFISAT MA'ARUF SHEHU
                                       💋💋 WURARH💋💋

🌟GEORGEOUS WRITERS FORUM🌟
         🌟G.W.F🌟

HOME OF GORGEOUS INTELLIGENTAND EXPERT WRITERS, WE ARE THE BEST AMONG THE REST

Page  40-42

Jini yafara fitowa antynsu ta baki Sakamakon tarinda ya caske tah,rushing nata sukayi zuwa nearest hospital domin ceto ranta ,kuka kam awajensu ba'a magana.
Suna isa hospital din  aka wuce da antyn emergency, bayan minti talatin aka fito da antyn zuwa resting room sannan doctor yamusu bayani akan cewa heart nata neh yaso bugawa ,Sun tsorata sosai dajin bayanin doctorn.  Sannan yakara dacewan mutum dayaneh xata kwana daita . Dakyar suka bari NADHIRA tazauna cos bb Wanda yakeson barin antyn ai kuwa Salim cewa yayi baisan zancen bah haka suka barshi cos bb yanda suka iya cos yaron akwai naci.Bayan sun tafine suka lura ko flask basu xoh dashi bah ,haka NADHIRA  tanace saita dauko ........

Suna isa gida suka samu babu Baba gateman akofar gidan ,akadai suka garzaya cikin gidan cikeda rashin damuwa Kuma yayi daidai da isowar Nadhira kofar gidan . Abinda suka tarar cikin gidan neh yasasu mutuwar tsaye, wato wasu mutane neh suka gani wanda daga yanayin faces nasu mutum xaigane basu da imani sai Kuma guda daya Wanda yake da face mask ,itakuma Nadhira lokacin take karasowa cikin sanyin tafiyanta kawai saitayi Gamdatakar  da abinda ya tsoratata ,aikuwa atake tafasa Wani ihun daya sa su Momma  farfadowa daga suman tsayen dasukayi,itakuwa bata Hankara bah taji saukan Abu akanta , Wani ihun takuma yi tareda zubewa  kasa  kwallan wahala nafitowa da fuskanta , a saba'in suka karasa wajenta cikin kuka tallabo tah sukayi  sai sukaji muryan Mai mask din nacewa "kukaraso kuji naku hukuncin" jiki na bari suka  hantaya wajen shi  yayinda suka bar Nadhira cikin mawuyacin hali ......

"Kunga wancan" ya nuna Nadhira da finger

"Saina yih raping dinta, kai bama ita kadai bah  harda Ku "
Ai sai suka Kara fashewa da Wani kukan

"DanAllah Karka taba min yarana, narokeka da girman Allah kafadi konawa kake so  ni maibaka neh amma pls Karka lalatamin rayuwar ya'ya na " Momma tafada cikin hot tears .

Sanda yakare wa gidan kallo  kafin yace

" Ina takadar wannan  gidan?"
Dum kirjin Momma yabuga cos  a halin yanxu gidan shine abu dayan dake mallakinsu, amma there's no other option left for them

"Yana upstairs " Momma  tafada cikin cracking voice

" kai, bita kudauko" yayi commanding daya daga cikin boyz nashi.

Suna haurawa yafito da string din allura daga cikin bag dinsu, Kuma yayi daidai da lokacin da  Nadhira  takarasa crawling zuwa wajen Nafhi, hugging din junansu sukayi cikeda tausayin kansu,basu Ankara bah sukaji yaraba su dakarfin tsiya, afirgice suke kallonshi  shikuwa tsayawa yayi yana kallonsu one after the other , kawai saiya fixgo Nafhi  bodynshi ,atake kuwa sigar jikinshi yafara tashi  cikin Wani irin voice yafurta" kinga wannan  allurarna lalata mahaifa neh , innamiki babu ke babu haihuwa har abada" dariya yafashe dashi  tareda shafar neck dinta zuwa kirjin ta  Wanda kana iya jin bugawanshi  har up and down breast nata yakeyi , ganin abinda yake Shirin mawa yar'uwar ta yasata karfin halin fadin

"DanAllah karka cutarmin da yar'uwa ta ,nayarda ni kamun alluran amma Karka mawa yar'uwa ta komai " tafada tana hada hannayenta waje guda , kawai Saiya wullar da Nafhira gefe  hade dah karasawa wajen Nadhira da Allauran,  Nafhira Kuma ganin abinda yake shirin mawa yar'uwa ta  yasata yunkurawa tatashi  amma sai boyz nashi suka ririketa .

Daidai ya iso wajenta ta Hango Wani ring a finger nashi , atake kuwa tafara tunano inda tasan ring din, ai nan kuwa ta tariyo lokacinda  dadynsu  yadawo daga China .......

"Dadynmu"

" Na'am babynmu"

" wannan fah?" Ta tambaya tana nuna abindake hand nashi,

"Yamin kyau sosai , Kuma fah Kaman pure silver neh koh " tafada tana rolling eyes nata

" eh mana babynmu"

"Amma dadynmu  nawaye haka ?ta tambaye shi

"Wlhy  wa big daddynku  nasa akayi wa  sbd inaga Kaman zai mai kyau "
Rola anime eyes nata tayi  sannan tace

"Gaskiya kam nikam mah bantaba ganin design din da  yamin kyau kaman wannan bah, amma akwai tsada koh?"

"Babu wani tsada  sosai cos 25m nasa akamin" .

"Gaskiya nikam baxan iya siyan common ring  da 25m bah ai it's a like waste of money"
Dariya yayi kafin yace " nida harna riga nayi ordering din twins ring wa keda yar'uwarki "

" kai dadynmu Allah yasakada Alheri yakuma Kara budi"
Shafa silky hair nata yayi wanda har kugunta yakai atsayi,  murmushi yasakar mata cos sosai yaji sweet din adduan ta.....

"Dadynmu Ina naka ring din  inason na saka maka myself" ciro ring din yayi acikin Wani beautiful box , mika mata hannu shi yayi ,itakuwa cikeda jin dadi tazuramai , sumbatar hannun tayi sannan tace

" I really love you dady " tafada hade da mikewa domin tafiya bacci cos dareneh

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login