Showing 3001 words to 6000 words out of 26903 words

Chapter 2 - AUREN KATIN KASA

Start ads

02 Sep 2025

90

Middle Ads

kazanta, ko ina kamshi yake sbd basuda kazanta kwata kwata, saidata dauro alwala tukunna ta fito anan ta tarar da salima ta kwanta ta fada tunani, kallonta amra tayi har zatayi mata maganar salla saita tuna cewa batayin sallah, wucewa tayi wajen wardrop din nasu ta jikin bango, hijab ta dauko tare da sallaya, ta fuskanci qibla sannan ta tada sallah, atsanake take ibadarta harta sallame sannan ta fara kwararo adduói neman gafara ma iyayenta awajen Allah sannan ta nema masu ita da ‘kannenta kariya daga duk wani sharri na mutun dana aljan da kuma karfe, ta dade tana rokon Allah daga bisani salim ya shugo cikin daki, zama yayi gefen salima yana jiran amra ta shafa yayi mata Magana sbd yunwa yakeji dama shi baya jure yunwa kwata kwata. ..Shafawa tayi sannan ta miqe ta ninke sallayan da hijab din ta maida cikin wardrp… kallonta Salim yayi ya bude baki zaiyi Magana karaf amra ta amshe da ‘’nasan me zaka ce, muje kitchen na baka daman nasan baka jure yunwa, wucewa tayi ya biyo bayanta itadai salima tana zaune kwata kwata bata cikin annushuwa. Kitchen din suka wuce, bude tukunyan

tayi sannan ta zuba mashi sauran abincin data rage masu dama sukam basa cikin jerin yan cin abinci a dining , bayan ta zuba mashi sannan ta zuba masu itada salima sannan suka fito bayan ta dauko masu ruwan da suke durawa a bottle daga dispenser domin kuwa shima ruwan bottle water baya cikin ruwan da aka yarda su dinka dauka suna sha, dakin su direct suka wuce sannan suka zauna suka fara cin abinci, santin abinci salim ya fara yi bayan ya cinye lomar karshe sannan ya kalli amra yace ‘’ adda wallahil azeem kin iya girki nidai duk sanda mama rabi tazo ta amshi girki da aiki wallahi bana jin dadin girkinta har sai girkin ya dawo hannunki, wallahi cikina ya koshi amma bakina bai koshi ba beef sauce din tayi dadi sosai’’…bayan ya gama ya fara tandar hannun shi kallonshi amra da salima sukayi sannan suka kwashe da dariya, amra ce ta kalleshi sannan tace ‘’kai salim wallahi ka iya abin dariya har dasu sude hannu’’ dariya itama salima tayi sannan tace “wallah adda da gaske yake fah, wallahi babu ranar da zakiyi girki kunne na bai motsa ba anya bazaki shiga gasar kirki ba kuwa’’ dariya amra tayi sannan tace kudai kun iya zuzuta abu, dariya dukkansu sukayi sannan suka cigaba da hirarsu.

Free page….



Chapter 3-4



Bayan tafiyar su jabir da jalal kuwa sama suka wuce wajen part din su, suna shiga sitting room maman su suka tarar azaune hajiya kareema tana waya..,itace uwar gida yayanta bakwai maza biyar mata biyu (Abdulwahab 27yr Ibrahim 25yrs Muhammad 22yrs Khadija 20yr Amina 18yrs ishaq 15yrs sai jabir 10yrs jalal 7yrs) Abdulwahab shine babba acikin yayan babansu wato Alhaji Mustapha badaru gambo, abdulwahab yayi karatunshi ah England inda ya karatan mass com yanxu haka baya nigeria yana aiki da babban gidan talabijin na channels tv company dake England,abdulwahab shine wanda ya gado halin babansu, bashida hakuri ko kadan ga fada sannan yanada son nashi baya qaunar bare, Ibrahim kuwa yana da sauqin kai ba laifi amma kuma shi nashi halin baka taba sanin ina ya fuskanta, shima ya kammala karatunshi ah London inda ya karanta international relations ayanxu haka baya nigeria amma yana gab da dawowa, daga shi sai Muhammad wanda ya kammala secondary school dinshi amma shi yace baya buqatar komawa makaranta sbd shi kasuwanci yake son yi sai Khadija wadda suke kusan class mate da amra, ita kuma tana ss3 yanxu haka suna second term sun kusa fara exams din second term, tana karanta art, Khadija irin yarannan ne masu ji dakai da dagawa bata ragawa kowa sannan itama halin uwarsu tayo ta iya kirsa da kisisna da baqar mugunta itama bata qaunar bare,sai amina wadda take ah ss 2 itama tana karanta art itama dai ba a barta abaya ba saidai ita miskila ce sai ishaq wanda yake sa’a da salima, ishaq mutunne mai son mutane babu ruwanshi bashida rowa sannan bashida zafi ko kadan, sai kananun jabir wanda yake sa’anni da salim yana jss 2 sai jalal wanda yake primary 2.



Hajiya kareema ita kadaice awajen iyayenta hajiya tabawa da alhaji sammani, mahaifinta mai kudine sosai lokacin zamaninsu, ita kadai Allah ya mallaka mashi shiyasa ya dora mata son duniya ita da yayanta. Shekarun hajiya kareema 40 chip aduniya hajiya kareema irin matannan ne da karatu yabi jikinsu, tana da business dinta ahannu inda take sayarda manya manyan sutura ta mata, atampopi laces wanda take importing daga kasashe daban daban, dalilin arzikin babanta dana mijinta shine ya bunqasa mata market dinta.



Hajiya kareem macece mai zafin kishi babu wanda ta sani sai nata, bata qaunar dan riko ko kadan sannan kwata kwata tanayima talaka kallon kaskantacce.sunyi auren soyayya itada alhaji Mustapha tun auren saurayi da budurwa, shekarun aurensu da alhaji Mustapha talatin cirr daga baya kuma ya auro mata kishiya, ba karamin hauka hajiya kareema tayi ba lokacin daya sanar da ita ya kara aure wanda auren nashi kwata kwata bai wuce wata daya ba da haduwar shi da amaryar tasa hajiya labiba,

Alhaji Mustapha ya hadu da labiba lokacin da kasuwanci ya kaishi niger inda yake saro wasu treasure gems masu shegen tsada wanda da kyar ake samun su ah Nigeria,inda yaje sarowa, anan ne ya hadu da mahifin labiba wanda shine babba ah manufactory gem din, ciniki ya barke tsakanin alhaji Mustapha da alhaji rilwanu mahaifin labiba inda mutunci har ya kullu tsakaninsu shida alhaji Mustapha anan ne ya gayyace shi gidansa domin yaci abinci kafin yabar kasar, bayan zuwansa kuwa iyalan alhaji rilwanu sukaje gaishesa masha allah dukkansu kuwa bade kyau ba yayanshi hudu mata haka suka jeru suka tsugunna har kasa suka gaishe sa, daga bisani kuma ya dora idonshi akan labiba alokacin ne yaji kawaii ita yake so, washe gari kuwa dakyar alhaji mustpha ya wayi gari babu jira ya nemi ganin alhaji rilwanu, anan ya mashi bayanin cewa shifa ya gani kuma yanaso,daga bisani alhaji rilwanu ya mashi alkawarin idan har da gaske yake zai tambayi itama yarinyar idan taji ta gani tanaso zai daura masu aure sbd ya yaba da halin alhaji Mustapha dukda bai tsaya yayi wani dogon bincike akansa ba. Bayan rabuwarsu alhaji rilwanu ya nemi ganin yarsa labiba domin ya tambayeta idan har itama tana ciki ay kuwa ta nuna tana so, murna kamar ta kashe alhaji Mustapha lokacin da yaji labiba tayi naám dashi kuma zata aure shi anan ya buqaci alhaji rilwanu ya daura masu aure shida labibarsa sannan idan ya koma gida bayan sati biyu idan ya kammala inda zai ajeta sai ya dawo ya dauka amaryarsa. Aykuwa bayan kiran sallar dhuhur aka daura auren labiba da alhaji Mustapha.

Free page….



Chapter 5-6

Alhaji Mustapha kuwa zumudi baisashi ya fada ma hajiya kareema ba saida akayi wata bayan y a gama yan shirye shiryen shi inda ya gyara gefen part din amaryarsa, dama asama part uku ne, na tsakiya nasa ne sai kuma na gefen left side na hajiya kareema saikuma side din inda su abdulwahab ke sauka in suka dawo Nigeria part dinshi ya gyara tsaf sbd amaryar sa don Har kujeru saida ya chanza, Bayan wata cur Alhaji Mustapha ya shirya tsaf domin dauko amaryar sa labiba daga Niger, aranar da zai tafi ya shiga part din kareema anan ne ya sameta tana waya da abokanan kasuwancinta saida ya samu waje ya zauna tukunna ya fara Magana ‘’ki aje wayan nan kareema zamuyi Magana mai muhimmaci,’’ aje wayar tayi sannan tace ‘’ina jinka oga’’ murmusawa yayi sannan yace daman Magana ce zanyi akan aure na, jin haka yasa kareema miqewa tsaye, idonta wiki wiki ta fara Magana, ‘’wani irin maganar aure alhaji haba wasa kake ko? don Allah yanxu da girman ka tsofe tsofe dakai maganar aure kake yi, me kake nufi Kenan” ..kallonta yayi sannan yace ‘’ ay ba maganar aure nake maki ba ay nayi auren ne nake so na fada maki ‘’gabanta ne ya bada daram, ay kuwa tana dagowa me zatayi banda ihu, masifa ihu zagi babu wanda bata gunduma mawa alhaji Mustapha ba daga karshe da yaga abin nata ya zama hauka kuma tanaso ta bata mashi lokaci anan take ya baza malun malun dinshi ya kara gaba, anan yabar kareema da ihu da masifa karshe dai ta koma daki tana bambami.



Alhaji Mustapha kuwa saida ya isa har gidan alhaji rilwanu suka gaisa yaga amaryarshi tukunna ya wuce masaukinsa, kwanan sa biyu ah niger ya shirya dawowa shida amaryar sa, su labiba kuwa ansha kuka sosai sbd rabuwa da yan uwanta, anan mahaifinta rilwanu ya danqa mata sadakinta sisin gwal guda ashirin da alhaji Mustapha ya biya, daganan suka wuce airport tana maqale da mijinta, bayan isarsu kuwa gida direct ya wuce da amaryarsa koda suka isa ranar ya taradda kareema batanan tayi tapiya zuwa turkey domin saro wasu kayayyaki bata san wainar da ake toyawa ba saida suka kwashi sati uku suna soyewa tukunna kareema ta dawo kodata dawo ta tarar da labiba sai taga ay idan har tace zatayi kishi da ita raini ne ma, amma dai da mugunta da kirsa dai saita kuntata mata. Aykuwa anan haka labiba ta samu cikin danta na farko Abdul -kareem inda tana haihuwarsa allah ya amshi abinsa, labiba tayi kuka sosai sbd ta saka rai sosai da cikin nan daga baya kuma allah ya kara bata wani cikin inda ta haifi yarta ta farko kyakyawa Halima suna kiranta da halim, halim nada shekara biyar allah ya kara bata haihuwar da namiji inda aka sa mashi Khalil shima yanada shekara uku ta haifi wani dan nata inda ta saka mashi suna khamis auta.

Hajiya labiba irin matan nan ne masu kyau fara ce ga gashi ga kyau saidai itama fa ba a barta abaya ba wajen makirci, batada matsala da dan kowa amma idan ka shiga gonarta tofa zaka sha wahala sbd ita harda yan tsubbace tsubbace takeyi, tunda tazo gidan ashirye tazo saidai kuma ganin hajiya kareema bata shiga sabgarta ba saita aje makaman yaqi amma duk sanda kareema ta takaleta tofa bata barinta sannan kuma basa shiri kwata kwata da yayan salima musammam abdul wahab da Khadija, bata qaunarsu ko kadan suma kuwa basa sonta basa son yayanta,ayanxu yayanta uku halim 17yrs wadda take ss2, Khalil 10yrs jss2, khamis 7yrs nursery 3). Halim irin yarannan ne sangartattu, tanada son gayu sannan abu qalilan yake bata mata rai amma inka iya zama da ita zakaji dadi, shikuwa Khalil irin yarannan suma da Magana bata damesu ba sai khamis dan cutie sarkin dariya da wasa.

Wannan sune ahalin gidan alhaji Mustapha badaru gambo, to bari muji su wanene amra da kannenta salim da salima, ya akayi sukazo gidan,waye mahaifinsu, sannan su asalin yan ina ne sannan menene taqamaiman matsayinsu acikin gidan.

Free page….





Chapter 7-8



Alhaji Badaru gambo, alhaji badaru haifanfan dan garin katsina ne, anan ya taso agaban iyayenshi da kaninshi alhaji sammani, alhaji badaru mutun ne mai mutunci mai hakuri da sanin yakamata kuma mai son yan uwanshi, su kadai ne awajen mahaifinsu, anan katsina ya hadu da larai wadda ta kasan mace mai hakuri da juriya, shekarar su goma da alhaji badaru allah bai basu haihuwa ba, alhaji badaru bai damu ba sbd haihuwa daga Allah ce, suna zaman lafiya shida matarshi bashida wata damuwa inda alhaji sammani kuwa kanin badaru ya koma kano domin yin kasuwanci anan katsina yabar dan uwanshi badaru, badaru shike kula da mahaifinshi sbd tun bayan haihuwar sammani mahaifiyarsa ta rasu allah ya karbi abarshi, akwana atashi babu wuya shekara wajen goma sha biyar larai babu ciki babu goyo at this point abin ya dan fara damun badaru dukda baya nuna mata cewa ya damu, ana haka har sammani yayi aure ya aure amaryarsa talatuwa inda ashekarar da sukayi aure ta haifi danta santalele inda yaci sunansa Mustapha, Mustapha nada shekara uku allah yayi mashi rasuwa,sammani yaji mutuwar danshi sosai harda yayan shi Mustapha sbd yaso yaron nan kamar dan cikinshi dukda sbd Mustapha sammani ya dawo katsina tare da matarshi talatu ana haka kuwa kanwar talatu wadda take mabiyar ta tazo katsina domin zama tare da yar uwarta anan ne asalin true color din talatu ya fito ganin kasuwancin badaru har yaso yafi na minjinta sammani, gashi bashida da balle jika, ganin haka saita fara kwadaituwa ta gidan badaru asannu cikin ruwan sanyi ta fara zuga sammani akan ya tilastawa dan uwanshi ya kara aure wataqila rashin haihuwarshi daga matarshi ne ba daga shi ba, aikuwa sammani ya samu dan uwanshi da maganar, shidai badaru har yanxu baida wani raayin aure sbd haka ya nuna bai amince ba, ganin badaru bashida niyar kara aure yasa talatu shiga malamai don ganin qanwarta ta samu shiga cikin gidan badaru gashi har lokacin arzikin da badaru yake yi har yaci uwar na sammani nesa ba kusa ba, anan ne Allah yayi ma mahaifinsu rasuwa, bayan rasuwar mahaifinsu badaru ya shiga damuwa sosai ba kadan ba, baya cikin walwala ko kadan daga nan ne kuma ya fara bullo da sabbin halaye na wulakanci, haka dai larai ta daure ta hadiya suna zaman dukda babu dadi, ana haka badaru ya bullo da zancen kara aure, anan ya shaidawa sammani cewa shifa yaji ya gani yana son qanwar matarshi binta, sammani kuwa yaji dadi sosai da kanshi ya nemawa dan uwansa auren kanwar matarshi kuma aka bashi aurenta. Bayan wata biyu aka daura auren badaru da binta kanwar talatuwa, ansha budiri kuwa, duk wannan abun akan idon larai amma bata taba tankawa ba shima kuwa baice mata komai ba, acikin dan zamansu larai ta fuskanci cewa makirci talatu da kanwarta suke shirya wa wadda kanwar talatu har taci uwar talatu ah iya mugunta da wulaqanci ana haka saiga ciki ya bullowa binta, murna farinciki babu wanda badaru baiyiba har Allah ya sauke binta ta haifi santalelen danta inda badaru yayi alkawarin maida sunan marigayi dan gidan sammani Mustapha, anyi suna an kashe kudi sosai ah katsina.,

Yaro ya taso cikin soyayyar ubansa da kawun sa sannan kuma ya taso da mugunta irin ta uwarsa don akan idonsa uwar ke shiryawa larai mugunta iri iri, haka ya taso dai tun baisan me ake nufi da kyamatar mutun ba har ya fara kyamatar larai wato kishiyar mahaifiyarsa, bayan shekarun Mustapha goma aduniya kwanci tashi yau da gobe sai Allah, Allah ya azurta larai da ciki, tayi murna ta godema allah ba kadan ba, daga nan ne ta fara neman tsari daga mugunji da mugun gani tana addua akan allah ya tsareta da abinda ke cikinta da mijinta, har larai takai wata takwas wata rana ta tashi domin kuwa ranar girkinta ne bayan ta gama shirya abinci ta zuba nasu itada badaru ta koma ta aje nata adaki sannan ta fita domin karban ruwan adduar naquda bayan fitarta kuwa saiga Mustapha ya shugo dakin innarsa rai abace dama itake zugashi akan cewa idan har yana kallo larai ta haihu to shikenan gatan da ake mashi yakare, aikuwa ranar ya dawo gida saboda babansa badaru wanda yayi mashi fada akan abokanan banza da yake tara wa,dakin innarsa ya fada nan ya taddata tana shirin fita hannunta rike da wani qulli da alamu batasan ya shugo cikin dakin ba, ganin ya shugo rai abace nan ta shiga tambayar sa me akayi mashi nan take ya zayyane mata komai dagana ta dora mashi da cewa ‘’ay matsiyaciyar matarshin chan ce ta zuga sa sbd haka yau zamu dauka fansa, kaga wannan kullin kaje uwar dakanta nasan yanxu malam ya wuce sallar magariba kaje ka zuba cikin kwanan abincinta dazarar taci nan take zata mutu kowa ya huta, ay kuwa yana karba ya wuce dakin yana zuwa ya tarar da kwanon larai anan ya zazzage duka maganin sannan ya juya miyar kukan datayi, ya fice daga dakin yana dariya,fitarsa keda wuya saiga malam ya dawo daga masallaci yana shiga daki baiga larai ba daman ta fada mashi zata je gidan malam liman domin karbo ruwan adduar naquda.

Free page….



Chapter 9-10



badaru na shiga dakin kuwa ya tarar da flask din data aje abinci dama da yunwarsa ya dawo, zama yayi ya zubama kanshi sannan yayi bismillah yaci ya koshi yayi dam daga bisani yayi sallar isha í sannan ya kishingida yayi kwanciyarsa, koda larai ta dawo ganin mijin nata yana barci yasa bata tashe sa ba, sallah itama tayi sannan tayi kwanciyarta already daman dataje gidan malam liman taci alala da matar liman tayi wadda ta bata sha’awa dama matar lima inno kawarta ce kut da kut, gab da asuba ta farka ganin badaru dai baccin shi yake hankali kwance yasa itama ta koma barcin ta, binta kuwa ganin malam bai fito ba kuma bataji sakamakon abinda take jira ba kawai saita wuce bangaren larai, tana zuwa kuwa ta fara doka masu sallama, larai ce kawai ke iya amsawa sannan ta fito ta sameta, ganin lafiya kalau larai ta fito yasa hankalin binta tashi sosai, gyara nutsuwar ta tayi sannan tace ‘’kicema badaru inason ganinshi’’ wucewa ciki larai tayi sannan ta fara tashin badaru, ganin ko matsi bayayi yasa hankalinta ya tashi, daga karshe dai ta dunga kwala mashi kira ganin baya nunfashi yasa larai kwala ihu nan take ta fadi assume, jin ihun larai yasa binta shugowa da hanzari koda ta shugo taga badaru babu rai saita fara ihu anan take kuwa gidan ya cika da mutane anan aka gane cewa badaru ya mutu cikin barcinshi itakuwa larai doguwar suma tayi bayan an taimaka mata ta farfado nan hankalinta ya tashi ganin badaru ya tafi ya barta tapiya ta har abada, tayi kuka tayi kuka ta godema Allah daga karshe ganin za ah kai badaru makwanci sa yasa larai nagudar dole anan matar liman inno ta taimaka ta kaita wani dakin kaya extra agida, anan aka kira wata nurse makwapciyarsu tazo domin taimakon gaggawa, matar bata ida zuwaba kuwa larai ta haifi santalelen danta kyakyawan gaske gashi black beauty.

Bayan kwana bakwai yaro yaci sunan mahaifinshi marigayi wanda ya rasu aranar da aka haifeshi wato Badaru…binta kuwa ashe tana dauke da sabon ciki

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login