Showing 18001 words to 21000 words out of 26903 words

Chapter 7 - AUREN KATIN KASA

Start ads

02 Sep 2025

87

Middle Ads

ta koma gida.



Wunin ranar da tunani batun scholarship dinta ta wuni daga karshe ta yanke shawarar tunkarar daddy tukunna idan ya amince fine idan ya hana babu yanda zatayi don shi ne wanda kawai zaiyi sponsoring upkeep dinta.



Dare nayi wajen karfe tara bayan ta daidaici lokacin hutawarsa sannan ta wuce sama domin ganin daddy, ahankali tayi sallama yana zaune sitting room dinshi shi kadai yana cin dambun nama yana kallon news, ahankali ta kutsa kai ciki, bayan ta gaisheshi sannan tadan nunfasa ta fara Magana ‘’ daddy daman munyi end of the year competition a school dinmu kuma nice na zo gwarzuwar shekara sannan na samu scholarship da kyaututuka’’… kallonta yayi sannan yace ‘’okay’’… shuru ta danyi sannan tace ‘’daddy daman naga tunda wannan opportunity ne mai kyau yasa nace bari naji ta bakinka ‘’… kallonta yayi sannan yace ‘’are you planning on accepting the schorlaship?”girzigiza mashi kai tayi sannan yace ‘’okay to naji harda accommodation ko? To shi kuma expenses dinki kuma fah da upkeep waye zai baki ko kudin da suka baki zai Isheki shekarun da zakiyi? Shuru tayi sannan tace ‘’daddy daman ina neman taimakon wannan awajen ka’’… kecewa yayi da dariya sannan yace zan iya taimakon ki yar badaru amma bashi zan baki,saboda dawainiya da nayi daku kawo yanxu nayi na Allah yanxu kuma lokacin biyan bashi yazo’’ shuru tayi hawaye na bulbulowa afuskarta wai wannan wan mahaifinta ne mafi soyuwar babanta’’ shuru tayi daga nan kuma wata jarumta tazo mata lokaci guda ta kalleshi har cikin idonshi tace ‘’na amince duk abinda kayi mana zan biyaka koda kuwa zai zama karshe nunfashina, saidai alfarma daya inason kannena su kasance kamar kowa agidan nan”. Tana kaiwa nan ta fuce, kwata dady yayi aranshi yana Kara jin tsanar yaran.



Amra kuwa Daki ta dawo inda ta samu salima nacin goruba anatse amra tayi mata bayanin amincewar ta wanda hakan ba karamin dadi yayima salima ba saidai bata gaya mata yanda sukai da daddy ba.

Free page….



Chapter 37-38



The next day,

Tana tashi ta kira mrs abida a yar wayarta ta shaida mata komai, mrs abida taji dadi sosai da amra ta yarda, nan mrs abida ta shaida mata cewa zasu fara processing passport dinta inda ta umarceta data zo school on Monday don ta kaita ayi mata passport, godiya tayi mata sannan sukayi sallama.



Komai dai yana tafiya daidai don har anyi ma amra passport yanxu visa ake jira saidai hankalinta atashe yake jin anytime visa ya fito za’a saya mata ticket daman already an shigo new year.



Yau visa amra ya fito sannan ayau ta fara processing komai na makarantar da zataje wato Middlesex university dubai inda zata karanta nursing, an shirya mata komai harda accommodation tana isa chan school kawai zataje tayi registrating sannan sai lectures.



Allah sarki amra za’a shiga sabuwar rayuwa……..😭



Something is waiting for amra, this is just the beginning, Amra is approaching her destiny…………………….✍️







Yau saura kwana biyu tafiyar amraa,tana kwance agadon su babu abinda take sai tunanin tafiya, yanxu shikenan haka zata tafi tabar kannenta, wazai tsaya masu, waye zai kula mata da su, kuka ne ya kufce mata, jin sallamar ishaq yasa ta saurin goge hawayen daya zubo mata,

kallonta yayi sannan ya shugo fuskarshi dauke da murmushi yace ‘’ sis nazo nayi congratulating dinki daxu nakejin salima da mama rabi suna hirar ah kitchen, yanxu sis ni baki daukeni dan uwanki bane banida darajar da za ah fada min wannan kyakkyawan labarin na tafiyar ki school, gaskia banji dadi ba sis’’, mumushin yaqe amra tayi sannan tace

‘’I’m so sorry bro, wallahi duk na shaáfa ne duk tafiyar ya fita kaina, ishaq bansan ya zanyi ba inajin tsoron barinsu salima su kadai, ishaq dan Allah ina neman alfarma awajen ka don Allah idan bana nan ka kula min da kanne na nasan kai kadai ka damu da walwalar mu’’



takai karshe hawaye na zubowa akan fuskarta, lallashinta ishaq yayi sannan yayi mata alqawarin zaiyi kokari wajen kula da kannenta, sallama yayi mata sannan ya fuce.



Shugowa dakin salima tayi da sallama sannan tace adda ki tashi mu shirya mu tafi domin ki samu ki bude account din sannan mu wuce kasuwan. Kasuwa sukaje inda anan amra ta sayama kanta kayan barci sabbi dasu bra da panties daidai kudin su masu arha sannan tayi ma su salima yan kananun sayayya wanda zaiyi masu amfani koda ace batanan, duk wannan hidimar da kudinda ta samu sukayi, wucewa sukayi wajen masu abayas, anan ta saya kala biyar masu kyau daidai kudinta, sannan suka wuce bank domin bude account, daganan suka tsaya shagon wayoyi na zamani anan ta bada karamar nokia ta cika da kudi suka musanya da android mai kyau domin tanason ta barma su salima domin jin lafiyar,wunin ranar awaje sukayi shi.



Bayan sun koma gida sai alokacin ta tuna da sabuwar wayarta wadda tundo tazo da ita ta aje while kudin da ta samu wanda aka bata cheque dinshi ta bama mrs abida ta aje mata

ko zata buqata nan gaba ko kuma idan kannenta zasu buqata dukda an diba kusan rabi wajen yi mata visa da flight ticket.



Yau thurday gobe Friday jirginsu zai daga wajen karfe uku na rana, kwata kwata bata cikin nutsuwarta lafewa tayi akan gado zazzabi yana neman lullubeta, salima kuma tana zaune tana shirya mata kayanta ah cikin akwati, saida ta hada mata komai duka yan kayayyakin ta sai yar jakar da ta saya mai chain guda biyu masu kyau da abayoyin da ta sayo, bata wani kwasa wasu kaya masu yawa ba.

Suna nan zaune taji shugowar daddy saida ta tabbatar ya huta sannan ta wuce sama part dinshi, kodata shiga yana nan zaune kamar kullum yana waya, karasawa tayi saida ta bari ya gama sannan suka gaisa nan ya miqa mata wasu papers yace tayi signing, karba tayi ya fara signing bayan ta gama ta miqa masa,

Karban papers din yayi yana murmushi ya bata wani envelop yace ‘’ first upkeep dinki ne wannan na rubutashi acikin contract da kikayi signing yanxu sannan duk sanda kika buqaci kudi zan baki idan har kika gama makaranta baki biyani ba acikin gadon ku Zan dauka wato gidan ubanku wanda yake Abuja a maitama’’



kallonshi amra tayi afurgice sannan tace ‘’amma daddy ba haka mukayi dakai ba, baka cemin zaka musanya yarjejeniya da gidan gadon mu ba shi kadai muka mallaka ni da qannena ,’’ baiko kalleta ba yace zaki iya tafiya



kuka ne ya kufce mata kawai ta fice daga dakin.

Koda ta koma daki saita fara dana sanin amincewa da batun biyan bashi da dady yace zatayi ashe tun farko manufarshi Kenan abinda yakeso, shiyasa yayi sauri ya amince da tayi mashi maganar school din, kuka kawai take yi koda salima ta shugo ta ganta saitayi tunanin kukan tafiyar da zatayi ne gobe, zama tayi gefenta tausayi yayarta ya gama lullubeta, rugume juna sukayi sai kuka, jin alamun shugowar salim yasa suka tsagaita don kar ya gane me suke ciki gudun karya shiga damuwa sbd ciwon zuciyar shi, Haka suka kwanta rungume da juna.

Cikin dare kuwa amra kamar an tsikareta ta fara jn wannan ciwon bayan nata dai alamun zata fara period dinta, tashi tayi ta nema Panadol kawai tasha, cikin ikon Allah barci ya dauketa.



Free page….



Chapter 39-40



Koda ta tashi da safe da ciwon ciki ta tashi kadan kadan kuma yau ta kasance ranar tafiya, anatse take yin komai don duk jikinta yayi sanyi, karfe bakwai daidai ta wuce toilet, tayi wanka sannan tazo ta zauna gefen su salima wanda bancin su kawai suke, zuba masu ido tayi sannan tace ‘’kannena banida kamar ku duk duniyar nan, zanyi kokari nayima kaina alkawari zan kula daku kuma insha Allahu zanyi ilimi na fitar daku daga qangin rayuwar nan insha Allah, salima wadda tashinta Kenan ta bude idununta ta kalli yayar ta wadda qwalla shar akan fuskarta tace ‘’adda dan Allah ya kamata ace kin daina koke koken nan saikace mutuwa zamuyi idan kika tafi, nayi maki alkwari wallahil azeem bazan taba yin abinda zaisa ki damu ba idan kika tafi, zan kula da salim zan zama uwa agaresa zan kula dashi kinji adda kidaina damuwa dan Allah”… dakyar salima ta lallashe ta sannan itama ta wuce don tayi wanka.



Bayan salima ta fito,kimtsawa itama tayi sannan suka wuce kitchen, a tare sukayi breakfast da mama rabi inda tayi ma amra fada akan ta kula da kanta da mutuncin ta sannan tayi Ma amra alkwari kula dasu salima.



Daki suka koma nan salima ta tashi salim ya shiga wanka ita kuma amra ta dauko sabuwar wayar ta sannan tayi exchanging number da sabon sim din data sayama su salima, ganin karfe sha daya saura yasa ta saka sabuwar abayar ta sannan ta wuce sama domin yima masu gidan sallama, koda taje part din haj kareema batama tsaya ta saurare ta ba ta koreta, fitowa tayi ta wuce part din Haj labiba, koda taje bangaren haj labiba kuwa, ba laifi tadan kulata hardasu Allah ya kiyaye,…direct kasa ta sakko abinta sannan ta koma wajen salima koda ta shiga dakin azaune ta ganta, hannunta dafe da cikinta, karasowa tayi tana tambayarta ko bata da lafiya, ganin hankalin yar uwarta zai tashi yasa salima saurin yin yaqen wahala tace ‘’laa adda dan period pain ne yama daina’’….magani amra ta bata tasha sannan itama ta shirya cikin atampa yellow doguwar riga. Wardrop dinsu amra ta bude nan taga envelop din da dady ya bata, daukar envelop din tayi sannan ta bude, kudi ne aciki dollars wanda akalla zaikai 5k dollars ajiyewa tayi aciki yar chain handbag dinta sannan ta dawo daki ta zauna, suna nan zaune ishaq yazo suka dan taba hira bayan kiran sallar zhuhr ya wuce masjid su kuma suka tada kabbarar sallah, saida suka idar sannan sukayi addua ita da kannenta, salim kuma ya fara kiciniyar fitar mata da akwatinta, lokacin it’s about 2pm batason tayi latti shiyasa ta shirya futa da wuri sbd flight din Karfe uku ne. Koda suka fito bayan sunyi sallama da mama rabi harda yan hawayenta sannan ta bata farar kasar data saya mata don kartayi kewa sannan suka karasa wajen haladu driver, shiga cikin napep din sukayi saiga ishq, shima shiga yayi domin yin rakiya.

Direct Aminu kano international airport suka wuce inda anan suka hadu da mrs abida wadda zata bata passpost dinta da visa dinta da komai na school, godiya tayima mrs abida sosai saboda tayi mata qoqari sosai sannan ta juya wajen kanneneta, salim wanda idonshi ya ciko da kwalla ya kalleta yace ‘’addana yanxu tafiya zakiyi ki barni ko’’ kallonsa tayi cike da kauna da kewarsa sannan tace ‘’ my salim karkayi kukakaji ko I promise to buy you a big army jet toy and I will come back soon so that I can bring you and salima kaji ko ‘’… dariya yayi jin tace zata dawo ta tafi dashi, kallon salima tayi sannan tace ‘’salima dan allah ki kula kinji, ku dinga kirana idan kuna buqatar wani abu sannan ga ishaq nan zai kula daku kinji sannan duk wani abu dake damunku ga mrs abida ga mama rabi ga ishq na tabbatar zasu kula daku’’… rungume kannenta tayi sannan ta sakesu ta wuce da sauri cikin airport din sbd hawayen dake shirin zubo mata don idan Har ta tsaya suka fara koke koken nan toh fa tafiyar nan bazata yiwu ba ganin kusan Karfe uku ta kusa yasa suma suka wuce gida kowannan su dauke da kewar ta,… ita kuwa amra kuka sosai takeyi harta iso counter din emirates, anatse ta gama komai ta wuce da luggage dinta, abinma yazo mata da sauqi sbd sun taba tafiya lokacin iyayensu na raye lokacin sunje morocco wajen uncle din mamansu. Koda ta wuce ciki wuri ta samu ta zauna domin jiran jirginsu, ko five minutes batayi ba da zama aka kira jirginsu nan kowa ya Tashi domin yin boarding saida suka gama tukunna suka wuce harabar jirgi, anatse take tafiya sanye da abayarta wadda suka sayo black, tayi mata tsam gata dama akwai diri sai tabi shape dinta tayi irin A shape dinnan tayi mata kyau sosai sannann tayi rolling kanta da mayafin abayar sai yar chain hand bag dunta akafada har suka iso cikin jirgi, seat dinta atsakiya yake nan ta samu waje ta zauna while gefenta is empty by right sannan left dinta kuma wani bayarabe ne…..Bayan Yan mintuna kadan jirginsu ya daga zuwa abuja domin transit zasu fara yi daga abuja su wuce uae.

Free page….



Chapter 40-41



ABUJA NIGERIA.

Mota ce kirar range rover evoque 2020 black color, ko ina na window din is tinted, baka ganin komai daga waje,aguje ta shararo zuwa cikin airport din Nnamdi Azikiwe International airport abuja, daga gani sauri matukin motar yakeyi, koda akayi parking motor din, an dauka almost 5 minutes kafin abude bayan motar, ahankali ya fito da kafanshi ta dama sanye da sandals black color wanda suka haska farar kafarshi da yatsun dogaye, ahankali ya sauko da dayar kafar tashi sannan ya fito gaba dayanshi, Masha Allah😻wayace maqale akunnen shi, juyowa yayi yana fuskantar driver daya kawoshi, Allahu akbar …Allah yayi halitta, wato wani irin kyakyawan dogon saurayi ne😂wanda akalla bazai wuce shekaru talatin ba aduniya, dogone sosai kuma qaqqarfa, fuskarshi sai wani annuri take da glowing , ya aje sajen gashin baki wanda ya kewaye a fuskarshi baki wuluk ga bakinshi dan cute wanda yayi wani oval shape, hancinshi amike gwanin burgewa,ya rufe idanunshi da alamu ranar daya tsaya ta dan dame sa, ahankali ya bude idanunshi wanda suke wani irin sheqi da sparkling lokaci daya, yanada wani irin kwarjinin da you can’t resist him,lashes din idonshi zarr zarr dasu kamar ya saka eyelashes wanda yafi daukan idon mutane, ahankli ya fara magana cikin kakkausar muryarshi, ‘’get my baggage to the counter, I will be there in a minute..’’ ahanzarce drivern nashi ya fito ya bude booth ya dauka Hadadden Louis Vuitton baggage dinshi

ya wuce cikin airport din, shi kuma handsome din ya jingina ajikin motor waya maqale akunnenshi yana sauraro…a hankali ya soma magana…wato muryarshi har wani echoing yake yi, yana da irin harsh voice dinnan ga kuma dadi sauraro, yanda yake tafiyar da lebenshi kamar robot ahankali yace ‘’Amma I’m done with aman’s issue bazan kara Magana ba yaje yayi duk iskancin dayaga dama kawai dai bazan iya zama Ina kallon abubuwan da akeyi agidan nan ba wanda kwata kwata bai dace ba,’’ yatsine fuska yayi sannan ya daure fuska tamau alamun ranshi kamar abace yake sannan ya cigaba ‘’Amma wallahi bazan kara dawowa ba, tunda haka sukeso na bar masu garin, and besides kinsan zan koma training dina so now you can have peace of mind’’ …Magana akayi daga chan’… yatsine fuska yayi alamun ya qagu ya katse call din , cire phone din yayi daga kunnen shi ya kalla screen din ganin 2mins to his flight yasashi cewa ‘’Amma zanyi missing flight bye’’ katse wayan yayi sannan ya fara tafiya cikin isa da kasaita, jikinshi sai kamshin Emilio de pérfumè yake wanda akalla kudinshi zaikai kusan dala dubu uku, riga da wando ne ajikin shi na Nike, rigar rubber ne ta dameshi dam sosai wadda ta fito da builded body dinshi, wani irin murdadden jiki ne dashi wandon jikinshi same color da rigar shima nike, ta kasa yadan dameshi wanda ya fito da damtsen kafarshi he looks soo so damn cute and attractive ,kanshi kuwa babu komai kuma baibar suma ba sosai sai dan few gashii kadan, lunshe donshi yakeyi har ya karaso airport din kamar bazai karasa ba, tunda ya shigo airport dinnan ma’aikata da mutanen da ke kai kawo suke kallonshi, hannunsa rike da briefcase brand din mont’blanc dayan hannunshi kuma laptop ne da wayansa, anatse yake tafiya kamar bazaiba, saida yazo dab da driver din sannan ya zira hannu acikin aljihunsa ya zaro duka naira note din da suke ajikinshi ya bashi, godiya ya fara masa, anatse ya daga mashi hannu alamun ya tapi sannan ya karasa counter din emirates, anatse ya fara ma budurwar dake tsaye jikin counter din Magana, ‘’ evan any update?

anatse ta fara bashi ansa ‘’ you’re welcome sir and we’re very sorry sir, I just talk to our manager, the problem is we got your booking very late, I’m sorry I don’t know what to do about it,”lips dinshi ya ciza har saida ya danyi jaa sannan yace “get..me your manager now, I mean the overall manager of emirates air now!!!’’…. furgicewa evan tayi, da sauri ta jawo landline sannan ta kira akayi mata connecting to office din babban manager emirates air ganin surutan da suke zai bata masa lokaci kuma baya son atmosphere din wajen ya sashi mikewa yace ‘’tell him to meet me at the first class lounge and the flight should be delayed now!! Sanin ko shi waye yasa ta kira direct aka tsayar da jirgin da zai daga zuwa dubai… saida ya idar da sallar asr ah masjid din lounge din sannan ya zauna yana dan latsa waya……





oh araina nace kudi yana aiki ko shi wannan din waye kuma dan uban waye da har yana da ikon tsaida jirgin da zai daga zuwa dubai…. Fatan dai ba jirgin su amra bane😂😂😂 hahaha muje zuwaaaa…..



Anatse manager keyi mashi bayani ‘’sir we know you’re very important to uae government and it’s our loss to loose such important customer, so please sir understand that it’s not our fault, we received your call 10 minutes to takng off the flight but we promise when the flight is transiting to Saudi we’ll get things sorted we’re very sorry sir’’’ … kallon manager yayi kawai kanshi har wani sara mashi yake bayason amashi delay ko abata mashi plans dinshi, anatse ya miqe ya fara tafiya ko kallon manager baiyi ba saida yazo daida harabar filin jirgin sannan wata motor benz GLA-Class black color har gabanshi ta tsaya bude marfin motor yayi ya shiga, taja har gaban jirgin emirates babba wanda ya kamata ya tashi tun 3pm amma sai gashi anyi delaying dinshi saboda wannan masha hurin mutumin.. anatse ya fito yana taka stairs din benen duk

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login