Showing 15001 words to 18000 words out of 26903 words

Chapter 6 - AUREN KATIN KASA

Start ads

02 Sep 2025

88

Middle Ads

storage room karka fito saika tambatar da ka balle hannun mara kunya kafin ka fito’’’jin haka yasa azafafe Ibrahim ya dunga janta kamar dabba har storage room, hankalin amra fa ba karamin tashi yayi ba za’a illata yar uwarta ay kuwa aguje ta bishi kafin ta karasa ma ya rufe kofar storage room din, babu abinda yake sai jibgar salima tun tana rokonshi da Allah ya kyaleta harta sume, saida ya tabbatar ta jigatu sannan ya fito ya rufo kafar yasa key din a aljihun sa, kuka dai amra tayi kuka harta godema Allah, su kuwa kowannen su wucewa part dinshi yayi hankali kwance.

Free page….



Chapter 29-30



Bangaren salima kuma sumewa tayi dalilin bugun cikinta da ya Ibrahim yayi tun daga lokacin ta fita hayyacinta. Amra kuwa annan zaune bakin kofar ta zauna zaman dirshen tana kuka tana rokon Allah akan ya tsare mata yar uwarta, gashi storage room din ana dadewa ba ayi amfani dashi ba don babu komai aciki sai karafunan motoci da tsofaffin gas cylinders da aka gama amfani dashida ake ajewa idan sun tsufa. Anan suka kwana har safiya amra bata samu damar koda rufe ido ne ba babu abinda take sai kiran salima amma shuru, tsoronta kada ace kashe mata kanwarta sukayi, karshe dai dakin mama rabi mai aiki ta wuce lokacin tana kan sallaya tana lazimi batasan wainar da ake toyawa ba, ganin amra ta fado dakinta kamar wadda ta susuce idonta yayi rudu rudu tsabar kuka yasa ta mikewa tace ‘’ke amra lapiya meya faru?’’ hankali atashe amra ta labarta mata komai sannan tace mama rabi sun kashe ta sun kashe min yar uwata na shiga uku.



Saida mama rabi ta kwantar mata da hankali sannan tace inada extra key wanda ake barmin sbd ijewar kayan da suka lalace bari na dauko muje mu bude ta, cikin sauri mama rabi ta lalubo key din suka wuce direct dakin, suna budewa kuwa hankali atashe suka ciccibi salima wadda har yanxu bata farfado ba,jikinta duk ya kumbura hawayen fuskarta harya bushe, daki suka wuce da ita anan mama rabi ta dakko ruwa ta yayyafa mata aikuwa tana bude idonta ta fara kuka muryarta adishe ta fara sammabatu “adda wannan wace irin masifa ce maysa baku bari na mutu ba, adda kashemu mutanen nan zasuyi basa son mu innalillahi’’



Rungume ta amra tayi, hawaye sharr afuskarta, dakyarta lallashi kanta sannan daga salima da taimakon mama rabi ta wuce da ita toilet saidata gaggasa ta sannan suka fito daki, kaya ta dauko ta saka mata sannan ta kwantar da ita, kitchen ta wuce ta hado mata tea me dan kauri ta bata saidata tabbatar ya shanye sannan ta dauko pain killer da suke ajewa a locker sannan ta bata. kallon salim tayi wanda ya gama takurewa da alamun da yunwa ya kwanta yasa taji tausayi yan uwanta duk ya rufeta, Har lokacin hawaye bai daina saukowa daga idanun ta ba,saidata taimakawa salima tayi sallah sannan ta kwantar da ita, ta jawo mata bargo. Tashin salim tayi wanda duk ya takure agefe guda tayi domin suyi sallah koda suka idar shima tea din ta hado ta bashi yasha, kwanciya sukayi basu tashi ba sai wajen nine saboda rashin baccin da basu samu sunyi ba, ganin lokacin school ya kure yasa suka fasa kawai daman taso salim shi yaje school din ita kuma ta zauna ta kula da salima.

Wunin ranar adaki sukayi tsabar mugunta babu wanda yabi ta kansu, tunawa da kayan wankinsu yasa amra ta tashi inda tabar salima na barci salim kuma yana home work sannan ta wuce backyard. Tana karasowa ganin kayansu akasa yasa ta fara kwashewa tana cikin kwashewa kuwa khady tazo har inda take sannan ta fara kecewa da dariya, kallonta kawai amra tayi irin kallon ina tausayawa karshen ku.



Kallonta khady tayi sannan tace ‘’ai na fada maku niba tsarar yinku bace, kalli dai dan buga kaina da ni da kaina nayi ya janyo kun kusa salwantar da kanku, hahaha ina tausaya maku amra haka zakuyi ta wahala agidannan har karshenku, sannan zan kara warning dinki akan kiyima mara kunyar kanwarki magana don wallahi idan har tayi wasa zaman gidan nan zai gagareta, yanda na tsaneku haka na tsani mutuwa ta, bakuyi min komi ba amma bana qaunarku samm” tsaki taja sannan ta kara gaba, amra kuwa kallonta kawai tayi sannan ta cigaba da abinda take ta wuce dakinsu .



Jikin salima kuwa ya warke har sun koma school saidai kullum saitayi kukan ciwon ciki ana haka har suka fara exam din waec Sukuma su salima har sun gama exam sun fara hutu, haka kullum zata shirya ita daya ta tafi school tana gama exam kuma ta dawo gidan abinta, yanxu kam ta tsaya sosai akan kannenta, bata bari su shiga damuwa sannan ta tsaya masu sosai. A kwana a tashi babu wuya yau saura kwana biyu su gama paper, yau da gobe Tuesday da Wednesday Kenan sai on Saturday kuma zasuyi grand competition next week kuma za ayi walimar saukar yan ss3 wato su kenan, abubuwan sunyi ma amra yawa ga karatun waec ga preparation na competition, haka dai ta dukufa da karatu.

Yau Wednesday suka shiga last paper duk yan class dinsu kowa farin ciki yake za ah gama exam, bayan sun gama first paper amra ta fara jin ciwon baya kadan kadan, chan anjima kafanta ya rike jin haka ya tabbatar mata da period zatayi dama a day before ta fara alamun haka ke bayyana ajikinta, lallabawa tayi ta koma class har suka fara second paper wanda shine last one, gaba daya ta takure ahaka dai tayi managing kanta har suka gama sannan ta fito ta wuce gida, koda ta iso har zazzabi ya fara rufeta daki kawai ta wuce tayi wanka ta chanza zuwa simple riga da skirt, tana nan zaune salima ta kawo mata abinci taci sannan sukayi sallah.

Free page….



Chapter 31-32



Bayan sunyi salla suka danyi hira anan ne amra ke tambayan salima ciwon cikinta kallonta salima tayi tana kakalo murmushi sbd batason yar uwarta tana saka damuwa aranta sbd ita, hakan yasa tace ‘’adda ai ya daina wallahi dama chan stress ne na school activities yayi min yawa yanxu kuwa da akayi hutu kinga na daina kwata kwata’’ jinjina kai kawai amra tayi sannan ta hau kan gadon su ta lulluba sai barci.



Washe gari Thursday ta matsanancin ciwo amra ta tashi wanda ya janyo mata sumewa har sau biyu, dama yawanci haka period dinta ke azabtar da ita, idan azabar tayi yawa sumewa kawai takeyi, salima ne kawai ke kula da ita sai mama rabi mai aiki wadda ke lekowa dubata jefi jefi, haka tayi spending ranar akwance washe gari Friday tadan samu sauki wanda yasa ta fara prepation din competition dinsu na school, dukda tanajin ciwon marar nata amma haka ta daure ta fara practising, sai wajen sha biyu na dare ta gama komai ta rufe books dinta sannan ta kwanta gefen yan uwanta.



Washe gari karfe bakwai na safe daidai ta gama shiryawa tsaf cikin uniform dinta wanda salima ta wanke kuma ta goge mata, saida ta dan shafa powder tayi kyau fess fess sannan ta goga lip gloss kada, tadan fesa turaren ta mai sanyin kamshi sannan sukayi sallama da salima ta wuce wajen haladu wanda ke jiranta, gaishe sa tayi bayan ya amsa aranshi yana yaba kyawawan halayyarta da kannenta ba kamar sauran yaran gidan ba.



Karfe bakwai da rabi ta iso school wanda daga yan class dinsu duka sai malamai biyar da principal din school din, shiga cikin school bus dukkansu sukayi sannan suka kama hanyar makarantar NTIC, agaban parking space dake cikin compound din school din daga gefe sukayi parking inda sukaga hadaddun school buses suma suna sauke student din makarantu aciki, anatse su amra suka fara saukowa suka jeru waje daya gwanin burgewa, saida suka jira head of school dinsu hajiya abida da mijinta suka iso tukunna suka kutsa kai cikin school hall din inda ake event.

Tunda suka shiga school din suke ta faman kalle kalle, wato makarantar tayi mugun haduwa sosai, babu hayaniya kwata kwata sai sautin muryoyi da mic daga cikin hall din, anatse suka fara shiga ciki inda ake welcoming dinsu sannan aka basu sits da table wanda aka saka tag din school dinsu, zama sukayi na dan lokaci suna kora ruwa da juice da aka aje akan tables, karfe tara daidai kowa ya hallara, makarantu hudu cur, ko wacce school da garzo ko gwarzuwar su anan aka fara kiran sunayen participant, da yan NTIC aka fara, nan aka kira mutun uku sannan suka hau stage dinsu wanda shima da tag din school dinsu akai sai aka kira leader international school, bayan gabatarwa aka fara da first set of two schools din, tambayoyi akayi masu na wasa ‘qwaqwalwa sosai guda uku, daga bisani aka basu two minute each suyi solving,lokaci nayi aka karbi result din su, bayan yan mintuna judges sukayi announcing winners, tashin farko aka watsar da leaders school, bayan Yan mintuna kadan aka kira next set of schools, saida aka fara kiran aero school sannan aka kira makarantar su amra wato ar-rahman, anatse suka fara fitowa aka basu nasu questions din, after two minutes kuwa aka karbi results dinsu sannan aka mikama jugdes, result din da judges suka fada ya matuqar bama mutane mamaki sbd duk cikin schools din an dauka sune zasuzo ah karshen baya wato Yan ar-rahman school sai gashi sun samu point da yawa, sauka sukayi sannan aka kira yan NTIC da kuma Yan Ar-rahman wato school dinsu amra, anan take kuwa suka tapi stage, saida suka tsaya tukunna aka fara masu questions, first attempt kuwa dukkansu suka samu same points, ganin haka yasa aka kara basu mai zafi sosai, ganin haka yan NTIC suka fara cije hakora, time yana clicking kuwa aka karba result, kallon mamamki kowa yake ma yan Ar-rahman school sbd jin cewa sune winners, amra kuwa dadi kamar zai kashe ta because tayi contributing sosai, bayan an salami yan NTIC sannan aka dawo kan yan Ar-rahman nan aka shaida masu ana buqatar gwarzuwa daya acikin school din, wato zasuyi competing against each other, nan aka shiga bawa kowacce question dinta sannan aka umarcesu dasu rubuta ajikin paper, abinda basu sani ba shine same question aka basu kuma answer question din yana da wuya sai idan mutun ya kasance mai qwazo sosai very smart sannan zai iya ansa question din, ahankali presenter ya fara karban ta farko wadda ake kira da fadila,anan ya fadi ansa data rubuta anan take kuwa judges sukace wrong ansa, next student kuwa mai suna hamida itama aka fado nata,anan take judges sukace wrong, ahankali presenter ya karasa wajen amra wadda itace last, kallon paper dinta yayi sannan ya kalleta, ahankali ya fada ansa dinta ay kuwa nan take judges din sukace correct, tafi aka fara yan school dinsu amraa me zasuyi banda ihu don murna, kowa murna yake and kowa is so proud of her, ahankali aka umarci sauran da su koma anan kuma akace amra ta tsaya, nan shugabanni suka fara congratulating dinta murna ma ya hanata dago da kai ta kallesu, daya bayan daya aka dunga zuwa ana congratulating dinta, maza suna bata hannu mata kuma suna rungumeta, jinta ajikin wata mata wadda kamshin turaren oreal ya cika duk wajen sannan kuma wani connection me sanyi ya ratsa sakaninsu yasa amra dagowa ta kalleta, tana sanye da wani tsaddaden lace wanda akalla zaikai 300k anyi mata dinkin bubu, fuskarta fara sol tasha dan cute lipstick fuskarta dauke da murmushi, ‘’congratulation beautiful you’re re such a genius, I’m impressed, infact I am so surprised because this question is the hardest question that only a certified phd holder can answer it, weldone my dear Allah ya maki albarka,’… wanni irin nutsuwa da sanyi dadi ya sanya amra kasa daina kallonta, saitaji kamar ammin ta ce ta rugumeta, ahankali ta fara Magana ‘’Thank you so much ma,’’murmushi matar tayi mata.

Free page….





Chapter 33-34



Wucewa matar tayi sannan ta zauna a high chair domin tana daya daga cikin manyan guests, kiran presenter tasa akayi, bayan yazo da girmamawa ta mashi magana cikin sirri san nan ya wuce stage, anatse matar ta tashi ta futa daga hall din fuskarta dauke da murmushi, bayan futarta presenter ya fara bayani kamar haka ‘’muna farinciki zuwan kowa da makarantun da suka halarci wannan grand competition din sannan yanxu zamu fadi kyautar da makarantar da taci wannan competition zata samu hade da gwarzuwar data zo itace ta farko, each participant na school din ar-rahman yana da kyautar dubu dari biyu sannan school management din ar-rahman ta samu kyautar miliyan biyar domin bunqasa ilimi acikin makarantar daga karshe kuma mss amra ta samu kyautar scholarship a UAE (united arab emirates) sannan anyi sponsoring karatunta kona shekara nawa harta gama tare da accommodation, sannan tanada damar zabar duk makarantar da takeso ah uae, daga karshe kuma ta samu kyautar waya da check na miliyan biyu daga anonymous guest, mungode da zuwanku duka”.

Tunda amra taji wannan batu suman tsaye ne kawai tayi, she can’t believe it, wai ita aka yima wannan kyauta, hawaye ne suka gangaro afuskarta, daga bisani ta fuskaci alqibla tayi sujjada tare da godiya ga Allah, saida aka bama kowa kyautar sa sannan suka wuce school, anan ta samu haladu yazo yana jiran isowarta, ganin irin farin cikin da take yasashi tambayarta, murna ma kadai ta hanata fada mashi, saida suka iso gida kuma hankalinta ya tashi tunawa da yan uwanta, daga karshe dai ta kawar da baqin cikin ta karasa cikin dakinsu, koda ta isa ciki akwance ta samu salima tana barci abinta salim kuwa yana gefenta yana wasa da yar nokia amra wadda take bari agida, ganinta yasashi tasowa har gabanta yace ‘’ sannu da dawowa adda’’ kitchen ya nufa ya kawo mata ruwa lokacin ta shiga wanka saida ta fito ta nemi abinci tukunna ta tashi salima, ‘’albishirinki yar kanwata?” zumbur salima ta zauna sannan tace adda kicemin kinci kawai nama sani’’ girgiza mata kai amra tayi, ay kuwa aguje salima ta tashi tana rawar murna farinciki duk ya lullubeta, dakatawa tayi sannan tace adda fadamin kyautar da suka baku, aykuwa nan take fuskar amra ta chanza, tagumi tayi sannan tace scholarship aka bani, ganin abun farin ciki amma kuma amra ta bata rai yasata zama kusa da ita sannan tace ‘’adda scholarship fah kika samu kai alhamdulillah but why do you look so sad?’’ shuru amra tayi idonta na kawo ruwa, kollon salima tayi tace ‘’salima scholarship amma ba’a nan ba’’ jin haka yasa salima dariya sannan tace ‘’to sai me adda,inace idan kinje zaki dawo hutu ko and besides mu na tare mana tunda ba kasar zaki bari ba’’ kallonta amra tayi sannan tace ‘’ah Dubai ne fah salima’’ …zaro ido salima tayi sannan daga bisani kuma ta daka tsallen murna sannan tace wayyo allah na dadi kasheni, adda na dubai fa kikace wayyo Allah alhamdullih’’.. mamaki ya hana amra rufe baki ganin qanwarta na farin ciki, farin cikin abunda zai raba su wanda bazata taba yarda haka ta kasance ba, kallonta amra tay sannan tace ‘’salima kina tunanin zan karba schorlaship dinnan ne?, inaaa..ay bazan karba ba, bazan iya rabuwa dake da salim ba, zandai karbi wayarda aka bani sai cash din 200k din da aka bama kowa each sannan sai check din 2m din amma gaskia bazan karba schorlaship dinba,’’ tashi tayi kawai ta fuce salima kuwa dadi kamar ya kashe ta.



Washe gari Sunday amra bata cikin walwala kwata kwata salima kuwa sai tausasa ta take yi akan babu komi ta karba schorlaship din watakila shine zai zame masu alkhairi don idan ta gama karatun kamar sun tsallake baqar ukubar da suke ciki ne ayanxu, zama tayi kawai tana sauraron salima amma bata jin zata iya amincewa. Bangaren Yan gida kuwa babu wanda yasan maganar scholarship din sai daddy wanda yana kallon news da safe yaga program din da akayi na grand Competition din NTIC kuma ya ganta lokacin da ake bata grand kyaututuka daga karshe dai dariya yayi aranshi yana cewa ‘’this is the beginning’’.



Free page….



Chapter 35-36



Washe gari Monday da kyar salima tasa amra ta amince domin zuwa school ta karbo kyaututtukanta dukda tace bazata karba scholarship ba.

Futowa tayi haladu ya dauketa har school dinsu, ba laifi da akwai mutane a school din wanda rabi teachers ne, wucewa tayi wajen head office bayan tayi sallama, kallonta mrs abida tayi fuskarta dauke da murmushi sannan tace ‘’my beautiful student, I’m so proud of you my dear zoki zauna kinji’’… samun guri amra tayi sannan ta gaisheta sannan ta fara mata bayannin cewa bazata karba scholarship ba, tambayrta mrs abida tayi dalilinta, nan ta shaida mata cewa bazata iya tapiya tabar kanneneta ba, sanin irin rayuwar da su amra keyi ah gidan ruqonsu yasa mrs abida ta gane inda zancen amra ya nufa,



nunfasawa kawai tayi sannan ta fara Magana ‘’ amra inason kisan cewa karatunki yana da matukar amfani bake kadai bama harda kannenki, kece uwarsu kece ubansu yanxu idan baki nemi ilimi ba dame zaki taimaki kannenki harsu dogara dakai, shawara zan baki kamar yanda uwa zata bama yarta, idan har kinason cire kannenki daga rayuwar da kuke ciki to ya zama dole ki tattara courage dinki ki natsu ki kwantar da hankalinki, ki karba scholarship dinnan, dama ce kike samu don wallahi idan kika bari ta kufce maki bazaki kara samun kamarta ba, shawara ce na baki, sannan if you’re worried about siblings dinki, Allah yana tare dasu koda kina nan ko baki nan idan har abu zai samesu toh duk isarki duk karfinki bazaki iya hanawa ba, sannan nima zan taimaka maki wajen kula da kannenki da harkar iliminsu kinji ko’’

girgida mata kai tayi alamun gamsuwa sannan tace to shikenan ma’’..

sundan tattauna daga bisani ta bata check dinta na 2m da cash sai latest iphone xmax dinta, godiya amra tayi sosai, daga bisani mrs abida tace ‘’kije kiyi shawara sannan ki fada ma mai riqonku duk yanda kika yanke saiki dawo koki kirani awaya sai mu fara processing komai kinji ko’’ godiya amra tayi mata sannan ta wuce

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login