Showing 9001 words to 12000 words out of 26903 words

Chapter 4 - AUREN KATIN KASA

Start ads

02 Sep 2025

89

Middle Ads

iri daya suka wuce parking space koda suka iso babu wanda ya sakko acikin yaran gida ga bus din nan anyi parking driver din har ya gaji da zama ya fara barci abinshi. Salim kuwa ganin haka ya fara matse hawaye babu abinda yake tunanin face dukan lattin da kusan kullum sai anyi mashi shida sisters dinsa sbd lattin da yaran gidan suke saka su gashi su yaran gidan makarantarsu ta masu kudi ce ba a dukkan latti sukuwa su salim makarantar su batakai tasu jabir ba karatu ake sosai shiyasa ake dukan latti. Ganin haka yasa amra ta fara lallashin sa ‘’ salim idan kana cikin fargaba ka dunga fadin “nnalillahi wa inna ilaihi rajiun” acikin ranka kaji ko, kayi hkuri ka daina kukan, share hawayen shi yayi sannan suka shiga chan kuryar bayan moton suna jiran fitowar su, saida suka bata wajen 30mins kafin dukkansu suka fito kowa da irin nashi kalar rashin mutuncin shugowa cikin motor ahaka dai aka lallaba aka fara tafiya,anan ishaq ya taimaka ma amra da assignment dinta sannan aka sauke su ishaq, tsabar rashin adalci da akeyi masu kuwa sai an fara sauke yayan gwal tukunna sai asauke su, alhalin makarantarsu itace akusa kafin tasu jabir. Driver na parking ah Royal international school kowannen su ya sauka tukunna ya juyo da motar domin komawa school din su amra adaidai Ar Rahman international school, makarantar tasu babu laifi sbd makaranta ce ta masu hali ba laifi amma ko kusa bazaka taba hada ta da royal international school ba fitowa sukayi adaidai gate kuwa wani malami yasha suite da katuwar bulala ahannun yana tare Yan latti, koda salim yaga haka sai hankalin shi ya qara tashi, karasa wa sukayi bayan amra ta rike hannun shi, yara ne kusan biyar atsaye da uniform dinsu blue and white riga da wando sai hijab wasu kuwa riga da skirt ne wasu kuwa doguwar rigace kamar amra itama doguwar riga akayi mata yanayin jikinta, bayan anzo kan su anan amra ta kalli malamin sannan tace mashi ‘’sir we are very sorry for coming late Wallahi ba laifinmu bane,its not our fault but please sir don’t beat my siblings you can beat me and punish me instead,,’’ yakai karshe idonta tap da kwalla, kallonta malamin yayi sannan yace they can go in but you will have to face the purnishment after break for now zona maki bulala tunda kin fanshi yan uwanki.. salima najin haka hankalinta ya tashi tace ‘’sir I will also take the punishment along with my sister’’, kallonta yayi sannan yace okay you can come with her to my office during break”..Wucewa salim da salima sukayi anan kuwa saida teacher nan yayi ma amra bulala biyar sannan ta wuce class koda ta shiga har first teacher ta fita sai second teacher ta shigo. Anatse ta zauna a class har aka gama classes sannan aka fita break kodata je office din displine master umarni ya bata data wanken toilet din section din yan nursery, fita tayi sannan taje ta wanke, Allah sarki amra baiwar allah tana wankewa tana kwalla toilet din yayi budu budu sosai dama abinka da shaänin yara duk sun bata toilet seat da kashi sosai, tana wankewa tana kuka ahaka harta gama sannan ta wuce class lokacin har an gama break, a wunin ranar batada wata walwala gashi babu abinda tasaka acikin ta inbanda farar kasar da mama rabi ta sayo mata, har aka tashi suna nan zaune har lokacin islamiyya yayi dama school din tasu hade take da islamiyya saida biyar tayi sannan aka tashesu, fitowa sukayi suna jiran habu driver saida suka dau almost 30 minutes azaune bakin gate tukunna sai gashi, duk sun gama jigata koda suka shiga motor babu kowa acikin motorn daman su sauran tun 2 ake tashin su sannan agida malami ke zuwa yayi masu karatu. Isarsu gida Kenan sukaga manya manyan motoci parker ah coupound din amra na ganin haka ta gane cewa daddy ne ya dawo daman yaje china domin saro wasu kaya achan, hannun kanneneta taja suka wuce cikin gida babu kowa akasa da alamu duk sunci abinci sun wuce sama, daki kawai suka wuce saida sukayi wanka suka kimtsa lokacin ana kiran sallan magrib, sallah kawai sukayi tukunnan salima ta karbo masu abinci wajen mama rabi, zama sukayi sukaci suka koshi, duk wahalar dasuke sha agidan ba a hana su abinci da kuncen kayan sawa, saida sukayi sallah isha’I sannan suka fito ajere, sama suka wuce direct part din daddy salima da amra suna sanye da hijabinsu har kasa sai salim dake sanye da riga yar shara baka da yar hularsa wadda hajia labiba ta bashi kuncen kayan Khalil da suka mashi yawa. Koda sukazo bakin kofar shiga babu abinda kake ji sai kaye kayen yaran gida sonata daddy ka sayomin tsaraba, daddy ni ka sayo min kayan kwalliya,….kallon juna kawai su amra sukayi ita da salima sannan suka kwankwasa suka shiga cikin parlorn koda suka shiga yaran duk suna zaune akasa while wani babban mutun wanda akalla zaikai shekaru 54 aduniya yana hakimce akan kujera yaran kuwa Suna zaune gefensa suna mashi tadi shima yana masu… koda su amra suka karasa dai dai inda dadyn yake har kasa suka tsugunna suka fara gaishesa atare suka hada baki wajen cewa “daddy ina wuni an iso lpy?” kallonsu yayi sannan yadanyi murmushi ta gefen baki yace ‘’lpy kalau yayan badaru, ya makaranta hope kuna karatu ba’a sani asarar kudi kuma Ina fata kuna tursasa wannan kanin naku mai kwakwalwar kifi yana karatu,” sunkuyar dakai amra tayi ranta ya sosu sosai duk sanda daddy zai gansu sai ya ambaci sunan mahaifinsu abinda yafi bata mamaki shine lokacin da abbansu yake raye babu wanda yakai daddy sonsu harda yaransa ma amma yanxu komai ya sauya, hawayen daya zubo mata ne ta share da sauri, salima ce kawai ta iya dago kanta ta kalli cikin idon daddy sannan tace ‘’ ai shi mai kwakwalwar kifinnan kuwa izifinshi talatin ta sama sannan izifin shi goma ta kasa saura izifi ashirin ya sauke alkur’ani kallonta daddy yayi dakyau sannan ya jinjina kai yace ‘’dan ubanki badaru Magana kike fada min ne?’’ charaf amra tayi sannan tace “laa daddy ba haka take nufi ba daman progress din da yake samu ne take fada maka yanxu yana kokari sosai alhamdlh mungode sosai da yanda ake dawainiya damu”, tana kaiwa nan taja hannun salim da salima suka fice, koda suka fito abakin staircase suka hadu da mama kareema, kallonsu tayi sannan ta cigaba da wayar da take yi, gaisheta sukayi sannan suka wuce ta gefenta, dakin direct suka wuce.

Free page….



Chapter 19-20



Kallon salim amra tayi sannan tace kaje wajen mama rabi ka jira yanxu zanzo nima, fita yayi sannan ya jawo kofar ya fice, kallon salima amra tayi sannan tace ‘’salima da alamu bakida hankali ko, mekike shirin yi ne salima so kike ki jefamu cikin masifa kinsan yanda zaman mu yake acikin gidan yanxu mene amfanin mayar ma da dady Magana dakikayi, salima barikiji baki fini jin zafin abinda akeyi mana agidan ba don tun kafin ki mallaki hankalinki na fuskanci wulaqanci iri iri amma duk na koyi shanyewa kuma na hadiye, ina baki shawara ki yi kokari ki dunga danne wannan zafin zuciyar naki inba haka ba da ranki da nawa duk baci zaiyi.

kukan da salima ke hadiyewa ne ta fashe, sheshekar kuka kawai takeyi sannan ta dago ta kalli amra tace ‘’ adda na gaji da wulaqancin da ake mana, na gaji da zagin iyayenmu ta akeyi, yau shekara bakwai Kenan da rasuwar su amma har yau ba adaina zaginsu ba mai sukayi da suka chanchanci wannan wulaqanci da rashin mutunci…mutuminnan ada yafi kowa qaunar mu lokacin da iayeyn mu suna raye amman ayanxu da kasa ta rufe masu ido shine yake wulaqanta mu”.., tana kaiwa karshe ta fashe da kuka,..zama kusa da ita amra tayi ta rungumota jikinta tana lallashinta, saida taga tadaina kukan sannan tace salima ‘’I’m so sorry dan Allah kidaina bari damuwar ahalin gidan nan tana damunki baki ganni ba harna saba, duk rintsi duk wuya allah yana tare damu kinji shine zai kawo mana sassauci yanxu ki share hawayanki kizo muyi game ah yar nokia ta kinji”… dariya salima tayi tana kallon yar uwarta cikin so qauna tace ‘’thank you big sis, adda na, wallahi adda bansan ya zanyi ba idan babu ke”,



kallon ta amra tayi sannan tace ‘’salima ina nan tare daku babu inda zanje zamuyi rayuwa atare insha Allah kinji small sis’’.. dariya salima tayi daga bisani salim ya shugo cikin dakin, anan suka zauna suka sha hiransu su kadai sannan suka kwanta asuba ta gari…….



Haka kwanaki suka dinga tafiya har suka fara exam din second term ayau kuma Friday zasuyi last paper sannan ayi masu hutun term din, dadi sosai su salima sukeji sbd wahalar bulalar latti ta kare.

Bayan an taso su daga school gida direct suka wuce domin su shirya don washe gari za ah tafi katsina gaba daya gidan domin aje agaida kakannin wato kaka larai da kaka binta sai kawu aliyu.

Sammako sukayi don tafiyar hanya zasuyi daddy ne agaban sienna sai driver habu akujerar baya kuma hajiya kareema ce da Khadija azaune, chan quryar baya kuwa ishaq ne sai Muhammad sannan sai jabir da jalal motar bayansu kuwa itama sienna ce irin ta gaba, hajiya labiba ce abaya sai halim agefenta chan kuryar baya kuwa Khalil ne da khamis sai amra da salima, a gaba kuwa driver haladu ne wanda ke tuqawa tare da salim, tafiyar awa uku sukayi suka iso katsina suna parking kuwa kowa ya fito, gidane dan matsakaici amma kuma anyi mashi gyara dan kuwa ginin bulo ne akayi part biyu acikin gidan daya yafi daya sosai nesa ba kusa ba, direct babban part din duk suka wuce hardasu salima suna shiga wata tsohuwa ce tukuf zaune akan tabarma daga gefe wata yarinya da bazata wuce shekaru goma sha takwas ba tana yi mata tausa, ganin masu shugowa yasa kaka binta Shewa tana fadin ‘’ lale lale maraba yau manya manyan baki nayi acikin gida Mustapha na kaine yau agidan …ke tsigai tashi kwaso tabarmu ashimfida kowa ya zauna,’’ wucewa yarinyar tayi uwar daka sannan ta fito da tabarmu ta fara shimfidawa, zama kowa yayi akasan sannan suka fara gaggaisawa, kareema ce ta kalli kaka larai sannan tace “inna mun sameku lafiya?”, kallonta kaka larai tayi sannan tace aikuwa muna nan kalau tunda gashi kin ganni garau, ina waccar farar kishiyar taki?”

kallon labiba kaka tayi sannan tace au ashe gaki nan ko ni zan fara gaisheki ne?’’ kallonta Haj labiba tayi sannan ta yatsine fuska tace sannu kaka mun sameku lafiya?”

ko amsata kaka batayi ba ta maida hankalinta ta kalli jikokin nata tace, “jikokin kaka babu ko gaisuwa”? , gaisheta sukayi gaba dayan su anan ne ta kalli su amra sannan tace, ke Aisha haka kike kiba saikace balan balan lallai Mustapha kana kokari ince suke cinye maka shinkafar gida har sunfi yayan ka qiba ma’’ ..

dariya Mustapha yayi sannan yace ‘’inna ai ina kokari kam, ya muka sameku kuwa, kwanaki na bama aliyu sako ya kawo maki fatan dai an sayo maki komai da kike buqata ragowar wanda ba ah cinye ba kuma kin aikama uwar badaru ko ?,… kallonshi kaka binta tayi sannan tace “eei ankai mata sauran sannan aliyu ya kawo min sabbin buhunhuna allah yayi maka albarka dannan,’’ kowa ya amsa da ameen… nan ne tsigai ta kawo masu lemu da ruwa daga firjin dakin mama binta, ganin an faara salla yasa kowa ya shiga daga cikin domin yin salla, dakuna hudu ne acikin dakin kaka binta, daya dakinta sauran kuma nasu ne idan sunzo, wanda daya kareema da yayanta ne ke shiga shikuma dayan labiba da nata sannan dayan kuma su ishaq ne suke kwana daddy kuma hotel yake zuwa ya kwana har su koma gida kano.

Chapter 21-22



Ganin hankali kowa yayi gaba yasa su amra da kannenta fitowa suka wuce dakin mahaifiyar babansu wato kaka larai, koda suka shiga baiwar allah tana bakin murhu duk tsufanta wanda akalla zata bama binta shekaru kusan bakwai amma ita da kanta take komai,…suna shigo wa tsakar gidan da gudu sukaje suka rungume kakar tasu, allah sarki farin ciki ya cika kaka larai ganin jikokinta saida suka gaggaisa sannan ta jasu har dakinta wanda dakuna biyu ne kawai aciki,sallah kawai sukayi bayan sun kammala ta zuba masu abinci sukaci suka koshi, hira sukayi sosai da jikokin nata wanda idan ta kallesu take tunawa da badarun ta bawan Allah. Da daddare kuwa amra ce ta dafa masu taliya jollof sukaci suka koshi sannan sukayi kwanciyarsu, kwanan su goma chur suka tattara suka dawo kano. Kwanci tashi abin babu wuya awurin Allah hutun makaranta ya kare har sun koma school, su amra kuma

an fara preparation na waec da neco, amra dadi kamar zai kasheta amma kuma tana baqin cikin rabuwa da kanneneta idan ta kammala school, sbd zasu sha wahala sosai daman itace ke karba masu duk wani punishment da za ayi masu na lattin makaranta.

Akwai wata ranar laraba da suka je makaranta

bayan an tashi sun zauna jiran habu driver kusan awa biyu suna zaune shuru babu habu ga yunwa na nuqurqusar su har aka fara kiraye kirayen sallar magrib suna zaune ganin haka yasa hankalinsu ya tashi sosai gashi babu kudi ajikinsu balle su nemi abin hawa, ganin har kusan karfe takwas yasa hankalin amra tashi ga salim yanata murqususun yunwa haka yasa ta yanke shawarar su fita bakin titi dama a gate din school suka tsaya don babu kowa acikin makarantar duk an tafi sai mai gadin school din wanda ko naira goma baza su samu awajen shi ba, tafiya suka danyi mai nisa lokacin Har garin ya soma duhu sosai don ko abin hawa ma ya gagara sbd titin makaranta kamar waje wajen gari take, ganin sun galabaita sosai yasa suka tsaya bakin titin,suna nan tsaye wani mai mota yazo ya gifta ta gaban su, Har yayi gaba sai kuma yayi reverse ya dawo, ganin tsayuwar moto a gaban su yasa suka dan tsorata sbd rayuwa babu tabbas, fitowa matuqin yayi daga moto ya zo har gabansu, kallon Shi sukayi gaba dayansu hannayensu sarqe dana juna kamar za’a raba su.

Saurayi ne dogo akalla zaikai sa’an ya Ibrahim amma shi wannan fari ne, shima ganin su awaje kamar haka ya bashi mamaki shiyasa ya tsaya don yaji ko taimako suke nema gashi ya gansu da uniform. Kallon da yaga suna mashi ne ya sanyashi murmushi yace,’’ hey boy me kukeyi anan kaida sisters dinka’’ …kallonshi salim yayi sannan yace ‘’ driver ne ya manta mu baizo ya dauke mu ba’’ .. tausayi suka bashi ganin yanda suke tsayuwa da kyar… anatse ya soma magana yana kallon amra ‘’idan ba matsala kuzo na sauke ku agida”, da sauri salim yace “zamu bika’’.. bude masu motor yayi sannan suka shiga duk sun takure suna qanqame da juna,saurayin kuwa daya dauko su idonshi nakan amra wadda ta lumshe idanunta kamar mai bacci,,haka kawai yaji ta burgeshi yarinyar domin yaga alamun nutsuwa atare da ita, ahankali suke tafiya har suka iso gida wanda duk salim ne ke yi mashi kwatancen gidan, koda suka iso gidan godiya sukayi mashi sannan suka fara fitowa daga cikin motor din, dai dai nan wata haddaiyar honda ta kunno kai har gaban gate din, habu driver ne ke tukawa sai wani abayan motor wanda ba ah ganin fuskarshi sbd motor akwai tint ta baya, horn Habu yayi sannan mai gadi ya wangale gate din, parking yayi ah wajen da suke parking motocin gidan, su amra kuwa basu tsaya ganin wanda ke cikin motorn ba suka wuce hanyar da zai sadaka da main door, jin muryar ya abdul

-wahab yasa suka tsaya ‘’kai kuzo nan,’’ ahankali suka fara takowa har gaban motorn wajen inda yake zaune ya bude kofa ya zuro kafanshi dake sanye da loafers baqaqe kasa, kallonsu yayi daya baya daya, sannan ya sauke idonshi akan amra yace ‘’ ke uban waye ya sauke ku yanxu nan, kuma maisa sai yanxu kuke dawowa daga school?” Shuru sukayi suna sunkuyar da kansu, ganin sun tsaya suna mashi zuru zuru da ido yasa ya daka masu tsawa, a furgice gaba dayan su suka kalleshi, amra ce tayi kokarin tattara natsuwarta sannan tace ya wahab ba’azo daukan mu bane muna zaune har akayi sallar magrib,’’ shuru yayi chan kuma yace “shikuma wanchan daya kawoku fah?” ..da sauri salima tace yaya ya ganmu ne akan hanya shine ya taimake mu ya kawo mu gida” ..girgiza kai kawai yayi sannan yace “kuje”,… da sauri suka wuce cikin gida, shi kuma yaa juya ya kalli habu yace “kai wake dauko yaran nan?” Atsorace habu yace “nine yallabai”, …. “meysa baka dauko su ba yau?” Kallonsa habu yayi yace ‘’bayan na sauke su ishaq da rana shine hajiya tace wai na wuce airport na jiraka sbd bakason jira”

Murmushin gefen baki yayi sannan yace “good” fitowa yayi daga motor ya nufi cikin gidan direct yah hau sama part dinsu, dakinshi ya wuce dake cikin part din mamansu ko zuwa gaisheta tsaya yayi ba saida ya wuce toilet ya sakarma kanshi shower sannan ya fito ya sanya jallabiya dama already sunyi sallah ah masallaci akan hanyansu na dawowa daga airport, fitowa yayi ya wuce dakin mummyn su inda ya sameta tana zaune gefen gadonta tana waya, waje ya samu ya zauna akan kujerar dake gefen gadonta, saidata kai karshe wayan sannan tace, “hajiya madina bari na kiraki anjima kadan” sannan ta aje wayan, tana fuskantar shi, ‘’mummy ina wuni na sameku lpy” ya fada yana kallonta, murmushi tayi sannan ta ce “ya hanya kai iso lpy wahab?” amsa mata yayi da alhamdlh,

…kusan minti biyar shuru babu wanda yayi magana sbd akwai dan kunya tsakanin su ta dan fari, sun dauka kusan five minutes sannan ya kalleta yace ‘’mummy naga yaran uncle sai magrib suka dawo yau meysa ba’asa dayan driver ya dauko suba?’’ tabe baki tayi sannan tace ‘’dazu danasa habu ya dauko ka saina manta ma da sha’anin su Akwai matsala ne?”…sunkuyar dakai

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login