Showing 27001 words to 30000 words out of 95534 words

Chapter 10 - GURBIN IDO COMPLT

Start ads

11 Aug 2025

603

Middle Ads

dan wannan rugar,muna zaune tare da ita tsahon shekaru,kwatsam tayi baquwa,wadda ta shigo rugar nan tare da furera da taje ganin gida,matar itace shatu,wadda tazo da diyarta maimunatu......sun shigo tare da tarin dabbobi wadda dukka dabbobin nan mallakin shatu da diyarta maimunatu ne,amma kuma a idanun kowa dabbobi na furera ne,don a haka ta gayawa kowa wannan labarin,ta shaidawa mutane cewa gadonsu dama taje gida karbowa ta taho dasu,ta kuma hado da wadda zafa dinga mata kiwo tana biyanta wato shatu,abinda zai baki mamaki,shatu ba kowace bace a wajen furera face 'yar uwarta da suke uba daya,bata da ikon musawa ko qi,saboda a sannan shatun na cikin wani yanayi na tashin hankalin rayuwa,tana neman mafaka,mahaifin maimunatu baqo ne,irin baqin dake shigowa garin na gembu saboda huldar kasuwanci da kuma yawon buda idanu,a nan yaga shatu ya kuma tsaya kai da fata sai daya aureta,a nan garin ya barta saboda ta nuna tafison zama cikin danginta,yana zuwa yana ganinta yayi mata kwanaki ya koma,mutum ne mai arziqi,don haka gida na alfarma ya ginawa shatu,ya zuba mata dukka kayan alatu da more rayuwa,ta yadda gidan shatu shi ya zama abu kwatance da kuma burin kowa cikin garin nasu,wannan ya haifar da hassada daga zuciyar 'yan uwanta da suke 'yan uba,saboda ita shatu su biyu mahaifiyarsu ta haifa a gidan,ita da 'yar uwarta sa'ade,kusan jinin dakinsu ne haka,sannan kuma da baiwar zallar kyau da Allah yayi musu fiye da sauran 'yan uwansu,itama sa'ade nata mijin me hali ne sosai,hakan ya sake haifar da zallar 'yan ubanci a tsakaninsu,saidai sunata dannewa saboda suna rabarta suna kuma samun akhairai da abun duniya daga wajenta,kasancewarta ba mai rowa ba,a haka ta haifa maimunatu,dukka alhaji na zuwa wajenta ne yayi mata satittika ya tafi,bayan ta.haifi maimunatu yake maganar zai kaita taga danginsa,saidai kuma wata tafiyace ta taso masa,wanda ya dauki tsahon watanni kafin ya dawo,koda ya dawo din kuma shima yana da niyyar kaita,har sun shirya sun saka rana,yace zai taho takanas daga kano ya dauketa. Shiri sosai shatu tayi domin zuwa ganin surukanta,ta shirya maimunatu da kyau wadda ke samun gata kamar babu gobe,itama haka,saidai haka ta yita jiran alhaji amma shuru babu shi babu dalilinsa,nata da wayar hannu bare ta nemeshi,haka tayita zaman jiransa har dare yayi ta fidda tsammani,ta sanyawa ranta qila wani abune ya tareshi,ta barwa gobe. To washegarin ma dai haka ta yita jiransa shuru babu shi babu labarinsa,haka wata washegarin,wasa wasa sai ga kwanaki nata tafiya shatu bata sake ganin gilmawar alhaji ba,abun ya daga hankalinta qwarai da gaske,tafi tafi watanni suka fara shudawa shuru babu shi babu dalilinsa,ga ciki da ya bayyana a jikinta,ita dai ta yarda da alhaj dari bisa dari,saboda iya tsahon zamata dashi tsakaninsu ita dashi babu komai sai son barka,mutum ne mai son addini da kuma kiyaye dokokin Allah,kusan a wajensa shatu tayi karatun addini mai dan dama wanda ta dinga koyawa maimunatu,duk da a sannan ta sanyata makarantar islamiyya da boko,amma kamar tasan yadda rayuwa zata juya musu,sai take zama duk bayan sallar magariba take mata nata karatun,ganin cewa yarinyar tana da budaddiyar kwanya dake saurin kwashe karatu,don tun bata isa sakawa a makaranta ba ta sanyata,tace tayi wayon acan,hakan yasa adan lokacin ta samu karatu me yawa,tana cika shekara tara zata shiga ta goma ta gama primary,mahaifinta nada niyyar yi mata shirin shiga makarantar gaba wannan abun ya faru"

*Follow my arewabooks account for more new pages*

HUGUMA



*11*


"Yau da gobe bata bar komai ba,hakanan zara bata qyale dami ba,dukka kayan abincin da shatu ke dasu wanda alhj ke jibge mata suka faru suka qare,ta fara kame kame,a sannan yan uwanta suka fahimta,sukayi mata caa,yar uwarta saade tace kada ta kulasu,ita ta dinga taimaka mata har zuwa wani lokaci,wanda kishiyar mahaifiyarsu wadda wajenta suka rayu sanadiyyar rasuwar mahaifiyarsu tun suna qananu ta tayar da borin qarya,ta tara manyan gari,ta fada musu qabli da ba'adi kan rashin dacewar zaman shatu ita daya cikin gidan,tace saidai lallai ta dawo gabanta da zama,saade yayar shatun bata qalubalanci hakan ba,hakan yayi,duk da tasan badon Allah inne tayi hakan baAmma kuma bayan giya akwai wata caca,maza maza tayi ta sanya aka saida gidan da shatu ke ciki,tunda mallakin alhj ne,ya ginawa shatun,ta tattara kudin ta siyawa shatun dabbobi ta damqa mata,saboda gudun abinda kaje yazo,babu jimawa shatu ta tattara ta koma gida ita da maimunatu,gidan da suka fara sabuwar rayuwa me cike da qunci da kuma takura,wahalhalu iri daban daban,zuciyar shatu na cike da qauna da kuma begen mijinta,jiki da zuciyarta sinqi yarda da zancan daketa yawo a garin kan cewa,mijinta guduwa yayi ya barta,tafi kowa sanin halinsa,tayi imani bazai aikata mata haka ba. Zama ya sake tsanani a wajenta sanda inne ta fahimci cikine da ita,tayi tsalle ta dire kan ba za'a haifa mata dan da bashi da uba ba,maganar data tsayewa shatu da saade a rai,ta kuma kusan haifar mata da ciwo,a lokacin saade bata kusa da ita,kasuwanci ya shillata ita da mijinta zuwa benin republic,wanda tayi matuqar baqincikin hakan,saboda sanin halin da 'yar uwarta take ciki,amma babu yadda zatayi dole tabi mijinta. Ana tsaka da wannan fa shine inna furera taje garin,ita tunda ta qyalla idanu taga dabbobin da shatu ke dasu tayi mata romon bakin ta biyota rugarsu tayi xamanta,ta kula da dabbobinta ta haihu a can babu takura. A zaton shatu ta samu mafaka a wajen yayartata,saidai tun basu kai ga shigowa rugar ba ta fara yanka mata sharuda tare da shaida mata dokokin da rugar ke dasu,suka kuma yi yarjejeniyar dabbobinta zasu shiga a mazaunin na ita fureran,idan ba haka ba zaayita kawo musu farmaki ana kashesu tunda ita baquwa ce. Ko a sannan shatu shekarunta basu fi ashirin da hudu ba,saboda auren wuri akayi mata kamar yadda aka saba.

Shatu ta shigo baquwa a rugar nan,wadda hatta da kyanta ya banbanta da irin namu,babu tausayi ko tsoron Allah furera ta maida shatu da maimunatu tamkar bayi da basu da 'yanci,shatu bauta maimunatu bauta,Allah ya zubawa shatun wani irin haquri juriya da kuma kau da kai wanda cikin irin nata ta sanwa maimunatu,don babu lallai tayi yakai irin nata,a haka dai suke rayuwar. Abinda ya faru ya kuma janyo shatu da maimunatu suka zama abun qyama shine......a al'darmu ta fulani,baka ganin nagge ko sauran dabbobi ka nuna su tankasu,komai kyau da burgewar da suka baka,cikin irin haka,cikin rashin sani shatu taga wasu nagge na bappa labaran,yana gab da fita dasu kudu,ranar an fiddasu kiwo ta nuna wata babbar nagge a cikinsu tace a haka kamar lafiyayya me kyau da ita,amma kuma bata da lpy,suka yita fada dame kiwon,aka mata ca,ta bada haquri,saboda mantawa da tayi ta aikata hakan,kuma tace tana musu tsoron asara ne,magani ya koma a maidata gida a bata,koda suka dawo gida baice bata da lafiya ba yadda shatu ta fada,ba'a wayi gari da naggen ba ta rasu,rigima sosai daada taso a tayar,amma bapp ya hana,abinda basu sani ba ni da kaina bayan asuba na fita zan dora sanwar safe,na lura da naggen bata da kuxari yadda ya kamata,ni da kaina nasan tabbas bata da lpy,to amma dana fada qaryatani daada tayi,tace kawai dai don tana zuwa wajena ne yasa nakeson kareta,anyi wannan rigimar ta mutu,shatu da tsohon cikinta taje diban ruwa matan gidan barau daya daga cikinsu ta takaleta da fada yadda suka saba mata,tunda muke da shatu bata taba gayamin ko kawomin qarar kowa ba,amma inajin labarin yadda wasu cikin rugar suka matsanta mata,a ranar taso dauke kai amma yau da gobe,ga yanayin tsohon ciki haihuwa ko yau ko gobe,talatu bata duba wannan ba ta dinga ja mata riga shatu na gocewa,daga qarshe dai da talatu taga ba zata kulata ba sai ta tureta,wanda sauran kadan ta afka cikin rafin,Allah ne kawai yayi ruwan ba shine ajalinta ba,sosai ran shatu ya baci bayan tasha da qyar,cikin bacin rai idanuwanta cike da hawaye ta kalleta

"Na dauka ko banci darajar komai a wajenki ba zanci darajar cikin dake jikina,tunda kema macace,idan kinyi hakane don ki tozarta ni kije,Allah yana gani,kuma ina fatan kiga sakayya da gaggawa anan kusa" daga haka shatu bata qara ba bata rage ba,ta dauki ruwanta ta wuce,suka taru suka yita maida magana,tare da maido maganar nagge,a nan suka fara qulla wataqil mayya ce ita din,kwana biyu tsakani kuwa talatu taje diban ruwa ruwan yayi ciki da ita,ya kuma zama ajalinta,aka fara lugwigwita magana tare da fara yada jita jitar shatun mayyace,kafin kace me?,magana ta fantsama a gari,dangin talatu da sauran mutane 'yan bani na iya suka dauki sanduna sukayi gidan furera kan sai an fiddo shatu sun kasheta,ya tabbata mayyace ita,da qyar da sudin goshi qurar ta lafa,baiwar Allah shatu,ashe sanadin wannan tashin hankalin naquda ta tasammata,furera haushin abinda ya faru tayi banza da ita,daga ita sai maimunatu ne suka yita fama,daga qarshe tace maimunatun ta lallaba ta kirawo mata ni,har maimunatu takai bakin qofa ta qwala mata kira,saita tsaya,ta yafitota da hannu ta koma gaban shatun ta duqa

"Daada,akwai wani abun da kike so ne?" Murmushi ta sakar mata,ta daga hannayenta ta cirw dukka duwatsun jiki da maimunatu ta dade tana qulafucin tabar mata ta zura mata su,saidai yarinyar a sannan sam bataji farincikin da take ayyanawa zataji ba duk sanda daadar tata tabar mata dutsunan

"Daada kin barmin ne wai?" Kai ta gyada

"Na bar miki maimunatu......kiyi haquri kiyi haquri.....kiyi haquri kinji,ki fuskanci rayuwa duk yadda tazo miki,ki zama mai gaskiya da amana,karki yadda a kamaki kinci amanar wani,idan kinga saade,kice ina mata fatan alkhairi" sanda yarinyar ke gayan abinda uwar tace nayi mamakin yadda ta iya riqewa,hankalin maimunatu a sannan ya tashi sosai duk da qarancin shekarunta,ba kowa zai gane hakan ba sai wanda irin haka ya sameshi,cikin rudewa tace

"Daada" hannu ta daga mata

"Barci nake ji,yi sauri ki kiramin yuuma" maganar data sanya maimunatu tashi ta fita a dakin da gudu,fitar da ta zama silar rabuwarta da mahaifiyarta kenan rabuwa ta har abada,don koni sanda na shiga wajen shatu rai yayi halinsa,haka akayi mata sutura bata ko haife abinda yake cikinta ba,sanda na koma gida da daddare randa shatu ya rasu,tunda na tsaya na taya maimunatu da bata dame rarrashinta zama,mahaifiyarta ta rasu ta barta babu ko mutum daya da zata jingina dashi tayi kuka taji sauqi cikin ranta,Bappa da kansa ha sameni,ya shaida min ya yanke hulda da wata alaqata da duk abinda ya shafi shatu matuqar shike aure na,duk randa na kuskurewa hakan kuwa,zai dauki tsatstsauran mataki a kaina,bansan me aka gayawa bappan ba bayan fitata wajen shatu,amma dai na sani cewa akwai qullin daadar himu da kuma furera a ciki da suka sake tunzura komai,don kuwa bappan mutum ne mai sanin ya kamata,sannan ta yaya zaa rabani da maimunatu kuma abar mu'amalar dake tsakanin furera da daadar himu?,bayan duka gida daya ne,abu daya ne?,duk da furera ta cikasu da labaran qarya na cewa babu abinda ya hadata da shatun illa aikin bauta data dauketa,mutuwar shatu sai furera ta sake sakankancewa,ta mallake dukka dabbobin shatu da maimunatu suka zama nata,maimunatu bata tashi a komai ba illa me aikin bauta,ta riqeta wani irin riqo na qunci da kuma wahala,dole inaji ina gani na dauke idanuna daga kan maimunatun,nayi kamar bansan tana raye ba,saidai ban fasa mata addu'a ba da nema mata sasauci"

"Yanzu 'yan wadan nan abubuwan sune suka zama hujja da kuma dalilin da ake qyamatar yarinyar bayan cikin abun babu wani abu guda daya data aikata?"

"Sune anni" kada kai kawai anni keyi,wani abu ya tsaye mata a zuciyarta me taba rai,tana kwatanta yuuma da maimunatu,inda an samu sakaci ko wani abu makamancin hakan haka zai iya faruwa da yuuma kenan sanda tana qarama,duk da ita tana gaban mahaifinta ne cikin soyayya da kulawa a sannan?.

"Wannan duka ba hujja bace,zallar jahilci ne da kuma son zuciya,kuma tabbas sai Allah ya yiwa yarinyar sakayya,zan dauke maimunatu daga wannan garin don bata cancanci zama a nan ba,maraya?,maraya wasa ne?,daka taba maraya hawayensa guda daya tak ya diga a qasa saboda kai,gwara ka rasa dukkan abinda ka mallaka ciki harda lafiyarka,kukan maraya masifa ne bare a sakashi a damuwa" yalwataccen murmushi ne ya bayyana fuskar yuuma

"Da nafi kowa jin dadin hakan anni,tabbas zanfi kowa murna"

"Kafin na wuce zan karba maimunatu zan wuce da ita,in sha Allah qarshen kukanta yazo,lallai mahaifiyarta macace mai nagarta,nagartar da nake jin yaqini da tabbcin akwaita tattare da maimunatu,tunda dukkan alamu sun bayyana"

"Amma anni wani hanzari ba gudu ba.....anya kinyi duba da tarin banbanci da tazarar dake tsakanin ja'afar da maimunatu kuwa?,shirinki me yuwuwa ne?" Tambayar dake rai da zuciyar laila kenan,labarin ya dauki hankalinta cike da mamaki da kuma al'ajabi,zuciyarta kuma ta narke matuqa da tausayin maimunatu

"Nasan ta inda zan bullowa lamarin,ki tayani da addu'a,kiyimin fatan dacewa" ajiyar zuciya mai qarfi yuuma ta sauke

"Allah to yasa a dace,yasa ta silarki marainiya maimunatu zata samu salaama a rayuwarta"

"Ameen ya hayyu ya qayyumu" anni ta fada tana lanqwasa yatsunta,tare da tunanin ta inda zata fara.


*_Arewabooks::huguma_*


❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K'ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107

*_THANKS FOR CONTINUES PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰


12

Ajiyar zuciya ta sauke sanda ta tabbatar ta maida sarqar wa anni,ta godewa Allah da ya hani inna furera sanya son zuciyarta a gaba ta hana a maidawa anni sarqar,ta tabbata da ta aikata haka ba zata taba samun nutsuwar zuciya ba,haka zuciyarta take,bata qaunar haqqi koda qanqani a kanta,dalilin da yasa ta guji kiwon dabbobinta da bugu kenan,ta zabi horar dasu da magana.

Sosai hankalinta yayi nisa cikin zuzzurfan tunani,abinda ya sanya kwata kwata bata ankara da tahowarsa ba,sai da taji ta bugi wani abu sannan ta tsaya cak,ta kuma ja da baya da sauri tana kai dubanta gabanta.

Himu ne,sanye da kayan fulani,ya fito a bafullataninsa sak,kayan sun matuqar karbarsa sun kuma haskashi matuqa,saidai babu fara'a ko walwala kwata kwata saman fuskarsa.

Gabanta ne yayi mummunar bugawa sanda ta tuna da gargadi da kuma izayar da tasha hannun inna furera duka akan himu,abinda ya sanyata yin gaba da sauri ta rabeshi zata wuce,saidai cikin hanzarin shima ya matsa ya tare mata hanyar,da azama ta koma daya hannun nan ma ya bita ya tare,ya kare ko ina,bata da zabi illa ta roqeshi

"Don girman Allah ka bani hanya na wuce"

"Saboda me maimunatu?,me yasa kike guduna?" Tsoro ne ya sake kamata,sam bazai fahimci halin da take ciki ba,wannan tsaiwar da yayi a gabanta sai takejin kamar ana tsigar ranta

"Magana nakeso muyi dake maimunatu" wace magana?,a yanzun akwai.maganar kuwa da ita din zata fahimta?

"Kayi haquri,bazai yiwuba,ka barni na wuce"

"Dole ki tsaya ki saurareni maimunatu,don me yasa zaki saurin bada kai akan soyyayarmu?,kodai dama bakya sona?ni daya nake kidina da rawata?" Tuni hawaye ya balle mata,himu so yake kawai ya janyo mata bala'i,baisan yanayin da take ciki ba,da bai tsaya haka a gabanta ya tilasta mata sai sunyi magana ba,bayan ita bafahimta take ba,ta juya baya a matuqar razane sanda taji takun tafiya,take qafafunta suka fara rawa,sai shima ya waiwaya yana duban hanyar.

Kaf jinin jikinta sai daya daskare sanda taga inuwar mutum kuma macace a wajen,abinda ta baiwa ranta shine daada ce ko zubaida ko safiya,ta saddaqar ta gama yawo,kashinta kuma ya bushe,tun daga fuskarta zuwa tafin qafarta sukayi sanyi qalau

"Kuyi haquri,na katse muku jin dadin ku ko?,zan dan wuce ne?" Laila ta fada tana dan sakin fuskarta,ta fuskanci akwai wani abu me kama da soyayya a tsakaninsu,to amma anni tasan da haka kuwa?.

Jin baquwar murya da sautin da ba na fulani ba ya taimaka wajen dawowarta hayyacinta,matsawa laila himu yayi ta fara wucewa,abinda ya baiwa maimunatu damar yin wuf tabi bayan lailan

"Maimunatu" ya kirayi sunanta,saita qara hanzari da kyau ta fara shawarar bi ta duhuwa don kada ma ya biyota ya jawo mata jarfa

"Ina sonki.maimunatu,kuma wallahi bazan fasa sonki ba koda ke baki sona,zanci gaba da sonki har sai na sameki a matsayin matata" kalamai na qarshe kenan dataji daga bakin himu,ta qara hanzari,tana jin cewa inama itadin tana cikin nau'in mata masu hanzari wajen tafiya,lallai da tayi amfani da wannan don ganin ta sake yin nesa da ibrahim.

"Haba 'yammata,saurin me kike haka?" Muryar laila dake biye da ita ta ratsa kunnuwanta,yadda ta juyo kawai zai gaya maka har yanzu a tsorace take

"ya kike gudun wanda yake sonki?" Laila ta fada a tausashe bayan ta iso gaban maimunatu ta tsaya,ta kuma dora hannunta saman kafadar maimunatun zuciyarta na narkewa a tausayinta.

Daddadan qamshin dake tashi jikin laila maimunatu ta zuqa zuwa hancinta,laushin turaren ya sanya zuciyarta karyewa,yadda lailan ta tambayeta cikin taushi da nuna kulawa yasa rauninta ya ninku,take hawaye ya cika idanunta,a wannan lokacin gaza tareshi tayi,sai kuka ya qwace mata.

Kasa hanata laila tayi,duba na tausayi takewa maimunatu,tana kwatanta kanta a matsayinta,tana kwatanta inda itace ta yaya zata rayu babu abbi babu momma?,ya rayuwarta zata kasance?,maimunatun jaruma ce qwarai kuma abar tausayi ce ga dukka wani me tausayi.

Dole ce zata sanyata ta guji himu ba din ya cancanci a gujeshi ba,bata da yadda zatayi matuqar tana son tsira da lafiyarta da kuma rayuwarta,goge hawayen

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login