Showing 51001 words to 54000 words out of 95534 words
mayafinta
"Ba zaki gane ba fatima....na jima inason yaa ja'afar,ba zaki gane me nakeji ba a kansa" kalaman hafsa da suka sake shiga kunnuwanta kenan,ta dan kauda kanta tana jin kunya da mamakin yadda budurwar keta haqilo akan namiji,ta tayar da sallah abinta.
Kafin ta idar sun gama maganar,wanda fatima ce ta sakar mata ganin ba zata fahimci abinda takeson nuna mata ba,a nan suka zauna suna taba hira ita da fatima,wanda dukka kusan akan islamiyya ce,da alama itama mayyar islamiyyar ce kamar yadda maimunatu take,kusan bata taba ganin fatima a gidansu ba,saboda yawanci tana islamiyya,ko a makarantar boko bangaren islamic take,abinda ya bawa maimunatu sha'awa sosai,har taji itama islamic take sha'awar yi inda zata samu dama,saidai ba zata iya buda baki ta yiwa anni ko dr maganar ba.
Daya daga cikin yaran gidan ne ya leqo bayan sallar magariba,yace maimunatun tazo inji anni taci abinci zasu wuce gida,da hanzarinta ta tashi,abinda yasa fatima zolayarta
"Dama kin gaji da gidan namu,da alama so kike dama a tafi" murmushi maimunatun ta sakar mata ba tare da tace komai ba
"Allah yasa ki iya zuwa mana ma da bikin anty amira ki kwana"
"Allah ya kaimu" ta amsa mata tana murmushi,sai fatiman ta taka mata zuwa falon da annin ke zaune.
Tun kafin ta qaraso muryar mai kauri da zurfi take ratso inda suke,matashi ne mai cikar haiba da kamala zaune sosai gaban annin suna magan,da alama akwai sabo sosai a tsakaninsu,farin bafullatani sak,wanda yake diban kama ta sosai da haj munira.
"Dole cikin satin nan kije,ko fatima saita rakaki,tunda kina jin dadin maganin bai kamata a fara fashi ba,zan kirashi na gaya masa sati daya zakuyi" ya qarashe maganar yana daga kansa,dai dai sanda idanuwansa suka sauka kan fuskar maimunatu dake takowa a hankali jere da fatima.
Tamkar haduwar mayen qarfe da maganadisu haka yaji wani abu mai qarfi ya fusgeshi,duk yadda yaso ya dauke idanunsa daga kanta hakan ya gagara,harta qaraso ta soma gaidashi a darare tana lafewa daga gefan anni.
Da mamaki fatima ke satar kallon yaa khalid din,shi da baya yiwa mace kallo uku amma yau gashi ya kafe idanunsa akan maimunatu?,sai daya fuskanci fatiman na kallonsa sannan yajanye idanun nasa ya kuma bata rai yana komawa ga batunsu shida annin,saidai lokaci lokaci yana satar kallon ta.
Iya tafiya ta tafi dashi,duk da bata qarasa kalar macen da yakeson aure ba,amma fa hada komai da komai,special care kawai zata samu ta wasu bangarori ta yiwa mata fintikau.
"Nidai bansan me kakeson maidani ba khalid,wannan jewar fa ta isheni,nidai a barni,ciwo ai ba mutuwa ba,idan lokaci kuma yayi dole na tafi" anni tayi statement din qarshe tana miqewa tsaye da zummar tafiya,bayan maimunatu taqi cin abincin da aka kawo mata,sam ba zata iya ba,tana jinta ne duk a daure saboda kallon data fuskanci saurayin yana ritsata dashi,wai shin kam haka samarin family dinsu suke ko kuwa su din su biyun daga garesu ne?.
Shi ya musu tattaki har zuwa bakin motar da sunan yiwa anni rakiya,fiye da rabin hankalinsa yana kan maimunatun,duk da yana yine yana basarwa har motarsu ta daga.
Yayi tunanin da sun yafi shikenan,saidai kuma kasa nutsuwa zuciyarsa tayi,har sai da yakai kansa gida dr marwan,ya kuma sakeyin ido biyu da.maimunatu,tun daga sannan abun ya zame masa kamar wani jarrabi,duk bayan kwana biyu daga office yake zartowa nan din,baya barin gidan sai bayan sallar isha'i.
*********Karfe shida suka dawo daga islamiyya,tana sanye da babban hijabinta da ya saukar mata har qasan qafafunta,kalar blue black,abinda yasa yayi matuqar haskata tare da yi mata kyau,tana rungume da qur'aninta a qirji,laila na gefanta tana amsa waya.
Suna sallama a falon sukayi idanu biyu dashi,qirjinta yayi mugun faduwa,taja da baya kamar zata koma sai kuma ta kasa,ganin ya ganta sarai,cikin zuciyarta bata son haduwarta dashi,saboda kallon da yake tsareta dashi da kuma sanyata cikin lamuransa da yawa,har fiye dasu laila da suke jininsa.
A hankali ta biyo bayan laila kamar me tsoron wani abu zai iya kamata,tana jin laila na masa sannu da zuwa sai itama tabi sahunta,ta kuma sulale da niyyar wucewa dakinta,saidai ya tsayar da ita da tambayoyi kan karatunta,abinda ya bawa laila damar wucewa ta barsu su daya a wajen.
Sallamar hisham daga bakin qofa ya ja hankalinsu duka,suka hada idanu da dukka su biyun,take fara'ar dake saman fuskarsa ta bace bat,ya fara shigowa falon cikin rashin walwala yana faman shan qamshi.
Kowa a cikinsu cikakken matashi ne mai jin kansa,wanda ya hada komai da komai,musabaha sukayi da juna kowa yana dauke wuta,ba kamar yadda suka saba ba,har zuwa sannan kan maimunatu yana qasa,ta yiwa hisham sannu da zuwa,maimakon ya amsa,sai ya koma da baya ya zauna cikin daya daga cikin kujerun falon yana cewa
"Je kitchen ki kawomin ruwa" a hankali ta tashi tana jin wani nauyi na raguwa daga cikin zuciyarta,zamanta a wajen tana jinta ne kamar cikin wani matsatstsen keji ne da babu sakewa.
Shuru ne ya biyo baya a falon,hisham na danne danne a wayarsa,khalid kuma yana kallon news,kowanne da tunanin da yake a ransa game da dan uwansa,ba tun yau ba duka sun tsargu da juna,sun kuma fahimci mawuyaci ne idan basiu tarayya akan wani abu guda ba.
Ruwan ta kawo masa hade da cup,ya dauki gorar ruwan yana cewa
"Ba daga islamiyya kike ba?" Kai ta gyada masa
"Bita ce ta kamaceki ba ki zauna kina surutun banza ba...wuce daki ki ajjiye qur'anin hannunki" cikin jin kai da isa khalid ya gyara zamansa sosai yana kuma dubansa kai tsaye
"Dakata mana hisham?,wanne irin nonsense ne zaka same mu tare sannan kace ta wuce ciki?.... please kada ka shiga hurumin da ba naka ba" wani kallo hisham ya watsawa khalid sannan ya saki murmushi
"Nonsense?......hmmmm,dani da kai za'a samu wanda ya dace a gayawa hakan,wuce maimunatu tun raina bai fara baci ba"
"Ba zata wuce ba!" Khalid ya fada a tsawace,dai dai sanda anni ke qarasowa falon,ta bisu da kallo cikin mamakin yanayin data taras dasu.
_To fa masu karatu,khalid dinne ko hisham?,ko kuma ja'afar?,waye zaiyi wining?,muje zuwa yanzu aka fara wasan_
21
"Kai.....kai,meye hakan?" Anni ta dakatar dasu cikin tsawa,ganin zasu fara sa'insa a tsakaninsu
"Ya zaizo ya samemu zaune,sannan kawai yace sai ta tashi ta shiga daki anni?,wannan wanne irin raini ne?" Khalid ya fada cikin jin ciwon abinda hisham yayi masa,yana jin ya disgashi abinda ba'a taba yi masa ba
"Anni,dawowarta kenan daga makaranta,da alama ko ke bakisan ta dawo ba,don nace ta shiga ta ajjiye qur'aninta sai ya zama laifi?" Shuru ne ya biyo baya,anni tana nazartar kowannensu cikin sakannin da basu wuce biyar ba,sai taji hankalinta ya dan tashi,zata iya cewa bata taba ganin irin wannan sabanin ba a tsakanin jikokinta,wannan shine karon farko da hakan fa faru,duk da tasan dama tsakanin khalid da hisham ba jituwa bace can can,amma kuma basa cecekuce,tabbas ya kamata ta yuwa tufkar hanci da wurwuri
"Wuce ciki maimunatu" anni ta bawa maimunatu dake daskare a wajen umarni,da hanzarinta kuwa qafafunta na rawa tayi ciki,kamar ta tashi sama haka takeji,har ta samu ta isa ga dakinta,ta tura qofar ta shige,ta zame a hankali a qasa ta zauna qafafunta suna rawa saboda tsabar tsoro,me ya kaisu fada a kanta?,shin wai basu duba kamanninsu da darajarsu ba da zasu tsaya suna fada a kanta?,kamar ita maimunatu?,wadda bata da komai?,bata kuma mallaki komai ba?,me yasa?,abinda ta dinga tambayar kanta kenan cikin mamaki da kuma tsoron abinda ya farun yanzu.
"Ku zauna" anni ta fada musu itama tana lalubar wajen zaman
"Ka zauna mana nace!" Anni ta fadawa khalid tsaye cikin matuqar bacin rai a tsawace.
Sun kusa minti biyu shuru kowanne anni tana karantar fuskarsa,kafin daga bisani ta kirayi sunan kowa a cikinsu
"Me idanuna suke gani?" Ta jefa musu tambayar da ba wanda ya shirya amsa mata,sai cin d'aci da kowannensu yakeyi
"Tun ina raye hakan zata fara faruwa ina ga ace qasa ta lullube idanuna?......to in sha Allahu wannan abun ba dai cikin ahalina da zuria'ta ba,haihata haihata,bazan lamunta ba kuji da kyau,na meye zaku dinga sa'insa akan maimunatu?,to dukkaninku ku dauketa a matsayin qanwarku,banason kowa ya sanya wani abu a ransa bayan wannan.......kuma inaso a yanzu yanzu ku baiwa junanku haquri"
"In sha Allah" kowa ya fada a cikinsu saidai murya ciki ciki,hisham ne ya fara bawa khalid din haquri,tunda ya girme masa da watanni kusan shida,shima khalid din ya maida masa,sannan khalid din ya miqe hannayensa zube a aljihunsa yana shaidawa anni zai tafi
"Aiba yanzu k saba tafiya ba,ko don na muku fada?" Kai ya girgiza yana duban agogonsa
"A'ah,dama da wuri naso na koma yau din,ina da abinda zanyi" tabe baki anni tayi
"Oho maka.....a sauka lafiya" qaramin murmushi ya sake ya juya yana ficewa daga falon,qasan ransa yana juya maganar anni da tace su dauketa matsayin qanwa kawai,shikam.dai Allah ya sani ya gani yana so,zai kuma yi duk iyakar bakin qoqarinsa,zai kuma fafata da kowa don ganin ya samu maimunatu,bawai ya haqura bane.
Sun fita sun bar anni ne da dogon nazari da tunani,tana tsoron kada abubuwa suzo su kwabe ba kamar yadda take shiryawa ba,tana hangen al'amura masu nauyi a idanun kowannensu tsakanin hisham din da khalid,wannan tunanin ya sanyata daga waya ta laluba number dr marwan,ta shaida masa idan ya shigo gida da wuri a yau tana son ganinsa,idan kuma bai shigo akan kari ba gobe da sassafe ya nemeta kafin ya fita ya amsa mata da to,saita maida akalar kiran nata zuwa number jabir.
"Me kuke har yanzu a qasar nan ne jabiru?" Ta tambayeshi kai tsaye ba tare data tsaya bi takan tambayarsa,sumarsa yaci gaba da tsanewa da towel
"For now dai ni na gama duk schedule din da nake nasu a turkey,matsalar tana ga mutuminki,sam bashi da sha'awa ko nufin tahowa" gyara zamanta anni tayi sosai
"Nan da yaushe kake ganin harshi xai iya dawowa gida?"
"Karshen watan nan nan da 2weeks kenan komai nasa zai kammala"
"To ka shaida mana,lalai dakai da shi din ina da buqatar dawowarku qasarku zuwa farkin sabon wata......kai kaga ma,hadani dashi a waya"
"Okay, hold on karki kashe" yayi maganar yana maqale da wayar,gami da ajjiye wandon hannunsa da yake da niyyar sanyawa ya fita a dakin.
Kofar dakinsa da sassanyar qamshin turarukansa suka kamashi ya tura,luf luf dakin yake,saidai bashi a nan,ya kalli a gogo,lokacin da yake shiga gym ne,tabbas yana can,don haka ya juya da 'yar sassarfa yayi can.
Sanye yake da farin wando qal me ratsin green daga gefe da gefansa,iyakar wandon wasan gwiwarsa,hakan ya sanya sambala sambalan qafafunsa dake cike da gargasa suka bayyana,sai rigar kayan armless shirt,yana tsaye daga bakin window,hannunsa riqe da qaramin towel yana goge zufar jikinsa,idanunsa kuma na ga waje.
Duk da yaji sautin bude qofar amma bai juyo ba,haka ya sanya jabir din takowa ya iskeshi a wajen da yake tsayen
"Anni na magana" ya fadi masa a taqaice,kamar bazai motsa ba,sai kuma ya cilla towel din gefe yana juyowa duk da har yanzu idanuwansa naga wajen
"Duk randa mutanen can suka shiga gonata zasu gane shayi ruwa ne" ya fada fuskarsa na nuna alamu na bacin rai,wajen jabir yakai idanunsa,wasu 'yan asalin turkey dinne,baisan me yasa mutanen suke da jin kansu da alfaharin su turkawa bane,ba yau ba sun saba wulaqanta baqar fata kamar yadda yanzun sukewa wasu,duk da laifinsu ne,yawanci suke zubar da kansu
"Kar ka fara,ka rufa mana asiri,a qasarsu kake fa?"
"And so what" ya fada cikin nuna halin ko inkula,kana ya miqa hannu ya zame wayar daga kunnen jabir ya maidata kunnensa,yana qara taku zuwa gaba gami da gaida anni.
Waje ya samu ya zauna bayan ya gama jin dukka bayananta,yatsunsa ya nutsa cikin lallausan gashin kansa,baisan me zai gayawa anni ta fahimta ba,kamar yadda ya rasa gane taqamaimen dalilinta na birkice masa,tare da bashi umarnin tahowa gida next month,bayan kuma shi bai shirya hakan ba,banda amna ma,baya tunanin xai koma nan kusa
"Zan duba,zanyi qoqarin zuwa" wannan itace amsar daya bata.
Sanda anni ta ajjiye wayar saita qwalawa tabawa kira
"Ina maimunatu ne?"
"Tana dakin karatu,kinsan lokacin karatunta ne yanzu,kin santa kuma da himma" murmushi anni tayi,ita kanta tasan yarinyar daban take cikin dukka yara data sani,ba sawa ba fitarwa ba,babu hayaniya hakanan babu hargowa,uwa uba bata dauki rayuwarta da zafi ba,har cikin ranta kullum kwanan duniya tana jin nutsuwa da kuma gamsuwar hadin da take shirin yi da yarinyar
"Kiramin ita tabawa,wannan maganar ce ta taso,inajin lokaci yayi da zata san da zaman maganar,saboda ta sama zuciyarta tun kafin qarasowarsa,bawai sai daga bisani taji maganar sama taka ba,uwa uba ina hango wutar rikici dakeson ruruwa,gwara na yima tufkar hanci" kai tabawa ta gyada
"Gaskiya ne wannan haj anni,ubangiji ya tabbatar mana da alkhairi,yasa komai yazo mana cikin nasara da sa'a,ya kuma sanya qarshen abun ne yazo" cikin jin dadin addu'o'in tabawa anni ta amsa
"Ameen,ameen ya hayyu ya qayyumu tabawa" daga haka tabawan ta juya ta fice.
Sosai yau din takejin dadin karatun,hakanan Allah ya sallada mata qaunar hadith,dalilin da yasa zaiyi wuya ayi musu qarin hadith bata haddace su ba,kamar yau din,saura guda biyu ta gama haddar qarin da akayi musu jiya juma'a tabawa ta turo qofar tare da sallama ta shigo.
Qaramin murmushi ya wanzu saman fuska da siraran labban maimunatun,ta rufe hadith din tana duban tabawa
"Yau ban shigo kitchen ba ko?,karatu ne ya tsaidani amma na kusa kammalawa" murmushi itama tabawan ta maida mata,maimunatu nada saurin shiga rai saboda sauqi da dadin mu'amalarta
"A'ah muna,bansan me yasa kike takura kanki ba wajen zuwa kitchen kullum"
"Bana takura baaba tabawa,inajin dadin zuwan sosai,na qaru da kalolin girke girken da bansan ana yinsu ba,ina kan qaruwa ma,hakan yana min dadi"
"Gaskiya ne" tabawa ta amsata tana murmushi,don ita shaida ce,tuquru maimunatun ke maida hankali tana koyar duk wani girki da tazo ta samu zasuyi,daga inda taga anyi sau daya a gabanta to tabbas ta haddaceshi kenan,idan ta maimaita irinsan kuwa zakayi mamakin yadda ya bada ma'ana,kamar wadda ta jima tanayi.
"Yanzun ma anni ce take kiranki"
"Tom,gani nan zuwa" tace da baba tabawan tana qoqarin ajjiye Hadith dinta a take,ta kuma miqe tabi bayan baba tabawa,suna dan zancan islamiyyarsu,har zuwa sanda suka isa qofar dakin annin
"Tana ciki,zan koma kitchen mu qarasa hada abinci,don yau anan Alhj Dr(haka tun da baba tabawa take kiran dr marwan) zaici abincin dare"
"Idan na fito zan sameki a can saimu qarasa in sha Allah" ta fada saboda gwada kyautatawarta akansu itama komai qanqantarsa
"To ba laifi" ta amsa mata tana komawa zuwa hanyar kitchen,ita kuma ta tura dakin anni ta shiga,bakinta dauke da sallama.
,kamar ko yaushe,cikin nuna matuqar kulawa ta amsa mata tana gyara zamanta
"Kinga miqon wancar jakar kafin ki zauna" anni tace da ita tana mata nuni da wata jaka dake gefan gadon,miqa matan tayi sannan ta zauna tana fuskantar annin.
Zuge jakar anni tayi,ta fiddo wani abu,sannan ta daga kai tana duban maimunatu tana sakin qaramin murmushi
"Yau hira zamuyi dake" murmushin nan nata dake nuni da nutsuwarta gami da kamun kai ta sakewa anni
"So nake naji samari nawa kika taba yi maimunatu,sannan a cikinsu wa kikafi so?,inaso kuma naji har yanzu kina sonsa?" Sosai maganar anni tayi mata nauyi fiye da zaton ita annin,taji kamar qasa fa tsage ta shige ciki,ta yaya zata fara irin wannan hirar da anni?,bayan ko dasu laila ba zata iya wannan maganar ba?.
"Uhmmm,ina jinki,ki bude baki ki gayan" sake daureta kunyar annin tayi,sai kawai ta hau kada kai a hankali,dan bata fuska tayi
"Kina nufin ba kowa?" Da sauri ta daga kai alamun eh,sai annin ta motsa tana ajewa maimunatu hoto a gabanta
"To ga jikana,zaki iya aurensa?" Kasa daga kanta tayi bare ta kalli hoton,tanajin kamar ta kulle idonta ta bude taga bata a gaban anni,kayan kunyar yayi yawa
"Da gaske nake miki maimunatu,zaki auri ja'afar?" Wannan karon sautin muryar annin ya fito da wani irin amo dake nuna babu wasa cikin maganganunta,abinda ya sanya maimunatu cira kai,a maimakon ta kalli hoton sai ta kalli anni,suna hada ido ta jinjina mata kai
"Inaso ki taimaki rayuwar ja'afar,ki aureshi,inajin qamshin alkhairi a tattare dake,bansan me yasa zuciyata take gayamin ke zaki fitar dashi ba" a nutse ta zayyanawa maimunatu waye ja'afar,ta koma dora da
"Kiyimin wannan alfarmar maimunatu,bansan me Allah yake nufi ba da yasa nakejin ke zaki iya....."
"Kiyi duk abinda ya dace dani anni,don Allah basai kince neman alfarma kike daga gareni ba" maimunatu ta fada,dukka jiki da muryarta suna rawa.
Kai anni ta girgiza tana kallonta a nutse
"Aiba baiwa bace ce,'ya ce ke kamar kowa,don haka ya zama dole a nema daga wajenki cikin baki cikakken 'yancin yin zabin eh ko a'ah,kije kiyi tunani maimunatu,na baki dama,idan har kikaji baki gamsu ba,ko ba zaki iya wannan alfarmar ba,kada kiji komai,ki gayamin kanki tsaye,ni kuma nayi miki alqawari har tsakanina da